Search
You have no alerts.

    KIDA A RUWA Book 1

    Kayan hannunsu duk suka ajiye suna zubewa a gadon kowa na faɗin wash, dai-dai nan Ruky data rigasu shigowa ta fito daga bayin alamar har tayi alwysSuma duk miƙewa sukai, dan rashin yin sallar akan lokaci na tsaye a ran kowannensu. Bintu ce kawai ke period dan haka taja ledar snaks ɗinsu ta fara ci tana faɗin, “Bari muga mi Sayyadin ya aiko mana da shi shi kuma”.
    Tsaki Nimrah tayi a karo na farko tana shigewa bayi abinta. Fiddo ta sanya dariya dan Ruky ma harta kabbara salla. Dariyar su Bintu data cika ɗakin ya saka Nimrah fitowa da sauri, itama Ruky dai-dai tana idar da sallar ta juyo tana kallonsu. Litattafai ne a ledar saƙon Sayyidi Kamal suka nuna musu. Feedo ta ce, “Wannan fa shine auren ustaz ɗin, kaga wata lukutar jaraba wai saƙon littafai. Ninah kina cikin yanayi gaskiya”.
    Nan ma dariya suka sanya harda Ruky yanzu kam. Dan haka Nimrah ta watsa musu harara ta kabbar sallarta itama. Koda ta idar sun gama mata shaƙiyancin nasu, dan haka bata sake tada zancen ba ta haye gadon ta kwanta wai kanta ke ciwo. Da ƙyar suka lallaɓata ta zauna suka ƙarasa shan Ice-cream ɗinsu da snaks ɗin bayan Feedo ta idar da salla itama. Dan haka koda Aunty Mimi tai kiransu suzo su ɗeba abinci sukace mata sun ƙoshi. Bata takurasu ba dan taga abinda suka shigo da shi, ta kuma san aikin Haneef ne……

    <<<<<<(⁠✷⁠‿⁠✷⁠)>>>>>
    ★CAMPAIGN★

     Kwanaki 100 na campaign suna gab da cika, dan kuwa ana satin ƙarshe na kammala taron kowane kamfen. Dan haka amsa kuwwar cikar kwanakin tamburan siyasa na gab da cika, tako ina ƙasa ta kara hargitsewa dan kowa burinsa satin ƙarshen nan ya tumfayesa da zuciyar yan kasar. Baka iya jin komai sai sautinkan waƙoƙin da aka rairana ƴan siyasa. Yayinda hankalin matasa kacokan ya koma can. Wasu ma sun ajiye harkokinsu da sana'o'in su ne kacokam. Kamar dai yanda aka saba alƙawuran nasu guda huɗu ne ga al'ummar ƙasa a lokacin da suke kan munbarin campaign. Zamu gyara muku harkar karatun, zamu inganta wutar lantarki, zamu wadata ku da ruwa, zamu gyara asibitoci. 
       Cikin rashin lissafi da auna abubuwa a yanda ya dace, da taro da kwabon da ake raba mana mu talakawan ƙasa da ɗan sabulai da zannuwan ɗaurawa mai hoton ƴan siyasar a jiki sai kaji mun sallama muna bada kai bori ya hau. Babu ruwanmu da tantance wane shugaban ya dace damu? Mi muke so a ƙasar da kawunanmu bayan waɗan can lissafin huɗu da ko a karatu sukazo ya kamata ace mun haddace su tsaff zuwa yanzu daga daɗin bakinsu mu nemo cigabansu. Amma ina babu batun tantancewa, a wasu wajajan ma siyasar ta haɗa rigima ne tsakanin ƴan uwan juna saboda ni ina son wannan wane ɗan uwana yana son wancan ba jam'iyyar mu ɗaya ba. Wasu har gaba zakaga ta ƙullu mai girma a tsakaninsu. Yayinda su ƴan siyasar da sukeyi domin su suna can tare suke shan shayi, tare suke ƙulla mai fishshesu musamman akan abinda zasu ribantu da shi game da kuɗaɗen da suka kashe wajen jawo ra'ayinku idan sun haye. Wanda ma bai haye ba akwai hanyoyin da za'a bi dan maida masa wahalarsa ta bayan fage kune a ruwa...
    
     Alhamdullahi duk da irin tasu tafiyar bata banbanta data Janar Yusuf ba a yau kasancewar a ƙarƙashin damarsu ya ke shima a siyasar kamar saura abinda shekarun baya suka zo da shi wajen campaign shima dai shine a yau yake zuwa da shi. Kuma Alhamdullah zamu ce akwai nasara a al'amarin dan yana da magoya baya sosai a cikin jam'iyya da al'ummar gari. 
         Abinka da soja, a kwanakin kai-kawon duk da wahala da jigatar rashin barci dana hutu zuciyar maza a tsaye take da ƙyaƙyƙyawan fata. Tun ana farkon satin nan da sukai zama da Imran ya kuma gana da Uncle Nasiru basu sake haɗuwa ba. Dan a zahiri Imran baida alaƙa da siyasar Janar. Gara-gara ma Uncle Nasiru har campaign ya rakashi sau biyu. Duk wani abinda ya dace su tattauna sun kammala sun ajiye kundin shirinsu gefe har sai ta ALLAH ta kasance. Wato aci zaɓe ko a faɗi...
      Tsahon kwanaki sun cika cir, awanni 48 ya rage a fara jefa kuri'a, dan haka batun campaign komai ya lafa a koma jiran ranar jefa kuri'a da gwamnati ta riga ta fitar kuma kwanaki 2 ne kacal, dan yau alhamis....

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!