JADEEDAH
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
[01/07/2025]
PAGE 1 ❤🔥
FREE PAGE
Bismillahi Rahamanir Rahim
“Ummie Maryama dan Allah kiyi haƙuri ki bar ni in yi zamana anan wallahi tsoro na ke ji ,ji na ke kamar da zaran na fita zan ci karo da Baba Ƙarami na tsaye ya na jiran na fito ya hukunta ni”,ta ƙare zance ta na mai share hawayen da su ke ta faman kwaranya a kyakyawar fuskarta.
” Haba Hibbah ki kwantar da hankalin ki mana,domin tuni Baba Ƙarami ya tafi Masallaci don gabatar da Sallahr Azuhur kuma kin dan ba zai dawo dan yanzu ba,ke kuma kin ga tun safe ki ke a cikin ɗakinnan ko kayan barci fa ba ki samu kin sauya ba”.
“Ni dai ki bar ni a haka ban ƙi ba ma in kai tsawon sati a cikin wannan Bedroom ɗin ba muddin hakan zai sa in tsira daga faɗa ko hukuncin Baba Ƙarami ,sosai na ke jin tsoran haɗuwata da shi,ban san me zai faru ba in hakan ta kasance”.
“Ba wai zan faɗar ma ki da gaba ba ne ko in sagar ma ki da gwuiwa ba ne ba, A’a amma kin sa ni kuma ni ma na sa ni ,dole ce haɗuwar ki da Baba Ƙarami ke ba ma sh ƙadaii ba har da Baba Malam ,da sauran Yayyen ki sai sun neme ki duk iya zille-zillen da za ki yi ma hakan”.
” Innalillahi wa’ina ilaihirraju’una Ummie Maryama na shiga uku ,Ni yanzu ina zan sa kaina da rayuwata ,ko ɗaya ba na son haka ta kasance domin ban san me zan fuskanta ba a haɗuwata da su”.
“ki yi haƙuri amma duk tsoranki da hakan sai ta faru domin ta hakan ne kawai za a iya samo hanyar da za a warware wannan rikitaccen al’amari da ya shigo cikin Gidannan “.
” Ummie Maryama ba zan iya ba Zuciyata ba zata iya ɗaukar hakan ba ,a yanzu ma haka ji na ke kamar zata tsaga ƙirjina ta fito waje ta tarwatse,saboda tsoro da fargaba”.
Sai da Ummie Maryama ta sa ki wata gajeriyar dariya kana ta ɗora da cewa,”Kin ga har kin ba ni dariya sai ka ce ba Hibbah da na sani ba duk ina dakakkiyar zuciyar da jarumtar da na san ki da ita ?”.duk ta ana yin haka ne don ta ɗan kwantar mata da hankali.
Ka sa cewa da ita komi ta yi sai Ummie Maryama ɗin ce ta ɗora da cewa ,”Komi yai farko zai ƙarshe ,yanzu haka wani al’amarin ne babba ya ke tunkaro ki shiyasa Allah ya jarabce ki da wannan ƙaddarar don haka ki daure kuma ki jajurce har zuwa sanda za ki cinye wannan jarabawar kin ji Hibba”.
” Ta ya ki ke ganin haka za ta kasance tun a yanzu na sare zuciyata ta karye ba na tunanin zan iya cin nasara a cikin wannan lamarin mai cike da rikici,Sarƙaƙiya tare da ruɗarwa ba”.
“Ban san ki da irin wannan halin ba,duk da nasan cewa kin sa ni cewa saurin sarewa ko miƙa wuya ga lamarin da ba kasan me Gobe zata haifar ba,babban kuskure ne,dan haka ki kwantar da hankalin ki zo mu je yanzu ki yi wanka daganan ki ci abinci”.
” Ni ba na jin yunwa ko kaɗan, sunan abinci ma ba na son inji an ambata”.
“Hakanan za ki daure ki ci ko da one cup na tea ne”,” Ni dai a’a Ummie Maryama,ba zan iya cin komi ba a halin da na ke a ciki yanzu”.
“Oh ba ki so wannan lamarin ya zo ƙarshe ba kenan ba,domin ba shakka na san wata cutar ce za ta kama ki kin ga anyi ba ai ba kenan ko,gara ma ki haƙurƙuntar da kan ki da zuciyar ki ki samu ki ci wani abun”, da haka dai Ummie Maryama ta samu ta shawo kanta har ta amince su ka fito tare da nufin ta je tai wanka ta ci abinci.
Suna isowa Parlour su ka iske Mama Hadiza,Umma Maimuna,Umma jamila,Umma Hafsat da kuma Baba Asabe zazzaune da dukkanin alamu suna tattaunawa akan abinda ya faru ne.
Zaraf Umma Maimuna ta miƙe ta nufe su tana mai cewa,Yauwa Ummien Jaheed,sannu da ƙoƙari kin samu kin shawo kanta ta fito kenan ?”.
Cikin girmamawa ta ta bata amsa da cewa,” Eh na samu ta fito wai ko ta samu ta ci wani abun ko ya ya yake,tunda ba yanda za ayi mutum ya zauna da yunwa,daga nan sai ta samu ta yi wanka”.
“Ai kamata yai ta fara cin abinci in yaso sai tai wankan daga baya kamar zai fi”, Cewar Umma Jamila.

0 Comments