[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: *DINGISHIN KWADO 3* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* *Barar addu'arku* *A irin wannan ranar ta 09/09/2000 Allah ya karbi rayuwar mahaifiyata*. *Ina barar addu'arku da ku taya ni yi mata addu'o'in smaun rahamar Allah*. *Saboda haka na saki page din a maimakon 10 ha wata da na ambata a farko*. *Allah ya jiƙanki Mamah yasa aljannar firdaus makoma da dukkan musulmai gabad'aya*. PAGE 1 Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba. Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara. Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba. Duk yadda sakin nan ya yi mata wata irin mahangurba sai da ta yi jarumtar had'iyewa a gabansa. Da murmushi ta dinga fad'in "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ubangiji na gode da abin da ka yi mini, na gode da abin da kake yi mini. Na kuma gode da abin da zaka yi mini a gaba". Ta kalle shi sai ta ga tamkar nadama ce ta shige shi ta farat d'aya. Gabad'aya jikinsa ya sake ya yi tub'us. Yayin da ita ta kasa fahimtar komai. Ya koma ya kwanta. Tsawon lokaci tana zaune tana sauraran yadda yake barcinsa sannu a hankali ba tare da tunanin komai ba. Ganin ta kasa barci bar biyun dare ya sanya ta yi alwallah ta fara nafila. A cikin sujjuda take kuka tana yiwa ya'yanta addu'ar Allah ya tsare mata su ya kuma k'addara musu kyakkwar rayuwa cikin imani da lafiya. Tana zaune har asuba ba abin da take yi irin tufka da warwara. Ina zata je ne? Sai yanzu ta fahimci girman k'alubalen da yake gabanta. Ta dinga kuka tana yiwa iyayenta da Yaya Sulaiman addu'a. Sai da aka fara k'iran assalatu ya farka. Ya shiga bayi ya d'oro alwallah. Shi ma nafilar ya yi. Sai da ya idar ya ce "Bilkisu ina ba ki shawara ki janye kalaman da kika jefe ni da su, sannan ina ba ki umarnin ki ba ni hakuri don bana son na barki ki tafi kina garari tunda dai nasan ba ki da inda za ki je". Bak'in ciki har mak'oshinta ta ji tamkar ta danna masa ashariyoyi kala kala tsabar bak'incikin da ya taso mata. Amma ta yi kamar ba da ita yake ba domin tana bude baki la shakka zaginsa zata yi wanda hakan kuma ba d'ab'iar mace kamila mai ilimi ba ne. Dan haka ta yi masa bakam. Har aka fara kiraye kirayen sallar asuba bata tanka masa ba. Ya tafi masallaci yana fad'in "Ki yi shawara da zuciyarki kafin na dawo. Ta bi shi da kallon mamaki wataƙila bai fahimci girman tozarcin da ya yi mata. Bai fahimci cewar da ya yi wai bata da inda zata je ma cin zarafinta ya yi ba. Ya manta da kalaman da ya yi wajen sakinta. *Ki je dan iyayenki masu son zuciya na sake ki saki biyu"* Zuciyarta ta buga da k'arfin gaske. Ta ke ce da kuka a bayyane domin k'arshen kaskanci da cin mutunci Sahal ya yi mata. Bayan haka bai ishe shi ba shine yanzu ya zo yana sake cin mutuncinta. Wato ga ni yake yi gidansa ne kad'ai mafakarta? Ashe shiyasa yake tuka mata tuwon wulakanci kala kala tana ta yin hak'uri da kawar da kai tare da yi masa uzziri kan uzziri. Ashe shi duk kallon bata da yadda zata yi, bata da gata yake yi mata? Ta girgiza kai tana fad'in "Ko duk zuri'armu sun k'are ba zan sake zama k'arkashin ikon ka ba. Ko da hakan na nufin na dinga kwana a titi ne. Bare kuma Ubangiji ya riga ya rufa mini asiri. Kuka ta ke sosai wanda ba na zafin sakin ba ne , kuka take yi na yadda gidansu na Funtua ya zama kongo. Da ace Baba Babba na cikin gidan da ko bangarensu zata je ta bude ta zauna har zuwa ta samu nutsuwa. Amma a yanzu fa? Maiduguri zata tafi gidan Ansari ta zauna a hannun yarinyar matarsa ko kuwa Kano zata tafi gidan Yaya Hamida? [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Gidan Yaya Hamida ai ba dolenta ba ne tunda itama a k'arkashin wani take. "Ina zan tafi ni Bilki?" Ta fad'a cikin rawar murya irin ta kuka. Ta yi shiru tana tunani. Gidanta ne ya fado mata. Tana da gidaje a Katsina. Bata son ta zauna a gidanta da suka zauna domin ya yi mata girma a matsayinta na marar aure. Sannan zata so ace ba ita kad'ai zata zauna ba. Take ta tuno da d'aya gidanta mai hawa biyu wanda akwai y'an haya a k'asa, saman ne babu kowa watanni uku da suka shud'e aka yiwa wanda yake ciki sauyin wajen aiki zuwa jihar Jigawa. Shine iyalinsa basu tashi ba sai sati biyu da suka shud'e. Wanccan satin ta je ta ga gidan ta saka a gyara a yi sabon fenti don idan za'a sake karɓa a bata kudi da daraja. Take ta lalubo lambar wanda yake kula da gidajen. Ya dauka yana fad'in "Hajiya da fatan dai lafiya?" Murya ba amo ta ce "Zan tambaye ka ne an kammala aikin gidan nan kuwa?". Da girmamawa ya ce "An kammala fenti Hajiya sink din kicin ne ba'a saka ba amma na siyo sabo yanzu haka ma yana gidan." Ta ce "To ka yi kokari a saka zuwa goman safiyar sannan a share a wanke gidan kafin zuwa azahar din yau. " "To za'a yi hakan Hajiya da ikon Allah. " " Ta ajiye wayar tana jin saukin tashin hankalin da take ciki. Gidan a unguwa mai kyau yake babu hayaninya awon gwamnatine. Matsalar d'aya ce ba ruwan famfo sai dai da rijiya a harabar gidan. Zata samu almajirin da zai dinga d'ebo mata kullum. Zata tafi da Alti da Alawiyya. Duk da auren Alawiyya wata d'aya ya rage . Nan da sati biyu ma zata tafi garinsu. Kawai matsalar da tafi damunta makomar Amrah da Faruk ne. Ya ya zusu yi idan suka tashi Babu ita, babu Farha babu Alti ba Alawiyya?" Ta kifa kanta a akan gado tana gunshekin kukan tausayin ya'yanta. Bata jin zata fasa barin gidan Sahal. Amma tausayin ya'yanta yana matuk'ar tayar mata da hankali. A haka ya dawo ya tarar da ita. Ya zauna a gefen gadon. Ya ce "Ki daina kuka Bilkisu. Ni kaina haka nake jin jikina babu k'wari. Amma maganganunki sun mini ciwo sun tayar mini da hankali. Ki janyesu, ki yi tuba shike nan sai na mayar da ke ki cigaba da zama a d'akinki.". Ta zuba masa ido hawaye yana ambaliya. Ta ce "A a Sahal ai zama a tsakaninmu ya riga ya k'are, tunda na fahimci baka sona, baka bukatata nake ta faɗawa Allah ya kawo mana mafita a tsakaninmu. Ka san ai ban yi shekarun da zan ce bana buk'atar namiji ba. Kai ka samu mafita, ka samu wata ni ce ban samu ba. Da haka kuma ya faru na yi imanin nima tawa mafitar ce ta zo". Da iyakacin gaskiyarsa ya ce "Wallahi Bilki ina son ki. Har yanzu bana jin Hawwah irin yadda nake jin ki a zuciyata. Amma ban san meyasa bana jin sha'awar ki ba. Na dade ina zargin ko saka hannune don ina jin sha'awar matayen da ba su kai ki komai na cikar halitta ba. Amma watan jiya da na ji karatun Shaikh Ibrahim Khalil da yake bada tabbacin ana cirewa namiji sha'awar matarsa ko da kuwa yana sonta. Ganin ina cikin wannan matsalar ya saka na dinga nazarin to ai ni da ke bamu yi irin wannan shekarun da zamu kai ga wannan bigiren ba. Bayan haka na gasgata ina da rauni a wannan fagen sabanin ke da kike da k'arfi bukatar al'amarin. Sai na ji tamkar na ba ki dama ki je ki yi aurenki, amma sai na ji gara mutuwa ta riske ni kafin na ga kin zama matar wani. Amma jiya sai da kika yi mini cin mutuncin da ya zame mini dole na sallama ki". Na goge hawayen na ce "Zaman ne ya k'are." "Yanzu Bilki ba za ki karbi shawarar da na ba ki, akan ki janye kalaman da kika yab'a mini ba? Ba za ki bi umarnina ki ba ni hakuri ba?" Ya fad'a a zabure. Cikin nutsuwa ta ce "Ai duk duniyar nan ba mai sakawa na baka hak'uri Sahal. Don ban yi lalacewar da za'a zagi iyayena yayin da za'a sake ni sannan na bada hakuri ba. " Ya mike yana fad'in"Girman kai ba na ki bane ina jiye miki ragaita duk kasaitaacciyar mace za'a same ta ne a gidan mijinta ko na iyayenta ko na d'anta ko kuma na y'anuwanta shakikai". PAGE 2 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Bata kula shi ba don bata da abin fad'a kuma. Ya sake zama ya sassauta ya ce "kin yi nazarin ya ya rayuwar ya'yanki zata zama idan nabu ke a kusa da su?" Rauni irin na uwa ya shige ta nan da nan, amma ta shanye ta ce "Idan na mutu ya ya zasu yi ne? Kuma a gidan ubansu zan barsu, don ba zai yiyu da gatansu na tafi da su muna ragaita a titi ba. Ni dai da ba ni da gata zan tafi, ko barance na yi". Ya yi shiru da alamu ya gane magana ta cab'a masa. Ta numfasa ta ce"Duk irin musgunawar da ka yi mini na yafe maka darajar ya'yanka. Wannan gidan da aka gina shi da dukiyata Allah ne shaidar na bar maka halak malak, na yafe maka. Amma dan Allah ko ban ci arzikin komai ba a gunka ka dubi Allah ka rike y'ay'anka da amana da tausayawa, na barsu a hannun Allah na barsu a hannunka." Daga haka kuka na sosai ya k'wace mata. Ya kamu da ciwon tausayinta ainun, a sanyaye ya ce "Bilki ki zauna na mayar da ke". Ta kuwa yi wata irin zabura ta mik'e tare da fad'in"Wannan kuwa shine gangan Sahal! " Ina yi maka rantsuwa da Ubangijin al'arshi zama ni da kai ya k'are ila yaumil k'iyama. Ka mayar da ni, na kuma maidu a fuskar shari'a sai dai tunda shari'ar ta ba ni damar idan ina cutuwa na bijire. To ba zan zauna ba. Aure ya haramta a tsakaninmu tunda ka yi gigin mayar da ni dan kuwa a yanzu ba sai anjima ba sai ka sake ni ". Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya ce "Idan ba za ki zauna saboda ni ba, to ki zauna ki reni ya'yanki". A zafafe ta ce"Ba zan zauna ba. Na barwa Allah amanarsu, na barsu a hannun ubansu. Zan je na nemi wanda zai mini adalci, wanda ba zai ga tsufana ba, ba wanda zai ga son zuciyar iyayena ba, wanda zai kashe mini k'ishin da nake fama da shi tsawon lokaci." Kishi mai tsananin gaske ya shak'e shi, har kan harshensa yake jin d'aci. Ya ce "Yanzu so kike na furta miki na ukun a zo a jarrabe mu Bili?" Ta ce "Ba wata jarabawar da zamu shiga ai an gama, ina binka a hankali ne saboda alfarmar da Ubangiji ya baka a kaina amma Wallahi komai zai iya faruwa a tsakaninmu idan ka kafe! Ta fad'a cikin tashin hankali da matsanancin fishi. Ganin zai fita ya sanya ta yi maza ta wuce shi ta rufe k'ofar d'akin. Ta sunkuya ta ja plate din da ta ci tufa a daren jiya. Y'ar karamar wuka ta dauko mai tsini da kaifi ta ce "Ka sake ni ko ka mini sanadin da zan rasa rayuwata gabad'aya don da na zauna da kai gara na kashe kaina na huta da azabar da kake gana mini da raina! Ganin gabadaya ta rikice kuma iyakacin gaskiyarta yake ga ni har cikin kwayar idanuwanta ya sanya ya ce "Na sake ki Bilki! Allah ya yi miki musayen alheri". Ya zauna don sai ya ji jiri na katantanwa da shi. Dukkansu kuka suke yi irin kukan nan mai taɓa zuciya, kukan kaico, kukan da ake jin an tsinci kai ba a yanayin da ake so ba. Shi ya yi jarumtar ce wa "To ki yi zamanki a nan Bilki. Na amince ba zan zo wajen ki ba, kinsan nasan dokokin Ubangiji ina kokarin kùma kiyaye su." Ta girgiza kai ta ce daga yau zuwa gobe zan tafi ba zan zauna ba Sahal. Kuma Wallahi har zuciyata na yafe maka duk irin musgunawar da ka yi mini. Duk hakkina da ka danne mini a zamanmu Ubangiji ne shaidar na yafe maka, bana fatan sakayya ta dawo maka ko ta sauka akan Amrah." Ya ce "Na gode, na gode Allah ya hana ki kuka Bilki. Amma dan Allah zan roke ki arzikin abu d'aya tak. Ki bar Farha a tare da yaran nan, zan rike ta amana." Ba ja in ja ta ce "Ka roki abin da ba zan iya yi maka ba. Mutuwa kad'ai zata raba ni da ita, ko uwarta da ubanta a yanzu basu isa su ce na basu ita ba. Bare kuma ace na bada ita a inda ba dolenta ba. Na dai yi maka alk'awarin zata dinga zuwa hutu wajen y'anuwanta ba kuma kowanne hutun ba. Duk inda rayuwa zata wulla ni to zata wulla ni ne tare da ita, itace kad'ai abin da na mallaka da ba wanda zai mini iko ko ya yi mini gayya da ita." Ta fad'a hawayen tausayin ya'yanta na zuba. Don a yanzu sune damuwarta. Yadda zasu shigo su ga babu ita, babu Farha babu su Alti sai su kad'ai yana matuƙar d'aga mata hankali. PAGE 3 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ya share hawayen idonsa ya ce "Ki yi hakuri, in sha Allah zan iya k'ok'arina akansu sai dai ai ba kamar suna tare da ke ba. Ya mike tsaye ya ce "Ni fa ji nake yi idan har na bar ki kika tafi ni kuma na zauna da wata matar a wannan gidan na yi zalunci." Ta zuba masa ido ta ce "katon zalunci ma kuwa Sahal. Ai ko sakina da ka yi cikin izgilin ba ni da inda zan je ma zalunci ka yi. Shiyasa ni kuma na haramtawa kaina zama da kai. Amma kuma Wallahi tunda aure ya k'are a tsakaninmu har abada, to na yafe maka dukkan kuskuren da ka yi mini har zuciyata in sha Allah ba zaka tashi da haƙƙina ba. Ni kuma Allah ya mini sakayyar alheri albarkacin hakuri da afuwar da na yi maka". Ya rasa me zai ce mata amma har cikin zuciyarsa yasan bai taɓa cin karo da mutum a duniya mai karamci da hakurin Bilki ba. Ya yi asara ba kad'an ba. Sai dai ya yi murna da ya bata dama don ta nemi farincikinta a gaba don idan ba haka ba, hak'kinta kad'ai ya ishe shi zunubin da zai hana shi kwanciya cikin salama. Ya tausasa harshe ya ce "Allah ya yi miki alheri da kansa Bilina na gode Allah ya had'amu da alheri ya shirya mana zuri'armu da ya bamu". A hankali ta ce "Ameen. Daga haka ta tashi ta bude masa kofar ya fice a rikice. Sai da ya yara suka tafi makaranta ta k'ira Alti d'aki ta fad'a mata halin da take ciki. Suka yi kukansu suka more don Altin ma da take bata hak'uri a yau kukan ta taya Bilki sosai. Da k'yar suka hak'ura. Alti da Alawiyya suka fara had'a mata kayan sawarta. Kafin Yara du dawo sun gama had'a wadanda zasu iya. Sai da daddare ta zauna da ya'yanta cikin hikima ta fad'a musu gobe ko jibi zata koma gidanta amma su zasu zauna a gidansu ne. Amrah ta ce "Mamah kun rabu ne?" Ba boye boye ta ce "Aurenmu ne ya k'are amma tunda muna da ku ai bamu rabu ba". Hawaye ya k'wacewa yarinyar. Yayin da Farha da Farouk suka yi tsamo tsamo. Ta yi jarumtar rarrashin Amrah da fad'in kina babba kina kuka su kuma su yi ya ya ke nan?" [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Da k'yar ta shawo kanta ta nutsu ta yi shiru. Ta dinga yi musu nasiha. Farouk ya ce "Yanzu mu kad'ai zamu zauna a nan side din Mamah?" A tausashe ta ce "A a tare da Dady sannan Antin ma zata dawo nan din". Ya yi shiru amma ba haka ya so ba. Can ya ce "Amma ki fad'awa Dady kada ta ce zata dinga takura mana. Sannan Mahma if possible ki bar mana Alti". Bilki ta shanye tausayinsu ta ce "Ku zauna lafiya da Antinku, kada ku yi mata rashin kunya. Duk abin da ta ce ku yi, to ku yi mussaman ke Amrah." Amrah da take kuka sosai ta kasa magana. Farouk ne ya ce "Mahma to ki bar mana Alti please ". Sai lokacin Amra ta ce "Maimakon ka bata hak'uri ta zauna da mu sai ka ce ta bar mana Alti?" Kaitsaye ya ce "Ba zan bata hak'uri ba. Kullum fa sai na ga ta yi kuka duk yadda bata son mu gane. Kullum Dady ne ya kai anty school da duk inda zata je a mota. Amma when last ya dauki Mamah a motarsa ko kuma mu?Kina ganin Dady yana siyo abu a leda ya kawo side din nan? Amma kullum sai na ga ya kaiwa ta sama abu a leda. Kawai Mahma ki je inda ba za ki dinga kuka ba." Ni fa tuni na gaji kawai dan ba ni da kudin da zan siya mata gida ne. Duk ranar da na je Abuja zan faɗawa uncle Farouku senior ya siya mata gidan tunda uncle Sulaiman ba dawowa zai yi ba" Wannan karon Bilki ta kasa jarumta danne kukanta. Ta fashe da kuka ainun yayin da Amra da Farha suke kukan suma amma da yake namiji tun yana k'arami zuciyarsu mai taurice Farouk bai yi kuka ba. Amma idanuwansa sun yi tsilli tsilli tabbacin yana cikin damuwa sosai. Gabaɗayansu har Alti sai da kukan ya k'wace musu don kuwa duk abin da ya fad'a gaskiya ne. Sannan basu yi zaton Faruk yana ankare da komai ba. Shi kad'ai ne idonsa babu hawaye. A hankali ya ce "ku daina kuka ai ba mutuwa za ki yi ba. Shi kuma Dady sai ya cinye gidan ". Da sauri Bilki ta bige masa baki tare da galla masa harara da manyan idanuwanta da suka yi ja tsabar kuka. Ya mik'e ya fice yana gunguni. Bilki ta bishi da kallon mamaki da tsoro. Baya rikici da Hawwa shi, asalima da Amrah kawia yake fad'a a gidan. Amma yanzu kam ta ga alama idan ta tafi shine zai fi bawa mutanen gidan matsala ba Amrah ba. Ko da yake Amrah ma ba shiga shirgin Hawwah take yi ba. Kawai ita ce take ce wa Amrah ta raina ta ko ana sakawa ta yi mata rashin kunya. Amma ta lura shi Farouku laifukan ubansu ne danƙare a zuciyarsa. Ta fara lissafin adadin shekarunsa nan da watanni uku zai cika shekaru goma sha uku. Lallai zata tafi ta bar baya da kura don yanzu shekarun balaga zai fad'a, shekarun da idan ya'ya suka farawa kaiwa sai iyayensu sun kara hak'uri da juriya akan sha'aninsu bare kuma ace suna hannun yarinyar da shekaru kawai ta basu dan shakaru biyar ne tsakaninta da Amra. Washegari a salube yaran suka tafi makaranta. Suna tafiya mai kula da gidajensu Bilki wanda tun ma kafin a raba a basu nasu gidajen shi yake kula da su gabad'aya. Don har na baba Babba duk shine wakilinsu. Ya iso da masu k'atuwar motar d'iban kaya. Dama kuma tun jiya masu kunce gado sun zo sun warwaresu an jingine su, duk kayan kicin dinta masu daraja sun hadesu a kwali wasu ta sake k'arawa Alawiyy akan siyayyar da ta yi mata. Kayan yara kuwa ba abin da ta dauka illa gadon Farha. Kuma ta bar musu duk abin da tasan zasu bukata na amfani. Sai lokacin Hawwah ta fara ankara da gidan nasu akwai abin da yake faruwa. Gabadaya Sahal ya susuce ya rasa kuzarinsa ta yi tambayar Har ta ga ji da amsar da ya bata na babu komai. Bilki bata bar gidan ba sai wata washegarin sassafe a dalilin bata son ta tafi akan idon ya'yanta. Duk da sun fara girma sun wuce a yi musu wanka ko wankin kashi, amma tashin hankalin da suke ciki ba kad'an ba ne. Ita Farha da aka ce da ita za'a tafi bata daina kukan a wajensu zata zauna ba. Babban zullimin Bilki akan yaranta maganar abincinne da harkar makaranta. Amma ba yadda zata yi, ta barsu a hannun Allah. PAGE 4 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Tare da Alti suka hau saman Hawwah. Ta karbesu ba yabo ba fallasa. Cikin mutuntawa ta ce "Hawwah zuwa na yi takanas na yi miki sallama zan tafi don Ubangiji ya k'arar da zamana a gidan nan. Bayan haka kuma na damƙa miki yara a hannunki. Na sani rikon d'an da ba naka ba akwia wahalar gaske. Sai dai idan aka yi dan Allah aka yi hak'uri za'a ci riba a gaba. Ga yara nan ki yi hak'uri da su, ki sake ninka juriyarki idan sun miki ba daidai ba, ki gyara musu ta yadda zasu fahimce ki. Idan kuma abin yafi k'arfinki ki faɗawa Babansu. Allah ya sauke ki lafiya ya ba ki hak'urin zama" Daga haka ta mik'e tana fadin"Allah ya sadamu da alheri." Jikin Hawwah ya yi sanyi sosia ashe abin da ya kwantar da Sahal ke nan a kwanaki biyun nan? Ta tabe baki. A k'asan zuciyarta tana jin dad'in yadda zata mamaye gidan ita kad'ai. Don kuwa falon Bilki zata mayar da falon yin dabdala ita da jama'arta. Tana kallo suka fice amma ta rasa kuzarin yi musu rakiya. Yayin da Sahal yake kwance tunda ya yi sallar asuba ya koma bai tashi ba. Ba barci yake yi ba, wani irin zazzabi ne yake nukurƙusarsa. Bilki da kanta ta ja motar tare da Alti suka tafi ta bar Alawiyya sai an tashi zata je ta ɗauko Farha sai su same su a gidanta. Tunda suka isa gidan ta shige d'akin da aka shirya mata gadonta da kayanta. Kwanciya ta yi, ita ba barci ba, ita ba ido biyu ba. Komai ya k'wace mata, ita da kanta bata san hak'ik'anin matsalarta ba. Amma dai tunanin ya'yanta yafi komai dagula mata lissafi. Har yamma tana kwance mussaman da fashin salla ya same ta a safiyar nan. Alti sau uku tana lek'o ta. Amma ganinta a kwance idanuwanta a rufe sai ta fice a zatonta barci ta samu tunda kwanaki biyu basu yi barci ba. Sai da magariba ta kawo kai sannan Alti ta sake shiga ta ce "Mahmah kwanciyar zata yi miki yawa. Ke ba azumi ba amma tun safe ba ki saka komai a bakin ki ba." Da k'yar Bilki ta bude idanuwanta da suka yi ja sosai ta ce"Ina Farha?" Alti ta ce "Tana can tare da su Amrah ta k'i yarda ta biyo Alawiyya". Murya ba amo ta ce "Dan Allah Alti ki je ki dauko mini ita komin kukanta ". Cikin rarrashi ta ce"A a mahma rabu da ita. Ai kinsan yadda take ƙulafuncinki da kanta zata neme ki. Amrah zata kula da ita." Kan dole Bilki ta hak'ura. Sai dai duk kokarinta na ta ci abinci hakan ya ci tura don kuwa tana yin loma d'aya ta ji komai ya cushe mata. Kwanaki uku Bilki na cikin wannan yanayin ba cin abinci sannan kullum tana d'aki. Wanka kawai take yi. Hankalin Alti ya tashi k'warai da gaske. Ta tura Alawiyya gidan Basma akan ta taho da ita sabon gidan da suka dawo tunda Bilkin ta kashe wayoyinta gabad'aya ta adana su. Basma bata yi jinkiri ba, don tare suka iso gidan Bilki a motarta. Tun yammaci take gidan amma har magariba Bilki na kwance uffan bata ce ba. Kan dole ta hak'ura ta tafi gidanta. Amma washegari kafin ta je wajen aikinta ta biyo ta d'auki Bilki da Alti kaitsaye asibiti ta kaisu ta ga likita ya rubuta Mata maganin da zata dinga barci da cin abinci don ya ce stress ne da damuwa suka yi mata k'awanya. Akai akai Basma take zuwa sai dai kullum a sanyaye take tafiya a dalilin yanayin Bilki kullum babu cigaba sai sake cabewa. Gabadaya yanayinta ba na lafiya ba ne amma kuma ba ta ce bata jin dad'i ko ba lafiya ba. Abin da ya damu Alti da Alawiyya yadda take kwana ta yini a kwance kuma ba cin abinci. Ranar da suka yi kwanaki takwas su Amrah suka zo gidan. Babansu ne ya kawosu, Farha suka rako a dalilin ta fara kukan wajen Mahma zata. Sai ya taho da su gabad'aya tunda weekend ne ya barsu akan zai dawo ya dauke su da daddare. Ganinsu cikin rashin damuwa sosia bai sanya Bilki ta ware yadda Alti ta yi tsammani ba. Don haka hankalinta ya rub'anya tashi tare da tunanin uwardakinta ta had'u da lalura basu fargaba. Cikin kwanaki goma sha biyun da suka yi a gidanta sun yi ne cikin mawuyacin hali don al'amarin na Bilki kullum ba sauki. Idan har ta bude baki ta yi magana to kuwa Farha ce a kusa da ita. Ban da haka sai dai ta rufe idanuwanta ko ta yi k'uri tana kallon gefe d'aya. Alti da Alawiyya ba abin da suke yi sai kuka. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Sannan tafi son zama ita kad'ai. Wani zuwa da Basma ta yi juyin duniya ta yi da Bilki ta bude baki ta fadi inda ya jefa wayoyinta amma uffan bata ce musu ba sai ido kawai take binsu da shi. Ta yi wata irin rama ta farat d'aya. Ta birikice sosia tamkar ba Bilki sola ma'abociyar kyan fuska da zati ba. Basma bata da lambar Abida yanzu. Ga shi bata da ta Yaya Hamida. Ta kalli Alti ta ce "Ban Ga wayarta bare mu shaidawa wani nata halin da take ciki. Da hanzari Alti ta ce "Ina da lambar Farouk da Saddiqa." Nan da nan Basma ta ce "Ba ni ta Yaya Farouku ". Alti ta mik'a mata wayarta ta ce "Duba za ki ga Faroukun Mahma". Basma ta lalubo layin bugu biyu ya dauka ya ce "An buga an bar ki Altin Bilki". * Ya fadi hakan a zatonsa Alti ce. "Ba Alti ba ce Ya Faruƙu. Basma ce kawar su Abida" Shima da ya ke ya santa nan da nan ya gane ta suka gaisa. Cikin hawaye Basma ta ce"Ya Faruk za ku bar Bilki ta mutu ne ba wani a kusa da ita?" Cikin tashin hankali Ya Faruku ya ce" Subhanallahi wani abu ne yake faruwa da Bilkin?" Basma ta karɓe da ce wa" Abubuwa da dama sun faru. Aurenta ya mutj sannan kuma tana kwance cikin mawuyacin hali ". "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Tun yaushe?" Ya tambaye ta a sukwane . A sanyaye Basma ta ce "kwanaki sha shida ke nan". "Subhannallah ya furta a takaice". Ya numfasa ya ce "Yanzu a ina take ?" Tana gidanta na unguwar Alkali". Ya ce "Zan zo in sha Allah. Allah ya bata lafiya." Ta amsa da ameen a sanyaye. PAGE 5 Washegari wajen azahar kamar daga sama sai ga yaya Faruku a gidan Bilki. Ganinsa da Bilki ta yi ya sanya kukan da ya kafe mata tunda ta shigo gidan ya k'wace mata. Ta dinga yinsa tamkar zata hadiye zuciyarta. Gabadaya ya rikice ya rasa kalmar da zai yi amfani da ita wajen yi mata magana. Komai ya tsaya masa cak domin ya ganta cikin mawuyacin halin da duk dakiyar zuciyar mutum sai ta motsa. Da ƙyar ya bude baki ya ce "Bilkisu ki yi hak'uri, ki daina irin wannan kukan! Duk abin da ya samu bawa mukaddarine daga Allah. Bawa kuma ba ya wuce k'addararsa." Bilki ta tsananta kukanta ainun wanda ya sake jagula zuciayar Yaya Farouku. Ya tausasa harshe ya ce "Fad'a mini damuwarki na magance miki ita Maigado" Ta kasa ba shi amsa saboda kukan da take yi. Sai da ta numfasa don kanta. Cikin kuka ta ce" Ba ni da matsala, ina kukane saboda jiya aka fad'a maka halin da nake ciki, amma yau ka yi asubanci ka bar komai ka taho tunda ga Abuja don ka ga halin da nake ciki. Ko na rasa komai a duniya na tabbatar ba zan rasa ka ba yaya Farouku". Karon farko da ta bude baki ta yi maganar da bata shafi Farha ba. Tausayinta ya yi matuk'ar kama shi, don ya fahimci ta yi amannar ta rasa duk wanda yake da muhimmanci a duniyarta. Dawowarta gidanta alamace na ta gamsu ta rasa dukkan muhimman mutane a duniyarta da zata zauna a kafaɗarsu. Ya sunkuyar da kansa idonsa ya cika da k'wallar alhini. A ransa yake fad'in zumuncinsu bai yi lalacewar da Bilki zata yi zaman kanta a shekarunta ko da kuwa babu Baba Babba a duniya ba. Ya tausasa harshe ya kalle ta da kulawa sosai ya ce "da yau zan juya don ban yi zaton aurenki ya mutu ba. Amma tunda hakane zan kwana kafin su Alti su shirya miki kayanki tare da ke zan tafi". Ba ja in ja ta ce "Na gode sosai na kuma tabbatar zaka yi mini komai a rayuwata, ban tankwabar da kokarinka ba. Amma bana son na kawo maka hargitsi a gidanka. Ka yi hak'uri duk abin da zaka yi mini, ka yi mini ina da ga nan". Tsawon lokaci suna muhawara amma fir Bilki ta kafe ba zata bar Katsina ta gode da k'ok'arinsa. Alti ta kyafta masa ido fahimtar hakan ya sanya ya yi shiru, yayin da Bilki ta runtse idanuwanta a zuwan barci take yi. Daidai lokacin Alawiyya ta kawo masa abinci. Ya zuba ya ci abinsa suna hira jefi jefi da Alti. Ganin haka ya sanya Bilki jan bargo ta lullube jikinta har fuskarta. Da ya kammala ya yi mata magana amma babu amsa kan dole ya hak'ura ya yi musu sallama. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Alti ta bi shi k'ofar gida ta ce "Yaya Farouku kada fa ka yi fishi da Mahma gabad'aya fa ba a hayyacinta take ba. Sannan ba zata yarda ta bar Katsina ba, ba don komai ba sai don ya'yanta." Ya girgiza kai tare da fad'in "Ko zata mutu kuwa sai ta bar Katsina. Su mata basa tunanin komai da kowa sai ya'yansu? To idan ya'yan suka mutu suka bar ta sai ta fasa rayuwa ke nan? Ko kuwa idan ita ta mutu ya'yan suma mutuwa zasu yi?" Alti ta yi shiru don bata da ta ce wa akan sha'anin, amma itama kam da za'a samu a raba Bilki da garin da tafi son hakan tunda zullimin da take ciki kada mijinta ya ce ya mayar da ita don bata yiwa Bilki fatan komawa hannun wannan mutumin. Ya ce "mu je na sake yi mata sallama ko zata amsa" Suka shiga har d'akin suka tarar har lokacin tana lullube ruf ya kaurara murya ya ce "Maigado! Ta bude fuskarta sannan ta bude idanuwanta ta zuba su akan fuskarsa. Ya numfasa ya ce "Zan je na bincika asibitin da ya dace Ki dinga ganin likita. Gobe da safe ki shirya da wuri zan zo na d'auke ki da Alti zuwa asibitin". Kai ta daga masa tabbacin ta ji. Ya numfasa ya ce "Za ki je ai ko?" Nan ma sake gyada masa kai ta yi alamun zata je din". Daga hakan ya ce "To na tafi sai goben". Ta d'aga masa hannunta na dama alamun bye bye. Ya fita a matuk'ar sanyaye don ba zai yaudari kansa ba. Bilki ta samu matsala. Har mota Alti ta raka shi tana ta yi masa fatan alheri mai yawa. Tunda ya tafi yake ta nazarin asibitin da zai kai Bilki. Karshe dai ya ya make shawarar ya kaita babbaan asibitin gwamnati don yafi son kwararren likita ya ganta. Sai yamma ya samu nutsuwa bayan abokinsa da yake pharmacist ne a cikin asibitin ya ba shi tabbacin Su zo karfe tara na safe zai had'asu da likitan da zai duba ta. Washegari kuwa k'arfe takwas a gidan Bilki ta yi masa. Ya tarar Alti na fama da ita ta kurbi ko ruwan shayi ne amma ta k'i. Haka ya ɗebe Su zuwa asibiti. Basu sha wahala ba suka ga likita. Ya yi dube dubensa tare da tambayoyi wanda sau d'aya Bilkisu ta amsa Duk Alti ke ba shi amsa. Ya kalli Farouku ya ce "Depression ne ya shige ta! Don duk alamomin cutar sun bayyana a tare da ita. Zan d'ora ta akan magani sannan a dinga samar Mata da nutsuwa tare da yi mata abubuwan da zai ɗebe mata kewa tare da sanya nishadi." A sanyaye Yaya Farouku ya ce"Za'a kiyaye Dr. Ya mik'a masa hannu suka yi musabaha, ya yi godiya sannan suka tafi. Mota ya bude musu suka shiga, shi kuma ya wuce ya siyo magungunan sannan ya yiwa abokinsa godiya. Tunda suka hau titi ya tausasa harshe ya dinga yi mata nasiha da muhimmancin yarda da k'addara. Ba zato suka ji ta ce '"Na gode sosai Yaya Faruku. Zuwan da ka yi Katsina don ni ya tabbatar mini ina da sauran gatana". Idanuwansa suka cika da k'walla amma ya sanya jarumta bai bari sun zuba ba. Da suka isa gidan ya ce "Maigado ki daure ki ci abinci don na tabbatar kin ji dad'in zuwana da gaske." Ta yi k'asa da kanta. Ya ce "A zubo miki?" A hankali ta ce "Eh." Da azama Alti ta zubo mata kunun gyada da ta yi mata tun dare ya zuba a flask amma bata sha ba. Ta karba ta kafa kai ta shanye nan da nan ta mik'a mata kofin. Dad'i ya kamasu sosai. Alti ta ce "To ke fa? Rashin cin abincin ma ai jinya ce babba." Ya numfasa ya ce "Bilki ina son na tafi da ke Abuja kuma tare da Alti zamu tafi ta cigaba da kulawa da ke ". Nan da nan idanuwanta suka cika da k'walla ta dinga girgiza kai tabbacin ba zata bi shi ba kenan. Ganin zata sake rikice wa ya sanya ya ce "To Shi ke nan ki zauna a nan din amma ki dinga shan maganinki akan kari. Idan lokacin komawa asibitin ya yi zan dawo da kaina na mayar da ke". Murya ba amo ta ce"Ubangiji ya fini yaba maka Yaya Farouku ". PAGE 6 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Sai ta yi kamar ta fad'awa yaya Farouk batun motar da ya ce zai siya mata, tunda ya saka ta bayar da tata, har Anisa ta k'ira ta yi masa godiya. Sai kuma ta fasa tare da tunanin bai manta ba. Rannan wajen karfe d'ayan dare ta tashi ta yi fitsari, ta fito a band'aki sai ta ga wayarta na haske. Sai da ta kwanta sannan ya dauki wayar ganin wasu lambobi a jere iri d'aya ta gane layine na mussaman. Ta ajiye bata dauka ba. Kafin ta yi tunanin waye mai layin, k'iran ya sake faɗowa wayarta. Ta saka hannu ta amsa tare da kangawa a kunnenta. Murya ba amo ta yi sallama. Ya amsa ba alamun barci a muryarsa. Gabanta ya buga Yaya Asad zai bugo mata waya da tsakar dare?" Kafin ta samu amsar tambayarta. Ta ji cikin wata irin ya ce "Maigado na tashe ki ko?" A sanyaye ta ce"Ba komai". Ya numfasa ya ce "Ya yanayin aikin ba kya samun matsala ko?" "Ba wata matsala". Ta ba shi amsa a takaice. "Ya ce "Ma sha Allah! Dama zan tambaye ki ne wacce irin mota kiki so , don bana so ki dinga tahowa a taxi ba idan an tashi tunda na ga Abida ke kai ki da safe ko?" "Eh ita ce, amma mun yi magana da Yaya Farouku zai siya mini. Ka bar ta na gode". Ya sake tausasa harshe ya ce "Ga shi kuma na yi niyyar yi miki alheri Maigado. Shike nan sai ki had'a biyu, ko ki ce masa ya siya miki wani abin amma mota kam ni zan siya miki". Abin alheri ya yi mata amma ko kusa bata ji dad'in alherin ba. Don kuwa ta tabbatar akwai abin da zai biyo ba. A takaice ta ce"To na gode, Sai da safe ". Ya sake yin k'asa da muryar ya ce "Ko za ki daure na turo miki hotunan motocin ta what'sapp ki zaba so nake a kawo miki da wuri " Har cikin zuciyarta sai da ji nishin da ya yi kunne a kunnenta. A kidime ta ce "To" tare da katse kiran zuciyarta na bugawa sosai. A fili ta furta "Duk masifarka bana sonka, ba namijin da zan sake sa shi a zuciyata idan ba Yaya Farouku ba." [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Tsabar kidimar da ta shiga ya sanya bata bude what'sapp din ba. Sai da ta ga yana k'iranta ta what'sapp din sannan ta katse ta duba. A zabure ta tashi ta zauna ganin motocin gararin da ya turo mata da zasu lashe millions of naira wai ta zabi wacce take so. Ta murtsuke idanuwanta sosai dan ta sake gasgata ita Bilki ake yiwa tayin ta zabi guda cikin wadannan motocin? Ta tabbatar dai ba gizo ba ne . Sai ta rubuta masa wadannan duk sun yi mini yawa. Waɗanda basu kai wannan ba ta isa. Ya ce "Amma tunda ba rokona kika yi ba, bai kamata na ce ga yadda nake so, ke kuma ki ce yadda kike so za'a yi ba ko?" "Hakane" Ta fad'a a takaice domin ta ji tamkar ya ji haushi ne. "Kawai ki zabi kalar da kike so". Ya fad'a cikin sigar umarni. Maimakon ta yi masa voice irin yadda yake yi sai ta sake rubuta masa "Farar". "Yauwa Maigadona! Na gode miki sosai Allah ya saka da alheri". Tana mamakin jin godiyar da yake yi tamkar ba shine ya kamata ta yi masa godiyar ba. Ta jijjiga kai tana fad'in komai ma kake nufi ba yiwuwa zai yi ba dan ba kunyar wadda zaisa na k'wari kaina. "Wai Maigadona! Ta furta a bayyane. Ta juya tana gyarawa Farha kwanciya. Ta saki tsaki tare da fad'in "Ko ta ina na zama tasa?" K'ira ya sake fadowa wayarta. Ta rasa yadda zata yi haka ta dauka akan dole. "Maigado kin yi barcine?" "A a Farha na gyara ta kwanta kan hannunta ". "Sannu da kokari to" Ta share tamkar bata ji ba. Ya nisa ya ce "Maigado barci kike ji ne?" Murya ba amo ta ce "um" "To bari na k'yale ki haka nan, zamu yi magana da safe. Stay blessed". Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa ta bi wayar da kallo cikin sake mamakin sabbin hallayar da yaya Asad ya tsiro da shi zuwa gare ta, sai take jin wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara. Ita fa ba yarinya ba ce ta san manufarsa akanta kuma sai dai ya yi haƙuri ba zata taɓa sonsa ba, ba ruwanta da kuɗinsa balle muƙaminsa ya je wani waje ya nemo matar aure dan kuwa ita bai mata ba. Tunda ga ranar yaya Asad kullum da daddare sai ya kirata yana kashe mata murya, tare da hilatarta. Ita dariya ma yake ba ta ɗauka yake yi ba ta gane manufarsa ba nan ko kallon shi kawai take yi tana dai biye mishi sama sama domin ta ga iya gudun ruwansa, har zuwa ranar da zai furta manufarsa ita kuma a lokacin za ta taka masa burki ta faɗa masa gaskiyan cewa ba ta son shi daga nan sai ya kama kan shi da ita. Haka Bilki ta cigaba da gudanar da kyakyawan rayuwarta a gidan Baba Babba ba ta da matsalar komai, gata da wani irin tattali ake nuna mata kamar su lashe ta, ihum kawai za ta ce a taso mata ana tambayanta ko tana son wani abu, ta samu kwanciyar hankali ta fara mai da jikinta kamar ba Maigadon da Sahal ya sukurkutawa rayuwa ba. Ta dawo cikin natsuwarta sai da ta ɗan sauya, wasu sabbin daɓi'u ta fito da su na abu kaɗan ne yanzu yake ɓata mata rai nan da nan za ta ruɗe ta fara faɗa daga nan sai kuka saboda cutar da ta yi na depression shi ya sa yanzu kowa ke lallaɓa ta, har Abida duk tsiyataku ta ta daina yi mata, kaffa kaffa take da ita sosai, zama suke yi su yi hira na tsawon lokaci suna dariya har da shewa, sannan su kan raba dare a ɗakunan juna suna hira. Ana cikin haka ne irin zuwa ɗakinta da Abida take yi suna hira, ranar ma sun daɗe suna ta hira har wajen sha biyun dare Yaya Asad yana ta k'iranta a waya ta ƙi ɗauka Allah ya taimake ta, ta sanya wayar a silent da Abida ta lura da ta yi mata ɗan biki. Suna cikin hirar Abida ta zama serious. Tace "Maigado zamu yi magana muhimiya! Amma amanatul amana". Bilki ta fara dariya tana tuna yarintarsu da lokacin da Abida ta ke siyar da jarida, idan kuma ba na kuɗi ba ne sai ta ce Amana ne. "To Abida idan kuma subutar baki yasa na faɗa ma wani fa. A ranar lahira ta ci ni gudan jini ya faɗo?" Suka kwashe da dariya har suna tafawa suna tuna lokacin yarintarsu da abubuwan da suka faru. "Kai ba abin da ya fi ƙuruciya daɗi Abida."; Bilki ta faɗa tana ɗan share ƙwalla daga gefen idanuwanta. "Kamar jiya ta dawo. Kowa ya fi more lokacinsa a lokacin yarinta." Bilki ta ce "haka ne kam suna tuno yaya Munnira suna cikin tsananin kewarta. PAGE7 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ta fad'a da alamun rashin sukuni. Nan da nan Abida ta bata rai ta ce "Wallahi tunda na shirya sai mun je, ke ba dama a yi miki abin arziki sai kin gwasale mutum?" A sanyaye Bilki ta mik'e ta ce "To jiramu mu shirya". Don tasan tunda Abida ta rantse to idan har bata kubutar da ita daga yin kaffara ba sai sun yi rikici mai tsananin gaske. Ita kuma a yanzu da suka shirya bata son su sake b'atawa da Abida. Farha ta fara shiryawa cikin wani leshi Mai kyau Wanda aka yi masa kawataccen dinkin da ya sake fito da ainihin kyaunsa. Kai gaskiya telan d take bawa dinkin Amrah ta k'ware wajen iya d'inkunan yara.() Ta fesa mata turare, sannan ta ce ta je falo wajen junior ta jirata. Tunda suka dawo Abuja fir Farha ta ki sakewa da Abida. Duk da ko ina ta yi sai junior ya bita shi kam yana sonta tamkar yadda take son Yaya Farouk. Ita ma cikin Egyptian abaya din ta Maman asalan da asala ta shirya () Ta kalli fatarta a madubi yadda farinta ya sake bayyana ga shi fatarta ta yi taushi ainun. Tunda matar Yaya Asad ta rasa rayuwarta a dalilin canja surar halitta da canja launin fata Bilki ta yi matuk'ar tsorata. Ta tsaya a iya mayukanta na oriflame da Aisha Lame ta zaba mata tun shekaru biyu da suka shud'e. Ta kuma gasgata ingancin products din oriflame. Babban abin da yasa ta likewa Aisha Lame saboda yadda ta nakalci rabe raben fatar dan adam tamkar wata shararriyar likitar fata. Ta shafa hoda ta gogo man lebe a bakinta. Sai ta feshe jikinta da turarenta mai dad'in gaske. Ta same su a falo tare da Momi. Suka yi mata sallama sannan suka fice tare da y'ayansu. A motar Abida suka fice. Bilki a gaba yaran a baya yayin da Abida take tuki. Kaitsaye millenium Park suka je. Suka dan yi chilling da hotuna. Sannan Bilki ta yanka cake tare da taimakon Farha. Wani hoton da Abida ta d'auki Bilki ya yi matuk'ar yin kyau Ta saka shi a status ta yi caption da cewa" Happy Birthday Maigado." "Haka Mai gadon ta fita?" Yaya Asad ya yi tagging hoton yana tambayar Abida. Sai ya ga kamar kyan da ta yi, kamar kowa a wajen ita yake kallo. Kishi ya ji ya turniƙe shi from no where. Ganinta a status din Abida duk sai ta sukurkuta shi ya ji ba zai iya sake wani dogon jira ba, yana son ya mallaki maigado cikin gaggawa kafin soyayyarta ta yi masa illa. Abida ko da ta ga maganarsa sai ta tura masa emojin dariya. "Haka muka fita dai." Sai ta tura masa wanda suka ɗauka tare da Balki itama abayan ne a jikinta amma na ta ɓaka ce. "Lalle zan zo na samu Baba Babba. Ya sake muku da yawa." Haka ya ce mata ta bi shi da dariya. Abida tana mamakinsa to menene abun da bai kyautu ba a tare da su? Ranar sai dare suka koma gida washe gari dalleliyar motar ƙirar Toyata da Yaya Asad ya siya mata ta iso gida tunda Abida ta ƙyalla ido ta ga motar nan ta buga tsalle ta ce itama ba ta yarda ba sai an siya mata irinta. "Tab lalle ne ma Yaya Asad ɗin nan, tunda Bilki da dawo gidan nan ya manta da ni. Wallahi nima sai ya siya mini wacce tafi ta Bilki tsada." Ta fad'a tana kumfar bakin ya yi son kai, tana shinshino wani abune a ransa game da Maigado. Momi ta gaji da mitar Abida ta saka baki da cewa ita ba tana da mota ba, ya siya mata kwanaki baya. "Ai itama Bilkin tana da mota. In adalci ne ya siya mana gabaɗaya mana." Abida ta fad'a tamkar ta fashe da kuka. Baba Babba ya dinga dariya yana fad'in" Abida rigima." Duk da haka ba ta haƙura ba sai da ta bi Bilki har ɗaki ta tsare ta da tambayoyi. "Bilki me yasa yaya Asad ya siya miki wannan motar? "To ni ina zan sani, ki kira shi ki tambaye shi mana" Bilki ta bata amsa tana cunno mata baki. Abida ta yi jim kafin ta ce" Baku da gaskiya daga ke har shi. Kuma idan bai siyo mini tawa ba. Billahillazi abin da ya faru a 2022 zai sake maimaituwa a wannan shekarar da muke ciki." "Ya dade bai faru ba Abida ". Bilki ta bata amsa cikin murya marar amo. "Haka kika ce ko Maigado? Da ni kike zancen, Allah sai na fasa kwan ai tuni na harbo jirginsa." PAGE 7 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Bilki to be sincire magana nake so mu yi dake, amma heart to heart." Abida ta faɗa tana mai kallon Bilki a tsanake itama ganin haka yasa ta gyara zama tana sauraranta da dukkan nutsuwarta. "Bilki ki ji tausayina! Ki duba halin da na ke ciki don Allah ba na ba ki tausayi?" Ta faɗa tana mai nuna kanta muryarta har ya fara karyewa tana shirin ta fara kuka. Abida mai taurin taurin zuciya amma yanzu rayuwa ta sanya duk ta yi laushi. "Abida ina tausayin ki mana. Amma me ya faru ne?" Bilki ta faɗa itama cikin damuwa ganin sauyawar Abida lokaci ɗaya. "Dube ni fa Balki. Magana ta gaskiya ki ji tausayina ki faɗa mini in da Ya Sulaiman yake in kin sani. Ki duba shekaru uku ba kwana uku bane, ba sati uku bane haka nan ba wata uku ba ne, don girman Allah ki faɗa mini in dai kin san inda yake Bilki.". Abida ta faɗa cikin karyewar zuciya. Bilki ta yi tsam tana kallonta cikin wani yanayi na tausayin Abida tare da madaukakin mamakin yadda take cikin alhini da kewar Yaya Sulaiman. A sanyaye ta ce "Wallahi Abida na rantse miki da Allah tun ranar da Yaya Sulaiman ya bar gida ban ƙara ji daga gare shi ba. " Ta faɗa tana mai kallon Abida da ta yi tsuru kawai tana kallon Bilki. "Ki yarda da ni. Wallahi da na sa ni da zan faɗa miki." "Na yarda da ke Bilki. Shike nan mu bar maganar. Ba sai an ji ba" Kawai sai ta fashe da kuka har da gunji, jikin Bilki ya yi sanyi k'alau itama bata san ta fara hawaye ba sai da ta ji danshi a saman kumatun ta. Tare suka zauna suka sha kukansu, ita Abida tana kukan gararin rashin mijinta ita kuma Bilki tana yin na rashin Yayanta da tausayin Abida. Tasan kuma danne abin take yi a ranta dan kada a fahimci fargar jajin da take ciki. Ranar ma tare suka kwana bayan sun gama kukan su nan Abida ta bingire ta fara barci sai da asuba ta farka. Haka rayuwa ta cigaba da garawa Bilki ta hak'ura da dukkan zuciyarta mussaman da fahimci ya'yanta basa cikin mawuyacin hali sai kewarta da suke yi. Kullum ne sai sun yi waya sau biyu sau uku. Domin tana ganin yadda take shiga farinciki in ta ga Ya Faruku ko ta ji ana mganarsa har gobe Maigado ba ta daina son Ya Faruku ba, kamar yadda shima tana da tabbacin bai daina son ta ha amma dai a yanzu ne ta kasa gane yanayin shi tun da yadda yi ma Balki wani kulawa ta musamman. Washegari ya kama Birthday ɗin Bilki ne sai ga wani kayataccen cake mai delevery ya kawo dauke da sunan Maigado at 36 ɓaro ɓaro a jiki. Mamaki ya kama Bilki domin kuwa ita gabad'aya ta manta da yaune ranar haihuwarta gabad'aya. Ta dinga tunanin wa ya aiko da wannan tsadadden cake din?. Zuciyarta ta harba don kuwa take ta hasaso mata Yaya Asad. Don shine ya lank'aya mata Maigado har kowa ya kama, sannan shi ko kudi da yake raba musu a envelop lokaci zuwa lokaci Maigado yake rubutuwa a jikin tata. Koma wanenne ta ji dad'i don sai kana da muhimmanci a wajen mutum yake tuna alamuranka mussaman har a rike ranar haihuwarka, ita ta shaafa'a ma 1 ga watan Aprilu ce yau. Abida na ta fad'in tasan Ya Faruƙu ne ya aiko da sh. Itama Bilkin fata take yi ace daga Yaya Farouku din ne. Ta dinga jin farinciki na mamamyarta. Tabbas tana son Yaya Farouku zata jure komai indai zata same shi. Duk sababin Jamila wannan karon ba zata bar mata shi ba. Duk da Balki jin ta kawai take yi amma ita jikinta ya ba ta ba kowa ya aiko da wannan cake ɗin ba sai Ya Asad. Nan da nan Abida ta yi wanka ta shirya cikin tsaleliyar Egyptian abaya ta() Ta shirya junior. Da yake asabar ne duka muna gidan. Ta leko ta ganni kwance a gado Farha ma a kwance amma ta yi filo da cikinsa. Tana tambayar sauara kwana nawa su yaya Farouk su zo wajensu Kafin Bilki ta amsa mata. Abida ta bude kofar. Ganinsu a kwance ba alamun komai ya snaya ta bude baki ta ce "Bilki wai ba shirya kuke yi ba dama?" A sanyaye ta ce "Ni kawai ki dauko mu yanka anan. Me ya mini dad'i ne da zan tafi wani waje da sunan ina birthday! PAGE 8 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Tun daga ranar Abida ta fara tsokanta da Amaryan yaya Asad, yayin Balki ta yi ta masifa tana kufuluwa, don bata son wannan maganar ta yi tasirin da Yaya Farouku zai sake janyewa daga kud'irinsa akanta. Dan haka kullum take bawa Abida amsa da fadin "Allah ya tsare ni ya je can ya nemi amaryansa." Abida kuwa bata fasa ba, don sosai take dariya idan ta ga yadda take fusata, ji take yi da auren Maigado da Ya Asad zai tabbata da tafi kowa farinciki da murna, amma tana ganin Bilki zata yi gardama, tunda ta lura da Bilki tafi son fararen maza. Ya Faruku ma da ya zo ya ga mota sai da ya furta. "Lalle Babban yaya alama da zafin sa ya kutso. Mu yara sai mu mu yi baya " Balki ta ji zafin maganarsa sosai ta ɓata rai tana kallon shi kafin ta ce" Ya Faruku abin da za ka yi mini ke nan?" Kana nufin abin da nake ga ni a idanuwanka wannan karon ma iska zai bi?" Ya kasa bata amsa sai kawai ya tafi babu sallama. Zuciyarta ta yi kunci bata yi zaton zata sake son wani namiji kwana kusa ba. Amma tabbas son Yaya Farouk ya kutso da k'arfin gaske daga inda ta sakaye shi a zuciyarta. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ana cikin haka sai ga Yaya Asad ya zo gidan. Bilki na wajen aiki. Gidan ba kowa sai Baba Babba, Momi ta je asibit ganin likita a dalilin ciwon k'afa ya matsa mata. Dan haka suke ta hirarsu da Baba.Tsawon lokaci yana zaune so yake Baban ya ɗan taɓo masa maaganar aure sai ya kawo masa maganar Bilki amma shiru Baban Allah bai sa ya yi masa maganar ba. Haka nan ya tashi jiki ba ƙwari . Ya yi masa sallama tare da ce wa gobe zai dawo ya duba momi. Yana harabar gidan ya ga an bude kofar ya ga motar Abida ta danno. Ya tsaya har ta fito ta nufo shi suka keɓe daga shi sai ita. Dama tana jiransa ne tana zuwa ta fara masa kukan me yasa ya siyawa Bilki mota ita bai siya mata ba. Kowa sai ya rika nuna ya fi son Bilki akan ta, haka ma Yaya Faruku yake yi mata tun suna yara yanzu ma sun girma ba a daina banbanta su ba. Ya nisa ya ce "Ho Abida! Yanzu nutsu ki saurare ni da kyau. Zan siya miki mota irin ta Bilki. Wacce kala ki ke so?" Ta shagwabe fuska ta ce "Golden". "To zamu yi magana, idan kin ba ni gudunmawa akan lamarin to da wuri motarki zata iso". Ta murmusa tana jin ba abin da ba zata yi masa ba. Ya maze sosai sannan ya ce "Abida yanzu ba za ki taimaka mini a halin da nake ciki ba,? Kin fa son har yau ina son Maigado ba sai na zo na faɗa ba ya kamata ki taimaka ki taya nemin soyayyarta ba sai na fad'a miki ba". Abida ta kunshe dariyanta tana kallon yadda yayan nata ya yi wani laushi Shegiya Bilki tasan gwara kan maza, mazan ma irin su Ya Asad. "Abida ki yi wani abu in son na killace Maigado a gidana cikin lokaci ina matukar son haka in kika tabbatar da faruwan haka zan jiyar dake dukkan daɗin duniya ba mota ba har ko jirgi idan ina da hali zan siya miki Abidan Baba." Abida ta ji wata dariya ta sake kawo mata wannan karon ta kasa dannewa sai da ta fito "Abida na zama abin dariya ne?" Ya tamba a kufule. "Abida da gaske nake yi ba. Ina son Maigado.". Ya faɗa yana bayyana mata yanayin da yake ciki tausayin shi ya kamata ta san cewa yana sonta tun suna yara idanuwan Bilki ne suka rufe a wancam lokacin saboda wannan yaron yanzu kuma bata son me yasa ta sake runtse idanuwanta akansa ba. "Ya Asad kaima da taka matsalar fa gaskiya.'" "Menene matsalan tawa faɗa mini zan gyara in dai Maigado za ta saurare ni." "Matsalar mu mata bama son idan ana son mu a yi ta kewaye kewaye. Gwara kawai ka fito ka faɗa mata gaskiyan abin da yake zuciyarka. Ballatana yanzu Maigado ba yarinya ba ce ta san abin da take so ta san abin da ba ta so, gwara ka tunkare ta da full confidence ka faɗa mata abin da yake zuciyarka. Ya yi shuru yana sauraranta kafin ya jinjina kai ya ce" Haka ne Abida na gode. Cake ɗin nan da na aiko Maigado ta so shi kuwa?" Abida ta yi wata dariya kafin ta ce' Daman kai ka turo shi,? Munafuka shi ya sa ta ƙi yin magana ashe ta san daga kai ne." Dariya kawai ya yi bai yi magana ba. "To kai Ya Asad ma kana da makamai a hannunka. Yanzu kawai harsashinka za ka dasa in ya shiga ka fara harbi. Ka samu lokaci ka zo ka ɗauketa ku je wajen da bakowa sai ku kaɗai ku yi magana. Ka jajirce ka nuna mata soyayya ɗan text massages ɗin nan na Friday da na good morning, sannan ka riƙa kiran ta a waya, kana nuna mata ita ce sarauniya duk yadda kake busy ka samu lokacinta sosai. Yadda za ta ji cewar aikinka bai sha gaban ta ba, idan kuma duk ka yi haka ka ga bata fahimta ba sai ka samu babanku ka faɗa masa, shi sai ya yi mata magana." Ya Asad ya gyaɗa kai kafin ya ce" To kina ganin idan Baba ya yi mata magana za ta amince ne?" Abida ta yi shuru kafin ta ce" Wallahi ban sani ba, ka san yanzu Bilki ta canza tunda ta yi deperession ta zama wata irin fitinanniya abu kaɗan ke sakata fushi da kuka, ni saboda yanayinta yasa bana ma shige mata kar na cika matsawa a samu matsala." Duk ya aminta da mganganun Abida cikin kwarin gwiwa ya ce" Na gode Abida zan yi kuma amfani da shawarwarinki." PAGE 9 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ta jinjina masa kai kafin ta ce' Allah ya ba a sa',a Ya Asad Ubangiji ya taka yaƙin nan." Ta fada tana dariya shima yana taya ta. Juyawa ya yi ya koma gaban Baba Babba. Ya fara yi masa jirwayen cewa za a tura su seminar Lagos kuma daga can yana tunanin za a tura shi America domin samun horo kan matsslolin tsaron da muke fama da su a Nigeria. Baba Babba ya kalle shi yana faɗin" Kai Asad a kullum ba ka da wata magana sai ta aiki. Aiki aiki dai ba ka tunanin ma sake ajiye iyali ko ba domin kanka ba domin mutumcinmu iyayenka da yayan ka, kana da yara yanmata da suka isa munzalin aure. Da bakinka ka ce mini iyayen manemin Aysha suna so zo tambaya, a haka zasu zo su same ka, ba ka da mata sai yawon an tura ka can aiki, an tura ka can, kana ganin zaman ka a hakan alheri ne? Anya ka yiwa kanka adalci Abubakar?" Ya faɗa yana kallon Asad ɗin da ya sadda kan shi ƙasa. Sai da Baba ya dire faɗan sa, sannan ya ɗago ya gyara zema yana faɗin. "Baba sai ka ta yi mini faɗa akan zancen aure. Alhalin bani kaɗai ba ne bani da auran nan, ga yara nan a gaban ka. Gwara Abida da aure a kanta Maigado fa? Ai ba ta da aure amma ba a takura mata ba sai ni?" Ya faɗa cikin ɗan ɓata rai shi a dole ba shi kaɗai ba ne. Baba Babba ya karɓe da ce wa" Kai ba ka duba Bilki lallaɓata ake yi? Ta shiga gararin rayuwa kala kala ga rashin miji, ga mutuwar iyaye ga shi an raba ta da garin da yaranta suke yaka ke so ta yi? Ai Bilki abar tausayi ce, idan ba a rarrashe ta an gayyato mata farinciki ba me kake so a yi?" Ya Asad ya ji daɗi an zo gabar da take so. "To ni Baba ka bani ita na aura. Sai na taya ka rarrasan maka ita." Ya faɗa yana sosa kansa alamun kunya. Cikin mamaki Baba Babba ya kalle shi kafin ya ce" Asad da gaske kana son Bilkisu?" Kansa na ƙasa ya ce" Wallahi Baba ina son ta, tsakanina da Allah! Farinciki ya bayyana a fuskar Baba Babba. "Idan kana son Balki to ka nemi yardarta idan ta amince, nima na amimce kasan yanzu ba yarinya ba ce tana da wannan damar sannan kar ka manta ko da suke yara ban yi musu auren dole ba bare yanzu tana da y'ancin ta yiwa kanta zaɓin da take so. Idan ta amince da kai to zan fi kowa farinciki zan kuma taya ka da addu'a Allah ya tabbatar. Idan har hakan ya faru komai zai daidaita, wakiar da ta nisantamu da juna zata bushe a zukatanmu. Ƴan'uwanta za su samu damar zuwa gidanka su yi zumunci, kai ma naka za su je gidanta, daga nan komai da ya faru na rashin jituwa a baya zai wuce ba na fatan na mutu na barku a cikin wannan halin. Sulaiman ya tafi ba mu san inda yake ba, idan yana raye Allah ya bayyana shi. Idan kuma ta san inda yake ta boye mana, idan ta zo hannunka kana hillatar ta duk za mu ji komai." Yaya Asad ya ji ƙarfin guiwar tunkarar Bilki a wannan gabar tunda ya samu amincewar Baba Babba da Abida. Dama Abidan yafi ji da Usman amma tunda Abida bata botsare ba yasan Usman ba zai samu tallafi ba. Mamakin yadda Abida ta huce ta yi sanyi akan ahalinsu Bilki yake yi. Da Bilki ta dawo ba wanda ya yi mata zancen zuwan Asad shi yasa ba ta san ya zo gidan ba. Shi kuma tun tafiyar shi kullum da safe zai tura mata sakon gaisuwar safe da asubar fari. Da daddare ma akwai na mu kwana lafiya. Ga k'iran waya akai akai, yana kashe murya yana yi mata kalamai irin na jirwaye duk da ta fahimci manufarsa amma sai ta nuna masa bata gane komai ba. Kuɗade masu nauyi yake turo mata akai akai, idan ta ce sun yi yawa ko ya daina. Ce mata yake yi idan Sulaiman ne ya tura mata kuɗi ai karba za ta yi ta gode masa, ba ta ce bata so ba jin haka yasa jikinta ya yi sanyi, bata sake ce masa komai ba, idan ya tura mata kuɗi sai dai ta yi godiya amma a cikin zuciyarta ta kudire yayaa Asad ba zai iya siyan soyayyarta da kuɗi ba. Kuma tana jiran ranar da zai gaji da ƙumbiya kumbiyarsa ya fito fili ya faɗa mata, daga ranar za ta fada masa ya daina wahalar da kansa don kuwa bata ra'ayinsa.[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: A ranar da take wannan tunanin ya yi mata sakon yana so ya shigo gobe tana gida? Ta amsa masa da cewa tana wajen aiki. Bai ce mata komai ba sai ta ɗauka tunda ta ce tana wajen aiki ya fasa zuwa ne. Sai me? Washegari zuwan da yamma tana ma shirin tashi daga wajen aiki sai ga wayarsa har sau uku, ba ta ɗauka ba sai da ya sake kira ta ɗaga nan yake shaida mata yana harabar ma'aikatansu ta NAFDAC. Mamaki ya kama ta, ta ɗauka wasa yake yi sai da ta leka ta taga ta gan shi tsaye shi kaɗai ba masu tsaron shi sannan kamar ba da mota yazo ba. Dariya ta kusa subuce mata ganin gogan ya ci k'ananun kaya har da uban zanzaro. Dole ta tattara komai nata ta yi sallama da abokan aikinta ta fito haraba tana mai kallon Ya Asad tana danne dariyantan in har saboda ita ya yi wannan gayun, to ta gwasale domin ba ta jin zai sace zuciyarta da haka. Ita ta ɗauke shi a motarta suka bar haraban ma'aikatar. Cikin nutsuwa ta ce "Gida zamu je ko gidanka zan ajiye ka?" Cike da kulawa ya ce "Yunwa nake ji sosai Maigado. Mu je L&N mu ci abinci ". Zuciyarta ta harba amma ta had'iye komai. A hankali ta ce "To sai ka dinga nuna mini inda zan bi kasan ba ko ina na sa ni a Abuja ba. Idan kuma zaka karbi tukin to?" Murya ba amo tsabar yadda ya shagala da kallonta tare da ayyana al'amura masu yawa akanta. Ya ce "Mu je zan yi guiding din ki in sha Allah ". Bata ce komai ba ta cigaba da tukinta. Bayan sun je sun natsu ya yi musu oder abinci daga ita har shi suka ci abincin domin itama yunwa take ji, kuma bai dame ta da magana ba sai da suka gama cin abincin suka natsa.. Sannan ya kalle ta yana sake gyara zama. Bilki itama kallon shi take yi tana raya saka kananun kaya ba zai zama tawaya gare shi ba, tunda kullum cikin zanzaron kakinsu na yan sanda yake. "Maigado." K'iran sunanta da ya yi shi ya katse mata tunaninta. "Na'am Baban Bilkisu." Ta amsa tana kallonsa. "Yau ga ni a gabanki ba a matsayin yayanki ba sai a matsayin masoyinki. Mai barar neman yardarki." Ya yi shiru yana kallonta domin fahimtar yanayinta. Ta yi k'asa dakanta tana wasa da zoben zinaren da yake hannunta. Ya numfasa ya ce "Ina sonki kamar me, wani irin so nake yi miki da ba shi da alak'a da sha'awa, k'yale kyalen rayuwa. Tun kina budurwa nake sonki har yau din nan da kika zama uwar ya'ya ban ji son nan ya gushe ko ya ragu ba. Dan Allah Maigado kada ki bari ki sake subuce mini a karo na biyu. Ki ji tausayina ki kalli dinbin soyayyar da nake yi miki. K'addara ce mai karfi ta sake had'a mu. Idan a da kin k'i karɓar soyayyata saboda ina da mata, to Ubangiji ya sake hadamu a yanzu alhalin ba ni da mata. Ki ba ni dama na nuna miki dinbin soyayyar da nake yi miki Balkees". Ta yi shiru ta kasa ce wa kanzil. Maigado ɗago ki kalle ni.' Ya sake faɗa cikin wani irin amo. Amo irin na ma'abota soyayya da bege. A hankali ta ɗago tana kallonsa saboda jikinta ya mutu da kalamansa. "So nake na killace a d'akina, na yiwa sauran maza kwalelenki. Dama ɗaya nake so ki ba ni. Damar da zan mayar da ke sarauniya da ta yiwa mata dubu zarra. Don Allah Balkees kada ki tankwabar da soyayyata, na yi miki alkwarin za ki yi farinciki a tare da ni in sha Allahu." Ya faɗa kamar ya yi mata kuka. Bilki ta ga idan ta zauna tana jin kalaman bakinsa tausayinsa zai kamata ta iya ba shi dama, shi ya sa kawai ta haɗe rai tana kifta idanuwana kafin ta nisa ta ce "Gaskiya Baban Bilki ka yi hakuri. Ba yanzu na shirya sake aure ba " Ta fada kai tsaye tana kallonsa Gabansa ya faɗi murya na rawa ya ce'" Haba maigado, me yasa za ki ce haka? Ai ba za ki dauwama ba ki yi aure ba, tunda ya zama mahadin rayuwa kuma aurene mutuncin mutum mussaman mace." "Ni dai gaskiya ka yi hakuri. Kai yayana ne shi ya sa ba zan so na ɓata maka lokaci ba." Cikin mazarin jiki ya ce" Maigado ba za ki bukaci yin shawara ba?" "Bana bukatar yin wata shawara na riga na faɗa maka matsayata." Saboda kar ya sake yi mata wata magana ta ɗau jakarta ta bar shi a wajen. Yana kiranta, amma ba ta dawo ba, ta bar sa a wajen ta shige motarta ta kama hanyar gida. Shi kuma hankalin shi ya tashi nan take ya kira Abida ya fada mata abin da ya faru. PAGE 10 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Cikin ruɗewa Baba ya ce" Subhanallah me ya faru kuma Maigado?" Amma ta kasa daina kukan, yi take yi har tana gunji yana fidda sauti har sai da Abida ta baro ɗakinta zuwa falo domin ta ji kuken Balki sai ta yi turus ganinta durƙushe gaban Baba tana kuka, duk da ba ta san dalilin kukan ba amma a zuciyarta ta zargi kan maganar Asad ba ne. "Daina kuka yi shiru Maigado. Ki faɗa mini matsalarki, Ai ba dole zan yi miki ba. Ya faɗa cikin sigan lallashi ganin yadda Balki ta ruɗe da kuka kamar ranta zai fita. "Baba." Bilki ta kira shi da girmamawa "Na'am Bilkisu." Ya amsa mata cikin kulawa. Kai tsaye ta ce" Baba don Allah ka bar wannan batun. Ni gaskiya kallon d'anuwana nake yi masa, bayan haka babu wata alak'a da zan k'ulla da shi". Ta fad'a cikin kuka na sosai. "Share hawayenki magana an barta. Amma abin da nake so da ke, dan Allah Maigado ki bawa masu sonki dama. Kada ki ce za ki juyawa aure baya. Aure sutura ne kuma mutunci ne. Allah ya yi miki zabin alheri " Daga nan ya sallame ta ganin har lokacin ba ta daina kuka ba. Abida ta ji haushin Bilki ainun ko kunya ba ta ji ba? A gaban Baba Babba za ta ce ba ta son ɗansa? Gaskiya Bilki bahaguwa ce ta k'arshe. Ba ta nuna mata ba, amma dai ta rage mata walwala alamun ta hasala ita kam Bilki bata san tana yi ba, murna ma take yi tun da Baba ya ce an bar maganar tana son kuma zai dakatar da yaya Asad daga nacin da yake yi mata, shi ya sa ba ta ma kula da yanayin Abida ba, ballatana ta fahimci tana jin haushinta ne. Ba zata yi auren da bata so ba. Bilki ta sakankance Baba ya takawa Ya Asad Burki akanta tunda ta ce ba ta so, amma sai me? Sai ta ga ma kamar ya sake kunno kai ne zuwa gare ta da cewa ba gudu ba ja da baya kiran waya saƙonni haka zai baro wajen aikinsa ya zo mata yana takurata mata ita kuma ba za ta iya masa wulakanci ba da za ta iya wallahi da ta yi masa ko ya shafa mata lafiya. Ranar juma'a ya tafi Auka ta jihar Anambra. Tun yamma yake k'iranta tana ga ni ta yi biris da shi. Asabar tana idar da salla wayarta ta fara kuwwa. Tasan shine , ta k'yale. Sai dai Kiran ya cigaba da shigowa babu gajiya. Ta gaji ta amsa amma a zafafe don kuwa ya yi matuk'ar shiga rayuwarta. "Assalamu alaikum Maigado! Ya fad'a cikin taushin murya sosai. Ta amsa murya babu amo. "Jiya na yi ta kiranki, baki dauka ba, sannan ba ki biyo baya ba". "Ban samu lokaci ba ne". Ta fad'a a gajarce tana tuna lokutan baya da take k'iransa da niyyar gaisuwar zumunci baya dauka sannan ba ya biyo sawunta. Ya tausasa harshe ya ce "Yanzu Maigado ba za ki ji tausayina ki raba ni da zaman kad'aicin da nake ciki ba. Menene aibuna ne da kike ta yi mini yawon k'i tuntuni?" Ya bata tausayi amma ta maze ta ce "Baka da aibu amma gaskiya Baban Bilkisu bana ra'ayin aure a yanzu, sannan ko zan yi to gaskiya ba da kai ba. Kallon yaya nake yi maka, ka yi hakuri kawai, mu bar shi a haka". "Gaskiya ba zan iya hak'uri ba Maigado! Ya fad'a da dukkan gaskiyarsa. Ta hassala ainun tare da fadin "Ni fa na ce bana yi, na faɗa maka, na faɗawa Baba kuma na san ya faɗa maka. To gaskiya ka shafa mini lafiya dan kuwa gaskiya ka takure ni ". "E tabbas ya faɗa mini kin ce ba kya so na." Ya faɗa cikin wani irin sauti marar amo. "To kuma duk ka san da haka binbinin da kake yi mini na mene ne?" Ta tambaya a fusace saboda ta gaji, yana takura mata da yawa. Maimakon ta ji ya fusata ya ce ta yi masa rashin kunya. Sai ta ji yana fad'in "Saboda ina son ki. Ina son na killace ki a gidana shi ya sa na kasa haƙura na ƙyale ki." Mamaki ma ya hana ta magana sai kawai ta yi masa shiru tana jin sa yana ta mata magiya cikin wata yar murya mai kama da nishi wai shi a dole sai ya ja ra'ayinta, shi bai san ma haushi yake ba ta ba. Da ta rasa yadda zata yi da kasalar da yake haifarwa gangar jikinta sai kashe wayarta ta yi saboda gabad'aya nishinsa ya ruru mata jikinta. PAGE 11 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "To ka bar komai a hannuna Ya Asad ba dai ka fada mata ba ai ka gama mai wahalan." Daga haka suka rabu saboda damuwa da tashin hankali ma. Tawagarsa ya k'ira suka dauke shi tamkar yadda suka kai shi Nafdac office. Abida kuma ba ta yiwa Bilki maganarsa ba ko da ta dawo, saboda ba ta so ta fahimci kamar za ta yi mata dole ne, amma tana lura da ita domin ta samu wata damar da za ta kawo mata maganar. Kwana uku tsakani, ranar jumma'a bayan Baba Babba ya dawo daga masallacin Bilki ta zo wajensa suna hira. A cikin hiran ne ya kalle ta yana fadin"Bilki ina son na yi wata magana da ke." Bai ba ta damar maganar ba ya cigaba da fadin" Aure nake so na yi miki Bilki. Saboda ina son na ganki kin samu natsuwar irin ta aure, ko Abida da kika ga ban yi mata maganar aure ba ina ji a jikina Sulaiman na nan a raye kuma ina ji a jikina zai dawo in sha Allahu " Bilki ta yi shiru kawai gabanta na faɗuwa. "Idan har zai yiwu ina son na ba da auranki a karo na biyu Bilkisu." Baba Babba ya sake fada mata.. So take ta ji wa kuma Baban zai aura mata. "To Baba." Ta amsa mishi tana son jin wane ne? "Idan kin amince Asad zan aurawa ke. Ya zo ya duka mini da rokon na ba shi auranki, nima kuma na so ku da juna amma duk yadda na so abin idan har ba kya so, to ba zan yi miki dole ba saboda sharia ba ta ce na yi miki dole ba" Bilki ta kalli Baba Babba ta kasa fadin uffan sai kawai ta fashe da kuka har da gunji kamar wata k'aramar yarinya. *Surayya Dee* [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Duk wulakancin da take yi masa bai saka ya karaya ba. Ya dinga yi mata manyan kyautuka masu gigita tunani. Ana haka ya je Dubai. Sai ga shi ya siyo mata wani murtukeken bangle da zobensa kallo daya zaka yi ka gane zinare ne sannan ya lashe manyan kudade na gaske. A lokacin Momi ta farga ta gane Asad zawarcin Bilki yake yi ka'in da na'in. Bata nuna adawa da lamarin ba, tunda ta san Baba Babba zai yi faricinciki idan al'amarin ya tabbata, tunda auren nasu ne zai ƙara daidaita zumuncin gidan da ya shiga halin ni y'asu. Sai da ya fara nunawa momi tsarabar Bilki. Ta ga ni da walwala a fuskarta ta ce "Amma ina na Abida kasan tana ga ni zata hau rikici tunda Bilki kishiyarta ce". Ya yi murmushi ya ce "Rabu da ita Momi sau nawa ina siyo mata? Ina ce bara ma da na je Saudiyya sai da ta ce na siyo mata sarƙa kuma na siyo mata. Bilkin ma dan ta gane da gaske nake yi ne ba wasa ba." Ya kammala fad'a yana shafa kansa . "To ma sha Allah, Allah yasa rabonka ce, zan yi farinciki da hakan." Ta faɗa tana mirmishi, ba shakka idan ya samu Bilki ta san ya gama morewa. "Amin Momi. Gata nan tana ta yi mini tutsu ki taya ni shawo kanta." Ya fada cikin jin kunya. "Ba ruwanmu a ciki. Ka cigaba da ƙokari in sha Allahu za ta amince." Ya amsa da Allah yasa tunda kowa na ba shi k'warin gwiwa ai sarewa bana shi ba ne yanzu. Bai tafi ba, yana zaune yana dakon isowarta. A falo ta tarar da shi, shi kad'ai, fuska babu sukuni ta zube sosai ta gaishe shi tare da yi masa sannu da dawowa. Daga haka ta doshi k'ofar da zata shige ciki ta nufi d'akinta. Takaici ya mak'ure shi. Ya bude murya ya ce "Maigado ke nake ta jira, zo ki ba ni mintina goma mu gaisa nasan a gajiye kike." Kan dole ta dawo ta durkusa har k'asa daga gefe tamkar basarake gaban basarake. Ya yi tsam yana jin wulakanci ne kawia yake Sawa take yi masa irin haka. "Maigado tunda na yi tafiyar nan nake ta mafarkinki. Yau kuma sai na yi mafarkin kin haifa mini boy". Ta tsuke fuska sosai ba ta tanka masa ba. Ya nisa ya ce "Wannan bacin ran fa? Ki daina yi mini haka mana dan Allah! Ya tura mata k'aramar leda mai kyau wacce take d'auke da tambarin United Arab Emirates. Ledar kanta abin sha'awa ce bare kuma kayan cikinta. A sanyaye ya ce bangle da ring ne suka birge ni na siyo miki su a Dubai kin san k'asar suna da gold sosai". Da k'yar ta bude baki ta ce "Na gode ". "To ki bude mana" A hankali ta ce "Ina fama da indigestion afuwan zan shiga ciki". Ya mike da sauri yana fad'in "Sai na sake zuwa Maigadona". Washegari kuma ya dawo da Kaya fal leda na Farha da su Amrah. Da girmamawa ta ce "Hidimar fa ta yi yawa Baban Bilkisu dan Allah ka daina". "To ni ai ba ke na siyawa ba. Ya'yana ne babu ruwan ki a ciki." Sai ta kasa yin magana dole dai kanwar na k'i ta yi masa godiya. Tunda ya dawo ta kuntatawa kanta ta daina walwala. Idan zai kwana yana k'iranta a waya ba zata dauka ba. Idan ya zo gidan kuwa bata yarda su kebe. Ganinta ma sai idan ta dawo yana gidan to dole ya ganta, nan ma sai ta gabatar da uzzirin band'aki zata shiga. Daga haka kuwa ba zata yarda ta fito ba. Abida ta Fara kufula da alamarinsu, yana tsananin son Bilki, ita kuma tana tsananin k'insa. To ya hak'ura mana shi da ake ta yi masa tallan y'anmata zabga zabga ma. Wajen shadayan dare ta k'ira shi a waya. Da kaushin murya ta ce "Dan Allah dan girman Allah Yaya Asad ka hak'ura da Bilki haba na gaji da wulakancin da take yi maka." Asad ya yi shiru yana jin ta. Kafin ya sauke numfashi yana fadin" Abida ina son Maigado irin son nan mai wuyar a bar shi". "To yaya Asad za ka yi ta bin ta ne tana maka wulakanci? Da girmanka da darajarka! Abida ta fada cikin hassala. "To ya zan yi! Allah ne ya jarabace ni.". Idan ba za ki taimaka mini ba kar ki ce na daina bin Maigado Abida." Ya fada kamar zai yi kuka, sai ya bata tausayi. "Ya Asad tunda har ka yi mata magana ba ta amince ba, Baba ma ya yi mata magana ba ta ji ba to mafita daya ne yanzu ya rage." "Mene ne mafitan Abida?' Ya tambaya a sukwane. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Ya Faruku ne. Shi ne kadai mafitar da ta rage maka. Idan kuma ka gwada a bangarensa ba a dace ba to ka rabu da Bilki ba za ta amince ba Wallahi." Shiru ya yi kafin ya ce" Kina ganin idan Faruku ya yi mata magana za ta amince? "Tabbas domin nan duniya Bilki tana ganin girmansa da mutuncinsa, sannan komai ya yi mata umarni tana yi, amma idan dai har shima ka tura shi ba ta amince ba am sorry to say Ya Asad ka haƙura da ita kawai." Tafaɗa cikin ba shi tabbacin haka. Shi kuma ya ce mata ya yi mata alkwarin idan har ya turo Faruku ba ta amince ba to zai hakura da ita. Da haka suka rabu da Abida. Da maganar ya kwana a cikin ransa gari na wayewa, ya kira Faruk ya ce masa ya zo gida ya same shi yana son ganinsa Faruku bai kawo komai ba tunda daman yana kiran shi a gida su zauna su tattauna. Sai dai yau ya ga bambamci domin Asad ɗin wani mazurai ya fara yi masa yana tsare gida sannan ya fara masa wasu tambayoyi. "An ce mini yarinyar nan Maigado na jin maganar ka ko? Sannan idan ka bata shawara tana karɓa?" "Haba kwamishina ba girman ka ba ne. Wannan muzaran fa? Faruku ne fa? Ka yi maganarka kawai in sha Allahu ina tare da kai." Ya Asad na jin haka ya gyara zama yana fadin" Faruku ba za ka taimake ni ba, tunda dai tana ganin mutuncinka, ka taimaka mini na samo kanta, kana ganin ina zaune ba mata kuma burinku na yi aure, itama tunda ba mijin gwara mu haɗu mu sanya Babanmu farinciki, tana ta wahalar da ni, na kuma san idan kai ne ka ce kana sonta, ba za ta yi maka haka ba, kuma tunda har ka ambata ka bar mini ita, ka taya ni mana ni na same ta, ko hankalina zai kwanta ina son ta Allah ya sani an jarabce ni akanta. Ina son ta kuma zan cigaba da son ta har abada, wallahi zan rike ta amana da gaskiya, kuma na yi maka alkawarin zan sanya ta farinciki. Don Allah ka taimaka mini Faruku na aminta da kai a cikin y'anuwana na sake jin ce wa kai na musamman ne daga lokacin da ka hakura da ita saboda ni, ka haramtawa kanka ita saboda ni, na kuma shaida ka yi mini kara da kyautatawa mai yawa" Hankalin Faruku ya tashi idanuwansa suka kawo k'walla. Ba domin Asad ba, da shima ba gudu ba ja da baya akan Bilki sai dai ya shaida kuma ya san ce wa Aasad ya fi shi sonta, ya fishi buk'atar mace a kusa da shi, ita ma kuma tana bukatar namijin da zai so ta ya kula da ita, ta samu gidan da za ta huta wahalarta ta baya ta shafe daga tunaninta. Nan take ya ce masa kar ya damu ya ba shi lokaci in ya yi magana da Bilki zai neme shi domin ya ji yadda suka yi. Asad ya yi ta masa godiya har ya ji kunyan shi ya ɗan daɗe a gidan suna hira kafin ya yi masa sallama ya tafi yana fita ya kira ta a waya suka yi magana. Ya fad'a mata zai tura mata wani adireshi za ta zo gobe da yamma ta same shi akwai wata maganar da za su yi tunda asabar ce babu aiki. Bilki na ta murna kamar an biya mata hajji, a tunanin ta yaya Faruku ya gaji da boye boye zai bayyana mata sirrin zuciyarsa kwana ta yi farinciki ita dai fatanta ta rabu da maitar Yaya Asad. Washegari bayan la'asar Bilki ta sha kwalliya ta yi kyau har sai da Abida ta zolaye ta da cewa ko wani bazawarin ta samo musu? Sai ta ki magana ta fice tana ta dariya farincikinta ya kasa boyuwa. Wani garden ne inda Ya Faruku ya tura mata nan ta nufa da taimakon map ko da taje ma ya riga ta isowa. Bayan sun gaisa sun yi hira sannan ya gangaro kan batun da ya zo da shi. "Bilkisu." Ya kira sunan ta ta amsa cikin dakewa. "Naam" Ta amsa cikin shauƙi. "Kina da burin sake komawa gidan uban ya'yanki?" Kai tsaye ta ce masa "a a ba ni da wannan fatan har abada." Ita fa murna kawai take yi anzo wajen. Yau Ya Faruku zai furta yana son ta. Ita kuma yana cewa yana sonta za ta amsa, ta kuma ce ya faɗawa Baba Babba sati daya ma ya isa su yi auransu. Ya faruku ya yi shuru yana kallonta kafin ya ce" Kin tabbata kin hak'ura da Sahal?" Ta sake ba shi tabbacin ita fa ta hakura sannan ta kara da cewa. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Ni fa Ya Farouku ba ka san ma wata mgana ba. Ko Alti ba ta sani ba. Aurena da Sahal ya haramta. Saki biyu ya yi mini ni kuma na saka shi ya karishe mini dayan saboda wani dalilina da ba sai na fada maka ba." Jikin Ya Faruku ya sake yin sanyi ya kalle ta yadda take kallon shi tana mirmishi. Jira kawai take yi ya furta ta amince masa. "Bilkisu! Ya sake k'iran sunanta a nutse sosai. "Na'am" Ta amsa cikin zakuwa. "Maigado idan na yi iko da ke za ki yarda na isa na yi din ne! Ba za ki ga na so kaina ba?" "Ba wannan tsakaninmu yaya Faruku ka isa da ni kada ka yi kokwanto" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Ina so na bada aurenki " Bilki ta yi kaseke tana kallonsa saboda ba haka ta yi tsammanin ji daga gare shi ba. "Ga wa?" Ta tambaya cikin mamaki k'warai da gaske. "Ga Yayanki Asad" Hawaye suka kece mata, ta kasa magana saboda ya shammace ta irin sosai din nan ". "In dai kin aminta da kaunar dake tsakaninmu. To ki sani ba zan cutar dake ba, ba zan yi miki sanadin wahala ko tozarci ba". A wannan karon kasa amsa masa ta yi. Ya sake tausasa harshe cikin rarrashi ya ce "Ki duba ni, ki amince ki karbi auran nan da zuciya d'aya ki jira ki ga yadda Ubangiji zai karrama rayuwarki." Bilki ta fara kuka mai sauti tana fadin" Ya Farouku me ya sa ba kai ba? Me ya sa ba ka ce kai ne za ka aure ni ba ? Kana cutar da ni. Tun ina budurwan kasan ina son ka, kai ma na san kana sona amma saboda wani banzan dalili ka haramta mans cikar burinmu. Yanzu kuma bayan na dawo ka daɗa ja na a jiki ka sanya mini sonka da mararinka, ina ta tunanin ce wa wannan karon zan same ka mu yi rayuwa tare. Zuciyata tana girmamaka tana sonka, shi ne za ka zo mini da wannan maaganar alhalin ina jin nauyinka. Ni dai gaskiya tunda ba sona kake yi da gaske ba, to kawai mu bar shi a hakan, ka bar batun mutumin can". Ta gama fada tana kuka wurjajan kamar wata karamar yarinya. Hankalinsa ya tashi ya ji ina ina ma da ace zai iya da shima ya murza hularsa ya fito zawarcinta amma kuma ina ba zai iya ba. "Bilki ki yi hakuri don Allah ki saurare ni". Ya fada cikin karfin hali kafin ya cigaba da fadin. "Ba ki ga gwara na zauna a matsayin danuwanki yafi akan mu yi aure ba? Ana iya yin aure a rabu duk matsananciyar soyayyar da take tsakani kuwa. Amma duk lalacewar zumunta ba'a rabuwa gabad'aya, ba yadda za'a yi ace mini tsohon yayanki ne, saboda har abada ba za'a rabu ba, duk hargitsin rayuwa kuwa. Ina sonki sosai, ina kaunar ki har cikin zuciyata ina mana fatan Allah yasa mu cikin masu soyayya saboda shi wanda sakamakonsu aljanna ne. Sau tari rayuwa tana zuwa mana ba yadda muka tsammace ta ba. Ba sai mun yi aure ne cikar soyayya ba Bilki! Don kuwa ina tabbatar miki ko kin rasa kowa a duniya ki ji a ranki kina da ni ". Jikinta ya yi laushi zuciyarta ta narke mussaman yadda ta ga k'walla ta cika idanuwansa ga soyayyarta ta bayyana a cikin idanuwansa da gangar jikinsa gabad'aya. Hakan da ta ga ni ya sake sanya kukanta ya tsananta ta dinga goge hawaye da majina da tissue. Yayin da jarumtar Yaya Farouku ta k'wace don kuwa hawayen shi ma yake yi ba tare da ya ankara ba. Ya yi maza ya zaro tissue ya goge idanuwansa. Tsawon lokaci sun kasa ce wa komai, fama kawai suke yi da tafasar zuciya. Sai shine ya sanya jarumta ya ce " Ya kike ganin za a yi yanzu Bilki?" Cikin shakewar murya ta ce. "Ni kam wannan bawan Allah ya matsa mini. Tsakani da Allah ya zalunce ni! Ya je ya nemi wata mana. Dole sai ni, tsofai tsofai da shi zai ce yana sona " Ta faɗa cikin taɓara da shagwabar da ta sake narkar da zuciyarsa. Dariya ya yi kafin ya ce" To ban da abin ki Maigado ai ni da Asad ɗanjuma ne da ɗanjummai ni nake binsa fa, shekaruna da nasa gaf suke ai". Cikin shagwaɓa ta ce "Ni ina ruwana ko ka girme shi ni dai kai nake so ba shi ba." Ya kalle ta yana sake yin dariya kafin ya ce" Maigado ba kara, ba ki ji kamar zan ji wani iri ba, a gabana kike kushe Kwamishina?" Tana hararan shi ta ce" Oh Yaya Faruku nuna mini kake yi wata kusan ta fi wata ko? Da sauri ya ce" Ba haka nake nufi ba Bilkisu ki yarda da ni". PAGE 12 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "To yanzu ya ke nan kin amince na ba shi auranki?" Tana tura baki tace" ya ci arzikin ka, ba dan ina sonsa ba" "To na gode da nake da arzikin da zai ci. In dai zaki zauna lafiya ki ba shi farinciki ki mutunta shi, ki girmama shi ai kin gama mai wuyar son da yake yi miki ya isa ya rike auranku." Haka ya zauna yana ta faman lallashintaa da ban baki har ta saki jiki ta ce ta amince. Sai gab da mangriba duka suka bar wajen kowa ya shiga motarsa, kafin su rabu sai da ya sake jin ta bakinta ta ce ta aminta. Tana mota ma kafin ta kai gida sai da ya kirata. "Bilki kin aminta da kwamishina ba sauya magana?. Kaitsaye ta ce" Na amince yaya Faruku." "To zan turo shi " Ya faɗa yana yar dariya. "To amma ka faɗa masa bana son wannan k'ananun kaya da yake sanyawa ya ci zanzaro ala dole shi bai tsufa ba. Ka fada masa ya saka native wears gaskiya." Ta faɗa tana tura baki kamar yana ganin ta. Dariya mai k'arfi ta k'wace masa sosoa. "Abida ta koya miki iya shege gaskiya" Ya fad'a cikin dariya sosai. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "E mana da girmansa amma sai ya wani tsuke sannan ga naci kamar me haba!. Ya Faruku yana dariya yana sauraranta. "Bilki bar cika baki kada wani lokaci na ga kina bare bare a kansa fa". Ta ce "idan zan yi din saboda kai ne amma ba wai don ina sonsa ba. Shi dai ya yi mata godiya sosai da ta yarda ya isa da ita. Ya ce "zai zo in sha Allahu" Da haka suka yi sallama. Tun yana hanya ya k'ira shi. Daidai lokacin yana office d'insa shi kad'ai ya kishingida akan kujera sai tunanin me zai biyo baya idan har Faruk bai iya shawo masa kanta ba. Kwatsam k'iran Faruk din ya fado cikin wayarsa. Ya dauka da zumudi sosai. "To Magana ta zaunu sai ka shirya ka je ku tattauna sosai "Da gaske mun yi magana kuma ta amince." Asad ya fara murna yana ta godiya. "Me kake son na yi maka a matsayin godiya Faruku? "Ba sai ka yi mini komai ba. Ni ai ba abin da ba ka yi mini ba. Amma ta ce na fad'a maka ka daina yin wannan zanzaron idan zaku hadu, domin ba zai boye tsufanka a idanuwanta ba". Ya kammala fad'a masa cikin matsananciyar dariya. Shi kansa Mai girma kwamishinan y'an sanda dariyar ce ta k'wace masa tare da tunanin wato ga ni take yi ya tsufa? Ya jijjiga kai tare da alwashin da kanta zata yi alkalancin ya tsufa ko akasin hakan. Ya matse ya ce "Wato na fara gasgata Abida da take yawan fad'in "Tsiyatakun Bilki sun fi nata tsanananta, kawai ita a nutse take yine sabanin Abida yar hayagaga." Faruku dai dariya yake yi kawai don sosai batun ya sanya shi darawa. Daga nan suka yi sallama. Haka ta koma gida sukuku kamar ba ita ce ta fita da farinciki ba yanzu shike nan Yaya Asad za ta aura ko a mafarki ba ta taɓa hasashensu a matsayin miji da mata ba domin ba ta sonsa, bata son bak'in namiji amma yaya Faruku ya wuce komai a wajenta shi ya sa kawai ta amsa masa. Yanzu tana amsa wayarsa amma sau biyu. Idan ya k'ira da asuba zata dauka sai kuma da daddare. Amma da rana ko da yamma har ya yi ya gama bata dauka bare ta ji me zai ce. Duk dare sai ya tambaye ta yaushe zai zo su tattauna? Ta ba shi lokaci. Kullum fada masa take zata duba ta ga ni. Ya gaji da yawon da take yi masa da hankali. Hankalinsa a tashe ya k'ira Farouku. "Farouk anya Maigado kuwa ta amince da gaske? Har yanzu fa ban ga wani sauyi da zai tabbatar mini ta amince ba. Ta bari mu had'u ma yarinyar nan ta k'i fir ". Da mamaki Farouk ya ce "Ban jin Bilki zata yi magana biyu amma zan tuntube ta." Ya katse wayar ya k'irata. "Yanzu Bilkisu dama dad'in baki kika yi mini? Sai wahalar mini da dan'uwa kike yi, kuma ke kika ce na turo shi fa. Ban san ki da magana biyu ba sarauniyar shaiba. Dan Allah yau zai zo, ko gobe?" "To ya zo gobe da yammaci ". Ta ba shi amsa murya ba amo bai damu ba ya hau yi mata addu'ar fatan alheri. Tunda ta bawa Yaya Asad damar zuwa take cikin damuwa amma ranar da zai zo bai hana ta yin kwalliya ba. Abida na ganin komai amma ba ta yi magana ba, tana ganin Bilki ta sha kwalliya a ranta tace munafuka ta ce bata so kuma tana kwalliya, domin duk halin da ake ciki yaya Asad ya k'irata ya fada mata har zuwansa na yau da zai yi. Shi yasa da zata fi kai Momi asibiti ta tafi da yaran don kuwa Farha ba yadda zata yi ta zauna a d'aki ba sai ta ce sai ta bita. Amal da Noor kuma idan sun ga babansu suma ba zasu bar shi ba. Karfe huɗu da rabi ya iso gidan ya ci gayu ya sha babban riga kamar yau ne ranar auren. Da farko bai shigo ba a haraba ya tsaya ya kirata wai yana waje ita kuma ta ce ba za ta fita ba ya shigo falo. Ya sassauta ya ce "Su Baba na ciki fa! A gajarce ta ce"Bamu da gaskiya ne? Sannan Baba na ciki Momi kuwa ba fitowa zata yi ba". Ganin ta dage tana jero masa hujjoji ya fahimci ba zata fito su zauna a harabar gidan ba. Dan haka ya shiga falon da shine farko a gidan. Kunyar Baba da Momi yake ji amma tunda haka Maigado take so, dole ya bi ra'ayinta tunda shawo hankalinta yake yi. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:43] Ya jima yana zaune, yana yi yana duba tsadadden agogon da yake daure a hannunsa ƙirar Rolex. Yana tunanin yadda mata suke son shanya masoyansu da sunan jan aji. Mintina kusan talatin yana zaune shi kad'ai yana dakonta. Ban da rashin mutuncin soyayya ya za'a yi yarinya kamar Bilki ta dinga yi masa haka. Shi da idan yana cikin kakinsa dubban zarataan maza suke kame masa tare da sara masa. Amma ita ganinsa take yi tamkar takalmin sawarta. Ya numfasa a fili ya ce "Mata ne jarabawar mazaje a duniya". A hankali ya dinga jiyo k'amshinta na turaren oils na mkbees perfumery da baya jinsa a ko ina sai wajenta na iso shi kafin ya jiyo sautin takunta cikin nutsuwa. K'amshin ya yi matuk'ar saukar masa da kasala da bege. A ransa yake fad'in Ko ina take samo wadannan turarukan? K'amshinta na sake mayar da ita yar gayu ta sosai. Mkbees perfumery na kawo muku oils perfumes masu matuƙar dad'i da Zama a jiki. Mkbees sun yi fice wajen sanin sirrin gayu don kuwa kamshine Kan gaba wajen mayar da mace mai aji. Mkbees Perfumery .Kano 07032456061 A hankali ta iso ta zauna bayan ta yi masa sallama a hankali. Ba ta yi masa magana ba sannan ba ta kalle shi ba ta juyaar da fuska tana tura baki. Shi kuma ya shagala da kallon ta domin ta yi kyau sosai sai tashin kamshi take yi. Material din Malaysianfabrics da take gown da su suna matuk'ar yi mata kyau. Bai san ya shagala da kallonta ba sai da ta ɗan kalle shi kafin ta ce" Ni don Allah ka daina yi mini wannan kallon bana so." Ta faɗa cikin yar shagwaɓa kamar wata yarinya. Gabad'aya duk ta sukurkuta shi, ya neman rasa yar natsuwan shi. "Mai gado kin yi kyau ne. Kamar na sace ki zuwa gidana." Harararsa ta yi ta gefen ido, tare da juyar da manya idanuwanta . Hakan ya kara masa nishaɗi. Ya yi dariya ya ce "Ko yau Baba ya ɗaura mana aure kawai Maigado? Ta kalle shi da mamaki amma bata ce komai ba . "Allah Maigado ina cikin tsananin buk'atar na yi aure. Kin san ni ba yaro ba ne, na dad'e ba na tare da mace, ke ma kuma a irin takalmina kike ko?" Ya faɗa har yana rage murya. Kunya ya kamata ta yi maza ta yi k'asa da kanta kafin a hankali ta ce " Ni ba ruwana" Dariya ya sake yi kafin ya ce" Da ruwan ki kuwa Maigado". Shiru ta yi masa yana ta sakin layi, wanda mamaki yake ba ta, ko kunya ba ya ji daman haka yake? Yaya Asad ne a gabanta yana kunyata ta amma shi ko a jikinsa, kai maza da abin kunya suke. Kan dole take zaune yana ta kunyatata. Ita ke jin kunya amma shi ko a jikin shi. Suna cikin haka Baba ya fito zai fita tattakin da yake cikin unguwar da yammaci, ya gansu a falo, ya kalle su ya yi dariyarsu ta manya kafin ya ce" A a garin yaya haka Asad ka zo zance gidana amma ba ka nemi izinina ba?" Ya fada yana mai bayyana murnar ganinsu har a saman fuskarsu. "Baba Faruku ne ya ba ni izinin zuwa, har aurenma ya ce ya ba ni." Baba Babba ya yi dariya kafin ya ce" To to haka aka yi? Lallai kuwa tunda Faruku ne ya baka to Bilkisu ta badu babu tantama. Dole kuwa ka ce masa Baba ". Shi da Yaya Asad suna ta dariya Bilki ta yi gum fuskarta a k'asa nan Baba ya fita haraban gidan ya bar su. Ya Asad na cigaba da zolayarta idan ta turo baki sai ya ji ya fara mazari kamar ya kamata ya matse ya tsotsi bakinta amma ba hali sai dai yana fatan lokaci kaɗan ne zai yi hakan ta halastaciyar turba. Haka dai aka gama zancen tana ɓata fuska da zai tafi ya ce su je mota ya bata sako, dole ta bi shi ya bata leda cike da kayan kwalliya da dogayen riguna, ta karba tana godiya ya shiga mota yana fadin" Maigado ki bar tura baki kwana nawa ne? Ni fa ko yau aka daura na shirya " Nan ta bar shi yana ta kiran sunanta ta yi bakam ta wuce cikin gidan, don tasan yana yanko mata zancen da sake kunyata ainun. Da daddare tana kwance Farha na gefenta tana barci. Ya k'irata ta saka hannu ta dauka tare da sallama. A hankali ta ce "Ka je gida lafiya?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:53] A sanyaye ta ce"Hakane Baba amma dai ka sanar masa din zan fi samun nutsuwar zuciya." "To Zan fad'a masa a yau din nan Maigado ". Ta Numfasa ta sake ce wa "Sannan dan Allah Baba zan je Katsina na bar kayayyakina masu muhimmanci a can, ina son na je na harhadasu tunda muka taho gidan a rufe yake". "To shike nan zan yi magana da Faruku sai ya kai ku tare da Alti ku yi kwanaki biyu ko uku". Daga haka sallame ta yana cigaba da yi mata addu'o'i masu dadi da sanya farinciki. Kwance yake kan tafkeken gadonsa yana waya da babbar diyarsa Aysha da take shirin kammala Bar school ta Enugu. Cikin nutsuwa ya sanar mata upper week zai tafi America daga can zai biya London ya ga Khadija. Juma'a mai zuwa kuma zai daura aure. Zuciyarta ta harba da tsananin gaske. "Aure Daddy! Da wa kuma?" Ta tambaye shi a rude don har cikin zuciyarta ta ji wani irin kishi mai tsananin gaske ya shak'e ta gabad'aya. A hankali ya ce mata da "Anti Maigado ". Ta yi shiru tabbas watanni biyu da suka shud'e ta tarar da ita a gidan Momi. Ashe aurenta ne ya mutu ba wai jinya kawia take yi kamar yadda Anti Abida ta fad'a mata ba? A sanyaye ta ce "Amma Dady su Mama ba sun ce sun baka Anti Laura ba?" Da sauri ya ce "Ai na fad'a musu ba zan iya aurenta ba domin kallonta nake yi tamkar yarinyar da na haifa. So ba zan iya aurenta ba". Ta kasa magana amma tabbas ba ta ji dad'in hakan ba. To Akan me ma zai sake aure yanzu shekara d'aya kacal da mutuwar mominsu! Kan dole ta ce "Allah ya sanya alheri. " Ya amsa da "Ameen" Ya numfasa ya ce "Ina fatan babu matsala ko damuwa?" A hankali ta ce "Babu komai Dady". "Stay blessed sai mun sake magana". Da ga haka ya katse wayar. Jikin Aysha ya yi mugun sanyi bata san dalilin da ya sanya ta ji wani abu ya soke ta da ya ce 'Anti Maigado zai aura ba'. Kamar yadda Baba ya fad'a yaya Farouk ya kaisu Katsina. Farha tana ta murnar zata ga su yaya Farouk. Kaitsaye gidanta suka yada zango. Komai tsab sai dai gidan ya yi kura. Cikin gaggawa Alti ta hau gyaran gidan tamkar ba gajiyar tafiya a tare da ita. Sai da komai ya yi daidai sannan ta D'ora girkin abin da zasu ci. Nan da nan gidan ya kaure da k'amshi. Daidai lokacin Yaya Farouku ya dawo daga masallaci. Ya zauna a falon ya bude murya ya ce "Alti saboda Allah da wanne irin abu kike girki ne? Gabadaya layin ya cika da k'amshin girkin dan Allah fad'a mini abin da kike zubawa Idan kina girki dan na siyawa Jamila, don k'amshi da nake ji a gidana idan ana yin girki bai haka dad'i da k'arfi ba, tunda na doso kusa da gidan fa hancina yake shakar k'amshin dad'i ". Ta fito da robar curry da spice's din Amreesh spice's Kano ta ce "Ga wasu da Ga cikinsu tafi da su a fara yi maka don nasan Mahma zata siya amarya package". ....... Ya kwashe da dariya yana fad'in "Ashe haka Alti ta iya turanci ban sani ba?" Ta koma kicin ta kawo musu abinci falo sannan ta shige d'akinta don ta yi wanka da sallah. Cikin nutsuwa Bilki ta zuba masa ta saka cokali ta ba shi sannan ta zubawa kanta. Farha tuni ta yi barci don Indomi aka fara dafa mata tana ci kuwa bata jima ba ta yi barci. Ya kammala cin abincin da ya yi masa kyau a ido, ya cika hancinsa da k'amshi, ya yi masa dad'i a baki. Ya nisa ya ce zan saka kudin spice's din nan a asusunki sai ki yi muku order tare da Jamila." A nutse ta ce "To". Ko godiya ta kasa yi masa don haka siddan ta ji wani irin abu ya turnike ta mussaman da yake ta ambaton sunan matarsa da son sai dandanon girkinta ya yi irin nata. Daga haka ya mike ya yi mata sallama zai tafi masaukinsa ya huta shima. "Idan Alti ta fito ki ce mata na tafi sai gobe zan zo da rana dan haka kada ta yi abin karyawa da ni". "Allah ya kaimu ka huta gajiya". Bilki ta fad'a a takaice tana jin haushin Jamila da na Yaya Asad na kutsowa tunda ga k'asan zuciyarta. Don tabbas sune mutane biyu da suka yi mata shamaki da samunsa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:55] Ya fita bai sake ce wa komai ba don ya lura so take ta hargitse tunda suka iso komai yake neman k'wace mata. Tana jin sautin takunsa a kafar bene ta ja dogon tsaki tare da fad'in "Yan ta'adda kawai masu son kansu" Daidai lokacin k'iran gogan nata ya faɗo wayarta. Tana kallo har ta katse bata d'aga ba don sosai ta ji haushinsa ya dirar mata. Sai dai cigaba da kiran ya yi, akan dole ta dauka ta yi sallama murya a mak'oshinta. Yayin da hakan ya jefa Asad cikin wani irin yanayi. Ya yi k'asa da muryarsa ya ce"Ba ki da lafiya ne?" ke nan?". "Lafiyata k'alau". Ya nisa ya ce Saboda Allah Maigado za ki yi tafiya sai dai na ji a bakin Farouku. Da safe ma mun yi waya na ji alamun a mota kike, na tambaye ki, inda za ki je kika ce wajen aiki, ashe Katsina za ki tafi shine ban isa ki fad'a min ba ko? Amma ni da zan taho Lago din nan sai da na fad'a miki tun ana gobe zan tafi, ina cikin jirgi kafin na tashi ma sai da na sanar da ke ". Haka kawai ya fad'a ta ji ta harzuk'a tunda dama haushinsa da na Jamila ke ciciiyarta a daidai lokacin. Dan haka ba tare da ta tauna kalamanta ba ta ce "Amma ai ban rok'e ka, ka fad'a mini ba, sannan akan me duk abin da zan yi sai na fad'a maka?". Jikinsa ya yi sanyi k'alau tare da tunanin ko ya yi mata wani abu ne? A sanyaye ya ce "Me yake faruwa ne Maigado?". "Kamar na me fa?" A hankali ya ce "Sai da safe". Ba tare da ta amsa ba ta yi maza ta riga shi katse wayar. Yana kwance shi kad'ai kan makeken gado na alfarma cikin tsadadden hotel a birinin na Ikko. Ya yi sororo da waya a hannunsa a fili ya ce "Tooh! Zuciyarsa na bugawa tare da kitsa masa ta je Katsina ta ga mijinta da ya'yanta shine zata birkice ta nemi juyawa maganarsu baya? Ban da haka bai ga dalilin fishi da fisgar da ya ji a tare da ita ba. A fili ya ce "Allah ka k'addara mini auren yarinyar nan, Allah ka sa rabona ce". Don gabadaya hankalinsa ya yi mugun tashi. Tunda yasan ba sonsa take yi ba komai na iya faruwa. Tun Daren suka yi waya da su Amrah ta fad'a musu ta zo garin. Sassafe Babansu ya dawo daga masallaci Amrah ta tsaya a falo. Ta gaishe ta ce "Dady dan Allah anjima ka kaimu wajen Mahma ta zo kuma ta ce ba zata dade ba, zata juya". Daidai lokacin Faruk ya shigo falon. Da sakakkiyar fuska ya ce "To ku shirya tunda hutu kuke yi anjima zan kai ku ranr da zata tafi sai ku dawo". Dad'i ya kamasu suke ce "Mun gode". Ya haye sama don yanzu kan dole idan ya dawo masallaci yake hawa saman tunda Hawwah ta kafe kwana Kawai zata yi a k'asa amma ba zata yarda ta dinga biyo shi da abinci ko wani abu daban k'asa ba tunda bata d'aki a gun. Dan haka ya amince dan ra'ayinta tunda ya kafe k'asa na y'ayansa ne ba mai takurasu kuma ba zasu dinga kwana su kad'ai ba. Dan haka itama ya lallaba yake bin ta saman da zarar ya dawo daga masallaci da asuba don su samu daidaita a tsakaninsu. K'arfe takwas sun gama shirya ko barcin safe basu koma ba. Gabaɗayansu zumundin ganin uwarsu ya dabaibaye zuciyarsu. Farouk ya kalli Amrah ya ce ",Yaya ai dai bana yi miki rashin kunya ko?" Dariya kad'an Amrah ta yi ta ce "Yaushe rabon da ka ce mini Yaya Farouk?" Ya yi dariya kad'an ya ce ",Saura ki je Ki faɗawa uwata zancen da zai dame ta". Amrah ta kalle shi ta ce "Me zan fad'a kuwa da zai dame ta ?" Ya make kafada tare da fad'in "Idan kika ce bana magana da anty ta yi mini fad'a Allah muka dawo ke ma daina kula ki zan yi". Ta jijjiga kai tare da fad'in"Tun yanzu daina kula ni kawai". Ya yi dariya ya ce "Don dai bana son ki yi kuka ne". Itama dole ta dara don ya bata dariya sosai. Ta shiga dakinta ta fito da yar jaka Karama mai kyau d'auke da kayanta set biyu ta ce "Za ka dauko kayan naaka na saka maka ko kuwa?" Ya make kafaɗarsa ya ce "Ki je d'akin nawa ki dauko mini idan ba haka ba, da iya na jikina zan je sai na ga wa za'a yiwa fad'a a tsakaninmu." Ta kalle shi ta ce "Allah ya shirya ka Farouk ". Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:58] Sannan ta wuce zuwa d'akin nasa don idan bata d'auko masa ba haka zai tafi, kuma ita Mahma zata yiwa fadan ba ita ce babba ba. Yayin da shi kuma yake tsaye rungume da hannuwansa yana yiwa kansa waka wai shi Yayan Mamah mai kafaciti dole a bi shi". Amrah ta fito ta ce"Ka daina cika bakin dole na bika. Kawai tausayinka nake ji". Ya k'yalkyale da dariya yana ce wa "Yayan Mamah ba abin tausayi ba ne Haj Amrah". Dolenta ta k'yale shi don masu gidan ma hakuri suke yi da shi, don su ba ya kula su, tsakaninsa da su gaisuwar safe, sai ko idan zai faɗawa Babansu zai sayi abun makaranta. Amrah dai yake mu'amala da ita kawai. Basu da wata babbar matsala a gida don su kad'ai suke rayuwa a wajensu, da daddare kuma iyayen su sauko su kwana. Sun sake samun saukin matsala ne da mijin Alawiyya ya dawo da ita cikin Katsina. PAGE 13 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Kuma basu da nisa da unguwarsu. Dan haka duk sati suke zuwa gidanta Su yini, mamarsu ta turo musu ita da Amrah su yi samosa da springrols da numa meatpie sai Su tafi da shi su saka a fridge. Duk sadda suke so sai su soya abinsu. Sosai Alawiyya take kulawa da su dan har gidan take zuwa jifa jifa tana yiwa wajensu kyakkwan gyara. Dan haka basu wani tagayyara da yawa ba, mussaman da Hawwah ta kasa samun tasirin da zata dakile hankalin ubansu a kansu. Tun Bilki bata dad'e da barin gidan ba ta fara cin karo da matsaloli da ashe zaman Bilkin a gidan ne ya hana ta lura da su. Lafiya take zaune da mijinta amma kuma babu wannan rawar jiki da tarairayar da ya dinga yi mata a watannin farkon na zamansu. A da kafin ta bukaci wani abu sai dai ta ga ya kawo, yanzu kuwa sai ta yi ta fad'a kafin ya samu sukunin siyowa. Sannan su yaya Turai sun koma suna jan kunnen mijinta akan lallai ya saka ido akan ya'yansa kada ya bari su yi kukan rashin wani abu tunda uwarsu da take nan ba abin da bata yi dan ta rufa masa asiri ba. Tuni sun fahimci Bilki ce ta sanya gidan Sahal ya zama gidan masu wadata ta yadda zaka ci abinci laifayye ka k'oshi. Amma tunda ta bar gidan ba dama ka je a baka abinci sai dai ruwan pure water. Idan kuwa yini zaka yi to abincine dai ga shi nan amma ba wani sha'awar da zai baka. Sun sa ni kuma iya k'arfinsa ke nan tunda Hawwah bata da shi dole iya yadda ya bata haka zata yi. