ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
…….Tsaff sashen nasa yake an gyara komai tamkar koman bai faru ba. Yasan aikin Mama Balki ne wannan. Dan hatta bedsheet ɗin saman gadonsa da blanket an canja su da wani fari tass mai ƙyau da masifar laushi. Bathroom ya shiga, can ma ɗin dai an tsaftacesa. Sai kawai yayi wanka tare da ɗauro alwala ya fito. Sai da ya fara gabatar da shafa’i da wutri sannan ya kwanta dan barci sosai ke cin idanunsa ga ciwon kai da baya raba ɗayan biyu a dalilin zaman sashen Ummie da yayi ne. Dan lafiya lau suka shigo gidan sai gajiya dake damunsa. Yana kwanciya kuwa barci mai nauyi yayi awon gaba da shi…
Da asuba makarar da yayi ce ya sashi yin salla a ɗakinsa ya sake kwanciya. Barci ne mai nauyi ya ɗaukesa har ya manta ma safiya ce ba dare ba. Duk da kuwa shi da wahala kaga yana barcin safe ko rana. To inama yaga wannan lokacin kullum abubuwa sun ma kansa yawa. Idan har kagansa yini guda a gida yana hutawa lallai ba lafiya ba. Ko kuma akwai wani ƙwaƙwƙwaran dalili. Dan ko nan ta samu ya gudo dan ya huta baka rabashi da laptop ko tab a hannu yana harkokinsa.
Cikin barci sautin knocking ɗin ƙofa ya addabesa. Dole ya buɗe idanunsa yana mai karanto addu’a. Sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya miƙe zaune cike da takaicin wanda ke damun nasa. Agogo ya kalla goma da wasu mintuna na safe. Yaɗan furzar da iska kaɗan tare da zuro clean ƙafafunsa ƙasa. Nan ɗin ma sai da yaja wasu sakanni sannan ya ɗauki remote ya danna ƙofar ta buɗe kanta. Paah ne ya shigo, dan haka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Good morning”.
Amsa masa Paah ɗin yay da, “Morning dear, ka tashi lafiya?”.
“Alhamdullah”.
“To masha ALLAH. Dama Baba ne yazo tun ɗazun, da yace kar a tashe ka harka tashi da kanka, sai kuma ga baƙi munyi da ga human right, wai sunzo ne akan case ɗin yarinyar nan. Bamu san wanene yaje ya sanar musu ba a gidan nan. Muhammad wai miya kaika aikata al’amarin nan? Bayan nasan wannan ba halinka bane ba. Baka aikata a waje ba sai a cikin gida, haba Muhammad da mahaifiyarka na cikin lafiyarta mi kake zato”.
Komai Maash bai ce ba har Paah ya gama maganarsa. Cikin ɓacin rai ya juya ya fita yana mai bashi umarnin fitowa yanzun nan ana jiransa kada ya ɓata musu lokaci. Da kallo kawai ya bishi na tsawon mintuna har biyu, kafin ya furzar da nannauyar iska ya miƙe. Bathroom ya nufa, bai wuce mintuna biyar ba ya fito. Ba tare daya canja pyjamas ɗin jikinsa ba ya zura bedroom slippers ɗinsa masu taushi farare tas kamar pyjamas ɗin nasa ya fito. Baiyi zaton a falonsa suke ba. Dan haka yay ɗan turus yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Gaba ɗaya manyan gidan ne sai baƙi fuska mata biyu da maza biyu. Ɗauke idanunsa yay cike da basarwa, a dakile ya furta, “Good morning”. Yana kaiwa cikin kujera da ke gefen Baba prof alamar shi aka barma wajen zaman dama. Duk da dai kowa ya samu nasa gurin kasancewar falon bawai kujeru bakwai bane ba kawai. Yanda ya tsuke bakinsa da ga gaisuwar farko kowa ya fahimci jam’i yayi. Kuma bazai sake wata ba. Harara Hajiya Mammah ta watsa masa. Hakama Hajiya ƙarama sai da ta ɗan cija lips. Maman Malika ce kawai tayi ɗan murmushi da faɗin, “Awwab babu dai wata matsala ko?”.
Kansa ya jinjina mata. Sai kuma a hankali ya ɗan motsa lips ɗinsa ya ce, “Alhamdullah Mamy”.
Da fara’a itama ta ce, “Alhamdullahi mun gode ALLAH. ALLAH kuma ya kiyaye gaba”.
Baba prof, Paah, Uncle Abdullahi suka amsa da amin. Duk da dai fuskokinsu babu walwala suma. Kallonsa Baba prof yayi kamar mai nazari, kafin ya masa nuni da baƙin fuskar yana faɗin, “Baƙine daga human right. Wai sun zo ne akan case ɗin yarinya da akai raping anan gidan. Sunyi-sunyi da ita tun jiya wai ta faɗa musu amma taƙi. Shiyyasa suka zo domin ganawa da kai, suna son a basu izinin yin bincike akan case ɗin”.
Shiru babu alamar Maash zai amsa kamar ba da shi Baba prof ɗin ke magana. Dan tun kallo ɗaya da yayma mutanen bai sake ba. A yanzu ɗin ma da yaji bayanin komai daga baba prof ɗin bai kallesun ba bai kuma tanka ba sai da ya mula dan kansa. Zamansa ya gyara cike da ƙasaita a wulaƙance ya kallesu a karo na biyu. Cike da gizagonsa ya furta, “Ko zan iya sanin mai kai report ɗin?”.
Kallon juna sukayi, sai kuma cikin ƙarfin hali namijin dake facing Maash ɗin ya furta, “Ranka ya daɗe wannan ai sirri ne bama buɗesa. Duk wanda ya kawo mana report akan wani case yana da cikakkiyar kariya a garemu tako wace fuska. Amma idan munyi kuskuren shigowa bada izini ba ayi mana afuwa. Muna akan aikinmu ne”.
Kamar bazai tanka ba dan har sai da kowa ya zuba masa ido a falon, sai kuma ya yunƙura ya miƙe yana faɗin, “Okay tunda har kuka fahimci hakan da kanku ina fatan zaku gane hanyar da kuka shigo. Dan bana buƙatar fitowa na sameku koda a gate ɗin gidan nan ne”. Daga haka yay wucewarsa cike da takunsa na izza.
Duk binsa sukai da kallo, sai da Baba prof ya katse yanayin cikin wayancewa ya saki murmushi da faɗin, “Kufa yi haƙuri, shima tun jiya ransa a ɓace yake da faruwar al’amarin. Wani dalili ne ma daya ɗan gitta yasa bai ɗauki mataki ba. Amma na tabbatar tunda har kuka zo nan da kansa zai nemeku idan ya huce. Maybe shigowar karan tsaye da kukayi mana ne ya tunzurashi. Amma in har komai ya dai-daita ni da kaina zan nemo ku in sha ALLAH”.
Badan sun gamsu da bayanin Baba prof ɗin ba suka miƙe. Sai dai sun tabbatar da yanda suka karanci tsagwaron rashin mutunci a fuskar Maash ɗin to lallai idan har ya dawo ya same sun komai zai iya faruwa. Har gate Baba prof yay musu rakkiya yana ƙara basu haƙuri. Sai da ya ga fitar motarsu sannan ya dawo. Zama suka sake yi jugum-jugum amma babu alamar Maash zai sake fitowa. Hajiya Mammah ce ta katse zaman shirun nasu da faɗin bara ta sake kiran Maash ɗin. Amma sai Baba prof ya dakatar fa ita akan ta barsa yana son yanzu shi yaje asibiti yaga yarinyar kafin su san ta hanyar da zasu ɓullo ma al’amarin. Sam bata so haka ba, sai dai ganin sauran duk sun bada goyon baya yasa ta yin shiru….
Maash kam daga falon hanyar da zata sadashi da sashen Ummie ya nufa. Ya samu sashen na sabon ƙamshi alamar an masa gyara. Sosai yayi mamakin waye kuma? Tunda yasan ita tana asibiti. Yana shiga yaci karo da mama Balki na shirin fitowa. Cikin kasa ɓoye mamakinsa ya ce, “Mama kece?”.
Murmushi tayi cike da kulawa ta ce, “Eh Alhaji ƙarami. Ai mutuniyar taka ce tun asuba data farka take ta roƙona nazo na duba mata Ummie, tasan maybe bata ci abinci ba. Harda kukanta. Dan haka ina yin sallar asuba gari yay haske nai shirin tahowa sai kuma ga Hayatu ma yaje kai abinci shine na biyosa ya kawoni. Gata nan har ma taci abinci tasha magani barci ya ɗauke ta. Sauri nake kuma na koma can asibitin yanzu dan zata iya ƙin shiga ruwan zafin dana bar mata itama”.
Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya. Sai kuma a hankali da silent voice ɗin nan nasa ya furta, “ALLAH ya saka da alkairi Mama”.
“Amin Alhaji ƙarami ai yiwa kaine. Bismillah ka shiga, Bara naje Hayatu na jirana zai maida ni”.
Shiga yay ita kuma ta fice. Ya jima a ɗakin yana kallon Ummie har sai da kansa ya fara juya masa sannan ya fito. Da gaske sauƙi ya fara samuwa. Dan inda dane a yanda ya shigo ɗin nan komai barcin da take yi saita tashi kansa. Amma kalla jiya yafi zaman awa biyu amma harya fita bata ko motsa ba sai shine da ciwon kai ya addaba. Sashensa ya koma batare daya bi takan su Paah dake a falo ba. Yay wankansa ya shirya tsaff da shi. Bayan ya gama fesa turarurtukansa masu ƙamshi da tsada kala kusan biyar, shiyyasa ba’a gane ainahin turaren da yake amfani da shi yay zaman saka takalmi. Wayarsa da akai kira ɗazun bai ɗauka ba ya duba. MD ɗin companyn sa ne na Kano. Kiransa yay back, dan yasan akan maganar Musaddiq ne. Cike da girmamawa baturen mutumin ya gaishesa da ga can. Kafin ya ɗora masa bayani akan komai na Musaddiq ɗin ya kammala. Zuwa next week zai biyo jirgi zuwa nan Lagos daga nan sai ya wuce. Kamar yanda ya saba amsa wayarsa bata wuce ɗaya biyu koda zakuyi maganar awa ne ya amsa masa da “Okay” kawai ya yanke wayar. Daga haka ya ƙarasa shirinsa ya fito.
Hayatu da Tj kawai ya samu a falon suna jiransa. Bai zauna ba da ga tsayen ya amsa gaisuwarsu yana mai ɗan kallon agogon hannunsa mai shegen tsada da ƙyau. Sai kuma a hankali ya furta, “Let’s go”. Duk miƙewa sukayi, yana gaba suna binsa a baya, sai ma Hayatu ne dake ɗan masa bayani daya shafesu dan akan kasuwanci ne har suka iso gaban motocin da aka gama shiryawa domin fitar tasa. A tare guards ɗinsa da sauran ma’aikatan gidan suka dinga kawo gaisuwa da jajanta abinda ya faru, tare da masa addu’ar kariya daga sharrin duk wani abun sharri. A karo na farko ya ɗan saki gajeren murmushi tare da haɗe hannuwansa a waje guda alamar ya gode. Kamar ko yaushe yana baya TJ na mazaunin driver Hayatu a gefensa. Sai motar guards ɗinsa guda biyu ata gaba da baya su suna tsakkiya.
Sam yawo da guards ɗin nan ba sonshi yake ba. Sai dai baida wani zaɓin daya wuce hakan saboda yanayin ƙasar tamu balle shi mai yawan maƙiya da masoya. Yasha tsallake tarko da aka shirya halaka rayuwarsa. Ana kusan ƙarshe ne da har ya samu harbi gab da shirin buɗe Companynsa na kano har aka harbesa, ALLAH dai ya taƙaita wahala harbin ya samesa a gefen kafaɗarsa ta hagu, daga nan ne Hayatu ya dage akan fitarsu da Guards ɗin.
Tsaiwar motocin ya sashi kauda tunanin ya ɗago, ganin asibiti ya sashi ɗan kallon Hayatu daya buɗe masa ƙofa. Murmushi Hayatun yayi yana duƙar da kai da sosa ƙeya. Komai baice masa ba face ɗan girgiza kansa kawai ya zuro ƙafafunsa ya fito. Ciki suka nufa batare da ya lura da motocin su Paah ba, amma shi Hayatu sarai ya gansu dan tsakanin isowar tasu da tasu ma ƴan mintuna ne………✍️
To Masha ALLAH. Barkan mu da dawowa, ku tayani addu’ar dagewa na gama book ɗin nan kafin salla😀🥰
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓
……A ɓangaren su Paah kuwa isowarsu kenan asibitin suma. Ba kuma su san da su Maash a bayansu ba. Kai tsaye suka nufi cikin ɗakin bisa rakkiyar Mama Balki da sukai kira a waya. A tsorace cikin damuwa ta musu jagora dan bata san dami suka zo ba. Sai dai babu yanda zatayi dole tabi umarninsu. Sauƙin ma taga akwai Baba prof a tare da su. Sun shigo Samraah na zaune a kan gadon jingine da filo tana shan tea ɗin da Mama Balki ta haɗa mata a hankali. Fes take dan har tayi wanka saboda gashin ruwan zafi da Mama Balki tai mata bisa umarnin likitan. A hankali ta ɗago ta kallesu.
Sai da zucuyata ta motsa da ganin waɗanda banyi zato ba. Idanuna na maida na rissinar ina ƙoƙarin haɗiye mamakina da ƴar tsorata. Sai da suka gama zama a inda Mama Balki ta nuna musu sannan na gaishesu cikin muryata da sam bata fita saboda kukan da naci na kwana da yinin jiya. Wasu sun amsa wasu basu amsa ba. Ni kuma sai banji damuwar komai ba tunda nasan dama ba lallai duk su amsa ɗin ba. Kasa cigaba da shan tea ɗin nayi ban kuma ɗago na kalla kowa ba a cikinsu, suma kuma babu wanda ya sake yin magana. Dai-dai nan aka ɗan sake knocking ƙofar. Mama Balki ta zabura domin buɗewa. Jin yanda take jaddada kalmar sannunku da zuwa cikin jin daɗi ya sani ɗan ɗago idanuna na kalla ƙofar. Tamkar abin shiri sai karaf suka faɗa a cikin nasa. Wani irin ɗan jan nasan yayi yuuuu zai lumshe nai saurin fara ɗauke nawa da maida kaina na duƙar. Sai kuma naji duk zaman yama gundireni, ga wani bugawa da zuciyata keyi dan harga ALLAH ko ganinsa tsoronsa yake ƙara min, ni kaɗai nasan kalar masifar dana gani a daren shekaran jiya hannun mutumin nan, dan haka ko matsoraciya kika kirani a wannan gaɓar Bily ni bazan damu ba. Kofin tea ɗin na ajiye a side drawer ɗin gadon na zame a hankali na kwanta tare da lumshe idanuna. Ƙasa-ƙasa na tsinkayi wata muryar dattijo da kamar na taɓa jinta na masa magana. Banji amsar daya bashi ba kasancewar shi dama idan zai yi magana sai in yaso kowa ya jisa ne. Ya ringa yinta acan ƙasan maƙoshi kamar mai jin haushin mutane. Kaɗan nai ƙoƙarin buɗe idanuna dan ina son ganin mai muryar nan sai naga ya nufo inda nake gadan-gadan. Sai da zuciyata ta sake harbawa. Babu shiri na maida idanun nawa na lumshe. A bazata, matuƙar bazata naji alamun rankwafowar mutum da mayataccen ƙamshin turarensa da saukar numfashinsa akan fuskata. Ai babu shiri na ware idanuna. Shi ɗin ne kuwa, gaba ɗayansa yamun rumfa hannayensa duka biyu ajiye a saman gadon ta gefe da gefena. (Kambu! Anya mutumin nan nada kunya?) Na faɗa a zuciyata ina waro gaba ɗaya idanuna waje. Amma shi sai ya wani kaɗa min cat ɗin nasa da ɗage gira hankali kwance. Tuni ƙwalla sun cika min ido, cikin marairaicewa na shiga motsa lips ɗina zanyi magana. Sai kawai naji saukar yatsarsa a saman bakin nawa, idanunsa cikin nawa, cikin salon lumshe idanu da maida muryarsa low sosai ya ce, “Shiii!! Bana son surutu”.
Kunya takaici suka lulluɓeni a lokaci ɗaya. Gefe na kauda kaina tare da ture yatsansa daga saman lips ɗina, dan kalmar baya son surutun faifan taswirar daren shekaran jiya ta dawo min da shi fes. Hannun ya saka ya taro fuskar tawa ya maidota inda take. Baki na tura masa, ina son na hararesa amma shakkarsa da kwarjininsa sunyi masifar min ɗaurin goro, ga mayataccen ƙamshinsa dake tsarga min zuciya.
“Bakin nan yana buƙatar wani abu ne halan?” ya faɗa cikin soft voice yana ƙoƙarin maida yatsarsa a saman lips ɗin nawa. Hannu na na kai da sauri na rufe bakin ina zaro idanu, amma shi ko gezau zama ka iya rantsewa ba shine ke maganar ba. Hankalina sake tashi yayi na saci kallon inda ƴan gidansu suke. Duk suna nan a ɗakin har Mama Balki ma. Tamkar zan fasa ihu idanuna cike da ƙwalla na ce, “Duk suna kallonmu fa”.
Ƙoƙarin juyawa yay zai kallesu, ai bamma san na kai hannuna ba da sauri kan fuskar tasa na dawo da shi.
“What? kuma. Bakin ce na faɗa musu ne su fita kina son mijinki ya ɗanyi kissing ɗinki ba”. Ya faɗa cikin salon kashe ido da ɗan ɗage gira sama murya can ƙasa kamar mai raɗa yana ɗora hannunsa kan nawa da nake ƙoƙarin janyewa daga fuskar sa.
Harararsa na ɗan yi hawaye na cika min ido na ce, “ALLAH ya kiyaye ni yaushe na ce hakan? Kuma ni ba ƴar iska bace”.
“Oh really”. Ya faɗa cikin ɗage gira sama yana ɗan taɓe baki kaɗan da sake matso da fuskarsa daf da tawan. Wani irin bugawa zuciyata ta shiga yi da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirjina ta fito. A hankali na fara jin saukar iska da ƙamshin mouth freshener mai ƙamshin strawbarry. Luff nayi zuciyata na sauka a hankali daga bugawar da take da motse-motse a cikin ƙirjina, harda tura baki batare dana sani ba.
Ɗal ya ɗalle lips ɗin da yatsunsa murya can ƙasa ya furta “I’m not interested maida bakin”.
Cikin sauri na buɗe idanuna wani irin tuƙuƙi na turnuƙe min zuciya da takaicinsa. Dai-dai nan yake ɗagawa da ga duƙowan yana wani yin fuuuu da idanun nasa. Jinai kawai hawayen da nake riƙewa sun wani irin silalowa a hankali…
Maash kam da ya ɗago kallo ɗaya yayma kowa na ɗakin ya ɗauke kansa tamkar baiga irin kallon da duk suke masa ba na tsantsar mamaki da tu’ajjibi. A zafafe Hajiya Mammah ta yunƙura zatayi magana Baba prof ya girgiza mata kai alamar kar tace komai ba. Badan taso ba tai shiru, sai dai kallo ɗaya zaka mata ka fahimci yanda ta gama cika tai famm. Duk abinda ke faruwa hankalinsa na kansu ta wutsiyar ido, amma yay tamkar hankalin nasa akan file ɗinta daya ɗauka yake dubawa. Dai-dai nan likitar da ke dubata ta shigo ɗakin Nurse biye da ita. Ita ta fara gaishesu, dan duk inda akaga Family ɗinsu ana gurmamasu saboda Maash ɗin.
Sai da suka gama gaisawar sannan shi da bai ko kalleta ba ya ɗago shanyayun cat idanunsa ya ɗan kalleta, sai kuma ya kauda kansa cikin dakewar nan tasa ya mika mata takardar daya zare jiya a cikin file ɗin ya miƙa mata. Amsa tayi cikin mamaki, sai kuma ta kalla takardar. Ɗagowa tai cikin rashin damuwa, sai ma gani da take ai tayi abin arziƙi dan haka baki a washe ta ce, “Sir komai da ya kamata mun rubuta kamar yanda binciken mu ya bamu akan fyaɗen, dan a yanzu haka ma muna muku albishir ɗin samar da ƙwararriyar lawyer da zata tsaya mata akan case ɗin. Yau kuma zan kai report ɗin ma police dama izininku kawai nake jira kasancewar ita Hajiya tace ba huruminta bane sai kai yayanta kazo. Amma gaskiya sir ina ƙara bada shawaran kowa ya aikata irin wannan zalincin ga baiwar ALLAHr nan shima ya ɗanɗana kuɗarsa. Dan ALLAH ne kawai ya taƙaita al’amarin da zata ma iya kamuwa da matsalar yoyon fitsari. A yanzu haka ma dole tana buƙatar kulawa sosai saboda ɗinkin dake jikinta abin sam babu daɗi, dan ban taɓa ganin case ɗin fyaɗe na tsagwaron zalunci irin wannan ba. Banama jin mutum ɗaya ne ya aikata abi…..”
“Ina buƙatar sallama by now”.
Ya faɗa cikin katseta da yanayin da kowa ya kasa fassarawa daga garesa. Sororo likitar tayi tana kallonsa. Sai kuma ta ɗan marairaice fuska cikin nuna damuwa ta ce, “Sir ko akwai wani kuskure da mukayi ne anan ɗin? Wlhy duk kulawar da kake buƙata muna kan bata ita yanda ta kamata. Yanzu fa nake maka bayanin har lawyer ƙwararriya mun samar akan case ɗin”.
Komai baice ba, sai ma ɗauke kansa da yay cikin nuna ƙosawa da maganar tata. Da yaga bata da alamar fahimtar shirun yake buƙata sai kawai ya nufi gadon da Samraah take cikin takun ƙasaita da bajinta hannayensa duka zube a aljihu. Duk abinda ke faruwa ina jinsu, dan haka zuciyata ke wani irin gudu raina fal mamakinsa. Guy ɗin nan he is stubborn mutum wlhy. Rayuwarsa har mamaki take matuƙar bani, mutum kamar wani dutsi baka taɓa iya gane gabansa da bayansa. Cak ɗin da aka ɗagani ya dawo dani hayyacina, sosai na zazzaro idanuna waje cikin matuƙar mamaki da ruɗani, rawa lips ɗina suka kamayi. Da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi…miye haka kake yi?”.
Ko kallona bai yi ba, sai ma takawa daya fara a hankali babu wani alamar jin shi yayi ba dai-dai ba ya bi ta tsakkiyarsu ya fice. Nikam ai sai naji bazan iya jurewa ba kawai na cusa kaina cikin ƙirjinsa tare da saƙalo duka hannayena ta wuyansa na saki kukan da ban san dalilin yinsa ba……..✍️
Ehem ehem Yayanmu ikon ALLAH, na Samraah bada kanka a sare kace ma su baba prof ya faɗi🤣🤣🤣
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆
…….Da sauri Hayatu dake tsaye daga bakin ƙofa yaja da baya kansa a ƙasa yana ƙoƙarin ƙumshe dariyar dake neman kufce masa. Isowarsa dai-dai saitinsa ya sashi haɗiye dariyar da ƙyar ya buɗe masa ƙofar da sauri yana ƙoƙarin matsawa.
“Kuzo da kayan”.
Ya faɗa a hankali dai-dai yana ficewa gaba ɗaya daga ɗakin.
“A lallai Mu’azz ka haifoma kanka jaraba wlhy.”
Hajiya Mammah ta faɗa cikin tafa hannaye da riƙe haɓa. Babu wanda ya iya cewa da ita komai dan duk abin faɗar ya gudu musu a bakuna. Sai ma Baba prof ne daya motsa a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki yabi bayansa. Dole duk suma sauran duk suka motsa suka take masa baya. Sai da suka gama fita Hayatu ya ƙarasa gaban doctor ɗin. Kallon Mama Balki yay yayi murmushi. Itama sai ta murmusa tare da nufar kayayyakin su kawai ta shiga haɗawa. Doctor data gama shiga cikin ɓacin rai kallon Hayatu tayi zatai magana. Da sauri ya katseta da faɗin, “Doctor kiyi haƙuri kawai ki bada takardar sallamar nan. Dan wlhy boss da kike gani baya magana biyu. Tunda ya yanke hukunci ya yanku, ya kuma fiki sanin muhimmancin wannan patient ɗin taki”.
Cikin ɗan ɓacin rai ta ce, “Wane muhimmancin ta ya sani anan?. Ana gaya masa haɗarin da yarinya ke a ciki saboda zaluncin da akai mata yana nuna kamar ma baya fahimta. Ni ban taɓa sanin guy ɗin nan stubborn bane sai yau. Idan ma ɗakin ne bai masa ba way not yay magana sai a canja mata da wani”.
Murmushi kawai Hayatu yayi dan ya fahimci bafa zata fahimta ba. Itama sai ta fita rai a ɓace tana mita dan gani gake shima Hayatun neman raina mata hankali yake yi. Binta kuwa yayi bayan ya amshi kayan da Mama Balki ta haɗa suka fito tare. Yana zuwa office ɗin doctor ta miƙo masa takardar sallamar a harzuƙe. Komai baice mata ba ya ɗauka ya juya abinsa ya fito.
Samunsu yay suna shiga mota, dan shi gogan nasa ma har ya shige abinsa. Gaba ya buɗe ma mama Balki ta gefen sa ta zauna, shima yana ƙoƙarin shiga Baba prof ya ƙaraso wajen, umarni ya bama Mama Bilki kan ta fito ta koma motarsa, shi kuma ya shiga gaban ya zauna yana bama Hayatu umarnin suje KARAMCI HOSPITAL asibitin Hajiya ƙarama kenan. Amsawa Hayatu yay yana satar kallon Maash dake a baya tare da Samraah ta cikin mirror. Jingine kansa yake da kujera idanunsa a lumshe tamkar bai san mike faruwa ba. Shi kuma ya tabbatar duk yana jinsu. Kallo ɗaya yay ma Samraah dake kwance kanta a saman cinyar Maash ɗin itama idanunta a rufe ya ɗauke kansa yana ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya……
🌿❤️🔥🌿❤️🔥🌿
Hajiya Sakeena na kai ƙarshen bayaninta Mansoor ya fasa wata gigitacciyar ƙara da ɗaga Centre table ɗin gabansu ya wancakalar. Babu wanda bai firgita ba. Ƙafa yasa ya bugi table ɗin da masifar ƙarfi, badan takalmin dake a ƙafarsa ba babu abinda zai hanashi jin ciwo. Da sauri Attahir ya miƙe yana ƙoƙarin riƙo hannunsa da kiran sunansa. Amma sai shima yay wani irin wancakalar da shi gefe har sai da Attahir ɗin ya zube a kujera. Cikin zafin zuciya da basu taɓa sanin yana da ita ba ya nuna Hajiya Sakeena da Mamynsa da take wani irin kuka tamkar ranta zai fita. Cikin kaushin murya da rufewar idon da fushi ya haifar masa ya ce, “Na tsane ku. Ku biyun nan ba bana son sake ganinku a rayuwata har abada. Kuma yanda kuka zama sanadin rabani da ita kuma na barku har abada!!!!!!”.
Daga haka ya figi bag ɗinsa fuuuu zai fice. Ƙoƙarin miƙewa Attahir yay cikin ƙarfin hali yana kiran sunansa. Yayinda Mamy tai wani irin fashewa da kuka ta bisa da gudu ta riƙo rigarsa. Ko juyowa ma baiyi ba yasa hannu ya kaɓe natan tare da hankiɗata yay ficewarsa. Kafin ta miƙe tabi bayansa tuni yama fice a gidan ko mai kama da shi babu a compaund. Nan ɗin ma fita Attahir yay a guje, sai dai yana fitowa napep ɗin data ɗauki Mansoor na barin ƙofar gidan. Komawa yay cikin gida da gudu bawan ALLAH duk ya ruɗe. Dan key ɗin mota yake lalube amma ya gagara ganin ko guda ɗaya. Haka ya sake fitowa da gudu ya fita shima ya tare napep ya shiga suka bi bayan Mansoor. Amma ko mai kama da shi basu gani ba. Har airport yasa suka bishi a tunaninsa can zaiyi. Sai dai nan ɗin ma babu alamar Mansoor ɗin. Abinda bai sani ba kuma Mansoor bai je airport ba, dan ya fahimci abu na farko da zasu farayi kenan dan haka yaje ya kama hotel anan anguwarsu da yasan bazasu taɓa tunanin zai tsaya anan ba. Na kwana ɗaya ya kama, dan daga yau zuwa gobe yake son sake barin ƙasar nan. Sam bazai iya zama ba. Gara yayi nesa nesa can inda bazai sake ganin kowa ba a cikinsu har ƙarshen rayuwarsa…
Duk wannan budiri da ake Dad bai ko motsa ba. Yana zaune ne kawai kamar saƙago a falon. Ba haka Hajiya Sakeena taso ba. Taso ace tana gama bada labarin nan yanda Mansoor ya fusata shima Dad ya fusata ya dinga ɗirkar Mamy da jera mata kalmomin saki uku sannan yace ta bar masa gida. Amma ba komai, ko yanzu ma ai tasan ƙurar bawai ta ƙare bane ba. Dan ita shaidace akan zuciyar Dad tamkar akku kuturu yake. Kusan zuciyar tasa ce ma yau Mansoor ya kwatanta. Shi kansa shirun da yayi ta tabbatar zuciyar ce ta kume ƴan maza wayaga kutu-ban-ban. Haka ta fito babu tausayi babu imani ta tsallake Mom da nunfashi ke neman ƙwacewa tai ficewarta. Acewarta ai itama haka Mansoor ya tsallake tata ɗiyar ɗaya kwallin kwal a duniya ya tafi babu tausayi balle imani bayan ya gama zana mata kalaman saki uku da gasa mata magana iya son ransa…
Duk neman daya dace Attahir yayi ma Mansoor amma bai gansa ba. Dole ya haƙura cikin maɗaukakin tashin hankali ya koma gida ransa duk a dagule. Yana zuwa kuma ya iske Mamy a sume a farkon shiga falo. Tashi hankalinsa ya sake yi, dan ga Dad zaune tamkar saƙagon gunki zuciya ya kumesa tamkar shima ɗin ya suma. Baima san ya sunkuci Mamy yay waje ba cikin tashin hankali yana kwala kiran sunan drivernsu…..
🪴🪴🪴🪴🪴
KARAMCI HOSPITAL asibiti ne da zamu iya kiransa tsaka tsaki a girma. Dan bai kasance ƙaton gaske ba, bai kuma kasance ƙarami ba. A ɓangaren kayan aiki komai an wadatashi da shi. Duk da sunansa asibitin kuɗi ana aiki a cikinsa tamkar ƙyauta ne saboda sauƙi da sauƙaƙama al’umma. Hakan yasa mafi yawan talakawa suke saurin garzayowa jiyya da karɓar magani a cikinsa. Sai dai da yake komai nasu a tsare yake bazaka taɓa samunsa barkatai ba komansu a tsare yake.
Kamar dai yanzu daya kasance rana ta fara ɗagawa, tako ina tsaftace yake sai ma’aikata dake ɗan kai kawo. Sannan shiru yake babu wata hayaniya ko yawan kai-kawon mutane bayan ma’aikatan saboda dokarsu ce irin yanzu ba’a zuwa duba mara lafiya sai yamma daga huɗu zuwa shida. Koda motocin su Maash suka iso ma da farko securitys ɗin ƙin tashi sukayi su buɗe saboda dokarsu ce ba’a ganin mara lafiya da dare ko safiya zuwa kafin cikar huɗu ko kai wanene, sai da Hayatu yay kiran number Hajiya ƙarama sannan securitys ɗin suka tashi cikin rawar jiki suka wangale gate ɗin. Suna gama parking Tsaki Hajiya Mammah tayi tana mita harda zagin Hajiya Ƙarama lokacin da take fitowa. Babu dai wanda yace da ita komai.
Hajiya ƙarama da kanta ta fito tana musu barka da zuwa dan ita tunda safe tana anan asibiti batama san sunje duba Samraah ɗin ba, ana gama case ɗin human right ta baro gidan. Cikin girmamawa ta gaida Baba prof.. ya amsa mata tare da mata bayanin maido Samraah da sukai nan dan a cigaba da kulawa da ita duk da dai shi ba sunanta ya ambata ba ya dai ce yarinyar dake jiyya. Amma kuma yanata tunanin a ina yasan fuskar yarinyar ne tun ɗazun. Cike da girmamawa Hajiya ƙarama ta amsa musu. Tare da musu jagora har cikin manyan ɗakunan jiyyarsu na vip na ƙarshe a daraja. Kowa baiyi mamakin rashin biyosu da Maash yayi ba, dan sai da Baba prof ya koma da kansa ya masa umarnin bari a shiga da ita kasancewar tare ya tafi da nurses dake ɗauke da gadon ɗaukar mara lafiya. Amma mi, ammakinsu ma ko kallon inda Nurses ɗin suke baiyi ba yanzun ma ya sake ɗaukarta camak yay cikin asibitin. Da kallo kawai Baba prof ya bisa abubuwa da yawan gaske na masa kai-kawo. Dan a wannan gaɓar ya gama sarewa da al’amarin jikan nasa. Sai ma yake wasiwasi anya kuwa shine ya aikata fyaɗen nan kamar yanda Nafisa ta faɗa. Dan al’amarin akwai matuƙar ban al’ajabi a cikinsa da ma ban tsoro.
Acan daga ciki suma kansu kallonsa kawai suke kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa musamman ma Hajiya ƙarama da bata ga abubuwan daya faru a farko ba sai wannan ɗin. Dan baki ta hangame har sai da taji iska na kai mata har maƙoshi sannan ta iya haɗiyewa da ƙyar………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙
……Baba prof da bai koma ciki ba Nurse ɗin nan ya aika yace a sanarma su Paah su fito yana jiransu. Babu jimawa kuwa sai gasu ɗaya bayan ɗaya. Hajiya Mammah da Mama Balki da Hayatu sai shi uban gayyar kawai aka bari. Dan haka Baba prof ya sake aika Uncle Abdullahi yace yay kiran Hajiya Mammah saboda sanin halinta shi kuma baya buƙatar jan wannan maganar a waje shiyyasa ma da Maash ɗin yace a bama yarinyar sallama bai tanka ba. Ya kumace a kawota nan ɗin ne tai jiyya dan yasan asirinsu zai kasance a rufe tunda dai Hajiya Ƙarama ta gida ce. Rai a ɓace Hajiya Mammah ta fito. Dan itafa gaba ɗaya an ɓata mata shirinta. Dan har magana ta gama da waccan likitar akan ta riƙe Samraah har sai nan da wasu ƴan kwanaki da za’a iya fahimtar da ciki ko babu. Idan akwai ta fallasa a gaban kowa, idan kuma babu zata biya ko nawa ne aima Samraah dashensa sai kowa ya gama sani sannan ta tafi plan na gaba da za’a zubar da cikin wajen zubarwar a kashe Samraah. Sai kuma gashi cikin abinda bai wuce awa guda ba shegen yaron nan daya zame mata masifa da bala’i ya hanama rayuwarta rawar gaban hantsi tun yana mitsitsinsa ya rushe komai. Suma waɗan nan ƴan human right ɗin sai taci abu takazansu dan sun mata aiki ba’a yanda tace musu ba. Idan kuma basuyi himmar ƙarasawa ba ALLAH sai sun biyata maƙudan kuɗinta…
A ɓangaren Maash kuwa bai bar asibitin ba sai da aka gama yima Samraah dukan abinda ya dace. Duba magungunanta da sake bincikata in and out. Sai dai kuma anan ɗin ma dai doctor ɗin data duba Samraah ɗin dan ba Hajiya ƙarama bace saboda ba faninta bane. Abinda ta fara bincike da tambaya shine reping ɗinta akayi ne?. Shiru Maash bai tanka ba, bai kuma da alamar tankawar. Dan haka Mama Balki ta girgiza mata kai alamar a’a. Rasa abin cewa tayi, dan dukkan alamu na jikin Samraah ya tabbatar da anje mata babu tausayi. Amma tunda ita Mama Balki tace ba haka bane sai ta tambayi mijinta, acewarta tana son ganinsa taji dalilinsa na nuna irin wannan rashin tausayi akan yarinya ƙarama. Kasa sake cewa komai Mama Balki tayi, sai ɗan satar kallon Maash ɗin da take ta gefen ido. Shi kuma yay masifar haɗe girar sama data ƙasa dan haka doctor ta haɗiye maganganunta a cikin rai dole.
Ruwa tasa aka sakama Samraah dan tana buƙatarsa. Kasancewar akwai cannula ɗin wancan asibitin da ba’a cire ba sai hakan ya sauƙaƙa musu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa barcin ya fara ɗaukarta dan shi dama suke buƙata tayin. Kiran wayar da Paah ya addabesa da shi ya sashi miƙewa cikin ɗan ɓacin rai sai dai bai ce komai ba bai kuma ɗaga wayar ba. Ƙofa ya nufa abinsa batare da yayima ko Mama Balki sallama ba.
Dishi-dishi nake ɗan hangosa, cikin mayen barcin dake ɗaukata a hankali batare da tunanin zai ma jini ba na furta, “Dan ALLAH ka dinga duba min Ummie akai-akai da bata abinci da maganinta. Kace kuma ina gaishet….”
Cak ya tsaya daga yunƙurin fitar da yake yi, hannayensa duka a cikin aljihun wandon suit ɗin nasa. Tamkar mai ciwon wuya ya juyo da kansa a hankali ya zuba su a kanta. Idanunta masu cikar gashi dake a ɗan kumbure har yanzu a lumshe suke. Kallon kusan minti ɗaya yay mata ciff kafin ya motsa a hankali cikin tafiyar nan tasa tamkar baya so ya fice. Da kallo Mama Balki ta bisa, sai kuma ta saki murmushin da har haƙoranta suka bayyana. A hankali ta furta, “Humm Alhaji Ƙarami”. Sai kuma ta juya ta zubama Samraah da har ta fara sauke munshari idanun nata. Shigowar Hayatu ne ya katseta. Sallama yay mata dan yasan ba lallai yau ya samu damar sake shigowa asibitin ba tunda suna tare da boss. Gashi ma acan office jiransu ake sakamakon meeting da yasa Juliet ta tara na gaba ɗaya exco ɗin companynsa na cikin Lagos dama wajen Lagos masu alaƙa da abinda ya faru. Ya kuma tabbatar dole meeting ɗin zai jasu lokaci mai tsayi….
🌺🌺🌺🌺🌺
“Magana ta gaskiya sai kun kula Attahir. Kun fa san Hajiya nada hawan jini. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba a wannan faɗuwar da tayi fa komai zai iya faruwa. Dan ɗayan biyu ne. Paralysis ko heart attack. Saboda a kwanakin nan bincikenmu ya nuna zuciyarta na samun matsi sosai da yawan damuwa. Dan haka dan ALLAH ku kula. Zamu riƙeta anan zuwa 2days, ga wannan sai kaje konan pharmacy na asibiti ka samo dan data farka za’a buƙacesu”.
Numfashi mai nauyi Attahir ya sauke tare da jinjina kansa. Kafin a hankali ya ɗaura da yima doctor ɗin godiya sannan ya miƙe. Tafiya kawai yake amma shi baima san a inda yake jefa ƙafa ba. Dan shi a karan kansa yana buƙatar gadon ne a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya kai kansa pharmacy ɗin cikin asibitin ya miƙa musu takardar da doctor ɗin ya bashi kawai. Koda pharmacist ɗin ya duba ya sanar masa kuɗin baima bi takansa ba ya zaro ATM ɗin sa a wallet kawai ya miƙa masa. Hakama da aka saka adadin kuɗin bai wani dubaba ya amsa ya saka pin ɗinsa. Ledar ya amsa ya koma ɗakin da aka kwantar da Mamy.
