KUYI MANA ADALCI
Marubuciyar
Aure A Yau
Sandar dukan uwargida
Ranar Kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Iya ruwa
Wani auren
Da Walakin
Wutar Ƙaiƙayi
Matar shige. Dss
Duniya juyi-juyi, kawaɗo ya faɗa a ruwan zafi, ina yawan tunawa da wannan karin maganar cikin zuciyata, saboda a yanzu dai yana taka ta shi rawar a cikin rayuwar aurena. A baya idan wani ya ce mini zan iya yin bacci ba a kwance a ƙirjin mijina ba alhalin muna kwance a gado ɗaya, zan shiga shakkun tabbatuwar hakan, inda a ce wani ya taɓa faɗa mini akwai ranar da za ta zo muna gida ɗaya da mijina mu raba ɗaki kowa ya kwana shi kaɗai a na shi ɗakin wallahi nan take zan daka tsalle na musa cikin isa, amma sai ga shi zamani ya jujjuya da rayuwar aurenmu ya watso mu ƙadamin da muke ciki a yau, wanda ya fi kama da rayuwar maƙiya ba masoya ba.
Juyi na yi a makeken gadon nawa, na lalubo filo na rungume, ina sane da hasken wayata da yake ta kawowa a karo na babu adadi, alamun mai kiran wayar har yanzu bai gajiya ba, na mirgina na kalli wayar, ba don neman sanin mai kiran ba, don na san wannan, agogon wayar na duba wanda ya nuna ƙarfe sha biyu na dare da minti goma, idan na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, sai yanzu Sadam ya gama waya da chatting ɗinsa da matan da yake ganin sun fi ni daraja a halin yanzu, wanda nake ƙarfafa zargin sun kunna shi ne, yake neman yadda zai kashe wannan wutar ta wajena, don haka na ƙudure ba zan iya amsa kiransa ba, duk da ban manta da hukuncin matar da mijinta ya kira ta shimfiɗarsa ta ƙi amsa kira ba.
Ina sane ƙofar ɗakina a buɗe take, don haka shigowarsa ba ta ba ni tsoro ba, amma ta ba ni mamaki, nan take na tuna da rantsuwar da ya taɓa yi mini a ranar da nake kuka ina tabbatar masa ba zan sake kwana a ɗakinsa ba, ya ce”Na rantse da Allah Sayyada babu macen da ta isa na bi ta ɗakinta na kwana da ita, kuma tun da ni mijinki dole ki amsa kirana a duk lokacin da na buƙaci hakan”.
Shin na karya masa rantsuwarsa ne tun ba a je ko’ina ba? Lumshe ido na yi kamar mai bacci, daidai lokacin da ya kai hannu ya kunna globe ɗin ɗakin, ya taka a hankali ya ƙaraso ya zauna a gefen gadon “Sayyada, Sayyada”.
Ya shiga kirana da taushin murya kamar munafiki, ban ko motsa ba, don haka ya kai hannu ya fara taɓa fuskanta, na janye hannun na shi da sauri tamkar wanda ya taɓa ni da bakin wuta, ya riƙe hannun nawa ƙam ya jijjiga shi sannan ya ce”Tashi mana, ina ta kiran wayarki ashe kin yi bacci”.
Na fizge hannun na ce”Ban yi bacci ba, zuwa ne ba zan yi ba! Kenan ba ka yarda ba da na ce maka ba zan sake kwana a ɗakinka ba ko?”
Ya sauke numfashi, har yanzu da wannan sanyin muryar wanda yake yaudarata da shi a da, ya ce”Haba Sayyada, na zata wannan ya wuce ai”.
Na ce”Ba zai wuce ba har abada”.
Ya ce”Yaushe kika koyi gardama ne? Yaushe kika koyi musu da ni?”
Kamar zan yi kuka na ce”Tun ranar da ka nuna mini matsayi da darajata sun ɓare a wajenka”.
Tsaki ya ja, a wannan karon sai ya canza murya ya kaurara ta ya ce”Dalla tashi ki wuce mu je”.
Na yi banza da shi, zuciyata ta fara yi mini zafi, ina tuna miyagun kalamansa a kaina.
“Ki tashi mu je ki ba ni hakkina Malama!” Ya maimaita mini cikin daka tsawa.
Ni ma ɗin a tsawace kuma cikin kuka na ce”Ba zan bayar ba! Na ƙarfi ne”.
Ya tashi tsaye yana ce”To ai ina da ƙarfin”.
Ƙarfin kuwa ya saka ya fizgo ni daga gadon, abinka da ‘yar ƙarama mai ƙaramin jiki ba tsayi ba ƙiba, shi kuma dogo mai ƙiba ƙaƙƙarfa, nan take ya ɗauke ni cak, duk shure-shuren da nake yi da dukansa bai sare ba har sai da ya dangana ni da gadon ɗakinsa, irin abin da ya faru a daren da na ce ba zan sake shiga ɗakinsa ba shi ne ya faru a yau ma, fyaɗe Sadam ya yi mini karo na biyu a tsayin zaman aurenmu, duk miyagun kalaman da na dinga jifansa da su ba su saka ya sare ba, har sai da ya kai inda yake son zuwa, na yi laƙwas a gadon ina kuka mai sauti, irin mai cin rai ɗin nan, na yi mai isa ta babu mai rarrashi, sanda na taƙaita na rarrashi kaina kuwa shi tuni ya yi bacci, na kalle shi ta hasken ɗakin, baƙi ne mummuna, amma a yanzu na gane hakan, domin kuwa a shekarun baya kafin zamanmu ya hargitse wallahi gani nake yi ko gasar kyau Sadam ya shiga zai iya shiga sahun farko-farko, ashe soyayya tana ɓoye muni? Tirr! Ni Sayyada na la’anci kalmar soyayya da masu bauta mata indai a haka ƙarshenta yake ƙarewa kowa.