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛:. Haba ba sai sai kuma suka koma suna son ya'yan Bilki ba. Hawwa kullum cikin kuka take tunda yanzu ita aka saka a gaba ana fadin itace farar k'afa ba Bilki ba. Sannan iyashegen da Faruku ya tisa ta a gaba da shi cikin lumana kad'ai na matuƙar damunta. Tsiyataku iriiri yake yi sannan ba dama ya ga Amrah ta hau samanta zai k'ira ta ya dinga yi mata sababin ta tafi neman suna ta bar shi, shi kad'ai. Ba yadda ta iya da shi tunda ubansa ma rarrashinsa yake yi da son ganin dariyarsa. Da kanta ta fahimci babu riba ko kad'an idan har kishiya ta tafi ta bar maka ya'yanta gara ku zauna kowa ta rik'e ya'yan har Allah yasa su girma. Yanzu ba abin da take so irin ace Bilki ta dawo d'akinta ko dan mijinta ya samu nutsuwa sannan ta tabbatar idan tana nan wulakancin Faruk ba zai yi tasiri ba. Sannan hankalin Sahal ba zai zama kacokan akan su Amrha ba. Yana son d'iyarta tabbas tunda ba abin da ba ya yi mata amma sai take ganin ba kamar manyan ba. Idan zata kwnaa tana Kiran Faruku ba zai amsa ba, ko da kuwa ta bar samanta ta sauko. Idan da safe ya gaishe ta bata amsa ba, Babansa ya yi fadan yaro yana girmamata tana yada girman. Idan ta ce ai baya mata magana sannan ko mai zata ce masa ba zai nuna ya ji ba bare ya tanka. Ya kuwa ce mata ai yaro ne, sannan tunda yana gaishe ta ai ya kyauta kada ta sake ta biye masa watarana ba zai yi ba, bata ga Amrah ma hak'uri take yi da halinsa ba. Bak'inciki kan bak'in amma ba yadda ta iya haka take hakuri tare da amannar yaran sune jarabawar gidan aurenta. Da zai kaisu ya yi kwalliya irin wadda Hawwah ta dade bata ga ya yi irinta ba. Ta kasa hak'uri ta ce "To ko dai kome zaku yi ne Baban Amra?". Ya yi murmushi ya ce "Idan zaman bai k'are ba sai a yi". Duk da zuciyarta ta buga amma da murnarta ta ce "Allah ya nufa gara ta dawo d'akinta ko Faruk ya janye kiyayyar da ya d'ora mini haka siddan." Bai ce komai ba. Don kuwa ya riga yasan Bilki ta yi masa nisa har sai idan aure ta yi ta fito. Da kansa kuwa ya tabbatar matuk'ar ta had'u da namijin da zai biyar da ita ta samu gamsuwa ba zata yi marmarin sake zama da shi ba. Ya dauki d'auki d'iyarta data ke zaune akan gado ya daga sama tana yi masa dariya sannan ya ajiye ta ya ce "Zan tafi daga can Zan wuce d'aurin aure kinsan yau asabar su kuma zan barsu a can sai ta tafi zasu dawo". A sanyaye ta ce "A dawo lafiya". Ta fito ya same su a falon sun Tisa jakar kayansu a gaba. Suna ganinsa suka mike. Ya ce ",Oya ku je ku yiwa Antinku sallama". Ba musu suka hau k'afar benen yayin da shi kuma ya dauki jakar kayan ya fita zuwa wajen motarsa. Amrah ce kawia ta hau ta yi sallamar. Amma Faruk nokewa ya yi daga k'afar benen. Suka sauko a tare Amrah na yi masa fadan ya dinga jin maganar Dady Menene dan ya yi sallama? Uffan bai ce mata ba. Ya shiga gaban mota Amrah ta shiga baya. Har k'ofar gidan ya kaisu sannan ya ce su ce yana gaishe ta, haka nan su gaida Alti da Farha. Ya ja motarsa ya tafi yana jin wani irin nauyi da nadama suna sake mamayarsa tabbas har ya mutu ba zai daina jin ciwon asarar da ya tafka ba. Da gudu Faruk ya hau saman yayin da Amrah ta hau a hankali tana rike da jakar kayansu. Alti ya tarar a kicin dan haka ya shiga ya rungume ta yana fad'in "Altina! Itama ta rungume yaron tana jin dad'in yanayin da ta ganshi tabbacin basa cikin takura. Daga haka ya sake ta da hanzari ya doshi d'akin da zai ga Mahma. A bakin gado ya tarar da ita tana gyarawa Farha zaman hularta. Ai tana ganinsa ta ruga suka rungume juna. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:02] Sakwanni goma suna haka kafin ya sake ta yana fad'in "Farha ya Abuja?" Ta ce "Lafiya lau ina Yaya?" Daidai lokacin Amrah ta shigo d'auke da jakar kayansu. Itama ta rungume ta. Yayin da suka zauna gefen uwarsu suka sanya ta a tsakiya. A nutse Amrha ta gaishe ta shi kuwa Faruk jingina ya yi a jikinta. Bilki ta yi matuk'ar sanya jarumta ta karbi gaisuwarsu da sakakkiyar fuska. Amma k'asan zuciyarta tausayinsu fal yake yagalgala ta. Da sanyin murya Amrha ta ce "Dady na gaishe ki, ke ma Farha ya ce yana gaishe ki ". Farha da take zaune kusa da Faruku tana tambayarsa k'awayenta na makaranta. Bilki ta ce "Ina amsawa ina kanwarku? Ya ma sunanta?" Faruku ya yi fit ya ce"Lubaba". Bilki ta ce "Sunan Hajiyar ne haka gatsal a bakinka?". Amrah ta ce"Yana ji fa ina ce mata Ifrah amma dan iskanci indai ya ganta a hannuna ko wajen Dady sai ya wani ce mata Lubaba kullum ya fad'a haka sai Dady ya ce masa baka jin nauyin baro mini Faruk? Amma ba ya dainawa. Gaskiya Mamah ki yiwa yayanki fad'a baya jin magana kullum da abin da zai yi na rashin ji". Bilki ta rungume shi sosai ta ce "Yayana da dai nasan ba ka neman fitina amma me yasa yanzu ka canja?" Ya yi murmushi ya ce "Ba na neman fitina har yanzu amma bana son a takura ni ne, Yaya Amrah da Dady sai su dinga takura ni sai na shiga hanyar matar gidan ni kuwa ba zan shiga ba, ta yi harkarta na yi tawa". Amrah ta ce "To me yasa kake mini sababi idan na je sama ko Idan na dauko Ifrah?" Ya galla mata harara ya ce "Tunda Mamah bata tare da mu dole ki dinga kula da ni sosai. Akan me za ki tafi ki bar ni? Ki dinga neman shisshigi ai dama zan fad'awa mama ba ki rik'e amanata da kyau ba". Dariya ta subucewa Bilki don ta lura da gaske yake maganarsa ba wai wasa ba. Sosai suka hi hirarsu cikin nutsuwa duk da yawan hirar k'orafi Faruk yake ta gabatarwa akan Amrah tana takura shi wanda duk na shagwaba da iyashege ne kawai don uwar tasu da kanta ta gane Amrah ce take hakuri da shi tare da lallaba shi. Da azahar ta yi Alawiyya ta iso. Gidan ya sake kaurewa da murna suna tuna rayuwar da suka shafe tsawon lokaci tare tamkar ba za'a rabu ba, yanzu kuwa had'uwa gabad'aya irin haka zai dinga yi musu wahalar gaske. Wannan kad'ai ya isa a gane ba abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah. Da taimakon Bilki da Amrah Alti da Alawiyya suka shirya dukkan kayan da Bilki ta ke so wajen d'aya . Duk abin da su Amrah suke so ku suke da bukartarsa ta bar musu. Babban gadonta Amrah ta ce ta bar mata tunda yanzu itace a d'akinta Kuma Dakin babbane gadonta da wadirof sun yi kankanta da yawa. Faruk ya yi tsalle ya ce ",Ba za'a bata ba, na d'akin baki ya ishe ta tunda suma set ne." Ta harare shi ta ce "Kai ka d'auki na d'akin bak'in tunda nasan ce wa zaka yi kai ta baka." Ya girgiza kai ya ce "A a ni nawa sun ishe ni. Alawiyya zata barwa ita kuma ta siyar da nata ta fara business da kudin, ba ki ga yadda take yi mana kirki ba har yanzu? Duk sati sai mun je gidanta mun yi abin da muke so, haka nan ita take zuwa ta yiwa wajenmu general sanitation duk karshen wata. Har firizar can ma ita za'a bawa ". Amra ta yi maza ta ce "Hakane a bata to". Bilki ta yi shiru tana nazarin hukuncin da Faruk ya yanke kaitsaye ba tare da neman shawara ba. Amma ta sani gaskiya ya fad'a. A ranta ta ji yafi dacewa da ya amsa sunan Sulaiman don kuwa halayyarsa rabi irin tasa ce. Dan haka duk ta barwa Alawiyya kayanta har kujerun falon, yayin da Alawiyya ta dinga kuka tana hodiya tare da mamakin yadda ta mallaki kayan alfarma tashi guda. Tuni kuma ta amince zata siyar da nata kayan wasu kuma ta aikawa kanwar Babanta da ta rik'e ta tunda marainiyace ita. Alti ta dinga taya ta godiya a wajen Bilki. Da yamma Basma ta je mata suka yi hira ta yi murnar ganin Bilki ta samu nutsuwa zuciya sannan ta ji dad'in auren da zata yi. Ta jaddada mata zata kula da su Amrah iyakacin iyawarta. Itama Bilki ta bata warmers sabbbi sannan ta ce ta duba duk abin take so na amfani ta dauka. Gaf da magariba ta yi sallama suka ta tafi. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:11] Sai dare mijin Alawiyya ya zo daukarta a mashin d'insa wanda dan kasuwane yana siyar da kayan vegies da yake sarowa daga Raudatul Jannah foods Jos.. A zuwan da Alawiyya take yi siyo kayan snacks da na amafanin gida suka hadu. Har saman ya hawo ya gaisa da Mahmah tunda dama a gidan ya san Alawiyya sai da suka amince da junansu sannan Bilkin ta tura shi K'afur garinsu Alawiyya ya gana da wakilanta. Ya dinga yin godiya alherin da aka yi musu tunda Alawiyya waya ta yi masa ta fad'a masa kyautar bajinta da aka yi mata duk kuwa da kayan d'akinta na yanzu Bilkin ce ta yi mata su sabbi Sai dai ai Basu kama k'afar wanda aka bata ba yanzu. Kafin ta tafi Bilki ta ja ta d'aki ta fad'a mata zata yi aure a cikin sati mai kamawa ta taya ta da addu'a. Farinciki har cikin ran Alawiyya don kuwa bata yiwa uwardakinta sha'awar yin kome. Ta dinga yi mata addu'o'i masu sanyaya zuciyata tare da sake yi mata alkawarin matuk'ar tana cikin garin Katsina to Faruk da Amrah suna da Yaya tamkar uwarsu d'aya ubansu daya zata kula da su irin yadda ta kula da ita. Hankalin Bilki ya sake nutsuwa don kuwa ta gasgata Alawiyya. Ga su Faruk sun sake bada shaidar ba abin da bata yi musu. Suka yi sallama suka rabu cikin sanyin jiki da fatan alheri. *Na ce kina yiwa masu aikinki adalci da sassauci kuwa?* *Ba ki san ta yadda zasu taimake ki a gaba ba. Kowanne dan adam akwai ranarsa, da ace Bilki bata yi mata adalci ba, da bata kular mata da yaranta a lokacin da babu idonta a kusa ba*. Sai da daddare bayan sun kammala cin abincin dare tuni kuma Farha ta yi barci. Ita da Alti suka faɗawa yaran batun auren da zata yi. Dukkansu yaran jikinsu ya mutu ba karsashi suka ce "Allah ya sanya alheri". Amma k'asan zuciyarsu sun ji wani iri shike nan ta bar gidansu da dadynsu for ever? Murya ba amo Amrah ta ce "Mahmah waye shi sannan a ina za ki zauna?" Ba walwala ta ce "Uncle Asad ne sannan a Abuja zan zauna". Amrah ta yi shiru ta rasa me take ji a ranta. Amma dai zuciyarta sai ayyana mata take yi mai kudine fiye da dadynsu amma kuwa Babansu ya fi kyau yafi kirki tunda shi ba ya dariya. Kafin ta ce wani abu Faruk ya ce "Mahmah uncle police wai?" Kai kawia ta daga masa tabbacin eh. Ya rik'o hannunta ya ce "Amma takwarana ya fi shi kirki da kyau Mahmah". Murya ba amo ta ce "Ba kyau na duba ba, sannan haka k'addara ta zaba mini kawai ku dinga yi mini addu'a". A sanyaye suka ce to don hatta Faruk da yake ganin gara ta tafi inda ba zata dinga kuka ba, batun auren nata ya yi awon gaba da kuzarinsa. Wato kishi bala'i ne, ba ga yara ba, ba ga manya ba.😄Ba ga mazan ba, bare kuma mata masu duniya. Allah kasa mu wanye lafiya. Washegari suka bar Katsina wanda su Bilkine suka kai yaran gidan Alawiyya akan da yamma su wuce gidansu tunda da sassafe suka tafi a dalilin zasu tsaya a Kano wajen Yaya Hamida. Suna nisa da Katsina kewar ya'yanta na sake kama ta. Akan dole ta yi hak'uri mussaman da yara basu tayar da hankalinsu sosia ba, amma dukkansu sun yi kuka. Haka Farha har suka kusa isa Kano kuka take yi akan a barta a wajensu ba zata koma Abuja ba. Sai da barci ya sure ta sannan ta yi shiru. Taran safiya a gidan Yaya Hamida ta yi musu, suka karya sannan suka shiga daki Bilki ta sanar mata batun aurenta da Yaya Asad. Take Hamida ta fara kuka tana fad'in tabbas na huce dan ke na ji wa'azi akan illar gaba mussaman ace jini guda ke yin ta. Amma ki sa ni sai da kwakkwarn dalili za ki ga k'afata a gidanki. Me za ki yi da wannan mugun marar mutunci dattijo da shi zai dage sai ya aure ki. Allah ne ya rufa miki asiri bai lalata ki tun kina yarinya ba, masu kakin nan fa kad'an ne na kirki amma wominzers ne na k'arshe. Ai ni tunda bai zo ta'aziyar uwarmu ba, sannan ya daurewa yar iskar Abidan nan gindi akan Yaya Sulaiman Wallahil Azim ba ni ba shi. Dan haka soyayyar da zan nunawa ya'yanki sai na nunawa su Amrah da Farha amma nasa kam kadaran kadaran hakan ma saboda ta jikinki suka fito." Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:13] Sai dare mijin Alawiyya ya zo daukarta a mashin d'insa wanda dan kasuwane yana siyar da kayan vegies da yake sarowa daga Raudatul Jannah foods Jos.. A zuwan da Alawiyya take yi siyo kayan snacks da na amafanin gida suka hadu. Har saman ya hawo ya gaisa da Mahmah tunda dama a gidan ya san Alawiyya sai da suka amince da junansu sannan Bilkin ta tura shi K'afur garinsu Alawiyya ya gana da wakilanta. Ya dinga yin godiya alherin da aka yi musu tunda Alawiyya waya ta yi masa ta fad'a masa kyautar bajinta da aka yi mata duk kuwa da kayan d'akinta na yanzu Bilkin ce ta yi mata su sabbi Sai dai ai Basu kama k'afar wanda aka bata ba yanzu. Kafin ta tafi Bilki ta ja ta d'aki ta fad'a mata zata yi aure a cikin sati mai kamawa ta taya ta da addu'a. Farinciki har cikin ran Alawiyya don kuwa bata yiwa uwardakinta sha'awar yin kome. Ta dinga yi mata addu'o'i masu sanyaya zuciyata tare da sake yi mata alkawarin matuk'ar tana cikin garin Katsina to Faruk da Amrah suna da Yaya tamkar uwarsu d'aya ubansu daya zata kula da su irin yadda ta kula da ita. Hankalin Bilki ya sake nutsuwa don kuwa ta gasgata Alawiyya. Ga su Faruk sun sake bada shaidar ba abin da bata yi musu. Suka yi sallama suka rabu cikin sanyin jiki da fatan alheri. *Na ce kina yiwa masu aikinki adalci da sassauci kuwa?* *Ba ki san ta yadda zasu taimake ki a gaba ba. Kowanne dan adam akwai ranarsa, da ace Bilki bata yi mata adalci ba, da bata kular mata da yaranta a lokacin da babu idonta a kusa ba*. Sai da daddare bayan sun kammala cin abincin dare tuni kuma Farha ta yi barci. Ita da Alti suka faɗawa yaran batun auren da zata yi. Dukkansu yaran jikinsu ya mutu ba karsashi suka ce "Allah ya sanya alheri". Amma k'asan zuciyarsu sun ji wani iri shike nan ta bar gidansu da dadynsu for ever? Murya ba amo Amrah ta ce "Mahmah waye shi sannan a ina za ki zauna?" Ba walwala ta ce "Uncle Asad ne sannan a Abuja zan zauna". Amrah ta yi shiru ta rasa me take ji a ranta. Amma dai zuciyarta sai ayyana mata take yi mai kudine fiye da dadynsu amma kuwa Babansu ya fi kyau yafi kirki tunda shi ba ya dariya. Kafin ta ce wani abu Faruk ya ce "Mahmah uncle police wai?" Kai kawia ta daga masa tabbacin eh. Ya rik'o hannunta ya ce "Amma takwarana ya fi shi kirki da kyau Mahmah". Murya ba amo ta ce "Ba kyau na duba ba, sannan haka k'addara ta zaba mini kawai ku dinga yi mini addu'a". A sanyaye suka ce to don hatta Faruk da yake ganin gara ta tafi inda ba zata dinga kuka ba, batun auren nata ya yi awon gaba da kuzarinsa. Wato kishi bala'i ne, ba ga yara ba, ba ga manya ba.😄Ba ga mazan ba, bare kuma mata masu duniya. Allah kasa mu wanye lafiya. Washegari suka bar Katsina wanda su Bilkine suka kai yaran gidan Alawiyya akan da yamma su wuce gidansu tunda da sassafe suka tafi a dalilin zasu tsaya a Kano wajen Yaya Hamida. Suna nisa da Katsina kewar ya'yanta na sake kama ta. Akan dole ta yi hak'uri mussaman da yara basu tayar da hankalinsu sosia ba, amma dukkansu sun yi kuka. Haka Farha har suka kusa isa Kano kuka take yi akan a barta a wajensu ba zata koma Abuja ba. Sai da barci ya sure ta sannan ta yi shiru. Taran safiya a gidan Yaya Hamida ta yi musu, suka karya sannan suka shiga daki Bilki ta sanar mata batun aurenta da Yaya Asad. Take Hamida ta fara kuka tana fad'in tabbas na huce dan ke na ji wa'azi akan illar gaba mussaman ace jini guda ke yin ta. Amma ki sa ni sai da kwakkwarn dalili za ki ga k'afata a gidanki. Me za ki yi da wannan mugun marar mutunci dattijo da shi zai dage sai ya aure ki. Allah ne ya rufa miki asiri bai lalata ki tun kina yarinya ba, masu kakin nan fa kad'an ne na kirki amma wominzers ne na k'arshe. Ai ni tunda bai zo ta'aziyar uwarmu ba, sannan ya daurewa yar iskar Abidan nan gindi akan Yaya Sulaiman Wallahil Azim ba ni ba shi. Dan haka soyayyar da zan nunawa ya'yanki sai na nunawa su Amrah da Farha amma nasa kam kadaran kadaran hakan ma saboda ta jikinki suka fito." Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:17] Hawaye a fuskar Bilki ta ce"Ni ma ba sonsa na ke yi ba, Yaya Faruku ne ya matsa mini amma ko Baba ma ce masa na yi bana sonsa". Yaya Hamida ta ce "Ni dai tunda kun shirya ke da su ba zan ce komai ba, amma ki sa ni Wallahi mu ba ruwanmu da su mussaman ma Asad mugun mutum mai bak'ar fuska da zuciya.". Kan dole suka goge idonsu suka yi hirar sannan aka yanka cake din d'iyar Hamida ta biyu wanda ranar take yin birthday da sai yamma za'a yanka amma Saboda ayi hotuna da su Bilki da Farha aka yanka a lokacin. Duk da Bilki harkar snacks ta k'ware Sai da ta tambayi wacce ta yi cake din tare da su samosa da springrols saboda dad'insu sannan da aka fad'a Mata Farashin sai da ta jinjina tare da karɓar lambar dan ta had'a ta da kawayenta na Kano da suke ta fad'in har yanzu basu samu wacce ta iya snacks irinta ba. PAGE 14 Sai azahar sannan suka kama hanyar Abuja bayan Yaya Faruku ya azalzale su. Shi Yaya Faruku har yanzu ba wanda yake fishi da shi tunda dama tun filazal na kowa ne. Sai dare sosai suka isa gida. Kushen Yaya Hamida akan Asad ya sake tsananta kinsa a zuciyarta sai dai ba zata iya ce wa ta fasa ba tunda ta ce ta amince, amma gabad'aya abin ya sake fita a ranta. A daren ya k'irata yafi sau biyar bata daga ba ya damu k'warai. Haka da safe. Yayin da ita kuma zuciyarta ce ke ta yi mata rawa tare da wasiwasin ta zazzage shi kawia ta yadda zai hak'ura da kansa. Amma ko kusa ba zata iya yin haka ba tunda ta samu tarbiyar girmama babba tunda ga tushe. Washegari k'arfe sha d'ayan safiya a gidan ta yi masa. Sanye yake cikin tsadadden farin yadin filtex. Ya shiga falon ciki ya gaisa da iyayensa suka dan taɓa hira akan tafiyarsa Lagos. Bai wani jima ba ya fito ya dawo falon farko ya zauna. Daidai lokacin Amal da Noor tare da Farha suka fito suka nufe shi suna yi masa oyoyo. Ya d'an biye musu ya basu alawowi da cookies kowa ledarsa daban. Noor ta ce "Dady yaushe zaka d'auke mu koma gidanmu?" Ya jata jikinsa ya ce ki k'ara hak'uri, ba na ce miki yanzu Mahmah itace mominku ba?" Ta daga kai. "Good idan muka yi tafiya muka dawo zamu zo ni da ita mu d'auke ku har da Farha mu koma gidanmu gabadaya ". Amal da tafi wayo ta ce"Shi ke nan sun zama y'an gidanmu?" Ya ce "Haka nake nufi my Amal". "To amma Dady Ammie da junior fa?". Ya ce "Su anan zasu zauna kafin dadynsa ya dawo ya dauke su suma. Murna ta kama Farha jin zasu koma tsalelen gidansu Noor ya zama nasu. Ya ce "To ku je ku shirya yanzu lesson teacher dinku zai iso. Ku faɗawa Mahma ta zo ta karbi sweet dinta tunda Ammi na hospital." Suka tafi da sauri dan faɗawa Bilki sak'onsa da kuma dauko jakunkunan karatunsu. Ya jima a zuane yana dakonta. Amma bai kosa ba mussaman da yake ta amsa waya daban daban. Can ya ji fitowar yaransu suka wuce shi suna fad'in bye dad don suna ganin kafin Su kammala ya tafi. Sun jima da fita kafin ya jiyo takunta hadi da k'amshin turarenta. Cikin nutsuwa ta zauna a kujerar da take fuskantar wacce yake zaune. Kanta na k'asa ta ce "Ina yini?" Ya amsa da fad'in lafiya but not fine! Kin rikita mini tunanina Maigado! Me na yi miki, me ya faru kika daina daukar wayata sannan komai ya zo bakinki sai ki fad'a mini kai tsaye. What's going on?" Ya tambaya a rude. Kanta na k'asa bata yi magana ba. Ya zuba mata ido ya ga gabad'aya ta yi wani iri babu kuzari a tare da ita. Ya tabbatar zuwanta Katsina na kan gaba wajen sauyawarta. Ya tausasa harshe ya ce "Maigado! Bata motsa ba bare ta amsa. Ya numfasa ya ce "Ya su Faruk junior?" Murya ba amo ta ce "Suna lafiya Alhamdulillah! Ya gyara zama ya ce "Ki ba ni lambar Babansu na roke shi ya ba ni su na sanya su makaranta a nan". Ta d'ago a hanzarce don maganar ta zo mata a bazata, har cikin zuciyarta kuma ta ji dad'in hakan. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:19] A sanyaye ta ce "Na gode sosai amma Babansu ba zai bada su ba, suna karatun ma a can". Ya dan ji dad'in ganin yadda ta dan fara warewa. Ya ce"To kuwa da zarar sun kammala sakandire dolensa ya bada su don su shiga manyan jami'o'i. Babbar ta kusa kammalawa ne?" "A a da saura yanzu ma shiga aji biyar(s.s.2)." "To ai kamar yanzu ne". Faruk so nake ya yi b'angaren likitanci. Ai yana da kokari ko?" Ta murmusa tare da fad'in "Wannan Yayan nawa ai sai a hankali ban san zuwa gaba ba. Amrah ce hazik'a irin Abida! Ya yi maza ya ce"Ma sha Allah! Da ikon Allah kuwa zata yi karatu a d'aya cikin best universities da ake ji da su a duniya". Da walwala a fuskarta ta ce"Allah ya ida nufi". Haka ya dinga yi mata hirar yaranta nan da nan ta warware suka yi hira irin wacce basu taba yi ba. Ganin ya shawo kanta ta ware ya sanya ya yi mata sallama ya tafi bai yi mata maganar soyayya ko aure ba. Sai da daddare suna waya ta ce "Baban Bilkisu ko za'a bari auren nan sai ka dawo daga tafiyar da zaka yi don gaskiya ni bana son tafiyar". Zullimi ya yiwa zuciyarsa k'awanya ya ce"Ki yi hakuri kin ji ai ba dadewa zamu yi ba." Ta yi shiru tabbacin bata yarda ba. Ya ce "za'a daura auren juma'a mai zuwa ba za'a sauya ba. Zan nemi wajen aiki su tura wani zuwa kwas din, gwara na rasa k'arin girman da na rasa ki Maigado ". Murya a mak'oshinta ta ce"Ni gaskiya ka tafi, idan ka dawo a daura. Tsakanina da Allah jibi ya yi mini kusa da yawa" Yana kwance ya zabura ya zauna a tsakiyar gadon. A kidime ya ce "Saboda me Maigado, me ya faru, me ya canja miki shawara haka? Dan Allah kada ki zama mai yin magana biyu. Allah ne shaidar yadda nake son ki nake tsananin son na aure ki, ba kya jin tausayin zamana haka Maigado? Fad'a mini me na yi miki da ya sanya kika sake shawara?" Ya yi mata tambayar cikin rarrashi da kwantar da harshe. Ya bata tausayi ainun. Amma duk da haka ta ce "Gaskiya Baban Bilkisu baka son y'anuwana duk cikinmu da ni kawai kake yin mu'amala mun sake gane hakan ne da Mami ta rasu ba ka zo mana ta'aziya ba sai ta waya, wayar ma a layin Baba ka k'ira aka hadaka da ku, idan ma baka k'asar da gaske me ya hana da ka dawo baka zo mana ba?" Sannan a matsayinka na babba baka tsawatarwa Abida ta koma d'akinta ta zuaan da mijinta lafiya tunda bai yi mata komai ba, sai ka zuba mata ido saboda kawai baka son Yaya Sulaiman ". Ya yi shiru ya kasa ce mata komai amma gabad'aya kansa ya kulle. Ya nisa ya kasa furta kalma ko guda don ya tabbatar zuwanta Kano Hamida da sauran suka soki lamarin aurensu tare da gabatar mata da hujjar da ita a da bata gano su ba. Ya yi imanin kitsa mata wadannan kalaman aka yi don da ta k'ulla ce ba zata zo masa ta'aziyar Rukayya ba, tunda kaf ya'yan Baba k'arami ita kad'ai ce ta zo masa ta'aziyar Sai Saddiqa Wanda ya tabbatar ita ta matsa mata suka taho tare, amma ko Ansari waya ya yi masa duk da shi su na d'an gaisawa jifa jifa. Murya ba amo ya ce "Wallahi Billahi Maigado bana k'asar nan mami ta rasu. Sai da aka yi watanni biyu da rasuwar kafin na dawo. Ba wai dan ina jin haushinta ko dan ina fishi da ku ba ne. Dan Allah ki yarda da ni. Batun Abida kuma kowa da nasa kason na laifi da mu, da ita, da shi Sualiman din da ya gudu. Shi ma da ace Baba k'arami na da rai bai isa ya yiwa Baba Babba fishi irin haka ba. Ni yanzu ba tone tone zamu yi ba. Don kuwa Abidan da kuke ganin mun zuba mata ido ai a cikin nadama take mai tsananin gaske. Kada mu saka matsalolin gidanmu akan lamarinmu Balkees pls. So nake al'amarinmu ya yi tasirin da zai zama tsananin sulhu da afuwa a tsakaninmu. Yanzu ba kya tunanin irin murna da farincikin da Baba Babba yake ciki a kanmu, kin ce masa kin amince sai kuma ki dawo ki ce kin fasa? Yayanki Faruku yana ta rawar jiki da farincikin kin yarda ya isa da ke, sai kuma ki watsa masa k'asa a ido ki kunyata shi? Ki yi hakuri, in sha Allah sai na zame miki alheri, sai gidanmu ya dawo tamkar yadda muka taso muka ga iyayenmu sun kafa Shi, hakan kuma ba zai yiwu ba sai kin ba ni hadin kai, kin yi hak'uri kin jure duk wata gutsuri tsoma. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:22] Sannan duk inda Sualiman yake da ikon Allah zai dawo cikinmu ya rayu da mu, zan yi kokarina ya dawo gida, don kuwa tabbas ban ji a jikina ya rasu ba." Jikinta ya yi sanyi ainun. Ta rasa yadda zata yi a kan dole ta ce "To". Ya dinga yi mata godiya har ta ji wani iri. Don sai ya bata tausayi yadda ya kwantar mata da kai tamkar ba babban dan sanda ba. Ganin ya shawo kanta ya sanya ya ce "Bari na bar ki, ki yi barci Maigadona, zamu yi magana da asuba in sha Allah stay blessed and I do luv you my dear. Save Restricted Contents Bot, [Sep 13, 2025 at 12:55] Daga haka ya katse wayar ba tare da ya jira amsawarta ba. Sai da ya yi matuk'ar tura sako mai nauyi a zuciyarta kalaman nasa sun saka ta cikin nishadi da nutsuwar hakura ta karbe shi a matsayin mijinta. Ta yi shiru tana tunanin yadda zata kasance a matsayin matarsa. Yayin da shi kuma ya kasa kwanciya. Tabbas da aiki a gabansa tunda a bayyane k'arara iyalin Baba k'arami suke gaba da shi. Sannan dukkan fishinsu akansa suka d'ora. Zai yi komai dan ya auri Bilkisu don hakan ne kad'ai hanyar da zai daidaita Shi da su dari Bisa dari don Idan tana hannunsa dolensu su yi mu'amala da gidansa sabanin Idan watace ko da sun shirya ba lallai su zo gidansa ba, sai da kwakkwaran dalili. Da k'yar barci ya sure shi. Da asuba yana idar da salla ya k'ira ya dinga tarayyarta da rarrashi da maganganu masu nauyi kafin ya k'yale ta bayan ya tabbatar jikinta ya tsumu da manyan kalamansa. A daren ranar Baba ya sake zama da Asad tare da Farouku. Ya kaurara murya ya ce "Na yi magana da Bilkisu ta kuma ba ni tabbacin ta amince da batun aurenku! Amma ka saurare ni da kyau. Duk cikinku kai ne babba, ba sai na maimaita abin da ya faru na rikicin da ya gitta a tsakaninmu ba. Na yi faricinciki da Ubangiji ya k'ulla wannan alherin a tsakaninka da kuwa a duniya ba abin yake saurin yafe gaba irin auratayya. Yana daga cikin dalilan da Annabin Rahma ya auri mata daban daban daga kabilu mabanbanta, duk kuma kabilar da ya auri y'arsu gab'ar da suke yi da musulunci tana zagwanyewa. Dan haka ka yi iya k'ok'arinka ka daidaita zumuncinku da ya yi rauni da y'anuwan Bilki. Ka buda musu k'ofar da zasu zo gidanka su sake, haka nan ka yi atiya kokarinka wajen ganin kun sake hadewa kuna zumunci ko da bana raye. Sannan ka cigaba da bincike akan Sulaiman. Kana ganin dai yadda Abida take zaune bata kaunar ayi mata maganar ko zata yi gaiba, a haka ta kwashe shekaru kusan hud'u babu shi, babu alamarsa ga ya'yansa nan basu san shi ba! Baba ya yi shiru a dalilin kuka na neman kubuce masa. Sai da Asad ya dinga ba shi hak'uri sannan ya dan nutsu. Ya numfasa ya ce "Bilkisu ta ce 'Na sanar maka da d'iyarta d'aya zata zo gidanka da kuma Alti. Mamaki ya kama shi ya murmusa ya ce "Baba ka fad'a mata idan wad'anccan na Katsina ma Babansu zai ba ni to ta zo mini da su zan rikesu gabad'aya". Sai Monday Kuma in sha Allah. *Surayya Dee,* PAGE 15 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: [Sep 15, 2025 at 09:44] Yake furzarwar da k'arfin gaske wanda ya ja hankalin Hawwa da take samanta wanda itama ta ga sanarwa tunda ya koya mata kallon labaran k'asa. Amma Amrah da Faruk tuni suka yi barci dan haka basu ji hirjinsa ba. Gulma da son ganin halin da yake ciki ya sanya Hawwah gangarowa a sukwane. Sai dai yanayin da ta ganshi yana ta sa'a'i tare da suratai ya yi matuk'ar sanyaya mata jiki don kuwa muraran tashin hankali da yake zuciyarsa ne ya bayyana masa a gangar jikinsa. A sanyaye ta ce "Baban Amrah nutsu ka zauna mana kada ka fadi ka hadu, da jinya fa". A matuƙar gigice ya ce "Idan har irin wannan suyar mata suke ji idan mijinsu zai ƙara aure to la shakka sun cancanci a yi hak'uri da su a kuma rarrashe su iyakacin rarrashi. Hawwah so nake na mutu ko na huta da azabar ciwon da k'irjina yake yi mini. Da ace nasan haka Bilina ta dinga jin radadin aurenki da na yi a zuciyarta da ban auro ki ba, bare ki zama sanadin rabuwata da masoyiyyita ta gaskiya ". A zafafe Hawwah ta ce "Hala dai bayan kishi da yake yagalgalaka har kanka ne ya tab'u? Menene nawa a cikin rabuwarku? Wuka na saka maka ko bakin bindiga akan sai ka sake ta?" Cikin fitar hayyaci ya ce ", Aurenki ne dai sila. Kullum zuciyarta na zafi da turiri amma ban kula ba, ban rarrashe ta ba, Sai ma danne mata hak'kinta tare da fifita ki a kanta da ya'yanta. Ga shi na rabu da lu'ulu'u na kama azurfa". Bak'in ciki mai tsananin gaske ya shak'e Hawwah da muryar kuka ta ce "Ni ka misalta da azurfa ka kwatanta wacce take shirin zama matar gabjejen jarumin d'an'sanda irin Asad Funtua da lu'ulu'u? Ta nisa ta had'iye kukan ta ce "Ina tabbatar maka sai Anty Bilki ta ga banbancinka da sabon angonta fiye da banbancin da ka ga ni a tsakanina da ita. Don kuwa shi ba zai yi mata butulci ya yaudari budurwa da dukiyar da take mallakinta ce ba, don kuwa shi gabjejen attajirine ba da kudin mace ya yake tutiya ba. Bak'in ciki kan bak'in cike ne ya dinga k'wamushe shi. Ga wani irin azabben ciwon da yake barazanar fasa masa k'irjinsa ya yi masa k'awanya. Take jiri ya kwashe shi ya fadi yaraf kan kujera. Yayin da Hawwa ta ja tsakai mai tsananin gaske ta wuce zuwa samanta tana fad'in "Idan aka wayi gari da kai lafiya to tabbas soyayyarka bata cika ba, don kuwa kamata ya yi ka bak'unci lahira kafin wani ya fara sukuwa a kan matar da kake ƙirarin kana sonta". A wannan dare Sahal ya gane me kira da nisan dare don kuwa ya Ga tsayinsa matuk'a gaya. Sannan shine dare Mafi tsaurin a dukkan rayuwarsa. Wani irin Kishin Asad da tsanarsa ne suke ta walagigi da shi. Ya dinga addu'ar Allah ya gajartawa Asad kwana Bilki ta yi masa takaba ta dawo masa shi da Ya'yansa. A masallacin juma'a na k'asa na birnin tarayyar Nigeria aka sake daura auren Bilkisu a karo na biyu da sadaki mai k'ololuwar daraja. A lokacin da ta ga alert din kudi mai nauyi a asusunta daga kuma Yaya Farouku. Murmushin da babu nishadi ya k'wace mata domin so ta yi ace shine da kansa ya bata sadakin ba waninsa ya biyawa ba. Bata ce komai ba don sosai alhini ya kutso mata. Abida ta dinga yi mata d'an bikin ta yi daraja da yawa. Ba wani shiri Bilki take yi ba Abida ce ta ce sai sun yi walima ta kuma karbi kudade a hannun Ango, na kwalliya da gyaran jiki, masu nauyi. Ango kuma bakin shi har kunne a wajen yin hoto yana ta kama Balki tana bige masa hannu amma shi bai damu ba, a ransa yake fad'in an daura dai hankalina ya kwanta. An sha walima a gidan zuwa biyar aka kai Amarya kayattacen gidan Ya Asad bayan Baba Babba ya yi mata nasiha sannan ya damkawa Baba Faruku ita ya ce ya kai ta gidan mijinta, tare da fad'in "ko na mutu ka tsaya mata Farouku!. Abida da Saddiqa da Momi, da matar Ansari suka bisu a baya. , [Sep 15, 2025 at 09:52] Yaya Hamida dai ta ce zata zo bayan biki, don kuwa ta ji haushi da Bilki ta auri Asad mutumin da bai zo musu gaisuwar mami ba. Ba su wani jima ba suka tafi bayan Abida ta yiwa Bilki raɗa. "Saura ki matsewa yayana cinya". Bilki ta ture ta tare da fad'in "Abin da yake ranki ke nan ko?" Abida ta kyalkyale da dariya tare da fad'in "ke kika koya mini irin wadannan zantukan, dan haka gobe da azahar zan zo na ji bayani". Bilki ta yi mata k'aramin tsaki tare da fad'in ki zo sassafe ma Abida ". Ta yi dariya ta fice ta samu sauran a falo suka tafi suka bar amarya ita kad'ai. Tana tunanin yadda zasu kwashe da angon nata da yake ta rawar jiki tamkar ya yi shekaru goma babu mace tare da shi. Tasan yau dai kam ba zai daga mata k'afa ba Rawar k'afar da yake yi kadai ya isa ya nuna ya matsu. Kuma da gaske ne tun mangariba ya shigo gidan, ta dauka lamarin sai dare za a fara amma ina bai jira ba, mangariba kawai ya ja su jam'i ya ciyar da su kaza da madaran da ya shigo da shi, ita ba ta wani ci sosai ba, amma duk da haka bai saurara mata ba. Sallar nafilar ma sai ta ga a gaggauce ya ja suka yi. Suna idarwa ya juyo ya rungume ta gabad'aya. Jikinta sai b'ari yake yi yayin da zuciyarta take bugawa da k'arfi sosai tamkar yaune karon farko da namiji ya bak'unci gangar jikinta. Ya dafa goshinta ya yi addu'a, sannan ya mikar da ita tsaye, yana rungumarta sosai. Hannayensa na kai komo a bayanta har zuwa mazaunanta da suke matuƙar tafiya da imaninsa. Yadda yake rawar jiki ne yasa ta sakar masa jiki, kai yaya Asad namiji ne ba ta taba tunanin za ta iya samun bambamci mai yawa tsakanisa da Sahal ba, mussaman da ta ga ya girmi sahal din sosai, sai ga shi a bugu daya ta fahimci ya yiwa Sahal nisan da har abada ba zai kamo shi ba. Ga shi itama ta sha gyara da saiwowin asali marasa illa na Surayya Halin yau ta hade tamkar bata haihu ba. Nan fa ya susuce ya yi ta sambatu Allah yasa ma su kad'ai ne a gidan. Ita ma sai dai ta ki fada amma ta samu gamsuwar zuciya da gangar jikin da ta dade ba ta samu ba, bata san ta ba shi goyon baya sosai ba, sai da suka natsa ta fahimci ta saki jiki da yawa ta dawo tana jin kunya. Shi dai godiya kawai yake yi mata domin ta ba shi mamaki sosai, yadda ta sakar masa jiki ya yi abin da yake so. Sai ta ji tausayinsa ganin yadda gabadaya ya rude a kanta. K'arfe takwas din dare suka samu nutsuwa, sannan suka yi wanka don sallatar Isha. Daga haka suka kwanta yana rungume da ita tamkar zata gudu ta bar shi. Bakinsa daidai saitin kunnenta ya numfasa murya ba amo ya ce "Maigado kin san na sha yin mafarkin wannan al'amarin da ke? Daga baya har tsoron lamarin ya dinga ba ni, na dage da addu'a akan Allah yaye mini tare da yawaita addu'ar tsari daga shaidanun aljanu don har na a fara tunanin ko wata aljana ce zata shige ni take zuwa mini a siffarki! Ashe akwai lokacin da Allah zai tabbatar mini da faruwarsa a zahiri bayan na cire rai da samunki na hak'ura gabad'aya".. "Uhum". Kawai ta ce don ita gabad'aya kunyarsa ce ta takure ta. Yaya Asad din nan da take jin tsoronsa kamar me wai shine suke kwance gado d'aya? Shine suka yi tarayya? Ikon Allah yafi ga haka. Ya dinga yi mata hira yana shafa gashin kanta, yayin da ta yi luf a k'irjinsa har cikin zuciyarta irin haka take fatan ace mijinta na yi mata. Ya sumbaci kunnenta ya ce. "A yi barci lafiya Maigadona. Yau Allah ya cika mini burina na mayar da ke Maigadona ta gaske." Ta yi murmushi kad'a ta ce "Dama manufar sunan a zuciyarka kenan?" Ya yi murmushi mai sauti ya re da ce wa "Har cikin zuciyata". "Hmm" Kawai ta ce don abin ya yi mata nauyi. Sai me wajen karfe d'ayan dare ta ji yana lalubarta hakan ya sanya ta farka, gane da ta yi maimai zai yi, ya sanya ta ce "fitsari zata yi. Ta shiga bayi ta wanke baki ta dawo. Al'amarin da ya shayar da ita ba mai saukin bayyanawa bane kawai dai a ranar ta samu nutsuwar da bata san da ita ba. Hatta abubuwan da ya yi mata bata taba tunanin ana yinsu ba don ita bata same su ba. Da asuba ma sai da ya sake komawa bayan ya tambaye ta idan ya sake babu takura? Ta fahimci ya yi hakuri tsawon lokaci bai jefa kansa a tsila tsillar mazan yau ba, shi yasa ba ta yi masa gaddama ba, ta ba shi hadin kai, suka biyawa kansu bukata kuma dukkansu suka samu gamsuwa. Wani irin amarci suke barjewa don babu kakkautawa. Da alamu tafiyarsu ta zo d'aya don duk yadda take fad'in bata sonsa to bata yi masa k'wange kanta, kuma tana matuƙar enjoying al'amarin. A kwana na uku Abida ta zo gidan maigidan na nan tunda baya fita ko ina, yana hutun angwanci, itama hutun take yi, ba zata koma aiki ba sai sun dawo daga tafiya. A lokacin da zata fita zuwa wajen Abida. Tana daf da bude kofar ya isa ya rungume ta tsamtsam yana shinshinar gashinta da ya sha gyara. K'amshinta yake shaka, yayin da ta yi lamo a jikinsa. A duk sadda ya rungume ta gabad'aya gangar jikinta take karɓarsa, haka nan har kan yatsun kafarta take jin shauki na binta A kunnenta ya yi mata magana a hankali. "Kinsan dai autar momi yarinyace mai giggiwa da son jin abin da bai shafe ta ba. Kada ki sake ki yi hirata da ita. Bana son raini". Ta kalle shi ta gefen ido a hankali itama ta ce "Tunda ka ke tubewa a gabana, sannan kake yi mini abin da ban yi zatonsu ba ai ka ajiye batun wani girma a gefe kawai". Ya cizar mata kunne ta shige jikinsa tana zillon ya sakar mata kunnenta. Ya saki din amma sai ya ce "Maimaita me kike ce?" Tana jikinsa cikin shagwaba ta ce "Haka kawai ka samu yarinya kana caje ta, kana neman mayar da ita chopping the rice sannan ka ce wai ba zata bawa kawarta labarin yadda ake gurzarta ba?". Dariya ta k'wace masa sosai. Ya nisa cikin kwantar da harshe ya ce "Amma dai kinsan raini za ki janyo mini ko?" A hankali ta ce "Ba wani raini. Nima ta ba ni labarin yadda Yaya Sulaiman yake take ta amma hakan bai saka na raina shi ba". Ya ce ",Waton dai sai kin cire mini rigar girma ko?" Kanta na k'irjinsa ta ce "Ba zan fad'a mata komai ba, amma idan ka yi alk'awarin yau barci zan yi tunda ga farkon dare har k'arshensa." "Ya sumbaci goshinta tare da ce wa "Ban yi alk'awarin haka ba. Amma na yarda sau d'aya zamu yi sai da asuba kuma". Ta d'ag fuskarta tana yi masa wani irin kallo mai d'auke da anya kuwa? Ya yi murmushi ya ce "Maigado da gaske nake yi mana, amma idan kika ga an yi to ke ce kika rikita ni ". Ta zame ta ce"To bari na tafi kada ta ce na yi mata wulakanci." Ta isa falon da Abida take zaune tsuru ita kad'ai sai k'arar a.c da babatun tafkekekiyar talabijin. Abida ta mike tana k'ure ta da kallo. K'warai ta ga Bilki ta k'ara kyau. Dankararen leshin da yake jikinta ya yi matuk'ar yi mata kyau ga shi an zuba masa dinki na gaske. Ta isa kusa da ita tana fad'in "Abida na dauka fa sara mini za ki yi da kika zabura kika mik'e din nan?" Abida ta yi maza ta ce "Saboda kin zama matar d'ansanda ai dole a dinga kame miki Haj Maigado Mrs Asad Musa Funtua." Bilki ta murmusa don tasan gatse ta yi mata. "To zo mu shiga ciki ". Bilki ta fad'a tana nufar k'afar benen da yake falon. Hawan farko suka shiga falo sannan suka shiga katafaren d'aki. Basu zauna ba sai da Bilki ta cika gaban Abida da kayan ciyeciye da na shaye shaye. A hankali Abida ta ce "Kin ga wani ja da fresh da kika yi Sola?" Bilki ta d'aka mata duka a cinya tana fad'in "Na raba ki da sunan nan kada ki hadu da fishin kwamishina fa". Abida ta ce"Na hadu da shi din. Yanzu Bilki me kike ci kika yi wannan uban canjawa cikin kwanaki uku kacal, me yake ba ki anan wanda mu bai ajiye mana b?" Cikin iyashege Bilki ta ce "Vitamin A-z nake sha kinsan shine sinadarin gyaran fatar mace lamba d'aya. Abin da nake ci da sha anan ya banbanta da na gida mana Abida.". Abida ta kasa ce wa komai amma kallo kawai take bin ta da shi tare da tausayin kanta. Ita kam da tasan hukuncin da Sulaiman zai yi mata ke nan da bata taho Abuja ba, tunda sai da ya ce mata bai barta ba. Ga shi yanzu ya yi mata nisan da bata san inda zata gan shi, don kuwa ita jikinta bai bata ya mutu ba. Ga wata irin matsananciyar soyayyarsa da take yi mata mahangurba. Kan dole ta sanya jarumta ta danne kukan da yake neman kubuce mata. Bilki ta je ta rufe kofar d'akin Har da murza mukulli. Ta dawo ta ce "Magana zamu yi heart to heart Dr Abida." Ta zauna daf da Abida har jikinsu na gogayya, ta yi k'asa da murya ta ce "Ba da shakiyanci ba Abida! Fad'a mini a likitance akwai illa ne idan ana yin harkar na ta baki?" "Abida ta kalle ta da dukkan nutsuwarta amma sai ta shiga rudu tare da kasa gane manufar Bilki kaitsaye. Murya ba amo ta ce "D'an sake bude maganar ta yadda zan fahimta har na yi miki bayanin da zai gamsar da ke." Kan Bilki na k'asa ta ce "Ba'a ance miji ya zowa matarsa duk ta inda yake so ban da ta bayanta da kuma idan tana jinin al'ada ba?" Abida ta ce "Hakane ". Kan Bilki a k'asa bata yarda ta dago ba ta ce "Shine nake son na ji ya ya matsayin yin harkar ta baki?" Abida ta dinga kyalkyala dariya mai k'arfi mussaman da ta ga Bilkin da dukkan zuciyarta take neman fatawa akan lamarin, kunya kuma ta hana ta d'ago su kalli juna. Har Abida ta yi dariyarta mai isar ta bata katse ta ba, kuma bata ce komai ba. Da kanta ta numfasa ta ce "Maigado fatawar addini zan yi miki matashiya ko kuwa ta likitanci.?" Murya ba amo ta ce "Duka Abida ni gabad'aya na shiga rudun ne. Kin san kanki yafi nawa ja, tuna mini ma na islamiya din". Abida ta zama serious tunda ta gasgata da gaske take yi a rude take. Amma k'asan zuciyarta sai mamaki take yi duk shekarun da Bilkisu ta shafe a gidan aurenta bata taɓa sanin oral sex ba sai yanzu? Ta numfasa ta ce "Bari na fara yi miki bayanin a mahangar musulunci a takaice" Bilkisu ta gyada kai tabbacin tana sauararen ta. Abida ta fara da ce wa "Malaman da suke ganin halaccin saka al'aura a baki sun yin haka ne saboda babu wani dalili bayyananne a cikin Hadisi da Alqur'ani da ya haramta irin wannan aiki. Malaman musulunci irin su Yusuf al-Qaradawi suna da wannan ra'ayi! Haka nan kuma ba a ambaci wannan aiki a matsayin wani bangare na farfaganda ba a Hadisi, duk da cewa Musulunci ya jaddada muhimmancin aika d'an sako kafin fara mu'amala tsakanin ma'aurata kamar su sumbatar juna da tabawa da makamantansu da suka zo a Hadisi k'arara. Mazhabobin tunani (Mazahib) irin su Shafi'i da Hanbali sun dauki hakan a matsayin halattacce, sannan a matsayin wani bangare na yin wasannin da zai ƙara armasa mu'amala. Yayin da wasu mazhabobi ke daukar al'aura a matsayin najasa, suka haramta yi ta baki." Da k'yar Maigado ta d'ago ta ce"Na fahimta to menene hangen likitoci kuma?" Abidan ta nisa ta ce "A likitance ana iya yin mu'amalar ta bakine muddin babu wata cuta a al'aurar ma'aurata wadda baki zai iya kamuwa da wani ciwo sanadin hakan, sannan kuma babu rauni ko kuraje a wajen! Likitoci na ba da shawarar amfani da kwaroron roba ko dam ɗin hakori kafin yin kowane nau'i na jima'i na baka. Amma gaskiya mutane basu karbi amfani da wannan abubuwan ba ko kad'an. ". Bilki ta ce "To shike nan na gamsu na kuma fahimta". Abida ta ce "Amma ba'a son idan har za'a yi mace ta bari a dinga tura mata har makwogaronta don kuwa tana iya kamuwa da infection din baki mai tsananin gaske wacce take rikidewa ta koma( Oropharyngeal) Sai dai maza sun fi mata had'arin kamuwa da cutar Oropharyngeal (tana kasancewa tsakanin wasu kofofi biyu ta makogwaro) . Idan har miji zai saka bakinsa a wannan wajen a tabbatar an tsabatce wajen sosai mussaman yadda halittar mace take da lungu da loko! Zaku iya yin abinku amma ki tabbatar kina tsabtace wajen da kyau, ke kuma kada a dinga kai miki har makoshi sannan kada a tsananta yinsa babu kakkautawa. Anfi son yin mu'amalar baki once in a while kin ga ne?" Bilki ta ce "Na gane sai dai ai shi din ne kuma, ko zai yarda? ". Abida ta ce "Ban ce kada a yi gabad'aya ba, amma kada ya wuce harshe da lebenki da zagayen bakinki. Kada a dinga yi har can cikin. Sannan ke ma ki tsananta kula da wajenki. Sai kuma a takaita yinsa ya zama a marmarce ta yadda ba zai zama kullum ba." Gyada kai kawai ta yi tabbacin ta ji. Ta ce "Farha ta daina kukan nema na?" Abida ta ce "Jiya ma ta yi, yau dai ban tashi ba suka tafi makaranta. Amal da Noor suna d'an lallashinta. Abida ta bude maltina ta sha ta kalle ta ta ce Wato shanye abin da yake zuba miki kike yi shiyasa kika ce mini vitamin A-z?" Bilki ta mik'e tana fad'in "Kin baci Abida maganganunki sun fi k'arfin kunnuwana." Maimakon ta yi shiru sai ta ce "Yanzun saboda Allah shi Sahalun ashe kansa a duhu yake ko kuwa tsabar mugunta ya sanya bai taɓa jiyar da ke dad'i mai ratsa kwanya ba?". Bilki ta zuba mata ido ta rasa abin fad'a. Abida ya zarce da fadin ko da yake "Gwara hakan kin ga yanzu ai kin banbance mazan ma daban daban ne, na tabbatar kuma cikin k'ankanin lokaci yayana zai sa ki fara jin haushin soyayyar da kika yiwa wanccan yaron. Ba za'a d'auki lokaci mai yawa ba, za ki fara jin kunyar kiyayya muraran da kika dinga nuna masa tunda yana caje mini ke da kyau da kyau". Kan dole Bilki sai da dariya sosai ta k'wace mata tana fadin"Ba dai zan ce miki komai ba". Sai gaf da magariba ya sauko daga samansa wanda shine a k'ololuwar k'arshe. Har dakin da yake jiyo muryoyinsu ya shiga da sallama. Abida ta amasa sallama tana kuma gaishe shi. Ya amsa yana ce wa "Autar momi sai yau kika zo mata?" Ta ce "Yau din ma ina laifi?" Ya kalli Bilki ya ce "To na fita masallaci sai na dawo. "A tausashe ta ce "A dawo lafiya". Daga haka ya fice. Abida ta dinga fad'in kin ga mutum ya washe ya k'ara k'uruciya wa ma zai ce ba sa'an aurenmu ba ne ? Oh oh Yaya Asad duniya ne, ya ga y'ar yarinya ta ji kayan aiki, shine ya rik'e wuta sai da aka kawo masa ita yake yin yadda ya ga dama da ita. To ki fad'a masa na ce ya batun motar tawa, na ji shiru fa. Tunda ya same ki sai ya cika alk'awarin da ya yi mini." Bilki ta zabura ta ce"Gaskiya ciccibin nan yana da kyau fa Abida gabad'aya fa na hade na ciko". Abida ta ce. Bata tafi ba sai da ta yi sallar magariba sannan ta tafi a gaggauce. A harabar gate ta iske shi. "Yaya ya batun motar tawa ne?" Ta tambaye shi kaitsaye. "Tana daf da isowa Abida ai kinsan bana alk'awarin bogi" Ta ce "Hakane". Ya kasa sakewa da ita kamar da, domin sai yake ganin sun gama yin gulmarsa da Bilki tunda mata suna son hirar oza room. Cikin kwanaki biyar da suka yi suna cin amarci Bilki ta san ta auri jarumin maza kuma sadauki ji da ita yake yi kamar tsoka daya a miya ba ya fita ko'ina sai masallaci har wayoyinsa ya kashe abinci kuma safe da rana da yamma Abida ke aiko musu da shi daga gidan Momi. Bilki ta samu nutsuwar jiki da ta zuciya cikin sati daya a gidan Asad. Sannan ta gane zaman da ta yi a wanccan auren kusan zaman lalata kuruciya ne kawai. PAGE 16 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: [Sep 15, 2025 at 21:55] A haka suka tafi k'asar America. Soyayyar da ya nuna mata da gata ya sanya ta fara jinsa a ranta ta dinga tuno lokacin da suka je hutu gidansa daidai haihuwar Bilkisu. Yadda yake shiga kicin ya yiwa kansa abinci a dalilin matarsa na da tsohon ciki. Tabbas yana cikin maza kadan da suke yiwa mata hidima da zuciyarsu da aljihunsu. Don a yanzu ma da ya girma bai fasa komai ba. Tana zaune sai ya hado musu coffee ko ya shiga kicin ya hado musu abin motsa baki dangin fruits ya kawo gabanta. Yawan motsa jikin da ya rayu akansa ya taimaka masa don kuwa bai tara teba ba, sannan kuma a tsaye yake kan k'afafuwansa ga kuzari da hanzari tunda ya rayu yana motsa jiki. Idan ya fita Allah Allah take yi ya dawo ya dinga damuk'arta, yana yamutsa ta tana jin dad'i har cikin kanta, abin da bata samu a inda ta zaci zata samu ba, take samunsa a inda ta yi zaton ba zata samu ba. Amarci gangariya suke zubawa wanda Bilki bata taɓa zaton ana samun irin haka ba. Shi kansa a zuciyarsa yake tambayar kansa wai mata dama ko wacce da irin taste dinta ne ko kuwa dan ita Bilki tafi matarsa k'uruciya ne? Gabadaya ji yake tamkar yanzu ne yake samun gamsuwa da nutsuwar da yake so. Har cikin bargonsa yake jin son Bilki irin yadda bai taba ji akan kowacce mace ba. Na ce ba? Kina nan kina ta yin tashin hankali akan namijin da idan kin mutu wata zai aura ya sota kamar yadda ya so ki koma fiye da ke har ya manta da soyayyarki? Dan Allah mata mu yi ibada, mu yiwa mazanmu biyyaya iyakar iyawarmu don kuwa aljannar mace zata fi gamsu ne idan mijinta ya amince da ita. Mu rungumi sana'a ko aikinmu da kyau a sassauta soyayyar da zata saka matsanancin kishin da zai hanamu sukuni ya halakamu. A guji canja halitta da nufin burge rijalu! Wallahi ba abin da zai sauya su daga zama polygamist. 😅 Kwanaki ashirin ya kammala aikin da yaje yi k'asar. Suka k'ara kwanaki biyar suna yawon bude ido a cikin birnin California. Daga nan kuma suka wuce London ta k'asar Birtaniya. Kwanansu biyu a garin suka kaiwa Khadija ziyara makarantarsu. Itace kuma Bilki ta d'ade bata ganta ba a cikin ya'yansa, tun tana karama sosai. Kallo d'aya tak ta gane yarinyar ta juye Babanta sak ba abin da ya rabata da shi na kammani har hanzarinsa ta kwashe. Aysha da Amal ne suke kama da uwarsu. Sauran yaran kuma gasu nan ruwa biyune. Amma Noor ma kam kamarsu d'aya da Khadijan. Da walwala ta karbesu da girmamawa. Bilki ta ji dad'in girmamata da ta yi. Ta kudire a ranta zata iya kokarinta ta basu fuskar da zata zame musu uwa, su kuma shigo gidan ubansu ba tare da zullimin babu uwarsu ba. Ya ce tunda a hutu take ta zo su tafi masaukinsu. Cikin mintina kad'an ta fito janye da k'aramin akwatinta. Basu koma masaukinsu na sai da Khaditta jagorance su zuwa gidan abincin da suke da halastaccen abinci (Halal food). Daga nan suka koma hotel din ya kamawa Khadija d'akinta wanda tazarar gaske da nasu d'akin. Sosai suka huta suka sha hotuna wanda Khadija take yi musu wani sun sani wani ma kawia daukarsu take yi basu ankara ba. Zamansu na London ta fahimci Baban Bilkisu mai tsananin son ya'ya ne. Don kuwa asuba yake k'iran Khadiha ya ji ko ta tashi sallah. Idan zasu koma barci bayan sun idar sai ya sake k'iranta yana fad'in "Idan kin ji yunwa ki yi order duk abin da kike son ci kada ki ce sai kin jiramu". Idan sun tashi, sun yi wanka sun shirya sai sauka k'asa ta fito su hadu sannan a wuce wajen karya su karya tare. Sannan kuma ta fahimci shi mutum ne mai yin abu babu nuku nuku ko cutar da kai don idan Khadija zata yi musu hoto ita ce take nuna masa yadda zai tsaya ko zai rik'e Bilki. Ya yi kuma yadda ta ce din babu jin nauyi ko kunya. Haka itama yake rungume ta Bilki ta yi musu. Ana jibi zasu bar London Khadijah ta ce "Dady zamu je gidan Anty Ayusha fa na fad'a maka tana mini kirki, Ina zuwa na yi weekend a gidanta, k'asan idan y'an arewa muka hadu a turai duk zama muke yi dangin juna. Ita da mijinta suna mana kokari suna guiding dinmu sosai." Ya ce"To zuwa anjima idan mun je yiwa sisters dinki tsaraba sai mu je gidan". Sosai Khadijah da Bilki suka saba suka samu kyakkwar fahimta duk da Khadija tana yawan tuna mominsu tare da jin da yanzu itace a gefen Dady ba Anty Maigado ba. Sannan yadda yake zumudi akan amaryarsa ta gane ko momi na da rai zai iya nad'e k'afar wando ya yi zawarcinta har ya aure ta duk rikicin da za'a yi kuwa. Amma ta danne don kuwa gara ace auren ya yi da ace Babansu na harkar banza da zubar da mutuncinsa da nasu. K'arfe biyar saura na agogon GMT Ummi ta karbi ziyarar manyan baki cikin sa'a suka tarar da Baban Husna a gida dan haka da karramawa ya karbi kwamishina a falonsu. Cikin mintina kad'an aka cika gabansu da cimaka iri iri. Sosai ya yi musu godiyar yadda suke kula da su Khadija suka basu kofar zuwa wajensu. Ya yiwa yaransu kyautar bajinta sannan suka tafi. Bilki tana yaba kirkin Ayusha da mijinta tare da yiwa Husna, Hanan da Aryan addu'ar su zama masu albarka. Fatan alheri ga kanwata marubuciya Ummi Ayusha Muhammad da iyalinta da suke zaune a birnin London. Washegari suka mayar da Khadijah makaranta suka yi bankwana suka rabu cikin sanyin jiki don sun ji dad'in zamansu taree que ne illa tuna mominsu shike nan su da ita sai a darussalam. Ta dinga yi mata addu'o'in neman gafara har ta samu nutsuwar zuciyarta. Ta dauki wayarta ta shiga what'sapp ta shiga ta tura hotunansu cikin group dinsu da Aysha ta bude musu su kad'ai. Su hud'u ne a ciki Aysha Khadija Hafcy sai Bilkisu tunda itama da wayarta Amal da Noor ne babu su. Cikin mintina kad'an Aysha ta yi tagging hoton Bilki da Babansu ta ce amma kuwa Khadija kin ci amanar momi da kika turo mana wannnan abin, na rantse tunda na zo duniya ban tab'a ganin abu mai muni a zuciyata irin wannan pic's din ba. Yanzu Dady abin da ya zama ke nan, ji yadda ya wani mak'ale ta? Ke kuma da yake sarai sunanki shine har da turo mana?" Hafcy ma ta ce "Yaya Khadijah kam ai gabadaya al'amarinta babu kishin kai ". Bilkisu dai stickers din dariya take ta turawa babu adadi don gabad'aya Dady ne ya bata dariya yadda yake sanye da k'ananun kaya ya dawo kamar saurayi yana ta soyewa abinsa. Aysha kuwa ta kufula ta zazzage ta tare da fad'in zata cire ta daga group din tunda take dariya bayan abin kuka ne ya same su. Khadija ta ce "Ya Aysha ki yi hakuri Anty Maigado bata da damuwa. Da ya auro wacce bamu santa ba ta zo ta cutar da shi muma ta cutar da mu fa? Ai gara ita duk tsiya dai y'aruwarmu ce". Nan da nan Aysha ta danna voice na tsawon lokaci tana fad'in "Ta ina ta zama danginmu? Sun kai Baba Babba fa kotu? Sannan an ce za'a ba shi anty Laura don ta cigaba da kula da su Noor tunda sun saba da ita amma fir ya k'i ta. Sai kawai ya kwaso mana wannnan mai tafiya mazaunai na sittin, saba'in, sannan yanzu na gano tuntuni ya so aurenta tunda har mai suna ya yi mata." Ta fara kuka murya na rawa ta ce"Na tausayawa poor momi! Allah sarki ta sha wahalar haihuwa an tashi an sakawa d'iyarta sunan budurwa wohoho me za'a ce da maza ne?" Ta kammala cikin tsananin kuka. Khadija tana kwance tana sauararen Aysha jikinta ya mutu tabbas itama ta ji babu dad'i amma kuma ya zasu yi ne tunda ba zata dawo ba, sannan basu isa hana shi yin aure ba. Kanta ya kulle mussaman ita bata ga aibun Anty Maigado ba. Sannan zuwansu duk abin da zai yi mata baya shawara da matarsa kawai bata yake yi, kuma bata ga ko a fuska Anty Maigado tana jin babu dad'i ba. To shi ke nan duk kokarinsa na ya faranta musu, sai kuma su k'i kwnatar masa da hankali ta hanyar zama lafiya da matarsa. Ta kuma fahimci Aysha tana son jagorantarsu su musgunawa matar Babansu ta yadda zamanta da shi zai gagare ta. A sanyaye ta yi nata voice din da fad'in Momi is gone ba zata dawo ba forever. Mu yi hak'uri mu zauna da matar da Dady ya aura da girmamawa dan yasan mun gode da hidimar da yake yi da mu babu gajiyawa. Idan ya gane muna da damuwa da matarsa zai kasa samun nutsuwar da ta dace da shi. Don haka mu yiwa Momi addu'ar samun rahamar Ubangiji shine abin da tafi bukata. " Nan da nan Aysha ta ce "Hidimar da yake da mu ashe ba Allah ne ya kallafa masa ba? Tunda ke ba kya kishin uwarki sai ki k'arata ke kad'ai sannan kada ki kuma turo mana wannnan bak'incikin! Hafcy ta yi tagging da fad'in "Wlh kuwa Yaya Aysha duk yadda nake son matar nan yanzu haushinta nake ji, tunda ta yi kuskuren auren Dady ai ba sauran girmanta a idona tamkar mai jiran momi ta mutu ta aure shi". Bilkisu dai bata ce komai ba sai dai ta shiga tunanin maganganun yayarsu na cewa saka mata sunan anty Maigado ma cin amanar mominsu aka yi. Daga haka Khadija ta sauka daga what'sapp din tare da tunanin Aysha zata d'agawa masu gidan hankali dama ita bata da dad'in mu'amala. Yayin da Aysha ta dinga jan kunnensu Hafcy saura su ce zasu shige mata. Tirk'ashi. Ranar juma'a da daddarre suka sauka a birinin Abuja suka tarar da tawagar y'an sanda na dakonsu. Har gida aka kawo su. Ita dai Bilkisu tana kallon yadda ake ta k'ame musu tare da sarawar girma. Wannan nau'in gaisuwar na matuƙar yi mata dad'i a zuciyarta. A daddafe suka yi wanka da ruwan zafi sannan suka yi salla suka kwanta barci ya yi awon gaba da su don sun gaji lik'is. Da yake asabar ce da suka yi sallar asuba sake rungume ta ya yi suka koma barcinsu. Sai wajen 12 suka farka. Suka yi wanka sannan suka nufi kicin don karyawa don kuwa a cikin katafaren kicin din dainin eriya yake. Tuni an tanadar musu abinci kalakala na alfarma. Da kansa ya zuba mata sannan ya zubawa kansa. Ita dai cikin tsantseni take cin abincin duk kuwa da ba shi da makusa kawai ita yadda duka ba musulmai ba ne suke yi musu abinci ne ya dame ta. A tausashe ta ce "Baban Bilkisu mu je gida anjima mu gaida su Baba daga nan mu dauko yara da Alti". Ya girgiza kai tare da fad'in "A a Sai na gama hutuna zasu dawo". Ta zuba masa ido ta ce "Baban Bilkisu ka ce mini fa za'a sake baka hutun tafiyar da ka yi na sati biyu. Kuma yanzu sai mu yi ta zama haka?". Ya zuba mata ido cikin wani irin salo ya ce "Ba za su dawo su dinga katse mana amarci ba. Dan haka gobe zamu je mu gaishe su amma ba da yara zamu dawo ba". Ta yi k'asa da kanta don har zuwa lokacin nauyinsa da kunyarsa basu gama barinta ba. Ya cigaba da kallon yadda ta sake yin fari, fatarta ta yi wani irin smooth na ban mamaki. Zuciyarsa ta harba da sauri don kuwa ta sauya sosai wanda bai lura da hakan ba sai a lokacin. Zuciyarsa ta amince masa cikine da ita don gabad'aya ta danyace ta sake zame masa yarinya sosai. Ya tafi lissafin aurensu idan har daidaine suna cikin sati na bakwai don anyi bikin da sati biyu suka tafi America. Sun shafe satika biyar kafin su dawo, ke nan suna daf da shiga watanni biyu. Zuciyarsa ta cika da farinciki a duniya yana son yara yana son ya'ya da yawa. Tun kafin ya tabbatar da zatonsa ya ji son abin da yake cikinta yana ratsa shi ta ko ina. Ya tausasa harshe ya ce "Me yasa kike son su dawo tun yanzu?". Cike da tab'ara ta ce "Gaskiya ban son abincin wannan matar na fi son na Alti". Ya yi shiru tare da tunanin yadda shi da iyalinsa suke son girkin charity mussaman ya rabota da hotel d'in da take aiki ta dawo zama a gidansa gabad'aya. Tana da d'akinta a sashin y'an aiki. Ya numfasa ya ce"To kafin su dawo ki dinga yi mana dan gaskiya ba zan yarda hankalinki ya kasu biyu ba a wannan kwanakin. Kawai ki bari na kammala cikace su". Ta rausayar da kai ba tare da ce masa komai ba domin duk zalamarta akan al'amarin yayan nata ya k'ure ta. Matuk'ar ya mu'amalance ta sai ya gurje ta da kyau. Ta fara jinsa cikin zuciyarta, duk wani kallon da ta dinga yi masa a baya na baibai ya fara gushewa daga idanuwanta. Ta gasgata Abida da take yawan fad'a mata bak'in namiji ba shine muninsa ba, sannan yayansu ba mummuna bane kawai dan ta rufe zuciyarta akansa ne. Yanzu kam ta amince ba mummuna bane sannan tabbas jarimi ne ko cikin jarumai. Washegari sai yamma lis ya dauke ta zuwa gidansu, da ledar tsarabar mutanen gidan. Da kansa yake tuki, yayin da take gefensa a zaune. Gabaɗayansu sun yi kyau na ban mamaki. Sassanyen k'amshi na tashi a jikin kowannensu. Da farinciki sosia Baba Babba ya gaisa da su yana jin auren Asad da Bilki ne tsanin yin sulhu a zuri'arsu don kuwa ya lura ya'yan Baba k'arami gabad'aya basa iya yin mu'amala mai yawa da shi da ya'yansa dama Bilkin ce tafi sassauci. Yanzu kuwa saboda ita zasu yi mu'amala da gidan Asad daga haka kuma har komai ya warware albarkacin addu'ar da yake yi a kullum na kada zumuncinsu ya waste gabad'aya. Ya dinga sanya musu albarka tare da nasiha mai ratsa jiki. Yayin da tausayinsa ya kama Bilki ya tsufa sosai gabad'aya rauni ya baibaiye wanda ba na rashin gata ba ne illa na rashin cikakkiyar lafiya da kuma rauni irin na gajiya da duniyar da tashin hankalin da yake cikinta. Suka ajiye masa tasa tsarabar wnada jallabiyoyine fararen sai turaren alfarma. Haka momi ta dinga yi musu addu'a cikin bayyananen farinciki. Ta yunk'ura a hankali ta yi ciki wajen yaran tare da adduar Allah yasa Abida na gida. Dakin Abidan ta fara shiga ta tarar da ita kishigide a gadonta junior na kwance jikinta yayin da Farha ke can gefe a zaune tana cin cookie's. Amal da Noor kuma na kan kafet suna game a tablet. Farha na ganinta ta zabura ta mik'e ta nufe ta a guje. Yayin da Bilki ta yi yunkurin d'agata amma ga mamakinta sai ta kasa. Mamaki ya rufe ta don ba wani girma Farha ta k'ara ba haka nan ba nauyinta ne ya k'aru ba. Kan dole ta hak'ura ta rungume ta tare da jan hannunta suka zauna bakin gado. Ta kalli yarinyar ta ga idanuwanta sun cika da k'walla ta ce "Menene?" Muryarta na rawa ta ce "Mahma na dauka nima guduwa mini kika yi kamar yadda muka gudo muka bar su Yaya a Katsina". Jikin Bilki ya yi sanyi. A tausashe ta ce "Amma ai na sha fad'a miki ce wa "Duk inda zan je da ke zan tafi mutuwa ce kawai zata rabamu". Ta goge hawayen idonta tare da rik'o hannun Bilki ta ce "Dan Allah Mahma to zan biki yanzu ni dai na gaji". Ta fashe da kuka sosai. Bilki ta jata jikinta ta ce"Zan zo na d'auke ku tare da su Noor next week inji dadynsu ke ma yanzu shine dadynki". Ta yi shiru can ta ce "To dadynmu na Katsina fa?" A hankali ta ce mata "Dadynki ne mana. Amma tunda zamu koma gidansu Noor to ba uncle za ki ce dinga ce masa ba sai Dady". A hankali ta ce "To! Amma dai Mamah yau zan biki gaskiya. Junior ya yi ta tsokanata amminsa ta hana ni dukansa, su Noor ma su dake ni Ammi sai ta ce ",Ni na tsokanesu na rufe bakina na dame ta da kukan shagwaba. Alti ce kawai take kula ni". Na jijjiga kai na ce ki yi hak'uri idan kuka dawo gida ba zan bari su dinga dukanki ba, amma ke ma ban da rashin kunya tunda basu Yaya Amrah bane da basa iya dukan ki". Abida ta jijjiga kai ta ce "Duk yadda ake kaffa kaffa da ita ki ji sharrin da take hadawa?". Bilki ta yi murmushi kad'an ta ce "Ke dai Abida ki yi shiru amma Farha bata karya kawai kina bawa d'anki kariya idan ya tsokane ta. Abida ta jijjiga kai tabbacin mamakin yarinyar ya yi matuk'ar kamata. Daidai lokacin su Amal suka iso kusa da ita suna fad'in "Mahma sannu da zuwa, ina yini tare da Dady kuka zo?" Ta mik'a musu hannunta suka rik'e ta amsa da fad'in "kuna lafiya? Dady na falo". Suka fice da azama ta bude hadaddiyar jakar hannunta da ta siya wajen umm asalan Egyptian items..... Ta fito da tissue ta gogewa Farha hawayen idonta cikin rarrashi ta ce "Oya je ki gaida Dady ki yi masa welcome kada ya hana ki tsarabar da muka siyo miki ". Ta sauka da sauri ta fice. Sai lokacin ta mayar da hankalinta ga Abida da ta lura ta kafe ta da kallon k'urillah. Murya ba amo ta ce "A a Abida wanne irin kallo ne haka ne?" Da dariya ta ce "Ga ni na yi tamkar cikine da ke Maigado". Zuciyarta ta tsinke don kuwa ita da kanta tana k'alubalantar sauyawarta tashi guda. Sannan kasala ta dabaibaye ta. Kasa d'aga Farha d'azu ya sake jefa mata shakku a zuciyarta. Duk da bata da tabbas din cikin ne. Ta nisa ta ce "Daga dan zamanmu ne har za ki fara yi mini batun cikin Abida? Inace ban gama rufa watanni biyu da auren ba?". Abida ta watsa mata wani irin kallo ta ce "ko jiya kuka tare sai ciki ba zai shiga ba? Wannan gagarumar sauyawar da kika yi fa, ko duk vitamin A-z din da yake zuba miki a baki ne?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 15, 2025 at 22:07] Wata irin kunya mai yawa ta dirar mata. Ta yi maza ta yi k'asa da kanta tare da fad'in "Allah ya shirye ki kawai". Abida ta kyalkyale da dariya tana fad'in ".Yaya Asad ya hada wata da aiki nan da watanni zamu ga sakamakon da zata ba shi. Kafin Bilki ta ce komai, Alti ta turo kofar da hanzari bakinta d'auke da sallama. Bilki na ganinta ta yi karfin halin mikewa da sauri suka rungume juna. Abida ta kallesu tana jin babu yadda za'a yi ta yarda ta had'a jikinta da na y'ar aikinta duk da dai Bilkisu ta yi matuk'ar yiwa Alti wanka babu wani abin aibu ko na k'yama a tare da Altin. Sakwanni biyar suka saki junansu dukkansu fuskokinsu d'auke da bayyananen farinciki. Alti ta zauna a gefen kafet yayin da Bilki ta zauna a inda take zaune. Suka gaisa cike da karrama juna. Jimawa kad'an Alti ta fice. Jummai wacce yar kabilar Nufe ce ta shigo d'auke da tiren ruwa da lemo ta dire a gaban Bilki sannan ta durkusa cikin gurbatacciyar hausarta ta ce "Anty barka da yanzu, sannu da zuwa". Bilki ta amsa da fad'in "Ba hausa mun same ku lafiya?" Ta murmusa ta ce "Lafiya kalau Alhamdulillahi Anty. Sannan ta fita. Jummai zata yi shekaru ashirin da biyar ta taba aure har da yaranta biyu suna can garinsu a Bidda a wajen Babansu, tunda suka rabu. Tun kafin a yi mata aure take hannun marigayiya Rukayya sosai ta iya gyara babu gajiya, haka nan ta iya girkin gargajiya daban daban dan idan tana yin sakwara sai ka zaci ba da hannu ake yi ba. Sannan ta iya rainon yara da juriyar fitinarsu. Amal da Noor sun yi matuk'ar shak'uwa da ita. Shiyasa har yanzu take nan tana kula da su. A zuciyatar Bilki ta kudire Alti da jummai kawai sun ishe ta amma charity sai ta bar gidan ba zata zauna ahalil kitabu na yi mata girkin abinda zata ci ba. A matuƙar sanyaye Abida ta ce "Yanzu Maigado ba za ki tausaya mini ki fad'a mini gaskiya akan Yaya Sulaiman ba. Ke ko tausayina ba kya ji. Dubu yadda vitamins din da ake zuba miki na watanni biyu kacal ya mayar da ke amma ni kullum k'ara baki nake yi ina yamushewa, sai na bude baki na fad'a miki ina da buk'atar a zuba mini ne?" Dariya ta subucewa Bilki ta sosai. Ta numfasa ta ce "Allah Abida kalamanki na kashe ni da kunya. Amma fa watannin baya na yi miki rantsuwar ban san inda yake ba. Wallahi tunda ya tafi ban sake ji daga gare shi ba." Hawayen nadama suka k'wacewa Abida babu zato. Cikin rishin kuka ta ce "Na gaji Bilki, Wallahi na gaji, ni kam na shiga ukuna". Tausayinta ya kama Bilki sosai ta matsa kusa da ita ta rik'e ta. Murya a dakushe ta ce "Sannu Abida ki k'ara hak'uri mu cigaba da addu'a da ikon Ubangiji idan yana raye zai bayyana.". Cigaba Ta d'ago idanuwanta hawaye na tsere duk wata izza da jin kai sun k'wace mata ta ce "Wallahi yana nan da ransa, Wallahi bai mutu kawai tsabagen wulakanci da zalunci ne". Bilkisu ta kasa ce wa komai. Can ta numfasa ta ce "Abida tunda dai kad'an ya rage ki cika shekaru hud'u a dakon dawowarsa kawai ki yi gaiba idan kin samu miji ki yi aurenki tunda har kika furta mini kin gaji na tabbatar kin kai k'ololuwar gajiya ne tabbas". Takaicinta ya shake Abida a zafafe ta ce "Ce miki na yi ina marmarin wani rijalun ne bare ya biya mini nasa littafin ra'asin? Yaya Sulaiman din nake kewa kuma gangar jikina take mararinsa ba waninsa ba. Kawai idan za ki taimake ni, ki taimake ni, idan kuma ba wani taimakon da za ki iya yi mini to yaune rana ta k'arshe da za ki ce na yi gaiba don kuwa daga nan har mahdi ya bayyana zan jira shi ". Ta fad'a cikin kuka na sosai. Maigado ta kasa ce wa komai don sosai Abida ta bata tausayi Duk yadda take danne al'amura a ranta tare da jin kai matakin Yaya Sulaiman ya yi matuk'ar bugunta ta yadda ta fara sauke al'amura masu yawa. Ta tabbatar saukowar da ta yi take mu'amala da ita da kyau har da soyayyarsa da son sanin inda zata gan shi ko ta samu wani bayani gamshasshe. Da ƙyar ta shawo kanta ta yi shiru. Tsawon lokaci suna zaune jugum jugum don sosai suka shiga alhini. A sanyaye Abida ta shiga bayi ta wanko fuskarta ta fito ta shafa hoda sannan ta fita dan gaida Yaya Asad. Suna gidan aka yi sallar magariba da isha. Basu bar gidan ba sai da Bilki ta damkawa duka yaran tsarabarsu kowa da ledarsa tunda ga kan Amal har zuwa kan Noor. Yan aikin gidan mata ma duk ta bisu da turare. Abida kuwa gwangwajeta ta yi da haddun materials din Malaysianfabrics....07020695644 Wanda take ta yi mata nacin tana so saboda kyaunsu da rashin nauyinsu. Suka tafi baba da Momi suna ta saka musu albarka. A hanya ya kalli yadda ta takure ta kasa sukuni. Ya tausasa harshe ya ce "Sarauniyar shaiba ya dai?" Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya yi shiru don ya riga da ta gane ta idan ta shiga yanayi irin haka tafi son shiru. Maimakon ya sake yi mata magana da baki sai kawai ya kunna musu karatun alkur'ani suratul Maryam ta fara tashi da muryar sheik Afif. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: PAGE 17 Sosai karatun ya daidaita mata rud'un da ta shiga na ina Yaya Sulaiman ya shiga tunda Abida ta kore mata tunanin ko ya hadu da ajaline. Suka isa gidansu da y'ansanda suka yi masa k'awanya. Ya kammala daidaita parking. Ta ga bai motsa ba. Sai kuma can ta ga ya sauke gilashin danƙareriyar motar, y'ansanda sun fi goma gabad'aya sun k'ame tare da sara masa. Hannu kawai ya daga musu suka sake sake sarawar sannan suka bar jikin motar kowa ya koma inda yake tsarewa a kusurwaowin gidan. Ta saka hannu da nufin ta bude murfin k'ofar sai ta ji ta a rufe. Ta kalle shi amma ta kasa ce wa komai. Sai ta ga ya bude ya fita. Ya kewaya ya bude mata k'ofar da kansa sannan ya yi mata irin gaisuwar da ta ga yaransa sun yi masa yanzun nan. Har cikin ranta tana matuƙar jin dad'in sarawar da yake yi mata. A duk sadda ya yi mata hakan har zuciyarta take jin lallai ita din sarauniyar zuciyarsa ce. Ta murmusa ta ce "Na gode Baban Bilkisu! Daga haka ta dan yi gaba ta bar shi yana rufe motar tare da magana da wani d'ansanda da bata ji me suke ce wa ba. Kaitsaye d'akinta ta nufa ta fara rage kayan jikinta. Daga nan ta fad'a bayi don ta yi maza ta yi wanka kafin ya shigo don sai ya ce shima wankan zai yi su yi tare. Duk saurinta ya shigo d'akin kafin ta kammala wankan. Abin da take zaton shine ya afku don kuwa bayin ya shiga babu jin nauyi. Ya tube kan dole sai da suka yi tare. Daga suka fito kuma abin da ya biyo baya masu nauyi ne. Da safe Bilki zaune gaban madubi daga ita sai tawul iya cinya tana k'arewa kanta kallo don gabad'aya bata yarda da kanta ba. Maganganun Abida na cewar tana da ciki sun yi matuk'ar tsaya mata a zuciyarta. Zuciyarta ta harba ganin yadda breasts dinta suka cika suka tsaya sannan ya k'ara gari tamkar mai shafa mai. Haka nan ta ciko. Ta gasgata cikine da ita don kuwa rabonta da period tun wanda ta yi satin da za'a daura Mata aure. Ga shi wata na biyu ke nan. Ta furta 'Tirk'ashi ' a bayyane don gabadaya al'amarin wani iri take ganinsa. Wai itace d'auke da cikin Yaya Asad? Duk yadda ta gama fad'in bata sonsa shike nan sai a ji ta haihu wata tara da aure don kuwa tabbas kwanakinta a gidansa kwanakin cikin jikinta. "Wanne irin rabo ne na gaggawa haka?" Ta fad'a a fili . Yara basu dawo ba sai da ya cinye sati biyunsa da ya fad'a. Soyayya da riritawa ba wacce bata ga ni ba. Ita da kanta idan yana yi mata wasu abubuwan sai ta ga kamar ya wuce ya yi su. Bata fad'a masa batun cikinta ba shima kuma ya kife ta a baibai bai nuna mata ya gano ba. Alti Jummai da yaranta uku Amal Noor da kuma Farha sun dawo gidanta wanda Abida ce ta kawo mata su. Da farko Bilki tana zaune lafiya da Amal da Noor. Komai tare suke yi da Farha sannan bata banbanta su akan komai. Tana jinsu tamkar ya'yan cikinta. Yaran sun saba da ita tun a gidan Momi. Mahma sama Mahma k'asa kamar yadda Farha ta ke k'iranta. Sosia take jin dad'in zamantakewarsu. Tuni ta koma aikinta, kullum Kuma suna waya da su Amrah mutanen Katsina. Hankalinta ya kwnaata tabbas yanzu ne ta yi aure a da kam ba wani abu da zata idar na jin dad'i ko na nutsuwar zuciyarta. Har dinga ganin ba zata samu wata a gidan Yaya Asad ba don kuwa ta yi amannar yana matuƙar sonta k'warai da gaske. *Bayan wata d'aya* Yana kishingide gefen gadonta ta shigo d'akin hannunta rike da bowl fari kal mai dan zurfi ta zauna gefe daga k'asa kan kafet. Tana cin abinta cikin nutsuwa. Ya zura mata ido yana nazarin yadda ta zama mai ciye ciye sannan ta ninka farinta, haka nan ta zama mai kwadayi. "Madam ko dai na yi ajiya ne ba a faɗa mini ba?". Ya fad'a da wata irin murya mai kashe jiki. Ta matse ta ce "Ajiya a ina ke nan?" Ya yi murmushi mai sauti ya ce a cikinki mana ". Yadda ta kalle shi tana tura masa ɗan bakin nan nata ne yasa ya san cewa tabbas ya yi ajiyar bakin shi ya ƙi rufuwa saboda murna nan da nan ya ta so daga inda yake kwance ya rumgume ta yana sumbatar ta, cikin tsananin farinciki da murna. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Yayin da ita kuma take jin wani iri takura da zullimin yadda cikin ya yi mata shigar sauri. Amma kuma soyayyar da yake gwada mata tare da yin bare bare akan sha'aninta yana matuƙar k'warara ta. Kwanci tashi har aka yi hutu. Hafcy da take hostel a Skyline University ta kammala aji d'aya zata shiga biyu. Bilkisu kuma ta kammala sakandire. Aysha ta kammala da Enugu ta dawo gida Sai Dai kwanakin sati ta yi ta wuce Lagos yin wani kwas na watanni uku zuwa yanzu ta cinye wata guda. Tun a kwanakin da ta yi Bilki ta gane Aysha tsagera ce, Sai dai bata nuna mata ma ta gane tana mata kallon riani ba. Yaran Basu Dade da dawowa gidan ba yaran ta fahimci halin kowacce daga cikin su. Bilkisu ta fi sauƙi sauki, kullum tana gaishe ta da safe, amma ba ta sake mata kamar da, duk da tana kokarin jawo yaran a jikinta. Hafcy kuma ba ta da kunya idan ta ganta sai kallon sama da k'asa tana tabe baki ko ta yi mata dariya, abin ya fara damunta amma ba ta nuna ba, kuma ba ta taba yi mata magana ba. Amal dai da Noor sune nata komai itace ke yi musu tare da Farha. Abu daya ne yake bata mata rai da Hafcy ko ba ta ci darajan matan ubanta ta gaisheta ba, to ta ci darajar ita kanwar uban su ce su girmamata amma yarinyar nan sam ba ta ganin girmanta da mutumcinta kamar za ta yi mata magana sai kuma ta fasa, ta zura mata ido kawai ta ga iya gudun ruwanta amma idan ta zauna shiru ko a wajen aiki ne sai ta yi ta tunanin kar dai ta baro gidan Sahal a dalilin rashin adalcin miji yanzu kuma ta faɗo l gidan da ya'yan miji za su tayar mata da hankali domin ga Hafcy nan ta dau hanya. Hafcy dai tata da suke son Juna. Duk shekarar Duniya Sai ta yi mata dinkin sallah, haka nan lokacin uwarsu na da rai akai akai take k'iranta ya gaishet Konda aka yi rikicin Ladi farm bata fasa k'iranta ba hakan ya tabbatar lwa Bilki ba'a hana yarinyar mu'amala da ita ba. Amma tunda ta dawo ta tarar da zama matar Babansu Shike nan take yi mata abubuwan Raini iri iri. Ko abinci aka dafa a gidan ba ta ci sai abin da taga dama zata bawa umarni Jummai ta yi mata ko Charity. Kullum za'a yi girkin gida amma Hafcy zata bada umarnin ayi musu nasu daban. Koada yaushe abinci kibikibi Kuma ba'a iya cinyewa haka aka barinsa ya lalace. "Mahma anya ba za ki yiwa yaran yaran nan togaciyar girkin da suke Sawa ana yi musu wanda ya wuce bukartarsu ba? Abin da suke yi bai kyautu ba, idan megidan ya ga ni ba zai ji dadi ba." Alti take wannan batun da taa ga almobazarancin ya yi yawa . Balki ta yi shuru kawai tana jin Alti na kora mata jawabi, yau ma hadaddiyar fried rice da coslow Ga Kuma pepper chicken aka dafa, amma Hafcy ta sanya aka dafa musu brown superghetti da pepper fish wai k'awayenta zasu zo. Har dare ba Wanda ya zo Kuma abincin gal warmers ko ta kansu bat sake bi ba. "Mahma bai kyautu ba gaskiya. A matsayinki ta uwa a gare su ya kamata ki tsawatar musu." Bilki ta jinjina kai, tasan gaskiya Alti ta fada, uwa take a wajensu kuma hakkinta ne ta gyara musu idan taga an yi ba daidai ba. Duk da ba ta so ta yi magana ba, amma ya zama dole tun kafin Megidan ya ga ni ransa ya baci kuma daga karshe laifi ya dawo kanta. "Haka ne Alti je ki abin ki zan yi musu mgana in sha Allah" Ta tashi ta tafi ta bar Balki na nazarin yadda za ta tari yaran da magana, da ƙyar dai ta yi kundubslan tashi ta nufi dakin yaran har Farha duk suna cikin dakin tare da su, da yake suna da tibi a dakina suna ta kallon cartoon su kuma manyan na saman gado kowacce na latsa wayarta. Shigowar Balki ya ba su mamaki, domin ba ta taba shigowa dakin su ba. Tana shiga ta kalli su Amal ta ce "Ku je falo ku ce Alti ta kunna muku cartoon din a can Farha." Ta fada tana kallon ta da sauri ta yi gaba tana fadin" To Mahma Noor mu ku zo je." Sai da suka fice sannan Balki ta mayar da hankalinta wajen manyan tana kallonsu. "Sannu da gida Anty."[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: In ji mai sunanta Bilkisu. "Ya hutu?" Ta fada tana kallonta. Sai ta amsa da lafiya lau, da ma ita suna gaisawa marar kunyar ta k'arshe Hafcy ce. Yanzu ma ko kallon Bilki ba ta yi ba, hankalinta na kan wayar hannunta Stool din madubi Bilki ta jawo ta zauna lokaci daya tana fadin" Sannu Hafsat." Da gayya ta yi mata sannu domin ta ji kunya, idan ita ba za ta gaisheta ba, ita bari ta watsa mata kunyar gabadaya. Amma yarinyar nan ba ta ji kunya ba sai ma ɗagowa da ta yi, ta sakar ma matw wani kallo kafin ta amsa da lafiya kawai ta cigaba da latsa wayarta. Ta ji wani iri amma sai ta danne ta numfasa ta ce "Bilkisu da Hafsat me ya sa ba kwa cin abincin da na saka ake dafa mana gabadaya?" Ta tambaye su tana kallonsu. "Muna ci mana." Bilkisu ta amsa amma ban da Hafsat.. "Ba kwa ci, sai dai ku saka Jummai ta yi muku naku daban. Kunsan kuma ba yadda za'a yi a dora tukunyar abinci a gidan nan a hanaku. Sai mu yi d'aku ku k'i ci, ku saka a dafa muku fiye da cikinku, abincin yana yin yawa da safe sai an zubar me ya sa haka?" Bilkisu ta yi shuru domin ita ko tana son ci sai Hafsy ta hana ta. Hafcy kuma ko nuna ma tana jin su ba ta yi ba. "Ba zan takura muku sai kun ci abincin da na saka aka dafa ba. Amma ina so ku sani in har ba za ku ci ba, ku fada min, sai na fad'a mata ta daina sanwa daku idan jummai ko charity kuke son su dinga dafa muku ya wadatar ba sai an yi barna da yawa ba." Suka yi shuru ba wacce ta yi magana. "Ina fatan kun fahimta? "E Anty" Bilkisu ta fada kafin ta cigaba da fadin" Ki yi hakuri Anty." Bilki ta mike tana fadin" ba komai ni dama saboda b'arnan abincin ne ya sa na yi magana." Har ta kama hanyar fita ta ji Hafcy na magana cikin gunguni "Ai ko mun yi b'arnar Daddynmu ke kawowa ba wani ba " Ta fada tana hararan ta gefen ido. Bilki ta juyo tana kallonta da kamar za ta ce mata wani abu sai kuma ta kasa hadiyewa ta ce" Haka ne shi yake kawo wa." Daga haka ta fice daga dakin nasu, ta koma nata ta dade a gefen gado tana fama da zafin zuciya, yarinya karama take yi mata rashin kunya amma ta kasa daukan mataki. Ta dade zaune tana tunanin kafin kiran sallar mangariba ya tashe ta, ta shiga tiolet ta dauro alwala amma a ranta ta kud'iri niyyar ko mai za su yi ba zata sake yi musu magana ba, kamar yadda suka fada gidan ubansu ne, su yi yadda suka ga dama. Tun daga ranar ta kawo ido ta sanya musu, duk sun manta da tara sun da mahaifinsu ya yi farkon dawowarsu gidan a gaban Bilki ya ce su yi mata biyayya su darajata idan har suka yi mata rashin da'a shi suka raina ba ita ba, amma duk Hafcy ta manta da wannan karatun, shi kuma baya yini a gidan bai san abin da yake faruwa ba, da daddare yana tare da yaran sai sun kwanta sannan yake zuwa wajen Bilki. Ita kuwa tana zaune tana zaman jiransa wani lokacin ma barcinta take yi tunda ta fara fahimtar Kakar hak'urin da zata yi a nasa gidan. Wani dare ya shigo d'akinta ya tarar tana ninke sallaya da alama shafa'i da wuturi ta idar. Ta cire ƙaton hijab dinta na gunis collection . Sanye take cikin rigar barci ta garari fara kal wacce umm asala mazauniyar Eggypt ke kawo su Nigeria.... Cikinta ya fara turowa ta sake budewa ta kasa. K'amshinta na mussaman na tashi ko ya ya ta motsa. Shima ya yi wanka sanye yake cikin hadaddiyar jallabiya ruwan madara. Kamshinsa ya cika mata kofofin hanci. Ya matsa daf da ita ya rungume ta a hankali ya ce "Maigado ki rika zama tare da yaran nan da haka ne za su shaku da ke.". Ba ta ce masa komai ba illa to domin ita bata son ta fara magana ahalin yanzu, ga cikin jikinta ba ya son hayaniya yanzu abu kadan zai bata mata rai, ta fara jin za ta yi kuka, sannan yana saka ta hassala nan da nan amma duk da haka tana ta daurewa. Tunda ya yi mata magana ta ke dan fitowa suna zaman hiran amma ba mai sako hira da ita to gwara ma Bilkisu, amma Hafcy yi take tamkar bata san da ita a wajen ba, da ubanta kawai take hira. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Har suka kammala ayyukan Bilki na zuba idon ganin Aysha ta fito ta tanka ko ta ce sai an yi mata girkin dole. Sai ta ji shiru. Ta dinga ganin ashe ma rashin motsa kwanjine ya sanya suke yi mata cin kashi. K'arfe shida sun kammala komai an shirya abinci abinci a saman tsakiya inda suke shan ruwa gabad'aya. Bilki ta fito a wanka ke nan ta ji ana bude mass get. Gabadaya gida ya kaure da k'amshin spice's din girki na Amreesh spicy Kano.... Ga kuma k'amshin tuararukan Dubai masu tsada na tashi sannu a hankali cikin burner. A takaice dai gidan tamkar aljannar duniya ne. A takaice ta shirya cikin bubu abaya ta elsisi Mai zuwa da mayafinta wacce itama dai a wajen mazauniyar Eggypt din nan uwar Yan biyu ta yi order din ta Umm Asalan da asala mai rigunan kasaitaaccun Mata..... Ta saka hularta da ta ce da rigar. Ta ajiye mayafin akan gado. Ta dauki sallayar tare da mayafin ta sauka zuwa inda zasu sha ruwa don da shi da ita da yaran Syke Shan ruwa gabad'aya tunda aka fara azumi yaunkuma na biyar zasu kai. Abin jin dad'i Shi yake jansu sallah. Sallar Isha da asham kuwa a can k'asa suke yi ya jasu tare da dukkan ma'aikatan gidan maza da Mata. Zamanta da shi ta gane ba shi da girman kai ko kad'an sannan Yana da kyakkwar mu'amala da na kasa da Shi. Rashin faraarsa ba ya hana shi kirki da saukaka mu'amala da jama'a. Kawai inda take ganin rauninsa ta fahimci tamkar yana cikin mutane masu tsananin son ya'ya. Amma sai bata wani ganin laifi tunda bata ga wani abu da zaisa ta tuhume shi akan son ya yi yawa ba. Dama ba yadda za'a yi ka haifo d'a ace baka sonsa. Ta sauko daga samanta, shi kuma ya hawo dan haka suka hadu a tsakiya. Ya cire hularsa ya sara mata da taushin murya ya ce "Ranki ya dad'e sarauniyar shaiba ya ibada?" Ta murmusa tare da mika masa hannunta na dama ta ce "Alhamdulillahi, ya aiki dafatan dai yau baka ji k'ishin ruwa sosai ba?". Ya sumbaci hannun sannan ya ja ta zuwa tafkeken falon da suke zama. A ciki ya tarar da yaran har kananun. Ganinsu bai saka ya sakar mata hannu ba sai da ya kaita kujera ta zauna. Ya dunkule hannunsa na dama alamar jinjina ya ce "Sannu da k'ok'ari Maigado gabad'aya k'amshin girkinki na daban ne wani irin k'amshi yake bayarwa da ba'a jinsa a ko ina sai a girkinki." Dad'i ya ratsata don kuwa tana matuƙar son ta ji yana yabon ta, sannan shi a gaban kowa yaba mata yake yi ba ruwansa da yara Sai da ya ga ta zauna sosai sannan ya juya ga yaran ya karbi gaisuwarsu. Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Ku bani mintina goma na watsa ruwa". A ranta kuma tasan spice's din Amreesh babu na biyunsu wajen k'amshi da fitarwa girki dandano na mussaman. Aysha na kishigide wayarta na hannunta ta gefen Ido kuwa Bilki take kallo. Haka kawai ta ji wani abu ya mintsine ta ganin yadda ta yi kyau ta haska maroon din rigar da take jikinta. Sannan cikin jikinta ya fara turowa ana ganinsa duk kuwa da ya bi jikinta. Sosia ta ji ciwon da ya ce wai k'amshin girkinta baya jinsa a ko ina sai a gunta. Wato har na mominsu kenan? Ta yi k'aramin tsaki tabbas ba zasu shirya da Anti Maigado ba mussaman da dazu ta nuna mata iyakarta a gidan ubanta. Bari a sha ruwa itama ta nuna mata tasirin y'a a wajen uba. Mintina shabiyar ya fito sanye da jallabiya coffee k'amshinsa ya baibaiye su tun kafin ya shigo. Yana shigowa ana kirian sallah. Suka yi addu'ar buda baki sannan suka hau cin dabino da inibi ga kuma kankana da ruwan roba da ya yi raba don sanyi. Suka dan huta sannan ya jasu sallah. Bayan sun idar suka fara cin soyayyar doya da kwai da kuma ferfesun kaji sai kunun gyada, da shayi. Ga kuma su samosa a gefe. Sai kuma farrar shinkafa aka dafa da kayan lambu irinsu kara's, pea's, da koren wake da za a ci da soyayyiyar miyar kaji. Ga hadin salad mai kyau. Ga kunun aya mai dad'in gaske. Duk abin da kake son ci shi zaka zuba da kanka. K'ananun ne ake zuba musu zabin da suke so. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Sannan har yanzu girkinsu suke sawa a yi musu. Basu fasa yin yadda suke so a kicin ba. Bilki ta rasa yadda zata bullowa lamarin sai kawai ta ce a daina girki da su, ta rika dafa iya su da su Amal su kuma Jummai ta dinga dafa musu abinda suke so, hakan kuma da aka yi shike nan Bilki ta samu zaman lafiya, ba ta shiga harkansu suma ba sa shiga tata, tana zuwa wajen aikinta suma suna zuwa makarantatsu tunda dama hutun da Hafcy ta samu ba mai yawa ba ne . Bilkisu ma a sati biyu da suka shud'e ta fara zuwa makarantarsu Hafcy ta samu gurbin karatu zata karanta pharmacy, dan haka sai dare suke haduwa, idan kuma sun hadun Bilkisu za ta gaishe ta amma Hafcy matsewa take yi tamkar bata ganta ba. Al'amarin Hafcy na matuƙar ciwa Bilki tuwo a kwarya, kawai hak'uri take yi, don ba zai yiwu ta biyewa yarinya k'ank'anuwa ba. Amma dai tabbas ta gama tabbatarwa jarabawar aurenta da Asad yaransa ne don sune zasu hana ta zaman lafiya. Bilki bata san ce wa Hafcy lafiya ba ce sai da Aysha ta kamalla kwas dinta ta dawo gidan anan ne ta tabbatar da Hafcy ba ta yi mata komai ba. Ta dauka Aysha da take babba za ta fi su hankali mussaman yadda idan sun je hutu Funtua tana makale da ita tunda Abida bata kula yara. Tundaa ta dawo gidan komai ya fara sauyawa, kai tsaye ba ta yi wa Bilki rashin kunya amma ta zuge yaran har da Bilkisu mai dama dama yanzu ta kasa gane kanta. Su Amal kuwa tana dawowa duk ta kwashe kayansu ta mayar dakinta ta raba su da Farha, duk Billki ba ta yi magana ba amma lamarin ya ba ta mamaki sannan ya daure mata kai. Kuma ta koma ita ke yiwaa yaran komai. Alti ke yi musu abin kari da wanda za su tafi da shi amma tana dawowa ta ba da Umarnin jummaia ce za ta dinga yi. Alti ta yi mata magana ta ce "Mahma kada ki bari ta raba su Amal da Farha. A sanyaye ta ce "kyale su kawai ai su gidan ubansu ne ita kuwa fa? Ubanta ya yi nisa nice nake zaman uwa da uba a gare ta dan haka ki dinga yi mata kawai". Ta kamalla maganar da kuka don gabad'aya ta fara gajiya. Ta koma kawai ta zama yar kallo shi kuma megidan bai san wainar da ake toyawa ba. Duk tsiyar Hafcy bata taba nunawa akan Farha ba amma tunda Aysha ta zo ta tisa mata yarinyar da hantara da zare ido da dukkan alamu Aysha bata son Abida duk yadda aka yi. Idan ita basa sonta to Farha fa? Kuma idan yaran basu san ba ita ta haifi Farha ba, to Aysha ta san Abida ce ta haife ta. Abida kuwa uwarsu d'aya ubansu daya da ubansu. Amna gabad'aya ta hana su Amal kulata daga Bilki har d'iyarta Aysha ta takurasu matuk'a da gaskeq . Tun Bilki na mamakin lamarin har ta fahimci Aysha dai kishi take yi da ita mai tsananin gaske. Sannan dangin babarsu sun fad'a mata rabon auren Bilki ne ya kashe uwarsu. Bayan haka ya k'i auren Laura wacce ita yafi cancanta ya aura don kanwar Momi ce da ta girma a hannunta ba zata taba cutar da su ba. Sannan ba zasu zama bak'i a gidan ubansu ba. Da haka suka sake cusa mata kin Bilki tare da kud'irewa sai sun matsa mata ta bar musu gidan. Antinsu ta shigo tunda wata kusar ai tafi wata. Da yake da iliminta cikin ruwan sanyi ta baza makaman yaƙin musgunawa Bilki. Ana cikin haka aka shiga watan azumin ramadan. To da wuri megidan yake dawowa in dai yana gari ya yi bude baki tare da iyalinsa da haka ya saba tun filazal. Ganin haka da Bilki ta yi ya sanya karbar ragamar girkin buda baki sai dai a taya ta don kama wasu ayyuakan don kwadayin samun ladan ciyar da mai azumi. Don haka tun azahar suke shiga kicin ake Fara hidimar abin shan ruwa tunda ba iya cikinsu suke yi ba har da ma'aikatan gidan. Amma ga mamakinta sai Aysha ta saka Charity da Jummai yin wani girke-girken na daban. Karon farko da Bilki ta taka birki akan ba za'a yi wani girki ba matuƙar tana kicin din. Sannan abin da aka yi shi kowa zai ci. Aysha ce ta ce "Na yi fa Anty". Jummai ta fadaa dan tsorace. Kaitsaye Bilki ta ce "Ki ce mata na hana ina aiki a kicin din". [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Cikin kyawawan plates din ralzaplace suke cin abincin.08109544470 Cikin nutsuwa suke ci a hankali ya fahimci Aysha da Hafcy Basu zuba komai ba. Tun kankanar da suka sha da ruwa basu taɓa komai ba. Ya ajiye cokalin hannunsa. Da kulawa ya ce "Aysha, Hafcy bakwa cin abinci what's wrong?" Suka yi shiru nan da nan idon Aysha ya cika da k'walla ta zuba masa ido take ya gano kuka take yi sannan bata cikin sukuni. Tausayinta ya kama shi yasan mominsu ta tuna tunda sun saba da ita suke zama irin haka, bana kuma ba da uwarsu ba dole hankalinta ya tashi. Atausashe ya ce "Menene?" Da rawar murya ta ce "Dady kasan bama cin doya da aka soya da kwai ni da Hafcy, sannan ni bana cin kaza. *Dingishin KWAD'O* *Book4* PAGE 1 *Na* *Surayya Dee* *Dan Allah masoyan rubutuna ku daure Ki cicciba mini labarin nan ta hanyar yi mini likes a YouTube.* *Gasa ce da yawan likes da za'a fitar da gwarzon labari*. *A daure a mini like an saki episode 1-3 wadanda suka yi Allah ya saka musu da ALHERI, waɗanda Basu yi, a daure a yi, Ubangiji ya taimakemu gabad'aya.