Har dare yay nisa babu Dad babu Mansoor. Babu kuma wanda ya kirashi koda sau ɗaya yaji yaya Mamyn take. Haka ya kwana cikin asibitin shi kaɗai, sai a washe gari bayan sallar asuba yana fitowa a massalaci fita yay a asibitin dan likita ya tabbatar masa Mamy zata iya kai sha ɗaya ma bata farka ba. Kai tsaye gidan ƙaninsa na ɓangaren Ummie ya nufa. Kakarsu mace ta rasu, sai tsoho mai ran ƙarfe da ya ragema Ummie kawai. Bai tsaya kwana-kwana ba ya zayyane masa komai dake faruwa. Sosai hankalin kakan nasa ya tashi, Attahiru na gabansa ya shiga bugama sauran ƴaƴansa waya duk yace suzo yana buƙatar ganinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa duk sai gasu, ALLAH ya taimaka ma abin ya haɗa da weekend. Sake saka Attahir yay ya maimaita duk abinda ya faɗa masa. Suma ransu yay matuƙar ɓaci da wannan hali na ƴar uwarsu. Tun tana budurwa sunyi matuƙar yaƙi na ganin ta ajiye waɗan nan banzan halayen amma a banza. Kullum shari’arta da miji bata wuce akan wannan halin na son kuɗi da ƙarya. Gashi nan dai sai da takai ta watsa farin cikin gidanta da kai wa matsayar da suka dinga guje mata sannan hankalinta ya kwanta. Itama autar tasu Sakeena zama da gurɓataccen miji ashe ya canja musu ita ta koma irinta. Ɗunguma sukai su duka harda tsoho zuwa asibiti suka dubata. Sunko samu ta farka, haka duk suka jajanta mata sama-sama. Gaba ɗaya kunya ta hanata iya kallon kowa a cikinsu musamman ma Attahiru. Nauyin yaron take ji, dan yanada matuƙar haƙuri da kawaici. Duk irin banbancin da take nunawa tsakaninsa da ɗan uwansa bai taɓa ɗauka ya sakama ransa balle har taga ɓacin ran hakan akan koda fuskarsa ce. Yau ga wanda take matuƙar nunama soyayyar ya tsallaketa ya wuce akan mace. Duk da dai tasan ita duk ta jawo komai, sosai take jin dana sani da nadamar ƙwaɗayayyar rayuwarta a yau.
Kwananta biyu a asibiti babu ko ƙyallin Dad. Tana son ta tambayi Attahir tana jin tsoron jin abinda bashi zuciyarta take son ji ɗin ba. Dan tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Hasalima kamanninsa da Mansoor ya ɗebo yasa take fifita soyayyarsa akan sauran yaranta. A ranar aka basu sallama. Tun da suka baro asibiti taga an ɗauki hanyar gidan babanta gabanta ke faman faɗuwa. Sai dai tsoro ya hanata tambaya har suka iso. Isowarsu babu jimawa suma su Amal suka iso. Dama suna Abuja gidan kawunsu ne. Sanda zasu wuce India su aka turasu can sai yau suke dawowa.
Anan ɗin ma babu wanda yace mata komai har tsawon kwan biyu, abu ya dameta amma itama tsoron jin abinda bashi take son ji ba ya hanata iya tambaya. Zuwan Sakina biyu gidan babu mai tankama wani ita da ita. Su duka sun ɗauki zafi da juna tamkar ba ƴan uwa ba jini ɗaya. Hasalima a baya sun fi shiri da juna matuƙa, dan rayuwar ƴammatanci gaba ɗaya Sakeenar a gidanta tayita ma..
Attahir dai yakan zo da safe kullum kafin ya wuce aiki ya gaisheta. Hakama idan ya tashi sai yazo nan ya gaisheta sannan yake wuce gida. Kamar wasa a haka kwanaki suka dinga tafiya tana a gidansu. Ga baba ma sama-sama yake amsa mata gaisuwa. Baya shiga sabgarta baya kuma bata damar shiga tashi har gata da watanni biyu cif a gida. Su Amal ma tuni suka tattara kayansu suka gudu gida. Dan sunce bazasu iya zama gidan Baba ba saboda gidansu komai najin daɗin rayuwa suna da shi. Nan ko duk da ƴaƴan baban maza sun tsaya akan al’amuransa shima kasancewar matarsa ba itace kakarsu ba abubuwa da yawa sai a hankali kawai. Ta kankane komai daga ita sai nata jikokin Mamy ma sai tayi da gaske wataran take samun abinci a gidan. Dan ma Attahir baya gajiya da kawo mata kayan shayi da ƴan kayan maƙulashe. Amma itama da tuni yunwa ta kai rayuwarta ƙasa kam………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏
……..Tun fitarsu a ɗakin jiyyar yarinyar har barinsu asibitin akan idanunta ne. Numfashi ta sauke mai nauyi tare da ture ɗan kwalin kanta baya. Dauriya kawai take da danne abinda ke matuƙar cimata zuciya. Wayarta ta ɗauka a ɗan zafafe, tai ƴan danne-danne tare da kaiwa kunnenta. Ana ɗagawa daga can ta ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin ɗan farin ciki mai gauraye da sauran damuwa ta furta, “Sabon labari”.
Cike da zumuɗi daga can akace mata “Name fa Hajjaju masu Lagos da kayan cikinta.”
“Hummm Jannifer bar batun wasa Please. Yarinyar nan ce fa suka maido asibitin nan yanzu”.
“What! Kina nufin Samraah?”.
“Yess. Yanzu haka tana nan tare damu. Ban san miya faru ba suka maidota nan ɗin. Naga dai mutuniyarki a zafafe cikin matuƙar damuwa kuma. Yanzu kam na fara zargin akwai abinda take ƙullawa. Na kuma yi alkawarin sai na bincikosa a koma ina taje ta bizne shi”.
“Karki wani damu Hajjaju wannan duk mai sauƙi ne. Ko ni nan na isheta. Har mi akai akayi Alaja Nafee kuma. Matar da bata iya komai ba sai da shawaran banzan Madan Rubayya ɗin nan. Ni dai kawai yanzu shawaran da zan baki kawai kiyi ƙoƙarin ki kula da yarinyar nan da ƙyau, tunda dama tun farko kayanki ce. Kin zauna sakaci ne Alaja Nafee ta nema ƙwacewa. Banzama irinta da ta ƙare a ƙarƙashin guzumomi irin su Rubayya. Dan bana raba ɗayan biyu shakkar Rubayya ɗinne ya hanata taya yarinyar kafin ke, tunda itama ai mayyar ce. Saboda haka kiyi amfani da wannan damar akan ita yarinyar kiyita banka mata maganin da zai fidda mata sha’awar namiji gaba ɗaya a ranta, ina tabbatar miki da kanta zata kawo miki kanta tana kukan ki mora albarkacin jikinta. Haba Alaja Lawusa kamar baku bane Lagos ɗin. Ni fatana ma idan zakije honeymoon da ita aje dani koda a ƴar riƙon handbag ce”.
Dariya mai ƙayatarwa Hajiya ƙarama ta saki, tare da sake lume kanta a cikin kujera idanunta a lumshe tana siffanta cikakkiyar surar Samraah data jima tana birkita mata lissafinta. Dan tun randa Jannifer tayi kiranta ta sanar mata da zuwan yarinyar gidan matsayin gift da Mashi’a tai shirin kawoma Hajiya Babba dan ta kula da ita ta gama jin ƙaguwa da son ganin yarinyar. Saboda haka ta azalzali Paah suka dawo Nigeria washe gari badan ma sun kammala abinda ya kaisu ba. Koda suka iso tai ido biyu da Samraah sai da numfashina ya nema shiɗewa. Dan yarinyar irinsu ne ake kira da full option. Komai yaji yanda ya kamata. Sai dai kash abubuwa da dama sukai mata katanga da hakan, tayi ƙoƙarin riƙe kanta har zuwa sanda ta gama shiryawa sai kuma ga wannan abin ya faru da yay matuƙar ƙona mata rai, dan a yanzu haka ita kaɗai tasan irin kalar zafin yaron nan Awwab da take ji a rayuwarta. Wani irin kishi take ji tamkar ta kashe banza a wuce wajen dan son Samraah take na gaske. Har ma ta gama yankema kanta shawarar auran yarinyar zatayi ta ɗauketa daga Nigeria zuwa duk ƙasar da take so sai ta dinga kai mata ziyara….
“Alaja!”.
Jannifer ta katse mata tunani. Firgigit ta dawo hayyacinta tana mai sauke nannauyan numfashi. Cike da basarwa taja ɗan sirrin tsaki da faɗin, “Sorry Jannifer na tafi wata sabgar ne kuma.”
Dariya Jannifer ta ƙyalƙyale da shi daga can, cike da shaƙiyanci ta ce ko dai kin tafi tunanin kayan alatu ba”.
Murmushi Hajiya Ƙarama tayi tana mai cije lips ɗinta. Kafin a hankali ta ce, “Ke dai Jannifer sheɗaniya ce wlhy. Lallai da ace bakiyi ridda daga musulimci zuwa kiristanci ba da ba ƙaramar sheɗaniyar matar hausawa musulma akayi ba. Amma yanzu mun bar musu, dan inba ma wanda ya sani ba taya zai taɓa yarda kin haɗa iri da fulani. Humm ALLAH dai ya jiƙan General. Ya tafi yabar baya da ƙura. Maybe da za’a shawarcesa a dawo da shi duniya yaga Munirra ɗinsa yanda ta koma kamar bata taɓa haɗa jini da yan arewa da musulunci ba da dakansa zai kashe kansa ma wlhy”.
“Hummm Hajjaju kenan masu Lagos da jama’ar cikinsa. Ai duk nawa wasan yara ne. Idan kuna guri mu kuma wake ta tamu ƙananun ƙwari. Mufa a riddar kawai muka tsaya sai ɗan cinikin goron nan da muke kafawa a faifai da ɗan hutawar nan muna more ƙuruciya. Ku kuwa fa, idan akace ai tone-tone ai kema musulman sai sun gwammace riddar kikayi wlhy”.
“Uhhm to ya isa. Dan ke baki gajiya da zakuɗe-zakuɗe. Yanzu dai sai anjima idan na tashi zan zo gida na sameki mu ƙarasa. Dan zan ɗan shiga theater”.
“Hummm” kawai Jannifer tace daga can tare da yanke wayar tana dariya. Itama sai Hajiya ƙaramar tai dariyar kawai tana ƙoƙarin ajiye wayar, a dai-dai nan wani kiran ya sake shigo mata. Ido ta zubama number na tsawon lokaci, YALLAƁAI ɓaro-ɓaro ya fito. Mamaki ya sake kamata dan rabon da mai number yay kiranta ta jima sosai, dukan tara-tara ƙirjinta ya shiga hi har sai da wayar ta kusa yankewa ta dawo a hayyacinta. Da sauri ta ɗauka tana miƙewa ta nufi ƙofar office ɗin ta murza key cike da rashin gaskiya….
🤔Hummm wai ina matan nan suka dosa ne? Sannan waye yay kiran Hajiya Ƙarama kuma? Idan na fahimta dai Hajiya Ƙarama na waya da Madam ne a farko, matar data ɗakko Samraah daga Abuja zuwa Lagos. Tab ɗin babbar magana. Ashe ita ɗin musulma ce shine tai ridda. Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un. Anya wannan duniya kuwa. ALLAH mun tuba badan halinmu ba😭🙏.
__
THREE DAYS LATER
Kwanaki uku kenan da faruwar komai. Sam Maash yaƙi yarda ya zauna da family ɗin nasa akan batun Samraah. Dan haka ran kowa a matuƙar ɓace yake. Amma shi ko’a jikinsa sai manna musu hauka kawai yake. Dan gaba ɗaya ma ya maida hankalinsa ne akan binciken yanda akai containers ɗin companyn sa suka ɗiba yara da wiwi saɓanin lodin kayan abinci. Dan suna shirin tunkarar Mr Paul ne da ƙarfinsu a court saboda sun shigar da ƙara ne kafin shi bisa shawarar lawyers ɗinsu.
Ta gefe kuma ga jikin Ummie da ya rikice. Ga kuma Samraah dake asibiti har yanzu ba’a sallamota ba itama, sai dai wata irin kulawa take samu ta musamman da tattali a wajen Hajiya ƙarama har Mama Balki ta fara shan jinin jikinta. Sai dai abinda Mama Balki bata sani ba ita kanta Samraah nazartar Hajiya ƙarama take sannu a hankali. Gefe kuma tana kaima ALLAH kukanta. Koda labari Mama Balki bata sanar mata da ciwon Ummie ba sai yau da Falak tai kiran wayar Mama Balkin, a lokacin ita kuma ta ɗan fita dan haka Samraah ta ɗaga. Har yanzu basu taɓa haɗuwa da Falak ba sai dai tana cin abincin gidanta kullum. Bata da lafiya ne tana fama da tsohon ciki shiyyasa bata zo tama dubata ba, sai dai sun gaisa ta waya har kusan sau uku. Yanzun ma sun gaisa cike da kulawa ma juna tamkar dama can sun san junan nasu, kafin Samraah ta sanar mata Mama ta ɗan fita ne, amma idan ta dawo zata faɗa mata sai ta ƙara kira.
Daga can Falak tai murmushi da faɗin, “Okay ba damuwa ALLAH ya ƙara lafiya, dama zanji ko yaya jikin Ummie ne dan na kira Yaya Hayat ashe garin sauri yama bar phone ɗin a gida, gashi yanda ya fita a hargitse duk na kasa nutsuwa”.
Ɗan jimmm nayi zuciyata na bugawa da sauri-sauri jin ta ambaci Ummie, da ƙyar na iya tambayarta “Ummien Maash Mansion? Wani abu ne ya sameta?”.
Batare data fahimci kan tambayar ba cikin damuwa muryarta na rawa ta ce, “Eh ita, kin san kwana biyun nan jikin nata duk babu daɗi, to yau dai da alama ya tsananta ne dan shima Yaya Hayat a rikice ya fita TJ ya kirashi. Wlhy ina tausayawa Ummie, da ace inada wata babbar dama akan baiwar ALLAHr nan abinda zan farayi shine tsayawa akan samun lafiyarta, amma muna gani an hanamu taimakonta. Wanda keda ƙarfin yin hakan kuma an kulle masa tunani gaba ɗaya, dan wlhy da ace Yaya Awwab basu shiga tsakaninsa da lafiyar baiwar ALLAHr nan ba da kowama yaci ubansa, ai sun san shi ɗin ba kanwar lasa bane har Baba prof ɗin da Paah ba iya tankwarashi suke ba. Amma ba komai ALLAH yana nan, watarana sai labari”.
Tuni ma ni ba fahimtar zantukanta nake da ƙyau ba, rawa sosai jikina ke mun, ga hawaye suna bala’in gudu a saman fuskata. Ashe shiyyasa duk jiya bai zo asibitin ba, yau ma haka. Ko Hayatu mai ƙoƙarin zuwa sama da sau uku yana kawo musu abubuwa jiya sai dare ya shigo ya duba ta. Abinci ma TJ ne ke kawowa. Amma Maash tun daren shekaran jiya da zai tafi take cemasa ya dinga duba mata Ummie da bata abinci bai sake zuwa ba, harta ƙullacesa ma ita da, da tunanin ya gama cin moriyat ganga zai yada kwautrnta, ashe abinda ke faruwa kenan…
“Ya subahanallah Samraah! Wani abu ke miki ciwo ne? Ko tashi kikayi da ƙarfi kika fama ciwon?”.
Mama Balki ce mai maganar nan a rikice. Ɗagowa nayi ina kuka mai tsanani dan shashshekar da nake tasa har fisga numfashina keyi. Lallashina Mama Balki ta shiga yi tare da bani ruwa tace nasha. Da ƙyar na amsa nai maƙwarwa uku, jikinta ta jawoni ta rungume, hakan sai ya taimaka min wajen samun nutsuwa na fara sassauta kukan. Kaina na a saman cinyarta tana shafa gashina ta ce, “Samraah”.
Cikin dasashjiyar muryata na amsa mata da, “Na’am Mama”.
“Mike faruwa?”.
Da ƙyar na iya danne kukan dake taho min na ce, “Mama Ummie. Ashe bata da lafiya amma shine babu wanda ya sanar min”.
Iska ta ɗan furzar cikin damuwa. Kafin ta ce, “Waye ta faɗa miki?”.
“Falak”.
Na bata amsa ina sharce hawaye…….✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕
……Kanta ta girgiza da faɗin, “Ni ban san sai yaushe bakin Falak zai iya dinga koyon shiru ba. Kiyi haƙuri an ɓoye miki ne saboda kema ga yanayin da kike ciki. Shekaran jiya ne Alhaji ƙarami ya shiga yana ƙoƙarin bata abinci shine fa kawai jikin ya rikice. Ta jimasa ciwo sosai a hannu da ƙyar aka iya fiddoshi a ɗakin, daga nan duk wanda ya shiga da duka take korosa, to yau kuma sai ta yanke jiki ta faɗi saboda kwana biyun nan bata ci bata sha rashin abinci jikinta yayi week. Amma ki kwantar da hankalinki zuwa yanzu sun ce Alhamdullah komai ya dai-daita. Dan Hayatu ma ya tabbatar min tana barci saboda drip ɗin da aketa ƙara mata.”
Duk da na ɗan ji nutsuwa sai da na sake sharce hawaye, ɗan shiru mukayi kafin a hankali nace, “Mama”.
Da kulawa ta amsa min da, “Na’am Samraah”.
“Mama a yanzu sai nake ganin kamar shi yafi dacewa ma abinda ke tare da shi ya rabu da shi kafin a samu nutsuwar yima Ummie magani. Duk da dai wani abu ya jima yana damuna. Yanzu duk kuɗinsa ace gidan nan babu cctv camaras tako ina?”.
“Tabbas gaskiya kika faɗa Samraah. Sai dai mun kwatanta hakan muma bai yiwu ba, a dalilin tsanar magani da Alhaji ƙarami yayi tun yana ƙaraminsa. Ko yaya ruwa ya surka wlhy bazai sha miki shi ba koda da kala ne. Shiyyasa yin maganinsa keda matuƙar wahala. Gashi kuma shi ba’a zaune yake ba waje ɗaya, duk yanda muka so fara bashi koda ruwan addu’a ne sai kiga abin ya zama shiririta. Ina da tabbacin kuma wanda ke wannan aikin kullum cikin sabuntashi suke bawai sun koma sun kwanta bane suma. Maganar camara kuwa ai Alhaji ƙarami yasha sakawa amma sai a wayi gari duk an ciresu. Har ɓoyayyar camara an saka a gidan nan amma kamar abin maita wlhy sai da aka cireta. Hakan na nufin koma su waye a biye suke, shiyyasa ma kikaga ina sake jin tsoron al’amarin gidan nan da mutanensa. Dan idan bana jikinka ba banga wanda zai dinga maka wannan bita da ƙullin ba a nesa da kai”.
Baki na buɗe zanyi magana sai naji kamar amalar motsin tsayawar mutum a ƙofa. Shiru nayi bance komai ba, sai kuma kamar ance na ɗaga ido na hango inuwa ta jikin window. Magana Mama zatayi na wayance ina mai zame kaina da ga cinyarta na ce, “Mama barci nake ji. Dan ALLAH idan Nurse ɗin nan tazo kice bana son allurar nan ni nama warke karki bari tamun”.
Kallon mamaki da naga Mama namun yasa nai mata nuni da window da ido. Tuni ta ɗauki haske kasancewar dama a ankare take. Itama sai ta wayance ta shiga ƴar dariya da faɗin, “Ja’ira ai allurar nan sai an kaita har ƙarshe, bari ma Hajiya tazo zance ta sake ƙara miki kwana biyu kiyi digir dake yanda zamu koma gida da ƙarfinki”.
Shagwaɓa na shiga mata da faɗin ni bana so. Itako tana dariya. Daga haka mukayi shiru. Kwanciya nayi zuciyata na faman kai-kawo. Tabbas lokaci yayi fa dazan dawo hankalina. Dan na fahimci in har shi bai fita a halin da suke sanyashi ba baiwar ALLAHr nan bazata taɓa samun ingantaccen lafiya ba. Domin sauƙi yana samuwa a gareta, sai dai yanayin kwan-gaba kwan-baya da ake fuskanta yasa al’amarin ke taɓarɓarewa. Idan kuwa har za’a iya hana cctv camaras zama lafiya to lallai waɗan nan mutanen ba ƙaramin shiri sukai ba. Suma kuma suna buƙatar a shirya musu yanda ya kamata. Dan dole wayo al’amarin yake buƙata da hikima kamar yanda suma suke komai ta cikin basira”. Wannan tunane-tunanen da hawayen da suka kasa barin idanuna ne suka haifar min da zazzaɓi mai zafi, gashi naƙi gayama Mama har bayan sallar isha’i. Dan da ƙyar ma nayi alwala saboda sanyin da nake ji. Ina idarwa na haye gado na kwanta tare da duƙunƙunewa cikin bargo. Sosai na gaji da zaman asibitin nan, fatana kawai ALLAH yasa yazo dan shine kawai zaisa a sallameni. Yan gidansu dai dama babu wanda ya sake zuwa sai Hajiya ƙarama da nake gani, ita kam kullum ne sai ma tazo sama da sau uku, sai daga baya na fahimci ai dan asibitinta ne shiyyasa itama muke yawan ganintan…..
🩸🌟🩸
Sosai damuwar halin da Ummie ke ciki a kwana biyun nan yasa bai sake waiwayen asibitin ba. Duk da kuwa wani sashe na hankalinsa na’a can ɗin. Sai dai rashin isashen lafiya shima dana lokaci ta sashi baiyi wani yinƙuri ba. Yau kuma zafi da ƙuncin da gidan ya masa matuƙa ya sashi ɗan kimtsawa bayan ya dawo sallar isha’i. Tun la’asar ya kora Hayatu gida dan haka shi kaɗaine a sashen sai Laalah da TJ dake leƙowa akai-akai duba shi shi da Shu’aibu amintaccen guard ɗinsa. Tsaff ya fito yana zuba mayataccen ƙamshin nan nasa tamkar ba dare ba. Tj da Shu’aibu na ganinsa suka miƙe da sauri, hakama sauran ma’aikatan gidan sai gaisuwa suke miƙawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan kwana biyun nan miskilawan ne a kusa. Da ga shi sai TJ da Shu’aibu sukai fitar dan hana sauran guards ɗin binsu yayi. Tj ke driving Shu’aibu a gefensa. Shi kuma yana baya zaune idanunsa akan wayarsa yana daƙila. Kicin-kicin fuskar nan take babu alamar ya taɓa sanin minene ma dariya.
Cike da girmamawa TJ ya ce, “Boss ina muka nufa?”.
Shiru bashi da niyyar amsawa. Sai da ya mula dan kansa ya furta, “Hospital”.
Cike da girmamawa TJ ɗin ya amsa masa tare da ɗaukar hanya. Har sun gota wani bakery yace TJ ɗin ya dakata. Tuna duk lokacin da zasu je asibitin tare da Hayatu sai ya sa an tsaya ya sayi wasu abubuwan ya sashi cewa a dakatan. Shima TJ ɗin tun bai furta ba ya fahimci abinda yake nufi tunda dai koda yaushe da shi ake zuwa asibitin shima. Fita yayi zuwa cikin bakery ɗin batare daya amshi wani kuɗi ba, dan boss ya wuce fiye da haka a wajensu ai. Bai wani jima ba ya fito ɗauke da ledoji masu ƙyau har guda uku. Booth ya buɗe ya sakasu sannan ya dawo cikin motar. Zuwa yanzu ba wayar yake daƙila ba kansa ya kwantar a jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Koda suka iso ma sai da ya ja kusan mintuna biyu tamkar mai nazarin ta yanda zai shiga cikin asibitin sannan ya fito. Yana gaba cikin takun nan nashi na ƙasaita da isa su TJ na biye da shi. Babu yawaitar mutane har ma ma’aikatan jefi-jefi ne. Ko kallon wanda suke a reseption ɗin kuwa baiyi ba yayi wucewarsa. Sai su TJ ne suka gaishesu. Suko suka bishi da kallo tamkar wasu tsoffin mayu. Sai faman washe bakuna suke yau gasu ga Maash, mutumin da yafi kuɗi wahalar gani a Nigeria. Dama wasu a abokan aikinsu sun sanar musu da zuwansa a kwana biyun nan, sai dai su basu taɓa cin karo da shi ba sai yau ɗin…
Har yanzu duƙunƙune nake a cikin bargo ina rawar sanyi dan zazzaɓi nake ji sosai. Ga hawayen damuwa da halin da Ummie ke ciki sun kasa tsayawa a idanuna. Ita mama Balki ta ɗauka nayi barci ne, dan haka ta maida hankalinta a kallon tv tana sauraren wa’azin malam Ali isa fantami da aka saka a African tv3. Knocking ƙofa da akayi a hankali kamar abin dole ya sata rage ƙarar tvn, shiru kamar baza’a sake ba sai kuma aka ƙara. Miƙewa tayi zuwa jikin ƙofar tana tambayar waye? Jin ba’a amsa ba ta buɗe. Ni dai duk ina jinsu amma da yake har kaina na’a cikin bargo ba ganin komai nake ba.
Murnar da naji tana yi da ambaton sunan Alhaji Ƙarami ya sanya gabana faɗuwa. Sai ko ga mayataccen ƙamshinsa ya gama isowa har cikin hancina. Wasu muryoyi biyu naji suna gaisheta da tambayarta mai jiki. Na gane muryar driver ɗinsa. Ɗayan ne dai ban gane waye ba amma nasan ba hayatu bane ba. Sai da naji alamun fitarsu da rufe ƙofa sannan shima naji muryarsa a daƙilen nan can ƙasa-ƙasa kamar abin dole yana gaida Mama. Ita ko da kulawa take amsa masa da tambayarsa jikinsa da kuma na Ummie. Nan ɗin ma da ƙyar ya amsa itama yana tambayarta ya mai jiki. Itako da fara’a ta ce masa, “A jiki da sauƙi sosai. Yau ne ma ta so birkicewa saboda samun labarin jikin Ummie daya motsa da tayi. Dan har bayan sallar magriba ɗin nan tana shartar hawaye sai da na ɗan mata nasiha sannan tai shiru, inaga shine ma dalilin kwanciyar da wuri sai kuma barci ya ɗauke ta. Banji yace komai ba, sai dai haka kawai na dinga jin kaifin idanunsa a jikina. Shiru ɗakin na kusan minti ɗaya sai kuma naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa. A zatonta shine ya fita, dan haka cike da shagwaɓa na janye bargon daga saman fuskata zanyi magana da Mama. Zuuuu naji jinina na falfala uban gudu ta cikin jijiyoyina tsabar shock ɗin cin karo da abinda nai zaton shi ya fita. Da sauri na kauda kaina na sake maida fuskata cikin bargon.
A bazata naji alamar an zauna a kusa da ni, Ji nai na sake daburcewa kamar zan fasa ihu, amma sai na dake tare da yin luff a cikin bargon ina addu’ar ALLAH yasa kada yace sai na buɗe kaina……..✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆
……Shiru ɗakin har na fara murna. Kusan mintuna uku muna a haka babu motsin komai sai naji yayi ɗan gyaran murya. Idanuna na sake rumtsewa da ƙarfi batare da na yarda na motsa ɗin ba dai. Sake yi yayi, nan ma naƙi na motsa, sai da yay ta uku sai kuma a hankali ya ɗaura da faɗin,
“Dama Ummie c….”
A zabure na yaye bargon gaba ɗayansa. Na ware dukan girman idanuna a kansa. Lips ɗina na rawa a marairaice na ce, “Ummie mi?”. Maimakon amsa min sai kafe cikin idanuna yayi da nasa cat eyes ɗin masu matuƙar girma da yalwar gashi. Wani irin tashi tsigar jikina tayi, sai kif-kif kawai nake faman yi da idanu. Sai faman kokawa nake da numfashina dake seizing.
“Stubborn girl”.
Nakasashiyar muryarsa ta daki cikin kunnena duk da kuwa cikin low voice yayi ta, badan ma idanuna na akansa ba babu yanda za’ai na jisa dan pinkish lips ɗinsa ne kawai suka motsa a hankali. Kamar wata sakarai na jujjuya masa kaina a hankali. Motsa lips ɗina dake ƴar rawa na shiga yi, da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi ya sa mu Um mie?” a rarrabe ina rissinar da idanuna da suka ciko da hawaye. Dan duk yanda na ƙudirci masa tsiwa ko kallon cikin idanunsa nayi magana sai naji sam na gagara yin hakan. Mutum ne mai masifar kwar jini da cika wuri. ALLAH ya azurtashi da wani irin girma a gaban duk wanda ya tsaya koda ace ya fisa a shekaru da matsayi. Saukar tattausan tafin hannunasa saman fusakata ya sani sake ɗago idanu da sauri na kallesa. A cikin nashi cat idanun suka sake faɗawa. Kallon juna muke a wani irin yanayi har na tsawon shuɗewar wasu sakanni. Kafin a kasalance na motsa nawa dake tara ƙwallan da ban san na minene ba. Shi ko har a lokacin kallon nawa yake yi batare da ya ƙyafta ba, sai ma cikin wani irin soft voice and silent and slowly ya furta, “She is missing you, and she need you”.
“I miss her too”. Na faɗa nima a hankalin ƙwallar data cika min idanu na gangarowa. Idanunsa ya sake ɗan lumshewa tare da buɗewa a lokaci guda ya cigaba da kallona ina kuka sosai harda shashsheka. Shi bai lallasheni ba, bai kuma janye hannunsa dake a kan fuskata ba har yanzu. Tsawon mintuna biyu ina kukana, dan shirunsa sake tunzurani yake. A bazata matuƙar bazata cikin low voice ɗin sa ya furta,
“Samrh”.
Cak na tsaya da kukan da nake, tare da ɗago jiƙaƙƙun idanuna na kallesa. Kallon nawa shima yake da shanyayun nashi da suka canja launi zuwa golden an blue.
“Why are you crying?”.
Ya sake faɗa muryarsa na sake komawa can ƙasan maƙoshi. Samun kaina nayi da sake sakar masa sabon kukan. Tare da riƙo hannunsa dake akan fuskata na ƙan ƙame.
Idanunsa da suka gama canja launi kawai ya zuba mata. Sai Adams apple ɗinsa ne ke faman kaiwa da komawa a cikin maƙoshinsa. A hankali ya kai ɗayan hannunsa saman kafaɗarta, riƙota yayi tare da ɗagota gaba ɗayanta batare da ya janye hannun nasa data ƙanƙame ba sai da ya kaita gab da jikinsa sannan ya janye ya turata cikin jikin nashi gaba ɗayanta. Tsam ya rungumeta yana mai lumshe idanun nasa ƙam-ƙam shima saboda zafin da jikinta ya ɗauka duk da da akwai kaya a jikinsu su duka sai da ya bala’in ratsashi.
Ni kam jina a jikin nasa ya sakani sake fashewa da kuka. A hankali na fara ɗan dukan bayansa ina faɗin, “Why! Why? Why? Suke wahalar da rayuwarta? Mita musu da zafi haka? Da ga ganinta She is an innocent and strong woman. Basu barta haka ba, sun rabata da ku jininta da zata ji sanyi a wajen ku. Natsane su, wlhy na tsanesu. I promise my self sai na ɗaukar mata fansa koda zasu maidani fiye da yanda suka mata. Sai na sakasu gudun ceton rai da babu mafaka Ya Awwab. I promise….”
Kuka ya sake sarƙeta. Sai wani irin jan nunfashi take a sarƙe kamar mai ciwon asthma. Da sauri ya rabata da jikinsa, tare da kwantar da ita a kan cinyarsa. Sosai numfashin nata ke fisga, hannayensa ya saka duka biyu a kumatunta ya shiga ɗan bubbugawa da kiran sunanta.
“Samrh! Samrh! Please keep calm. I know you can, please calm down. Hundred percent I am with you.”
Ina da gaske ƙoƙarin ƙwacewa numfashin nata yake. Ai baima san ya figi bottle na ruwa dake a side drawer ba ya zuba a hannu ya shafa mata duk da kuwa tana numfashi, sai kuma yay saurin kai mata ruwa a baki amma bakin ya gama datsewa ruwan yaƙi shiga. Da sauri ya kai kan nasa bakin ya zuƙa, batare da wani tunani ba ya ranƙwafo kanta ya ɗaura lips ɗinsa a saman nata ya shiga juye mata ruwan tare da riƙe hancinta. Wani masifar jan nunfashi tayi ta baki sai gashi ta zuƙe ruwan gaba ɗaya. Hancin nata ya saki tare da janye bakinsa. Ita kuma ta fara tari sosai. Sake ɗagota yayi a hankali ya maidata jikinsa ya rungume suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sunfi mintuna uku a haka sai da ya tabbatar zuciyarta ya gama sauka sannan ya raba jikinsu ya kwantar da ita a gadon a hankali…
Kasa buɗe idanuna nayi, sai ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jajjere. Jin saukar abu mai taushi da ƙamshi a saman fuskarta ya sani buɗe idanuna a hankali. Shine ke goge min hawaye da farin handkerchief ɗinsa tass. Idanunsa ya saka cikin nawa har ya gama. Batare da ya janye handkerchief ɗin ba da ɗan yanayin lumshe idanu da buɗewa ya furta, “Miyasa fitina baya miki wuya? Samrh! Ba’a gaggawa a al’amarin maƙiyi, idan ba haka ba zai fika gudu ne wajen cimma manufa. Lokacin da zaka isa sai ka samu shi har ya gama ya juyo. Be a gentle okay”.
Sosai zantukan nasa suka shigeni tare da canja min wasu tunanina da yawa a kansa. Cikin suɓutar baki muryata a dusashe na furta, “Kana nufin kaima duk abinda ke faruwa kana sane?”.
A bazata naga ya wani ɗan taɓe gefen small pinkish lips ɗinsa da lumshe idanunsa sannan ya saki murmushi. Bily idan nace miki kaɗan ya rage zuciyata ta ɓaro akan murmushin nan nasa da salon da yayisa ki yarda da ni kawai. Badan yafi kowa iyawa bane, sai dan murmushi ya kasance ba ɗabi’arsa bace. Amma tabbas magana ta gaskiya murmushin ya ɗebeni iya ɗiba. Dan kaɗan ya rage na fallasa ɓoyayyen al’amarin da na jima ina binnewa a kansa.
(Kin sani a duhu mutuniyar, kodai kin jima kina son Maash ne?).
“Hummm Bily kenan abar dai zancen sai lokacin yinsa yayi”. Na faɗa cikin ƴar dariya.
(Lallai kam, to shike nan na bari muje zuwa labari).
Yanda yay murmushin har ban san na kafesa da mayataccen kallo ba. Idanunsa ya ɗan waro min waje da ɗagesu alamar kallon fa?. Cikin sauri na kauda fuskata gaba ɗaya ina tura baki da faɗin, “Miye abin kallon ma anan”.
Bai tanka min ba, sai ma ɗan kauda kansa da yay gefe. Banyi zaton jin shirunsa a wannan gaɓar ba. Amma nima dai sai na basar kawai tare da ture hannunsa na janye sauran jikina dake a nasa tare da jan bargo na juya masa baya. Dan in banyi hakan ba akwai babbar matsala, dan komai zai iya fitowa saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri abinda ke can ƙasanta a ɓoye na azalzalota.
Shiru ban sake jin motsinsa ba. Ban kuma yarda na kallesa ba har fin mintuna biyar. Sai a lokacin naji motsin buɗe ƙofa, ɗan juyawa nai kaɗan. Sauka idanuna sukayi akan bayansa dai-dai yana ƙarasa ficewa da jan ƙofar ya rufe a hankali. Nima lumshe idanuna nayi ina sauke ajiyar zuciya. Sai kuma na sake dunƙule jikina a cikin bargon dan ji nake kamar zazzaɓin na ƙaruwar min ma. Mintuna bai fi huɗu da wasu sakanni ba aka sake buɗe ƙofar, idanun na sake buɗewa a hankali. Yanzun kam Mama Balki ne da Doctor sai shi a ƙarshen shigowa. Hannayensa duka biyu a cikin aljihun baƙin wandonsa. Idanun na maida kawai na rufe, dan nasan bai wuce akan zazzaɓin jikina yaje yayo min wannan gayyar ba.
🩸🌟🌟🌟🩸
A hankali take faman kaiwa da komawa a cikin ɗakin nata kai kace safa da marwa take ko motsa jiki. Sai dai sam ba haka bane. Abubuwane masu yawa ke matuƙar damunta da cizar mata zuciya. Dan tun zaman da sukai da Yallaɓai ɗazun da magrib ta gagara samun sukuni. Gaba ɗaya taji ta kasa komawa asibitin da taci burin komawa dan akwai wani baƙo da zatai mai muhimmanci. Maganganunta da Yallaɓai ne suka shiga dawo mata dalla-dalla tamkar a yanzu suke tattauna su....
“Yaushe yarinyar nan tazo aiki gidanku? Waye kuma ya kawota?”.
“Lokacin muna Dubai muma zuwa kawai mukai muka sameta anan. Amma ance Mashi’a ce ta kawota”.
“Mashi’a?!”.
“Yes ita fa. A cewarta kuma ta kawota ne as a birthday gift wa mahaukaciyar matar can. Tunda masu aikinta sun sake guduwa a lokacin babu mai kula da ita”.
“A ina ta ɗakkota?”.
Ɗan jimm tayi, sai kuma ta ce, “Gaskiya wannan ne ban sani ba”.
Kasa sake cewa komai yayi, sai ma kai-kawo daya shiga yi hannayensa goye a bayansa……….✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒆𝒏
…….Yayi kusan sau fin huɗu sannan ya dawo ya zauna. Cikin kaushin murya da dakewa ya furta, “Dole ne yarinyar nan ta mutu a asibitinki. Kuma a yau zuwa gobe nake buƙatar sanin daga inda ta fito? Miye dalilin Mashi’a na kawota?. Zaki cigaba da riƙeta har zuwa kwanaki uku da za’a gama min bincike na”.
Idanu Hajiya Ƙarama ta zubama mutumin zuciyarta na gudu da sauri-sauri a ƙirjinta. Cikin ɗan rawar lips muryarta na seizing ta ce, “Amma yallaɓai hakan fa zai iya zama kuskure. Dan yarinyar nan gaba ɗaya komanta ya gama dai-daita raunin daya jimata ne kawai ya rage ya ƙarasa warkewa mu sallameta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko jibi. Sannan case ɗinta bama fa a hannuna yake ba doctor Larai ce ke kula da ita. Daɗin daɗawa Awwab. Yaron nan fa ya wuce duk inda kake zato da tsammanin sa kaima ka sani. Ni wlhy zuciyata ma ta fara bani kamar a ankare yake da abubuwa da yawa. Gashi sam baya jin tsoro ko shakkar kowa. Yanzu ka dubafa yarinyar mutane yama fyaɗe a cikin gidansu amma komansa bai canja ba face ma wani irin kulawa da yake bata ga girman kai sabo da yake ji da sam na gagara fassara al’amarin nasu”.
“Mtsooww Lawusa, ke kin san dai idan na faɗi magana ko zartar da hukunci bana canjawa ko? Dukan waɗan nan hujjojin naki basa gabana. Gawar yarinyar nan kawai nake buƙatar gani fine and done”. Ya ƙare maganar a wani irin hankali yana zazzaro mata idanunsa da sukai mugun kaɗawa saboda giyar da yake ta faman lodama cikinsa tun kan tazo. Yawu masu kauri ta haɗiye. Sai kuma ta shiga jinjina kanta. “Okay shike nan naji zan kashe yarinya bayan ansan wacece. Sai dai fa kaima ya kamata ka tuna lokaci yayi da zaka yi komai a wuce wajen. Nifa ina buƙatar shares ɗina, dan lokaci yayi da zan mora wahalata ta shekaru gaskiya. Tunda ba ƙuruciya nake ƙarawa ba. Yaron can Fahad banga amfanin saba ai, shima ya cancanci mutuwa. Sannan magana ta gaskiya mahaukaciyar matar nan na gaji da shiga da fita ina shan warin sashen ta itama. Ya kamata kayi wani abu, dan nasan dai zuwa yanzu kaima ka fanshe dukan alƙawarinka da alwashinka a kanta. Kaga sai muje next target wato Awwab. Dan Doctor Ram ya tabbatar min ko a yau muke son poison ɗin nan a shirye yake da aiko mana shi Nigeria.”
Iska mutumin da tunda ta fara maganar ke kallonta yake ta faman furzarwa. Sai da ta kai har ƙarshe kafin ya ɗauka kofin giyarsa ya kai baki, ƙarasa shanye wanda ya rage a ciki yayi ya dire glass cup ɗin a saman Centre table ɗin gabansa yana wani girgiza kansa. Sai kuma ya maido jajayen idanunsa ya zuba mata. “Dont warry Lawusa. Komai da kika sani a tsare yana nan bai canja ba. Sai ma ƙarin shares da kowannen mu ya samu sakamakon sake hauhawar dukiyar nan. Dan yaron nan ba ƙaramin mahaukacin arziƙi ya tara mana ba. Shiyyasa nake son ki fahimceni akan kashe yarinyar nan. Dan sam na kasa jin nutsuwa akan barinta raye tun kan nasan wacece ita. Kije ki ƙarasa aikin ki a next zama zaki ji mina tsara game da Fahad ɗin shima”.
“Shike nan yallaɓai ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana. Na barka lafiya a huta gajiya”.