Na daɗe kwance a haka hawaye yana gangara ta gefen idona, ji nake zuciyata ta yi mini nauyin da nake jin kamar babu macen da ta fi ni shiga ƙunci, a hankali na yunƙura na tashi, na ɗauki yaloluwar rigar baccina da ya yaga rabinta na bar ɗakin. Bayan na yi wanka na kwanta sai na fara jin ciwon kai kaɗan-kaɗan, tsallen da na yi na afka kogin tunani kuwa ya ta’azzara hauhawar farashin ciwon kan, wanda dama tuni ya zame min jiki.
Sautin kiran sallar farko da ya karaɗe unguwar ne ya ankarar da ni tabbas yau na kwana ban runtsa ba, idan aka cire baccin da na samu tsakanin bayan sallar isha’i zuwa ƙarfe goma da dawowar Sadam ɗin ta tashe ni, sai da na yi sallar asuba sannan bacci ya ɗauke ni a kan sallayar. Sai wajen ƙarfe tara na tashi, na yi wanka na saka doguwar rigar leshi na faɗa kitchen, a raina ina addu’ar Allah Ya sa bai fita ba, ruwan shayi kawai na dafa, na ɗakko biredi da bota na ajiye a dining, na haɗa nawa shayin na koma falo na zauna ina sha.
Ban yi nisa da fara sha ba ƙamshin turarensa ya cika hancina, hakan ya tabbatar mini da fitowarsa, na juya a hankali na kalle shi, fes yake fuskarsa da walwala alamar bai tashi da wata damuwa ba, ina kallon shi muka haɗa ido, ya sakar mini murmushi ya ce”Morning”.
Duk yadda na so na mayar masa murmushin na kasa yi ko da kuwa na gefen baki, amma dai na amsa masa da faɗin”Morning”.
Sannan na tashi na ƙarasa dining ɗin, ya zauna, ni kuma na tsaya na haɗa masa shayin na tura masa gabansa, zan bar wajen ya riƙo hannuna ya ce”Idonki ya kumbura, sorry”.
Na gyaɗa masa kai alamar na ji, sannan na zame hannun na koma ɗakina, mayafi da jaka na ɗauka na saka wayata a ciki, na zura takalmi, na dawo falon na zauna, ina jira ya gama na ji yadda za mu kwashe, duk tunanin da na kwana ina yi jiya mafita ɗaya na samu a kan burin gyaran rayuwata, shi ne na ziyarci asibiti a yau na fara gyara kuskurena, don a yanzu shi ne kuskuren da ya fi damuna kuma ƙarami cikin kura-kuran da na aikata.
Yana gamawa ya zo ya saka kai zai bar falon, bayan ya yi mini kallo ɗaya, na tashi da sauri na bi bayansa, tun da na lura hauka yake son manna mini, ai dai ya sani gari banza ba zan saka mayafi da takalmi har ma da jaka don na ji daɗin zaman falo ba.
“Amma dai ka san ba haka kawai na saka mayafi ba ko?” Na faɗa a gadarance.
Ya yi tsaki ya ce”Allah wadaran naka ya lalace, na ga ranar da za ki iya magana da miji ke dai”.
‘Idan ya zama dole sai na kira ka da miji to dole na ƙara da faɗin mijin ƙaddara’ Na faɗa a raina, a fili kuma kau da kai na yi ƙwalla tana kawo idona na ce”Ka sauke ni a asibiti”.
“Ba ki da lafiya ne?” Ya tambaya hankalinsa na kan wayarsa da ya ciro daga aljihu.
Na ce”E, ba ni da lafiya”.
Ya ce”Mene ne yake damunki?”
Na ce”Tsakanina da likata ne”.
Ya ce”Ok, idan na fita zan turo likita sai ki yi masa bayani”.
Na ce”Asibitin nake son zuwa”.
Kai tsaye ya ce”Ba za ki je ba”.
Da sauri na sha gabansa a harzuƙe na ce”Na gaji! Na gaji da wannan mulkin mallakar da kake yi mini, na gaji da yadda kake tauye ni, ba zan zuba ido ka kashe min rayuwa ba fa, na gaji da zama babu haihuwa, ina son ganin jinina, don na gane a yanzu su ne gatana kuma abun ɗebe kewa ba kai ba!” Na rushe da kuka ina tuna girman kuskuren da na yi na biye wa namiji cikin guguwar soyayya, wacce ba ta juye ni a ko’ina ba sai cikin karmamaki.
Tsaki ya yi, ya raɓe ni zai wuce, ai kuwa na daka tsalle na tsaya a gabansa ina cewa”Ya zama dole na haihu Saddam, ya zama dole ka je ka ƙaryata cewar ni juya a idon duniya, ko da kuwa ba za ka fasa ƙara aure ba”.
Da sigar rainin hankali ya ce”To kin tanadi loud speaker da zan yi sanarwar?”

0 Comments