* Kuma duk abincin akwai kaza a ciki." Da sauri ya ce "Hakane to ai da kin fad'a mata tunda bata sa ni ba ". A nutse kuma a hankali ta ce"Na saka Charity ta yi an ce ba zata shiga Cigaba kicin ba, na tura jummai tunda ita mai sallace an ce ba zata yi ba, dole abin da aka girka shi zan ci, alhalin mu ba haka muka saba ba." Ta fad'a tana goge hawaye da tissue hannunta. Ya juya ga Bilki ya ce "Maigado ki dinga bari ana yi musu duk abin da suke so. Yanzu charity da Jummai ai kusan zamansu suke yi tunda sun san me suke so. Mun Saba rayuwa kowa yana cin abin da yake so ne ba takura ". Mamaki ya hana Bilki magana. Ya tashi daga kusa da ita ya koma kusa da Aysha da Hafcy da suka koma gefe. Ya dinga rarrashi tamkar yara k'ananun akan su yi hak'uri su ci snacks kafin charity ta yi musu abin da suke son ci kada yunwa ta illata su. Idonsa ya yi ja tamkar ya taya su kukan. Bilki ta sandare tana kallonsu gabad'aya ma ta rasa me zata ce. Ya danna k'ira shashin ma'aikatan. Charity din ce ta dauka. Cikin harshen turanci ya ce "Ta zo yanzun nan". Mintina uku ta iso ta gurfana gabansa. Ya ce "Me zaku ci?" Hafcy ta ce "Fried yam da onion soup ma is ok. Tunda yunwa muke ji. Aysha da ƙyar ta ce "Ki yi mana dambun kuskus da zamu ci anjima". Ta amsa a ladabce ta mik'e. Abincin da bai ci ba kenan don yana kusa da su har aka kawo musu farar doya soyayya da miyar albasa. Daidai lokacin kuma an fara k'iran sallar isha. Amal da Noor suna ta kallonsu tare da Farha. Bilki ta yi sukuri tana kallon uba da ya'yansa yana ta yi musu sannun jiran da suka yi don ga ni yake yi yunwa ta ci ta cinye su. Bilkisu junior kam ta ci abinda da Bilkin ta girka babu musu ko inkari ita bata da matsala kawai yayyen nata ne suke tursasata akan ta bijirewa Bilki. PAGE 2 Bayan sun idar da salla sundawo Aysha ta ce "Dady na san kana son kuskus na zubo maka kadan tunda dazu baka wani ci abinci ba". Zuciyarsa d'aya ya ce "Zubo mini Aysha". Ta tashi ta zubo masa daidai cikinsa. Ya ce kawo wani spoon din zan je mu ci da Antinku a ido ma ya yi kyau." "Kai Dady ka zauna ka ci anan idan zaka tafi sai na zubo maka nata. Ita ai ta nadi doyar nan ba kad'an ba". Ya zauna kuwa ya cinye suna hira tana babshi labarin Enugu da mutanen garin da irin banbancin da ta gani na aladun inyamurai da kuma na yarabawa da ta ga ni a Lagos. Har shadayan dare kafin ya yi musu sallama ya haye saman Bilki. Ya tarar da ita tana kwance ta lullube Rabin jikinta da bargo idanuwanta a lumshe. Ya shiga bayi ya sake wanka ya yi brush sannan ya kashe fitilar dakin Ya laluba da taimakon hasken da yake shigowa ta windo ya Isa gadon ya kwanta a bayanta ya saka hannunsa ya rungume ta sosai. Bata motsa ba, dan kuwa kuka take yi na sharb'e. Ta rasa ta yadda zata bude baki ta yi masa k'orafi akan ya'yansa. Sannan shi kansa yana yin abubuwan da suke musgunawa ne a gareta. Sai ya kai kusan shabiyun dare tare da su a falo da sunan hira. Sannan k'aida da su zai karya ko da ace ba zai fita da wuri ba to Duk abin da yaran suke son karyawa da shi Idan an yi musu Sai su yi masa waya wai suna jiransa Su karya haka zai katse barcin ya fita. Sai idan zata karya sai ya zauna da ita suna hira yana bata a baki sannan ya dan taba kad'an. Ta taba yi masa maganar da ita ya kamata ya dinga karyawa fa. A tausashe ya bata amsa da fad'in "Ki yi hak'uri ni so nake ma ki dinga shiga cikinmu muna karyawar da abin da suke so din, tausayinsu nake ji mun riga mun saba tare muke karyawa, so ina matuƙar jin tsoron kada damuwar rashin mamamnsu ta yi musu yawa. Shiyasa nake yi musu komai kada su dinga ganin dan sun rasa uwa sun rasa gata." Tunda ya fada mata haka ta debi ido ta zuba musu. Yanzu kuma me zata ce masa?" Ya gama lalubeta ta yi bakam. Ya hura mata iska a kunne tare da murza kirjinta nan da nan jikinta ya amsa k'iran nasa. Ta kasa cigaba da share shi. A kunne ya rada mata kina iya yin barci ba a k'irjina ba ne? Nasan idonki biyu. Babyna ba zai bari ki yi barci ba tare da na zo na tabo shi na zuba masa ruwan dumi da zai kara masa kuzari ba". Haka ya dinga rura mata jiki har sai da ta sakar masa jiki yadda yake so, ya cudata sosai sannan suka yi wanka suka kwanta barci mai dad'i ya sure ta, ta manta takaicin yara. Tun ranar bata sake hana ayi musu girki ba. Don cewa ya yi a dinga yi musu nasu a kicin din samansu. An kai azumi goma suna buda Baki Aysha ta ce "Dady Anty Laura zata zo mana hutu ". Ba tare da tunanin komai ba ya ce "Ah ta zo mana itama ai nan gidansu ne". Nan da nan zuciyar Bilki ta motsa. Lauran da ake ta yi masa tallan ta aura ne za'a turo fa gidan ta zauna?. Ta hadiye tunda maigidan aka faɗawa shi kuma ya bada damar ta zo har yana fad'in gidansu ne. Ta jijjiga kai wataƙila dai hak'urin da take ta yi da shi da ya'yansa ya kusa k'arewa dan kuwa idan har Laura ta ce zata yi mata shakiyancin da yaran suke yi mata lallai zai sha mamakinta tunda ya amince da zuwanta ba tare da ya shawarce ta ko tunanin komai ba. Laura ba ta zo gidan ba sai ranar azumi na shaa bakwai. Ta kammala digiinta a B.u.k Tunda Laura ta dawo gidan sai aka canja salo don kuwa daga ita har Aysha yamma na yi suke yin wanka su kece da kwalliya yadda suka ga Bilki na yi. Sannan a gabansa mutuntunta suke yi suna fad'in "anty sannu da shan ruwa, sannu da aiki." Gabadaya Laura ta sake koyawa Aysha da Hafcy dabarun yin kisan mummuke. Ta yadda idan ma ta kai ƙararsu za a ga itace bata da hakuri. Idan ba ya gidan kuwa mp ce dasu su mai tsada mai fitar da sauti mai k'arfi yini suke yi suna kunna wakokin gwanja na habaici kalakala su kure volume duk tazarar samanta da nasu sai ta jiyo. Abubuwan suka fara yi mata tsauri. Mafi tayar mata da hankali cin zalin Farha da suke yi, sannan sun hana su Noor kulata. Idan yana nan bai ganta a gunsu ba ya ce ta je wajensu sannan ya yiwa Bilki fad'a tana makale da yarinya ba zata barta ta shiga wajen yara ba. Ta kasa bude baki ta ce masa zalinta suke ci tare da zare mata ido da razanata. Ranar asabar ya je Ilorin, kwana d'aya zai dawo. Da daddaren ranar tana kan sallayarta ta kalli agogon bango ya nuna mata k'arfe uku da rabi na dare. Ta sake kai ganin ta ga gadonta Farha ke barci cikin nutsuwa. Zuciyarta babu dad'i amma ta dukufa addu'a don kuwa al'amarin yaran kullum kara tsananta yake yi. Washegari lahadi k'arfe d'aya na rana da y'an mintina Farha ta shigo d'akinta a guje sannan a matuƙar tsorace ta dumfare ta, ta makale a bayanta jikinta na b'ari. "Wa ya biyo ki?" Kafin ta bude baki ta yi mata magana Hafcy ta shigo d'akin a matuƙar fusace. Ba jin nauyi ko kunya ta finciko ta a bayan Bilki ta faffala mata mari har guda biyu masu zafin gaske. Wani irin fishin da Bilki take yawan addu'ar Allah ya tsare ta da shi ya taso mata, hak'urinta ya k'wace. Ta yunk'ura ta mike daidai lokacin Hafcy ta juya da nufin fita daga dakin yayin da Farha take daderen kuka rike da fuskarta. Da azama Bilki ta finciko ta da k'arfin gaske ta dawo da baya ta fadi kan hannunta. Bilki bata lura da hakan ba ta yi maza ta rufe kofar d'akinta ta cire key din dakin ta jefa kan gado. Cable din jikin standing fan ta ciro irin wacce ake cajin ta. Ba tunanin komai ta isa ta dinga labtawa Hafcy ta koina babu tausayi ko kad'an. Ihun Hafcy ya tsananta Aysha da Laura har ma da Alti suka dinga bugun k'ofar amma bata k'yale ta ba sai da ta yi mata ligi ligi. Bayan ta jiyo kukan Alti tana fad'in kada ta bari zuciyarta ta rinjaye ta, ta yi aikin da zai zama Fargar Jaji. Ta wurgar da wayar gefe ta shiga bayi ta wanko idonta don kuwa hawaye ke zubar mata tamkar famfo. Ta dauki key ta bude k'ofar d'akin, gabad'aya suka shigo d'akin da gaggawa suka nufi Hafcy da take kwance tana kukan neman agaji don kuwa sosai jikinta ya karbi kebra. Laura da ta ga jikin Hafcy ya yi rudu rudu wani gefen har jini ya kwanta. Ta ce "Kan uban nan wanne irin duka ne haka tamkar an samu jaka?" Bilki tana tsaye bata ce uffan ba. Aysha kuwa ta saki ashariya tare da fad'in "Ai kuwa ko sama da k'asa zasu hade ba zan yarda ba, zan ga inda aka bawa wata banza lasisin cin zarafin d'anadam haka siddan. Daga kaidojojin addini har na constitution ". Bata Ankara ba Bilki ta d'auki cable din ta shimfida mata a gadon baya da iyakacin k'arfinta. Tsananin azabar da ta ratsa ta ya sanya ta girba a guje ta fice don kuwa gabad'aya ta kidime. Laura ta yi wuri wuri a tsorace ta ce "Anty lafiya kuwa?" A sanyaye Bilki ta ce ", Lafiyar ce ta kawo haka. Ki kama hanya ki fice mini a d'aki. Don idan kika yi kuskuren zagina a dakin nan Billahillazi ba za ki sake tako k'afarki da sunan kwana gidan nan ba. Ba zan doke ki ba, amma za ki ga yadda zan saka a yi miki korar kare tunda dai ke ba dolen gidan ba ce. Su kuma kada su fasa taɓa ni, ba a haifi wacce zata shigo dakina ta yi mini cin mutunci na bar ta salin alin ba. Komai zasu yi mini a waje zan yi hak'uri don nasan komai lokacine, wata rana ba zasu yi ba, dan haka zan yi hak'uri har komai ya wuce, amma ba zan yi hak'uri idan aka tako har cikin d'akina aka taɓa ni ba tabbas. Sannan zan gargade Ki da babbar murya ki bi a sannu don ke ma ina da kalar na ki hukuncin, akan idonki kin ga yadda na zane su ko? To ki taka a hankali " . Ta kasa magana ta sunkuya ta ciccibi Hafcy ta mike tana rusar matsanancin kuka rik'e kuma da hannun da ta fadi a kansa. Awa d'aya a tsakani Haj Surayya ta iso wacce kanwa ce ga marigayiya Rukayya, yayar Laura. Ta girmi Bilki sosia don kuwa sa'arsu Yaya Salaha ce. Hamshakiyar mace fara sol mai jiki, ma'aikaciya a hukumar sufuri reshen Abuja. Tana zaune da mijinta da wajen aikinsu d'aya da yaranta. Bilki Sai labarin Alti ta bata na cewa ta tafi da yaran duka gidanta. Hankalin Alti ya tashi matuƙa don kuwa ta fahimci hannun Hafcy ya samu matsala da gaske sannan tafiyar da aka yi da su, abin da zai biyo baya ba mai sauki ba ne. Yayin da Bilki ko a jikinta ta riga da ta saba da ganin tashin hankali iri iri, tana jiran ya dawo su fad'a masa ya sauwake mata. Don kuwa ba zata bari su manna mata ciwon zuciya ba. Yayin da Alti ta yi jarumtar rufe ta da fad'a tamkar ba uwargijiyarta ba. Fad'i take yi "akan me za ki biyesu. Ai kin ringa kin tsere musu ko suna so ko basa so sun kin yi musu nisa tunda kina ganin babansu a tube, da uwarsu ta nan itace abokiyar burminki, idan sun mutunta ki, ki mutuntunta uwarsu, idan sun fitine ki, ki fitini iyayensu. Amma yanzu tunda babu ita ai dole ki yi hak'uri mai yawa mussaman ma da aka yi sa'a y'ay'a mata ne nan ba da jimawa ba, ko wacce tana d'akinta itama tana fama da matsalar gidan aurenta. Amma dan rashin hak'urin da yanzu kika koyo shi, ki kama masa yarinya, ki yi mata mummunan duka irin haka ai bai yi ba. Ai ubansu za ki duba, idan karaya ta samu a hannun ya ya zamu yi ne?" A sanyaye Bilki ta ce "Sai ya sallame ni mana. " Alti ta jijjiga kai tana mamakin yadda Bilki ta zama mai taurin zuciya. Da yammaci sosai ya iso gidan. Ba wata alama na ya san gidan a rikice yake. Ya fito a wanka yana tsane jikinsa da tawul. Ya ce "Farha kawai na ga ni, ina sauran yaran?". Murya ba amo ta ce "Basa nan k'anwar mominsu ta zo sun bita" Ya rik'e rigar ya fasa sawa ya ce "Don me ba ki saka sun fad'a mini ba, ko kuma ke mai ya hana ki fad'a mini a waya kafin su tafi?" Ta yi shiru don bata san me zata ce ba. Ya numfasa ya ce "To me yasa basu tafi da Farha ba, ban hana ki dinga cire ta a cikinsu ba?" Idonta ya ciko ta yi k'asa da kanta, ta kasa cewa komai. Ya zura rigarsa ya fesa turare ya nufi hanyar barin d'akin. Har ya bude k'ofar sai ya rufe ya dawo. Da tarin bacin rai ya ce "Ba kya yi mini abinda ya kamata fa Bilkisu! Gabad'aya kin nade hannunki kin bar mini yara, kin k'i sakin jikinki da su, tunda ba sona kike yi ba". Kanta na k'asa hawaye ya k'wace mata. Yayin da shi kuma ya fice ya barta. Ranar dai haka suka sha ruwa daga shi, sai ita da Farha wanda ko kad'an babu armashi don ba wanda ya ci abincin kirki a tsakaninsu. Sun idar da sallar isha kenan wayar Haj Surayya ta shigo wayarsa. Ya amsa ta shaida masa zasu zo yanzu da yara amma tana son ganinsa akwai babbar matsalar da zasu tattauna. Ya amsa mata da fad'in babu damuwa yana gidan zai jirasu. Tara daidai suka iso gidan, ita da yaran. Hannun Hafcy an nad'e shi da bandage mai yawa. Ga zazzabi ya rufe ta, haka nan ana iya ganin wasu daga shatin kebran da ta sha. Aysha kuwa kuka take yi sosai idanuwanta sun yi luhu luhu. Ganinsu a haka ya yi matuk'ar tayar masa da hankali yayin da zuciyar Bilki take yin lugude sosai. Ba tsoron ya sake ta take yi ba, kawai kada ta wulakanta ta a gabansu ne zulliminta. Ya amsa gaisuwar Haj surayya hankalinsa na kan Hafcy. Ya kasa hakuri ya tashi ya isa inda take ya ji jikinta zafi ainun sannan uban bandejin da yake nade a hannunta ya dungunzuma masa lissafi. A rikice ya ce "Menene, me ya same ki?" Ta kasa magana illah hawaye da yake sintiri a idanuwanta. Ya juya ga Aysha da take kukan sharb'e yana tambayar me ya same su. Duk sun kasa magana. Yayin da Bilkisu junior da su Amal suka yi tsamo tsamo. Ya kalli Haj Surayya ya ce ". Wai menene, fad'uwa suka yi ko kuwa?" Rai a b'ace a kuma takaice ta ce "Dukan rashin imani aka yi musu babu gaira babu sabar". A zabure ya ce "Duka! Wa ya dake su irin haka?" Da kaudi Laura ta ce ", Anty Maigado ce". Mamaki ya yi matuk'ar kama shi. Ya kalli inda Bilki take zaune ya zuba mata ido tare da son gane da gaske ita ce ta yi hakan ko kuwa sharri za'a k'ulla mata. Take ya gano ita din ce don babu alamun razani ko mamakin da ta shiga akan jawabin Laura. Falon ya yi tsit don kuwa ya rasa ta yadda zai bude baki ya yi magana. Amma ransa ya rub'anya baci. Jin ya yi shiru ya sanya Haj Surayya gyara zama ta ce "Abin da ya sanya na zo takanas shine na ji ba'asin da zata kama manyan y'anmata ta jibga son ranta, ko ita ta haifesu ai ba zata yi musu hakan bare ba d'aya. Akan me ba za'a k'yalesu su ji da azabar rashin mahaifiyarsu ba? Ban da rabon haihuwa mai kauda wani! Ya za'a yi ace wata mace ce a cikin wannan gidan ba wacce aka yi gwagwarmayar rayuwa da ita ba? Sannan dan rashin adalci sai a mayar da yara marasa galihu a gidan ubansu. To Wallahi ba zamu lamunci duka ba, ko wannan din ma ba zai tafi a banza ba." Baban Bilkisu ya kaurara murya ya ce "Surayya ina ganin ki bar maganar nan a hannuna tunda ina nan nine yafi cancantar na yi hukunci a gidana. Ita matatace su kuma ya'yana ne, dukkansu suna k'arkashin ikona ne dan haka ki bar maganar hannuna zan dauki matakin da ya dace ". Ta hassala don kuwa sai ta ga fishinsa ya ragu sosai. A hassale ta ce "Ni ce nake zaman uwarsu dan haka sai ta fad'a mini dalilin da zata yi musu wannan cin zarafin, ai tasan zafin haihuwa, idan aka kama nata ya'yan aka yi musu irin wannan izayar ai ba yarda zata yi ba". Cikin nutsuwa Bilki ta zuba mata idanuwanta duka biyun ta ce "Dalilin da ya sanya kika zo don ki bi musu kadin zaluncin da na yi musu a matsayinki na k'anwar uwarsu, shine dalilin da ya sanya na gyara musu tarbiyar da ta yi musu k'aranci a matsayina na k'anwar ubansu, idan ban isa dukkansu a matsayin matar tsohonsu ba, to na dakesu ne a matsayina na goggonsu, kuma ina kan bakana ko yanzu suka biyo ni d'akina da nufin su ci mutuncina sai na yi musu dukan da zasu gigice don kuwa gidanmu gidan tarbiya ne dan haka ba zan bari su fita zakka a zuri'armu ba". Bak'inciki ya kama Surayya tamkar ta tashi ta rufe yar iskar yarinyar nan da duka. Yaushe Bilki ta yi bakine? Tana tuna ta da wata sumu sumu da ita. Ta kalli yadda ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi, uffan ya kasa ce mata duk da yadda ya dinga rawar jikin b'acin rai kafin ya ji itace ta duke su Ta ji tamkar ta ce mata a wanne zumuncin da kuka kai ubansa kotun ne za ki yi ƙafafar zumunta irin haka? Sai dai ta sa ni idan ta fadi hakan shi da ita abin zai juye dan marigayiya Rukayya ta taba fad'a mata har aka yi abin aka gama bai taba buda bakinsa ya fad'a mata ba, bai kuma bata fuskar da suka yi maganar rikicin Ladi farm shi da ita ba, har ta bar duniya. Kan dole ta shanye ta mike ta ce "Dadyn Aysha zan tafi tunda ka ce hukunci na hannunka to dan Allah a kiyaye don ba dan girmanka da mutuncinka ba sai dai a jimu da yarinyar nan a media ko kotu don keta haddin ya isa. Dubi hannun Hafcy. Ace an doki mutum har k'ashinsa ya tsage ai ansan da mugunta a ciki" Ya fesar da iskar b'acin rai ya ce "Allah ya sauwake. Ta yi masa sallama ta tafi Laura ta yi mata rakiya zuwa wajen motarta. Su Aysha suka yi sai da safe suna daga zaune. Ya kalli Bilkisu junior ya ce "Bilkisu ku je ku kwanta". Ta mike Amal da Noor suka bita. Ya kalli Aysha ya ce "Me kuka yi mata ta doke ku?". Aysha ta fashe da kukan bak'in ciki ta ya ya ma zai tambaye su, ita duk zatonta kawai zai yi fad'a na tashin hankali mussaman idan ya ga Hafcy da bandeji da shatin duka. Sai kawai ya tambayi me suka yi? Tabdi jam! Ya tsare gida sosia ya sake maimaita tambayarsa. Cikin nishin ciwo Hafcy ta ba shi labarin Farha ce ta yi mata rashin kunya shine ta bita d'akin Anty Maigado ta doke ta, shine itama ta rufe ta da duka" . Ya juya ga Aysha ya ce "Ke kuma menene sanadin na ki dukan?" Murya a dakushe ta ce"Hafcy na je ceto kada ta kashe ta, ban ankara ba kawai ta zabga minin bulalar da iya k'arfinta har wajen ya fashe ". Ya ce "Idan na fahimta dukkanku a cikin d'akinta ta doke ku, hakane?" Ya yi tambayar hankalinsa yana kan Aysha. Ta kasa amsawa. Ya gyara zama ya ce "Yaune rana ta k'arshe da wata a cikinku zata bi yara d'akin Maigado ta dokesu. Haka nan na haramta muku dukan yaran nan ba Farha kawai ba, dukkan yaran ban yarda ba. Ya zubawa Aysha ido ya ce "Maigado kanwata ce. Ko ban aurenta ba Antinku ce, aurenta da na yi kuma ya sake mayar da ita uwa ta sosai a wajenku. Ban ji dad'in dukan da ta yi muku ba mussaman na Hafcy amma tunda ta ce ta doke kune bisa hujjar ita din kanwata ce to magana ta wuce ba zan iya ce mata komai ba. Dole ku bita, ku girmamata don matata ce. Duk wacce kuma ta ce zata yi fito na fito da ita to tabbas da ni ta shirya yin tashin hankali ". Dukkansu kuka suke yi tare da hakkake ta doke su a bulus ba wani matakin da zai dauka. Gabad'aya sun gane tsoronta yake ji da gudun zuciyarta. Ba dan haka ba, ba yadda za'a yi a yi musu hakan ya kasa rikicewa ya dauki mummunan mataki. Laura ta yi sakare tana kallonsa tare da jinjina yadda bai d'auki al'amarin da zafi ba. Ta tuna ko momi idan ta daki wani ya dinga yi mata fad'a, yana rarrashin wanda aka doka. Amma yau an yiwa manyan ya'yansa dukan kawo wuka ya kasa motsa k'wanji. Ya kalli Bilki ya ce "A dafa mini shayi a hau mini sama da shi". Ta mike ta yi kicin dan yin abin da ya ce din, ta sa ni kuma sallamarta ya yi. Ta samu k'warin jiki a dalilin bai tsinkata ba, illah girma da ya siya mata. Ta yi imanin zasu shiga taitayinsu. Ta dafa shayin ta fito ta wuce su. Bayan ta tafi ya dinga yi musu nasiha da rarrashi tare kuma da jaddada musu dole su mutuntunta matarsa, bayan haka kuma wannan ne karon k'arshe da za'a taba jikinsu da sunan duka ya yi musu wannan alk'awarin. Sun dan ji dad'in rarrashin da ya yi musu sai dai sun so a gabanta ya yi musu wannan rarrashin tare da alak'awarin ta yi na farko ta yi na k'arshe bayan ya gama cin mutuncinta. Gabad'aya sun dauka zai sake ta tunda uwarsu ma baya kaunar ya ga ta daga musu hannu. Ya raka Hafcy d'akinta ya ce Laura ta kwana da ita. Sannan ya dawo falon ya kashe fitilu da AC ya hau saman Bilki tunda haka siddan ta k'i samansa. Ya same ta daure tawul ta fito daga wanka. Cikin jikinta ya turo sosai. Duk yadda ya tunzura da ita ganin cikinsa a jikinta sai ya tafi da kaso sittin na zafinta da ya ji. Band'aki ya zarce ya yi wanka, ya fito ya ga ta ajiye masa shayi a wajen da ya saba zama ya sha din. Ya saka jallabiya ya fesa body spray ya zauna ya fara shan shayin, yayin da ita tuni ta shirya ta haye gado ta lullube rabin jikinta da duvet. A nutse ya kammala ya kashe fitilar sannan ya tarar da ita. Ya kwanta a bayanta. Tsawon lokaci tana dakon ta ji hannunsa a jikinta amma shiru. Ta ji babu dad'i sai dai ta matse ta k'i yin ko da motsi. Can ta ji ya ce "Maigado". Cikin murya marar amo. "Na'am" ta furta a sanyaye. Ya ce "Zamu yi magana a matsayin yayanki ba mijinki ba". "To" ta fad'a a takaice. "Idan yaran nan sun yi ba daidai ba ki yi kokarin yi musu hukuncin da ba zasu ji ciwo ba. 'Ya'yana ai ya'yanki ne. Sannan bai kamata akan diyarki ki dokesu ba, na sa ni tunda suka zo cikin dakinki sun yi babban laifi, amma tunda akan Farha ne bai kamata ki dau irin wannan hukuncin ba don kuwa zan ji a raina, kin banbanta tsakanin ya'yana da ya'yanki ko na Ansari! Zuciyarta ta harba mussaman da ta ji b'acin ran da yake zuciyarsa ya bayyana har cikin muryarsa. Gabad'aya jikinta ya mutu. Tsawon lokaci bai ji ta ce komai ba. Ya numfasa ya ce "Yanzu kuma Zan yi magana a matsayin mijinki ba yayanki ba. Kada ki kuma dukansu duk abin da suka yi miki, ki fada mini, nine zan dauki mataki ba ke ba. Ina fatan yaune rana ta k'arshe da za ki d'agawa yaran nan hannu da sunan duka, bana so, bana so, kuma dokar nan har akan d'iyar gold din ta ki Farha! Daga haka ya juya mata baya tare da jan bargo. Ba'a jima ba ta ji saukar numfashinsa tabbacin ya yi barci, hakan da ta ga ni ya tabbatar mata fishi ya yi da ita. Don duk gajiyar da ya kwaso idan ya yi tafiya baya hana ya sauke mata gajiyar sannan ya rungume ta a k'irjinsa su yi barci. Amma yau ba d'aya. Gabad'aya ta ji wani irin al'amari mai kama da nadama ya mamaye ta. Mussaman yadda ya juya mata baya ya yi barcinsa ba tare da ya rungeme ta ba. Wannan abu ya yi mata ciwo. Ta yi tsam da ranta tana nazarin sauyin da ta samu cikin rayuwarta. Ta fara auna banbancin aurenta na farko da wanda take ciki yanzu. A yanzu bata siyan kayan abinci, bata siyan komai ma da kudinta ko da kuwa abin ita kad'ai ya shafa. Bandir bandir din kudi yake ajiye mata masu yawa. Store din gidan duk wani nau'in abinci akwai shii tamkar banza. Kifi da naman rago da na kaji kuwa har yan aikin gidan bai zame musu abin kwadayi ba, haka k'wai. Mafi dad'i da kwanciyar hankali. A yanzu gangar jikinta bata kewa, bata kwana da ciwon mara, bata kwana tana kukan son a marabci gangar jikinta. A yanzu ana yabon kwalliyarta ana yabon girkinta. Sannan a zahiri yana nuna mata tana da muhimmanci. Wadannan sune abubuwan da ta rasa a gidan aurenta na farko. Ta numfasa tana ayyana a can kishiya ce da ita ba wai ya'yan mijine kishiyoyin ba. A can ba yaron da zai mata sharri ko ya zage ta, haka nan a can ya'yanta sun girma suna sanya ta farinciki babu kuma mai zalintar. Haka nan a can ba a yi mata yarfe ko ba'a. Da ace a can ne ake suburbudurta yadda ake yi mata a nan da ta ce gwara can don duk yadda take hidimar rik'e gidan da aljihunta gara can da masifar ya'yan miji sangartattu irin wadannan. Ta nisa ta sake yin istigifari tare da yiwa Annabi salati ta daga dukkan hannayenta sama ta ce "Ubangiji ka taimake ni akan sha'anin yaran nan, Allah ka kawo mini mafita ka shirye su ka fahimtar da su ba ni da niyyar zaluntarsu, Ubangiji a duba hak'urin da na yi a baya a sassauta mini wannan matsalar. Allah ka mini zabin alheri ka ƙara mini hakuri da juriya. Hawaye ya k'wacewa mata. Ta rufe addu'a da yiwa iyayenta addu'ar samun Rahma. Tana jin k'addarar cikin jikinta ya saka ta auren uban marayu. *DAN ALLAH A MINI LIKES DIN LABARIN NAN A TASHAR LIMAMIN TSAKAR GIDA TA YOUTUBE EPISODE 1-10 KAD'AI ZA'A DANNA MINI DON LABARIN YA KAI GA MATAKIN NASARA*. PAGE 3 Da suka tashi sahur bata wani gane kansa ba. Haka dai ta gabatar tar masa da inibi da kankana hadi da ruwan roba. Ita kuma ta sha kunun gyada. Sassafe ya fice daga d'akinta. Tana zaune har wajen takwas akan sallayarta. Ga mamakinta sai jin tashin motarsa ta yi. Karon farko da ya yi mata hakan tunda ta zo gidansa. Ta jijjiga kai don kuwa a yadda yake son ya'yansa ta dauka ma hukuncin da zai dauka a kanta zai fi haka tsauri. Ta yi shiru tana nazarin yadda jiya ya ƙi yarda Surayya ta taka ta, sannan ya ki yarda ya nuna ta yi laifi a gaban yaran. Hakan ya fahimtar da ita son da yake yi mata ne ya hana shi kuzarin ci mata mutunci bare ya bari a ci mata. Don haka duk abin da zai yi yanzu ba zata ji ciwo ba, tunda ya daura zani a kasuwa. Bai dawo gidan ba sai daf da shan ruwa. Suna idar da salla Isha ta ga sun yi dakunansu, Farha ta matsa kusa da ita ta ce Mahmah ki ba ni kayana Dady ya ce "mu shirya za'a je shopping ". Zuciyarta ta tsinke wato fishin nasa har ya yi tsananin da ba zai mata magana ba?" Ta jijjiga kai tana fad'in tabdi jam a k'asan ranta. Ta yi tamkar ta ce Farha ba zata je ba, sai kuma ta tuna hakan ma laifine. Ta yunk'ura da ƙyar ta hau samanta Farha na biye da ita. Ta dauko mata doguwar rigarta mai kyau ta fesawa rigar turare. Ta watsa mata ruwa sannan ta shirya ta. Ta yi kyau sosai. Ta ce "Mahmah mai zan siyo miki?" Ta murmusa ta ce "Duk abin da kika zabo mini ina so" Ta fita da sauri tana fad'in "Sai mun dawo". Tana zaune a bakin gadonta da yake Farha bata rufo mata kofar d'akin ba. Ta ga wucewarsa zuwa samansa. Ba jimawa ta ga ya sauko ya nufi k'asan da yaran suke. Ta yunk'ura ta bi bayansa. Yana shiga falon itama tana shiga. Ta ga duk yaran sun shirya wani irin k'amshi ya cika falon tunda sun yi amfani da turaruka daban daban. Sosai suka yi kyau. Hafcy ba za'a ce hannunta da ciwo ba ta shirya ta yi fes da ita. Ta ji sha'awar haihuwar y'anmata ya kamata haka nan sai ta ji tausayin anty Rukayya ya dirar mata ta mutu bata ga auren zaratan y'anmatanta ba. Haka Allah ya so. Itama ta ji tausayin al'amarin ina ga ubansu? Da kanta ta fahimci dole ta canja taku akan yaran matuk'ar tana son ta samu kan Babansu. Ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa ya fito da ATM din asusun Zenith. Ya damkawa Hafcy tare da fad'in ki siya komai kike so don ke zasu raka. Ya juya ga Aysha ya bata wani ATM din ya ce "Dukkanku kowacce ta siyo abaya biyu da takalma biyu, sai turare da inner wears. Kada ku wuce hakan". Ta shagwabe fuska don kuwa wanda ya bata takaitattun kudade yake zubawa sabanin na hannun Hafcy na babban asusunsa ne da komai za'a siya ba zai girgiza ba. "Dady amma nima ya kamata ka jingina ni a wanccan ATM din gaskiya". Aysha ta fad'a cikin shagwaba. Ya rausayar da kai ya ce "Yau kam a hannun Hafcy yake ita kad'ai zata rik'e shi ta yi yadda take so. Ban da ita kuwa kowa ya yi hak'uri". Bilki na tsaye tana kallonsu, take ta fahimci ya yiwa Hafcy haka ne don ta huce daga dukan da ta sha. Suka rankaya suka tafi sai lokacin Laura ta fito itama sanye cikin tata Egyptian abaya ta maman asalan da asala. Da wani irin salo ta ce "Sai mun dawo Dady". Wani irin abu mai kama da kishi ya caki Bilki. Yayin da shi kuma ya ce "Ki kula da yaran fa Laura" . Bai zauna ba sai da ya ji an rufe gate tabbacin sun tafi. Ya zauna yana danna remote ya kamo TRT. Fitacciyar yar jarida Halima Umar Saleh tana bayanin k'alubalen tattalin arziki da nahiyar Africa take fuskanta. Sosai ya nutsu yake saurarra. Ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya. A hankali Bilki ta ja ƙafafuwanta ta isa kujerar da yake zaune mai cin mutum biyu ta zauna daf da shi. Ta saka hannunta ta rik'e nasa a hankali ta ce "Baban Bilkisu how far?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Fine". Ta sake jin wani iri da gaske dai fishi yake yi ta dukar masa y'ay'ansa. Ta sake daurewa ta ce "Ka tura yara su siyo abayas din zuwa sallar idi babu ni. To ni da wacce zan je?" Tana rufe baki ya ce "Ki shirya gobe James ya kai ki, Ki siyo". A sanyaye ta ce "James kuma? Ni kai zaka kai ni ". Ta fad'a tana turo baki irin na shagwaba. Ya girgiza kai ya ce "A a ina da ayyukan da zan yi kada ma ki saka rai". Ya fad'a idanuwansa na kan tafkekekiyar allon talabijin din da take girke ƙirar zamani. Ta ce "Tom shikenan Allah ya kaimu goben ". Bai amsa ba. Ta yunk'ura ta ce "Sai ka hawo". Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Tom". Ta hau samanta, kaitsaye wanka ta shiga ta fito ta tsane jikinta da tawul ta shafa tuararukanta kalakala masu dad'in gaske. Ta sanya wata irin rigar barci mai bayyana komai mai kyaun gaske. Ummu asalan da asala k'arshe ce wajen kawo mana abayoyi da rigunan barci masu tafiya da imanin mazaje. A ranta kuwa ayyanawa take yi duk tsiyarsa yau sai ya huce da fishin da yake yi da ita tun daren jiya. Ta zunduma hijabinta na gunis hijab... Ta shiga kicin dinta na saman nata ta hado masa shayinsa ta shigo masa da shi. Daga nan ta yi sallar isha. Ta Dade tana lazimi akan sallayarta. Sai wajen shadaya saura ta ji motsin dawowarsu. Don haka ta mik'e da hanzari ta sauka ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ya dago ya kalle ta don k'amshinta ya cika masa kofofin hancinsa. K'ananun ne suka fara shigowa kowa da ledarsa a hannunsa Amal da Noor da kuma Farha suka nufe ta suna nuna mata abin da suka siyo. Da murmushi ta duba na kowa a cikinsu tare da yaba musu sun iya zabe. Bilkisu ma ta nuna mata. Sababin Aysha da Hafcy da suka nunawa Babansu kawai. Hafcy siyayyar da ta yi tamkar da gayya don kuwa har da zoben gold ta siyo da hadaddun turaruka designers. Ban da dogayen riguna da takalman da ya ce. Ya kalli Laura da ta gefe ya ce "Ke ina na ki kayan?". Ta matsa kusa da shi ta bude ledar ta fito da su ya ga ni. Daga haka ya karbi ATM d'insa ya ce "Oya ku je ku kwanta don ku tashi qiyamul lail". Kowa ta debi kayanta cikin murna suka haye samansu. Suna fad'in "Mun gode Dady". Tuni an kammala labaran TRT. Don haka ya latsa remote ya kashe talabijin din a sanyaye ta ce "Mu ma muje mu kwanta kada mu makara". Bai ce komai ba, ya mike ya rigata tafiya, ta tsaya ya kashe komai sannan ta bishi. Ta tarar ya zauna ya fara shan shayin da ta ajiye masa. Yayin da ta shiga bayi ta yi fitsari ta fito kaitsaye ta haye gado. Sannu a hankali ya gama shan shayinsa ya shiga wanka, ya fito ya shirya, sannan ya kwanta. Mintina goma bata ji ya kai hannunsa ba, ta ji wani irin takaicinsa na kamata. Tsawon lokaci suna kwance kowa na tunanin zuci. Cikinta ya cure ya dunkule waje d'aya sannan sai harbin inda ya dunkule din yake yi sosai. Da azama ta kamo hannunsa na dama ta d'ora akan cikin daidai inda ya dunkule din yake bouncing da k'arfin gaske. Jin yadda cikinta yake yin lugude tamkar ana kokawa a ciki ya sanya jin tausayinta har cikin zuciyarsa ya ratsa shi. Da sauri ya matso gabadaya ya rungumeta ta baya yana fad'in sannu "Maigado, sannu kina jin zafin naushin nan ko?" A tausashe ta ce "Tun jiya fa har yanzu ban huta ba." Murya na rawa ya ce "To ko asibiti zan kai ki a duba a ga ni, kada ya taba miki kidney ko liver! Ya fad'a da firgici. A shagwabe ta ce "A a da zarar ya samu an zuba masa abin da yake so zai k'yale ni na huta". Murya na rawa ya ce "me yake so to?" Da wata irin murya ta ce "Baku gaisa shekaranjiya, da jiya ba, yau ma ya jika shiru" . Jikinsa na rawa ya hau kai mata kisses masu zafi daga nan kuma suka lula sama jannati. Tsawon lokaci suna dirzar juna kafin su samu nutsuwar da ta dace da su. Da kansa yake mamakin yadda ita bata gajiya da harkar, takaici ya kama shi na yada waninsa ne ya horar da ita da son wannan al'amarin. Matarsa ba mai yawan sha'awa ba ce, bata kuma da juriya a fannin amma Maigado kam ya lura sun yi matching da juna, mai juriya ce duk yadda zai gurje ta bata nuna ta gaji ko ya gundure ta kawai ruwa take feso masa da yake k'ara masa kuzari da gamsuwa. Cikin jikinta bai rage musu komai ba illah k'ara mata zalamarsa da ya yi. Ya dinga jin kishin yadda Sahal ya kwashe shekaru masu yawa yana kwasar ganima da babbar mace irin Bilki alhalin ita din matar manyan maza jarumai ne ba irinsa da yake a lankwashe ba. Tare suka yi wanka suka kwanta Yana shafa cikin da ya yi luf da alamu suka nuna ya yi barci. Murya ba amo ya ce "Maigado na ji ya baje daga nan". Ta taya shi d'ora nata hannun ta ce "Ya ji ruwan dumi, ya ji lafiyar babansa, ya yi barci". Dariya ta subuce masa ya ce "Maigado bana son sharri fa ke dai ki fad'i gaskiya kina son a jijjiga ki kawai, ba sai kin jinginawa unborn ba" Da murmushi sosai ta ce "Allah Dady shine ga zahiri ka ga ni, yanzu ba ya daina hautsinawa ba?" Ya yi saki gauron numfashi ya ce "Na yarda." Ta karya harshe sosai ta ce "Baban Bilkisu gobe idan an sha ruwa tare zamu fita ka yi askin sallah, nima a wanke mini kaina. Jiya na yi Oder din abayas a wajen Maman asalan da asala mazauniyar Eggypt din nan". Da hanzari ya ce "Tom Allah ya kaimu, zamu je. Amma ban da kin fad'a mini ai har da yaran Sai a siyo musu daga can din". Dad'i ya ratsata waton dama ba wani abin da zai yi? A tausashe ta ce "Yanzu ma tunda bata turo mini ba, sai ta hado da nasun, gobe zan yi magana da ita sai Slsu zabi design din da suke so. Na gode ka ƙara hakuri da ni Allah ya tsare ka daga dukkan sharrin zamani". Dad'i ya ratsa shi ya amsa da fad'in "Ameen Maigadona Allah ya sauke ki lafiya na k'osa na yi tozali da abin da ke cikinki k'warai da gaske. Tun ban gan shi ba ya samu matsayi mai yawa a zuciyata. Ina sonki ina son duk abin da ya shafe ki sarauniyar shaiba! Daga haka ya latsa makunnar wutar. Ya karanta falaki da nasi tare da ayayul kutsiyu ya tofa a hannayensa ya shafe mata jikinta.Wani irin faricinciki ke tunda ga k'asan zuciyarta tare da wani irin shaukin da bata taɓa jinsa akan kowa ba sai akan Baban Bilkisu. Ta kasa magana amma tabbas yanzu tasan ta yi aure, yanzu ne ake jiyar da ita dad'i tare da gusar mata dukkan sha'awarta. Tana jin ya sake karanto wasu surorin tsarin ya shafe nasa jikin sannan ya kwanta ya rungume ta a haka barci ya sure su. Daga haka ya warware bai sake yi mata fushi ba. Da daddare kuwa ya dauke ta suka fice basu dawo gidan ba sai wajen shabiyun dare. Aysha da Hafcy sun shiga hayyacinsu da ita, sun daina yi mata habaici haka nan sun fita a harkar Farha basa dukanta. Sai dai kuma basa yiwa Bilki magana. Sun tafi a fahimtar ba haka kawai ta bar ubansu ba. Abubuwan da yake yi a kanta ba iya soyayyar Allah da Annabinsa ba ce. Dan haka ta samu sauk'in matsaloli amma bata jin dad'in yadda yaran suke gaba da ita. Da kanta ta fahimci duniya haka take babu wani cikakken dad'i. Wannan auren tabbas shine abu mafi dad'i gareta a yanzu. Don auren Asad ne ya fahimtar da ita akwai wani abu farinciki a duniya. A duk sadda cikin jikinta ya motsa sai Yaya Asad ya faɗo mata sannan kuma sai ta ji zuciyarta ta motsa a kansa. Zuwa yanzu babu k'insa da take ylji babu dalili a zuciyarta. Sannan ta gamsu ta fara sonsa, irin son nan mai shiga da sanɗa kafin an ankara ya yi tasirin gaske . Tun ba'a je ko ina ba ta fara jin takaicin dogon zaman da ta yi da Sahal kuruciyarta na tsiyayewa a banza. Da tasan haka al'amarin yake da Yaya Asad zata aure tun farko Allah bar shi su fafata da matarsa. Don ko yanzu da Rukayya take kwance a k'asa duk yadda suka yi mu'amala mai dadi kishinta take ji, saboda hotunanta da suke samansa da dakin barcinsa ya sanya ta haramtawa kanta kwana a d'akinsa. Kuma tabbas nan gaba kad'an zai san yadda zai yi da su dan kuwa yadda ya girke su da hannuwansa to kuwa da hannayen zai kwashe su ya sakaye a wani lokon. Ranar sallah Asad da kansa ya tuka iyalinsa a mota zuwa masallacin kasa na birnin tarayya(National mosque) don yin sallar idi. Sai dai motor y'ansanda tana binsu a baya don kare lafiyar maigidansu da iyalinsa. Daga masallaci gidan Baba suka zarce. A gaban ya'yansa da yaransa ya fito ya budewa Bilki k'ofa ta fito ya sara mata bayan ya karbi jakar hannunta. Ganin hakan ya sanya ayarin y'ansanda ma suka yi abin da ogansu ya yi tare da fad'in "Madam barka da sallah!. Aysha da Hafcy suka ido suna kallon ikon Allah ya yin da Bilkisu junior take vedio da tsaleliyar wayarta. Don abin burge ya ya yi tare da fatan itama ta auri jami'in tsaro ya dinga saluting dibta8cike da soyayya da girmamawa a gaban kowa. Aysha da take lauya cemm tuni ta gama lissafinta ta gano dalilin da ya sanya mominsu yin surgery wato Dady na son mata masu mazaunai da cikar kirji ita kuma bata da su. Idonta ya cika da hawaye a dalilin ta yi amannar ko momi na da rai zai nade k'afar wando ne ya auro mata Anti Maigado ya kuma sha shagalinsa da ita, a yanzu kuma da babu ranta yana holewarsa da ita a gaban kowa yake nunawa ita din ta mussaman ce babu alhini ko tunanin tsohuwar matarsa. Ta saki gauron numfashi a dalilin Su din bai gaza musu da koami ba, komai suke so haka zai yi musu, Duk kuma soyayyar da yake yiwa Bilki da suke adawa da hakan bai hana ya basu lokaci musu tattauna ko ci abinci tare ba. Haka ma Anty Maigado bata yi musu komai ba, illah auren Babansu alhalin ya k'i anty Laura. Sannan dangin uwarsu kaf fad'a musu suke yi rabon auren Bilki ne ya kashe uwarsu. Tunda shi ba mai ra'ayin aure aure ba ne. Amma yanzu Aysha ta fara kokwanton dan Babu Momi ne ya sanya ya aure ta. Tabbas ko ta na nan sai ya auro ta. Kuma ta yi imani takwarar da ya yi mata tun tana budurwa ba dan zumunci ba ne, dan yana sonta ne yana kuma rarrashin zuciyarta ta amince masa. Duk zumuntarsu da anty Abida bai sanya sunanta ba. Kuma dukkansu sun san anty Abida ce favourite sister d'insa. Shiyasa take yiwa mominsu wulak6da isgili ba tare da iya yi mata hukunci ba, a karshe ma Sai Dai ya ce momin ce bata son y'anuwansa, shi kuwa duk mai sonsa to ya so Abida. Haka ta ja jiki ta bisu a baya zuwa cikin gidan gabad'aya jikinta a sanyaye tana ta tunanin da shine ya rasu to da Momi zai yi wahalar gaske ta yi aure. Idan har kuwa zata yi to ba zata yi a kusa irin haka ba, idan kuwa ta yi shekararsa d'aya kacal a k'asa society Sai sun fitine ta da fad'in bata damu da mutuwarsa ba tunda ya bar kudi daga mutuwarsa har ta yi aure saboda tsananin fitina. A babban falon ta tarar da dadynsu da dukkan tawagarsa sun gurfana gaban Baba da Momi da suke zaune a kan kujera. Itama ta durkusa gefen Bilki tana mik'a tata gaisuwar. Baba ya dinga addu'a da fatan Allah ya karbi ibada. Yayin da jikin Bilki ya yi sanyi tana hasaso ita nata mahaifan babu ko d'aya. A hankali y'ansanda suka fice suka bar iya ahalin gidan. Tuni kuma an cika musu gabansu da cimaka iri iri. Abida ta fito sanye da gown ta Malaysianfabrics...... Ta yi kyau sosai duk ba kwalliya ta yi ba junior na biye da ita cikin shudiyar tsadaddiyar shadda. Aysha da su Laura suka dinga gaishe ta cike da girmamawa. Dama haka suke kaffa kaffa da ita tunda ba ta yi musu. Ta isa gaban Yaya Asad ta yi saluting d'insa ta ce "Barka da sallah Baban Bilkisu I.G.P din gobe da yardar Allah ". Dad'i ya kama shi ya mike ya cire hularsa ya yi saluting dinta ya ce "Barka dai Abidan Baba k'anwar Bilkisu ". Bilki ta kalle su cikin shauki da tuna baya, ta sani Yaya Asad da Abida wata irin kaunar juna suke yi ba kad'an ba, tamkar dai yadda suke ita ta da Yaya Sulaiman. Karon farko Abida ta sunkuya ta cicciba Bilki ta yi saluting dinta ta ce "Yaya Maigado barkanmu da ibada". Dad'i ya ratsa Baba Babba yana jin had'uwar kan mutanen ukun nan za'a ji ci lagon gabar da ta yi k'arfi a tsakanin ya'yansa da na Baba k'arami. Shiyasa tunda al'amarin ya faru Bai sake barci cikakke ba Sai bayan auren Bilkinsa Asad. Wannan auren shine tsanin yin sulhu da afuwa a tsakanin ya'yansa da na k'aninsa. Don kuwa gidan Asad zai zama kowa na da alaka da gidan kaitsaye. Shiyasa kullum sai ya yi musu addu'ar Allah yasa albarka a cikin aurensu ya kuma dauwamar da shi. Da dabara Abida ta janye Bilki suka yi d'aki. Ta ce Maigado cire mini wannan bubu abayar na ganki sosai. Wato watannin aurenki watannin cikinki, ke Maigado ki rage had'ama". Dariya ta k'wacewa Bilki ta ce "Ni da kika raina kya fad'a mini haka mana, alhalin shi ya kamata ki tambaya ki kuma jingina masa had'amar." Abida ta ce "Ke da shi dai sak kun dace halittarku d'aya. Na taɓa jin matarsa na faɗawa wata aminiyarta cewar shi mabukaci ne na sosai ita kuma tsaka tskai ce. Kin ga kema tuni na san mabukaciyar ce kin ga ai abu ya yi kyau dole na jiki shiru babu wani borin ba Kya sonsa." Kunya ta lullube Bilki don ta san gaskiya Abida take fad'a. Can ta nisa ta ce "Bilki na fa k'osa wanccan birkitattancen yayan naki ya dawo, na k'osa k'warai da gaske ki faɗawa mijinki nima irin halittarmu d'aya da ku, an fara bincikem inda yake kamar yadda ya yi mini alk'awari ko kuwa na fara fita nemansa da kaina?" Idonta ya ciko da k'walla. Na yi shiru amma dariyar da ban shirya ba ta k'wace mini. Na ce "Ni wacece ta ce mini ita dakhila ce ne?" A hassale ta ce "Abida ce amma sadda na fad'a din AI ban gane kaina ba, yanzu kuma an rataue ni shekaru uku ai dole na k'osa tunda raine da ni". Ni dai dad'in yadda aka jarrabi ta akan Yaya Sulaiman nake yi don kuwa a bayyane yake tana da tasiri a cikin y'anuwanta tunda ta sauko ta huce da mu, to fishin kowa ba zai ma abin damuwa ba tunda hatsabibiyar tasu ta yi laushi irin tub'us din nan. Sai dai Bilki ta san da sauran rikici a gaba don Yaya Sulaiman ya fusata da ita takaddama ce mai tsananin gaske zata sake Tashi. A ranta ta dinga addu'ar Allah ya shiga don kuwa ga ni take ba k'aramin jan Abida zai yi a k'asa ba. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:31] *Surayya Dee* PAGE 4 Hakurin nan dai shi Bilki ta bawa Abida. Tare da adduar Allah ya bayyana shi. Sai azahar suka tafi nasu gidan su ya'yansu. Daga kan Bilkisu, Amal da Noor basa bata matsala don kuwa tunda ta zane Hafcy suka sake nutsuwa. Yayin da Aysha da Hafcy har ma da Laura ido ne a tsakaninsu. Suna yin yadda suke so a gidansu. Yayin da ta koma gefe take kallonsu. Bilki na zaune tana cin hadddedn kulikulin da ya Asad ya koya mata ci na Ummiel foods 08036355535....wayarta ta hau kuwwa. Ta dan murmusa ganin sunan Baban Bilkisu ke yawo a fuskar wayar. Ta dauka da walwala ta ce "Baban Bilkisu ka sauka ne?" Da take yana cikin tawagar da suka raaka Shugaban Yan sanda na k'asa (I.G). Zuwa jihar Sokoto kan sha'anin tsaro. Jiya suka tafi, yau kuma zasu dawo. Ya ce "Eh mun sauka sai dai zamu fara raka oga gida. Tuwo nake son ci, ki mini da kanki if possible Maigado". Da kanzagi ta ce na shinkafa ko na semo?" Na fi son na masalina fa". Cikin hanzari ta ce ka samu Baban Bilkisu. Allah ya kawo ku lafiya". Ta mike ta nufi kicin ta shiga store ta fito da garin masalina leda d'aya. Kad'an zata yi tunda yaran basa ci. Manyan kuma abin da suke so suke sawa a yi musu. Ta bude murya ta k'ira Alti. Ta iso tana fad'in me kike so ne Mahmah?" Daidai lokacin Laura ta shigo kicin din. Ta bude sink tana wanke hannunta. Bilki ta ce "Baban Bilki yake son cin tuwo ya ce na yi masa da kaina." Farinciki ya bayyana a fuskar Alti a dalilin ta fara gamsuwa Bilki ta fara son mijinta, nan gaba zata dawo da hakurinta ta yadda zata jure duk wani k'alubalen zamanta a gidan. Don gabad'aya Alti a ankare take da ita kada ta yi musu sanadin da zasu bar wannan aljannar duniya tunda ta gane Bilki irin mutanen nan ne da basa neman hujja a so ko a kiyayya. Idan suna son mutum to suna sone da dukkan zuciyarsu duk kuma nak'asun wanda suke so zai zama an amsa uzziri. Idan kuwa basa son mutum komin kirkinsa da abin duniyarsa basa so, dole a k'yalesu. Da azama ta ce "To da me zan taimake ki?" "Ki fito da kaza ki wanke, ki silala mini, miyar ayayo zan yi masa ". Alti ta ce "Yanzu kuwa. Ta bude firiza. Laura ta fice tana jin takaicinsu gabad'aya ya kamata. Tare da tunanin yadda zata b'ata girkin tunda kishinta take yi sosai, so take a ce itace a gidan tana bada umarni ayi ko a bari. Amma ya tashi ya dauko bazawara yana b'are b'are a kanta. Ta fice ba wanda ta yiwa magana illa tafiyar tak'ama da take yi. Bilki ta jijjiga kai tana ayyana al'amura masu yawa, idan su Aysha suna yin dibar karan mahaukaciya da ita tana hakuri tare da zuba ido to lah shakka Laura ta yi kad'an. Amma dai zata sake daurewa tunda idan ta yi magana Alti balbale ta zata yi da fadan ta koyi rashin kawaici. Sai da Alti ta dora ta ce "Da su Amrah nake yin waya, d'an nawa ya ce mini suna tafe cikin satin nan". Bilki na dauraye tukunya ta ce "Haka suka ce mini dazu, zasu biyo matar k'anin babansu zata zo wani aiki, wai da motar ofis zata zo kuma zata yi kwanaki biyar." Cikin nutsuwa da k'ware wa suka shirya masa tuwon da lafiyayyar miyar ayayo da aka burge gudar kaza a cikinta. Ta hada masa salad don ya samu daidaito a cikinsa. Ta shirya masa a falon saman da suke shan ruwa. Sannan ta zarce nata saman don yin wanka da kintsawa. Ta bata lokaci tana shiryawa sosai ta yi kyau. Farha ta kalle ta ta ce "Mahamah kina da kyau fa! Kuma na ga fuskata irin ta ki ce, nima zan yi kyau kenan?" Ta murmusa tare da fad'in "U are so beautiful Farha, kina da kyau ma fiye da ni". Dad'i ya sanya Farha yin dariya har da tafi. Bilki ta kalle ta ce "Ki je wajen su Noor Dady yanzu zai dawo kada ya yi fadan bai gan ki a gunsu ba". Ta fice a guje don kuwa ya fad'a mata idan bata zama a samansu to babu ita a zuwa London wajen Yaya Khadija. Sanye take cikin super wax karshen tsadar, doguwar riga free size haka ayi ta babu ado illa tsadaddun stones da aka watsa a rigar. Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:35] Ta yi kyau har ta gaji, ta yi fari, fata ta yi taushi k'warai da gaske. Zai yi wahalar gaske ka kalle ta sau daya baka sake na biyu ba. Tana tafe k'amshi na alfarma na biye da ita. Gabad'aya samanta ya karade da k'amshinta. Cikin nutsuwa take sauka zuwa inda tasan zai yada zango. Sai dai turus ta yi cikin tsananin alajabi a dalilin yadda ta tarar da Hafcy da Laura suna zaune suna cin tuwon da ta ajiyewa maigidan. Aysha na gefensu tana cin salad a bowl. Bak'inciki ya turniƙe ta. Daidai lokacin kuma aka bude gate din gidan tabbacin ya iso kenan. Da tsananin b'acin rai ta ce "Wa ya baku izinin taɓa abincin nan?" Kaitsaye Aysha ta ce "Abinci a gidan nan kuma har sai mun nemi izni?" Yayin da Laura ta ce "Mun dauka namune tunda daddy yana son mu dinga cin wanda kika saka aka dafa." Yayin da Hafcy uffan bata ce ba. Bilkisu tana d'akinta yayin da su Amal da Noor da kuma Farha suka yi waje don taro Dady. Bilki ta kalli Laura ta ce "Ke ki tsaya a matsayinki kada ki yi kokarin wuce iyaka, idan su sun xama dole su zauna ke fa? Babu dalilin zamanki tare da mu". Aysha ta ce "Ai kuwa zamanta daram don a tare da mu ta rayu". Yayin da Laura ta fara kukan an mata gori. Daidai lokacin kuma ya iso inda suke shi da yaran. Ganin Laura na kuka su kuma sun yi cirko cirko ya sanya shi tambayar ba'asi. Hafcy ta yi fit ta zayyane masa kanun labari ta sigar da ba zai ga laifunsu ba. Ya kalli Bilki ya ce "Kada ki damu don sun ci, idan sun rage zan ci sauran, idan kuma babu bari na saka charity ta yi mini wani abin, kada wannan cin abincin ya zama abin damuwa. Takaici ya mak'ure ta. Ta kasa ce wa komai a dalilin sun cinye gabad'aya tunda dama dauri uku ta yi, ta saka masa guda biyu ta zubawa Alti d'aya tunda itama masoyiyar tuwon ce, kuma tun lokacin ta zauna a kicin din ta ci bare ta dauko masa na Altin. Murya babu amo ta ce "Sannu da dawowa." Ya amsa da fad'in "Sannu sarauniyar shaiba ya gida da yaran?" Ya zuba salad din ya fara ci kana ganinsa ka san ya kwaso gajiya da yunwa. Ta had'iye kukanta ta shiga kicin ta yi maza ta d'ora ruwan tuwo tunda da miyar a tukunya. Tana cikin aikin charity ta shigo ta yi mata sannu ta fara hidimar abincin da ta tabbatar shi ya bada umarnin ta yi masa. Bata hana ba. Ta kammala ta shirya a tray ta kinkima ta nufi inda ta bar shi. Yana ganin ta da tray ya zabura ya mik'e ya karbe ta yana fad'in kina ganin halin da kike ciki mai zai saka ki dauko da kan ki?" Ita dai bata ce uffan ba. Ya kai ya ajiye ya zuba tuwon yana fad'in "Sannu da aiki Maigado " Ta isa ta zauna amma ta kasa amsawa. Daidai lokacin k'iran Amrah ya faɗo wayarta. Ta dauka ta kara a kunnenta. Ta ji muryar yarinyar a sanyaye tana ce mata "Mahmah zuwan namu ba zai yiwu ba sai next time , an daga zuwan Antin da zamu biyo, lokacin fa5 zata zo din kuma hutunslku ya k'are ga yayanki ki masa magana tun dazu yake mini kuka, abin da ba ya yi, amma yau ko abinci ya k'i ci duk ya tayar mini da hankali". Ba kuzari ta ce"ba shi wayar". Murya a dakushe ya ce "Mahma! Bilki ta aro jarumta ta ce "Yayana ya da haka kuma, ina ce wanccan hutun kun zo? Ka yi hak'uri idan ka daina kuka to ana yin hutu zan turo a d'auko ku. Ku yi duka hutunku anan tare da su Farha ". Murya ba amo ya ce"To". Yauwa Yayana ka daina kuka ai ka girma, ina kanwarku?" Kaitsaye ya ce "Tana can tare da uwarta". Billki ta yi maza ta ce "Tana wajen anty dai ko". Bai amsa ba ya ce "Ki aiko mini kayan da kika ce kin siya mini, ina Alti, ina Farha?" "Duk suna lafiya anjima zan kiraku sai ku yi magana da su." Suka yi sallama. Ya kalle ta ya ce "Farouku rigima". Ta yi yak'en dole ta kasa cewa komai. Ta tafi tunanin yadda take gwagwarmaya da su Hafcy haka Hawwah take gwagwarmaya da Faruku don kuwa Amra mai sanyi hali ce irinta. Yana cin tuwon ya ce "Na ji dad'in tuwon nan gobe ma ki yi mini irinsa, thank you". Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:46] Kafin ta amsa masa ta ga Aysha ta mike ta fice Laura da Hafcy ma suka tashi suka bi bayanta. Daga su sai k'ananun kan dole ta hak'ura ta sakar masa fuska amma abin da suka din ya yi mata ciwo tunda dai da gayya suka yi hakan sannan su ba cin abincinta suke yi ba, sawa suke yi a yi musu, shine yau suka shammace ta suka yi mata haka ta kuma tabbatar Laura ta ji lokacin da take faɗawa Alti Baban Bilki ke son cin tuwo. Zaman yarinyar a tare da su ya fara gundurarta don ta fahimci ita ta take sake koya musu wasu shakiyancin tunda ta fisu shekaru da budewar ido, bayan haka ta fahimci son Baban Bilkin ta fara yi, don rashin kunya da rashin mutunci, shiyasa take ganin kishinta a fuskarta muraran. Bilki ta numfasa tana jin idan yarinyar ba ta bar gidan ba, ba zata taɓa daidaito da su Aysha ba. Gara ta koma gaban uwarta ta zauna amma ba a gidanta ba. Sai da suka kwanta yana ta damƙarta cikin rawar jiki. A tausashe ta ce "Baban Bilkisu ina ganin Laura ta koma gidansu hutun nata ya isa haka". Da azama ya ce "Ki yi hakuri ya za'a yi bata ce zata tafi ba, ace mata ta tafi, k'anwar Rukayyace fa, kin san kuma a hannunmu take tun tana da shekaru goma." Kaitsaye Bilki ta ce "To da yake ai yanzun ba Rukayyan ba ce matar gidan, na gaji da zamanta a cikin gidan nan gaskiya". Ya yi shiru yana ayyana yadda Bilki ta ce Rukayya gatsal duk kuwa da mutumiyarta ce ta sosai don ya sha jin suna waya sannan yadda take nan nan da Bilkin bata yiwa Abida haka. Ya nisa ya ce "Yanzu dai bari na gaisa da unborn na kuma yi barci ma tattauna daga baya". A wannan ranar a dole ta biye masa, don gabad'aya zuciyarta ta yi nauyi ainun. Don haka babu wani aramshin a zo ga ni a had'uwar. Washegari sassafe ya fita office ko karyawa bai yi ba, tunda zai dawo. Tana barci bai tashe ta ba, k'arar bude gate ya tashe ta. Ganin bakwai bata cika ba ma ya sanya ta koma ta kwanta don ta san sai wajen shadaya da ya dawo, a kuma wajen yaran zai yada zango su karya. Bata tashi ba sai wajen goma da rabi. Kaitsaye wanka ta shiga, kafin ta fito tuni Rahina sabuwar yar aikin da ta dauka matashiya ta gyara d'akin sosai. Tana fitowa kuma ta fad'a toilet ta yi wanka. A nutse ta shirya duk yadda zuciyarta ta yi mata nauyi kwalliya ta yi sosai ta fece tamkar zata je babban taro. Ta fita falonta daidai lokacin Alti ta shigo ta zauna suka gaisa. Ta ce "Na yi miki kunun gyada na kuma soya doya, na yi ferfesun naman rago". Da girmamawa ta ce "Sannu Alti zuba ki bawa Rahina ta kawo mini, su Farha sun karya ne?" Ga su can a saman tsakiya suna karyawa da Bilkisu ". Ta ce "To sannu da aiki Alti. A ranta kuma ta gasgata mutanen da suke fad'in suna na tasiri. Gabad'aya Bilkisu yanayin halayyarta ne da ita. Shiru shiru babu hayaniya bata da matsala sannan aminiyar yara ce. Cikin nutsuwa take karyawa tana tunanin Baban Bilkisu da ya fita bai karya ba. Ta ja k'aramin tsaki a dalilin ko yana nan ma tasan barinta zai yi ya tafi wajen ya'yansa su karya tare. Ta kammala Rahina ta kwashe kayan, tana zaune tana nazarin rayuwarmu da bata zuwa mana yadda muka zace ta, kira ya faɗo wayarta. Da hanzari ta dauka murya a sake ta ce "Maman Abdul me ya samu wayarki ne? Na yi ta k'iranki har na gaji". Ta amsa da fad'in "Ke dai bari Maman Amrah sace mini aka yi, kin san kuma yanzu tashin hankaline idan ka rasa sim dinka. Har na ce na hak'ura zan siyi sabo to kuma komai nawa da layin na bude shiyasa na daure na dawo da shi ". Bilki ta ce "Haba na yi nema har na gaji, jiya na ce wa Alawiyya ta fad'a mijinta ta je ta dubo mini ke, amma muna gama wayar nan zan k'ira na fad'a mata na same miki". Basma ta ce "uwargida kuma amaryar Yaya Asad kina tafe kina amon bullet". Dariya ta kama Bilki ta ce "Amon bullet ki ce na zama fasa taro kenan?" Basma ta yi dariya ta ce "Zan so na gan ki Bilki nasan yanzu kin dawo sarauniyar shaiba ta gasken ba wacce dan tsakon nan ya ajiye ba. To ya ya yanzu dai babu matsalar oza room ko?". Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:49] Bilki ta numfasa ta ce "Babu Basma, duk matsalar da ta dame ni a gidan Sahal yanzu ba ni da ita, amma kuma na sake faɗawa wata matsalar mai zafin gaske har nake jin tamkar na girgije na bar zaman". Salati mai tsananin gaske Basma ta saka tana fad'in "Eh hakane wato hakurine ba za ki yi a inda ake sonki ake daraja ki ba? Aurenki da Yaya Asad fa al'amura masu yawa yake nufi a cikin gidanku. Idan kin kwantar hankali kin jure, komai zai daidaita muku gabadaya. Idan kuma kin kasa jurewa to ina tabbatar miki komai zai sake k'wacewa ne, ku sake jefa Baba Babba cikin tahsin hankali. Haba Bilkisu menene ba ki yi hak'urinsa ba a inda ma bai kamata ki yi hak'urin ba, amma kin yi. Yaya Asad ai alfarmarsa yawa ne da su a gunki ko bai ci arzikin jinin da ya gaurayaku ba, to lallai ya kamata ya ci na dakon soyayyar ki da ya wanzu yana yi, ya kamata ki ba shi hadin kai ya daidaita ahalin gidanku waje d'aya! A sanyaye Bilki ta ce "Ni fa babbar damuwata da shi akan yara ne, baya kaunar abin da zai sosa musu rai, kirikiri suke musguna mini amma ba zai dauki mataki ba, ina son mu dinga karyawa tare amma sai ya tafi gunsu su karya, da daddare kuwa wani lokacin sai na yi barci kafin ya zo d'akina, yana gunsu fa". Tsaki Basma ta yi ta ce",Eh lallai kin samu guri dole ki yi shanya, to dan yana sonki sai ya k'i kula ya'yansa? Wai yaushe kika zama hakane?". Murya ba amo Bilki ta ce ba za ki gane pain din ba. Amma ai bai kamata yara sai abin da suke so za'a yi musu ba. Dan dai ba ke kike gidan ba ne. Sannan ga k'anwar matarsa ta kammala B.U.K. Tana nan tare da mu tana sake koya musu dabarun musguna mini." A sanyaye Basma ta ce"Ki yi hak'uri ai tunda aka yi sa'a mata ne to matsalar gajeriya ce kamar yau duk zasu bar gidan kowacce ta je ta fara fuskantar nata k'alubalen auren. Abin da nake so dake ki dinga binsa kuna karyawar tare, zai ji dad'i sannan za ki daina ganin hakan a matsayin laifi. Da daddaren ma ki dinga shiga cikinsu ana yin hirar da ke". Ta ce "Basa saka ni a ciki, shine yake kula ni sai ƙanƙananun yaran kawai". Basma ta ce "Tunda yana kula ki ai shikenan sai ki yi da shi da k'ananun yaran, da lokacin barci ya yi sai ki tura yaran su kwanta, ke kuma ki fara gyangyadi da ya ga haka zai sallami manyan". Bilki ta numfasa ta ce "Hmm amma zan yi trying". Basma ta nisa ta ce "Ni fa Duk wannan ban d'auke su matsala ba, ban yi zaton kema zasu zame miki matsala ba don kuwa kin fuskanci wadanda suka fi haka tsananin gaske kin kuma hak'ura. Me yasa ba kya zuwa d'akinsa sai dai shi ya zo?" A sanyaya ta ce "Hoton tsohuwar matarsa ya girke a d'akin da kuma gefen gado, ni kuma Wallahi ba zan je na kwanta alhalin da hotunan a d'akin ba". Basma ta ce "Da kin iya, kin kwantar da kai da tuni bai cire ya saka su cikin shirgi ko a saka su saman yaranta da dakunansu! Bilki Bilki, ki sauya takunki, ba shine kawai yake da laifi ba. Ni gaskiya ma nafi ganin aibinki. Shi Sahal da yake kina sonsa kin jure kin cinye dukkan tuwon iskanci da wulak'ancinsa ko?" Bilki ta yi shiru ta kasa cewa komai don kuwa tasan halin Maman Abdul ba zata saurare ta ba, tunda itama bata son Sahal har cikin zuciyarta shiyasa yanzu ba zata gane halin da take ciki ba. To tunda Alti ma bata fahimce ta ba, ai ba kowa zai gane yadda take ji a ranta ba. Sai wadanda suke fuskantar irin wannan k'alubalen da take fuskanta. Kan dole ta numfasa ta ce "To Maman Abdul zan gyara". Dad'i ya kama Basma ta dinga yi mata addu'o'i da fatan alheri tare da haska mata nasarar da auren zai janyo matuk'ar ta nutsu ta yi hak'uri. Ta rufe bayanin ta da fad'in "Ai na je na gano su Amrah suna nan fes da su komai suke so suna da shi a k'asansu, ranar ma na ga Alawiyya a gidan suna yin samosa tare da Amrah." Sosai kuwa batun ya farantawa Bilki zuciyarta ta ce "Madallah da Maman Abdul na gode". Daga haka suka yi sallama. Basma ta ajiye wayar tana fad'in sokuwa kawai, kin bar alakakai kin fad'a niimar duniya amma kina neman kwafsawa kanki." Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:54] Haka rayuwar ta cigaba da gurgurawa cikin hak'uri da godiyar Ubangiji. Watanta bakwai da aure, haka kuma watannin cikin da take dauke da shi. Ya yi girma sosia tamkar yanzu zata haihu a asibiti an tabbatar mata y'an biyun ne a cikin hakan ya sake saka mata tsoron Allah tare da girmama sha'anin Ubangiji. Y'a'yan Asad a cikinta ita da kanta abin mamaki yake bata, bata fad'a masa y'an biyu zata haifa ba, amma ya sha fad'a mata bai taba ganin girman ciki irin nata ba, don gabad'aya ta bude ta sake girma sosai. Ba wanda zai ganta ya dauka ba zata haihu yau ko gobe ba. Laura ta nan bata tafi ba. Tsiyataku kuma basu fasa yi mata ba. Yayin da shi kuma baya zafafawa, hakuri kawai zai ce ta yi. Ana haka rannan ya fita tana barci ya yi ta kiranta bata d'auka ba, tunda ta saka wayar a DND. Tana falo tana zaune da bowl mai dauke da kulikulin da ya zarta kilishi da d'adi na Ummiel foods.. A hankali take cinsa tana jin dad'insa har cikin kwanyarta. Bilkisu ta hawo da sauri ta bata wayarta tana fad'in Mahma ga Dady don ta bi bakinsu Amal wajen ce mata Mahmah. Tana bata ta juya don game take yi a system dinta. Ta kara a kunne tare da fad'in "Hello." Ya amsa da fad'in "I salute you sarauniyar shaiba. Na yi ta k'iran wayarki no response, shine na ce a kawo miki wayar ya jikin dai?" Can kasa ta ce "Da sauk'i". Ya ce kin tashi kin yi wanka kin karya ne?" "Um" Ta fad'a a takaice. Ya nisa ya ce "Wai ba ki huce bane? Pls mana Maigadona". Ta tura baki ta ce "Na huce yanzu". Ya murmusa ya ce "Kin samu duniya yayar Abida." Ta murmusa don tana jin dad'i idan an ce mata Bilkisu yayar Abida mussaman ace Baba Babba ne ya fad'a mata hakan. Ya yi mata sallama. Ta rike wayar Bilkisu tana juyata. Waya suke rikewa masu daraja sosai. Baya shayin kashe kudi ko don ya tarasu ne da yawa oho. Da yake wayar babu security kuma akan manhajar what's app take ya sanya ta ga wani group messages na ta shigowa ga sunanta na bayyana Maigado ko Anty ma babu. Kaitsaye ta bude group din da aka yi masa suna da *we are one*. Ta ga iya su biyar ne a ciki. Laura, Aysha. Khadija, Hafcy, sai Bilkisu. Gabad'aya maganarta suke yi maganganu masu tayar da k'ura. Wai asiri ta yiwa Dady ban da haka yaushe da uwar kud'insa zai auro bazawara bayan haka ma, me zai sa ya auro wacce suka yi shari'a da ubansa. Shi ko duba uwarta ba mutumiyar arziki ba ce bai yi ba, kuma ko tantama basa yi Maigado ta tsosto halayyar uwarta. A hankali take bin hirar wanda Aysha Laura da Hafcy ne suke yin ta. Amma Khadija tana ciki bata tanka musu ba, asalima ta jima bata yi magana ba, haka nan Bilkisu ma bata cewa komai. Wayar na hannunta Hafcy ta ce na rasa me ya ga ni a jikinta yake sonta irin haka. Ai tunda ta dake ni ya yi mukus nasan ta gama da shi, uwarmu ma idan ta duke mu sai ranta ya b'aci amma wannan mandiyar ta sarrafe shi idan yana gabanta ba shi da kuzari bare ya motsa k'wanji." Laura ta yi tsaki ta ce "Manyan mazaunanta ne suke tsole masa ido, ai na ga alamun su yake so a tare da mace kun manta tashi guda Momi ta yi su, to dan wa ta yi? Ga shi ta rasa rayuwarta gabad'aya akan hakan, shi kuma ya samo irin wacce yake so ya aura yana yin yadda ya ga dama tabbacin ya manta da ita! Dad'in abin ma amafanin da zasu yi masa ya shafasu, ko spanking sai kuma ta yi masa tusa, dan idan ya ce zai ci walakiri makarsa zai yi babu amfanin da kudi ko mukaminsa zasu yi masa." Ran Bilki idan ya kai dubu to ya b'aci. Sai dai kuma nan da nan Aysha ta yi tagging Laura tana tambayar Dady ta jinginawa Homosexual? Haka ma Hafcy. Ba sai jiyo tashin hayaniyarsu ta ji ba, da alamu maganar Laura ta bugesu sun ajiye wayar zasu yi a zahiri. Hawaye ya cika kwarmin idonta. Tana rasa inda zata tsoma ranta. Sun jima suna tashin hankali kafin ta ji sun yi shiru. Ta yi vedio record din hirar ta turawa kanta sannan ta goge vedion a wayar Bilkisu. Yini ta yi cikin tsananin b'acin rai. Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 12:01] Da daddare sai da ta bari ya gama uzzirinsa sannan ta fad'a masa. Yana bude baki ya ce "Ki yi hak'uri ai yara ne." Ranta ya rub'anya baci Ta ce su Aysha ne yaran? Kuma ya kamata su saka Bilkisu a group suna irin wadannan zantukan na rashin tarbiya?. Ta bude masa wayarta ta kunna masa vedion hirar ya ji. Ya ce ai har ni ma sun taba ni. Ki yi hakuri zan yi musu fad'a ". Takaici ya kamata ta ce "To gobe Laura ta bar gidan nan". Kaitsaye ya ce ba zan kore ta a gidana ba fa". Ta mik'e ta ce "Baban Bilkisu na rantse da Allah sai ta tafi, ko ni na tafi". Yana daga zaune ya ce ba inda zaki je sarauniyar shaiba, sannan fa ba zan iya korar k'anwar Rukayya daga gidana ba, a hannuna ta girma, yadda ba zan kori su Aysha ba. Haka itama ba zan kore ta ba saboda alfarmar Rukayya." Kishi mai tsananin gaske ya turnike Bilkisu. Cikin fitar hayyaci ta ce da Rukayyan da Lauran duk sun ci uwarsu Talatu, itama Talatun ta ci uwarta! Mamaki mai tsananin gaske ya lullube shi. Kishi ne ko kuwa tsabar rashin mutunci ne ya sanya ta zagi Rukayya da uwarta har ma da kakarta? PAGE 5 Mamaki mai tsananin gaske ya lullube shi. Kishi ne ko kuwa tsabar rashin mutunci ne ya sanya ta zagi Rukayya da uwarta har ma da kakarta? Ransa ya b'aci matuk'a da gaske. Ya mik'e ya isa kusa da ita ya ce "Wanne irin abune ya same kine kanki d'aya kuwa?" A harzuke ta ce "Na maimaita maka kalamaina ne don ka gane a hankalina nake ko kuwa?" Ya juya ya tsaya a bayanta ba zato ta ji ya rungume ta, ta baya, a hankali ya dinga ja da baya ya ísa bakin gadonta ya zauna a hankali, sannan cikin nutsuwar ya zaunar da ita akan cinyoyinsa, fad'in mazaunainta da nauyin cikinta sun danne shi sosia irin yadda yake so. Ya daidaita mata zaman tamkar wanda zai shayar da ita. Ta shige kirjinsa tana rusar kuka sosai. Ya sunkuyar da fuskarsa daf da tata, suka dinga shakar numfashin junansu. Duk da a yanayin b'acin rai suke sai da jikinsu ya amsa. Ba zato ya rik'e mata hannunta da k'arfi ta yadda ba zata iya kwakkwaran motsi ba. Ya kai bakinsa kan nata bakin ya tsoste shi da kyau a k'arshe ya gasa mata cizo. Ta kidime amma bai sake ta ba, ya sake tsosatar wajen, sannan ya sake skaar mata cizon. Ta fashe da kuka daidai lokacin ya dago da fuskarsa ya kalli yadda take kukan azabar da ya gaana mata cikin wani irin salo mai birkitarwa. Ya sake mayar da fuskarsa daf da tata ya ce "A ina kika samu tarbiyar zagin? Ki janye zagin nan ko na cigaba". Ta ki yin motsi bare ta janye din. Ai kuwa ya sake maimatawa, dad'i da azaba suke ratsa ta a lokaci guda. Cikin kuka ta ce "Ka yi hak'uri zan janye". Ya sake ta ya zuba mata idonsa da suka yi jawaur gabad'aya shima ya birkice da bukatarta. Ya sassauta rikon da ya yi mata. Murya ba amo ta ce "Fitsari zan yi". Ya sake ta ta yi maza ta sauka daga jikinsa ta koma kan gado nesa da shi ta zauna ta bude baki tana rusar kuka wiwi. Ya numfasa ya ce "Tabdi jam wato janyewa ne ba zaki yi ba shine kika ce band'aki za ki, k'arya za ki koya?" Ya fad'a yana matsawa kusa da inda take zaune. Da sauri ta sake matsawa ta ce "Na janye zagin Talatu da uwarta. Amma Wallahi ban janye na Rukayya da na Laura ba". Daga haka ta yi wuff ta shige bayi ta rufe kofar". Duk yadda yake cikin bacin rai sai da ya murmusa. Ta jima bata fito ba, ko da fito a Inda ta bar shi a nan ta tarar d shi bai motsa ba. Ta wuce shi ta zauna can gefe tana kokarin warware duvet d'in da zata lulluba. Ya numfasa ya ce "Wataƙila dai kin manta mu gidanmu na tarbiya ne, dole ne kuma a ladabtar da duk wanda ya nemi ya yi watsi da tarbiyar da aka d'ora shi a kai wala yaro wala babba. A gabana za ki zagi matar da ta haifi wanda ta fiki, hakan bai ishe ki ba, sai kin had'a da uwarta itama? Cikin kuka ta ce "Kada ka fake da haka, kawai ka gana mini azaba ne dan na zagi matarka! To na janye na uwarsu da kakarsu amma ko zaka tsire ni ba zan janye na Laura da na Rukayya ba." Ta fad'a cikin matsanancin kuka. Ya yi shiru yana kallon yadda take kuka mai d'auke da shesshekar ajiyar zuciya. Ya taso daga inda yake, ya zauna kusa da ita, ya ruko ta ya sassauta murya ya ce "Yi shiru sarauniyar shaiba, yi hak'uri." Ta fisge cikin kukan ta ce "Ni Wallahi ba zan yi hak'uri ba sai Laura ta bar gidan nan". Ya ce "Lallai kin shiryawa rikici sarauniyar shaiba, ga shi kuma ina kan batuna na ba zan kore ta a gidana ba". Ta sake harzuk'a ta rushe da kuka ta ce "To kuwa ba zan zauna ba, ita ta zauna ta maye maka gurbina tunda na lura tana yi maka irin amfanin da nake yi maka! Ya hassala k'warai da gaske. K'warai ya ji zafin kalamanta. Laura tana yi masa irin amfanin da take yi masa? Tana zarginsa akan Lauran kenan. Wai su mata haka suke ne dukkansu? Mafi yawansu basa mallakar hankalinsu akan batun kishi. Kuma dan iskanci ma ko da zargi suke yi ba tabbas ba sai su rufe ido su yi rashin mutunci tare da d'iban albarka! Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:21] Murya babu amo ya ce "Sa'arki d'aya cikin jikinki ba dan haka ba dan kin dandana kudarki Maigado". Cikin kuka ta ce "To ka mayar da shi jikinka mana idan ya so ni ka kashe ni tunda ba ni da gata". Mamaki ya lullube shi ya ce "Da kika tashin yi baki sai kika yi na rashin kunya Bilkisu? Wanne irin k'arkon kifi kika yi haka?" "Eh! Ta ba shi amsa a takaice. Ya jijjiga kai ya ce "Zan kuwa goge miki shi". Cikin kunkuni da kuka ta ce "Idan na zauna da kai ba". Ya yi shiru yana kallonta amma zuciyarsa na suya. Tsawon lokaci tana kuka yayin da ya zama mutum mutumi. Haka suka kwana zuciya babu dad'i. Sassafe ya fice bai yi mata sallama ba. Ta yi wanka ta samu leda ta zuba dogayen rigunan Malaysianfabrics na Umm Nihla....... Don sosai take jin dad'in saka su tunda basu da nauyi ga taushi. Ta leka d'akin da Alti take ta ce mata ta shirya zasu fita. Farinciki ta ya da ya kasance asabar ce don kuwa zata tafi da Farha babu wani shamaki. Ta zuba turarunkata na Mkbees perfumes da mayunkata na lame skin ........ A motarta suka tafi. Mamaki ya kama Alti da taga Bilki tana ta gararanba da su a manyan titunan Abuja. A tausashe ta ce "Da alama dai tafiyar ba ta lafiya ba ce. Tunda kika dauko ni tare da Farha nasan ba k'alau ba." Bilki bata tanka ba, tafiya kawai take yi. Alti ta kaurara murya cikin sigar umarni ta ce "Samu waje ki tsaya ". Babu musu ta gangara ta yi parking. Hakuri da rarrashi Alti ta fara yi mata akan ta daure ta koma d'akinta ba abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah. Cikin rishin kuka ta ce "Ba zan iya zaman ba. Gaskiya na gaji! Hankalin Alti ya yi tashin gauron zabi ta ce "Muje gidan Momi ". Bilki ta kece da kuka tana fad'in yaushe zan iya zuwa wannan gidan, ai cutar da ya yi mini kenan ta ya ya zan je na fadawa Baba da Momi bana son d'ansu, na gaji da zama da shi, ta yaya zan k'i zaman gidansa na koma gaban iyayensa alhalin shi ya siyi gidan. Wayyo Allah wayyo Yaya Sulaiman! Ta rushe da kuka wiwi. Alti itama sai ta shiga taya ta kukan, tsawon lokaci suna yi, kafin Alti ta yi jarumtar had'iyewa. Ta numfasa ta ce "Da dai za ki amince da kin yi hak'uri kin koma gidanki idan Allah yasa kin haihu lafiya sai mu tattara mu bar masa gidan. Amma yanzu kina cikin wannan hali ina za ki je? Ki daure ki haife cikin nan a gidan ubansa." Bak'inciki ya sake turnike Bilki, tabbas cikin nan ya yi mata shigar sauri daga zuwanta gidan ta same shi. Murya ba amo ta ce "Ba zan koma ba fa Alti gaskiya! "To na yarda ba za ki koma ba, amma a cikin biyu Wallahi sai kin zabi d'aya ". Bilki ta yi shiru tasan kuma tunda Alti ta rantse to dole kuwa ta zab'a. Alti ta numfasa ta ce "Ko dai mu je gidan Baba Babba ko kuma mu je gidan Farouku ". Hawaye ya k'wacewa Bilki ta ce "Cikin cutar da Yaya Asad ya yi mini har da shamaki da ya gindaya a tsakanina da Yaya Farouku, ta ya ya zan je na zauna a gidansa alhalin na ce bana son d'anuwansa, duk yadda yake sona ai nasan yafi son Asad da ni". Alti ta ciro wayarta ta lalubo sunan Faruku tunda tana iya karanta wasu daga cikin kalmomin hausa, don ta yi yaƙi da jahilci tun kafin ta yi aure. Bugu d'aya ya dauka ya ce "An buga an bar ki Altin Bilki". Ba kuzari a muryarta ta ce "Kana Abuja ne?". "Ina nan Alti, Allah yasa lafiya na jiki wani iri ". Ta ce Farha me aka rubuta a jikin wanccan dogon ginin?" A sanyaye Farha ta ce "Sheraton Hotel". Don tunda ta ga uwarta na kuka gabad'aya ta rasa kuzarinta. Alti ta ce "Ka zo muna tsallaken sharaton hotel". A hanzarce ya ce "Lafiya kuwa amma dai ga ni nan zuwa yanzu". Mintina talatin da yi masa waya ya iso. A sukwane ya yi parking ya fito ya doshi motar Bilki. Ya bude gaban motar. Alti ta ce "Farha dawo nan.". Farha ta tsallaka ta koma baya, Shi kuma ya zauna. Juyin duniya ya tambayi dalilin kukanta da fitowa ta bar gidanta amma ta k'i magana sai kuka. Ya numfasa ya ce "Yanzu mu koma gidanki, ki yi hak'uri, nasan kina yi to ki k'ara hak'uri, Annabi ya ce aljannar mace tafi samuwa ne idan ta yi hak'uri ta yi biyayyaa a gidan aurenta.". Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:24] Sai lokacin ta numfasa cikin rishin kuka ta ce "Gaskiya ba zan koma ba Yaya Faruku, ina cutuwa, ni gaskiya ina buk'atar na samu gidan da zan kama". Ransa ya b'aci ya ce "Bilkisu Baban na da rai ne za ki kama inda za ki zauna? Me yasa kuke yi masa haka ne? Ko ni nake da rai ai ba kya yi mini wannan wulakancin ba bare Baba". Jikinta ya mutu ta ce "To ya zan yi tunda ya dage sai da ya aure ni don ya shiga tsakanina da ku". Faruk ya ce "Bai isa ya rabamu da ke ba. Yanzu na amince ba za ki koma gidansa ba. Amma ki zaba ko dai gidana ko wajen Baba". Cikin kuka ta ce "Zan je wajen Baba ". Ya numfasa ya ce "To mu je." Ya fita ya shiga motarsa ya ja, sannan ta bishi a baya suka tafi. Ba kowa a falon gidan sai talabijin da take babatu, k'amshin air freshener na mkeebs perfumery da yake tashi sannu a hankali tare da sanyin a.c ya sake sawa falon ya zama gun hutawa. Alti da Farha ne suka shiga ciki suna sallama. Momi da take kan sallaya tana lazimi ta idar da walaha ta tsinci sallamar Alti. Kafin ta amsa Farha ta tura k'ofar d'akinta ta shiga. Nan da nan ta shafa addu'a tana fad'in "Farha kune da sassafe haka? Ta kalli agogon da yake makale a bango ta ga goma saura na safiya. Alti ta durkusa tana gaida Momi cikin sanyin jiki. Ta amsa a sanyaye tare da fad'in "Alti kune da sassafe haka ice ko lafiya?" "Lafiya k'alau momi tare da ita muka zo tana falo da Yaya Faruku". Nan da Momi ta ce "A a ba k'alau ba, tunda ta ja tunga a falo bata shigo ciki ba". Suka fita momi na ganin yadda fuskarta ta yi ja ga idanuwa sun yi luhu luhu zuciyarta ta harba ta tabbatar babu lafiya. Da hanzari ta isa kusa da kujerar da take yayin da Maigado ta mik'e kaitsaye momi ta jata jikinta ta rungume. Jin haka ya sanya Maigado rushewa da sabon kuka don a yanayin da take ciki so take a ce ta je gaban mahaifi ko mahaifiyarta ta yi kukan da take ta rik'e shi a ranta. Sun jima a hakan kafin Momi ta sake ta, ta ce "Zauna Maigado sannu!. Maimakon ta zauna kan kujerar sai ta zauna a k'asa tana fad'in "Momi ina kwana?" "Da kin zauna a kujerar ai sai tafi miki dadi Maigado". Murya a dakushe ta ce "Babu komai momi". Yayin da Momi ta kalli Farouku ta ce "Sannun Farouku Ubangiji ya yiwa kokarinka albarka". A sanyaye ya ce "Ameen momi. Baba ya tashi kuwa?" Ta ce "Har ya karya ya yi tattaki kwanciya ya ce zai yi amma ai dole ya taso". Ta juya don zuwa d'akin Baba. Tare suka fito da Baban kamar kullum yana sanye da farar jallabiya mai asalin tsada. Duk da shekaru sun ja masa ainun da dan sauran kuzarinsa, ba dan mutuwar k'aninsa da takaddamar da ta biyo ba, da yafi haka kyan gani don tun lokacin bai yi cikakkiyar lafiya ba. Alti ta gaishe shi, ya amsa da walwala, ya mik'awa Farha hannun tare da fad'in "Zo kusa da ni Bilkisu d'iyar Bilki". Ta tashi daga kusa da Maigado ta isa kusa da shi ta gaishe shi yana tambayar ina ta baro Amal da Noor?" Zuciyar Bilki ta doka, sai dai bata ji a ranta zata koma gidan da za'a dinga bawa yara lasisin su dinga zaginta suna aibata mata uwa haka siddan ba. Cikin hikima Alti ta zame ta nufi kicin da ta jiyo motsin momi. Momi ta fito ta ja Farha zuwa d'akinta inda junior yake barci don sassafe Abida ta fita zata yiwa wata patient c.s. A nutse Bilki da Farouku suka gaisa da Baban nasu. Ya k'are musu kallon nazari ya ce "Dukkanku ba kwa cikin walwala menene damuwarku ne?" Cikin nutsuwa Farouku ya ce "Bilki ce ta samu matsala da mijinta, ga kuma halin da take ciki." Baba ya yi shiru tsawon lokaci bai ce komai ba. Yayin da dukkansu suke dakonsa. Ya numfasa ya ce "Yau ne karon farko da kika taba barin gidan aurenki da sunan bacin rai, ban so kika karyawa kanki record din ke ce kad'ai baki taɓa yin yaji ba tunda aka yi miki aure, sai ga shi kin fara yi a inda ban yi zaton za ki yi ba. Na kuma shaida alamarine ya kerewa haƙurinki, amma da sawa kika yi Farouku ya kai miki ni gidanki da yafi mini dad'i." Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:31] Bilki kanta na k'asa tana zirar da hawaye ta kasa magana. Ya nisa ya ce "Menene matsalarki?" Ta kasa ce masa komai, Farouku ma ya yi tambayar duniya, amma bata ce komai ba sai kuka mai tayar da hankalinsu". Baba ya ce "Ai kin yi k'uruciya Maigado, da zaki taho da kin sa ni kin had'o da Amal da Noor amma sai kika tsame y'arki a cikin y'anuwanta alhalin ni kika saka na fad'a masa za ki je masa da ita, na fad'a masa ya kuma ce ya amince zai saka ta cikin jerin y'a'yansa, yanzu dan kun samu matsalar da ba sakinki ya yi ba sai ki watsar masa da y'ay'ansa k'ananu ki taho da taki kad'ai? Anya kuwa! Wannan ba halayyarmu ba ce, ba mu da wannan halayyar ta banbantawa." Kukan Maigado ya tsaya cak. Domin kuwa iyakacin gaskiyarsa yake furtawa wanda ta yarda babu son kai ko na zuciya a cikinsu. Take kuma ta gamsu ta yi kuskuren barin yaran mussaman da su basu yi mata laifin komai ba. Ya nisa ya ce "Ki zauna zuwa yamma idan mijinki ya tuntube ni, ko Farouku to za ki koma a yau din nan. Hakan ma dan na ga yanayin da kike cikine ya sanya zan barki, ki d'an huce. Amma da yanzun nan za ki koma inda kika fito". Ta shi ki je dakinki ki kwanta ki yi barci kafin Dr Abida ta dawo". Ta yunk'ura da ƙyar ta tashi ta nufi ciki yayin da Baba da Farouku suka bita da kallon yadda ta aune ga ciki ya habaka tamkar a lokacin zata haihu. Sai da ta k'ule sannan Baba ya nisa ya kalli Farouku ya ce "Ban da k'uruciya ma a wannan halin da take ciki me zai saka ta bar d'akinta? Faruku ya ce "K'ure ta ya yi ne Baba ai Maigado mai hakuri ce kowa ya shaida hakan". Baban ya nisa ya ce "Ai kuwa zai hadu da fishina Wallahi akan Maigado zan yi matuƙar sab'a masa, bata son aurensa amma ya dage ya matsa sai da ka shawo masa kanta shine tun auren bai je ko ina ba zai fara tayar mata da hankali?" Baba ya yi tambayar yana kallon Farouku tamkar shine Asad din. Farouku ya saukar da kansa k'asa ya ce "Ka yi hak'uri ni kaina ban ji dad'in al'amarin ba, zan fad'a masa gaskiya idan ya yarda shikenan, idan ya yi wasarere da matsalar kwabarsa ce zata yi ruwa." Sai shadaya sannan Faruku ya yi sallama da iyayensa akan da yamma zai dawo. Abida bata dawo ba sai azahar. Junior da suke wasa da Farha ya ruga ya rungume ta. Yayin da Farha ta yi mata sannu da dawowar ba tare da bar wasan da take yi ba. Ta kalle ta ta ce "Ke da wa kuka zo?" "Da Mahma tana ciki tana barci". Abida bata kawo koami ba, tunda Maigado na da ciki don ta yi barci ba komai ba ne. Ta leka d'akin Momi ta fad'a ta dawo sannan ta shiga dakin Maigadon. Ta idar da sallar azahar tana ninke sallaya. Ta ce "Maigado kin ga yadda fuskarki ta yi kozai kozai kuwa, me ya same ki haka?" Ta yi k'arfin halin ce wa "Ba komai. Jikin Abida ya yi sanyi a dalilin ta gane ba k'alau ba. A sanyaya ta ce "Bari na je na yi sallah na dawo ". Da ta yi sallar ta dawo ta tisa ta a gaba da tambayar menene matsalarta. Haka siddan Bilki ta ji ta kasa fad'a mata. Kan dole Abida ta numfasa ta ce "Indai da dama ki yi hak'uri ki koma dakinki Bilki, ki dubi halin da kike ciki mana, ki cire b'acin rai tun ba ki yiwa kan ki da abin da za ki haifa illah ba. Menene abu mai dad'i ne a zaman gida? Babu dad'i fa Maigado, Wallahi babu dad'i, kin ga dai a gaban Momi nake ko? To Wallahi kullum dare sai na yi kuka, ba zan so mu yi kuka tare ba Maigado. Yaya Asad na sonki, lallaba ki koma dakinki, ki daure har Allah yasa ki shawo kan matsalar da ta dame ki". Cikin kuka ta rattabawa Abida halin da take ciki da yara da kuma yadda Babansu yake fad'in yara ne hak'uri kawai yake bata. Sannan ta gano Laura da uwarta sune suke yiwa yaran famfo ta ce masa ta koma gida ya ce ba zata tafi ba saboda alfarmar Rukayya." Abida ta yi shiru can ta nisa ta ce "Ai kuwa sai ta tafi ko sama da k'asa zata hade. Dama ni ba son tsohuwar nan nake yi ba tunda take taya Rukayya kishi da ni, ko tunanin yana rik'e da d'iyarta a gidansa basa yi, sun dauki tsangwama sun dore mini duk abin da yayana zai yi mini na kan idon Rukayya. Allah dai ya jiqanta amma ai ta mutu da kuttuna a ranta. Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:38] Kuma na ga take taken Aysha gaisuwar da take yi mini tabbas uwarta ta cusa mata k'ina zan ko ci uwarta Wallahi ". Bilki ta rik'o hannun Abida ta ce "Ni dai kada ki taso da wani batu akan matsalata, kawai ni dai ba zan koma gidansa ba matuƙar Laura tana nan, ko Baba ya mayar da ni, to kada ku ga laifina akan na bijirewa Baba Wallahi yana tafiya zan gudu, ba zan zauna ba". Abida na jin haka ta mike ta fice, kaitsaye d'akin Momi ta shiga, ta fad'a mata komai na matsalolin Bilki. Yayin da itama ta nufi d'akin Baba ta rattaba masa batu. Ta kara da fad'in "Kada a mayar da ita tunda ta fad'a masa Laura ta koma gidansu, ko ita ta tafi nasu gidan, tunda yafi buk'atar zaman yarinyar to sai ta yi ta zama". Baba ya ce "A a zata koma kuwa daga nan zuwa dare, ai itama ta yi rashin alkunya. Idan kin ga bata koma yau ba to sawunta ne bai biyo ba, Laura kuwa tunda uwarta da ranta sai ta koma gabanta idan aurenta ya zo sai ya yi mata duk abin da ya kamata. Batun Aysha kuma ai k'alilan ne da anzo batun neman aurenta ba za'a saka dogon lokaci ba tunda itace fitananniya idan aka kawar da ita an karya lagon sauran yaran ". Momi ta ce "To shikenan Alhaji yadda ka ce hakan za'a yi". Farouku tunda ya fita yake neman dukkan layukan C.P amma basa tafiya ga shi har yamma ta yi. Yayin da shi kuma maigirma C.P. aiki ne ya yi masa yawa da yamma kuma suka shiga meeting da Mr President da sauran masu rik'e da madafan iko. Sai wajen takwas na dare ya samu kansa. Kaitsaye gida ya dosa a lokacin tara har ta gota. Ya tarar da yaran su kad'ai a falon da suka fi zama. Suka dinga welcoming d'insa. Ya zuba musu ido sosia yana nazarin waye babu a cikinsu. "Noor Ina Farha?" "Mun tashi tun safe bamu gansu ba, mun hau saman Mahmah duk bamu gansu ba". Nan da nan ransa ya sosu. Ya ce "Alti na nan?" Bilkisu da tafi takura da rashinsu ta ce duka fa basa nan tun safe, na k'ira mahman wayarta a kashe". Ya numfasa ya ce "Kun ci abinci ne?" Hafcy ta ce "Ga shi can jiranka muke yi". Murya ba amo ya ce "Ku je ku ci, mun yi dinner tare da Mr president tea kawai zan sha". Aysha ta ce "Anty Laura ta kawo maka ne?" Takaicinsa ya kamata. Bai amsa mata ba ya ce "Hafcy ta kawo masa saman Mahmah ". Takaici ya shak'e Aysha da Hafcy yadda yake fad'in Mahmah a gabansu shi ala dole so yake su dinga k'iranta da Mahmah su kuwa ba zasu ce Mahmah ba sai Anty Maigado hakan ma don ba yadda zasu yi ne. A saman Bilki ya yada zango tunda anan yake kwana. Kaitsaye d'akinta ya shiga ya fad'a bayi. Ya fito da alwallah. Ya idar da sallar kenan Hafcy ta kwnakwasa kofar d'akin. Yana Kan sallayar ya ce "Come in". Ta shigo da sallama sannan ta ajiye masa tare da fad'in "Dady gaskiya ka gaji, ya kamata ka kashe wayoyinka ka yi barci, kada stress ya yi maka yawa. Murya ba amo ya ce "Je ki k'ira mini yayarku, ku zo tare". "To Dady". Ta juya ta tafi, yayin da ya bita da ido. Suka shigo a nutse bayan ta yi sallama, k'asa suka zauna kusa da shi. Cikin nutsuwa Aysha ta ce "Dady ga mu'. Ya nisa ya ce "Wayarki za ki ba ni". Kaitsaye ta mik'a masa. Bai karɓa ba ya ce "cire mini password din". Ta cire don yana yawan yi musu irin haka, ya gama bincike ya basu amma baya taba shiga groups dinsu na whtsapp. Contact yafi dubawa da waɗanda suke magana ta pc. Kaitsaye whtsapp ya shiga ya yi searching sunan group din we are one da ya ga ni ta vedio record. Ai kuwa ya shiga ya ga maganganun da suka tayar masa da hankalin Bilki. Daidai inda Laura ta ce kudi ko mukaminsa baza su amfane shi ba idan ya ce zai jewa Bilki ta baya. Ya tsaya ya mayar mata da wayar. Ta karanta ta ji zuciyarta ta buga, hankalinta ya tashi. Murya na rawa ta ce "Dan Allah ka yi hak'uri Dady duba ka ga duk mun yi mata ca akan wannan batun da ta yab'a maka". Murya a dakushe ya ce "Dama kuka bata shiyasa ta zage ni, kin bude group kuna zagina a fakaice ita kuma tunda ni ba ubanta ba ne sai ta zage ni a bayyane akan idanuwanku da kunnuwanku". Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:41] Hankalin Aysha ya kai k'ololuwar tashi ta ce Wallahi Dady bama zaginka a fakaice. Duba ka ga ni". Ta fad'a a rude matuk'a da gaske. Yayin da Hafcy ta yi wuki wuki tana jin kunyar duniya na kamata duk kuwa da bai ambace ta ba. Ya yi murmushin da ba shi da alaka da nishadi ya ce"Duk wanda ya zagi matarka ai kaitsaye kai ya zaga, ke ce babba kina da ilimi har kin zama Barista, makarantun da kika yi tun daga matakin nursery har jami'a duka na alfarma ne. Ba abin da ban yi miki ba na gata da soyayya tunda aka haife ki. Amma wai yau ke ce kike yak'ata kike son ki nukurkusa ni da bak'inciki!Kina tunanin ko uwarki na da rai zan kasa yin aure ne? Tunaninki bai alamta miki cewar auren da na yi rufin asirinku ne ba? Da ace Babanku ya yi aure bayan mutuwar matarsa da ace Babanku na yin lalata da yara sa'aninku wanne yafi muku?". Gabad'aya Aysha ta ji ta muzanta hankalinta ya rub'anya tashi, kuka ya k'wace mata saboda ta ga b'acin rai mai tsanani a fuskarsa da muryarsa gabad'aya. Murya na tawa ta ce "Dan Allah Dady ka yi hak'uri! Ya numfasa ya ce "Ke ce da hak'uri Aysha. Ni dai nasan ke na ke bi ba shi, ba ni kike bina ba. Ruwanki ne ki bar ni na samu nutsuwar da ta dace da ni, ruwanki ne ki cigaba ta tayar mini da hankali, idan na fad'i na mutu sai ki ji dad'in jagorantar kannenki yin duk abin da kuka ga dama. Idan an raba gadon y'anuwana sun baku naku sai ku ci duniyar da tsinke tunda dai mu dai mun ga ayar da ba zamu sake barin gado ba tare da an raba shi da wuri ba". Hafcy ma ta fara kukan don kuwa yanayin Dadynsu ya yi matuk'ar tayar musu da hankali. Hafcy da kuka sosia ta ce "Ka yi hak'uri Dady". Ya ce "Kune fa da hak'uri don idan kun zauna lafiya da matata kune da riba don hankalina zai kwanta na yi ta binku da fararen addu'o'in da zasu yi tasiri a kanku. Idan kuma kun cigaba da zaginta, kun ga ai nima zata cigaba da gigita mini nutsuwata kuma ko ban ce muku komai ba ai ba zaku ga daidai ba tunda kun jefa ni cikin b'acin rai da tashin hankali. Ace kuna y'ay'ana ban isa da ku ba, ban isa ku mutunta iyalina ba, ta ya ya wacce na auro zata ga k'ima ta, tunda ta gane ban isa da ku ba, sannan baku da tarbiya! Shi yasa ba abin da ba zan yiwa Khadija da Bilkisu ba, don sun yarda na isa da su, kuma sun gamsu ni ubansu ne da zasu taya ni mutunta abin da nake so, su kuma taya ni k'in abin da bana so". Kuka sosia Aysha da Hafcy suke yi suna ba shi hak'uri. Ya nisa ya ce "Zan hak'ura ne kad'ai idan kun daina cin mutuncin Maigado don kuwa ko ban aure ta ba ai uwarku ce, sai kuma k'arfin k'addara ya sanya ta zama matata, kenan tudu biyu ne da ita a wajenku. Idan ta haihu ashe haka zaku dasa mini y'anubanci a gida tunda ni ba kwa sona uwarku kawai kuke so ko?" Ya yi musu tambayar yana kallonsu gabad'aya. PAGE 6 Hak'uri kan hak'uri suke ba shi don kuwa ba k'aramin muzanta suka yi ba. Kalamansa sun yi matuƙar bugunsu. Kunyar ganin tattaunawarsu a group dinsu da ya yi ta kannade su. Nadama mai tsananin gaske ta shige su. Ya kalle su ya ga yadda suke kuka sosai, hakan ya tausasa masa zuciyarsa. Ya nisa ya ce "Abin da nake so ku fahimta guda d'aya ne ko mominku na da rai ba zan kasa auren Maigado ba. Kuma tabbas da ace Maigadon ta amince mini a farko da a gabanta zaku girma don kuwa da tuni na aure ta. Da bata amince mini ba a dalilin ta yiwa uwarku alkunya, ai na hak'ura, yanzu kuma da na samu damar aurenta na aure ta din, na tabbatar Kuma ta amince ne saboda babu ran uwarku da Kuma tausayinku. Sai ga shi kun nuna mata halin tsiya, halin rashin tarbiya. Ku bude kunnuwanku da kyau ba zan rabu da ita saboda ku ba, ku bini a hankali mu rabu lafiya, ku bini a hankali mu rabu lafiya Aysha da Hafcy! Ya fad'a cikin sigar gargadi. A tare suka ce "To Dady ! Cikin kuka sosai. Hakuri kan hak'uri suke ba shi tare da alak'awarin sun canja zai kuma ga canjin a aikace. Ya sallame bayan ya ce "Zai huce da sune idan ya ga sun canja da gaske". Bayan sun tafi ya sauke gauron numfashi yana jin ya samu sauk'in matsaloli da kaso saba'in cikin dari. Ya fad'a tunanin ta inda zai bullowa Bilki. Don kuwa itama ta yi masa laifin da zai mata hukunci mai tsauri. Ta gama cin mutuncinsa na zarginsa da yarinya k'ank'anuwa sannan ta fice da y'arta ta bar masa nasa su kad'ai babu tunanin komai. Ya hurar da hucin b'acin rai yana jin babu abin da yake susuta namiji irin rashin samun kwanciyar hankali a gidansa. Daga Bilkin har yaran cikin k'ank'anin lokaci sun firgita shi, wato mata babu mai iya musu sai Ubangijinsu. A fili ya ce "Da suna da damar ja da hukuncin Ubangijin ma zasu ja bare kuma namiji da suka dauke shi abokin gaba kuma abokin adawa. Daidai lokacin k'iran Faruku ya shigo wayarsa. Ya dauka murya babu kuzari ya ce "Ranka ya dade masu k'asa". Faruku ya yi murmushi ya ce "Kune da k'asa, kune ake yi muku jiniya" Asad ya ce "Masu dala ai suen da k'asa ko na ce duniyar ma a hannunky take gabad'aya". Faruku ya numfasa ya ce "Tun safe nake nemanka ban same ka ba". Kaitsaye ya amsa da fad'in "Ayyuka suka sha kaina, ban jima da shigowa gida ba" Faruku ya yi turus tare da tunanin har ya koma gida ashe ya ga Bilki bata nan amma bai neme shi ba? Ya nisa ya ce "To bari na barka ka huta a gaida iyalin". Kaitsaye Asad ya ce "Zasu ji tare da kashe wayarsa. Jikinsa na ba shi Farouku yasan bata gidan shiyasa ya k'ira shi a wannan lokacin. Shi kuma bikon ta ne ba zai je ba, tunda ta yi masa wannan wulakancin zai gwada masa kalar nasa. Wayewar lahadi a gida ya yini bai fita ko ina ba, sannan ya ce da yaran su karya kada su jira shi. Ya dawo sallar la'asar yana ta tunanin ya kamata ya fara neman ta ko dan halin da take ciki, Allah bar shi idan ta dawo itama ya fara bata nata hukuncin don kuwa ba zai yarda ta dinga caba masa duk maganar da ta zo Mata ba da sunan kishi. Daidai lokacin suna daki ita da Abida suna tattauna yadda bai biyo bayanta ba. Gabad'aya zullimi ya bayyana a jikin Abida ta ce "Bilki kada fa mutumin nan ya yi irin ta Yaya Sulaiman ni fa gabad'aya a tsorace nake, ban yi zaton zai iya kai wa wannan lokacin bai kawo kansa gidan nan, ko gidan Yaya Faruku a birkice ba". Bilki da zuciyarta ta yi nauyi sosai a sanyaye ta ce "Ai zuciyarsa a bushe take sannan a kan ya'yansa ba ya ji, ba ya ga ni". Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:26] Abida ta ce "Bari na dauko jotter din da na rubuta wuridin da aka ba ni na kiranye mu fara doka masa kada bak'in cikin Baba ya zama biyu, kai maza na kan sharafinsu". Duk da zuciyar Bilki a kuntace take matuƙa da gaske sai da kalaman Abida suka saka ta tuntsire da dariya don bilhakki Abida a firgice take da rashin zuwan Yaya Asad. Ta gimtse dariyar ta ce "Dr Abida ba dai malamai kika fara bi ba?" A sanyaye ta ce "A a sadakar kudi na bawa wani mutumi ya kawo mahaifiyarsa asibiti, k'arfinsa ya k'are sai na cika masa 1 million din da yake nema dan ayi mata aiki, shine ya ji dad'i yana ta mini addu'a. Ni kuma ganin Malamin addini ne da alamun tak'awa a tare da shi, shine na fad'a masa bala'in da nake ciki akan ya taya ni da addu'a, ya tausaya mini shine ya ba ni wuridin ya ce 'Ni da mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko y'aruwarsa shakikiya mu dinga yi babu kakkautawa, matuƙar yana da rai zai bayyana mana cikin gaggawa". Da azama Bilki ta ce "To d'auko mu fara Abida idan mun ga fatahi akan wannan sai mu taru mu yi akan Yaya Sulaiman dan na lura mazan nan sai da addu'a mai zafi". Abida ta ce "Sosai fa Allah dai ya sanya muna da zafin yawu Bilki". Abida ta fice zuwa ɗakinta da hanzari yayin da Bilki ta sake tsorata idan har Abida yadda take cikakkiyar yar boko, mai kuma baudadden hali, sannan a bayyane yake Abida bata son maza, kusan ma feminist ce amma ta shiga tarkon namiji take karban kebra masu radadin gaske ai dole ita da take sonsu ta lallaba ta iya takunta tun kafin abin ya dawo kanta. Sai dai kuma tabbas ba zata bari ya dinga daukar hakkinta yana bawa yara ba, haka nan ba zata lamunci su dinga cin zarafinta yana kallo ba zai dauki matakin da ya dace ba. Daidai lokacin Abida ta dawo d'auke da jotter da biro a hannunta. Ta zauna gefen gadon ta mikawa Bilki ta ce "duba ki ga ni." Bilki ta karɓa tana karantawa. Ta kammala ta ce "Zamu iya yinsu ai babu wahalar yi. Kin ga kiranye yaya Asad ba zai yi wuya ba tunda kiran sunan nasa daga kansa ne zuwa kan kakanmu na biyu. Amma na Yaya Sulaiman fa zai bamu wahalar gaske ina muka san kakanmu na shida?" Abida ta ce "Na rantse idan har na ga wannan ta ci zan gurfana gaban Baba ne ya fad'a mini sunan kakansa na biyar ". Bilki ta gimtse dariyarta akan dole don idan ta tsananta yin dariya yanzun nan gayyar zata waste. Sun yi alwallah zasu fara yin sallar daga nan su zarce da yin wuridin kafin junior ya tashi. Bilki ta ce "Idan na yi Ladifu d'ari ba d'aya cikon na d'arin ne zan ce "Asad ibn Musa ibn Garba ibn Bello ko?" Cikin gasgatawa da yin imani Abida ta ce "Yauwa kin fahimta haka ma za ki yi idan kin yi iyaka na abudu 99 cikon na 100 din ki kamo sunansa har zuwa kan babansa na uku. Damu suke zancen". Suka yi sallar la'asar suka dukufa wuridin Iyaka na abudu wa iyaka nasta'in da kuma ya Ladifu. Fiye da shud'ewar awa guda suna yi, tun Bilki na yi da cikin iyashege da dariya har ta gimtse take yi da gaske, tabbas tana son ya zo amma idan ya so din ba binsa zata yi ba, tare da an baje magana a faifai ba. Suna daf da kammalawa wayar Bilki ta hau kuwwa alamun k'ira ne. Abida ta yi maza ta ce uhum uhum tare da girgiza kanta da k'arfi alamun kada ta katse wuridin. Bilki ta fahimci manufarta dan haka bata katse ba ta bar wayar ta katse dan kanta. Sai dai k'iran cigaba ya yi da shigowa har sau uku sannan aka tsagaita. Sai biyar da kwata suka kammala. Abida ta ce "Bari na dauko wayar mu ga ko shine aka fara tsikarin zuciyarsa, ai ba dan so nake ya ji jiki ba, da na tab'o shi na ji halin da yake ciki". Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:29] Jikin Bilki ya yi sanyi da yadda ta ga Abida ta dage tana taya ta jin ciwon abin da ya yi mata duk kuwa da a bayyane yake Baba da Momi ne kawai suka sha gaban Yaya Asad a wajenta. Akwai kauna ta mussaman a tsakaninsu kamar dai ita da yaya Sulaiman. A zuciyarta take ayyana ko zata iya taya Abida dankwafe Yaya Sulaiman kamar yadda take yi mata akan Yaya Asad a yanzu? Ta kasa bawa kanta amsa don ita kanta bata sani ba a yanzu sai zuwa gaba tukun. Abida ta yi shewar murna tare da fad'in "Wallahi shine! Ta jijjiga kai cikin gamsuwa ta ce "Yanzu muka fara har sai ka kawo kanka gaban Baba." Daidai lokacin k'iransa ya sake faɗowa wayar. Abida ta dauka ta gaishe shi ta ce masa barci take yi. Ya numfasa ya ce "Autar Momi wai mun bata ne?" A sanyaye ta ce "Me ka ga ni Dady?" Ya ce "Tun shekaranjiya yarinyar nan ta baro gida ban sa ni ba, amma ko ki k'ira ni Abida?" Ta numfasa ta ce "Ai da yake ni mace ce, kasan duk haka muke bama son a taka mu". Jikinsa ya yi sanyi don Abida bata fadan rashin gaskiya, duk anincin da kusancinta da mutum bata bin bayan k'arya. Hakan ya sanya suka yi ta samun sabani na gaske shi da Rukayya don zai iya ce wa duk rikicin da zasu da ita mai tsanani akan Abida ne. Bisa hujjar Rukayya na yana fifita Abida fiye da ita, sannan ba dama Abida ta ganta da zani ko gold sai ta ce tana so, shi kuma sai ya siya mata fiye ma da nata. Bayan haka ta ce Abidan ce take b'ata ta a wajen Momi, shiyasa Momi tafi son matar Faruku da ta Usman a kanta. Shi kuma ya gane Abidan gaskiya ta fita, itace take k'yashin hidimar da yake yiwa kanwarsa, ta kuma yi kuskuren da ta bari Abida ta gane tana kishi da ita shiyasa ita kuma take baje mata kalolin shegantaka kalakala tare da yin shagulatin bangaro da ita, tana kanbabama sauran surukan gidan fiye da ita. Jikinsa ya yi sanyi don ya lura itama fishi take taya Bilki. Ya numfasa ya ce "Siyar mini jarida Abida! Me ta fad'a miki na yi mata da ya sanya ta yi mini yaji?" Ta murmusa a dalilin ya ce ta siyar masa da jarida tabbacin tuna mata da k'uruciyarta ya yi. Ta ce "Yara na zaginta har kuma da yar sakabu tsabar samun wuri, kai kuma ba zaka tsawatar ba, ba gara ta gusa ba". Ya yi turus don kamar camfi Idan Abida bata baka support ba, baka yin tasiri. A sanyaye ya ce "Yanzu tsakaninki da Allah ya kamata ta banbanta y'a'yana da nata?" Kaitsaye ta ce Bai kamata ba". Yauwa autar momi ita Maigado wata irice, kullum tana mak'ale da Farha Amal da Noor a ware da k'yar na banbare wariyar da take nunawa, yanzu da zata yi yaji sai ta dauke Farha ta watsar da sauran indai don Allah ne mai zai saka ta bar su tunda sun saba da ita sun Kuma Saba da Farha. Na fita Sai kawai na dawo na tarar Babu ita babu Alti da Farha, zan ji dad'i? " Jikin Abida ya yi sanyi ta ce "Ta yi kuskure amma fa bai kai naka ba gaskiyar magana. Ko rashin zuwanka nasan daga Yaya Faruku da ya baka ita har baba sai sun diga maka ayar tambaya". Ya nisa ya ce "Gobe zan zo in sha Allah bana jin dad'i ne yanzu. Bata wayar". Nan da nan Abida ta ce "A a barci take yi, zuwa bayan magariba ka sake k'ira, sannan ta tashi." "To" Ya fad'a a sanyaye. Yayin da Abida ta jijjiga kai ta ce "Duk taurin kanka Sai mun lausasashi da wuridin nan ". Ta kalli bilki6da take zaune ta ce "Maigado this very powerful du'a. Zamu fara yiwa yayanki". Bilki ta murmusa ta ce "Bayan kin k'wace mini shi Abida! Murmushi Kawai Abidan ta yi. Washegari sassafe zai fita a motarsa ya d'auki Bilkisu da Laura, suka kai ta har makaranta shi da tawagarsa ya k'i daukan Hafcy ya ce direba ya kai ta wanda hakan ba k'aramin damuwa ya jefa ta ba, karon farko da ya fita a harkarta don kuwa kowa ga ni yake yafi sonta. Har cikin gate din makarantar suka shiga da ita. Sosai Bilkisu ta ji dad'in wannan k'aramcin da Dady ya yi mata don ba zata iya tuna rabon da ya kawo su makaranta da kansa ba. Dan haka zata sake kamewa daga shiga rikicin da ba zai amfane ta da komai ba, tunda ta yi ba dawo da Momi zai yi duniya ba, ba kuma shine dalilin da zai saka ya auri anty Laura ba. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:32] Kaitsaye Kaduna suka nufa suka kai Laura har gidan gaban Hajiya, kaitsaye ya mata bayanin rikici suke yi da matar gidan tunda itama yarinyace zaman nasu ba zai yiwu tare ba. Dan haka a yi hak'uri amma har gobe shi ne ubanta dan haka ba abin da ba zai yi mata na hidima ba, komai ya shafe ta yana kansa zai yi, kada kuma a ji nauyin fad'a masa dukkan al'amarinta. Sannan idan maneminta da gaske yake yi to ya turo a yi maganar aure. Ya ajiye mata bandir din y'an dubu dubu sabbi k'al guda uku. Bayan kayan abinci da aka ta shigowa da su masu yawan gaske. Ba kuzari Hajiyar ta yi masa godiya. Ya yi sallama ya tafi. Hajiya ta ja dogon tsaki ta ce "Namijin hotiho sallamamme na namamajo ko yaushe Bilkin ta zama yarinya? Abu da tana da budurwar yarinya. Kawai ita ta saka ya koro ki tunda tana ganin da aure a tsakaninku, don babu yadda zata yi da su Aysha. Zaman lafiya kuwa babu shi a gidansa". Laura cikin kuka ta ce "Wallahi Hajiya "A kanta ne, dama ta fad'a mini "Sai ta saka ya yi mini korar kare ga shi kuwa don da asubar yau din nan da ya dawo daga masallaci ya ce mini na shirya zai zo Kaduna ta'aziya zai sauke ni a gida, su Ayshan ma gabad'aya ya fita a harkarsu cikin kuka na barta ita da Hafcy. Bilkisu da su Amal kawai yake kulawa." Hajiya ta sake jan dogon tsaki ta ce "Dama Bilkisu ba tamu ba ce tunda ya saka mata sunan shegiyar ai dole ta zama munafuka don kuwa suna na tasiri! Ta fad'a cikin k'unan rai. Ta sake zabura ta ce "Irin kuttun da Rukayya ta sha akan yaran nan ba dama ta doke su ko ta hana su cin abin da suke so ita da ta haife su ma, amma wannan ja'irar harbta samu lasisin karya Hafcynsa amma ta kwashe kalau, sannan har tana da kuzarin hana a yi musu girkin da suke so Duk yana kallo? Tabbas ita ta biyo sawun uwarta na dibar albarka, ban da ta fita ta shiga ta ga gidan daula ta karkato da hankalinsa da na ubansa har ya kalle ta mabare aure ya gitta a tsakaninsu? Ai ko Alhaji Musa ba haka ta bar shi ba, tunda kotu suka maka shi Allah ne yasa bai kanannade ba saboda tsananin bak'incikinsu da na shedaniyar uwarsu, ta ta baza mugun iri." Da kuka Laura ta ce "To Hajiya kawai ke ma ki shiga, ki fita ki wasko mini kansa dan Wallahi sonsa nake yi! Ta fad'a cikin kuka na tashin hankali. Jikin uwar ya yi sanyi tub'us. A sanyaye ta ce "A a Laura ba ni da halin da zan yi shiga da fita irin nasu, kinsan an ce kudi ne da ita, sannan gadonsu da aka raba ai ba k'aramin kuɗade da kadara suka samu ba. Irin wnanan don su kashe milyoyin kudi akan buk'atarsu ba komai ba ne. Ki dai yi hak'uri tunda Har ya kawo ki gabana da kansa ai kinsan tafi k'arfinsa Idan ma kin shiga ke ce a ciki. Ni kuwa da ki yi zmaan boranci a gun miji gara ki hakura, ki auri Wanda kike so ba Wanda ke kike so ba. Mu duk zuri'armu Bama boranci ba kuwa zan yarda ke ki fara ba, shi din ma AI kwallon shege ne wacce wuyar ce Rukayya bata sha a hannunsa ba? Kawai idan mace tana auren mai wadata sai a yi ta mata kallon jin dad'i. Amma yadda ya fifita ahalinsa akanta da yadda yana ganin ibilishiyar Abida take mata isgili kala kala, take wareta tana son sauran matan y'anuwanta amma ita tana kallonta kamar kashi kinsan dama ya bayar a taka Rukayya ai. Tunda ya ce kallon diya yake yi miki, to ki yi hak'uri ki yi kwance kwance ki ta tatsar ja'iri. Wurin azahar ya isa Abuja sai dai ba samu zarafin isa gida ba sai wajen azahar saboda a dalilin matsanancin goslow. Kaitsaye gidansu ya zarce. Cikin sa'a ya tarar da baba da Faruku suna zaune a babban falon dawowarsu daga masallaci kenan, ruwa ya goce. Jira suke yi jiran ruwan ya dauke Faruku ya raga Baban tattakin da yake yi da yammaci don sosia tlyake jin dad'in jikinsa idan ya yi atisaye din. A cikin motar ya bar yaransa a dalilin ruwa zai jikasu. Kaitsaye ya shiga cikin falon ya yi sallama suka amsa masa babu wani walwala. Jikinsa ya yi sanyi ya isa gaban Baba ya cire hularsa ya yi saluting d'insa sannan ya tsugunna yana gaishe shi. Baban ya amsa ciki ciki fuska a daure. