You have no alerts.

    GUDUN AURE BK2

    *1*

     Mintina goma da yin posting din maigidan ya kira ina d’aga waya ya fara fad’a cikin tashin hankali wai akan wane dalili zan zauna na yi dogon rubutu na ‘batanci ga babban mutum irin Alhaji Tajo. Ashe wato duk ko’karin da yake yi mini bana gani kenan har sai na zartar da hukunci babu umarninsa. Na dinga ko’karin gaya masa cewa babu fa ta inda na ‘bata mutumin kawai dai na tura sa’kona ne ta social media wanda nake ganin hakan zai sanya ya d’auki lamarin da muhimmanci. Bai saurare ni ba. Ya dinga fad’a cikin damuwa sai kawai na kashe wayar na zauna a wurin kuka mai karfi ya kwace mini. Wai ni ya zan yi ne. A ranar har gajiya na yi da amsa wayar mutane wasu na ganin beken abinda na yi, wasu kuma suna ganin hakan da na yi shine daidai, tunda yanzu rubutuna ya karad’e medi’a, kowa yana tofa albarkacin bakinsa akai.  Na tabbata kuwa sa’ko ya riski wanda aka yi dominsa.

    Da maigidan ya dawo muka dinga musayar yawu duk akan rubutun da na yi.  Yana ta tayar da jijiyar wuya wai na bashi kunya kuma idan masifar ta taso a kaina zata ‘kare tunda wawa shine yake fad’a da mai kudi.

    Jin cin mutunci ya fara biyo baya ya sanya na bud’e wuta. Na ce.” Ba na tsoron kowa sai Allah. Kuma kudinsa ba zai hana na nemi hakkina ba. Na baka ha’kuri ka ki ha’kura duk hukuncin da za ka yi bai dame ni ba a yanzu rayuwar yarana ce a gabana.”

    Maganata ta k’ara tunzura shi. Kishi muraran ya bayyana a fuskarsa. A lokacin ne mai afkuwa ta afku ya ce.” Ki je gida na sake ki saki daya tunda ke ba wanda ya isa ya gaya miki magana ki ji.”

    Na shiga rashin hankali mai tsananin gaske. Bakina ya dinga karkarwa ina so na bashi ha’kuri amma ya fice daga d’akin a gaggauce. Sai kawai na dinga nanata Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un. Har zuciyata ta dan yi sanyi na tashi na fara had’a kayana cikin akwati. Ban tafi ba tukkuna sai da Yusi ya dawo daga makaranta.

    Babanmu dai bai tsananta ba. Ya ce na share d’aki na zauna kafin kura ta lafa. Baba Sule ya zo da daddare ya dinga zazzaga mini bala’i wai na rikitowa kaina aiki, ga masifar nan na fara ga ni Alhaji Muntari ya sake ni, duk abinda ya biyo bayan rubutun da na yi zai k’are kaina.

    Mamaki nake yi yadda suka d’auki lamarin da zafi. Wato na yi shiru kenan shine abinda kowa yake so. Saboda mutumin Yana da kudi duk abinda ya yi daidai ne. Ni dai ban zage shi ba, ban fad’i mummunan magana a kansa ba, na fito ne na yi magana a matsayina uwa. Shine abin tashin hankali. Har yanzu ban tsorata ban kuma sa a raina cewa mutumin zai yi nasara a kaina ba.

    Ban ta’ba ganin b’acin ran Sahura ba sai a ranar dan kirana ta yi a waya ta dinga yi mini fad’a wai me yasa ban yi shawara ba kafin na yi rubutun. Mahaifiyarsa ce bata da lafiya shiyasa a ka samu tsaiko.

