Dingishin Kwado book 3&4
DINGISHIN KWADO
BY
SURAYYA DEE
MARUBUCIYAR
HALIN YAU
SABO DA KAZA
BAK’AR TA’ADA
*Barar addu'arku*
A irin wannan ranar ta 09/09/2000 Allah ya karbi rayuwar mahaifiyata.
Ina barar addu’arku da ku taya ni yi mata addu’o’in smaun rahamar Allah.
Saboda haka na saki page din a maimakon 10 ha wata da na ambata a farko.
Allah ya jiƙanki Mamah yasa aljannar firdaus makoma da dukkan musulmai gabad’aya.
Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.
Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k’addara.
Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad’a bai san abin mayarwa ba.
Duk yadda sakin nan ya yi mata wata irin mahangurba sai da ta yi jarumtar had’iyewa a gabansa.
Da murmushi ta dinga fad’in “Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ubangiji na gode da abin da ka yi mini, na gode da abin da kake yi mini. Na kuma gode da abin da zaka yi mini a gaba”.
Ta kalle shi sai ta ga tamkar nadama ce ta shige shi ta farat d’aya.
Gabad’aya jikinsa ya sake ya yi tub’us.
Yayin da ita ta kasa fahimtar komai.
Ya koma ya kwanta. Tsawon lokaci tana zaune tana sauraran yadda yake barcinsa sannu a hankali ba tare da tunanin komai ba.
Ganin ta kasa barci bar biyun dare ya sanya ta yi alwallah ta fara nafila. A cikin sujjuda take kuka tana yiwa ya’yanta addu’ar Allah ya tsare mata su ya kuma k’addara musu kyakkwar rayuwa cikin imani da lafiya.
Tana zaune har asuba ba abin da take yi irin tufka da warwara. Ina zata je ne?
Sai yanzu ta fahimci girman k’alubalen da yake gabanta.
Ta dinga kuka tana yiwa iyayenta da Yaya Sulaiman addu’a.
Sai da aka fara k’iran assalatu ya farka.
Ya shiga bayi ya d’oro alwallah. Shi ma nafilar ya yi.
Sai da ya idar ya ce “Bilkisu ina ba ki shawara ki janye kalaman da kika jefe ni da su, sannan ina ba ki umarnin ki ba ni hakuri don bana son na barki ki tafi kina garari tunda dai nasan ba ki da inda za ki je”.
Bak’in ciki har mak’oshinta ta ji tamkar ta danna masa ashariyoyi kala kala tsabar bak’incikin da ya taso mata.
Amma ta yi kamar ba da ita yake ba domin tana bude baki la shakka zaginsa zata yi wanda hakan kuma ba d’ab’iar mace kamila mai ilimi ba ne.
Dan haka ta yi masa bakam.
Har aka fara kiraye kirayen sallar asuba bata tanka masa ba.
Ya tafi masallaci yana fad’in “Ki yi shawara da zuciyarki kafin na dawo.
Ta bi shi da kallon mamaki wataƙila bai fahimci girman tozarcin da ya yi mata. Bai fahimci cewar da ya yi wai bata da inda zata je ma cin zarafinta ya yi ba. Ya manta da kalaman da ya yi wajen sakinta.
Ki je dan iyayenki masu son zuciya na sake ki saki biyu”
Zuciyarta ta buga da k’arfin gaske. Ta ke ce da kuka a bayyane domin k’arshen kaskanci da cin mutunci Sahal ya yi mata. Bayan haka bai ishe shi ba shine yanzu ya zo yana sake cin mutuncinta. Wato ga ni yake yi gidansa ne kad’ai mafakarta? Ashe shiyasa yake tuka mata tuwon wulakanci kala kala tana ta yin hak’uri da kawar da kai tare da yi masa uzziri kan uzziri. Ashe shi duk kallon bata da yadda zata yi, bata da gata yake yi mata?
Ta girgiza kai tana fad’in “Ko duk zuri’armu sun k’are ba zan sake zama k’arkashin ikon ka ba. Ko da hakan na nufin na dinga kwana a titi ne.
Bare kuma Ubangiji ya riga ya rufa mini asiri.