Hannu kawai ya ɗaga mata da maida idanunsa luuu ya rufe cikin mayen barcin buguwar da yayi……
Iska ta furzar mai zafin gaske. Tare da tura hannunta cikin hular kanta. A take hular ta zame ta faɗi, gashinta mai ƙarancin tsayi da cika ya bayyana. Bata damu ba, dan abinda ya dame ta shi ya dameta. Tunda ta haɗu da Yallaɓai bai taɓa saka mata doka ko sanyata aiki ta gagara yinsa ba, saboda ra’ayinsu bai taɓa banbanta ba. Sai dai a wannan gaɓar an samu akasi. Dan yallaɓai ya sakata yin aikin da ita kanta tasan idan tayisa sai ta cutu. Matuƙar cutuwa. Domin kuwa ita kaɗai tasan irin son da takema yarinyar nan with all her heart. Duk da tana jin zafin abinda shegen yaron nan mai kama da ɗanyen attaruhu yay mata ɗigon sonta bai ragu a zuciyarta ba. Jinta take a yanda ta jure kwanakin baya akanta yanzu bazata iya ba. Dan wani irin mayataccen buƙatar son kasancewa da ita takeyi. A jiya kaɗan ya rage tabi dare a asibitin ta lalubeta. Sai dai ba haka take so ba. Tafi son su mori juna yanda ya kamata. Dan tana jinta a ranta banban da sauran waɗanda ta mu’amalata daga fara wannan harkar zuwa yanzun. Yarinyar akwai kayan marmari fresh a jikinta matuƙa da har wani sashe na zuciyarta na ƙin ganin bebekin Awwab akan abinda yay mata. Yo ita mace ma ta kasa nutsuwa balle shi namiji mai ji da shekarun ƙuruciya da hutu. Sosai tana jinta a tsaka me wuya…
“Yau ma wani ɗinne ya mutu da kika kasa nutsuwa?”.
Firgigit ta dawo hankalinta tare da juyawa tana kallonsa. Shima kallonta yake fuska babu yabo babu fallasa. Paah ya sake watsa mata kallo murya a kausashe ya furta, “Dan iskanci kinzo nan kin shanyani bayan ina can ina jiran ki kawo min coffee”.
Ajiyar zuciya Hajiya ƙarama ta sauke da ƙoƙarin controlling kanta. A hankali ta saki murmushi tare da canja yanayinta like she is innocent woman, cikin kwantar da murya ta ce, “Kayi haƙuri Abban Awwab. Ƙafata ce fa ta riƙe daga fitowa a bayi shine nake ɗan mammotsata. Amma wlhy kana raina tunda naga lokacin shan coffee ɗinka yayi. Amma ganin baka kirani ba yasa nai tunanin ko baku dawo daga masallaci bane”.
“Tunda nine limamin masallacin ba”.
Ya faɗa a gatsine cike da sake tunzura. Sake kwantar da murya tayi da shiga bashi haƙuri. Uffan bai sake cemata ba ya fita fuuuu yana harare-harare dan dama borin kunya ne kawai ya naɗe da hauka. Tun ɗazun yana a garden ɗin Maash tare da Siyama suna holewarsu. Dan tunda ya fahimci Maash baya gidan ya tura mata saƙo a waya kan ta samesa a garden ɗin Kasancewar yasan anan ɗine zasu iya zama safe fiye da ko’ina a gidan irin wannan lokacin. Sai yanzu ne yake fitowa dan yasan duk inda Awwab yake yana gab da dawowa gidan….
Itama da kallon harara ta bisa. Kafin taja tsaki da faɗin, “Nadai kusan yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda stupid man. Dan ɗauke beauty yarinyar nan zanyi mubar ƙasar zuwa can muyi aurenmu mu more rayuwar mu. (Umarnin yallaɓai fa?) Zuciyarta ta ayyana mata. Kanta dake wani irin sara mata ta dafe kawai zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Lallai dole ne tasan mafita a daren yau basai gobe ba. Dan tafi kowa sanin wanene yallaɓai akan duk abinda ya sa gaba. Amma bari taje ta bama wannan sakaran coffee dai ta dawo…..
(Tofa 🤔 kaji kuma wani lissafin 🥱🤫)
💢🪴💢🪴💢
A gidan Abba Imamu rayuwa ta matuƙar juyama Mom baya. Dan sam ta kasa gane komai akan al’amarin Halime. Yarinya ce shu’uma matuƙa. Ga kalolin baƙin ciki da take tura mata iri daban-daban. Yanzu har takai Abba ya sallami mai aiki yace kowa tai aikinta ranar girkinta. Mom son jiki, Bibaa da Baby basu iya komai ba. Sai yazam a gidan duk ranar aikin Mom yini ake da yunwa, dan ko anyi abincin da wahala ya ciyu. Daga ƙarshe su ƙare da rigima ita da Abba. Dan ya tabbatar mata shi kam bazai ɗauki wannan banzan halin ba da almabazarancin abinci. Ashe da can duk wahalar gyaran gidan da abinci dama Samraah ce keyi ita kaɗai nata ƴaƴan na kwance. To ta sani bata cutar masa ɗiyar ƴar uwa ba kanta ta cuta. Dan ba baki ya mata ba ƴaƴanta in har a haka zata kaisu gidan miji to ta shirya kuwa za’a dinga koro mata su. Wannan magana tasa ta ƙona mata rai a ranar sai da suka tafka rigima sosai data kaisa da bata wan shika. Aiko dai tace babu inda zata. Kota kanta baibi ba yay ficewarsa.
Sam Halime bama tasan abinda ke faruwa ba ita. Dan kwanakin nan gaba ɗaya bata ganema kanta. Kullum bata da aiki sai barci, itama dai aikin gidan a ranar girkin nata ƙarfin hali kawai take yi wajen yinsa. Sai yamma taji zazzaɓi yace salamu alaikum. Bazata taɓa samun nutsuwa ba sai irin sha ɗayan nan na dare. A yau ɗin ma da aka tafka rigimar har ya bama Mom sakin tana barci bata san bikin da akeyi ba. Amma mi, Bibaa da Baby na ganin Abban ya fita suka afka ɗakin Halimen wai zasu daketa. Sun san itace ke ƙullama Mom ɗinsu munafunci. Miye-miye dai magana tsaff a bakunansu. Cikin barci kawai Halime taji an sauke mata uban dundu. A firgice ta farka tare da sakin ihu. Sai kuma ta tsaya cak ganin Bibaa da Baby tsaye kanta suna huci. Kallon mamaki ta bisu da shi, sai kuma ta tashi da ƙyau cikin dakewa ta tambayesu ko lafiya?.
“Uwarki zamu ci, shegiya annoba. Wlhy yau sai mun miki jina-jina a gidan nan dan ubanki”.
“Tofa babbar magana, wai kishiya taga abin cikin zanen kishiyarta”. Halime ta faɗa tana yayimar ɗan kwalinta ta aza bisa kai tare da sakkowa a gado. Waya ta ɗauka tana cigaba da faɗin, “Ai ku jira bani kaɗai ya kamata ku cima uwar ba, dole na kira Imamu kamar abin zaifi armashi. Kunga sai ku tuɓe ƙaton banza ku haɗamu ku lakaɗa mana dukan tsiya tunda shine ya kawoni gidan”.
Sororo Baby da Bibaa sukai suna kallonta. Kafin cikin ƙarfi hali da tsiwa Bibaa ta ce, “Badan Abbanmu ne ƙaton banza ba dan ubanki. Sai dai idan kece ƙatuwar banza. Kuma wlhy yau sai kin ban mana gidanmu”.
Dariya sosai Halime ta sheƙe da shi, kafin ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni Halimatu. Gidanku dai gidanku dai. To ke banda abinki Habi wace sakarar mace ke alfahari da gidan tsohonta? Ai macen data kai mace gidan mijinta take ma fata da alfahari, dan acan ne idan ta tadda komai rigijif-jif-jif sai kiga ta gyara gidansu albarkar iyaye ta bata tsaro tako ina. Dan haka riƙe cika bakin nan naki wannan gidan Halime ne da Jalilah, Habi dai har yanzu bata da gida sai na raɓe-raɓe. Garama ita wannan galwalin ta kusa shiga daga ciki”. Tai maganar tana nuna Baby..
Cikin fusata Baby tace, “Waye Galwali? Aiko yau sai na tabbatar miki na fiki hauka da tashanci”. Fuuu tayo kan Halime…….✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏
……Kafinma ta kai hannu kanta ita ta ɗauke fuskar Baby da maruka. Ta shaƙo wuyan Bibaa dake bayanta itama ta bata nata. Basu gama dawowa a hayyacinsu ba ta shiga musu dukan kan mai uwa da wabi. Yo har a gayawa Halime iya danbe. Ita da ake kira giwar dambe a wajen ɗibar ruwa a garinsu. Kai hatta a islamiyya duk wanda ya sake ta haɗosu da Halime aka haɗu a lungun kaci uwaka bayan an tashi to ranar kuwa sai yaci uwar tasa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta musu lis da duka. Sai gasu a ƙasa suna faman ribzar kuka. Itako ta ɗauki sabuwar wayarta da Abba ya siya mata kwanan nan tayi kiransa tana kuka wai yazo gasu Baby da taɓare zasu bigeta.
Bawan ALLAH sai gashi a haukace harda Alhaji Sadisu. Suka ko sameta kwance tana ɗan nishi ita adole ga wadda taci duka. Gashi ta kawo jan baki ta ɗan sassaka a wasu wurare na fuskarta da hannu wai duk sayin duka ne. Abinka da fara saika ɗauka haka ɗinne. Ido rufe Abba ya dinga sauke musu maruka abinda bai taɓa koda kwatanta yi ba. Sai dai ma idan Mom ta zugashi akan Samraah yana mata faɗa ita yana marinta suna dariya. Haukace masa Mom tayi da kuka da ihu, amma ada idan ta zuga aka mari Samraah daɗi take ji, ya kuma tabbatar mata idan har ta matso shi sai ya ƙara tsinke igiyar aurensu data rage. Dole taja birki tana kuka sai Alhaji Sadisu ne ya amshesu da ƙyar. Amma sai da yay musu lilis da duka ga wanda Halime tayi musu. Ya kuma tabbatar da ya matso da auren Baby nanda ranar juma’a ko daga shi sai mutanen anguwa ne za’a ɗaura ta tafi haka dan ta ishesa. Itama kuma Bibaan idan bata kama kanta ba zai aurar da ita ga duk wanda ya masa babu abinda ya shallesa da wani karatunta. Haka suka dinga kuka. Shiko ya kama Halimensa sukai ɗaki yana lallashi. Sai dai ita kuma duk jikinta yayi sanyi, dan harga ALLAH batayi zaton zai dakesu haka ba. Ita kawai tayi ne a tunaninta faɗa kawai zai musu a wuce wajen. Koda suka shiga ɗaki sai ta kasa haƙuri ta fito ta sanar masa gaskiyar abinda ya faru harda dukan datai musu. Tama nuna masa video data ɗauka dan sanda tace zata kirashi da farko bashi ɗin ta kiraba ashe video tajeyi.
Wannan halin nata shine abu na farko da yake sakashi jin ƙaunarta fiye da koda yaushe. Dan a ɗan zamansu sam ya fahimci Halime bata iya ƙarya ba. Sannan bata taɓa kawo masa ƙarar Mom ta mata wani abu a gidan ba idan baya nan kosu yaran sun mata. Sai dai ita Mom ɗin ta tonama kanta da kanta asiri ta hanyar gaya masa. Shiyyasa yau data kirashi ya taho a rikice. Amma Mom wani lokacin ma tun suna rigimar take kiransa ta sanar masa ƙarya da gaskiya cikin kunfar baki. Idan ya dawo gida yana jiran yaji Halime tace wani abu sai yaji shiru, ko yama samu tana firinfijimarta a gidan hankali kwance tamkar komai bai faru ba. Dan ita in har akwai wuta tv na kunne shikenan tace bata da sauran takaici a duniya. Balle ta haɗa uban shayinta cikin ƙaton kofi da burodi ta soya ƙwai ta zauna tana sha tana kallo ai ji take duniya babu ya ita. Har da rana da yamma shan shayi take saboda masifar ƙaunarsa da takeyi tun tana ƙaramarta. Abinci ma bai cika damunta ba in dai akwai shayi da burodi balle ga madara a ciki yaji da sauran kayan shayi ace kuma akwai soyayyen ƙwai wayyo jinta take kamar a aljanna. Yasha gwadata akan magana da Mom take sanar masa game da ita. Amma mutuniyar sai ta basar tama nuna ita yaushe akayi hakan, idan ma anyi to ta manta. Koda yake harga ALLAH bawai tanayi don makirci bane ko wani abu. Kawai ita har cikin ranta da halayenta da anyi abu ya wuce shikenan kawai sai wani ya taso kuma. Wannan dai ta gama da babinsa. Idan ko har kakaga Halime ta riƙe abu a rai ya dameta to lallai al’amarin babbane matuƙa. Dan wahalar data sha a hannun innarta da ace tana riƙewa a rai da tuni hawan jini da ciwon zuciya sun kai rayuwar yarinyar ƙasa….
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
Ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna suke shigowa gidan. Har gaban dashensa TJ ya faka motar, da sauri Shu’aibu ya fito ya buɗe masa. Koda ya fita maimakon shiga sashen nasa sai ya koma ainahin ƙofar shiga babban sashen gidan. Babu kowa a falon sai Azizat dake dakon jiran dawowarsa. Yana shigowa kuwa ta miƙe zambar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta nufosa tana masa sannu da zuwa cike da shagwaɓa. Sai da tazo gab da shi ya wani watsa mata mummunan kallo yayi wucewarsa upstairs. Kai tsaye sashen Ummie ya nufa ya barta nan tsaye baki sake tana binsa da kallo ga hawaye na gudu a fuskarta. Sai kuma ta kwasa da gudu tai sashen Hajiya Mammah itama. Sai dai tana murɗa ƙofar bedroom ɗin ta tajita a rufe gamm. Jingina tayi jikin ƙofar tana sake fashewa da kuka. Sai kuma wani ɗan nishi-nishi da take juyowa kamar daga cikin bedroom ɗin ya sata fara sassauta kukan nata tai tsai alamar saurare. Tabbas daga ɗakin mahaifiyar tata ne. Knocking ƙofar ta farayi da kiran sunan ta amma babu alamar za’a buɗe, sai dai kamar anyi shiru an daina nishin. Sake fashewa tayi da kuka tare da barin jikin ƙofar da gudu tai ɗakinta.
Wata shegiyar dariya Arwa dake laɓe tun ɗazun tana kallonta dan komai akan idonta ya faru ta saki, sai kuma cike da farin ciki ta furta, “Iska na wahalar da mai kayan kara” ta juya cike da takun girgiza jiki ta koma nata ɗakin dake a sashen uwarta Hajiya ƙarama. Dan su dukansu kowanne a sashen mahaifiyarsa yake har suma su Malika….
★ A ɓangaren Maash kuwa bai wani jima ba a sashen Ummie ya fito, dan ya samu tana barci ne alamar sauki na samuwa. Baya buƙatar wata matsalar ta sake samuwa a dalilin shigowar tasa dan haka ya juya ya fita a kan lokaci. Har zai wuce sai kuma yay tunanin shiga sashen Paah dan akwai maganar da yake sun suyi. Gobe in ALLAH ya kaimu kuma ya sanar masa da baƙi da zaiyi da wuri zai fita a gidan ba lallai su haɗu ba. Sashen Paah ɗin ya nufa da tunanin shi kaɗaine dan yasan da wahala Hajiya ƙarama idan tana a gidan kasancewar ya ganta a asibiti ɗazun. Knocking yay har sau biyu amma baiji motsin komai ba. Yasan Paah da kallon labarai yanzu haka hankalinsa nacan baima jisa ba. Dan barci dai yanada tabbacin baiyisa ba zuwa yanzun kam. Kansa tsaye ya tura ƙofar ya shiga kawai, sai dai kuma da saurin tsiya ya tsaya cak dai-dai yana ɗaga kafarsa zaiyi taku kusan na biyar a cikin falon sakamakon furucin da Paah ɗin yayi waya a kunnensa. Da ƙarfi yaja numfashinsa da ke neman fisgewa daga cikin ƙirjinsa. A wani irin harzuƙe da kaushin harshe ya furta, “Paah!!”.
A bala’in rikice Paah ya juyo tare da sakin wayar ƙasa yan zazzaro idanunsa. Fuuuu Maash ya juya ya fice a falon tare da bugo masa ƙofar da masifar ƙarfi har sai da ya zabura. “ Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un”. Ya shiga maimaitawa cikin tashin hankali. Shi ya haifi Awwab, amma wlhy zai iya rantsuwa da baya jin tsoron wani sama da yanda yake shakkar yaron nan. Kai hatta Baba prof daya haifesa baya jin yana shakkarsa kamar Muhammad. Koda wasa baya son Muhammad ya kamasa da wani laifi musamman akan abinda za’ace ya shafi mahaifiyarsa koda kuwa ɗan kaɗan ne…
Sashen Maash ɗin Paah ya nufa a ɗarare cikin kuma tashin hankali, dan Gara yaje suyita kawai baya son ya ɗauki fushin nan da shi. Kasancewar ta ainahin ƙofar shiga sashen ya fita yabi kansa tsaye ya shiga. Shu’aibu ya samu a falo da TJ. Cikin girmamawa suka shiga gaidashi. Da ƙyar ya iya danne yanayinsa ya amsa musu. Kafin ya ɗora da tambayar ogan nasu. Kai tsaye TJ ya amsa masa da, “Alhaji yana ciki”.
“Okay to bari na gansa ko?”.
Da girmamawa suka amsa masa da to. Shi kuma yay gaba kai tsaye sashen bedrooms ɗin Maash, suma sai suka fice dama abubuwan da suka dawo da shi a mota suka shigo da su ciki. A bedroom ɗin da yafi ƙyautata zaton samunsa yay knocking. Kusan mintuna biyu aka buɗe ƙofar. Ɗan zuba masa idanu Maash dake ɗaure da towel jikinsa na raɓar ruwa alamar daga wanka ya fito yayi. Sai kuma ya ɗauke kansa fuskarsa na sake zama kicin-kicin. Batare da ya ce komai ba ya saki ƙofar ya juya ciki. Bin bayansa Paah ɗin yay shima, a bakin katafaren gadonsa ya zauna, yayinda shi kuma yake daga ɗan lungun closet ɗin sa yana ƙoƙarin zira jallaniya fara tass mai gajeren hannu. Fuskarsa a tsananin ɗaure ya sake fitowa. Batare daya kalli Paah ɗin ba ya jingina da mirror daga tsaye yana kallon wani gefen. Kaɗan ya motsa lips ɗinsa wajen faɗin, “Good Evening”.
Karan farko Paah ya saki murmushin ƙarfin hali, sai kuma ya amsa da, “Evening dear, how are you?”.
Shiru Maash bai amsa masa ba. Sai ma ƙara ɗauke kansa da yay gefe. Shiru ɗakin shima Paah bai sake magana ba yana ƙulla ta inda zai fara. Kafin ya nisa a hankali ya sake furta. “Muhammad magana nazo muyi”.
“Ina jinka”.
Ya amsa masa a daƙile. Kai kawai Paah ya girgiza. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Kana fushi da ni ko? Akan abinda kaji ina faɗa. Haba Muhammad, kafa san yanda nake ƙaunar Ummu-Hidaya. Taya zan iya wofantar da ita saboda ta samu lalura”.
“Paah ka faɗi abinda ya kawoka kai tsaye Please”. Maash ya katsesa cikin zafin rai………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆
……Zuru Paah yay masa yana kallo, sai kuma ya haɗiye yawu masu kauri yana jinjina kansa. “Muhammad wai sai yaushe zaka yarda dani akan mahaifiyarka ne? Ƙarshen maganata da kawai kaji baka san akan mi nakeyi ba, ba kuma kasan dawa nake yi ba”.
Fuska sosai Maash ya yamutse ransa na ƙara masa suya akan halin mahaifin nasa. Duk yanda yaso danne kar ya biye masa bazai iya ba, a fusace ya bashi amsa da, “Sai randa ka canja Paah. Sai randa ka ajiye son zuciya ka tuna da halacci. Bazan hanaka yin dukkan abinda kai niyya ba. Sai dai wlhy ina gab da ɗaukar mummunan mataki. Sannan yaronka na bashi nan da kwana uku ya sallami waɗan nan ƴan iskan yaran daya tara min a company, idan ba hakaba duk wani mai alaƙa dasu ya kuka da kansa. Kuma shima ya ajiye aiki da hannunsa kar ya bari na ziyarci Company yana ciki”
Cikin ɓacin rai da tsarguwa Paah ya ce, “Muhammad kana zargina ne?”.
Shiru yay yaƙi tankawa. Sai da Paah ya miƙe zuwa gabansa. Cikin sauke murya ya sake furta, “Muhammad miyyasa kai baka yafiya ne? Miyyasa kake da riƙo? Sai yaushe zaka yarda dani? Dan kawai kaji ina waya sai ka fasaarata da wata siga daban har kana tunanin sallamar waɗanda basu ji ba basu gani ba daga aiki”.
“Sai randa ka daina saka wannan ɗan iskan yaron na maka kawalcin yara ana kawosu da sunan wai ma’aikata. Paah na sanka fiye da yanda nasan kaina. Dama na jima ina zargin waɗan nan yaran zaman iskanci suke min a company. To wlhy na basu daga daren yau zuwa gobe su koma inda suka fito, in ma gidan karuwai zaka buɗe musu bai shafeni ba rayuwarka ce”.
Rumtse idanu Paah yayi da ƙarfi. Sosai kalaman ɗan nasa ke masa amsa kuwwa a cikin kunne. Yasan wanene Awwab idan yay fushi. Sam baya tauna magana yayin faɗarta balle shakka. Jin alamar zai bar wajen ya sashi buɗe idanunsa. Cikin ɓacin rai ya dakatar da shi da faɗin, “Miyasa baka tauna magana yayin furtata? Ina matsayin mahaifinka amma baka shakkar tauna magana yayin furta min ita. Komai ya zo maka a rai saika yaɓosa waje”
A daƙile da yanayin zafin rai shima Maash ya furta, “Ni ɗankane bani da hurimin hanaka duk abinda ka tsarama rayuwarka kam. Amma ka sani bazan iya cigaba da jurar ganin kana kana takamin mahaifiya a ƙarƙashin takalman ƙafarka ba Paah. Abinda na ɗauka kafin yanzu bazan iya ɗaukarsaba a yanzu. Idan da kace rashin mace ke saka aikata abinda kake aikatawa yanzu minene hujjarka kuma tunda kana da wata matar? Kai da kanka kamin alƙawarin dainawa, ashe baka fasa ɗin ba. Idan mace ɗaya ta maka kaɗan ka ƙara auren mana. Ka ƙaro uku su zama huɗu yafi min wannan mummunar ɗabi’ar taka mai zubar da mutunci ga zunubi wajen UBANGIJI…..” ya ƙare maganar cikin ƙaraji dasa hannu ya watso kayan saman mirror ɗinsa gaba ɗaya. Sai kuma ya kaima mirror ɗin naushi, a take kuwa ya shiga tsatstsagewa. Sake kai masa wani naushin yayi, ya kuma tsagewa tare da jimasa ciwo. Sai ga saman yatsunsa duk jini ya ɓata. Da sauri Paah ya kamo hannun nasa jikinsa har rawa yake. Amma Maash ɗin sai ƙoƙarin ƙwacewa yake yi. Dan so yake kawai ya ƙara kaima mirror ɗin duka ko zai samu sauƙin zugin da zuciyarsa ke masa…
“Please sweetheart relax. Dan ALLAH try to calm down. Jifa yanda kake jima kanka ciwo Muhammad”.
“Is not your business Paah. I beg you leave me alone”.
“Naƙi ɗin, nace maƙi na barkan! Miyasa kake da zuciya ne Muhammad. Fushinka yayi yawa. Taya zan Barka ka cigaba da jima kanka ciwo. Nace kayi haƙuri! Haba Muhammad”. Ya ƙare maganar cikin sanyin murya tare da jawoshi jikinsa ya rungume. Abinka da su duka dogaye, sai gasu kai ɗaya. Ƙarfi da cikar zati kawai Maash zai nuna masa saboda shi yana akan ƙuruciyarsa, shiko koba komai girma ya kamashi.
Luff Maash yayi a jikin mahaifin nasa, sai faman sauke zafafan ajiyar zuciya yake a jajjere. Yayinda Paah ke jin yanda zuciyar tasa ke gudu da ƙarfi. Sunfi mintuna uku a haka sannan ya ɗagosa. Kama hannun nasa yay suka nufi wajen gadon, zaunar dashi yay sannan yaje ya ɗakko first aid box ya dawo kusa da shi ya zauna. Hannun nasa dake ta tsatstsafo da jini ya kamo, cike da kulawa ya fara masa treating. Ko sau ɗaya Maash bai motsa ba, bai kuma kalla mahaifin nashi ba har ya kammala ya naɗe masa da bandage. Zama yay zai fara magana Maash ɗin kawai ya miƙe, da sauri Paah ya riƙosa ya maida shi ya zaunar. Bai musa ba ya zauna, sai dai yaƙi kallonsa yanzu ma. Shiru Paah yay yana kallonsa, sai kuma ya sauke numfashi a hankali yana sake tattaro abinda yake son faɗar. “Muhammad kayi haƙuri, tabbas nasan bana ƙyauta muku, sannan ban yima kaina adalci ba. Bazan kira abinda nake aikatawa da ƙaddara kawai ba, harda sa kai. Shiyyasa tabbas a rayuwa ka guji aikata mummunan aiki a ƙuruciya, idan kuma ya zama jarabawarka ce ka fara kayi gaggawar tuba. Idan ba haka ba wannan abin zai ta bibiyarka ne a lokacin girma, a lokacin da kuma kake son ka daina ɗin amma abin yabi jininka. Wannan maganar mahaifiyarka tasha faɗa min ita da maimaita min a duk sanda ta sameni a halin rashin gaskiya. Amma mi a lokacin bana gane karatunta, gani nake ai duk sanda na shirya zan iya dainawa”. Yay murmushin takaici, mai nuna ainahin ciwon da yake ji a zuciyar yasa. Cikin ɗan yarfar da hannu ya cigaba da faɗin, “Abubuwa da yawa sun faru, wasu ma suna kan faruwa da ni kaina ban san adadi ba. Ni ne ya kamata ace na tsaya muku, amma sam ban taɓa yunƙurin hakan ba koda sau ɗaya. Hatta da rashin Fahad a kusa da mu yana damuna. Sai dai ban san taya zance komai ba. Muhammad! Banso ace halin da nake ciki yayi nason da zai shafeku ba kamar yanda mahaifiyarku tasha yin fata. Sai dai a wannan gaɓar na fahimci zancen nan na masu iya magana da kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Wlhy bazan ɓoye maka ba, case ɗinka akan yarinyar nan ya tsaya min ta yanda na kasa haɗiyeshi, sannan yanda kake bama yarinyar kulawa tamkar ba abinda ake gudu bane ya shiga tsakaninku na sake ɗaga min hankali. Bana son ace sunanka ya ɓaci a duniya Muhammad, wlhy bana son abinda wani zai aibantaka da shi, koda bazan ce komai ba ina jin zafi, matuƙar zafi a cikin zuciyata. Dan ALLAH ina roƙonka idan an sallami yarinyar nan daga asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zan haɗa mata sha-tara ta arziƙi tare da siya mata ticket ɗin jirgi idan ba ƴar cikin garin nan bace ta koma garinsu. Idan kuma a cikin garin nan take da iyayenta nasan zata iya yiwuwa a gidan haya suke ko wani muhalli ƙaskantacce. Zan saya musu gida a ɗaya daga cikin jihohin arewa su koma can, kar su sake waiwayar Lagos har abad….”
Karan farko Maash ya zuba masa idanun kawai yana masa wani irin kallo mai wahalar fassara. Kallon ne ya dinga ratsa Paah sai ya gagara ƙarasa abinda ya faro ya ja bakinsa kawai yayi shiru. Wani irin murmushin ƙasaita da ɓacin rai Maash yayi, sai kuma ya ce, “Ya kayi shiru kuma, ina jinka Paah.”
“Saurarena kawai kake amma ba jina ba Muhammad abar maganar kawai”. Ya faɗa cikin ɗan borin kunya da kame-kame. “Ka kwanta ka huta dare yayi, zuwa safiya sai mu ƙarasa, amma ka daina kira min ƙara aure har ma na mata uku, kai ka sakar min Ummu-Hidaya ɗin ne da kake cireta a matsayin matata”. Ya sake faɗa yana nufar ƙofa cikin ƴar sassarfa ya fice. Tsahon lokaci Maash ya ɗauka yana kallon ƙofar kawai. Sai kuma ya cije lips ɗinsa da masifar ƙarfi zuciyarsa na masa wani irin suya. Yasan mahaifinsa fiye da sanin da kowa ya masa a rayuwa. Amma bazai ce komai ba ALLAH mai ji ne mai gani. Yana kuma roƙonsa ya shiryeshi…
🤥Humm, kai dai Paah ALLAH ya shiryeka dai to gaskiya😏. Yayanmu kayi haƙuri mahaifi mahaifine koda na banza ne😭.
💦✨💦✨💦
Tun wucewarsa daga asibitin abubuwa suka sake cinkushe min kai. Kalamansa sai faman maimaita kansu suke a cikin kaina. Duk da nasha magani zafin zazzaɓin nan yaƙi bari na. Zaune na tashi ina kallon Mama Balki da barci ya ɗan fara figa. Sai kuma na miƙe cikin sanɗa na nufi ƙofar fita.
“Samraah ina zaki je?”.
Muryar Mama Balki a bazata ta daki cikin kunnena. Cak na tsaya tare da runtse idanuna. Sai kuma na juyo a hankali cikin son wayancewa zanyi magana ta dakatar da ni.
“Baki iya ƙarya ba Samraah, kada ki farata yanzu”.
Sosai furucin nata ya dakeni, dan haka na sauke ajiyar zuciya tare da dawowa a hankali na koma saman gadon na zauna. Kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna nace, “Kiyi haƙuri Mama. Ba wani abu zanyi ba. Reception zanje na samo pen da takarda zanyi amfani da su”.
“Amma a daren nan Samraah. Na kula tunda Alhaji ƙarami ya tafi baki da nutsuwa. Bana fatan ace kina son samo takarda da biron ne dan kiyi rubutun da zaki bar masa ki gudu”.
A karo na farko nayi murmushi tare da girgiza mata kaina. “Haba Mama, ai a yanzu wlhy koda shine da kansa yace na tafi gidanmu bazan je ba. Dan insha ALLAHU sai na sauke alkawarin dana ɗauka akan Ummie. Kawai zanyi amfani da sune dan ina son yin lissafi dalla-dalla. Ba kuma zai yiwu a cikin ƙwaƙwalwa ba dole sai da taswira a rubuce”.
Ajiyar zuciya Mama ta sauke. Batare da tambayata abinda zanyin ba ta miƙe. “Shike nan ki zauna ni bari na fita na samo miki. Kin san dai ba’a son ki yawaita motse-motse mai ƙarfi saboda ɗinkin jikinki”.
Bance mata komai ba sai duƙar da kaina dana sake yi. Itama sai ta fice abinta bayan ta zumbula Hijjab ɗin ta……….✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏
……Mintuna basu fi biyar ba kuwa sai gata ta dawo. Cike da farin ciki ta miƙa min takarda da biron tana faɗin “Kinga Alhamdullah na samu ƴar arziƙi a reception ɗin ma. Ina tambaya babu musu ta ciro ta bani har shida, gasu kuma manya nasan dai zasu isheki ai ko?”.
Nima fuskata a washe da murmushi na amsa ina faɗin, “Yauma Mama Nagode sosai. In sha ALLAHU zasuyi harma ƙila suyi yawa.”
File ɗina na ɗauka na ɗaura a samansu tare da gyara pen ɗin. Gaba ɗaya ahalin Maash Mansion na shiga lissafowa a jere. Wanda na manta ina tambayarta. Hatta da adadin masu aiki maza da mata da aikin kowa sai da na rubuta su. Kafin nabi duk manyan gidan na zana halin kowa dana fahimta agaban sunansa. Hatta shi kansa Maash ɗin harda shi. Daga haka nai shiru ina nazari tsahon lokaci, kafin na ɗaga katifar na saka takardar. Toilet na nufa na ɗauro alwala. Duk da yanda nake jin jikina haka na nutsu na kabbara salla domin miƙama UBANGIJINA kukana tare da kai ƙarar wasu mutane garesa dan ya shigemin gaba wajen gano ainahinsu kozan san inda zan kama a wannan tafiyar dana shirya yi….
🌿💞🌿💞🌿
Sosai biki ya kankama a gidan Abba Imamu. Sai dai gaba ɗaya bai zoma Mom a yanda ta shirya shi ba. Dan har yanzu Abba yaƙi maidata ɗakinta. Babu irin haƙurin da bata bashi ba, hakama Ummanta tazo ta saka wanda yake jin kunya amma yaƙi sauraren kowa. Kasancewar tana a cikin gidan har yanzu yasa mutane da yawa basu san abinda ke faruwa ba. Abun zai baku mamaki idan nace muku tunda Halime ta fuskanci abinda ya faru tsakanin Mom da Abban itama ya kasa gane kanta. Kuka ta dinga masa da magiya da roƙon ya maida matarsa, idan ba hakaba itama gaskiya sai dai ya saketa. Ita haka kawai yaja mutane su tsaneta a dinga cewa dan ya aurota ne ya saki uwar ƴaƴansa. Duk yanda ya nuna mata babu ruwanta a ciki taƙi haƙura ta barsa. Kullum cikin masa nagiya take da kuka gashi bata da lafiya sosai. Dan ta kai ma a yau sai da suka je asibiti saboda yanda take amai gaba ɗaya ta galabaita. An tabbatar musu tana da shigar ciki. Zo kuga murna wajen Abba. Yayinda Halime ido yay gwalo-gwalo. Tabbas tana son yara sosai, kodan yanayin rayuwar data gashi ta tsangwama da rashin sakewa. Bata da wani wanda zatace yau ya zame mata amini tunda ƙaninta ya rasu. Ba kunya Abba na dawowa gida ya barbaɗama Auta. Murna da tsalle Auta ya dinga yi da ga ƙarshe ya kwasa da gudu yaje ya barbaɗama Mom dake tare da ƙanwarta da Ummanta da suketa tsare-tsaren biki da za’a fara nan da kwanaki biyu. Neman ɗaukewa numfashin Mom ya yi, har sai da takai hannu ta dafe goshinta dan wani irin sara mata kanta yayi na masifa. Ganin tana neman ɗagama kanta hankali Ummanta da ƙanwarta suka shiga lallashinta da mata nasiha akan tafa kwantar da hankalinta. Wata fitina ko nuna wani abu a yanzu ba nata bane. Ita da ake lallaɓawa ya maidata ɗakinta ya kamata ace ta nutsu, kai kodan bikin nan da za’a tara mutane ta rufama kanta asiri karta bari ƴan uwansa su samu lagonta. Dan yanda bata riƙesu hannu biyu ba sumafa a yanzu dole su ringa nuna mata cewar amarya ta fita a wajensu. Sannan duk hanyar da zasu ƙuntata mata a shirye suke da nemota komai ƙanƙantarta. Shi kansa Abban yanda yake jin kansa on top akan yarinyar nan yanzu idan fa ta cigaba da matsawa sauran igiya biyun ya tsinketa ba abinda zai damesa bane.
Wannan nasiha da ƙanwarta ta mata ne ya sakata kama kanta badan taso ba. A haka aka shiga shagalin bikin Baby. Danginta da ƴan gwarzo sun cika gida tako ina. Tun ranar alhamis aka fara event, dan wasu irin mahaukatan kuɗaɗe mijin Babyn ke kashewa tamkar baisan ciwonsu ba. Duk da kuwa bikin Abba ya dawo dashi baya ne akan yanda aka sanyashi an zaftare har sati biyu a ciki. Ranar juma’a aka kawo lefe na nunama tsara harda key ɗin motar da aka zubo kayan. Wannan bajinta ta ragema Mom raɗaɗin dake damunta a cikin zuciya game da cikin Halime. Ta dinga yanka ƙananun habaici da ɗagawa ma mutanen Gwarzo. Faɗa take yanzu ne akai biki na ƴar gata ba irin na Samraah da har yanzu basu san ina ya dosa ba. Maybe ma Abba da Musaddiq sun saidata ne ko turata karuwanci. Yo inba haka ba wane irin aurene wata kusan takwas basu taɓa sanin miji ba itama bata taɓa zuwa gida ba. Ai dole ne akwai abin ashshar da ake ɓoye wa. Duk da kalamanta sun tada hankulan su Gwaggo Gudidi duk da zuwa yanzu suna waya da Samraah dan hatta su Kawu Musa tana ɗan kira sai suma suka ji kamar basu ƙyautama Samraah ɗin ba. Amma dai sun shanye a fuskokinsu babu wanda ya tanka Mom da haukarta. Washe gari asabar aka ɗaura aure. Abu na farko daya fara bama mutane mamaki shine ango daga shi sai abokansa guda uku yazo wajen ɗaurin auren. Sune suka amsa masa auren a matsayin waliyyay. Kowa yayi zato da tsammanin yanda yake faman ɓarin kuɗi kamar babu gobe sai ƙofar gidan Abba an rasa wajen faka motocin gayyarsa data ango. Amma sai gasu su huɗu a mota ɗaya rak kamar dangin mayu. Jikin Abba shi kansa ya fara sanyi, sai dai bai iya yace komai ba har aka kammala. Zuwa dare maimakon an shirya amarya a miƙata ɗakinta sai akacema Abba wai ai wajen dinner za’aje sai zuwa gobe ango zai ɗauki amaryarsa daga gidansu sai airport zasuje honeymoon ne. Sai bayan sun dawo zai wuce da ita gidanta. Tofa anan ne fa ƙananun magana suka ɗan fara tashi, haka aka shirya tafiya dinner kowa bakinsa da abin faɗa. A wajen dinner an ɗan ga wasu mata a matsayin danginsa. Sai abokansa da suka ɗan zazzo da matansu. Dan ko wajen bada tarihinsa ƙanwarsa ce ta bada. Dinner kam tayi dinner, dan anci kaji ansha lemon roba gwargwadon iko. Ga bag da aka raba cike da kayan rabo a ciki. Amarya baby da ƙawayenta sai feleƙe ake abin nema ya samu. Haka Mom dan tare da ita akaje dinner sai nuna isa ake. Hatta da Umma sai da taje abinta ko kunya. Ƙarfe ɗaya da wani abu na dare aka tashi, su dai ƴan Gwarzo ma tun kusan goma da wani abu suka saka Musaddiq ya dinga fito da su yana sakawa a napep ana maidosu gida dan sun gaji. Lokacin da su Mom suka dawo su tuni sunyi nisa a barci. Ita kam Halime dama bata da wani sakewa a bikin saboda laulayinta mai addaba ne. Koda yaushe tana ɗaki kwance. Da ƙyar take ɗan yin dauriyar fitowa ta gaida ƴan gwarzo. Dan hakama dinner ɗin bataje ba sukai zamansu ita da Abba a gida yana tattalin kayarsa da lallashi itako tana zuba masa taɓara..
Washe gari lahadi da aka tashi da shirin wucewar baby da mijinta shi kuma Musaddiq ya shirya wutowa Lagos. Sunyi waya da mijin Samraah zai je wajenta ya kwana washe gari litinin zai haɗu da wanda zai masa jagorar wucewa ƙasar Chaina kamar yanda MD ɗin sa ya bashi a rubuce. Dan haka ya shiga sallama da ƴan uwa anata koke-koke. Abinka da tsoffi gani suke tafiya Chaina ɗin nan kamar tafiya lahira ne. Dan wasu ma da farko da ca sukai basu yarda Musaddiq ɗin yaje ba. Sai da Abba ya dinga basu haƙuri da nuna musu muhimmanci da cigaban da Musaddiq ɗin ya samu har suna wataran zai shafesu sannan suka haƙura badan sun so ba. Sai dai sunyi farin ciki da jin shi da Hafizzullah zasu je wajen Samraah ne a yau kafin shi ya wuce gobe. Dan rigima da Hafizzullah ya saka masa akan son zuwa shima yaga Samraah ɗin ne yasa shi fidda yan kudaɗensa ya saya masa ticket ɗin jirgi saboda shi ta sama zaibi zuwa Lagos ɗin sai ya saima Hafizzullah ɗin shima zasu wuce tare. Kafin ma mijin Baby ya iso su sun fito, dan motar company ce zata kai Musaddiq ɗin airport. Haka suka wuce ƴan uwa da abokan arziƙi na musu fatan alheri. Tare da saƙon gaisuwa ga Samraah buhu-buhu aunty Zakiyya harda saƙo a cikin kwali datai nannaɗe da su Musaddiq basu sani ba. Hakama Gwaggo Gudidi ta haɗa kayan maƙulashe irinsu tuwon madara, carbin malam, gullisuwa, aya, gyaɗa, riɗi, cike da leda viva tace a kaima ɗiyarta. Wai maybe tanada ciki kunya ta hanata faɗa, ba kuma a raba masu ciki da son kaya kwaɗayi irin waɗan nan. ALLAH sarki Halime itama sai da ta bada zuma mai yawa a gora da uban aya da take saidawa a kaima Samraahn duk da a hoto kawai ta santa. Ta kuma saka Abba dole ya bada naira dubu hamsin a kaima Samraah ɗin. Sosai Musaddiq yayi mamaki bada waɗan nan kuɗi, amma haka kawai sai yaji a ransa aikin aunty amarya ne. Sosai yaji kima da darajar yarinyar na ƙaruwar masa a rai, har sai da ya share ƙwalla. Dan tunda tazo gidan nan abubuwa da yawa suka sauya. Abincinsa, tsaftar ɗakinsa bata ƙyashin shiga ta gyara, komai kuma tana yimasa a mutunce da girmamawa. Yana kiranta aunty tana kiransa Yaya. Da yay magana sai tace ai ita ɗan uwa take kallonsa kuma babban yaya bawai ɗan mijinta ba. A bata da lafiyar nan duk rintsi bata bari ya fita da safe bai karya ba koda ba ranar girkinta bane. Haka tunda Hafizzullah yazo take hidima da shi da jansa a jiki shima kai kace ƙaninta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Duk yanda Hafizzullah keda ƙin sakin jiki da mutane sai gashi dandanan ya saki jiki da ita. Hatta da jakar kayansa yanzu haka a ɗakinta ya bari dan ɗakin Musaddiq ɗin akwai baƙi maza yan gwarzo da basu kai ga wucewa ba………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏
……Lokacin da suka iso airport ɗin su duka sai da ƙwalla ya cika musu idanu. Dan abune da basu taɓa zato ko tsammani ba a rayuwarsu. Sune yau da hawa jirgi daga Kano zuwa Lagos. UBANGIJI al-musawirru mai sassauya al’amura a sanda yaso ga kuma wanda yaso. Da suka shiga jirgin sai Hafizzullah ya rungume yayan nasa yana hawaye. Dole shi ya haɗiye nasa ya dinga lallashinsa. Bayan yayi shiru kuma ya dinga musu video wai dolene ya nunama Aunty Samraah yau sun hau jirgi. Dariya Musaddiq ya dinga masa har ALLAH ya saukesu lafiya garin Lagos. Sunyi mamakin ganin zuƙeƙiyar motar da tazo ɗaukarsu. Amma sai Musaddiq bai kawo komai a ransa ba tuna cewa dafa companyn Maash yake aiki, mai lamba ta ɗaya a Africa, na uku a duniya a matasa. Ai hakan ba komai bane ba. Sunyi da MD dama motar company zata daukesu daga airport ta kaisu duk inda zai je, sannan idan ya kammala gobe idan ALLAH ya kaimu zai kira aje can gidan ƴar uwar tasa a ɗaukesa zuwa wajen GM, daga nan zai wuce kuma….
