Search
You have no alerts.

    510 Results in the "Hausa Novels" category


    • Kura a Rumbu – Chapter Fifteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa "Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga…
    • Kura a Rumbu – Chapter Eleven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Daƙyar na koma cikin falo na zauna ina jin kaina yana saramun. Me yasa Bilal yake haka? Kullum ace abinci ne ze ringa haɗa mu rigima? Ina nan zaune ya fito daga ɗaki yanayin shigar sa na gane nisa ze yi. Ko kallo na be yi ba ya fice sabbin hawaye suka ɓalle mu. Zuciya ta tana raya mun na barshi naga iya gudun ruwan sa amma gangar jiki na taƙi bani haɗin kai, bazan ce ga sanda na miƙe na bi bayan sa ina kiran sunan sa ba amma ko a jikin sa ya yi ficewar sa daga gidan ya bar ni a tsaye ina hawaye. Se…
    • Kura a Rumbu – Chapter Eighteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka shafe tsayin…
    • Kura a Rumbu – Chapter Eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — "Sannu Halims, kin tashi" Bilal ya faɗa yana nufo ni se dai shigowar Anty Labiba ɗakin ta katse masa hanzari se ya ja gefe yana shafa kansa ita kuma ta balla masa harara kafin ta nufo ni ta kamani ganin ina ƙoƙarin tashi zaune. "Sannu" ta faɗa tana gyara mun ɗankwali na daya zame. Bilal ne ya fita ya kira wo likita suka dawo ɗakin tare da Abba. Bin su kawai nakeyi da kallo har likitan ya gama dubani yace babu komai jiki na ya dai dai ta amma a barni na sake hutawa. Abba yayi mana sallama akan ze je…
    • KURA A RUMBU Thumbnail

      [12/10/2024, 12:57 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU* *(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)* *LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI* Zaku ce ya akayi haka ? na fiku takaici da baƙin ciki rasa rubutun nan a karo na biyu ?? in shiga in duba folder tace dubani in da kika ajiye.…

      Download • Download • Hausa Novels • hausa novels
    • Story

      Kura a Rumbu

      Kura a Rumbu Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — “Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka” na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa’u data kalli ɗaya ɓangaren ba nace “Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu…
    • KIDA A RUWA Book 1 Thumbnail

      Kayan hannunsu duk suka ajiye suna zubewa a gadon kowa na faɗin wash, dai-dai nan Ruky data rigasu shigowa ta fito daga bayin alamar har tayi alwysSuma duk miƙewa sukai, dan rashin yin sallar akan lokaci na tsaye a ran kowannensu. Bintu ce kawai ke period dan haka taja ledar snaks ɗinsu ta fara ci tana faɗin, “Bari muga mi Sayyadin ya aiko mana…

    • KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Thumbnail

      KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg [6/25, 11:52 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA* Na © Rahma Kabir MrsMG. Page 1. *Gargad’i* _Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan…

    • Karfe A wuta na Aisha Adam (Ayshacool) Thumbnail

      Karfe A wuta na Aisha Adam (Ayshacool)       ⚔️?ƘARFE A WUTA?⚔️ Page 1 Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar gudun AC. Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako. Wata matashiyar budurwa ce, durƙushe a kan gwiwoyinta, fuskarta ɗauke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali, fuskarta tayi sharkaf da hawaye.…

    • Karfe A wuta Complete Book Thumbnail

      Karfe A wuta Complete Book Continuation. Cikin hanzari ya kalli Nabila, yana mamakin a ina ta san wannan sunan, dan sam bai san Walid ya gaya mata labarin sa ba. Ya ƙureta da ido, ta kawar da kanta gefe, ta ce “Eh, idan ka kashe ni, ka ci amanarta, ta barka ka kusa dawowa hanya, amma ka koma ruwa fiye da baya. Zan so…

    • KARAGAR MULKI Thumbnail

      Bismillahi Rahamanir Rahim “Ki yi haƙuri Malikat Juwairiyya amma ba zan iya bin ki ba,na riga da na saba da rayuwata anan,kuma ta fi ma’ana da alfanu a gare ni,kai bama a gare ni kaɗai ba har da ita kanta Sarauniyar, ke da ma mutanen gari baki ɗaya,”….” A’a kar ki ce haka Gimbiya Junainah domin a yanzu zamanki anan yana cikin haɗari,barazana,firgici harma…

      Download • Download • Hausa Novels • hausa novel
    • Kanwar Maza Chapter 6 Thumbnail

      P6 Iya ƙarfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan. Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya ɗago ya kallesu ya ce “Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?” Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi”Mama tana nan?”…

    Note
    error: Content is protected !!