489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Kafin mu gana gane me ya faru Mu'azzam ya shigo ɗakin babu kuma ɓata lokaci ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukan Bilal yanda ka san Allah ya aiko shi. Gefe na ja da sauri cikin tashin hankali na ɗora hannu biyu a ka na fasa ihu ina kiran sunan Mu'azzam ɗin, abin takaici Nasir da yake namiji daya kamata ko murɗe Mu'azzam ɗin yayi ya ƙwace bulalar idan ma yana tsoron kaiwa Bilal ɗin agaji ya haɗa da shi wai sai ya tsaya daga gefe yana ce masa ya bari. Bilal kuwa kamar mace haka ya shiga birgima…-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar. Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin da na musu tar tamkar a lokacin abun yake…-
247.6 K • Completed
-
-
ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…-
247.6 K • Completed
-
-
Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga gare shi ko me? "Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce "Ka sameni a gidan Anty Labiba bayan Magriba" "Gidan Anty Labiba kuma?" Ya faɗa kamar a ɗan…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Forty
Tunda yaga babur ɗin Kawu Sani a ƙofar gidan gabansa ya shiga faɗuwa domin ya san abinda akw ɓoyewa ya rigada ya bayyana. Sai dai kuma shima yana buƙatar hakan ko dan ya samu a wuce gurin Zulaiha ta tare amma kuma ya san da wahala su kwasheta da daɗi da Hajja. Tun daga tsakar gida yake jiyo maganganun Hajjan tamkar zata ari baki tsabar masifar da take zazzagawa, yana ɗaga labule suka haɗa ido kallon data jefa masa sai da yaji yan cikin sa sun juya, ta ce "Yawwa gara da kazo, dama Bilal idan har ni…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Five
A motar Nasir na ganshi, ya kame a ciki yanda kasan tasa. A raina nace kuɗi dai ze yi wa Bilal kyau dan kalarsu aka masa. Yanayin surarsa da irin kayan da yake sakawa ba zaka kalli gidansu kace daga nan ya fito ba. Yana son gayu, sau tari na kan raya a raina nan yake kashe kuɗin sa gurin siyan sutura da takalma haɗi da agogo masu tsada duk abin da samari sa'anninsa suke yayi zaka ganshi dashi hakan kuma yana burge ni duk da ba wadata ce dashi ba amma ba yanda za'a yi ka ganshi ka raina shi. A gaban…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifty-two
Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke mu'amala da su balle makaranta. Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa…-
247.6 K • Completed
-
-
"Lallai su Bilal anyi Amarya, toh Allah ya zaunar lafiya" amsar da Hansa'u ta bani kenan duk kuma yanda na so da naji ƙarin bayani bata sake cewa komai ba, Da na isheta da tambaya ma balbaleni tayi da faɗa tana cewa "Wai menene haɗin ki da matarsa ne Halima? Mutum ya rabu dake tuni ma shi ya manta ya taɓa rayuwa da wata Halima har yana shirin fara rayuwa da wata amma ke ashe kina nan kina dakon wahala sai anyi magana ki fara rantsuwar kin cireshi a ranki gashi kina bibiyarsa". Tilas na bar maganar…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifty-six
Kwana uku Jalilah tayi a Kano ta wuce Abuja bayan ta bar alhakin sauke kayan da suka fara isowa a hannun Bilal. A tsakanin kwanakin har rama yayi; duk wanda ya sanshi kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yana cikin damuwa matuƙa, duk in da yake tunani zai buga lissafi ya fita abu ya gagara, idan ya haɗo nan sai can ya rushe ga Alhaji Lawan ya taso shi a gaba da zancen kuɗinsa dan tuni ya kwashe kayansa ya bar gidan kamar yanda ya ce har Ahlan mamallakin gida na asali ya saka an sake gyara ko ina sai jiran…-
247.6 K • Completed
-
-
BILAL Yana kwance a gida Hajja ta kirashi wai ya kawo musu kayan miyan da za'ayi tuwon ɗaurin auren Fadila da za'a ɗaura a gobe Juma'a. Da yake a tsini suke yayi mata laifi shiyasa bai musa ba ya tashi ya tafi kasuwar Yankaba ya yiwo musu cefanen ya tafi ya kai. Zagayewa yayi yaje ya samu Kawu Ɗayyabu, Yayan Hajja ne da suke uba ɗaya da yake mutum ne mara ɗaukar raini shiyasa duk rashin mutunchin Hajjan take shakkarsa ko da wasa kuma bata bari wani abu ya gilma a tsakaninsu shi Bilal ɗin yaje ya samu…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifty-one
Ranar Alhamis suka je jere ko ya ce ganin gida tunda dai shi yayi jere, yan buhun hunan da suka je da abinda suka kira kayan kitchen tsabar takaici kallo ɗaya ya musu ko gaisuwa mai kyau basuyi ba ya fita ya barsu da yayyensa banda Anty Amina da sukaje tarar masu jere. Bai san munafukin daya gayawa Hajja shi ya siya mata kayan ɗaki ba ai kuwa ya sha tijara wannan kuma ya sake ruguza ɗan shirin da suka farayi ta kuma ja masa kunne akan ba fa zata saɓu ba, ita da wahalar haihuwa da raino can wasu a gefe…-
247.6 K • Completed
-
-
Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 22 23 24 … 46 Next