🩸🩸🩸🩸🩸
Kamar kullum alarm ɗinsa ne ya tashesa. Hannu ya kai idanunsa a rufe ya lalubosa a saman side drawer ya danne wajen kashewar dan shifa ko yaya ƙara take damun rayuwarsa take. Shiyyasa bazaka taɓa ganin wayarsa da ringing ton ba. Kullum cikin vibration phones ɗinsa suke. Hakama television da wahala kiji ya buɗeta caaa tana surutu. Cikin mayen barcin da bai gama isarsa ba ya nufi toilet. Sai da yay wanka kamar yanda abun ke neman zame masa sabo saboda mafarki duk da ba kullum yake tashi a irin yanayin ba sannan ya ɗauro alwala ya fito. A ɗan gurguje ya busar da kansa ya shimfida sallaya yay raka’atainul fijir sannan ya fice masallaci. Ana idar da salla bai yarda sun haɗu da Paah ko Uncle Abdullahi ba ya dawo gidan. Jallabiyarsa ya zare ya ɗauka sports wear ya saka masu kalar blue da rashin white. Sosai kayan sukai masa ƙyau duk da baya sakasu ne domin kwalliya ba. Ya kama gashinsa ya haɗe a tsakkiya tare da ɗauresa da siririn baƙin band. Duk da gudu zai fita sai da ya sakama jikinsa turare ya maƙala bluetooth a kunensa sannan yay zaman saka takalma spots na companyn nike. Yana fitowa falo Laalah dake kwance ya miƙe ya nufosa. Kansa ya shafa cikin lumshe idanu da silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Let’s go my friend”. Cikin kaɗa bindi kuwa ya bisa abin cike da mamaki. Daka gansu kasan karen ya gama samun training na musamman a hannun uban gidan nashi. Gashi fari tass babu alamar wani dattin ƙazanta a tare da shi. Wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka ba kare bane saboda yanda jikinsa ke duguzum da gashi. Yana nufar gate da ɗan gudu Laalah biye da shi ƙafa da ƙafa dan a jere suke tafiya su Sha’aibu dake zaman jiran fitowarsa na take musu baya suka fice yana ɗagama ma’aikatan daketa faman gaishesa hannu. Gudun ya fara tun daga wajen gate ɗin a hankali Laalah a gefensa guards ɗinsa biye da su. Haka suka miƙe street ɗin nan. Sosai sukayi nisa bana wasa ba. Jefi-jefi suna gamuwa da mutane da suma suka fito jogging ɗin. Hannu kawai suke ɗagama juna kowa ya wuce. Sai wasu ƴammata ne da suka dai-daita gudun kusan da shi dan suna a ɗan gabansa kaɗan amma ko kallo basu ishesa ba. Sunyi nisa sosai ya jiƙe sharkaf da zufa har yana ɗiga sannan suka sake juyowa bayan ya kalla agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Suna isowa kwanar da zata sadasu da gida ya tsaya cak. Nuni yayima Shu’aibu daya bashi ruwa cikin sauke numfashi da sauri-sauri. Da sauri ya nufesa tare da ajiye ƴar jakar da abubuwan da zai buƙata ke’a ciki. Kamar su bottle water, towel da abinda ba’a rasa ba. Ruwan ya amsa ya buɗe murfin haɗaɗɗiyar bottle water ɗin ya kai bakinsa. Kansa ya ɗaga sama ya shiga kwararawa. Wani irin kaiwa da komawa maƙoshinsa ya shiga yi, illahirin ƙofifin gashin jikinsa na buɗewa zufa na fitowa da gudu. Sai da ya sha fin rabi sannan ya sauke gorar yana sauke numfarfashi. Laalah ya zubama kaɗan a jiki, shiko yay wani irin matsawa yana girgiza jiki. Yanda yay ɗin ne ya saka Maash ɗin sakin wani ɗan guntun murmushi yana sake kai goran bakinsa ya ɗan kurɓa sannan ya rufe ta ya miƙama Shu’aibu da suma duk suke shan nasu ruwan tare da masa alamar ya bashi towel. Da sauri ya miƙa masa fari tass ɗin towel ɗin hannunsa dake a linke. Sai da ya fara gogo wuyarsa zuwa gashi dake kwance a kumatunsa sannan yay magana batare da ya kalli su Shu’aibu ba.
“Kira Tijjani ya samemu anan da mota”.
Duk da a hankali yay maganar sarai Shu’aibu ya jisan. Sai dai yayi mamakin jin abinda yace ɗin. Amma bashi da hurumin musawa. Sai ma waya daya zaro yay kiran TJ ɗin. Cikin ƙanƙanin lokaci motocin biyu suka iso. Ta farkon aka buɗe masa ya shiga shi da Laalah. Ta bayan guards ɗinsa ne. Sai TJ da Shu’aibu a gaba tunda ba Hayatu. A ɗan ɗarare TJ ya ce, “Sir ina zamu je?”.
Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma can a ƙasan maƙoshi ya furta, “Hospital”.
Da girmamawa TJ ya amsa da, “An gama ranka ya daɗe” yana tada motar. Kansa kawai ya kwantar jikin kujera ya kumshe ido. Har lokacin zufa na faman tsatstsafo masa. Bai ɗago ba har sai da suka isa asibitin. Shu’aibu ya buɗe masa da sauri ya fito. Sai dai banda Laalah shi an barsa a motar. Cikin takun nan nasa ya nufi cikin asibitin Shu’aibu da TJ biye da shi. Tako ina tsirarun ma’aikatan cleaners da ma Nurses da sauransu sai kalonsu suke. Koda suka shiga reception tuni yammatan dake a kan katan sun miƙe bakunansu a washe suna masu Barka da zuwa idanunsu a kansu kamar tsoffin mayu. Ko kallo basu ishesa ba sai su TJ suka amsa musu…
Kuka na gama zabgama mama Balki akan nifa yau ko su sallamen daga asibitin nan kona gudu gida. Dan bazan sake kwana banje naga halin da Ummie ke a ciki ba. Lallashina taitayi akan nayi haƙuri jikina ya ƙara ƙyau tunda doctor tace sai nan da kwana biyu, jikin Ummie kuma da sauƙi sosai. Tirjewa nayi akan nifa sai na tafi. Ganin yanda nake zabga uban kuka yasa Maman cewa shike nan naje nayi wanka idan Alhaji Ƙarami yazo anjima itama zata sake masa magana da kanta. Badan naso ba nabi umarninta. Kamar kullum sai da ta fara taimaka min na shiga ruwan zafi na mintuna goma sha biyar zuwa ashirin da nake yi sau uku a rana. Sannan ta fito akan nayi wankan bara taje ta dawo.
Wankan na ƙarasa batare da tunanin kowa zai iya shigowa ba na fito ɗaure da towel kawai. Dan masu shara tun sanda zan shiga cikin ruwa Mama Balki ke cemin sun shigo aikinsu. Haka dama sukeyi, kullum tunda sassafe zaki gansu, wani lokacin ma ana idar da sallar asuba. Daga nan kuma sai da rana, sai kuma yamma. Fes kuwa na samu ɗakin harda turaren wuta sun kunna. Jikina na goge da ɗan hanzari. Bana son Mama Balki ta shigo ban saka kaya ba duk da nasan ko tazo ɗin tsayawa take bakin ƙofa sai ta tambayi na shirya sannan ta shigo, dan kunyarta nake ji matuƙa. Ƴar jakar kayanmu na buɗe na ciro b&p da zan saka dan ni ina amfani da kayan asibitin ne. Bra ɗin na fara ƙoƙarin sakawa da sauri-sauri, na saka hannu ɗaya ina ƙoƙarin saka ɗayan kawai ya zaro ta baya. Fuska na ɓata kamar zan fasa kuka, abinda dai nake gudun sai ya faru, tunda dole na jira Mama Balki tazo ta maƙala min ko kuma na cire na sake sakawa tazo ta sameni, amma bari muga na gwada dai kozan iya nawa ƙoƙarin. Kicin-kicin maidawa na fara ina famar cizar lips, sai kawai naji saukar lallausan hannu mai bala’in sanyi akan nawa dake riƙe da hannun bra ɗin. Tabbas wannan ba mama Balki bace, dan wani irin mayataccen ƙamshi ne ya shiga ratsa ƙofofin hancina. A birkice na juyo gaba ɗaya na nama manta da wani batun saurin da nakeyi. Saukar idanuna cikin lulu cat ɗin nashi ya sani ja baya jikina har tsuma yake. Shiko ko gezau, sai ma wani irin kallon ƙurilla yake bina da shi idanunsa a shanye. Inda naga ya kafama idanun nima na kalla da sauri, ai da sauri na naɗe hannayena a wajen ina tura baki kamar zan fasa kuka. Kafaɗa ya ɗan ɗage tare da taɓe baki irin shi baiga abin kallo ba, ina ƙoƙarin sake juya masa baya sai kawai ya shiga takowa a hankali. Baya na sake jan jikina yana cigaba da biyoni duk na ruɗe. Jin na dangane da abu yasa na juya da sauri na kalla, sai naga bangone, tashin hankali anzo the end kenan inji bature. Banda zaɓin daya wuce kawai na juya masa baya na kalla bangon. Idanuna a runtse murya na rawa na ce, “Wai da ALLAH minene haka kake yi? Ni dai ka fita kayafa zan saka, sai Mama ta shigo ta ganka”.
Maimakon amsa min ko ya fitan sai kawai naji ya saukar hannunsa akan kafaɗata, da ƙarfi na sake matse idanun nawa jin yanda yake wani irin tafiya da yatsun kamar mai yi da gayya……..✍️
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏
…Hannun bra ɗin ya maƙala min a inda ya zare, a tunanina zai matsa ne sai naji saɓanin hakan. Matsoni ya sake yi ta yanda har nake jin saukar numfashinsa a saman wuyana, sai kuma ya saƙalo hannun nasa ɗaya ta saman cikina. Yanda na sake matsewa a bangon bai hanashi jawoni baya ba a hankali, kansa ya ɗoro a saman kafaɗata tattausan gashin kumatunsa dake da laimar da nake ƙyautata zaton zufa ce tunda sports wear ne a jikinsa na gugar gefen fuskata. Ɗayan hannun ya ɗaura a saman nawa dake rufe da ƙirjina har yanzu zai zame, aiko naƙi yarda na sake ƙanƙamewa.
“Na cire towel ɗin kenan?”.
Soft voice ɗin sa dake fita low sosai cikin maƙoshi ta ratsa kunnuwana. Kaina na girgiza masa alamar a’a idanuna na cika da ƙwala.
“Oya remove your hand kona ciresa tas”.
Nasan zai iya, dan kaɗan daga ƙaramin aikinsa ne. Dan haka na shiga zamesu a hankali hawayen da nake maƙalewa na sake taruwa cikin idanun. Sake matsesu nayi jin yanda yake jan towel ɗin a hankali, har ya gama sauke b ɗin kan jikina babu kunya babu tsoron ALLAH ya gyarata ta zauna da ƙyau sannan ya maida min towel ɗin a sama.
“I love white musamman yanda wannan ta miki ƙyau”. Ya faɗa cikin kunnena cikin raɗa.
Da sauri na toshe kunnena tare da ture masa kai dan bana ma son ji. Maimakon ya barni kamar yanda naso sai ma ya sake nanne ni da jikinsa tare da sumbatar wuyana da hannun dana toshe kunnen. Ni kaɗai nasan kalar masifaffiyar kunyar da nake a ciki da mamakin tasa rashin kunyar dan shi komai yana yinsa ne kansa tsaye. Mun kai tsahon mintuna biyu a haka sannan ya janye jikinsa a nawa tare da kama hannuna. Ban buɗe idanuna ba, sai alamar zaunar dani da naji yayi a bakin gado. Jin kamar ya jawo kujera ya zauna gab dani dan har ƙafafunmu na a cikin na juna ne ya sani buɗe idanuna dake mar-mar. Kamar yanda nayi hasashen hakanne kuwa. Ya jawo kujera gab da ni ya zauna hannunsa ɗauke da rigar asibitin da aka ajiye min a saman gadon. Idanunsa kan p ɗin dana ajiye. A zabure na kai hannu na ɗauke ina ɓata fuska kamar zan yi kuka na cikukuyesa a hannuna na tura ƙarƙashin cinyata. Mayatattun idanunsa ya zuba min tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Hand”.
Bani da zaɓin daya wuce miƙa masan kawai, dan nasan ko cewa nayi bana so bazai barni ba. Inaji ina gani ya saka min rigar sannan ya miƙar dani a gabansa kamar wata ƴar yarinya ya zare towel ɗin ya ajiye gefe. Hannu ya miƙa min wai na bashi p ɗin dana sake saurin ɗaukewa. Kafaɗa na maƙe masa ina juyar da kaina gefe. shima sai ya taɓe nasa bakin kawai. Turaren dana ajiye gefe ya ɗauka ya ɗan duba jikinsa, sai kuma ya ɗan sake taɓe baki kaɗan, batare da yace komai ba ya ɗan fesa min ya maida ya ajiye. Ni dai uffan bance masa ba, kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna. So nake na tambayesa yaya Ummie amma duk ya dabaibaye ni da salon da ban taɓa zaton gani daga garesa ba. Gashi duk abin nan da yake fuskar nan na’a tsukenta kamar bashi keyi ba. Da ƙyar na iya dauriyar faɗin, “Ina kwana? Yaya jikin Ummie?”.
Jin shiru bai amsa ba ya sa na ɗago idanu na a hankali kamar wata matsoraciya. Kamar yanda nayi zato shima nasan a kaina suke, dan haka da gudu nai yunƙurin kauda nawa amma sai ya riƙo haɓata da yatsunsa biyu.
“Ina miki aiki bazama kince kin gode ba”.
Baki na tura masa. Cike da ƴar jarumtar dana tattaro a tsiwace nace, “To ni dai ai bance ina so ba”.
Maimakon ya bani amsa sai naga ya saki wani shegen murmushi. Cike da suɓutar baki da mamaki na ce, “Lah yau ma kayi murmushi”.
Janye hannunsa yayi, tare da tsuke fuskar. Ni sai ma abin ya bani dariya. Sai kace wani ɗan yaro. Dariya nayi ina ƙoƙarin kare bakina na ce, “Ikon ALLAH, to kai baka so ace kayi murmushin ne? Sai kace wani abun mugun abu. ALLAH idan ma kayi murmushin kafi ƙyau. Amma kullum fuska a ɗaure kamar wani ma’aikin mutuwa.” na ƙare maganar ina haurawa saman gadon gaba ɗaya tamkar banga irin kallon da yake faman bina da shi ba. Sai da naja bargon na rufe ƙafafuna sannan na kuma marairaice fuska. A hankali na ce, “Yaya Awwab!”. Shiru yaƙi amsa min, sake maimaita kiran sunan nashi nayi a shagwaɓe. “Yaya Please answer me”.
Nan ɗin ma kamar bazai amsa ba. Na sake ƙoƙarin yin maganar cikin harara ya katseni da faɗin, “Ba kunni ke ji ba ne”.
Baki na tura sosai. Na ce, “To ai dai ba daɗi mutum yayi magana aƙi amsa masa.”
Banza yay min bai tanka ba. Nima sai na cigaba da faɗin, “Dan ALLAH ka taimaka a sallaman yau a asibitin nan. Idan ba hakaba ALLAH zan gudo gida. Ina missing ɗin Ummie sosai. Ni wlhy na warke fa”.
“Na gani”.
Ya faɗa kamar bashi ba yana ƙoƙarin yaye bargon dana rufama ƙafafun nawa. Da sauri na waro idanuna ina riƙe hannunsa. Kaji mun mutum to mizai gani?. Shanyayun idanunsa ya ɗago ya zuba min, ni kuma na marairaice fuska har idanuna na tara ƙwalla. Hannun ya janye kawai batare da yace min komai ba. Nima sai na sauke ajiyar zuciya dan al’amarin wannan mutumin yasha kan nawa ƙaramin tunanin gaskiya. Sake matsar da kujerar da yake zaune yayi gaban side drawer. Batare da yace komai ba ya shiga ƙoƙarin haɗa tea dan akwai babban basket mai murfi dake cike da kayan shayi kala-kala da su chocolate da kullum Hayatu baya gajiya da sayowa. Yo ni Hayatu ai zance tunda dai shine ke zuwa da su. Banda jiya da bai zo ba ɗayan yaron nan nasa da har yanzu ban san sunansa ba ya kawo snacks. Tea ɗin ya haɗa a zatona shine zai sha, har na fara gulmarsa a zuciyata sai naga ya miƙa min mug ɗin. Tsayawa nayi kawai ina binsa da kallon mamaki, dan haka muka ƙurama juna ido. Kusan minti ɗaya muna a haka kafin ya janye nasa da suke juyewa golden ƙwayar tsakkiya na zama siririya a wani irin salon yuuu ya ɗan lunshe su. Nima nawan na ɗauke da sauri ina haɗiyar wani yawu mai kauri dan gaba ɗaya jinai maƙogwarona ma ya bushe. Kofin ya ƙara miƙamin kansa a gefe, sai kuma ya miƙe.
Haka kawai kallon nima yay matuƙar min tasiri a cikin jiki da ma jinina, dan haka na gagara sake kallon inda yake har ya buɗe ƙofar ya fita. Ajiyar zuciya mai nauyi na sauke tare da rumtse idanuna na cije lips da ƙarfi. Tea ɗin na cigaba da sha da ɗan zafi-zafi batare dana san abinda nake ba. A haka aka sake buɗe ƙofar, a zatona shine dan haka na gagara ɗaga ido na kalli wajen. Sai da mama Balki ta rangaɗa sallama sannan na ɗago da sauri fahimtar itace.
Inda nake ta ƙaraso cike da tsokana take faɗin, “A lallai ɗiyata ta fara samuwa. Yau kece da haɗa shayi da kanki batare dana sha fama ba kina bata fuska da korafin bakinki ba bu ɗanɗano. To UBANGIJI ya ƙara sauƙi.”
A hankali nace Amin, dan a zatona bata haɗu da wannan pepper ɗin mutumin ba, sai naji hakan yamun daɗi. Sai dai me, bayan kamar mintuna biyar da zaman Mama Balki sai gashi ya sake dawowa tare da doctor. Miƙewa Mama Balki tayi fuskarta ɗauke da murmushi tana faɗin, “Har an kammala Alhaji ƙarami?”.
Cikin girmamawa, muryansa can ƙasa ya ce, “Eh mama sai ku shirya”. Jin abinda ya faɗa ɗin ya sani ɗagowa da sauri na kallesa. Sai muka haɗa ido. Da gudu na janye nawa na maida kan doctor dake min magana ɗan ji nake kamar ma kowa zai gane abinda ya faru tsakaninmu yanzu. Tambayoyi tamun tare da bani shawarwarin yanda zan kula da jikina yanda ya kamata har komai ya ƙarasa dai-daita. Duk bayan kwanaki biyu kuma zata zo har gida koni nazo asibitin za’a dinga sake dubani. Dan ba yau suka so sallamata ba. Sake ɗagowa nayi da mamaki sashen da yake. Yana tsayen dai har yanzu sai Mama Balki ce ke fita da kayayyakin mu tana dawowa alamar a iya ƙofa ake amsarsu. Yanda ya maida hankalinsa akan wayar hannunsa sai naji nutsuwa da alama baya jin duk abinda doctor ɗin ke faɗa. Taimaka min doctor tayi na sakko a saman gadon, hannunta riƙe da nawa ta ce, “Muje ki ɗan tattaka ƙyaji daɗin ƙafafunki tunda kwana da kwanaki kina zaune waje ɗaya babu ko babban motsi. Kaina kawai na jinjina mata, ta ɗauki hijjab da Mama Balki ta ajiye sabo ta saka min da kanta. Har ƙasa hijjab ɗin ya kaimin kamar wanda nake amfani da su a gida. Sai naji daɗi sosai dan yaushe rabo. Ta gabansa mukazo muka gitta bai kallemu ba bai kuma motsa ba har sai da muka fice gaba sannan. Kusan ƴammatan Nurses ɗin nan da suka dinga kulawa dani dasu aka ɗunguma min rakkiya har gaban mota. Sosai motar tai min ƙyau, banyi tunanin yana bayanmu ba, sai da muka iso ina sallama da Nurses ɗin da doctor naga an buɗe masa ya shiga, ba’a rufe ƙofar ba alamar ni ake jira. Ji nai kamar na fasa kuka, dan hakan na nufin a kusa da shi zan zauna kenan. Babu yanda zanyi, dan doctor da kanta ta taimaka min na shiga. Sai da aka maida ƙofar aka rufe har Mama Balki itama ta shiga gaba an ma tada motar muna shirin barin asibitin sannan na lura da shegen karen nan nasa dake tacan jikin waccan ƙofar. Wani irin fasa ƙara nayi tare da daka tsalle na faɗa jikinsa a matuƙar firgice, bazaki gane yanda nake masifar tsoron kare ba wlhy Bily………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏
……Da uban sauri TJ ya taka birki dan shima firgita yayi, hakama Mama Balki, ya juyo zaiyi magana da sauri ya kauda kansa dan gaba ɗaya Samraah ta koma saman jikin ogan nasa ne. Mama Balki ma kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta tana Murmushi. Shiko gogan tun faɗa masa jiki da tayi idanunsa kawai ya lumshe saboda ƙarar da tai har cikin tsakkiyar brain ɗinsa ya jita. Shi mutum ne da sam baya son hayaniya. Taɓasan da Laalah ya ɗan yi yana gurnani ya sa ya fahimci abinda take ma tsoro. Lumsassun idanunsa ya buɗe, ya ɗan kalli Laalah ɗin sai kuma ya kalleta. Tayi masifar cikuykuye sa daga ita har ƙatoton hujjab ɗinta. Shi sai abinma ya so bashi dariya. Amma sai ya danne baiyi ba.
Cikin silent voice ɗin nan tasa yay kiran sunan TJ. Amsa masa yay da girmamawa, sai kuma ya buɗe motar ya fita. Kasancewar glass ɗin ta inda Laalah yake an saukesa ya sa ya ɗan duƙo ta wajen sai dai kansa a ƙasa ba kallonsu yake ba. Maimakon amsa masa sai ya ɗan shafa kan Laalah ɗin tare da furta, “Maidashi wajen su Shu’aibu”. Kaɗa bindi Laalah yay alamar dai yaji ubangidan nasa. Tj na buɗewa ya dira da kansa.
Duk abinda suke ina jinsu. Ina jin ya fita na sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da zame jikina daga kan nasa. Ban yarda na kallesa ba na koma can jikin ƙofa na lafe. Ban kuma sake yarda na ɗago ba har muka iso gida. Sosai naji wani irin farin ciki da zaƙuwar ganin naje ga Ummie, dan bazan ɓoye miki ba har cikin tsakkiyar rai nake jin ƙaunar baiwar ALLAHr nan wlhy bily. Ƙagara nayi motar ta tsaya, amma sai bata tsayan ba sai da akaje har ƙofar sashensa. Muna fitowa ina zumuɗin tafiya na koma waccan ƙofar Mama Balki ta dakatar da ni, magana na ɗago zanyi ta dakatar dani, tare da jan hannuna muka shige sashen nasa dan shi tuni yama shige abinsa. Mamaki ne ya kamani, yanzu kam kasa haƙuri nayi sai da nai magana kamar zanyi kuka.
“Mama mi kuma zamuyi anan? Dan ALLAH mu tafi sashenmu ko wajen Ummie”.
Kanta tsaye ta ce, “Banda ikon yanke wannan hukuncin Samraah. Sai dai mu jira daga bakin Alhaji ƙarami”.
Sosai mamaki ya ƙara kamani, zan sake magana ta kama hannuna tai ciki dani. Zaune muka samesa a falo TJ na ajiye masa kofin coffee daketa tururi alamar yanzu nan ya haɗo masa shi. Tj ne ya amsa sallamar tamu, amma shi ko kallon ta inda muke ma baiyi ba. Wajen zama Mama Bilki ta nuna min, ban musa mata ba na zauna fuskata a kumbure. Kobi takaina batayi ba ta juya ta fita. A zatona wani abu zata ɗakko ta dawo, sai naji shiru har tsawon wasu mintuna. Ga TJ shima ya fice da ga ni sai shi. Karo na farko cike da ƙosawa na ɗaga kai na kallesa. Coffee ɗin sa yake sha hankali kwance tamkar ma bai san da zamana a wajen ba. Jinai raina ya sake ɓaci, amma sai na danne murya a sanyaye na ce, “Dan ALLAH zanje wajen Ummie na ganta”.
Kamar bai jini ba, sai da ya mula dan kansa sannan ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla ta inda nake. Dai-dai na ɗan hararesa ni kuma batare da tunanin zai ɗago ɗin ba.
“Oh hararata ma kike?”.
Ya faɗa fuska a dake. Da sauri na marairaice fuskata kamar bani ba, cikin kalar tausayi na ce, “No ALLAH ba haka bane. Kawai an samu kuskure ne ni yazan harareka”. Na ƙare maganar a matuƙar karyar da kai. Ɗauke idanun nasa yay cike da basarwa ya cigaba da shan coffee ɗinsa. Naji tamkar na fasa ihu kona kamashi da duka. Amma duk babu dama. Sai kawai na dake tunda na fahimci ƴan wulaƙancin ne a kansa….
🌜💮🌛
Kamar kullum tsaff ta fito cikin gayunta. Arwa ce riƙe da handbag ɗinta tana mata shagwaɓar ta bata kuɗi. Itako sai faman latsa waya take tana tafiya kamar ma bata jin ɗiyar tata. Sai da suka gama sakkowa da ga upstairs ɗin sannan ta miƙa mata hannu alamar ta bata handbag ɗin. Sake marairaicewa Arwa tayi da maida hannunta baya ta ɓoye jakar. “ALLAH Ummy ni bazan baki ba, just 200k fa nake so bawani kuɗi masu yawa ba. Gift da zan sayama Lubnah yau birthday ɗinta. Kuma motana fa nace miki duk friend ɗina sun sanni da shi, dan ALLAH ki bani baƙin naki, ALLAH bazanyi tuƙin banza ba i promise ”.
“Riƙe promise ɗinki. Dan bazan baki motana ba. Ga dai 100k nan na saka miki je kiyi manage da shi banda kuɗi yau. Give me my bag jare. Kuma ki tabbatar kin dawo gidan nan kafin ten na dare. Dan karna shigo ban sameki ba. Zan ɓata miki rai”.
Baki cike da iska Arwa ta miƙa mata handbag ɗin, babu ko godiya ta juya fuuuu ta koma sama. Kai kawai Hajiya ƙarama ta girgiza ta juya tai tafiyarta. Babu kowa a falon sai su A’i dake gyarawa. Gaisheta sukeyi cike da girmamawa. Itako tana amsa musu a nutsen nan nata babu alamar hayaniya a tattare da ita. Daka ganta kaga mace mai haƙuri da iya zama da mutane. Compaund ta fita, kai tsaye tai wajen motarta dan ita sam bata da driver. Bata yarda da kowa ba ita ke tuƙa kanta, tana ƙoƙarin ajiye handbag ɗinta a side ɗin mai zaman banza dai-dai nan Hajiya Mammah ke fitowa itama cikin wani shegen shiga na manyan mata dake ji da kansu. Kallon juna sukai, amma sai Hajiya Mammah ta watsar da Hajiya ƙaramar tamkar bata ganta ba ma. Lips Hajiya ƙarama ta cije tare da faɗin, (zanyi maganinki ne) a zuciyarta. A zahiri kam sai ta saki murmushi tare da nufar Hajiya Mammah ɗin cikin girmamawa ta gaisheta. A ɗage Hajiya Mammah ta amsa tana ƙoƙarin shigewa motar da drivern ta ya buɗe mata. Itama sai Hajiya ƙaramar tai murmushi ta juya ga tata motar ta shiga. Kusan a tare suka fice a gidan. Sai dai suna fitowa babban titi kowa yay hanyarsa. Ita Hajiya Mammah gidan Baba prof ta nufa, itako Hajiya ƙarama asibiti ta nufa…
⭐⭐⭐
Gidane babba mai ƙyau kuma sosai. Ga masu aiki tako ina nakai kawo maza kai kace akwai wasu mutane da yawa a ciki. Guri drivern Hajiya Mammah ya samu yayi parking, sannan ya fito cikin rawar jiki ya buɗe mata, sai faman cika take da batsewa wa ma’aikatan dake ta faman gaisheta da girmamawa. Ko sau ɗaya bata amsa musu ba, sai ma tana fitowar tuni wani yazo ya amshi handbag ɗin hannunta dan sun san halinta sarai. A yatsine take bin jibga-jibgan motoci ukun dake fake a compaund ɗin wanda bata san da su ba a gidan da kallo. Cike da isa ta dubi wanda ya amsa mata bag ɗin ta ce, “Waɗan nan motocin fa?”.
Muryarsa har rawa take wajen bata amsa da, “Na baƙine da Alhaji yayi ranki ya daɗe”.
“Baƙi?”.
Ta maimaita da sigar tambaya, sai dai kuma kafin ya bata amsa tayi gaba bakinta a taɓe. Bayanta yabi da sauri. Kanta tsaye ta shiga ta main perlor ɗin gidan ta shiga ainahin falonsu. Babu kowa a ciki, sai ƙamshin air fresheners dake tashi da kuma ɗan sanyin ac kamar ba safiya ba. Baba kam akwai son tsafta. Duk da rayuwarsa yake shi kaɗai a gidan babu mace zaka samu komai tsaf-tsaf. Dan tunda mahaifiyarsu ta rasu bai sake aure ba. Suma kuma ko yace zai yi ɗin bazasu bariba wlhy. Dan yanda ba’ama uwarsu kishiya tana raye ba bayan ta mutu ma baza’ai mata ba. Zaune takai saman luntsuma-luntsuman kujerun falon. Tuni ta wani lume a ciki dan sunada bala’in taushi. Baban nasu ɗan gata ne, dan duk shekara sai Awwab ya canja komai na gidan an sake masa sabon fenti. Kukun gidan daya fito ne yana gaidata ya katse mata tunani, a ɗage shima ta amsa masa fuska a yamutse. Har zai juya ta dakatar da shi, umarnin haɗa mata breakfast ta bayar. Cike da girmamawa ya amsa mata yana komawa ciki. Babu jimawa kuwa ya kammala komai ya kawo ya ajiye gabanta. Zama ta gyara da ƙyau ta fara kwasar girki tana chart da Rubayya dake ƙara tsara mata yanda zata tunkari Baban. A haka Baba prof ya shigo falon ya sameta. Kanta dake duƙe ta ɗago ta kallesa, yana sanye cikin farar jallabiya tas data ƙara fiddo tsufarsa. Dan bashi da wani jikin kirki, gashi dogo masha ALLAH kamar dai su Paah dan duk shi suka biyo har su Maash duk tsahonsa ne. Kanta ta ɗan rissinar tare da faɗin, “Barka da fitowa Baba”.
“Yauwa Nafisatu kece a gidan?”.
Ya faɗa yana kaiwa zaune. Murmushi tayi, tare da sake rissinawa ta shiga gaishesa. Da kulawa ya amsa mata yana tambayarta mutanen gidan da jikin Ummie. Cikin ɗan ɗage kafaɗa ta ce, “Da sauƙi to Baba. But ba shiga nake ba dan tun dai randa ta faɗin nan gaskiya”.
Fuskarsa a ɗan ɗaure yace, “Ban gane ba?”.
Fahimtar katoɓarar da tayi yasa ta ɗan ƙaryar da kai gefe. “Baba ba wani abu nake nufi ba fa. Wlhy ina jin tsoro ne shiyyasa. Kasan idan Ummu-Hidaya na’a wannan yanayin akwai haɗari shiga inda takene. Amma nasan da sauƙi gaskiya, tunda kaga ba’ai kiranka ba”.
Kansa ya jinjina cikin nuna gamsuwa. Ita kuma ta sauke numfashi. Sai kuma tayi murmushi da sake ɗan dubansa. “Baba wai motocin suwaye na gani haka a gidan nan?”.
Hannunsa ya ɗan yarfar da taɓe baki, sai kuma ya ɗauka black tea ɗin da kuku ya kawo masa ya fara kurɓa, sai da yay kusan sau uku kafin ya kalleta. “Shugaban jam’iyyar ACC ne na ƙasa da wasu ministoci guda biyu. Suna damuna a kwanakin nan akan son na shiga siyasa. Ni kuma abinda bai taɓa birgeniba kenan Nafisatu. Yanzu ma shugaban ƙasa ne da kansa ya turosu. Ni dai na faɗa musu gaskiya ina akan bakana. Amma sun dage matuƙa. Shine nace suje zanyi shawara”.
Cike da zumuɗi da zamala Hajiya Mammah ta gyara zamanta. Gaba ɗaya 32teeth ɗinta washe suke. “Amma Baba mizai hana ka amshi tayinsu. Ni banga wani aibu ba a siyasa ai. Sannan kowane irin sharuɗɗa ka cikasu da ko ɗar bazakaji na shiga ba. Tayinfa kujera suke maka mai matsayin farko a jihar nan. Zamu kasance cikin matuƙar farin ciki a kiramu first family na wannan state mai girma irin Lagos. Baba dan ALLAH ka amsa”. Ta ƙare faɗa cikin shagwaɓa. Ajiyar numfashi ya sauke tare da gyara zamansa………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏
…….Tsahon lokaci muna zaune shiru batare da ya sake magana ba. Coffee ɗinsa kawai yake sha a hankali yana kuma daƙilar tab da ke a saman ƙafarsa da yay crossing.
“Wane hukunci kika yanke?”.
Tambayarsa ta iso cikin kunnena a bazata. Ɗan ɗagowa nayi na kalla inda yake, dan da farko ma banyi zaton shine yay maganar ba. Yanzu ɗin ma daƙilar tab ɗin kawai yake, dan haka na ce, “Wai kaine kayi tambaya?”.
Ɗago manyan idanunsa yayi a hankali ya kalleni. Sai kuma ya sake maidasu kan abinda yake yi. A taƙaice ya ce, “Uhmm”.
Ajiyar zuciya na sauke da faɗin, “Okay. Amma ban gane tambayar ba. Akan mi kake nufi?”.
“Komai!”.
Ya faɗa can ƙashan maƙoshi. Jimmm kawai nayi ina tunani bayan na sake maimaita komai ɗin a zuciyata. Kai gaskiya ban gane ba, dan duk da ina zargin ahalinsa ai nake ga bai dace na fito fili na nuna ba, tunda ba sanin nasan tarihin gidansu yay ba. Gara idan shine ya sanar min wani abu ai. Fuska na marairaice a sanyaye na ce, “ALLAH kuwa Ya Awwab ban gane ba”.
Komai baice min ba. Yanzu ma ko ɗagowa ya kalleni ɗin baiyi ba. Kusan mintuna biyu ya ajiye kofin coffee ɗin da yake sha sai kuma ya gyara zamansa. Da hannu yay min alamar nazo. Idanu na waro masa alamar mamaki, amma sai ya ɗauke kansa cike da basarwa yana sake tsuke fuska. Banda zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan sam bazan iya musa masa ba. Ina jinsa da wani irin girma da kima fiye da ko yaushe a yanzu. Sannan wani irin shakkarsa nake ji, kwarjinin sa gaba ɗaya ya cika falon har ina jin yama mana kaɗan. A hankali na miƙe kamar wadda tai laifi take tsoron duka. Dan da sanɗa na isa gabansa. Ƙoƙarin kaiwa ƙasan carpet nake ya min nuni da saman cinyarsa. Kaina na maƙe masa alamar a’a, sai ya ɗan taɓe baki ya nuna gefensa batare da yayi magana ba. Dole na canja na koma kan kujerar gefensa dai na zauna. Sai kuma na ɗan saci kallonsa ta gefen ido. Da sauri na maida kaina ƙasa dan dai-dai shima yana ɗagowa ne. Wani irin ratsawa muryarsa ta sake min har cikin kaina, duk da kuwa yayi maganar ne ba cikin tsawa ko hayaniya ba, dan ko a falon kake ba lallai ka jisa ba dan nima na kasance gab da shine. Amma ban sani ba, kodan sai da ya kamo yatsun hannuna cikin nashi tattausan hannun ne sannan yay magana oho. Sake matsa yatsun nawa yay a hankali ina kuma jin kaifin idanunsa har cikin jijiyoyin da jinina ke yawo.
“Idan nace komai ina nufin ina nufin komai da komai. Nasan zuwa yanzu kin san wanene Awwab a zahirance da baɗinance. Dan kinji komai a wajen Mama, kin kuma san komai a makwancinsa”.
Da sauri na ɗago ina ware idanuna duk da zancensa na ƙarshe ya bani kunya. Cikin ɗan rawar lips da nuna mamaki na ƙarara akan fuska na ce, “Ya akai ka sani mama ta faɗa min?”.
Wani ɗan makirin murmushi ya sakar min da lumshe idanunsa sai kuma ya buɗesu luuuu ya zuba su a cikin nawa. Ƙyaƙyƙyafta idanu na fara da ƙoƙarin janye yatsuna dake a cikin nasa har yanzu. Amma sai ya hana hakan ta hanyar sake riƙesu da ƙyau yana girgiza min kansa. Sai kuma ya janye idanun kamar a kasalance ya ɗaura yatsarsa manuniya mai ɗauke da dogon farce fari tass har wani ƙyalli yake tsabar yanda yake fes, akan zobena ya saka yatsan yana wani zagayawa. Zoben na kalla da sauri nima dan sam ban gane inda ya dosa ba. Sai da ya gama zagayesa sannan ya zaresa a hankali daga cikin yatsata. Ɗan jujjuya min shi yay akan fuska, sai kuma ya runtsesa a cikin hannunsa yana kallona gira ɗaya a ɗage.
“Ke yarinya ne Samrh, tsiwanne kawai yayi miki yawa da shegen kauɗi. Shin bakiyi tunanin taya akai kika zo gidan nan ba haka kai tsaye bayan kin gudu min? Nasan hakan zai iya faruwa, amma dai abune da zai zama mai wahalar gaske musamman idan mukai duba da hannun da kika faɗa….”
Kasa haƙuri nayi, cikin tare numfashinsa na furta, “Dama da saninka nazo nan gidan ke nan?”.
Idanu ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kaina. A bazata naji saukar hannunsa kan hancina. Ya ɗan jashi kaɗan da faɗin, “Yanda kike stubborn ɗin nan ai sai da kula. In ba hakaba zaki ɓaro min aiki ne ƴar jarida”.
Duk da naji kunya sai da na ɗan tura masa baki. A shagwaɓe na ce, “Ai ALLAH kaine stubborn a gidan nan. Ni dama nata wasi-wasi, duk da nasan kaɗan daga ikon UBANGIJI hakan ta kasance. Amma dan ALLAH Ya Awwab ya akayi nazo?”.
