KARAGAR MULKI
Bismillahi Rahamanir Rahim
“Ki yi haƙuri Malikat Juwairiyya amma ba zan iya bin ki ba,na riga da na saba da rayuwata anan,kuma ta fi ma’ana da alfanu a gare ni,kai bama a gare ni kaɗai ba har da ita kanta Sarauniyar, ke da ma mutanen gari baki ɗaya,”….” A’a kar ki ce haka Gimbiya Junainah domin a yanzu zamanki anan yana cikin haɗari,barazana,firgici harma da ɗimuwa”,”Ni kaina ai haɗarin ce wacce ke barazanar illata duk wanda yake kusa da ita ko ya raɓeta,to kinga in haka ne meye amfanin zamana da ku?,gara kawai ku bar ni in cigaba da zama na anan ,ko na ƙarasa sauran rayuwata a cikin wannan lambun da ke gefan gari,domin rayuwata da ku kasancewarta da kamar wuya Wai kiɗan ganga da lauje”,”Ba za ta sa`ɓuba wankan kuturu da sabulu domin a baya kin faɗi irin haka na amince amma a wannan karon ina mai tabbatar maki da yanzu ba za ki yi nasara ba,”,”Malikat Juwairiyya ki yi haƙuri amma bazan iya bin ki ba domin ina tsoro a koda yaushe zan iya rikiɗewa in zama halitta mafi tsoro da muni gaba ki ɗayana to in hakan ta faru ya zakuyi da ni,na daɗe da sanin Gurin kwanan balbela daban ya ke da na hankaka,ba abu ne mai kyau zai faru ba in su ka haɗu guri guda, ko kin manta ba ku da wani magani da za kuyi ko ku bani a kan haka ? “,Ba mu da shi amma hakan ba yana nufin zamu bar ki ki cigaba da zama anan daga ke sai dabbobi da namun daji anan ba,tunda daganan inda ki ke ba sauran gida gaba ko gida baya,me ya sa za ki tsorata gami da fidda rai dangane da samun lafiya a gare ki,ki ƙaurace wa mutane shin ki na tunanin hakan shine mafita,bari ki ji wani abu da a ce zaki ya ji tsoran mutane da tuni sun fara kiwata shi a gidajensu kamar yanda su ke kiwata Kare da sauran namun daji amma da ya jajurce gami da sa dakiya a zuciyarsa, kuma da bai tsorata ba sai ya juye gami da rikiɗewa zuwa Sarkin dawa,to me ya sa ba za ki kwatanta abinda ya aikata ba ?, “,”Aikata hakan abu ne mai matuƙar wuya wai gurguwa da Auren nesa to meye aibun haka, ni ina jin daɗin rayuwata haka kuma Kiki tana ɗebe min kewa fiye da duk sauran mutanen da suke a tare da ni anan cikin masarautar tunda ina da tabbacin bazan cuceta ba haka itama ba zata cutar da ni ba,saboda ko da na rikiɗe zuwa wata halittar bazan cuceta ba tunda itama dabba ce kamar ni,in ma na cutar da ita za a ce duk ɗaya wai anyi ma tuwo barin miya”,”Wai Giwar ce ki ke ikirarin tafi mi ki daɗin rayuwa fiye da kowa da kowa ?,wannan da ace mutum ce sai in ce bita da ƙulli ta ke mi ki bugun kabarin kishiya,to sai dai an samu akasi ita ɗin dabba ce ,”,”Kwarai da gaske Malikat Juwairiyya,ita kaɗai ce wacce nake da ita a rayuwata ta yanzu wacce bata taɓa yunƙuri ko ƙoƙarin nisa gami da son rabuwa da ni ba,amma itafa Sarauniya da kanta ta zaɓa mana muyi rayuwa irin wannan da ta ke gudana a tsakanina da ita”,….”To na gaji,dama can zura miki Ido nai taya za’ai mutum ya rayu a wuri daga shi sai itatuwa,dabbobi da kuma tsirai,to Wai ma daɗin me kuturu ya ji ga Allah da za ki ce kin fi san ki cigaba da rayuwa anan ?, bazan amince gami da lamuntar hakan ba,kuna bani mamaki da ga ke har Mahaifiyar taki,nice na haifeta ita kuma ta haife ki bisa hannuna kuma akan idona to amma ban taɓa ji ko gani makamancin yanda ku ke rayuwa ba,ke ko a hikaya,labari,tarihi da tarihihi har ma da tatsuniya ban taɓa ganin ko jin irin ta ku ba, ace ke da Mahaifiyar ki baku haɗa idanu ,ba ku ga maciji a tsakanin ku,balle a kai ga kun sha inuwa ɗaya da ita ,Kai abun da sake,Wai an ba me kaza Kai da ƙafa”,” Ita ta zaɓa mana haka,kuma ke ia kin san halina da nata ba ɓaya ba ne,

0 Comments