Kuka ta ke sosai wanda ba na zafin sakin ba ne , kuka take yi na yadda gidansu na Funtua ya zama kongo. Da ace Baba Babba na cikin gidan da ko bangarensu zata je ta bude ta zauna har zuwa ta samu nutsuwa.
Amma a yanzu fa?
Maiduguri zata tafi gidan Ansari ta zauna a hannun yarinyar matarsa ko kuwa Kano zata tafi gidan Yaya Hamida?
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Gidan Yaya Hamida ai ba dolenta ba ne tunda itama a k’arkashin wani take.
“Ina zan tafi ni Bilki?”
Ta fad’a cikin rawar murya irin ta kuka.
Ta yi shiru tana tunani. Gidanta ne ya fado mata. Tana da gidaje a Katsina. Bata son ta zauna a gidanta da suka zauna domin ya yi mata girma a matsayinta na marar aure. Sannan zata so ace ba ita kad’ai zata zauna ba. Take ta tuno da d’aya gidanta mai hawa biyu wanda akwai y’an haya a k’asa, saman ne babu kowa watanni uku da suka shud’e aka yiwa wanda yake ciki sauyin wajen aiki zuwa jihar Jigawa. Shine iyalinsa basu tashi ba sai sati biyu da suka shud’e. Wanccan satin ta je ta ga gidan ta saka a gyara a yi sabon fenti don idan za’a sake karɓa a bata kudi da daraja.
Take ta lalubo lambar wanda yake kula da gidajen. Ya dauka yana fad’in “Hajiya da fatan dai lafiya?”
Murya ba amo ta ce “Zan tambaye ka ne an kammala aikin gidan nan kuwa?”.
Da girmamawa ya ce “An kammala fenti Hajiya sink din kicin ne ba’a saka ba amma na siyo sabo yanzu haka ma yana gidan.”
Ta ce “To ka yi kokari a saka zuwa goman safiyar sannan a share a wanke gidan kafin zuwa azahar din yau. “
“To za’a yi hakan Hajiya da ikon Allah. “
“
Ta ajiye wayar tana jin saukin tashin hankalin da take ciki. Gidan a unguwa mai kyau yake babu hayaninya awon gwamnatine. Matsalar d’aya ce ba ruwan famfo sai dai da rijiya a harabar gidan. Zata samu almajirin da zai dinga d’ebo mata kullum.
Zata tafi da Alti da Alawiyya. Duk da auren Alawiyya wata d’aya ya rage . Nan da sati biyu ma zata tafi garinsu.
Kawai matsalar da tafi damunta makomar Amrah da Faruk ne. Ya ya zusu yi idan suka tashi Babu ita, babu Farha babu Alti ba Alawiyya?”
Ta kifa kanta a akan gado tana gunshekin kukan tausayin ya’yanta.
Bata jin zata fasa barin gidan Sahal. Amma tausayin ya’yanta yana matuk’ar tayar mata da hankali.
A haka ya dawo ya tarar da ita.
Ya zauna a gefen gadon. Ya ce “Ki daina kuka Bilkisu. Ni kaina haka nake jin jikina babu k’wari. Amma maganganunki sun mini ciwo sun tayar mini da hankali. Ki janyesu, ki yi tuba shike nan sai na mayar da ke ki cigaba da zama a d’akinki.”.
Ta zuba masa ido hawaye yana ambaliya. Ta ce “A a Sahal ai zama a tsakaninmu ya riga ya k’are, tunda na fahimci baka sona, baka bukatata nake ta faɗawa Allah ya kawo mana mafita a tsakaninmu. Ka san ai ban yi shekarun da zan ce bana buk’atar namiji ba. Kai ka samu mafita, ka samu wata ni ce ban samu ba. Da haka kuma ya faru na yi imanin nima tawa mafitar ce ta zo”.