Shiru yayi kamar bazai tanka min ba. Sai da na marairaice masa kamar zanyi kuka sannan. Yana a kwancensa jikin kujera idanunsa a lumshe yanzu. Hakan ya bani damar zuba masa idanuna ina kallon yanda yake motsa lips kamar abin dole. “Tun a guduwan farko nasan zaki iya maimaitawa. Shiyyasa na samar da zoben nan exactly irin naki ta yanda zan san duk wani motsinki. Kina asibiti a Abuja na sa miki, bayan dinga nuna kin inda kike har magana idan akayi ko kikayi zan iya jinki”. Ya ƙare maganar yana nuna min abinda ke a kunnensa kamar bluetooth sai dai shi ƙarami ne bai kai bluetooth girma ba
Cikin ɗan yarfar da hannu da mamaki na ce, “Bala’i, dama kaje asibiti ka duba ni ne? Wlhy naci kai. Taya ban taɓa ma lura da zoben nan ba nawa bane?”.
Idanu ya ɗan buɗe yana kallona. Kamar bazai ce dani komai ba sai kuma ya motsa small pinkish lips ɗinsa a hankali. “Saboda ke yarinya ce”.
Jinai kamar na harararesa amma bazan iya ba. Sai wani cemin yarinya yake. Amma duk da haka sai da na ɓata fuska. Hannu na miƙa masa na ce, “Bani zoben na gani dan ALLAH”.
Idanunsa ya maida ya lumshe. A taƙaice ya furta, “Ya gama aikinsa. Ina jinki mi kika yanke dan bani da lokaci zanyi baƙi”.
“Ni ban yanke komai ba, akan samun lafiyar Ummie kawai nake da plans”.
Idanu ya buɗe sosai yana kallona. Sai na ɗauke nawa daga kallonsa dan bazan iya jurewa ba. A hankali kamar mai jin tsoro na furta, “Ya kamata Fahad ya dawo gida kamar yanda kowa yake gida”.
“Nooo!!”.
Ya faɗa a tsawace yana ƙoƙarin miƙewa. Duk da yanda ƙirjina ya buga da rawar da jikina yake yi sai da nai saurin kamo hannunsa. Muryata a karye kamar zanyi kuka na ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka zauna. Bafa kaji ƙarshen maganata ba Please”.
Ƙin zaman yay har tsawon lokaci. Sai faman huci ma yake yi abin mamaki da tsoro. Hatta da gashin jikinsa duk sun mimmiƙe. Muryata na rawa cike da magiya na sake faɗin, “Dan ALLAH dan ALLAH. Burinka fa shine samun lafiyar Ummie, kuma wannan hanyar da zan faɗa maka in sha ALLAHU ina fatan zata taimaka mana. Kayi haƙuri ka danne duk abinda kake ji game da ɗan uwanka. Dan wlhy komai bazai yiyu ba sai mun haɗa ƙarfi da ƙarfe. Ni, kai, shi, Hayatu, Mama, Baba, da duk wanda ka aminta da shi a cikin yaranka. Idan har wanda baka haɗa komai da su a duniya ba zasu ci arziƙinka yanda suke so har su bama ƴan uwansu kai mi kake jira akan naka gudan jinin ɗaya tilo. Kana ganin idan lafiyar Ummie ƙalau zata barku a cikin wannan halin? Ko a yanzu da take a cikin halin jarabawa wlhy maybe tana jin zafi da kewar rashin ganin ɗan uwanka dan bata san taya zata furta bane kawai. Karfa ka manta shima nan gidansu ne Ya Awwab. Yanda kake da iko da komai na cikinsa shima haka yake da iko da shi dan ko’a addinance matsayin magada masu kaso kai ɗaya kuke amsawa. Duk duniya fa baka da kamarsa, kamar yanda shima baida kamar ka. Duk mu ɗin nan da muke zagaye da kai son zuciya ko wani dalili zai iya sakawa mu gujeka, amma shi komi ka zama bazai daina jin ƙaunarka a zuciyarsa kamar yanda kaima nasan kana ƙaunarsa. Wannan ƙiyayyar dake tsakaninku ƙirƙirarriyar ƙiyayya ce, kune kuma ya kamata kuyi yaƙi da zukatanku wajen ganin kun canjama abokan gaba nasararsu. Kaifa ka tunatar dani ba’aima maƙiyi gaggawa, idan ba haka ba zai rigaka kai inda kake hari harma ya juyo kai baka kai ba. To kenan in har zaka tafin sai ka kasance mai kula gudun kar ya saka maka tarkon da zai riƙeka ya hanaka isar kafin shi ɗin ya iskoka kuma. Dawowar Fahad gidan nan shine first target ɗin mu akan kowa da komai wlhy. Amma na baka dama kaje kayi tunani ka gani, sannan ka nema zaɓin ALLAH. Ni kuma na maka alƙawarin duk abinda ka yanke zanyi biyayya a kansa sai muje plan na gaba, ni dai fatana kawai Ummie ta samu lafiya ne”. Daga haka na saki masa hannu a hankali. Kaina na duƙar na saki kuka. Dan harga ALLAH yanzu wani masifar tausayi yake bani. Bawan ALLAHn nan yana cikin wani irin bahagon ƙulli ne mai tsaurin gaske. Shiyyasa aketa amfani da shi ana azabtar da mahaifiyarsa da ɗan uwansa. Nayi zaton tafiyar tasa zaiyi, sai naga a hankali ya koma ya zauna cikin kujerar tare da dafe kansa da duka hannayensa yay masifar cije ɗan ƙaramin lips ɗinsa kamar zai hudashi da haƙori. Ha jima a haka kafin ya ringa sauke wasu irin zafafan huci da naji ƙarin tsoronsa a raina. Dan tuni na maƙure a cikin kujera kamar mage taga ƙare a lungun mai hanya ɗaya tal………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏
…….Mun jima zaune a hakan kafin ya mike a fusace. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, batare da ya juyoba cikin kaushin murya ya furta, “Daga yau zaki cigaba da zama anan”.
Wani irin zabura nayi yan hanjin cikina na wantsalawa tare da bugun zuciyata. Bamma san sanda na furta, “Anan kuma?”. Ko kallon inda nake baiyi ba yayi wucewarsa hanyar bedroom ɗinsa. Wani irin bugawa zuciyata keyi diff-difff!! Dan har ga ALLAH maganar tashi tayi masifar ratsa min ƙashi da bargo. Wane irin neman bala’ine haka dan ALLAH. Taya zan cigaba da zama a side ɗinsa bayan Mama Balki ta sanar min babu wanda yasan akwai aure tsakanina da shi. Sannan yan uwansa ma abinda ya faru kallonsa suke ama tsayin fyaɗe. “Na shiga uku ni Samraah mutumin nan zai kasheni. Ni wlhy koma ba duk wancan ba bazan iya zaman anan da shi mu biyu kacal ba. Mutumin daya nema kusan kasheni ina gaskiya bashi yiwuwa. Gara ma tun kan wankin hula ya kaini dare na kama gabana. Inama laifin yace na koma sashen Ummie dan ALLAH. Zaram na miƙe, har haɗawa nake da sassarfa na nufi ƙofar fita. Sai dai kuma gam take alamar an kulle. Idanuna ne suka cika da ƙwalla. Ji nake kamar na saki ihu. Na jima a wajen kafin na yanke shawarar zuwa na bashi haƙuri tare da fahimtar da shi illar wannan hukuncin nasa dan bazai haifar mana da ɗa mai ido ba daga ni har shi ɗin….
🌜🌜💮🌛🌛
“Nafisatu ai ba amsar bane matsalar. Maganar kuma zamowarmu kuma family na farko a jihar nan a tunanina tuni muna ɗaya daga cikin masu wannan matsayin ama Nigeria ba jihar Lagos ba. Ɗanki ya jima da samo mana wannan sunan ama duniya ba'a ƙasar haihuwarmu kawai ba. Siyasa ta wuce duk yanda kike tunani, cike take da rikice-rikice da matsaloli iri-iri. Bazaki gane hakan ba sai mun farata. Amma dai ki bari zan tattauna da Awwab. Kin sanshi yanada experience akan irin waɗan nan abubuwan”.
“Baba yanzu nan duk mu yawan yaranka har mu huɗu cif babu wanda zaka iya shawara da shi a shekarunmu sai jika. Awwab har wani hankaline da shi wanda ko aure baiyi ba.”
“Humm Nafisatu, aure ai lokacine da shi ko?”.
“Baba yana da lokaci, amma kuma kaima ya kamata ka motsashi, yanzu irin wannan abun daya faru idan da maganar nan ta fita mi muke tunani? Ni yanzu ma tsorona ALLAH tsorona yaji daɗi ya cigaba da aikatawa tunda ba kunya garesa ba. Ballema yaga ba’a ɗauki wani mataki ba akai ai kaga abun bamusan kuma ina zai tsaya ba. Tun fa yana taɓa ƴan aiki wlhy wataran kan ƙannensa zai dawo. Dan Awwab yariga yayi gaurin da macen kawai yake buƙata fa. Ya kamata a duba wannan zancen Baba. Idan yana akan bakansa shi baiga wadda yake so ba ai ga ƴar uwarsa nan Azizat. A haɗasu mana kawai tunda Ita dai bazataƙi bin umarninmu ba. Shima kuma idan yaga kowa yaƙi saurarensa ai dole ya amince a wannan karon tunda koba komai yana son asirinsa ya rufu kar duniya ta sani”.
Jinjina kai kawai Baba yake. Sai da takai har ƙarshe sannan ya nisa. “Shawararki abar dubawace Nafisatu, kuma zan duba. Awwab ɗinne sai a hankali, yaro ne mai shegen taurin kan tsiya. Yanzu fa ki duba ki gani saboda yasan abinda yay ba dai-dai bane sam yaƙi zuwa gidan nan. Idan naje can duk yanda zai zame ya gudumin ya sani. Amma barshi nasan mi zanyi. Zanzo yau da dare na ritsashi in sha ALLAHU. Da zarar ya shigo gida ki kirani kawai”.
Cike da farin ciki Hajiya Mammah ta amsa da, “To in sha ALLAHU kuwa Baba. Amma maganar siyasar nan itama dai dan ALLAH a duba mana. Yaya kaga Nafisatu Adams K/Mashi ɗiyar gwamnan jihar Lagos”.
Yanda tai maganar tasa baba ƙyalƙyalewa da dariya. Itama dariyar takeyi….
❤️❤️❤️❤️
Kamar mai tsoron a jita a hankali nai knocking ƙofar, shiru babu motsin komai. Sake yi nayi har fin sau uku. Ganin dai bazai kulani ba na yanke shawarar buɗewa kawai ma shiga. A hankali na murɗa handle ɗin kuwa. Sai ko gashi ya buɗe. Sai da na sauke ajiyar zuciya tare da tsayawa na daidaita kaina sosai sannan na tura na shiga da sallama. Turus na tsaya ina kallonsa dan zaune yake akan sofa daga shi sai towel da waya a hannunsa yana magana cikin yanayin nan nasa a daƙile kamar wanda akama dole. A hankali na maida ƙofar na rufe ina mai duƙar da kaina dan bazan iya jurar kallonsa a yanda yake ba. Nafi minti biyu a wajen ina sauraren wayar tasa dana fahimci da Hayatu yake yinta. Sai dai abinda ya ɗan ja hankalina jin yana faɗin idan sun huta Hayatun ya kawosu nan gida. To ko su waye keda irin wannan matsayin haka. Dan na fahimci tunda nazo gidan nan ban taɓa ganin wani baƙo daya shafesa ba yazo. In banda ranar birthday ɗin nan da Bahijja tace min wanda suke zaune a waje ɗaya abokansa ne, kuma duk ba’a ƙasar suke ba idan ka cire ɗan sarkin Lagos ɗin. Ganin har ya kammala ya miƙe yana ƙoƙarin nufar mirror ya sani gyara tsaiwata. Dan ya wani basar tamkar baima ganni ba. Kuma na san yasan na shigo ɗin rainin hankalinsa ne kawai. Kaina a ƙasa daga ƙofar ɗakin na furta, “Dan ALLAH ina son muyi magana”.
Bai tanka min ba, bai kuma fasa abinda yake ba. Sai da ya mula dan kansa kusan minti biyu sannan ya magantu. Cikin silent voice ɗin nan tasa a daƙile ya furta, “Ki wuce wanka baƙi zasu shigo”.
Ji rainin hankali, ina masa wata maganar yana min wata. To ina ruwana da wasu baƙinsa. A zahiri kam sai na ƙara sauke murya har lokacin kan nawa a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni naje can inda na saba. Ko kuma na koma sashen Ummie tunda dama a yanzu kusan acan ɗin nake. Ya Awwab taya zan dawo nan bayan kasan akwai matsala. Babu fa wanda yasan akwai wani maganar aure a tsakaninmu a gidan nan. Mi kake tunani zasu fassara zaman nawa?”.
“Su fassara duk yanda yay musu! Idan kuma kina buƙatar su sanin ne, yanzun nan sai na tarosu su sani”.
Da sauri na ɗago ina kallonsa. Yanda yay maganar kansa tsaye babu wani alamun ya ɗauki zancena da muhimmanci. Kai wlhy stubborn mutumin nan ya fara isata. Da ƙyar na iya dannewa muryata na ɗan rawa na ce, “Idan kai zaka iya fuskantar su ka kuma ɗauka komai wlhy ni bazan iya ba. Sannan ba wannan rigimar nake so ba yanzu lafiyar Ummie ce damuwata. Dan ALLAH ka duba zance na yana da muhimmanci…”
“Kin dameni Madam wuce wanka kafin nazo kanki”.
Ya faɗa da ɗan kaushin harshe yana ajiye cumb ɗin hannunsa yana barin wajen. Karan farko naji hawaye sun gangaro min.
“Karna fito na sameki a wajen”.
Ya sake faɗa dai-dai yana shigewa cikin cikin closet ɗinsa. Hannuna na dunƙule kamar zan kaima bango naushi sai kuma na tausayama kaina dai. Dan nasan nice zan sha wahalar a ƙarshe hannunna ya rugurguje a banza. Hararar inda ya shige ɗin nayi ina cizar lips ɗina da ƙarfi, ga hawaye share-share a fuskata. Jin motsin kamar zai fito ya sani zabura na nufi bathroom ɗin. Dole ina ji ina gani na haɗa ruwan wankan nai ƙoƙarin fara yi. Wankan nake ina hawaye da hango irin bala’in da zai iya biyo baya. Dan wlhy abin bazai zama mai sauƙin ba a gareni. Gara sashen Ummie da nake zama shi wannan suna ganin ai kamar ina cutuwane shiyyasa aka ɗagamin ƙafa. Amma nan fa? Ni kaina idan an titsiyeni ban san mizan ce ba. Dan nayi alƙawarin in har bada kansa ya fito ya bayyana musu wacece ni ba wlhy ko za’a kasheni bazan faɗa ba. Sai da na kammala wankan sannan hankalina ya tashi, dan ban san yaya zanyi da kayan sakawa ba kuma. Bathrobe ɗin sa na ɗauka na saka. Sallar walha da nake son zuwa nayi dan lokacinta yayi ya sani haƙura na fito, amma sai da na leƙa cikin ɗakin sannan. Shiru babu motsin komai, sannan a iya hangena ban hango alamar akwai mutun ba. Ɗan ajiyar zuciya na sauke na fito a ɗan ɗarare. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganin tabbacin baya ɗakin, tunanin sauri na shafa mai yazo min, dan haka na nufi gaban mirror ɗin nashi. Zama nayi tare da bin kayan dake akai da kallo, cikin ɗan taɓe baki na furta, “Sai kace mace”. Da ƙyar na iya gane man shafawa, ina son na fara dubashi ina tsoron yin jinkirin da har zai dawo ya saman a wajen. Da sauri-sauri na shafa man da duk abinda zan iya amfani da shi a wajen. Na miƙe raina fal tashin hankalin kayan daya kamata ace na saka ya shigo. Daburcewa nayi dan abin yazo min a bazata. Rasa makamar riƙewa ta sani komawa kan stool ɗin kujerar na zauna tare da duƙar da kaina. Baiyi magana ba, sai madaidaicin akwati da yazo ya ajiye gab dani. Juyawa yay yayi ficewarsa yana faɗin, “Zanje wajensu, da munyi salla zasu shigo. Zaki iya zuwa duba Ummien kafin”. Daga haka yay ficewarsa. Da kallo na bisa duk kaina duk a ɗaure. Sai dai furta zan iya zuwa duba Ummie ne yay matuƙar wanke min zuciya. Mikewa nai cike da zumuɗi harda daka tsalle dan farin ciki, tuni na nema damuwata da tunanin wasu baƙi da ya ishi mutane da zancensu na ɗauki akwatin daya ajiye ɗin. Saman gado na kaisa na buɗe………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏
…….Mun jima zaune a hakan kafin ya mike a fusace. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, batare da ya juyoba cikin kaushin murya ya furta, “Daga yau zaki cigaba da zama anan”.
Wani irin zabura nayi yan hanjin cikina na wantsalawa tare da bugun zuciyata. Bamma san sanda na furta, “Anan kuma?”. Ko kallon inda nake baiyi ba yayi wucewarsa hanyar bedroom ɗinsa. Wani irin bugawa zuciyata keyi diff-difff!! Dan har ga ALLAH maganar tashi tayi masifar ratsa min ƙashi da bargo. Wane irin neman bala’ine haka dan ALLAH. Taya zan cigaba da zama a side ɗinsa bayan Mama Balki ta sanar min babu wanda yasan akwai aure tsakanina da shi. Sannan yan uwansa ma abinda ya faru kallonsa suke ama tsayin fyaɗe. “Na shiga uku ni Samraah mutumin nan zai kasheni. Ni wlhy koma ba duk wancan ba bazan iya zaman anan da shi mu biyu kacal ba. Mutumin daya nema kusan kasheni ina gaskiya bashi yiwuwa. Gara ma tun kan wankin hula ya kaini dare na kama gabana. Inama laifin yace na koma sashen Ummie dan ALLAH. Zaram na miƙe, har haɗawa nake da sassarfa na nufi ƙofar fita. Sai dai kuma gam take alamar an kulle. Idanuna ne suka cika da ƙwalla. Ji nake kamar na saki ihu. Na jima a wajen kafin na yanke shawarar zuwa na bashi haƙuri tare da fahimtar da shi illar wannan hukuncin nasa dan bazai haifar mana da ɗa mai ido ba daga ni har shi ɗin….
🌜🌜💮🌛🌛
“Nafisatu ai ba amsar bane matsalar. Maganar kuma zamowarmu kuma family na farko a jihar nan a tunanina tuni muna ɗaya daga cikin masu wannan matsayin ama Nigeria ba jihar Lagos ba. Ɗanki ya jima da samo mana wannan sunan ama duniya ba'a ƙasar haihuwarmu kawai ba. Siyasa ta wuce duk yanda kike tunani, cike take da rikice-rikice da matsaloli iri-iri. Bazaki gane hakan ba sai mun farata. Amma dai ki bari zan tattauna da Awwab. Kin sanshi yanada experience akan irin waɗan nan abubuwan”.
“Baba yanzu nan duk mu yawan yaranka har mu huɗu cif babu wanda zaka iya shawara da shi a shekarunmu sai jika. Awwab har wani hankaline da shi wanda ko aure baiyi ba.”
“Humm Nafisatu, aure ai lokacine da shi ko?”.
“Baba yana da lokaci, amma kuma kaima ya kamata ka motsashi, yanzu irin wannan abun daya faru idan da maganar nan ta fita mi muke tunani? Ni yanzu ma tsorona ALLAH tsorona yaji daɗi ya cigaba da aikatawa tunda ba kunya garesa ba. Ballema yaga ba’a ɗauki wani mataki ba akai ai kaga abun bamusan kuma ina zai tsaya ba. Tun fa yana taɓa ƴan aiki wlhy wataran kan ƙannensa zai dawo. Dan Awwab yariga yayi gaurin da macen kawai yake buƙata fa. Ya kamata a duba wannan zancen Baba. Idan yana akan bakansa shi baiga wadda yake so ba ai ga ƴar uwarsa nan Azizat. A haɗasu mana kawai tunda Ita dai bazataƙi bin umarninmu ba. Shima kuma idan yaga kowa yaƙi saurarensa ai dole ya amince a wannan karon tunda koba komai yana son asirinsa ya rufu kar duniya ta sani”.
Jinjina kai kawai Baba yake. Sai da takai har ƙarshe sannan ya nisa. “Shawararki abar dubawace Nafisatu, kuma zan duba. Awwab ɗinne sai a hankali, yaro ne mai shegen taurin kan tsiya. Yanzu fa ki duba ki gani saboda yasan abinda yay ba dai-dai bane sam yaƙi zuwa gidan nan. Idan naje can duk yanda zai zame ya gudumin ya sani. Amma barshi nasan mi zanyi. Zanzo yau da dare na ritsashi in sha ALLAHU. Da zarar ya shigo gida ki kirani kawai”.
Cike da farin ciki Hajiya Mammah ta amsa da, “To in sha ALLAHU kuwa Baba. Amma maganar siyasar nan itama dai dan ALLAH a duba mana. Yaya kaga Nafisatu Adams K/Mashi ɗiyar gwamnan jihar Lagos”.
Yanda tai maganar tasa baba ƙyalƙyalewa da dariya. Itama dariyar takeyi….
❤️❤️❤️❤️
Kamar mai tsoron a jita a hankali nai knocking ƙofar, shiru babu motsin komai. Sake yi nayi har fin sau uku. Ganin dai bazai kulani ba na yanke shawarar buɗewa kawai ma shiga. A hankali na murɗa handle ɗin kuwa. Sai ko gashi ya buɗe. Sai da na sauke ajiyar zuciya tare da tsayawa na daidaita kaina sosai sannan na tura na shiga da sallama. Turus na tsaya ina kallonsa dan zaune yake akan sofa daga shi sai towel da waya a hannunsa yana magana cikin yanayin nan nasa a daƙile kamar wanda akama dole. A hankali na maida ƙofar na rufe ina mai duƙar da kaina dan bazan iya jurar kallonsa a yanda yake ba. Nafi minti biyu a wajen ina sauraren wayar tasa dana fahimci da Hayatu yake yinta. Sai dai abinda ya ɗan ja hankalina jin yana faɗin idan sun huta Hayatun ya kawosu nan gida. To ko su waye keda irin wannan matsayin haka. Dan na fahimci tunda nazo gidan nan ban taɓa ganin wani baƙo daya shafesa ba yazo. In banda ranar birthday ɗin nan da Bahijja tace min wanda suke zaune a waje ɗaya abokansa ne, kuma duk ba’a ƙasar suke ba idan ka cire ɗan sarkin Lagos ɗin. Ganin har ya kammala ya miƙe yana ƙoƙarin nufar mirror ya sani gyara tsaiwata. Dan ya wani basar tamkar baima ganni ba. Kuma na san yasan na shigo ɗin rainin hankalinsa ne kawai. Kaina a ƙasa daga ƙofar ɗakin na furta, “Dan ALLAH ina son muyi magana”.
Bai tanka min ba, bai kuma fasa abinda yake ba. Sai da ya mula dan kansa kusan minti biyu sannan ya magantu. Cikin silent voice ɗin nan tasa a daƙile ya furta, “Ki wuce wanka baƙi zasu shigo”.
Ji rainin hankali, ina masa wata maganar yana min wata. To ina ruwana da wasu baƙinsa. A zahiri kam sai na ƙara sauke murya har lokacin kan nawa a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni naje can inda na saba. Ko kuma na koma sashen Ummie tunda dama a yanzu kusan acan ɗin nake. Ya Awwab taya zan dawo nan bayan kasan akwai matsala. Babu fa wanda yasan akwai wani maganar aure a tsakaninmu a gidan nan. Mi kake tunani zasu fassara zaman nawa?”.
“Su fassara duk yanda yay musu! Idan kuma kina buƙatar su sanin ne, yanzun nan sai na tarosu su sani”.
Da sauri na ɗago ina kallonsa. Yanda yay maganar kansa tsaye babu wani alamun ya ɗauki zancena da muhimmanci. Kai wlhy stubborn mutumin nan ya fara isata. Da ƙyar na iya dannewa muryata na ɗan rawa na ce, “Idan kai zaka iya fuskantar su ka kuma ɗauka komai wlhy ni bazan iya ba. Sannan ba wannan rigimar nake so ba yanzu lafiyar Ummie ce damuwata. Dan ALLAH ka duba zance na yana da muhimmanci…”
“Kin dameni Madam wuce wanka kafin nazo kanki”.
Ya faɗa da ɗan kaushin harshe yana ajiye cumb ɗin hannunsa yana barin wajen. Karan farko naji hawaye sun gangaro min.
“Karna fito na sameki a wajen”.
Ya sake faɗa dai-dai yana shigewa cikin cikin closet ɗinsa. Hannuna na dunƙule kamar zan kaima bango naushi sai kuma na tausayama kaina dai. Dan nasan nice zan sha wahalar a ƙarshe hannunna ya rugurguje a banza. Hararar inda ya shige ɗin nayi ina cizar lips ɗina da ƙarfi, ga hawaye share-share a fuskata. Jin motsin kamar zai fito ya sani zabura na nufi bathroom ɗin. Dole ina ji ina gani na haɗa ruwan wankan nai ƙoƙarin fara yi. Wankan nake ina hawaye da hango irin bala’in da zai iya biyo baya. Dan wlhy abin bazai zama mai sauƙin ba a gareni. Gara sashen Ummie da nake zama shi wannan suna ganin ai kamar ina cutuwane shiyyasa aka ɗagamin ƙafa. Amma nan fa? Ni kaina idan an titsiyeni ban san mizan ce ba. Dan nayi alƙawarin in har bada kansa ya fito ya bayyana musu wacece ni ba wlhy ko za’a kasheni bazan faɗa ba. Sai da na kammala wankan sannan hankalina ya tashi, dan ban san yaya zanyi da kayan sakawa ba kuma. Bathrobe ɗin sa na ɗauka na saka. Sallar walha da nake son zuwa nayi dan lokacinta yayi ya sani haƙura na fito, amma sai da na leƙa cikin ɗakin sannan. Shiru babu motsin komai, sannan a iya hangena ban hango alamar akwai mutun ba. Ɗan ajiyar zuciya na sauke na fito a ɗan ɗarare. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganin tabbacin baya ɗakin, tunanin sauri na shafa mai yazo min, dan haka na nufi gaban mirror ɗin nashi. Zama nayi tare da bin kayan dake akai da kallo, cikin ɗan taɓe baki na furta, “Sai kace mace”. Da ƙyar na iya gane man shafawa, ina son na fara dubashi ina tsoron yin jinkirin da har zai dawo ya saman a wajen. Da sauri-sauri na shafa man da duk abinda zan iya amfani da shi a wajen. Na miƙe raina fal tashin hankalin kayan daya kamata ace na saka ya shigo. Daburcewa nayi dan abin yazo min a bazata. Rasa makamar riƙewa ta sani komawa kan stool ɗin kujerar na zauna tare da duƙar da kaina. Baiyi magana ba, sai madaidaicin akwati da yazo ya ajiye gab dani. Juyawa yay yayi ficewarsa yana faɗin, “Zanje wajensu, da munyi salla zasu shigo. Zaki iya zuwa duba Ummien kafin”. Daga haka yay ficewarsa. Da kallo na bisa duk kaina duk a ɗaure. Sai dai furta zan iya zuwa duba Ummie ne yay matuƙar wanke min zuciya. Mikewa nai cike da zumuɗi harda daka tsalle dan farin ciki, tuni na nema damuwata da tunanin wasu baƙi da ya ishi mutane da zancensu na ɗauki akwatin daya ajiye ɗin. Saman gado na kaisa na buɗe………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏
…….Kayane ɗinkakku har kala biyar, sai kayan ciki b&p 12-12. Sosai naji kunya ta kamani. Wani gefe na zuciyata kuma na mamakin inda yasan seize ɗina. Hatta da ɗinkunan dai-dai jikina cif. Zumuɗin tafiya wajen Ummie ya sani ajiye komai gefe na shirya cikin doguwar rigar lass pink mai ƙyau mara nauyi kuma. Komawa nayi gaban mirror ɗin ina kallon kaina fuskata cike da murmushi. Na dawo Samraah ta ƴar jarida ƴar gayu. A take yaya Musaddiq yazo min a rai. Hawaye naji sun cika min ido na kewarsu. Tunda abin nan ya faru bamuyi waya ba. Dolene idan na dawo wajen Ummie na roƙesa aron waya nayi kiransu har su aunty Zakiyya ma. Da wannan tunanin na ɗauki turarensa na fesa tare da ɗaukar ɗankwalin nai simple ɗauri. Mayafin cikin akwatin guda uku na ɗauka ɗaya nayi salla dan babu hujjab. Ina idarwa na miƙe cike da zumuɗi na tattare duk kayayyakin dana baza na maida bathrobe ɗin danai amfani da ita da towels ɗin daya cire na maida bayin. Sake ɗan gyara fuskata nayi da faran fauda ɗin dana gani sannan na fice.
Nayi mamakin ganin falon ƙal yanzu yana zuba ƙamshi ga sanyin ac duk da dai ɗazun ma ba wani datti bane. Amma daga gani yanzu kasan an sake gyarashi. Kaina tsaye na fito batare da jin damuwar idan na haɗu da wani yaya zanyi ba. Koda na shiga sai da na sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin babu kowa a falon. Dama ba lallai na samu masu aiki ba, dan yanzu lokacin hutu ne an gama na safe sai kuma azhar tayi. Kaina tsaye na haye sama harda ɗan guduna.
Naji matuƙar farin cikin samun sashen Ummie fes da shi, ga ƙamshi na tashi tako ina. Da alama aikin Mama Balki ne kuwa. Ilai kuwa a ciki na sameta tana bama Ummie abinci. Da gudu na naje na faɗa jikin Ummie ina mai sakin kuka. Dariya Mama Balki ta sanya min, niko ko’a jikina murnar ganin Ummie kawai nakeyi. Sai da na gama murnata na ɗago ina kallonta. Itama kallona kawai takeyi kamar ta samu television. Murmushi na sakar mata idanuna cike da ƙwalla na ce, “Ummie na i miss you”.
A bazatar da ta bamu matuƙar mamaki mukaga ta saki murmushi tare da kai hannu ta shafa kaina. Sai kuma ta saki kuka. Ruɗewa mukai mu duka. Ƙoƙarin miƙewa nake a jikinta amma sai ta riƙeni da ƙyau, sai kawai na sake rungumeta nima ina kukan. Mun jima a haka kafin na ɗago jin kamar jikinta ya saki. Mama na kalla, ta sakar min murmushi itama tana share ƙwallar idonta. A raunane ta ce, “Tayi barci. Dan tasha maganinta bayan na gama bata abinci. Gani nayi ga sake jawo kwanon sai nayi zaton bata ƙoshi ba shine na sake zaman bata kika shigo.”
Nawa hawayen nima na share. Sai kuma na tashi a jikinta muka taimaka mata ta kwanta. Zama nayi a kusa da ita hannunta cikin nawa ina jin matuƙar farin ciki da ganinta. Sai matuƙar tausayinta dake cimun rai da zuciya dan duk ta rame min a ido alamar ciwon ya bugeta sosai wannan karon…
🩸🩸🩸🩸
“Kamar ya an sallamesu? Waye ya sallame sun?”. Ta faɗa cikin daka tsawa. Ƙanƙame jiki nurse ɗin tayi jikinta na rawa. Cike da tsorata da birkicewar Hajiya ƙaramar ta ce, “Am sorry Maa. Wlhy ni ban san wanda ya sallamesu ba, naga kawai sun fito ne amma Dr Larai ce ta musu rakiya har mota. Muma ganin haka yasa muka rakasu”.
Wani irin tashi sama jijiyoyin Hajiya ƙarama sukayi, a fusace ta sake dakama Nurse ɗin tsawa. “Get out of my side!!”.
Ai da gudu Nurse ɗin ta fice kuwa. Har neman faɗuwa take, ALLAH dai ya taimaketa ta dafe bango. Tana fita itama Hajiya Ƙarama ta fice a fusace. Sai da taje ƙofar office ɗin Dr Larai sai kuma ta gyara yanayinta cikin jan numfashi da saukewa. Knocking ƙofar tayi, aka bata iznin shiga. Dr Larai na zaune da waya a hannunta da alama akwai abinda take yi. Shigowar Hajiya ƙaramar ya sata ajiye wayar tana murmushi. Da girmamawa matsayin Hajiya ƙarama na shugaba a asibitin ta ce, “Welcome Doctor ashe kin shigo? Yanzu nake tunanin zuwa na duba kafin na wuce gida ai dama”.
Murmushin yaƙe Hajiya ƙarama tayi, tare da jan kujera ta zauna. Hakan yasa itama Dr Larai komawa ta zauna. Gaisuwa sukai a mutunce. Kafin Hajiya ƙarama ta tambayi bataga petient ɗinta ba. Kota canja musu ɗaki ne?. Da ɗan mamaki Dr Larai ta ce, “Kunyi saɓani kenan? Dan sun wuce gida. Yaron nan naku rigimamme ne na bugawa a jarida. Dan har office ɗin nan yazo ta tirkeni sai na bama yarinyar nan sallama. Babu irin son fahimtar da shi ɗin da banyi ba dan ya barta ta ƙara samun sauƙi sosai amma fir yaƙi. Wai a dinga zuwa gida ana dubata. Ko kuma ya kawota asibitin kullum. Rikitaccen mutum ne na lura mai ra’ayin riƙau gaskiya.”
Da ƙyar Hajiya ƙarama ta ƙaƙaro murmushi. Sai kuma ta miƙe tana faɗin, “Ai in dai Awwab ne ƙyaga da yawa wlhy. Shike nan bari zanje gidan mu haɗu ai.”
Murmushi itama Dr Larai tayi da faɗin, “To shike nan hakan ma yayi, amma ina tausayama matarsa dan zata sha fama. Stubborn namiji irin wannan idan baka karancesa ba wahalar zamane da su. Dan su abinda suke so kawai za’ayi tilas.”
Murmushi kawai Hajiya ƙarama tayi dan ita abinda ya dameta shi ya dameta. Cikin wayancewa dai tace bara taje taga petient sun taru. Miƙewa itama Dr Larai tayi tana tattara kayanta. “Okay nima ai wucewa zanyi. Nasan Alhaji bazai wuce ba sai na koma.”
💦🩸💦🩸💦
Tuni ganin Ummie yasa na manta da dokarsa ta kar na daɗe. Na shagala sosai da kwance mata gashinta bayan nayi sallar azhar, kanta na a saman cinyata ƙamshin turarensa ya cika ɗakin. Da farko ban maida hankali ba saboda nasan na saka wani a jikina. Sai da naji alamun mutum na nufoni sannan na farga. Shi ɗinne dai sanye cikin brown wando da ash ɗin riga mai gajeren hannu. Gashin nan a ɗaure ta can ƙasa sosai dan har yana taɓa bayansa. Saukar iska a cikin idanuna ya sani jan numfashi da ƙarfi na lumshe idanun, sai kuma duk kunya ta kamani irin wannan abin kunya haka na kure bawan ALLAH da ido. A zatona zaiyi maganar kallon sai naji baice komai ba. Sai ma hannunsa da ya ɗaura saman nawa dake tsefe kan Ummie. A hankali na ɗan ɗago na kallesa. Shima ni ɗin yake kallo. Ƙure juna mukai da ido ga hannayenmu akan Ummie.
“Kinga mamanki kin manta da umarni na ko?”.
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Fuska na ɗan marairaice masa da karyar da kaina gefe a shagwaɓe na ce, “Kanta ne fa ya tsufa”.
Idanunsa ya ɗan ja luuu kamar zai lumshe sai kuma ya buɗesu tar akan nawa. Bazan iya jurar salon kallon nasa ba a yanzu dan haka na janye nawa a hankali na duƙar da kan. Shima sai bai sake cewa komai ba ya ɗan janye hannun nawa ya ƙarasa tsefema Ummien. Dama ɗayan da nake yinne ya rage. Dan bana mata kitson da yawa. Koda ya kammala cumb dake saman cinyata ya ɗauka ya taje mata kamar yanda naima sauran. Sannan ya tattare gashin cikin hannunsa. Kallona yay a hankali ya furta, “Cire band ɗin kaina, idan kin dawo kwayi kitson”.
Kai kawai na jinjina masa. Kafin a kunyace na kai hannuna saman gashinsa dake kwance luff yana ƙyalli kona wata macen albarka na zame sililin baƙin band ɗin daya haɗe da gashin sai ma ka ƙura ido kake ganewa. Koda yaushe kuma zakaga da irinsa yake ɗaure gashinsa. Ina gama zarewa gashin nasa ya tarwatse a baya. Sai kawai na shagala da kallonsa har sai da naji saukar hannunsa cikin nawa zai zare band ɗin sannan na dawo hankalina. Duƙar da kaina nayi kunya duk ta isan. Yau dai na kula kamar ina sakin layi da yawa. Sai dai yanda ya basar yasa na ɗan ji nutsuwa. Yana gama ɗaure mata ya gyara mata kwanciya shima ya miƙe yana faɗin, “Lets go”.
Dole na mike a hankali ina gyara mayafin jikina. Wani kallo ya dinga bina da shi daga sama zuwa ƙasa. Sai kawai nai gaba da sauri. A falo muka samu mama Balki ashe bata fita ba. Tana ganinmu ta saki murmushi da faɗin, “Har kun fito.” a kunyace na jinjina mata kaina. Shi kuma ya sanar mata akwai baƙi a gidan zuwa anjima zai kira wayarta tazo su gaisa. Ya kuma roƙeta ta rufe ƙofar falon ko Paah ne yazo karta barsa ya shigo. Maganar tasa ta ɗan ban mamaki, har na kasa haƙuri sai da na kallesa. Amma sai ya ɗauke kansa kamar ma bashi ne yay maganar ba…
A falon ƙasa muka ci karo da su Azizat. Tunda muka fara sakkowa duk suka miƙe tsaye tamkar waɗan da ke cikin shock. Dan su duka bakunansu a buɗe suke kallonmu idan ka cire wata farar budurwa da ban sani ba a gidan dake zaune ita bata tashi ba. Sai dai itama ta zuba masa ido kamar zata cinyesa. Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina. Kamar yanda shima naga baima nuna yasan da zamansu ba ya wucewarsa. Ina jiyo Malika na yin ashar a hankali. Ban san miya basu mamakin ba. Ganina a gidan? Ko kuwa ganina tare da shi?. Oho dai can ta matse musu. Dan ni su duka ukun a yanzu na shirya duk wadda tace zata shigo sabgata wlhy sai na mata zanen yarabawa a fuska.
Koda muka iso ƙofar shiga sashen nasa sai da na tsaya na ɗan gyara mayafina sannan na bisa dan shi har ya riga ya shiga. Da Hayatu na fara cin karo tsaye a ƙofa yana waya, muna haɗa ido ya wani rissinar da kai. Harara na balla masa na wuce ciki abuna. Bana ganin fuskar waɗanda ke a zaune, sai dai haka kawai zuciyata ke wani irin sanyi da jikina. Gani nike kuma kamar na sansu. Tamkar wadda ƙwai ya fashema a ciki na ƙarasa sosai cikin tsakkiyar kujerun ina sake yin sallama ƙasa-ƙasa batare dana kallesu ba. Turus na tsaya zuciyata na bugawa da ƙarfi sakamakon jin muryoyin da ko’a cikin barci bazasu taɓa iya su ɓace min ba. Jikina har rawa yake na ɗago dan tabbatarwa. Sai kawai naci karo da fuskar Yaya Musaddiq da ke faman min murmushi da ta Hafizzullah. Yanzu kam sosai rawar jikina sake bayyana tayi, ga lips ɗina na rawa kamar yanda hannuna ke rawa ina son nunasu amma na kasa……..✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚
……..
……Cikin rawar jiki na nufesu da wata irin sassarfa na faɗa jikin Yaya Musaddiq na saki wani irin kuka da ni kaina bamma san na minene ba, sai kuma na jawo hannun Hafizzullah shima na haɗasu na rungume. “Oh oh Kandala na ashe bata canja hali ba har yanzu jama’ar ALLAH”. Yaya Musaddiq ya faɗa cike da tsokana yana ɗagoni a jikinsu. Cikin dariya da sharar hawaye Hafizzullah ya ce, “ALLAH Yaya bata canja ba sai ma abinda ya ƙaru.” hannu nasa a kansa na dungure nima ina sharar hawayen na ce, “Magulmaci kana nan da hali”.
Dariya muka sanya mu duka ukun. Kafin na sake kamo hannayensu cikin nawa su dukan. Cikin shagwaɓa na sake fashe musu da kuka ina faɗin, “Ya akai kuka zo nan? Waye ya kawoku? Yaya wlhy nayi kewarku, kullum da dare sai nayi kukan rashinku. Yaya dan ALLAH kuce kun dawo nan zaku zauna tare dani?”.
