489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Jinyar stitches ɗin Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi yakeyi, sannan ya kula da ita a ɗan taƙin lokacin kuma ya ɗan fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka ɗaura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare, maganin na…-
247.6 K • Completed
-
-
Tarin missed calls ɗin da ya gani daga Alhaji Lawan mutumin daya siya gidan Jalilah a hannunsa ya tabbatar masa da ba lafiya ba, a maimakon ya kira Alhaji Lawan ɗin kai tsaye sai ya fara kiran Nasir domin shi yayi hanyar cinikin. "Yanzu nake shirin kiranka dama; kana ina?" Nasir ya faɗa bayan daya amsa wayar Bilal ya ce "Mai ya faru naga mutumin nan daya siya gida a hannuna yana ta kirana a waya ban lura ba sai yanzu?" "Shiyasa na ce kana ina? Akwai matsala gaskiya" Nasir ya bashi amsa. Bilal ya…-
247.6 K • Completed
-
-
HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifty
Turus yayi yana bin falon da kallo zuciyarsa tana ƙara gudu, shiga yayi ciki da kyau har sannan yana ƙoƙarin gane abinda yake faruwa. Ƙofar ɗakin Halima ya tura, nan ya tarar da gurin shima tamkar falon babu ko tsinke anyi shara da alama ma har mopping akayi. Sakin ƙofar yayi ya matsa ya buɗe ta ɗayan ɗakin da yake mazaunin nasa; a nan ne ya tarar da kaya zube a ƙasa wanda kallo ɗaya ya musu ya fahimci nasa ne. Ɓacin rai haɗi da baƙin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, fita yayi daga nan ya…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifteen
Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa "Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Eleven
Daƙyar na koma cikin falo na zauna ina jin kaina yana saramun. Me yasa Bilal yake haka? Kullum ace abinci ne ze ringa haɗa mu rigima? Ina nan zaune ya fito daga ɗaki yanayin shigar sa na gane nisa ze yi. Ko kallo na be yi ba ya fice sabbin hawaye suka ɓalle mu. Zuciya ta tana raya mun na barshi naga iya gudun ruwan sa amma gangar jiki na taƙi bani haɗin kai, bazan ce ga sanda na miƙe na bi bayan sa ina kiran sunan sa ba amma ko a jikin sa ya yi ficewar sa daga gidan ya bar ni a tsaye ina hawaye. Se…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Eighteen
Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka shafe tsayin…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Eight
"Sannu Halims, kin tashi" Bilal ya faɗa yana nufo ni se dai shigowar Anty Labiba ɗakin ta katse masa hanzari se ya ja gefe yana shafa kansa ita kuma ta balla masa harara kafin ta nufo ni ta kamani ganin ina ƙoƙarin tashi zaune. "Sannu" ta faɗa tana gyara mun ɗankwali na daya zame. Bilal ne ya fita ya kira wo likita suka dawo ɗakin tare da Abba. Bin su kawai nakeyi da kallo har likitan ya gama dubani yace babu komai jiki na ya dai dai ta amma a barni na sake hutawa. Abba yayi mana sallama akan ze je…-
247.6 K • Completed
-
-
Blog
KURA A RUMBU
[12/10/2024, 12:57 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU* *(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)* *LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI* Zaku ce ya akayi haka 🥲 na fiku takaici da baƙin ciki rasa rubutun nan a karo na biyu 😭😭 in shiga in duba folder tace dubani in da kika ajiye.…
-
Story
Kura a Rumbu
“Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka” na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa’u data kalli ɗaya ɓangaren ba nace “Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu…-
3.4 K • Sep 17, '25
-
3.5 K • Sep 17, '25
-
3.6 K • Sep 17, '25
-
-
KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg [6/25, 11:52 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA* Na © Rahma Kabir MrsMG. Page 1. *Gargad’i* _Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan…
-
Karfe A wuta na Aisha Adam (Ayshacool) ⚔️🔥ƘARFE A WUTA🔥⚔️ Page 1 Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar gudun AC. Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako. Wata matashiyar budurwa ce, durƙushe a kan gwiwoyinta, fuskarta ɗauke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali, fuskarta tayi sharkaf da hawaye.…
- Previous 1 … 23 24 25 … 46 Next