Da iyakacin gaskiyarsa ya ce “Wallahi Bilki ina son ki. Har yanzu bana jin Hawwah irin yadda nake jin ki a zuciyata. Amma ban san meyasa bana jin sha’awar ki ba. Na dade ina zargin ko saka hannune don ina jin sha’awar matayen da ba su kai ki komai na cikar halitta ba. Amma watan jiya da na ji karatun Shaikh Ibrahim Khalil da yake bada tabbacin ana cirewa namiji sha’awar matarsa ko da kuwa yana sonta. Ganin ina cikin wannan matsalar ya saka na dinga nazarin to ai ni da ke bamu yi irin wannan shekarun da zamu kai ga wannan bigiren ba. Bayan haka na gasgata ina da rauni a wannan fagen sabanin ke da kike da k’arfi bukatar al’amarin. Sai na ji tamkar na ba ki dama ki je ki yi aurenki, amma sai na ji gara mutuwa ta riske ni kafin na ga kin zama matar wani. Amma jiya sai da kika yi mini cin mutuncin da ya zame mini dole na sallama ki”.
Na goge hawayen na ce “Zaman ne ya k’are.”
“Yanzu Bilki ba za ki karbi shawarar da na ba ki, akan ki janye kalaman da kika yab’a mini ba? Ba za ki bi umarnina ki ba ni hakuri ba?”
Ya fad’a a zabure.
Cikin nutsuwa ta ce “Ai duk duniyar nan ba mai sakawa na baka hak’uri Sahal. Don ban yi lalacewar da za’a zagi iyayena yayin da za’a sake ni sannan na bada hakuri ba. “
Ya mike yana fad’in”Girman kai ba na ki bane ina jiye miki ragaita duk kasaitaacciyar mace za’a same ta ne a gidan mijinta ko na iyayenta ko na d’anta ko kuma na y’anuwanta shakikai”.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Bata kula shi ba don bata da abin fad’a kuma.
Ya sake zama ya sassauta ya ce “kin yi nazarin ya ya rayuwar ya’yanki zata zama idan nabu ke a kusa da su?”
Rauni irin na uwa ya shige ta nan da nan, amma ta shanye ta ce “Idan na mutu ya ya zasu yi ne? Kuma a gidan ubansu zan barsu, don ba zai yiyu da gatansu na tafi da su muna ragaita a titi ba. Ni dai da ba ni da gata zan tafi, ko barance na yi”.
Ya yi shiru da alamu ya gane magana ta cab’a masa.
Ta numfasa ta ce”Duk irin musgunawar da ka yi mini na yafe maka darajar ya’yanka. Wannan gidan da aka gina shi da dukiyata Allah ne shaidar na bar maka halak malak, na yafe maka. Amma dan Allah ko ban ci arzikin komai ba a gunka ka dubi Allah ka rike y’ay’anka da amana da tausayawa, na barsu a hannun Allah na barsu a hannunka.”
Daga haka kuka na sosai ya k’wace mata.
Ya kamu da ciwon tausayinta ainun, a sanyaye ya ce “Bilki ki zauna na mayar da ke”.
Ta kuwa yi wata irin zabura ta mik’e tare da fad’in”Wannan kuwa shine gangan Sahal!
” Ina yi maka rantsuwa da Ubangijin al’arshi zama ni da kai ya k’are ila yaumil k’iyama. Ka mayar da ni, na kuma maidu a fuskar shari’a sai dai tunda shari’ar ta ba ni damar idan ina cutuwa na bijire. To ba zan zauna ba. Aure ya haramta a tsakaninmu tunda ka yi gigin mayar da ni dan kuwa a yanzu ba sai anjima ba sai ka sake ni “.
Hankalinsa ya kai k’ololuwar tashi ya ce “Idan ba za ki zauna saboda ni ba, to ki zauna ki reni ya’yanki”.
A zafafe ta ce”Ba zan zauna ba. Na barwa Allah amanarsu, na barsu a hannun ubansu. Zan je na nemi wanda zai mini adalci, wanda ba zai ga tsufana ba, ba wanda zai ga son zuciyar iyayena ba, wanda zai kashe mini k’ishin da nake fama da shi tsawon lokaci.”
Kishi mai tsananin gaske ya shak’e shi, har kan harshensa yake jin d’aci.
Ya ce “Yanzu so kike na furta miki na ukun a zo a jarrabe mu Bili?”