Murmushi kawai yaya Musaddiq keyi, sai Hafizzullah ne cikin dariya ƙasa-ƙasa ya ce, “Sai dai idan zaki bimu mu koma Kano. Dan ni ban wani yarda kinyi kewarmu ba Addah. Jibeki kinyi wata fresh kamar ɗanyan nama sabon yanka. Ga ƙiba kin haɗa kamar ke kaɗai ake ma tirka a gidan. Kai gaskiya ba wani kewarmu ke dai gidan miji daɗi kinma manta da mu”.
“Yaya ka ganshi yana tsokalana ko?”. Na faɗa a shagwaɓe batare dama nasan mi nake ba. Dan wlhy duk jina nake a ruɗe kamar a cikin mafarkin dana saba. Dana farka zan nemesu na rasa ne. A hankali Yaya Musaddiq dake murmushi har yanzu yana kallona kawai ya kai hannu ya share min hawayen yana faɗin, “Manta da shi, har kin manta da halin auta ne ma. Bayan da yaji zanzo badashi ba ya zauna ya dinga rusa kuka harda birgima a tsakar gida wai shi idan baizo yaga Addarsa ba zai faɗa rijiyan gidan su Mama Sadiq maƙotanmu”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi, tare da kai hannu kan fuskar Hafizzullah daya kwaɓe ta cike da shagwaɓa naja kumatun, sai kuma na dunguresa da faɗin, “Ashe dai yaron nan na sona har yanzu”…
Duk abin nan dake faruwa yana zaune a falon. Binsu kawai yake da kallon ƙasan ido wani abu na masa motsi a zuciya. Daka gansu kaga waɗanda sukai matuƙar shaƙuwa da juna, suke kuma tsananin so da ƙaunar juna. Wani irin lumshe idanunsa yay murmushi na suɓuce masa a bazata. Hoton Fahad ne ya fara masa gizo a cikin idanunsa dake rufe, da sauri ya buɗesu yana cizar lips. Dan wani irin zafi zuciyarsa ta fara masa. Ƙoƙarin ture tunanin dake neman kutso masa a zuciya yayi ya sake maida dubansa kansu. Hakan sai yay dai-dai da Samraah ta juyo suka haɗa ido kuwa. A mamakinsa sai ta sakar masa murmushin da har ya bayyana haƙwaranta. Sai ya samu kansa da lumshe idanun da buɗewa. A hankali ya furta, “Dama haka ake tarban baƙi da surutu?”.
Murmushin ta sake sakar masa tana miƙewa daga durƙuson da tayi a gabansu. Muryarta kanta na nuna alamun farin ciki ta ce, “Ya Awwab ALLAH daɗine naji kamar ya kasheni. Ashe dama kasan yan gidanmu amma baka tafa faɗa min ba? Nagode, Nagode kaima ALLAH ya faranta maka fiye da yanda ka faranta min”.
Kansa ya ɗan girgiza yana sakin murmushin daya kasa riƙewa. Sai kuma ya maida kallonsa ga su Yaya Musaddiq da suma ke murmushin, muryarsa da alamun tausasawa ya furta, “Bara na ɗan je bazan jimaba zamu dawo. Please ku ƙara cin abinci sosai nan ɗin gidanku ne.”
Faɗaɗa murmushin yaya Musaddiq yayi, cike da girmamawa ya ce, “Mun gode sosai ranka ya daɗe. ALLAH ya saka da alkairi”.
“Don’t say me thanks you or ranka ya daɗe ɗin nan. You are my brothers. By now we are family ne okay. Nine zan kiraka Yaya, sai kuma small kiddo Hafiz a gefe”.
“Yes babban Yaya”.
Cewar Hafizzullah cike da farin ciki. Yayinda Yaya Musaddiq keta murmushi dan shi sake ganin al’amarin yake kamar a mafarkinsa. Duk da bayanin da Hayatu yay masa tare da Maash ɗin kafin shigowar Samraah zuciyarsa ta kasa daina mamakin komai. Cikin jinjina kai ya furta, “Ni ne ya kamata na kiraka Yaya, kaga dama ni kaɗaine banda Yaya. Yanzu kuma na samu. I am so happy inada wanda idan nayi ba daidai ba zai tsawatar min, inada wanda nima zan yima kuka a jiki. Ka mana komai na rayuwa. Daba dan kai ba da yanzu ban san a wane hali muke ba, dan in har wani abu zai taɓa rayuwan Samraah mu dukanmu tamu rayuwar zata girgiza ne. Saboda mu duka biyun itace rauninmu. ALLAH ya faranta maka fiye da yanda kai mana”.
Hayatu da Maash ɗin suka amsa da Amin. Dan gaba ɗaya ma Maash ɗin ya rasa abin faɗa. Idanu suka haɗa da Samraah dake kallonsa tana murmushi. Cikin ɗan ƙanƙance cat eyes ɗin nashi ya ɗage gira sama da ɗan ɗage kai alamar kallon fa.
Samun kaina nayi da jin kunya, dan haka na duƙar da kan nawa kawai ina murmushi. Dan har ƙasan raina ban taɓa jin ya sakani a farin ciki irin na yau ba. Ji nake kamar naje na rungumesa. Amma ina jin kunya. Ɗagowa nayi na ɗan kalli Hayatu, shima a karo na farko na ce masa, “Thanks You”.
Murmushi shima ya sakar min yana yin ƙasa da kansa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Nine zan gode ai Aunty na”. Yanzu kam Harara na balla masa ina ɗauke kaina da murguɗa baki. Sai ko muka sake haɗa ido da ogan nasa. Ɗauke fuskata nayi gaba ɗaya daga sashensu. Sai da naji Hayatu nama su Yaya Musaddiq sallama akan sai sun dawo sannan…
🌿🌿🌿🌿
A hargitse Hajiya ƙarama ta koma office ɗinta. Kofar ta kulle dan bata buƙatar ganin kowa. Kai-kawo ta shiga yi cikin Safa da marwa. Kafin ta jawo waya ta shige cikin toilet. Sau uku tana kira amma ba’a ɗaga ba. Kanta ta dafe cike da takaici. Yanzu haka yana can yasha giyar tashi yana shaɓar barci. “Motsoww” taja tsaki tare da fitowa. Wayar ta wurga saman desk ɗinta, itama ta zube a kujera tana mai dafe kai. Ji take yana wani irin sara mata. So take tai magana da wani ko zataji daɗi. Amma dawa ɗin zata yi. Da sauri ta sake rarumo wayar ta danna ma Jannifer kira. Bugu ɗaya kuwa ta ɗauka. Jin muryarta wani iri ta sata jan tsaki. “Malama dalla koma dawa koke tare ta tashi taba mutane waje magana zamuyi.”
“Bara dai ni in tashi”.
Jannifer ta faɗa tana ƴar shaƙiyar dariya. Tsaki kawai Hajiya ƙarama tayi batace komai ba. Sai da Jannifer ta sanar mata ta fito tana jinta sannan ta sake jan tsaki da fara magana. “Jannifer wai ina kika samo yarinyar nan ne? Wlhy tunanina gaba ɗaya nan birkicewa yake a wannan gaɓar?”.
Da mamaki Jannifer ta ce, “Kamar ya? Wani abu ne ya sake faruwa?”.
“Miye ma bai faruba. Yanzu nan nazo asibiti na samu wai banzan yaron nan Awwab yazo ya ɗauke yarinyar nan sun wuce gida?”.
“Tofa babbar magana. Wai Maash kike nufi?”.
“To in ba shiba waye zaima mutane wannan gadaran”.
Dariya ce ta kufcema Jannifer, sai da tayi mai isarta kafin da ƙyar cikin dariyar ta ce, “Kai amma yaron nan ƙwallon shege ne wlhy. I like him style wlhy. Komansa yake baya tsoron uban kowa. Ya taka na waje kuma na gidan bai barku ba ciwon kan da gwale-gwale yake baku. To wai kodai son yarinyar nan yake ne? Abinfa da mamaki wlhy, dan ni bammaga wani damuwa a tattare da shi akan abinda ya aikata ɗin ba. Ka ɗirkama yarinya fyaɗe amma ka dinga abu It’s like you don’t care, I really like this boy’s style.”
“Mtsowww!! Jannifer ban son shirme. Ina miki maganar serious kina mun wani soki burutsu.”
“Ehm sorry Maa. ALLAH abunne ya ban dariya ya kuma burgeni. Samun irin stubborn mazan nan ba ko inaba. A Abuja nasan yarinyar ni gaskiya……” ta kwashe komai data sani akan Samraah ɗin tun daga haɗuwarsu da abinda ya faru kuma duk ta gaya mata”.
Cikin damuwa Hajiya ƙarama ta ce, “Amma kema kinyi ganganci da baki san labarin nata ba”.
“To banda abinki Hajjaju mizai sa na damu da labarinta. Ni fa dama irinta na fita nema. Sai kuma na samu miya rage min. Kaiwa na ɗako nazo na samu kuɗaɗena ai.”
“Mtsoww!! Aikin kenan. To ita kuma Mashi’a ya akai ta zaɓi yarinyar? Bayan nasan idan kin kawo yara sai sunyi fin wata biyu ma kafin ki saida su. Musamman irinta ma ai baki badata a masu aiki?”.
“Hummm ki bari kawai, wlhy kuɗaɗe kawai na gani. Dan an samu kuskure ne dana aika a kira min su ta biyosu. Nace ta koma Alaja Mashi’a ta ganta ta nace ita take so harda ninka min kuɗi. Ni kuma kawai naga bazan iya ba na sallama. Dan nasan ko ƙasar waje na kaita ba lallai na samu abinda na samun ba a wajenta. Kuma ina ma jin nauyin Alaja Mashi’a wlhy. Kin san dai ba wannan karon ne na farko dana fara samo mata masu aiki ba. Tunda kusan yaran gidankun nan duk a wajena aka amshesu mafi yawanci kuma itace ke zuwa da ɗauka musamman ma masu kula da Hajiya Babba.”
Numfashi Hajiya ƙarama ta furzar, dan tasan gaskiyar zance Jannifer ke faɗa mata. Mashi’a tana kallon Jannifer ne kawai a mai kawo ƴan aiki. Kuma zama ta iya cewa itace ta nuna mata gidanta a lokacin da take neman masu aiki da zata wuce da su can Germany, shine take faɗa mata gidan Jannifer ɗin. Tunda ta ɗauka wancan yaran biyu ta wuce da su taji daɗin zama da yaran sai yazam duk sanda ta shigo Nigeria takan ɗaukama Hajiya Babba masu kula da ita. Ko idan taji wasu nason masu aiki takan musu hanya. Da yake itama halin Maash ne da ita yanzu haka yaran data ɗauka su biyu duk sunyi karatu a can. Ɗaya a cikinsu ma ta kusa aure da ƙanin mijin ita Mashi’a ɗin. Ƙaramin tsaki taja da ture batun Mashi’a ta koma wanda zai amfaneta. Amma ba komai, ita Awwab ɗin ma ya saukaƙa mata aiki, a gidan ma wasan zaifi armashi tunda yarinyar a sashen masu aiki take. Zata dakata ta dawo sashenta da kwana, ta nuna saboda abinda ya faru ta ƴanta yarinyar. Zata nema mata makaranta kawai a wata ƙasar daga haka shikenan ta gama samun cikar burina……….✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆
…..Suna gama ficewa cike da zumuɗi na maido hankalina kansu Yaya Musaddiq. Ƙoƙarin zama nake Hafizzullah ya ce, “Wlhy ji nake kamar a mafarki. Wai aunty Samraah kece matar mutum kamar Maash. Ya ALLAH Maash fa. Wai dan ALLAH Adda yaya akai haka ta kasance? Kodai dama ke kin san wa kika aura? Dan wlhy duk da sun sanar mana komai yanzu kuma a gabana komai ta faru lokacin auren sai nake ganin kamar dama dai kuna son junan ku ne ke da shi.”
Harararsa na ɗan yi, sai kuma na koma kusa da Yaya Musaddiq na zauna ina sauke ajiyar zuciya. “Yaya dan ALLAH mi sukace muku? Sannan dama kaima baka san shi bane?”.
Murmushi sosai Yaya Musaddiq yayi yana kallona. Sai kuma ya jinjina kansa. “Samraah wlhy har yanzu ni kaina ina a cikin yanayin da Hafizzullah ɗin yake ciki ne. Dan harga ALLAH ban taɓa sanin Maash ne mijinki ba, taya ma zan kawo hakan a raina to. Bama ni kaɗai ba, hatta su Abba babu wanda yasan wa kika aura. Koda aka ɗaukeni aiki a companynsa na amsa ne saboda dalilai uku. Na farko dai bazan iya bijirema umarnin ogana ba. Saboda yana treating ɗina like uba. Ko Abba dake ƙanin mahaifiyata muke a hannunsa tun bamu san kammu ba bana jin ya damu da tarbiyyata kamar yanda ogana ya tsaya a kaina. Hakan yasa babu abinda zai ce nayi a rayuwar nan naƙi yinsa sai dai ina na saɓama ALLAH ne ko cutar da wani. Wannan kam bazan masa biyayya ba. Na biyu maganar video ɗin nan. Na yarda zanyi aiki a companyn da tunanin ko zan fahimci wani abu dan na sanki da naci akan abu, komai tsahon lokaci da za’a ɗauka bazaki taɓa barin maganar video ɗin nan ba. Na uku amsar aikin kamar samun wata hanyar cigaban rayuwa ne yazo mana mu duka. Dan bamu da kowa sai junanmu. Dolene nayi aiki tuƙuru in har bana saɓama ALLAH bane domin cigaba da gina rayuwarmu. A lokacin da aka samu matsala game da aurenki, mahaifiyar Mansoor tazo har gida taci mutuncin su Abba akan ɗanta bazai taɓa ya aureki ba, su bazasu haɗa zuri’a da ke ba, idan kuma muka matsa zata iya ɗaukar kowane irin mataki dan ganin ta rabaki da ɗanta. Kin san Kawu Musa da zuciya, dan haka shima ya balbaleta, sai kawai ta ɗaga hannu ta maresa. Kafin ta sauke hannunta mukaji itama an sauke nata marin. Ta gigita sosai, haka muma da mamaki muke kallon bawan ALLAHn daya maretan. Mutum ne cikin shigar kamala harda gemunsa, maganganun daya gayama mahaifiyar Mansoor a lokacin sun matuƙar birgemu. Sai muka ji sauƙin yanda kalamanta suka ƙona mana rai dama kowa na wajen a take muma mukace ko Mansoor ne autan maza kin barsa har abada. An gama duk wannan rikici Maman Mansoor ta wuce bawan ALLAHn nan shima zai wuce Kawu Musa ya dakatar da shi. Godiya ya masa muma haka. A mamakin mu sai kawai muka ji ya fara jera masa tambaya. (Yaro munene sunanka?) Yace masa Muhammad. Anan kake? Yace masa eh to yana aiki anan amma asalinsa ba mazaunin nan ɗin bane. Kana da aure? Sai da yay jim kamar mai tunani kafin yace masa a’a. Kana shirin yi ne? Nan ma ya amsa masa da a’a. Iyayenka fa? Yace suna nan a raye. Sai mukaga kawai Kawu Musa yayi murmushi. Batare da wani tunani ba kawai ya ce (kowa ya shaida. Ni Musa a matsayin yayan Abdul-wahab na bama wannan bawan ALLAHn Muhammad auren ɗiyata Samraah. Ina fatan bazaka taɓa watsa min ƙasa a ido ba. Ina fatan zaka tabbatar min da ƙyautata maka zato da nake yi. Ina fatan zaka riƙeta amana bazaka taɓa cin amanata ba. Idan kuma har akwai matsala ka fito ka sanar min wlhy zan fahimceka. Nima kuma badan bana son Samraah na baka ita ba. Ba kuma dan na zubar mata da darajanta nayi hakan ba. Yarinyata mai ilimin addini ce dana zamani. Sannan ƙyaƙyƙyawace mai tarbiyya. Kaga dai ban sanka ba, ban san daga inda ka fito ba. Komai daya faru daga UBANGIJI ne ba daga mu ba. Dan abinda kayi yanzu yasa nake ji a raina ko daga ina ka fito kai ɗin mutumin kirki ne, dan ɗan halak shike kare martabar tsoho a duk inda yaga za’a yaga masa rigar mutunci.”
“Wlhy Kandala ya matuƙar jimawa tsaye bai motsa ba a wajen. Har sai da Kawu Musa ya dafa shi da faɗin. Idan fa har kaga akwai matsala kada ka saka kanka a cikin damuwa. Mu duka dake nan babu wanda zai zargeka da rashin ƙyautawa har abada. Kuma mun ƙulla zumunci da kai kenan har abada. Murmushi yayi, sai kuma ya ɗan jinjina kai da roƙon a bashi wasu mintuna zaiyi waya. Kai tsaye Kawu Musa ya bashi dama. Tafiyarsa waya muka samu damar tattaunawa muma, Kawu Musa ya fahimtar damu dalilinsa na yanke hukuncin nan. Ni dai dan banda yanda zanyi ne bazan iya jayayya da su ba na amince. Hakama Hafizzullah atake yace shi dai dan ALLAH a barki. Amma sai Kawu Musa ya mana nasiha da nuna mana illar barinki ba’a ɗaura auren a ranar ba. Ya kuma ce mu cigaba da miki addu’a in sha ALLAHU sai kinci ribar wannan auren. Dawowarsa ta katse zancen mu. Ya tabbatar ma su Kawu ya amshi aure, sannan waliyyinsa na tafe in sha ALLAHU kafin lokaci yayi. Shima kuma zai je ya dawo. Badan muna da hope ɗin dawowar tasa ba muka barshi, amma abin mamaki na takaice miki sai gashi muna ƙoƙarin wucewa masallaci. Sunzo tare da babban malamin nan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain a matsayin waliyyinsa. Sai wannan Hayatu da suke tare yace ƙaninsa ne. Sheikh Muhammad dai ba ɓoyayyen mutum bane a garin Kano dama Nigeria baki ɗaya, dan haka duka damuwarmu da wani wasiwasi ya kau. Sheikh Muhammad ya tabbatar mana Muhammad tamkar ɗa yake a wajensa, kuma in sha ALLAHU bazamuyi kukan haɗa jini da shi ba. Idan ma muna tunanin wani abu mu cire, dan wata hikima ce ta UBANGIJI shigowarsa rayuwarmu. Bai kuma ɓoye masa komai game da abinda ya farun ba. Kawu Musa yafi kowa shiga a farin ciki. Dan haka a take aka ɗaura aurenku bayan idar da sallar juma’a, aka kuma kwaso kayanki da aka kai gidan Mansoor aka maida gidan daya bada matsayin nasa. Bayan an kaiki kuma sai aka samu akasin ciwo da kika shiga har ya taho dake Abuja, daga baya ya sanar mana kuna Lagos wajen iyayensa. Koda yaushe muna waya da shi, amma bai taɓa gaya min komai da ya shafeshi ba. Sai a yau da muka iso an kaimu masauki kawai naci karo da fuskarsa matsayin mijinki. Bayan kuma ni sai a gobe zan gansa matsayin ogana bayan munzo wajenki. Kin san kuwa ruɗanin dana shiga Samraah. Har kusan faduwa nayi sai da Hayatu ya rikeni. Bayan sun bani ruwa nasha mun zauna a ɗarare Hayatu ya min bayani komai tun daga batun ɗaukar video har zuwa kidnapping ɗinki da mahaifiyar Mansoor tasa akayi, da karɓarki da yayi a hannunta sanadin bincike da yayi saboda kuɗi da aka nema a hannunsa da sunanki har 500m. Bayan ya gano bake bace amfani kawai ake son yi da sunanki ya kuma gano anyi kidnapping ɗinki shine ya kubutar dake. Yaso amsar video ɗin a hannunki lokacin kodan gudun kada ki sake shiga wata matsalar sai kikaƙi bashi. Sai kawai ya haƙura ya sake ki akan zai cigaba da bibiyarki har sai ya amsa dan in ba haka ba yasan wataran wani zai iya sake yunkurin cutar dake a kansa in har akasan da shi. Ya tabbatar mana shi ya kubutar dake daga auren Mansoor ne saboda kawai yasan bazaki taɓa samun farin ciki ba dan mahaifiyarsa da ƙanwarta ya tabbatar da zasu iya aikata komai akanki, yanda kuma basu samu kudin nan ba kema bazaki samu yanda kike so ba. Ko ran daurin auren da yazo ya biyo mahaifiyar Mansoor ne cikin ɓadda kama dan ya tabbatar tayi abinda auren zai fasu amma sai kawai tai abinda ya sashi tilas bayyana kansa garemu alhalin shi beyi niyyar hakan ba. Sai kuma kawai Kawu Musa ya masa ƙyautarki. Yace bazai iya watsama tsohon kasa a ido ba saboda sun bashi tausayi, koba komai shine ya saka auren rugujewa, idan bai amsa ba ai ya sake raunanasu kema kuma an cutar dake shiyyasa kawai ya amince. Sai kuma gashi auren shima ya zame masa alkairi, dan ya ce mana yanzu kin tallafi rayuwar mahaifiyarsa dake fama da jiyya shekara da shekaru. Nagode Samraah, Nagode matuƙa da kikayi haƙuri kika amshi ƙaddararki da hannu biyu, Nagode da kika kasance ɗiya ta ƙwarai, Nagode da kika cigaba da riƙe tarbiyyar ki. Dan tabbas naga tsagwaron jin daɗi a fuskar Maash game da ƙyautatama Mahaifiyarsa. Na tabbatar da koda a baya ba soyayya ce ta haɗaku ba yanzu kam yana sonki. Yana ƙaunarki, dan wannan alkairin naki ne muma ya jawo mana alkairin. Yanzu na fahimci dama Maash yaje garejinmu kai tsaye ne domin kawai ya ɗaukeni aiki, dan sai yanzu nake sake tariyo yanda aka ɗaukeni aikin cikin sauƙi ake kuma mutuntani da girmamani sama da ma’aikata da yawa. Gashi har an turani karatu wata ƙasa. Samraah tabbas ke ɗin alkairi ce. Gaba ɗaya halayen iyayenmu kin kwashesu. Dama ance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. tabbas na yarda da wannan batu na malam bahaushe”. Ya ƙare maganar yana share hawaye.
Da gani har Hafiz muma kukan muke. Dan labarin ya matuƙar girgizani. Ashe haka abubuwa suka faru ni ban sani ba. Ashe mahaifiyar Mansoor ce tasa akai kidnapping ɗin a da farko. To amma tayaya akai hakan? Da sanin Mansoor ɗin kokuma? Idan bada saninsa ba taya akai tasan da videon nan? Shiyyasa ba’a son zargi, na daɗe ina zargin Maash akan ɓata min aure dan shi ya aureni ya cutar dani ya amshi video ashe abin duk ba haka bane ba. Kai jama’a, lallai masu iya magana sunyi gaskiya da sukace zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya. Nagodema ALLAH da ban taɓa masa tambaya akan auren ba duk da nasha son yin hakan kwarjininsa da shakka na hanani. Sosai nake jin kimarsa na sake ƙaruwa a cikin zuciyata. Ashe shine ma ya kubutar da ni daga hannun mahaifiyar Mansoor. Kai ban taɓa zaton matar nan zata iya aikata irin wannan al’amarin ba. Wato mutum kai dai kawai gansa ka barsa yanda ALLAH yayisa, akan kuɗi baka iya banbance mutumin banza dana ƙwarai da wuri, dan sanin zuciya sai UBANGIJIN kawai……..✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐
……Sai ƙarfe kusan uku mijin Baby ya iso gidan cikin ƙatuwar motar da ta sake haukace imanin su Mom. Sam ita bama damuwarta rabuwa da ɗiyar ba. Sai santin motar suke da sake kambama irin dukiyar mijin Babyn. Faɗa ma ta yarda akai baby iyayenta na Gwarzo su mata batayi ba. Sai sake shiryata da akai ciki wata alƙyabba mai ɗan karan ƙyau. Itako ido ƙemaƙayau ba ko ɗigon hawaye. Hasalima inda kwalliyarta batayi ba gyara abinta take ko tace a sake mata kaza bata son kaza. Su dai su Gwaggo Gudidi sunyi sororo suna kallon ikon ALLAH.
Abba baya nan ya fita, dan baiyi zaton mijin Babyn zai iso a lokacin ba kasancewar yasha jira kafin azhar amma shiru. Sai Alhaji Jafaru babban ɗan Gwaggo Gudidi ya jashi suka tafi wata gaisuwa a gyaɗi-gyaɗi. Su Gwaggo Gudidi suna tunanin ai za’a jira Abban su dawo. Amma mi sai gani sukai an fito da amarya baby tana taku ɗai-ɗai ko irin rufe fuskar nan ta amare batai ba. Sai ma hirarsu suke da kakarta Umma suna dariya. Babu wanda aka kalla a cikinsu aka wuce da Baby ƙofar gida aka sakata a narƙeƙiyar motar da angon nata yazo a ciki. Abu mafi ban mamaki mijin ko kallonsu baiyi ba. Sai Mom ɗin da Umma ne suka gaisheshi yana amsawa cike da shan ƙamshi. Baki a washe Umma tace, “ALLAH ya tsare to Alhaji. ALLAH kuma yasa ku dawo lafiya da babbar tsaraba ta tattaɓa kunnena. Alhaji mu ya maganar tafiyarmu saudia ne?”.
Duk maganar da Umma take harararta Baby keyi, miye na wani tabbayar zuwa makka dan zubar da mutunci. Badai shine da kansa yace ya biya musu ba ai sai tayi hakuri taga lokacin yayi baice suje ba ko. Shikam ma ɗan mannin rainin wayon hannu kawai ya ɗaga musu a taƙaice ya ce, “A jira lokaci”. Daga haka ya ɗauke kansa tare da bama drivern sa umarni ko kallon amaryar tasa baiyi ba. Driver kam umarnin ogansa ya cika. Ya tada mota abinsa yay reverse har yana neman taka su Mom dake tsaitsaye. Ai tuni mutane suka shiga faman jinjina kawunan mamaki. Ƴan anguwa suka guntsa kowa da abinda ya fassara al’amarin. Dan kuwa dai sunga sabon salon ɗaukar amarya ganin idonsu.
Duk abinda ake Halime batama sani ba. Tana can tunda ta idar da sallar azhar ta kira Abba tace ya saya mata rake da gyaɗa tai kwanciyarta. Har aka tafi da Babyn kuma bata sani ba. Sai da hayaniya ta fara tashi ta ƴan gwarzo sannan ta farka…
💦🌟💦🌟💦
Duk yanda Hayatu ke ƙoƙarin danne abinda ke cimasa zuciya ya kasa. Sai satar kallonsa yake ta cikin mirror har suka iso babban companyn da Ummie ta fara ginawa da hannunta tun mahaifinta na da rai wanda Paah ne ke riƙe da ragamar komai na companyn. Ƙatone bana wasa ba, sannan akwai ma’aikata jingim a cikinsa. A farkon ginashi ana sarrafa kayan suturu ne, bayan abubuwa sun kwaɓe akan ciwon Ummie companyn ya durƙushe harma ya daina aiki na tsawon shekaru. Sai daga baya Maash ɗin ya farfaɗo da shi tare da sake faɗaɗashi aka maida shi wajen sarrafa kayan abinci. Kusan kowane nau’i na kayan abinci har su mai magi duk companyn na fitarwa. Suga, gishiri, harsu omo da sabulai sannan kayan abinci tun daga kan shinkafa, taliya, fulawa, garin alkama, da ire-irensu, da dangoginsu. A yanzu dai a Africa babu companyn dake fidda kayan masarufi irinsa gaskiya. Dan tako ina suna kai abinci kuma sunada wasu reshika a wasu kasashen da dama.
Duk ta inda suka gitta gaisuwar girmamawa ake bama Maash. Shi ko yana mai amsa musu a daƙilen nan nasa dan motsin lips ɗinsa kawai suke gani sai kuma hannu da yake ɗaga musu. Duk wanda yayma Maash farin sani a rayuwa yasan wannan halin nasa ba wulaƙanci bane yanayinsa ne kawai a haka. Dan magana inba ta zamar masa dole ba, da wahala kaga yana yinta. Idan ma yayin bazaka taɓa jin sautin muryarsa sama ba. Sai fa idan an ɓata masa rai yayi matuƙar iya hargagin da ke gigita mutum.
Kai tsaye office ɗinsa ya nufa Hayatu biye da shi dan shima yana da office a companyn. Har yanzu suna kan bincike game da case ɗin nan na samun yara a containers ɗin sa na kaya da suka tura Ghana. Monday ɗin nan zasu shiga court yau kuma zai sake zaman meeting da lawyers ɗin su da Paah, duk da dai kwata-kwata an nuna case ɗin bai shafesa ba duk da kasancewarsa shugaban companyn shiyyasa ma yake tsula tsiyarsa da matan da ake ɗauka aiki a ciki har Maash ɗin ya gano sa ranar yake tujara. Sun samu Paah ɗin baya nan, lawyers ɗin kuma basu kai ga ƙarasowa ba. Sai hakan ya bama Hayatu damar fidda abinda ke ransa.
Kallon Maash dake zaune cikin kujerarsa ta office ɗin yana daƙilar keyboard ɗin computer ɗin saman desk ɗinsa yayi. Sai kuma yayi ƙasa da kansa cikin girmamawa yace, “Yaya kamin afuwa, zan sake maimaita maganar nan dai ta kwanaki dana taɓa maka kaƙi cewa komai”.
Shiru kamar maash ɗin bazai amsa ba. Sai kuma can yace, “Uhumm ina jinka”.
Kai hayatu ya ɗan sosa yana sake ƙasa da kansa ya ce, “Nifa ALLAH yaya yau saina sake ganin kamanin Yayan Aunty sosai da Baba Abdull sun sake fitowa. Shi kuma ƙanin nan nasu Hafizzullah banbancinsa da Falaq kawai ita mace shi namiji. ALLAH tun ɗazu a ruɗe nake dauriya kawai nake yi. Ita kanta Auntyn yau sai naga suna fisgar kama da Falaq ɗin, kawai dan ita farace ita kuma aunty bata kaita has……”
Ruff bakin Hayatu ya rufe batare daya ƙarasa faɗa ba saboda kallon da Maash ɗin yay masa. Sai ya wayance da faɗin, “Yaya ALLAH ka duba lamarin nan iya gaskiyata nake faɗa”. Ya ƙare maganar cikin shagwaɓa kamar ba Hayatu PA ba. (Wato na lura akwai lokacin da Maash matsayin oga yake a wajensa. Akwai kuma lokacin da yaya yake😀).
Hararsa kawai Maash ɗin yayi ya ɗauke kansa ya maida ga aikinsa….
🩸🩸🩸🩸
“Ban gane mi kike son faɗa ba? Kin san dai bana son rainin wayo ko”.
“Wlhy yallaɓai babu rainin wayo a maganata. Kai ma kasan bazan yi hakan a gareka ba. Naje na samu nima ta sallameta. Kuma shi Awwab ɗin ne yaje ya sakata yin hakan”.
Wata shegen ashariya Yallaɓai ya kutuntuma. Sai kuma ya miƙe zaram yana kaima Centre table duka har sai da Hajiya ƙarama ta zabura tana ƙanƙame jikinta. Sai kuma ya juyi a fusace yana nunata da yatsa. “Idan har na samu matsala a aikina saboda ke na rantse da ALLAH sai na koya miki hankali”.
Sosai hankalinta ya tashi, dan tasan mugun nan komai zai iya aikatawa akan buƙatarsa. Amma ba komai lokacinsa ne. Zata bisa yanda yake so gaba kaɗan zatayi maganinsa ai itama. Dan ta gama shirinta a kansa tun shekarun baya. Murya ta sauke cikin nuna tsorata ta furta, “Kayi haƙuri nayi kuskure, amma na samo hanyar gyara kuskuren nawa. Na tabbatar bazai kaita ko’ina ba sai gida. Koda yake nama bincika an tabbatar min suna gidan. A wannan karon zan nuna abinda ya faru ina jin tausayinta na dawo da ita sashena. Kokuma na nuna zan share mata kukanta akan abinda ya faru ta hanyar nema mata makaranta ta cigaba. Da ganan sai musan abinda ya dace, kaga munma samu sauƙi”.
Shiru ya ɗan yi alamar nazarin maganarta. Sai kuma ya kai zaune yana mai jinjina kai. “Hakan ma yayi, sai dai ina mai gargaɗarki ki kiyaye. Dan bana buƙatar wata matsala kuma.”
“In sha ALLAHU babu abinda zai faru, shi mai bincike a kantan ya dawo ne?”.
“Zuwa jibi ne ƙarshen kwanakin daya ɗiba min. Dan ko jiya munyi waya da shi ya kuma tabbatar min da aikin na tafiya yanda zanyi farin ciki”.
Itama murmushin ta saki duk da ba haka taso ba. Dan a nata ɓangaren tasa itama a bincika mata wacece Samraah ɗin?.
✨✨✨✨
Gaba ɗaya ganin ƴan uwana ya wanke min duk wata damuwata. Hirarmu muke cike da farin ciki suna bani labarin cakwakiyar gidan Abba ta yanzu da amaryarsa, tare da yanda auren Baby ya kasance, sun dai baro ana jiran miji yazo ya ɗauke ta. Matsama Yaya Musaddiq nai ya kiramun aunty Zakiyya. Daga nan fa mukaita gaisawa da mutane harda amaryar Abba da kawai naji matuƙar ƙaunarta. Daga ƙarshe jikina yayi sanyi jin batun zuwan mijin Baby yanzu babu jimawa da yanda tafiyar ta kasance. Mun cigaba da jimanta abun bayan katse wayar. A haka lokacin sallar la’asar ya riskemu. Ina tunanin yanda zasu fita salla sai ga guard ɗinsa yazo yace suzo boss yace ya kaisu suyi salla. Kafin su dawo nima nayi tawa, na sake gyara sashen naje kuma na gano Ummie. Alokacin nake cema Mama Balki tazo su gaisa da bakin da yace. Ta ce tana zuwa idan ta kammala abinda take yi. Harta bani abinci na kai musu. Duk da sunci sun ƙoshi dan acan inda aka fara saukesu sunce sunci abinci, nan ma kuma da Hayatu ya rakosu da kayayyakin ciye-ciye suma mukaita ci muna hira sai da na ɗauka musu abincin. Sake zaman hirar mukayi, dan ji nake kamar mu dawwama a haka. Koda suɓutar baki ban sanar musu komai daya shafi gidan nan ba. Hirar abinda ya shafemu kawai mukeyi hankalinmu kwance. Hatta zancen alaƙar Mama Balki da nake zargi da baba ban gaya musu ba, shiyyasa ma na matsu tazo su gaisa. Dan duk wanda yasan mahaifinmu ya kallai Yaya Musaddiq yasan suna matuƙar kama, musamman yanzu da yake sake girma kamanin na sake fitowa sosai. Wajen ƙarfe biyar ina shirin zuwa na sake ganin Ummie da ga nan nayi kiran Mama sai gashi ya dawo. Sannu da zuwa su Yaya suka shiga yimasa da gaidashi. Ganin haka yasa nima na gaisheshi batare dana yarda na kallesa ba. Sai dai shi ina jin idanunsa na yawo a jikina, dan haka ma naƙi kallon nasa. Ciki ya shige yana faɗa musu bari ya ɗan watsa ruwa. Sukai masa fatan fitowa lafiya. Na gyara zama zan cigaba da hirata Yaya Musaddiq ya hararen, tare da mun nuni da ƙofar da ya bi.
Baki na tura cikin shagwaɓa nace, “Kai yaya mi kuma zanyi”.
Sosai yake kallona fuska a tsuke, “Oh kice karatun Mom kema kin ɗauka kenan?”.
Da sauri na shiga girgiza masa kaina. “Wlhy Yaya a’a”.
“Inafa a’a tunda gashi na gani da idona. Abba yakan dawo gida bai ishi Mom kallo ba. Kema ga mijinki ya dawo ko kallon inda yake bakiyi ba. Abba yakan dawo gida Mom bata bashi ruwa ba, ya shige yay hidimarsa. Kema kuma gashi mijinki ya dawo babu ruwa babu abinci, maimakon ki bishi kiji yaya ya dawo, miye matsalarsa kin gyara zama ke ga mai ƴan uwa sunzo ko. Haka kike so muma idan munyi aure matanmu suna mana?”.
Da sauri na sake girgiza masa kai idanuna na cika da ƙwalla. Ya ce, “Okay to aya maza tashi, haba Kandalata ina islamiyyan ya tafi? Mu kin bamu munci mun ƙoshi yan uwanki shi dake wahalar nema ko oho. Ko kina so Hafiz ya rainaki”.
Da sauri na sake girgiza kaina ina Hararan Hafiz ɗin dake kumshe dariya. Tashi nayi na nufi ƙaton freight ɗin dining room. Ruwa na ɗauka da lemo na sa a tray dana ɗakko a kitchen sai glass cup mai ƙyau. Ni sai ma naji abun banbara ƙwai wai namiji da suna Hajara. Haka dai na daure dan bazan taɓa iya bijirema Yaya Musaddiq ba…….✍️
🥱A fito lahiya matar yayanmu.
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
=========
…….A hankali nake tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki, koda na isa ƙofar bedroom ɗin na yi kusan minti ɗaya kafin nayi knocking a hankali. Banji motsin komai ba balle na saka ran za’a buɗe min. Hannu na kai zan sake knocking ɗin aka buɗe ƙofar. Da sauri na janye hannun nawa na riƙe tray ɗin da ƙyau kaina a ƙasa. Jin shiru ya sani ɗagowa a tunanina juyawa yay ya koma. Amma sai na gansa tsaye kawai ya zuba min cat eyes ɗin nan nasa. Sosai tsigar jikina ta tashi, dan wani irin kallo yake min mai wahalar fassara gashi da ga shi sai guntun towel iya gwiwa. Kaina nai ƙoƙarin sake saukewa cikin ɗan rawar harshe na furta, “D… dama ruwa ne…”
Bai bari na ƙarasa ba ya matsa min hanya alamar na shiga. Raɓawa nayi na wuce, kai tsaye na ajiye tray ɗin saman Centre table na buɗe ruwan na tsiyaya a cup tare da ƙoƙarin ɗagowa. Ido muka haɗa da shi, yana tsaye jikin mirror ƙafafunsa a harɗe yay folding hannayensa a ƙirji ya zuba min ido kawai. Ƙasa nayi da nawa, tare da takawa a hankali inda yake, batare dana kallesa ba na miƙa masa kofin ruwan. Shiru babu alamar zai amsa, dan haka na ɗago cikin yanayin kamar mai shakku na kallesa, har lokacin idanunsa a kaina suke, samun kaina nayi da marairaice face ɗina kamar zanyi kuka na ce, “Pleaseeee!”.
Ɗan luuuu yayi da idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya buɗe a kaina har sai da naji tsigar jikina ta tashi, hannuna dake riƙe da kofin ya ɗan fara rawa-rawa kamar zan saki kofin. Hannayensa dake harɗe a ƙirjinsa ya warware a kasalance, dan haka na ƙara ƙasa da kaina dan bazan iya kallonsa a yanda yaken ba. Jin saukar hannunsa a saman nawa mai riƙe da kofin ruwan ya sani lumshe nawa idon batare dana ɗago na kallesan ba. Ina ƙoƙarin sakar masa amma ya hana hakan, sai ma saukar ɗayan hannun nasa naji akan gefen cikina, a hankali ya fara tafiya da shi har zuwa bayana, kafin ya matsoni ya manne da jikinsa. Sannan ya kai ruwan da ke a cikin hannayenmu saman lips ɗinsa. Yasha kusan rabi ya zare kofin ya ajiye. Ni dai har lokacin ban sake yarda na kallesa ba. Sai dai na furta, “Nagode sosai Ya Awwab. ALLAH ya saka da alkairi, ya bama Ummie lafiya da tsohon rai mai albarka. ALLAH ya kareka da sharrin masu sharri. ALLAH ya yarda dakai”.
Jinai kawai ya ɗora ɗayan hannun nasa ta saman bayana shima ya mannoni da jikinsa gaba ɗaya ya kwantar da kaina a saman faffaɗan ƙirjinsa. Luff nayi ina mai shaƙar narkakken ƙamshinsa mai matukar tasiri da saka nutsuwa a zuciyar mai shaƙa. Munfi mintina biyar a hakan har wani bacci-bacci nake ji yana neman ɗaukata. Sai naji ya ɗagoni a slowly tare da juyamu na koma jikin mirror ɗin shi kuma ya koma inda nake da. Dagowa nai da nufin yin magana ya ranƙwafo ni gaba ɗayansa, daɓas na koma saman mirror ɗin na zauna, shi kuma yamun rumfa hannunsa ɗaya dafe da mirror ɗin, ɗayan kuma ya saukesa akan haɓata ya ɗago fuskata. Cikin matuƙar low voice ya furta, “Open your eyes”.
