You have no alerts.

    HAIHUWA DA HANJI

    Wannan littafi nawa mai suna HAIHUWA DA HANJI ban san ta ya zan fasalta muku ba amma tabbas yayi matuƙar shan bambam da sauran littatafai na don labari ne na wata baiwar Allah da ya faru a gaske, kashi saba’in cikin ɗari duk ya faru sai kaɗan da za mu ƙara ta yadda zai ƙayatar ya kuma isar da saƙon da muke buƙata ba tare da tangarɗa ba. I promise it’s going to be a hit kar ku ga don free ne yana daga cikin labaran da na jima ban rubuta irin shi ba don haka ku shirya shan karatu domin duk wacce bata karanta ba an barta a baya.

    *GARGAƊI*

    haƙƙin mallakar HAIHUWA DA HANJI na Fatima Muhammad Gurin ne ban amince ba ban lamunci a sauya min labari ko ta wani ɓangare ba ko a yi amfani da shi ba tare da sani na ba.

    *SADAUKARWA*

    Na sadaukar da littafin HAIHUWA DA HANJI ga ɗaukacin makaranta littatafai na.

    *001*

    Wani irin ruwa ake tsulawa kaman da bakin ƙwarya, kusan duka bil’adama suna kwance lub cikin tattausan katifa lulluɓe da bargo suna bacci kaman yadda dare ya zama mahutar bawa amma ita tana duƙe a kitchen ɗin dake tsiyaya saboda rashin kyaun kwanon da aka lulluɓe kai da shi.

    Wuta ne take hurawa Dukda bayanta dake ta jiƙewa har hakwaranta suna haɗe wa saboda sanyin dake shigarta hakan bai sa ta damu ba sai ma ƙara mayar da hankali da ta yi ga haurawar da bata sarara ba sai da ta ga wutar ta kama yadda ya kamata, babbar tukunya ce da za’a iya naɗe ta a sanyata ciki kuma tsaf ya ɗauketa saboda rashin ƙiba da kumarinta ta shiga kokawar janyowa da ƙyar ta ɗora bisa murhun kan ta nufi wani bokiti ta fara aikin ɗibo ruwa a kimtace tana zubawa sai da ta tabbatar yayi yadda ta saba kan ta rufe ta fito, kifi ɗanye da suke sanyawa cikin ƙanƙara a wani babbar kula ta juye ta shiga wankewa don an riga an yi mata yanka tun jiya da Magrib a bakin kasuwan, sai da ta wanke tsaf ta ɗauko wani tukunyar ta zuba su sai a lokacin aka soma kiraye-kirayen sallah daga chan nesa.

           Na yi mamakin yadda ko tsoro babu a fuskarta haka take ayyukan nan cikin ruwa a take ta sake haɗa wani murhun ta ɗora dahuwar miyan kifin nan, sai da ta tabbatar komai ya mata yadda take so kan ta shiga tattaro kwanukan gidan don ta san in ta bari ma gari ya yi haske ta shiga uku, wanke wanke take sauri-sauri yayinda ruwan da ya koma zuba chab chab ya cigaba da jiƙata, har ta gama jikinta babu inda ba ya kakkarwa sauri sauri ta wanke shinkafa ta zuba cikin tukunyar farko kan ta yi alwala har kuma lokacin babu mahaluƙin da ya leƙo a gidan Dukda kuwa wasu masallatan ma har sun idar da sallah.

    Akurkin ɗakin da shi ne nata a gidan ta duƙa ta shige ta cire kayan jikinta bakkon kayanta ta janyo da kyar ta zaƙulo wata kodaddiyar doguwar riga ta saka ta janyo hijabinta ta ɗora tare da tada sallah, ga mamakina tsaf ta gabatar da Sallar ta yadda addini ya tanadar, bata jima tana azkar ba ta fito don gudun magana amma bata tsira ba domin a kitchen ɗin ta tarar da Inna larai da sauri ta duƙa ƙasa

    “Ina kwana inna?”

    Kallonta tayi ta taɓe baki ta buɗe tukwanen ganin miyan ya yi ta juyo gareta

    “Uban me kika shiga ɗaki kike yi har miyan nan ya nuna saura ƙonewa baki shirya kwashewa ba? Asara kike son ja min ko?”

    “A’a inna sallah ne na je na yi”

    Tsaki ta ja tare da nuna mata kular da suke kwashe miyan tallar, ta je da sauri ta ɗauko inna larai ta kwashe tsaf kan ta ɗaura dumamen gidan a murhun, ita kuma ta wuce ta ɗauko kular kwashe shinkafa ta taho ta janyo ledar sugar ta buɗe a cikin kular kan ta shiga kwashewa turirin na Dakar ta yana ƙonata yadda ta saba har ta gama duk sanyin da ake ta jiƙe jagwaf da gumi, kwanukan tallarta ta cigaba da haɗawa a wani bokitin fenti har ta gama filate na roba da ruwa da gutsuren dollof da take wanke plates idan ta sayar aka ci aka dawo mata dashi.