Ta ce “Ba wata jarabawar da zamu shiga ai an gama, ina binka a hankali ne saboda alfarmar da Ubangiji ya baka a kaina amma Wallahi komai zai iya faruwa a tsakaninmu idan ka kafe!
Ta fad’a cikin tashin hankali da matsanancin fishi.
Ganin zai fita ya sanya ta yi maza ta wuce shi ta rufe k’ofar d’akin. Ta sunkuya ta ja plate din da ta ci tufa a daren jiya. Y’ar karamar wuka ta dauko mai tsini da kaifi ta ce “Ka sake ni ko ka mini sanadin da zan rasa rayuwata gabad’aya don da na zauna da kai gara na kashe kaina na huta da azabar da kake gana mini da raina!
Ganin gabadaya ta rikice kuma iyakacin gaskiyarta yake ga ni har cikin kwayar idanuwanta ya sanya ya ce “Na sake ki Bilki! Allah ya yi miki musayen alheri”.
Ya zauna don sai ya ji jiri na katantanwa da shi.
Dukkansu kuka suke yi irin kukan nan mai taɓa zuciya, kukan kaico, kukan da ake jin an tsinci kai ba a yanayin da ake so ba.
Shi ya yi jarumtar ce wa “To ki yi zamanki a nan Bilki. Na amince ba zan zo wajen ki ba, kinsan nasan dokokin Ubangiji ina kokarin kùma kiyaye su.”
Ta girgiza kai ta ce daga yau zuwa gobe zan tafi ba zan zauna ba Sahal. Kuma Wallahi har zuciyata na yafe maka duk irin musgunawar da ka yi mini. Duk hakkina da ka danne mini a zamanmu Ubangiji ne shaidar na yafe maka, bana fatan sakayya ta dawo maka ko ta sauka akan Amrah.”
Ya ce “Na gode, na gode Allah ya hana ki kuka Bilki. Amma dan Allah zan roke ki arzikin abu d’aya tak. Ki bar Farha a tare da yaran nan, zan rike ta amana.”
Ba ja in ja ta ce “Ka roki abin da ba zan iya yi maka ba. Mutuwa kad’ai zata raba ni da ita, ko uwarta da ubanta a yanzu basu isa su ce na basu ita ba. Bare kuma ace na bada ita a inda ba dolenta ba. Na dai yi maka alk’awarin zata dinga zuwa hutu wajen y’anuwanta ba kuma kowanne hutun ba. Duk inda rayuwa zata wulla ni to zata wulla ni ne tare da ita, itace kad’ai abin da na mallaka da ba wanda zai mini iko ko ya yi mini gayya da ita.”
Ta fad’a hawayen tausayin ya’yanta na zuba. Don a yanzu sune damuwarta. Yadda zasu shigo su ga babu ita, babu Farha babu su Alti sai su kad’ai yana matuƙar d’aga mata hankali.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ya share hawayen idonsa ya ce “Ki yi hakuri, in sha Allah zan iya k’ok’arina akansu sai dai ai ba kamar suna tare da ke ba.
Ya mike tsaye ya ce “Ni fa ji nake yi idan har na bar ki kika tafi ni kuma na zauna da wata matar a wannan gidan na yi zalunci.”
Ta zuba masa ido ta ce “katon zalunci ma kuwa Sahal. Ai ko sakina da ka yi cikin izgilin ba ni da inda zan je ma zalunci ka yi. Shiyasa ni kuma na haramtawa kaina zama da kai. Amma kuma Wallahi tunda aure ya k’are a tsakaninmu har abada, to na yafe maka dukkan kuskuren da ka yi mini har zuciyata in sha Allah ba zaka tashi da haƙƙina ba. Ni kuma Allah ya mini sakayyar alheri albarkacin hakuri da afuwar da na yi maka”.
Ya rasa me zai ce mata amma har cikin zuciyarsa yasan bai taɓa cin karo da mutum a duniya mai karamci da hakurin Bilki ba. Ya yi asara ba kad’an ba. Sai dai ya yi murna da ya bata dama don ta nemi farincikinta a gaba don idan ba haka ba, hak’kinta kad’ai ya ishe shi zunubin da zai hana shi kwanciya cikin salama.