Jinai Sam bazan iya masa gardama ba, dan haka na shiga yin far-far da idanun kafin na buɗesu da ƙyar na saukesu akan ƙyaƙyƙyawar doguwar fuskarsa dake ƙawace da kwantaccen gashi baƙi siɗik. Kallon juna muke cikin ido da mu kammu bazamu iya fassara yanayin da muke a ciki ba. Sai wani irin tashi tsigar jikina keyi, a hankali a hankali idanuna suka fara tara ƙwalla. Kasa jurewa nayi na lumshesu slowly ina sauke tagwayen ajiyar zuciya. Dan mutumin nan zai kasheni da salonsa. A bazata matuƙar bazata naji saukar abu mai sanyi da taushi saman lips ɗina. Da sauri na buɗe idanuna. Ai babu shiri na maida su da gudu na kulle zuciyata na tsargawa. A salon da yake kissing ɗin nawa yasa gaba ɗaya jikina ya saki har ban san na kai hannuna saman kansa ba nariƙosa. Har ga ALLAH hakan da nayi kawai nayi ne amma bada wata manufa bane, tsabar na rasa ina zan dafa na samu sassaucin ruɗanin dana shiga ne yasa hannuna sauka a saman kan nashi batare dana shiryama hakan ba. Ashe shi hakan armashi ya ƙara masa, dan wajen kicin-kicin ganin na janyesa harda zame band ɗin dake ɗaure da gashinsa na tura yatsuna duk biyar cikin gashin ina yamutsawa. Munfi mintuna uku a haka, kafin ya janye lips ɗin nasa tare da ɗaura goshinsa saman nawa, hancinanmu na gogar juna, kowannenmu na sauke numfashi. Wajen minti ɗaya sannan ya ɗago kansa, kasa kallonsa nayi, sai ma hawayen da suka cika min idone suka ɗan silalo badan ni kaina nasan dalilina nayin su ba, gaba ɗayana ya jawo ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Nima samun kaina nayi da ƙanƙamesan dan jikina rawa yake yi.. nan ma mun kwashe wasu mintuna biyun a haka kafin ya kai bakinsa saitin kunnena cikin raɗa ya furta, “Kema baƙi ƙoshi ba ko? A ƙara”.
Ji nai kamar na tsaga jikinsa na shige dan kunya, sai kawai na sake ƙanƙamesa. Wani irin ratsa kunnena sassanyan sautin murmushinsa yayi a bazata. Sai kuma ya ɗagoni yana ƙoƙarin kallon fuskata amma naƙi yarda yay hakan….
A dai-dai lokacin da acan Maash da Sam-G ke a wata duniya anan falo Mama Balki ce ta iso domin gaishe da baƙi. Cikin fara’arta da kazar-kazar ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Amsawa su Musaddiq sukayi dama ransu fal tunanin ganin wannan uba-uban ƙaton gida amma basuga giccin kowa ba sai masu aiki maza. Ɗagowa sukayi su duka a tare da nufin gaisheta, kawai saita ja birki da uban sauri har tana buge ƙafa da kujera. Kallon Musaddiq take kamar zata cinyesa da idanunta, jikinta sai rawa yake yi. Sai kuma ta sake maida kallonta ga Hafizzullah shima. Sai kawai gani sukai ta fashe da wani irin kuka tana faman jan jikinta baya.
A ruɗe duk suka miƙe suna tambayarta lafiya? Mike faruwa?. Sam ta gagara basu amsa, sai sake cin tuntuɓe da tayi da carpet hakan yasata tafiya gaba ɗayanta zata faɗi ta baya suka hau salati da nufarta su duka biyun suka tare a tare….
Cak Maash ya dakata daga yunƙurin sake maida lips ɗinsa da yake saman na Samraah. Itama sai ta buɗe nata idanun da sauri duk suka kalla ƙofar. Dan su dukansu sunji salatin su Hafizzullah ɗin Kasancewar da ƙarfi sukayi. Kallonta yay, itama ta kallesa, sai kuma a hankali ya zame hannayensa da ga jikinta ya ɗaga gaba ɗayanta ya sauke daga saman mirror ɗin daya ɗaurata.
Zan nufi ƙofa da sauri ya riƙoni, fuska na marairaice masa kamar zanyi kuka. Sai yay min nuni da gyalena da ɗan kwali dake yashe a ƙasa. Gyalen kawai na ɗauka dan hankalina ya tashi, kada wani ya cutar min ƴan uwafa a gidan nan? Da wlhy sunga ainahin baƙin halina dan saina gallabi kowa da kowa har uban gayyar tasu bazan bari ba. Dai-dai ina isowa falon suke ƙoƙarin zaunar da Mama Balki a kujera, sai nai turus ina kallonsu. Ruwa Yaya Musaddiq ya bata, yayinda Hafizzullah daya juyo ya ganni yake sanar min abinda ya faru. Da sauri na nufi Mama Balki. Zama nayi a kusa da ita cikin damuwa ina tambayarta mike faruwa?. Dai-dai nan ya fito shima sanye cikin baƙar jallabiya da tai masa wani masifar ƙyau. Muna haɗa ido na kauda nawa da sauri.
Mama dake kallonsa itama fuskarta share-share da hawaye ta nuna masa Yaya Musaddiq. “Alhaji ƙarami dan ALLAH kalla bawan ALLAHn nan. Kalla yanda yake tsananin kama da Babanku. Inda ace mutum na mutuwa ya dawo da ƙuruciyarsa babu abinda zai sa bazan dage Abdul-wahab bane ya dawo Alhaji Ƙarami”.
Shiru kamar bazaice mata komai ba, sai kuma ya ɗan nisa a hankali tare da kaiwa zaune cikin kujerar dake facing ɗinta. Zaman ƙafa ɗaya kan ɗaya yay yana mai kwantar da kansa a jikin kujera tare da lumshe idanunsa. A haka ya furta, “Please Mama relax. Wannan ba Baba bane, dan Baba ya tafi ya barmu tafiya ta har abada.” ɗagowa yay da kansa ya ɗan zuba mana idanu mu duka sai kuma ya sake furzar da iska kaɗan yana ɗan mana nuni da Mama Balki. “Wannan matsayin uwa take garemu mu duka. Ban sani ba ko kun san Baba yana da mata a zamansa na Lagos harda yarinya ɗaya. Itace wannan”.
Da sauri Yaya Musaddiq ya kalla Mama, sai kuma ya juya ya kalla Maash ɗin. Sake gyaɗa masa kai yay cikin lumshe idanunsa tabbacin haka ɗin ne. Ni ko da Hafizzullah a ruɗani muke kallonsu. Gwarama ni dama na jima da wannan al’amarin a zuciya. Sai kawai mukaga Yaya Musaddiq ya duƙar da kansa yana hawaye. Kafin ya miƙe a hankali yaje gaban mama Balki ya tsugunna. Hannunta ya kamo cikin nasa hawaye na cigaba da masa gudu a fuska ya furta, “ALLAH na gode maka daka saka inada rabon ganin wannan rana kafin nabar duniya. Mama dan ALLAH kiyi haƙuri, kiyi haƙuri kiyi haƙuri. Tun daga randa nasan kaina, tare da labarinki a wajen Gwaggo Gudidi ban taɓa fashin addu’ar ALLAH yasa kafin nabar duniya na haɗu da ke da ƴar uwarmu da akace tana tare dake ba. A dalilinki sau biyu ina zuwa Lagos bayan na tuhumi iyayena akan kuskuren da sukayi suka nuna min nadamarsu suma, sai dai dan basu san ina zasu ganoki ba suma shiyyasa suka cigaba da zama da damuwar a rayukansu. Tabbas mama an cutar dake. Muma kuma an cutar damu, tunda da mun sanki na tabbatar bazamuyi kukan rashin iyaye a duniya ba. Dan ALLAH mama kiyi haƙuri ki yafema ahalinmu kada hakkinki ya cigaba da hanasu kwanciyar hankali a rayuwarsu. Kuskure ne sukayi a wata gaɓar da mu kammu bamu tsira ba. Dan mu ɗin ma komai sai da ya ƙwaɓe tsawon shekaru tsakaninmu dasu babu wani jituwa sakamakon amsata da ƙanin mahaifiyar mu yayi ya riƙe bai bar musu ba, duk da dama tun raduwar mahaifiyarmu ita Samraah da Hafizzullah suna a hannunsa ne. To nima sai yace zan koma hannunsa, amma suka nuna basu amince ba suma su Samraah sai a dawo musu da su. Kowa ya fahimci gadon da aka barmana sukemawa shiyyasa dangin mahaifiyarmu suka dage shine akai rabuwar tashin hankali suka manta damu sai da ga baya naita bibiyarsu har komai ya dai-daita. Zamma iya cemiki dawowarsu garemu sosai-sosai lokacin amsar kuɗin auren Samraah ne”. Kuka yaci ƙarfinsa………✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓
……Muma kukan muke ni da Hafiz sosai. Hakama Mama kuka take har tana siƙewa. Sai da ya mana magana cikin gyaran murya sannan kowa ya ɗan tsagaita. Cikin yanayinsan nan na rashin son hayaniya ya furta, “Kuka ba shine alama ta godiyar ALLAH ba. Abinda ya faru ya riga ya faru, ku fuskanci wanda yake a yanzu itace rayuwa. Ya kamata bayan magrib itama Falaq kuje can dan ta ganku tunda tana fama da kanta bazata iya tazo nan ba. Gashi babu wani lokaci shi Musaddiq zai wuce gobe in sha ALLAHU”.
Duk mun gamsu da zancensa, yayinda Mama ke jinjina kai ta ce, “Alhaji Ƙarami dama kasan inda suke kenan? Shiyyasa ka auro Samraah?”.
Ɗan luuu yay da idanunsa kamar abin dole ya saki murmushi. Babu wanda ma yay zaton zai amsa a cikinmu saboda yanda ya jima baice komai ba. Sai kuma ya ɗan furzar da iska cikin sauke numfashi. Kansa ya girgiza a daƙile ya furta, “A farkon ganina da ita ban san ita wacece ba. Ban kuma taɓa kawo wani abu game da ita ba. Sai dai sunanta ya ɗan so ya ja hankalina har ya tunamin da Baba a ranar. Abubuwa ne da yawa suka faru da suka alaƙanta wannan auren Mama, dan har ga ALLAH ni banje da nufin ɓata mata aure ni na aureta ba. Kawai na hana wancan ne dan na kuɓutar da ita daga halin banza na mahaifiyarsa. Sai kuma Uncle nata yace ya bani, naso kawo musu wani dalili sai kawai naci karo da fuskar Musaddiq nima a lokacin, shine kawai nace na amsa. Bayan barina wajen kafin a ɗaura auren na saka akamin bincike shine na gano su ɗin yaran Baba ne”.
Sosai kowannenmu ke jinjina iko da hikima ta UBANGIJI. Hafizzullah da bai fahimci komai ba a zancen yay tambaya. Nice na masa bayani. Sai kawai ya hau murna wai muma ashe munada Mama. Abinda yay ɗin ne ya sakamu darawa mu duka. Hatta shi uban gayyar ina kallon sanda yay ɗan munafukin murmushin nan nasa dai-dai yana miƙewa. Ciki ya koma ya barmu anan da Mama. Aiko sai labari ya ɓalle a tsakaninmu, dan Mama wayayyar mace ce mai kuma tsananin kirki da dattako. Fita tayi sai gata tazo da Malam Baba. Mahaifin Hayatu kenan, mijinta kuma a yanzu, aminin mahaifinmu. Shi kansa ya shiga mamaki matuƙa, ya kuma yi farin ciki da ganin ƴaƴan amininsa. Duk da ya jima zuciyarsa na masa wasi-wasi a kaina ashe. Shiyyasa tun ranar farko daya ganni agidan yake kallona. Dan duk da bana kama da Babanmu, gaba ɗaya komaina na mahaifiyarmu ne idan ka cire ɗan duhun da nake da shi dan mahaifiyarmu farace tass, su su yaya Musaddiq duk sun ɗakko farinta amma kamanin Baba. Maganar aure kuma dake a tsakanina da Maash ya sani Hayatu ya faɗa masu dama.
🌺🌺🌺🌺
Ganin har gab da magriba bai sake fitowa ba munata hirarmu da Mama a falo Yaya Musaddiq yay min nuni da hanyar bedroom ɗinsa cikin hikima. Jinai duk kunya ta gama kamani, sai dai bazan iya musa masa ba. Dan haka na tashi sum-sum na wuce. Yanzun kam ban tsaya knocking ba na murɗa handle ɗin ƙofar a hankali na shiga kaina a ƙasa. Dan har yanzu ina jin nauyi da kunyar abinda ya faru a tsakaninmu ɗazun. Jin ɗakin shiru kamar babu motsi ya sani ɗan ɗagowa ina kallon ko ina. Sauka idanuna sukai a kansa. Yana zaune a cikin sofa sanye da bathrobe alamar bai cire ba tunda ya fito wankan, bowl ne na glass a saman cinyarsa da uban chocolates a ciki. Da mamaki nake kallon chocolates ɗin kafin na ɗan ɗaga idanuna akan fuskarsa. Da farko na zata ma barci yake a hakan, sai da naga gashin idonsa dogaye sosai sun ɗan motsa alamar kallona yake ƙasa-ƙasa. Kauda nawa idanun nayi kamar zan juya naji ya furta, “Zo nan”.
Idanuna na ɗan rumtse, dan duk sanda saukar muryarsa zai shiga cikin kunnuwana sai na jisu har tsakkiyar brain ɗina. Sai da na ciza lips da sauke numfashi sannan na juya kaina a ƙasa na nufesa. Ban zauna a kujerar da yake ba doguwa sai na zauna akan ɗayar dake gefensa dan guda uku ne dama. Doguwa ɗaya sai biyu masu zaman ɗai ɗai a gefe da gefen ta.
“Mi kike buƙata?”.
Ya faɗa a daƙile yana kai sauran chocolate ɗin hannunsa ƙaramin bakinsa. Satar kallonsa nayi ina mamaki a raina, namiji da cin chocolate, ai kayan yara ne da mata, duk yau banga ni dai ya ci abinci ba, sai dai ko da suka fita yaci. Ganin ya zuba min ido na ɗan girgiza masa kaina da faɗin, “Ba komai, kawai na jika shiru ne baka fito ba. Ga kuma abinci duk yau naga baka ci ba”.
Shiru bai tanka min ba tsahon kusan mintuna biyu, kafin ya ɗago a nutsensa zaune sosai tare da ajiye bowl ɗin chocolates ɗin nashi a Centre table. Murya can ƙasa ya ce, “Gashi ina ci”. Yay maganar yana nuna bowl ɗin chocolates ɗin. Da mamaki na ɗago idanuna sosai na warosu a kansa. Tare da furta, “Chocolate ne abinci? Abin kwaɗayin yara ne fa. Kai kuma ƙatoto da kai ka zauna kana ci, kuma amma ce fa maza basa cin zaƙi hak…..”
Ganin yanda yake kallona da mayatattun idanunsa na kasa ƙarasawa, sai ma na miƙe cikin wayancewa na ce, “An kira magrib bari na shirya kar su zo suna jirana”. Na wuce bayi da sauri.
Da kallo ya bita harta shige, sai kuma ya girgiza kansa shima yana miƙewa zuwa closet ɗinsa yin shirin massalaci.
💕💕💕
Bayan sallar magrib Hayatu da kansa yazo ɗaukarmu. Ogan nasa bai dawo ba. Amma tunda shi yace zamuje dama sai ban damu ba na shirya tsaff cikin atamfa riga da skirt a kayan daya kawo min. Ni da Hafizzullah da Mama a baya, Yaya Musaddiq da Hayatu a gaba. Yanda naga bakinsa yaƙi rufuwa saboda farin ciki nasan Mama ta gaya masa komai ko mahaifinsa. Nayi matuƙar mamakin ganin ƙayataccen gidan da shima yake a ciki. Sai na sake yarda da batun Mama Balki da tace su suna zaune a Maash Mansion ne kawai saboda Ummie. Shine gaba muna biye da shi, sosai ta ciki ma gidan yay ƙyau da tsaruwa. Sai da muka zauna ya kwala kiran mai aikinsu wata ƴar budurwar yarinya ta fito. Gaishemu tayi sannan ya bata umarnin kawo ruwa da abinci shi kuma yay sama. Babu jimawa sai gashi ya fito riƙe da ƙyaƙyƙyawar matashiya, gaskiya zata iya girmata koda shekara uku ne, da ƙyar take tafiya saboda cikin jikinta da yay girma sosai. Duk da fuskarta ta ɗan yi fushi irin na masu ciki hakan bai ɓoye kammaninta da Hafizzullah ba. Yanda muka zuba mata ido haka itama ta zuba mana nata. Lokacin da suke isowa gab da mu jikinta har rawa yake yi. Haka ta dinga bimmu ɗaya bayan ɗaya da kallo, kafin ta maida kan Mama da ke kallonta itama fuskarta ɗauke da murmushi. Cikin langaɓar da kai ta ce, “Mama ina ji a jikina su ɗin jinina ne. Dan ALLAH Mama kada kuce dani ba haka bane ba. Yaya Hayat yace bazai faɗa ba sai dai na gani da ido na”.
Murmushi mukayi mu dukanmu, kafin Mama ta gyaɗa mata kai. “Tabbas su ɗin jininki ne Falaq. Ga babban yaya Musaddiq, sai Samraah ban ƙanwa, sai auta Hafizzullah”.
Kuka ta saki a hankali idonta akanmu muduka ta ce, “Wlhy yaya kamar Baba, suna kama sosai”. Ta faɗa tana sake fashewa da kuka mai ban tausayi. Gaba ɗaya muka miƙe muka rufu kanta. Yaya Musaddiq akwai son ƴan uwansa, tuni ya janye ta daga jikin Hayatu ya kamata ya zaunar a kujera, gabanta ya durƙusa cikin lallashi yake mata daɗaɗan kalamai. Sai ta fara dariya ga hawaye. Ganin haka nima na zauna a kusa da ita na shiga share mata hawayen nata. Sai ta haɗamu ta rungume, tare da miƙawa Hafizzullah hannu alamar shima yazo. Ta ɗayan gefenta ya zauna shima muka haɗe kai waje guda muka bar Mama da Hayatu ƴan kallo. Mun jima a haka kafin Mama su dinga lallashinmu. Sallar isha’i data gitta ya samu miƙewa, mazan suka fita mu kuma mukayi anan gida. Koda suka dawo sabon babin hira muka buɗe, Yaya Musaddiq da Mama nata bamu labarin Baba. Dan Hayatu fita yayi wai Maash ya kirashi akwai inda zasu je. Banyi mamaki ba, dan sukam ko aljanu haka suka gansu suka barsu saboda shegen yawonsu. Sai naji tausayin Falaq ya kamani, haka take haƙuri (kema haka zakiyi haƙurin) zuciyata ta ayyana min. Da mama ke sanarma Falaq ɗin ni matar Maash ce a yanzu wani irin ihun farin ciki ta saki tana rungumeni, koba komai ƴar uwarta ta dawo kusa da ita. Tsaff suka bata labarin yanda komai ya faru, ta dinga farin ciki da ƙorafin Hayatu ita bai sanar mata ba. Kamar wasa sai ga lokaci yaja. Dan sai da sha biyu tayi sannan Hayatu ya dawo, shine yake cewa ga Maash a waje yana jiranmu. Kuka Falaq ta sanya wai anan zamu kwana, ita bata gaji da ganinmu ba. Cikin dariya Hayatu yace, “Nikam babu ruwana Hubby, keda yayanki jeki gashi can”.
Aiko miƙewa tai tana ɗaukar mayafina, itako Mama Balki ta miƙe tana faɗin, “A’a nidai kam nayi nan”. Dariya muka sanya mata, dan muma ba son tafiyar muke ba, saboda hirar bata ishemu ba. Sai addu’a nake a zuciyata ALLAH yasa ya yarda. Kusan mintuna biyar sai gata ta dawo tana tuttura baki. Mayafina ta cire ta miƙamin tana faɗin, “Ya yarda da ƙyar su Yaya su kwana anan ɗin, amma wai ke kije lil sis…”.
Ɓata fuska nayi nima kamar zanyi kuka. Nace, “Amma baki roƙesa ba ko Aunty?”.
“ALLAH har kuka na masa. Kin san taurin kan Yayana kuwa. Idan yace a babu mai canja masa zuwa b. Cayay da ma wai idan na haihu zaki zo. Bama gobefa kenan”.
Dariya Hafizzullah ya fashe da ita, harara na balla masa da ɗaukar mayafina fuuu na nufi hanyar fita…
Shima dai Yaya Musaddiq da ke riƙe dariyarsa da Hayatu sai da suka dara, kafin su miƙe subi bayanta.
Sanda suka iso ina tsaye jikin motar ta saitin inda yake ina masa magiya amma ɗan mannin bai ko buɗe idonsa dake lumshe ba ya kallan bare ya tanka. Haushi da takaici ya sani balla masa harara na koma ta ɗayan side ɗin dan Mama ce a gaba kusa da TJ, da sauri TJ ɗin dake a waje ya buɗen ƙofar yana wani risinawa. Ko kallonsa banyi ba na shiga na zauna na juya ƙeyata. Koda su Yaya Musaddiq suka iso wajen inaji yana magana da su wai ƙanwarsa ta masa fin ƙarfi shi da baƙi ita da ƙwacesu su kwana. Ina jin yanda suke ƴar dariya da bashi haƙuri. Basu wani jimaba yace ma TJ muje Mama ta gaji. Suna min sallama ƙin kallonsu nayi, ina jiyo dariyarsu su duka ukun sai naji idanuna sun cika da ƙwalla……..✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
*_Typing📲_*
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
__𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ 𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty five…
Tun a balcony ɗin take faman jera manya-manyan ashariya wa Maash. Koda ta afka bedroom ɗinta gaba ɗaya ta kasa haƙuri saboda yanda zuciyarta ke mata hanƙoro. Wai mi yaron nan ke shirin maidasu? Ƴan iska ko mi? Yanzu har Ummu-Hidaya ta haifi abinda zaifi ƙarfinsu kenan. Yarinyar da aka haifa a gabansu, balle shi karan kaɗa miya. Kai wlhy bazai yiwu ba. Dole ne ta ɓaro aikin da dolema ayita ta ƙare a gobe. Ina dalili Rubayya ta sakata aikata abinda ke neman juyewa da ita. Banda yaron nan ƙwallon ɗan iska ne ka haikema yarinya amma ka koma kana wani abubuwa irin ga matarka ɗin nan kayi first night ko. To wlhy daga daren yau zuwa gobe sai ta tada hankalin kowa na gidan nan sai dai anyita ta ƙare. Munafukai kowa yayi shiru da bakinsa irin komai ma bai faru ɗin nan ba. Waya ta jawo, ta shiga daddanawa. Number baba prof ta kira. Sai da ta kusa tsinkewa ya ɗauka cikin alamun wanda ya fara barci. Kuka ta fashe masa da shi a maimakon sallama. Cikin tashin hankali ya shiga tambayarta abinda ke faruwa?. Amma taƙi magana sai kuka. Sai da ya mata tsawa cikin tashin hankali kafin ta fara magana tana jan sheshsheka. “Baba wace irin ƙazamar rayuwa kuma ke neman zuwa mana gidan nan. Mun shiga uku Awwab ya ɓalle. Baba kaga kuwa abinda na gani yanzun nan. Ya gama lalata wata gata can kwance a asibiti gashi can kuma yaja wata sashensa zai ƙara. Kuka yarinyar take tana roƙonsa amma bai barta ba. Har magana nayi masa amma ya hauni da zagi, wai bamun damesa yay aure ba, to haka zaita haye ƴaƴan mutane har ƴaƴanmu ma su jira zuwansa. Mu kammu idan bamu kama kammu a gidan nan ba sai layi ya biyo ta kanmu. Baba wlhy Awwab ya gama iskancewa, yaro ya tambaɗe ya lalace, kai ko jinin turawa na yawo a jikinsa. In baiyi bama ai bai cika jikan sifanawa ba (Spain 😂). Wayyo Baba mun shiga ashirin watan zubewar mutuncinmu yazo a duniya. Ƙilama a wannan karon har bbc saita bugamu…” A rikice Baba yay mata tsawa, dan gaba ɗaya ta gama ruɗar da shi yama kasa yin tunanin daya dace. Ƙitt ta yanke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya. Dariya ta sanya cikin yanayin basanci ta ce, “A’a badai nice ba. Ai sai kaci baban uwarka Alonso Awwab. Gobe-gobe sai ka zama mijin Azizat ɗina. Kwantar da hankalinki ƴar albarka kukanki na kusa sharesa, nima kuma burina ya kusa cika.” ta sake ƙyalƙyalewa da dariya…….✍️
*_Typing📲_*
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
__𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty six
🌿❤️🌿❤️🌿
Ni a karan kaina ban san iya adadin kukan da naci ba. Dan gwara waccan ranar daga ƙarshe suma nayi, yau kuwa har ma fata nake ko zan suman na samu sassauci amma sumar taƙi zuwa. Azaba iya azaba da kwantata badai baki ba. Ban sani ba, ko hakan ya faru ne dalilin ina cikin tsoro da kuma ban gama farfaɗowa a waccan baƙar wahalarba oho. Duk da a yau komai yana yinsa gently ne ni banga wannan gentle ɗin ba sam. Kuka na gidan duniya na shashi har ina jin idanuna kansu sun min wani uban nauyi. Roƙo magiya harda cizonsa nayi amma bawan ALLAHn nan sai da ya kai inda yake buƙata. A Bathroom ma wani sabon kukan na sha, amma sam baiji tausayina ba sai da ya tabbatar ruwan zafin ya ratsani sosai yanda ya kamata sannan ya taimaka min na tsaftace jikina. Yanda ya ɗaukeni da kansa ya kai haka ya sake ɗakkoni ya maido saman gadon. Da ƙyar na amshi magani daya bani, ina gama sha ya kwantar dani, bamma san barcin wahala yay awan gaba dani ba. Dan tun ina jinsa sama-sama yana salla har nayi barcin ban san ya dawo saman gadon ya kwanta ba sai asuba…. ★★ Yanda Maash bai bari sunyi wani barcin kirki ba a wannan daren haka mafi yawan iyayensa basu runtsa ba. Hajiya Mammah dai na sake ƙulla abinda zata zo da shi gobe idan ALLAH ya kaimu. Paah na cikin tashin hankali da damuwa tare da nadamar abinda yake aikatawa. Dan shi kawai zuciyarsa na bashi TSUTSAR NAMA CE TA ZAMA NAMA. Ɓarnar da yake aikatawa ce tai naso wa gudan jininsa. Shiyyasa masu iya magana ke cewa ƊAN GADO HAR YA ZARTA. A wannan gaɓar kam ya yarda. Dama ance zina na bibiyar jini, idan kayi da ƴar wani sai anyi da taka. To shi bashi da ɗiya mace, shine ALLAH ya jarabci ɗansa babba da wannan ta’asar da ƙila zata zama sanadin tashi fallasar shima. Harga ALLAH bai taɓa fyaɗe ma kowa ba, amma fa tun yana secondary school ya fara neman mata. Saboda irin rayuwar da suka tashi, rayuwar turai. Uwa babu kwaɓa uba ba tsanani. Dan Ummansu nada faɗa, amma gasu ƴaƴanta soyayyace ziryan take musu. Garama mahaifinsu, yakan ɗan yi faɗan idan yaga abubuwan sunyi yawa. Shi kansa bai san adadin matan dayay mu’amala da su ba a rayuwarsa. Tun ma yanayin mai aji har gashi ya koma mu’amala da mai aiki. Dan da Siyama kawai yake mu’amala a gidan, hasalima ya santa ne tun kan ta fara aikin, koma yace saboda shi ta dawo aiki gidan, dan tace suyi aure yace a’a, shine ta zagaya ta samu aiki a gidan sai kawai ganinta yayi. Ya shiga matuƙar shock a lokacin, amma da yake ƴar duniya ce sai da ta maida shi ruwa a kanta duk da kuwa shi in har ya mu’amulanci mace ya rabu da ita da wahala ya koma. Amma akan Siyama sai tarihin ya canja, dan ta rantse masa in har yay sanadin data bar gidan sai ta tona masa asiri, shiyyasa ma ya barta saboda ya fahimci yarinyar hatsabibiya ce kwarai da gaske. Amma yau sai gashi ɗansa nayin yanda yaso a cikin gida batare da kunya ko shakkar wani ba. Ita ko Hajiya ƙarama tashin hankalinta kada ace Maash ya sake haikema ƴar gaban goshinta Samraah ne. Har bayi ta shiga ta gwada kiran Mama Balki sai kuma ta fasa, saboda tunawa da Mama Balki nada miji fa. Ita dai damuwarta kawai kada Maash ya sake taɓa mata yarinya. Acan Uncle Abdullahi da matarsa sun shiga wasi-wasi. Dan su zukatansu sun fara nusar da su anya kuwa ba magauta bane suka asirce Maash ɗin ke wannan irin ta’asar babu kunya babu tsoron ALLAH a cikin gida kamar wata rayuwar kafurci. Kai da sakal fa. Yaron nan na buƙatar manyan malaman ruƙuya a kansa. Ita dai Maman Malika ma harta fara batun maida Malika Niger sai abubuwa sun dai-daita. Idan har abinda Hajiya Mammah ta faɗa Awwab ɗin ya faɗa to lallai basuga ta zama ba kuwa. Dole abar gidan da ƴammatan yaran nan guda huɗu zankaɗa-zankaɗa. (😂Yayanmu kaga idi. Kowa zai fara killace ɗansa saboda kai🌚, wannan aiki yayi tsamari🤣). A ɓangaren Baba prof shima ba barcin daɗin ran yayi ba. Dan ya jima ma bai runtsa ba bayan ajiye wayar da yayi. Har gwada kiran wayar Maash yay amma ba’a ɗauka ba (😂ina zai ɗauka kuwa kandala ta kanainayesa, danginta na murna an kwace mana Yayanmu🥶). Haka ya dinga kai-kawo kamar mai Safa da marwa, sai da yaji ƙafafunsa na neman sagewa ya haƙura ya kwanta. Aiko asubar fari ya miƙe dan ko’a barcin nasa mafarkin Maash ɗin kawai yake yi ya haikema yarinyar mutane (kuji masifa🥱. Yo banda sa kai a uku kai tsoho ina ruwanka😝).
🩸🌟🩸🌟🩸
Saukar iska mai sanyi akan idanuna ya sani buɗesu a hankali dan sun min nauyi jingim saboda kukan dana sha. Ga barci da nake ji matuƙa dan sam ɗan wanda nayi bai wadaceni ba. Dishi-dishi nake ganin abinda ke gab da ni, cigaba da huramin iskar ya sani ƙarasa buɗe idanun sosai. Fes suka shige cikin nasa da sukai wani irin fitowa blue sosai, hakama golden ɗin daya ratsasu ya sake yin garai-garai tamkar zinare na ƙyalli a cikin glass. A hankali na ƙoƙarin sake maida nawa zan kulle saboda wani irin kunya ne ya baibayeni. Cike da karsashi ya ɗaura soft hannunsa saman fuskata yana sake matso da tasa fuskar gab da tawa, har hancinmu na gogar juna. Da silent muryar nan tashi mai fita acan ƙasan maƙoshi kamar abin dole ya furta, “No! Baby. Open your eyes”. Baki na taɓe kamar zanyi kuka. Cikin shagwaɓa da ban san ni kaina nayi ba na ce, “I’m not baby”. Sake manne fuskarsa da tawa yayi, tare da sake maida muryarsa can ƙasa ya ce, “Yes you are not ni shaida ne”. Yanda yay maganar yana kai hannunsa saman jikina da sauri na saka nawa na ɗan buge nasan ina sake ɓata fuska zan saki kukan. Na kuma janye fuskata da ga jikin tasa na juya baya. Zafin da naji ya sani sakin ƴar ƙaramar ƙara. A hankali ya kwanto ta bayana duk da ma ya rufeni gaba ɗaya ƴar tsitt dani a jikin nasa. A cikin kunnena ya furta, “Still Pain?”. Maimakon amsa kuka na sakar masa. Sautin murmushinsa naji a cikin kunnena, sai kuma ya saka hannunsa a saman fuskar tawa ya shafo hawayen. Hannuna nasa na ture nashin in ƙara ƙarfin kukan. Baice komai ba ya miƙe, har nayi tunanin ya barni ne sai naga ya zagayo ta gabana. Duvet ɗin da nake ciki ya yaye, tare da duƙowa ya ɗagani gaba ɗaya. Luff na kwanta a jikinsa tare da lumshe idanuna. Sai da muka shiga bayin na buɗe ganin yana ƙoƙarin cewa zai min wankan ma. Da sauri cikin shagwaɓa na ce, “Ni ka fita zan iya”. “Kin tabbatar?”. Ya faɗa cikin tsatstsareni da idanu. Kaina kawai na jinjina masa. Shima sai baice komai ba ya juya ya fita, yana gab da ƙarasa ficewar ya ce, “Ki tabbatar kin shiga ruwan nan”. Daga haka ya ficewarsa. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, ni ba haushinsa nake ji ba. Tausayin kaina kawai nake ji, in dai haka zata cigaba da faruwa wlhy na kaɗe har ganye na. Dan al’amarin sam bashi da sauƙi. Ban cuci kaina ba na nutsu na gyara jikina yanda ya kamata, kamar kuma yanda Mama Balki ta koya min hakama Doctor. Sai kuma naji na ƙara jin nutsuwa. Wanka nayi na ɗauro alwala. Cikin sanɗa da jan ƙafa na fito. Naji daɗin ganin babu kowa a ɗakin, sai doguwar riga mara nauyi da hijjab dana samu a saman sofa. Ɗauka nayi cikin sauke ajiyar zuciya na saka dan har shida da wasu mintuna. Sallar asuba nayi, koda na idar duk yanda naso yin karatun Alqur’ani kasawa nai, anan inda nai sallar na ɓingire barci. Bamma san ya shigo ya ɗagani ya maida a saman gadon ba……….✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛_* _(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ 𝑷𝒂𝒈𝒆twenty- seven.
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛_*
(Itama nama ce)__
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆 _𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty-eight
…….Tsuru-tsuru kawai sukayi suna bin ƙofar da kallo, sai Hajiya Mammah ce ke zazzaga masifa cikin borin kunya. Dan sosai maganarsa ta ƙarshe ta wani irin shigarta. Ganin kallon da Baba prof ke mata yasa ta miƙe. Murya a ɗan zafafe ya ce, “Koma ki zauna Nafisa”. “Amma Baba kana fa jin abinda ya faɗa min, wlhy sai naci uwar yaron nan a gidan nan. Yanzu har lalacewar wannan gidan takai kamar Awwab ya gaya min baƙaƙen magana a gaban Mu’azz amma yay kamar baima ji ba. Ba shi ba hatta uwarsa a gabana aka haifeta.” Cikin damuwa da ɗan ɓacin rai Paah ya ce, “Amma Adda mi kike so nace muku?. Duk dai mai hankali yaji wannan furucin na Muhammad zai fahimci akwai wani abu a tsakaninku ke da shi. Tabbas Muhammad bashi da ragowa, kuma in ransa ya ɓaci komai yazo bakinsa faɗa yake, amma tunda muke da shi bai taɓa maidama wani murtani ba a cikinmu sai yau. Duk kuwa abinda kiga Muhammad ya magantu a kansa to lallai wannan abun ya kai karen kure. Kuma ni kam gaskiya zuwa yanzu zuciyata ta fara bani akwai abinda yaron nan ke ɓoye mana, inda ace abinda ya faru a farko ne kawai zan iya yarda ƙaddara ta kaisa ga aikatawa. Amma muyi tunani, Muhammad fa duk da tsagerancinsa bazai zauna yana lalata yara ba irin haka a cikin gidan nan, dan duk da mahaifiyarsa na’a halin rashin lafiya bai haɗa mutuntakarta da komai ba. Mudai ƙara bincike gaskiya. Domin mu dukanmu mun san waye Muhammad”. Da ga haka ya miƙe abinsa ya fice shima. Shiru falon yay babu wanda ya iya motsawa. Sai Hajiya Mammah dake wani irin cika da batsewa da famar jinjina kai. Ta bakin baba prof kowa ke son ji amma babu alamar zai ce wani abu. Sai ma miƙewa da yay shima ya fice a binsa. Ganin haka shima Uncle Abdullahi da Matarsa suka miƙe. Wani irin shegen murmushi Hajiya Ƙarama da ke kallon Hajiya Mammah ta ƙasan ido ta saki, sai kuma ta mike itama batare da tace komai ba ta fita. Dan ta ciki na ciki ne kawai…..
🪴🪴🪴🪴
Watanni huɗu kenan Mamy na gida, babu labarin Mansoor tako ina. Gashi Dad baizo gida ba kuma kowa bai sanar mata ya saketa ba ko bai saketa ba. Gaba ɗaya ta fige ta rame saboda damuwa. Dan har ga ALLAH tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Ta tura masa text message yafi sau dubu. Ta kirashi yafi sau dubu goma. Amma babu amsa babu reply na masseges ɗinta. Ga ciwo ya addabeta a tsaitsaye har dai sai da ta kaita da kwana asibiti ranar. ALLAH sarki Attahiru shine tsaye akan komai. Ganin fa yanda jikin Mamy yay tsamari a wannan karon yaje ga Dad ɗin su ya dinga kuka yana roƙonsa ya yafe mata, sannan ko sau ɗaya yazo ya ganta. Dan sam Mamy bata a cikin hayyacinta. Babu abinda take faɗi sai neman gafarar Dad ɗin. Da farko Dad koran Attahiru yayi, sai da yaga yanda ya riƙe ƙafafun nasa yana rabzar kukan abin tausayi sannan. Dan har ga ALLAH a yanzu tausayin babban ɗan nashi yake yi. Attahir akwai haƙuri, gashi da son ƴan uwansa. Ga biyayya a gare su. Yanzu tunda aka fara abin nan yazo neman ma Mamy afuwa ya masa gargaɗin kada ya sake masa maganar ta bai sake koda kwatantawa ba duk da abin na damunsa. Amma kullum dare yana lura da shi sai yaci kuka. Haka kuma zaita salla yana neman ɗaukin UBANGIJI da yima Mansoor addu’ar ALLAH ya karesa a duk inda yake. Shima sai hakan yaja hankalinsa yake tashi yin ibadar daren. Yanzu da yake roƙonsa duk sai jikinsa yay sanyi, kamashi yay ya rungume. Sun jima a haka kafin ta ɗagosa yana lallashi. Ya kuma tasashi gaba suka je asibiti suka duba Mamy. Abinda Dad ɗin yayi ya faranta ran kowa. Dan duk wanda yasan Mamy yasan ta horu da horonsa matuƙa. Wannan zuwa na Dad shi ya kawo masalaha ga ciwon Mamy, ta dinga jin sauƙi har al’amura suka fara daidaita. Koda aka sallameta sai suka koma gida. Nan ma ta cigaba da roƙon Dad ɗin gafara yaran suka tayata har sai da yace mata ya yafe mata. Ya kuma kafa mata sharuɗa da dokoki. Ko guda ɗaya kuwa bata musa ba a ciki. Doka ta farko data fara bi shine shiryawa sukaje har gidan Abba suka bashi haƙuri tare da neman gafarar Abban da sauran mutanen Gwarzo da basu wuce ba da su Gwaggo Gudidi. Sun so ganin Yaya Musaddiq aka sanar musu ai ya wuce Chaina yau ne ma ranar tafiyar tasa zai bi ta Lagos. Abin ya basu mamaki. Sun kuma tayashi murna. Sun kuma yi alkawarin zuwa weekend zasu je har gwarzo domin bama su Kawu Musa haƙuri, dan su tunda suka zo aka ɗaura aure da su suka kama gabansu tunda bikin bana ɓangaren su bane ba. Wannan ban haƙuri da su Mamy suka zo sukayi har gida ga ƙonama Mom rai, dama ga baƙin cikin tafiyar Yaya Musaddiq na cimata zuciya. Har ta kasa haɗiyewa sai da tai ta zabga habaici. Da yake dama Abba a ƙufule yake da ita akan tafiyar Baby basu bari ta masa sallama tama danginsa ba ya ce idan har Mom ta sake cewa ko uff a bakin aurenta. Dan ya tsinke sauran igiyoyin biyu da suka rage. Wannan magana ta matuƙar girgiza Mom da duk danginta. Nan fa suka shiga tausarta da nuna mata kuskurenta. Daga nan akayi zaman sasanci aka sakata bama Abban haƙuri da su Gwaggo Gudidi….
