Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    154 Results with the "paid" tag


    • KANWAR MATATA Thumbnail

      *🦜 _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_     _K’anwar Matata ba kirkirarren labari bane! Sai da na samu yarda da aminta sannan na soma rubuta shi. Dan haka idan yayi shige da naki irin labarin, arashi aka samu. Sannan ina gargad’i da babbar murya, ban yarda a juya min labari ta ko wani siga ba, ba tare da izini na ba ko kuma a d’aura min…

    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Turus yayi yana bin falon da kallo zuciyarsa tana ƙara gudu, shiga yayi ciki da kyau har sannan yana ƙoƙarin gane abinda yake faruwa. Ƙofar ɗakin Halima ya tura, nan ya tarar da gurin shima tamkar falon babu ko tsinke anyi shara da alama ma har mopping akayi. Sakin ƙofar yayi ya matsa ya buɗe ta ɗayan ɗakin da yake mazaunin nasa; a nan ne ya tarar da kaya zube a ƙasa wanda kallo ɗaya ya musu ya fahimci nasa ne. Ɓacin rai haɗi da baƙin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, fita yayi daga nan ya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina 🙏🏽🙏🏽 Cike da ƙaguwa da zancen ya ce "Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma kuɗin za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?" "To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita ya kamata ka tambaya itama kaji wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce "Ai na gaya miki yanda mukayi da ita, dama…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Tarin missed calls ɗin da ya gani daga Alhaji Lawan mutumin daya siya gidan Jalilah a hannunsa ya tabbatar masa da ba lafiya ba, a maimakon ya kira Alhaji Lawan ɗin kai tsaye sai ya fara kiran Nasir domin shi yayi hanyar cinikin. "Yanzu nake shirin kiranka dama; kana ina?" Nasir ya faɗa bayan daya amsa wayar Bilal ya ce "Mai ya faru naga mutumin nan daya siya gida a hannuna yana ta kirana a waya ban lura ba sai yanzu?" "Shiyasa na ce kana ina? Akwai matsala gaskiya" Nasir ya bashi amsa. Bilal ya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya. Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da ɓarna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-one Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama 🙏🏽🙏🏽 A hankali na buɗe ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na buɗe idon ya saka Mama janye hannunta, ganin da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce "Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazzaɓin ya sauka". Na yunƙura na zauna ina cije baki saboda kaina daya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) HALIMA Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce, "Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki…
    Note
    error: Content is protected !!