Ya tausasa harshe ya ce “Allah ya yi miki alheri da kansa Bilina na gode Allah ya had’amu da alheri ya shirya mana zuri’armu da ya bamu”.
A hankali ta ce “Ameen.
Daga haka ta tashi ta bude masa kofar ya fice a rikice.
Sai da ya yara suka tafi makaranta ta k’ira Alti d’aki ta fad’a mata halin da take ciki. Suka yi kukansu suka more don Altin ma da take bata hak’uri a yau kukan ta taya Bilki sosai.
Da k’yar suka hak’ura.
Alti da Alawiyya suka fara had’a mata kayan sawarta. Kafin Yara du dawo sun gama had’a wadanda zasu iya.
Sai da daddare ta zauna da ya’yanta cikin hikima ta fad’a musu gobe ko jibi zata koma gidanta amma su zasu zauna a gidansu ne.
Amrah ta ce “Mamah kun rabu ne?”
Ba boye boye ta ce “Aurenmu ne ya k’are amma tunda muna da ku ai bamu rabu ba”.
Hawaye ya k’wacewa yarinyar. Yayin da Farha da Farouk suka yi tsamo tsamo.
Ta yi jarumtar rarrashin Amrah da fad’in kina babba kina kuka su kuma su yi ya ya ke nan?”
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Da k’yar ta shawo kanta ta nutsu ta yi shiru. Ta dinga yi musu nasiha.
Farouk ya ce “Yanzu mu kad’ai zamu zauna a nan side din Mamah?”
A tausashe ta ce “A a tare da Dady sannan Antin ma zata dawo nan din”.
Ya yi shiru amma ba haka ya so ba. Can ya ce “Amma ki fad’awa Dady kada ta ce zata dinga takura mana. Sannan Mahma if possible ki bar mana Alti”.
Bilki ta shanye tausayinsu ta ce “Ku zauna lafiya da Antinku, kada ku yi mata rashin kunya.
Duk abin da ta ce ku yi, to ku yi mussaman ke Amrah.”
Amrah da take kuka sosai ta kasa magana.
Farouk ne ya ce “Mahma to ki bar mana Alti please “.
Sai lokacin Amra ta ce “Maimakon ka bata hak’uri ta zauna da mu sai ka ce ta bar mana Alti?”
Kaitsaye ya ce “Ba zan bata hak’uri ba. Kullum fa sai na ga ta yi kuka duk yadda bata son mu gane.
Kullum Dady ne ya kai anty school da duk inda zata je a mota. Amma when last ya dauki Mamah a motarsa ko kuma mu?Kina ganin Dady yana siyo abu a leda ya kawo side din nan? Amma kullum sai na ga ya kaiwa ta sama abu a leda. Kawai Mahma ki je inda ba za ki dinga kuka ba.” Ni fa tuni na gaji kawai dan ba ni da kudin da zan siya mata gida ne. Duk ranar da na je Abuja zan faɗawa uncle Farouku senior ya siya mata gidan tunda uncle Sulaiman ba dawowa zai yi ba”
Wannan karon Bilki ta kasa jarumta danne kukanta. Ta fashe da kuka ainun yayin da Amra da Farha suke kukan suma amma da yake namiji tun yana k’arami zuciyarsu mai taurice Farouk bai yi kuka ba. Amma idanuwansa sun yi tsilli tsilli tabbacin yana cikin damuwa sosai.
Gabaɗayansu har Alti sai da kukan ya k’wace musu don kuwa duk abin da ya fad’a gaskiya ne. Sannan basu yi zaton Faruk yana ankare da komai ba.
Shi kad’ai ne idonsa babu hawaye.
A hankali ya ce “ku daina kuka ai ba mutuwa za ki yi ba. Shi kuma Dady sai ya cinye gidan “.
Da sauri Bilki ta bige masa baki tare da galla masa harara da manyan idanuwanta da suka yi ja tsabar kuka.