🌜🌜❤️🌛🌛 ki
Tunda ya shigo ɗakin yay tsaye kawai yana kallonta nannaɗe a ƙasa kamar ƴar mage. Barcinta take hankali kwance. Kaɗan ya ɗan jaa idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya buɗe. Durƙusowa yay ya ɗauketa gaba ɗayanta ya maida a saman gado, kafin ya shiga ƙoƙarin zame mata hijjab ɗin. Firgigit ta buɗe idanunta dake jajur duk sun ɗan kumburo alamar anci kuka an gode ALLAH. Sosai ƙirjina ya shiga bugawa da sauri-sauri ganin yanda ya ranƙwafo kaina, zaram nayi ƙoƙarin tashi jikina na rawa, sai dai zafin daya ratsani ya sani komawa da sauri na kwanta hawaye na ziraro min. Cikin ɗan jujjuya masa kai, lips ɗina da suka sha wahala a wajensa na rawa muryata a ɗashe na ce, “Please Ya Awwab don’t do wahala for me again. Wlhy zan iya mutuwa. I’m just 23years only zakai child abuse fa”. Shiru bashi da alamar cewa uffan, sai idanunsa masu tsananin kaifi da ya zuba min kawai kamar zai cinyeni da su. Cikin kuka sosai na sake buɗe baki zanyi magana ya ɗaura yatsarsa manuniya akan lips ɗin nawa yana mai sake matso da fuskarsa gab da tawa ya ce, “Shiii! Oya sleep”. Ya ƙare maganar can cikin maƙoshi da ɗaura hannunsa ya rufe idanuna. Babu musu na rufe ɗin duk da a cikin tsoro nake. Tun ina ɗari-ɗari har wani barci mai daɗin tsiya yay awan gaba da ni saboda yanda yake shafa kaina a hankali. Ganin yanda ta fara sauke numfashi a hankali alamar tayi barci ya sashi yin ɗan guntun murmushi. A hankali ya furta, “You are a tiger, Samrh”. Sai kuma ya sake sakin murmushin gefen baki saboda tuno kalmar child abuse data faɗa. Sam yarinyar nan bata jin magana. Ga baki kaman parrot. Vibration ɗin da wayarsa keyi alamar shigowar kira ya katsesa da ga kallon da yake mata. Dan kallon wayar yay dake a kan side drawer. Sai da ta kusan tsinkewa kamar abin dole kafin ya kai hannu ya ɗauka. Ɗagawa yay ya kai kunnensa yana ƙoƙarin barin wajen. Koda Juliet da tai kiran ta gaishesa a taƙaice ya amsa mata. Bata damu ba ta fara masa bayani kan aikin da ya sakata. Ta tabbatar masa ta kammala komai yanzu haka jirgin da zai taho da shi ya ɗakko hanyar Nigeria. Cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara ya lumshe idanunsa dake canja launi. Shi kaɗai ya san mi yake ji a zuciyarsa, amma zai jure in sha ALLAHU. Sunayin sallama kiran Hayatu na shigowa. Gaisawa sukai shima sannan ya bama su Yaya Musaddiq suka gaisa. Kasancewar tafiyar ta Musaddiq sai dare ma ya bama Hayatun umarnin zagayawa da su suga gari zuwa anjima sai ya kawosu nan. Dan yau shi bazai fita ko ina ba zai yini a gida. Murmushi Hayatu yayi da ga can, amma duk da haka sai da ya tambayesa ko baida lafiya. Dan yasan abinda zai iya hana ogansa kuma yayansa fita ba ƙarami bane. A taƙaice yace masa no kawai ya yanke wayar, Hayatu ya jima shiru yana nazari sai kuma yay ƴar dariya. Anya kuwa! Anya ogan nasa bai faɗa lobayyar pepper ƙanwar tasu ɗin nan ba. Rashin mai bashi amsa ya sashi haɗiye komai ya cigaba da sabgarsa. Shi kam koda ya kammala wayar shiru yay a cikin kujerar lafe na kusan mintuna ashirin, kafin ya miƙe a hankali ya bi ƙofar dake sadashi da Ummie, ko’ina fes sai ƙamshi yake, ganin kwanikan abinci ya sashi tabbatar da har ta karya. Kusa da ita ya ɗan zauna ya shafa kanta dan barcinta take hankali kwance. Ga wani irin annuri da fuskanta keyi ƙyawunta da dauɗa ya dusashe na sake fitowa. Hawaye ne ya cika masa idanu, amma sai ya haɗiye su dan ƴan mazan maza ne akoda yaushe. Ya ɗan jima a ɗakin har Mama Balki tazo ta samesa duk da yanda kansa ke juya masa da ciwo. Bayan sun gaisa yana ƙoƙarin danne damuwarsa da ciwon da kansa ke masa yay mata bayanin a saka cikin yaran can wasu su gyara sashen Fahad. Yana gama faɗa ya miƙe da sauri ya fice a ɗakin kamar wanda ake tunzurawa. Da kallo Mama da har tsigar jikinta ke tashi da jin wannan batu ta bisa. Sai hawaye sharrr suka shiga ɓulɓulo mata, ga murmushin farin ciki. Wani irin ƙaunar Samraah na ratsa mata zuciya. Yarinyar nan ta cika alƙawarinta kenan. Dan dama ta mata alƙawarin sai ta masa maganar dawowar Fahad ɗin gida. Kasa haƙuri tayi sai da ta koma ta sanarma mijinta. Shima farin cikin ne ya dabaibayesa har murmushi ya gagara barin fuskarsa. Ranar da wannan farin cikin suka yini, tuni kuma an saka masu aiki gyaran sashen Fahad dake manne dana Maash ɗin batare da kowa ya sani a gidan ba. Dan su suna can ma ran kowa ɓace da abinda Maash ɗin ya musu yau……..✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛_* _(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
_𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty-nine…
🪴🌼🪴🌼🪴
Tunda ta iso asibitin ta gagara taɓuka komai. Sosai abinda ya faru a gidan keta mata faman kai kawo a zuciya. Kalaman Awwab sun farkar da ita wasu abubuwa. Tabbas sau biyu tana kama Hajiya Mammah ta fito a sashen Awwab, na farko ranar da ta aiki Yarinyar nan da abinci, na biyu daren ranar da abin ya faru kusan misalin ƙarfe ɗaya ta fito daga ta backyard kamar wacce ke a firgice. Abinda yasa a lokacin bata maida hankalinta a kanta ba itama daga wani waje ta dawo. Abu na uku Hajiya Mammah ta damu akan zancen fyaɗen nan a safiyar ranar, sannan jiya ma itace tazo musu da zancen ga Awwab da wata. Da farko bata damu ba, sai yau da safe data bincika yarinyar nan a sashen masu aiki akace mata bata dawo ba ai. Bata samu damar ƙarasa binciken ba Baba prof ya iso gidan.. Mikewa tai tana mai girgiza kanta, dolene taje ta ƙarasa binciken data fara kafin wankin hula ya kaita dare. Daga nan tana buƙatar yin magana da Yallaɓai a wannan gaɓar. Handbag ɗinta ta ɗauka ta fice a office ɗin. Ko kallon tulin patients ɗin dake zaman jiranta batai ba dan hankalinta ma baya a kansu gaba ɗaya…..
✨💞✨💞✨
Barci sosai nasha. Dan ban tashi farkawa ba sai wajen sha biyu. A hankali na buɗe idanuna bakina na ambaton sunan ALLAH da karanto addu’ar tashi a barci kafin na yunƙura da ƙyar na tashi zaune saboda ciwon da illahirin jikina ke mun. Sam banyi tunanin yana a ɗakin ba, dan haka na miƙe cikin ƙarfin hali saboda wani irin fitsari nake ji sosai. Wani irin motsawa zuciyata tayi sakamakon saukar idanuna a kansa. Zaune yake cikin sofa kamar wani saraki. Laptop ɗin jarabar a saman ƙafarsa sai dai ya saka throw pillow sannan ya ɗaurata. Ta gefensa a saman side table ɗin kujerar bowl ne da chocolate a ciki sai mug alamar ansha coffee ko tea. Ledojin chocolate ɗin da yaci ya zubar a ƙasan na bi da kallo, haka kawai sai naji tausayinsa ya kamani. Dan abinda na fara fahimta da shi kamar bai damu da cin abinci ba sai waɗan nan tarkacen kayan chocolate ɗin. Tabbas koda ace bai son cin abincin akwai ƙarancin gatan mai tsayawa ya bashi ya ɗin.. ganin ya ɗan dakata da danna keyboard ɗin computer ɗin alamar yaji a jikinsa ana kallonsa ya sani saurin kauda idanuna da ƙoƙarin son barin wajen, a ko dai-dai nan ya ɗago manyan idanunsa ya sauke a kaina. Basarwa nayi kamar ban gansa ba na wuce bathroom ɗin. Ina shiga na jingina da ƙofa ina mai sauke ajiyar zuciya mai nauyi da godema ALLAH da ya taimaken bai kamani ina kallonsa ba. Wanka nayi da ruwa mai ɗumi sosai na sake gyara jikina yanda ya kamata, dan har ruwan zafin na shiga. Yau banyin walha ba ina barci, alwala nayi dan naga har sha biyu da kusan rabi yanzu. Hankalina duk yana akan su Yaya Musaddiq shiyyasa ban zauna wani noƙe-noƙe ba na fito sanye cikin bathrobe ɗin sa sky blue. Inda na barsa anan na samesa. Sai da na zo gab da shi ya ɗago kai ya kallan. Murya a sanyaye alamar nasha kuka batare dana kallesa ba na ce, “Ina yini”. Bai amsa min ba, sai idanunsa masu azabar kaifi daya zuba min. Ji nai duk ina neman daburcewa, dan haka nai ƙoƙarin barin wajen amma sai ya miƙa min hannu alamar nazo. Jinai kawai bazan iya musa masa ba, a hankali na fara takawa zuwa garesa, ɗan nesa kadan da shi na tsaya kaina a ƙasa. Soft hannunsa ya ɗaura akan nawa da nake wasa da su ya matsoni gabansa sosai, a bazata na jini zaune a saman cinyarsa alamar ya ajiye laptop ɗin da pillow ɗin. Sake matsoni yay cikin jikin nasa ya rungume tsam har ina iya jin bugun zuciyarsa kaɗan-kaɗan. Luff nayi wata nutsuwa na ratsani. “Yaya jikin ya daina zafi?”. Ya faɗa cikin silent muryansa a cikin kunnena. Sosai kunya ya sake ƙamani, maimakon amsa masa sai na sake ƙanƙamesa ina ɓoye fuskana a jikin nasa. Kaɗan naji yunƙurin murmushin sa cikin ƙirjinsa. Shiru kusan mintuna biyu ya sake furta, “Kona duba ne?”. Kafaɗa na maƙe masa da faɗin, “Uhm-uhm” cikin shagwaɓa ina ƙoƙarin tashi. Amma sai ya hanani yin hakan, hannayena ya kama cikin nashi ya zubama fuskata ido sosai yana kallo. Kasa kallonsa nayi ni dan bazan iya jurewa ba sam. A hakan ma ji nake kamar na gudu. Sake maida muryarsa ƙasan maƙoshi yay da kai hannu a haɓata ya ɗago fuskata da ƙyau ya ce, “Look at me”. Da ƙyar na iya ɗago idanun na kallesan. Cikin ɗan ɗage gira ya ce, “Shin bakin ƴar mutan Gwarzo ya mutu ne kwana biyu?”. Bakin na ɗan tura masa kaɗan. Girarsa ya ɗan ƙara ɗagewa da jinjina kai ya ce, “I see, bai mutu ba ashe. Yanzu idan su Ya Musaddiq suka zo mi zaki ce da su ya samu wannan idanun da ya kumbura?”. Karan farko na ɗago na kallesa. Idanun nawa ya sarƙe cikin nashi, kallon juna muke cikin wani yanayi mai wahalar fassara. Jin yanda tsigar jikina ke tashi jinina na yamutsawa ya sani lumshe nawa a hankali. Murya ƙasa-ƙasa kamar mai koyan magana na ce, “Zan ce kai ne”. Na ƙare maganar in ɗan buɗe idanuna kaɗan. “What a surprise, ni ne fa? To nayi me?”. Ai babu shiri na buɗe idanun gaba ɗaya ina harararsa da tura baki. Sai kuma na yunƙura zan tashi ina ƙunƙuni. Sake maidani yay ya zaunar ya ce. “Answer me”.Shagwaɓe fuska nayi ina kaucema kallonsa na ce, “Ni dai ba ruwana. Ka sakan na saka kaya na je na ga Ummie na”. Ɗan lumshe idanunsa yay ya sake buɗewa, sai kuma ya ɗan sauke numfashi, kamar wanda ke shirin sakin murmushi ya ɗan taɓe baki. Yatsun hamnuna dake cikin nasa ya ɗan matsa da murza farcen. “Shi wannan hannun yaushe za’a masa lalle?”. Hannun na kalla nima, sai kuma a hankali nace, “Ai babu lalli ne. Da dai nasan su Yaya zasu zo da sunzo min da shi. Kuma ma ina son wanke kaina ya fara cushewa.” Kansa ya jinjina min alamar amsawar kenan. Nima sai nai ƙoƙarin miƙewa. Taimaka min yay na tashi, ina shirin barin wajen shi kuma zai maida laptop ɗin sa a ƙafa ya ce, “Mi zaki ci?”. Kallonsa na ɗan juyo nayi muka haɗa ido, sai kuma na kalla ledodin chocolates ɗin da yasha batare da nayi magana ba na nuna su. Idanunsa ya ɗan ƙanƙance a kaina. Sai kuma ya girgiza min kai a daƙilen nan nasa. “Kince ba abinci bane ai”. “To kaima ai shi kake ci”. “Humm”.Kawai yace ya maida kansa ga wayarsa daya ɗauka. Ganin ya kai kunne alamar wani ya kira ya sa na wuce abina dan na shirya. Ban wani jima ba na fito cikin skirt da riga na atamfa. Sosai kayan sun min ƙyau tare da fiddo ainahin surar jikina. Ni kaina sai da na sakarma kaina murmushi ta cikin mirror. Dauri nayi mai sauƙi bayan na shafa turarensa da mansa. Koda na juyo sai na samu ni yake kallo shima. Da sauri na ɗauke kaina kunya na kamani. A ɗan daburce nace, “Zanje can sashen na ɗakko kayan kwalliyana Please Ya Awwab.” Sai da ya maida kansa ga aikinsa kamar bazai kulani ba kafin a hankali ya ce, “No”. Baki na ɗan tura batare dana sake cewa komai ba na nufi gadon. Tsaff na gyarashi, na tattare net ɗin. Dai-dai nan shima ya miƙe ya shiga bathroom. Babu jimawa ya fito alamar yin alwala………✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛_* _(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
__𝑩𝒐𝒐𝒌 3 _𝑷𝒂𝒈𝒆- thirty.
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛 (Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-one.
🪴🪴🪴🪴
Su amarya Baby an isa ƙasar California lafiya. Sai faman iyayi take da wani yauƙi ita a dole ga amarya. Ƙalubale na farko data fara fuskanta a wajen angon nata shine tun a airport ya sakata a taxi wai taje zai ƙaraso. Ya bama mai taxi address ɗin hotel ɗin daya riga yay booking musu tun kafin su iso. Hankalin Baby ya ɗan tashi, amma dai tai ƙoƙarin dannewa tunda yace mata uzirine daya shafesu. Batasha wahala ba kasancewar ta samu mai jiran isowarta cikin ma’aikatan hotel ɗin. Da alama dai mijin nata sananne ne a wajen. Sai ta sake jin kanta ya fasu sama sosai. Wani irin santi da sambatu ta dingayi ganin irin katafaren ɗakin da aka kawota, gashi ya jiƙu da kayan alatu. Dama tun a wajen hotel ɗin take faman sambatu a zuciyarta. Sai da ta gama taɓe-taɓenta da kalle-kalle da santi sannan ta kwanta barcin gajiya, babu batun salla ko duba lokaci, dan a cikin jirgi ko tuna tashi tai salla batayi ba. Yanzu kuma sun sauka maimakon tayi ƙoƙarin ramawa ko’a jikinta. Wankan ma tunda ta shiga tai fitsari taga ta kasa amfani da kayan bathroom ɗin shiyyasa ta haƙura. Tayi nisa a barci sosai aka tasheta. A firgice ya buɗe ido babu addu’a babu komai ta mike zambar tana ƙoƙarin ɓarka ihu. Tsawa ya mata da zabga mata harara da manyan idanunsa. Sosai tsoro ya kamata da ganin yanda duk kamaninsa suka canja. Idanunsa sunyi wani irin jazur kamar ba mijin nata ba. Har ga ALLAH ba wani sonshi take ji ba, kawai kuɗinsa da zigar su Mom yasa ta amince da aurensa. Ta kuma gama shiryama ranta da shawarar ƙawayenta zaman shekara biyu zatayi da shi ta tara abinda ta tara tasa ya saketa ta samu dai-dai da ita yaro mijin wuce sa’a ta aura. Da ƙyar ta danne wata irin tsanarsa da ta sake ji na tsarga mata. Dan komawar idanunsa jajayen nan sai ya sake fito da tsufarsa. Duk da kuwa a fuska ƙyaƙyƙyawane, sai dai ƙaton cikin nan ya masa cikas da tsufa daya fara taso masa. Ɗan murmushi tayi cike da wayancewa da danne abinda ke ranta ta faɗa jikinsa ta rungumesa tana zabga masa kalamai wai tayi missing ɗin sa. Shiru bai rungumeta ba, bai kuma tureta ba, har sai da ta gaji dan kanta ta ɗago. Matsawa yay daga gaban gadon yana ƙoƙarin cire kaya. Da sauri ta kauda fuskarta, dan tulelen cikinsa kamar na mace mai cikin ƴan uku dake gab da haihuwa. Tas ya gama sannan ya nufi hanyar bayi daga shi sai boxer. Yana gama shigewa ta sauke ajiyar zuciya. Itako taga takanta, wai tayaya zata iya dauriyar bin shawarar ƙawayenta? Tuna burikanta ya sata sauke numfashi. Tana nan zaune abin duniya ya isheta sai gashi ya fito. Yanzu dai towel ne a jikinsa. Zaram ta miƙe tana faɗin, “Bara nima nayi wankan to, dama gajiya tasa banyi ba na kwanta kawai ga yunwa kuma ina ji”. “Okay”. Kawai yace mata ya cigaba da harkar gabansa. Da ƙyar ta iya samu ta kunna shower tai wankan, cikin son ta birgesa ta fito da ɗan guntun towel. Tako birgesan, dan duk inda tayi biye yake da ita da kallo kamar tsohon maye musamman bayanta. Bayan ta gama shiryawa cikin ƙananun kaya kamar yanda shima ya zuba ƴar shara da wando ta dawo kusa da shi ta zauna. Kamar abin arziƙi suka ci abinci tare tana faman masa shagwaɓa ita a dole ga amarya. Sai da yaci yay nak abinsa yay miƙar ƙoshi sannan ya miƙe a wajen. Barci ya ɗan fara figarsa a kujerar tana jikinsa akai kiran wayarsa. Janyeta yay ya tashi ya fita, kusan mintuna goma sai gashi ya dawo.. Da kallo ta dinga binsa, dan abinda aka ɗirka mata sai tsikarinta sukeyi. So take ko ɗan taɓata yayi, amma mutumin nan bashi da wannan niyyar. Ganin fa wankin hula zai kaita dare ga shi tun a yau take son fara tatsar kuɗaɗe dan Mom taci bashi sosai a bikin nan wajen shirya mata ɗaki tana son ta tura a biya kada asirinsu ya tonu. Tashi tai tsam ta nufi gadon da taga yaje ya kwanta. Cike da shagwaɓa ta faɗa masa a jiki. Shiru yay yana kallonta, itako babu kunya babu kawaici ta fara masa abubuwa. Barinta yay tai kiɗanta tai rawarta, kafin shi kuma ya fara maida mata murtani. Abinka da wadda tasha kayan iri-iri harda wanda bai kamata abama amarya irinta farin shiga ba. Gaba ɗaya ta gama sallama masa har bata ma san mi take ba. Hankalinta ya matuƙar gushewa taji kawai yana ɗaɗɗaureta. Da mamaki take kallonsa. Sai ya sakar mata makirin murmushi. Bata iya ta maida masa ba, dan a yanda ya kifata rufda ciki ya ɗaure ɗin ya sokar mata zuciya. Kafin ta samu damar neman ba’asi ya bita ya taushe. Duk da bata wani nutsu tayi islamiyya ba sosai hanyar da mijin nata ke neman bi a jikinta ya matuƙar firgitata. Cikin tashin hankali ta shiga tambayarsa mi yake sonyi haka? Abinda yake son aikatawa fa haramunne, taya zai yi ƙoƙarin mu’amalatar ta ta baya kamar wasu aladu. Ko kallo bata isheshi ba, tana ji tana gani ya aikata saɓon ALLAH da ita, maimakon bin hanyar da ALLAH ya halatta masa yabi wadda ya harta masa. Babu kuma tausayi babu imani sai da yay mata fata-fata. Tun tana kuka da roƙonsa da magiya harta ma suma dan azaba. Gashi ya ɗaureta duka hannayenta da ƙafafu babu damar koda kare kanta ne…..
❤️🔥✨❤️🔥✨❤️🔥
A ɓangaren Baba prof koda ya koma gida a jiya yaso bama al’amarin lokaci dan yay nazari, sai dai hakan na neman gagararsa. Washe gari duk da uziririn dake gabansa bai iya fita a gidan ba har kusan sha biyu na rana, dan ya kwana da tunane-tunane ne ya tashi dasu. Wayarsa ya ɗauka har ya danna kiran number Maash sai kuma ya yanke yana mai girgiza kansa. Akalar kiran ya maida kan Hajiya Mammah. Harta tsinke ba’a ɗaga ba wai tana waya. Sake kiran yay dan bazai iya jira harta gama ta kirashi ba. Yanzun ma tana wayar, sai dai kuma tana gab da katsewa aka ɗaga. Cikin bada umarni ya ce, “Nafisa ki sameni a gida yanzun nan”. Daga haka ya katse kiran. Shiru kawai Hajiya Mammah da tun jiya abin duniya ya isa tayi tana bin wayar da kallo. Ita bata motsaba ita bata ajiye ba. A haka kiran Hajiya Rubayya ya shigo mata. Da ƙyar ta iya ɗagawa takai kunnenta. Daga can cikin zumuɗi Hajiya Rubayya ta ce, “Miya faru? Ya kukayi da Baban?”. “Ca yay na samesa a gida. Ni kuma bana jin zanyi hakan Rubayya. Dan ban san mizan ce da shi ba, kin dai san halin Baba akan ɗan iskan yaron nan”. “Uhm uhm kar kice haka kije. Ai idan kikaƙi zuwa zai ma yarda da abinda ya faɗa kenan. Wannan fa wata gaɓace da zamu kama mu riƙe. Dan ita kawai ta rage mana yanzu. Dan haka tashi kije. Ki kirani ina jin abinda Baba ke faɗa zan dinga faɗa miki amsar da zaki bashi”. Matuƙar yarda Hajiya Mammah tama Hajiya Rubayya. Dan haka bata kusa ba ta miƙa ta hau shirin tafiya. Ta fito cikin takun nan nata na isa da taƙama sai dai daka ganta kasan ranta a ɓace yake. Gaisheta ma’aikatan gidan keta faman yi cike da girmamawa. Sai dai gaba ɗaya hankalinta ba’a garesu yake ba. Dan dai-dai nan ɗaya daga cikin ƙosassun motocin Maash da ba kasafai yake fita da su ba sai abu mai muhimmanci ta shigo, sai motar guards ɗinsa ɗaya biye da ita. Da farko ta ɗauka Maash ɗinne ya fita yake dawowa, sai da aka buɗe motar taga wanda ya fito a ciki tai tsaiwar sojan badakkare kamar wadda ta suma a tsaye… A hankali black beauty matashin saurayin dogo mai tsananin kammani da su Paah sai dai idanunsa sak irin na Maash ya wani yamutse fuska da bin gidan da kallo. Sam gidan baya wani birgesa a zahirance. Amma acan ƙasan ransa yana jin kewar Ummien sa da son kasancewa da ita. Matsala ɗaya ke masa katanga da yunƙurin zuwa gareta, ɗan uwansa. In har Yayansa na waje komai buƙatar da yake ma wajen shi bazai taɓa iya kasancewa ba. Dan yana jin kamar ya soka masa wuƙa ko ɗaukar bindiga ya harbe masa kai kawai. Sai da ya gama ƙarema gidan kallo batare da hankalinsa ya kai kan Hajiya Mammah ba ya ɗauka side bag ɗinsa irin ta maza matasa masu ji da gayu ya saka. Kansa tsaye babban ƙofar sashen ya nufa, dan sai ya fara zuwa yaga Ummiensa kafin ya ƙarasa sashensa. Yasan dai yanzu su Paah duk basa gida suna office……..✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛_*(Itama nama ce)__
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-two
🌛🌜❣️🌛🌜
Ya ALLAH🙏 Wanda ke da rabon shiriya a masu ɗakkowa, da masu yaɗawa, da masu jiran a ɗakko su karanta a matsayin bati, ya UBANGIJIN al’ashi. Ya mai RAHAMA da jinƙai. Ya mai fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Nayi tawasalli da sunayenka masu tsarki, waɗanda ka kirayi kanka da su ka kuma sanar damu, da wanda ka barwa kanka saninsu ka keɓancesu gareka. Nayi tawasalli da ɗan gatan nan naka, wanda kace idan muka so shi, mukabi abinda yazo mana da shi na shiriya ka gafarta mana. Ina roƙonka ka shiryar dani da su. Ya rabbi kafisu sanin wahalar da nake sha a yayin rubutun nan. Nakan hana kaina barci domin sauke hakkin masu saya a lokacin da su suke barcin, nakan yini da ciwon kai, ina fama da ciwon idanu, ina fama da ciwon yatsu. Ina fama da ciwon baya. Wataran nakan wayi gari banama jin farin ciki ko sha’awar rubutun, wataran na tashi da uzirin baƙi ko fita. Amma duk nakan kuntata kaina domin naga nayi. Idan har ban kasance na cutar dasu da komai ba a rayuwarsu, ya rabbi! ya rabbi! ya rabbi!! ka shiryar dasu su guji taɓa hakkin daba nasu ba. Ka shiryar dasu su guji ɗaukarma kansu nauyin da zasuyi dana sani a ranar da ake fansa da lada da zunubi. Ya rabbi ka gafarta mana kurakuranmu. Ka shiryar damu, ka nisanta mu ƙuntata zuciyar kowa koda kuwa dabbace. ALLAH kasa mu samu sauƙaƙƙen hisabi batare da an jinkirta mana ba saboda hakkin wasunmu da mukaci a duniya. Dan ALLAH, dan ALLAH. Dan girman ALLAH mu saukaƙama kammu kunji bayin ALLAH. Ni kaɗai nasan a yanayin da nake wannan rubutun musamman a ɗan tsakanin nan, kada ki bari UBANGIJI ya kamaki da laifin hakkina nima bazan so haka ba. Dan bana son akai gaɓar da zan iya tashi tsakkiyar dare domin miƙama UBANGIJINA ƙararki ko ƙararka. Dan ALLAH, dan ALLAH, dan ALLAH. In har da gaske ke masoyiyar MANZON ALLAH ce kina fatan tashi a tawagarsa ranar da kowa ke fatan hakan, idan har da gaske kin yarda da mutuwa da ranar hisabi, idan har kin yadda wannan rubutun hakkina ne ALLAH zai iya cirar min hakkina a jikinki, idan har kin yarda ban taɓa cutar dake da komai ba, idan har kina fatan kema ALLAH ya kiyaye hakkinki ko hakkinka, ku daina ɗakkowa a inda na killacesa, ki daina yaɗawa, kema ki daina karantawa. Wannan itace maganata ta farko kuma ta ƙarshe in sha ALLAHU, ALLAH ya yafe mana kurakuran mu baki ɗaya.🙏
🪴🪴⭐🪴🪴
Ran Baba prof a ɓace yake kallon Hajiya Mammah dake gaishesa. Bai amsa ba, sai nuna mata agogon dake falon nasa mai shegen ƙyau da ɗaukar hankali yayi. “Kalla time, sai yanzu ne kike zuwa bayan tun 12 da wasu mintuna nai kiranki Nafisa?”. “Kayi haƙuri Baba. Wlhy na fito zan taho sai ga Fahad. Bamma ko tsaya ya ganni ba na taho dan kar kaita jirana. Wlhy duk a tsorace nake, kada su sake ƙoƙarin ƙona mu a cikin gida kamar wancan karon. Ban san wace jaraba ce ta dawo da yaron nan ba ana zaune lafiya.” Ɗan jimmm na wucin gadi ne ya riski Baba prof.. kafin tamkar mai koyon magana ya ce, “Wai wane Fahad ɗin?”. Cikin rashin damuwa Hajiya Mammah ta ce, “Fahad namu mana Baba. Wlhy gashi can ya dawo abinsa. Abinda ma dai ya ɗan bani mamaki shine ganin a motar fitinannen ɗan uwan nasa aka ɗakkosa. Ko sun shirya ne bamu sani ba. Idan ma hakanne ta kasance ai mu abin farin ciki ne a garemu, dan wlhy tsoron tashin hankalin nan nasu nake suzo wataran su ƙonemu ƙurmus mu da gidan kana dai ganin wancan karon da ƙyar muka sha suka so sakamu a tara. Kai ai nikam wannan jini na Ummu-Hidaya ai ba’a cewa komai. Bala’i kala-kala daga wannan sai wancan”. Yanda Baba prof yay shiru da alama ba fahimtar zantukan Hajiya Mammah yake ba ma shi. Dan sai da ta ɗan kai hannu ta taɓashi sannan ya dawo firgigit. Murmushi yayi zai yi magana dai-dai nan akai knocking ƙofa. Tsaki Hajiya Mammah tayi tana hararar ƙofar dan tasan bai wuce ma’aikatan gidan ba. Cike da wulaƙanci ta bada izinin a shigo. Ilai kuwa cikin ma’aikatan ne. Kansa a ƙasa da girmamawa ya kai durƙushe yana sanarma Baba prof yana da baƙo. Agogo Baba prof ya kalla, cikin ɗan ɓacin rai yace, “Bani da apartment da kowa yau, koma su waye a sanar musu suje sa dawo next time”. Kai hadimin ya jinjina. Har zai miƙe sai kuma ya koma ya durƙusa. Kansa a ƙasa cikin ɗari-ɗari ya furta, “Ranka ya daɗe Commando ne fa, kuma kaine kace ko baka gidan nan yazo nemanka a sanar da kai”. Cikin masifa Hajiya Mammah ta juya zata fara danna masa zagi Baba prof ya dakatar da ita. “Uhmm Nafisa kinga barshi umarni na ne. Kinga jeki gida kawai idan na gama da shi zan zo na sameki. Komi ke faruwa ki dinga sanar dani ta waya. Sannan kiyi ƙoƙarin Mu’azz da Abdullahi su dawo gida gudun tashin hankali, idan kuma Awwab baya a gidan ki sanarma Mu’azz ya hanashi komawa gani nan zuwa yanzu nima”. Maganar yake yana tafiya, dan haka kafin ma ta bashi amsa har ya shige hanyar da zata sadashi da falon baƙi. Galala tai kawai tana kallonsa, can ƙasan ranta mamakin miya rikitashi haka take yi. Tare da mamakin girman wannan baƙo a wajensa. Amma dai koba komai ita hakan yayi mata. Dan ta kuɓuta daga abinda take gudu dai ke nan. Cikin taɓe baki ta miƙe, tare da saɓar handbag ɗinta ta fice hankalinta kwance. Ai garama taje taga show ɗin can gidan, dan babu wasu su Paah da zata kira sai abubuwa sun kankama……….✍️
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛_* _(Itama nama ce)__
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
__𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆 _𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-three.
🩸🩸🩸🩸
Cikin yanayin gajiya ta shigo gidan. Ga damuwar dake a ƙarƙashin zuciyarta a kwanaki biyun nan game da rashin ganin Samraah. Tun a jiya bincikenta ya tabbatar mata da Samraah ce a sashen Awwab dai Hajiya Mammah da bata san an sallamota ba ta gani ba wata ba. Taso sanar ma Yallaɓai amma ta kasa hakan dan tana son ta fara sanin mi bincikensa ya samo masa akan yarinyar. In har wanda zata iya canja ra’ayinsa ne daga kasheta daya ambata sai ta fara shirinta. Idan kuma na wanda bazai iya canja ra’ayin nasa bane nan ma sai ta ɗauki mataki. Dan a wannan gaɓar bazata taɓa bashi goyon baya ba. Tanama Samraah wani irin mahaikacin so mai taɓa zuciya. Ita kaɗai tasan a halin matsanancin kishin da take ciki na Awwab a ƴan kwanakin nan musamman daga jiya zuwa yau. Babu kowa a falon sai ƙamshi da sanyin ac. Tasan su Arwa sun fita yawonsu, dan Muhseen ne kawai ke zuwa makaranta yanzu a gidan sai Aneesa autar Hajiya Mammah ƙanwar Azizat kenan. Cikin rashin kuzari ta kama ƙarfen upstairs zata fara haura steps ɗin ta tsaya cak. Rawa jikinta ya nema fara yi sakamakon abinda idanunta ke kallo. Cikin wani irin bugawar zuciya da rawar baki ta furta, “Fahad!”. “Yes Ummy. Surprise”. Ya faɗa cikin fara’a yana ƙarasowa gareta. Cikin rashin kula da yanayinta ya bata side hug abinsa. Da ƙyar Hajiya ƙarama ta iya jan numfashi da kokarin controlling kanta. Amma ina jikinta karkarwa yake. Dan koda Fahad ya ɗago yana gaisheta sam bama fahimtarsa take ba. Sai da ya ɗan tanƙwaɓeta da zai gittata yana dariya sannan taji abinda yake faɗi na ƙarshe. “Oh Ummy mamakin ganina da alama ya sumar dake. Bari naje dai yanzu zan dawo karki faɗama su Azizat na dawo”. Daga haka yay wucewarsa ya barta a yanayin ƙaulani. Sosai taji fitsarin dake a mararta na ƙoƙarin zubowa. Tuni ta saki handbag ɗinta a wajen ta juya ta fice a falon ƙafafunta na matuƙar rawa. Tana shiga motarta motar Hajiya Mammah na shigowa gidan. Ko bi takanta batayi ba ta wani irin yin reverse da mahaikacin gudu kamar ba’a cikin gida take ba ta fice har tana kusan takama ɗaya a cikin securitys ɗin ƙofar ƙafa ALLAH dai ya taƙaita yaja baya da sauri. Babu wanda ya kawo komai a ransa sai tunanin kiran gaggawa maybe ta samu daga asibiti. Dan sometimes takan yi irin wannan fitar idan hakan ta faru. Sai in ta dawo ta basu haƙuri da sanar musu abinda ya rikita tan. Shiyyasa kowa a gidan ke mata uziri da mata kallon innocent woman dako hannu ka saka mata a baki bazata ciza ba. Wani irin mahaikacin gudu tayi ko’a titin. ALLAH dai ya taƙaita titin anguwa ne. Gashi kuma anguwan masu kuɗi ba wani yawan kai-kawon mutane ake samu ba, motocin ma sai jefi-jefi. Yanzu kam dama rana da wahala ka gani kasancewar duk ana wajen aiki. A cikin ƙanƙanin lokaci ta iso gate ɗin gidan yallaɓai. Horn ta dinga dannawa daya rikita maigadi, jikinsa har rawa yake wajen buɗewa. Ruɗanin da take ciki ya sata mantawa gaba ɗaya yau bata saka niƙaff ba. Sannan kuma da motarta ta amfanin ko yaushe ta shigo gidan bata ɓadda kama ba kamar yanda ta saba. Kasancewar a duka kamanni biyun na baɗini dana zahiri tana da power ɗin shigowa gidan yasa babu wanda yay mamakin ganinta sai dai mamakin yanda ta shigo. To amma idan suka auna da kafin zuwanta wadda tazo zasu iya kallon abin a wani abu daban kuma. A dai-dai ƙofar falon gidan tai parking, ko rufe motarta batayi ba ta afka ciki. Babu kowa a falon, sai tv dake magana ƙasa-ƙasa. Hannunta ta kalla da nufin neman waya, wayam babu handbag. Tunanin ta barta a mota ya sata jan tsaki. Juyawa tai da nufin ɗakko wayar dai-dai nan wanda zata fita ɗakowar dominsa ya fito. Baiyi mamakin ganinta ba, dan yasan zata iya zuwa ɗin dama.. Zaune ta kai dan wata irin hajijiya take ji na neman ɗibarta. Da ƙyar ta iya haɗa kalmar, “Fahad ya dawo, yanzu haka yana gida”. Zaune ya kai shima a hankali batare daya ce mata komai ba. Sai ma file ɗin hannunsa daya ajiye yana mai dafe kansa da duka hannayensa biyu. Jin shiru baice komai ba ta ɗago ta kallesa. Muryarta har rawa take wajen sake faɗin, “Yallaɓai baka ji abinda na faɗa bane?”. Wani irin murmushi ya saki, mai bayyanar da tsantsar ɓacin rai da tsufarsa. Ya ce, “Na jiki sarai, shima wanda ke bincike akan yarinyar nan ya kawo sakamakon yanzu”. Bai gama rufe baki ba ta ɗauki file ɗin ta fara dubawa cikin rawar jiki. Abubuwa masu muhimmanci kawai take dubawa. Abu na farko daya fara jan hankalinta shine cikakken sunan yarinyar. Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Na biyu aikin mahaifinta da sanadin rasuwarsa har ma da inda ya rasu. Na ƙarshe MATAR AURE. Rawa bakinta ya fara da ƙyar ta iya haɗa kalmar, “Ba…ban fahimci komai ba yallaɓai”. Murmushi ya sake saki, sai kuma ya kalleta da idanunsa dake jazur kamar tsohon maciji. Musamman yanda tsufarsa ta sake fitowa fili sai taga har baƙinsa ma ya sake bayyana fiye dana baya mai tsananin shining ɗin hutu. Shima ɗin kallonta yake cikin ido, batare daya janye ba ya furta, “Ita ɗin ɗiya ce ga Abdul-wahab Gwarzo (jirgin mota)”. Kaɗan ya rage zuciyar Hajiya ƙarama ta ɓaro. Ta wani irin miƙe zambar jikinta na karkarwa tace, “What! Jirgin mota? Drivern mahaifin Ummu-Hidaya da kenan?”. Kansa kawai ya ɗauke daga kallonta alamar tabbatarwa. Cikin kaushin murya ya cigaba da faɗin, “Tabbas nayi kuskuren ƙin bibiyar bayan Abdul-wahab kamar yanda nake biye dana Ibrahim Alonso. Idan baki manta ba nayi hira da yarinya shekara ɗaya data gabata a Kano sakamakon turamin program ɗin bikin buɗe Company da Awwab yayi. Zargin akwai dalilin da yasa ya amsa mata zaiyi hira da ita alhalin bai taɓa yi da ko manyan channels ba yasa na baro India nazo danna tabbatar da ko akwai alaƙa a tsakaninsu. Tako ina bincikena babu ta inda wata alaƙa ta alaƙanta su, dan haka ban maida hankalina ga cikakken sunan yarinyar ba….” “Wai kana nufin itace yallaɓai?”. Hajiya ƙarama da gaba ɗaya take a gigice ta jeho masa tambaya cikin katsesa. Iska ya furzar mai kauri tare da miƙewa tsaye. Taku ya fara hannayensa duka biyu a goye ya ce, “Of course itace yarinyar”. “Tashin hankali. To amma tayaya tazo Lagos bayan ma’aikaciya ce? Ta yaya kuma Lagos ɗin ma take zaune a Maash Mansion? A ƙarshen zance shine tayi aure bayan fasa aurenta da saurayinta da suka jima a tare. Abin tambayar anan waye ya auretan? Waye kuma yay kidnapping ɗinta kafin auren har sau biyu? Tabbas akwai abinda ya kawota Maash Mansion, minene shi?. Yallaɓai wlhy zan haukace, wane irin ruɗani da tashin hankali ne haka yazo mana a rana ɗaya? Gashi mun gagara magance batun likitocin nan abu sai ƙara nisa yake, duk da dai ba wannan bane kaɗai hope ɗinmu wancan ma zasu iya mana illa tunda ko ganinta bamayi a yanzu balle sanin halin da take ciki”. Amaimakon amsa mata dukkan tambayoyinta da maganganunta a mugun fusace yay wurgi da ɗan abin deco.. ɗin dake a saman Centre table ɗin gabansu……..✍️
*_🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
_(Itama nama ce)__
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-four
Tnx
idan wani littafi sai kumana magana
Allah ya saka da alkhairi ameen.. sannan muna cigiyan wasu littattafai yanci da rayuwa, bakon munafiki da masarauta Allah yasa akwai
su kike bukata kina a cikin a group din ma na Whastapp
Barka da kokari, so interesting novel, amma don Allah ba a Gama book din bane complete
eh har yanzu ba’a gama ba
Tsutsar nama book 3 page fifty six
Masha allahu alhamdulilah
Thanks,Amma yaushe za’ayi sauran
Ahah.
A ina zanga link din?
https://chat.whatsapp.com/Gbut9ibvwWM8JPk0qoMEiZ wannan shine group din mu na WhatsApp
Tsutsar nama babu complete ne dun Allah a taimaka mana da sauran. Thank you
Barka da qoqari
assalamu alaikum cigavan tsutsar nama book3
ai bata gama ba