    “Je ki bugawa su Iro su zo su ɗaura miki a baro su kai miki yanzun nan”

    Da to ta amsa cikin sanyinta ta nufi ɗakin na yaran mazan ta shiga bugawa, sai da ta kwashe sama da mintuna ashirin tana bugu da ƙiran suna kan wasu matsakaitan samari biyu suka fito ɗayan ya sa hannu ya hankaɗeta sai da ta faɗi ƙasa.

    “Don uban ki bamu hana ki wannan bugun bala’in ba? Shegiya kullum ba ki da aiki sai na uzzurawa mutane ko wani farar safiya…”

    “Ɗahiru ƙaniyar ka…! Kun wuce kun zo kun fitar min da abinci ko sai kun janyo min asara?”

    Babu ruwanta da sun yi sallah ko ba su yi ba damuwarta kawai su kai mata kayan sana’ar ta.

    A hankali ta miƙe tsaye tana kaɓe jikinta dama ta sani ba dai a yi musu faɗa a kan an ci zarafinta ko an zalunce ta ba, kowa a gidan na ganinta tamkar juji da in sun kwaso sharar su babu inda suke zubawa sai bisa kanta.

    Sumsum haka ta taho suka kama suka ɗora suna ta mitar da kullum safiya sai sun yi haka har suka fice, tana shirin fita daga gidan kenan Inna larai ta kwala ƙiran sunanta.

    “Afifah Ke!”

    Waigowa tayi da sauri kuma cikin sanyinta

    “Saura in ga ba daidai ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daaɗi kuma kika sake kika ci kai ko lasa kika yi Allah ya isa ban yafe ba ki je ki dawo ga dumamenki nan zan ajiye miki”

    Girgiza kai tayi fuskanta ɗauke da murmushi mai nauyi da ciwo ta amsa da

    “Toh”

    Kan ta fice daga gidan.

    A inda ta saba zama gefen rumfar masu tura finafinai nan ta zauna bayan sun sauƙe mata suka buɗe suka cika fillet biyu idanunta cike da hawaye tace

    “Iro wallahi in…”

    “Na uwarki ne ko na ta mu uwar? Ina ruwanki? Kuma wallahi ki sake ki faɗa mata ki ga yadda zamu yi da ke Annoba kawai”

    Da ƙarfi ta runtse ido sunan ba wai sabo bane a gareta sai dai a duk sadda aka ƙira ta da hakan ta kan ji zafi da ciwon fiye da ɗanɗanon maɗaci a kan harshenta.

    “Mai shinkafa sa min na ɗari uku..!”

    Haɗiye abin da ya taso mata tayi ta karɓi kudin ta saka a Jakan ƙugunta kan ta fara zuba shinkafar kaman ko yaushe fuskanta babu ɗigon fara’a ko sassauci ba kuma don komai ta ɗauki wannan mataki ba sai don kare mutuncinta.

    Hakan da take ya sa maza dayawa masu kawowa ‘yan mata yan tallah wargi basa samun dama kowa ya santa duk tsiyarka tana da kwarjinin da in ta tsume hakan babu mai iya kawo mata wargi… Saboda tsafta da kuma natsuwarta yasa dayawa suke tururuwa wurin sayan abincinta.

    Ita ɗin annoba ce kaman yadda wasu ke ƙiran ta dayawa sun santa a Mayya! Dukda ita bata taɓa sanin menene maitar ba amma ta wurin kasuwanci su kan saya abin hannunta don ko babu komai akwai zaƙin hannu muddin ita tayi girki.

    Kan ka ce awa biyu duk ta sayar da abincin tas ta janyo baro ta ɗora kulolin a kai tana jin jiri na fusgarta saboda rabon ta da abinci tun jiya da rana gashi yanzu ana neman goma da rabi, haka ta turo wheelbarrown ta nufi gida…

    Razana tayi ta daka tsalle tayi baya sun saba yi mata hakan sai dai ta kasa sabo ita

    “Ina kudina?”

    Inna larai ta miƙa mata hannu a zauren wanda ko kanta bata gama sanyo wa ba, Jakan ta sunce ta miƙa mata a wurin ta zazzage ta kirga ta ga riba yadda suka saba samu ta saɓi kayanta ba sannu bare na gode tayi cikin gida abin ta, Afifah ta bita da kallo har ta ɓace kan ta turo baron zuwa cikin gida ko sauƙe kwanonin bata yi ba ta nufi bakin kitchen inda inna larai ɗin ke zaune ta duƙa

    “Abincina fa inna?”

    “Laaaa kin ga mun manta da ke wallahi ina fa ta zuci zucin ajiye miki”

    Runtse ido tayi da ƙarfi tana danne hawayen dake taso mata idan da sabo ya ci a ce ta saba, kusan koyaushe za su yi rabon abincinsu muddin bata gidan to za’a ce mata an manta da ita ne, wani lokacin ma sai an sauƙe sai a aiketa kan taje ta dawo an rabar kuma a hana ta, hanjinta har murɗewa suke saboda yunwa amma ya zata yi?

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!