Ya mik’e ya fice yana gunguni. Bilki ta bishi da kallon mamaki da tsoro. Baya rikici da Hawwa shi, asalima da Amrah kawia yake fad’a a gidan. Amma yanzu kam ta ga alama idan ta tafi shine zai fi bawa mutanen gidan matsala ba Amrah ba. Ko da yake Amrah ma ba shiga shirgin Hawwah take yi ba. Kawai ita ce take ce wa Amrah ta raina ta ko ana sakawa ta yi mata rashin kunya. Amma ta lura shi Farouku laifukan ubansu ne danƙare a zuciyarsa.
Ta fara lissafin adadin shekarunsa nan da watanni uku zai cika shekaru goma sha uku. Lallai zata tafi ta bar baya da kura don yanzu shekarun balaga zai fad’a, shekarun da idan ya’ya suka farawa kaiwa sai iyayensu sun kara hak’uri da juriya akan sha’aninsu bare kuma ace suna hannun yarinyar da shekaru kawai ta basu dan shakaru biyar ne tsakaninta da Amra.
Washegari a salube yaran suka tafi makaranta.
Suna tafiya mai kula da gidajensu Bilki wanda tun ma kafin a raba a basu nasu gidajen shi yake kula da su gabad’aya. Don har na baba Babba duk shine wakilinsu.
Ya iso da masu k’atuwar motar d’iban kaya. Dama kuma tun jiya masu kunce gado sun zo sun warwaresu an jingine su, duk kayan kicin dinta masu daraja sun hadesu a kwali wasu ta sake k’arawa Alawiyy akan siyayyar da ta yi mata.
Kayan yara kuwa ba abin da ta dauka illa gadon Farha. Kuma ta bar musu duk abin da tasan zasu bukata na amfani.
Sai lokacin Hawwah ta fara ankara da gidan nasu akwai abin da yake faruwa. Gabadaya Sahal ya susuce ya rasa kuzarinsa ta yi tambayar Har ta ga ji da amsar da ya bata na babu komai.
Bilki bata bar gidan ba sai wata washegarin sassafe a dalilin bata son ta tafi akan idon ya’yanta. Duk da sun fara girma sun wuce a yi musu wanka ko wankin kashi, amma tashin hankalin da suke ciki ba kad’an ba ne. Ita Farha da aka ce da ita za’a tafi bata daina kukan a wajensu zata zauna ba.
Babban zullimin Bilki akan yaranta maganar abincinne da harkar makaranta.
Amma ba yadda zata yi, ta barsu a hannun Allah.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Tare da Alti suka hau saman Hawwah. Ta karbesu ba yabo ba fallasa. Cikin mutuntawa ta ce “Hawwah zuwa na yi takanas na yi miki sallama zan tafi don Ubangiji ya k’arar da zamana a gidan nan. Bayan haka kuma na damƙa miki yara a hannunki. Na sani rikon d’an da ba naka ba akwia wahalar gaske. Sai dai idan aka yi dan Allah aka yi hak’uri za’a ci riba a gaba.
Ga yara nan ki yi hak’uri da su, ki sake ninka juriyarki idan sun miki ba daidai ba, ki gyara musu ta yadda zasu fahimce ki. Idan kuma abin yafi k’arfinki ki faɗawa Babansu.
Allah ya sauke ki lafiya ya ba ki hak’urin zama”
Daga haka ta mik’e tana fadin”Allah ya sadamu da alheri.”
Jikin Hawwah ya yi sanyi sosia ashe abin da ya kwantar da Sahal ke nan a kwanaki biyun nan?
Ta tabe baki. A k’asan zuciyarta tana jin dad’in yadda zata mamaye gidan ita kad’ai. Don kuwa falon Bilki zata mayar da falon yin dabdala ita da jama’arta.
Tana kallo suka fice amma ta rasa kuzarin yi musu rakiya.
Yayin da Sahal yake kwance tunda ya yi sallar asuba ya koma bai tashi ba.
Ba barci yake yi ba, wani irin zazzabi ne yake nukurƙusarsa.
Bilki da kanta ta ja motar tare da Alti suka tafi ta bar Alawiyya sai an tashi zata je ta ɗauko Farha sai su same su a gidanta.