    Na ce.”Sahura dukkaninku kun kasa fahimtar halin da nake ciki ko?  Kamalu yaro ne k’arami. Me kike tunanin zai faru a lokacin da aka had’a shi da garadan maza wad’anda suka jima suna aikata lalata. Za su koya masa wasu dabi’un marasa kyau, Sahura ki dubi azanci na da kyau, yau kusan sati uku kenan ana abu daya mutumin nan idan da Yayi niyyar yi wa yaran nan adalci daga can inda yake ma zai bugo waya ya ce a sake su. Amma kowa idan zai bud’e baki sai ya ce  za su samu sassauci to Ina adalci anan. Na yarda mahaifiyarsa bata da lafiya amma me yasa ba zai magantu ba yau kwanansa hud’u da dawowa ya kamata ya dubi lamarin da muhimmanci. Yadda yake cikin damuwa dalilin rashin lafiyar mahaifiyarsa mu ma iyayen yaran nan, haka muke cikin damuwa, a ganina wannan ce hanya mafi sau’ki da sa’kona zai riske shi. Amma ki je ki sake duba rubutun da kyau ki ga ni, ban zage shi ba wallahi.”

    “To ai kin kwatanta zagin ‘kawata. Ba wai ka fito ka d’urawa mutum ashariya ba shine zagi. A a wasu kalmomin ma sun fi zagin muni. Kuma kin yi amfani da su wajan tura sakonki, babu tausasawa ‘kawata mutumin nan fa ba yaro ba ne da shekarunsa, bayan haka kuma ke kanki kin san girma da daukakar da Allah Ya yi masa.”

    Na ce.” Kin ga Sahura babu ruwana da wannan mafitata nake nema kawai. Ni kenan na zauna zuciyata ta yi bindiga saboda tunane tunane. Sahura koyaushe Ina gaya miki masu kudin nan fa ba su fiye bawa abinda ya shafi talaka muhimmanci ba. Sai sun ga sunansu zai ‘baci tukkuna. Ina nan ina jiran abinda zai biyo baya. Wallahi yanzu na riga na bushe tunda babu irin masifar da ban gani ba. Ni da aure har abada.”

    Kashe wayar na yi sakamakon mugun kukan da ya kufce mini.

    Ta dinga kira na kasa d’agawa saboda ba ni da wani karsashin da zan bata amsa. Kukan da ya jima yana ci mini towo a kwarya shi na dinga rizga kamar babu gobe.

    Ummansu Hadiza ta shigo d’akin tana tana kiran sunana.

     Kasa amsawa na yi saboda kukan da ya ci karfina. Ta ce.” Ha’kuri za ki yi, kukan ba shine mafita ba, lamarin da ciwo da radadi a zuciya, to amma kowane bawa akwai k’addararsa, wasu a kansu, wasu akan abinda suka haifa, ki yi ta addu’a Allah Ya tsayar iya nan, ‘kuruciya ce kowa da irin tasa.”

    Na ce.” Ummansu Hadiza don Allah menene lefina anan? kawai dan na shiga media na nemi mafita sai kowa ya juya mini magana, shikkenan masu kudi sai su yi abu su kwana lafiya, talaka kuwa akan hakkinsa sai a nemi salwantar da rayuwarsa, kuma ace ba zai yi magana ba.”

    “Amina ba wai an hanaki magana ba ne, a a hanyar da kike bi da salon rubutunki wurin tura sakon shine abinda yasa iyayenki da duk wani mai k’aunarki shiga cikin damuwa, sanin kanki ne mutumin nan babba ne, to mai zai sanya ki rubuta masa wasika cikin izgili, ki watsa shi duniya bayan shi akayi wa lefi, idan hakan ya ‘bata masa rai zai iya yin shiru. hukuma su ri’ke yaran sai baba ta gani kuma.”

    “Umma ba zaku fahimci yadda nake ciki k’unci ba ne, ba na iya rintsawa fa, ga Yusi kullum cikin koke-koke, sannan yaronan fa shine k’arami a cikinsu mai kike tunanin zai faru, ni wallahi har yanzu ban ga aibun abinda na yi ba.”

    Ta girgiza kai cikin jimami ta ce.” Shikkenan to Allah Ya jishshemu alheri, idan k’urar ta lafa sai ki nemi mijin naki ki bashi ha’kuri dan gaskiya kin yi kuskure ba ki kyauta masa ba da kike zartar da hukuncin nan ba ki gaya masa ba alhalin Yana iyakacin bakin kokarinsa.”

    “Umma ku ajiye maganar Alhaji Muntari na gama aure har abada, ba zan koma gidansa ba.”

    Ta zuba mini ido na minti daya. Ganin babu rahama a fuskata yasa ta gyada kanta ta fita daga d’akin.

    ****

    Kwana daya biyu uku har zuwa sati babu wata magana da ta ‘bullo daga bangaran Alhaji Tajo. Dukda cewa kuwa sakon ya riske shi amma yau tsayin kwanaki bakwai kenan bai ce uffan ba. Hankalina ya Kai ma’kura wurin tashi, na rasa yadda zan yi da rayuwata babban tashin hankalina yadda ciwon damuwa yake nema kwantar da Yusi ni dashi duk mun zama zautattu. Hamusu kuwa kullum idan ya dawo daga kasuwa sai ya zo wurina mu zauna mu yi ta tunanin hanyar da za mu bi. Jin labarin Hamusu yana zuwa wurina ya sanya Alhaji Muntari kara yin fushi. Karin takaicinsa ma tunda na fito daga gidan ban kira shi a waya ba. Bayanin da ya yi wa Baba Sule kenan, ni ce na yi masa lefi ni ya kamata na neme shi na bashi ha’kuri, kuma yana da labarin bibikon da kanin tsohon mijina yake yi mini, dan haka muddin Ina son zama dashi sai na bashi ha’kuri kuma na kar’bi kuskurena.”

    Na cika da mamaki mutuka gaya a lokacin da baba Sule ya zo yana gaya mini yadda suka yi, dan shine yake ta faman bin sa yana bashi ha’kuri ya mayar da ni d’akina. Ban ja maganar ba saboda na riga na san halinsa sai  na ce masa shikkenan zan kira shi na bashi ha’kuri. Na fadi hakan ne kawai dan mu rabu lafiya amma ba na tsammanin zan ta’ba kiran mutumin nan na bashi ha’kuri, babbar damuwata a yanzu fitowar yarona ba auransa ba.

    Na kira Sahura cikin k’askantar da kai da nuna mata na kar’bi kure na, ban kyauta ba, amma ta yi mini hanyar ganin ogan nasu, ina son magana dashi baki-da-baki.”

    Ta ce.” ‘Kawata da tun farko ta wannan hanyar ki ke biyo abin bai zai yi tsamari da yawa ba. Tabbas oga ransa ya ‘baci ainun da ganin sakonk’i, amma da yake mutum ne mai sanyin hali ya share bayan yana da hanyoyi da yawa da zai hukuntaki. Wallahi na fi ki shiga damuwa, amma tunda kin amsa kuskuranki, zan yi kokarin ganin mun samu ganinsa zan yi miki jagora.”

    Na ce.” To shikkenan Sahura na gode sosai Allah Ya bar zumunci.”

    Bayan kwana biyu cikin farinciki Sahura ta kira ni take sheda mini ranar asabar ya ce mu same shi a ofis d’insa. Ta d’ora da fad’in.” Kawata d’an Allah ki tausasa harshenki, ki kuma bashi ha’kuri bisa abinda ki ka yi, ba daidai ba ne ke kanki kin san haka. Kada ki tuno abubuwan da suka faru a baya tunda nema ki ke yi a wurinsa, kuma wallahi mutum ne mai adalci.”

    Na ce.” Shikkenan Sahura zan yi kokarin yin hakan in sha Allahu rabbi.”

    Babanmu na samu na gayawa yadda muka yi. Ya ce.” Hakan ya yi, ki je ki bashi ha’kuri sannan ki iya bakinki, wannan ya kara tabbatar miki da cewa ba a fad’a da mai kudi ko da kuwa kaine da gaskiya.”

    Ban ce masa komai ba na tashi na shige d’aki na kwanta abin duniya ya yi mini yawa.

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!