Tunda suka isa gidan ta shige d’akin da aka shirya mata gadonta da kayanta.
Kwanciya ta yi, ita ba barci ba, ita ba ido biyu ba. Komai ya k’wace mata, ita da kanta bata san hak’ik’anin matsalarta ba. Amma dai tunanin ya’yanta yafi komai dagula mata lissafi.
Har yamma tana kwance mussaman da fashin salla ya same ta a safiyar nan.
Alti sau uku tana lek’o ta. Amma ganinta a kwance idanuwanta a rufe sai ta fice a zatonta barci ta samu tunda kwanaki biyu basu yi barci ba.
Sai da magariba ta kawo kai sannan Alti ta sake shiga ta ce “Mahmah kwanciyar zata yi miki yawa. Ke ba azumi ba amma tun safe ba ki saka komai a bakin ki ba.”
Da k’yar Bilki ta bude idanuwanta da suka yi ja sosai ta ce”Ina Farha?”
Alti ta ce “Tana can tare da su Amrah ta k’i yarda ta biyo Alawiyya”.
Murya ba amo ta ce “Dan Allah Alti ki je ki dauko mini ita komin kukanta “.
Cikin rarrashi ta ce”A a mahma rabu da ita. Ai kinsan yadda take ƙulafuncinki da kanta zata neme ki. Amrah zata kula da ita.”
Kan dole Bilki ta hak’ura. Sai dai duk kokarinta na ta ci abinci hakan ya ci tura don kuwa tana yin loma d’aya ta ji komai ya cushe mata.
Kwanaki uku Bilki na cikin wannan yanayin ba cin abinci sannan kullum tana d’aki. Wanka kawai take yi. Hankalin Alti ya tashi k’warai da gaske. Ta tura Alawiyya gidan Basma akan ta taho da ita sabon gidan da suka dawo tunda Bilkin ta kashe wayoyinta gabad’aya ta adana su.
Basma bata yi jinkiri ba, don tare suka iso gidan Bilki a motarta.
Tun yammaci take gidan amma har magariba Bilki na kwance uffan bata ce ba.
Kan dole ta hak’ura ta tafi gidanta. Amma washegari kafin ta je wajen aikinta ta biyo ta d’auki Bilki da Alti kaitsaye asibiti ta kaisu ta ga likita ya rubuta Mata maganin da zata dinga barci da cin abinci don ya ce stress ne da damuwa suka yi mata k’awanya.
Akai akai Basma take zuwa sai dai kullum a sanyaye take tafiya a dalilin yanayin Bilki kullum babu cigaba sai sake cabewa.
Gabadaya yanayinta ba na lafiya ba ne amma kuma ba ta ce bata jin dad’i ko ba lafiya ba. Abin da ya damu Alti da Alawiyya yadda take kwana ta yini a kwance kuma ba cin abinci.
Ranar da suka yi kwanaki takwas su Amrah suka zo gidan. Babansu ne ya kawosu, Farha suka rako a dalilin ta fara kukan wajen Mahma zata. Sai ya taho da su gabad’aya tunda weekend ne ya barsu akan zai dawo ya dauke su da daddare.
Ganinsu cikin rashin damuwa sosia bai sanya Bilki ta ware yadda Alti ta yi tsammani ba. Don haka hankalinta ya rub’anya tashi tare da tunanin uwardakinta ta had’u da lalura basu fargaba.
Cikin kwanaki goma sha biyun da suka yi a gidanta sun yi ne cikin mawuyacin hali don al’amarin na Bilki kullum ba sauki. Idan har ta bude baki ta yi magana to kuwa Farha ce a kusa da ita. Ban da haka sai dai ta rufe idanuwanta ko ta yi k’uri tana kallon gefe d’aya. Alti da Alawiyya ba abin da suke yi sai kuka.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Sannan tafi son zama ita kad’ai.
Wani zuwa da Basma ta yi juyin duniya ta yi da Bilki ta bude baki ta fadi inda ya jefa wayoyinta amma uffan bata ce musu ba sai ido kawai take binsu da shi.
Ta yi wata irin rama ta farat d’aya.

0 Comments