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:35] Faruku ya mik'a masa hannu ba wani karsashi.a Nan da nan ya fahimci fishi suke yi da shi. Bai zauna ba yana durk'ushe Kan k'afafuwansa tamkar mai zaman tahiyya. Murya ba amo ya ce "Baba ya jiki dafatan baka cikin damuwa?" Baba ya harzuk'a matuƙa da gaske. "Cikin kunar rai ya ce "Kusunuwarka Asad! Ba Asad din da aka zaga ba, hatta Farouku zabura ya yi don kuwa basu taɓa jin ya yi zagi irin haka ba, duk kuwa da yadda ransa zai baci dama Baba k'arami ne ainihin Bakatsine shine yake danna musu ashariya kala kala. Hankalin Asad ya yi mugun tashi wannee irin abu ya yi mai muni haka da ya saka mahaifinsu fusata ya yi masa zagin da bai taba yiwa wani sun ji ba. A gigice ya ce "Dan Allah Baba ka yi hak'uri, a gafarce ni! Baba ya ce "Ni zaka yiwa wulakanci irin haka? Me kake da shi, waye kai?" Murya na rawa ya ce "Dan Allah a yafe mini Wallahi ban san me na yi ba". Ran Baba ya ce "Oh baka san me ka yi ba kake fad'a mini? Na d'auki yarinyar nan na baka bayan an sha dogon fama da ita kafin ta amince da kai shine da ka cimma manufarka sai ka mayar da ita banza da wofi a cikin gidan, ka k'ure hak'urinta ta taho wajena, shine ka yi zamanka idan na matsu zan neme ka da kaina saboda kana ganin kai wanine ko?" Murya ba amo "Ya ce "Ko kad'an ba haka bane Baba, amma na gamsu na yi laifi a duba Allah a yi mini afuwa, fishinka irin haka a kaina guba ce dan Allah Baba! Ya fad'a a rikice ainun. Nan da nan kuwa baba ya sassauta ya dinga yi masa nasiha tare da nuna masa illar gooyin gatan da yake yiwa ya'yansa da sunan tausayi. "Ka bari sun sangarce su an kai su d'akinsu su kasa zama lafiya da mazajensu saboda ba'a masu tarbiyar da ta dace da su ba". Kan Asad na k'asa ya ce "Duk na d'auki matakin gyarawa, in sha Allah Baba za'a ga sauyi, a mini hakuri". "To batun yarinyar nan k'anwar matarka lallai ta koma gaban gyatumarka duk abin da zaka yi mata na alheri ka aika mata zaman ya isa haka". Cikin nutsuwa ya ce "Yanzu ma daga Kaduna na ke da kaina na mayar da ita gida. Dan Allah Baba ka yi hak'uri". Baban ya numfasa ya ce "Ai yanzu tunda Bilki ta kwnaa biyu baka nemeta ba na gasgata Lallai Sulaiman ba ni kad'ai zai iya yiwa wulakanci ba Har Baba k'arami don kullum sai na yi kukan da mahaifinsa na da rai AI ba zai yi mini abin da ya yj ba, amma kai ma da gwada mini Sai na gane ashe fahimta ne ban yi daidai zai yi mini ko baban naku na da rai". Faruk6ya kamu da tausayin Babansu don kuwa babu yadda za'a yi rana ta fito ta fadi Baba Bai yi maganar Sulaiman ba, kullum bakinsa da zuciyarsa na ambatonsa amma Shi dan tsabar iskanci ya yi tafiyarsa ya bar kowa da kowa babu waiwaiye. Ya k'udire a ransa duk ranar da ya dawo gida tabbas sai ya saka saka dorina ya zane shi ciki da Bai yasan ba zai cukume Shi da fad'a ba, amma bak'incikn da ya kunsa musu ya kunsawa baba Babba ba zai tafi a banza ba. Sai ya tabbatar masa dan babu baba Karami ba shine zai yiwa Baba Babba wannan dibar albarkar kuma ya share kalau ba. Hankalin Asad ya kai k'ololuwar tashi ta ya ya baba zai kwatanta laifinsa da na Sulaiman din da ya shafe shekaru uku yana cikin ta hud'u da fantsama duniya? Kwanaki biyu kacal da bai zo ba, alhalin shima ta ci mutuncinsa, bayan haka ba cewa ya yi ta taho ba ai, inda wanine mijinta ya tabbatar a take za'a mayar da ita tunda zaman Abida a gabansu ba k'aramin dukansu yake yi ba gabad'ayansu. Murya babu amo saboda tashin hankali ya ce "Ka yafe ni Baba, na ci darajar manzon Allah! Gabad'aya suka ce "S.A.W.. Baba ya nisa ya ce "Na hak'ura amma lallai ka yi gyara a gidanka, ka san me kake ci, sannan lallai ba Aysha kad'ai za'a aurar ba har da Hafsatu , itama Khadijah da take London tunda bana zata gama duk a had'asu a kawar da su. Idan babu maneman sai a nemo musu". "To" Baba ya amsa a ladabce. Sannan ba zan ce Bilki ta koma ba, Faruku ma ba zai saka baki ba, ka yi mata magana da kanka idan ta yarda zata bika ku koma haka nake so, idan ba ta yarda ba to lallai zata cigaba da zama har zuwa sanda zata sami nutsuwa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:39] Asad a zuciyarsa ya ce "Ai kuwa Wallahi ba zan yarda da wannan hukuncin ba tunda tauye ni aka yi da nuna son kai". A fili muma ya ce "Na gode Baba Allah ya k'ara lafiya." Daga haka ya mike ya nufi d'akin Momi . Jikinsa ya sake mutuwa a dalilin a shake ta amsa gaisuwarsa har da yi masa shaguben ba zai hucewa Baba Babba takaici ba, tunda tun yanzu murnarsa ta fara komawa ciki na kyakkwan zaton al'amura zasu daidaita a dalilin aurensa da Maigado. Ya dinga bata hak'uri. Ta ce ita ba ruwanta amma tabbas ba zata saka baki Maigado ta koma gidansa ba tunda ba tsarin musulunci yake bi wajen yiwa yara tarbiya ba. Idan ya shawo kanta ta huce ta ce zata koma shikenan. A sanyaye ya bar dakin ya nufi na Abida. Ya ga bata nan. Ya tuna Ashe bata dawo daga asibiti ba. Ya fito ya shiga na Maigado ya tarar tana kwance. Ya Kira sunanta yafi sau biyar ta yi bakam ita ala dole barci take yi. Murya a dakushe ya ce "Duk wulakancin da kika yi mini na zargina da yarinyar da nake yi mata kallon d'iya hakan bai isa ba sai kika saka k'afafuwanki kika bar gidana babu iznina, kika dauko diyarki, kika watsar mini da yara. Sannan kika mini sanadin fishin Baba da Momi ko?" Ta yi shiru tana sauararensa zuciyarta ta fara karyewa don yadda yake magana babu kuzari tasan a rikice yake ainun. *Surayya Dee* PAGE 7 ✍ [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ta cuno baki cikin fishi na sosai ta kawar da fuskarta daga kallon gabas ta mayar zuwa arewa. Ya sassauta ya sake matsowa kusa da ita sosai ya ce "Zo mu tafi gidanmu kin ji Maigadona. So nake yau mu jijjiga gadon zinaren nan na ki da kyau. Ta so mana ai na ce ba zan sake ba, ki huce dan Allah kin sa duk ahalin gidan sun dau fishi da ni ba kuma wanda ya yi nufin taimakona a cikinsu." Ko uffan bata ce ba. Ya gurfana a gabanta ya ce "Zo ki d'are na goyo ki, mu tafi gidanmu". Dariya ta subuce mata, dattijo da shi zai wani ce ta ta zo ta d'are alhalin Baba babba ko momi zasu iya ganinsu. Wato dai shi namiji babu ruwansa da kunya. Ta kawar da fuskarta tare da ce wa "Ba fa zan koma ba, ka yi tafiyarka, na riga da na gane ba zan iya wannan zaman ba. Ban iya yaudara ba, idan ma na iya ai ba zan yaudare ka ba Baban Bilkisu! Ka yi hakuri kada maganar nan ta sake cakalcakala mana al'amarinmu". Ya mike tsaye cak. Ya zuba mini idonsa na saci kallonsa na ga har wani tsumuwa yake yi watakila da wani k'aramin d'an sanda ne ya bata masa rai da ya d'and'ana kudarsa domin ya fusata ainun. Da kakkausan harshe ya ce "Kawai dama dai ki ce auren manufa kika shirya yi da ni?" Ya yi mata kwarjini k'warai da gaske, tsoronsa da ta rayu da tashi ya taso mata. Ta kasa ce wa komai. Jin bata ce komai ba ya sanya ya sake maimaita tambayar da ya yi tabbacin amsatra yake dako. Murya na rawa ta ce "Ba Hakan bane ko kadan. Ban same ka a yadda na zace ka bane. Na dauka ka aure ni dan kana sona kana kuma burin ka rayu da ni cikin adalci da jink'ai tare da wanke mini dukkan bak'inciki da na kwankwada. Sai dai tun tafiya bata yi nisa ba na gane manufar aurena bata wuce ace kana da iyali a idon jama'a ba, sai kuma dan ka sauke buk'atarka a duk sadda ka so. In ka cire hakan babu wani dalilin so, ko tausayina a tare da kai da na ga ni a aikace idan kuma akwai to tuna mini dan ni ban gansu ba." Ya numfasa ya ce "Amma ai na ba ki hakuri, na ce zan gyara dukkan laifukuna, indai ba wani abu bane a ranki ai sai ki bani wata damar, idan ba ki ga sauyi ba, na amince da kaina zan dawo da ke gaban Baba babba cikin mutunci za'a yi komai tamkar yadda ya ba ni ke cikin mutunci. Da hankalinki Maigado ba za ki taimake ni ba, gabadaya fa daga Momi har Baban fishi suke yi mini. Ba akan komai sai a kan ki" Hawaye ya b'alle mata ta ce "Saboda hakan ai na ce zan tafi na kama haya, ba zai yiwu na ce ba zan zauna da kai ba, sannan na zauna a gabansu indai ina da kunya da mutunci " Kuka sosai ya k'wace mata, yinsa take yi tunda ga k'asan zuciyarta. Tare da ayyana dama dai ta yi hakuri ta rayu da y'ay'anta, da ta yi hakuri bata tirsasa mijinta ya sake ta ba, da yi zamanta a gidanta ta rayu da ƴay'nta. Idan mijin ya zo fine Idan bai zo bama fine. Don ta riga da ta saba da rik'e gida, dan haka ba zata gaza ba. To ko bai kawo komai ba. Tana da rufin asirin da zata rik'esu ba tare da ta ji komai ba. Amma yanzu ta bar yaranta suna ragaita a hannun yarinya k'ank'anuwa, ta zo tana hidima da yaran da suke ganinsu daidai da ita sannan babu godiya ko yabo a wajen mahaifinsu. Kukan da take yi, ya yi matukar tayar masa da hankali domin dai ba yaro bane ya fahimci kukane na tsantsanin damuwa. Kukane mai nuna kololuwar gajiya da kunsar bak'inciki. Jikinsa ya yi sanyi sosai ya ce "Dan Allah ki yi hak'uri! Gaggawa fa kika yi, dama zan d'auki mataki kuma yanzu haka fa na mayar da Laura gida tunda kin ce ba zata zauna miki a gida ba. Ki yi hak'uri ki yi mini uzziri." Ita dai bata iya bude baki ta ce masa uffan ba. Ba kuma ta ji a jikinta zata motsa bare ta ba shi amsa ba. Don kuwa ita dai ta riga ta gaji da yadda take rayuwa cikin gidansa. Ya yi rarrashi, iya rarrashi amma bata tanka ba. Ya gaji ya zauna yana fad'in "Innalilahi wa inna ilaihir rajiun! Ya dafa kansa da alamu suka nuna juya masa yake yi ko kuma ciwo mai tsananin gaske. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Murya babu amo, kuma cikin bacin rai ya ce "Da kina sona Bilki na tabbatar za ki yi hakuri da dukkan laifukana, za ki jure, bare na ce ki yi hakuri zan gyara. Amma kin kafe na tabbatar da ace Faruk kika aura za ki yi hakuri da matsalar da tafi wannan tsanani a tare shi, na kuma yi imani kin ci karo da matsalolin da suka fi wannan nauyi da tozarci a cikin aurenki da yaron can, amma ba wanda ya taba ji ko ganin kin yi yaji kin bar gidan duk da k'arancin shekarun da kike da shi a lokacin.! Duk da a cikin kuka take sai da maganganunsa suka yi mata dabaibayi, suka nemi d'arsa mata tausayinsa tare da haifar mata da sanyi jiki magashiyan. Bai jira jin ta bakinta ba, ya sake tsananta rukon hannunta ya ce "ki ji tausayina Maigado. Kin sani tun kina budurwa nake son ki, dan haka zancen ki ce ba dan ina sonki na aure ki ba ai tatsuniya ce kawai irin ta shifcin gizo. Don a lokacin haihuwar Bilkisu da kin ba ni dama da tuni na aure ki. Amma kika bijire mini, kika yi tamkar ba ki gane inda na dosa ba. Na tabbatar zuwa yanzu an kwashe shekaru kusan sha takwas, idan kuwa hakane ai bai kamata ki ce bana sonki ba, ko da wasa ba kuwa, domin Wallahi tunda ga lokacin har zuwa yanzu ban huta da bugawar zuciya a dalilin soyayyarki ba. Na tabbatar Ubangiji ne ya musanya mini da ke a daidai lokacin da ya yi mini jarrabawar mutuwar uwar ya'yana, tunda ya sani ya jefa mini soyayyarki mai yawa a zuciyata, idona da gangar jikina gabadaya." Na sassauta kukan da nake yi domin yadda yake magana kasan yana yi ne cikin tsantsar k'arfin zuciya. Domin tamkar ya rushe da kuka. Tsawon lokaci ina shesshekar kuka yayin da ya yi bakam yana saurarona. Can ya numfasa ya ce "Tashi mu tafi". Ko kwakkaran motsi ban yi ba a karo na biyu. Ya saki hannuna daya ya dago hab'arta ya zuba mata ido sosai, itama ta zuba masa nata idanuwan da suka yi luhu luhu, suka yi jawur tsabagen kuka. Ya yi kasa da murya ya ce "ki yi hakuri, daure mana, ki ji tausayina, idan har ke da kike jinina kin gaza akan lamarina da yarana wa kike tunanin zata rungumemu? Ba ni dama guda daya tak idan har ban sauya ba na amince da duk hukuncin da zaki dauka. Ina son ki, ina son rayuwa da ke, dan Allah ki daina tayar da hankalinki, me yasa kike son mayar mini da abin da yake cikinki sabon maraya, zuciyata zata iya bugawa idan ke ma na rasa ki tamkar yadda na rasa Rukayya. Hawaye ya sake balle mata domin tabbas ya bata tausayi ta yadda ya raunana kwarai da gaske. Ta kuma gasgata shi mutum ne mai k'arfin zuciya na gaske. Ya zaro tissue a aljihunsa ya hau goge mata hawaye yana ce wa "sorry Maigadona, very sorry! Murya babu amo ta ce"Zan kwanta sai da safe" Ya ce "Na dauka fa zamu tafine Sarauniyar shaiba! Ta girgiza kai ta ce "ka yi hakuri kaina ciwo yake yi, kasan kuma likita ya ce na dinga yin barci a wadace." Nan da nan ya hau gyara mata gadon da shimfidarsa take a hargitse. Ta bishi da ido tana kallon yadda yake gyara mata gado mutumin da zai iya ajiye zaratan yan sanda dubu su yi masa. Amma da kansa yake yi cikin rawar jiki da son ta ga gwanintarsa. Ya dawo kusa da ita ya ce "za ki shiga bayi ne?" Kai ta girgiza tunda fitowarta daga bayin ke nan ya shigo. Ta mik'e ta d'ingisa ta hau gadon domin ji ta yi ƙafar ta yi mata tsami. Ya tofe ta da addu'o'i tare da shafe mata jikinta. Tana jinsa yana ta faman laluben k'irjinta dan ya gane sune weak points ɗinta. Ilai kuwa nan da nan jikinta ya amsa ta nemi birkicewa. Sai kuma ta yi jarumtar saka hannu ta make masa tare da ce wa "Bana so, da iyayenmu a tare da mu kake yi mini haka?" Ya mike daga durk'ushen da ya yi, murya babu amo ya ce "Na tafi Maigadona ki yi hakuri ki huce so nake gobe na zo mu tafi gidanmu. Kin san ba ni da juriya akan ki Balqees ki taimaki yayanki kin ji". Ta gyara bargon sannan ta ce "Ni fa ba zan koma ina kallon yadda ka zuba ido yara na mini yadda suke so ba, ba zan koma kana daukan alamuran da suke hakkinane kana basu ba. Wannan shine gaskiyar magana ". [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ya fesar da iskar damuwa ya ce "Amma na ce "Zan gyara ko? Akan me ba za ki ba ni dama ba? Na gamsu na yi kurakurai, na kuma yarda zan canja menene kuma ya yi saura indai ba tada zaune tsaye kike so ba! Ya fada cikin fishin da yake ta danne shi kar ya k'wace masa. "Hmm" kawai ta furta dan kuwa ba yarda zata yi ta koma ba, sai an baje maganar nan a gaban manya. Ta riga da ta fahimci kawaicinta ba zai yi tasiri akan lamarin yaran nan ba. Ba wacce take mamakinta irin Hafcy. Yarinyar da shekarar da aka yi aurenta yar yayace, tare da tuna irin soyayya da take a tsakaninta da Hafcyn har su Aysha amma wai yau sun yi girman da suke ganin bata kai ta zame musu uwa ba. Sun washi su bude ido su ga babansu ya shiga al'amarinta ko dakinta. Tunda dangin uwarsu sun zugesu, tare dafad'a musu rabon aurenta ya kashe musu uwarsu. Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba. Ta idar da azahar ke nan ta koma gado k'arfe shida na asuba. Wayarta ta dinga gumza(vibration). Ta saka hannu ta duba ganin Baban Bilkisu ne ya sanya ta ajiye wayar ba tare da ta amsa ba. Amma tana katsewa k'iran ya sake shigowa. Ta dauka ta yi masa sallama murya babu amo. Cikin taushin harshe tamkar ba shine ya tafi da fishi ba jiya. Ya ce "Maigadona tafiya ce ta kama ni kwatsam zuwa Calabar dan Allah, dan Allah na roke ki, ki raka ni domin kowa da matarsa za shi. Ki mini wannan rufin asirin sarauniyar shaiba. Na gamsu na amince idan mun dawo nan zan dawo da ke ba gidana ba" . Ta yi shiru tana tunani tare da nazarin yadda zata ce wa su Baba zata yi masa rakiya alhali ta ce musu ta gaji da zama da shi. Ya tausasa harshe ya ce "Pls sarauniyar shaiba ki kubutar da ni kunyata a idon magauta. Taron karramaq manyan jaruman tsaro za'a yi ki taimake ni, alk'awari na yi zan dawo da ke inda na d'auke ki." Ta numfasa ta ce "To me zan ce wa su Baba?". Da sauri ya ce "Kawai ki fad'a musu na roke ki za ki raka ni Calabar za'a yi bikin karrama mu". To yaushe za'a dawo? Yini ne kawai, ya yi tsananin gaske ne a tsallaka gobe". Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To". Dad'i ya ratsa shi yana ganin nasara a k'udurinsa. Ya ce "Ki shirya jirgin k'arfe goma na safiyar nan zamu shiga. Zan sanarwa da su Baba. Me da me zan dauko miki?" A sanyaye ta ce "To". Dan gaskiya ta yi missing d'insa da kalolin jagwalgwalonsa masu tsuma zuciyarta da gangar jikinta gabad'aya. Ta zarce da fadin "Sabbin abayas din nan da ka siya mini a wajen Umm Aslan mai Egyptian abayas har da rigar barcin nan da ka ce ta yi maka kyau". "Na gane su, rigunan barcin ma ai kamar a wajenta ne ko?" Ya tanbaye ta a hankali. "Eh duka a wajenta ne lokacin da muka je Eggypt, ka tuna har da su jewelleries da su jakunan mata na k'asaita". Ya amsa da fadin"Ai zan sake siya miki wasu don ina matuƙar son products din da take siyarwa dukkan kayanta da wahalar gaske ka ga irinsu a wani waje." A hankali ta furta na gode. Tare da fad'in zan yi barci ko na 1 hour ne ". Ya ce "Amma ki tashi kafin takwas don ki shirya, zan zo kafin tara kin ga kafin mu isa iyafot ma tafiya ce mikakkiya." Murya babu amo ta ce"To" Alarm ta saita ya tashe ta k'arfe 7:45, ta ajiye wayar a gefe sannan ta gyara ta yi kwanciyarta. Bata fita ba sai da ta yi wanka ta shirya tsab , cikin jikinta ya bayyana alamun ta fara nauyi ke nan. Sosai ta yo kyau, filazal bata rabuwa da materials din Umm Nihla. Don sosai take jin dad'insu bare yanzu da ta yi nauyi ba abin da take sanyawa sama da su, shafal suke babu zafi babu takura. Gasu farashinsu daidai da aljihun kowa ne. Yanzu haka ma tattaunawa take yi da ita akan ta dinga turo mata daga Malaysia ta dinga siyarwa a Abuja tunda duk wacce ta ganta da shi sai ta tambaye ta a ina zata same su?" Gara kawai ta dinga sarowa tana siyarwa. Malaysianfabrics raina kama ne. Tana rike da jaka da ledar kayan da ta zuba, sai kuma ta fara tunanin yadda zata fadawa musu zata yi masa rakiya zuwa wani gari. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Kan dole ta fita ta tarar da su a falo. Ta zauna a kan kafet yayin da su suke kan kujera. Cikin nutsuwa ta gaishesu. Sai kuma ta kasa cewa komai. Cike da kulawa Momi ta ce "Ki je ki zuba abin karyawa a kicin ya ce zai zo ya kai ki, ki ga likita daga can zaku je Calabar amma yau zaku dawo". Ta yi shiru tana tunanin ni ya ce mata zasu kwana d'aya zuwa biyu. Su kuma ya ce musu tafiyar yini ce. To ko dai basu fahimta ba ne?. Ta furta hakan a fili. Na tarar da Alti na dama kunu mai aikin Momi na soya dankali turawa dan Jos wanda kaitsaye dukkan ahalin suke siya duk abin da ya shafi dankali d doya da kuma kalolin vegies daban daban ta hannun Haj Rumanatu shugabar Raudatul Jannah foods Jos. Kai dankalin Jos duniyane don shine asalin dankali mai dad'i. Da girmamawa ta ce Mamah ina kwana?" Ta amsa cikin mutuntawa don kuwa dattijuwa ce sosai fiye da Alti. Da azama ta dauko plate ta zuba mata wanda ta kwashe. Ta sake dauko bowl ta zuba mata ferfesun kaji. A dining din da yake kicin din ta zauna dan haka da ta bata sai ta ta cika katon kofin tangaran da kunun gyada. Tana fadin "na sanki da son kunun gyada". Bilki ta murmusa ta ce "Na gode kuwa". Cikin nutsuwa take karyawa. Sai da ta kammala ya iso. A gurguje ya gaisa da su Baba a dalilin lokacin tashinsu ya kusa. A sanyaye ta yi musu sallama ta wuce sukuku, tamkar marar gaskiya. Haka kawai take jin wani irin yanayi na takura a tare da ita. Ba dan tana kewar jagwalgwalonsa ba da ba inda zata bishi. Sallar azahar a hotel d'in da suka sauka suka yi. K'afafuwanta suka d'an kumbura kad'an saboda dogon zaman da ta yi. Da suka idar ya zauna ya dinga matsa mata k'afafuwanta sannu a hankali. Yana yi fad'in "Sannu Maigado." Yayin da take jin dad'i na ratsa ta tunda ga tafin k'afar har kwanyarta saboda dalilai biyu. Na farko ta yi kewarsa ba dan kad'an ba, na biyu kuma ta yi amannar shi baya cikin masu biye biyen mata. Sosai ya tsiyayarata da ruwan kanta ya mantar da ita wai fishi take yi masa. Kwanansu biyu suna holewarsu tamkar kwanakin farkon amarcinsu. Kwanansu biyu bata ga ya je ko ina da sunan taro ko meeting ba. Tunda suka dira d'akin hotel din bai fita ba, tunda babu masallaci a wajen sai sune idan sun ga lokacin sallah ya yi yake janta su yi tare. Wannan zaman da suka yi sun shaku da juna ainun, zuciyoyi sun huta, sannan kuma sun kashe wa juna k'ishin kewar junansu. Kwana na uku tana kwance a k'asan kafet ta yi filo da cinyoyinsa ta ce "Baban Bilki yaushe zamu koma ne tunda na lura ba wani aikin da ya kawo ka?". Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Marmarin jihar Cross River ne ya fitine ni kinsan birinin mai dad'i da kyau, shekarar da aka yi aurenki aka dawo da ni jihar nan, a lokacin ina cikin tsananin gaske a dalilin rashinki sai gabad'aya garin ya yi mini kunci a dalilin zuciyar a kuntace take. Ban wani ji dad'in zaman ba, shekaru biyu na fara warwarewa sai kuma aka tura ni jihar Ebonyi. Shine yanzu na dauke ki don na rayu da ke na wasu kwanaki a garin da na yi ta kukan rashinki a boye babu kakkautawa ". Ta murmusa ta ce "Hmm ai cuta ta ka yi, da baka bayyana da k'arfinka ba, ka tsaya yin raragefe, ni sai na dauka tsoron matarka kake ji, nima kuma ga ni na yi a lokacin ta fini ilimi da shekaru, ga yara ta haifa maka ai wahalar gaske zan sha idan na shiga cikinku". Ya ce "Ke dai kada ki fake da wannan kawai Baban Su Amrah ya yiwa zuciyarki kamun kazar kuku idonki ya rufe, sannan da yawa mata ai ba kwa son mai mata! Da kin amince da kin gane ba abin da zai hana ni sonki, Idan an kere ki da wasu abubuwan ai ke kuma kina da k'uruciya, kinsan alfarmar k'uruciya kuwa?" Ya girgiza kai tabbacin al'amarin babba ne. A ranta kuma ta gasgata shi don itama ta ga tasirin kuruciyar yadda Sahal ya dinga rawar jiki akan Hawwah. Sai dai shi Yaya Asad ya yiwa matarsa adalci tunda mutuwa ce ta rabasu duk yadda ake ganin Sahal da kad'an ya girmeta to tazararta da Sahal tafi tazarar Asad da Rukayya don kuwa shekara d'aya tak ya bata shiyasa Abida take ce mata Anty Gyatum. PAGE 8 [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Da wayo da hila da gwada soyayya mai zama a zuciya sai da suka yi kwanakin sati. Ko maganar su tafi ma bata yi. Sai dai Akai akai ta kan ce Farha na can na kukan nemana. A duk sadda ta fadi hakan kuma baya tankawa, asalima sauya fuska yake yi. Idan su Amrah sun k'irata a waya yana karba su gaisa ya yi ta yi musu tambayoyi akan karatunsu da kuma menene matsalarsu. Amma maganar Farha baya um bare um um. Jiya ma da Alti ta k'ira ta had'a su da ta ce a bawa Dady bai amsa ba, ya ce dai yana gaishe ta. Har zuciyar Bilki bata kawo komai ba. Ranar da zasu koma Abuja daidai da satinsu guda. Ya kalle ta ya ce "yanzu sarauniyar shaiba duk yadda kika dinga makale mini ba zai saka mu wuce gidanmu kaitsaye ba, duk kirkin da na yi miki, kalli fa yadda kika zama tamkar yanzu za ki haihu? Kawai mu wuce gidanmu washegari sai muje mu gaida su Baba mu ce musu mun shirya! Ta girgiza kai ta ce "Daga rakiya sai na ce musu na koma gidana alhalin na ce musu na gaji ba zan koma ba, gaskiyar magana kunya ma zan ji, kawai ka bari sai na haihu din". Ya jijjiga kai yana gasgata bata da wayo. Ban da rashin wayo akwai kunyar da ta wuce ta koma musu gidan bayan ta biyo shi ta yi sati guda tare da shi, sannan ta koma da sunan cigaba da zama a gabansu. Amma bari ya zuba ido ya ga yadda zata kwashe tsakaninta da Baban nata da ya zuba mata ido take yin yadda ta ga dama, kafin ta dawo ya mata hukuncin da zata dinga sanin me zata dinga furtawa a gabansa. Ya rausayar da kai ya ce "Shikenan Maigado amma kada ki dinga kashe wayarki, sannan duk ranar da zaki je awo zan zo da kaina na kai ki, idan an kammala sai mu je mu na gaisa da unborn, tunda kin nesanta ni da jinsa duk sadda na so". Ta sinne kai tana murmushin kunya da jin dad'i. K'arfe goma na safe suka dira a airport din Nmadi Azikiwe da yake birinin tarayya. Motocin y'ansanda sun kai shida da suke takewa tsaleliyar motar da suke ciki baya. Shadaya daidai a kofar gidansu ta yi musu. Har cikin gate din motar da suke ciki aka shigar dasu, yayin da motocin yan rakiya ya ce su tsaya a wajen. Daga bakin falon ya ce "Ki gaishe su da kyau. Sai dare ko gobe zan zo na gaishe su, offiice zan wuce ana jirana da gaggawa". Ya mik'a mata jakar kayanta. Ta karba a sanyaye don so take ya rakata cikin, saboda tana sauka daga motar ta ji kuma wani abu mai kama da kunya na bibiyarta. Daga tafiyar yini ko kwana d'aya ne ta kwashe kwanaki bakwai? "Dankari". Ta furta a bayyane. *Surayya Dee*[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:10] Kuka ya k'wace mata don bayan kunyar da ta yi mata dabaibayi kalaman Baban sun yi mata tsauri matuƙa da gaske , haka nan idon da su momi suka zuba musu ya sake muzanta ta ainun. Baban kuwa bai kula da kukanta ba don sosai ya ji haushin sakarcinta ya kuma lura idan ba tausayinta ya cire a ransa ba to ba zai ga yadda yake so akan aurenta ba, tunda har Asad ya gwada masa irin wannan rashin kunyar cikin dabara, to nan gaba ba abin da ba zai yi ba, na nuna iyaka. Da b'acin rai ainun ya ce "Ashe sadda kika zo nan kika ce mini na zubawa Abida ido ban mayar da ita d'akin mijinta ba rashin kunya kika yi mini, ba wai fad'a mini damuwarku kika yi a matsayina na ubanku ba! Yana rufe baki ta bude baki ta rushe da kuka sosai don gabad'aya bak'in cikin Asad da kunyar duniya ne suka rufar mata. Baba ya yi waiwaiye bai ga wani abu da zai dauka marar illa da zai makata ba. Don haka ya zakudo ya dawo bakin kujerar sosai ya saka dukkan hannuwansa biyun ya rik'o dukkan kunnuwanta ya murd'e da k'arfi tar da fad'in "Rufe mini wannan ja'irin bakin na ki, dukanki na yi ko me?" Ta sassauta kukan ya ce "Borin kunya kike yi tunda kika yarda kika bi miji hotel akan idona, amma kika k'i binsa gidansa. Yanzu kenan duk sadda yake da bukatarki zai zo ya dauke ki, idan ya gama sai ya dawo mini da ke tunda haka kika zabar mana ni da ke ko?" Tashin hankali ya sanya jikinta b'ari ga kunnuwanta na hannunsa , kamar zai cire mata su, azaba ta sanya kukan ya tsaya cak, illa zufa da take yanko mata. Tunda take a duniya bata taɓa tozarta irin yau ba. Bai saki kunnen nata ba ya ce "Ba za ki zauna mini a gida ba, yanzun nan ki k'ira babban ja'irin ya dauke ki, don na tabbatar bai yi nisa ba, ba wani office da zai je. Sannan bana son na kuma ganin k'afarki a gidan nan har sai na bukaci ganinki da kaina. Idan kin so ki ce na yi son kai. Idan kin so ki zauna lafiya da mijinki da iyalinsa, idan kin so kuma ki gudun, ki je, ki yi zaman kanki tunda na fuskanaci taketakenki na raini a kaina. Zan zuba miki ido irin yadda nake zubawa duk wacce na bawa umarni ta kafe akan ni zan bi ra'ayinta saboda tana ganin ta yi ilimi mai zurfi". Nan da nan Abida ta muzanta tare da shiga wani irin tashin hankali farat d'aya. Don kuwa lah shakka wannan karatun nata ne. Cikin kuka na sosai Bilki ta ce "Dan Allah Baba ka yi hakuri". Murya ba amo ya ce " Zan huce da ke ne idan na ga mijinki gurfane a gabana yana yi mini godiyar ba shi aurenki da muka yi. Zan huce da ke idan kin kwantar da hankalinki tare da bada gudunmawar daidaituwar zumuntarmu. Kina tunanin idan su Ansari suka ji kina jele tsakanin gidanki da nawa gidan da sunan bacin rai zasu sassauto gabad'aya ne su sake mayar da ni ubansu?" Cikin kuka ta ce "Baba kai ubanmu ne babu abin da zai sauya hakan ". Ya ce "Kayya Maigado ke din dai da kuma Saddiqa haka ma Ansari yakan gaishe ni idan ya bushi iska amma Sulaiman Hamida Abida Anisa da Ansari kullum da bak'incikinsu nake kwana nake tashi. Indai na mutu a yanzu tabbas suna da alhakin mutuwata, ki yi a hankali kada ki shiga sahunsu a idona da zuciyata". Hawaye ya dinga tsere a fuskarsa a sanyaye ya saki kunnawanta ya koma cikin kujerar sosai ya jingina. Jikin kowa ya mutu ba abin da ake ji sai gunshekin kukan Maigado da na Abida. Abida a ran take jin zahirin wanda Baba yake so duk cikinsu daga su har su Sulaiman gabad'aya Bilki ce. Ita ya tsaya mata kada aurenta ya taɓarbare, yayin da ita ya barta ta yi yanda take so, da komai ya k'wace mata kuma ya koma tsakaninsa da ita ido ne, komai ta ce zata yi to kawai yake cewa, haka momi wannan zurun da suke yi mata tare da bata cikakken dama da y'ancin ta zaɓarwa kanta yadda zata yi da rayuwarta ke saka ta kuka kullu yaumin, tunda ta yi gardamar ba zata zauna da Sulaiman ba, aka kyaleta har yau babu wani da Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:14] ya taba yi mata batunsa ko nuna tausayawa ga HALIN YAU din da take ciki. Yaya Asad ne kawai shima sai da ya fara zawarcin Bilki yana son ta shawo masa kanta, ya sanya yi mata alak'awarin za'a fara binciken inda yake, ga shi har matarsa zata haihu bata ji komai game da batun ba. Ita kam tana ganin tasku da ainihin kuttun namiji. Kuka ta yi shi irin wanda bata taɓa zaton wata mace ta yi irinsa ba. Ba abin da ta nema ta rasa, amma bata samun walwalar iyayenta irin na da duk da basu taba ce mata komai ba. Amma yanzu ta fahimci tana cikin garari tunda duk yadda take a wajen Baba ya saka ta cikin wadanda suke tayar masa da hankali, suke k'ulla masa bak'in ciki. Don haka zata fara neman Sulaiman duk inda yake a duniya, idan ta gan shi kuwa sai ta shekara bata zo gidan ba sai dai waya, ko zai dinga dukanta kullum kuwa, zata yi hak'uri ta zauna a d'akinta duk runtsi. Har sai BABA ya je nemanta da kansa in sha Allah Baba ba zai mutu da bakin cikinta ba. Tsawon lokaci suna kuka ba wanda ya ce musu kanzil. Bilki na ayyana wannan rayuwa da wahalar gaske take. Babu wani cikakken jin dad'i. Gabad'aya k'alubalen da yake cikin rayuwar yafi jin dad'insa yawa. Ba macen da zata ganta ta zaci tana da matsala a gidan aurenta. Ga tsalelen gida, ga tsaleliyar mota, ga ingarman miji mai rike da madafan iko, ga lafiya Allah ya bata ga kuma satisfaction, ga niimar haihuwa. Amma kuma sai aka jingina mata k'alubalen fuskantar kiyayyar y'ay'an mijin da ubansu yake tsananin sonsu. A da ta d'auka idan ta rabu da Sahal ta samu wanda zata dinga samun satisfaction to duk wata matsalar da zata zo ba zata d'auke ta a a matsayin damuwa ba. Ashe ba hakan ba ne, mutum na girma matsalolinsa na sake bunkasa, matsalar y'ay'an mijin da babu uwarsu babbar jarabawace da ba mai gane girmanta sai wadanda suke cikin matsalar, gara yaran masu uwa, idan har sunada tarbiya Kuma suna mutunta uwarsu AI dole su mutuntunta Matar ubansu, Idan kuwa basu da tarbiya basa mutuntata uwarsu ai shafawa Kanka ruwa zaka yi ka Koma gefe ka yi kallon yadda sakayyar rayuwa zata hau kan kowa. Da ace Rukayya na da rai suke mata irin haka, to da ita kuma a kanta zata rama iyashegensu tunda itace abokiyar burminta, idan y'an arziki ne sai su kiyaye ta. Amma yanzu ba yadda zata yi sai fatan Allah ya kawo musu miji su je suma su fara fuskantar yadda rayuwar take, tunda haka rayuwar take kowa hak'uri yake yi da yadda k'addara ta zaba masa. Allah dai yasa mu wanye lafiya kawai. Cikin muryar umarni ya ce "Ki tashi ki koma d'akinki, Alti na gidan Faruku sai jibi zata dawo matarsa ce ta je biki shine ta je ta taya yar aikinta kula da yara. Jibin ko gata direba zai kawo ta tare da d'iyarki". Ta kasa tashi tsabar kunya da nauyin da jikinta ya yi mata na tausayin Baba. Gabad'aya k'arfin hali yake gwadawa akan su Yaya Hamida da suka share shi. Cikin kuka ta ce "Dan Allah Baba Yaya Faruku ya raka ni". Murya babu amo ya ce "Ba zai raka ki ba, shi ja'irin mijin naki ya zo ya dauke ki, ko ki shiga ki dauko mukullin motarki ki tafi ai kinsan hanya". Sai lokacin Momi ta ce "Alhaji da dai ka yi hak'uri ya kaita din, ba zata iya tuki cikin nutsuwa ba, kuma ta inda aka hau, ai ta nan ake sauka. Shi ya kawo ta ranar da ta yi yajin, yanzu don ya mayar da ita ai babu komai, daure dai Alhaji kada ta tafi ita kad'ai." Baban ya ce "Yadda ta fito haka zata koma, ina ce a gabanmu ta wuce ta bi miji uwa duniya, don zata koma gidansa ita kad'ai sai ya zama abin jin nauyi? Kin san Allah Asad na k'ofar gida yana jiranmu ni da ita. Ai wannan abin da ya yi sakone mai harshen damo ya yi mini, kin ga ai ya fahimtar da ni da yaren da na ji shi har cikin k'wanyata. Momi ta kasa magana don gabad'aya kunya Baba yake bata a gabansu. Yayin da shi kuma ko a jikinsa yake ta nanata rashin kunyar Bilki da rashin mutuncin Asad. .. Sai lokacin Yaya Faruku ya bude baki ya ce "Baba da ka yi hak'uri dai na rakata, Allah bar shi idan na gan shi a wajen ko a hanya sai na ba shi ita su tafi". Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:17] Baba ya jijjiga kai tare da fad'in "Oh oh ikon Allah sai mutuwa ta d'auke Babanku ni kuma aka bar ni ina ganin waki'a iri iri Faruku! Cikin tausayawa Yaya Faruku ya ce "Allah ya jiƙansa, kai kuma Allah ya baka ladan hak'uri Baba ". Murya babu amo ya ce Ameen Faruku! Allah ya yi maka albarka, ya yiwa dukiyarka da zuri'arka albarka, kai kadai gayya ne Faruku. Abida da Bilki suka yi tsuru tsuru don kuwa gabad'aya jikinsu ya sake yin sanyi tare da sha'awar ina ma sune Yaya Faruk. Kafatalin gidansu Yaya Faruku abokin kowa ne maza da mata kuwa. Duk wanda yake son yi shawara ta sirri to ya tuntubi Yaya Faruk. Har yanzu da shekaru suka rufar masa shiga cikinsu yake yi ana hira ana tafawa. Idan kuwa aka ha fishinsa to lah shakka ba k'aramin al'amari bane kai da wuya ma. Duk yadda rikicin Ladi farms ya yamutsa hazo wani mahaluki bai ji tarinsa akan batun ba. Shi dai kula da lafiyar baba ya mayar da hankalinsa tare da da kwantar masa da hankali akan ya yi hak'uri kowanne d'anadam akwai inda Allah yake jarabtarsa don gwada k'arfin imaninsa, haka nan shi kad'ai ne bai nunawa su Sulaiman b'acin rai ba ko da kuwa a fuskarsa, don ko Munira da take da kusan irin halayyarsa an fahimci fishinta a wanccan lokacin. Da muryar kuka Bilki ta ce "Dan Allah Baba ka ja masa kunne akan zubawa yara ido suna cin mutuncina amma baya iya tsawatar musu da sunan tausayinsu." Baba ya tausasa harshe ya ce "Na yi masa, zan kuma sake yi masa, kuma idan har kika koma ba ki ga canji akan mu'amalarsu da ke ba, kaitsaye ki faɗawa Faruk zai kawo ni har gidan. Ko ki k'ira ni kaitsaye ki fad'a mini ko ki faɗawa mominku." Ya kalli momi ya ce "Dauko mata zamzam din nan na d'akina". Momi ta tashi da sauri ta nufi d'akinsa. Ya ce "Kina tashi a barci ki fara shansa, idan za!ki kwanata ma ki sha, In sha Allah za ki haihu lafiya kuma abin da za'a haifa zai zama mai fikira. Momi ta fito d'auke da babbar robar 5litr cike da zamzam ta bata. Faruku ya mike ya ce "Kawo na dauka ai zata yi miki nauyi". Ba musu ta bashi. Ko sallama bata yi ba ta juya ta tafi Momi ta bude murya ta ce "Ki k'ara hak'uri kin ji". Yayin da Baba ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. A fili kuma ya furta "Allah ya daidaita al'amarin da kansa, Yara na neman fasa mini kai da zuciya." Murya babu amo Abida ta ce "Dan Allah Baba ka yi mini nasiha mana". Ya nisa ya ce "Abida ai na yi miki a farko kika tankwabar da ita da sunan an taɓa ni, wanene Ni da ba za'a taba ni ba? Kinsan me yasa aka jarrabe ki akan Sulaiman da ɗansa?" Ta girgiza kai tana rushewa da kuka na gaske. Tausayinta ya tsirga masa, don kuwa ya shaida Abida ta gama yin tub'us, tun tana boyewa har abin yafi k'arfinta. Ya ce "Alfarmar aure kika keta, ba abin da Allah yake saurin yin hisabi akansa irin cin dukiyar maraya da keta alfarmar aure. Auren nan fa da kike ga ni Ubangiji ne da kansa ya kewaye shi da dokoki iri iri bai barmu da ra'ayin kanmu ba! Ko da na haife ki, ai mijinki yafi ni iko da ke, kin yi fishi saboda sun yi k'arata. Sai kika kasa gane uwarsu ce ta yi k'arata ba su ba. Su kuwa tunda ta haife su babu yadda zasu yi da ita, da kin yi hak'uri Abida Sulaiman sai ya zo gabana ya bavni hak'uri. Wallahi saboda Aurenki ya tsira na kafa muku sharadi ke da Usman duk wanda ya yi inkari akan hukuncin Munira ban yafe masa ba a cikinku, baki yi magana ba tabbas amma kin yanke alaka da Sulaiman a lokacin ba ni da lafiya. Bana sanin me yake faruwa, ban san kina tare da mu a Abuja ba, sai da kika yi wata guda. Lokacin da uwarsa ta rasu anan na ce miki ki yi hak'uri idan munje ki zauna a d'akin mijinki, ki koma gabad'aya ki zauna tunda ba sakinki ya yi ba, sanadin hakan sai a samu daidaito, zai zo har nan tare da y'anuwansa su ba ni hak'uri, na tabbatar Sulaiman zai yi haka. Amma kika dinga rusa ihun ke zuwan ma ba zaki yi ba. Dole nine na sauko na ce to muje ki yi gaisuwar sai mu dawo. Na yi imani kuma zamanki tare da mune ya hana Sulaiman zuwa gabana tunda Bilki ma ta tabbatar mini mun barki kin zauna ne saboda ubansu ya mutu Sulaiman ba shi da wata alfarma a wajena. Daidai nan kuka ya k'wace masa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:21] Hatta Momi ma kukan take yi, Abida kuwa har da shessheka. Ya nisa ya ce "Da kin ji shawarata kin zauna a d'akinki bayan mutuwar uwarsa Abida da tuni komai ya wuce, zai yi ta lallaba kine tunda yana sonki da gaske, amma mutuwar uwarsa bai saka kin ji tausayinsa kin huce ba, kinsan kuwa ko ya yi niyyar zuwa gabana zai fasa tunda mun tabbatar masa baki da manya, duk yadda kika yi haka zamu biki. Ni kuwa ba ruwana da maganar aurenku a yanzu, kuma da ace ba kece matarsa ba, ya shafe wannan lokacin bai waiwaiyi gida ba, tabbas duk ranar da ya dawo sai na tara dukkanku y'ay'an gidan nan na saka an zane mini shi a gaban kowa dan ya gane shi din ba kowa bane face yaron da muka haifa. Amman tunda idan na yi hakan zai zama na yine saboda barinki da ya yi da aurensa da cikinsa ne dalilin dukansa to ba zan ce komai ba, ba kuma zan dake shi ba, tunda kema da na haifa da cikina ai ban isa da ke ba. Na tabbatar kuma Munira ba zata taɓa yi mini hakan ba. Duk runtsi idan na ce ga yadda nake so zata bar ra'ayinta ta bi yadda nake so. Bijire mini da kika yi, da yadda kika bar d'akin mijinki alhalin ba sakinki ya yi ba shiyasa aka jarrabe ki da tsananin son Sulaiman da ɗansa, shikuma ya fantsama duniya waya sani ma ko yana da sabbin iyali tunda ya tafi da fahimtar ba shi da kowa a yanzu". Abida ta rushe da kuka mai tsananin gaske, zuciyarta tana turiri, tana fad'in "Baba ni ce fa Abidanka tsakani da Allah da ka mini dole irin yadda yiwa Bilki yanzu a gabana, Ni ai baka motsa mini k'wanji irin yadda ka yi mata yanzu ba, ni Wallahi ba wanda ya matsa mini! Ta kece da kuka na tashin hankali, bakinta kuma bai mutu ba ta zarce da fad'in kai fa suka kai kotu Baba, suka kuma dunkule wajen kalubalantarka da danne musu hakkkisu, ban da dai an so jarabbata me zai saka ma na so Sulaiman har haka ne?" Zuciyar momi ta karye haka ma ta Baban. Da ƙyar ya daidaita zuciyarsa ya ce "Yadda kike ganin dole ki tsaya mini idan aka taɓa ni haka Sulaiman ba shi da zabi wajen tsayawa uwarsa ko min rashin gaskiyarta ba shi da ikon tursasata sai dai ya lallaba ya bi a hankali har ya shawo kanta, ke da me kika taimake shi a cikin wannan cankacakaren da ya shiga? Duk cikinku y'ay'an gidan nan daga ku harsu Bilkin ba wadda rikicin yafi yiwa illa irin Sulaiman da Bilki. Na farko Sulaiman al'amarin yafi yiwa tsanani da ace bake yake aure ba, sai yafi gwadawa uwarsa k'wanji a kaina, amma tunda ke ce matarsa, uwarsa ba zata saurare shi ba, bare ta tausaya masa tunda zata ce ya bi bayana ne a dalilin ki, ba a dalilin ni ubansa bane. Ke kuma idan ya zo wajen ki babu wani tallafin da kike ba shi da zai daidaita masa zullimin tashin hankalin da yake ciki. Ke yanzu ai uwace ya ya za ki ji idan tashi guda junior ya bijire miki? Ya ya kike tunanin junior zai ga farin matar da yake aure bata tausaya masa ba a loakcin da yake cikin tashin hankalin rayuwa da kuma rashinki kwatsam! Uwarsu ba ni da alaka da ita tunda k'anina da ya aurota ya mutu, don ta yi ƙarata ban yi mamaki ba don kuwa mune muka yi kuskuren da Allah da kansa sai da ya fad'i yadda za'a yi. Ko ba shi za'a karba Allah bai barmu kara zube ba, sai da ya ce mu yi rubutu, mu kuma muka bijire bamu yi ba. Kin ga kuwa ai dole mu ga jarabawa sai dai ina fatan wannan waki'ar da ta sauka mana ta zama aya ga masu hankali.." Tsawon lokaci bai sake magana ba. Yayin da tashin hankalin Abida ya sake rub'anya, a dalilin ta tuno baranbaramar zagin Mami da ta yi a gaban Sulaiman tare da fad'a masa ba zata yarda ta sake had'a jini da uwarsa ba. Tabdi jam . Wai ya aka yi ta manta halayyarsa ta daban ce baya daukar raini ko isgili komin ƙanƙantarsa kuwa. Lallai kuwa akwia sauran kallo don matuƙar yana raye a duniya sai ta nemo shi kuma sai ta koma d'akinsa ko ta halin kaka duk tijararsa kuwa. Baba ya ce "Bilki kuwa duk ta fi shak'uwa da ku, ke da Munira fiye da y'anuwanta, tashi guda kika yanke mu'amala da ita, ya zama bata da kowa a Katsina, babu ke, babu Sulaiman kai yarinyar nan ta sha wahala da bak'incikin rayuwa shiyasa yanzu zan saka k'afar wanda da yayanku da y'ay'ansa akan Bilki. Duk yadda kuka share ta kafatalin y'ay'an Babanku ita kad'ai ce bata fasa mu'amala da ni ba, duk juma'ar duniya sai ta gaishe ni, da kika haifi junior kaf dinsu ita kad'ai ta wanko kafa ta zo gidan nan da kaya irin na uba, ta kuma sake yin jarumtar raɗawa yaro suna. Bayan haka haka da Rukayya ta rasu ita kadaice sai Saddiqa suka zo dan yin ta'aziya. Kai madallah da Bilki madallah da masu irin zuciyarta. Ai ko ban fad'a ba ita da Sulaiman da Munira sun fi kama da ni a kaf dinku, kin sani kuma ba wanda zai ce ke ce k'anwar Munira matuƙar Bilki na wajen saboda kamarsu, to ita bayan kamata da ta kwaso, har halayyata ba abin da ta bari. Shi kuwa Sulaiman da ya yi kamata sai ya yi halin mahaifinsa na rashin d'aukar wargi. Kamar yadda kema halin Baban naku kika yi amma ke fa ba ki da ragayya Abida. Cikin halayenki wannan ne bana so, ki koyi ragayya dan Allah. Tunda kuma kika zo a mace dole ki dinga tauna harshenki, ki kiyayi yin fito na fito da mutane akan dole a bi ra'ayinki mussaman Sulaiman tun kuna yara kinsan shi kad'ai ne ba kya taɓa shi ki kwashe kalau, dan haka idan da rabon zaku sake zama da shi, ki yi matuƙar shiga taitayinki da shi, yafi k'arfinki matuƙar kika ce za ki yi masa izza. Amma idan kin bi shi a hankali sannu sannu sai ya zame miki irin yadda kike so! Yanzu ki yi ta istigifari don kuwa duk wacce ta bar d'akin mijinta babu yawunsa tana cikin had'arin gaske." Takaici ya shak'e Abida duk sai yanzu ne za'a yi mata wadannan bitar? Sai da aka bari duniya ta gwada aya a kanta? Ta dinga kuka mai ciwo tana ayyana la shakka idan Sulaiman ya dawo ba za'a sake ganinta a gidan ba, har sai sun yi jajenta. Ta gaji, ta gaji matuk'a da gaske. Faruk suna tafe Bilki na zaune gefensa tana ta kukan sharb'e. Da farko kamar ba zai kula ta ba, Sai kuma ya kasa wannan jarumtar. Ya bude murya ya ce ",Ki fa rufe mini bakinki, menene abin kuka tunda ke kike son komawa. Ki dauki k'afa ki bi shi wani gari sannan yanzu ki dawo ki cigaba da yin yaji? Shi da kika yiwa yajin kin huce da shi, to yanzu yaransa kike yiwa yajin ko wa, kenan? Ki fa sauya takunki Bilkisu! Ta ce "Yaya Faruku ina yin k'ok'arina akansu amma baya ga ni ". "Ta ya ya zai ga ni tunda kin bari ya fahimci ba kya sonsa, ai ko ni yanzu na gane sonsa ne ba kya yi da gaske shiyasa kika k'asa jure wannan yar matsalar! Har yaran nawa suke ne dan ubansu? Kin fad'a mini ne? Da ko Usman zuwa d'aya tak zai yi ya saita musu zama. Amma dan rashin wayo da wauta a gaban Baba kika debi k'afa da jiki kika bi shi Allah ya shirye ki kawai, amma na taya ki jin kunyar wannan ta'asar da kika yi". Kunyar duniya ta rufar mata ta fara kuka mai sauti tana fad'in"Wallahi Yaya Faruku matsa mini ya yi fa". "Uhum uuuum oh oh haka fa". . Faruku ya fad'a a gajarce. Ta yi tsit tunda Yaya Faruku bai gasgata ta ba, babu wanda zai fahimce ta. Sai da suka kusa gidan sannan Faruku ya sassauta ya ce "Ke ko yar kissar nan ba ki iya ba ne, ai wadannan yaran k'ananun za ki jure har ki shiga jikinsu ta yadda ko unguwa kika fita sai sun zama wani iri, manyan kuwa idan sun gaishe ki, ki amsa, idan basu gaishe ki ba, babu ruwanki da su, Amma idan yana nan yi ta saka su cikin mu'amalarki ba tare da kin lura da d'auke kansu ba, fata dai ya gane sune basa ra'ayinki, idan baya gidan kuwa yadda suke bawa banza ajiyarki ke d'iban karan mahaukaciya za ki yi da su. Kin ga da Bilkisu, Amal da noor ki yi iya k'ok'arinki su zama suna tare da ke sune zaku jima da su mussaman Amal da Noor. Kuma ma ai y'ay'ankine Maigado. Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:41] Idan kina duba hakan za ki sake yin hak'uri da su. Mu maza da kika ganmu muna tausayin y'ay'anmu da uwarsu ta rasu ko ta fita hankalinmu yana karkata a kansu kwarai da gaske. Yanzu da uwarsu tana nan da kin yi kallon yadda zai dinga musguna mata tare da dora mata alhakin ita take sawa su ci matuncinki, ita take zugasu. Wallahi ba zata ji dad'insa ba saboda su. Amma yanzu tunda bata nan akwai buk'atar ki koyi juriya da kissa da kuma azanci". Ta hadiye kukan ta ce "Yaya Faruku ni ban iya fuska biyu ba fa! A tunzure ya ce "Dan ubanki ki koya! Wani abin ai duniya ce take saka ka koye shi, ba dan ka iya ko dan kana so ba. Sannan ban ce ki k'ulla musu karya ko ki ta sukansu a gabansa ba don kiyayyarki za ki dasa a zuciyarsa, idan suna son abu bai yi musu ba. Ki yi iya k'ok'arinki wajen tuna masa har sai ya yi musu din, idan yana musu fad'a ki shiga ki yi ta ba shi hak'uri har ya huce, muhallin shahid shi ya gamsu ba ki da niyyar cutar masa da yara ko kina k'yashin abin da zai yi musu, idan kika rufe wannan k'ofar a zuciyarsa shikenan. Duk shegiyar da ta nemi tayar miki da hankali za ki ga yadda zai saka ta a gaba. Kuma kina haihuwa ma aurensu zamu yi su matsa su ba ki waje Bilkin kwamishina". Kunya ta kamata tana jin kaunar Yaya Faruku kwatankwacin yadda take jin ta Yaya Sulaiman. Har suka isa gidan yana yi mata nasiha akan lallai ta saiya takunta sannan dole sai ta k'ara da hak'uri. A falon k'asa suka tarar da shi yana zaune shi kadai da tray gabansa mai d'auke da kayan shayi. Hannunsa rike da jaridar daily trust. Yana ganin Faruku ya yi maza ya ajiye jaridar ya mik'e tsaye ya yi saluting d'insa tamkar ya Ga ogansa na gaske. Farouku ya d'auke kai tare da fad'in ban karbi wannan gaisuwar ba gaskiyar magana " . Nan da nan mai girma C.P ya durkusa k'asa ya ce "Baba Faruku barka da safiya ya iyalin? Ya aka ji da girma da kuma hak'urin rayuwar nan?" K'aramin tsaki Farukun ya yi, ya zauna yana fad'in "Shigo ki wuce d'akinki ki huta". Bilki da ta safare a gefe a dalilin yadda ta ga ya yi tamkar bai ganta ba alhalin sun had'a ido. A sanyaye ta wuce su. Gidan ya yi shiru Sai tashin k'amshi daban daban cikinhae da na mkbees perfumery da ake fesawa labule da kujeru. Cikin mintina k'alilan an cika gaban Faruku da cima kala kala tunda ga na ci har na sha. Sama sama suke dan hira. Sai can Faruku ya ce "Mai girma CP ba fa haka muka yi da kai ba. Ba abin da baka ce mini a lokacin da kake son yarinyar nan ta saurare ka ba. Yanzu kuma tun ba'a je ko ina ba amanar da na baka, ban gamsu da yadda kake rik'e ta ba". Oga Asad ya daure fuska ya ce "Wallahi Faruku ina iya kokarina kasan matsalar da aka samu bata sona ne. Da ace tana sona ba zata dinga yi mini irin wannan wulakancin ba, da ace tana sona komai na yi mata ba zata fice ta bar mini gidan ba, bare kuma akan laifin da ba ni na yi ba, sannan ba ta zuba ido ta ga iyakacin gudun ruwana ba. Kawai Sai ta d'auki doka a hannunta yara sun zage ta, ni kuma ta zo gabana ta zage ni, ta zagi Rukayya da uwarta dan Allah Faruk yau d'aya tak ka mini adalci akan Bilki, a yadda nake ba dan ina sonta da kuma gudun fishin Baba ba, ai tabbas ka sa ni da ba wannan batun ake yi ba! Ya kammala cikin bacin rai mai tsananin gaske. Kafin Faruku ya yi magana ya zarce da fad'in "Shekaru nawa na bata? Dan na aureta ina lallabata sai kuma ta dinga zagina tana zage zage a gabana kamar wacce ta girma a ghetto ba a irin gidanmu ba. Kusan shekarunmu d'aya da Rukayya amma ko da wasa bata taɓa gigin zagina ba. Duk yadda take tashin hankali akan kishi, amma wannan yarinyar ido da ido ta ce mini amfanin da take yi mini irinsa Laura k'anwar Rukayya take yi mini shiyasa na ajiyeta a gidana, sannan ta kama sunan Rukayya da uwarta da kakarta duk ta antaya musu zagi, bayan haka kuma da zata tafi maimakon ta bar Farha cikin y'anuwanta ai tasan zata dawo ta tarar da ita lafiya tunda ba sakinta na yi ba. " Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:45] Faruku ya shiru don ya fuskanci da gaske ran oga Asad ya b'aci ba kad'an ba. Yasan kuma halinsa ba dad'i ne da shi ba idan aka taɓa shi mussaman raini baya son a raina shi tun suna yara haka yake da son girma. Sanin halinsa da Faruku ya yi sai ya yi maza ya sassauta nasa fishin ya ce "Ka yi hak'uri ai yarinyace Sulaiman ma nawa yake a gabanmu bare su Bilki. Maganar bata sonka ma ai bata taso ba, don sai da so ake kishi kuma idan ka lura da kyau a8 kishi ne ya sanya ta yin wannan katobarar. Da bata sonka fa ba zata bika Calabar alhalin tana zaune a gida da sunan yaji ba. Dan Allah ka fahimce ta da kyau. Duk mutanen da suka yi fama da desperation sai ana yi musu uzziri don tunaninsu gabad'aya sauyawa yake yi. Sannan kai ma ina jan hankalinka with dew respect ka canja tsarin tarbiyar yara ba dan maigado ba sai don rayuwarsu ta gaba." "To na ji Faruku na kuma yarda Zan gyara duk inda nake da laifi na kuma gode maka da baka yi mini fad'a a gabanta ba. Amma lallai ka fad'a mata ta yi hankali da ni, ta shiga taitayinta, don Wallahi idan ta ce zata dinga yi mini taurin kai da raini idan na murd'e mata, sai ta kasa fahimtar komai". Da hanzari Faruku ya ce "A a Mai girma C P ba hakan za'a yi ba, ai yarinya ce ka dai yi hak'uri ba zata sake ba". "Hmm ba wani yarinya kawai dai samun gu da iyashege ai dama Abida ta sha fad'a Bilki ta fita tsiya kawai fahimta ne ba'a yi ba, amma ni yanzu ai ina fahimtar tsiyatakunta bi da bi". Faruku ya yi murmushi ya ce "Oga Asad na Bilki uban Bilki". Dole ya murmusa tare da fad'in "Faruku kana da son kai ka ki yarda ka ga girman laifin kanwarka ko?". Faruku ya ce "Na ga fa laifinta kuma na yi mata fad'a yanzu ma da na ji wannan laifukan nata zan sab'ar mata, na kuma yi maka alk'awarin ba zata sake yin zagi a gabanka bare ta yi maka maganganun da suke nufin ta zage ka". Ya rausayar da kai ya ce "Allah yasa don gabad'aya yarinyar nan ta sauya" Asad ya fad'a babu kuzari a tare da shi. Faruku ya ce "In sha Allah ba zata sake ba, fatana ka ƙara hak'uri sannan ka rufe kofofin da ka bude da suke sawa jin ta gaji da zaman gidanka." Daidai lokacin Aysha ta sauko ta tsugunna a gefensu da girmamawa ta ce "ABBA Ina kwana?" Faruku ya ce "lafiya lau Aysha ya gida ya kannenki?" Ta amsa da lafiya lau a sanyaye don gabad'aya yanzu bata jin dad'in zaman tunda dadynsu yake share su ita da Hafcy. Kanta a k'asa ta ce "Dan Allah ABBA ka bawa Dady ya daina yi mana fishi. Ba zamu sake yin masa ba daidai ba". Ta fad'a kuka na k'wace mata sosai. Don tunda ya yi tafiyar nan wayar Bilkisu kawai yake amsawa ko ya k'ira. Ita kuma sai ta had'a shi da su Amal. Yau kuma da ya dawo ita kadaice a gidan duk sun tafi makaranta, yadda amsa mata gaisuwarta ya sake tayar mata da hankali ainun. Jikin Faruku ya yi sanyi don kuwa da ya kud'ire sai ya turo musu Usman ya ci musu tunda jibi ake saka ran zai dawo Nigeria. Yana k'asar Faransa, shekara guda kenan da gwamnatin tarayya ta tura sojojin sama don koyon dabarun tsare sararin samaniyar k'asarmu. Ya numfasa ya ce "To magana ta wuce amma lallai ki shiga cikin hankalinki, Maigado ai kanwarmu ce idan kuka ci mutuncinta kun ci namu, aurenta da Babanku ya yi kuma ya sake k'ara mata daraja a wajenku, amma shine kika made k'afar wandon cin mutuncinta, kin manta Idan kika taba ta daidai yake da kin tabamu gabadaya tunda ba ita ya kawo Kanta ba, aure ne ya kawo ta gidanku, bayan an shawo kanta da ƙyar. Aure ya zama tilas ya yi shi, sannan zai auri wacce yake so ne, ba wai wacce ake so ya aura ba. Ki faɗawa mai zuwa wajen na ki ya turo da magabatansa, Khadijah kam tunda a can mai son nata yake aurensu za'a daura musu su tare kawai. Wallahi kada na sake na ji ko da kallon banza kin yi sake yiwa Maigado bare kuma a kai ga jallin kina jagorantar kannenki kina kitsa musu shegantaka. Ya ya ina yabon hankalinki da illiminki sai kuma ki bamu kunya? Kullum da ke nake bugawa kaninki Ammar misali ashe kin sauya halayyar k'warai kin aro ta marasa da'a masu yin fito na fito da kwanciyar hankalin iyayensu? Ki yi maza ki gyara tun ba ki fara girban shukan da kike yi ba." Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:48] Da kuka sosai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba". "Yauwa Aysha Allah ya yi miki albarka, Allah ya jiqan mahaifiyarku, daina kuka kin ji, ya huce komai ya wuce." Ta yi masa godiya ta tashi ta koma d'akinta.Tana jin nutsuwar zuciya, tana da tabbacin tunda ABBA ya ce Dady ya huce to babu haufin ya huce din. Faruku ya mike yana fad'in"Bari na wuce "Allah yasa ba zan sake zuwa gidan nan da sunan bacin rai ba Oga Asad". Murmushi Asad din ya yi tare da ce wa "Idan ta ji faɗanku ta kwantar da hankalinta ta ajiye tsiyatakun da ta aro ba zaka sake zuwa ba mana Baba Faruku". Suka fita waje tare. Har jikin motarsa ya raka shi suka yi musabaha. Yana tsaye yana jallon Faruku har ya fita daga gate din aka rufe sannan ya yi ciki. A ransa yana ayyana Duk cikin family lmsu ba wanda ya more irin Faruk. Shine bai taba aikin gwamnati ba a rayuwarsa, amma kuma attajirine na sosai. Sannan yafi kowa yiwa iyayensu hidima da jikinsa don shine yake da lokacin kansa, kullum yana tare da Baba yana yi masa hidima. Haka duk jinyar da zai yi Faruku na gefensa yana kula da shi. Shi kad'ai ne ya yi wannan sa'ar, su kam sai dai su yi da aljihunsu. Hak'uri da sadaukarwarsa ya sanya hatta Momi da Baba kunyarsa suke ji bare kuma su. Yadda suke yi masa kacakaca ko su share shi basa taba yiwa Faruku haka. Ya nisa ya ce "Allah ka sake son Faruku." Ya shiga cikin gidan har ya zauna a falon sai ya tuna ya tashi da hanzari zuwa saman. A d'akinta ya tarar da ita tana zaune a k'asan kafet ta mikar da ƙafafuwanta da suke a kumbure. Murya ba amo ta amsa sallamarsa. Ya zauna a k'asan yana fuskantar ta. "Maigado ya aka yi kuma kika dawo alhalin kin ce Sai kin haihu, Babanki ma ya jaddada mini hakan?" Takaici ya shak'e ta. Ta yi masa shiru amma idanuwanta sun cika da k'wallar takaicinsa. Ya yi murmushi kad'an ya ce "To ya aka yi ne? Fasawa kuka yi ne ko ya ya ne?" Murya na rawa ta ce "Na gode da muzancin da ka janyo mini Baban Bilkisu ". Ya cije ya ce "Wacce magana kike yi ne haka. Me na yi miki?" Hawaye ya k'wace ta ce "Akan me zaka ce mini yini kawai za'a yi ko kwana d'aya alhalin ba hakan bane a ranka." Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskarsa tare da ce wa "Hakan ne a raina mana. To yadda kika dinga mak'ale mini ne ya sanya na fahimci kina buk'atar mu k'ara kwanakin, da na ce zamu k'ara kuma ba ki yi inkari akan haka ba. To menene laifina dan Allah, dole na yi mike ko kuwa kin tayar mini da hankali akan sai mun dawo?" Ta kasa ce masa uffan tunda bata da bakin magana. Ta girgiza kai ta ce ka koya mini darasi zan kiyaye a gaba". Ya dauke kai ya ce " Allah ya nuna mana gaban lafiya." Ya gyara zama ya ce "Ki saurare ni da kyau ki fahimci jawabin da zan yi miki da kunnen basira." Ta goge fuskarta da tissue sannan ta nutsu sosia alamun shi take saurare. Ya ce "Na mayar da Laura gida kamar yadda kike so, na sallami Jummai haka Charity goba zata koma inda na samar mata wani aikin, abin da yasa ma bata tafi ba kenan tuntuni, ba zai yiwu na rabata da wajen aikinta na farko ba, sannan yanzu na sallame ta ba tare da na samo mata wani aikin ba." Bilki dai ido ta cigaba da zuba masa. Ya zarce da fad'in "Yanzu za'a samo sabbin masu aiki, kin ga wanda za suzo basu saba da yara ba, bare su dinga girmama umarninsu sama da na ki." Ta dan ji dis amma ta maze ta ce "Tom amma da ba'a kawo wasun ba, tunda dai akwai ma'aikata da yawa. Ga masu shara da wankewanke da goge goge, ina ganin hidimar girki a bar mini tare da taimakon Alti zamu yi komai" . Ya ce "Kina iya shiga kicin duk sadda kike so, amma gaskiya ina son na ga ina da chef a gidana." Zuciyarta d'aya ta ce "Ka manta nima girke girken na karanta? Sannan Alti ta iya girke-girke kala kala na ban mamaki". Ya daure fuska ya ce "Alti ai ba zata dawo mini ba, tunda ta biki kuka tafi bata hana ki yi mini yaji ba, to na dakatar da ita. Wani irin al'amari ya daki zuciyarta. Nan da nan idonta ya ciko da hawaye ta ce "Baban Bilkisu ya haka kuma? Alti fa bata da kowa a duniyar nan sai ni, tun haihuwar Faruku muke tare da ita, yanzu idan an sallame ta ina zata je dan Allah?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:51] Ta je koma ina ne". Ya fad'a a dake. Bilki ta zuba masa ido tana ayyana abubuwa masu yawa, ba k'aramin artabu zata sha da wannan mutumin ba lallai. Ta tausasa harshe ta ce "Amma tun kafin mu yi aure sai da na ce Baba ya fad'a maka da ita zam zo gudun irin haka fa". Kaitsaye ya ce "Na amince a farko ne ba tare da na yi tunanin komai a kanki ba. A yanzu da na gane inda kika dosa a kaina ba zai yiwu kuma na bi yadda kike so ba. Wallahi ba dan Baba ba, da kinsan kin zage ni a gabana. Amma tunda dole wani ya ci albarkacin wani na hak'ura na k'yale ki, amma Alti da Farha su zauna a gidan Baba wajen Momi." Wannan karon bayan bugawa zuciya har y'ay'an cikinta sai da suka motsa da k'arfin gaske. Ta fashe da kuka mai tsananin gaske. Takaici har makoshi. Cikin fitar hayyaci ta ce "Na rantse da Allah ba zan yarda ba, kawai ka sallame ni, dama ba sona kake yi ba tun filazal, ka samu abin da kake so shiyasa kake fito mini da halayya iri iri. Ko tafiyar nan da ka yaudare ni muka dade da kana sona ai ba zaka mini sanadin da zan muzanta irin haka ba, ka cigaba da cin zalina yadda ka saba tuntuni ". Ya yi murmushin da babu nishadi ya ce "Ai da muka je din ba dole na yi miki ba, yanzu ma kuma ai ban daure ki ba, sai dai ki sani idan kika yi kuskuren sake saka k'afarki kika bar gidan nan, sai kin yi kuka na gaskiya don kuwa za ki dawo ne ki tarar da wata a cikinsa". Kuka ya tsaya mata cak, ta zuba masa ido a maimakon ta ji tsanarsa yadda take ji a da, sai bata ji ba, ta kasa gane me take ji a ranta game da shi tunda babu so, kuna babu kiyayyar. Ta tuna yadda suka rabu da Baba Babba da yadda ya tabbatar mata tashin hankalinsa ace bata zaune lafiya da mijinta, farincikinsa da burinsa bai wuce ace ta bada gudunmawar da zai daidaita zumuntarsu ba, bugu da ƙari Baba ya ce" Ba zai huce da ita ba sai ya ga Asad tsugunne a gabansa yana yi masa godiyar auren Bilkisu da aka ba shi. Wanne irin nauyi Baba ya dora mata, wacce irin biyyaya yake son ta yi, wanne irin dabaibayi Baba ya yi mata? Zata yi komai, zata jure komai amma ban da rabata da Farha. Haka nan ba zata rabu da Alti ba har sai Faruku ya girma ta damka masa amanarta, shi take rikewa ita, yadda ta ci wahalarsa da rainonsa da ikon Ubangiji zai rik'e ta akan tsufanta a lokcin da zata fi koka rashin y'aya' da dangi. Hawaye face face a idonta ta ce "Ayyah Baban Bilkisu amma alk'awari bai ce hakan ba. Magana biyu ba taka ba ce. Ni fa zan iya rabuwa da komai da kowa amma rabuwa da Farha mutuwa ce kad'ai zata gitta a tsakaninmu". Ya sake harzuk'a ya ce "Asad ya rabaku alhalin ba mutuwa kika yi ba. Ai tunda kika gwada mini wulakanci kala kala akanta to ba zan zauna da ita ba. D'iyar Sulaiman ta fi ta kowa saboda rashin kara da wulakancinki ya kai k'urewa." Ta yi sakare tana jin wani irin abu na mamayarta ashe shi a haka ya fassarata? Murya ba amo ta ce "A haka ka dauka kenan? Ni fa Wallahi mantawa nake yi ba ni na haife ta ba. Gaskiya ni ba haka a raina, ban yi zaton zaka mini irin wannan fassarar ba, haka zalika ba zan iya rayuwa babu ita ba, na tsallake na bar y'anuwanta a Katsina amma ita kam tabbas ba zan iya ba. " Ya sake girgiza kai ya ce "To zan ga yadda za'a yi na zauna da waɗanda bana son zama da su a gidana kuwa". *Na gode sosia da soyayyarku ga rubutuna*. *Na gode da uzzirinku* *Surayya Gwaram* ✍️ PAGE 9 Bak'in ciki ya yi mata k'awanya ta rasa yadda zata yi sai kawai ta dage ta dinga zabga ihu da iyakacin k'arfinta. A farkon ya dauka wasa ne amma da ya ga tana neman shidewa ya sanya ya bude baki ya ce "Wanne irin abu kike ne haka? Sai ka ce jahila?" Bata saurare shi ba, ta cigaba da kukanta bilhakki. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya matsa kusa da ita da niyyar rik'e ta, ta goce ta ce "Kada ka taba ni, da ikon Allah na barka Yaya Asad dama dan a kirga mini aure ne ya sanya ka matsa ka kafe sai da ka aure ni". Cikinta ya cure ya dunkule ta rasa yadda zata yi kawai ta kwanta rigingine tana murdaddawa tare da kuka mai gunji. Ya kalli yadda cikin ya yi k'asa tamkar zai fito duniya a lokacin. Murya ba amo ya ce "Ba za ki kwantar da hankalinki ba? Sai kin janyo mana sanadin wahala? Cikin kuka ta ce "Da ikon Allah mutuwa zan yi na bar maka duniyar nan, in sha Allah sai na mutu na barka da sabbin jariran da zaka rasa mai basu nono, da ka raba ni da Farha gara na mutu na huta, in sha Allah sai ka sake samun sabbin marayu a gidanka" Ta sake kecewa da matsanancin kuka. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi mussaman yadda ya ga ta jik'e da zufa duk sanyin AC da na iskar da standing fan take bayarwa a d'akin. A firgice ya dagota, ta fisge ta sake komawa tana cigaba da ihu da murkukusu. A sanyaye ya ce "Ta shi mu yi magana na janye batuna to". Ta sassauta kukan amma ta k'i tashin. "Tashi mana! Ya fad'a da sigar umarni. Still ta k'i ko da motsi. Ransa ya b'aci ya ce "Kin ga taurin kan nan na ki ne bana so, ba yadda za'a yi na ce da Rukayya ga yadda zata yi mini, ta kalle ni ta watsar da batuna. Amma ke ban isa da ke ba kwata kwata." Hawaye na zuba a idanuwanta ta ce "Allah sarki ai sai ka bita makabartar ka cigaba da bata umarnin da ba zata sab'a maka ba." Ya yi shiru yama rasa mai zai ce mata. Kan dole ya ce "Ki cigaba da yin fito na fito da ni". Babu fargaba ta ce "ka cigaba da kwatanta ni da mai murabus". Duk yadda ransa ya b'aci Sai da dariya mai sauti ta subuce masa. Sai ya gintse fuska sai dariyae ta sake k'wacewa. Da ƙyar ya yi jarumtar danne dariyar ya ce "Yanzu Bilkisu duk yadda baiwar Allan nan take haba haba da ke ba zai saka ki dinga raga mata ba? Ya za ki ce mata maimurabus don ta mutu, ai bata mutu a zuciyata ba, saboda Allah fa?" Ta d'auke kai tare da zumbura baki, a yadda take jin takaicinsa cikin jikinta ne cikas din da ya hana ta nada masa duka da sunan jinnu ne suka tashi. Don idan ta shammace shi ta dinga kai masa bugu da cizo kafin ya ankara ya ji jiki. Sai dai ba zata iya ba, tunda ita kanta fama take yi da kanta. Amma matuk'ar suna tare ya cigaba da yi mata batun mai murabus tare da nuna mata tafi ta yi masa biyayya zata dauki mataki. Murya ba amo ta ce "Ya za'a yi ta mutu a zuciyarka tunda nima victim ce na shaida ba'a daina son first luv duk tsawon lokacin da za'a dauka ba'a tare kuwa". Zuciyarsa ta harba. Gatse ta yi masa ko kuwa. To waye first luv din da take so Faruku ko wanccan sahalallen? Ya ce "Da na janye batun rashin dawowar y'arki da Alti. Amma yanzu na jaddada dokar tunda babu nadama a lafuzanki". Kuka ya sake k'wace mata duk da hakan sai da ta ce "Ba zan yi nadama ba, baka biyo ta hanyar da zan risina maka ba. Kuma in sha Allah sai ka fini nadamar wannan hukuncin da ka d'auka. Na yiwa Baba alk'awarin ba zan sake fita da sunan yaji ba, Sai Idan kai ka sake ni. Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:22] Amma Wallahi yadda ka kuntata mini ka shirya fuskantar naka kuntatar zuciyar, babu kai babu farinciki a gidan da kake ƙirarin naka ne. Kuma Wallahi ba dan ina tsoron kada ka kawo wata bane zai hana na fice na bar maka gidan ba. Kunyar Baba ta sanya zan cigaba da zama a cikinsa har zuwa lokacin da zaka gama bayyana dukkan manufarka a kaina". Ta yunk'ura ta mike. , kai tsaye bayi ta shiga don gabad'aya zufa ke yanko mata ta tashin hankali. So take ta ba shi hak'uri amma tunda ya kawo maganar Rukayya a muhallin da bai shafe ta ba to ba zata ba shi hak'urin ba. Zata yi hak'uri har zuwa ta haihu lafiya ya ga kalar tata tsiyar.. Shower ta sakarwa kanta. Mintina biyar sannan ta tsane jikinta ta fito. Yana zaune inda ta bar shi. Yayin da isa gaban wadirof ta bude ta jima tana nazarin kayan da zata sanya wanda bai da nauyi. Can ta hango riga da wando irin na Pakistan din nan masu taushi da tsada. Ta dauko ta saka bayan ta fesa spray din oriflame na lame skin care. For your order contact Aisha 07036662633. Ta sake fesa turarenta na weekend. Kaitsaye ta fice zuwa kicin dinta na da yake falon nata na samanta. Kulikulin Ummiel foods ta dauko ta juye shi a plate. Ta bude firij ta dauko fresh milk ta zuba a glass cup sannan ta fito ta dawo falo ta zauna tana ci tana duba wayarta. Amma gabad'aya bata gane komai. Duk d'adin kulikulin nan a yau taunawa take yi kawai. Haka fresh milk din ma bata jin dad'insa a baki. Sakin da Sahal ya yi Mata ya yi mugun bugunta a dalilin ya zo Mata a bazata sannan yadd6ua ce don iyayenki masu son zuciya ya yi mata tsauri k'warai da gaske. Amma a yau hukuncin rabata da Farha ya buge ta fiye da sakin. Hawaye ya dinga silalo mata. Ta kasa jurewa ta lalubo lambar Baba. Bugu d'aya ya dauka bai yi mamaki ba don kuwa yasan za'a sha artabu da ita. "Ya ya ne Bilkisu?" Ya tambaye ta cikin kulawa. "Baba ka fad'a masa sakon da na faɗa maka na cewa da Farha da Alti zan je gidansa?" Ta fad'a cikin shesshekar kuka. A sanyaye ya ce "Na fad'a masa, ya ce kuma ya amince. Amma ranar da na yi masa ba dadi akan lamarinki da yadda ya zuba ido tarbiyar y'ay'ansa ta lalace ya bani hakuri tare da alk'awarin zai gyara, zai kuma yi garanbawul a gidan. Ya roke ni arzikin na rik'e miki Farha har zuwa lokacin da zai kammala gyare gyaren da zai yi a gidan ". Ta yi shiru. Ta nisa ta ce "Ka amsa masa ka amince da wannan batun nasa Baba? D'iyar da aka bani ita tun bata zo duniya da shekeru sama da goma ne zai yanke ta a jikina? Sahal da ba ni da alakar jini da shi ya zauna da ita cikin adalci sai shine zai ce ba zai rik'e ni da ita ba, alhalin sai da na ce a faɗa masa da ita zan zo masa, ya amince da hakan. Baba ni kam gaskiya wannan hukuncin ya yi mini tsananin gaske tsakanina da Allah ba dan kai ba, da na yi rikicin da kowa zai san an taɓa ni.". Baba ya nisa ya ce "Na gode da kika hango ni, yanzu ki saurare ni da kyau. Ai ya ce mini ya baki Bilkisu, Amal da Noor to yanzu ki jasu a jikinki irin yadda kike yi da Farha suma y'ay'an ki ne kin ji Maigado.". Ta kasa cewa komai don kuwa bata taba ganin mutum irin Asad mai son kansa ba. Shi dai a yi masa yadda yake so ba ruwansa da damuwar wani, tun tana k'arama ya dasa mata k'insa saboda azabarsa shine har yanzu ba zai shafa mata lafiya da takurarsa ba? Cikin kuka ta ce "Baba yanzu shikenan an raba ni da ita? Ni kad'ai nasan yadda nake ji a zuciyata da tunanin y'anuwanta na Katsina. Ban gama warkewa da rashinsu ba sai a sake raba ni da ita kuma duk a zuba ido ana kallo?" Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:25] Ta fad'a cikin kuka na tashin hankali. A sukwane ya ce "Zata dawo fa, ya ce yana gyare gyare ne. Ki yi hak'uri mu ba shi nan da ki haihu, idan bai yi magana ba, zan shiga maganar a lokacin. Kin ga mu maza bama son a zo a yi mana hukunci a gidanmu. Ki yi hak'uri, ki zuba ido ki ga iyakacin gudun ruwansa. Tunda ya ce ba dama ya baki umarni ki ce to kaitsaye sai ya yi fama da ke". Ta kasa cewa komai wato dai Asad mugune lamba d'aya. Sai da ya gama fadan laifukanta sannan ya yaudareta ta bishi a gabansu. K'arshen tozarci da muzanci ya yi mata. Ba kuma komai bane ya sanya ya yi Hakan ba saboda Yana ganin ita nympho ce. To kuwa zata ba shi mamaki. Matuk'ar ita mace ce yadda ya gurfana gurfana gaban Baba ya ce a bawa Momi rik'on Farha, da kansa zai sake gurfana akan ya je d'auko ta. Shine da kansa zai dauko ta ya kawo mata ita ba waninsa ba. Ta had'iye kukan ta ce "To Baba." Ya dinga sanya mata albarka da fatan Allah ya sauke ta lafiya. Ta ajiye wayar tana mai tsurawa cikinta da ya yi tsiri ido. Lah shakka wannan ciki ya yi mata shigar sauri, k'addararsa ne ya sanya ta auren Asad. Gabad'aya ta ji duniyar ta yi mata zafi tunaninta ya kulle. Ba wacce take so ta faɗawa wannan matsalar Sai Abida. Amma kuma Duk yadda Abida bata jingina Farha gare ta hakan ba zai kore itace ta haife ta ba. Bayan haka ta sani bayan baba da Momi Abida bata so wani kamar Asad a gidansu ba. Ta tuna a ranar da suka kammala Fgc Bakori. A ranar da ta yi alkawarin bata abin da zata fara haifa ta ce ina sonki Bilki fiye da Yaya Faruku da yaya Munnira. Ita kuma ta ce so nake ki soni fiye da Yaya Asad. Amsar da ta bata shine ba zan miki karya ba Maigado don kuwa ban so wani a cikinmu kamar Yaya Asad ba. Ta zukar da fuskar b'acin rai tana hakaito yadda shima baya iya karar daidaita su a lokacin da suke yara, sai da suka zama y'anmata ne da ya fara sonta shine yake nuna equal suke har ma ya fara dank'a mata abu idan zai basu tare a maimakon ya bawa Abida yadda ya saba. Yaya Faruku ne da Munira basu taba nuna mata Abida ta fisu asalima Munira bata shiri da Abida ne a dalilin yadda take takura mata. Haka ma Yaya Faruku. Amma Asad kam dama tun can mai son kai ne na gaske yanzune take sake fahimtar haka tunda da ya daina banbantasu ma ai jarrabarsa aka yi da sonta ba dan haka ba, ba zai daina ba. Yanzu kuma lah shakka ta sani laifin Sulaiman ya jingine Abida har tana kukan nemansa ne ya sanya shi hucewa akan y'ar da bata san shi ba. Ya manta ba Sulaiman ne ya bata Farha ba Abida ce. Kuma ko da ba Sulaiman ne ubanta ba, zata so ta, zata yi mata riko na amana sannan a bakinta dai wani ba zai ji ta furta ba ita ta haife ta ba. Sai kuma aka yi sa'a irin na gam da katar Sulaiman ne ubanta. Yadda yake jin yana son Abida haka take sonsa, haka nan yadda yake jin yana son ya'yansa fiye da haka take sonta don idan ta ce tafi jin yarinya a ranta fiye da su Amra ba k'arya ta fad'a ba. Duk tijararsa matuƙar zata amsa sunan matarsa to sai ya zauna da Farha, ko baya so kuwa. Ta janye tunanin faɗawa Abida wannan badakalar don kuwa tasan ko ya ya sai ta ji babu dad'i. A dalilinta kuwa ba zata so su sami sabani ba. Kaitsaye ta kira Faruku. Ta daure ta had'iye kukanta. Ta yi masa bayanin halin da ake ciki. Yana bude baki ya ce "Ki yi hakuri Momi zata rik'e miki ita, kuma ma ba kwaanan za ki haifi wata ko wani ba?" Ta ce "A a Yaya Faruku kafin na haifi wannan din da kake maganar zan haifa, ai ina da wasu. Amma kuma dukkansu ba zasu maye mini gurbin Farha ba". "Bilkisu ki yi hakuri mu zuba masa ido kin ji". Ta kasa cewa komai. Ya dinga rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta, tare da bata labarin yadda yau Aysha ta dinga kukan a ba shi hak'uri. Ki bi shi a hankali ya gamsu ya isa da ke, da kaina zan kawo miki ita. Don hankalinki ya kwanta ya sanya na d'aukar miki Alti. Idan komai ya daidaita zasu dawo kin ji Maigado ". Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:27] A sanyaye ta ce "To Yaya Faruku na gode. Amma fa gaskiyar magana raina ya b'aci da wannan abin da ya yi mini, kuma Wallahi darajar baba da k'imar ka ya sanya zan yi shiru na zuba idon na ga ni din. Amma ba dan haka ba da mun yi tawarwatse a yau din nan". Ya ce "Na gode miki Maigado ai tunda kika yi sa'a kina jin maganar manyanki ko bata yi miki dad'i ba komai zai daidaita miki sannu a hankali." Daga haka suka yi sallama. Daidai lokacin ya fito daga dakin nata. Ya kalle ta ya ce "Kin gama buge bugen waya kina kai k'arar a tursasani na zauna da waɗanda bana son zama da su ne?" Uffan bata ce masa ba. Ya gama tsayuwar jiran ta tanka. Amma tsawon lokaci bai ji ta ce uffan ba. Ya ce "Ai tunda rashin kunya ne makamanki sannu sannu zan bi na karairayesu." Still bata ce komai ba illah ido da ta zuba masa babu kiftawa. Ya tsargu da kallon da take binsa da shi. Don ya ga ta zama wata iri. Don haka ya had'iye maganarsa ya hau samansa. Ba jimawa ya fito sanye da kakinsa hakan ya tabbatar mata office zai wuce. Kwanaki suna ta shud'ewa Bilkisu ta dank'ware ranta. Tsawon sati kenan da ta shata layi da mijinta. Tsakaninta da shi gaisuwar safe bayan haka bata sake bude baki ta yi masa magana. Ta koma yanayin shirun da tun filazal yake fad'in ya yi masa yawa. Ta k'i bari ya kebe da ita, Idan ya matsa sai ta fara kukan ciwon ciki, kuka kuwa mai tsananin gaske. Haka ya hak'ura ya zuba mata ido. Bilkisu Amal da Noor suna tare da ita ko da yaushe, sai dai ita din bata da walwala. Haka Aysha da Hafcy sun ajiye shakiyancinsu da kaso tamanin cikin dari. Kawai hawa samanta su zauna ne basa yi. Amma suna gaishe ta cikin mutunci.. Yanayin da ta koma ya damu oga Asad k'warai da gaske. Haka suke tafiya har aka shafe kwanakin wata. Ranar da ta cika kwanaki talatim da dawowarta gidan tura ta kai bango ya kusance ta a dole wanda babu armashi a had'uwar ko kad'an k'arshe sai da kuka aka kammala. Daga bisani kuma ciwon cikin da take karya da shi kullu yaumin ya taso mata haikan. A gigice ya shirya ta sannan Shima ya kinsta ya sunkuceta zuwa mota ya saka ta sannan ya shiga ya ja motar da kansa ya fice. Y'ansanda da suke tsaronsa suka bisi a mota d'aya. Kaitsaye asibiti kai zaman kansa() da take awo ya nufa da ita. Nan da nan kwararrun likitoci suka rufa a kanta. Shud'ewar awa guda, sannan likitar da ta jagoranci dub Baki ta fito zuwa ofishinta. Asad ya bita. Da girmamawa take yi masa bayanin halin da Bilki ke ciki. "Oga jininta ya hau fiye da kima sannan yaran a zaune suke Wanda ba'a son Hakan". Da yake a rude yake sai bai fahimci kalmar jimillar yaran da aka yi ba. Murya ba amo ya ce "Yanzu ya za'a yi ne, bana son ta samu matsala Dr. Last year na rasa first wife d'ina bana son na sake rasa wannan! Dr ta numfasa ta ce "Dole zamu rik'e ta on bed rest don gaskiya tana buk'atar hutu da nutsuwar zuciya. Bayan haka kuma zamu dinga duba yanayin zaman cikinta har zuwa komai ya daidaita don idan ba a bata kulawa ta mussaman zata iya haihuwa a yanzu wanda da sauran lokaci a k'aida. Ka yi hak'uri zamu rik'e ta har zuwa ta fita daga had'arin da suke ciki ita da abin da yake cikinta. Hankalinsa ya dungunzuma ya tashi tare da k'alubalantar kansa me yasa ya yi mata batun da shine sanadin da janye dukkan walwalarta? Me yasa yau ya matsa mata alhalin da gaske bata son ya kusance ta? Gabad'aya ya ji so yake ya fita da ita zuwa UK don lafiyarta da ta babynsu ta tsira. Haka ya kwana da ita tana kwance ana kara mata ruwa bata san inda kanta yake ba. Sai washegari sassafe ya buga ya faɗawa Momi sannan ya k'ira Faruku ya sanar masa a asibiti suka kwana. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:05] Daidai lokacin Jamilan Faruku ta iso tare da Alti d'auke kwandon da abinci. Sai kusan azahar Abida ta mayar da Baba da Momi gida. Yayin da aka yanke shawarar Abida da Alti su kwana da ita. Da yammaci direba ya kawo su Aysha dukkansu suka dubata. Daidai lokacin Abida ta dawo tare da Farha da junior akan Yaya Faruku zai juya da su tare da matarsa. Farha ta kalli Bilki da take kwance tana barci . A fili ta ce "Allah na gode maka da Mahmah ba guduwa mini ta yi ba kamar yadda muka guduwo su Yaya ba." Asad da yake gefe ya ji wani irin abu ya soke shi. Gabad'aya k'alubalantar kansa yake yi. Akan me zai mata wannan batun a halin da take ciki? Me yasa bai bari ta haihu lafiya ba? Ga shi yanzu ya janyo ta shiga tashin hankalin da bai san yadda zai dire ba. Ba abin da yake tayar masa da hankali irin yadda aka tabbatar ita d abin da ke cikinta suna cikin garari. So yake ya ganta cikin nutsuwarta ya bata tabbacin zai dawo mata da d'iyarta har ma da Alti. Sai dai da alamun komai ya k'wace masa don tun jiya take kwance tana barci bata san wanda yake kanta ba. Gabad'aya hankalinsa ya yi mugun tashi. Daga Faruku har Baba ba wanda ya tuhume shi. An zuba masa ido. Komai ya tsaya masa cak. Idan ya koma gida ya ga yara ne su kad'ai suke rayuwa sai ya ji damuwarsa ta sake rub'anya ga su Noor da suke tambayarsa yause Mahmah da Farha zasu dawo ne a kullum? Sa'a daya ma bai sallami y'ansanda mata da ya dauko lokacin da zai tafi Calabar ba. Wasa wasa sai da Maigado ta shafe sati biyu a asibiti. Zuwa lokacin ma an hana yin zarya da sunan dubata. Alti da Abida ne a wajenta sai shi da kullum sai ya je sau uku. Ta shiga watan haihuwarta ta kuma dawo cikin hayyacinta. Sai dai kuma ta koma yanayi na shiru sosia. Yana wahalar gaske ta yi magana mussaman ace da Asad ne. Gara gara tana yiwa Abida da Alti suma ba haka siddan ba. Amma ko Farha da Alti take cewa a kawo mata ita idan ta zo hannu kawia take mik'a mata. Hankalin Amrah da Faruk ya tashi da basa jin muryarta, kullum Alti da Abida cikin kwantar musu da hankali suke yi tare da basu tabbacin jikinta da sauki. Ranar juma'a Abida ta zauna kusa da ita ta ce ",Yanzu Bilki ba za ki dinga yiwa yaran nan magana ko hankalinsu ya kwanta ba? Ba hutun school ake yi ba bare su taho su gan ki. Idan ba za ki yiwa kowa magana ba, ki taimakemu su da basa kusa ki yi musu mana. Haba da tausayi fa! Ta dinga yi mata nasiha da rarrashi har ta samu ta bude baki ta ce "Ni maganar ce bana son yi Wallahi! Da kulawa Abida ta ce "Kada ki yiwa kowa amma su ki daure ki dinga amsa wayarsu. Yanzu tunda suna gida bari na kirasu ku gaisa dan hankalinsu ya Kwanta". Bugu d'aya Amrah ta d'auki wayar tare da fad'in "Ammi ya jikin Mahmah dai?" Da walwala ta ce "jiki da sauk'i gata ma". Ta mik'a mata wayar. Ta masa suka gaisa. A sanyaye ta ce "Amrah na ji sauki sosai idan na yi magana da yawa gajiya nake yi ne, ba wai ciwon ne ya tsananta ba. Ai kinsan ko da ina nan wani lokacin maganata na daukewa ko?" "Eh Mahmah ".. Amrah ta masa babu kuzari. To idan baku jini ba ku daina damuwa, da sauki sosai jikina. Ina Yaya Faruk?" Ya karbi wayar ya ce "Mahmah idan bamu jiki ba, gaskiya munsan ba ki da lafiya, maganar kada mu damu kuwa babu ita". Ta murmusa kad'an ta ce "To yanzu da kuka jini hankali ya kwanta?". "Eh amma ba sosai ba, sai mun zo mun ganki da idonmu. Ina Farha?" Ta ce "Yau bata zo ba." Daidai lokacin oga Asad ya turo kofar d'akin ya shigo. Alti ta gaishe shi ta fice, don shi kam bata saba da shi ba, babu sakin jiki a tsakaninsu. Ya tsaya a kusa da Abida yana sauraren Bilki na magana cike da mamaki. Daidai lokacin ya jiyo Faruku na fad'in "Dady ma ya ce "Idan mun yi waya na fad'a miki yana yi miki sannu". Ya kurawa Bilki ido mussaman da ya ji ta ce "Na amsa ka ce masa "Na gode, ina k'anwarku?" "Lubaba tana nan an yayeta jiya." Faruku ya fadi hakan. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:08] "To ka siya mata biskit da sweet idan Daddy ya baka kudin break ranar Monday ". "To Mahmah guda nawa zan siya mata?". "Guda shida shida". "To zan siya mata , dazu ma Yaya Amrah ta soya mata samosa ta kai mata". "Ta kyauta, to sai anjima" Daga haka ta mikawa Abida wayarta. Ta gyara ta kwanta. Abida ta mike ta ce "bari na je asibiti sai dare Zan dawo in sha Allah." Ta dauki jakarta ta fice. "A dawo lafiya". Asad ya amsa mata babu wani karsashi don sosia ya ji wani iri da ya ji Bilki na magana da yaranta amma shi tunda ta zo asibitin nan bata taɓa bude baki don ta amsa masa ko da sannun da yake yi mata ba. Kuma ta ga ya shigo amma ta bude baki ta ce ta amsa gaisuwar tsohon mijinta. Sai da Abida ta fita sannan ya zauna a kujerar gaban gadon. Ya ja kujerar daf da ita, ya zauna ya kama hannunta na dama ya rik'e Yana dannawa a hankali. Murya ba amo ya ce "Sannu Maigado" Bata amsa ba, ya sake maimatawa a karo na biyu, maimakon ta amsa da baki sai ta daga masa hannu tabbacin ta ji ta amsa. Takaici ya mak'ure shi tunda ya fahimci tafi tsananta rashin yin magana a kansa. Ya numfasa ya ce "Na so mun tafi London kin haihu a can. Momi kuma ta ce 'ba zai yiwu ki yi tafiya a yanzu ba'. "Ba zan iya ba, kuma bana son tafiyar ma". Ta fad'a a hankali. Daga haka bata sake magana ba, Duk yadda yake ta yin maganganu na rarrashi da kwantar da zuciya. K'arshe ma sai ya ga barci ya yi awon gaba da ita. Ya tsura mata ido abubuwa masu yawa na taso masa a kanta. Ya fahimci gabad'aya ta hak'ura da shine. Damuwa ta yi masa ya yawa. Ya rasa inda zai tsoma ransa. Suna cikinn haka k'iran Yaya Hamida ya faɗo wayarta. Ta dauka suka gaisa ta yi mata sannu, daga suka yi sallama tunda tasan bata iya doguwar magana. Mintina biyu a tsakani k'iran Ansari ya shigo, Shima ta amsa, bata ajiye wayar ba na Saddiqa ya shigo, haka ma na Anisa. Oga Asad yana zaune yana jinsu kowa jikinta yake tambaya tare da fad'a mata ta yi hak'uri ta cire damuwa bawa ba ya wuce k'addararsa. Ya yi shiru yana nazarin wato Hamida ce Duk ta fad'a musu yau ta samu Bilki shine duk suka k'irata d'aya bayan d'aya amma su basa k'iran kowa a cikinsu hatta Baba kuwa in aka cire Saddiqa da Ansari da su din ma sai an d'auki lokaci mai yawa. Auren da yake kan Hamida kad'ai ne ya shatawa Oga Asad layin cin mutuncinta amma tabbas ya washeta tamkar yadda ta washe shi. Bata da mutunci ko kad'an. Tunda ya auri Bilkisu ya ga bata zo ba, har yau kuma bata tako ta zo gidansa ba, ya tabbatar da gaske take gaba da shi. Rashin zuwa yi mass ta'aziyar Rukayya bata bige shi ba kamar rashin zuwanta aurensu. Anan ya tabbatar hatta ubansu ma bata ganin kimarsa ko kad'an tunda gidan da yake nr ba zata zo. Shiyasa bai cika zafafawa akan kiyayyar da suka girka masa ba haka siddan, tunda wan ubansu ma bai tsira ba. Ya kuma yi ammanar ita ta cusa wa k'annenta k'insa don ya yi imani da Allah ita ta zuga Bilki ta so fasa aurensa bisa hujjar baya son uwarsu bai zo musu ta'aziyar rasuwarta ba9baya son yayansu Sulaiman. A yanzu ba zai ce musu komai ba amma idan Sulaiman din ya bayyana ya ci ubansa a gabansu sa yi a hankali da shi. A hakan dai ake tafiya ta fara samun sauk'i sosia amma fa babu magana. Baba da Momi da Yaya Faruku kawia take bude baki ta gaishar, suma daga gaisuwar bata sake ce musu uffan sai ido. Su duk suka damu yayin da Abida ta fahimci ba matsalar da sauki tunda tana gaida wadanda ta san ya kamata ta gaishe da su. Oga Asad ne kawai bata gaisarwa, sai kuwa su members. A ranta ta ce yanzu zaka gane Bilki ta fini daru da gaske, ni hayaniya na fita sannan kalata a bayyane take. Amma irinsu Bilki kafin a gane azaabr da suke ganawa mutum ai sai ya kusa shekawa lahira. Tana kallon yadda idan ya zo yake bare baren yiwa Bilkin magana tare da rarrashi da tambayar me take so ita kuma tana yin biris tamkar wacce ta hadu da lalurar rashin ji. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:11] Har zuciyarta take dan jin babu dad'i na yadda take yi masa, amma ta yi maza ta cire abin a ranta tana fad'in kun fi kusa, matsalata kad'ai ta ishe ni. Amma ita da kanta Abida mamakin zaman Farha a wajen Momi take yi. Tunda Bilki ta koma ta ga Farha da Alti na gidan ta tambayi momi akan yaushe zasu tafi ne, gara Farha ta tafi tunda makarantarsu d'aya da Noor. Kuma makarantar tafi kusa da gidan Bilkin. Haka kawai ta fad'aomi ta balbale ta da fad'a ina ruwanta da maganar Farha. Bilki take rikewa ita kafin ta haihu. Ta daina tisa ta a gaba tana yi mata tambayar da ba huruminta ba ne. Guiwa a sake ta bar d'akin Momi tana ayyana tunda zamanta ya yi nisa dole a gundura da ita. Abu kad'an zata yi momi ta yi ta mata sababi. Yanzu Hatta junior idan yana wasan tsaleltsalle momi zata hau fadan ya fitine su, baba baya son hayaniya amma ta bar d'anta ya cika musu gida da k'iriniya. Har ta kai ta kawo matuk'ar suna gida rufe su take yi a d'aki shi da ita tana ayyana Sulaiman ne ya janyo mata ta zama mujiya a gidansu. Ita mamaki take yi wai kuwa ba a canja zuciyar iyayenta a kanta ba? A yadda take ganin take take momi ba dan kullum tana fita asibiti ba, da sallamar y'an aikinta zata yi. Tunda indai tana gidan bata saka y'an aiki hidima kowacce irice. Komai Abida zo ki yi kaza, Abida je ki wanke mini band'aki, Abida zo ki yi mana girki ni da Babanku. Abida na fi son ki wnake mini kayana da kanki. Abubuwan dai tamkar da gayya, ta tabbatar momi ta gaji da ganinta a gidanta. Bata da wanda take iya faɗawa laifin momi sai Yaya Salaha da take Ibadan a yanzu. Itama hak'uri take bata tare da fad'a mata ta bita a hankali komai zai wuce. Tun yammaci Bilki ke ta fama da ciwon cikin da ta tabbatar yau kam haihuwa za'a yi ta da ikon Allah. Da yake tare da Abida zasu kwana sai bata faɗawa kowa ba. Sai dai wajen asuba ciwo ya tsananta hankalin Abida ya tashi ta fara tunanin ta amince a yi amince a yi mata c.s. Ta shige cikin likitoci asibitin aka fara shirin yi mata aiki. Ana idar da sallar asuba ta kira baba ta fad'a masa halin da suke ciki. Tana kashewa ta k'ira oga Asad ya sanar masa. A kidime ya ce "Sai da na ce zan tafi London da ita aka ki". A sanyaye ta ce "Just pray Daddy in sha Allah aikin will be successful." Daga haka ta katse wayar a dalilin yadda haihuwar ta taso gadan gadan. Nan da nan suka kewaye ta. Ta haifo yaro kukansa ya cika dakin. Aka yi kokarin rabasu. Jikin Abida ya mutu a dalilin yadda ta ga Bilki ta galabaita Anya zata iya sake haihuwar na biyun da kanta? Tunda ita tasan twins zata haifa tuntuni ta fad'a mata, yanzu kuma da take duba file dinta ta ga ni. Itama kuma bata faɗawa kowa ba, zata taya Bilki bawa family suprise. Haka dai aka yi ta fama da gurmuzu suka sake tayar mata da nakuda. Cikin taimakon Ubangiji na biyun ya iso duniya. Shima da kukan ya iso tamkar gyare. Sai da suka kwashe mata jini bayan mabiya ta fito sannan aka yi mata dinki dan kuwa ta samu tear sosai. Tunda Bilki take haihuwa bata taɓa cin ko da kwata din azabar da sha a wannan haihuwar ba. Sai Dai kuma ana gama mata dinkin da aka gyara mata jiki ta sha tea sai ta ji babu wanccan azabar da ta kwana a cikinta. Ana kammala shirya yaran Abida da rawar jiki ta d'auki guda d'aya ta fita da shi. Kaitsaye Baba ta mikawa da suke zaune a reception tare da Momi da oga Asad da kuma Yaya Faruku. Ya karbe shi da Bismillahi ya yi masa addu'a ya duba kunnenta ya ga da duhu ya ce "To wannan bamu bane su baba K'arami aka kwaso" . Asad bai ce komai ba don kuwa ya fahimci duhun fatarsa ya d'ebo. Wani irin tsuma yake yi so yake ya karbi yaron ya gan shi da idanuwansa ashe dai zai samu boy a duniyarsa? Sai dai nauyin idon iyayensa ya saka ya had'iye zakuwarsa. Baba ya yi mass addu'a Abida tana Shirin cewa zata basu suprise Kawai baba ya ce "Je ki dauko mini d'ayan Abida". Da mamaki ta ce "Ai d'aya ne Baba! Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:15] Ya girgiza kai ya ce "Na kai wata a jere kullum sai na yi mafarkin Bilki ta haifi tagwaye. Tun abin bai shiga raina ba har na gamsu tunda tsohonmu tagwaye ne ya biyo. Haka a dangin gyatumarmu sun gaji haihuwar tagwaye." Abida ta yi murmushi ta ce "A a Baba to Dai dan d'aya ta haifa ". Ya jijjiga kai ya ce Idan na yi mafarki na rik'e ban manta ba, sannan na sake yin irinsa to Sai na Ga abin nan a zahiri bare wannan na yi jar na kagu na ga yanbiyu cikin ahalinmu". Ta murmusa ta ce "To menene tukuicin wannan jaridar Baba?" Daga shi har ita jikinsu ya yi sanyi a dalilin sun tuna da, don da a shekarun baya ne da saniya ko tunkiya zai bata. Ganin hakan ya sanya ta juya da sauri. Yayin da oga Asad ya mik'e tsaye ya kasa zama, gabad'aya sai kai komo yake yi, tare da tunanin dama Bilkisu da Babanta har ma da Abida sun sani shine ba wanda ya taba fad'a masa. Ikon Allah yake ta fad'a a fili a k'asan zuciyarsa kuwa hailala yake yi tare da istigifari. Haka ya hango Abida sabe da sabon jariri lullube cikin shawul irin na d'anuwansa. Tabbas Bilki ta san twins zata haifa tunda ga kaya nan iri daya a jikinsu tabbacin an yi musu shiri. Kai wannan shine mafi girman ba zata da aka yi masa da bai taba jin dad'i irinsa ba. Baban ta sake mikawa ya ce wanne ne babban kenan?" Ta nuna wanda ta kawo yanzu. Ya ce "To Abdallah ne ga kuma Abdulrahman". Abida ta ce "Baba gaskiya ba haka za'a yi ba, ka yi mini alfarma nima na yi iko irin wanda Bilki ta gwada mini akan sunan junior ". Murmushi na sosai Baba ya yi tare da fad'in "Ho Abida". Dad'i ya ratsa ta don kuwa rabin da ta ga wnanan murmushin na gaskiya a tsakaninta da shi tun komai bai taɓarbare musu ba. Ya yiwa wanda ta kawo addu'a ya duba kunnensa shima ya ce "A a wannan ma baya bangarenmu duk kune Abida. " Ta ce gara da ya biyo mu ai Baba, don kun fimu yawa." Daga haka aka bawa Momi ta gansu sannan aka mikawa Yaya Faruku. Abida ta ce "ABBA duba ka ga wadannan layinmu ne ba naku ba." Ya karɓa da Bismillahi tare da kurawa yaron ido yana mamakin fuskar oga Asad akan ta yaron. Haka da ya duba d'ayan ma sai ya ga dukkansu kama suke da junansu irin sosia din nan, tamkar babansu ya yi kakinsu. Ya yi musu addu'a. Ya kalli Abida ya ce "Wanne sunan za ki saka musu rigimatu?" Ta ce "Sunan Baba Babba da Baba K'arami zasu amsa. Dukkansu har baba da Momi na wanda ya tanka tabbacin sun aminta da ra'ayinta. Faruk da kansa ya kaiwa Momi yaran. Ita kuma ta rik'e Su a jikinta. Baban Bilkisu tamkar ya je ya karbe su ya gansu Amma ya daure ya cije ya yi jarumtar kawar da kai. Amma k'asan ransa ba k'aramin takura ya yi ba. Har aka dawo da Bilki ainihin d'akin da take kwance suna asibitin Basu tafi ba. Gabad'aya suka dunguma zuwa d'akin don yi mata sannu. Tana zaune ta shirya tsaf tamkar ba itace ta tsallake siradi ba Sannu suke ta yi mata, tana amsawa a hankali. Abida ta ce "Yanzu me yake yi mini ciwo?" A hankali ta ce "Ciki amma ba sosai" . "Sannu zai daina tunda an yi miki allura. Yanzu bari Ki ci abinci ki sha magani sai ki kwanta ki huta". Abida ta fadi hakan da kulawa. Momi ta mik'a mata yaranta cikin tufafi iri d'aya farare kal. Ta noke ta k'i karɓa ta ce "A a zan gansu ne momi". Asad ya ji wani iri Ashe da gayya Shi ta ki ba shi yaran. Momi zata sake da kowa amma ban da shi har yanzu bata ware da Shi ba. Zata yi hira da Faruku tamkar ta goya shi amma shi indai ta ja doguwar magana a tsakaninsu laifi ya yi. To nan kam ta dinga yi masa fad'a tare da yi masa jirwayen Faruku ne dattijo mai halin manya. Kai Hausawa da kuttu suke Wallahi. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:18] Idan ka zo a dan fari a shekarun baya kana cikin talajaurar duniya. Daidai da sunanka uwarka mahaifiya ya haramta ta fad'a kaitsaye. Har ya yi aure wannan yaron take ce masa. Sai da y'ay'ansa suka fara girma ne ta koma cewa yayanku. Amma da kunnensa bai taba jin ta ce Asad ba, kai ko Abubakar ma bata fad'a. A ransa ya fara jin takaicin zamowarsa dan fari dama Faruku ne babba ba shi ba. Ya numfasa tare da auna banbancin iyayen da na yanzu. Y'ay'an yanzu don sun zo a farko iyaye mata basa yin alkunya a gaban kowa suke nan da nan da su ko da kuwa a gaban iyayensu ne ba ruwansu. Muryar Abida ta katse masa tunaninsa da ta ce "Ya kamata su sha nono, dazu basu sha sosia ba." Ta kalli inda Asad yake zaune a takure ta san kuma ganinsu Baba ya hana shi sukuni. Ta karbi yaran a hankali tare da fad'in "Bari Dady ya Gansu momy ". Cikin nutsuwa ta bashi Su sannan ta ce "Ga Baban Abida da Baban Munira nan Allah ya raya su." Bilki bata ce komai ba, jikinta ya gama bata matuk'ar ya tabbata maza ta haifa to kuwa Sunan da zasu amsa kenan. Amma a yadda Abida ta ce Babanta da na Munira ta fahimci so take ta gane itace ta zaba musu suna. Don a da da suke yara idan ta so bakanta mata sai ta ce "Baba Babba babanta ne Baba k'arami kuma na Yaya Munira ne ita yar rik'o ce daga danginsu baba shiyasa take kama da shi". A lokacin Bilki ba wayo sai ta yi ta kuka. Baba K'arami kuma ya gasgata batun Abida na cewar rik'o aka kawo ta gidan. Bilki ta girgiza kai tare da murmushi kadan Abida ta yi tsiyataku mata kala kala. K'asan zuciyarta kuma zargi take yi itama iko ta nuna mata kamar yadda itama ta nuna mata akan junior. Zata yi magana Kawai hankalinta ya kai Kan talabijin din da take makale a jikin bango inda tashar T.V.C News ta rubuta breaking news. Hankalin Bilki ya raja'a ta mayar da hankalinta kan talabijin din. Tabbas ba gizo idonta yake yi ba. Sunan dai shine babu kuskure. Ta kalli y'an d'akin duk hankalinsu ba ya kai, mussaman oga Asad da yake rungume da yara yana ta faman kallonsu. A ranta ta ce "Ya tisa yara a gaba da kallo a gabansu Momi. Bakinta ya yi nauyi ta kasa fad'in komai kawai ta fara nuni da hannunta izuwa talabijin din. Hankalinsu ya kai kan fuskar talabijin din don ganin abin da take yi musu nuni. PAGE 10 Asad Musa Funtua as A.I.G of the Federation. Haka aka dinga jero sunayen wadanda suka zama A.I.G. din. Baba Baban sai hamdala take yi yayain da momi take addu'ar fatan alheri, da fatan Allah ya yi riko da hannayensa. Faruku kuwa yana bude baki ya ce "In sha Allah dukkanmu nan sai mun ga ka zama I.G gabad'aya." Oga Asad kuwa Alhamdulillahi yake ta fadi a zuciyarsa da kan harshensa. Yau ranar ta mussaman ce a kundin tarihinsa. Twins da k'arin girma duk kuma sun zo masa a bazata k'warai da gaske. Blessings bi da bi. Farinciki da zumudinsa basa boyuwa, kowa ya gane ya jarrabu akan yayan nan tamkar yanzu aka fara yi masa haihuwar. Bilkisu ta sake gasgata shi mai son ya'ya ne matuƙa don idan ya zo har ya tafi suna jikinsa yana yi yana duba su. Paediatric daban daban ya sanya suka duba yaran aka tabbatar masa lafiyayyayu ne. Amma duk da hakan idan ya dauke su sai ya dudduba jikinsu tare da bude idanuwansu don ya sake tabbatar basu da shawara(joindince). Kwanaki biyar ta k'ara suka sallame ta tunda jininta ya daidaita sannan yara lafiyarsu k'alau. Tana isa gidan ta tarar da ko ina stickers mai d'auke da welcome to the world twins. Ga balloons. Ko ina haske ke tashi wal wal a duka kusurwaowin gidan cikin da waje. Sosia abin ya k'ayarta da Bilki. Tana hawa samanta kuma ta ga falonta tsadaddun stickers mai dauke da welcome to Home Mahmah. Idonta ya cika da k'walla don sai take ganin Amrah, Faruk da Farha ne kad'ai zasu yi mata irin haka. Ga shi kuma nabu su a tare da ita. Zuciyarta ta harba lallai Bilkisu ce zata yi hakan don kuwa Amal da Noor ba su kawo k'arfin yin haka ba. Ta juya ta ga Bilkisu rik'e da yaro d'aya, yayin da Hafcy take rik'e da d'ayan. Aysha na janye da akwatin kayanta, Abida kuma na rik'e da jakar hannunta. Har ranta ta ji sanyin tarbar da ta samu daga yaran. A gidan suka tarar da Alti ta yi mata kunun tsamiya da awara mai dad'in gaske. Ta sake jin dad'i sosai. Da yamma da yara suka dawo sai ga Farha sun dawo tare. Ita da Noor suka kasa tsaye da zaune wajen ganin jariran. Aka bawa kowa d'aya ta rik'e. Amal na tsaye tana fad'in "To ku bani nima. Duk suka hana ta, kowacce ta ce "Nata ne." Bilki ta lallabata tare da fad'in ai su yara ne Adda Amal bar musu, ke za ki dinga goyasu idan ba school." Ta yi tsalle tare da tafin jin dad'i. Oga Asad na gefe yana kallonsu, yana jin dad'in yadda ya ga ta warware a cikin yaran. Sai dai shi bata bude baki ta yi masa magana ba. Da ya dawo daga masallacin sallar magariba ya tarar Abida ta tafi . Ya shiga dakinta ya zauna k'amshin turaren wuta da freshener din mkbees perfumery ya cika d'akin. Ta yi wanka ta shirya duk wani kumburi ya safe sai dan saura. Ya tausasa harshe ya ce "Sannu Maigado! Kai ta daga tabbacin ta amsa. Ya had'iye ya ce "Zan je na karbo miki kayan Farha a wajen Momi. Ta dawo zata zauna da mu". Ta yi shiru. Ya sake maimaitawa A sanyaya ta ce "Da ka barta dama jira nake yi na samu lafiya sosai zan yi magana da Ansari ya zo ya dauke ta ya rik'e mini ita tunda shine yafi cancantar ya rik'e diyar Sulaiman tunda baba ya danne ni akan na yi hak'uri, na zuba maka ido, ka yi yadda kake so a gidanka". Hankalinsa ya tashi ganin babu alamun wasa a yanayinta. Ya matsa kusa da ita ya sassauta murya ya ce "Haba Maigadona ba magana ta wuce ba, me ya kawo wannan batun da babu dad'in ji a cikinsa? Idan Baba ya ji kin ce haka zai shiga damuwa ne". Ta yi yake ta ce "Ai kuwa zai ji don Wallahi Momi ba zata rik'e Farha a yanzu da girma ya hau kanta tana buk'atar hutu ba. Diyata ce halak malak, ka ce ba zaka zauna da ita ba, dole kuwa na mikawa dangin ubanta ita a maimakon na takura ta yi zaman sakabu a inda ba dolenta ba". Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:51] Takaici ya mak'ure shi ya rasa mai zai ce mata. Ya mike ya fice. Kaitsaye gidansu ya nufa. A masallacin unguwar ya yi sallar isha Shi da musulamn cikin Yan rakiyarsa. Tare da Baba suka isa cikin gidan. Sosai Baba ya yi masa nasiha akan ya rike gaskiya cikin aikinsa sannan ya yi iya kokarinsa wurin kaucewa cin haram. Daga haka ya zarce da nanata masa ya kula da kannensa gabad'aya, ya yi tsayuwar daka wajen gyaruwar zumuntarsu. A tausashe ya ce "Na gode Baba a cigaba da yi mini addu'a in sha Allah komai zai daidaita. Sannan na zo karɓan kayan Farha ne.". Baba ya murmusa ya ce "Ka gama gyare gyaren ne?" Kansa na k'asa ya ce "Eh Baba ". Ya numfasa ya ce "Zan yarda ta koma gidanka ne bisa sharadin wannan ne karon k'arshe idan ka samu matsala da Bilki ka ce zaka taɓa nata yarinyar nan. Zata jure komai amma ina rantse maka da Allah ba zata jure akan yarinyar nan ba. Kuma saboda na baka damarkw ta maigida ka yi hukuncin da ya gamsar da kai a gidanka shiyasa na danne maka ita, amma da tuni ta sake fitowa ta bar maka gidan. Komai zaku yi kada ka sake ce wa Farha ta dawo, ka sakata cikin y'ay'anka babu banbanci. Kuma ko yanzu ai ka b'ata al'amarin don kuwa zata sake gasgata baka son Sulaiman, tunda a gabana ta taba fad'in Sulaiman ba Shi da alfarma a wajena da wajenka. Kuma abin da ka mance ba Sulaiman ya bata yarinyar nan ba, Abida ta bata ita. Bilki kuma bata dauki alamrin da ya Shafi Abida da sauki ba, sai kuma aka yi sa'a Sulaiman nata ne uban d'iyar. Ina tabbatar maka idan ka matsa zata iya zubar maka wadannan tagwayen da ka mak'ala su a ranka don ta rayu da Farha kad'ai ". Murya ba amo ya ce "Baba to ai da tun lokacin ka ankarar da ni hakan ". Baba ya yi tari ya ce"Da ka zo fad'a mini ai ba shawarata ka nema ba. Hukuncin da ka yanke ka fad'a mini. Ni kuma na ce maka to ne, saboda ni uban Bilkine ba naka ba, kada ka zarge ni da bin bayanta tamkar yadda Sulaiman ya yi mini akan Abida ". Jikin Asad ya yi sanyi a ransa kuwa kuzawa Sulaiman ashariya yake yi kala kala. A duniya a yanzu ba abin da ya damu ubansu irin rashin ji daga Sulaiman. Babu yadda za'a yi su zauna a gabansa bai yi musu maganar Sulaiman ko ta kannensa ba. A tsukun nan ma abin yafi ta'azzara ainun. Shiyasa jiya Farouku ya ce masa jinin Baba ya hau sosai da suka je asibiti ganin likita. A ransa ya yi alk'awarin idonsa idon Sulaiman sai ya gaggaura masa maruka Allah bar shi ya cakume shi da fad'a. Amma tabbas sai ya wulakanta shi kamar yadda ya wulakanta Baba don yana ganin babu Baba K'arami tunda da ya san yana raye bai isa ya yi masa hakan ba ko da giyar wake yake sha kuwa." "*Oh oh ni Surayya da kaina na matsu na ga wannan danbarwar ta Sulaiman da y'anuwansa, matarsa da ma Babansu gabad'aya.😀 Ko yana raye ko ya mace sai Allah sai alkalamina.*" Oga Asad ya numfasa ya ce "Ka kara hak'uri Baba. Ina ganin ya kamata ka je ka yi umrah ka dan samu nutsuwar zuciya daga nan Sai Ga likita a can. Faruku ya ce 'Idonka ya matsa maka a kwanakin nan, duk Sai ka Ga likita a can". "Kayya Asad bar batun asibitin nan zan dai je na yi ibada amma kasan da Faruku zan tafi ko?" Wani irin kishin Faruku ya kama Asad wanda ba shi da alak'a da hassada ko k'yashi. Kawai dai ji yake yi inama dai shine Faruku? A raunane ya ce "Na sa ni baba da shi za ku tafi har da Abida itama ta je ta tayaka addu'ar Allah ya bayyana wannan yaron da kuka makala shi a ranku alhalin shi ya manta da ku". Babu kuzari Baba ya ce "Abin da yaoe had'a ni da kai, baka gane girman da ya hau Kanka Yana buk'atar hak'uri da juriya Hadi da kawaici. Abida na son mijinta. Ni muma ina son d'ana to ya za'a yi mu ga farinka idan kana kushe mana shi? Ya ya zaka samu kan Bilki idan ta gane baka damu da dan'uwanta ba? Ka dai dinga lissafi daidai oga Asad". Dariya ta subuce masa yadda Babana ya ce masa oga. Ya ce "Baba Allah yaran basu da mutunci gabad'ayansu Wallahi! Raininsu ya kai k'urewa haba, haba dan Allah! Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:53] Baba ya ce "Ina dai yi maka nasiha ka gama girmanka ka ƙara hak'uri ka koyi yafiya da sadaukarwa.". Daga haka momi ta shigo d'auke da tray din kayan shayi. Da sauri Asad ya tashi ya karbe ta yana jin dad'in yadda har yau momi take hidimar Babansu da kanta babu gajiya, ba yadda za'a yi ta saka yan aiki su yi mata hidimar Baba. Sannan har yanzu Baba baya tafiyar kwana ba da ita ba. Ko asibitine matuk'ar zasu bar k'asar nan. Ita da Faruku kam tamkar rigar sawarsa. Fuska ba walwala ta amsa gaisuwarsa. Baba ya ce "Kayan d'iyar Bilki ya zo karɓa". Ta d'auke kai ta ce "Ai ni ba dan kai ba Alhaji da tuni na aikawa Ansari ko Saddiqa ita, tunda su dolenta ne ai". Baba ya yi maza ya ce "Kash amma ban rufe kofar fadar wannan maganar ba ne?" A tausashe ta ce "Ka yi hak'uri Allah ya bata mini rai dattijo da shi amma idan ya tafka wani abin ko Aysha d'iyarsa ce ta yi a yi mamaki, gabad'aya Faruku ya fishi dad'in kasafi". Oga Asad ya yi k'asa da kai yana tu'ajjibin yadda fahimtar Bilki da ta momi ta zama iri daya wanda shi a ransa babu wannan tunanin ko kad'an. Gaskiyar magana mata sun iya damalmala magana ba ga yaransu ba, kazalika ba ga manyansu ba, duk haka suke da sakawa maza tension. Kafin ya ce komai baba ya ce "Kin ji wai umrah zamu tafi daga nan na ga likita". Tana bude baki ta ce "Allah ya bada lada amma da Faruku zamu tafi" Oga Asad ya tsinci kansa da fad'in "Ni da Usman aikin damara ya nisanta mu a zuciyarku." Nan da nan suka ji wani iri soyayyar d'a da mahaifa ya taso musu. A tausashe Baba ya ce "Asad babu wani d'a da arzikinsa ya yi mana rana ya hana mu kuka irinka. Daga nan har karshen rayuwarmu muna roka maka Ubangiji ya tsare ka ya yiwa dukiya da zuri'arka albarka! Faruku kuwa ya shiga ranmu saboda shine duk cikinku gabad'aya bai taba nisa da mu ba. Haka nan shi wani irin mutum ne da mu kanmu da muka haife shi kunyar mu bata masa muke ki don tsananin biyayya da sadaukarwa. Duk abin da ya gane muna so ya dinga son abin nan kan jiki kan k'arfi, haka nan idan ya gane bama son abu zai taya mu kinsa da dukkan iyawarsa. Ubangiji ya azurta shi da wata irin kyakkwar zuciya da ba kowa yake rabauta da irinta ba. Allah ya yi muku albarka gabad'ayanku". Murya ba amo Asad ya amsa da fad'in "Ameen Baba Allah ya k'ara muku lafiya da nisan kwana mai albarka." Daga haka momi ta tashi ta fito masa da akwatin kayan Farha. Ya karba ya yi musu sallama ya dauka da kansa ya fice. ... Sai bayan goma ya isa gidansa. Ya shiga dakin Bilki ya tarar da Amal Noor tare da Farha sun yi barci akan gadonta. Alti kuma ta shimfida ƙaton bargo a kan kafet tun tana zaune amma jariran kowanne nad'e cikin lallausan bargo suna kwance a gabanta. Yayin da Bilki ke kan kujera daga gefe tana shan shayi. A ladabce Alti ta ce "Sannu Alhaji, sannu da dawowa". Ya amsa a nutse. Idon Alti ya sanya Bilki yi masa barka da dawowa. Da kanzagi ya amsa da fad'in "Sannu Maigado ya jikin dai?" A hankali ta ce "Alhamdulillah". Ya mayar da hankalinsa kan Alti ya ce "Jarirai a k'asa Alti? Ba zasu takura ba kuwa?" A ladabce ta ce "Babu komai kafet din ai mai nauyi ne, ga bargo sannan ga nasu bargunan." " A a Alti wadancan da suka haye gado suka bar nasu a d'akinsu a sauko da su inda kuke. A mayar da jariran kan gado kada su kwashi sanyi". Da girmamawa Alti ta ce "To Alhaji! Ta mike ta kinkimo Amal, sannan ta ɗauko Farha, Noor da take k'arshen gadon ita ta dauko a k'arshe. Sannan ta mayar da twins kan gado. Yana kallo har ta kammala shimfida su. Ya ce "sannu Alti. Ko da rana ban son a kwantar da su a k'asa gadajensu na hanya in sha Allah". "Za'a kiyaye, Allah ya raya su kan sunnah". Ya ce Ameen na gode". Ya mike yana fad'in "Bilki zo ki karbo muku maganin da ba'a samu a asibitin ba, an siyo a pharmacy." Ya fice zuwa falonta ya zauna bayan ya rufo musu k'ofar. Ya ji dad'in ganin yaran a d'akinta suna barci duk da ya fi so su kwanta a d'akinsu amma yasan dokin y'anbiyu ya sanya su kwana a d'akinta. Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:57] Tsawon lokaci Alti na dakon ta ga Bilki ta tashi amma ko motsi bata yi ba. A kufule Alti ta ce "Ki ci gaba dai da zubar mini da mutunci a idonsa yana ganin bana fad'a miki gaskiya. A gabana ya kira ki amma ko gezau ba ki yi ba, wai ya ya haka ne gabad'aya kina ta watsi da kyawawan dabiunki ne Haj Bilki?" Bilki bata ce komai ba ta mik'e ta nufi hanyar fita don amsa k'iransa. Yana ganin ta fito ya mike ya yi saluting dinta. Ta wuce shi ta zauna akan kujera. Ya biyo ta ya zauna a hannun kujerar da take zaune. Hucin tsadadden tureen Boss da nata na weekend suka cakude suka bada k'amshi na ban mamaki. A tausashe ya ce "Sannu Maigado. Kin shayar da ni mamaki fa. Amma menene hujjarki ta boye mini twins za ki haifa mini?" Ta yi masa wani irin kallo ta ce "Wai dan na takaita maka zumudi da zak'uwar isowarsu". Ya ruko hannunta da azama ya ce "A a da kin fad'a mini ai da na yi musu shirin tarba ta mussaman". Bata ce komai ba haka nan fuskarta ba walwala. Yanzu me kika tsara za ki yi?" Bata kalle shi ba ta ce kamar me kenan?" Batun suna nake nufi". Ta girgiza kai ta ce "Bana taron suna ni". "Wannan kuwa za'a yi Maigado. Mu samu tagwaye mu kasa yin walimar da za'a ci a sha! A godewa Allah?" A takaice ta ce "Kullum cikin godiyar Ubangiji muke ai." Ya yi shiru yana kallonta yayin da ita kuma ta kurawa allon talabijin ido duk da ba a kunne take ba. Ya nisa yana jin wani iri, a takure yake jinsa a dalilin shariyar da take yi masa. Ya nisa ya ce ",Ina deciding a bar taron sunan sai upper week sai a yi ranar zagayowar haihuwata wataƙila ma ya yi daidai da ranar da za'a yi mana bikin karin girma" "To" Ta fad'a a takaice. Ya yi shiru don ya tsani wannan shirun da ta gindaya a tsakaninsu. Duk yadda ya so ta ware su yi hira, bata yi hakan ba. Kan dole suka yi sallama ta tafi d'akinta yayin da ya haye samansa. Komai na tafiya daidai gidan oga Asad don hatta Hafcy idan ta dawo school tana zuwa ta ga twins Aysha kuwa kullum safiya tana zuwa ta gaida Bilki sannan ta ga tagwaye sai ta koma wajensu. Kakarsu, uwar Rukayya da k'anwarta Surayya tamkar su hadiye zuciya tsabar bak'in cikin haihuwar maza da Bilki ta yi. Fadi suke yi rabon haihuwarsu ne ya yi sanadin rayuwar Rukayya babu tantama. Tsabagen hada'ma ma sai ta fara da biyu wataƙila ma ibilishiyar Abida ce ta dinga bata magani da allurar da zata haifi y'an biyu tunda ita tana sonta.' Aysha dai da a yanzu an karya lagonta bata ce uffan ba, haka nan bata jin son yaran kazalika babu kiyayyar yaran a ranta. Amma ta ga Hafcy sosai take son yaran dan har ta fara sauko da su wajensu. Gagarumin biki aka yi a ranar goma ga watan goma. Ranar da gwamnatin tarayya ta shirya tabbatar da su oga Asad a hukumunce. Sannan a ranar aka yi taron sunan twins hadi da birthday celebration din mai girma oga Asad. Tsayawa fayyace irin kudin da aka narkar da hidimar bikin zai zama kauyanci amma dai tabbas an yi harkar girma. Abida da Bilki sun yi gayu mai sunan gayu. Tun safiya har yammaci kaya na garari iri d'aya suke sawa. Aysha ta bisu da ido tana jin Anty Abida yanzu ta samu yadda take so babu Momin da bata so. K'walla fal a idanuwanta a dalilin kallon banza ma bata ta yiwa Anty Abida ba. Yayin da Surayya da Laura suke d'auke hawaye akai akai na bak'in ciki da alhinin rashin tasu y'aruwar. Ba abin da yake d'agawa Surayya hankali irin yadda Rukayya ta yiwa kanta sanadin rayuwarta, a dalilin ta burge oga Asad ta je ta yi surgery din da ya yi sanadin kaita kushewa. Shekara d'aya tak da mutuwarta ya samo irin macen da yake so, yarinya akanta, sannan mai cikakkiyar halittar da yake so. Yana ta bare bare akanta, tamkar budurwa ya dauka. Ga shi y'ay'a mazan da bai samu ba, tana zuwa ta haifar masa. Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 11:01] Ita gani take yi sune kad'ai ma suke tuna Rukayya tare da kukan rashinta shi kam shan sharafinsa yake yi da wacce ta fi matarsa k'uruciya. Ta kuma yi amannar duk tsananin son ya'yansa da yake yi yanzu sai yafi son wadannan akan nasu yaran. Bilki ba juyin da bata yi da Yaya Hamida akan ta zo ta ce taa yi hak'uri ba zata samu zuwa ba, amma tabbas zata zo ta ga tagwaye nan ba da jimawa ba. A zuciyar Hamida kuwa ta kud'iri aniyar zata je, amma sai oga Asad da Baba sun yi tafiya zuwa wata k'asar. Don ba zata iya shiga Abuja bata je ta gaida Baba ba, ita kuma zuwan ne bata son yi, idan kuwa baya nan ai shikenan. Oga Asad kuwa ganinsa ma bata buk'atar yi, mugunta ne da zalunci ya sanya shi makalewa Bilkisu. Ba don Bilki ba, ko hanyar da ya bi ba zata bi ba matuƙar ta sa ni, bare ta je gidansa da ƙafafuwanta mugu mai azabar son kansa. To da ya d'auke ubansa daga cikin gidansu bai ji labarin suna yawo a titi suna neman wanda zai zame musu uba ba. Haka nan da ya yi sanadin b'acewar yayansu bai gansu durk'ushe a gabansa suna neman alfarmar ya zame musu bangon jingina ba. Ko auren Bilki dan dai Baba ne ya d'aura auren sannan Bilkin bata yi turjiya mai yawa ba, ba dan haka ba da ya ga masifar duniya don kuwa sai ta yi masa tijarar da idan ance ma ya kalli y'ay'an Mamin da bai zo ta'aziyarta ba, saboda yana jin haushinta da sunan so ba zai fara ba, ba dan Baba ba na da rai ba, sai ta maka shi a kotu don a nemawa Maminsu hak'kinta, akan me ya washeta! Amma zai aurar mata d'iya yana amfanar kuruciyarta? Alhalin ko ita ba sa'an aurenta ba ne bare Bilki. Ya ga halitta iya halitta shine ya shiga ya fita tare da taimakon ubansa da y'anuwansa masu son zuciya ya aure ta. Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:37] *Surayya Gwaram* PAGE 11 Wadannan kalaman da ta amayarwa Anisa ya sanya Anisar jin itama ba zata iya zuwa gidan oga Asad ba. Don haka Saddiqa ce kawai ta zo, matar Ansari ma ba ta zo ba, bisa hujjar tana da tsohon ciki itama. Amma shi ya zo ya duba Bilki tun tana asibiti ya ga twins sai dai bai zo wannan bikin ba. Rashin zuwan y'anuwan Bilki wannan gagarumin taron da oga Asad ya shirya ya sake tunzura shi akansu tare da tayar masa da hankali, ya kuma fahimci gyaruwar zumuntarsu zai yi wahalar gaske tunda Bilki ta yi jinya, ta haihu amma basu zo ba saboda kasancewar shine mijinta. Da ya yi nazari sai ya gane gidansa ne ba zasu zo ba, tunda ko Ansar da ya saukaka gabar iya asibiti ya je, yanzu da a gidansa ko gidan Baba zai yi masauki sai bai zo ba". Wannan rashin zuwan nasu ya tabashi fiye da zatonsa. Hakan kuma ya sake ragewa Bilki kuzarinta matuk'a da gaske. Idan ta kalli yadda Basma da Alawiyya suke shiga suke fita a cikin hidimar sai ta ji hawaye yana k'wace mata, tare da fad'in ina ma Yaya Hamida da Anisa ne. Don sun fi Saddiqa kazar kazar. Duk da ba'a hutun makaranta ake ba, tare da Amrah da Faruk suka taho mata. Ganin yaranta cikin nutsuwa da rashin takura ne ya rage mata damuwar rashin ganin y'anuwanta. *Katsina* Hawwah gabad'aya ta susuce a dalilin cikin ya yi mata shigar sauri d'iyarta Ifrah bata kai watannin yaye ba aka cire ta. Don haka kukan yarinyar da karatunn makaranta hadi da rashin cikakkiyar lafiya sai suka yi mata rubdugu. Gabad'aya ta yi yaushi ita da Ifrah. Sannan tun makwanni biyu da suka shud'e da Sahal ya ji labarin haihuwar Bilki. Ya zama wani iri, ya rikice komai nasa ya sauya, ko kad'an bata gane masa. Yayin da shi kuma haihuwar tagwayen da ta yi a wani gida yake nukurkusarsa tare da saddakarwa ya rasa ta forever. Ya tabbatar a yanzu Allah ya yi sakayya tsakaninsu duk da kuwa ta furta mass ta yafe masa. Ita Allah ya bata wanda ya fishi komai, shima Allah ya bashi wacce ta dace da shi daidai da irin matsayinsa. Nauyin da suka yi masa k'awanya babu kuma mataimaki ya sanya babu ta bayyana masa. Amma dai cikin ikon Ubangiji nai rasa abinci irin wanda zai iya affording ba. Sannan yana biyan kudin karatun yaransa booko da islamiya. Hidimar Hajiya da ta Hawwah ma yana iya kokarinsa sai dai da yake bai iya harkar kasuwa ba sai iya aikin Slsai ya zama a takure yake ainun. Rashin samun nutsuwa daga wajen Hawwa ya sanya ya fara tsufa ba tare da ya kai shekarun da zai zama haka ba. Tsakaninta da shi ana zaune ne kawai. Amma ita kallon mayaudari azzalimi take yi masa. Duk abin da zai mata bata godewa bare ta yaba kokarinsa tunda ita fiye da hakan ya nuna mata zata samu. Daga lokacin da ta fahimci duk wani k'yallin da ta ga ni a tare da shi ba nasa ba ne, na matarsa ne tun lokacin ya fita a ranta tamkar kibau, tana zaune saboda bata da wani cikakken gata, sannan tausayin d'iyarta Ifrah na yi mata dabaibayi, tare kuma da son ta kammala karatunta da take yi a Katsina. Tunda Bilki ta haihu ta ga ya rikice itama ta sake murde masa tana ta zungure zunguren maganar da take sake k'ona masa rai. Har zuciyarta ta daina kishin Bilki ko na y'ay'anta don ta gane ba kowacce mace ce zata yi kawaici kan bak'in cikin da Sahal ya shayar da ita ba. Ita da kanta idan ta tuna da kudaden Bilkin ya rudeta ta amince masa sai ta ji ta fashe da kuka tare da taya Bilki jin wani irin kuttu mai yunkurin fasa zuciya da mak'oshi. Kai maza na sharafinsu k'warai da gaske. Allah ya yafe musu don kuwa iyayenmu ne, garkuwarmune. Ya zamu yi to?😅 Na ce ba kina sallah akan lokaci kuwa? Dan Allah kina yin walaha don yiwa kanki guzuri? Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:45] Kina kiyaye hak'kin mijinki tare yi masa biyayya kan jiki kan k'arfi tare da yin imanin Allah ne ya kallafa mana yi musu wannan biyayyr? Kina sane da cewar aljannar mace tafi samuwa ne da yadda mace ta yi hak'uri da biayyyar aure? Amma ina fatan kin yarda su din a halittarsu polygamist ne? Na ce kin gamsu ba abin da zai hana su so mace sama da guda? Wai kuwa kin fahimci zurfafa soyayya hana sukunin zuciya take yi tare da haifar da wani irin zazzafan kishi mai saka azabben ciwo a k'irjinki a kullum? Kin san idan kina da sana'a ba ki da lokacin kanki balle ki yi lokacin sakawa miji ido akan hurumin da ba na ki ba? Yauwa na ce ba kina mayar da hankalinki wajen yiwa yara tarbiyar da zasu amfani kansu kema ki moresu a gobe, ko kuwa kina nan kina ta kushe ubansu a gabansu tare da fad'a musu ba ya yi miki adalci, yana cin mutuncinki?. Kina mayar da hankali wajen yiwa yaranki addu'ar a tsare musu zuciya daga hassada da kyashin junansu? Kina musu addu'ar a jefa musu tausayi da soyayyar junasu kuwa? Abubuwan k'alubale masu tayar da hankali sun mana k'awanya amma basu dame mu ba sai lamarin kishi, akan me zamu fitini kanmu ne irin haka fisabidillahi, tunda har a aljanna ma mataye birjik za'a halatta musu🥲 Y'ar uwa kin yarda ke mai kyau ce a duk yadda kike? Doguwa, gajeriya, siririya, lutiya, dirarriya ko ramammiya fara ko bak'a dukkanmu muna da kyau a yadda muke. Kada fa ki yi gangancin sauya halittarki don kawai ki burge Rijalu. Duk yadda kike ba zai hana su so wata ba, sai dai idan k'addararsu ce zama da mace d'aya. Ni kuwa an fahimci wanda ma ya k'ara auro wata macen ya kawo ta gidansa yafi mutunci da kiyaye ka'idojojin shari'a akan mai zuwa yana yi miki tsome tsomen jijiyar nan da ake so da wasu matan banzan bila adadin? Mu yi ibada, mu yi biayyyar aure, mu kula da tarbiyar yara, sai kuma mu k'ulla soyayya mai yawa da neman kud'i na halali. Idan kuma kin bijire, kin kafe kin fi k'ulla soyayyar rijalu a ranki to fa ki sani at your own risk. I come in peace my fans. 😅😅 Sati guda kenan da hidimar suna da murnar k'arin girma da ƙarin shekarun Oga Asad. Wanda ya yi daidai da wata guda da isowar tagwaye wannan duniyar mai cike da hargitsi. Zuwa lokacin sun yi girma kammaninsu da juna sun sake bayyana. Bilki kanta ta girgije ta yi kyau, tamkar ba mai shayar da yara biyu ba. Alti na nan tana kula da ita da cima iri iri. Komai suke bukata ga shi nan birjik tamkar banza. Amma wata k'addara kuma zuciyarta ta kasa nutsuwa. Rashin zuwan y'anuwanta gidanta tare da korar Farha da oga Asad ya yi ya kasa barin zuciyarta. Ga shi ya dawo da ita amma abin na mintsininta tana ganin yarinyar bata da security a kowanne lokaci zai iya cewa ta bar masa gidansa tunda dai d'iyar Sulaiman ce. Ta kasa faɗawa Abida, ta kasa faɗawa Basma. Ta kasa faɗawa Yaya Hamida. Shiyasa abin yake cinta matuk'a da gaske. Ta kuma kasa sakewa da shi duk k'ok'arin da yake yi mata kan jiki kan k'arfi. Yayin da shi kuma yake zargin y'anuwanta ne suke zugata tunda a bayyane sun fahimtar da shi basa sonsa da gaske. Don haka shima ya fara zuba mata ido tare da rungumar shariyar da take yi masa. Gabad'aya ya zama desperate. Idan ya fita ayyuka ne a birjik a sabon office d'insa, idan ya dawo gida babu walwala. Ga batun tafiyarsu Baba umrah, don ma ya barwa Faruk shige da ficen neman visa da sauransu. Shirye shiryen tafiya umrah ya kankama. Ranar ake jira kawai. Ranar lahadi da yamma Abida ta isa gidan Bilki. Sun gaisa da Alti ta fice ta basu guri bayan ta turo Saudatu da abin motsa baki da kayan ruwa. Tana cikin sabbin maiakataj da aka kawo. Yarinya ce da bata wuce shekaru sha biyar ba. Bayan yarinyar ta fita suka gaisa. Abida na kare mata kallo ta ce "Kin yi kyau kin sake fari amma kin rame fa uwar Farha". Bilki ta ce "Wataƙila shayar da yaran nan ne amma lafiyata k'alau". Ta numfasa ta ce "Nasan zuwa yanzu kin fara sallah zuwa na yi mu fara wuridin nan akan wanccan mutumin Bilki". Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:47] Bilki ta yi murmushi ta ce "To Abida ai bamu samu sharadin da k'aidar ta cika ba. Iya kakanmu na uku muka san sunansa. Ko kin tambayi Baban ne?" Ta girgiza kai ta ce na dai gano yanzu zuwa na hud'u mu fara a hakan zuwa gaba idan Baba ya samu lafiya ko da a Saudi ne sai na tambaye shi. Idan ya fad'a mini sai na fad'a miki ke ma". Bilki ta ce "Hakan ya yi Dr bari na doro alwallah mu fara". Abida ta ce "To don ni da alwallahta". Bata jima ba, ta fito da alwallarta. Ta ce "Tuna mini ma abin da zamu karanta. Ta fad'a mata sannan ta bude jaka ta fito da jotter ɗinta tana nunawa Bilki ta ce duba ki karanta dan ki rike". Bilki ta ga an rubuta Sulaiman bin Isa, bin Garba, bin Bello bin Uzairu". Dariya ta k'wace mata ta gaske ta ce "Abida a ina kika samo mana Uzairu ne?" Ba wasa a fuskarta ta ce "Wallahi ba wasa Uzairu ne ya haifi Bello. Yanzu sunan uban Uzairu da kakansa ne ya rage sharadin ya cika. Da mu larabawa ne sunan ubanka na dari ma ba zai zama abin wahalar samuwa ba bare ubanka na bakwai kai Hausawa basa rik'e nasabarsu da kyau". Bilki ta guntse baki. Har ta yi shiru sai kuma ta ce "Ko dan irin haka kuwa ai ya kamata a dinga kiyayewa." Daga haka Abida ta bude ledar da ta shigo da ita ta fito da wani irin rafkeken carbi ta fara ja. Dariya kara kubucewa Bilki tana ayyana tsananin ya kai tsananin a wajen Abidan Baba don kuwa ba dan da idonta ta ganta da wannan carbin da ya kai guda dubu goma ba, zata yi musun idan ance Abida zata kalle shi. Wato daukarsu ma kad'ai jidali ne. Amma Abida ta kinkimo ta zo da shi. Asalifa Abida na cikin jerin mutanen da suke bin mazahabar da basu yarda da jan carbi ba kwata kwata. Dariyar da take yi bai saka Abida ajiye carbinta ba, illa iyaka ta tsume ta shiga jansa da dukkan zuciyarta. Ganin hakan da Bilki ta yi ya sanya ta yi maza ta had'iye dariyar ta mike ta saka hijab sannan ta dauko counter dinta da fara wuridin kiranyen mijin Abida. Sai daf da magharib suka kammala. Abida ta ce "Gobe a gida zan yi. Idan zan fara zan k'ira ki ke ma ki fara. Da ni yake zancen. Duk inda yake a duniya sai wannan addu'ar ta susuta shi ya dawo da kansa". Bilki ta ce "Allah ya amsa Abida, Allah ya kawo mana shi lafiya". Daga haka ta rakata zuwa kasa ta tafi da ledar carbinta ta shiga tsaleliyar motarta irin ta Bilkin da bata jima da isowa ba. Ranar tafiya da safe Abida ta kawowa Bilki junior. Idanuwanta kozai kozai tabbacin kukan rabuwa da shi ta yi. Bilki ta daure bata ce komai ba ta karba. Sai dai tun tana gidan ta rik'e hannunsa suka hau saman Dady. Yana fad'in "Mahmah Ammi ta ce "Zan dinga kwana a nan tare da su Farha da Noor". Da murmushi ta ce "Haka kuwa junior amma fa idan ka yi kuka to ba zasu yarda su yi wasa da kai ba bare su barka ka je d'akinsu." "Idan na yi kuka twins ne friends dina?" Bilki ta ce "Sune kuwa tunda sune masu kukan banza". Ya make kafaɗarsa tare da fad'in "Ba zan yi kuka ba Mahmah ". Daidai lokacin suka isa falonsa. Yana zaune daga shi sai singileti fara kal da boxer. Yana ganin junior ya mik'a masa hannu Yana fad'in young police come closer". Junior ya saki hannun Bilki ya isa gunsa. Ya yi saluting d'insa. Oga Asad ya murmusa ya shafa kansa ya ce "Magajin Dady how far, ina momi ina Ammi?" Momi na gida, Ammi kuma na d'akin Mahmah". Bilki ta ce "kawo shi aka yi ya zauna kafin su dawo daga umrah". To bana son sai ta tafi ka ce ba zai zauna maka a gida ba". Ya hassala ya kalli junior ya ce "Je wajen Ammi muna zuwa." Yaro ya juya ya tafi bayan ya sake saluting oga Asad. Ya mike tsaye ya nunata da yatsa ya ce "Billahillazi a wannan yanayin da nake ciki idan kika nemi tayar mini da hankali sai na miki cin mutunci. To idan na ce ba zai zauna din ba sai ya ya?Wacce bata barin abu ya wuce cikin dad'in rai. Sai anyi tsiya tsiya. Yaune last time da zaki mini irin wannan rainin ki fita a idona. Haba a yi mace da taurin zuciya ba ki iya komai ba sai rik'o da kullaci ba wani alherin da zan samu daga gare ki sai da b'acin rai, ni ba haka na saba ba, komai matata da girmamawa take yi mini sannan bata iya fishi da ni ya zarce na kwana da yini, amma ke zuciyarki bata da kyau saboda kina da wata Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:51] manufar da kika boye a ranki. Bilki! Bilki! Bilki! Billahillazi ki kiyaye ni." Hawaye ya k'wace mata mussaman da ta ga tafkeken frame irin window size din nan mai d'auke da hotonsa da maimurabus dukkansu sanye cikin k'ananun kaya ya rungumota ta baya fuskarsu da murmushi. Ba a k'asar nan suka yi hoton ba tabbas. Ita sun yi hotuna kala kala a America da London amma kusan shekara bai sa an yi frame don ya saka a wajensa ba tabbacin ba sonta yake yi ba tunda gashinan ya girke na wacce yake so. Da muryar kuka ta ce "Ni ce ba ni da alheri ko Baban Bilkisu?" Ido cikin ido ya ce "Fad'a mini alherin da kika yi mini don ni ban san shi ba". Ta jijjiga kai ta ce "Shikenan! Ta juya ta fice. 2ga watan 9 jirgin suka shiga Saudi Airlines ya tashi da su. Kaitsaye a Madina suka yada zango. Dukkansu sun sauka da farinciki da walwala. Da yake shigar dare suka yi kaitsaye masauki suka isa wanda yake makwabtaka da babban masallacin Arrasool(S.W.A). Da asuba suka tafi masallaci. Bayan an idar da sallah sun yi addu'o'i sannan suka isa wajen ziyarar Annabi da sahabbansa. Suka shiga rauda. Baba Babba duk da yana cikin yanayi na rashin sukuni sai da nutsuwar zuciya ta same shi. Haka ma momi haske da farinciki ya cikasu. Ba inda ya kai Madina sauakr da walwala da annushuwa a zuciyar musulmai mussaman ace ka shiga babban masallaci sai ka ji ka manta komai da kowa saboda tsananin farinciki da k'aruwar imani. Basu bar masallacin ba sai da aka fara kokarin za'a rufe sannan suka koma masaukinsu suka fara barcin gajiya. Kwanaki biyar suka yi a madina sannan suka shiga mota zuwa Makka. Kullum Sai ta yi wuridin kiranyen Sulaiman a wannan masallaci mai alfarma tana Kuma gasgata addu'ar zata karɓu tunda ba shirka take yi ba. A daren da suka shiga Makka a daren suka sauke Umrah. A wannan lokacin ma sai da rafkawa Malam Sule kiranye. Kullum kuma ta what'sapp sai ta ce da Bilki kina yin wuridin nan kuwa?" Ita dai Bilki dariya take yi tare da madaukakin mamaki don Har zuciyarta mamakin Abida take yi k'warai da gaske. Tun washegari Abida da Yaya Farouk suka fara fita zuwa asibitin Saudi-Germany dan sanin tsare tsarensu na ganin likita. Kwana biyu suka yi suna jele sannan aka basu ranar da zasu ga likita. Kwanaki uku masu zuwa. Washegari sun je Harami suna d'awafi kamar an ce wa Farouk juya sai kawai ya hango wani tamkar Sulaiman ya kammala dawafi ya fice da sauri. Nan da nan ya burzana ya bishi sai dai shige da ficen mutane a wannan wajen ya sanya ya bace masa b'at. Ya rasa k'ofar da zai bi ya gan shi don kuwa zuciyarsa tana bugawa da k'arfin gaske tabbas da ba Sulaiman ba ne ba zai ji irin wannan bugun zuciyar ba. Kan dole ya juyo ya dawo tare da adduar Ubangiji ya k'addara wahalarsu ta sanin yana raye ko a mace ne ta zo k'arshe. Sai dai me? Abida ya tarar a gefe tana tsaye ta kasa cigaba da yin d'awafin. Da azama ya isa kusa da ita yana fad'in "Menene?" Hawayen da ta goge ya sake k'wace mata. A sanyaye ta ce "Na rantse na ga Yaya Sulaiman yanzun nan". Da hanzari ya ce "Wallahi nima na gan shi, shi na bi fitar nan da na yi, amma ya bace mini kamar kibau . Share hawayenki kada Baba ya ga kina kuka ya tambayi ba'asi. Ko Momi kada ki faɗawa mun gan shi. Idan ba haka ba, Baba zai rikice ne sosai." Yana rufe baki kukan ya k'wace mata tana fadin "Mun had'a ido da shi fa Yaya Farouk. Ganin na gan shi shine ya zabura ya fice. Ni ina nan ina ta yi masa addu'ar Rahma idan mutuwa ce ta sure shi, idan kuma a raye yake Allah ya tsare shi ya bayyana shi, ya yaye masa dukkan kuncin rayuwa. Ashe shi baya ko k'aunar ganina?" Yaya Farouk ya ce "Na ce ki yi shiru ko. Tunda yana Makka idan Allah ya amince ba zamu bar garin ba sai mun sake had'uwa. Ai gamu a guri mai alfarma. Mu dage da addua. Na yi imanin tasirin addu'ar da muke yi ya sanya muka gan shi da idanuwanmu ai da bamu da tabbacin yana mace ko yana raye ma." Da k'yar ya shawo kanta ta nutsu. A ransa sai mamakin yadda ta rikice sosai yake yi. Ko da yake mijinta ne uban d'anta. Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:54] Har suka dawo gida Abida bata da kuzari duk wata jarumtarta ta nema ta rasa. Haka suka koma hotel dinsu momi na tambayar ta dalilin sauyin nata. Baba ya ce "Ah kya tambaye ta dalili, bayan dalilin a bayyane yake tunda ta baro Sulaiman junior ai kinsan ba lafiya." Momi kuwa ta hau kai ta zauna ta dinga yi mata fadan ta rage ƙulafuncinsa. "Me zai same shi? Yaro yana ta harkokinsa amma ke kin takure zuciyarki haba me za'a yi ne da rashin kawaicinki akan yaron nan." Kan dole ta yi shiru aka tafi a haka. Amma gabad'aya nutsuwar zuciya ta yi mata tutsu. Yaya Farouk kadai yasan damuwarta duk da shima a rikicen yake. Washegari tun safe Abida ta tafi masallaci bata koma ba sai yamma bata ga wanda ta je nema ba. Haka ta daure don gobe ne zasu je asibiti. Washegari sai dare suka je asibitin. Aka fara yiwa Baba gwaje gwaje da na'urori daban daban. Har asuba suna asibitin. Wajen takwas suka koma hotel dinsu akan da daddare zasu koma asibitin sannan dukkan sakamakon gwajin sun bayyana. Abida da Baba suna zaune gaban likita yayin da Momi da Yaya Farouk suke waje suna dakonsu. Komai na baba na tafiya daidai Sai dai dole zai dauwama yana shan maganin hawan jini. Sai kuma idonsa d'aya da dole sai an masa aiki an cire hakiyar da take son mamaye idon . Dan haka likitan ya ce su je b'angaren ido su ga likita sannan a basu ranar da za'a yi aikin. Likitan ya yaba da hazak'ar Abida har yana mata tayin zai bata takarda ta cike zasu debi likitoci mata a bangaren gynecologist. Don sosai ya gane hazik'ar likita ce. Ta yi godiya tare da gabatar da uzzirin k'asarta Nigeria na bukatar irinta. A hanyarsu ta komawa gida suna cikin mota momi ta ce "Ni kam ba dan za'a ce gizo idona ya yi mini ba da na ce tabbas na ga Sulaiman." Abida ta yi fit ta ce "A ina kika gan shi?" Momi ta bata amsa da fad'in a asibitin amma shi bai ganni ba, don nima bayansa na ga ni yana sanye da rigar likitoci yana tafiya da sauri gilmawarsa na ga ni, da farko kamar yayanku(Asad). Kunsan tafiyarsu iri d'aya ce, sai kuma na ga gefen fuskarsa kafin na ankara ya b'ace mini, lokacin Farouk ya je siyo magani ke kuma kin koma ofishin likita d'auko gilashinki". Baba ya ce "Sulaiman nawa kike magana?" Momi ta ce "Shi fa Alhaji! Ya ce "Ai kuwa idan har shine k'afata k'afarsa da shi zamu koma gida." Abida tana son ta ce suma sun gan shi amma tunda bata ji Yaya Farouk ya ce ya gan shi ba, ta daure ta yi shiru. Hankalinta ya tashi ainun domin a yanzu take dandana azabar soyayya da alamu shi kuma ya shafe ta tunda ya ganta amma ya arce saboda baya ko son ganinta. "Farouku ka k'ira yayanku ya tuntubi abokin nasa da yake aiki a asibitin nan a bincika mana idan Sulaiman Isa Funtua a asibitin yake aiki yasan yadda zai yi ya kawo mini shi gabana". Baba Babba ya fadi hakan cikin sigar umarni. Cike da nutsuwa Yaya Farouk ya ce "To Baba". Yayin da d'adi ya kama Abida ta samu nutsuwa sosai don a yanzu bata da matsala a duniya irin ta Sulaiman. Bata taɓa hararo zai iya tsallakewa ya barta shekaru uku babu waiwaiye ba. Ya bace bat don kusan kullum sai ta duba dukkan handles d'insa na media amma ba alamun yana amfani da su. Dama kuma shi bai damu da su ba. Twitter yake yi to account d'insa da ta sani ta tura sak'o ya kai sau hamsin amma babu reply ko d'aya. Da yamma suka tafi asibitin za'a yi masa wata allura a idon sannan bayan awa uku sai a shiga da shi tiyata. Abida da Farouk sun je sun biya kud'i. Yayin da Baba da Momi suke d'akin da aka kwantar da shi. Suna tafe suna hira Yaya Farouk ya ce "Ta je bari ya siyowa Baba laban a store din waje tunda idan anyi aikin ba zai ci abincin da za'a tauna ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:56] Kamar ta bishi sai kuma ta fasa ta ce "Sai ka dawo, idan ka ga gashasshen kifi zan ci". Ya ce "Anya kinsan yawanci sai dare suka fi hada hada, amma zan duba miki, idan ban samu ba sai na siyo miki da daddare." Ta ce "Na gode ". Tana shan kwana ta shiga wani korido kawai suka yi kicibus. Had'uwa ta gaba da gaba idanuwansa suka fad'a cikin nata. Ya maze ya dauke kai, ya yi wura Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:58] wura ya rasa yadda zai yi. Ai kafin ta ankara ya juya da mugun sauri ya yi waje ba tare da ta ankara ba.. PAGE 12 A guje ta bi shi tana ayyana yau duk bala'insa ba zata ba'ri ya sake tserewa ba. Ganin da gaske yake ya sanya ta k'ara gudun da take yi, ta isa gare shi, bata jira komai ba ta sanya dukkan hannuwanta tare da tattaro dukkan k'arfinta ta cakume shi. Ya yi iya k'ok'arinsa ya fizge amma ya kasa don idan ya ce zai fincike ta k'arfi to sai dai ya wancakalar da ita, bai san kuma a yadda zata fadi ba. Dan haka ya dinga kokarin banbare hannunwanta a jikinsa tun ba'a ankara da su an baibayesu ba. Ya kuma tabbatar kyamarorin asibitin suna ɗaukarsu. Da k'yar ya bude baki murya ba amo ya ce ",Wanne irin wulakanci kika shiryo mini haka? Akan me za ki karya mini darajata akan titi, me na yi miki, wace ce ke?" Mamakinsa ya shak'e Abida. Ta kasa ce masa komai amma ta k'udire ba zata bari ya tafi ba har sai Baba Babba ya gan shi. Ya ce "Sake ni tun ban miki sanadin da za ki tozarta ba." Ta d'auke kai ta ce "Ba wani tozarcin da zaka yi da zai fi wanda ka yi mini. Ka tafi ka bar ni da aurenka a kaina shekaru hudu babu waiwaiye, kuma ba wanda yasan inda ka ke, sannan yanzu ka ce zaka tozarta ni, wanne irin tozarcin kuma?" Ba fargaba ya ce "Jira nake yi na ji kin yi aure na dawo mu sake shiga kotu, kinsan na tsotsi kafiya da rashin mutuncinta". Ta rikice gabadaya take ta ji ta rasa kuzarinta don har rikon da ta yi masa sai da ya yi sakwasakwa. Idanuwanta sun ciko da k'wallar nadama ta ce "Na janye kalamaina, ban tab'a jin nadama a dukkan tsayin rayuwarta irin wacce na yi akan kalaman da na jefeka da su ba, ka yi hak'uri. Na yarda ban kyauta ba. Allah ya baka hak'uri! Ya murmusa ya ce "To sake ni." Ni fa ba zan sake ba har sai Baba Babba ya gan ka.". Abida ta fad'a idanuwanta cikin nasa. Ya zabura ya shammace ta ya fizge ya fara k'ok'arin tafiya wajen adana motoci. Ta kuwa sake kai masa wawura. Takaici ya k'ume shi ya ji tamkar ya gaggaura mata maruka masu zafi ko ta shiga taitayinta amma ba zai iya ba. Juyin duniya ya b'anb'are hannunwanta tuburan ta k'i ba shi damar hakan tabbacin da gaske take yi sai ya gurfana gaban Baban nasu. Suna cikin haka securities suka zo wajensu. Suka yi magana da Sulaiman da larabci ita dai ba ta ji me suka ce ba ta ga sun tafi ne kawai. A hassale ya ce "ba za ki sake ni ba ko?" Ko uffan ba ta ce masa ba illa iyaka tsananta rikon da ta sake yi. Ita da kanta mamakin cakuikuiye shin da ta yi take yi, bata gane matsanancin son da take yi masa ba sai a ranar. Don kuwa ji ta yi matuk'ar zai sake kubuce mata bayan ta gan shi gara ta mutu ko ta huta da azabar da ke dandana ta rashinsa. A haka ta hango ya Farouk ya shigo. Nan da nan ta bude murya ta ce "Yaya Farouk ga shi na rik'e maka shi". Da hanzari ya iso kusa da su ya kallesu kowa fuskarsa babu walwala sai suka tuna masa shekarun baya da suke y'ar tsama da junansu. Ya kaurara harshe ya ce "Sake shi Abida ya za ki cakume shi irin haka?" Nan da nan Sulaiman ya ce "Ba ta riga ta raina ni ba. Saboda tana da gatan da zata yi komai yadda take so, ba tare da an kwabe ta ba. Ya fad'a cikin fishi sosai. Ta sake shi a sanyaye don ta lura fishi mai tsananin gaske ya yi da su. Yayin da Faruku ya hassala da kalaman Sulaiman. Amma ya yi jarumtar had'iyewa ya ce masa "Wuce mu je ciki". Cikin sigar umarni. Bai musa ba ya yarda suka tafi ba don komai ba sai saboda Yaya Farouk mutum ne da kowa a gidan nasu yake jin kunyar yi masa rashin kunya saboda tsananin kirkinsa da haba haba da yake da su ba tare da tunanin su din k'annensa ba ne. Tiryan tiryan har d'akin da su baba suke ciki. Kaitsaye gadon da Baba Babba yake zaune Sulaiman din ya nufa ya durkusa tare da fad'in "sannu Baba ya jikin, ya kuma iyali?" Duk d'akin aka zuba musu ido domin dai Baba Babba bai amsa masa gaisuwar da ya yi masa ba, asalima d'auke kai ya yi tare da juyar da fuskarsa d'aya gefen. Hankalin Sulaiman ya tashi ya yi k'asa da kansa cikin girmamawa ya ce "Ka yi mini hakuri Baba a gafarce ni dan Allah". Baba bai ce komai ba, bai kuma juyo ba. A sanyaye yaya Farouk ya ce " A yi hakuri Baba.". Amma ko motsi Baban ya k'i bare ya tanka musu. Karon farko da suka ga an gaishe shi ya tankwabar da gaisuwar a dukkan tsayin rayuwarsu gabad'aya. Ganin haka ya sanya Momi ta ce "daure Alhaji, sake yin hak'uri." Hankalin Sulaiman ya yi tashin gauron zabi duk da shima cike yake da gillin ba'a yi masa abin da ya kamata ba, amma ya gamsu ya yi laifin da Baba zai yi masa fishi. Fishinsa a kansa kuwa tamkar fishin mahaifinsa ne don haka zai yi iya k'ok'arinsa don ganin Baban ya huce ya karbi gaisuwarsa har ya saka masa albarka. Ya mik'a hannunsa ya rik'e hannunsa cikin girmamawa da taushin harshe ya ce "Dan Allah Baba ka yi hak'uri, na yi kuskure ban kyauta ba. Dan Allah a gafarce ni! Sai lokacin Baban ya juyo da fuskarsa ya d'ora akan ta Sulaiman sai ya ga ya sake girma da kuma alamun yana cikin nutsuwarsa. Ya ce "Anya kuwa Sulaiman zan hak'ura da abin da ka yi mini? " Kansa a k'asa ya ce "Da kaina ina k'alubalantar kaina Baba. Amma dai ka daure ka yi hak'uri ka karbi tubana da gaisuwata dan Allah! Baba ya nisa ya ce " Zan karbi gaisuwarka ne kad'ai idan ka yarda ka zo mun tafi gida, don sai mun je gida zan fad'a maka sharadina akanka idan ka amince da sharadina to sannan zan hak'ura na kuma huce. Idan ba haka ba kuwa to lah shakka ba zan karbi gaisuwarka ba, bare na huce da kai, kuma yanzu na gane kai ne Dr Isa din da zai yi mini aikin ido to kuwa ba zan amince a mini aikin ba gabad'aya ". Nan da nan Sulaiman ya ce "Zamu tafi tare Baba. Zan nemi izinin tafiya da hukumar asibitin, idan da rabon zan dawo na cigaba da aikin da su sai na dawo, idan kuma iya adadin da k'addara ta rubuta zan yi aikin da su shike nan sai na yi zamana a asibitin k'asata." Dad'i ya kama Baba Babba ya ce"Madallah da Sulaiman ya bayan rabuwa?" Kunya ta kama shi ya yi k'asa da kansa ya kasa amsawa. Daga haka ya juya ya gaida momi daga durk'ushen da yake. Ta amsa da sakakkiyar fuska tare da tambayarsa aikinsa. Bai tashi ba sai da ya gaida Yaya Farouk duk da shi Farouk din hannu ya ba shi tare da mik'ar da shi yana fad'in Dr Sule sai kuma Dr Abida ta yi mana ram da kai! Gabadaya d'akin aka hau dariya ban da Sulaiman da ya maze. Ita kuwa Abidan murmusawa ta yi wanda tun daga k'asar zuciyarta yake kutsowa. Dadai lokacin nurse din da zata yiwa Baba allura ta iso d'akin. Ta yi aikinta ta fice. K'arfe goma na dare aka shiga da Baba dakin tiyata k'arkashin jagorancin d'ansa Dr Sulaiman Isa Funtua! An yi aiki cikin nasara kwana d'aya ya sallame su. Sulaiman da kansa ya kai su masaukinsu tare da bawa Baba tabbacin zai sayi ticket din da zai bisu Nigeria in sha Allah. Baba dai duk hidimar da Sulaiman yake yi masa kallonsa kawai yake yi don kuwa da ace yana cikin shekarun k'arfinsa, kuma ba Abida ce matarsa ba da zane Sulaiman zai yi tabbas. Washegari momi da Abida suka fara shiga kasuwa yiwa yara tsaraba. Tun ranar da aka ga Sulaiman Baba ya gargade Slsu gabad'aya akan kada a sake a bayyana an gan shi, a bari sai Allah yasa sun isa lafiya kowa ya gan shi. Duk zumudin Abida akan ta sanarwa Bilki wuridin kiranyensu ya ci haka ta had'iye ta kama bakinta bata fad'a mata ba. A hanya Momi ta kalle ta ta ce "Abida ban ga kina gaida Sulaiman ba, ba sai na fad'a miki komai akan halayyarsa ba. Ki bi shi a hankali ki ajiye girman kanki ki lallaba ku sasanta ki koma dakinki tunda dai bai sake ki ba. Kin ga dai yadda ya jingine ki tsawon shekaru babu waiwaiye, idan kuma kin ki jin shawarata ki tabbatar kwabarki ce zata sake cabewa. Ya bar ki da k'aramin cikin da wataƙila ma bai san da shi ba. Ga yaro nan yana gudu har yana gwalantun surutu. Duk sababinki Sulaiman ya dame ki ya shanye kin sani sarai, dan haka ki kwantar da kai har Allah yasa ki koma dakinki". "To momi shine fa baya ko kallon inda nake, sau biyu ina gaishe shi yana yin kamar bai ji ba tsabar dan sababi ne, shiyasa na daina, ni dai ki taimake ni, ki fad'awa Baba a cikin sharadin da zai gindaya masa har da ya dauki iyalinsa ya zauna da su lafiya". Dariya momi ta yi ta ce "Sannu Abidan Baba! Amma ai kinsan ba zai yi hakan ba. Da dai ace ba ke ce iyalin nasa ba zai yi hakan. Yanzu ke za ki gyara laifinki, tunda ke ce a k'asansa." Abida ta ce "Ni Wallahi Momi wulak'ancisa ne bana so. " Da sauri momi ta ce "Ai tunda ya fara sonki ya daina yi miki, sannan kin sani da kuka yi auren ai rarrashin zuciyarki yake yi. Daga baya kuma ke kika bijire akan ba za ki zauna da shi ba, akan laifin da ba shi ya yi mana ba. Ni dai na fad'a miki gaskiya ki yi maza ki gyara tazarar da kuka haifar a tsakaninku. Don kuwa ke kanki kin san na gaji da ganinki a gidana". **** PAGE 13 A sanyaye ta ce "To." A zuciyarta kuwa itama ta gajin kawai bata son dan tijarar ya gane ne, bare ya sake samun kuzarin cin kasuwa akanta yadda ya so". Don gabad'aya tunanin ta inda zata bullo masa take yi. Ta tabbatar ba k'aramin artabu zasu yi ba, mussaman da ya ce ya yi jirwayen an zuba mata ido tana yin yadda ta ga dama babu mai kwabarta. Murmushi ya k'wace mata a dalilin ta tuna fad'ansu na k'uruciya a duk sadda aka tare shi idan ya yi nufin kai mata duka sai ya tunzura ya ce 'Ana bata lasisin ta cigaba da raina shi, a yiwa Allah a taimake shi a bar shi ya yi mata dukan da ko mai irin sunansa ta ga ni sai ta shiga taitayinta. Ana marawa Abida baya ta cigaba da yin isgili yadda take so". Ta tuna mafi yawa baba Karami yake hana shi dukanta. Ya kan ce masa "Sulaiman ai ba'a kanta zaka gwada kwanjinka ba, daure ka daina kula ta ai kanwarka ce. Ni dai zan so na ga k'arshen wannan fadan naku da baya k'arewa. Ba dama ku zauna a inuwa d'aya. Shiyasa da ya ji suna soyayya har sun amince a yi musu aure ya dinga jinjina k'arfin k'addara dan dai shi ba mai barkwanci bane irin baba Babba ba. Amma tabbas ya yi mamaki, ya yi murna ya dinga ce wa 'Sulaiman ashe da na sani na bari ka yi mata dukan da zaka targad'a ta da shikenan sai ka zama mijin gurguwa.' Gabadaya wata irin nutsuwa da walwala ne ya dabaibaye zuciyar Abida. Ta dinga jin wata irin soyayyar Sulaiman na sake bin dukkan ilahirin jikinta. Amma a yadda ya karbe ta ta tabbatar ba k'aramin gumurzu zasu yi ba kafin su daidaita. A zuciyarta ta kud'ire duk inda k'arfin zuciyarta ya buya sai ta lalubo shi, duk yadda ta matsu ya bayyana, duk yadda take jin soyayyarsa ba zata bari ta bayyana masa muraran ba tunda shima k'wallon kansa ne, to ba zata bari ya jata a k'asa don tana son ya zauna da ita ba. Barinta da ya yi tsawon shekaru hud'u ya isa hukuncin zaginsa da ta yi ba zata bari ya sake wani hukunci mai yawa ba. ** Abuja Oga Asad da Bilki dai zama ya yi tsami kowa harkarsa yake yi a tsakaninsu. Abinci ma sai ya dawo yake saka Angela sabuwar chep din gidan ta yi masa abin da yake son ci. Hakan ba karamin sake tunzurata ya yi ba. Yana gama uzzirinsa kuwa zai saka Bilkisu ta karbo masa twins ya dinga fama da su har sai dare ya fara nisa sannan zai mayarwa Alti su. Ya tattara ya fita a harkarta. Sai dai daga shi har ita kowa ya shiga damuwa. Bilki ta fara gasgata lallai ta fara sonsa. Fishin da ya dauka ya dameta ainun. Ranar alhamis tura ta kai masa bango. Har sha d'ayan safiya yana gida tamkar ba ranar aiki ba. Tun goma kuma twins suke wajensa. Wayar Bilki ya dinga k'ira tunda ta ga shine take biris har sai da hankalin Alti ya kai kan kiran da yake shigowa. Ta ce "Mahmah duba ana ta miki waya ko Alhaji ne ga kukan Baba Babba Ina dan jiyowa." Bilki ta ce kunnenki ne Alti, ni ban ji ba". "To amsa k'iran dai". Dole ta amsa. Tana dauka cikin sigar umarni ya ce "Ki zo yanzun nan". Takaici tamkar ta yi ta zunduma ihu. Kan dole ta tashi ta nufi samansa tana jin idanuwan Alti na takura mata ba don kada ta dinga jin babu dad'i a ranta tare da jin bata isa da ita ba da ba zata je k'iran nasa ba. Tana isa ta tarar kuwa baba Babba ke kuka sai dai kukan ya ragu ba kamar dazu ba. Ya sassauta ya ce "Zo ki zauna. Bata musa ba ta zauna din. Ya dad'e yana kallonta. Ta gama sacewa duk wani kumburi ya sace ta yi kyau sosai hannuwanta d'auke da kalle mai ban sha'awa ga kuma zobunan gold suka sake kawata yatsun nata. Ya nisa ya ce "Maigadona da alamu dai kin kwashe kayan rankatakaf a gaban ma'aikin Allah!. Ta kawar da fuskarta gefe yaune zai ce Maigado. Kwanakin baya ai Bilki ya dinga cewa gatsal wanda Har zuciyarta ta ji wani iri tunda tun filazal baya ce mata Bilki. Amma saboda ya so k'ank'anci ya dinga fad'in gayan sunan nata". Ya sassauta ya ce "Amsa mana sarauniyar shaiba ke dad'ina da ke rashin wayo". Ta sake matsewa ta ce "Na'am ". Ya nisa ya ce "D'akina ne ya yi kura sosai, da kanki nake son ki gyara mini mussaman shimfida gadon nan". Nan da nan ta gane jirwayen nasa ya gaji da fishin don yana da bukatarta. Ta jijjiga kai lallai kuwa zasu sake hawa sama don kuwa ba zata taba yarda ta kwanta akan gadon da aka girke hoton wata mace a gefensa ba ". Ta mike ta ce "Bari na gyara maka ". Ya yi maza ya ce "To zauna ki ba shi ya sha ban son idan kin fara gyara shimfidar ya katse ki da kuka". Kaitsaye ta ce "Ai tuni bana Basu nono Sai Madara tunda ka ce baka san alherina ba, na daina basu Sai Idan Alti ta matsa, tunda shari'a ma ta ce idan ba zan iya ba, ka nemo wata ta shayar da su ka dinga biya ". Ya yi sakare yana kallonta. Tabbas akwai matsala babu tantama Hamida and co sun yi tasiri a cikin gidansa. Ya had'iye fishinsa ya ce "Na janye kalamaina. Dan Allah ki yi hak'uri, kada ki yi mini haka mana". Ta yi shiru. "Pls Maigado kin ga dai fiye da watanni biyu rabonmu da juna. Tsakanina da Allah na gaji hakanan, sannan bana son mu sake samun matsala da ke. Dan Allah kada ki gwada ni ta nan, akansu zan iya haduwa da hawan jini tsakanina da Allah. To ban da ma abinki, alherinki ai na daban ne, twins fa kika haifo mini sannan ke ce kika haifa mini boys din da ba ni da su, don kuma raina ya b'aci na yi subutul kalam sai ya zama kin manta komai". Ta numfasa ta ce "To shikenan amma ka zaba ko dai na shayar maka da su ko na gyara maka shimfidar." Ya yi shiru ya ce "Duka biyun nake so Maigado". Ta kwakkwabe fuska har k'walla sun cika idon ta ce "Wallahi d'aya zaka zaba". Ya yi kalar tausayi can ya nisa ya ce "Na hak'ura ki shayar da su sarauniyar shaiba". Ta mik'a masa hannu akan ya bata yaron. Bai ce komai ba ya mik'a mata. Ta gyara ta fara shayar da shi, yayin da ya tsura mata ido yana ganin yadda ta zarta yaron hasken fata. Sosia suka yi masa kyau. Ya shiga tashin Baba K'arami don shima ya sha. Har zata yi magana sai kuma ta k'yale shi. Sai da yaron ya k'oshi dan kansa. Sannan ta saka shi a kafaɗa ya yi gyatsa. Ta kwantar da shi a gefenta. Shi kuma ya yi maza ya mik'a mata Baba k'arami ta karɓa babu musu ta shiga shayar da shi. Shima sai da ta saka ya yi gyatsa sannan ta kwantar da shi kusa da d'anuwansa ta mike ta ce "Sai anjima". Ya kasa cewa uffan, illa ido da ya bita da shi har ta bacewa ganinsa. A zuciyarta kuma ta kud'ire Wallahi indai a d'akinsa zata kwanta to kuwa sai idan babu hotunan maimurabus duk sababinsa kuwa. Ya numfasa a fili ya ce "Yadda na shaida musulunci gaskiya ne, haka na shaida mata ja'iran halittu ne masu tsiyatakun da suke gigita mazaje. Mata da manta alheri suke. Ka ciyar da su safe, rana, dare cimuka kuma gwargwadon k'arfin arzikinka, haka suturar ma, mazaje su sha wahalar gina gida su saka mataye a ciki har a koma fad'in gidansu, su kula da lafiyarsu amma idan ka kuskure musu sai su manta komai na alherin namiji har su iya bude baki su ce me ake yi musu? Ai ciyarwa da tufatarwa ba alfarma ba ne wajibine hak'kinsu da ya rataya aka sauke. Mata da butulci suke shiyasa Annabi ya ce butulcin mace ne ya sanya suka fi yawa a wuta. Ya nisa ya ce "Allah ka shirya mana wadannan karkattatun halittum tunda ka jarrabe mu da sonsu. Duk wahalarmu akansu ce amma gabad'aya sun rantse idanuwansu sun mayar da maza abokan hamayyarsu".🤣 Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 15:52] *Saudiyya.* Tunda Abida ta ga Sule ya yi d'iban karan mahaukaciya da ita sai ta yi maza ta kame kanta. Tsakaninta da shi ina kwana, ko ina yini idan ya zo duba Baba. Gabad'aya sai ta canja salon addu'ar ta. Tunda ta yi imani addu'ar kiranyen da ta dinga buga masa ne ta karbu sai ta koma buga masa ta a jarrabe shi a kanta fiye da yadda aka jarrabe ta a bayan ya bace mata. Ta yi dawafi akan kada ta wulakanta a hannunsa ba adadi. Tana kammala dawafin kuwa zata yi ta buga nafila tana kama sunansa a sujjuda akan a cika zuciyarsa da tausayinta da zai hana shi matsa mata. A kuma cika k'irjinsa soyayyarta da zata hana shi jarumtar damfara ta da k'asa. Sai ta yi addu'a ta jero sunansa har kan ubansa na biyar. Duk sadda ta gan shi ta ga ya dauke kai itama sai ta kwafse a ranta kuwa tana fad'in "Da ni kake zancen Malam Sule dan Uzairu. Babzai yiwu ka tafi ka bar ni shekaru uku da watanni sannan yanzu na yarda da wani nau'in wulakanci ba. Duk sababinka da zarar na koma d'akina Sai mu fafata don kuwa ba yarda zan yi na bayyana maka soyayyarka da take k'irjina ba bare ka samu Dama a kaina ". Sulaiman. Yana kwance shi kad'ai a d'akinsa ya yi shiru yana tunanin yadda zai bi su Baba Nigeria a jibi. Zuciyarsa sai harbawa take yi a dalilin yadda al'amura masu nauyi suka dabaibaye shi. Ya rasa me yasa yake yawan jin fad'uwar gaba matuƙar ya d'ora idanuwansa akan Abida. Bai zaci sonta na da k'arfi a zuciyarsa ba har yanzu. Ba sonta ya daina ba dama, amma dai ya yi raunin da yake jin zai rabu da ita, rabuwa ta har abada kuwa. Don bai yi lalacewar da zata zagi uwarsa ya kuma tsaya rarrashinta ba. Bayan haka ta cire ciki nisa hujjar ba zata sake had'a jini da shi ba. Duk kuma aka zuba mata ido saboda sahaffafiya ce y'ar Madara. Ya juya yana tuno siradin da ya tsallake wanda bai samu kansa ba sai shekara d'aya da ta shud'e. Tunda ya bar Nigeria ya isa Germany kwanansa biyu kacal gwamnatin k'asar ta kama shi tare da wasu bakaken fata su uku bisa zargin suna kai yara mata k'ananu karuwanci k'asar ba bisa k'aida ba. Birinin Barlin ya sauka. Ya yi niyyar ya dan yi kwanaki biyu kafin ya wuce birin Hermburg. Da aka tsananta bincike sai aka sake jingina masa laifin ya shiga k'asar ne ta haramtacciyar hanya. Ya yi kokarin nuna shaidarsa amma ya nemi passport d'insa sama ko k'asa ya rasa. Wanda ba shi da laifi ko kad'an illa mugayen mutanen da suke aikata laifin sun had'a wurin zama a jirgi da shi. Da aka kamasu ne don tsananin k'eta da mugunta suka ce tafiyarsu d'aya da shi. Haka aka tattrata aka kai su prison. Ba'a waiwaiye su ba sai da suka shafe watanni goma sha uku. Bisa hujjar da embassy ta gabatar basu shiga k'asar legally ba don haka ba zasu bibiye su ba. Sa'a daya ma kurkukun ba irin namu ba ne. Amma dai kam nadama da kaicon barin gida Sulaiman ya yi shi yafi cikin kwando. Kan dole ya hak'ura ya koma ga Allah ya dinga Ibada tukuru. Amma gabad'aya ya gigice da tunanin makomarsa. Idan ya mutu a wajen nan shikenan ba wanda zai san ya mutu. Idan ya tuna Bilki, Baba da Farha sai ya sake rikicewa k'warai da gaske su kad'ai ne idan ya tuna su ya kan ji rauni na kama shi. Yana cikin haka kwatsam tawagar likitoci da hadakar kungiyoyin jin k'ai daban daban suka kai ziyara gidan yari. Nan ya ci karo da babban malaminsa kuma ogan asibitin da ya yi aiki da su shekarun baya. Da madaukakin mamaki yake tambayar Sulaiman ba'asin zamansa. Tiryan tiryan Sulaiman ya yi masa bayanin azal din da ya fad'a ya nuna wanda yake sanye da irin kayansa ya ce "Ga masu laifin nan daga k'asar Alge suke. Sune da alhakin komai." Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 15:59] Gabad'aya aka kamu da tausayinsa don kuwa hatta b'acewar passport d'insa sune suka cire masa a ƙaramar jakarsa bayan sun isa masaukinsu a ranar da suka sauka a birinin Berlin. Sai da suka ga sun dade a gidan suke neman afuwarsa tare da ba shi hak'uri wanda ya zama na banza. Gabad'aya wajen duk jikinsu ya yi sanyi tare da tausayin Sulaiman k'warai da gaske. Haka wannan Malamin da sauran kungiyoyin suka shiga al'amarin Sulaiman bayan an kai komo mai yawa sannan ya shaki iskar y'anci bayan watanni biyu. Idan an fahimta Sulaiman ya shafe watanni sha biyar a gidan yari a babban birinin k'asar Jamus. Da ya fito yana k'arkashin kulawar hukumar jami'iar da ya yi karatu da taimakon kungiyoyin sa kai. A haka dai har kes d'insa ya kai gaban mahukuntar k'asar da taimakon ofishin jakadancin Nigeria a k'asar. Watanni biyu da fitowarsa ya samu aka yi masa passport din da zai iya barin k'asar sannan gwamnatin k'asar ta ba shi makudan mahaukanta kudade don ya rage radadin bata masa lokaci da aka yi ba bisa hakkinsa ba. A lokacin ya so barin k'asar amma malaminsa ya hana shi, ya saka ya koma makaranta don ya sake kwarewa a b'angaren ido wanda zai yi kwas na watanni goma sha biyar. Gabad'aya nadama da danasani sun masa k'awanya. Ya tabbatar hakkkin barin Baba Babba a halin jinya ba tare da ya yi masa sallama ba, bare ya saka masa albarka ne ya sanya ya hadu da taskun duniya. A dole ya zauna yake karatun nan. Ya kammala karatun cikin nasara, da ya ce zai tafi gida shine aka tura shi aiki asibitin k'asar Jamus da ke Birnin Riyadh, da nufin Idan ya fara aikin a hankali Sai ya je ya Ga iyalinsa. Watansa shida aka dawo da asibitin da yake birinin Makka. A yanzu watansa biyu a birinin Makka. Zuwa lokacin hankalinsa ya karkata matuk'a da son komawa gida don ya murmure ba wanda zai gan shi a tagayyare, kud'i kuwa ya yi shi ba na wasa ba. Yana yawan tuna Baba dasu Hamida. Bilki kuwa yana da labarinta Hatta ajiye aikin da ta yi ya ji, da barinta Katsina ta bakin abokinsa Salim Buba wanda sanadinsa ya samar mata aiki a UmYU. Wanda ya samu lambarsa a Facebook ne bayan ya fito da gidan yari. Sai dai bai ji labarin auren da ta yi ba. K'arshen wata dama ya yi booking din tafiya Nigeria sai kuma suka yi kicibis da shi a tsakiyar wata. Ya juya ya numfasa wato ba k'aramin nauyi da kunyar Baba ne suke yi masa rubdugu ba. Zai bi shi Nigeria zai kuma karbi dukkan sharuddan da zai gindaya masa, amma kam bai huce da Asad da Abida ba. Yana kwance yana hakaito ta, tabbas har yanzu bai ji ya tsane ta ba, amma kuma a shirye yake da ya rabu da ita don kuwa uwarsa tafi komai a wajensa. Matar da yake aure kuwa ta yi kad'an ta rainata ko ta fadi maganganun banza akanta ta kuma kwashe k'alau. Har a bayan ranta tana da alfarma matuƙar yana shakar numfashi. A yadda kuma yake ganin take takenta tanan nan da sauran zafin kanta, bai gama goge mata hadda ba. Ya nisa a fili ya ce "Da sauran ki kuwa, da sannu za ki gane na kerewa duk wasu tsiyatakunki." *Abuja* Bilki na zaune a d'akinta k'arfe shabiyun dare tana bawa Baba K'arami nono. Alti na zaune tana jiran ta gama ba shi ta mik'a mata Shi tunda ita take barci da su. Kira Sai shigowa wayarta yake yi ba kakkautawa. Ta Kuma san oga ne. Kan dole ta amsa k'iran.urya ba amo ya ce "Ki kawo mini shayi yanzu." Daga haka ya katse wayar. Har d'aya saura kwata bata tashi ba, ita kuma Alti bata san komai ba. Amma ita da kanta tana ganin tunda Bilki ta fara sallah tuntuni ya kamata ta koma turaka mussaman da ta ga sati biyu da suka suka wuce an kawo mata kayan mata na mussaman daga Kano na Bojuwa herbals 08032773332. Ita ce ma ta dumama mata kazar da ta iso da sanyinta tunda idan wani garin za'a tura sai an yi freezing dinta ta zama kankara sosai gudun kada ta lalace ko ta yi tsami. Haka na matsi duk ta kammala amfani da su da taimakon Alti da take tafasa mata., Sanyi flusher kuwa tun dadewa aka kawo ta sh na sati biyu. Amma duk wannan gyaran da take yi bata ga tana zuwa wajen miji ba. Shiyasa yake yini da kwana yana zarya tsakanin samansa da na Bilki wanda Alti take jin kunyar hakan k'warai da gaske. Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 16:00] Cikin rarrashi da girmamawa ta yiwa Bilki magana da ta ga wayar da ta amsa don tasan ba mai k'iranta a daren sai shi. "Mahmah gaskiya fishin ya isa indai ba so kike na bar miki gidan ba. Yini yake yi yana son ya faranta miki, magana d'aya tak idan kika yi masa kamar an masa bushara da gidan aljanna don zumudi amma sai tumbatsa kike sake yi kullum. Idan fa kika koya masa jurewa fishinki ke ce a ciki. Haka nan irinsu Alhaji fa da kud'i da ilimi ya zauna musu har ofis dinsu ake kai musu mata da suka kai mata. So kike sai ya fad'a tarkon shaidan ne. Haba abin ya yi yawa fa gaskiyar magana. Ki tashi ki sake wanka ki tafi dakin mijinki." Da rawar murya ta ce "Allah Alti nima ina son na huce amma gaskiya ba zan je d'akinsa irin zuwan da kike nufi ba, kowacce kusurwa fa hotonsa da na matarsa ce. Ya je na barwa hoton shi. Kuma fa abu kad'an sau ya ce ita ba haka take yi masa ba, ita mai biyyaya ce" . Ta fara kuka sosai. Alti ta yi sakare tana mamakin Kishin da take ganinsa har a idanuwanta. Wanda ita kam bata ga ta yi kishin Hawwah irin haka ba. A fili ta ce "Tirk'ashi. To ban da abinki Mahma ba sai ki fad'a masa a hankali cewar ba kya so ya daina ba, sannan da kin iya AI da tuni an cire hotunan daga dakin ya dawo da su dakin y'ay'anta". Ta girgiza kai ta ce "Da Dai yana sona ne zai yi hakan, nima ai mun yi hotunan da suka fi nata kyau ma amma bai girke su ba , saboda baya sona". Hawaye ya sake k'wace mata. Alti ta numfasa tare da fad'in "ko makaho ya zauna da ku yasan yana sonki mana, ki yi hak'uri, ki kwantar da hankalinki da sannu za ki mayar da shi irin yadda kike son ya zama. Amma wannan fishin da kauracewar da kike yi masa nisanta kanki kike yi a zuciyarsa fa". Daidai lokacin k'iran ya sake shigowa bata amsa ba suka ji an yi knocking k'ofar sau d'aya. Kan dole ta bawa Alti yaron ta d'auki hijab ta saka sannan ta fita. A bakin k'ofar ta gan shi. Ya saka hannu ya ruko nata hannun. Bai ce komai ba, itama bata ce komai ba, tiryan tiryan har samansa. A falo ta turje ta ce "Bari na hado maka shayin". Ya girgiza kai tare da fad'in "Ke nake bukata ba shayi ba, tunda ke ba kya gane al'amura sai an bayyana miki". Ta bata fuska ta ce " To zo mu je wajena". Da hanzari ya ce "Alti ta nan ga yara nan kin dawo da su kwana wajen ki, shine nima zan je cikinsu na kwanta?" "D'akina guda nawa ne?" Ta tambaye shi idonta a cikin nasa. Ya juyar da kai ya ce "Ina ce d'aya d'akin su Amal ke kwana a ciki?" Ta ce "To d'ayan fa na kusa da shi?" Kaitsaye ya ce "Amma dai kinsan zasu iya jina tunda bana iya kama bakina idan ina tare da ke ko?" Ta ce "Sai ka fara rikewa ko na samo salatif na manne maka shi". Ya zuba mata ido baya son ya tunzura tunda a matse yake. Kan dole ya kwantar da kansa cikin rarrashi ya ce "Tunda fa kika zo gidan nan sau uku tak kika kwana mini kullum ni nake bin ki. Tunda yanzu gun na ki da mutane ya kamata ki mutunta ni ki dinga zuwa mini, ta ya ya zan yi ta jele a gaban yara da masu aiki fisabidillahi fa Maigado?" Ta cuna baki tare da juyar da fuska gefe. Ta kasa bude baki ta ce masa hotunan matarsa ne ba zasu bari ta iya kwna ba. Ganin tana tsaye ba alamun zata yi masa yadda yake so ya sanyaa shi fad'in"Shikenan je ki abinki, tunda ba son yi kike yi ba. Idan na matsa ma b'acin rai zan tarar, je ki kawai Allah ya bani ladan hakuri. ". A sanyaye ta juya ta bar shi. Amma ta kasa shiga dakinta. Tunda ta sauko tana zaune a falo har aka aka fara kirayekirayen sallar asuba. Tana zaune ya zo ya wuce ta ya yi k'asa dan zuwa masallaci. Jikinta ya sake sanyi don ta ga ya koma Yaya Asad ba Baban Bilkisu ba. Da ƙyar ta ja jikinta ta shiga dakin. Alti ta dinga yi mata sannu. Wanda kunya ta dabaibaye ta. Bayi ta fad'a ta doro alwallah. Bayan sun gaisa Alti ta kalle ta ta ce "Basu su sha sai ki kwanta ki yi barci ki huta". Ita dai ba baki don gabad'aya wani iri take jinta. Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 16:02] * Karfe shida na asuba jirgin da Baba da ahalinsa suke ciki ya sauka a filin saukar jirage na Nmadi Azikiwe na birinin tarayyar Abuja. Tare da Dr Sulaiman. Bai sha wahalar sahalewar hukumar asibitin ba tunda dama tun watan jiya ya mik'a takardar neman izinin zai ke gida. An ba shi watanni biyu. Yaya Asad da tawagarsa suka zo ɗaukansu, don suna idar da sallar asuba suka nufi airport din. Motocin da suke biye da motar da yake ciki guda uku. Mamaki ya kashe oga Asad da ya ga Sulaiman rike da Baba suna tafiya a hankali yayin da Faruku yake binsu a baya da k'aramar jakar Baba a hannunsa. A kan dole Sulaiman ya shiga tsaleliyar motar oga Asad da ya zo a ciki don d'aukar Baba da da Momi. Yayin da Abida da Faruku suka shiga d'ayar. Mutanen da suke airport suna kallon y'an gatan tsofaffin da aka zo d'aukarsu in comboy. Bayan haka yadda yan snada suke sarasu musu abin sha'awa ne k'warai da gaske. Oga Asad da shi yake tuka motar da kansa. Ya kasa hak'uri ya ce "Baba a ina kuka ga wnanan yaron?" Baba da yake fama da mura ya ce "A Saudi ikon ai ikon ALLAH yafi ga hakan. Addu'armu ta karbu sai ga shi kamar jifa Abida ta gan shi, da yake nemansa take yi, sai ta yi jarumtar rike mini shi da ai so ya yi ya tsere". Momi ta ce "Ba tserewa fa zai yi ba Alhaji! Kaucewa rik'on da Abida ta yi masa yake yi". Daga Baba har oga Asad suka kece da dariya yayin da Sulaiman ya matse. Bai bude baki ya gaida yayan nasu ba. Shi ma kuma oga Asad bai ce masa kanzil ba. Har suka isa gida Sulaiman kala kanzil bai ce ba. Daman Baba Babba bai faɗa ma kowa sun ga Sulaiman ba, ya kuma ce Faruku da Abida kada su faɗawa kowa, su bari kawai sai dai a ga Sulaiman ɗin kawai. Karfe takwas da rabi daidai a falon gidan ta yi musu. Oga Asad ya tunzura iya tunzura ganin ga shi ga Sulaiman amma uffan bai ce masa ba yana jira ne shi ya gaishe shi kenan? Alhalin har magana ya yi masa yana tambayar a ina aka gan shi. Bayan duk wulakancin nan da ya gwada musu shine zai sake dawowa da mugun kulli a ransa? Cabdi jam aikuwa sai dai Baba ya yi hak'uri ba zai dauki wannan rainin da iyashegen da yake ga ni a idanuwan Sulaiman ba. Ya rasa me ya yiwa y'ay'an mami gabad'ayansu sun washe shi tamkar shi ya kashe ta ko kuma rashin zuwa yi musu ta'aziya an fad'a musu ba za'a yi mata Rahma a dalilin bai je ba. Haba ya gaji, ko Bilki ma ya yi imanin ba iya abin da ya yi mata ya sanya ta bijire masa haka ba. Gabad'aya ta taurare babu wata alama na tana sonsa ya yi imanin maganganu take ji iri iri akansa a bakin makusantanta. Shi yanzu ma ga ni yake gidan mijinta take son komawa. Ya gama gasgata k'arfin k'addara da rabon haihuwar twins ya sanaya ya kafe ya matsa sai da ya aure ta, ban da haka mai ma zai saka ya kafe akan ta irin haka ne? Tunda ya san ba sonsa take yi ba, alfarmar Faruku ya shiga. Cikin mintina k'alilan ma'aikatan gidan suka baibaiyeshi da cima iri iri tare da yi musu barka da zuwa cikin farinciki da girmamawa. Abida ta shige daki tana son ta faɗawa Bilki kiranyensu ya karɓu sai kuma ta cije ta hak'ura tunda Baba ya ce kada a faɗawa kowa. Sai da ta yi wanka ta fece da kwalliyar da aka jima ba'a ga ta yi irinta ba, ban da sunan twins da ta taya Bilki yin kwalliya. Amma ko sunan junior haka ta yi shi babu kwalliya babu kuzari. Sai da ta daure fuska iya daurewa sannan ta fita falon inda ake karyawa. Zuciyar Sulaiman ta buga da ganinta k'amshinta ya kai masa caffa. Ya yi iya kokarinsa wajen kin dagowa amma daga k'asa idanuwansa na kanta. Ta zauna kusa da Baba ta fara serving kanta. Baba ya ce "Abida har kin yi wanka? Irin wannan gayu haka Sulaiman aka yiwa ko kuwa har za'a tafi dauko junior ne?" Nan da nan ta samu mafita don kuwa ba wacce take son ga ni irin Bilki. "Baba zan je na ga Bilki tunda mun barta babu lafiya daga nan sai na d'auko shi". Baba ya murmusa ya ce "To ki yi mata albishir wataƙila ma nasan ta biyo ki". Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 16:03] Nan da nan oga Asad ya mik'e ya yiwa Baba sallama akan zai je gida sai yamma zai dawo. A zuciyar Baba bai ji dad'in rashin gaisarwa da basu yi ba. Yasan dai oga Asad ba zai taba yarda ya gaisar da Sulaiman ba. Ai ko Usman da ya girmi Sulaiman da watanni uku suka taso tare ba zai yarda ya fara gaishe Shi ba bare Asad. Har Ila yau Baban sai ya tsinci kansa da jin tsoron ya ce da Sulaiman ya bai gaisa da yayansa ba? A ran Baba ya dinga jinjina wannan zamanin da ya riske Shi mai wuyar sha'ani yadda kirikiri ake kin tsoron y'ay'a. Da ace zai iya canja zuciyar Asad ta zama irin tasa da ya yi, to ikon sarrafa zuciya ba'a hannunsa take ba. Halin Baba K'arami ne da shi, Duk juyin da aka yi kuwa ba zai risinawa na k'asansa ba mussaman idan shima yana ganin akan gaskiya yake. Gabad'aya Baba ya ji ya takura don kuwa rashin jituwar Asad da Sulaiman tana nufin al'amura masu yawa marasa dad'i. Dukkansu kowa zai samu k'anne magoya baya, gyaruwar zumnta a tsakaninsu zai yi wahalar gaske matuk'ar wadannan biyun da kowa yake babba basu jitu ba. . PAGE 14 Makullin motarsa ya bawa Michel akan ya ja shi don gabadaya ya rasa nutsuwarsa ai kuwa la shakka sai ya lallasa Sulaiman kafin ya kiyaye Shi. Shi zai ga ni ya kalle shi ya watsar? A fili ya ce "Wai me na yi musu ne?". Ba sukuni Bilki ta ga ya dawo ya wuce wajensa ko ganin twins da ya zame masa k'aida kafin ya k'arasa wajensa bai yi ba. Haka ya wuce ta tana falo bai ce mata kanzil ba. Ta sake jin babu dad'i don a yanzu shima shariyar ya d'auka. Ya daina kula ta ko kad'an. Zai dai je ya ga y'ay'ansa, ya tambayi Alti lafiyarsu. Ko so yake a kai masa su sai dai ya saka Hafcy ko Bilkisu su kai masa. Idan kuwa suna school Aysha yake sawa ta dauko su. Amma tsakaninsa da Bilki ido ne. Ko ta gaishe shi a fizge ko a ciki ciki yake amsawa. Alti kuma ta saka ta a gaba da fad'in ai hakan ya yi mata kyau. Ita kam bata taɓa zaton zata yi haka ba. Dazu ma Alti har cewa ta yi idan ta yi sanadin da aurenta ya mutu Wallahi ba zata bita gidan baba Babba ta zauna ba. Ita tana da kunya sai dai ta tafi gidan gajiyyayu. Daga haka kuma ta dinga yi mata kuka tamkar dai mutuwa aka rafka. Bilki dai ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi. Tsakaninta da Allah oga Asad ne ka cin zalinta ta hanyar son kansa da yawa. Amma yanzu ya fitittike ya dauki gaba mai tsananin gaske don kawai ta k'i zuwa d'akinsa kwana. To yanzu ya zata yi masa kenan? Ta bi shi da ido tana ganin yadda yake tafiya gaf gaf tamkar zai kifa. K'afar bene ma bibbiyu ya dinga hadawa. Sai da ya b'acewa ganinta sannan ta numfasa tabbas ta takura da fishinsa sai dai tana nan a kan ra'ayinta ba zata je d'akinsa da nufin wata mu'amala ba matuƙar da waɗannan hotunan. Sai dai Alti ta yi hak'uri kawai. Ba jimawa soaai da dawowarsa Abida ta iso. Kusan a guje ta hawo saman tamkar yadda Farha take yi. Bilki ta zabura tana fad'in "Lafiyarki kuwa?" Suka rungume juna, kafin Abida ta ce "Allah yasa Dady bai shigo ya riga ni fad'a miki ba". Bilki ta ce "Ya shigo a gaggauce ya hau sama ko ta kaina bai bi ba. Gaba ya k'ulla da ni haka siddan". Abida ta rausayar da kai ta ce "Kina masa taurin kai ne, shi kuma haka yake da tauri tamkar goruba, amma zan samo mana mafita don na lura ba abin da yake tasiri akan rijalu irin a yi ta buga musu addu'a a sujjuda idan ba haka ba, a tsaye zamu mutu da bak'incikinsu! Bilki ta jinjina kai tare da fad'in "To Abida". Daga haka Abida ta ce "Jarida ce zan siyar miki da farashin da ban taba siyar da ita ba". Bilki ta fad'ada murmushi tare da fad'in "Idan jaridar d'auke take da kiranyenmu ya ci Malam Sule to tabbas zan siye ta da k'ololuwar tsada k'anwar Bilki". Abida ta ce "Kin riga kin sa ni Idan na fesa miki labari sai kin biya kudin dan haka Ki shirya". Bilki ta ce "fad'a mini kawai, Ni kuwa ba zan yi k'wangen Baki farashi Mai daraja ba tunda har yanzu baki gaji da tara dukiya a dalilin jaridarki ba." "Da murmushi sosai ta ce "To Dai kiranyenmu ya kama jikan Malam Uzairu sai muka yi kicibis a Saudi". Bilki ta gigice ta kasa magana. Da kyae6ta daidaita tunaninta ya ce "Kina nufin wai kun gan shi ra'ayil ayni?" Da k'arfin guiwa Abida ta ce "Sosai fa, na fad'a miki ya dinga guje guje Sai da Allah ya Bani sa'a na yi ram da shi. Ba yadda bai yi ya kubucewa rik'on da na yi masa ba ya kasa k'wacewa hae sai da na damka shi a hannun Yaya Faruku. Yaya Faruku kuwa ya tisa shi har gaban Baba. Baba kuwa ya taho da shi yanzu haka na barsu a falo suna cin abinci." Bilki ta sake kidimewa ta ce "Alhamdulillahi lallai kuwa na siya wannan jaridar don shine labari Mafi dad'i a cikin dukkan labaran jaridarki Abida!. Amma Baban Bilkisu bai san ya dawo ba ko?" "Ya sani mana ba da shi aka je d'auko mu ba, Yaya Sulaiman din ma tare da bada momi motar Dady din suka shiga". Jikin Bilki ya yi sanyi wato fishinsa har ya yi tsananin da ba zai fad'a mata wnanan daddan labarin ba? Lallai oga Asad ya fita iya gaba. A sanyaye ta ce "Bai fad'a mini ba ba fa Abida ". Abida ta ce "Hmm haka yake yiwa wacccar matar fa, ranar da na ji tana faɗawa shegiyar Surayya nan wai ya fi k'arfinta a shimfida, a ranar na ji tana kukan idan ta nemi bijire masa kuma ko ta nuna ta gaji sai ya yi fiye da sati biyu yana yi mata fishi mai tsananin gaske. Yanzu mu hadu mu sake had'a kanmu Bilki. Dama ni da ke bata b'aci kada ki kalle ni a k'anwar miji, nima ba zan miki kallon haka ba. Kawai mu taimaki kanmu, mu hadu mu wasko kan wadannan tsayayyun mazajen da Allah ya had'a mu da su. Idan ba haka ba zamu sha wuya a hannunsu. Yanzu mu je ki gaishe shi, sai ki faɗawa Baba ni na yafe masa rataye nin da ya yi babu waiwaiye, kawai ya ba shi Umarni ya d'auke ni salin alin mu tafi gidanmu. Idan kika yi haka to ni duk sababinsa indai ina gidansa zan jure, ina da wuridi iri iri da zamu dinga yi har mu raunana zukatansu." Dariya ta k'wacewa Bilki mai tsananin gaske. Yayin da Abida ta tunzura ta ce "To Bari na tafi kowa ya yi ta kansa tunda na ga alamun halin da kike ciki bai yi tsananin da zai hana ki dariya irin haka ba. Ni kuwa idan ba gani na, na yi a d'akin jikan Malam Uzairu ba, ban ga ta dariya ba. Kuma Wallahi idan ba ki taimake ni ba, ki tabbatar nan gaba ganina sai ya yi miki wahalar gaske bare ki nemi shawarar yadda zaki yi da wannan murdadden ba". Na da nan Bilki ta gintse dariyarta "To Abida, zan iya k'ok'arina! Ta fadi hakan da dukkan zuciyarta. Don a yadda take ganin oga Asad a kwanakin nan yana iya zabga mata mari don gabad'aya ya murd'e fiye da azancinta. Ta ciro zoben hannunta guda daya wanda na gold ne ta mikawa Abida tare da fad'in da wannan na sayi jaridarki". Abida ta karɓa ta ce "Lallai kin ji dad'in labarin nan na gode". Ta mak'ala shi a hannunta. Ya mike ta ce "Zamu tafi tare ne ko sai anjima za ki zo?" Bilki ta ce "Bari Alti su dawo na aikesu kasuwa tare direba ta tafi da junior. Kada su dawo bai ganni ba". Abida ta kalli agogo ta ga shabiyun rana ta gota ta ce "Sun jima da tafiya ne?" Bilki ta daga kai tabbacin sun jima din". Daidai lokacin kuma suka ji ana bude musu gate. Junior ya fara haurowa yana fad'in Mahmah Alti ta siya mini ball". Hannunsa d'auke da madaidaiciyar ball mai kyau. Ya yi turus ganin Abida sai kuma ya kwasa a guje yana fad'in "oyoyo Ammi". Ta dago shi tana fad'in "oyoyo my boy, ina su Yaya Noor da Yaya Farha?" "Suna school. Ammi nima a saka ni a school dinsu". Ta ce "To mu je ka faɗawa dadynka ya dawo". Ya zabura ya ce "Na pics din wayarki da kike fad'a mini zai dawo anytime?" Ta gyada kai ta ce "Shi fa kuma ya dawo junior ". Ya falfala d'akin Bilki ya dauko jakar kayansa ya kalli Bilki ya ce Mahmah sai wata rana". Haka kawai zuciyarta ta karye don kuwa irin haka Faruk ya ce mata a ranar da zata bar Katsina a harabar makarantarsu. Ga shi yaron kama yake yi da Farukun. Daidai lokacin Alti ta shigo falin hannunta d'auke da leda. Da murmushi take fad'in "Lale da mutanen Saudiiya, yasu Baba, ya kuma ibada?" Fuska a sake Abida ta amsa mata tare da tambayar lafiyar tagwaye. Daidai lokacin ta mik'e ta nufi d'akin Bilki don ta ga yaran da bata tambaye su ba sai yanzu. Bilki ta bita yayin da Alti ta had'a ruwa da lemo ta soya samosa ta kaiwa Abida. Bilki ta kalli junior "Zo mu je ka yiwa Dady sallama". Ya bita suka je. A zaune suka same shi ya rik'e kansa da hannuwansa. A sanyaye ta yi sallama ya amsa a ciki. Junior ya ísa kusa da shi ya yi saluting d'insa don sosia junior yake son ya yi masa haka. Oga Asad ya ya sauke hannunsa ya ce "Magajin Dady ya kake?" A nutse junior ya ce "Dady Zan tafi ammi ta ce "Dadyna ya zo". Oga Asad ya ce "To ka gaida Momi ya mik'a hannu ya janyo office bag d'insa ya fito da bandit din Yan 500 ya ce "Ga shi ka kaiwa a5mmi ka ce ta kaika ka yi shopping tunda har zaka tafi baku je shopping din ba." Ya karɓa da hannu biyu, ya mikawa Bilki shi Kuma ya kame ya yi gaisuwa gidan tsaro Wanda oga Asad dariyar da bai shirya ba ta subuce masa don yaron tamkar Wanda ake training d'insa. Kan dole ya mike Shima ya yi saluting d'insa tare da fad'in God bless you future police." "Thank you oga." Ya furta tamkar ba dan shekaru uku ba. Ya juya ga Bilki ya karbi kudinsa ya fice a guje. Bilki ta tsinci kanta da fargabar yi mass magana don ya tsare gida iya tserewa. Jikinta ya sake mutuwa wato Duk faricincikin da ake ciki na ganin Yaya Sulaiman ba zai saka ya huce Har ya nemi yi Mata albishir ba daga nan su shirya kansu ba. Kan dole ta ce "Zan bi Abida na Ga yaya Sulaiman ta ce ya dawo ". Ya yi bakam tamkar dai ba da Shi take ba. Ta sake maimatawa. Cikin nutsuwa ya zuba mata idanuwansa ya ce "Ba za ki je ba, daga nan har kwanakin wata kada ki sake ki ce mini za ki fita". Daga haka ya mik'e ya shige cikin d'akinsa. Idanuwanta ya cika da k'walla. Ita tunda ta yi aure ba'a taba hanata fita unguwa ba. Ko wani Gari zata je idan ya ce ba yanzu Idan ta nuna lallai tana son zuwa baya zafafawa, bare kuma Idan a cikin gari ne d'aukar mota take yi kawai ta je ta yi uzzirinya baya tambayar ba'asi. Babbr damuwar Bilki yadda ya fitittike ya koma mata wanccan azabben Asad din mai dealing din kannensa with iron hand. Yayin da shi kuma haushinta da na y'anuwanta da suka tsangwame Shi haka siddan ne ya tayar masa da hankali. Wai Shi Sulaiman zai ga ni a gaban Baba amma ya kasa bude baki ya yi masa magana. To Idan Baba na jin tsoron kada ace ya yi son kai tabbas shi baya tsoron maganar mutane sai ya ci masa mutunci ya tuna masa lokutan baya da yake saka su kneel down a rana ko frog jamb shi da Usman. Sannan idan Hamida bata kiyaye Shi ba Sai ya taka har gidanta ya ci Mata mutunci tunda ya gama nazarinsa ita da Sulaiman sune kan gaba wajen gaba da shi to duk zai ci kazar ubansu ya danna ashariya a fili. Wato rashin zuwa su ha twins ba fa k'aramin soya k'irjinsa yake masa ba, wanda hakan ne ya sanya ya sake tsananta fishinsa da Bilki tunda ya tafi a fahimtar zugata suke yi ta dinga wulakanta shi wanda ta yi kad'an. Ya kuma gasgata da a wani gidan ta haifi yaran ba a gidansa ba zasu so. Abin da Sulaiman ya yi masa a yanzu kuma ya sake gigita Shi don Ki yake tamkar ya yi ta zunduma ihu da iyakacin k'arfinsa. A kasalance ta koma wajen Abida. Murya na rawa ta ce "Ya hana ni fita Abida. Ko za ki masa magana?" A zabure ta ce "Ban isa na yiwa Dady magana a yanzu ba, ai tunda na ga ya fito a gigice nasan a birkice yake haka nan tunda Bai fad'a miki dawowar Dr Sule ba nasan to kin yi saken da zai fara yi miki fitinannen fishinsa mai cunkushe mak'oshi." Hawaye ke zarya a fuskarta wai duka aure haka yake zuwa da k'alubale. Shi ya yi mata laifi, sannan ya girke hotunan matacciya a d'akinsa da falonsa bayan haka motsi kad'an ya ce ta fita Kaza, Shai ba haka aka Saba masa, Duk bai yi tunanin yadda take jin ciwo a ranta ba,sl Sai Kuma ya gindaya gaba Mai tsauri irin haka a tsakaninsu? Ace Sulaiman ya dawo amma ya kasa fad'a mata? Ta ce zata je ta gan shi ya ce ba zata ba don gadara da son ya musguna Mata. Yayin da Abida ta sake tsotaya da lamarin maza wato dama har yanzu ana hana mace zuwa wajen da aka san mai muhimmanci ne a wajenta. Nan Duniya Sulaiman na cikin abubuwan da suke da daraja hadi da muhimmanci a duniyar Bilki. Ya yi shekaru kusan hud'u ba'a san inda yake ba, ya dawo kuma a hanata zuwa ta gan shi? Ita da kanta Abida al'amarin ya girgizata tana auna tamkar itace ta ce zata je ganin oga Asad bayan an shafe shekaru ba'a san inda yake ba ace kuma miji ya ce ba zata ba. "Tirk'ashi! Ta fad'a a bayyane. Ganin Bilki na kuka sai ta yi maza ta had'iye kaduwar da ta shiga ta ce "Share hawayenki, idan ya yarda zan rakito shi mu zo ya ga twins." Cikin kuka Bilki ta ce idan bai yarda ba fa?" Abida ta ce "Zan saka Baba ya yiwa Dady magana ya bari ki zo." Ta goge hawaye ta ce "To". Amma k'asan zuciyarta ya yi mata nauyi tare da jin k'ololuwar gajiya da zaman gidan oga Asad kisan mummuke kawai yake yi mata. Haka Abida ta tafi da junior. Sai da Bilki ta shanye kukanta sannan ta fad'awa Alti Yaya Sulaiman ya dawo. Alti murna sosia ta dinga tare da adduar Allah yasa ya dawo kenan. Bilki ko jikinta ya sake sanyaya don kuwa Idan ba sa'a ba Yaya Sulaiman ya yiwa oga Asad wulakanci shiyasa ya dawo a firgice bai kuma fad'a mata ya dawo ba, sannan ya hanata zuwa wajensa. A ranta kuwa ta san rikice ne zai sake tashi sai dai Allah ya shiga al'amarin kawai. .. Sulaiman ganin Abida ta fita ya sanya ya tausasa murya ya ce "Baba ina son na wuce yau. Amma zan dawo na ji sharadina da zaka gindaya mini satin sama". Mamaki ya tuke Baba a zaune Ya nisa ya ce "Ina zaka ke Sulaiman" Kansa a k'asa ya ce "Zan je Katsina Baba." Baba ya girgiza kai ya ce "Za ka je amma ba yanzu ba". Ya yi shiru ya ce "To Baba zan dan shiga cikin gari gobe zan dawo in sha Allah". Ran Baba ya yi k'ololuwar b'aci ba zato ya suri robar ruwan Eva da ba'a bude ba, rab'a ta lullube robar saboda sanyin ruwan. Da dukkan k'arfinsa ya kantaraqa Sulaiman a gadon bayansa. Babu zaton Sulaiman ya ji saukar dukan ya karade jikinsa a gigice ya mik'e yana waiwaiye tare da tunanin oga Asad bai tafi ba ne, don bai taba tunanin Baba ne ya kwada masa abu haka ba. Don kuwa suna k'ananu ma bai tana dukansu ba. Murya ba amo Baba ya ce "Ni ne na kwada maka ba kowa ba, matso nan". Sulaiman ya tsugunna nesa da shi don gabadaya ya rikice. Muryar Baba na rawa ya ce "Matso nan Wallahi Sai na Ƙara maka." Da sauri Sulaiman ya rarrafa gaban Baban kansa a kasa don ya kubutar da shi daga yin kaffara. Baba kuwa ya cire tausayi da rauni ya shiga kantara masa jarkar nan har a kansa ya dinga maka masa. Momi ta fito ganin Baba na dukan Sulaiman da iyakacin k'arfinsa l, shi kuma yana durk'ushe yana dan karewa da hannuwansa idan za'a kwada masa a kansa. Da hanzari ta iso ta janye shi tana fad'in "Yi hakuri, ayi masa nasiha dai ai ya wuce duka Alhaji". Hawaye na zuba a idon Baba ya ce "Da yake idan mutum ba shi da mahaifa sai gata ya yi masa yawa, sannan babu mai iko da shi ko?" Momi ta fashe da kuka tana fad'in "A a ba haka bane Alhaji". Yayin da Sulaiman yake durk'ushe hawaye na tsere akan fuskarsa wanda na tausayin Baba ne, ba na dukan da ake yi masa mai shiga kansa ba. Da rawar murya baba ya ce "Duk wulakancin da wannan yaron ya yi mini na jure na karbe shi, shine ya samu kuzarin fad'a mini zai tafi ya samu masauki saboda nan ba gidan ubansa bane! Da ace ubanka na da rai da ka ga yadda zan saka a zane mini kai, amma tunda babu shi, sai na yi maka iya yadda zan iya don wataƙila idan na saka guda cikin yayunka su lallasa mini kai, za ka yi zaton na saka ya'yana sun ci zarafinka tunda ni na haifesu.! Hankalin Momi ya yi tashin gauron zabi a dalilin yadda ta ga Baba ya shiga matsanancin b'acin rai. Ta dinga ba shi hak'uri tare da kokarin kwantar masa da hankali. Yayin da Sulaiman yake kuka marar sauti. Daidai lokacin Abida da junior suka dawo. A guje ya shigo sai dai ya yi turis ganin Momi da Baba suna kuka. A sanyaye ya ce "Menene?" Kafin su ba shi amsa Abida ta shigo. Ganin suna kuka bai bata mamaki ba. Sai kawai ta durk'use kusa da Sulaiman da kansa ke k'asa. Ta tausasa harshe ta ce "Ka yi hak'uri Baba! Dan Allah dan Annabi ka yafe mana ka cire mu a cikin sahun waɗanda suke tayar maka da hankali. Ni dai na bi Allah na bika, na yi kuskuren bijirewa umarnin da ka ba ni, akan na koma d'akina, yanzu kuwa tunda Allah ya sa ya dawo to zan tabbatar na gyara kuskuren da na yi, zan bi umarninka, zan bi shi duk inda za shi zan kuma zauna lafiya da shi". Baba ya ce "Ke ma ban isa da ke ba, bare shi da yanzu ya tabbatar mini ni ba ubansa ba ne, alhalin ubansa ma ni ubansa ne". Sulaiman ya dago da fuskarsa da ta yi face face da hawaye ya ce "Wallahi Baba ba hakan nake nufi ba". Dak'uwa Baba ya yi masa tare da fad'in ka ci ubanka! Me ka ke nufi to? Matso nan". Momi ta ce "A a Alhaji ai ya daku bar shi haka dan Allah! Yayin da Sulaiman ya yi k'asa da kansa yana fad'in "Ka yi hakuri Baba dan Allah". Junior ya yi tsuru tsuru. Abida ta yafito shi tare da fad'in "come to Dady junior". Ba kuzari ya isa kusa da ita ya tsaya a dalilin ya ga kan Sulaiman a k'asa yana kuka yana goge fuska da hankici. Abida ta zaunar da shi a jinyarta. A ladabce ta ce "Baba ina sake baka hak'uri, sannan Allah shine shaidar na yafewa Dr yaya Sule tafiya da ya yi ya rataye ni. Don haka ka daure ka yafe mana ka saka mana albarka komai ya wuce. Kawai ya d'auke mu yi tafiyarmu". Kansa na k'asa ya ce "Baba ka fad'a mata ba da ita kake magana ba, ta daina saka baki idan kana mini fad'a ". Momi ta ce "ina zata yi shiru kuwa". Abida ta yi maza ta kame bakinta. Baba ya ce "Kada ki sake bude baki ki yi magana, tashi ki shiga ciki ma". *DINGISHIN KWADO 4* PAGE 15 *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* Ta tashi a sanyaye. Baba ya kalli Sulaiman ya ce "Kana sane ai ban huce da kai ba, amma tunda mukaa sauka kake ta bata mini rai. Ga ka, ga yayanku ka kasa bude baki ka yi masa magana? Wanne irin al'amarine haka Sulaiman? Kullum addu'ata Allah ya bayyana mini kai, ta dalilinka zumunci zai daidaita sai kuma ka dawo da dabi'un jahilai?" "Ka yi hakuri Baba". Sulaiman ya fad'a a hankali. Baban ya nisa ya ce "Ya kamata kasan ka girma kuma dole ka yi hak'uri da sha'anin rayuwar nan mussaman a al'amarin zumunta. Yanzu ka kalli yaro an haifa maka har ya girma baka san shi ba, bai sanka ba, wanne irin Bakar Ta'ada haka ka yi?" Ya kasa magana wato cikin Abida bai zube ba kenan?" Baba ya zarce da fad'in zan "hak'ura na huce ne idan ka je ka tattaro mini y'anuwanka ka kawo mini su gabana don tunda ka tafi idan ka d'auke Bilkisu. Ansari da Saddiqa kad'ai na sanya a idanuwana suma zan iya lissafa maka.". Murya ba amo Sulaiman ya ce "Da ikon Allah zan kawo su Baba amma ka dubi Allah duk uzziri da alfarmar da zamu nema ka yi mana". Baba ya ce "Zan muku Sulaiman indai kun yarda ni din ubanku ne to menene ba zan yi muku ba?" Sai kuma kuka ya k'wace masa. Sosai hankalin Sulaiman ya yi tashin gauron zabi. Ya dinga bawa Baba hak'uri cikin rauni. Yanzu ka je d'aki ka yi wanka, Idan muka yi sallah sai mu dan kwnaata kafin laasar mu dan huta." Kafin Sulaiman ya yi magana Abida ta fito daga dakin mami hannunta d'auke da mukullin guest room, da confidence ta zo ta d'auki jakar Sulaiman ta rataya, ta ja trolley yayin da junior yake rik'e da tsintsiya da parker da detergents. Sulaiman ya ce "Ajiye mini ina da hannu". Abida ta d'auki salati mai tsananin gaske ta ce "Yaya Sule yanzu duk nasiha da Baba ya yi maka baka risina ba, ina jiye maka ya sake tunzura to ni dai kam darajar Baba na yafe komai. ba kuma zan sake yarda da fishinsa mai yawa ba a kaina ba." Ta kalli Baba ta ce "ka shaida na huce na yafe masa, ina kuma neman shiri saboda na riga na gaji da wannan danbarwar". Sulaiman ya yi shiru a ransa kuma mamakinta yake ba zata taɓa canjawa gabad'aya ba. Wato ta nan zata bullo masa? Kwatsam ya ji Baba yana saka mata albarka har da fadin tabbatuwar aurensu na cikin abubuwan da suke da muhimmanci a zuciyarsa, dan haka ta cigaba da juriya in sha Allah zata yi albarka, don yiwa miji biyayya da hak'uri da shi, alamun mace na kan turba madaidaiciyane. Gabad'aya Sulaiman ya ji duk wani azancinsa ya k'wace Abida ta binne shi da ransa. Baba kuma ya tula masa k'asa cikin girma. Yana ga ni ta fice da jakunkunansa wanda ya yi amannar sai ta bude masa kafin ya je d'akin tunda haka dabiarta take. Ya bi yaron da bai bar komai na halittarsa ba da ido da ya bita a baya da kaya a hannunsa yana ja. Cikin lokaci k'alilan ta karkade Dakin da kanta ta share, ta shi ga bandakin ta wanke toilet din da k'ura ce kawai a cikinsa. Sannan ta koma ta dauko bedsheet dinta wankakke goggage da blanket ta hado kuma ruwan moping. Baba yana ganin yadda take ta safa da marwa cikin rawar jiki da falli. A ransa dariya ne fal akan lamarin Abida sai dai ba ya so ya yi a gaban Sulaiman don ya lura gabad'aya Sulaiman din ya zama wani iri ya kasa katabus. Baba fad'i yake yi a ransa ja'irar yarinya ta ji jiki iya jiki, ta yi laushi tub'us ya kuma gane sulhu take so ko na dolen doliya ne. Mintina biyar suka ga ta shigo da sauri sosai ta yi d'akinta. Zuciyar Sulaiman ta harba ya ce "Baba k'irata na tabbatar ta ɗauko mini wani abu" . Baba ya ce "Haba Sulaiman ai yanzu ta yi hankali ba zata dauki wani abunka dan ta boye ba. " Sulaiman ya yi shiru ba don ya gamsu ba, sai dan ba zai yiwa Baba gardama ba. Amma tabbas ta d'auke masa wani abu. Ta fito fuska ba walwala hannunta d'auke da burner da kwalbar turaren wuta mai kyau. Ta wuce tana fad'in to na gama gyara maka da kaina Dr yaya Sule ". Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:04] *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Sanyi flusher kuwa best seller ne* . Bai amsa ba bare ya motsa. Ganin haka ya sanya Baba mikewa da ƙyar. Sulaiman ya yi maza ya mike ya rik'e shi har zuwa bak'in k'ofar d'akinsa. Sannan ya bar shi Abida ta yi maza ta fice kan dole ya bi bayanta. A harabar hate don ya hango junior na buga ball. Ba dan sadda ya bar k'asar Farukun Bilki ya fi shi shekaru Banda ya ce shine don tsananin kamarsu. Ba tantama dansa ne don ga shi nan sak shi tamkar kakinsa ya yi. Ba ya inkarin jininsa ne amma sai ya yamutsa Abida. Kuma tunda Baba ya yi masa fahimtar tafi ne don bai d'auke shi ubansa ba, to kuwa sai sun gurfana shi da ita a gaban Baba an baje komai a faifai da ya huce duk da dabararta kuwa. Sai tula masa k'asa take cikin dabara. Momi kad'ai ba Baba ba, kunyarta yake ji akan Abida. Dole ya hak'ura amma sai sun sake yinta da wajewa. Ba zai sake d'aukar wulakanci irin wadda ta yi masa ba. Don haka ba zai bata fuska da wuri ba. Suna shiga ta wuce bayi, tuni ta kai masa brush da makilin d'insa da ta ga ni cikin jakarsa Hadi da soso da sabulu. Sai da ta had'a ruwan wanka ta fito tare da fad'in "Dr , Yayana, mijin Abida, kuma Baban junior with dew respect nake sanar maka na had'a maka ruwan wanka, mu je na taimaka na dunduma maka kanka na ga gefen can ya dan kunbura kad'an. Gaskiya na tausaya maka Yaya Sulena ka bugu a hannun Baba". Sai hawaye shar shar a idanuwanta. Ya zuba mata ido yana ganin yadda hawaye ke tsere, hannunta rike da tawul dan k'arami da ya gamsu da gaske take yi dundumen zata yi masa. Ya rasa ma ajin da zai ajiye ta. Ya matse bai ce komai ba, jakarsa ya bude ya fito da tawul da jallabiyar sannan ya ce"kauce Malama! Don ya gama gasgata bai gama karantar halayyarta ba . Ta kuwa yi maza ta kauce din sai dai bata yi shiru ba. "Ba damuwa sai na yi maka dundumen da daddare." Yayin da ya wuce yana ayyana ai yasan duk juyin da zai yi ba zata yarda ta yi fishi ba a yanzu. Ya fito daga wanka sanye da jallabiyar. Sai da ya fesa body spray mai dad'in k'amshi sannan ya kwanta. Ta tausasa harsehe tare da fad'in "Yaya Sule na yi maka irin tausarrr nan da ka ke yi mini idan mun dawo daga asibiti?" Ya yi mata shiru. Ta sake maimaitawa Ya kaurara murya ya ce "A a ". "To yaya Sule bari na cire maka dattin kunne ka ga ma cotton buds din na d'auko, nasan zuwa yanzu datti ya cika maka kunne tunda baka iya cirewa da kanka". Kaitsaye ya ce "To idan kuma a can din ina da matar da take cire mini fa?" Zuciyarta ta buga don tasan wataƙila hakan zai iya kasancewa. Amma ta aro jarumta ta cije ta ce "Tunda yanzu ni ce tare da kai, ka bari na cire maka mana. " "To ba zan bari ba". Ya fad'a a takaice. Ta cuna baki tana kunkuni. Shi kuma ya yi kamar bai ji ba. Can ta nisa ta ce Yaya Sule na yi kewar chest dinka, na zo na kwanta zaka yi hugging ɗina da tausayawa?" Ya kasa ce mata komai don ya ga so take ta shashantar da shi ta rubta shi ya fad'a tarkonta. Daidai lokacin junior ya turo k'ofa ya shigo. Abida ta yi maza ta ce "koma ka yi sallama, ka jira a amsa maka". Ya koma din. Ya dinga knocking tare da fad'in assalamu alaikum cikin muryar yara. Ta amsa masa da fad'in walaika salam shigo Habibina". Sulaiman ya zuba mata ido shi gabad'aya mamakinta yake yi. Jiniyo yhigo ya isa kusa da ita. Ya ce "Ammi dadin nawa bai yi mini irin yadda Dady oga yake yiini ba". Ta murmusa ta ce "Ba shi da lafiya ne. Idan ya warke fiye da Dady zai dinga yi maka." Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:05] Sulaiman daga kwancen ya mik'a masa hannu ya ce "zo mu gaisa." Junior ya isa gare shi ya hau Gadon ya zauna Yana kallonsa. Yayin da Abida take mamakin tsananin kamar da suke yi da juna. Farha da junior da kuma Farukun Bilki ba inda suka bar Bilki da Sulaiman kwabo da kwabo kuwa. A hankali Sulaiman ya ce "ya sunanka?" Da hanzari junior ya ce "Sulaiman Sulaiman. Junior ake ce mini". Ina ne school dinku?" Ya ce "Ba'a sa ni ba, amma ammi ta ce mini zaka saka ni a makarantarsu Yaya Noor da Yaya Farha ". Zuciyarsa ta harba a dalilin suanar Farha da ya ji. Idan kuma har ba mancewa ya yi ba to Noor itace last born din oga Asad. Yasan Bilki na Abuja tunda an fad'a masa ta bar Katsina. Don haka idan makantarsu Noor aka saka Farha ba zai yi mamaki ba. Ya ce "Amminka ce zata saka ka ka ji". Junior ya ce "Amma fa Yaya Noor ta fad'a mini kowa dadynsa ne yake saka shi a school ". Ya nisa ya ce "Hakane ". "To ka ta shi mu je ka saka ni a makarantarsu pls". Sulaiman ya ce "Zamu je amma ba yau ba". Junior ya yi shiru ba dan ya ji dad'i ba. Ya sauka daga gadon ya nufi Abida fuska a kwakkwabe yana son yin kuka. Ta yi maza ta ja shi jikinta ta ce "Shhhh shima baya son kuka irin Baba. Zai saka ka fa, amma kana bude bakinka ka yi kuka to ba zai saka ba." Nan da nan kuwa ya had'iye kukan. Sulaiman ya bisu da ido yana mamakin yadda Abida ta k'ware a tarairayar yaron har cikin idonta yake ganin soyayyar yaron. Ya tuna yadda ta bar shi da rainon Farha. Matuƙar yana gida to fa shine mai raino duk juyin da zai yi kuwa. Tsakaninta da yarinyar ta bata nono amma canja diaper ma sai ta so matuk'ar ta k'yalla ido ta ga yana gida. Abida ta yi sharafinta iya sharafi don tana rayuwa ne akan uwa da uba duka sun yi tarayya akan raino da tarbiya ba wai uwace kawia mai lura da wannan b'angaren ba. Ga mamakinsa sai ya ji tausayin yadda ta yi fama da goyon ciki da haihuwa hadi da rainon yaron da babu wata kamarta da ya d'auka ko kad'an. Take kuma ya fahimci ita da yaron a takure suke rayuwa don tana cewa baya son kuka irin Baba nan da nan yaron ya kama bakinsa da hannuwansa. Wani sashe na zuciyarsa ya kore tausayin da ya taso masa tare da hujjar ita ta so hakan ta faru da ita. Tunda idan ya zo da bukatarsu bata yi masa k'wange ko raki. Haka nan idan suka fita asibiti har su dawo girmamawa mai yawa take yi masa a idon jama'a. Amma suna dawowa gida zata nade a gado da sunan ta gaji sai ya yi mata tausa. Kafin a samo Mata yar aiki raba musu aiki take yi shi da ita. Ba k'aramin jarumta ya gwada ba kafin ta daina cewa idan ta yi wanke wanke yau, gobe shi zai yi. Sai da ya yi da gaske ya yi rantsuwar ba zai yi wanke wanke ba sannan ta hak'ura akan dole take yi kullum. Amma sauran ayyuka tare suke yi. Rainon Farha kuwa ba k'aramin wahala ya sha ba, don idan ranar dutinsa ce komin kukan yarinyar ba zata karbe ta ba. Matuk'ar ta bata nono to fa sai sai dai ya yi ta fama da ita. Ganin ta bar masa kaso mai yawa na hidimar yarinya sanya ya tubure akana a raba. Don haka rana rana suke yi wato kowa da ranar da zai kula da yarinyar a tsakaninsu. Bai samu kansa ba sai da aka kaiwa Bilkisu ita wanda sau uku suna saka ranar da zasu kaita suna d'agawa don tsananin alhini. Abidar ce ta fishi jarumta a ranar da suka yi shahadar kaita don ita ce ta kafe a ranar kuwa zata tafi, alk'awarin da ta d'auka na bawa Bilki ita sai ta cika don ko mutuwa ta yi sai an bawa Bilki ita. Ga shi dai sadda ta yi alak'awarin bawa Bilkisu d'iyarta shi baya k'asar bai kuma k'ulla soyayya da ita ba. Amma q hakan da ta yiwa Bilki ya k'ara masa sonta tare da kaita matsayin a zuciyarsa. Duk da shi din ba k'aramin takura ya yi da rasnin Farha ba a lokacin .Ya Dade yana kokawa da zuciyarsa kafin ya hak'ura. Da kansa ya yi amannar kaf duniya Bilki zai iya yiwa hakan. A yanzu kuma ya rage Jim zafin da ta ce don ta bawa Bilki Farha ya sanya ya aure shi, don Idan ba shine uban Farha ba ai kyautar zai zama ba irin yadda take a yanzu ba. Don uban yarinyar da danginsa ma sun dinga yin abin da kowa zai gane ba ita ta haife ta ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:07] Ya kuma gasgata dukkan zuciyarta take son Bilki tamkar yadda yake sonta. Don ya dan rage jin zafinta kad'an ne a lokacin da Usman ya ce Wai ko zata tafi da d'iyarta? Wannan kalmar tana yawan fad'ar masa da gaba. Wai Usman nasa da suka taso tare ne ya yi masa irin haka akan laifin da ba shi ya yi ba? Bai taimake shi akan ya daidaita aurensa da kanwarsa ba.Sai ma yake bata kariya akan izgilin da take yi na na zata zauna da shi ba, tare da son ya nukurkusa Bilki da bak'incikin rabata da d'iyar da ta k'wallafa rai a kanta. Duk sadda Sulaiman ya tuna wannan batun yana yawan tambayar kansa ko dai Usman ya manta shine uban Farha ba wani ba? Shi kuwa a duniya ba zai taba yiwa Bilki gayya da abin da ya haifa ko ya mallaka ba. Wallahi ya so a ce Abida ta ce zata karbi y'arta da kuwa ya nuna musu lallai MAMI ce ta haife shi kuma nononta da ya sha bai furzar ba, yana kuma alfaharin kasancewarta uwarsa. Don sai ya yi wulakancin da zai sake girgiza gidan gabad'aya. Sai kawai suka yi sa'a daga ita har Usman din ta ce 'wai munafuki ne yake magana biyu.' Hakan da ta fad'a sai jikinsa ya mutu fishinsa ya sauka, sannan bak'inta ya ragu da kad'an a zuciyarsa. A fili ya furta "Dole sai an zauna". Abida ta ce "Me ka ce ?" Ya yi shiru tare da rufe idonsa alamun barci zai yi. Kan dole ta sunkuci junior da yake ta gyangyadi a jikinta. Ya bi bayanta da ido har ta bude k'ofar ta fita. Kukan Baba ya karya masa lagonsa kwarai da gaske har yake jin Idan ya ce ya saki Abida Baba zai tabbatar lallai baya ganin mutuncinsa ne. Amma ya ya zai yi da bak'incikin maganganun da ta yi akan uwarsa. Ko lokacin da ta yi eannan BAK'AR TA'ADA din ta zube jini ya tsinke mata ne. Ya kaita asibita da zummar jdan ta warke ta dawo sai ya yanke Ma3ta hukunci. Sai kuma bata dawo ba ta tafi. Ana cikin haka mamin ta rasu amma zuciyarta bata risina ba a cikin gayya ta yi masa gaisuwar, ta sake saka k'afafuwanta ta bi iyayenta duk kuma ana kallonta alhalin sun sa ni ba sakinta ya yi ba. Hawaye ya k'wace masa yana jin lallai ya hak'ura da ita shine ya zama d'an kirki, nakudar da mami ta yi kafin ya iso duniya bata yi a banza ba. To amma ya zai yi ne da Baba? Lallai tsugunne bata k'are musu ba. Don kuwa la shakka duk matsanancin son da yake yiwa Abida. Ya fi son MAMI. Sannan mami tana da alfarmomin da duk wanda yake k'arkashinsa sai ya girmamasu bare kuma ace wai matarsa ce zata keta mata alfarma cikin isgili a gabansa to ba yi wannan lalacewar ba kuwa. Mami ba zata yi wannan arahar ba ila yaumil qiyama ko me ta yi na kuskure kuwa. *Duk girman rikicin da zai gitta da mijinki kada ki yi gangancin zagin iyayensa matuk'ar ba shi da dabi'ar zagin iyayenki, basa manta zagin da macen da aurensu ta yi musu cikin sauk'i*. *Shawara ce kyauta*. * A zaune ta tarar da Baba bai shiga ciki ba. Ta isa kusa da shi ta kwantar da junior. Ta koma gefe tana dan haki. Ya kalle ta ya ce "Ina fatan baki fesa masa Bilkisu na tare da yayanku ba?" Murya a sanyaye ta ce "Tun a Saudi da ka ce kada na fad'a ban fada din ba Baba." "Madallah! Baba ya furta hakan a takaice. Ya ce "To anjima zaki kai Shi ya gaida yayanku daga nan sai ya ga twins kalarsu Baban Munira". Abida ta murmusa. Ta ce "Zai yarda na kai shi ne?" Ya ce "umarni zan ba shi ai, ke dai ki shirya kawai " Dad'i ya kamata. Da walwala ta ce "To Baba ". Daga haka Baba Babba ya mike ya nufi d'akinsa. Abida ta ciccibi yaron zuwa nata d'akin. * Bilki na zaune a d'akinta. K'ofar d'akin a bude kuka take yi k'asa k'asa yayin da Alti take fad'in "Abin da na yi ta guje miki kika ji. To wai menene ba za ki bude baki ki fad'a masa ba kya son hotunan ba?" Cikin kukan ta ce "Bai ba ni dama ba Alti. Tunda na zo gidan nan fa bai taɓa ba ni damar da zamu tattauna ba. Komai za'a yi mini kalmar d'aya ce 'ki yi hak'uri yara ne." Daidai lokacin oga Asad ya sauko basunji Shi ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:09] Kunnensa ya jiyo Bilki na fad'in "An zage ni, an zagi uwata ya ga ni bai ce komai ba illah k'uruciya da ya jingina musu. Amma ni da na zagi maimurabus da uwarta ai laifi na yi, laifin da ya zama sanadin da ya yi mini hukuncin da sai da na shafe sattitika a gadon asibiti. Duk ana ga ni an kasa tsawatar masa. Ke ma yanzu da nake ganinki ina jin dad'i ya k'wace mini ke kin koma bin bayansa to Allah dai yasa ni ce ta ki, ba shi ba. Yanzu ban da ya riga ya kud'iri aniyar sai ya kunsa mini bak'inciki ace Yaya Sulaiman din da ake nema ruwa a jallo ya dawo ace an shata mini layi da zuwa wajensa?" Kuka mai cin rai ya k'wace mata. Alti hankalinta ya tashi ta ce "To ki ba shi hakuri mana. Indai kina son zuwa ki gyara barakar da ke tsakaninku. Yanzu ki saka direba ya kai ni, na gaishe shi a madadakinki. Anjima ki je masa kwana ki ba shi hak'uri ku shirya gari na wayewa da kansa zai kai wajensa". Bilki bata ce komai ba. Illah gunjin kuka. Yayin da Oga Asad ya dinga istigifari tare da wanke Alti daga zargin da yake yi mata na bata faɗawa Bilki gaskiya. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:04] PAGE 16 Haka ya wuce su zuwa masallacin don yin sallar laasar. Kukan Bilki ya taba shi sosai. Amma shi so yake yasan me ya yi mata ne a yanzu? Me yasa zata kafe ba zata je d'akinsa ba? Kansa ya kulle ainun amma ya fi gamsuwa y'anuwanta da suka d'ora masa k'ahon zuk'a ne behind everything. Ko kuma ya ce Hamida kaitsaye. Kuma yanzu ya sake gasgata Sulaiman ma zai d'ora nasa famfon tunda daga dirarsa k'asar ya tabbatar masa shima gabar yake yi da shi. Ban da darajar idon Baba, da ba sai ya wulakanta Sulaiman ba. Idan juninsa zafin kai ne, da ya nuna masa bai iya komai ba, ya saka kafa ya bar mace da aurensa a kanta har da ciki shekaru hud'u ba kad'an. Sannan akan dole ya dawo, sai da aka yi masa tilas kuma duk wannan wulakancin da ya yi musu da ubansu har yana da kuzarin da zai sake yin wani sabon wulakancin da raini daga dirarsa? Ya hurar da iskar b'acin rai. Yana jin Baba babba ne cikas d'insa akan kudirinsa na cin mutuncin Hamida da Sulaiman. Sai dai kuma matuƙar Hamida bata kiyayi shiga tsakaninsa da iyalinsa tare da yi mata famfo a kansa ba, tabbas sai ya wulakanta ta idan ya so su sake shata layi da shi tunda shi kad'ai suka wasa, ko kad'an basu tisa Faruku a gaba da bala'i kamarsa ba. Tun lokacin aurensa da Bilki da ta zugata tare da ankarar da ita bai je gaisuwar mami ba yasan ta washe shi. Yanzu kuma rashin zuwa ta ga twins ya sanya har zuciyarsa ya washe ta don ya tabbatar shine bata so ba Bilki ba. Yana tafe yana sake saken yadda zai bullowa lamarin har ya iso gidan. Ya tarar Alti na falon k'asa. Ta yi masa barka da dawowa ya amsa ya wuce. Ita kuma ta shige d'akinta da a cikin falon yake. Kaitsaye d'akin Bilki ya yi burki. Ya tarar ta idar da sallah. Ya kalle ta zuciyarsa ta tsinke a dalilin yadda ya ga ta rame Ga fuskarta ta yi kuyes idanuwanta sun jan sun fito gwara gwara. Ya ji ba dad'i. Ya had'iye fishinsa ya ce "Me yake damunki. Ta girgiza kai ta ce "Ba komai". Ya ce "To kukan na menene?" Ta suake ajiyar zuciya bata ce uffan ba. Ya jijjiga kai ya isa gadon da yaran suke shimfide. Idonsu biyu dukkansu sai shure shure suke yi tabbacin a kwashe Duke. Sun yi bul bul da su tamkar sun kai watanni hud'u alhali kwanakin baya kad'an suka cika watanni biyu. Ya zauna ya dauki kowanne ya yi masa wasa sannan ya kwantar da su a hankali. Ita mamaki yake bata yadda yake yi musu tamkar k'wai. Idan aka ga yadda yake b'arin jiki a kansu sai a zaci gabad'aya bai samu haihuwar ba ne sai a yanzu da shekaru suka fara tura masa. Wani zubin ita da ta haifesu ganin gazawarta yake yi akan kula da yaran. Komin dare idan ya jiyo kukansu sai ya zo ya tambayi ba'asin kukan ko ya ce a daren zai kaisu asibiti a duba lafiyarsu. Da Alti ta gane shi sai take ce masa ai kukan ne alamun suna lafiya, sannan alamun zasu yi kwakwalwa ne. Tunda ya ji hakan kuma sai ya koma tambayar yau kuwa sun yi kuka da ba nan? Alti yau basu yi kukan dare ba fa? Ko dai basu da lafiya ne?" Aysha da kullum ita take gida tana kallon ikon Allah. Tasan dadynsu na sonsu k'warai da gaske. Amma da wayonta da hankalinta aka yi goyon Amal da Noor tabbas bai yi irin haka ba. Sannan ba ya taya Momi rainon yara, abin da ta san baya damuwa akan abinci ne, ta bude ido ta ga da daddare idan ya dawo zai bada order chep ta yi masa abin da yake so. Amma tun zuwan anti Maigado ta ga ya canja, matuƙar ta ajiye masa abinci sai ya ci. A yanzu baya iya saka chep ta yi masa sai ya dinga raragefe kafin ya sanya a yi masa abin da yake so. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:07] Duk abin da ta girka haka yake ci, babu musu wanda lokacin mominsu shine yake da lasisin zabar abin da zai ci bayan ya dawo har da tsirfar baya cin abincin da ya shiga warmers. Gara ma a kwanakin nan ta ga chep angela ke yi masa. Takaici ke cinta me yasa yake rianon wadannan, ko ita kanta jele take yi tsakanin samansu da saman anti Maigado da Kuma saman Dady ba don komai ba sai don ta kaisa masa yaran, ko ya ce ta je ta karbosu a wajensa suna jin yunwa. Kuma yaran da zata iya hadesu ta d'auke su sai ya ce da d'aid'ai zata kai su ko ta sauko da su. Idan kuwa ta d'auke guda a cikinsu ya dinga fad'in "Aysha handle them with care. Ki sauka a hankali ban da garaje! Me yasa yake wannan barin jikin akanasu, shin dan sun kasance maza ne ko kuwa don sun kasance y'ay'an Maigadon da yake so kuma Abida da mominsa suke sonta? Kullum sai ta yi kuka a d'akinta wanda na kishin yadda yake son wata macen alhalin uwarsu na kushewa. Gata da riritawa ba wanda ba ya yi musu amma gabad'aya zaman gidan ya yi mata tsauri so take ta barwa Maigado da Abida guri su cinye gidan ma gabad'aya. Tunda ta gama gamsuwa ya fi son Maigado akan mominsu. Ya dinga ganawa momi azaba da fishinsa akan ya'yan da ta haifa. Amma wata katuwa ta zo ta zanesu ya yi muk'us bai yi mata azababben fishinsa da yake sanya mominsu yini tana goge k'wallar bak'inciki. Amma wannan ko kwakkwaran motsi kasawa ya yi sai ma kwasarta shopping da ya yi suka raba dare a waje. Idan ta ga hips din Maigado har kan harshenta take jin ciwo tunda a dalilin momi na son ta zama irin yadda yake so ta salwantar da rayuwarta. Ga shi ya samo wacce take da su natural ba artificial ba yana sharafinsa yadda yake so. Sune kad'ai suka yi asarar rashinta sai ko danginta. Wadannan dalilan ya sanya Aysha ta kasa sakewa da Maigado amma kuma ko kallon banza ba ta yi mata. Ya mike ya fice ba tare da ya ce mata kanzil ba. Yayin da ita kuma kuttunsa ya zo mata har wuya. Idan har yana da imani ya tambayi ba'asin kukanta? Ya kumshe a gida yana faman Hana Mata azaba. Ace Sulaiman Yana Abuja a hana ta zuwa wajensa? Da ace maimurabus ce yama isa ya fara yi irin wnanan kama karyar? Oh namiji dai baya fita a wajen mace, baya gwaninta ko wacce ga ni take yi yafi son wata a kanta. Yan shiga d'akinsa wayarsa da layin da iya family ne suke da Shi ya hau kara. Ya duba ganin Baba ne ya sanya ya zauna sannan ya amsa cikin girmamawa. "Baba dafatan ka kwanta ka yi barcin gajiya?" Baba ya amsa da fad'in "Na dan yi. Sai dai ban wani jima ba a dalilin zuciyar babu dad'i". Ran oga Asad ya baci a ransa ya ce "Ina zuciyarka zata yi dad'i ka k'wallafa waɗanccan ja'iran a ranka." A fili kuma ya ce "Ayyah sannu Baba ka Ƙara hak'uri ka kuma dinga yawan istigifari.". "Ina yi, amma zan dage da yi. Ina son ka bude kunnuwanka da zuciyarka ka saurare ni da kyau". Zuciyarsa ta buga don kuwa la shakka al'amarin da za'a bijiro masa mai nauyi ne! "Asad Asad Asad! Baba ya k'ira shi har sau uku cikin dakakkiyar murya. A sanyaye ya ce " Na'am Baba". Anjima ka shirya tarbar Sulaiman a gidanka. Zai zo ya gaisheka daga nan ya gaisa da Maigado ". Tamkar an kwada masa guduma haka ya ji wannan batun na Baba Babba. Murya ba amo ya ce "Wallahi k'arya yake yi ba dan ni zai zo ba Baba wajen kanwarsa zai zo". "Wallahi bai san Maigado iyalinka ba ce bai san komai ba". Nan da nan Asad ya gamsu don kuwa baba ba ya rantsuwa.sai ta k'ure. Ya numfasa ya ce "To Baba ko direba ya kawo Maigadon kawai Su gaisa don yanzu fita da Zan yi". Baba ya ce "Sulaiman zai zo gidanka ya gaishe ka daga nan ya ga tagwaye duk da bai sna wacece ta haifa maka su ba". "Amma baba.. Baba ya yi maza ya katse shi da fad'in "Shi da yake na isa da shi, ina yi masa fadan bai gaishe ka ba, ya ba ni hak'uri, a take na zartar masa da hukuncin ya biyo ka har gida ya gaishe ka, to kawai ya ce mini saboda giyar kud'i da mulki basu fara bude masa idanuwansa ba". Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:09] Hankalin oga Asad ya tashi ainun ya shiga ba shi hak'uri tare da fad'in "Ka yi hak'uri Baba zan zauna na jira shi. Ina maraba da mijin Abida". Nan da nan dad'i ya kama Baban ya yi murmushi da ya isa har kunnen Asad din. Ya ce "Yauwa oga Asad Allah ya tsare ka da tsarewarsa." "A sanyaye ya ce "Ameen Baba". Don tausayi ya ba shi na yadda ya shiga tsakaninsa da Sulaiman da son ya yi musu sulhu. A fili ya ce "Allah ka karbi kyakkwar niyyar Baba akan zumunci. Allah ka shirya tsakaninmu gabad'aya." Baban ne ya katse wayarsa yana jin tunda ya danne Asad to ya samu sauk'in matsalar. Don ba k'aramin aikinsa ba ne idan Sulaiman ya je gidansa ya saka a hana shi shiga duk da Bilki na cikin gidan kuwa. Da kansa Baba mamaki yake yi yadda y'ay'ansa uku halayyar kaninsa suka kwashe tsaf ta kar ta san kar. Asad Usman da Abida wadannan ukun idan aka taɓa su basu da d'adi ko kad'an. Yayin da Faruku, Salaha da Munira idan ta sune kiyama ba zata tsyaa ba. Haka nan yana mamakin yadda Bilki ta kwashe kammaninsu da halayyarsa, haka Sulaiman shi dazu da ya rike shi yana dukansa sai ya ga ma duk yafi su Faruku kama da shi sak sai dai halayyarsu tazarace mai yawa don kuwa yana rukunin su Asad da suka samo halin Baba K'arami. Baba k'arami kuma ance halin mahaifinsu ya yi har kama, yayin da shi Baba Babba ya yi kamar gyatumarsu shiyasa ba wani kama suke yi da baba K'arami ba. Amma ya'yansu an garwaya musu saboda tsananin tasirin jini. Shi ya haifi masu kama da Kaninsa, haka shima baba Karami ya haifi masu kama da shi. Tunda suka dawo daga sallar laasar ya ce wa "Sulaiman zai aike su tare da Abida ya shirya zo. Ya ajiye wayar ba jimawa Sulaiman din ya shigo cikin tsadaddiyar Farar jallabiya. K'amshin ya cika falon. Sosai ya yi kyau ya Dora farar hula irin Dai yadda suka.ga Baba Babba Yana sanya Farin tufafi. Da walwala Baba ya ce "Sulaiman ka ga yadda ka juye ka koma tamkar sadda nake cikin shekarun k'arfi irin naka?" Sulaiman ya durkusa akan kafet din ya ce "Ai tunda na yi sa'a na yi kama da kai komai koyi nake yi da kai Baba ". Farincikin Baba ya dada fad'ada ya ce "Amma fa ni bana gaba, da kullaci sosia kuka nake son zumunta da dabbaka shi ". Zuciyar Sulaiman d'aya ya ce "Baba kullum Ina addu'ar na Zama irin Hakan, ina ji a jikina Kuma addu'ar ta karɓu jira nake yi Kawai na ji na gama sauyawa gabad'aya. Dariya Baba ya yi ya ce "To bari mu ga ko kai a karan kanka kana son ka canja din. So nake.ka me gidan yayanku ka gaishe shi sannan ka yi masa murnar haihuwar tagwaye da aka yi.a gidansa kuma karon farko da aka haifa masa yara maza." Zuciya Sulaiman ta harba baki mai yanka wuya. Zuwa gidan Yaya Asad ba k'aramin takura ba ne. Ya yi shiru. Nan da nan Baba ya gane baya son zuwa. Ya numfasa ya ce "Ka ga shi da yake na isa da shi, ina fad'a masa zaka je gidansa da murnarsa ya ce da fita zai yi amma ya fasa fitar zai zauna ya yi dakon ka". Kan dole Sulaiman ya ce "Ni ma ka isa da ni mana Baba. Zan je din" "To Allah ya yi maka albarka sai ku tafi tare da iyalinka ta raka ka." A kan tilas ya ce "To" Don kada Baba ya ji da ya'yan cikinsa kad'ai ya isa ba dan haka ba, ba abin da zai saka ya fita unguwa tare da Abida a yanzu. Daidai lokacin Abida ta fito cikin kwalliya ta burgewa. Ta tsugunna a kusa da Baba. Ta tausasa harshe ta ce "Baba ba Zan Ga ji da fad'a maka na yi kuskuren kin ji Umarnin da ka ba ni a baya ba. Ka ce na Koma dakin mijina na bijire, Sai Dai bijire maka da na yi ka zuba mini ido ka mayar da ni y'ancin yin Duk da abin da na so daidai ko ba daidai ba na matuƙar saka Ni tashin hankali. Ka yi hak'uri Baba nima ka dinga bani Umarni kan Duk abin da ya dace Konda ba na so dan Allah Baba ". Idonta ya ciko da hawaye. Tausayinta ya kama baba, sannan yadda take wanke shina idon Sulaiman da iyakacin gaskiyarta ya sanya kin ya huce da ita. Ya tausasa harshe ya ce "Zan fara yi miki hakan idan Allah ya sake ara mini na ga kin koma dakinki kin nutsu kina zaune lafiya da mijinki ". Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:13] Sulaiman ya ji wani iri Baba Sai tula masa k'asa take yi cikin hikima. Yayin da salama ta shigi Abida don har cikin zuciyarta take jin matsananciuar damuwa idan ta ga Baba na yin iko da y'an gidansu kaf dinsu amma ban da ita. Tun sadda ya yiwa Bilki kacakaca ya ce ta koma gidan mijinta ta gano tana cikin had'arin rayuwa don kuwa duk abin da zata yi a rayuwarta ido da to ne tsakaninta da Baba da Momi. Babu Mai ce mata a a , ko meyasa konba yanzu ba. Ashe ka samu mai saka da mai habaka ma ba k'aramin rahma ba ne? Sannan yadda suke nan nan da ya'yansu Yaya Faruku da na Yaya Asad basa yi da junior. Farha kad'ai suke nunawa soyayya mai yawa ita kuwa tasan don tana hannun Bilki ne. Junior kam saffa saffa. Idan bata nan suna kula mata da shi amma akan idonta kam basa wani jansa a jiki illah kyara akan yana da fitina tare da fad'a mata ta samgarta shi. Wanda hakan na cikin dalilan da ya sanya kullum sai ta yi kuka, sannan zaman gidan ya yi matuƙar gundurarta. Shiyasa Idan ta yi sadaka sai ta ce a yi mata addu'a Allah ya bayyana mijinta. Baba ya ce "Ku je ki raka shi gidan yayanku." Da azama ta ce "To Baba bari je yamma na yi." Ta mike tana fad'in "sai mun dawo tunda sai da ta shiga ta yiwa Momi sallama kafin ta fito falon. Haka Sulaiman din ya mik'e tare da fad'in "mun tafi". "A dawo lafiya ka gaida mini takwarorinmu". "To". Sulaiman ya amsa a nutse. Daga haka ya fita don tuni Abida ta fice. Abida ta kalle shi ta ce "Za ka jamu ne?" "Ba walwala ya ce "Nasan gidan ne?". Bata ce komai ba, ta bude mass gaban motar. Ya shiga babu musu a ransa ya dinga tuna da shi yake yi mata irin haka. Ya rufe, sannan ta zagaya ta shiga ta ja motar aka bude musu gate ya fice. Suna tafe Sulaiman na kallon yadda Abuja ta sake cigaba. Cikin wata irin murya ta ce "Yaya Sule wai baka kewata ne?" Cikin gatse ya ce "Ina yi mana dumudumu". Ta murmusa Yaya Sule gatse ko wasa?" Ya yi mata shiru. Ta nisa ta ce "Ba Zan iya zuwa guest room na kwana maka ba alhalin momi.da baba na nan, yanzu ya za'a yii taimaki kanmu". Ya yi shiru tare da mamakinta. Bata da kumbiya kumbiya ko kad'an. "Still cikin gatse ya ce "Ki kawo mana solution ". Kaitsaye ta ce "To idan mun dawo daga gidan Dady kawai.mu samu lodge." Ya ce "Mu kwana kenan?" Ta ce "a a, zuwa magharib idan muka gama da gidan Yaya Asad. Ko 10 muka koma gida ya yi ai". Ya ce bai yi ba. Idan zamu kwana na yarda mu je ki mana lodge Haj Abida. Idan kuwa Yan awowine to a bari kawai". "Ya Sule akwai batun da nake so mu tattauna tsakanina da Allah! Haka kawai ya ji ya ba shi tausayi don bata maganarsa zummar wake. Amma ya cije ya ce "Zamu tattauna ai gaggawr me kike yi?". Nan da nan ta ce "To gaskiya Yaya Sule zaka biya ni kudin kunyatar da na yi. Ta ya ya zan cire kunya na yi inviting ɗinka amma ka yi rejecting. Don haka Wallahi sai ka biya diyya". Da mamaki ya juya yana kallonta, gabad'aya ta yi kicinkicin da fuskarta. Ya kaurara murya ya ce "You are trying me ko Abida?" Ta tura baki ta ce "Gaskiya ne fa, don haka zan saka shi cikin lissafin basukan da nake bin ka". Da mamaki ya ce "Ni kike bi basuka ba ma bashi ba?" Kaitsaye ta ce "Kai kuwa". Ya yi shiru yana ayyana wai yaushe zata daina son kud'i ne" Kaf y'ay'an gidansu mata babu mai kudin Abida. Amma kudinta nata ne ita kad'ai. Bata yarda ko bashi ya had'asu, amma yanzu ta kaikaice tana fad'a masa basuka take binsa. A yadda kuma ya ga yanayinta da gaske take yi, kuma duk yadda yake jin zafinta idan har ya mayar da ita d'akinta sai ya biya basukan nan. Ya rasa me zata yi da kudade haka. Kud'insa nasu ne tare amma nata kam nata ne ita kad'ai. Basu sake magana ba har suka isa inda suka nufa. Oga Asad da kansa ya tarbe su a katafaren falon da yake ganawa da manyan mutane. Gabansa ya fadi da ya ga Sulaiman da shigar da ya yi. Take ya tuno Baba Babba a shekarun baya da ya ke kai su makaranta shi da Faruku mussaman sadda suke sakandire a Rumfa college Kano. Sak haka yake tamkar Sulaiman a yanzu. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:16] Bai san sadda ya daidaita ya yi saluting din Sulaiman tamkar yana saluting ogansu na koli I.G. Dad'i ya kashe Abida don a tsorace take tundaa ta gane Dady yana jin haushin Sulaiman na jingine musu ita da ya yi. Haka a dazu ta fahimci shima Sulaiman din haushinsa yake ji da gasken gaske. Don haka ta shiga rud'anin zuciya tamkar yadda baba ya shiga idan basu jitu ba, tana cikin tashin hankali don kuwa Baba da Momi ne kad'ai suka zartasu a zuciyarta. PAGE 17 Sulaiman ganin irin gaisuwar da Yaya Asad ya yi masa ta k'arshen koli a gidan tsaro sai kawai ya tsugunna a gabansa dan shima ya gaishe shi da k'ololuwar girmamawa. Hakan da ya yi ya burge Abida da take ta faman yi musu hotuna da vedios don tana ganin oga Asad ya k'ame ta fara yiwa Baba recording. Asad ya dago shi ya rungume Shi. Daga haka suka zauna a kujera. Gabad'aya Sulaiman ya ji yayansu ya kashe shi da kunya don baisan sadda ya zube masa tamkar mai neman gafara ba. Yayin da oga Asad kuma har cikin zuciyarsa ya ji tsanar Sulaiman da ta darsu a dazu ta gushe daga zuciyarsa. Cikin mintina k'alilan angela ta kewaye gabansu da cima kala kala. Oga Asad ya ce "Je ki karɓa masa y'ay'ansa ya gansu". Da hanzari Abida ta mik'e har tana tuntube da jakarta da ta ajiye a gefe. Ta hau saman farko. Ta wuce zuwa saman yara sannan ta isa zuwa saman Bilki. Ta tarar da ita a kwance lamo ga Alti na yiwa yara wanka. Da murna Abida ta ce "To ki taso ga shi ya zo". Bilki ta yunk'ura duk fuska ta yi ja. Jikin Abida ya mutu ba zata so Sulaiman ya ganta a haka ba. Ta ce "Akan ya hana ki zuwan ne kika zama haka ko dai wata matsalar ce?" Kuka na sosai ya k'wacewa Bilki. Ta dinga shesshekar ajiyar zuciya. Ta laluba ba hanata zuwa ganin Sulaiman ba ne matsalar kawai. Fishin da ya dauka da ita, ya shigo d'akinta ya duba y'ay'ansa ya fice na tare da ya ce mata uffan ba ne yake nik'arta. Sannan idan ya dawo da daddare ya k'ira Angela ta ba shi abinci na matuƙar nukurkusarta. Ga Alti ta tisa ta a gaba. Gabad'aya gidan ya yi mata tsauri komai zafinsa take ji. Magana sai ta k'ure da ya yi mata komai da y'ay'ansa yake yi ko da ma'aikatan gidan. To ita a me take kenan? Abida ta yi shiru ta ce "Hmm ke kuttunki yawa ne da shi Bilki. Saboda Allah menene matsalarki? Ki bude baki ki yi jawabi Da kuka ta ce "Gaba fa yake yi da ni Abida kuma shi yake cin zalina". Takaici ya mak'ure Abida ta ce "Kidahuma kawai har ki bari tasirin fishin miji ya bayyana miki haka baro baro? Kin ga yadda kika zama tamkar mai fama da ciwon tsi da ha?" Bilki ta kasa magana illah kuka marar sauti. Abida ta numfasa ta ce "To idan ba ki d'auki matakin gyara ba ina miki rantsuwa da Allah kafin nan kafin wata shekarar sai Dady ya nukurkusa ki da bak'inciki kala kala. Ki yarda ko kada ki yarda shi din miji ne mai tsada. Kuma a halittarsa bai son gardama da musu. Na ga alama ke kuma su kike gwada masa su. Haka siddan Dady ba zai hanaki zuwa wajen Yaya Sulaiman ba ko da kuwa baya magana da shi. Baya yiwa wani hukunci da laifin waninsa. Hanaki zuwa da ya yi na gane raini kike yi masa shiyasa ya fara bude miki k'wanjinsa.! Ta nisa ta zarce da fad'in "Anty Rukayya ma bata sha hannunsa ba bare ke." Bilki ta rushe da kuka wiwi. Da kuka ta ce "Saboda ta fini a gunsa kenan ko kuwa me kike mufi?" Bak'inciki ya sanya Abida fad'in "Na rantse da ace nice na baki watannin da kika bani sai na nada miki duka a d'akin nan idan ya so ki yi kukan jini." Alti ta ce "Na gode miki Abidan Baba". Bilki kuwa kuka take yi bilhakki don ita ji take yi tamkar an yi mata daurin huhum goro. Ga dai Sulaiman a cikin gidanta amma ta rasa sukunin zuciyar da zata marabce shi. Yayin da Abida ta had'iye kuttun da Bilki take cusa mata tunda ta shigo d'akin. Ta sanyaya murya ta ce "Ta shi ki shirya ba dadewa zamu yi ba. Yi hak'uri zan dawo mu tattauna kin ji Bilkisu yayar Abida". Bilki aka saki ajiyar zuciya tabbacin ta ji dad'in tausasa harshen Abida. Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:45] Ta mike ta d'auki mayafinta. Abida ta yi maza ta karbe ta ce "Dan Allah wanko fuskarki na gyara miki ita. A hakan kike so ya ganki?" Ba musu ta yi bayi ta wanko fuskarta. Abida ta bata mai ta shafa. Ita kuma ta ɗauko powder ta shiga gyara mata fuskarta. Ta goga mata wet lips sannan ta bude wadrof ta ciro mata dankareren leshin da ya cinye makudan kudi. Ta ce "Saka wannan mana Bilki. Bai san fa ke ce matar Dady ba. Gara ai ya ganki a babbar mace cikin walwala da wadata sai ya tafi da farincikin ganinki a kyakkwan yanayi". Ba musu ta karɓa ta saka. Abida ta daura mata dankali ta fito ta yi fes da ita. Cikin shakiyanci Abida ta ce "Kin yi kyau Maigado. Kada fa Dady ya kasa mallakar kansa a gaban k'annensa." Bilki aka cuna baki aka ce "Da dai yana ta tawa ne". Abida ta ce "Iyawa ne baki yi ba Maigado. Ke gabad'aya kin fi nuna jarumta a inda kike so ba inda ake sonki ba". Ta ji zuciyarta harba don kuwa ta san Abida shagube ta yi mata. Ta kasa cewa komai. Abida ta k'i barin batun ta ce "Tun a Saudi wanccan bawan Allah yake shagulatin bangaro da ni. Amma na cije nake ta bibiyarsa tunda nasan na yi masa ba daidai ba. Ke kanki idan aka ce zan yi wuridin kiranye akan rijalu za ki ce ba dai Abida k'anwar Bilkisu ba. Amma a yanzu da ruwa ya daki babban zakara na gamsu duk gatan mace dakin mijinta shine suturarta. Ni kad'ai nasan kuttun da nake shaka a zaman gidan nan da nake yi." Idanuwanta ya cika da k'walla. Jikin Bilki ya yi sanyi idan Abida da uwa da ubanta basa iya boye soyayyar da suke yi mata take fad'in zaman gida babu dad'i to wacece zata k'i zaman aure babu hujjar ana cutar da ita ta ji dad'in zaman gida? Kai ko tana da hujjar fa yadda take ganin hak'uri take yi a gidan mijinta to ko gidansu ma ta koma hak'urin za ta yi. Don haka idan ba tura ce ta kai bango ba, akwia yiyuwar zaman zai yiwu, to a yi hak'uri kada a fito, sai idan cin mutuncin namiji da keta haddinsa ne ya yi yawa. Bilki ta nisa ta ce "Abida to ya zan yi masa ne? Gaba fa yake yi sosai ya'yansa kawai yake dubawa. Idan zai tambayi lafiyarsu fa ga ni yana kallona sai ya tambayi Alti, haka siddan ya gindaya gaba mai tsananin gaske a tsakaninmu! Abida ta ce "Tunda kika haihu ba ki koma masa ba period". Alti ta ce kanki na ja Abidan Baba". Abida ta ce "Na yi zaman gidansa fa. Bayan haihuwar junior na kusan shekara tare da su a port. Sai da na samu aiki anan na dawo. Yanzu dai zo mu je zan dawo mu tattauna sosai.". Alti da ta kammala shirya yaran ta ce "Bari ki ji babbar matsalarta kishin kushewa ta ɗorawa kanta. Wai ba zata je d'akinsa ba tunda da hotunan marigayiyar matarsa." Abida ta ce "Eh cin fuskarsu ya yi ai gabad'aya. Anti Rukayyan ma ai ba'a yi mata adalci ba. Balle kuma sarauniyar shaiba yayar Abida ". Idon Bilki ya sake cikowa da k'walla. Abida ta ce "Allah ne ya yi mini sakayya. Ban da ba'a son a fad'i aibun matacce da na ce k'arshen mugunta kenan. Sadda ina tare da su a port a dole take karɓar gaisuwata, idan tana falo na zo na zauna, idan ta tashi ta bar mini falon kenan. Idan kuwa ni ce a zaune to ba zata yarda ta zauna ba haka ta yi mini wannan izayar. Ni kuma ina ta kaffa kaffa kada a ce na k'i zaman gidan mijina na dawo gidan yayana zan kashe masa aure. Kai na ga rayuwa Wallahi! Yaya Sule dole ya biya ni diyya kashi kashi." Ta kece da kuka na sosai. Bilki ta yi sororo tana kallon yadda take kukan da ba na iyashege ba ne na tsantsan bak'in ciki ne. Alti ma sai kawia ta fashe da kuka tana fad'in "Dole ki yi kuka Hajiya Abida ai irin wannan zaman kuttunsa yawa gare shi ka rasa inda zaka tsoma ranka." Cikin kuka ta ce "Haka matar nan zan ji tana k'iran Maigado suna hira ita ala dole mun samu sabani bari ta had'a kai da ita ta musguna mini, bata san ko da bama mu'amala, babu tsanarku a zuciyata ba, kanta ya toshe ta kasa gane tasirin jini girma ne da shi. K'ememe ta raba ni da y'ay'an d'anuwana bata bari su zo dakina haka na zama tamkar mujiya a gidan Dady" . Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:49] Ta sake kecewa da kuka tana fad'in "Ba wanda zan yiwa k'orafi akan tozarta ni da take yi cikin ruwan sanyi, tunda k'orafi na yi masa momi bata sakar mini fuska shine ya tafi da ni wajensa a kokarinsa na ganin na samu sauyin muhalli tunda jinina ya k'i sauka. Haka nake zaune ba um ba um y'an aikinta sun fini walwala, kanwarta ta fini sakewa a gidan dan'uwana. Na kasa cin mutuncinta ne kada ya ce laifina ne tunda uwata ma ai ba jin dad'in zama nake yi da ita.". Alti aka face majina da tissue aka ce Dr Abida yanzu kawai ki dawo gobe don wannan hirar ba a kurarren lokaci za ki yi mata bitarta ba, don ita bata fahimci girman k'alubalen da ake hango mata ba idan ta k'i kwantar da hankalinta ". Abida ta goge fuskarta ta ce "Anty Rukayya ta cuce ni bisa hujjar mijinta na sona da yawa. Yana mini hidimar da ta shake mata mak'oshinta alhalin bai yi mata iyaka da kuɗinsa ba. Yanzu ai ga karshen ta nan ta bar wa Maigadon da take nunawa tata ce gida da mijin da take mutuwar so, yayin da Maigado ta washi ko sunanta mijinta ya kama . Allah ne ya saka mini. Kuma Wallahi da ace tana raye ya aure ki, da ta gane tasirin jini. Da na hutar da ita zargin bana sonta don kuwa tabbas zan nuna mata bana ko kaunar ganinta. Ta kitsawa y'ay'anta mugun abu a kaina. Su Aysha a dole suke gaishe ni, ta zo ta same mu lafiya , ta nemi jefa mana gaba. Ya ya dady zai ga farina idan ya ga bana kula y'ay'ansa? Sai da ya gane sune basa zuwa inda nake sannan ya yi mata cin mutuncin ya ce ba ni ba ko Anisa da take karama cikin kannensa idan har y'ay'ansa zasu ganta su d'auke kai, ko a hana su zuwa wajenta to shima su daina gaishe shi, su kuma daina zuwa inda yake kawai. Sannan na samu sukuni fa". Billki ta yi lakwas. Tabbas suna waya da Rukayya. Ganin tana k'iranta don ta gaishe ta, ya sanya itama jifa jifa take k'iranta don ta gaishe ta. Murya ba amo Bilki ta ce "Kafin ki tafi Abida ji fad'a masa ya cire mini waɗanccan hotunan da ya girkesu babu ko sha'awar ga ni". Abida da Alti suka fashe da dariya. Cikin dariya Abida ta ce "Gaskiya Maigado ko hasidim iza hasad yasan hotunan sun yi kyau sun Kuma fita. Wai me yaushe kika yi zurfi a soyayyar Yaya Asad ne irin haka? Ashe har yanzu ba zaki Daina zafaffiyar soyayya irin haka ba? Yanzu ga shi nan tun baku ko ina a zaman ba kin fara kishi mai saka ciwo a kirji da shake kofofin shakar numfashi." Bilki ta yi shiru don kuwa Abida ba karya ta yi ba. Da ace idan ta faɗawa Abida tana jin son Baban Bilkisu ninkin na son da ta yiwa Sahal da ta fad'a mata. Sai dai ba lallai ta gamsu ba don idan akwai abin da Abida ta gasgata take sarhutu a kansa to son da yake yiwa Sahal na kan gaba. Abida ta katse Shirin ta ce "Ba ni da k'warin guiwar da Zan tsaya gaban Dady na ce ya cire hotonsa da na matarsa a gidansa, ban isa ba, ba hurumina ba ne. Ta kama baki alamun al'amarin babba ne. Bilki ta jijjiga kai ta ce "Amma Ina ce kin ce mu hada kaiu yako matsalarmu?" "Saboda Allah Maigado ke ce Zaki fad'a masa. Dady fa cewa yake yi raina shi na yi da nake gaba da matarsa duk da ina gaishe ta. Ya kuma san itace ta washe ni. Amma a gabana nunawa yake yi ba ni da kunya ne isgili nake yi mata alhalin ba sa'a ta ba ce. Yanzu kuma na ce masa ya cire hotunanta me zai ce mini? Ki mini adalci fa Maigado! A zuciyarta kuwa mamakin soyayyar da mata suke yiwa Dady take yi. Haka Rukayya ta so shi tamkar rai. Ga Maigado ma ta fad'a tsumdum. Yaya Sulaiman na cikin gidanta amma batun fishinsa take yi. Ta saki gauron numfashi ba ta furta komai. Don dama tuni tasan Maigado akwai zurfafa soyayya. Daga haka ta d'auki Baba K'arami tana fad'in" Bari na kai masa yaran tunda ba kya farincikin zuwansa." Haka Bilki ta d'auki Baba Babba ta bi bayan Abida zuwa falon oga Asad na k'asa. Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:52] Are11 Abida ta ce a gaba kaitsaye ta shiga da sallama. Yayin da oga Asad ya amsa mata sallama idanuwansa na kan Maigado da take biye da ita babu kuzari. Zuciyarsa ta motsa. Duk kuttun da yarinyar take cusa masa sonta yake yi da dukkan zuciyarsa. Bai son ya ganta a iron wannan yanayin na sanyin jiki da rashin kuzari amma ta alas gane hakan. Daidai lokacin Sulaiman ya dago fuskarsa da yake duba wayarsa. Idanuwansu suka sarke da na Maigado. Da azama ya mik'e ya k'arasa kusa da ita. Maimakon ya karbi yaron hannunta Sai kawia ya had'a su duka ya rungume. Yayin da Maigado aka bare baki aka rushe da kukan da take rik'e shi. Sun jima a rungume da juna oga Asad da Abida suna kallonsu cikin wani irin yanayi na tausayawa. Sulaiman ya yi jarumtar sakinta ya jata suka zauna a kujera mai cin mutum biyu. Ya zari tissue da take kan centre table ya dinga goge mata hawayen da ya ki yankewa. Shi Dai oga Asad kallon ikon Allah da shagwaba yake yi da dukkan nutsuwarsa. Yana kuma gasgata ta fi Abida sakalci nesa ba kusa ba. Tsawon lokaci kafin Sulaiman ya samu ta Daina kuka. Murya ba amo ta ce "Yaya Sulaiman dan Allah a ina kake tsawon lokaci, baka tuna Ni, baka tuna su Anisa?" Jikinsa ya yi sanyi ya ce "Ina nan Bilkina! Batun tuna ku kuwa ba sai na ce komai ba, amma ina tuna ki sama da sau goma a rana, ina kuma yi miki addu'ar ki zama jaruma , duk kuma abin da zai tunkare marar dad'i Allah ya warware miki, ya had'a ki da dukkan alkairi ". Hawaye ya cika gurbin idonta ta ce "Shikenan na huce da kam na yi fishi da kai Yaya Sulaiman don kasan ina bukatarka a kusa amma ka tafi babu waiwaiye, na hak'ura tunda Allah yasa ya ka dawo mun gana. Ya bayan rabuwa?" Ya saki gauron numfashi ya ce "Alhamdulillahi zan ce amma ko ina babu dad'i. Duk inda aka je hak'urin nan dai shine a gaba. Ina su Amrah da Faruku?" A sanyaye Bilki ta ce "Suna Katsina ". Daidai lokacin Abida ta mik'a masa yaron ta ce "Ga Baba K'arami ". Sulaiman ya karbe shi yana zuba masa ido. Ya d'ago ya kalli Abida ya ce "Sai a ce kece uwarsu. Ba su yi kama da Anty Rukayya ba fa ko kad'an". Oga Asad ya yi shiru tare da tunanin bai san Rukayya ta rasu ba, bai san kuma Bilki ce ta haifesu ba. Kamar zai yi magana sai ya yi shiru yana cigaba da kallon k'annem nasa gabad'aya. Abida cikin gigighiwa aka ce "Baka Ga junior da ita yake kama ba. Nima wadannan share mini zuciyata suka yi. Duk da daka khadija ma muna kama." Sulaiman bai gano manufar Abida ba. Yaron ya fara kukan neman nono tunda wanka aka yi musu, Sai sun sha nono Sai a kwantar da su Su yi barci. To yau Basu sha ba. Abida ta karbi yaron ta ce "Maigado ba Shi baba Babba da bai Fara kukan ba ki ji da wnanan". Ba musu ta mik'a masa ya karɓi yaron yana kura masa ido don ya ga banbancinka da d'anuwansa don kuwa tabbas yan biyu ne masu kama da juna (Identical twins). Ya cigaba da kallon yaron da ya idanuwansa suke a bude tarr. Gaban Sulaiman ya fadi a dalilin ya ga k'wayar idon yaron irin tasu ce. A kallon da ya yiwa junior d'azu ya ga kammanin idonsu d'aya ne. Haka kuma idanuwan Farha suke tana jinjira. D'ayan da ya karbe shi idanuwansa a rufe suke shiyasa bai ga idonsa ba. Tabbas da oga Asad suke kama da Abida amma idanuwansu ba irin nasu bane. Irin nasa ne. Ya d'ago da niyyar yin tambihi game da tasirin jini kawai ya ga maigado na shayar da yaro. Kansa ya kulle. Ya kalli oga Asad ya ga shima kallonsa yake yi. Ya yi masa kwarjini ainun ya kasa bude baki ya tambaye shi. Ya fara bitar kalaman Baba 'ka je ka gaishe shi ka ga tagwayem da aka haifa masa'. Ya koma ga Abida ya ce "Uwar yaran matsala ta samu ko kuwa?" Kaitsaye Abida ta ce "Kamar ya ya kana ganin ya ras a gabanka?" A dimauce ya ce "Abida Maigado Matar Yaya Asad ce ko kuwa shayar da yaran take yi?" A takaice ta ce "Matarsa ce ita ta haifi yaran". Bai musa ba don kuwa idon yaran ya tabbatar masa na Bilki ne. Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:55] Ya kalli Bilki ya ce "Yanzu Maigado idonki da kwalli like Kishi da Anty Rukayya?" Ta daure fuska sosia ta kasa magana. Oga Asad Yana lura da ita. Abida ta ce "Anty Rukayya kam tuni ta yi kwanciyar manya". Sulaiman ya sake shiga rudu yayin da oga Asad ya rasa gane iskancin Abida na fad'in wai kwanciyar manya ta yi". A daburce Sulaiman ya ce "Kina nufin ta rasu ne?" Abida ta tattaro alhini ta ce "Shekaru biyu kenan. Plastic surgery ta yi, ya yi failing ". Hankalin Sulaiman ya sake tashi. Cikin damuwa yake yiwa oga Asad ta'aziyar rasuwarta. Har cikin zuciyar Asad ya ji dad'in damuwa da kaduwar da ya gani a fuskar Sulaiman da gangar jikinsa da kuma yana k'asar ya shaida zai zo masa gaisuwa. To me ya yiwa Sulaiman kenan? Shi ya d'auka rashin zuwa yi musu ta'aziya ne laifinsa. A ransa hake ayyana ko da sun huce to akwai buk'atar su tattauna don dukkan kullikan da suke zuciya su warware. Falon ya yi tsit kowa Maigado yake kallo yadda ta yi kicin kicin da fuskarta tana shayar da yaro. Abida ta dinga mamakinta. Tana yi kuma tana ganin yadda duk motsin oga Asad ita yake kallo baya ko gajiya. A ran Abida take ayyana idan namiji ya so mace ta huta kawai. Itama irin haka Sulaiman yake sonta. Duk iyashegenta haka yake jurewa baya kuma son su yi fad'a. Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:06] *Surayya Dee* PAGE 18 Oga Asad ya katse shirun ta hanyar cewa "Kun ga yadda take kumburin nan to fa a haka nake da ita. Gabad'aya ta murd'e ta k'i dad'in kasafi. Ba dama na shigo ta faranta mini kullum cikin fishi da bijire mini take. Da kuma zan kaita k'ara kowa cewa zai yi Bilki mai hak'uri ce, bata da hayaniya alhalin ni kad'ai nasan yadda nake zaune da ita." Sulaiman ya yi shiru. Bai k'arya ta batun oga Asad ba. Amma tabbas yasan ba haka kawai ta sauya ba. Ya zuba mata ido haka nazarinta. Can ya nisa ya kalli Abida ya ce "Kamar fa tana da damuwa ya kamata ta ga likita". Abida ta fara ambata scientist word6da likitoci ke fahimtar yaren. Take ya fahimci ciwon damuwar da ta yi ne ya sauya ta. A yanzu ma akwai alamunsa a tare da ita. Ya tausasa harshe ya ce "Ka yi hak'uri Yaya Asad zata daina yarinya ce." Bilki ta kalli Sulaiman tana kallo yadda kaunarta da tausayinta ya cikasu. Tana kuma ganin da dukkan zuciyarsa ya bawa oga Asad hak'uri tare da gabatar da uzzirin yarinya ce ita. To ashe Baban Bilkisu da yake fad'in ta yi hak'uri da su Aysha ashe ba wulakanci bane ya sanya yake fad'in su yara ne ba. Tunda gata da ta girme musu nesa ba kusa ba, yayanta yana fad'in a yi mata hak'uri yarinya ce ita. Oga Asad ya ce "Hak'uri ya zama dole ai, amma idan na ga bata gane hak'urin da nake yi ba ai zan nemarwa kaina mafita." Bilki aka sake daure fuska ba'a tanka ba. Yayin da Abida take mamakinta matuk'a da gaske. Sulaiman kuma gabad'aya mutuwar zaune ya yi tare alajabin zamowar Bilki matar Yaya Asad. A ransa yake fad'in fad'a ya k'are a tsakaninsa da yayan nasu tunda ya auri Bilkisu. Ya Kuma gamsu Asad ba ya k'insu saboda baya son uwarsu kamar yadda suke zaton. Don da yana k'insu ba zai auri Maigado ba. Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ya mike yana fad'in Yaya Asad Allah ya raya su Baba. Allah ya jiqan anty Rukayya. A mini hak'uri dan Allah." Oga Asad ya mik'e ya mik'a masa hannu tare da fad'in "Ameen Ameen. Na gode sosai. Yanzu zuwa nan da ka yi nawa ne. Ya kamata ka samu lokaci ka dawo sai ya zama zuwan Maigado ne. Ko gobe ka zo ku yi lunch tare". Sulaiman ya ce "Zan dawo amma ba gobe ba. Kafin dai na wuce in sha Allah". Ya kalle ta ya ce "Bilkina zan tafi". Ta murmusa ta ce "Ka ji yara sun dawo bari su shigo ku gaisa". Bai musa ba, ya koma ya zauna. Mintina biyu suka ji Shigowaesu suna wucewa zuwa sama. Abida ce ta fita ta kirasu. Farha ta kalleta ta ce "Ina junior?" "Da walwala ta ce "Yana gida barci yake yi." Suka shiga falon. Ganin Dady ya sanya suka tsugunna suna gaishe shi. Sulaiman ya bi yaran da ido Zuciyarsa ta harba da suka had'a ido da Farha kowa ya ganta ya ga Bilkinsa. Ya kalli Noor ya ce "Noor ya school? Ina Amal da Bilkisu?" "Ta ce sun hau sama yanzu zasu sauko." Ya ce "Farha ya karatun Ina Su Faruku?" Murya a snayaye ta ce "Shan can gidanmu da dadynmu na Katsina. Ni ma Mahmah ta ce ana yin hutu za'a kai ni". Ya yi murmushi ya ce "Hakan ya yi. Yana ayyana bata son shine Babanta ba. Ta kalli Maigado ta ce "mahmah yayanki ne na Hoto da kika.ce na dinga addu'ar Allah yasa a ganshi ko?" Bilki ta ce "Shine fa Farha g ashi Allah ya karbi addu'armu ya dawo." Oga Asad ya yi shiru wato ma ta dauka wanccan sahalallen ne ubanta kenan?" Yayin da Abida take kallonsu. Amma tana mamakin yadda Farha take ganin soyayyarta a idanuwan Farha kamar hadd5taoe ganin soyayyar Bilki. Haka nan ita da junior son juna suke yi kamar me. Daidai lokacin Amal da Bilkisu suka shigo Har sun cire uniform. Suak gaida duka iyayen nasu. Sualiman ya mik'awa Bilkisu hannu ya ce "Zo nan Bilkina haka kika girma?" Kunya ya kamata. Ta karisa kusa da shi ta durk'usa. To Noor da Farha da Amal duk ku matso mu yi selfie." Suka matsa ya dinga yi musu hoto da wayarsa yayin da Abida ta mike tana yi musu a tata wayar. Ya ce "next Zan zo mu je shopping tunda na dawo babu tsaraba". Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:11] Dad'i ya kamasu suka dinga yi masa godiya. A gidan suka yi sallar magharib. Daga suka yi sallama suka tafi. Oga Asad ya nisu Har harabar adana motoci. Amal da Bilkisu suka d'auki twins suka koma sama da Bilki. Alti ta ce "Ba Dai sun tafi ba?" A snayaye Bilki ta ce sun tafi Alti Amma zai dawo". Cikin walwala oga Asad da sualiman suka rabu. Abida ce take tukin. Sun fara nisa a Kan titi ta ce "Ogana yanzu ina muka nufa?" Bai kalle ta ba ya ce "Ind kike so". "Yaya Sule inda nak so fa ka ce? Ni fa na dauka ganin maigado da na kaika ka yi zaka huce ka yafe mini tunda na baka hak'uri a aikace, na yi nadama, na baka hak'uri baki da baki, na cire girman kai haba yaya Sule ka yi hak'uri ka yafewa masoyiyarka dan Allah". Ya numfasa ya ce "Me kike son na yafe miki zagin mami ko cire mini ciki da kika yi ko kuwa nuna mini iyaka da kika yi na ban isa da ke ba?" Zuciyarta ta yi nauyi. Hawaye ya k'wace mata ta rage gudun da yake yi. Da muryar kuka ta ce "Ka yafe mini maganganun da na yi akan mami, ba a hayyacina na yi su ba. A lokacin marab'aina ne suka motsa, su suka bude mini baki da kunne har nake jin lallai na yi b'aranbarama amma ba daga k'asan zuciyata kalaman suka fito ba. Ban tab'a yin abin da ya sanya ni nadama irin maganganun da jinnu suka furta ya bakina. Allah ne shaidar na yi tuba, na kuma gamsu ban kyauta ba, amma ni ma da sharrin jinnu na h'adu, ka yiwa Allah ka bani dama ko da kuwa shine last chance". Ya yi shiru bai ce uffan ba. Jikinta ya yi mata nauyi na gaske. Gabad'aya ta ji ta rasa kuzarinta don sosai ta ga fishi a tare da shi. Hakan ya sanya ta gangara gefe sosia ta yi parking gudun kada ta je ta bugawa wasu. "Yaya Sule ko ban ci arzikin komai ba na ci na junior mana." Ta fad'a murya ba amo. Ya muskuta ya ce "Wai kina nufin jikan mami ne?" Ta d'ago a kidime ta ce "Haba Dr wacce irin magana ce haka?" Ba walwala ya ce "Ta gaskiya da gaskiya mana". "Amma dai Yaya Sule ko makaho yasan d'anka ne ai". Ya numfasa ya ce "Hakane amma bani biro da takarda na yi lissafi. Duk da ta kad'u sai da ta bude jakarta ta dauko biro da jotter ta ba shi. Ta kunna mass fitilar motar. Ya ce ni dai nasan a Germany kin samu ciki a had'uwar da kika k'irata k'addara. Ya rubuta ranar. Ta Kalla tabbas bai manta date din ranar ba. Bata yi mamaki ba don kuwa shima guru ne tamkar ita. Ya sake rubuta date din da ta yi masa cin mutuncin tare da yunkurin cire ciki da jini ya b'alle mata. Ya kalleta ya ce "Kin zubar da cikin da ya kai wata uku. Tunda ga lokacin bamu sake haduwa ba ko?" Murya ba amo ta ce "Eh. " "To ta ya ya kike ganin zan gamsu junior jikan mami ne?" Ta kasa cewa komai. Saboda yadda zuciyarta ta yi nauyi. A hakan ya daure ya rubuta mass ranar haihuwar junior, ya yi masa llissafin kwanaki wanda lissafin ya dire zuwa ranar da aka sami cikin. Ya tabbatar daii shine bai zube ba wani ne daban ba. Tsawon lokaci sun yi shiru zuciyarta na bugawa da k'arfin gaske. Wanne irin dan bala'i ne haka Sulaiman? Ta sake gasgata Baba da ya ce duk abinta Sulaiman ya dama ta ya shanye yafi k'arfinta. Dama ta gasgata Baba. Amma a yau ta sake yarda dole ta bishi a hankali idan ba haka ba ya rugurguzata bak'in cikin da ta zata kasa fahimtar komai. Tsawon lokaci yana rubutu a rubuce wanda duka lissafine. Ya gama buge buge lissafinsa hawa hawa. Ya dago ya ce "Na yarda d'ana ne bana inkari akan hakan, tunda na gan shi na gamsu jinina ne, jikan mami ne tabbas. Amma ki rike abinki na bar miki shi ban da buk'atarsa tunda ya zo ne bisa tsautsayi da k'addara ba dan kina so ba. Da kin yi aiki da lura ma da sai ki k'i fad'a masa nine ubansa ya dinga amsa Sulaiman Abida ba Sulaiman Sulaiman ba." Ta fashe da kuka mai sauti tana fad'in amma "Yaya Sule duk rawar jiki da hak'urim da nake baka ala dole sai ka saka mun yi tashin hankali? Na baka hak'uri fa. Na sa ni ban kyauta ba shiyasa na kwantar da kaina nake ta binka ashe kai kallona kake yi kana mini tanadi iri iri?" Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:14] Ya girgiza kai ya ce "Abida kada ki kwantar mini da kai dan Allah. Fito min a Abidan Baba kin ji. " Ta yi maza ta saka hannu a bakinta ta danne alamun ta so yab'o masa bakar magana ne ta yi maza ta fasa. Ya ja k'aramin tsaki ya kishiginda. Alamun ya gama magana. Ta zuba masa ido tana jin jarabawa ne kawia ya sanya aka saka mata sonsa da yawa. Ban da haka da bai isa ya tisa ta a gaba yana mata gadara da nuna mata iyakarta ba. Ta ci kuka ta k'oshi don ta riga ta gama ganewa duk dabararta Sulaiman ba yarda zai yi su shirya salin alin ba. Dole sai ya gurfanar da ita a gaban Babansu wataƙila ma da duka yayyensu. Ita babban tashin hankalinta ace y'anuwansa su ji ta zagi MAMI. Ta sani wasarta zasu yi, duk da ba komai zata NEMA a gunsu ba amma zata so ace akwai fahimtar juna da soyayya a tsakaninsu mussaman ma da ya kasance su yan uwan juna ne. Ai ko Bilki ta ji maganganun da ta yi akan uwarsu sai ta k'ullace ta, bare kuma su Yaya Hamida da Ansari da y'ay'an da ta haifa ma sai sun washe su matuƙar akan mami ne. Cikin rishin kuka ta ce "Ka yiwa Allah ka yiwa alfarmar zumunci kada ka fad'awa y'anuwan haihuwarka marab'aina sun kushe MAMI. Ni Wallahi ban soke ta ba. Wallahi summa Tallahi aljanun da suka hana ni aure tuntuni ne suka motsa a lokacin saboda sun kasa raba ni da kai". Hatta jinin da ya balle mini na cikin sharrinsu. Addu'ar da na dage da yi ne na fatattake su, ai har junior suka so shafa. Allah ne ya takaita." Ta fad'a tana kuka sosia. Ya zuba mata ido yana ganin yadda take kuka ainun. Ta kuma hakikance jinnu ne suka shige ta. Yanzu da jinnu zai yi rikici kenan ko me take nufi. A ransa ya ce "Kinayar mata babba ce. Yanzun nan zasu rufta mutum. Kuma yanzu tunda ta ce jinnu ne to kuwa akan haka zata tafi duk runtsi ba zata yarda ita ce ba. Ya rasa mai zai ce illah zuba mata ido tana ta rera kukanta tamkar sarewa. "Abida ja motar nan mu tafi na gaji". Ya fad'a a kausashe "Yaya Sule ba zan iya tuki ba Wallahi. Kana mini fishi irin haka ina zan iya to ta ya ya ma?" Ta fad'a cikin gunjin kuka. Ya bude k'ofar ya fita ya zagaya ya ce "Fito ki ba ni waje." Tana fitowa ba zato kawai ya jita a k'irjinsa ta rungume shi sosai. Gabad'aya ya ji shocked ya zama mutum mutumi. Ita kuma ta shimfide fuskarta tana tsiyayar masa da hawayenta a k'irjinsa. Da wata irin murya hade da gunjin kuka ta ce "Yaya Sule Kada ka hukunta ni da laifin shaidanun halittun da suke son rabamu Wallahi jinnul Ashiq ne suke shafata from time to time. Ka yi hak'uri ka yafe mini, ina sonka dan Allah ". Daga haka ta sake shi ta wuce ta zagaya ta shiga gaban motar. Mutuwar tsaye kawai ya yi. Komai na jikinsa ya amsa. Hawayenta ya raunana shi matuƙa gaya. Shi da kansa da ya karbi motar a kasalance yake janta. Har suka isa gida basu sake magana ba. Tuni an yi sallar isha. Basu tarar da Baba a falo ba, dan haka Sulaiman ya juya zuwa d'akinsa Abida ta shiga ciki. .... Yau ma ba za ki je d'akin mijinki ba Mahmah?" Alti ta tambayi Bilki da ta ga ta yi shirin barci ta haye gadonta ta kwanta. Uffan bata ce mata. Ta sake maimatawa a karo na biyu. Nan ma ko motsi bata yi ba. A kufule ta ce "Da wannan bak'in cikin da kike cusa mini gwara na tattara na baki waje. Kuma dan ban isa ba ne, da ace ina da kima a wajenki da ba ki mayar da ba a bakin komai ba. Dole Alhaji ya dinga ganina shekeke ya dauka na isa da ke, bana fad'aiki gaskiya nan kuwa isa ne ban yi ba. Da kina da hankali labarin da Abida ta bamu dazu da yasa kin je makantar ta nutsu amma tamkar ana zuga ki. Sam nabu nadama a lamuranki! Bilki da ta gaji da suratan Alti ba kakkautawa kawai sai ta mike ta isa gaban madubi ta sake fesa turarenta na weekend. Sannan ta bude kwalbar turaren mkbees perfumery.... Ta shafa. Ta d'auki hijab ta ce "Sai da safe." Alti aka ce "Yauwa Allah ya yi miki albarka aje lafiya a dawo lafiya ko ke fa?" Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:18] Bilki ta fice ta ja k'ofar. Alti ta gyara yara ta kwantar da su ta kashe fitila ta kwanta bayan ta yi addu'a. Bilki kuwa daya d'akinta ta bude a hankali ya shige ta yi kwanciyarta. Bata jima da kwanciyar ba wayarta ta dinga haske. Ta duba ya ga Baban Bilkisu ne. Da kamar ba zata d'auka ba sai kuma ta kasa sharewa. Ta dauka ta saka a kunnenta amma ta yi shiru. Murya ba amo ya ce "Yanzu Bilki ba kya jin tsoron hak'kina. Wai menene yake faruwa ne haka?" Ta yi shiru. Ya numfasa ya ce "Ki zo yanzun nan". A hankali ta ce "Ni na riga na yi addu'ar barci". "Ba za ki zo ba kenan?" "Ni gaskiya samanka gabad'aya bana sonta, tana saukar mini da takurarren yanayi gaskiya ". Ya sassauta ya ce "Dan Allah ki zo, just an hour's sai ki dawo ba sai kin kwana gabad'aya ba." Ta yi shiru tabbacin bata gamsu ba. Ransa ya fara b'aci ya ce "Yau ma wulakancin za ki sake yi mini?" Ta yi shiru. Ya katse wayarsa. Amma a yau hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi. Tabbas akwai abin da yake ranta, kuma sai ta fad'a da ya samu nutsuwa ya gaji da wannan bala'in da kisan mummuken da yarinyar take yi masa. Shi irin wannan nunkufircin ne baya so a halayyarta tuntuni. Baya son shiru shiru ya yi yawa. Ga shi yanzu da girmansa da mutuncinsa sai faman gana masa azaba take yi. Ta tashi hankalinta ta tashi nasa. Ranar bai yi wani barcin kirki ba don zuciyarsa ta rinjayar masa so take ta bar shi, ta koma gidanta wajen y'ay'anta. Duk juyin da zai yi tunanin twins da tausayinsu ke neman kassara shi. Wani shashi na zuciyarsa ya kore tunanin hakan ya kutso masa da tunanin y'anuwanta ke zugata ta bijire masa. Wadannan hasashen da suke bijiro masa sun sake dungunzuma masa lissafi ainun. Amma a gobe za'a yi komai a kare ya riga ya gaji k'warai da gaske. .. A daddafe ya kai asuba Yana dawowa daga masallaci ya dauki waya ya lalubo Faruku. Bugu d'aya ya d'auka tare da fad'in "Ran oga ya dade! Sassafe haka. Allah yasa lafiya?" A kidime ya ce "Faruk babu lafiya wannan k'anwar taka ta k'i dad'in kasafi. Ka zo goma ina jiranka. Zan fita 12 ka zo da wuri na riga, na gaji gaskiya." Faruku ya ce "Sai hak'uri oga yarinya ce kuma bata fahimce ka ba. Ka yi hakuri komai zai daidaita ". Oga Asad ya ce "Gaskiya fa Faruku ba zai yiwu ina lallabata tana mini wulakanci ba. Haka siddan ta d'ank'ware ranta sai rama take yi a tsaye. Dazu da Sulaiman ya zo ya ganta ta yi wani zuru zuru da ita tamkar na nutse tsabar takaici. Haba yarinyar nan tana cutata gaskiya. Gaba fa take yi da ni ba gaira ba sabar. Gaishe ni ma da ƙyar take yi wanne irin al'amarine haka. Yau kam komai zai iya faruwa a tsakaninmu. Matuƙar ba ta bude baki ta fadi me nake yi mata ba." Faruku ya ce "Zan zo in sha Allah. Ka yi hak'uri." K'arfe goma a gidan oga Asad ta yiwa Faruku. A falon da ya sauki Sulaiman jiya anan ya sauki Faruku. Suka gaisa Faruku na dariya ya ce "Yanzu saboda Allah oga ace ba zaka iya shawo kanta ba sai ana muku shari'a?" A kufule ya ce "To ai ba sona take ba shiyasa. Ba zaka gane gashin k'umar da take yi mini ba ne. " Faruku ya k'ira layinta ta dauka cikin nutsuwa take gaishe shi. Daidai lokacin tana shan shayin da ya zama k'aida sai Alti ta had'a mata ta sha da zarar ta fito daga wanka. Faruk da ya ji muryarta ba sukuni ya ce "Ko ba ki tashi bane?" "Na tashi Yaya Faruku". "To zo mu gaisa ga ni a gidanki". Tana jin muryar oga Asad yana fad'in "Na bata gidan ne da zaka ce mata gidanta?" Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:23] Jikinta ya bata k'ara ya kaita Da yake ta yi wanka ya shirya. Sai kawai ya d'ora tsadaddiyar Egyptians abaya ta umm asalan... Alti zan je k'asa Yaya Faruku ne ya zo". "To ki gaishe shi da kyau ". Ta fadi hakan da walwala. Tare ta tarar da su. Suna zaune a kujera. Fuskar oga Asad a daure ainun. Ya zauna a k'asa ta gaishe su . Faruku ya amsa yayin da oga bai amsa ba. Kanta na k'asa. Faruku ya ce "Maigado me yake faruwa ne, menene matsalarki?" Ta yi shiru. Ya sake maimaitawa. Ta ce "ba komai Yaya". "Ba komai amma kike bijirewa mijinki? Kinsan hukuncinatar da ta kangarewa mijinta, sanin kanki ne tana cikin fishin Ubangiji amma kika bi wannan turbar?" Murya ba amo ta ce "Ban kangare masa ba ni". A tunzure oga Asad ya ce "Kangarewa ta nawa kuma? Ai na riga na gaji da wulakancinki, na gane inda kika dosa. Ba kya son zama da ni saboda kina son komawa wajen y'a'yanki. To nima na shirya idan kin k'i zama da ni ai ba mutuwa zan yi ba. Mata suna nan birjik kowacce iri nake so zan auro na samu farin cikin da nake buk'ata." Ta yi k'asa da kanta hawaye ya fara yi mata tsere. Faruku ya ce "A a oga bi a sannu mana, take heart pls." A fusace ya ce "Ka san Allah ba zan bita a sannu ba yau. Shaida zaka zame mini a wajen Baba don na gaji gabad'aya. Sai ta bude baki ta fadi laifin me na yi mata ko kuma, a yita ta k'are! "Bilkisu". Faruku ya k'ira a tausashe. "Na'am". Ta furta cikin muryar kuka. "Menene damuwarki fad'a mini kin ji". Da kuka sosia ta ce "Na gaji ne, na gaji fiye da yadda yake ƙirarin ya gaji". "Ka ji ko Faruku na fad'a maka hankalinta ba anan yake ba. Ba dai na halasta musu zaman ba, ai dole ta butulce mini! Ya fad'a hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi. Jikin Faruku ya yi sanyi ganin yadda d'anuwansa ya daburce. "Bilki fad'a mini me yake faruwa kada na gasgata zatonsa. Da kuka sosai ta ce "Ka yarda da batunsa kawai Yaya Faruku. Bana son zama da shi, can nake son komawa ba shike nan ba! Save Restricted Content Bot, [Oct 24, 2025 at 13:48] Hatta Faruk ya shiga rudu. Ya ce "A a Maigado ba hakan ba ne." "Hakane Yaya Faruku". Nan da nan oga Asad ya bar kujerar da yake zaune ya isa inda take zaune ya durkushe ya kama hannunta ya ce "Ki ji tausayina dan Allah, ki duba jariran yaran nan sun fi waɗanccan buk'atarki. Ki dube ni da nake son zama da ke. Wanda yake son sonka, yake son zama da kai ai adalci kake yi masa. Ko ba kya sona ki yiwa Allah ki ji tausayin ya'yana, ni kuma ki yi mini adalci Maigado ya ya kike son na yi ne?" Faruku ya yi tsam yana kallonsu. Bai taɓa ganin abin da ya raunana oga Asad ba. Amma a yanzu dukkan rauninsa ya gama bayyana. Firgici sosai a tare da shi. A da gani yake yi ya fishi son Maigado. Amma yau ya tabbatar nan duniya ba mai sonta fiye da oga Asad. Ga mamakinsa sai ya ji zuciyarsa ta yi masa nauyi. Ba ko tantama kishine yake neman murd'e shi don kuwa ya hango soyayyar oga Asad baro baro a idanuwanta. Ya yi maza ya dinga a'uziya a zuciyarsa don kore shaiɗanin da yake neman kawata masa ita. Ya numfasa ya kaurara murya ya ce "Maigado ba zan sake tambayar ki ba. Tunda har na tako don na ji ba'asin halin da kuke ciki ai kinsan dan ya san na isa da ke ne, shiyasa ya k'ira ni. Idan kuma ban isa ki fad'a mini matsalarki ba sai na tashi na tafi harkkokina". Cikin kuka sosai ta ce "Tunda na zo gidan fa gabad'aya hak'uri nake yi. Baya binciken komai. Haka na sha wahalarsa akan yara bai taɓa ba ni dama mun tattauna ba. Sai dai ya yi ta yi mini fishi. Lokacin da yake ganin Farha kullum tare da ni bai taɓa tambayar dalilin da ya sanya bata zuwa cikinsu ba. Sai dai ya balbale ni da fad'an ina ware ta alhalin cin zalinta suke yi. Aka gama wannan danbarwar. Akan idonsa ya ga chart dinsu suna zagina suna zagin uwata bai d'auki mataki ba. Amma ni nan dan na zagi maimurabus da uwarta ba bala'in da bai yi ba. Wato uwata bata da kima a wajensa sai maimurabus da uwarta? Kuma tunda na ce ba zan zauna da Laura ba shine ya kori Farha tare da dakatar da Alti. Duk fa na yi hak'uri saboda Baba. A hakan kuma d'an kuskure kad'an zan yi masa ya hau sarhutun maimurabus ta fini biyayya, ta fini kaza, ta fini iya kaza, Maimurabus tana da alfarmomi a wajensa. Komai na yi masa haka zai kalle ni ya ce shi ba haka ake yi masa ba, shi matarsa ba irina ba ce, bata yi masa fishi. Ni ba ni da alheri. To na bar mata kayanta ya bita kushewar su had'ehta cigaba da sonsa da yi masa biyayya ina ce shikenan?" Faruku ya kasa bude baki ya yi magana don kuwa dariya ce fal a bakinsa. Wai Rukayya ce maimurabus. Wanne irin sababi ne haka take ga ni? Wato mata akan kishi babu kyua. Sannan ya Ƙara gasgata Bilki mai tsiya ce ta gaske. Kan dole ya mike ya ce "Ina zuwa". Kafin su amsa masa ya fice da azama. Gefe daya ya samu ya yi dariyarsa. Ba abin da yake ba shi dariya irin yadda take fad'in maimurabus ga kuma oga Asad da kansa gurfane a gefenta tamkar ba shi ya gama cika bakin yau komai zai k'are don ya riga ya gaji ba. Kai mata mata Allah ya shirye su kawai. Sai da ya nutsu ya shanye dariyar sannan ya koma fuska a daure. Ya bude murya ya ce "Yanzu ki yi hak'uri Maigado komai ya wuce. Kema ki dinga yi masa bayani idan ya bata miki, ki daina rikewa a zuciyarki indai ba so kike ki kwanta jinya ba". A hankali ta ce "To ai ni da na ga baya bincike na d'auka yana ganin komai ta cctv camera don kuwa gida irin wannan, kuma gidan jami'in tsaro ba'a yi tsamammanin babu ita ba". Oga Asad ya ce "Hadawa ne ba'a yi ba. Amma za'a had'a. Yanzu tunda na ji matsalar to komai ya wuce ba zan sake kwatanta ki da Rukayya ba." Ta yi shiru. Ya nisa ya ce tunda kin fad'i matsalolin na kuma yarda zan gyara to ki ware zuciyarki ki dinga walwala ". Nan ma bata amsa ba. Faruku ya ce "Shikenan matsalolin ko da saura Bilki?" Sai ta yunk'ura zata yi batun hoto sai ta kasa. Faruku ya ce "To me yasa ba kya zuwa samansa?" Ta d'ago ta ce "Yaya Faruku kada ka shiga wannan batun don gaskiya ina jin nauyinka. Kuma Wallahi ina kan batuna matuƙar ba zai kwashe ba, ba zan je ba, kar ma ka ce zaka tursasa ni don kuwa wannan karon lallai ba zan yarda ba". Save Restricted Content Bot, [Oct 24, 2025 at 13:51] A rikice oga Asad ya ce "me zan kwashe?" Ta kasa magana sai kawia kuka ya sake k'wace mata. Tsawon lokaci tana kuka mai nauyi kafin ta sarara. Faruku ya dinga rarrashinta har ya samu ta huce. Oga Asad ya ce "Faruku ka tambaye ta me zan kwashe dan Allah?" Cikin rarrashi Faruk ya ce "Menene zai kwashe? Faɗa mini n8a zan tilasata ki ba." Da muryar kuka ta ce "Hotunanta ya girke ba d'aya ba, ba biyu ba. Kuma don son ya muzanta ni har akan side drower din gado.". Jikin oga Asad ya mutu. Babu tantama tafi Rukayya zazzafan kishi.Ya kuma tabbatar sune suka fi nukurkusarta tunda tun farkon zuwanta ta daina zuwa saman. Shi zuciyarsa d'aya ya d'auka k'asaita ce kawai ta sanya ba zata bishi ba. Sai shi yake zuwa tare da yi mata uzzirin yarinya ce a kansa. Ashe hotunansa da na Rukayya ne ba za'a ajiye ba. A ransa ya furta wanne irin k'arfin hali ne haka? Shekara d'aya tak suka yi tare. Amma take kishin matar da aka yi shekaru masu yawa da ita kuma ma bata duniyar. A k'asan zuciyarsa kuma ya ji dad'i sonsa take, so kuwa ba dan kad'an ba. Oga Asad ya yi maza ya ce "Zan cire su indai sune matsalar da ta saka kika bijire mini to zan cire su. Na kuma yi miki alk'awarin ba zan sake kwatanta ki da Rukayya ba, bare na ce ta fiki ". Faruku ya ce "Bilki idan aka kwashe hotunan shikenan ko akwia sauran damuwa?" Kanta na k'asa ta ce "Shikenan." Oga Asad ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwar ba zugata ake yi ba, ba kuma so take ta koma gidan tsohon mijinta ba. Ya kalli Faruku ya ce "Kafin ka tafi ka roketa ta yi mini hakuri. Yau din nan zan d'auke na kan side drower ba sai gobe ba. Amma na falo ta yi mini hakuri sai nan da d'an lokaci k'alilan. Ban so tashi guda na cire, yaran nan sun ankara tunda suna hawa saman. Ni dai ba yadda zasu yi da ni, amma ita zata yi bak'in jini ne a gunsu mussaman masu wayon tunda zasu zargi na cire ne saboda ita. Daga nan zasu sake jan baya da ita. Ni kuma na fi son su zauna lafiya su sota ta zame musu tamkar uwarsu. Tausayinsa ya kama Faruku a dalilin ya fahimci ta kowanne bangare a cikin zullimin zarginsu yake. Kai sabga da mata akwai rud'anin gaske. Ba ga yaransu ba, ba ga manyansu ba. Sun iya kacacccala al'amura da yawa, yana wahalar gaske su yaba k'ok'ari da adalcin namiji". Faruku ya numfasa ya ce "Allah yasa yau ne zuwana na k'arshe gidan nan da nufin na yi muku sulhu". Oga Asad ya ce "In sha Allah! Ai tunda na gane inda matsalar take to zan kiyaye". Bilki bata ce komai ba. Faruku ya ce "Sarauniyar shaiba ba ki ce komai ba". Kaitsaye ta ce "Ai dama laifinsa ne, idan ya daina kunsa mini kuttu ta hanyar fad'in an fini a zuciyarsa, ya kuma cire mini hotunan maimurabus a wajensa ai shikenan. Yanzu ina ruwana da hotonsu na falon k'asa? "To Allah ya yi miki albarka na gode sosia Allah ya shirya miki zuri'a." Oga Asad ya yi maza ya ce "Idan shima zai zama issue duk zan cire su a hankali. Fatana ki daina damuwa, ki kuma daina tayar mini da hankali." Yaya Faruku ya ce "To kin ji ko Sarauniyar shaibà. Dan Allah ki kwantar da hankalinki". Daga haka Faruku ya mike ya yi musu sallama. Ya ce "Zan dawo mu zauna Maigado." gidan suka tsaya. Murya kasa k'asa oga Asad ya ce "D'an koma Faruku ka sake yi mata nasiha akan yau din nan ta huce, ta bar komai ya wuce, mai tsiya ce fa! Kuma batun hotuna ka sake jaddada mata zan ciresu ba da jimawa ba, ta yi minihak'uri. Don idan ka tafi tana iya ce wa sai lokacin da na cire din zata saurare ni". Bai ce masa komai ba ya juya din tare da amannar Asad bai so wani abu irin Bilki ba. Oga Asad zuciyarsa a tsaye take, ba shi da tsoro ko kad'an, shiyasa aikin d'amara ya dace da shi. Amma a yau ya tabbatar yana tsoron fishin Bilki. Yana tsoron ta bijire masa. A zuciyarsa murna yake yiwa Bilki don kuwa ta auri wanda yake sonta da dukkan zuciyarsa. Duk da itama a yanzu yasan oaga Asad take so. Ta kuma gane shi son zumunta take yi masa ba na sha'awa da birgewa ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 24, 2025 at 13:54] Yana shiga falon ya ganta a tsaye da wayarsa a hannunta. A sanyaye ta ce "Yauwa ga shi da kai maka zan yi, ka tashi ka barta." Ya karɓa ya ce "To zauna dama so nake ya bamu guri, mu yi sirri". Ta sake zama a k'asa. Ya sassauta murya ya ce "Yanzu ke Bilki ba ki iya y'ar kissar nan ta mata ba ko kad'an? Sai idan miji ya b'ata miki ko ya yi miki ba daidai ba. Ki ta kunci kina ta dogon fishi har ki lalace irin haka? To ba dabara kika yiwa kanki ba. Ai idan kika yi kuskuren da ya fara jurewa fishinki to zaku kai gwadaben da shi zai musguna miki kuma ke ce za ki ba shi hak'uri don kuwa shima fishin zai dauka. Matsalar hoto ce za ki bari ta dama miki lissafi tsawon lokaci irin haka? Yo ko tana raye ina ruwanki da ita, indai mijinki na sonki bare baiwar Allahn nan mutumiyarki ce". Ta kawar da fuskarta gefe ta ce "Kafin yanzu ba". Ya yi dariya kad'an a ransa ya ce 'ban da yanzu kenan?' Ya zarce da fad'in da kin iya ma, ai juyar da hotunan kawai za ki yi idan ba ya nan. Idan ya dawo ya ga ni zai gane yaren da kyau da kyau. Amma ki bar k'aramin abu a ranki har ya yi yunkurin haifar da matsalolin da ba zasu gyaru ba. Ki daina dogon fishi kin ji sarauniyar shaiba, kuma ki dinga bude baki kuna tattauna damuwarki. "Kwanaki da na ce ki koyi kissar da kika ce ba ki iya ba ashe kuwa zama kika yi ba ki saka d'ambar koya ba ko?" Ta yi shiru kanta na k'asa. Ya sake maimatawa. Murya ba amo ta ce "To ni ai tunda ya ce mini ba ni da alheri na kasa jure komai." Ya nisa ya ce "Bilkisuu gaskiya ki canja taku. Ta ya ya daga zuwanki za ki bari ya fahimci kishi kike yi da matar da ya shafe shekaru sama da ashirin da biyar da ita? Kuma abin kaicon ba cikin dabara da iya taku ba? Nasan kina da kishi amma ban yi zaton a yanzu da kika mallaki hankalinki za ki bari kishi ya rude ki da yawa irin haka ba. Tsananin kishin mace alamun tana cikin garari ne duniya da lahira kuwa. Wai kina lissafin idan har za ki dade a duniya ma kin cinye rabin rayuwarki kuwa? Menene ya yi miki dad'i da za ki bari matar da ba ki zauna da ita ba, ta dama miki lissafi, tunaninta ya hana ki nutsuwa balle ki samarwa da mijinki nutsuwar da ta dace da shi. Ita kinsan irin sadaukarwa da hak'urin da ta yi tsawon shekarun da suka shafe tare? Maimakon ki mayar da hankalinki wajen gina kanki ta yadda ko bai mance da ita ba, to kuma za ki hana shi tunaninta akai akai. Amma sai ki ta yi masa k'unci da tashin hankalin da zai saka ya yi ta tunaninta tare da ganin ba zai samu mai irin alherinta da hak'urinta ba! Ya nisa ya yi shiru yana nazarin yadda jikinta ya yi lakwas. Ya cigaba da fad'in "ki duba y'ay'an da ta haifa masa mana. Kada ki yaudari kanki dole tana da alfarmomi. Amma idan kin iya ina tabbatar miki zai ta jin kunyarki akan sha'aninta. Zan kuma fad'a miki wata magana da hakikanin gaskiya ce. Oga bai so wata mace a duniya irinki ba Hakan da na gasgata ya sanya na bar masa ke. Amma fa idan ba ki iya ba, sannu a hankali za ki ta wanke soyayyar nan da kanki, don kuwa mu maza dukkanmu mun fi buk'atar kwanciyar hankali da sadaukarwa a gun wacce muke so. Idan muka rasa samun nutsuwa to fa mace fita take yi a ranmu fit. Ki nutsu ki yiwa kanki gini mai k'arko a zuciyarsa ta yadda ba za'a tsere miki ba. Ki kula da y'ay'ansa iyakacin iyawarki. Ki yi masa biyyaya kan jiki kan k'arfi. Ki kuma amsa kiransa a kowanne lokaci matuƙar kina lafiya kina cikin tsarki". Kanta na k'asa ta ce "To " Ya zuba mata ido yana nazarin yanzu ne ya gasgata ta ajiye makaman yaƙin d ta shirya yi da oga Asad. D'azu dungu ta yi masa kawai. Surayya Dee. PAGE 19 *DINGISHIN KWAD'O* Ya numfasa ya ce "Sarauniyar sheba ya ya dambarwa ta kare ko kuwa da saura? Yanzu kin amince da rok'on da ya yi miki na batun cire hotunan. Za ki yi masa hak'uri kamar yadda ya roke ki ko kuwa?" Ba ja in ja ta ce "Na amince tunda ya saka ka a al'amarin sannan ya ce zai cire na cikin d'aki a yau." "Yauwa Bilkisu yayar Abida Allah ya saka miki da alheri, na gode. Lallai, lallai ya ga sauyi, ya gane yayanki ya zo gidansa ya yi masa gyara ". "To" Ta amsa kanta na k'asa. Ya mike ya ce "Da yake ba a nutse nake ba ban tambayi twins ba. Nasan manyan na school." "Wanka ake yi musu zuwanka". "To a shafa mini kansu". Ya fita ya iske oga Asad jingine a jikin motarsa. Dariya sosia ya yi ya ce "Oga ka kamu fa y'ar yarinya ta susuta ka irin haka?" "To ya zan yi Faruku? Al'amarin mata akwai tayar da hankali duk jarumtar mutum kuwa." "To sai ka shiga ka sake rarrashi har ka samu kanta na gama gyara maka komai. Kuma Wallahi ka kiyaye misali da mai murabus a gabanta." Faruku ya faɗa cikin matsananciyar dariya. Don shi sunan gabad'aya dariya yake ba shi. Ya kuma gasgata basu gama gane tsiyar Bilki ba. Cikin dariya oga Asad ya ce "Wane ni na sake! Faruku ya gintse dariyarsa ya ce "Oga ka kiyaye motsawa sarauniyar shaiba kishinta. Na rantse maka har yau ban ga mace mai kishinta ba a duniyata. Ka ga irin kishin Jamila, ka ga kishin Rukayya to Wallahi ba kishi suke yi ba. Tana fa yarinya bata fi 13 zuwa 14 na yi aure ba. Amma shekaru biyu ta yi bata yi mini magana. Hanyar da tasan ina bi ma, bata bi don kada ta ganni. Ba k'aramin jan ido baba K'arami da Baba Babba suka hadu, suka yi mata ba kafin ta yarda muke gaisawa. Hakan ma sai da ta ce zata gaishe ni amma a tabbatar mini ita ba budurwata ba ce. Kai duk baka san wannan ba tunda ka yi nisa ". Oga Asad ya ce"Zan kiyaye in sha Allah ai na ga jalala". Ya shiga motarsa ya tafi, yana cigaba da dariyar maimurabus. Oga Asad kuma ya nufi cikin gidan cikin d'oki mai yawa. Kaitsaye ɗakinta ya nufa ya tarar da ita zaune tana shayar da Baba Babba. Alti na rik'e da Baba Babba da shima yake ta kusur kusur din neman nono. Alti ta gaishe shi cikin girmamawa. Ya karbi yaron hannunta. Ita kuma ta d'auki hijab dinta ta fice zuwa d'akinta da yake k'asa don ta yi wanka. Ya zauna kusa da ita, kafaɗarsu na gogayya da juna. Ya ce "Sarauniyar sheiba my luv". Kawai sai ta ji dariya ta k'wace mata. Ta dinga dariya fararen hakoranta suka bayyana. Ya kalle ta yana sake samun nutsuwar lallai ta huce don zai iya cewa rabon da ta yi masa murmushi na sosai tun zuwansu Calabar . Da murmushi ya ce "menene ya saki dariya irin haka? Don na ce miki my love ko kuwa dan kin ga tasirinki mai k'arfi ne a zuciyata?" "Allah Baban Bilkisu dariya kake ba ni idan kana wani luv love din nan". Wannan karon shi ma dariyar ce ta subuce masa. Ya gyra zama ya ce "Fad'a mini menene abin dariya dan na ce miki my love. Wato tsufa na yi ne ko kuwa me?" Ta sake kyalkyalewa da dariya ta ce "Ni ai nasan baka tsufa ba. Tunda dai gamgam nake jin ka, kawai kunya ce take kama ni idan na tuna wai Yaya Asad din nan ne ke mini yar murya da ambaton kalmomin soyayya ". Ya murmusa ya ce "A gabanki idan ina son nutsuwa ai dole na warware fuska na kuma datse shekaruna su zama irin naki." Ta yi gajeriyar dariya bata ce uffan ba. Ya nisa ya ce ". Ya yi barci ne?" "Eh ya yi". To cire shi d'anuwansa ya sha". Ba musu ta daga shi. Ya yi gyatsa sannan ta kwantar da shi. Ta karbi d'ayan. Shima a hakan ya yi barci. Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:35] Ya mike ya ce "K'ira Alti ta zauna da su sai ki zo". Ta numfasa ta ce "Ai sun yi wayo ba sai ta zo ba". "A a k'irata dai nafi son ana kula da su ko suna barci". Bata sake musu ba ta ce "To". Ta k'ira alti ta dauka. "Alti zan kaiwa Baban Bilkisu shayi ki zo wajen yaran". Alti da murna aka ce "To ga ni nan , mai nake shafawa na fito daga wanka." Daga haka ya fice yana fad'in"ina fa jiranki ". "Ta ce" to". A sanyaye. Ta sake gogo oils masu dad'in k'amshi a duka gabobinta. Ta shafawa kanta man gashi masu dad'in k'amshi. Ta d'auko wata farar lingerie mai matukar kyau. Ta rik'e a hannunta bata snaya ba. Daidai lokacin Alti ta shigo. Da walwala ta ce "Je ki kai masa daga nan ma ki gyara masa d'akin". Bilki bata ce komai ba, amma dai ta gane hausar. Yana shiga ya cire ƙaton hotonsa da na Rukayya da yake kallon k'ofar shigowa yana maka barka da zuwa, ya mayar da shi bangon' da k'ofar take ma'ana ba zaka ganshi kamar da ba, dole sai ka shiga cikin falon ka nutsu. Sannan ya zarce bedroom ya d'auke na kan side drower ya saka a cikin drawer. A fili ya ce "Allah ya jiƙanki Rukky. Masalaha na bi. Allah ya yi miki Rahma ". Na ce ba. Rayuwa fa continuation ce. Idan kika mutu tabbas mijinki zai yi aure ya cigaba da rayuwa wataƙila ma ya so ta fiye da ke. Ki fa yi ibada Hajiya. Ki nemi kud'in halali. Ki yi alheri. Ki yi sadaka. Ki yawaita addu'ar a tsare miki imaninki, a tsare ki daga zazzafan kishi da zai saka ki shirkar da za ki kafirta don kuwa kwanciyar kabari kad'ai da take gabanmu abin mu ji tsoron Allah ne mu nemi lahira tamkar gobe zamu tafi. Tana fitowa ta shige d'aya d'akin ta cire rigar jikinta ta snaya wannan lingerie din da ta tsaya iya guiwarta. Gabad'aya rigar ya ji jikinta ya kwanta. Ta juya yana kallon yadda shape don mazaunanta suka fito sosai a cikin rigar. Ta isa gaban madubi ta warware gashinta da yake makale cikin ribon ta taje shi tare da sake shafe shi da mai ta kuma fesa masa turaren gashi. Duk wani lokon jikinta ta shafe shi da oils masu dad'in gaske don kuwa tasan yau ba dama lasar da za'a yi mata ba mai sauk'i ba ce. Ita da kanta zumudi take yi mai yawa don da kanta kewarsa take yi ainun. Open abaya ta dora akan lingerie din. Cikin sanda ta bude k'ofar d'akin ta fito a hankali ta janyo ta rufe d'akin ba dan komai ba sai don haka kawai bata son Alti ta leko ta ga irin kwalliyar da ta yi. Kaitsaye falonsa ta shiga. Ta yi turus ganin babu hoton da yake saka ta faduwar gaba. Ta juya Sai ta gan shi a d'ayan bango. Ta tsura musu ido komin hassadar mai hassada hoton ya zanu. Duk wanda ya zanasu lallai yana da fikira. Ta juya ta nufi dakin ta hangi side drower ta ga babu hoton. Ta yi sallama. Da hanzari ya kariso bak'in kofar ya rik'e hannunta yana fad'in "welcome welcome Maigado. Ya saka hannu ya cire abayar. Ya kalli yadda rigar ta bi jikinta. Ya riketa ya juyata ya kalli bayanta. Ya kasa hak'uri ya rik'ota tare kai dukkan hannuwansa bayan da suke daukar hankalinsa. Murya ba amo ya ce "Anya Maigado ba sai na saka an yi mana crossing of the sword ba kuwa?" Ta yi murmushi tare da fad'in."ka ga kuwa ina so yana matuƙar birgeni". "Za'a yi miki kuwa sarauniyar sheba. Ya sake juya ta, ta fuskance shi. Da wata irin murya ya ce "Wannan wanka da me zan siye shi ne. Iye cancadi, kin yi kyau Maigado irin totaly din nan". Kanta ya yi gingiringim. Ta ji dad'i. Abin da ya tokareta a k'ahon zuciyarta ya fad'a mata. Ya rik'eta zuwa kan kujerar da take cikin d'akin. Shi ya zauna sannan ya zaunar da ita akan cinyoyinsa. Ya ce "Na gode Maigado. Amma ina son mu yi wata magana guda d'aya don mu rufe duk k'ofar da zata iya kawo mana dogon rikici ". Cikin nutsuwa ta ce "To". Ya nisa ya ce "Ina son na fad'a miki ni ba'a mini tsarin iyali a gidana". Ta kalle shi ta ce "Yi mini bayani yadda zan fahimce ka." Ya ce "Ban son a tare mini haihuwa. Idan kika duba yaran nan za ki ga ba wani tsira a tsakaninsu idan kika cire Amal da ta bawa Noor shekaru masu dan dama." Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:36] Ta yi shiru. A tausashe ya ce "Pls mana Maigado Ki yi magana." A nutse ta ce "Amma Baban Bilki da Sai ka fad'a mini tun kafin mu yi aure ". A sanyaye ya ce "A lokacin fa ba Sona kike ba yaushe ma zan tunkare ki da wannan maganar. Yanzu kuma sai nake ganin ko ba komai ba zan kasa samun alfarma a wajenki ba. Ina son yara. Ina son ya'ya da yawa. Ubangiji ya wadata ni da lafiya, ya yi mini arzikin da ban san adadinsa ba. Dan haka ba zan yarda a tare mini haihuwa babu dalili gamshasshe ba. Don Allah Maigado ki fahimce ni ". Kanta na kasa ta ce "To ai ni Baban Bilkisu idan ina goyo ina yin period ka ga kenan zan iya samun ciki da wuri. Saboda Allah yanzu idan na samu ciki na yi ya ya da waɗannan jariran?" Ya sake rik'eta ya ce "Zan kula da su da k'arfina, lokacina da kuma aljihuna. Zan sake dibar miki masu rainosu. Ga Alti kuma, ke fa nono kawai za ki dinga basu. Dan Allah Maigado ban son planning idan Allah ne bai kawo ba shikenan. Amma ban son a tare mini haihuwa tsakanina da Allah ". ,, To Baban Bilkisu zuwa yaushe zan gama kenan?" Ya yi shiru ya ce "yanzu 32 ku ke ko?" Ta zuba masa ido tana ganin da iyakacin gaskiyarsa yake tambayarta. Ta ce "Lallai ma Baban Bilkisu wato dai kallo yarinya ainun kake yi mini. To 38 zan n cike next month." Ya zare ido kai Maigado duka duka yaushe aka haife kune ke da Abida? Muna fa Rumfa college ne." Cikin son ya gane ta girma ta ce "Wallahi 38 zan yi , ko Ansari ma ai 36 yake bare mu". Ya jijjiga kai ya ce "Gaskiya shekaru na gudu." "To Idan ba ki tare ta ba. Na miki alak'awarin idan kika yi 43 kin gama haihuwa sai kawai mu ta cin duniyarmu da tsinke". Ta yi dariya. Ta ce Baban Bilkisu cin duniya fa da tsinke?" "To tunda na auri yarinya ai reviving ɗina zata dinga yi". Wani dad'i ya dinga ratsata ashe mijinka ya dinga maka kallon yarinta ba k'aramin alfarma ba ce. K'uruciya dad'i ne a gun miji da ya kere maka shekaru.🥰🥰 Allah ya k'arawa irin wadannan mazan lafiya a cigaba da lallaba mu. Muna godiya da niimar Ubangiji. 😄😄😄 Ya rungume ta ya ce "To me kika ce?" "A hankali ta ce "Allah ya bamu masu albarka ". Dad'i ya kama shi. Ya rungume ta sosai yana bata kisses ta ko ina. Cikin k'ank'anin lokaci suka yamutsa junansu. Daga nan aka shiga cin uwar sabada. Basu rabu ba sai azahar sannan suka yi wanka ya tafi masallaci, ya barta tana busar da gashinta. Haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Alti. Amma ba zuciyarta Kawai ba gangar jikinta ma na cikin farinciki da annushuwa. Mararta kuma ta yi mata sakau don a an zubar da ruwa iya ruwa. Da wani irin murmushi ta ce "Oh oh Baban Bilkisu duniya ne". Da kanta ta sanya hannuwanta ta rufe fuskarta don ita kad'ai ma kunya ce ta mamayeta da ta abubuwan da suka wakana a d'azu. Shi da kansa ya gane itama kuntatawa kanta ta yi da ta kaurace masa. A d'akin ya dawo ya sameta. Ya zauna bakin gado. Ya kalleta ta mayar da lingerie din. Ya murmusa ya ce "Maigado danja. Ashe sosai kika yi kewata?" Ta yi k'asa da kanta, tana murmushin kunya. Ya numfasa ya ce "Yunwa fa nake ji me zan ci ne?" Ta d'ago da fuskarta ta harari gefe daya tare da fad'in "Angela d'in bata nan ne?" Murya a tausashe ya ce "Ai mun shirya nasan za ki ba ni abin da zanci". Ta tura baki ta ce "Baban Bilkisu dama bana hanaka kawai don kana son musguna mini ne ya sanya kake bata order ta yi maka abin da zaka ci. Kuma Wallahi bana so". Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:37] Da azama ya ce"Ai kinsan a kwanakin nan ne kawai na yi hakan amma daga yanzu ba zan sake ba. Yanzu samo mini d'an wani abu na ci, kafin ki kammala mini abin da zanci. Amma ki fara zuwa ki shayar da yaran nan, na ji sun farka Alti na fama da su. Bansan me ya hana ni shiga na karbo su ba". Ta yi dariya ta ce "Kunya ce ai tasan abin da kake yi da ni tsawon lokacin nan da nake d'akinka. Ya yi murmushi tare da fad'in "Ina jin haka ne. Yi maza ki je ban son su rikice". Ta dora abayar ta fice ya bita da ido yana jin duk wani zullimi.da takurar da yake ciki sun warware masa. Yarinya k'ank'anuwa ta saka shi tashin hankali. Mata da tsiya suke Ga su da wuyar sha'ani, idan basu so na kai da gidanka na zaka samu nutsuwar zuciya a cikinsa ba. Ban da wuyar Zama ta ya ya abinci ma sai ana controlling d'insa. Abin da take son ya ci, Shi zata yi masa kuma dole su ci tare if not ya yi laifi. Ya numfasa yana tunanin lokacin Rukayya dai ya dawo yake bada order din abin da zai ci charity ta girko ta kawo masa. Tunda ta gane haka yake so bata sake tayar da hankalinta ba. Amma y'ar yarinyar nan ta ce ba haka za'a yi ba, kuma dolensa ya hak'ura yadda take so din yake yi. A fili ya ce "ikon Allah oga Asad a hannun Maigado". D'akin da ta cire rigarta nan ta sake shiga. Ta cire na jikinta ta mayar da na farkon. Sannan ta fito ta shiga dakinta. Ta tarar Alti na fama dasu. Ta goya baba K'arami tana rike da Baba Babba a hannunta. Da sauri Bilki ta karbi na hannunta tana fad'in "Sannu Alti. " Sai da ta gama basu. Ta kalli Alti ta ce "Bari na kaisu wajensa. Ki yi sallah sai na zo mu d'ora abinci". Alti ta ce "To". Ta fita zuwa d'akinta da kuzari don tunda ta ga Bilki na b'are b'are tasan an shirya sannan walwalarta ta dawo babu k'unci da share k'walla akai akai. Ja'ira itama ta ji jiki". Alti ta fad'a a ranta. Ta hadesu a babban shawul ta ciccibesu ta yi samansa. Yana ganinta ya zabura ya mike daga kwanciyar da ya yi. Ya tare ta jikinsa har rawa take yi. Ya ce "A a wannan ganganci ne Maigado. One by one za'a dinga kawo su, ko ki dinga cewa na zo na d'auke su da kaina. Yayarsu bata nan ne da ba ki ce ta ɗauko daya ba?' Baban Bilki tunda ta fara service fa sai yamma take gida ai". Kuma su Hafcy kowa na makaranta." Ya kwantar da su yana duba jikinsu ko an matse su. Har ta juya ya ce "Wai me zan ci ne Maigado?" Ta dawo ta bude k'aramin firij din da yake cikin dakin. Ta d'auko fresh milk ta bude ta dauko tumbler ta cika masa ya karɓa ya kwankwade. Ta rufe ta mayar. Ta d'auko inibi ta fita zuwa k'aramin kicin d'insa ta wanke ta zubo a bowl ta kawo masa gabansa. "Na gode sarauniyar shaiba". Ya fad'a yana kallonta. Ta ce "Zan je na yi girki". "To a yi lafiya a gama lafiya". Ta duka ya sumbace shi kad'an. Ta juya ta tafi ba tare da kalle shi ba. Ya sake binta da ido. Shi kam ana masa k'arfin hali. Angela ba zata yi girki ba indai zai dawo gida ya yi lunch. Breakfast din yara da wanda suke tafiya da shi school kawai ne aikin angela na dole. Idan ba haka ba, sai ta ga dama take yarda ta yi girki a gidan. Sai idan za'a yi bak'i da yawa ko idan za'a kai masa office da yawa. Shine zata yarda ta yi wasu daga cikin abincin da za'a kai tunda kala kaala ake yi musu. A fili ya ce "Ban da dai na yi laushi ya za'a dinga mulkata irin haka? Kuma an hutar da ke amma don fitina ba zaki huta ba? Allah sarki Rukayya, Allah ya yi miki rahama ". Ya fad'a a sanyaye don ita a haka ta rayu. Komai yake so bata da y'ancin yi masa musu matuƙar abin kaitsaye shi ya shafa. Ya sa ni a bayan idonsa tana yin abubuwan da ta ga dama. Amma ko kad'an bata samu damar da Bilki ta samu a wajensa ba. Faricincikinsa d'aya ma yadda bai yi mata iyaka da kuɗinsa ba. Ta yi facaka da kud'i son ranta. Ya dawo sallar la'asar sannan ta gabatar masa da abinci. Ya sauko tare da ita suke ci. Yana ci yana yaba dad'in abincin. Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:39] Tabbas ya gamsu ta iya sarrafa girki daga ita har altin tata. Ranar haka bai fita ba. A gida Aysha ta dawo ta same shi. Haka ma sauran yaran. Ya zauna cikinsu suka dinga hira kowacce na fad'a masa abin da take so ya siya mata. Shi kuma ya amince zai siyawa kowa abin take so. Gida ya kacame da murna tunda cewa ya yi ma su shirya after Isha za'a fita shopping da kansa kuma zai tukasu. Idan ya fita da su da kansa suna jin dad'i don komai suka dauka baya iya hanasu sabanin idan su kad'ai ne account mai takaitaccen kudi yake basu damar tabawa. Ya kalli Bilki da ta bishi sama ya ce "Da ke zamu je ne ko sai daga baya zan kai ki?" Dan ya ji dad'i sai ta ce "A a zan biku na tayasu zabe kada yaran su debo abubuwan da ba wani amfanarsu zasu yi ba". Dad'i ya kama shi ya ce "yauwa Sarauniyar sheba dama nafi son na tafi da iyalina gabad'aya". Aysha da Hafcy suka hawo saman Bilki suka d'auki jariran suka fara ficewa. Farha ta kalli Alti ta ce "To me kike so na siyo miki?" Dad'i ya kama Alti don Farha na nunawa irin ita ce tata tunda tare suka zo gidan. Ta ce "Ki siyo mini Rufaida da kulikulin Ummiel ". Farha ta ce"To nasan Dady ma zai siyowa su Momi da Baba". Bilki na d'akin oga tana tsaye ya gama shiryawa. Tuni ta shirya cikin tsadaddiyar Yasmin abaya. Ya kalle ta ya ce "Dr Sulaiman fa ya ce ya kamata ki ga likita". Ta ce "Baban Bilkisu k'alauna fa Wallahi. Tsabagen kuttun da kake nausa mini ne ya nemi zautar da ni. Yau kad'ai duk wanda ya ganni ya ga real Bilki ba wacce aka share ake kuma nuna mata wata mace ta fita ba! Mamaki ya kama shi. Ya yi maza ya isa kusa da ita ya ce "Ba a fiki ba, ba kuma za'a fiki ba sarauniyar sheba. " PAGE 20 A yammacin wannan ranar Abida a falon baba na ciki. Kusa da Baban tske zaune tana nuna masa videon yadda ya wakana tsakanin.oga Asad da Dr Sulaiman. Dad'i ya kama shi k'warai da gaske. Da kuzari ya ce "Amma shine ba ki nuna mini wannan abin farincikin ba sai yanzu?" "Baba da muka dawo ka shiga ciki. Yau kuma sassafe na fita zuwa asibiti. D'azun nan na shigo ". Murna kan murna yake yi tamkar an zauna an yi sulhu komai ya wuce a tsakaninsu. Addu'ar fatan alheri ga oga Asad da Dr Sulaiman ya yi musu ba adadi. Motsi kad'an zai ce "Sake kunna mini na ga gaisuwar mai d'amara da civilian ". Abida aka dinga kunna amsa ba gajiya. Suna cikin haka ta ce "Baba dai har yanzu baka huce da ni ba. Kana ta yiwa Dady da Yaya Sule addu'ar tsari daga abin k'i da kuma albarkar rayuwa amma ni da na yi maka wannan vedion da ya sanyaka farincikin da kake ciki baka yi mini addu'ar ba." Ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki albarka Abidan Baba, Allah ya shirya miki zuri'a." Dad'i ya kamata don rabon da ya ce Abidansa ta mance. A sanyaye ta ce "Ameen Baba. Ya nisa ya ce "Dazu Sulaiman ya ce mini jibi ko gata zai tafi Kano. Zai yi aikin ido a asibitin Makka na cikin Kano . Wanda wata gidauniyar tallafawa k'asashe masu tasowa ta Saudiiya take d'aukar nauyi. Ya ce sati biyu zai yi ya dawo." Jikin Abida ya yi sanyi. Ta fara kukan da ya tayar da hankalin tsohonta. A sanyaye ya ce " menene na kukan kuma?" Tsawon lokaci ta kasa magana. Sai kuka take yi k'asa k'asa amma mai nauyi ainun. Jikin Baba ya yi sanyi. A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri Abida. Ki yi addu'a komai zai wuce tamkar ba'a yi ba". Da kuka sosai ta ce "Baba na yi hak'uri, na yi addu'a. Da kanka ka fad'a mini Yaya Sule yafi k'arfina. Yanzu da ya dawo ai sai ka taya ni. Nauyinka zai saka ya hak'ura. Kuma Wallahi Baba da ace Bilki ce a gida, Dady ya ce zai yi tafiya cewa zaka yi ya tafi da matarsa, ni nasan hakan zaka yi masa ko ba ya so, sai ya tafi da ita duk laifinta zai zama ka roka mata afuwa. Amma ni dukkanku ana kallo zai tafi ya bar ni, ana kallon bai yi wani motsin sama mini inda zan zauna ba. Duk tsawon lokacin da ya rataye ni amma ya dawo da niyyar cigaba da rataye ni. Kuma ba wanda ya yi ko da tari ne a cikinku" Ta rushe da kuka wiwi har Momi da take kicin ta fito a sukwane. Cikin kuka sosai Abida take fad'in "Baba ka shiga tsakanina da shi. Ka ba shi umarnin ya dauki iyalinsa ka gaji da rik'e masa. Ka yiwa Allah ka tursasa shi yadda ka ke tirsasa Dady da Yaya Usman. Wallahi na gaji. Ba wani aikin ido da zai je yi. Gidan iyayen yarinyar da yake nema zai je. Daliba ce a Saudiyya suka hadu. Yanzu da na dawo, wajensa na fara shiga, na tarar yana band'aki. Na ga wayarsa na dauka akan na k'ira lambata don na samu layinsa sai kawai na ga hirarsu. Wallahi Baba ce wa ta yi ya je ya gaida iyayenta daga nan sai ya tura manyansa". Murya a dakushe Baba ya ce "Nutsu ki saurare ni." Tsawon mintina biyu yana kallonta tana kuka mai dauke da nauyayyen gunji. Tausayinta ya daskarar da su hatta Momi idanuwanta sun cika da k'walla. Yadda ba ya nan nan da junior kad'ai ya sanya sun gane Sulaiman ya yi nisa bai zo da niyyar sulhu tsakaninsa da ita ba. Yaron kansa jikinsa ya yi sanyi baya wani d'okin ya je wajensa. Baba ya numfasa ya ce "Ki kwantar da hankalinki Abida. Kada ki mayar da duba wayar namiji dabi'arki. Yanzu ga shi kin ganowa kanki abin da zai hanaki sukuni. Abu d'aya ne ya sanya na Zan iya tursasa Sulaiman akan Ki ba saboda Ni na haife ki. Anan falon a inda kike Bilki ta fad'a mini na zuba miki ido ban mayar da ke d'akinki ba saboda Sulaiman ba Shi da wata alfarma. Kuma Wallahi a bakinsa ta ji wannan kalaman. Yanzu ta ina zan fara cewa ya d'auke Ki, alhalin a lokacin da ya kamata na ce ki kma din ban yi iko da ke kin yarda ba. Duk yadda zan mayar da Sulaiman ya zama dana ai Dai ke ce na haifa. Da ace ba ni na haife ki ba to da na gwada masa kwamjina amma a yanzu da ya tafi a fahimtar mun zuba miki ido kin bijirewa zama da shi alhalin bai yi miki komai ba, bai kuma sake ki ba , kin ga ai ni ba ni da bakin magana. Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:02] Kuma ma menene abin damuwa dan zai k'ara aure? Ina ce ko zaune kuke k'alau zai iya k'ara aure tunda an halasta masa. Kanta na kasa hawaye na tsere bi da bi. Wani irin cunkushewa mak'oshinta ya yi. Ga k'irjinta ya yi nauyi tamkar an d'ora gingimemen dutse. Wato dai da gaske Sulaiman sai ya nukurkusa da bak'in cikinsa. Ta dinga jin ya kamata ta tsayawa kanta. Ta yi laifi, ta karbi laifin, ta bada hak'uri, ta janye amma duk bai kalli nadamarta da bibikonsa da take yi ba. Tunda aure yake nema zata hak'ura don kuwa ko shine dagi wajen fad'a ba zai yi aure ita tana zaune a gidan ubanta bata san matsayinta ba. Tunda bai ga nadamarta ba bari Kawai ta ɗauko rigarta ta mayar. Zata koma Abidan Baba ta da, ba Abidan yanzu da ruwa ya daki babban zakara ba. Daidai lokacin suka jiyo shi a falon farko yana kwada sallama a sukwane. Momi ta mike tana fad'in "Sulaiman ga mu a nan". Da hanzari ya shigo yana fad'in "Ina Baba?" Ganin Baba ga Abida durk'ushe kanta na k'asa ya sanya tsugunnawa. A diririce ya ce "Baba ka ce mata ta bani kayayyakina da ta kwashe mini. Tun ranar muka dawo ban ga passport dina ba. Dazu da safe ta shiga ina barci ta kwashe mini duka ATM dina. Yanzu kuma ta dauke mini wayata guda daya da ledar takalmana." Baba ya yi shiru k'walla na cika masa ido don kuwa Baba k'arami ne yake masa yawo a zuciyarsa. Shine yake yi musu Sharia tun suna yara. Sai idan Sulaiman bai gamsu da hukuncin Baba k'arami ba sai ya zarto ya kawo masa kara tare da gabatar da hujjar Abida na kwashe masa kayayyakinsa tana boyewa saboda Baba k'arami yana bata kariyar tunda bai ga lokacin da ta dauka ba to kuwa ba ita ba ce, alhalin ita ce ba kowa ba. Shi kuma Baba Babba idan ya lallabata tare da yi mata kyautar talotalo ko dawisu ko tattabara sai ta je ta fito masa da abin da ta boye. Mussaman takalmi haka siddan idan ta ga takalminsa a bakin k'ofa sai ta kwashe ko ta d'auke kafa daya ta bar masa d'aya. Bisa hujjar yana ce mata bak'a mummuna, ko Abida kwaila mai gwalli. Baba ya numfasa tsawon lokaci ya kass magana. A dabarance ya goge k'wallar idonsa wanda Sulaiman ya ga ni. Jikinsa ya yi sanyi, zuciyarsa ta karye da tausayin Baban nasu. Ya kalli Abida ya tabbatar kuka take yi. A ransa tamkar ya rufe ta da dukan da zata yi kukan gaskiya. Har yanzu ba zata bar Baba ya huta ba. Ta zo ta tisa shi a gaba tana kukan munafurci ga shi shima har ya fara. Ya kuma san bincike ta yi masa a wayarsa shine ta ga abin da ya dameta. A ransa ya ce "Ki adana kukanki zuwa gaba yarinya. Baba ya yi k'arfin halin cewa "Je ki d'auko mini kayansa " Murya ba amo ta ce "Ni ban d'auke masa ba fa. Akan me zai dinga k'ala mini sata. Tun ina karama yake mini sharrin na yi mass sata kafatalin gidan nan Abida ce barauniyarsa akan me zai dinga keta mini haddi irin haka?" Ta kece da kukan da dama bata gama yinsa ba tunda kishine ke yagalgalata. Sulaiman ya yi mata k'uri yana kallon ikon Allah. Har cikin zuciyarsa yake jin kukanta. Ya masa magana don gabad'aya ya zama speechless. Ba wani kuzari ya ce "Wallahi ke kika d'auka ba mai shiga d'akin ya taba mini kayana sai ke, ko danki ba zai je ya zabe abubuwana masu muhimmanci ya bar ni da tarkace ba, babu mai yin wannan TA'ADAr sai ke." Baba ya kaurara murya ya ce "Tashi ki dauko mini kayansa Abida ". Yadda Baba ya yi magana cikin sigar umarni ya sanya ta tashi ta nufi d'akinta. Jimawa kad'an ta dawo da wayarsa da ATM. Ta mik'a masa ya karɓa ya ce "Saura passport". Nan da nan ta ce "Wannan kuma ban dauka ba. Ban san inda yake ba, ka dai duba a cikin kayanka". Da hanzari ya ce "Wallahi kin dauka yana hannunki ko kaffara ba zan yi ba akan haka." Baba ya ce ",Je ki kawo mini." Ta fara kuka tare da cin layar bata d'auka ba iyakacin abin da ta d'auka ta fito masa da kayansa. Juyin duniya ta k'i ta yarda ma ta dauka bare ta bayar. Baba ya ce "To ku je ta duba maka a nutse". Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:05] Abida ta yi maza ta mike tare da fad'in "To Baba" . Yayin da Sulaiman ya ce "Baba baya dakin nan Wallahi. Tunda ta je yi mini shara ta d'auke kuma tun a ranar sai da na faɗa maka." Baba ya ce "yanzu dai tashi ka je ku duba cikin nutsuwa ba da tashin hankali ba." Tuni Abida ta fice. Kan dole Sulaiman ya tashi ya bi bayanta amma ya riga yasan yana hannunta ba ganinsa za'a yi ba tunda ta fice da shi tun tuni. Yana shiga dakin kawai ya ganta a tube ta cire doguwar rigar jikinta ta wurgar kan kujera. Daga ita sai gajeran wando skin tight iya guiwarta sai half best. Ko brexiya bata saka ba tunda kananun nono gareta da suke a makale basu zube ba. Don haka bata cika saka bra ba Sai ta yi nishadi. Ya yi turus zuciyarsa ya buga. Ganin shatin nipples a cikin farar half best dinta da ta kamata. Ya dan diririce. Murya ba amo ya ce "Ke ban son shakiyanci fito mini da abubuwana kin ji." Gabad'aya ta tunkare shi ta ce "Caje ni, laluba ko a jikina na boye tunda baka gasgata ni ba. Kaitsaye ta rik'o hannuwansa akan ya laluba ko zai ga ni a jikinta. Gabad'aya jikinsa ya dauki mazari. Ya yi maza ya tsalla gefe. Da haki ya ce "Abida you are trying me fa". Kallonsa kawai ta gane sakonta ya bige shi. Ta daure fuska ta yi juyi tana fad'in "A a to indai ba a cikina na boye ba ina zan ajiye?" Ya zagaye ta ya zauna a bakin gado daga k'arshe ya juya mata baya Yana kallon window. Ta jijjiga kai tasan ba k'aramin jarumta ya yi da bai kai hannunsa kan nipples dinta ba mussaman da suka fito sosai irin yadda yake son ya gansu, alamun tsosto suke so. Ganin ta birkita shi Sai kawai ta d'auki rigarta ta sanya. Ta isa kusa da shi. Ba wani Dogon turanci Kawai ta zube a gabansa. Murya cike da rauni ta ce "Yaya Sule Ga ni na durkusa on my kneel ka karya mini Duk wata fiffika to ka yafe mini haka nan mussaman ma da ya kasance sharrin marab'ai na hadu da su. Amma Duk da haka na yarda na bata maka, ka yi hakuri." Daidai lokacin wayarta ta hau kuwwa. Tana durk'ushen ta d'auka ganin sunan Dady ne. Ta dauka. Tun kafin ya amsa gaisuwar da take yi masa ya ce "Ki kaiwa Sulaiman wayar". "Ga Shi ma". Ta mik'a masa. Ya karɓa yana fad'in wanene ne?" Yana jin muryar oga Asad ya daidaita ya ce "Yaya barka da yammaci ". "Yauwa Dama zan tambaye ka zaka zo me ko kuwa ita ta zo gobe?" "A a zan zo in sha Allah wajen 2 haka". "To shikenan sai ka zo". Ya kalli Bilki da take kallonsa.ya ce "Ya ce zai zo". "Tom shikenan Allah ya kaimu". Sulaiman ya mik'awa Abida wayarta. Ta karba ta had'a da hannunsa ta rik'e. Ta marairaice ta ce "Ka yafe mini Yaya Sulena?" Ya harareta ya ce "Ai na ga alamun da isgi6ma kike bani hak'uri. Yaya Sule, Yaya Sule tamkar kina son na ji baush6ne tunda ai idan kin so yi mini Ta'adi me kike fad'in Sule." Ta yi maza ya ce Dr yaya Sulaiman, mijin Abidan Baba, Baban junior. Allah ya taya ni baka hak'uri. Allah na son mai afuwa ka yafewa k'anwarka masoyiyarka. Ni fa Sai yanzu na gane ashe tun da can ma Yaya Sule kwamushe zuciyar Abida ya yi shiyasa take ganin sauran maza a ragwage ashe dr take Kira. Shiyasa yana tayawa Kara karbe shi babu gardama. Wataƙila fa da ka yi nauyin baki na rigaka furtawa tsabagen ka tafi da ni. ". Bai san sadda gajeriyar dariya ta k'wace masa ba tare da fad'in "Da dai ba Abida ce ba". Itama ta murmusa ta ce "Da gaske fa Baban junior ka ga yadda ka hadu ne? Ga ka dogo wankan tarwada ga hanci ga ka namiji a tsaye. Ga ilimin addini ga na zamani. Ga hak'uri da yafiya, ga girmama iyaye, ga son y'anuwa, ga adalci ga iyalinsa. Idan harkar odafare ne ba sauki sai an k'ure Abida. Ya ya kuwa ba zan mace a kanka ba Dr Baban junior?" Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:10] "Ya mike tare da fad'in "Allah ya shirye ki". Itama ta mike tare da bude masa dukkan hannuwanta alamun ya zo ta rungume shi. Shi gabad'aya sai ya ga tamkar da jinnun a tare da ita da gaske. Ta ce "Zo mana tunda dai mun shirya ka kuma gane sharrin jinnu ne masu son ganin bayan aurena". Hawaye ya k'wace mata. K'warai da gaske ta kife shi. Yaa rasa mai zai ce don kuwa tsakaninsa da Allah ta kunna shi tunda ta yi masa sanadin ganin k'ananun kirjinta da suke motsa shi. Ya yi jarumtar cewa "Yanzu za ki ba ni passport din, ko ba za ki ba ni ba?" Ta zuba masa ido, yayin da shima ya zuba masa nasa idanuwan. Tsawon dakika goma suna kallon junansu. Sulaiman ya gama gamsuwa Yana son Abida har yanzu. Shi ya fara janyewa daga kallon. Ita kuma cikin rashin kuzari ta ce "Ba zan baka ba, don kuwa ina da hak'kin kulawa da tarbiyarka. Ba zai yiwu na yi sakacin da zaka sake tserewa ba. Ko ina zaka tafi, kafata kafarka matuƙar da aurenka a kaina". Da mamkin kulawa da tarbiyarsa da ta ce. Ya ce "To kuma idan babu auren fa?" Zuciyarta ta harba ta ce "Ai nasan zaka yafe mini, ba zai yiwu na yi zaman jiranka a banza ba". "A takaice ya ce "ai kuwa kin yi ma". Nan da nan ta hauro. Ta ce "Yaya Sulaiman tsakanina da Allah Ina son ka yi hakura ka yafe mini, na fi son ka huce, ina son ka hak'ura Allah me shaidar Hakan. Amma fa gaskiyar magana na fara gajiya, don laifin nan ba da gayya na yi ba. Sharrin jinnul Ashiq ne amma ka cije ka kafe gaskiya kuma na fara kaiwa gejin rarrashinka ya ya haka ne?" Ya hassala ya ce"Abida ki fa bini hankali, ki fa shiga taitayinki." Idonta akan fuskarsa ta ce "Har a sannu na bika, yanzu muka a guje zan n bika don Wallahi na gaji. Ina da bukata mahaifata na buk'atar jin ruwa na gaji ko ka zuba mini, ko ka raba ni da zaman zullimi haba dan Allah shekaru hud'u ai ba watanni ba ne." Ya girgiza kai ya nuna mata k'ofar fita tare da fad'in "out". Ta rausayar da kai ta ce "Yaya Sulaiman tsakanina fa da Allah na gaji. Ko dai ka yi hak'uri ka yafe mini, ko ka gajarce mini zullimin da nake ciki akanka. Fito kawai ka fad'a mini makomata." Ya sake girgiza kai ya damko hannunta ya ce "na damka miki damar aurenki a hannunki, idan kin so ki rike, idan kin ga hagu ki tankwabar da shi. Ta yi maza ta fizge hannunta ta damke hannuwanta da kyau. Murya na rawa ta ce "Na damke shi da kyau." Hawaye ya k'wace mata. Ta ce "A ina zan zauna ina son komawa gidana". Kaitsaye ya ce "Ban da shi a yanzu". Daga haka ta ce "Ya yi kyau na gode sai anjima." *DINGISHIN KWAD'O 4* *BY* *SURAYYA DEE* PAGE 21 Cikin gaggawa ta fice ta bar masa d'akin tare da kudirin ba zata sake nemansa ko ba shi hak'uri ba. Ta yi iya yinta ta jure komai. Ta ba na shi hak'uri irim hak'urin da bata yi zaton zata bawa namiji irinsa ba. Don haka enough is enough ba zata sake bibiyarsa ba zata kame. Yayin da ya bita da ido, tare da ayyana ta yi fishi don ya ga yanayinta ya fita daga yanayin salamar da ta aro ta tafawa kanta tunda suka yi arba. Gabad'aya sai yake jin wata irin damuwa ta yi masa k'awanya tunda ga k'asan zuciyarsa. Kaitsaye ɗakinta ta shiga ta dinga kuka tamkar hawayenta zasu kafe. Ita kam ta gaji ba zata sake zuwa yana disgata ba. Idan Allah yasa an daidaita haka take so. Idan kuma ya gama yanke shawarar ba zai sake zama da ita ba, Kawai ya fito ya furta ya sahale masa idan ya so ya biyata basukan da take binsa ta cigaba da aikinta da addu'ar ta samu nutsuwar zuciya. Junior ya yi lakwas Yana kallon tana kuka wiwi. Murya ba amo ya ce "Ammi Ki Daina kuka. Ba kin ce Idan Dadyna ya dawo ba zamu dinga kuka ba, ba zamu dinga zama a d'aki ba?" Ta kasa bashi amsa a dalilin haka ta dinga fad'a masa a lokutan baya kafin bayyanar Sulaiman. Ga shi ya dawo kukanta na na neman ya zarta sadda ba'a gan shi ba. Gabad'aya ya taurare ya murd'e ya k'i barin komai ya wuce a tsakaninsu. Cikin Kuka ta ce "Ya k'i ya dauke mu, mu tafi gidanmu junior " Ya ce "To zan je na tambaye shi" Ta kasa cewa komai. "Ammi na je?" "Je ka". Ya sauka da gudu ya fice zuwa d'akin babansa. A bakin k'ofar ya tsaya ya dinga bugun. Dr Sulaiman cikin kasala ya ce " shigo". Junior ya shiga. Ya tsaya ya ce "Ammi na kuka, zamu tafi gidanmu". Sulaiman ya mike ya isa kusa da yaron ya d'auke shi ya daga sama. Ya zauna bakin bada ya rungume Shi a jikinsa. Yaron ya dinga sakin ajiyar zuciya. Haka kawai tausayi mai tsananin gaske ya shake Sulaiman jin yaro na ta sakin ajiyar zuciya jikinsa. Jini ba k'arya ba ne. Ya shafa kansa ya ce "Sulaiman". Junior ya kalle shi ya ce "Ammi fa ta hana su Farha da Noor ce mini Sulaiman ta ce sunan babana ne". Sulaiman ya murmusa ya ce "Ta ce " maka sunan dadynka Sulaiman" Kai junior ya daga masa. Ya ce "ka ce qwa Ammi ta daina kuka idan na dawo daga Kano zan d'auke ku mu tafi gidanmu ". Junior ya fara tafin murna ya ce "Zaka saka ni a school din su Farha" Sulaiman ya girgiza kai ya ce "Dadynsu mai kudi ne kai kuma dadynka mai allura ne. Zan saka ka a wacce zan iya idan muka tafi garinmu". Junior ya yi shiru ya ce "Ina ne garinmu?" Har Sulaiman zai ce Funtua sai ya yi maza ya ce Katsina ". "Ya ce "to yaushe zamu tafi?" Sulaiman ya dinga mamakin surutun dan yaron. Ya numfasa ya ce "Idan na dawo daga Kano". Ya mik'a masa hannu ya ce "promise?" Dariya ta kubucewar Sulaiman ya ce "promise". Suka k'ulla alk'awari. Yaron ya juya a guje don ya faɗawa uwarsa zasu koma gidansu ta daina kuka. Ya je ya fad'a kuwa. Ta daure ta daina kuka amma ta yanke shawarar ba zata kuma bibiyarsa ba. Za ta dinga addu'a tare da buga masa wuridin da zai kasa shareta. Amma ta gaji da yadda yake wulakantata. *** Washegari sassafe ya dawo daga motsa jiki ita kuma zata tafi asibiti suka hadu a harabar gate din. Fuskarta ba walwala ta ce Yaya Sulaiman ina kwana?" Daga haka ta shige motarta bata jira komai ba. Hakan ya bata masa rai ya sanya shi jimami. Ya kud'ire kuwa zasu zuba ne don ba zai sauko ya bita ba. K'arfe Uku Yana gidan Bilki. Suna zaune kan daining suna yin lunch daga shi sai ita. Alti na can da tagwaye, yaran kuma duka basa nan. Hira sosai suke yi. Ya bata labarin ibtilain da ya shiga bayan tafiyarsa. Sannan ya bata labarin irin kuɗaden da ya samu a yanzu. Ta jinjina kai ta tausaya masa. Ta yi masa jaje ta kammala da murnar ya zama kasurgumin attajiri. Ya nisa ya ce "Ina son na yi aure Bilki. Yarinyar yar Kano ce amma tana karatu a Jeddah." Kuka kawai Bilki ta rusa tana fad'i "Ka yiwa Allah Yaya Sulaiman kada ka yiwa Abida haka. Ta sha wahalar rashin ka. Laifinta bai kai haka ba dan Allah." Ya yi shiru yana jin ba zai iya faɗa mata abin da ta yi masa ba ko da kuwa bata roke shi arzikin kada ya fad'a musu ba. Cikin kuka ta sake fad'in "Baba ba zai ji dad'i ba. Dan Allah ka yi hakuri a shirya haka nan. Lokacin aurena da maigidan nan irin murnar da Baba ya yi sai da ya bani tausayi Wallahi yana son a shirya, ka ga mune k'ananu kuma shine uba mu kuma y'aya'." Sulaiman ya ce "Wallahi kuwa matuƙar yana Abuja ba za'a shirya gabad'aya ba. Sai ya yadda na d'auke shi na mayar da shi Funtua ta yadda kowa zai shiga gidan kansa tsaye. Sai ya yarda na mayar da shi inda duk zamu zama ya'yansa kamar yadda Yaya Asad ya dauko shi ya dawo da shi nan. Matuƙar yana Abuja to shi da iyalinsa ne kad'ai. Mu bamu da inda zamu fake." Ya fad'a idanuwansa sun kada. Jikin Bilki ya yi sanyi lallai akwai sauran rikici. Ya kalle ta ya ce "Ya ya aka yi aurenki da Yaya Asad?" Ta ba Shi labarin komai, har hard aurenta da Sahal ya k'are Cikin tashin hankali ya ce "Da Baba na Funtua Sahal bai isa ya yi miki gorin ba ki da inda za ki je ba. Anisa ta yi rikici daijinta Sai jiya ta koma gidanta. Maiduguri ta tafi wajen Ansari. Hawaye ya k'wace masa tamkar mace. Ya girgiza kai ya ce "Yanzun kina sonsa ko kuwa?" Ba noke noke ta ce "Ina sonsa, ina son zama da shi". A fili ya ce "Ila yaumil kiyamati ma huce da shi, rikicina da shi ya k'are. Amma fa batun a shirya a hade tamkar da sai an yarda na yi iko da Baba kamar yadda maigidan nan ya yi. Ya matsa da kujerarsa kusa da tata kujerar. Ya rike hannunta. Ya ce "Bilkina akwai yiyuwar rikici zai sake barkewa amma duk juyin da za'a yi kada ki shiga. Tun filazal ke a wajen Baba Babba kika girma. Yana sonki, yana ganin mutuncinki, ki yi kokarin tabbatar da wannan soyayyar. Mu da muke da laifi kan laifi barmu mu yi rikicin. Ki bi mijinki. Ba zan iya yi miki abin da yake yi miki ba. Ya fini iko akan ki ". Da rawar murya ta ce "Wallahi idan ban bi bayanka ba Yaya Hamida da Ansari da Anisa sake kullata zasu yi". Hawaye ya k'wace mata. Ya zari tissue ya ce "Zan wanke ki da kaina. Zan musu bayanin ni na baki umarnin yin hakan. Duk basu da hankali ne. Kubucewar oga Asad a hannunki ba k'aramin asara zamu tafka ba. Idan yana hannunki mun ringa mun zargo su gabad'ayansu dole su karbi dukkan uzzirn da zamu gabatar musu. Ga wacccar zakwakurar tasu ta yi laushi.". "Amma Yaya Sulaiman ka bar batun karin auren nan dan Allah ". Bilki ta fad'a cikin firgicin don sosia ta ji tana taya Abida kishi na ban mamaki. "Aure zan k'ara tabbas, don Wallahi ba dan na tarar kin zama matar Yaya Asad ba, da sakinta zan yi. Amma yanzu na yi imanin idan na sake ta komai zai sake cakalkalewa ne, mafi tayar da hankalina rasa aurenki ko rashin samun nutsuwa cikin auren ki. Don tabbas Oga Asad sai ya yi mini gayya ko bai sake ba to kuwa zaman naku ba zai yi wani armashi ba. Don haka zan yi hak'uri don aurenki ya tsira, na kuma gama lissafina aurenki da shi babbar nasara ce wajenmu, aurena da Abida kuma shine makullin rufe dukkan sabani." Bilki ta numfasa ta ce "Gaskiya Yaya Sulaiman bana son ka ƙara aure, ba zan so wata matar ka ba alhalin ina ina ganin Abida". Sulaiman ya nisa ya ce "Bilkina wato saboda Abida sai ba zaki yiwa iyalina adalci ba. Wannan ai son kai ne Matsayinta daban, matsayin abida daban, ko ba zaki so ya ba, to ki yi mata adalci. Yarinyar tana da kirki ba sakaliya ba ce, ba ta kuma da girman kai". Wani irin Malolo ya tokarewa Bilki. Murya na amo ta ce "kai ta zo wa a hakan. Amma baka da tabbas akan badinin halayyarta ". "A a Bilkina da gaske tana da kirki kuma yarinyace akanku ba zata fi Anisa ba fa ". Ta kasa jurewa kawai sai ta kece da kuka wiwi". Don kuwa a yanzu ta fahimci alfarmar k'uruciya, wato wacce tafi Abida k'uruciya sosai zai kwaso musu? Jikin Sulaiman ya yi sanyi don kuwa kishi muraran ne ya bayyana a dukkan gangar jikinta da k'wayar idanuwanta. A tausashe ya ce "Ashe duk wa"azin da jan kunnenku da ake ta yi akan ku sassauta kishi ji kawai kuke yi, yana wucewa ta bayan kunnuwanku! Irin wannan tashin hankalin da kika shiga to idan Yaya Asad ne zai k'ara auren ya ya kenan?" Ga mamakinsa sai ji ya yi ta daddage ta zunduma ihu da iyakacin k'arfinta." Daidai lokacin oga Asad ya shigo a sukwane. Ya dawo d'aukar wani file, ganin juyawa zai yi sai ya saka aka yi parking a waje bai shigo da mota ba. Jin ihun Bilki ya sanya ya shigo a sukwane a zatonsa ta hadu da wani ibtilain ne wala na gas ko zamowa daga k'afar bene. Ganinta zaune ga Sulaiman ya sanya cikin kid'ima ya ce "Menene Maigado, wa ye ya rasu?" Da kuka ta ce "Wai ashe aure zaka yi?" Da hanzari ya ce "in ji uban wa?" Ta kasa magana illah kallon Sulaiman. Oga Asad ya kalli Sulaiman ya ce "oooh wooh wato zuwa ka yi ka haddasa mini rikici ka tayar mini da hankali ko?" Sulaiman ya kasa magana a dalilin ya ga oga Asad ya shiga yanayin da yake dealing da su". A sanyaye ya ce "Wallahi misali kawia na yi mata". "To akan me zaka yi misali da ni? Ka yi mata misali da kanka ko da Usman mana, ni sa'anka ne?" Sulaiman ya yi k'asa da kansa cikin tsananin tu'ajibin Bilki da oga Asad. Yana mamakin Bilki ne yadda ta k'ulla masa karya yana zaune akan idonsa. Yana kuma mamakin oga Asad na yadda ya birkice tare da k'ok'arin gamsar da Bilki bai san maganar ba, shi ba zai k'ara aure ba, to mai ma zai yi da wata macen? Sulaiman cikin tsananin mamaki yake kallon yadda shi kuma ake yi masa muzurai, ita kuma ana rarrashinta cikin rawar jiki tamkar su Farha. Ya tsinci kansa da tambayar shi da oga Asad wa ya fi wani gudun zuciyar matarsa ne? Don kafin su bata da Abida haka take yi masa sangarta iri iri yana rarrashinta cikin rawar jiki". Bilki da Abida ja'iran yara ne na k'arshe. Ashe ba shi kad'ai ba ne yake zullimin a yi masa fishi. Son girma irin na Yaya Asad amma an saka shi yin b'are b'are a gabansa. Sai da ya ga walwalarta sannan ya koma office bayan ya jawa Sulaiman kunnen kada ya kuma saka ta kuka. Yana tafiya Sulaiman ya kalleta ya ce "Bilkina yaushe kika zama kwalba ne irin hak?" Da murmushi ta ce "So nake ka fahimci ita yarinyar da kake ta kwarzantata iya zahirinta ka sa ni, sanin badininta zai yi maka wuya don ga shi nima da ka rayu da ni na ankarar da kai baka gama gane ni ba, bare wata can. Ka bar batun karin aure ka fuskanci iyalinka. Abida ta yi kukan rashin ka, ta yi nadama mai yawa, dan Allah let gone be by gone." Ya nisa ya ce "Ki taya ni addu'ar zabin alheri. Yarinyar ta shiga raina haka take doguwa yar shawalwala bak'a tamkar dai Abidanki". Bilki ta cuna baki gaba bata ce komai ba. Ya mike yana fad'in "Gobe in sha Allah zan tafi Kano". Itama ta mike tana fad'in "Sai yaushe zaka dawo?" Ya yi shiru yana nazari. Can ya ce "Nan da sati uku ko wata daya don zan je Katsina. Ba kuma zan dawo na sai da su Hamida". Farinciki ya bayyana a fuskarta don tasan Yaya Hamida dolenta ta biyo Yaya Sulaiman ko ya yi mata tozarci a gaban mijinta. Bai tafi ba sai da aka kawo masa twins ya gansu. Ba yadda Bilki bata yi akan ya tsaya yara su dawo amma ya k'i. Ta murmusa tana jinjina kawaicinsa akan Farha. Farha ga ni take yi Sahal ne Babanta. Don yadda take ji da leshin da ya aiko mata wanda tare da Amra ya dinka musu da sallah kamar me. Idan har zata yi kwalliya duk tsadaddun kayanta sai ta ce leshin da dadinsu ya aiko mata zata saka. Bilki dai bata taɓa ce mata komai ba. Ta sani sannu a hankali zata gane su waye ainihin mahaifinta da mahaifiyarta. Ba Sulaiman kawai ba hatta Abida tana kashe Bilki da mamaki don yana wahalar gaske ta yi maganar Farha haka siddan. Suka yi sallama direban da ya d'auko shi, ya tafi mayar da shi. Yana isa k'ofar gidan motar Abida ta iso. Aka bude mata gate ta shiga. Da yake daga k'ofar gida ya sauka. Ya shiga cikin gidan daidai ta kammala parking. Ta fito gabad'aya a gajiye take. Kallonta kawai ya yi ya fahimci a tsaye ta yini tana kuma jin yunwa. Ba walwala, ba sukuni ta ce 'Yaya Sulaiman an yini lafiya?" Bata jira zai amsa ko ba zai amsa ba, ta rufe motar ta tafi rik'e da labcoat da jakar hannunta. Ido ya bi bayanta da shi yana ganin yadda take tafiya a gajiye. A ransa yake ayyana da a gidansu suke ta dawo gida a gajiye haka da sai ya yi mata tausa tilas. Yanzu kuma takaicin yadda ta shige cikin gida kaitsaye ne ya kwamushe shi. Akan me ba zata zo d'akinsa ta dinga hayagagar ita ta gaji tausa take so ba. Duk da yasan a yanzu ba zai yi mata ba. Amma dai ta zo mana. Wato da gaske ta gaji da ba shi hak'uri kenan? Ya jijjiga kai. A fili ya furta "Dole ki dawo da rarrashina Abida." Washe gari ya gama shirinsa akan zai je Kano. Ya yi sallama da su Baba. A ranar Abida evening zata yi. Dan haka Baba ya ce ta kai Shi airport da kanta. Har cikin zuciyarta a dole zata kai shi kawai gardama da Baba ne ba zata sake yi ba. Ta shirya junior ta tarar da shi a tsaye yana jiransu. Ta bashi mukullin ya karɓa don gabad'aya yanayinta irin wanda baya so ne. Sanyi k'alau ba kazar kazar ba takalar faɗa ko rintom tana binsa kud'i. Yadda ta ɗauko junior ya sanya ya gane ba zata yi wata doguwar magana ba, bare ta yi zantuka masu nauyi. Haka ya ja motar suka fice. Sun yi nisa sosai ba wamda ya ce uffan. Gabad'aya ya ji komai ya gundure shi. Ya waiwaiya ya ga junior ya yi barci ne. Ya numfasa ya ce "Amma ina ga na sha fad'a miki ban son wannan dan gyalen da bai fi daidai Noor da Farha ba". Tana kishingiden ta ce "Bubu ce a jikina ai babu damuwa". A tunzure ya ce "To ni a wajena da damuwa" . Maimakon ya ji ta hakikance tana fahimtar da shi sai kawai ta ce "Idan muna tare za'a gyara". Daga haka ta kame bakinta ta yi shiru. Ya rasa kuma mai zai ce don gabad'aya ba haka yake so ba. Shi yafi son su yi ta daru. Ya kasa hak'uri ya ce "Ke nan kina jiran na sallame ki ko?" Maimakon ta amsa masa da Baki Sai kawai ta fara kuka, kuka kuwa mai nauyi. Hankalinsa ya yi tashin gauron zabi. Ya zuba ido kawai yana kallonta cikin kaduwa da lamari. Sosia ta yi kukan sai da ta gaji dan kanta sannan ta bude jakarta ta goge fuskarta. Ya nisa ya ce "Wato dai so kike ki nuna na zalunce ki ko Abida? Akan me za ki dinga yi mini irin wannan kukan?" Bata ce masa komai ba. Ya rasa mai zai ce. Kan dole ya rage gudun da yake yi. Murya ba amo ta ce "Idan baka ji a jikinka ka zalunce ni ba. To ai baka da kaico kada ka damu kanka". "A hassale ya ce "To menene ya sanya ki kuka, menene damuwarki ne?" Hawaye ya sake k'wace mata. Ta ki yin magana illah hawaye da yake ta tsere a fuskarta. Hankalinsa ya yi tashin gauron zabi. Ya fara fad'a. "Ki cigaba da yi mini kuka ba gaira ba sabar. Ban yi miki komai ba, haka kawai sai kin tayar mini da hankali alhalin ma kamata ya yi na sake fita a harkarki tunda jiya da yau duk gaisuwar raini kika yi mini. Abida cigaba daga inda kika tsaya na wulakanci ai ba zan mutu ba. Ba dai aikin da zan je yi ne za ki yi sanadin da zan kwakwalewa mutane idanuwa ba. To Allah ya baki sa'a ki yi sanadin da za'a rufe ni saboda zan yi aiki babu nutsuwa a tare da ni." Save Restricted Content Bot, [Oct 31, 2025 at 11:58] Maimakon ta yi shiru. Ai kawai sai ta cigaba da zirar da hawaye tamkar ruwan famfo. "Har suka airport bata yi magana ba illah kukan sharb'e. A ransa fad'i yake yi "Wannan shine ga mari, ga tsinka jaka. Shi dai a yanzu ba zai wani rarrashe ta ba. Amma kukan da take yi ya yi matuƙar dungunzuma zuciyarsa. "Kai mata da kinaya suke barin ma dai Bilki da Abida". Kan dole ya ce "Dauki wayata ki yi dialling lambarki. Sai ki yi saving sabon layina. Dad'i ya kamata amma ta matse. Shekaranjiya ba irin rokon da bata yi masa akan tana son lambarshi kafin ta ga chart d'insa da budurwa amma ya hanata. Bayan ta ga chart kuma ta rasa kuzarin da zata kwafi lambar layinsa ko ta k'ira layinsa. Murya ba amo ta ce "Bar shi kawai Yaya Sulaiman ba sai na ajiye lambar ba, tunda ba da ni kawai zaka dinga yin waya ko chart ba, ni na hak'ura kawai". Ya zuba mata ido yana karantar yanayinta. Cikin sakwanni ya fahimci da dukkan gaskiyarta ta yi jawabin. Hakan kuma alamace idan har zai yi aure to zata bar shi gabad'aya ne. Ya hassala ya ce "Abida, Abida, Abida! Kanta na kasa ta ce "Na'am Yaya Sulaiman ". "Wallahi ki bini a hankali wato har kina da kuzarin da za ki saka mini sharadi, saboda na yi shiru ban bayyana abin da kika yi mini ba?" Ta fara kuka mai sauti ta ce "Ni ban yi komai ba, ba yadda za'a yi ace Abida mai hankali da ilimi ce zata soki MAMI. Sharrin jinnul Ashiq ne ba ni ba ce. Duk da haka na baka hak'uri kan hak'uri amma ka kasa yafe mini. Tsakanina da Allah na gaji. Kawai ka fito ka fad'i laifin nawa, sannan ka yanke mana decision, don na gaji da wannan takurarren yanayin da nake ciki. Idan zaka iya yafe mini komai ya wuce to hakan nake so. Idan kuma a zuciyarka kana ganin ba zaka iya yafe mini ba, to be sincere bata mini lokacin da kake yi ya isa haka". Ya yi shiru. Cikin sigar umarni ya ce"Abida d'auki wayata ki yi abin da na sanya ki". A wannan karon bata k'i ba. Ta dauki wayar ta kira layinta sannan ta ajiye masa. Sun isa airport ya yi parking a inda aka tanada. Ya ga bata motsa ba. Ya ce "Zan tafi" Kanta na k'asa ta ce "Allah ya k'addara had'uwarmu". "Kina daga zaune ba zaki taso ki rike mini jakata zuwa bakin entrance ba?" Murya ba amo ta ce "Ka yi hak'uri jikina babu kuzari, idan ka dawo zan zo har can din in sha Allah." Ya girgiza kai ya fice ya bude boot ya dauki jakarsa. Ya bude baya ya shafa kan junior sannan ya rufe motar. Ya ga tana zaune a inda take zaune ba alamun zata fito ta shiga mazaunin direba. Ya ce "Abida fito ki ja maotar nan". Bata kalle shi ba ta ce "Zan tafi ne." "Yanzu za ki tafi". Ba musu ta fito ta shiga ta yiwa mota key sannan ta yi gaba ta bar shi ba hon ko daga hannu. Ya saki ajiyar zuciyar ya ce "Allah ya shirye ku kawai". Don a yanzu ita da Bilki wani irin ga ni yake musu na daban. Kaitsaye gidan Bilki ta dira. ... Alti ta dinga murnar zuwanta. A gidan ta karya. Junior kuwa yana wajen wasan yaran da aka yi musu na mussaman. Bilki ta ce "Me ya samu idanuwanki ne haka Abida?" Ta ce "Hmmm wanccan yayan naki mana da yake neman kashe ni a tsaye. Tisa shi a gaba na yi da kuka mai gigitarwa kuma na k'i magana. Na fad'a miki ya rikice ya hau sababi da buyagin zan saka ya kwakwalewa mutane idanuwa". Bilki da Alti dariya sosai. Alti ta ce "Kina wuta Abidan Baba." Ta nisa ta ce "Allah Alti al'amarin ya fara fin k'arfina. To nasan baya son ya ga ina kuka, tunda shi juninsa taurin rai to idan zamu hadu sau goma,.zai ga ina kuka". Ta waiwaiya ta ce "Maigado ya fad'a miki yana neman aure a Kano?" Bilki ta girgiza kai cikin nutsuwa ta ce "A a ". Abida ta samun nutsuwar zuciya tunda bai faɗawa Bilki ba to kuwa ba da gaske ba ne". Ta nisa ta bata labarin chart d'insa da ta ga ni". Bilki ta k'i ta nuna mata wata alamar ta sani. Ta ce "Wane shi ya fara wannan katobarar ai da mun bar shi for life". Dad'i ya cika zuciyar Abida ta ce "Ai kuwa tunaninmu d'aya don Wallahi hak'ura zan yi da shi matuƙar ya ce bayan wannan dogon lokacin da na shafe ina dakonsa zai mini tukuicin kishiya to kawai na yafe shi. Zan ta dumama ruwan dumi da gishiri ina gasa wajen ba shikenan ba?". Save Restricted Content Bot, [Oct 31, 2025 at 12:06] Gabad'aya suka fashe da dariyar batunta. Sosai suka yi hira ta warware sai yamma ta koma gida. *Kano* Zuwa yamma ya kammala da asibitin Makka eye Hospital da yake Gadon Kaya. Ya saka hannun kan aikin da zai yiwa mutane 100 cikin kwanaki goma. Wand za'a fara kwanaki biyu masu zuwa. Ganin yamma ta yi kaitsaye ya zarce Bristol hotel da yake farm centre ya kama d'aki. Washegari wajen shad'aya abokinsa ya zo a mota ya d'auke shi zuwa gidan Hamida da yake court road. A bakin gate din gidan ya ajiye Shi akan idan sun gama ya masa waya ya zo ya dauke shi. Sulaiman ya yi mass godiya. Maigadin ya shaida shi don haka ya bude masa k'ofa babu bin ba'asin daga ina yake ko wajen wa ya zo. Ya shiga katafaren gidan Hamida. Amma tashin hayaniyar da yake jiyowa daga cikin gidan ya saka shi fargaba. Haka ya kutsa cikin gidan ya tarar tana zaune tana kuka yayin da mijinta ke tsaye cikin tsananin fishi ga y'arta ta farko da k'aninta a gefe suma cikin wani irin yanayi marar dad'i. Hamida na jin muryarsa ta zabura ta nufe shi ta rungume shi. Shima ya rungumeta. Kanta na kan kafaɗarsa ta kasa magana illah kuka mai tsananin gaske da take yi tamkar zuciyarta zata yi bindiga. Hankalinsa ya yi tashin gauron zabi. Ya rike hannunta ya Ta zuwa kan kujerar da tafi kusa da su. Ya kalli mijinta ya ga fishinsa ya ragu ba kamar sadda ya shigo ba. Da girmamawa Sulaiman ya Fara gaishe shi don kuwa na sa'ansu ba ne zai kai Yaya Asad. Shima Mai sharia da mutuntata ya karbi gaisuwar Sulaiman. Ya ce "Zo mu je ka sauka a wajena." Sulaiman bai ki ba, ya bishi zuwa falonsa. Da kansa ya gabatarwa Sulaiman ruwa da lemo sannan ya zauna suka sake sabuwar gaisuwar yaushe rabo. Jikin Sulaiman a sanyaye yake amsawa don halin da ya tarar da kanwarsa ya yi awon gaba da dukkan kuzarin da ya shigo da shi. Ya kasa jurewa ya ce "Ranka ya dade na ga gidan naku babu lafiya, gabad'aya na shiga rud'ani". Mai shari'a ya muskuta ya ce "Ai rufin asirinta daya da Allah ya turo ka a daidai wannan lokacin. Ba dan haka ba yau tabbas sai sun bar mini gida da ita wadannan yaran guda biya.". Sulaiman ya sake rikicewa. Murya na rawa ya ce "Subhannallah abu bai yi dad'i ba ranka ya dade. Lamarin mata ai hak'uri ne kawai, duk girmansu idan suka yi wani Abu sai a tamkar yara kananu da basu san komai ba. Ka ƙara hak'uri ai ba zaka biye mata ba. Ko ni nawa nake a gabanka bare ita yarinya ce ai". Mai shari'a ya ce "Dr ba wani yarinta ina ce Ga y'arta nan da ace tana kammala sakandire aka aka yi aurenta da tuni tana da jikoki ai kuwa ba maganar yarinta iyashege ne kawai da shakiyanci a wajen Hamida. Kuma tabbas ta kai ni bango. Nauyin iyayenku nake ji amma tunda ita ta riga ta kwashe kayanta a gaban ma'aiki to zan gwada Mata karshen iyashege." Sulaiman dai hak'uri yake b shi don ya lura ya yi fishi mai tsananin gaske alhalin Shi mutum.neai hak'uri sosia.marar hayaniya. A nutse Sulaiman ya sake cewa "Ka yi hakuri zata gyara in sha Allah". Ya numfasa ya ce "Tunda ta fad'a mini Anisa ta samu matsala da mijinta ta zo zata zauna a nan". Ban boye Mata ba, na ce Mata a a tunda Baba Babba da ransa ga su Asad gunsu yafi cancantar ta tafi daga Nan ma Sai Su samu gangara Su dinga zuwa komai ya wuce. Ido da ido ta ce mini ba zai yiwu ba, gidana da dai ba zata zo ba tunda bana son a zo a co arziki. A gabana ta yi waya da Anisa ta ce ta zo Kano ta je gidan kawarta da yamma ta shiga jirgi ta tafi Maiduguri. Hakan Kuma aka yi. Dama Kuma haushinta nake ji ta riga ta bata yaran nan, basa ganin mutunci y'anuwana, kullum fad'a musu take yi basa sonta. Ace yayata ta zo gidan nan ya'yana suka kasa zuwa su gaishe ta? Kuma tana kallonsu. To ni ba zata mini wnanan BAK'AR TA'ADA din ba, Babu dole. Kuma abin kaicon ma ita da kanta fa ta yi sanadin da y'ay'an basa ganin girmanta. Bata isa ta ce ku yi ko ku bari ba. Idan ka ji su lafiya to ita take bin ra'ayinsu. Matuƙar zata ce ba za su yi yadda suke so ba, to kuwa yanzu zaka ji suna cacar baki a tsakaninsu. To gaskiya na gaji, ta kwashesu su tafi inda zasu je tunda ita ta bata su, na gaji da wulakancin da rashin iya bada tarbiyarta. Save Restricted Content Bot, [Oct 31, 2025 at 12:11] Ga k'ananun yaran ma sun fara d'aukar samfur." Gabad'aya Sulaiman ya rasa abin cewa don kuwa al'amarin akwai tayar da hankali. Kan dole ya shiga ba shi hak'uri tare da alak'awarin zai ja mata kunne, zata gyara. Nauyin Sulaiman ne ya sanya shi hak'ura. Amma da babbar murya ya ce "Ka ja mata kunne, ka gargadeta ta kure hak'urina. Dole ne y'anuwana su zo gidana. Dole kuma ya'yana su mutuntasu, ta shiga hankalinta dan Wallahi a yadda suka kawo mini wuya zan iya bar mata su gabad'aya! Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:03] *DINGISHIN KWADO* PAGE 22 Daga haka ya mike ya ce "Dama fita zan yi." Sulaiman ya mike yana masa godiya ya taka masa zuwa waje. Ya shiga mota direbansa ya ja suka fice. A tunzure Sulaiman ya shiga ya sameta. Komawa ya yi Sulaiman din da mai cike da zafin kai. Don ashariya ya danna mata tafi goma. Ya gama zage ta sannan ya moma kan y'ay'anta suma ya dinga maka musu. Gabad'ayansu sun yi tsamo tsamo don kuwa suna yara sun san baya wasa da su. Hamida kuka kawai take yi. Don gorin da mijinta ya yi mata na bata zaune lafiya da y'anuwanta da wan mahaifinta da ahalinsa ba shine lasisin da zata yi gaba ko ta saka ya'yanasa gaba da y'anuwansa ba. Kuma yayar tasa da suke uba d'aya tabbas bata sonta akilo take yi ma ya k'ara aure. Amma ya kafe dole ta bita tunda ba shi da uwa ba shi da uba kuma ita ce ba lbbarsu a lokacin da ya yi karatu haka ta dinga siyar da kayan d'akinta tana ba shi kud'i yana hidimar makaranta. Shi kuwa ba yadda za'a yi a shata mata layi a gidansa ko a kan y'ay'ansa. Itama Idan ta ga ba zata iya girmamata ba to kawai ta yi gaba shi bai saba ganin gaba irin tata ba. Kukan da take yi bana korar da ya yi niyyar yi musu ba ne. A a gorin tana gaba da Baba Babba da su oga Asad ne yake saka ta kuka mai gigitarwa. Ga Sulaiman din da suke nema ruwa a jallo ya zo gidanta ya tarar da bak'incikin da ya yi sanadin a gaban y'ay'anta yake mata cin mutunci. Tsawon lokaci kafin ya daina cin mutuncinsu. A sanyaye Ummu da ita ce babba ta ce "Ka yi hak'uri uncle zamu gyara." A kufule ya ce "Kada ma ku gyara. Ai ni kam kun ba ni kunya ace wai kuna iya zagin uwarku, tana fad'a kuna fad'a, bata isa ku bita ba, sai dai ta biku?" Hamida ta sake rushewa da kuka don al'amarin da yake matuƙar gigita ta kenan. Amma ita bata gano sakacinta da matsanancitar soyayyar da take gwada musu na kan gaba wajen halin da suke ciki, sai kawai take ganin saka mata hannu dangin miji suka yi don basa sonta. Baffa mai bin Ummu kansa na k'asa Sulaiman ya ce "Kai zo nan". Da sauri ya isa kusa da shi ya tsugunna. Ya ce "Dago fuskrua ba ga ni?" Ya dago a tsorace Sulaiman ya zuba masa ido ainun cikin nazari. Kafin ya ce "Shaye Shaye kake yi sha ko?" Da sauri ya ce "Uncle wallahu bana sha! Hamida ta sake kecewa da kukan bak'in ciki don kuwa tabbas yana sha. Sulaiman ya ce "Kana fad'a mini baka sha ko?" Gobe da kaina zan kaika wajen Ansari su auna mini kai. Idan suak gano kana sha da kansu Kuma. To zan barka a gidansa ya ci uwarka da kyau". Hankali ln yaron ya tashi ya ce "Wallahi uncle last month na fara shan shisha, wiwi kam shekaranjiya ne kawai. Kuma Babanmu ya fad'a mini idan na cigaba da sha zai kori ni. Wallahi yau kwana biyar ban sha ba, dan allaj5ka yi hak'uri na daina na a kuma taya ni addu'a. Zuciyar Sulaiman ta karye. Ya rasa mai zai ce. Tabbas matasa sun jefa kansu cikin gararrin Shaye Shaye. Tarbiya ta shiga cikin halin ni y'asu. Wasu laifin iyaye ne yayin da wasu iyayen sun yi iya bakin k'ok'arinsu y'ay'an ne suka bijire suka tankwabar da kyawawan dabiun da ake dorasu a kai. A fili ya ce "Allah ya shirye ka, ya shirya na dukkan y'ay'an alummar Annabi da suka karkace. Ya kalli Ummu ya ce 'Ke kuma sai kika zabi ki ta cin mutuncin uwarki saboda kina son aure ko? To dan kan uwarki kin kawo mijin ne aka k'i yi miki? Da bakina zan faɗawa Babanki a katse karatun da kike yi tunda ba na hankali da nutsuwa kike yi ba, na raini da rashin d'a'a ne. Ban da haka kamar ki ace ki tisa uwarki a gaba saboda kina ganin kin kamo ta girma! Da kuka sosia take bada hak'uri. Don ga ni take yi kafin ya bar gidan zai iya zaneta. Tunda mamansu ma an mata ashariya kalakala. Sai da ya wanke su tas sannan ya sallame Su tare da gargadin ya dawo Kano gabad'aya. Kada Su fasa rashin tarbiya da cin mutuncin uwarsu da yan uwan ubansu. Suna fita ya kalli Hamida da take kuka tamkar ta fito da zuciyarta. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:06] Ya tausasa harshe ya ce "Hamida" . Ta kasa amsawa don kuwa kukan da take yi mai nauyi ne ainun. Ya yi shiru yana kallonta amma zuciyarsa tamkar ya rushe da kukan shima don zuciyarsa ta yi masa nau yi k'warai da gaske. Tausayinta ya mamaye takaicinta. Ya zuba mata ido yana ganin kammanin Maminsu sak a tare da ita. Dama ita kam komai na uwarsu ne hatta tafiyarsu iri daya ce. Ba yaudari kansa ba har halayyar ta kwashe. Don kuwa suma sun rayu ne tana fad'a musu y'anuwanta da y'anuwan Babansu basa sonta. Ya nisa ya ce "Kukan ya isa y'aruwata, share hawayenki ko kowa baya sonki, ai kinsan lina da ni, ba wanda nake so kaf cikinku irinki. Ni na saki nono kika kama. Ki yi hakuri". Nan da nan kuwa ta share hawayenta. Idonsa ya ciko da k'walla. Haka MAMI take yi Idan ta zaunar da Shi tana fad'a masa mutanen da suke kewaye da ita basa sonta duk munafukanta ne. Da zarar ya ce mata mu muna sonki MAMI. Irin son da zamu sadaukar miki da komai. Nan da nan sai ta wartsake su yi hirar arziki. Amma idan ya yi mata nasiha tare da fad'in ta daina damuwa irin haka ai sai ta harzuk'a ta hau fadan baya kishinta tunda baya sonta daga nan zaman ya watse. Amma da ya fahimci rarrashi da zuga take so sai yake yi mata hakan cikin siyasa, ya samu su rabu k'alau. To yau ha Hamida ma ta nuna masa haka take.. Ta mike ta shiga kicin ta hado masa abinci. Yana ci suna hira ya bata labarin komai har zamansa a gidan yari don yasan ba zata fad'a ba. Cikin dabara ya ce "Zan dai hutar da ke gorin mijinki na kina gaba da Baba. Zan zo da kaina na tafi dake ki gaida Baba gobe kuma sai ya samu wani abin fad'a. Amma lallai ki shiga hankalinki, idan kika yiwa kanki sanadin da aurenki ya k'are za ki shiga garari mai yawa. Mijinki mutumin kirki ne, mai addinine to ki yi maza ki gyara tun ba ki janyowa kanki sanadin wahala ba. Duk son da nake yi miki ba zan iya cike miki gurbinsa ba. Idan kin yarda da maganata idan ya dawo ki ba shi hak'uri, ki gyara mu'amalarki da y'anuwansa, ki kuma gyara kuskuren da kike yi akan tarbiyar yara". A sanyaye ta ce "To." Ya kalle ta ya ce nan da sati biyu zan n koma Abuja tare da ku zamu tafi gabad'aya.". Ga mamakinsa ya ji ta ce "To". Wani abu ya tsirga masa don ya yi zaton sai ya kai ruwa rana da ita kafin ta amince don kuwa ita din kafaffiya ce ta gaske. Amma tunda ta amince to kowa ma zai amince babu dogon turanci, don ita da Ansari shawararsu d'aya sune kuma yake fargaba akansu. Hamida da Ansari sune sak MAMI kuma sune aminanta. Saddiqa bata da wata matsala. Anisa kuwa ra'ayin Hamida take bi akan komai bisa hujjar ita ce babbarsu, to itace uwarta a yanzu. Shiyasa da ta ce mata ta tafi Maiduguri ta tafi babu musu. Daidai lokacin ya k'ira abokinsa akan ya zo ya d'auke shi. Ya dinga yi mata nasiha tare da rarrashi. Har abokin nasa ya iso ya mata sallama akan zai dawo, amma gobe sammako zai yi zuwa Funtua, kafin ya fara hidimar ayyukan asibiti. Bak'in ciki ya hanata yin magana amma da tambaye shi me zai yi a wannan garin? Da abokinsa ya dauke shi bai zame ko ina ba, sai office din Julius Berger. Ya gama tattaunawa da su, suka yi gobe zasu tafi Funtua da wakilansu. Washegari sassafe kuwa suka tafi a motar kamfanin. Kaitsaye gidansu da yake a garkame suka isa. Ba maganar neman makulli. Don haka aka yanke Shi. Gabad'aya k'ura da karashiya shin yiwa gidan k'awanya sosai. Sashin Baba Babba suka fara shiga kujeru da abubuwan bukata duk suna nan Sai dai kam ba ko dad'in kallo a dalilin yadda suka dade a haka. Suka shiga d'akinsu Abida Hatta gadajensu uku duk suna ciki. Ya daure suka Ga ko Ina a Shashi sannan suka wuce zuwa sashin MAMI. Nan kam ba kaya tunda komai nata sun sun bayar, wasu sun sadakar wasu kuma k'annensa mata sun dauka. A yanzu b'angaren MAMI zaman Ansari yake yi. Shima suka duba suka yi aune aunensu. Suka isa shashin yan aiki. Shashinsa ne na k'arshe. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:08] Shima komai na nan. Kurace dai kawia ta lullube komai. Amma har kayan Abida na wadrof duk suna nan da akwatinanta. Ba wani gyara ne sosai a nasa b'angaren ba, a dalilin lokacin aurensu Sai da aka canja fasalin ganin ya banbanta da na su Baba. Suka gama ganin ko ina suka fito harabar suka tsaya. Sulaiman idanuwansa sun cika da k'walla a dalilin memory dim da suka shud'e Yana ta dawo masa. Wai gidansu ne ya zama kufai, gidansune ya zama matattarar tururura da kwazazzabai da karashiyoyi. Hawaye ya k'wace masa. Ma'aikatan jikinsu ya yi sanyi don kuwa Su kansu yadda suka ga girman gidan da kuma alamun da an yi rayuwa a cikinsa Sai suka tausaya masa a dalilin sun yi tunanin ko duk iyalin sun rasu ne. Suka gama ya rufe gidan da Sabon kwadon. Tare da su suka rankaya gidan sarki. Ya yi gaisuwa tare da sanarwar ya dawo, a kuma kowanne lokaci zai iya buk'atar Ladi farm. Mai girma hakimi ya tabbatar masa babu damuwa ko yanzu idan yanzu so zai ba shi. Suka yi sallama suka fito suka d'auki hanyar Kano. Bai bar office din ba sai da ya cake musu milyoyin kudin da suka caje shi akan gyara da canja fasalin gidansu gabad'aya da yake su yi masa cikin k'ank'anin lokaci. Duk da milyoyin kudine masu yawa haka ya musu transfer ta dala account d'insa. Daga nan ya wuce zuwa gidan Hamida. Anan ya ci abincin dare. Bai fad'a mata kudirinsa ba. Daga nan ya shiga aiki a asibiti ka'in da na'in. Satinsa guda bai ga k'iran wayar Abida a wayarsa ba. Abin na mintsininsa sosai, sai dai matsanancin ayyuka da matsalolin da suka dabaibaye shi ya sanya shi mantawa da wannan matsalar. Sati biyu ya kammala contract din asibitin. Ya samu kuɗadensa. Ya koma Funtua ya tarar an kammala gyara shashinsa kamar yadda ya bukat su fara da nan. An wanke shi tas. Ya fito ya dawo tamkar yanzu aka gina. Kayan Abida da aka yi mata masu k'arshen tsada ba abin da suka yi. Amma ya tarkata su bayan ya k'ira kafinta ya kunce ya goge Su. D'iyar goggonsu ya kaiwa wacce da babarta da su Baba babba ubansu d'aya. Ta dinga yi masa godiya da fatan alheri. Ya tarar duk goggonin nasu sun rasu. Zuciyarsa ta harba. Ko ya ya y'anuwa Maminsu? Take ya wuce ainihin gidansu ya gaida yayyenta da kanneta da suke rayuwa a cikin gidan. Ya yi musu alheri suna ta yi masa nasiha tare da fad'an ya yi wauta da ya tsallake ya bar y'anuwansa da danginsa tsawon lokaci. Kawu Bala da suke daki d'aya da mami ya tambaye shi akan Ko ya je ya gaida Alhaji Babba?" Sulaiman da k'warin guiwar ya ce" A wajensa ma na sauka". Dad'i ya kama dattijon ya dinga yi masa addu'a tare da ba shi umarnin lallai ya dinga saka y'anuwasa akan hanya. Bilki ce kawai take yi musu waya har ma da aiken kayan abinci da kud'i, sai kuma Ansari da Shima yake kamantawa. Amma sauran kam ko gaisuwar wayar ma ta gagara. Haka Sulaiman ya tafi cikin murnar sa'ar da ya yi ba wanda ya mutu a cikinsu Allah ya k'addara zasu sake ganawa. Yana tafe a k'afa yana sake fahimtar irin koma bayan da ya same shi a dalilin tafiyar da ya yi. Nadama kam dama ya jima da yinta mussaman da ya yi rayuwar prison. Amma halim da kannensa suke ciki ya yi matuƙar dama masa lissafi. Idan auren Hamida ya mutu a yanzu ba ita ba shi kansa ya shiga uku ai. Ba zai iya daukar matsalarsu shi kad'ai ba. Matsalar da kud'i zata magance zai iya amma matsalolin da kud'i ba zai magance su ba, ba zai iya ba. Tabbas yana bukatar Asad da Faruk har ma da Usman. Matsalar Hamida kad'ai ta hana shi sukuni to ina ga ta Anisa da take k'aramarsu yake jin tausayinta fiye da kowa. A duk sadda ya samu zama ba abin da yake bijiro masa irin kannensa. Ko tunanin Abida da ya'yanta ba ya yi a dalilin yasan suna amintaccen hannu. Bilki ce kawai bata da damuwa idan ma tana da ita to tana da Baban da zai tsaya mata. Ya numfasa yana ganin girman k'alubalen da yake gabansu. Maimakon ya zauna ya huta kawai sai ya yi Katsina. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:11] Ya dira gidan Anisa. Bai wani tarar da tashin hankali irin yadda ya yi hasashe ba. Rikici ne irin na sabanin fahimta, har abin ya yi tsananin da ta bar gidan. Ta yi murnar ganinsa kamar me. Idanuwansa suka kada a dalilin irin murnar da ya ganta a ciki lallai ya yi kuskuren tsallake su. A ranar ya juya Kano. Yana tunanin gobe zai je Kaduna wajen Saddiqa. Ansari waya suke yi da shi, da har zai zo Kano wajensa ya ce ya bari nan gaba kad'an sai ya zo. A maimakon sati biyu ko uku sai da ya shafe wata guda a tsakanin Kano da Funtua. Ya sabunta gidansu an sake masa fasali na ban mamaki. An had'a sola a kowanne b'angaren. Ya yi furnishing din bangarensa sosia komai na garari ya zuba. Haka b'angaren Baba babba ya zuba musu komai na bukata sababbi na alfarma. Gadon Abida da yake d'akinsu na b'angaren Baba babba da kullum take fad'a masa tana son abinta har yanzu, ya saka an gyara mata ya kai mata bangarensu iya na Bilki da na Munira ne a d'akin yanzu. Bangare MAMI kuwa da yake zaman Ansari labule da kafet da talabijin da firij ya saka sai katifu a d'akuna biyu. Ba kowa ya yiwa hakan ba sai y'anuwansa idan sun zo su zabi duk inda suke so su sauka, wala gunsa ko gun Baba ko kuma ainihin wajensu. Bangaren yan aiki da yake mallakin Baba Babba ne an yi gyara ya zama iri d'aya da sauran b'angaren ammaa bai zuba komai ba. So yake idan Ubangiji ya taimake shi akan niyyarsa Yaya Faruku ya dawo su zauna tare da Baba tunda a Funtua Yaya Faruku ya rayu. Ya sha cewa ba inda yake jin dad'insa a duniya irin Funtua. Idan hakane to kuwa lokaci ya yi da ya kamata ya dawo gida. Ya shiga b'angarensa ya ga yadda aka kawata wajen ya tabbatar wajen zai burge Abida tunda y'ar gayu ce ta soaai. Yana kwance akn kujera yana hasashen kuɗaden da suka narke wajen gyaran gida. Tabbas zasu gina masa sabbin gidaje biyu. Amma kuma kowa ya ga gidan sai ya sake kallonsa. An sake masa fasali gabad'aya. Ya sha fenti da fitilu tamkar wata masarauta ko fad'ar gwamnati. Tun baba bai dawo ba yake jin dad'i a k'asan ransa yana jin tamkar komai ya wuce ne. Yanzu abin da ya rage masa ya tattara kan k'annensa su je su gurfana a gaban Baba. Ba ya jin fargabar faɗawa Baba kudirinsa na son ya dawo Funtua don ya tabbatar idan Baba ya gane hakan yake so zai yarda. Kawai wasu daga cikin y'ay'ansa ne zasu iya yin bara'a. Anan ne kuma yake tunanin rikici zai sake ballewa don shima ba zai yarda ba. Ko suna so ko basa so Baban ba nasu bane su kad'ai. Ansari ya Isa Kano da sassafe Sulaiman da kansa ya dauko shi a airport tunda ya sayi tsaleliyar mota da tsayawa fad'in kudinta kauyanci ne. Suna tafe suna tattaunawa cikin shauki da mararin juna. A hakan Sulaiman ya kutso masa da buk'atar gobe zasu tafi Abuja tare jibi kuma Hamida da Anisa zasu biyo su a jirgi. Ya yi magana da Saddiqa tana Abuja wajen mijinta dan haka zasu sameta a can ne, maimakon su tsaya su d'auke ta a Kaduna. Ansari ya yi shiru don bai gamsu da zuwansu gabad'aya ba. Sulaiman ya yi turus don bokarewar Ansari na nufin bokarewar Hamida da ya samu ta amince babu qabali da ba'adi. Cikin damuwa Ansari ya ce "Allah ne shaidar bana fishi da Baba don kuwa ina gaishe shi from time to time. Amma hakan ba yana nufin kuma na gamsu ya yafewa MAMI bane." Sulaiman ya ce "To yanzu mu je mu nema mata yafiya ta gaske Ansari. Ansari ya jijjiga kai ya ce "Yaya Sulaiman gaskiya ni ba zan je ba. Baba K'arami ne d'anuwansa ba MAMI ba. Har kuma Baba k'arami ya bar duniya ba shi da ra'ayin kansa mun sa ni sarai. Komai Baba Babba ya ce bai taɓa inkari ko yi masa gardama ba. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:14] To idan hakane ya kamata ya tattara ya barmu gabad'aya? Idan ya bar su yaya Hamida bisa hujjar sun bar shi to ni da Saddiqa da Bilki da muke gaishe shi fa? Har Anti Bilki ta gama rayuwarta a Katsina nai taɓa sawa an bibiyeta ba, duk kuwa da yasan tana mak'onsa tana mak'on ya'yansa. Duk satin duniya sai ta gaishe shi, amma kafin ta bar Katsina ba wani abu da ya yi mata da zata gane shi ubanta ne. Mami ce ta yi laifi sai ta yi mutuwar fuju'a ashe bai kamata ya tausaya mana ya danne laifin uwarmu ya rungume mu ba mussaman da muka rasa uwa da uwa a cikin shekara guda? Da ɗansa ya d'auke shi ai mutuwar MAMI kuma sai ta saka ya dawo ya gyara barnar da ta yi a matsayinsa na babba kuma namiji mai hankali. Duk bai yi ba haka ba. Da ya zo ta'aziya bamu ci arzikin Baba k'arami ya zauna da mu ya tayamu k'rbar gaisuwa ba. Sai ya sake bin y'ay'ansa suka bar mana gidan gabad'aya! Haka shi da Yaya Asad da Yaya Faruk suka zubawa Abida ido ta tozarta aurenta saboda kaine mijin, da ace wanine daban da sun ce ta koma d'akinta tunda haka muka ga ana yiwa Yaya Hamida da Yaya Salaha. Idanuwansa ya cika da k'walla. Ya numfasa ya cigaba da fad'in still na danne komai da aurena ya zo takanas na niki gari na je har Abuja na gurfana a gabansa akan shi nake so ya karɓa mini auren. Tabbas ya zo amma daga shi sai Yaya Usman a ranar kuma suka juya. Ba kowa a bikina sai imu imu sai dangin MAMI. Kenan laifin MAMI ya shafe nasabar baba K'arami, laifinta ya shafe hak'kin da muke da shi a kansa na shine d'anuwan mahaifinmu?" Hawaye ya k'wace masa ya saka dukkan hannuwansa ya rufe fuskarsa. Sai da ya shanye kukansa. Sannan ya zarce da fad'in "Duk fa da haka a duk sadda ya faɗo mini ina masa waya na gaishe shi. Fisabidillahi idan mutum na gaishe aka d'auki lokaci bai jika ba adhe bai kamata ya lalubo ka ya ji lafiyarka ba? Ni ban masa komai ba. Ra'ayin uwata na girmama wnada ko uban da ya haife ni zan iya girmama ra'ayin uwata na bar shi. Da ta rasu na shiga taitayina na zubar da makaman yaƙina na gyara mu'amala ta da Ubangiji da kuma jama'a. Amman Baba da iyalinsa sun kulle zukantsu basa ganin rashin adalcin da suke yi mana. Na tabbatar idan y'ay'ansa na cikinsa da suka saba gaishe shi ya ji su shiru zai bibiya ya ji ba'asin shirunsu. Ni fa ba d'aya, da ace ko ya ya idan ya jini shiru tunda na zubar da makaman yaƙina zai lalubo ni ai zan ji dad'i. To amma sai na fahimci ma gaishe shi din nake yi bai d'auke shi abin arziki ba. Idan na kira shi zai amsa da murna, idan ban kira shi ba ya manta da ni, na cigaba da gaishe shine saboda alfarmar mahaifina. Wallahi duk sababin Baba k'arami ba zai share su Yaya Asad akan laifin Momi ba, zai bada hujjar ba ruwansa da ita, ba dan ita zai yi ba, dan ubansu zai yi." Ya kammala da kuka na sosai tamkar ba namiji ba. Wato Sulaiman kansa gabad'aya ya kunce ji ya yi gabad'aya tamkar an yi masa d'aurin huhun goro. Ya yi ta maza ya aro jarumta ya ce "Ansari ka yi hak'uri. Ka sake hak'uri ka daure. Allah na son sulhu da kansa ya ce wa sulhu khair" . Ansari ya ce "Na ji". Dad'i ya kama Sulaiman ya ce "Yauwa Wazirin MAMI na gdoe maka". Ansari ya ce "Daina gode mini don kuwa jinka ya zama dole yarda kuwa ban yarda ba". Sulaiman ya ji tamkar an kwada masa guduma don yasan tantirancin Ansari. Murya ba amo ya ce "Yanzu dai ya sake shiga rigar mahaifinmu, ka huce, mu je mu ba shi hak'urin ai ba gazawa ba ne. Idan ya dawo gida mu kanmu fi sai mun fi samun nutsuwar zuciya, kannenmu zasu daina gararanbar neman mafaka, za'a daina yi mana gorin gidanmu ya dare! Sulaiman ya kammala jawabinsa cikin kwantar da harshe ainun. Ansari ya numfasa kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Ka raka Yaya Hamida da Anisa sune basa nemansa ko kad'an amma Ni da Saddiqa muna gaishe shi. Ita kuwa anty Bilki ai tana hannunsa ko". Da dan kuzari Sulaiman ya ce "To ko auren oga da Bilki da Baba ya k'ulla ai ya isa ka gane baya kinmu. Haka oga Asad din baya kin MAMI. Kuma ko dan Yaya Faruku ma wani abin Duk a barshi ya wuce.". A zafafe Ansari ya ce "Oga Asad kawai ina kallonsa ne. Wallahi ba dan mutuwar MAMI ta sauya mini rayuwata gabadaya ba da na marawa Yaya Hamida baya mun maka Asad a kotu bisa aurewa MAMI d'iya da ya yi. Zamansa Babba Bai amfane mu da komai ba. Ni fa da ya dauke Baba Babba a farko ban ga laifinsa ba. Yana da damar da zai yi hakan. Aman da MAMI ta rasu Bai yi tsayuwar daka ya dawo da gidanmu da ya wargaje ba tun lokacin nake kallonsa kawai gaba ne ba Zan yi ba. Amma ba ruwana da shi. Kai ko fa Yaya Farukun da kowa yake fad'in karamine Ni ban ga karamcinsa ba don kuwa ban ga gudunmawar da ya bayar wajen gyaran zumunci ba. Ni fa yini na gano Baba k'arami ba Shi da wata alfarma tunda MAMI ta yi laifi to shima ya yi. Ka ga ba dan ka tafi ka bar Anty Abida na tsawon shekarun nan ba da Slsai ka sahale mata idan ya so ta samu wanda za'a nuna masa daddatako. Amma tunda ka yi shekaru hud'u ka barta da aurenta ba kuma ta gajiya ba to nasan ta jiki. Kai kuma ka wuce iyaka wajen hukuncin shiyasa na hak'ura. Ba dan haka ba Wallahi matuƙar ka ce zaka zauna da ita to sai na gurfanar da kai gaban shari'a ina nemawa mami hak'kin an wulakanta ka saboda ita amma ka kafe kana zaune da ita". Save Restricted Content Bot, [Nov 4, 2025 at 21:17] Zuciyar Sulaiman ta harba wai waddane irin yan bala'ine su haka? Tabdi jam. Lah shakka idan suka ji kalaman Abida akan Mami sai yak'i ya sake ballewa kuma matuƙar bai sahale mata ba, sai sun maka shi a kotu ba wai daina mu'amala zasu yi da shi kawai ba. A a sai sun nemawa mami hak'kinta akansa. Lallai Abida kanta na ja da ta roki arzikin ya boye musu. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Sulaiman yake fad'a a fili don ya rasa kalmar da zai furta ko guda. *Abuja* Hafcy da murana ta dawo daga makaranta a dalilin an akfe musu result dinsu na second semester. Sosai sakamako ya yi kyau don kuwa tana matakin ajin farko(first class). Da kuzari ta nunawa Aysha. Ta ce Yaya aysha duba Ki ga ni". Ta karba ta gani ta murmusa ta ce "Hafcyn Dady lallai yau kina da kyauta. Saura ki tafi gunsa ban sa ni ba ". Hafcy ta murmusa ta ce "Idan zan hau saman ba zan manta ba Zan leko na fad'a miki. Daga haka ta wuce zuwa d'akinta. Da daddare sai da ya dawo daga sallar isha sannan Hafcy ta. Hau sama da yan rakiyarta Aysha da Bilkisu. Yana zaune yana rik'e da Baba K'arami yayin da Bilki ke gefensa tana shayar da Baba Babba. Suak shiga a nutse bayan an basu damar Su shiga. Kusa da shi suka tsugunna suna sake gaishe shi. Da murna sosia Hafcy ta ce "Dady albishir". Da walwala ya ce "Goro fari kal Hafcyna". Ta mik'a masa takardar hannunta. Ya gyara kwanciyar Baba Babba a jikinsa ya bude. Ya duba ya d'ago da garin ciki ya ce "Gaskiya kin cancanji albishir da abu mai daraja. Dad'i ya kashe ta don idan suka yi kokari kyautar bajinta yake yi musu tun suna yara. Ya ce ",Ki nutsu ki rubuta mini dukkan abubuwan da kike bukata, da ikon Allah zan yi miki. Kafin nan ma yanzu zan Baki kyautar abu mai k'ololuwar daraja a zuciyata. Ki taya ni adanawa, ki tafi da shi har gidanki, ki ta kallo kina jin dad'in na miki kyautar a in da nake matuƙar so. Farinciki ya lullube zuciyarta. Yayin da Aysha ta tafi tunanin wanne abune haka za'a baw Hafcy? Tana kallon yadda shimfide yaron da ya yi barci. Ya mike. Ya mik'a hannunsa ya d'auko tafkeken hotonsa da mominsu da aka zanasu tamkar a kirasu su amsa. Ya mik'a mata ba tare da ya ce "Uffan ba". Wani irin farinciki ya kamata. Aysha kuwa murnar ya ce hoton uwarsu na da k'ololuwar daraja ya sanya ta tashi ta rungume shi cikin shagwaba take fad'in "Amma ni fa Dady? Na kawo maka sakamakona.masi irin wannan darajar amma baka taɓa mini irin wannan kyautar ba." Bai ce komai ba ya sake ta ya dauko d'ayan da suke sanye da k'ananun kaya cikin snow a k'asar Canada ya mik'a mata ya ce "Ga shi ke ma shikenan?" Tana dariya ta ce "shikenan". Yana juyawa ya ga Bilkisu na kuka. Ya isa da ita ya ce "Zo nan y'aruwata menene". Cikin kuka ta ce "Ni ban samu ba daddy." Ya ce "Zan lalubo miki wani a d'aki ki saka a gefen gadonki. Idan kima na falon k'asa ma kina so na bar miki shikenan?" Ta daga kai tana goge hawaye. Bilki tana kallon Aysha da take ta fallin ya basu kyautar abin da yake tsananin so. Ta girgiza kai bata ce komai ba. Amma cikin ranta fad'i take yi da kinsan dalilin baku hotunan da kin sake takure zuciyarki da bak'in ciki. Suka tafi cikin murna da godiya mai yawa. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shikenan na kwashe hotuna, ba sauran damuwa ko sarauniyar sheba?" Ta yi gajeran murmushi ba ta ce uffan ba. Ya ce "To ki bugawa Faruku waya ki ce masa na cire hotunan maimurabus don akai akai yake tambayar na cire kuwa?" Dariya ta k'wace mata ta sosia. Ba dan komai ba, sai yadda ya ce maimurabus.da bakinsa. A d'akin Aysha suka dire. Ta kalli Hafcy ta ce "Oh Astagafirullah muna ta zargin Dady ya mance da momi yana cin duniyarsa da tsinke ashe ba haka bane. Ashe dai ta nan mak'ale a zuciyarsa. Hafcy ta ce "Yau na tabbatar Dady namijin duniya ne. A gaban anti Maigado ya ce hotonsa da momi shine k'ololuwar abu mai daraja a gunsa wow". Ta yi juyin nishadi. Save Restricted Content Bot, [Nov 4, 2025 at 21:19] Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allah ya jiƙan ki momi, yau kam munsan kina da alfarma." Bilkisu da bata fiye magana ba Ameen kawai ta ce. ....... *Kano* Sulaiman Hamida, Ansari da Anisa. Suna zaune a falon Hamida. Dukkansu kowa ya tunzura Idan aka cire Anisa da bata um bata um um a cikinsu. Amma dai tafi karkata ga ra'ayin Yaya Hamida. Yayin da Hamida kuma ta canja shawara tunda Ansari ya ce ba zai je Abuja ba itama ta matse akan bata da lafiya ba zata iya doguwar tafiya ba. Sulaiman ya ce su tafi a jirgi ita da Anisa shi kuma ya d'auki Ansari su tafi a motarsa. Yana kallonta tana kallon Ansari suna magana da ido. Sulaiman ya yi shiru yana kallonsu cikin tsananin mamakinsu. Da ido suke magana kuma su fahimci junansu. Suan cikin haka mijinta ya dawo. Ya zauna yana marabtarsu tare da tsokanar Anisa ina nassa Yajin? Ta sinne kanta a k'asa don bata iya sakewa da shi. Ya ce "Sulaiman yaushe ne tafiyar taku?" Sulaiman ya kass boye mass ya ce "Ni da a son Raina mu tafi gobe zuwa jibiu zauna don Ansari ya Koma saboda aikinsa. Amma ka gansu nan sun canja shawara wai kuma ba zasu ba". Mai shari'a ya ce "Amma Hamida ai mun gama magana gobe zasu tafi. Har na ce Baffah ya siyo mata ticket ta ce wai zaka siya musu. Na d'auki kudin na bata na ce ta rik'e sai ta yiwa Baba tsaraba tunda na yi niyya. Amma me ya saka ki canja shawara haka Hamida?" Ya tambaye ta cikin sassauci. Kanta na k'asa ta ce "Saboda an nuna mana bamu da kowa, to mun tsyaa a hakan Allah ya isar mana, gorin da ya janyo mana kuma a gidajen aurenmu nan ma da sanin Allah." Ta kece da kuka na tashin hankali. Anisa ma ta shiga yi. Ansari ma ya fara. Yayin da Sulaiman ma ya amsa jarumta shima ya kifa kansa a hannun kujerar hawayensa na diga. Jikin mai shari'a ya yi sanyi ainun. Ya sassauta murya ya ce "Ita rayuwar nan ai gabad'ayanta k'alubale ce. Hak'uri ne kan gaba. Idan har zan fad'a muku gaskiya ku yarda dole ku bi Baba Babba. Ko kuna so ko ba kwa so wan mahaifinku ne. Bari yau na fad'a miki abu d'aya ba dan na yi muku sulhu ko dan ki ji dad'i ba ne, a a iyakacin gaskiyata kenan. Ke ce kike gaba da shi amma shi ba ya yi da ke. Ko kinsan akai akai yake k'irana? Na saba gaishe shi, to idan ya jini shiru zai kira ya tambayi lafiyarki da ta y'ay'anki tare da sake jaddada mini na yi hak'uri da ke saboda ke mace ce mai rauni. Tabbas ina sake yin hak'uri da ke ne saboda shi. Ba irin rigar mutuncin da bai sanya miki ba a idona. Duk da kin shata layi da shi bai fasa siya miki mutunci a matsayinsa na uba kuma walliyinki." Da kuka ta ce "To yana yi maka hakan amma ka goranta mini ka tozarta ni har kana fad'in zaka kore ni a gidanka?" Ya sake sassautawa ya ce "Ba fa Har cikin zuciyata na fad'a ba, na fad'a ne dan kiji irin ciwon da nake ji idan rashin k'irkinki ya motsa. Na fad'a ne dan ki ji ciwo Ki gyara kuskuren da kike tafiya a kansa. Amma yanzu ki yi hakuri Hamida. Ki warware zuciyarki ki karbi gaskiya. Idan kika ji Maganata ni kad'ai nasan ke zan yi miki. Na farko da azumi da ke Zan tafi umrah kinsan bara ban tafi da ke ba, to bana Zan tafi da ke sannan ni da kaina zan raka ki Abuja. Yanzu gobe kai Sulaiman ka tafi da Ansari da Anisa. Ni Kuma zamu taho da hajiyata da yamma Sai Ku tare mu a airport ku kaimu hotel din. Da safe sai ka zo ak d'auke ta zuwa gidan Baba." Sulaiman ya yi maza ya dinga godiya da fatan alheri, yana jin nutsuwar ya samu mai taya shi saita su. Mai shari'a ya ce "Hakan ya yi ko Hamida?" Ta kalli Ansari da ido. Ya Mata alamar ya amince. Murya ba amo ta ce "Ya yi ". Da walwala ya ce "Allah ya yi mini albarka yanzu tashi ki kawo musu abunci. Kina Babba kin tasa su a gaba da kuka. Dan Allah ki zama jaruma ko Sulaiman din da yake babba Idan kin nutsu ai uwace ke. Maza maza je ki saka a shiryo musu abinci. Idan kin so ma ku dan fita wani wajen da zai saka ku nishadi da walwala sai ku ci abincin a can.". Ya tashi ya shige ciki. Ansari ya hak'ura ya yarda zai je don kuwa mijin Yaya Hamida da Yaya Sulaiman sun kashe shi da kabaki da ba'adi. Save Restricted Content Bot, [Nov 4, 2025 at 21:21] Sulaiman ya kalli Anisa ya ce "Yaushe kuka Koma Katsina ne?" Ta ce "Bamu wani jima ba. Yanzu ma kuma tashi zamu yi". An masa transfer zuwa Yola." "To Allah yasa albarka yanzu ina yaran?" Ta ce suna wajen Hajiyarsa tunda aka yi hutun makaranta".. Ya ce "Hakan ya yi". Ya sake cewa y'ay'an Bilki na zuwa gidanki kuwa?". "Suna zuwa sosai. Nima in zuwa na gansu ko na yi musu aika. Amrah ta shiga S. S 3 next year zata kammala sakandire ". "Ma sha Allah! Ni ban je ba, al'amura sun sha kaina sosai amma idan na dawo zan je na gansu" *Abuja* Da yamma Sulaiman suka isa Abuja. Anisa ya ta ce a kaita wajen Saddiqa ta kwana gobe Sai Su zo tare. Sulaiman ya Kira Saddiqa ta bada tabbacin akwia Dakin da zata sauketa. Don ya imyi zaton irin d'aki d'aya ne tunda a Kaduna suke zaune zuwa Abuja take yi kawai lokacin Hutu. Suka kaita sannan suka gaisa da ita cikin farinciki tunda ita ta bata ganshi ba sai lokacin. Suka rabu akan sai gobe mijinta zai kawo su tunda tasan gidan. A hanya sai da Sulaiman ya yiwa Ansari wuta wuta kafin ya yarda ya bishi ya sauka gidan Baba. Da ya ce zai je ya samu masauki ya zo gobe kawai. Tare suka shiga falon. Baba na zaune yana dakon a k'ira sallar magariba ya wuce masallaci. Ya dinga marabtarsu cikin walwala. Suna durk'ushe a gabansa kan kafet. Cikin girmamawa suka gaishe shi. Ya amsa cikin bayanannen farinciki. Tare da tambayar Ansari iyalinsa. Ya sanya su a gaba suka tafi masallaci tare. Sai da suka dawo Momi tasan sun zo, suka gaisheta ta amsa da tambayar maijego tunda matar Ansari ta haihu wata daya da ya shud'e an samu MAMI. Aka basu abinci. Suna ciki ci junior ya fito. Yana ganinsu ya tafi da sauri kusa da su. Ya tsaya yana kallonsu. Yayin da Baba Babba ya tsaya yana kallon yaron. Can ya matsa kusa da Sulaiman ya ce "Dady yaushe ka zo?" Sulaiman ya ce "Dazu na zo". Ya kalli Ansari ya ce "Uncle ina yini ?" Baba ya ce "A ina kasan uncle din?" Ya ce "Na gane shi fa. Ammi tana nuna mini hotonsa tana ce mini idan Dadyna bai dawo ba shine Dadyna kuma ta ce mini shine ya siya rago biyu na sunana". Jikin Ansari ya yi sanyi Ashe Abida tana nunawa yaron shine makaddashin ubansa ba su oga Asad ba. Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ya mik'a masa hannu ya ce "Lafiya lau junior ya kake?" Ya ce "Ina lafiya, ammina ma tana lafiya ta je hospital ta kusa dawowa". Ansari ya kafe shi da ido yana kallon carbon copy na Dr Sulaiman. Junior ya kalli Sulaiman ya ce "Dady yaushe zamu tafi gidanmu ne? Ina son ka saka ni a school ". Murya ba amo ya ce "Zamu tafi junior." Baba ya ce "Zo ka zauna kusa da ni ka barsu su ci abinci kai tambayoyinka bass k'arewa. Cikin nutsuwa Sulaiman ya ce "Baba dukkanmu zamu hadu da safe anan gobe matan zasu iso da wuri in sha Allah." Baba ya amsa da fad'in "Alhamdulillahi Allah ya yi muku albarka gabad'ayanku". Suka amsa da Ameen Baba. A daren Baba ya k'ira dukkan y'ay'ansa ya fad'a musu gobe su zo da safe. Cikin ikon Allah Salaha tana gari, tana gidan Bilki sai Abida ta tashi a asibiti zata biya ta d'auko ta. Sai da suka dawo daga sallar Isha sannan suka rabu da Baba. Suka yi d'akin da zasu kwana shi kuma ya yi cikin gida. A wannan daren Baba bai runtsa ba . Kwana ya yi yana sallah da adduar samun nasara da alheri cikin zaman da za'a yi. Idan ya yi addu'a, ya yi kuka a sujjuda, ya yi wuridi har asuba bai runtsa ba. Ya tashi da yaƙinin Ubangiji ya ji shi. Oga Asad ya murd'e akan Bilki ba zata je da twins ba. Ta bar su tare da Alti a gida. Daga shi sai ita suka zasu je. Kuma fuskarsa a daure ko ita bata ga fuskar tambayar dalilin da za'a bar yara a gida ba. A k'asan ranta kuma tana zaton tunda basu zo sun gansu bane da aka haife su shiyasa ya ce a barsu a gida baya son su gansu a yanzu. Zuciyarta na hirji take shiryawa. Don gabad'aya ya koma yaya Asad din nan da kowa yake ji tsoron yin iyashege a gabansa, ba na yanzu da ya koyi kawaici da sassauci ba. Addu'a kawai take yi kada Allah yasa rikicin da Yaya Sulaiman ya yi hasashen zai sake barkewa ya afku. Itama kwana ta yi tana addu'ar Allah ya sulhunta kullin da suke zukata su warware. Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:26] PAGE 23 Karfe goma da rabi Hamida ta iso kuma Sulaiman da kansa ya je ya dauko ta a inda suka sauka da mijinta. Kafin ta fito daga hotel sai da mijinta ya yi mata nasiha tare da gargadin lallai ta yi biyayya ta tausasa harshenta a gaban Baba". Ta ce "Zata kiyaye. Haka Sulaiman da suka taho a mota ya dinga jaddada mata tasan me zata ce idan an bata damar yin magana. Kuma idan zata yi magana ta yi da lafuzzan da ba za'a ga raini ta yi ba". Har falon gidan Sulaiman ya yi mata jagora Baba na zaune suan karyawa da Ansari. Ya mik'e ya ce "Maraba da Hamida, sannu da zuwa. Sulaiman ka kyauta da ka kawo mini ita". Kunya ta kamata ta tsugunna gefe tana fad'in "Sannu Baba" Don gabad'aya zuciyarta ta karye da ta ganshi yana yi mata maraba. Ya ce "Taso ki zo kusa da ni". Ba kuzari ta mike ta isa jikin kujerar da yake ta durk'usa kanta a k'asa. Ya zauna ya saka ya dafa kanta ya ce "Hamida ya ya iyali, ya kwana biyu, ya ya mijinki?" Ta kasa amsawa. Murya ba amo ta ce "Ina kwana Baba ya jiki jikin?" "Alhamdulillahi ya bayan rabuwa, ya kuma hak'uri?" A matuƙar sanyaye ta ce "Alhamdulillahi.". Sulaiman yana tsaye yana kallonsu. Ansari ma ido zuba musu ya kasa cigaba da cin abincin da bai jima da zubawa ba. Baba ya ce "Matso ki k'ara mana abinci tare zamu ci". Bata musa ba ta matsa ta k'ara zubawa akan nasa. Ya sauko kasa ya ce to saka mana a tsakiyarmu". Hakan kuwa aka yi. Suna ci momi ta shigo. Ta bude baki cikin mamaki ta ce "A a Alhaji yau lallai kana cikin alheri dumu dumu". Ya ce "Ke dai bari yau ga ni ga Hamida bayan tsawon lokaci ina mararin ganinta". Sulaiman ya ce "Baba nima na saka hannu?" Ya girgiza kai ya ce "A a zuba naka". Sulaiman ya ce "To shikenan Baba." Ana cikin haka Usman ya iso cikin kakinsa na soji. Don dai da ya je ya nemo excuse sannan ya taho gida. Suka gaisa yana tsokanar Hamida da lallai batan kai ta yi. Suka gaisa da Ansari da Sulaiman a takaice. Baba ya zuba ido yana nazarin yadda amincin Usman da Sulaiman ya yi rauni sosai. A haka Saddiqa da Anisa suka shigo, suma Baba ya karɓe su da walwala mussaman Anisa da ya jata jikinsa ya rungume hawaye na zuba masa. Itace k'arama kuma ita da Hamida ne bai sake saka su a idanuwansa ba tun rasuwar gyatumarsu sai a wannan ranar da Sulaiman ya kawo masa su. Gata nan haka take kamar Abida yanayinsu daya tamkar cikinsu daya. Abida ta iso sanye da labcoat dinta don sassafe ta je asibiti. Tana ganin Sulaiman da y'anuwansa gabad'aya gabanta ya yanke ya faɗi. Idan har ya faɗa musu abin da ta yi to la shakka tasan komai ya b'aci ba zasu karbe ta ba. Idan kuma ya had'iye bai fad'a ba to da sauk'i. Da walwala da kuzari ta ce "Yaya Hamida oyoyo". Ta isa kusa da ita tana gaishe ta. Cikin sa'a ta amsa gaisuwar bata daure fuska ba. Saddiqa da Anisa suka gaisheta ta amsa da fara'arta tana tambayarsu yaransu. Haka ma Ansari ya gaishe ta, ta amsa da fad'in "Jiya na dawo dare ya yi, amma junior ya fad'a mini uncle d'insa ya zo". Ya dan murmusa kad'an. Ta kalli Sulaiman da yake cin abinci ta ce "Yaya Sulaiman an dawo lafiya?" A takaice ya ce "lafiya lau". Don ba k'aramin tunzura ya yi da ita ba da ta bata yi mass waya ba tunda ya tafi. Ta mike tana ayyana Yaya Faruku da Dady ne basu iso ba, tunda ta ga Yaya Usman a waje yana amsa waya. Faruku ya shigo dukkansu kowa ya gaishe shi, ya amsa yana tambayarsu yara. Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:37] Baba ya kallesu ya ga sun cika gabansa. Daidai lokacin waya Hamida ta d'auki k'ara. Ta bude jakarta ta dauka ganin d'iyarta ce Ummu ya sanya ta fita waje. Tana cikin wayar aka budewa oga Asad gate da ya tuko motar da kansa, Bilki na gefensa. Har ya yi parking tana wayar. Suka had'a ido da shi ta yi kamar bata ganshi ba. Zuciyar Bilki ta harba ta fara yi mata yake. Ita kuma ta d'agawa Bilki hannu. Asad ya shaka amma ya maze suka shiga cikin don gaisawa da su Baba. Can oga ya tuna kwalin apple din su Baba. Har zai bawa Usman ya dauko ya fasa ya mike da kansa ya tafi daukowa. Yana fita ya ga ta gama wayar amma ta dauke kanta ta ci magani. Wani irin abu ya yunk'uro masa. Ya wuce zuwa motar. Ya juyo ya ga tamkar harara ta galla masa. Hak'urinsa ya k'wace ya dufafe ta da sauri. Tana ganin haka ta yi maza ta juya ta shige falon ta tsallake kowa ta isa kusa da Baba ta zauna har tana cin tuntube. Baba ya ce "Nutsu, yi a hankali Hamida". Asad ya shigo da huci yana ayyana ashe k'aryar rashin kunya take ji da shi. Ai tasan karonsu da ta tsaya, da ya nuna mata bata wuce ya bubbige ta ba. Abida ta taso Salaha da take barci. Ta fito. Duk yadda take da hak'uri sai da ta hak'ura da Hamida, ba irin bin ta da bata yi ba akan kada su yi gaba da juna amma Hamida ta toshe k'ofofin da zasu hadu ko su gaisa. Itama har ta gaji ta shareta gabad'aya. Sun gaisa sai dai ba yabo ba fallasa. .. Yaya Asad ya bude taro da addu'a. Baba ya yi gyaran murya ya yi musu sallama. Suka amsa a hankali. Ya ce "Dukkanku nan kunsan abin da ya faru wanda bai shafi kowa a cikinku ba. Ni Babanku da kuma Maminku shaidan ya yi wasa da zukatanmu. Na kuma fahimci Ubangiji ya ba shi nasara ne akanmu bisa hujjar taka dokar da ya yi da kansa da muka yi. Allah da kansa ya raba gado. Mu kuma Hausawa sai muke ganin rabawar kuskurene. A barshi a a had'e ko idan an raba din ma Babu rubutu Babu shaidu. Tsananin shak'uwa da soyayyar da kuma yarda ya sanya ni da dan'uwana bamu yi iyaka aakn dukiyarmu ba. Abin da nake son ku fahimta guda d'aya ne, al'amarin d ya afku aya Allah ya buga akanmu don ya Zama izna Ga waɗanda suka had'a dukiyarsu basa yin rubutu kamar yadda Allah ya umarcemu. Addininmu na musulunci ba abin da bai kawo mana ba. Hatta bashi idan zamu yi a tsakaninmu sai da ya ce mu yi rubutu don kaucewa rud'ani, ayar da ta fi kowacce tsayi a cikin alkur'ani akan bashi da ka'idojojinsa ne. Haka nan Annabi ya yi ta jan kunnenmu tare da gargadinmu akan dukiya da jinimu da mutunci abin kiyayewa ne. Duk alummar da take tozarta amana d, take danne maraya, da alummar da take tauye mudu, da alummar da suke girmama dokar d'anadam sama da dokar Ubangiji, da masu cinye dukiyar maraya, da masu juyawa zumunci baya Annabi ya ce talauci zai yad'u cikin waɗannan alummomin. Zalunci Shugabanni zai tsananta don kuwa za'a koma rayuwa ne irin ta kashin dankali. Har ila yau Annabi ya ce 'Duk alummar da suka tausayawa mata da k'ananun yara to zasu rabauta. Annabi ya ce idan mata suka tsare farjinsu daga zina, suka yi sallau cikakkiya, suka yi biyayyar aure, suka barranta daga yin shirka kowacce iri aljanna ta zama wajabat a garesu." Ya numfasa ya zarce da ce wa "Annabi ya ce "Bai yi zaton wahayi zai kammala ba tare da an saukar da ayar da zata ce makoci ya gaji makocinsa ba, saboda yadda Allah ya girmama sha'anin makwabtaka. Cikin nasihohin Annabi da ya yi masu tsanani sun had'a da barranta daga shedar zurr don kuwa ya yi ta gargadi da babbar murya har sai da gwadonsa ya faɗi, don haka a kiyayi shaidar zurr. Kada ka yi shaidar abin da baka da tabbas, kada ka jinginawa wani sharri ko ka yad'a ya yi wani mummuna al'amarin da baka da tabbas din ya yi. Shawara mafi girma da ya bayar ita ce kada mu zama masu fishi, kada mu zama masu yawan maganar da bata da amfani. Sannan ya umarcemu mu bi uwa, mu kyautata mata, mu yi mata biyayya, mu bi uba mu godewa kokarinsa sannan idan sun kai shekarun girma mu ninka yi musu biyyaya duk abin da zasu ce kada mu gajiya ko mu yi musu magana a zafafe, uffan kada muce musu matuƙar ba mai dad'i ba ce. Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:40] Har ila yau Annabi dai ya ce "Wanda baya sallah ba zai shga aljanna ba, wanda ya yi sanadin mutuwar mumini ba zai shiga aljanna ba. Wanda ya yanke zumunta ko aure ba zai ji k'amshin aljanna ba. Jikin kowa ya yi sanyi tub'us da matashiyar baba a garesu. Ya ce "Bana son tone tone, ba don komai ba sai don Annabi ya tsinewa wanda ya tono masifa. Don haka kowa ya warware zuciyarsa kada ya tono tahsin hankali. Ni dai ubanku ne gabad'ayanku. Duk wanda ya bata mini a cikinku Allah ne shaidar na yafe masa, duk wanda ya zo kusa da ni lallai ina tare da shi. Duk wanda ya yi nesa da ni to ina yi mass addu'a don duk sallar duniya sai na yi muku addu'a gabad'ayanku da iyalinku. Don kuma mutum ba ya yi da ni ai ba zan ware na ce ban da shi a addu'ata ba. Na yafewa kowa duniya da lahira nima wanda yake ganin ban masa daidai ba to a yafe ni dan Allah." Oga Asad ya ce "Baba dan Allah ka bada damar a tattauna cikin nutsuwa idan ba a amayar da gillinka da suke boye a zukata ba, ba za'a warware daga jin haushin juna ba, tunda na ga shaidan din ba shi kad'ai bane ya shigo cikinmu har da rundunarsa gabad'aya ya tattaro". Baba ya yi shiru cikin nazarin shawarar Asad. Ya nisa ya ce "Za'a tattauna amma duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira kada ya yi magana sai an ba shi dama. Duk yadda ka kai da son yin magana ba zaka yi ba sai an baka damar yi." Kowa ya ce "To cike da girmamawa. Oga Asad ya ce "Dan Allah Baba ina neman alfarmar a tambayar mini su Sulaiman gabad'ayansu me na yi musu, don a bayyane yake kowa a cikinsu a zafafe yake da ni". Baba ya kalli Sulaiman ya ce "Ka ji me ya ce Sulaiman?" Kan Sulaiman na kasa ya ce "Ya mana ba daidai ba ne Baba. Mun rayu a gidan nan muna ganin yadda kuke shugabantar da shi akanmu. Amma da wnanan tashin hankalin ya zo sai ya koma gefe ya ki taka rawar da komai zai daidaita kafin tafiyar ta yi tsayi. Sai kawai ya d'auke ka kacokan da sauran kannensa da ya gamsu k'annensa ne, mu kuma ko oho". Baba ya ce "Hakane Hamida kina da matsala da yayanku ne?" Kaitsaye ta ce "Matsalolima kuwa Baba. Ka ga na farko ya zo ya d'auke ka ya barranta mu da kai. Sannan bai zo ta'aziyar MAMI ba, sai na tafi a fahimtar don ta yi maka laifine, na uku da Abida ta bar gidan mijinta bai yi irin yadda kuke yi mana ba. Idan a lokacin baka da lafiya ai shi kam gar yake akan ƙafafuwansa, na tabbatar da ba Yaya Sulaiman ne mijinta ba, da ta dawo gida da sunan yaji da an mayar da ita ko bata so. Wadannan dalilan ya sanya na gane baya sonmu bai d'auke mu tamkar su Salaha ba. Shiyasa na hak'ura da shi, don ba zai yi mana adalci ba". Baba ya ce "Ansari fa?" Ansari ya ce "D'auke ka da ya yi a farko na gamsu lafiyarka ake nema maka tare da samar maka da nutsuwar da ta yi maka tutsu. Amma da mami ta rasu ka ce ka yafe mata ai da sai ku tausaya mana ka dawo gida don musan bamu rasa kowa namu ba. Baba har nan na zo na gaishe ka tare da sake baka hak'uri. Na roki arzikin ka karɓa mini aure, na yi hakan ne don ka yarda ba ni da uban da ya wuce ka. Amma Baba ba wani a cikinsu da ya bika daurin aurena sai Yaya Usman wanda ba dad'in zuwansa na yi ba don ya budr baki ya yi fatan alheri bai yi ba. Kai ma baka zauna a gida kowa ya ganka ba, sai ka barmu mu kad'ai. Mami ce ta yi maka laifi to shi kuma Baba k'arami mai ya yi da aka cire mana rigarsa aka barmu tsirara? Kuma ni datse mu'amalar da suka yi damu na d'ora alhakin hakan akan Yaya Faruku tunda kowa a cikinmu nan ya gamsu Yaya Faruku nasa ne. Me yasa bai yi amfani da kyakkwar mu'amalar da yake da ita a tsakaninmu gabad'aya ba ya kawo daidaito sai kawai suka ware mu suke rayuwa isu isu a gari daya tare da mahaifansu." Kuka ya sarke masa. Hankalin Baba ya tashi ainun ya gano akwai k'amshin gaskiya cikin hasashen Ansari tabbas suma da irin nasu laifin a cikin rugujewar gidansu da mu'amalarsu bakidaya. Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:45] Baba ya ce "A a ban da kuka Ansari share hawayenka ka cigaba da bayaninka. Yi hak'uri". Ansari ya jima yana goge hawayen idonsa kowa na kallonsa ana ganin hankali ya ratsa shi sosai. Dama kuma idan akwia wanda mutuwar MAMI ta yi masa mahangurba to Ansari ne. Don gabad'aya ta saita shi tun lokacin ya zubar da komai don mutuwar wa'azi ta zame masa mai saka nutsuwa da nadama. Ya kasa magana. Baba ya ce "Iya ni da Faruku ne bamu yi daidai ba?" Ya girgiza kai. Ya yi jarumtar had'iye kukan ya ce "Baba Yaya Asad yana nuna mana son kai da banbanci ba dan kad'an ba a tsakaninmu da su Anty Abida. Ta ya ya munsan shine babba kuma nan gaba uba zai zama a wajenmu amma ya kasa taimakon Yaya Sulaiman. Shin ya yi laifin da ya cancanci a kashe masa aure ne bamu sani ba ko kuwa laifin MAMI ne ya yi sanadin da za'a bar matarsa ta zauna a gida alhalin ba sakinta ya yi ba?" Kowa ya yi shiru ana ta auna maganganun a zuci. Baba ya nisa ya ce "Bilki na yi miki tsallake na fara bawa Ansari dama sai na yi ta ganin shine babba ashe kaninku ne. A sanyaye ta ce "Ba komai Baba. Ya ce "Fad'i na ki damuwowin.". Murya ba amo ta ce "Ba ni da matsala da kowa Baba". Ya ce "Ke yanzu kin gamsu da yadda yayanku yake tafiya, haka kin gamsu Faruku akan daidai yake?" Kanta na k'asa ta ce " So nake Yaya Faruku ya bude baki ya fadi abin da yake cinsa a zuciyarsa yana fad'a kuwa to ya huce domin duk danbarwar nan da ake yi bai ce kanzil ba, da kuma ya yi magana to da zai yi abinda ya dace na tabbatar." Baba ya ce "To yayanku fa? "Ba ni da matsala da shi". Hamida ta ce "Ki dai ji tsoron zatin Allah Bilki ki fad'i wariyar launin fatar da yake yi". Baba ya yi mata dak'uwa tare da fad'in "Hamida zan sab'ar miki, ba na saka dokar kada wanda ya yi magana matuƙar ba damar yin magana aka ba shi ba?". Ta yi k'asa da kanta tare da fad'in "Ka yi hak'uri Baba ". Baba ya kalli Salaha da take rik'e da biro da littafi ya ce "Kina rubuta korafin kowa ko?" A nutse ta ce "Eh Baba." "Ina Saddiqa?" Baba ya tambaya. Cikin sanyinta ta ce "Ga ni ". "To Bismillah". Kanta na kasa ta ce "Baba kawai ni babban tashin hankalina idan na hango gida irin gidanmu amma ya dare ya zama kufai. Idan na ji sha'awar na je gida sai na rasa inda zan dosa. Sai na yi kamar na zo nan sai kuma na tuna Yaya Asad ya dauko kune don ya barrantaku da mu, sai na fasa don ba ni da wajen zuwa". Kuka ya k'wace mata na gaske. Hankalin oga Asad ya yi wani irin tashin gauron zabi. Zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri fiye da kima. Gabad'aya ya ji kansa ya yi masa dundurus. Kawai a zaune yake amma babu nutsuwa a tare da shi ko kad'an. A wannan karon sai da Baba ya d'auki tissue ya goge fuskarsa. Cikin jarumta ya kalli Anisa da take zaune kusa da shi ya ce "Ke kuma fa Anisa?" Ta girgiza kai ta ce "Dangin miji na mini gorin gidanmu ya rushe wan ubanmu ya tafi da y'ay'ansa ya barmu saboda bak'in cikin uwarmu". Muryarta ta karye. Ta yi shiru ta kasa cigaba da magana. Tsawon lokaci ba wanda ya yi tari kowa tsit. Sai can Baba ya yi gyaran murya ya sake yin addu'a da neman tsarin Allah daga sharrin shaidan da hargitsin zuciya. Don ya fahimci gabad'aya yaran suna da hujjar an juya musu baya alhalin bai cancanji a yiwa Baba k'arami irin haka ba. Dukkansu kuma sun yarda an wulakanta Sulaiman akan Abida. Baba ya numfasa ya ce "Ina son kowa ya bude zuciyarsa a cikinku ya karbi gaskiya ya kuma rungumi hak'uri da afuwa. Duk wanda ya yi imani da Allah da manzonsa to ya yi hak'uri ya huce da d'anuwansa." Ya kalli Asad ya ga gabad'aya ya zama wani iri. Tashin hankali zane baro baro akan fuskarsa ya tausaya masa don kuwa dukkan yaran kowa ya bude baki laifinsa ne akan gaba. Bilki ma ta saya ne saboda mijinta ne. Ya ce "Asad menene taka matsalar?" Save Restricted Content Bot, [Nov 6, 2025 at 14:58] Mene ne taka matsalar Asad?" Ya yi k'asa da kansa, ya dago ya kalli mahaifinsa ya ce "Ba ni da hujjar da zan gabatar don duk hujjojina sun kawo sun kuma rushe bisa hujjar arzikin Baba K'arami zasu ci. Amma abin da nake so su mini adalci daya ne. Daukarka da na yi don nema maka lafiya ba laifi na yi ba, ba kuma zan yarda na yi kuskure akan hakan ba. Duk cikin kurakuran da suka jingina mini d'aya na karba na barin Abida a gida. Shima kuma a yanzu na rushe shi. Don duk cikinsu ba wanda ya k'alubalanci Sulaiman da fantsama duniya da ya yi ya barka da ciwon rashinsa, da kuma rainin da ya yi maka, ya barta da aurenta da k'aramin ciki. Don haka idan ina da son kai da son zuciya lah shakka kun fini . Maganar ban kawo daidaito ba, na d'auke baba na dawo da shi nan, akwia wani a cikinku da ya zo ya yiwa Baba k'orafi ko ya yi yunkurin d'auke shi kamar yadda na yi masa? Gabad'aya fa shata layi kuka yi da shi? Kai Ansari da kake fad'in ka zo ka gurfana akan ya karɓa maka aure, bayan haka sai yaushe ka zo kuma?" Ansari ya yi shiru. Oga Asad ya ce "Buk'atar kanka ce da nemawa kanka mutunci a idon iyayen matarka ya sanya ka zo, amma ba dan yana da rigar Baba k'arami a jikinsa ba. Da na d'auke shi, me yasa baku zo kun d'auke shi ba idan har ubannku ne da gaske, kuma kuna da buk'atarsa? Akwai wanda a cikinku ya taho dan ya duba shi tun ma kafin komai ya damalmale gabad'aya? Gabad'aya kun gamsu an ci mutuncin Sulaiman saboda bamu mayar masa da Abida ba. A daa na hak'ura da dukan da na yi niyyar yi mass na wulakanci da rainin da ya yiwa Baba na shiga duniya tsawon shekaru hud'u babu wanda yasan inda yake. Abida ce ta had'a su? Wacece Abida yaushe ma aka ba shi ita? Ba wani guda da ya yiwa Abida alkunya a cikinku. To a ina aka ce namiji ya tafi ya bar mace da ciki ba waiwaiye tsawon lokacin da wannan yaron ya yi? Wato ku mutuwar Baba gata da sangarta ta janyo muku kuna ganin baku da wani babba, komai zaku yine yadda kuke so babu mai taka muku birki. To kuwa a yanzu sai na zane shi, haka Hamida ki yi matuƙar shiga hankalinki, ki yi hankali da ni, ki kalle ni ki harare ni? Amma ai rashin kunyar karya kike yi me yasa kika gudo gaban Baba? Ko wanne irin laifi na yi muku auren Bilki da na yi bai ci ku huce da ni ba? Don da bana sonku da ban aureta ba. Amma na fahimci ke a wajenki ma zunubine aurenta da na yi saboda kin kwashe kayanki a gaban ma'aikin Allah. Ace ta haihu cikin jinya amma ki k'i zuwa ki ganta, bare ki ga abin da ta haifa, sannan kuma kika hana Ansari da Anisa su zo saboda nine mijinta kuma uban y'ay'an da aka haifa Hamida Hamida! Ta zumbura baki bata ce komai ba. Ta zumbura baki bata ce komai ba. Baba ya ce "Sassauta haka Asad ya isa haka". Don magana yake yi cikin daga murya da matsanancin fishi". Baba ya kalli Faruku ya ce "Yi magana Faruk ". A takaice ya ce "Ansari abin da yasa ban shiga cikin matsalar ko yin wani yunkurin komai ba a wanccan lokacin kid'ima na yi, tare da firgicin sannan na tsorata. Baba fa shine k'at to shima ga yadda ta kasance da shi a hannunku mussaman kai, to ni kuma fa? A wanccan lokacin kanka na zafin idan na yi magana kana iya faɗa mini komai. Sannan rashin zuwanku gaban Baba da nufin duba shi ko gaishe shi sai muka fahimci ku gabad'aya baku d'auki al'amarin Baba k'arami da muhimmanci ba kun tsaya ne a iya girman uwa da hak'kin a yi mata biyayya ta kowacce fuska, shi kuma uba ba shi irin wannan hak'kin. Bamu cire muku rigar Baba k'arami ba kune da kanku kuka cire ta kuka yiwa kanku tunbur. Duk abin da zamu yi muku ai saboda Baba ne to Baban kun nuna ba zaku bishi w ware sai mu yi ta binku don ku zo wajensa?" Ya jijjiga kai tabbacin ba zasu yi hakan ba. Save Restricted Content Bot, [Nov 6, 2025 at 15:02] PAGE 24 ... Jikin kowa ya yi tub'us da kalaman Farouku. Hatta Hamida kuwa. Ansari kuwa tuni ya gamsu iya gaskiyar Yaya Faruku kenan. Baba ya kalli Usman ya ce "Kai fa?" A takaice ya ce "Ba ni da matsala da kowa. Idan mutum ya huce nima na huce". Sulaiman ya daga hannu alamun yana son yin magana. Baba ya ce "Muna sauraronka". "Sulaiman ya ce" Yauwa Baba Usman ya yi mini ba daidai ba. A gabana akan idona da kuka zj ta'aziyar MAMI ya kalli Abida ya ce mata wai idan tana son tafiya da y'arta ya karbo a hannun Bilki. Bai fa tsawatar mata akan ta zauna a d'akinta ba a matsayinsa na wanta kuma dan'uwana aminina Sai yake kokarin sake tayar da wuyar rikici a halin tashin hankalin da muke ciki na mutuwar MAMI". Baba ya ce "Assha Usman Kaine ka yi haka?" Ba ja in ja ya ce "Na yi haka Baba, amma gani na yi sunsan girman uwa da muhimmancin bin ra'ayinta akan kowanne irin al'amarin da ta bijiro da shi. A lokacin na kalli k'wayar idon Abida na ga tana kallon Farha da wata soyayya irin ta uwa shiyasa na takaice mata wahala na tambaye ta idan tana buk'atar d'iyarta don kuwa itama uwa ce. Amma da yake ita bawa Bilki diya ne saboda alakarta da Baba K'arami ai bata karbeta ba." Gabad'aya Sulaiman ya yi lakwas don kuwa jirwayen Usman ya dage. Baba ya shiru kafin ya ce "Salaha fa?" Ta ce "Duk wanda na musgunawa ya yi hak'uri ya yafe mini, Nima na yafewa kowa". Baba ya ce "Allah ya yi miki albarka." "Abida." Ta nisa ta ce "Baba ina sake baka hak'urin gardamar komawa d'akina da na yi maka. Tabbas ka ce na koma na bijire, Duk laifin nan da ake jingina maka kai da daddy ni nake da alhakin d'aukarsa amma tunda na zama y'ar kuka dole ku shiga cikinsa. Ta kalli Sulaiman ta ce sun ce na koma ni na ki bisa hujjar zuciyoyinmu a tunzure suke komai zai iya afuwan marar dad'i. Allah me shaidar an yi haka. Laifi nasan na yi laifi, na janyowa Baba da Dady ma. Amma ina bada hak'uri, kowa ya yi hak'uri Allah ya kiyaye gaba." Gabad'aya jikin kowa ya yi sanyi don a yadda Abida take ba wanda ya zaci zata bude baki ya bada hak'uri a cikin taro iron hakan. Baba ya ce "To Alhamdulillahi Ina fatan kowa ya gama fad'ar abin da yake ransa?" Aka yi shiru. Ya sake maimatawa suka amsa da fad'in"eh. Amma oga Asad kala bai ce ba. Ya nisa ya ce "Alhamdulillahi ni yanzu a matsayina na uba na yafewa kowa. Allah ne shaidar da dukkan zuciyata na yi wannan kalamun. Amma fa Sulaiman ka yi mini laifin da ya mini ciwo, kukan da na yi a Kanka ban yi akan kowa ba, ba dan komai ba sai dan ka nuna mini k'arshen iyakata, ka nuna mini Abida na haifa ba kai ba. Tabbas na yafe maka sai dai mantawa Sai a hankali Idan ka tsaye kai da fata ka yi kokarin toshe kofofin da zan dinga tunawa. Tafiyarka ta sake rub'anya damuwa da b'acin rayuka da yawa. Tafiyarka ta cakalkala al'amura masu yawa. Amma Alhamdulillahi ka yi sa'a ka dawo ka tarar da sauran rayuwata ba dan haka ba da nadamar da zaka yi ba y'ar kad'an bace. Hankalin Sulaiman ya tashi daga Baba har su yayyensu suna k'alubalantar ya tafi ya bar Abida don Basu isa ba. Ta ya ya zai bude baki ya fadi abin da ta yi masa? Idan bai fad'a ba shikenan ya tabbata ya raina ubansu ya wulakantasu. Har su koma ga mahallici ba zasu daina kallonsa da wannan tabon ba. Amma kuma ya yi imanin idan ya fada su Hamida suka ji babu sauran sulhu. Zasu yi komai, zasu bantse matuƙar suka ji ta taɓa alafarmar MAMI ne." Ya numfasa ya ce"Baba ka yi hak'uri. Amma dare ko gobe dan Allah zamu zauna tare da kai da Yaya Faruku da yaya Asad". Save Restricted Content Bot, [Nov 6, 2025 at 15:05] Baba ya ce "Allah ya kaimu ko yaushe ni inan ku daidaita lokacin had'uwar a tsakaninku. Abida ta yi wuki wuki tasan laifinta zai fad'a don ya fita dava zargin ya rataye ya saboda ya raian Baba a idanuwansu. Hankalinta ya tashi amma ta samu salamar su Yaya Hamida ba su ji ba, ba kuma zai fad'a a gabansu ba. Zuciyarta ta yi nauyi, ko su Baba ma ba zata so su ji wannan katobarar ba. Kaifin harshe ya janyo mata nadama da kubucewar al'amura masu yawa a wajen Sulaiman. Ya janyo mata nadamar da har ta mutu ba zata daina kokawa ba don ta tabbatar lokaci zuwa lokacin Idan ya tuna ba dad'insa zata ji ba. Don ta riga ta gane Su suna da rik'o da kullaci kuma sun fi son uwarsu akan komai. A yanzu ma kunyar baba da tsoron abin da zai biyo baya ya hana dankara mata saki. Tunda ya tafi Kano bai nemeta ba Har ya dawo ta tabbatar asarar da ta yi babbace. Dan haka ta kud'iri aniyar yin hak'uri da duk abin da zai yi mata. Amma dai a yanzu zata daure ba zata dinga bibiyarsa ba. Idan Allah ya tarfawa garinta nono ta koma d'akinta ta yi ta bibiyar har ta shawo kansa. Sulaiman ya ce "Baba muna sake rokawa MAMI gafara dan Allah, dan Annabi ka yafe mata." Dukkansu suka Matso kusa da Baba suka hade waje d'aya suak maimaita kalaman Sulaiman Har da Bilki. Su oga Asad da su Abida suka bisu da ido suna kallon yadda suka hade da junansu tamkar sardine matan sun kewaye Ansari da Sulaiman. Baba ya ce "Na yafe mata tun ranar da ta rasu, ina kuma nema Mata rahamar Allah. Amma alfarmar ma'aiki ba zamu tsaya a gaban Ubangiji ba, na yafe mata duniya da lahira. Sulaiman ya dauki file din gabansa mai d'auke da takardu da mukullai. Sauaran suma kowa ya saka hannu suka rike. A hakan suka ce Baba idan ka yafe mata, to ga Ladi farm mun dawo da ita, ba tamu ba ce, ita da kanta da ka sadaukar Amma jikinta ya yi sanyi ta ce bamu ci gonar gabad'aya ba ta hanamu rabata. A yau kuma mun dawo maka da ita cikin gasgata kasonka ne yafi yawa a ciki, sauran kason ma da muke da hak'ki a cikinsa mun yafe maka duniya da lahira bamu da alaka da ita don munsan taka ce ". Idanuwan kowa sai da ya cika da k'walla hatta oga Asad kuwa. Yana kallon Bilki da ta ke safare a jikin Sulaiman. Ta ki shiga cikinsu ta k'alubalence shi ko ta k'alubalenci Baba Babba. Amma a yanzu ta shiga cikinsu tana nemawa uwarsu yafiya tare da mayarwa Baba Ladi farm cikin y'anuwanta. Yadda ya ga sun yi a gaban Baba gabad'aya sai suka bashi tausayi jarabawarsu akan uwarsu mai girma ne. Ba dan tasirin Baba k'arami ba da tabbas ko kallon inda suke ba zasu yi ba. Haka ma dangin uwarsu tasirin jini ne kawai ya sanya suke sonsu amma mami al'amuran da ta cakalkala masu yawa ne. Allah ya jiƙanta ya yi mata rahama kawai. Mafi munin jarabawar da namiji zai shiga rashin dace da mace ta gari. Mai take gaskiya, wacce bata siffantu da ilimin addini da aiki da shi ba, mai kuma tsananin kishi da hassada. Don sannu a hankali zata wargaza masa gida ta rushe ginin da yake tsakaninsa da y'anuwansa, ta jefawa y'ay'ansa rud'anin kowa baya sonsu ciki kuwa har da shi kansa ubansu. Duk juyin da za'a yi da irin wadannan matan ba zaka ga yadda kake so a cikin gidanka ko a tarbiyar yara ba. Shiyasa idan za'a yi aure a duba tarbiyar uwa a duba d'ab'iar yarinyar ba wai fara mai kyakkwar fuska ba. Kyakkwar zuciya da dabiun addini sune zasu daidaita maka al'amura. Ba dan Allah ya so Baba k'arami da rahama bata danne shi ba, da tun da ransa za'a yi wnanan tawarwatsen gidansa kuma sai ya gagari danginsa shiga ba kuma yadda za'a yi dole a hak'ura a sallama shi. Allah ka shirye mu kasa mu wanye lafiya. Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:13] *Surayya Gwaram* Baba cikin jarumta ya ce "Ina sake jaddada muku na yafe mata Allah ne shaidar hakan. A wannan lokacin Munira ta sadaukar muku da Ladi farm ba tare da nemi yardata ba, ni Kuma na amince da hukuncinta cikin gasgata ta yi abin da ya kamata. A yau kuma da kuka dawo mini da ita cike da yaƙinin kunsan tawa ce to ni kuma na bar miki ita duniya da lahira Har cikin zuc6na baku ne saboda mu ya'yana ne a yanzu kuma da rayuwata ya zo gargada ba ni d a bukartata. Idan Har akwia wanda ya dace ya mallaki Ladi farm to Faruku ne da mahaifinku, to shi mutuwa ya d'auke shi, Faruku kuma ya ci girma ya bar muku, ba kuma gillin komai a cikin bar muku Wallahi ". Sulaiman ya kallesu ya yi kasa da kansa a hankali ya ce "Ya zamu yi?" Suka yi magana kasa kasa. Sai suka mike suka tunkari Faruku suka tsugunna a gabansa suka had'a baki wajen cewa "Yaya Faruku ka duba alafarmar maaikin Allah da girman mahaifanmu, ka karbi kyautar da muka yi maka. Baba ya bamu mun karɓa da godiya, mu kuma mun baka da dukkan zuciyarki don munsan ba abin da kake so ka k'arar da dukkan dabarar wajen ganin ta kafu irin Ladi farm to a yau mun dawo maka da itaa matsayin taka halak malak. Bai ce komai ya saka hannu ya karɓa hawayen da suke idanuwansa suka zubo akan fuskarsa. Bilki ta saki ajiyar zuciyar nutsuwa don kuwa tabbacin ya huce ne. Da jarumta ya ce "Na gode muku Allah ya saka da alheri. Zan cigaba da kula da ita da dukkan iyawata, sai dai ban karɓa a aml matsayin tawa ba, na karɓa don ba kula da ita. Amma bata kowa ba ce, ta zama wakafi Ga baba Babba da Baba K'arami. Duk kuma wanda yake son wani abu a cikinta kaitsaye zai zo ya co ko ya sha amma ba ta kowa ba ce, ba mai gadonta ila yaumil kiyama za'a yi ta juya kud'in da zata dinga samawar wajen yiwa marayu d addini hidima da niyyar Allah ya kaiwa iyayenmu." Kowa ya amince da hukuncin Faruk. Wani irin abu da ya tokare zuciyar Bilki ya fad'a mata. Haka sauaran ma sai suka ji nauyin zukatansu ya warware. Baba ya dinga fad'in " Alhamdulillahi, Ubangiji na gode maka da na ga wannan rana, Allah ka saka k'arshen waki'ar da zan sake ga ni kenan. Allah ka jefa soyayya da tausayin juna a zukatan dukkan yaran nan. Allah ka kore shaidanun da zasu shiga cikin zumuntarsu. Allah ka saka albarka a cikin dukkan zuri'arsu da dukiyarsu, ka Basu lafiya ka saka su rayu cikin Salama ka azurta mu da zama yanki daya cikin aljanna. Allah ka jiƙan Isa da Habiba.". Kukan da Baba yake yi bai boye farinciki da jin dad'in da ya ji ba. Daidai lokacin ya ce a kira Momi. Ta zo ta ya fad'a batun Ladi farm da matsayar d saka cimma. Murna kan murna ta yi tare da addu'ar Allah ya yiwa kowa albarka tare da jaddada muhimmancin hak'uri da yafiya. Suna cikin haka aka fara kirayekirayen sallah. Anan falon suka yi sallah gabad'ayansu. Baba ya ja su sallar da suka idar suka mike suka yi nafila. Addu'a saosia Baba ya yi a bayyane suna amsawa da amin. Bayan an idar matan suak shige daki. Salaha da Hamida aka shiga hirar yaushe rabo. Hamida aka warware tamkar ba itace ta taho a dole ba. Bilki da Abida su dama tuni suka yi nasu sulhun. Saddiqa da Anisa suka samu aminci.a zuciyarsu tunda Yaya Hamida ta warware to sun suma suka saki ransu tamkar suna gida Funtua. Baba da mazan suna falo. Sai da aka yi sallar la'asar. James ya kawo abinci kala kala da Bilki ta saka Angela da Alti su yi kafin su taho. Baba da dukkan y'ay'ansa suka ci abincin. Aka yi hotuna da vedios tamkar ba za'a daina ba. Zuciyar kowa ta warware salama da soyayyar juna suka maye zafi da ƙullaci. Sulaiman ya ce "Bilki kamo mana Munira". Baba Babba ya ce "Allahu Akbar! Babanku kad'ai ke tunawa da ita yau kuma kaine ka tuni da ita lallai Babanku guda". Bilki ta k'irata vedio call. Cikin sa'a tana kwance akan gadonta ita kad'ai. Maimakon Bilki ta yi magana sai kawia ita da Abida da su Anisa suka jingina a jikin Baba ana haska mata fuskokin kowa. Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:15] Ta zabura ta tashi daga kwanciyar da take. Cikin mamaki ta ce "Kai Kai Maigado kina da babban tukuici ki ce yau kowa yana gaban Baba. Ice dai kowa ya yi tuba ko?" Suka dinga dariya. Ta ce "Baban Abida yau kana cikin alheri dumu dumu". Ya ce "Alheri mai girma kuwa Munira." Ta ce ",To Alhamdulillahi Baba barka, barka Allah yasa k'arshen jarabawar da zamu sake ganin kenan". Da karsashi ya ce "Ameen Ameen Munira ina yaran da maigidan?" "Suna makaranta shi kuma Yana wajen aiki". "To Ki gaishe shi." Ya ce Baba tsaya, dan Allah waye ya tuna da ni don nasan babana da baya mantawa da ni idan an hadu haka babu shi". Baba da alfahari ya ce "Ai kuwa yanzu ma Sulaiman ne ya ce "A kamo ki". Ta yi turus. Don jingine Abida da ya yi na shekaru hud'u ba k'aramin bugunta ya yi ba. Ya danne ta ce "To a ba shi wayar". Aka mik'a masa ya ce "Munee how far?" Ta rike haba ta ce "Gaskiya Yaya Sulaiman da Babanmu na nan ba zaka fantsama duniya irin haka ba. Ya ya haka? Kasan da na kud'ire idan ka dawo sai na gurfanar da kai don bibiyar zullimin da ka jefa mu na kana Raye ko kuwa ka mace." Ya murmusa ya ce "Double sorry Barista a yi hak'uri na dawo ba Zan sake tafiya ba". Ta ce "To yanzu nawa Abida ta yanka maka na diyya don nasan asussunka zai san ka jingineta". Ya yi gajeriyar dariya ya ce "Ba wannan batun ai Munira ". Itama ta yi dariya ta ce "Ai shikenan. Na gode Yaya Sulaiman Allah ya jiƙan Babanmu da Mamie na huce da kai". Har ransa ya ji dad'in addu'ar da ta yi mussaman da ta had'a da mami. Ya amsa da "amin muni na gode, na gode sosai Allah ya bar zumunci. Ki gaida yara da Babansu". Daga haka aka dinga bawa kowa suna gaisawa. Har aka yi sallama da ita tana jin tamkar ta yi tsuntsuwa ta sauka a cikinsu don ta taya Baba Babba farincikin da yake ciki. Abida tana son a yiwa Sulaiman batun ya bata gidan da zata zauna, tana jin tsoron kada ya yi batun da zai wargaza ta a wajen su Hamida. Dole ta shamik'e take ta yak'e Amma gabad'aya ba a nutse take ba. Ganin magariba ta kawo kai ya sanya Baba ya ce "Duk ku bani hankalinku nan. Daga yau na haramta ku tattauna rikicin Ladi farm. Na hana, na haramtawa kowa a cikinku. A yanzu ba ta kowa ba ce, ku yi komai a cikinta. Ku ci duk abin da kuke so na cikinta, ayi batun kasuwanci da waɗanda suke bukatr taimako tunda wakafi ce. " Suka amsa da fad'in"In sha Allah baba Allah ya kara lafiya ". Ya saka hannunsa na dama a kasa ya ce "Duk wanda ya yi imani da Allah, da manzonsa da ranar lahira, ya kuma yarda ni ubansa ne to ya d'ora hannunsa ya yi mubaya'a babu sauran gilli da tashin tashina a tsakaninmu gabad'aya". Oga Asad ya yi saurin d'ora nasa akan na Baba. Faruk ya dora. Ansari ya d'ora, Hamida da Salaha suka d'ora. Abida ta dora nata, Saddiqa da Anisa. Usman ma ya dora. Abida tana kallon Sulaiman zuciyarta na harbawa. Ya dora amma ba duka hannunsa iya rabi ya dosana. Ya ce Baba na d'ora, sauran sai dawo mun zauna akan alafarmar da na ce zan neman sannan komai na zuciyata zai warware". Dan haka bai yarda ya saka dukkan hannunsa ba. Ya bawa Faruku dariya sosai don yadda ya makale rabin hannun abin dariya ne sosai. A hakan Baba ya sake yin addu'a soaai. Sannan ya ce "Alhamdulillahi ko yanzu na mutu ban bar baya da k'ura ba. Allah ya sake had'a zuciyoyinku ya rufa muku asiri duniya da lahira." Gabad'aya suka ce "Ameen Baba". Faruku ya yiwa hannuwansu a yadda suke hotuna. Sannan kowa ya cire nasa hannun. Daidai lokacin oga Asad ya ce da Bilki ta tashi ya mayar da ita gida saboda yara yini guda basu sha nono ba. A hankali ta ce "Baban Bilkisu ko James ya dauko su tare da Alti?" Ya girgiza kai ya ce "A a mu tafi kawai ai an gama komai magharib ta kawo, yini guda su kad'ai". Kan dole ta bishi suka tafi. Don yadda ake hada hada ba zaka so tafiya ba. Magariba ma tare suka sake yi. Hamida da ta zo da ƙyar sai gata ta bugawa mijinta waya da kanta akan ya yi mata hak'uri zata kwana a gida. Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:17] Gobe Idan zasu tafi a kawo ta. Dad'i ya lullube shi ya ce "To yanzu dai mun fita da Justice Yunusa muna kusa da wuse din zan biyo na gaida Baba tunda jirgin sassafe zamu bi". Ta ce "Baban ummu da zaka lamince mini ba gobe zan tafi ba. Ina son na dan kwana biyu Salaha tana gari itama ta zo." Kaitsaye ya ce "Na baki sati guda ki yi zamanki tare da y'anuwanki. Amma ya ya za ki yi batun kaya? Kin ga irin gaddamarki dai da na ce ki debi kaya da dama kika ce kala biyu sun isheki tunda ba dadewa za ki yi ba.". Ta ce "Babu damuwa sai na saka na Salaha kasan itama ba auki gareta ba. Ko kuma na je boutique a aljihun Yaya Asad ". Ya ce "Ho Hamida tun yanzu za ki fara yi masa lissafi? Ta yi dariya ta ce Baban ummu da makudan kudade fa zan dawo, shekaru hud'u bai bani kudin kayan sallah da na azumi da ya saba bamu ba, ba zan bar Abuja bai lissafa abuna ya bani ba." Ya yi dariyar k'arfi halinta. Ya numfasa ya ce "Yanzu me kika siyawa baba da kudin da na baki ki yi masa tsaraba? Ta fara dawurwarar ai ta mance su a Kano gabad'aya ta shafa'a." Ya ce "Allah ya shirye ki kawai. Yasan tunda tare suka zo ba zata ba sai dai ya siyo da kansa kud'i kam sun zama nata. Amma tunda ta sauko ta rungumi sulhu ba abin da ba zai mata ba. Haka nan zai dage ya saita yaransu da suke kokarin bijire mata. Tunda shi suna shakkarsa. Kayan abinci da ruwa da lemo mai yawa ya kawowa Baba da rafar yan dubu dubu guda biyu. Baba ya dinga yi masa godiya da fatan alheri. Bai tashi ba sai da ya sake jaddada ya k'ara hak'uri da Hamida. Ya kuma gode da yadda yake rik'e da ita. Tana gefe tana jin tamkar an tsumduma ta a aljanna yanzu kam sai ya samo wani abin da zai fad'a dan ya musguna mata ba dai ta watsar da ubanta ba. Da zai fita ta bishi tana raragefe. Haka ya d'auki rafa guda ta dubu ce "Ga pocket money. Saura ki boye ki dinga jiran sai an yi miki". Ta marairaice ta ce "Baban ummu kana bada ni akan kud'i ". Ya murmusa tare da fad'in"Ai kin bari na gama gane ki. Ke da kanwarki Abida bansan me zaku yi da kud'i ba". Ta yi dariya ta ce "A a wannan ta kere ni a son kud'i tun tana karamarta ta tara abin duniya. Labari idan Abida ta bayar sai an biyata. Ya jijjiga kai ya ce "sai dai ku yi taya amma batun ta kere ki bai taso ba." Ta kwashe da dariya daga haka suka yi sallama ya tafi. Ta koma ciki ta wuce baba da mazan a falo. Zuciyar Baba fes yau shine rayuwa ta dawo masa daidai. Y'ay'ansa dana d'anuwansa suna shige da fice a gabansa cikin walwala. Motsi kad'an yake fad'in Alhamdulillahi ba kakkautawa. Bayan magharib Usman ya yi sallama ya fara tafiya. Faruku ma ya yi sallama akan sai da safe. Saddiqa ce kawai ta tafi, mijinta ya zo ya d'auke ta. Salaha Hamida Abida Anisa kwanan zaune suka yi. Hira soaai suka yi mai sanya nishadi. Washegari suna karyawa abida ta d'auke su a motarta suka rankaya gidan Bilki. A farfajiyar gidan suka tarar da oga Asad cikin kakinsa. Yana ganinsu ya juya da sauri ya koma ciki. Da azama Bilki ta gan shi ya dawo. Ya saka hannu ya dauki baba K'arami. Ya kalleta ya ce "Yi maza ki kawo mini na hannunki". Ba sukuni ta ce ", Lafiya kuwa?" Ya ce "Ki dai biyo ni da shi yanzun nan". Ta saba yaro ta bishi. Ya karbe shi ya kwantar da shi kusa da d'anuwansa akan doguwar kujera. Ya kalleta ya ce "Da Hamida da Ansari ba zasu gansu ba sai sun biya kudin ganinsu, tunda Basu komai ba laifina ya hana Su zo su ya ya'yansu.. Na ga su Hamida sun zo shiyasa na dawo dan na boyesu." Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:19] Bilki ta murmusa tare da fad'in "Amma dai an yi mubaya'a a gaban Baba. Kai ka fara aminta tunda kai ka fara d'ora hannunka akan na Baba. " Ya ce "Hakane to d'auke daya mu sauka". Ya saba Baba Babba a kafaɗarsa, ya fara fita, ta bishi a baya tana d'auke da Baba K'arami. Daidai lokacin sun shigo cikin falon. Asad ya bawa Hamida na hannunsa, Bilki kuma ta mik'awa Salaha na hannunta. Hamida ta zubawa yaron ido tana ganin fuskar oga akan fuskar yaron. Haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Bilki da oga Asad na rashin zuwanta ganin yaran. Amma haka ta matse ta waske. Suka gaishe shi ya amsa sannan ya fice. Daidai lokacin da junior ya fito daga wajen Alti don jiya da suka zo tare da Salaha kin bin ta ya yi saboda Farha da Noor. Ya zubawa Hamida ido. Sai kuma ya kalli Abida ya ce "Ammi kamar Maman Kano". Abida ta ce "Ai kuwa ita ce junior". Gaban Hamida ya yanke ya faɗi da ta ga junior. Ba buk'atar a fad'a mata dan Sulaiman ne don kammaninsu guda. Kunya ta rufar mata fiye da kunyar rashin zuwa ganin twins. Inama lokacin haihuwarsa ta yarda sun taho tare da Bilki? Shi ya santa amma ita bata san shi ba. Murya ba amo ta ce "Zo a ina kasan ni?" Ya je kusa da ita ya ce "Ammi tana nuna mini pics dinki ta ce "Ke ce maman Kano ce kuma sister din Dadyce kuma sister dinta ce". Hamida ta ji tamkar ya doka mata guduma. Ta yi dif ta kasa magana. A ranta kuma fadi take yi wato Abida tana nunawa d'anta su tunda dan yaro irin haka duk ya gane su. Ta kasa cigaba da yi masa magana tsabagen an kashe ta da kunya. Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:41] *Dingishin kwado* Sai kuma ya koma kusa da Abida yana fad'in "Zan biki ammi". Abida ta ce "Tare zamu tafi, Dady ma ya dawo". Ya ce "To yau zamu tafi gidanmu ne?" Ta girgiza kai ta ce "A a". Ya ce "Ya ce fa yana dawowa". Tace "Idan mun je Sai ka tambaye shi". Alti ta shigo musu da kayan motsa baki. Ta zauna ana hira mai dad'i tamkar komai bai faru ba. Sai yamma Salaha da Abida suka tafi suka bar Hamida zata kwana, gobe Abida zata dawo ta dauke ta. Bayan sun tafi Alti ma ta kauce ta basu guri. Hamida ta ce "Maigado ikon Allah yawa ne da shi. Allah dai ya yi Yaya Asad Sai ya aure ki. Ni dai yanzu na huce da kowa, na yi taubayan nasuha. Ki bi mijinki, nima yanzu zan gyra kurakuran da na rayu akansu. Tunda Allah yasa baba ya yafi kowa to duk wanda Zan faɗawa ya ji to muma mu yafe keta da warakin da suka gwada mana saboda babu idon ubanmu. Yadda ya yafewa uwarmu haka nake son Duk mu yafe masa gorin da ya janyo mana. Maigidan nan ma na yafe masa Har cikin zuciyata. Shiyasa na zo masa kwana." Bilki ta murmusa tare da fad'in "Oh ba ni kika zo wa ba kenan?" Da azama ta ce "A a gunsa na zo, kafin na tafi zan dawo na ki zuwan". Bilki ta sake murmusawa har cikin ranta ta sake samun gamsuwar rikicin gidansu ya k'are. Don bangrensu Hamida da Ansari ne masu kafiyar masifa kuma suna da tasiri a cikinsu. Idan har yadda ta sauko haka Ansari ya sauko ya karbi sulhu to tabbas babu saurin rikici don Abida ta yi rauni. Yaya Usman kuma Baba zai danne shi tunda suma sune kaffafu a nasu b'angaren. A farfajiyar suka tarar da Sulaiman yana zaune. Ansari ya fita da motarsa. Salaha ta wuce bayan ta ce "Yaya Sule wai ina tsaraba ta ne?" Ya murmusa ya ce "Salaha ai ba haka tsakaninmu mu bar wannan batun kawai.". Ta wuce tana fad'in "To shikenan, an bar shi". Abida da junior suka nufi inda yake. A hankali ta ce "Yaya Dr Baban junior kwana biyu". Ya d'auke kai ya ce "Kwana goma ma". Ta yi dariya kad'an ba ta ce komai ba. Junior ya ísa kusa da shi ya ce "Dady ka dawo, yaushe zamu tafi gidanmu to?" Ya yi masa murmushi ya ce "Ammi zaka tambaya. Ita ta dawo da ku nan, bansan sadda zata mayar da ku gidanmu ba". Zuciyarta ta harba. Murya ba amo ta ce "Ina ne gidan, a wacce unguwa ne?" Ya kalleta tare da mamakin yadda take ganin zai zauna a Abuja. Tsakaninsa da Abuja ya shigo ya yi uzzirin da ya kawo shi ya juya. A yanzu ma don Baba ne kawia ya sanya shi zuwa har da yin kwanaki. Ya d'auke kai ya ce "Junior shiga ka yi alwallah ka zo ka mu tafi masallaci." Ya juyawa kuwa ya tafi yin alawala. Ta ce "yaron nan ya isa a saka shi a makaranta, sa'anin haihuwarsa tuni an saka su, shima ya matsu a saka shi. Don Allah ka cire yaron nan a cikin matsalarmu". Kansa tsaye ya ce "Wai ban ce miki na bar miki shi ba ne?" Gabad'aya ta ji numfashi na neman gagararta zuk'a. Ta jijjiga kai ta ce "Baba ya yafewa kowa dan haka nima za'a iya yafe mini. Baba ya ce wanda ya yi imani da Allah da manzonsa kowa ya huce ya yafewa d'anuwansa ashe kai baka d'auki wannan batun ba?" Ya ce ban dauka ba tunda suna mini kallon na jingine ki ne saboda na wulakanta baba. Dole su san abin da kika yi don su gane ban raina baba ban kuma wulakanta aure ba". Idonta ya ciko da k'walla. Ta ce "Ka fad'a musu babu damuwa. Amma ka tabbatar ko da ka bar mini junior to dawainiyar da na yi, da wadda na yiwa kaina ban bar maka ba". Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:44] Ya ce "Ke ce kudi suke gabanki, fad'a mini nawa kika kashe?" Ta ce "Bari na d'auko littafin." Ta juya da sauri ya bita da kallon mamaki. Zuciyarta d'aya fa lissafin take yi da gaske. Bata jima ba ta dawo bayan ta ce da junior Dady ya ce ya jira sai ya K'ira shi. Kusa da shi ta zauna ta mik'a masa littafin. Ya karɓa yana bin rubutun daki daki. Ya kalli jimillilar lissafin. Ya dago a kidime ya ce "Wai ke lafiyarki k'alau kuwa?" Ba alamun kaduwa ta ce "lafiya sumul kuwa?" Da mamaki ya ce "Kina nufin kin kashe zunzurutun kud'i har milyan dari uku da sittin Abida?" Da dukkan gaskiyarta ta ce "Wasu ai diyya ne, wasu na kwanakin da na shafe cikin kewa ne, wasu na kuttun da aka dinga kunsa mini ne a inda kake ganin ba a yi maka alfarma an mayar maka da Ni ba, saboda sun haife ni, duk zaman nan na yi ne cikin taka tsantsan da zullimi ga kuma rashin fuska a wajen Baba da Momi saboda sun ba ni umarnin na koma d'akina na taurare.Wasu na yadda bamu da y'ancin yin walwala ne Ni da junior a gidan nan. Wasu na yadda na zama marar daraja ne a gidan yayana. Kuma ba kowa ya janyo mini ba sai kai. Wasu na wahalar raini da tarbiya ne da na yi ni kad'ai ". Ya mike tare da mik'a mata littafin ya ce "To bari sai na fara fashi da makami." Ta karɓa ba tare da ta ce komai ba. Ta juya ta tafi. Shi gabad'aya ma mamakinta ya kashe shi tabbas bai zaci ta kai nan ba duk inda yake zatonya ta kerewa tunaninsa. Yo ko milyan sittin din kai ta ambato mass ai ya yi mamaki bare wannan zunzurutun manyan kuɗaden. To wai me ma zata yi da su ne haka? "Dank'ari". Ya furta a bayyane. Yayin da Abida ta kasa cigaba da jarumta. Kuka take yi sosia a d'akinta. Ta kira Faruku a waya. Cikin kuka ta ce "Yaya Farouku ka yiwa Allah ka shiga tsakanina da Yaya Sulaiman. Ta tsara masa komai da suke tunda suka dawo. Ya rarrashe ta akan ta kara hak'uri. Da iyakacin gaskiyarsa ya ce " Amma ba zan tilasata shi ya zauna da ke akan dole ba. Idan yana sonki zai d'auke ki ne ku tafi. Idan kuma ba ya sonki hakan ba shine k'arshen farinciki ba sai ki yi hak'uri. Tana son ta faɗawa Faruku abin da ta yi masa amma harshenta ya yi mata nauyi. A daren wannan ranar Faruku ya zo gidan. Kaitsaye d'akin da Sulaiman yake ciki ya nufa. Cikin sa'a shi kad'ai ya tarar da shi Ansari bai dawo ba ya yi nisan kiwo. Da girmamawa Sulaiman ya dinga fad'in "Yaya Faruku sannu da zuwa. Barka da dare, ya ya iyalin?" Ya amsa da walwala sosai tare da zama a gefen gadon. Faruku ya ce "Zamu yi magana. Ka yiwa Allah ka fahimce. Duk runtsi ba zan k'i ka ba. Ba zan bi bayan karya ba". Sulaiman ya ce 'To na kuma gode". Faruk ya ce "Wai ka ce ka bar mata junior?" "Tabbas na fada mata kuma itama ta san ina da hujjar da zan fad'a mata hakan akan yaron" Sulaiman ya fad'a kansa a k'asa. Yaya Faruku ya ce "Yanzu tunda Baba ya yafe mana, ya ce mu yafi juna, ai komai sai ya wuce a tsakaninku mana". A nutse Sulaiman ya ce "Ai saboda matsalata da ita ya sanya ban d'ora dukkan hannuna akan naku ba. Ni yanzu kai da oga nake jira da Usman mu zauna da ita a gaban Baba. Idan aka yi sannan ne zan samu sassauci a zuciyata ". Yaya Faruku ya ce "Ni kam da so nake yi komai ya wuce . Na kashe koma menene dukkanku kowa da inda ya yi kuskure. Dan haka na kashe batun." Nan da nan ya girgiza kai tare da ce wa "A a bai kasu ba gaskiya. Ai tunda a farkon al'amarin aka zuba mata ido ta yi yadda take so, to nafi son a baje maganar a faifai don kowa ya huce gabad'aya. Idan na yadda aka tafi a dukunkune to fa zan rayu ne kuna mini kallon na ci mutunci baba ta hanyar jingine Abida a gabansa. Ni kuma na san ita ta jingine kanta". Yaya Faruku ya zubawa Sulaiman ido yana aiyyana shima kaffaffe ne tabbas. Ya numfasa ya ce "Sulaiman ya kamata ku fuskanci gaskiya fa. Ka janye wannan maganar kasan ba k'aramar magana ba ce idan aka fasata ta ya ya zaka ce ka bar mata yaron da kowa ya ganka ansan kaine ubansa" Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:47] "Yaya na sa ni mana. Ni ban ce mata ba d'ana ba ne ai, na ce na barta mata ne kawai". Faruku ya numfasa ya ce "Yanzu Sulaiman ace sulhun da aka yi jiya bai wanke komai ba?. Tunda ka iso hankalinsa bai kwanta ba, idan ita mace ce bata da hankali sai kuma ka biye ta ku sake tayar masa da hankali gabad'aya?" Yaya Sulaiman ya d'ago idanuwansa ya zubasu kan na yaya Faruku, ya ce "Abida fa har yau din nan bata gama risina ba. Yau ta bani hak'uri gobe ya yi watsi da ni, sannan har ta samu kuzarin ce mini na biyata makudan milyoyin kudi." Faruku ya ce "Ai yarinya ce ka yi hak'uri ". Wani abu ya tokarewa Sulaiman. Abidar ce yarinya?" Ya bude baki zai ce ba wata yarinya Sai ya tuna irin haka ya faɗawa oga Asad akan Bilki. Abida kuwa ai k'anwarta ce. Kan dole ya had'iye raddinsa ya yi shiru. Ya fesar da iskar b'acin rai ya ce "Tsakani fa da Allah an yi mini ba daidai ba Yaya Faruku. Ni fa kawai shiru na yi amma kai ma na jin zafinka akan wannan al'amarin. Me yasa a wanccan lokacin baka motsa mata k'wanjin ta dawo d'akinta ba? Me yasa baka nuna mata girman hakkina a kanta ba? Ban mata komai ba, ita ce ta mini laifuka masu ciwo da wuyar mancewa. Ko ban cin arzikin komai ba a wajenta sai na ci na jini. Amma ta iya tsayawa a gabana tana fad'a min dama ba sona take yi ba, auren cimma manufa ta yi da ni, mafi munin kuskuren da ta yi mini da ta furzar da munana maganganu akan uwata! Ai mami uwartace aurena da ita kuma ya sake kara darajarta a wajen Abida. Amma tsabar tsaurin ido da tink'ahon yadda take so haka ake yi mata, ta zage mini uwa akan idona sannan ta kwashi jiki ta tafi gida, aka kuma bata mafaka, bayan ta sha magani don ta cire ciki bisa hijjar bata son had'a zuri'a da uwata. Sai kuma Allah ya nuna mata iko ta haife shi ". Ganin da ya yi Sulaiman ya kai kololuwar fusata ya sanya ya sanyaya murya ya ce "Da kasan dalilin da yasa aka barta ta zauna din da ka gane ba mafaka muka bata ba, aurenku muka bawa kariya. A lokacin cikinta k'aramine ya zo ya fara kokarin faduwa ga jininta ya hau. Ta kuma ce idan aka tilasta mata ta koma hankali ba zai taba kwanciya ba. Ga likita ya ce tana buk'atar nutsuwar zuciyata saboda cikin jikinta ya zauna sosai , mu kuma muka tsareta tare da bawa cikin kariya. Ga Sulaiman nan tamkar ka yi kaki ne, lamarin mata ba'a biye su yanzun nan sai su yi abin da zasu jefa kansu cikin *Fargar Jaji (Janafty)*. Yanzu tunda kai ne babba kuma namiji ka yi hakuri komai ya wuce dan Allah Sulaiman ka ga dai yadda hankalin Baba ya fara kwanciya dan Allah kada ku tayar masa da hankali. Yaya Sulaiman ya numfasa ya ce "Wai yanzu so ake yi na je na tare ta na bata hak'uri ta dawo ta zauna da ni?" Cikin rarrashi Yaya Faruku ya ce "Maganar zaman da za'a yi zaka janye, sai ka sake daurewa ka d'auke ta zuwa gidanka shike nan maganar ta wuce, ina tabbatar maka Abida ta yi laushi Sulaiman ". Sulaiman ya ce "ka yi hakuri amma ba zan dauke ta da kaina na mayar da ita ba. Yadda ta fito da kanta, da kanta zata koma matuk'ar tana son zama da ni". Da hanzari Yaya Faruku ya ce "To ina ne gidan da zaku zauna ni sai na kaita da kaina inace shike nan?" Murya ba amo ya ce "Inda ta baro, Funtua zata zauna! Yaya Faruku ya yi shiru yana jin matuk'ar basu bi Sulaiman a hankali ba rikici ne zai sake barkewa a tsakaninsu bayan wanda aka yi akan Ladi farm. Ya riga ya gane Sulaiman bai fahimci da kyakkwar manufa suka bari Abida ta zauna a gida ba. Don haka zai iya yin komai tunda yana ganin basu yi masa kara ba. Tunda y'anuwansa ma sun kalubalance su da rashin yi masa adalci. Ya nisa ya ce "Aikinta fa Sulaiman? Inace kai ma kana shiga specialist Hospital na nan Abuja". Ya murmusa ya ce "Ko ina zan iya aiki ai Yaya Faruku ba ni da matsala akan hakan". Yaya Faruku ya ce "To ku zauna a gidana na Gwarinfa kafin zuwa lokacin da zaku koma Funtua. Ai yanzu gyaran da yake gidan ba kad'an bane tunda ya dade a rufe". Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:50] Gaskiya fa Yaya Funtua zata tafi, ni na riga na saka an gyara gidan gabad'aya dan haka ta koma can ta zauna, da amarya zan zauna a nan. "Sulaiman! Yaya Faruku ya k'ira shi da muryar gargadi. Bai amsa ba amma ya sha mur. Ya ce "So kake Baba ya sake rafkewa ko? Idan an bata maka ba zaka yi hakuri ba? Hankalin mace da na namiji ba daya bane ai." Ya za'a yi da sha'anin mata dole sai hakuri. " Sualiman da sauri ya ce "Yaya Faruku idan hakurin ba zai zama akwai wulakanci a cikinsa ko cutarwa ba. Amma Wallahi ta daina yaudarar kanta da ce wa zan nemi sulhu da ita." Da azama Yaya Faruku din shi ma ya ce "Dama tunda ita ta fara tsokanar ai ba zaka bata hak'uri ba. Amma idan ta k'ira wayarka ko ta yi maka message ka dinga amsawa. Tabbas ta yi laifi, Kuma ko Ni nan Sai na Mata ba dad'i, ka yi hak'uri, amma kaima hukuncin da ka d'auka ya yi tsair6da yawa shine ya bani kuzarin sake baka hak'uri akan ka bata dama ta gyara kuskuren ta." Ya ce "Gaskiya ka yi hak'uri mu zauna da ni da ita da ku. Idan ba haka ba zuciyoyi ba zasu huce ba". Faruku ya rasa yadda zai yi da shi. Ya ce "To ai shike nan ku da Babanku ni kam na gaji gaskiya! Ya sassauta ya ce "Dan Allah yaya Faruku ka fahimce ni, ina son a huce ne gabad'aya." Ya ce "Na fahimce ka da dukkan zuciyata." Washegari sassafe Sulaiman ya kai Ansari airport ya tafi Maiduguri. An rabu lafiya da shi, ya kuma karbu sulhu da yafiya da dukkan zuciyarsa. Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:19] *Dingishin kwado* PAGE 25 Karfe sha d'ayan safiya duk suna hallare gaban Baba. Oga Asad, Yaya Faruku, Usman, Sulaiman da Abida. Cikin nutsuwa Sulaiman ya rattabo irin halin tsaka mai wuyar da ya shiga a lokacin ake danbarwar Ladi farm. Zullimi da rud'anin da ya shiga bai samu sassauci da rarrashi daga Abida ba. Haka ya zama desperate gida da waje ba nutsuwa a tare da shi. Duk irin rarrashi da kwantar da kan da ya dinga yi mata bai saka ta samar masa da nutsuwar da ta dace da halin da yake ciki ba. Zaman wurinsu ma ta daina yi barci zai kawo ta shima yana shiga dakinta zata rufe k'ofar. Ana idar da sallar asuba zata sake ficewa. Duk ya yi hak'uri akan hakan tunda yasan MAMI ta yi ba daidai ba. Ya dago kansa ya ce "Sai kuma ta kasa gane irin hak'uri da taka tsantsan din da nake yi don kada komai ya sake k'wacewa. Ta tsaya a gabana ta zagi MAMI irin zagin tsamar nama da babu tarbiya da mutunci a cikinsa. Ganin idona na ga maganin lalata ciki a bakinta wanda hakan ya sanya jini ya balle mata. Duk izgilin da ta yi mini na zagin uwata hakan na kwashe ta zuwa asibiti da kaina duk da zuciyata na ingiza ni na mata dukan kawo wuka sai ta yi jinyar da hujjar. Amma saboda kai Baba sai ban yi hakan ba. Duk hidimar asibitin ni na yi alhalin nasan ita ta janyo ciwon da kanta. A hakan na daure nake ta zarya. Sai kuma na ji daga asibiti ta taho Abuja. Zuciyata daya na gamsu akan nasan zaku korota tunda ban sake ta ba, ban yi mata komai ba. Sai kawai na ga an barta, a yiwa Allah a duba wannan batun ya ya zan ji ne a zuciyata?Dole na zaci dukkanku da kuke da iko da ita kun gamsu na yi laifin da ya cancanci na rasa y'anci akan aurena. Shiyasa ban zo ba. Zagin mami kuma da ta yi ban sake ta ba. Billahillazi lah illah ha illah huwa nauyinka na ji Baba. Don kuwa babu macen da zata yi mini hakan a duniya na cigaba da zama da ita". Hawaye ya k'wace masa. Daga oga Asad har Faruku jikin kowa ya yi sanyin. Hatta Usman da yake da ra'ayi irin nata jikinsa ya mutu tub'us. Usman ya fara cewa "Lallai ta yi ƙaton laifin da yake da ciwon gaske ". Baba kuwa ya ce "A a lallai Abida ta kerewa tunanina Ai ba matar zama ba ce. Ni kaina ba zan zauna da mai zagin iyaye ba don mace ta gari ba zata yi wannan jahilcin ba". Abida ta rushe da kukan tashin hankali. Cikin kuka ta ce "A yiwa Allah a yi mini hak'uri a kuma fahimce ni. Ba kowacce mace ce zata iya tsallake halin da nake ciki ba. Ace uwar miji da mijin da y'anuwansa sun dunkule suna k'alubalantar uban mace da zalunci har a maka shi a kotu? Dan Allah a duba da kyau. Amma na janye kalamaina, na bada hak'uri kuma ni bansan ma sadda na fad'a ba. Wallahi jinnul Ashiq ne da suka hana ni aure suke shafata lokaci zuwa lokaci." Tausayinta ya kama oga Asad yasan jiki ta ji shiyasa ta jinginawa jinnu alhakin laifin da ta yi. Faruku ya ce "Ai kad'an ma kike ganin tunda ke jununki kaifin harshe". Baba ya ce "Yanzu na gane kana da hujjojinka masu k'arfi. Kuma na gode da ka ga girmama ni amma fa ka sani kana da dama da y'anci a cikin aurenka. Ni dai ka wanku tas a zuciyata. Idan kana sonta a haka zaka iya danne laifinta ka yi mata adalci to hakan nake so. Idan ba zaka iya ba to kada ka yi mata rokon da zaka zalunci kanka Allah ya kama ka da laifinta to ka sahale mata kuma ba zan ga laifinka ba". Abida ta fashe da kuka tana fad'in "A duba nadamata Baba. A duba shekarun da na shafe a rataye alhalin Annabi ya ja kunnen maza akan kada su bar mata a rataye su ba sakakku ba, su ba masu aure ba. A duba zaman goyon ciki da raino da na yi, a duba bak'incikin zura mini ido da kuka yi kai da momi. Gaskiya Baba ka yi mini adalci ". Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:22] Usman ya mike ya yi kanta yana fad'in Baban kike ce wa ya yi miki adalci? You are very stupid! Ya mike ya yi nufin kai mata duka Sulaiman ya tare shi tare da fad'in kada ka dake ta. Ba usman din da aka tare ba, kowa sai da mamakin Sulaiman ya daskarar da shi. Ganin hakan oga Asad ya samu kuzarin fad'in "Baba mu yi alkalanci na gaskiya a tsakaninsu. Abida ta yi laifi mai suna laifi. Lallai ta yi rashin tarbiya da rashin mutunci wanda ba gani ta yi ana yi a gidanmu ba. Ita tasan inda ta ga ana zagin miji da manyansa. Ko ba Sulaiman ke aurenki ba ai MAMI ta wuce ki zage ta don kuwa ta haifi waɗanda suka fiki bayan haka kuma matar Babanmu ce. Da ace a lokacin da kika yi wannan rashin tarbiyar mun ji da ni da kaina na saka Sulaiman ya rabu da ke don kuwa ba zai zauna da wacce bata tarbiya ba. Amma tunda shima ya taka alfarmar sharia wajen yin hukunci to shikenan, Sai a yi hukunci na gaskiya.". Ya nisa ya ce "Sulaiman tsakanina da Allah nake batuna, ba wani bangaranci ko son zuciya. Ba zan maka dole akan ra'ayinka mussaman akan aurenka. Kai kake da cikakken iko akansa haka kaine kake da da damar cigaba da rik'e aurenku ko ka gutsire shi. Amma abin da zan fad'a maka ka fahimce ni da kyau. Ka take dokokin sharia Sulaiman. Ba addinin da ya ce ka bar mace shekaru hud'u ba tare da tasan makomar aurenta ba. Hukuncin ya yi tsauri matuƙa da gaske. Kenan kai da ita duk kun yi laifi babba. Ita ta zagi uwarmu don itama MAMI uwarta ce. Kai kuma ka bijirewa kaidojojin sharia. To idan a mahangar addinin musulunci za'a yi alkalancin to gaskiya ka yafe mata ku cigaba da zama kaima sai Allah ya yafe maka d'ora ra'ayinka akan na shari'a da ka yi yayin hukunci". Abida ta rrarafa ta fad'a jikin oga tana kuka sosai. Don ya faɗi abin da ya yi mata dad'i bai ce a saketa ba. Kuka kawai take yi wanda babu shegantaka ko shakiyanci don hankalinta ya tashi ainun sannan ta muzanta sosai. Ya kasa ture ta a jikinsa don tausayinta ne ke kekketa shi. Zullimi da firgici ya bayyana mata barobaro mussaman da Baba ya yi kalamansa da yake nuni ba zai yiwa Sulaiman tilas ya zauna da ita ba. Sulaiman ya nisa ya ce "Shikenan na yafe mata amma gaskiya kada ta sake yi mini irin haka. Sannan ta fara yi mini bincike a wayata to ta bari, wayata ba huruminta ba ne. Ina neman aure ba ruwanta da batun karin aurena idan an k'addara mini zan k'ara to zan yi, idan kuma ba'a k'addara mini ba to shikenan amma kada ta fara saka mini ido tare da bin diddigin halin da nake ciki ". Abida ta dago daga jikin oga idanuwanta jage jagee da hawaye ta ce "Ba ruwana da wayarka. Aure kuwa da ikon Allah ba a k'addara maka ba. Baba babba da Baba K'arami matansu d'aya. Ga yayyenka nan duk matansu d'aya don haka kaima d'ayan ce". Oga Asad ya bige mata baki ya ce "Wai ke wacce irice ne? Ba za ki yi godiyar ya yafe miki ba, sai kawai ki hau raddin batun da ya ce bai shafe ki ba. Ina ruwan ki da Ƙarin aurensa?" Cikin kuka ta ce "Ayi hak'uri na yi shiru." Baba ya nisa ya ce "Na huce da kai Sulaiman na kuma fahimce ka, ba da gayya ka yi abin da ka yi ba. Na yafe maka b'acin ran da na shiga a dalilin tafiyarka. Allah ya yi maka albarka". Sulaiman ya amsa da ameen Baba na gode Allah ya kara lafiya da nisan kwana mai albarka." Dukkansu suka amsa da "Ameen". Abida ganin za'a tashi ba'a yi batun inda zata zauna ba. Ya sanya ta ce "Yaya Sulaiman ya bani inda zan zauna ". Ya yi shiru. Baba ya ce "Sulaiman ka ji rok'onta?" Ya yi k'asa da kai ya ce "Na ji Baba. Da na gama gyara mata gidanmu na Funtua don can zan koma. Sai kuma jiya ta gabatar mini da lissafin bashin da ta ke bina tun bayan tafiyata. Na gama lissafina ban ga ta yadda zan bata milyan dari uku da sittin da ukun da ta ambato mini ba. Dan haka ta zauna zuwa sadda zan hado mata kuɗaden sai ta koma". Ta yi fit ta ce "Ba zan jira ba. Ka bayar abin da ya samu a hankali sai ka dinga biya". Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:25] Ya yi maza ya ce "Kin manta babu bashi a tsakaninmu ne?" Ta goge hawayen idonta ta ce "Sai mu fara yanzu". Ya ce "Abida Wallahi ba za ki bini bashin kud'i ba." "To shikenan ka ba ni milyan sittin da ukun albarkacin yafiyar da ka yi mini, na yafe maka milyan dari ukun. Ya jijjiga kai ya ce "Na gode amma ki mini lamini zuwa na samu sararin samunsu idan na kawo sai ki koma d'akinki don kuwa ba zan yarda ki koma da sharadin kina bina bashi ba". Ta yi shiru amma yadda ta ga ba wanda ya tsoma musu baki ya sanya ta fad'in "Yanzu nawa zaka iya ba ni to?" Iya na magani da hidimar junior zan iya baki kawai. Amma bayan wannan duk wani lissafi ban karɓe shi ba, don kuwa ban ce ki bar d'akinki ba, ke ce kika tafi don rad'in kanki don haka kwabona ba zan bayar ba". "To yanzu nawa zaka iya ba ni?". Ta tambaya cikin rauni. "Milyan d'aya." Ya amsa a takaice. "Ta fashe da kuka sosai tana fad'in "Na rantse na kashe ninkin ba ninkin wannan kudin da ka ambata ka dai sake dubawa". Dariya ta k'wacewa Yaya Faruku. A ransa yake ayyana Abida tana da ban mamaki". Daga haka ta ce "Dady na gode Allah ya bar kauna, Allah ya saka maka da alheri. Baba na gode Allah ya k'addara saduwarmu gobe da asuba zan wuce ". Faruku ya kalleta wato shi da Usman sun yi laifi kenan. Ta mik'e ta ce Yaya Faruku na gode, Yaya Usman na gode Allah yasa zamu ganawa sai wataran". Baba ya ce "Koma ki zauna". Gargadin da jan kunne masu yawa Baba ya yi mata tare da babbar murya a k'arshe kuma ya ce ya soke batun bashi ko na diyyar da take nema a wajen Sulaiman. Ina kuɗaden da ta dinga karɓa a wajensa da wajen su Asad da yake bata na hidimar yaron? Ina kudaden da Ansari yake turo miki from time time, ina hidimar da Bilki take yiwa yaron?" Da kuka ta ce "Baba kenan dai saboda shi aka dinga ba ni kuɗaden ba dan ni da nake wahalar raino da tarbiya ba?" Oga Asad ya ce "Ni dai ina bayarwa ne a madadin Sulaiman ba dan ke ba, ai kina aikinki kina samun kudade amma nake baki don ina matsayin uban yaron ba wai yayanki ba." Takaici ya shak'eta ta ce "To shikenan na gode". Yayin da d'adi ya mamaye Sulaiman an kubutar da shi jidalin Abida akan bashin da ta kago masa. Ya kalleta ya tabbatar kawai ta amsa ne don tana son a kammala sulhu amma lallai sai ta karɓi wani abu a gunsa da hankalinta ya kwanta. Aka rufe taro da addu'a. Su oga kowa ya yi sallama da Baba da Momi suka tafi harkokinsu. Yayin da Abida ta shige d'akinta ta hau had'a kayanta da na junior. Ba dan azahar ta kawo kai ba duk runtsi yau zata tafi. Ta kuma ta gane Sulaiman ba zai yarda su tafi tare ba. Baba ma ba zai bari a raka ta ba tunda a gabansu ya fadi ba shi ya ce ta tafi ba, dan haka ta koma inda ta baro anan zata zauna. Kafin magharib ta gama hade duk wani abu mai muhimmanci a gareta ta k'ira oga Asad ta roke shi akan gobe James zai kaita Funtua a motarta sai ya shigo motar haya ya dawo Abuja. Ya amince mata. A daren ta d'auki mota ta tafi asibiti tunda dama night zata yi. Kafin asuba ta kammala komai ya rubuta takardar ajiye aiki da asibitin gabad'aya. Tana shigowa gidan ta shiga ta gaida Momi tare da yi mata sallama. Tausayinta ya kama Momi a dalilin ta ga tun jiya bata zauna ba. Ta yi zuruzuru tabbacin bata cikin nutsuwa. Momi ta ce "Allah ya kiyaye Abida. Lallai ki nutsu ki yiwa mijinki biyayya, ki girmama ra'ayinsa ki mutunta shi. Allah ya kiyaye gaba ". Hawaye na zubar mata ta ce "Ameen momi na gode dan Allah ki yafe mini". Momi ta ce"Ba komai Allah ya yafemu gabad'aya." Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:30] *Dingishin kwado* Daga haka ta kinkimi junior da yake barci akan gadon momi tana fad'in "Bari a yi masa wanka." Sai da aka yi masa wanka aka shirya shi sannan itama ta yi wanka. Razina mai kula mata da Junior ma ta shirya don da ita zata tafi. A tsastsaye ta kurbi ruwan tea. Sannan ta je Har dakin Baba bayan momi ta yi mata iso. Ta yi masa sallama tare da godiyar hidimar da aka yi da ita. Ta sake ba shi hak'uri." Ya bat tabbacin ya huce. Amma ta ninka biyyayarta ga Sulaiman. Ta ajiye dukkan ra'ayinta ta bi nasa, sannan ta yi hak'uri da shi." Da kuka ta baro d'akin, duk yadda ta matsu ta bar gidan sai da ta ji alhinin barin iyayenta. Daidai lokacin James ya iso. Yan aikin gidan suka dinga fita da kayayyakinta. Ta fita zuwa d'akin Sulaiman. Murya ba amo ta gaishe shi tare da fad'in "Zan tafi ba ni mukullin gidan". Bai ce komai ba ya dauko ya bata har ta juya ta ce "Ba addu'a ba komai?" A gajarce ya ce "Allah ya tsare sai na iso". Ta ce "Allah ya kawoka lafiya". Ta saka kai ta fice. Sai da suka je wajen Bilki ta karɓi frozen snacks da sauran tarkace sannan ta tafi. Bilki ta biyo ta tana fad'in Abida haka za'a yine ba wani dan gyara da zaki yiwa yayana irin wannan dogon lokaci ba'a hadu ba haba gaskiya tsaya Ki tafi da tsumin bojuwa herbs kin yi sa'a ma jiya kazar sababin da na yi order ta iso. Bari na yi miki warming dinta Ki ci hanya". Abida bata k'i ba ya tsaya ta karɓa don tasan kazar da gaske ta sababi ce. Ta ce "Ki yi mini order din Bridal package kawia Bilki sai a saka mini a motar Funtua. Ina son sanyi flusher irin sosia yake da kyau ". Bilki ta ce to zan miki ai zan so Yaya Sule ya huta da kyau da kyau". Abida ta tsume bata ce komai ba har aka yi warming kazar aka juye mata ta karɓa ta tafi. Contact 08032773332 for your order. Bilki tana mamakin yadda Abida ta yarda zata koma Funtua salin alin duk da yadda aikinta a Abuja yake. Dariya ta k'wace mata tana ayyana keburan Yaya Sule sun shige ta da kyau. Suka gaisa da Yaya Hamida d ta kwana a gidan ta yi musu sallama ta tafi. Hamida ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in Abidan Baba an yi tub'us. Sai ta bani tausayi Wallahi ". Bilki ta numfasa ta ce "Yaya Sulaiman ya ce ba inda zai zauna sai a gida. Amma sannu a hankali zasu raya gidan Shi da ita . Na gane manufarsa akwia kuma hikima mai yawa a hangensa. Allah ya k'ara daidaita mu gabad'aya." Hamida ta amsa da "Ameen ". Cikin kasala. K'arfe goma na Safiya oga Asad ya kammala shirinsa zai fice. Ya leka d'akin Bilki suka gaisa da Hamida. Ta ce masa yau zata je gidan Yaya Faruku ta yi masa nasa kwanan." Ya ce ,"kin kyauta Allah ya bada ladan zumunci. Yanzu yaushe za ki dawo zuwan Bilki Kenan tunda kin ce yanzu wajena kika zo?" "Zan dawo kafin na tafi ko yini na yi mata. Ko ban same ka ba dai zan dawo ". Dariya ta subuce masa yasan so take yi ya sallame ta kawai. Ya koma sama ya dawo ya mik'a mata rafar dubu dari ya ce "Ga shi ki sha ruwa a hanya na gode Allah ya sauke Ki lafiya." Ta karɓa ta yi godiya. Har ya kai falo ta zabura ta bishi Bilki na rik'eta ta fizge, Bilkisu ta sake rik'eta ganin zai sauka ya sanya ta bude baki ta ce "Yaya Asad". Ya juyo kan dole Bilki ta saketa. Ita kuma ta fita tana fad'in "Wallahi ba ki isa hanani na karɓa ba." Ta fita zuwa bak'in kofar ta dan diririce ganin yana saurarenta. Ta kwafse ta ce "Yaya dama ina sonu tattauna ne". Kaitsaye ya ce "To Bismillah ". Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:33] Ya dawo ya zauna akan kujera. Itama ta fito ta zauna a gefe. "Kanta na k'asa ta ce "Baba ya ce wanda ya yi imani da Allah da ma'aiki hadi da ranar lahira ya huce da d'anuwansa." Kaitsaye ya ce "Hakane". Ta nisa ta ce "To gaskiya na huce amma akwia abin ka yi mini wanda na kasa mance Shi, shine Zan fad'a maka don na daina ganinka da abin." Ya gyara zama ya ce "Ina saurarenki Hamida ". Bilki tana tsaye a bakin k'ofar d'akinta ta yi sororo tana mamakin k'arfin halin Yaya Hamida. Ta waiwaiya ta ga Bilki ta ce "Kina nufin dan kin zama matarsa sai ba zan zo gabansa da damuwata ba sai kin mini tsaye a kai tamkar dogari? Ya ya hakane?" Ya ce "Shiga ciki sarauniyar shaiba ". Kan dole Bilki ta shige cikin d'akin cikin matsanancin mamaki. Hamida ta muskuta ta ce "Ka saba yi mana alheri Kan alheri Yaya Asad Kuma muna jin dad'i tare da yi maka addu'ar cigaba da samun d'aukaka da gamawa lafiya. Kana da kirki dukkan halayyar iyayenmu biyu ka kwashe Su tsaf. Shiyasa kullum nake mamakin da ka danne hak'kina da nake da shi a cikin dukiyarka. Annabi ya ce "Idan Allah ya yiwa mutum arziki a zuri'a to y'anuwansa suna da hak'kin a yi musu hidima da dukiyar. Alhamdulillahi kai kana kwatantawa. Mun gode. Amma dan Allah me yasa da aka shiga danbarwar nan ka daina ba Ni kason azumi da na sallah? Wannan abu Yana mini ciwo don mijina na sake girmama ni Idan ya ga makudan kudaden da yayana yake ba ni, motsi kad'an zai ce ai ni yar gata ce, ni d'iyar dattawa ce kanwar manyan Kass masu wadata. Amma Yaya Asad Sai da ka kunce mini zani a kasuwa". Ta kece da kuka sosai. Jikin oga Asad ya yi sanyi. Ya ji wani irin rauni da tausayinta ya kama shi. Zuciyarsa d'aya ya ce "Share hawayenki Hamida kuskure duka mun yi Shi tare da taimakon shaidan da sharrin zuciya. Amma daga Bana za ki ga sauyi kuma kari Zan yi muku ma d aya wuce yadda nake baku a baya". Ta goge idonta da tissue din hannunta ta ce "Allah yasa, Allah ya k'ara Budi." Ya ce "shikenan matsalar?" Ta langwabe kai ta ce "Ai ni biyana zaka yi na bayan da baka bayar ba. Azumi hud'u sallah hud'u kenan. Ga na ragon layya shima hud'u ne". Ya yi sakare yana tuna danbarwar Abida da Sulaiman akan kuɗaden da ta ce zai biyata. Shine yau shi Kuma Hamida ta tisa a gaba da naata shakiyancin. Ko da yake da dukkan zuciyarta take magana ba tsokana ko ba'a take yi ba. Ya kalleta sosai yadda ta langwabe kai ta yi kalar tausayi take kuma dakon amsarsa sai ta ba shi dariya ainun. Ya dinga kyakyatawa. Ta jijjiga kai ta ce "Da kasan gorin da ake yi mini a dalilin rashin samun envelope Dinka ko alert dinka da ka tausaya mini k'warai da gaske. Har fa sai da aka kai jallin idan an biya Ni kudin hayar gidajena nake nunasu a matsayin kai ka ba ni". Ya matse ya ce "Har haka kike rufa mana asiri ni da ke?" Da azama ta ce "E to ya zan yi tunda mutanen yau sun siffantu da son yin gori don a saka mutum a bak'inciki mai tsananin gaske". Ya ce "Ki yi hakuri da ikon Allah kin wuce kowanne irin gori Hamida daga yau din nan". Ta dinga godiya cikin farinciki. Ya mike yana fad'in sai mun sake had'uwa. Ta yi maza ta ce "To lissafa ka ba ni na baya tunda na yi ta ranta maka ina nunawa mai shari'a kai ka bani." Dariya ta sake k'wace masa ya ce "Wai dan Allah ke da Abida haka tsarinku yake ne? Haka siddan idan kun so nishadi sai ku ce kuna bin mutum bashi?" Ta kwararrabe fuska ta ce "Yaya Asad Wallahi ina nuna kudi na ce kai ka bani, kuma dai tunda ka saba bayarwa ni ka daiana ba ni tunda an huce har na zo maka kwana gidanka ai sai ka yi mini adalci ka kirgo dukiyata ka ba ni cikin rarrashi da farincikin ka sauke nauyin zumunci". Ya ce "Yanzu nawa kika lissafa kenan?". Ka ga dai duk azumi kana bamu rabin milyan. Ka zo ka bamu barka da sallah sannan ka bamu kudin ragon layya. A kiyasina ba zasu gaza milyan biyar ba idan kuwa Keke da Keke za a yi sun saura sosai ". Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:36] A fili ya ce "Tirk'ashi ". Kan dole ya ce"Yanzu idan na je office na zauna zan turo miki abin da ya samu sai ki yi hak'uri ki yafe sauran". Ta ce "To shikenan amma dan Allah Yaya a duba hak'urin da na yi kada a takure ni da yawa tuni na gama kasafin da zan yi da kuɗaden, hidindimu ne sun yi mini k'awanya Wallahi ". A wannan karon ya kasa ce mata komai illah dariyar da yake ta sosai, a hakan ya fice ya bar gidan. Har ya isa office Yana dariyar Hamida. Tabbas ita da Abida danjuma ne da danjummai. Bilki ta fito Hamida ta galla mata Harara ta ce"To na fad'a sai kisan yadda za ki yi da ni?" Bilki ta murmusa tare da fad'in ya zan yi kuwa?" Awa da d'aya da fita ta ji alert tana dubawa ta ga milyan guda. Ta yi murna sosai. Amma ta kalli Bilki ta ce "Kawai na hak'ura ne amma ba haka nake binsa ba". Bilki ta yi tamkar ta ce "Kada Ki hak'ura mana". Amma tasan idan ta fadi hakan ta tsokano tsuliyar dodo ne. Dan haka ta murmusa tare da fad'in "Yaya Hamida kina sharafinki". * Da yamma Sulaiman a gaban Baba yana masa sallama zai tafi Katsina gobe da sassafe tare da Anisa. Ya sake ba shi hak'uri akan dukkan abubuwan da Sia wakana. Baba ya bashi tabbacin a yanzu Babu bacin ran kowa a zuciyarsa. Ya yi kowa afuwa ya yafe komai. Jin haka da Sulaiman ya yi sai y samu k'warin guiwar tuntubarsw da batun da shine ya yi musu saura. Kansa a k'asa cikin nutsuwa ya ce "Baba zan roke ka arziki da alfarma dan Allah". "Ina jinka Sule". Baba ya fad'a a takaice. "Baba so nake yi ka bani Dama na mayar da kai gida Funtua". Wata irin nutsuwa ta dirarwa Baba. Ya ce "Yaushe kake so na koma?" Kan Sulaiman na kasa ya ce "Ni dai ko yanzu na shirya Baba don tuni na gama gyara gidan gabad'aya cike da yaƙinin ba zaka juyawa buk'atata baya ba. Don idan momi ta kammala shirya muku kayayyakinku kawai waya zaka yi mini na zo na tafi da ku". "Allah ya yi maka albarka Sulaiman, Ubangiji ya yiwa kokarinka albarka. Yau muna 10 ga wata idan Allah ya kaimu 10 ga watan da zai kama sai ka zo mu tafi. Kafin lokacin duk mun kamallah da komai ". Sulaiman ya dinga godiya da fatan alheri ga Baba. Ya sake cewa Baba na sake rokonka?" Baba ya ce "Roke ni Sulaiman". Baba ka dawo tare da Yaya Faruku tunda shima a can ya rayu kuma duk mun sani yafi son zamansa a Funtua. Ya dawo na taya shi cigaba da kula da ladi farm ". Baba ya ce "Hakan za'a yi Sulaiman in sha Allah. Ai kasan ma ba zai yiwu muna Funtua Faruku na wata duniyar ba. K'afata kafarsa. Allah ya k'ara had'a kawunanku ya sanya muku tausayi da soyayyar junanku." Sulaiman ya dinga amsawa da ameen. Baba ya numfasa ya ce "Na roke ka Sulaiman?" Kan Sulaiman a k'asa ya ce "Umarni zaka ba ni Baba". Baba ya ce "Batun ba a gwadaben da zan baka umarni ba ne. Dan haka dole rokonka zan yi." Jikin Sulaiman ya yi sanyi mussaman da ya ga yanayin Baba ya sauya zuwa alhini. Murya ba amo ya ce ina jinka Baba". Ya ce "Ka yiwa Allah ka yi hak'uri akan Abida ka yafe mata, ka yi mata adalci. Mace ce ita mata kuwa suna da rauni akan komai. Ban tab'a ganin abin da ya raunana Abida ba sai kai, ta yi laifi tabbas, amma tunda ta yi nadama ta yi kuka, ta bada hak'uri dan Allah ka yi dukkan iyawarka ka manta da wanccan laifin ka rik'e ta da amana, ka ji tausayinta kada don tana sonka ka yi amfani da hakan ka kulle zuciyarka akanta dan Allah Sulaiman". Tausayinsa ya ratsa Sulaiman don kuwa a bayyane yake Baba na son Abida kowa yasan da hakan har ana rasa wa yafi so tsakaninta da Faruku. Murya ba amo Sulaiman ya ce "In sha Allah komai ya wuce Baba. Na yafe mata, har zuciyata na huce da ita". Dad'i ya kama Baba ya dinga fad'in "Allah ya saukar da albarka a tsakaninku, Allah ya shirya shirya muku zuri'a ya muku arziki marar yankewa.". Daga haka suka shiga hirar duniya iri iri. K'arfe uku daidai suka isa k'ofar gidan. Zuciyarta ta harba rabonta da garin gabad'aya tum rasuwar MAMI. Mamakin yadda aka to renovating gidan take to, don kowa ya kalla Sai ya sake kallon gidan an yi masa fenti mai kyau mai karshen tsada. Save Restricted Content Bot, [Nov 12, 2025 at 11:39] Ba kuzari ta bawa James mukullin don ba tantama gidan ne ba batan kai suka yi ba. Ya karɓa ya fita ya bude katafaren gate din zubin mahadi ka ture. Ya dawo ya shiga motar suka isa cikin farfajiyar gidansu. Abida ta dinga juya idanuwa tana tu'ajibin yadda gidansu ya Koma. Yaya Sule kud'i ya yi ne haka bata sani ba?" Ya yi kokarin gaske ta tabbatar milyoyin da gidan ya kashe ba kad'an ba ne. Ta nunawa James part din da zai kai kayanta. Razina ta dinga daukar wanda zata iya. Ta bude k'ofar shiga part ɗinta. Ta sandare a tsaye ganin yadda aka shirya mata falon tamkar a turai. Ta leka kicin ta ga nan ma komai sabo ne cooker kuwa har an had'a da alamun ya kunna ya yi amfani da ita. PAGE 26 Ta leka store ta ga ya ajiye komai na abinci. Ta fito ta shige d'akinta mamaki ya sake kasheta don kuwa kayan gadon masu k'ololuwar daraja ne. Ta shiga bayi ta doro alwallah. Ta shiga daya d'akinta ta tarar da k'aramin gadonta an yi k'aramar wadrof da ta dace da gadon. Dad'i ya kamata duk yadda aka gyara gadon sai da ta gane abinta. Yanzu ya zama na junior don d'akin yafi dacewa da shi. Sai da ta idar da sallolin azahar ta shiga kicin ta Fara soyawa James samosa da spring rolls dui da sun tsaya sun ci abinci a restaurant. Ta nade masa a poil pepper ta saka masa a leda tare da ruwa da lemo. Duk da tasan dady ya bashi kud'i sai da ta bashi wasu. Ya dinga godiya ya tafi . A Kaduna zai kwana da safe sai ya wuce Abuja. *Katsina.* Amrah da Faruk tare da Babansu da take dauke da Ifrah suna zaune a falo. Amrah ta ce "Dady muna son mu je wajen Mahmah wannan hutun da za'a yi." Ya nisa ya ce "To mamana idan na samu sukuni sai ku tafi". Ta ce "mun gode". Ya ce "Kwana nawa zaku yi to?" Amrah ta ce "Gabad'aya zamu yi hutunmu a can tunda sau d'aya muka je sai kuma sunan twins da muka yi kwana biyu muka dawo saboda school." Sai lokacin Faruku ya ce ",To zamu raba hanya kenan don kuwa ni kwanaki goma zan yi na dawo a gidan ubana". Amrah ta kafe shi da ido. Yayin da Sahal yake nazarinsu gabad'aya. Ya fahimci ita Amrah irin mutanen nan ne marasa damuwa tamkar dai Bilki. Komai nata bai tsole mata ido ba. Ko yadda bata bawa Hawwah matsala ya fahimci sak take bata ajiye damuwa a ranta ko kad'an. Yayin da Faruku yake a murd'e. Baya shiga shirhin Hawwah har yau din nan. Amma yana kula Ifra tare da siya mata abubuwan yara na ci ko na wasa irin wadda zai iya siya. Amma tsakaninsa da Hawwa gaisuwar safe sai kuma wata safiyar. To yanzu kuma ya fahimci ba zai mayar da oga Asad ubansa ba duk da yana yayan mahmansu. Dad'i ya ratsa shi a yadda ya ce zai dawo gidan ubansa. Daular da suke ganin uwarsu a ciki bata rude shi ba, don kuwa ba gidan ubansa ba ne. Ya numfasa ya ce "Faruku kawai ka yi hak'uri ku dawo tare ban so ku raba hanya idan zaku dawo". Kaitsaye ya ce "To zan duba na ga ni idan mun je. Kuma gaskiya Yaya ki rage yin kazallaha a gidan nan. " Ta harare shi tare da fad'in "Ba ka ce ba ruwana da harkar ba, to nima ba ruwanka da harkata". Ya yi dariya ya ce "Ni na huce fa Yaya. Kema ki huce da k'aninki. Amma gaskiya ba zamu yi 1 month ba. Na hak'ura mu yi 2 weeks sai mu zo Kano gidan Maman Kano mu kammala hutunmu. Idan kika yi candy sai ki je ki dade babu ni". Ta yi masa shiru". Ya ce "kin yi shiru yayar Faruk".. A dan tunzure ta ce "Tunda kaine ubana ka tsara yadda za'a yi dole na amince ai". Ya k'yalkyale da dariya ya ce "Nasan ma kin yarda yayata. Allah idan ba anan gidan ba, bana iya sakewa duk kayan alatun da suke can sai na dinga ji a raina ba dai gidanmu ba ne sai na ji duk na gundura na fi son gidan ubana fiye da ko ina ". Wani irin matsanancin dad'i ya kama Sahal. Tausayin kansa ya kama shi. A zuciyarsa addu'a yake Allah ya buda masa. Ya jiyar da y'ay'ansa farinciki. Daidai lokacin Hawwah ta dawo daga makaranta. Da ƙyar take tafiya ta gaji ga cikin da ya fara tsufa. Ta kallesu ta watsar. Ba dan Faruku na wajen ba, da tsaki zata yi masa. Kullum ita da Sahal babu nutsuwa a dalilin babu walwalar aljihu. Babu kwalliyar da yake tsalawa a lokacin da yake neman aurenta. Save Restricted Content Bot, [Nov 14, 2025 at 16:21] Ba komai a gidansa sai abinci irin na yaku bayi. Hatta kayan amfanin yau da gobe irinsu sabulu da Omo da ƙyar yake kaisu k'arshen wata. Motarsa ta nan amma yafi hawa machine tunda rike Mota da hidimarta ma daban yake. Shiyasa ya kukuta ya karbi loan din machine. Ita kuma bata hawa nisa hujjar karkon kifi ne an saba ganinta a mota sai ta koma hawa mashin. A halin da yake ciki kuma dole ya bata kudin napep. Don haka rayuwar dai sai hak'uri. Babban farincikinsa yadda Amrah da Faruku suke samun tallafin uwarsu. Har yanzu suna girkinsu. Basa rasa snacks. Sannan a cikin walwala suke. Wani lokacin ma a gun Amrah yake samun kud'i idan Faruku baya nan. Don idan yana nan cewa yake yi basu da kud'i. Idan kuwa jar ya ga Amrah ta ba shi . Idan suka kebe ya dinga mata masifar ba fa zai yiwu uwarsu ta dinga basu kud'i don su yi abin da bai yi musu ba, ta dinga dauka tana ba shi yana yiwa wata matar hidima da kuɗinta ta bari baya so. Dole take lallaba shi tana ba shi hak'urin ba zata sake ba, don bata son ya yi abinda babansu zai muzanta a gabansu. Faruku ya zama wani irin murdadden yaro na gaske. Amrah mamakin yadda baya tausayin Babansu ko kad'an take yi. Amma yau kuma ya shayar da ita mamaki da ya ce ba zai je ya d'ade a gidan da ba na ubansa ba ne. Kenan bai d'auki uncle police babansa ba? Lallai halayyarsa sai shi. *Abuja*. Juyin duniya Sulaiman ya yi akan ya wuce da Hamida da Anisa Amma Hamida ta ce "Sai ta yi sati ba zata tafi ba mijinta ya ce gidansa ne yafi yi Mata dad'i. Tunda ya ce ya bata sati to sai ta yi kwanaki takwas ma har da ƙari " Dariya mai tsananin gaske ta bwa Sulaiman. Ya ce "Ni wacece ta zo da ƙyar ne?" Ta ce "Hamida ce yanzu kuma ba zata fi ba sai ta huta". Dad'i ya kama Baba ya ce "Ki yi zamanki sai ku tafi rana daya da Salaha. Ku shiga jirgin Kano ita kuma ta shiga na Lagos. Tunda sun koma Lagos da zama." "Hakan za'a yi baba ". Sulaiman ya kalli Anisa ya ce "Ke ma ba za ki bini ba?" Ta ce "Eh sai Yaya zata koma zamu wuce tare." Ya ce "Ai shikenan kun hutar da ni zuwa Kano da Katsina kaitsaye sai na wuce gida Funtua." A daren suka yi sallama da shi. Faruku ya zo ya d'auke su ya tafi da su gidansa har da Salaha. Yana tashi gidan Bilki ya nufa don ya yi mata sallama. Farha na ganinsa ta ruga ya rungume ta. Haka take yi masa Shi da Ansari. Ya d'ora ta kan cinyarsa don ta ji dad'i. Noor ma ta zo kusa da shi. Itama ya d'ora ta kan d'aya cinyar yana tambayarsu karatunsu." Rairai suke masa state and capitals kuskure suka zarce da sabon national anthem da sabon shugaba ya dawo da shi. Ya ce "Ah lallai dole junior ya ce a makarantarku Zan saka shi. Ina Amal?" Suka ce ta yi barci. "Ya kalli agogo tara saura. Ya ce "To ku sai yaushe zaku kwanta?" Suka ce "9". Ya ce "Kuma lokacin ya kusa cika." Bilki ta ce "To ku k'yale shi ya ci abinci". Suka sauka daga jikinsa suka yi d'akinsu. Aysha Hafcy da Bilkisu suka zo suka gaishe shi. Ya dinga jansu da hira kafin suka tashi. A marairaice ta ce "Yaya Sulaiman sai kuma ka bar Abida ta tafi ita kad'ai?" Kaitsaye ya ce "Tunda fitowa ta yi babu iznina ba yadda za'a yi na tafi da ita." Ta numfasa ta ce "Dan Allah yaya Sulena yafe mata komai ya wuce ban son Abida ta janye nadamar da ta yi ". Ya murmusa ya ce "To dazu ma Baba Babba ya gama nema mata afuwa. Ai na huce tunda ta tafi Funtua babu dogon turanci ta yarda da hukuncina babu inkari". Dad'i ya kama Bilki ta ce "Allah yasa k'arshen alamarin kenan". Ya ce "Ameen Bilkina". Yaya Sulaiman amma zaku bar Funtua nan gaba?" Ya ce "A a matuƙar ina Nigeria to kuwa ina Funtua. Duk inda zan je zan dawo gida ne, iyalina zasu zauna a Funtua ". Bilki ta numfasa ta ce "Allah ya taimakemu gabad'aya ". Ya ce "Ameen Bilkina. Gobe da asuba zan kama hanya dazu na je wajen Saddiqa na yi mata sallama. Hamida da d'iyarta Anisa kuma sun ce suna nan Babansu kuma ya goyi bayansu". Save Restricted Content Bot, [Nov 14, 2025 at 16:22] Ta yi dariya ta ce "Ai kuwa d'iyarta don Anisa bata bin ra'ayin kowa sai na Yaya Hamida". Ya ce "Allah ya cigaba da ganar da ita." Bilki ta ce "ameen". Ya zarce da ba shi labarin yadda ta wakana tsakaninta da oga Asad. Dariyar da Sulaiman ya yi ba yar kad'an ba ce. Ya ce "Anya kuwa muna da cikkaken lafiyar kai, tsiyatakun alhalin gidanmu masu yawa ne tamkar muna da jinnu da gaske fa ". Bilki ma ta dinga dariya sosai. Ya ce "Allah ban da shakiyanci ya ya zata ce tana bin oga bashi, bata bar shi na kuma shaida ya bata. Kinsan adadin kudin da wacccar yar darun ta yanke mini na diyyoyi da bashin da ta yi ta ranta mini kuwa?" Ya faɗawa Bilki adadin kudin. Dariya ta k'wace mata. Ta ce yanzu ya aka karke Kuma?" Ya ce "Bori na dauka mana akan to ta cigaba da zama idan na samu na kawo mata. Ta ce ita na bata abin da yake hannuna zata bini ba shi. Na bijire akan babu bashi a tsakaninmu kuma yanzu ba Zan Fara ba. Milyan d'aya kacal na ce Zan bata. Idan kika ga yadda take kuka tana fad'in na dai sake dubawa sai abin ya daure miki kai wato y'an gidanmu y'an sababi ne na gaske kowa ba shi da sauk'i idan aka taba shi, barin ma su Abida da Hamida". Gaskiya Yaya Sule milyan d'aya ta yi kad'an gaskiyar magana kenan". Ya ce "Hmm ai tana can tana jirana duk yadda Baba ya ce ya soke maganar bashi nasan sai na bata wani abin da na samu nutsuwa. Abida Abida iron lady ". Bilki ta kwashe da dariya ta ce "Ta hadu da iron vendor". Ya murmusa bai ce komai ba. Daga haka ya fad'a mata next month zai zo ya dauki baba sun gama magana ya amince zai koma gida babu gardama ko neman shawara da kowa, wanda hakan ba k'aramin dad'i y yiwa Sulaiman ba". Jikin Bilki ya yi sanyi ta ce "Shikenan sai ku barmu mu kad'ai?" Ya ce "Eh dama a sama kuka same shi anan. Ke da Oga ku yi hak'uri. Mun fiku buk'atarsa. Sannan komawarsa can shine rufin asirin kowa da kowa shine darajarmu gabad'aya." Ya mike ya ce "yau oga ya yi nisan kiwo." Ta ce "Meeting suke yi." Ya ce "To ki gaishe shi ki fad'a masa na zo yi masa sallama baya nan Zan wuce da asuba amma zan masa waya in sha Allah". Daga suka yi sallama ya wuce. * Bilki na kwance kan kujera ƙafafuwanta na kan cinyar oga Asad yana jan yatsunta tamkar ba shine ya dawo a gajiye ba. Murya ba amo ya ce "Ta shi mu shiga ciki ki taimaka mini na watsa ruwa. So nake na sauke miki gajiyar da nake fama da ita". Bata ce komai illah mikewa da ta yi ta mik'a masa hannunta ya kama ya mik'e. Hakan kuwa aka yi,.tare suka yi wankan a daddafe ta shafa mai tare da shafe jikinta da turarukan *mkbees oil perfumery* masu sanyayyen kamshin dad'i da tsayawa a zuciyar masoya 07032456061. Yayin da shi ko mai bai shafa ba body spray kawai ya fesa daga nan ya shiga sauke mata gajiyar da ya yi niyyar yi. Ita kuma tana karɓan dukkan sakonsa cikin jin dad'i da walwala don haka ta sakar masa jiki tare da mayar amsa da martani irin yadda yake so". Na gode da hak'urinku. Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 15:50] *Dinginshin kwado* 08032773332. Suna dawowa masallaci da Baba ya shiga ya gaida Momi tare da yi mata sallama. Ta amsa da walwala tare da sake ba shi hak'urin akan sha'anin Abida. Ya amsa mata da fad'in "komai ya wuce ai momi a dai cigaba da yi mana addu'a." Ta shiga kicin ta juyo amsa pepper chicken din da aka yi masa tun dare. Tare da ruwa da lemo a leda. Ya karɓa da godiya ya fice waje tunda Baba na tsaye yasan sai ya ga tashinsa da ya shigo. Har mota Baba ya raka shi yana masa addu'ar ya sauka lafiya da kuma jan kunnen ya yi tuki a hankali cikin nutsuwa". Ya dinga amsawa cikin girmamawa. Baban kuwa bai shiga ciki ba sai da motar Sulaiman ta bar farfajiyar gidan. Ya sauke ajiyar zuciya a fili ya ce "Alhamdulillahi. Allah kasa k'arshen rikici da hatsaniya da zamu fuskanta kenan a cikin zuri'armu. Allah yasa duk fitinar da zata taso a cikinmu kada ta zama mai tsananin gaske. Allah ka sanya soyayya da tausayin juna a tsakanin dukkan yaran nan. Wanda aure ya shiga tsakaninsu Allah ka zauanr da su lafiya ka kade dukkan fitina da sharrin shaiɗan da na zuciya". Hawaye ya silalo masa wanda na farinciki ne, ko yanzu ya mutu ya tabbatar bai bar su a wargaje ba, bai barsu da gillin juna a zukatansu ba. A hankali ya ja kafarsa zuwa ciki. Gaf da azhar ya isa Funtua. Tun a farfajiyar gidan yake jiyo k'amshin turaren wuta da k'amshin girki mai tada yunwa. Ya rasa k'amshi irin haka. A gidan Bilki yake jin k'amshin spice's din nan har ma da k'amshin gidan da yake ji a yanzu irinsa yake ji a gidan Bilki. "Wato wadannan yara sun iya munuba." Ya fad'a a fili. Ya gama rufe gate din kenan ya taho wajen motarsa, ya ga an bude k'ofar wajensu. Ya tsyaa sai ya ga junior ya fito a guje ya nufo shi. Dad'i ya kama shi. Ya budewa yaron dukkan hannuwansa tare da durkusawa kadan. Ya iso ya fad'a masa ya ce "Dady kai ma ka zo?" Ya ce "Na zo junior ya ka ga gidanmu ne?" Ya ce "Very big and beautiful amma babu upstairs irin na gidansu Farha". Ya yi dariya ya ce "junior ka dinga addu'ar Allah ya bani kudi sai na yi mana irin nasu". Ya ce "To Dady. Jiya mun yi barci Ammi bata yi kuka ba, komai na gidanmu sabo ne". Sulaiman ya dire shi ya ce "Komai sabo da gaske?" "Junior ya ce "Da gaske fa, thank you Dady ". Ya ce "saura a saka ka a school ko?". Ya ce "eh Dady ". Ya ce "Zan saka ka a makarantar da tafi kowacce inganci a Funtua ". Dad'i ya kama shi ya dinga tafi yana fad'in thank you. Yayin da haka kawai k'walla ta cika idanuwan Sulaiman. Tausayin yaron ya kama shi from no where. Sannan yadda yake tsaye a harabar gidan nasu zuciyarsa ta karye ainun Yana fatan nan ba da jimawa ba gidan ya dawo da kwarjinin da yake da Shi a da. Haka nan yana son gidan ya dawo matattarar farinciki ga kowa da kowa a cikinsu. Ya ajiye yaron. Ya bude bayan motar ya ba shi ledar takalmansa shi kuma ya d'auki jakar kayansa da ta laptop d'insa. Ya rufe motar ya rik'e hannunsa suka nufi cikin gidan. A tsakiyar falon ya tarar da Abida ta ci kwalliya cikin dankareren leshin da ya lashe makudan dubba darirruka. Kalar ta haskata. Da yake bata kwalliya mai nauyi daga powder sai lipstick. Sai ya ga yau ta canja gabad'aya. Ya yi nutsu yana son ganin me ya sauya ta ne? Take ya gano janbakin da ta sanya ne sannan ta canja d'aurin dankwalinta da a kullum take yi na ture ka ga tsiya, yau sai ta yi irin Zahra Buhari. Ya saki hannun junior ya isa kusa da ita k'amshin turarenta design6 na cool water ya buge shi. Jikinsa na bari ya jata zuwa jikinsa ya rungume. Ba zato ya ji tafin junior a kunnensa. Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 15:55] Ya yi maza ya sake ta. Ya zauna ya jata zuwa kusa da shi ya zaunar da ita. Murya ba amo ya ce "Ba wannan Abidar nake so ba. Me yasa kike son canjawa?" Idanuwanta ya cika da k'walla ta kasa magana. Ya zaro tissue ya shiga goge mata janbakin da ta saka. Ya saka hannu ya cire mata dankwalinta. Ya ce "Ina abin da kike sakawa cikin dankwalin?" Ta ce yana kan madubi. Ya dauko ya saita shi ya nade sannan ya dauara mata irin daurinta. Ya ce this is my real Abida". Ta murmusa guntun hawaye ya ziraro mata. Murya ba amo ta ce "Sannu da dawowa ya hanya?" "Alhamdulillah". Ta ce "Haka ka gyara gidan?" Ya ce "Ya yi miki?" Ta ce "irin sosai fa". Ya ji dad'in yabawarta. Ta ce Amma na ga duka gidane ya canja". Ya ce "So nake Ubangiji ya taimake ni na dawo da shi yadda yake a da, dan haka na gyra Shi gabad'aya. Ta ce "To Allah ya taimaka, ya cika maka buri". Ya mike zuwa d'akinsa ta bishi da jakar hannunsa. Ya saka mukulli ya bude. Suka shiga ta ga d'akinsa ma komai sabo ne amma gadonta yafi nasa kyau da tsada nesa ma ba kusa ba duk da shi din ma mai kyau ne ba wai mai araha ba ne. Ta ce "Baban junior gaskiya ka kashe kud'i sannu da k'ok'ari Allah ya k'ara budi na halal. Allah kums ya bada ikon biyan bashi". A ransa ya ce "Nasan za'a yi haka". A fili ya ce"Ameen na gode ". Ya shiga wanka ita kuma ta fita zuwa kicin. Spice's din Amreesh duniya ne don daga jiya zuwa yau har k'amshinsu ya fara kama gidanta. Idan ta fara girki kuwa kamshi har waje. Tunda ta ji a gidan Bilki shine ta sa ta yi mata order din Bridal package din. For your order 09093510131. Yana fitowa ana k'iran sallar azahar. Dama ya d'oora alwallah dan haka ya shirya ya k'ira junior ya yi masa alwallah ya rike hannunsa suka tafi masallacin kusa da gidan wanda iyayensune suka gina shi. Ya dawo suka ci abinci tare sannan ya hau keken atisaye da yake d'akinsa don ya motsa jikinsa a dalilin gajiyar da yake ji a tare da shi. Abida ta shiga ta tarar da shi ya had'a zufa akan keken ta ce "Sannu." Ya ce "Yauwa. Wai so nake na warware dan kada na kasa iyawa da ke tunda kin ce kina cikin kewa sosai". Ta murmusa bata ce komai ba. Ya sauko ya shiga bayi don ya watsa ruwa tunda ya jike sharkaf da zufa. Ita kuma ta fita zuwa d'akinta. A falo ta tarar da junior yana barci a zaune. Ta saka hannu ta d'auke shi zuwa d'akin da yake da k'aramin gadonta. Ta kwantar da shi. Ta kalli Razina da take zaune a gefe daya. Ta ce "Ki je ki zubo abinci ki ci, idan kin gama ki yi wankewanke". Ta ce "To". Daga haka ta fice zuwa d'akinta itama ta shiga wanka. Da ta fito ta tsinci kanta da wani irin zumudi da bata tsintar kanta a ciki ba. Cikin gaggawa ta bude coconut oil na oriflame da Bilki ta koya Mata shafawa don ita tafi son verseline. Amma yadda man ya karɓi bak'ar fatarta ta yi taushi yake fitar da Mata ainihin kalarta mai duhu ya sanya take son shi. Bilki dai na da jama'a iri iri. Don duk abin da zata siya zata ce tana da wadanda suke da shi mai kyau Wanda babu tsada ko algush. Dan haka daga Kano suke siyan dukkan oriflame products wajen Aisha lame dama dukkanin da ya shafi costumes. ........ Hatta man gashi da turarenta zababbu lamen take basu. Don haka Abida cikin gigiggiwa take bin dukkan nau'in jikinta tana goga mai da turaruka daban daban. Ta shirya cikin irin rigar da yake son ya dinga ganinta a ciki mussaman ta yi order ta a wajen Maman biyu mazauniyar Egypt...... Ta zunduma hijab din gunis da ya sha kambasa. Ta zunduma hijab din gunis ta fita. Sai da ta shiga kicin ta d'aukar masa ruwan da ya zame masa k'aidar shi idan ya kammala jijjigata. Tana shiga ya mike a bakin gadon ya ce "Har na kosa fa, da bin ki zan yi ai". Ya karɓi ruwan ahannunta ya ajiye akan side drower. Ya juyo ya ga ta cire hijab din. Zuciyarsa ta harba da ya ganta a zahirinta. Ya bude mata dukkan hannuwansa. Bata tsaya yauki ba ta yi gaggawar isa ta fad'a mishi. Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 15:58] Ya rungumeta sosai har suna jin yadda zukantsu suke dokawa. Zuciyarta ta karye a dalilin rabon da ya yi mata irin tun safiyar da zasu yi hatsarin da ya yi ajalin Baba K'arami. Hawayenta har kan k'irjinsa. Murya ba amo ya ce "Kada ki yi mini haka, kinsan bana son kuka ko?" Cikin kukan ta ce "Dan Allah yaya Sule ka yafe mini, ka manta komai, Allah ya baka hak'uri ". Ya sake rik'e ta sosai yana fad'in"Is ok na huce na manta, amma kada ki sake, kada ki sake Abida! Murya na rawa take fad'in "Na gode sosai dadyn junior, ba sai ka ce komai ba, ba zan sake ba koda wasa kuwa". Ya d'ago fuskarta da ta yi jagejage da hawaye ya tsura mata idanuwansa. Itama ta zuba masa nasa da suke cike da k'walla. Gabad'ayansu shauk'i ya yi musu dabaibayi, soyayyar juna ta dinga taso musu. Ya saka harshensa yana lashe hawayen da bai daina silalowa ba. Daga ya hade bakinsu ya shiga laluben harshenta. Tsayuwar ta nemi gagararsu da ƙyar suka dangana da Gado suka cilla sama jannati. Abubuwan da suka biyo baya kuwa nauyinsu ya kai k'urewa wajen bayyanawa. Amma dai anci uwar sabada an yi tumbidin ruwa irin sosai din nan don dukkansu sun yi kewar juna a kuma matse suke. Barin Abida da ta sha gyara da kayan bojuwa herbs. Tsananin farinciki ya sanya dukkansu hawaye ba tare da Dr Sule ya fahimci hawayen.ke zubar masa ba. Don gabad'aya sun karaya da tunanin zasu sake samun kansu a cikin irin wannan yanayin. Kirikiri ya kasa zuwa sallar la'asar. Lokaci ya k'wace masa. Sai da suka samu nutsuwar da ta dace da su sannan suka yi wanka, suka yi sallar wanda biyar ta wuce. Suna kan sallayar tana nade a jikinsa. Ya ce "How far ya ya marar?" Ta rufe ido tana dariya ta ce "Da sauran nauyi nauyi kad'an. Ya kece da dariya ya ce "Kina sharafinki Abidan Baba ". Ta ce "Hmm Abidar Yaya Sule dai tuni ka k'wace masa ai. Da ƙafafuwana fa na taho Funtua na baro baba da Momi babu zullimin komai". Ya sake yin dariya ya ce "To ba kewata kike yi mai tsananin gaske ba?" Ta jijjiga kai tare da fad'in "Da kewa ce kawai da na cigaba da shan kanwa da lemon tsami, na dinga gasa wajen da ruwan dumi da gishiri. So ne mai tsananin gaske dadyn junior ". Karon farko da ta furta masa Kalmar soyayya babu kunbiya kunbiya. Ya ce "Amma fa Abidata bata yin soyayya bata ma yarda da ita ba". Ta boye idanuwanta a k'irjinsa ta ce 'A a Yaya Sule Abida dai bata son soyayyar nan ta masifa. Amma a yanzu ai ta gane wata soyayyar jarabawa ce. Don haka ta daina ganin beken masu yinta babu sassauci zata dinga yi musu addu'a kawai don ita kad'ai tasan tsananin da ta shiga a lokacin da ka yi mata nisa." Ta fashe da kuka sosai tana fad'in na ga rayuwa Yaya Sulaiman.! Tausayinta ya kama shi don duk abin da ya saka Abida yin laushi irin haka da kuka na gaske to tsananinsa ya kai k'urewa. Ya dinga shafa bayanta yana fad'in "Very sorry". Da kuka ta ce "Ka yi mini alk'awarin ba zaka sake guduwa mini ba Baban junior". Ya ce "Ba zan sake ba mana, ki daina kukan nan bana so". Sai daf da magharib ya shiga bayi don ya doro alwallah. Tare da ita suka fita a d'akin. Ya zauna a falo ita kuma ta shiga dakin junior. Daidai lokacin ya fito daga bayin fuskarsa da ruwa tabbacin Fitsari ya yi da kuma alwallah Razina ta yi masa. Don tana cikin bayin bata fito ba. Ta ce "Ka tashi, alwallah ka yi?" Ya daga mata kai don haka yake zama miskili idan ya tashi a barci. Ta ce to mu je ku tafi masallacin don ya riga ya saba zuwa masallaci tare da Baba. Duk lokacin sallah shine dan rakiya haka zai tisa shi a gaba su tafi". Suka isa falon Sulaiman ya mike ya daga shi sama. Ya ga bai yi masa walwala ba. Ya ce "Kana jin yunwa ne?" Kai ya daga masa tabbacin eh". Ya kalli Abida ya ce "A ba shi abinci ya ci, sai ya yi sallar a gida". Ta ce "To". Yayin da junior ya kwararrabe fuska zai yi kuka". Abida ta ce "Sai kun dawo zaka ci abincin?" Ya ce "Eh" cikin kuka. Save Restricted Content Bot, [Nov 17, 2025 at 16:01] Sulaiman ya jijjiga shi ya ce "Kada ka yi kuka mu tafi ". Bai dire shii ba sai da suka je koridon da zai fitar da su waje. Ya ajiye ya saka takalmansa da suke gefe. Da daddaren ma nasu sararawa juna ba. Ana ta biyan gangar jiki kewar da ta sha na tsawon lokaci mai yawa. Kwanakin biyun da suka biyo amarci ake sha gangariya wanda babu k'wange a gidan Dr Sulaiman na Dr Abida ". PAGE 27 *Abuja* Farinciki da walwala tare da fahimtar juna sun samu muhalli a gidan oga Asad. Don tunda ya gano abubuwan da yake yi suke tunzura masa sarauniyar sheba shikenan ya kiyaye yinsu a gabanta mussaman yin kwatance da maimurabus ta bakinta da fada. Ya barta a zuciyarsa yana bin ta da adduar rahama don kuwa ba zai yiwu ace ya manta da ita ba. Yayin da Bilki take kaffa kaffa tare da kiyaye yin abin da zai saka ya murd'e mata tunda ta fahimci so baya hana shi ya nukurkusa mace da bak'in ciki mai saka kuka da rama a tsaye, idan ta nemi raina shi ko bijire masa. Dan haka suke zaune K'alau cikin mutunci da girmama juna. Amrah da Faruk junior sun isa gidan sun samu karɓa daga dukkan ahalin gidan. Don Amrah ma a d'akin Bilkisu take, tare suke kwana akan gadonta. Haka Su Hafcy da Aysha basu bada matsalar koami ba. Ga khadija ta zo hutu wanda watanni kad'ai suka yi saura akan ta kammala gabad'aya. Don haka gidan a cikin hada hada yake mai dad'in gaske. Baba ya faɗawa ya'yansa Sulaiman zai mayar da shi Funtua. Gabad'ayansu babu wanda ya yi raddi. Oga Asad ne ya ce "To Baba ai sai an shirya don gyaran da za'a yiwa gidan nan ai ba kad'an ba ne". Baba ya ce "A a tuni Sulaiman ya kammala. Kai naka ido ne an hutar da kai an gode maka oga Asad". Yau ma dariya ya yi don kuwa idan baba ya ce masa oga tunda ga zuciyarsa dariyar take fitowa. Ammar din Faruku da yake shiga shekarar k'arshe a jami'a. Tunda ya k'yalla ido ya ga Amra ya ji a ransa ya yi mata. Rashin hayaniyarta da nutsuwarta sun yi matuƙar burge shi. Mutumin Bilki ne na sosai. Sannan yadda Faruk yake da haba haba da fatan faran haka shima yake. Da yammaci ya isa gidan. Kaitsaye ya haye saman Bilki yana fad'in "Mahmah Mahmah". Bilki na zaune akan kujera ita kad'ai. Alti ta bi yaran sun fita. Ta kalle shi ta ce "Ammar ka yi ta faman doka mini k'ira tamkar makaho". Ya yi dariya ya zube a gabanta akan kafet. Ta girgiza kai ta ce "Fadi yau kuma da me ka zo?" Ya ce "Mahmah kin ce ke ce mai saka mini lallen aure ko?" Bilki cikin alfahari ta ce "K'warai da gaske don kuwa Yaya Salaha da Yaya Hamida dolensu su hak'ura don sun san ni ce mafi kusa da Abbanka". Ya ce "To Alhamdulillahi Mahma. Yanzu kuma idan Amrah ce amaryar fa?" Zuciyarta ta harba da saurin gaske. Dole dai soyayyar nan ita da Yaya Faruku sai Allah ya kullata akan yaransu. Idanuwanta suka ciko da k'walla. Ta shanye kukan ta ce "Ko ita ce don kuwa kaine d'ana ba ita ba, ita ma k'anwar uba ko yayar ubanta ce mai saka mata lallen. Amma fa Ammar bata kammala sakandire ba yanzu ne take ajin k'arshe ". Ya jijjiga kai ya ce "Na sa ni Mahmah. Nima ai sai bana zan kammala digirin farko, kawai ina son ta san da zamanka Manya ma Su sani don ABBA ya ce mini nauyin baki na sakawa a rasa abin da ake so mai k'ololuwar daraja." Ta yi shiru amma so take ta rushe da kuka. Ta tabbatar Yaya Faruku ne ya ce ya faɗawa Amrah idan har yana sonta da gaske. Kafin ta yi magana ya ce "Ki faɗawa Dady don Allah. ABBA ya ce "Shine babana shii zan faɗawa, ni kuma ba zan iya faɗa masa ba". Cikin jarumta ta ce "Zan fad'a masa kuwa don tasan ba zai iya din ba da gaske saboda idan Baban Bilkisu na guri nutsuwar da yake yi ta daban ce. Ya nisa ya ce "Zan fad'a mata don nima a tsorace nake kada wani ya yi mini shigar sauri". Bilki bata ce komai ba don kuwa yana da gaskiya itama k'addara da rabon haihuwarta da Faruku ne ya sanya Sahal yiwa zuciyarta da take son fari mai kyau kutse alhalin bai fi ya zo a dan aikent ba. Sai dai dama ta kud'ire a ranta ba zata bari Amrah ta yi irin kasassbar da ta yi yayin zancen mijin aure ba. Shiya6duo sadda suka zauna take yi mata bitar kyaun namijine abu na k'arshe da zata duba. Addininsa da halayyarsa tare da nasabarsa sune a farko. A yanzu da Bilki take cikin shekarun hankali ta gane abin da take ji akan oga Asad shine so wanda bata ji ko da kwatar hakan a zuciyarta akan sahal ba. Haka nan yadda take girmama tare da mutuntunta duk abin da ya shafi Yaya Faruku ta gane kauna ce wanda babu abin da zai shafe ta a zuciya. A fili ta furta "Allah ya tabbatar da wannan batun, na yi murna. Allah ya saka albarka ". Ammar ya mike ya ce "Ameen Mahmah na samu k'warin guiwa dan haka na samu nutsuwa". Bata ce komai ba . Ya ce "Ina yanmatan na ki, yau gidan babu dad'i shirunsa ya yi yawa". Ta ce "Aysha te debe su sun fice". "Har da twins?" Ya tambaya a takaice. "Hmm har da su kasan Alti da son ta yi yawo ta ga Abuja. Har yanzu bata gaji da ganin titunan Abuja ba". Ya yi dariya tare da fad'in "Da fa zuwa na yi na d'auki takwaran abba mu yawata gari, shi kad'ai a cikin mata". Ta ce "Ai kuwa shiyasa ma baya wani d'okin zuwa sai dai ka dawo gobe idan Allah ya kaimu". Ya ce "Zan dawo". Ya tafi Bilki ta bishi da kallo tare da sake girmama ikon Ubangiji. Ta fad'awa oga Asad sakonsa shima ya yi murna ba kad'an ba. Amma ya ce "Karatu zata yi tunda tana da k'ok'ari dan haka ba yanzu za'a yi magana ba. Kawai dai ya dinga nuna mata cikin hikima yana sharewa kansa hanya. Can ya kalli Bilki ya ce Amma kuma idan itama ba mai fahimtar share hanya da raragefe ba ce ba fa?" Ta yi dariya ta ce "Baban Bilkisu ba fa zan gaji da baka amsa da fad'in cutata ka yi da ka k'i bayyana da k'arfinka ba. Wacce mace ce zata tankwabar da tsadadden namiji irinka a cikin hankalinta?" Dad'i ya kama shi amma cikin alhini ya ce "Amma Maigado a karo na biyu ma da na bayyana da karfin nawa ai kin tankwabar da ni. Sai da na shiga rigar Faruku fa sannan kika amince da ni". Ta dan murmusa tare da cewa"Yanzu fa? Baka gama mamaye zuciyata da kalolin soyayyarka da yakanarka ba?" Ya murmusa ba tare da ya gamsu ba. Ta sake shige jikinsa ta ce "Ban fa so wani a duniya irin ka ba Baban Bilki, don ban tab'a jin ina kishin wani namiji a duniya irin ka ba." Wani irin dad'i ya kama shi amma sai Ya ce "Maigadona ki fad'i gaskiya. Anya kuwa, kin fa so yaron nan, sannan Faruku fa?" Ta ce "Na fi sonka fa akan komai da kowa. Shi Yaya Farouku ina rasa wa na fi so tsakaninsa da Yaya Sulaiman. Amma babu tantama nafi jinsa fiye da Ansari ". Oga Asad ya saki ajiyar zuciya tabbas yanzu ya gamsu tana sonsa ba shine kawai yake dakon soyayyarta ba. Ya jata jikinsa ya kankame yana sake jin tana mamaye kowanne loko da sako na zuciyarsa. A wannan ranar suburbubudar da ta sha a hannunsa mai matuƙar tsayawa a rai ne, haka nan mai sakawa ta yi ta sonsa ne. Tana samun nutsuwa da gamsuwa a duk sadda ta shiga hannun oga Asad. Basa yiwa juna k'wange a wannan fagen. ***"" Sulaiman na zuwa Kano ya kwana biyu ya dawo Funtua. Yana ganin masu lalurar ido a matsayin babban likita a asibiti Makka eye Hospital. Abida Na zaune tana cin hadasden Ciccibin bojuwa herbs Kano da ta yi order dinsa jiya. Da yake da kankararsa ya iso Mata Sai ta jefa Shi a freezer shine Sai yau ta yi warming take ci. Sulaiman yana kallonta ta ce Na iya mata ne. Ya jijjiga kai ya ce "Ke da Bilki munubarku da yawa Wallahi. Ku dinga yi mana a hankali. Ku ta kid'ima mu haba dan Allah. Oga da kansa da na gansn a gaban Bilki Sai da na rike baki". Ta k'yalkyale da dariyar nishadi tare da fadin Baban junior ina ce dai kana jin Zamzam?" Ya Sosa kansa ya ce "Idan gaskiya zan fad'a cicif nake jin ki Abidan Baba ". Dad'i ya kamata ta kuma tabbatar kayan Bojuwa babu algush kodayake duk kayan da Bilki take tallata mata babu na banza. Ta ce "To kwalliya ya biya kudin sabulu tunda ka yaba". Kamar yadda aka yi alk'awari jiya tara ga wata Sulaiman ya dira a Abuja tare da junior. Ba yadda bai yi da Abida ba akan su tafi tare ba ta k'i. Ta kafe akan zata zauna ta yi musu girkin tarabarsu. Don tun jiya laraba aka bude wajen ta kamawa Razina suka gyara gidan ya yi fes. Ita dai Abida mamakin yadda Yaya Sulaiman ya kashe makudan kudade take yi wajen gyan gidan. Bangarensu baba ma komai sabo ya zuba musu. Ta tsinci kanta da addu'ar Allah yasa kada Dady ya ce Baba ba zai dawo ba. Ta tabbatar Dr Sule ba zai yarda ya dawo shi kad'ai cikin kwanciyar hankali bw mussaman yadda ya tafi da k'arfi da guiwa da farinciki. Haka gyara b'angaren Baba da ya yi ta tabbatar bai d'auki al'amarin dawowarsa da sauk'i ba. Ranar goma ga watan goma jirgin da ya dauko su daga Abuja ya sauke su a Kano. Suka shiga motar Sulaiman da ya barta a airport suka d'auki hanyar Funtu. Daga baba sai momi sai junior. Yaya Faruku zai dawo amma sai ya kammala da komai sai ya dawo tare da iyalinsa. Ammar dai zai zauna a gidan oga Asad ne ya cigaba da karatunsa da kuka da harkokin Babansa. Yan aikin Momi tare da mai gadin gidan wanda shima asalima dan Funtua ne James zai tuko su a motar Baba. PAGE 28 Cikin nutsuwa Sulaiman yake tuki don baba baya son gudu. Lafiya lau suka isa Funtua. Baba ya dinga mamakin yadda gidan ya zama sabo. Ya tsaya a farfajiyar gidan yana kallon tafkeken gidan nasu. Wanda tazarar da ta tsakanin shashi zuwa wani shashin ba kad'an bane. Amma gabad'aya Sulaiman ya gyare gidan ko ina sai d'aukar ido yake na ban mamaki. Wani irin abu ya mamayi zuciyarsa shikenan zai yi rayuwa a gidan babu Baba k'arami. Hawaye ya k'wace masa da ya hango jikin bishiyar da yafi Zama a k'arkashinta matuƙar bai tafi Ladi farm ba. A fili ya ce "Allah ka jiƙan Isah ka gafartawa mahaifanmu". Sulaiman ya yi maza ya ce "Ameen Baba. Allah ya kara maka lafiya da hak'uri tare da nisan kwana mai albarka." Momi ta ce "Ameen Ameen". Daidai lokacin Abida ta fito tana yi musu barka da zuwa. Suka dunguma suka shiga b'angaren Baba. Mamakinsa ya fad'ada ya ce "Sulaiman irin wannan hidima bata yi yawa ba kuwa? Ka yi ta'adin kudade masu nauyi fa". Cikin nutsuwa Sulaiman ya ce "Da ina da ikon yi muku fiye da hakan da na yi Baba ". Dad'i ya kama Baba ya ce "Kai madallah da Dr Sule angon Abida k'anwar Bilkisu ". Dad'i ya ratsa Abida ta ce "Ameen Baba ". Yayin da Sulaiman ya yi maza ya ce "A a malama daina yin murmushi don an ce angonki, ke uwargida ce." Ta yi dariya tare da fadin yaya Sule kenan". Saia suka yi salla suka huta. Sannan Abida ya gabatar musu da abinci. Tare suka ci gabad'ayansu a falon. Kuzarin Baba ya k'aru. Zuciyarsa ta cika da annuri. Yana jin zuciyarsa na warkewa daga takurar da take ciki. Addu'a ya yiwa Sulaiman tafi cikin kwando. Yana yi yana nasihar ayi ibada, a yi hak'uri da juna, a yi zumunci a kuma kuma kula da marayu don Annabi ya ce kafaɗa da kafaɗa zasu shiga aljanna da mai kulawa da maraya". Abida ta ce Razina ta zauna a shashin Momi ta dinga yi mata aiki kafin nata yan aikin su iso gobe. Sai yamma sannan ta yi musu sallama ta tafi wajenta. Sulaiman kuma ya fita cikin gari da junior. Oga Asad da Bilki sun fi kowa kewar Baba don sun kad'ai za'a bari a Abuja. Sai dai dukkansu sun gamsu tare da amannar komawarsa Funtua shine mafita mafi kyau. Don shi da kansa yafi son zamansa a Funtua. A hankali Faruku ya kammala parking din komawa Funtua. A wannan karon kuma a cikin gidansu zai zauna kamar yadda Sulaiman ya yi fata. Gidansa kuma an gyara an bawa local government hayarsa tana saukar baki a cikinsa. Sulaiman da Faruku sun fara shiga Ladi farms suna ganin durk'ushewar da ta yi ba kadan ba ne. Akwia dabbobi sai dai ko kusa ba irin na da ba ne. Madarar da ake yi a da yanzu ba a iya yinta. Ba gyara irin na da. Don haka su uku. Oga Asad, Farukun, Sulaiman suka zuba makudan kuɗaden wahen ganin Ga gargadi. Aka gyara duk inda yake da gyara. Aka yi orders din shanun da suke bada madara masu yawa. Sannan aka siyo k'ananun dabbobin da babu irinsu a yanzu a gidan gonar. Anyi haka bisa sharadin idan gona ta fara bada riba za'a biya kowa kuɗinsa da ya zuba da ribarsa. Sai a dinga biyan ma'aikatan tunda ga kan Faruku har zuwa masu shara. Sauaran kudin kuma yana asususn baital man da za'a dinga yin hidimar wakafi da su. Komai ya gama daidaita Ladi farm ta fara aiki k'arkashin Jagorancin Faruku Musa Funtua. Ba jimawa Sulaiman ya fara shirin tafiya saudiyya tunda watanni biyu aka bashi. Zai je ya ajiye aikin ne daga nan ya tattaro komai nasa ya dawo gida gabad'aya. Abida tunda ta ga haka ta tsiri kukan da yake daga masa hankali. Kuma bata yi sai yana gida. Juyin duniya ta ba shi passport d'insa kuma ta ce bata dauka ba. Wani dare tana zaune har shabiyun dare tana masa kuka tamkar Mai wake. Hankalinsa ya kai koluluwar tashii. Ya ce "Za ki dawo da halayyarki ko Abida? Bana son kuka amma kullum sai ki tisa ni a gaba kina tayar mini da hankali ko? Na ce miki ba dadewa zan yi ba, zan dawo. Amma kin ki yarda da ni. Yanzu fad'a mini menene damuwarki akan tafiyar da zan yi?" Cikin kuka ta ce "Zamu raka ka ni da junior." "Abida junior ba shi da passport kafin ayi ya samu visa long process ne, kuma bana son mu tafi gabad'ayanmu mu bar shi, shi kadai kuka zai yi". Ta mike ta fita zuwa d'akinta ba jimawa ta dawo da passport din junior da nata. Ta mik'a masa ta ce yana da passport ga shi nan". Ya ce "To d'auko mini nawa." Ta yi shiru. Ya ce "Kin ji". "Ni fa dadyn junior ban gan shi ba, amma ka gama mana namu shirin zan duba maka a hankali cikikn kayanka ko za'a dace a gan shi ai baka da matsala don ticket kawai zaka siya." Ya ce "Allah ka shiryi Abida ". Haka ya shirya musu tafiya tare da ita da junior sannan hankalinta ya kwanta. Sai da ta ga Komai ya tabbata kowa yasan tare zasu tafi. Ta lallaba ta ajiye masa cikin kayansa a inda zai ga ni. Ranar da ya ga ni kuma ta hakikance dama tasan a gunsa zai fito don ita bata dauka ba. Haka ya yi shiru yana kallonta. Sun sauka a Jiddah lafiya lau. Kwanansu uku a Jeddah sannan suka wuce Makka suka sauke umra. A hotel suka kwana Sai da ya je ya bude gidansa aka share aka gyara sannan ya je ya dauko su ya kai Su can. Shi kuma ya dinga zirga zirga a asibitin Saudi Germany har ya kammala da su. Basu yarda sun sallame Shi gabad'aya ba. Kasar jamus ta ce nan da shekara d'aya ya dawo ya cigaba da aiki da su don sosai suke jin dad'i aiki da Shi. Sannan rife shi da ta yi ba bisa k'aida ba sai suke ta girmama shi tare da rarrashi don sun san an shiga hak'kinsa. Yayin da k'asar Saudiya kuma suka d'auke shi aiki amma a asibitinsu Na Makka da yake Kano. Dan haka Idan shekara ta cika Yana son dawowa ya dawo ya cigaba da aikinsa. Idan kuma zai cigaba da yi a Nigeria shikenan. Kullum safiya zata tashi ta gyara gidan ta yi musu abinci, sannan tayiwa junior wanka. Komai da wuri take yi ta kammala. Rannan Sulaiman ya ce "Abida yanzu ba ni da duty ne a gidan tunda babu yar aiki?" Ta rike baki ta ce "Dadyn junior aljanna nake nema tuburan. Na yafe maka da din ma da na dinga raba mana duty ba a hayyacina nake ba duk sharrin jinnul Ashiq ne". Ya yi dariya sosai don ya tabbatar Abida ta ajiye duk wani zafin kanta da tunanin aure ba dole ba ne. Satinsu uku sannan sukka dawo Nigeria ya fara aiki a babban asibitin Funtua. Da kuma Makka eye Hospital. Zancen budurwa ya bi ruwa. Litinin da talata yake shiga asibitin Funtua. Sai ya tafi Kano laraba da safe. Ya ga marasa lafiya laraba da yamma da alhamis da safe Har zuwa yammaci. Sai ya dawo Funtua juma'a. Asabar da lahadi kuma yana tare da Yaya Faruku a Ladi farm. Abida ta cigaba da aikinta a general Hospital Funtua. Amma Sulaiman ya tabbatar mata zasu koma Saudiya da zama next year sai ta zurfafa iliminta a can ba zasu dawo ba Sai sun tumbatsa da ilimin likitanci. Ta ji dad'i sosia. An saka junior a makaranta mafi kyau a Funtua. Tare da yaran Yaya Faruku suke tafiya. Hutun December Na k'arshe shekara gabad'aya yayan gidan da ya'yansu sukanhadi a Funtua dan yiwa Baba barka da dawowa. Har munira ta zo k'asar. Oga Asad da iyalinsa kaf, Usman da nasa iyalin, haka Hamida da Ansari kowa kwansa da kwarkwata, Saddiqa da Anisa da Yaya Salaha. Gida ya cika damkam. Oga Asad ya tura mota aka d'auko Faruku da Amra. Tunda Anisa ya koma Yola. Su da kansu sun tabbatar Idan zasu yi biki ko basu gayyaci kowa ba to kuwa kowa yana isu isu zasu cika taron. Bare a hada da sauaran dangi. Su Bilki suka hadu gabad'ayansu suka ke gidansu su MAMI da gidajena y'anuwanta suka gaishe tare da yi musu alheri. Sati guda suna tare kafin a hankali kowa ya koma inda ya fito da iyalinsa. Zuciyar kowa cike da farincikin dawowar gidansu tamkar shekarun baya. Baba K'arami da MAMI suna shan addu'o'i don su kad'ai ne babu su. *Watanni biyar a gaba.* Oga Asad da iyalinsa cikin wani shararren shagon gwalagwalai a birinin abudhabi na k'asar Dubai. Shirye shiryen bikin ya'yansu suke yi gida uku. Aysha khadija da Hafcy. Dan haka ya shirya musu tafiya don su yi siyayya. Dukkansu ya ce kowacce ta d'auki sarka da bangles yaran kuma Bilki ta taya su zabe. Dan haka suka dinga d'aukar design da ya kawata da su. Yayin da Bilki take taya Amal, Noor da Farha zabe. Suka kammala ya ce "ke ba ki d'auka ba". Ta murmusa ta ce "Na ga ka siya mini sarka da bangles sannan ina da wasu ma. Sun isa. Ya yi shiru yana mamakin yadda sam bata da zalamar abin duniya haka take tin filazal. Ya hasaso kura Abida da ita ce da tuni ta d'auki makekiyar sarkar da zai yi wahalar gaske ta skaa ta a wuyanta. Da wata ce ta ga ya siyawa ya'yansa mata shida abubuwan da suke cinye kudi mai yawa da sai ta ɗiba itama. Ya numfasa idonsa ya sauka kan wani dunkulallen zobe da zai yi nauyi a ma'auni ya ce "Wannan zai yi kyau a yatsanki sarauniyar shaiba. D'auki ki mayar da gurbin wanda kika bawa Autar Momi da bata gajiya da tara dukiya." Ta ce "Na gode." Washegari ya fita shi da ita. Yayin da yaran ma suka yi tafiyarsu daban tare d Alti da tagwaye. Kaitsaye shagon jiya suka koma. Ta dinga mamakin hakan. Na zato ya ce "Ki d'aukarwa Amrah sarka da bangles irin Wanda bilkis6ta d'auka". Dad'i ya ratsa ta don kuwa ta kud'ire zata dawo ita kad'ai ta siya mata irin wacce zata iya siya. Sai ga shi ya shayar da ita mamaki. Sosia ta ji dad'i. Bata gama mamakin hakan ba ya d'auko mata wata iron sarka mai balls tamkar dai carbi. Kallo daya zaka yi masa ka gane ya kerewa gold daraja. Kudinsa ya zarta kudin duka sarkokin da suka siya. Ya ce ina son murjani tunda ga wannan sai ki dinga mini kwalliya da shi sarauniyar shaiba. A gun ta rungume shi tana fadin "Na gode Baban Bilkisu, Allah ya saka da alheri ya shirya zuri'a Khadija da ba za'a yi mata jere ba tunda a London zata zauna ya sanya Bilki ta saka aka kara mata sarka da manyan warwaraye tunda y'anuwanta siyayya ake yi musu ta alfarma. Sun kammala siyayyar suturu da kayan kicin a Dubai. Suka zarce Turkey don oga yafi son asalin katakon k'asar turkey masu k'ololuwar daraja fiye da na Dubai. A can aka yaye twins da suka shekaru d'aya da haihuwa. Hafcy da khadija masu son hidimar suka shirya musu birthday celebration a wani kayataccen waje a birinin Istanbul. Sati biyu da dawowarsu Abuja Wanda ya yi daidai da bikin Laura wanda dama tazarar sati uku ne tsakanin bikinta da na su Aysha. Tuni kuma Bilki ta yiwa Amare order din sanyin flusher tare da bridal package daga Bojuwa herbs Kano. Kazar sababi ce kawai sai sati biki za'a turo musu wataƙila ma sai sun isa Funtua. Yara suna ta shirin tafiya Kaduna. Oga Asad ma a cikin hidimar take don da gaske shine uba.m ba abin da bai yi mata ba. Saura hud'u a fara biki ya Bilki ta shirya jibi zasu tafi Kaduna tare da yara zasu yi kwanaki hud'u su dawo. Shi sai ranar d'aurin aure zai zo. Ta kasa boye yadda bata son ta je. Ta ce "Baban Bilkisu gaskiya yara su tafi ni kuma mu je tare ranar d'aurin aure mu dawo". Ya zuba mata ido sosai har ta tsargu. Ya nisa ya ce "Ku je tare Maigado. Yarinyar a hannuna ta girma k'anwar Rukayya ce da tana da rai ai anan za'a yi komai, da bata raye kuma sai iyalina suje gabad'aya ba a tura yara kawai ba." Ta yi shiru tabbacin ita ba hakan take so ba. Tasan Surayya na can haduwa zasu yi da Laura da sauran y'anuwansu su tisa ta a gaba da kallo da zunde iri iri cikin isgili. Amma shi ba zai gane hakan ba. Menene aibu dan ta je rana daya ta dawo? Ya kalleta ya ce "Kin yi shiru sarauniyar shaiba. Ta sake yin shiru. Ya mike ya ce "Bilki jibi zaku tafi Kaduna tare da yara". Ya saka kai ya fice. Takaici ya shak'e mata wuya. Idanuwanta ya cika da k'walla. Akan me za'a ce sai ta je ta yi kwanaki a gidan da ba dolenta ba? Ita bata son cusa kai da shisshigi. Yara ne dole su je ba ita ba. Ko da ya dawo fuska a daure haka suka kwana kowa zuciyarsa na tunzure. Ya riga kuma ya kud'ire sai ta je Kaduna a gobe ko kuma ranta ya yi mummunan b'aci. Yadda ya fitittike ya dauki fishi ya sake hassala ta. Wato duk abin da ya shafi Rukayya bai d'auke shi da sauk'i ba. Da a ce ba sabgar da ta shafe ta ba ce ta tabbatar ba zai yi mata tilas irin haka bare har ya shareta ba. Bak'inciki kamar ta rusa ihu. Da yamma kan dole ta yarda Alti ta shirya mata kayanta a akwati. Tana hadawa tana fadin "Ni ban ga abin b'acin rai irin haka ba Mahmah. Ai da gaskiyarsa a hannunsa ta girma dole ki je a yi komai da ke. Bilki ta yi shiru don ba zasu fahimci manufarta ba. Kan dole da yamma da ya dawo ta shirya ta hau samansa don tasan idan ya cigaba da fishin goben ma ficewa zai yi ba tare da ya tsaya sun yi sallama ba. Idan kuma ta bar yara suka tafi su kad'ai ba sharewa k'alau zata yi ba, tunda ya kafe sai ta je, to sai ta je din kuwa. Ta shiga falonsa baya nan. Ta doshi cikin d'akin. Ta tarar da shi a kwance shame shame tabbacin a gajiye take matuƙa da gaske. Ta mak'ale a gefe bata isa gare shi ba, ba kuma ta juya ba. Ya kalli yadda ta yi. Dariya ta kama shi. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:33] Tunda ta zo ai yasan ta sauko ne. Dan haka ya had'iye fishinsa ya ce "Zo kusa da ni sarauniyar shaiba". Ta cuna baki ta d'auke fuskarta zuwa gefe daya. Haka ya yunk'ura ya tashi ya isa kusa da ita. Ya rik'o hannunta ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyoyinsa ya ce "Na huce da Maigadon zinare. Ya ake ciki ne, menene?" Cikin shagwaba ta ce "Kai zan tambaya tunda kake yi mini fishi haka siddan". Ya ce " A a ba haka siddan ba dai sarauniyar sheba. Kin kasa gane ni me gabad'aya. Ni fa Na tsani gardama mussaman ace matar da nake aure ne zata dinga yin fito ma fito akan umarnin da zan bata. Na ce ki shirya ki raka yara biki menene abun damuwa ko bacin rai a ciki?" Ta yi shiru don idan ta ja al'amarin rikicewa zai yi. Daga nan ya zarce da rattabo mata alfarmomin Rukayya. Ta nisa a dole ta ce "To zan je". Ya rungume ta yana fadin yauwa Bilkisu yayar Abida". Ta murmusa ta ce "Amma dai Alti da twins su zauna a gida bana jin dad'i kuma su rikicinsu yawa ne da su". Ya ce "Anya Maigado kasalar nan ta ki da saurin hassala ba gamo kika yi ba?" Ta yi masa shiru don kuwa tabbas cikin ne da ita. Ya ce "Ku tafi tare da su. Alti ta dinga tafiya da su gidan saddiqa suna kwana. Amma ke da Farha da tare yaran nan kuna wajen Hajiya". Ta yi shiru a zuciyarta kuma fadi take yi shi a dole a ce kaf iyalinsa sun halarci bikin k'anwar maimurabus. A fili kuma ta ce "To". Washegari suka shiga jirgin kasa da yamma zuwa Kaduna. Suka tarar da motar y'ansanda suna jiransu. Hajiya ta karɓe su ba laifi. Amma da ta shiga dakinta sai da ta yi kukan ganin ahalin Rukayya babu ita sai wata. Surayya ma bata nuna mata komai ba sai dai kuma ba wata fuska. Anyi hidima lafiya an kammala lafiya. Oga Asad kuma ya yi musu mugun k'ok'ari ko Rukayya na da rai iyakacin abin da zai yi kenan. Hatta ruwan roba da lemo da aka dinga wadaka da du duka daga gare shine. Kayan d'akinta kuma masu kyau ya yi mata. Hakan ya rage musu zafin Bilki da tagwayen ya'yanta don sun gane bata gama da shi ba, kamar yadda suke hasashe. Bilki kam a matuƙar takure ta yi wannan zaman don yini ake ana shiga ganinta a d'akin da aka sauke ta tamkar hoto. Tana ganin Laura da sanyi flusher da sauran kayan gyaran Amare ta gane Aysha ce ta yi mata Oder din kayan don da lambar a jikin dukkan kayansu. Shine ta dauki lambar a jikin nata kayan ta yi mata order itama. Ya zo d'aurin aure ya ce su gobe zasu dawo tunda yau za'a kai amarya. Ta roke shia akan idan akan kai amarya ta wuce gidan saddika ta kwana mana gobe sai ta zo ta d'auki yaran su yi sallama da Hajiya. Bai k'i ba ya amince don ya tabbatar ta yi iya kokarinta kuma zuwa gidan saddika ya kamata. Washegari kuwa sai shida jirginsu(train) ya tashi zuwa Abuja. Ya dinga yi mata sannu da tare da godiya har kunya ta kamata. Kwanaki kad'an suka fara shirin tafiya Funtua don a can za'a yi biki da d'aurin auren su Aysha. Kowa a zuri'arsu kokari yake ya yiwa oga Asad alheri don ya gane sun gode da hidimar da yake da su da dukiyarsa da bata tsole masa ido ba. Mazansu da matansu kuwa. Ba yadda za'a yi a dumfare shi da sunan bsbu waji abu ko ana buk'atar abu kaza kowa yi yake yi kawia da dukkan k'ok'arinsa. Hakan ya dada sanyaya zuciyar Baba tare da gasgata Allah ya karbi rokonsa na a jefa soyayya da tausayin juna a tsakaninsu gabad'aya. Bilki da Abida tare da amare Kano suka tafi takanas don yin lalle. Don yin Bilki a Kano ta tabbatar bata sake samun wacce ta iya kunshi irin Maman Farhan ba. Tiryantiryan har Farawa. Yini guda su aka yiwa kunshin da ya amsa sunasa. Oga Asad kuwa mita yake ace sai an tafi Kano yin kunshi don tsabar fitina da wuyar zama iron na Maigado. Sulaiman na gefe na taya shi da fadin ai Abida da Bilki fitina da munubarsu ta kai k'urewa. A hanasu zuwa su tisa mutum da matse matsen k'walla mai sake rauni a kirji". Ya bawa oga Asad dariya k'warai da gaske. Ya ce "Haka kuwa suke yi Dr Sulaiman to ya za'a sai hak'uri yara ne ai ". Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:35] Duk wata nasiha da ta dace ba wacce ba'a yiwa Amare ba. Haka ma Baba da Momi da dukkan iyayen Amare kowa ya yi musu fad'a tare da jaddada musu hak'uri ne kan gaba a cikin aure. Dangin Rukayya sun zo da yawansu aka dinga ina ka skaa da su tare don kuwa komai da su ake yi ba'a barsu sun koka rashin wani abu ba. Sai dai duk inda Bilki ta gilma idonsu na kanta. Basu gaji da nunata ga waɗanda basu gama ganeta a bikin Laura ba. Lallen Bilki da Abida da na Amare ba k'aramin kyau ya yi ba. Kowa sai ya tambayi wacce ta yi. Yaya Hamida ta karɓi lambar ta ce tana komawa Kano zata je itama a ta yarfa mata. For kanawa contact her for your special lalle......09076460821 farawa layin Alkairi suya. A lokacin bikin ne da manyan y'ansanda suka je d'aurin auren suka tisa da D.p.o da fad'an ace gida irin na su Oga Asad a garin Funtua babu d'ansanda ko daya da yake tsaron lafiyar iyayensa da danginsa? Ya dinga bada hak'uri tare da girke y'ansanda har shida a gidan. Wasu a bakin gate wasu a farfajiyar gidan. Wasu kuwa a bayan gidan. Sai da oga Asad ya ce sun yi yawa a bar guda biyu sun isa. Anyi taro lafiya ana gama lafiya an kai amare gadajensu a Abuja Aysha da Hafcy. Khadija kuma satin sama zasu wuce da mijinta London a can zata zauna. Dangin Rukayya sun koma da shatara na kayan arziki iri iri. Tunda kan kayan gara har zuwa kayan sabeniyos kala kala masu d'auke da sunan amare. Mussaman irin plates din ralzaplace08109544470. Da aka ci abinci da su a bikin sannan kuma har da su aka raba. Wato anyi harkar arziki, bikin girma aka yi. Da kansu sun gamsu Rukayya ta yi aure a cikin ahalin da suka san alheri suke kuma kamanta shi. Don kuwa oga Asad da dukkan iyawarsa yake girmamasu fiye da sadda take raye. Hidimar da ya yi a auran Laura da yadda aka karrama su a wnanan bikin ya rage jin zafinsa da Hajiyarsu Rukayya take yi. A hankali kowa aka fara tafiya. Munira ta fara wucewa. Sannan Usman da Salaha da Ansari. Kowa cikin farinciki yake. Oga Asad kuwa sai da ya yi kukan murna na yadda kafatalin kannensa suka hana shi jigata a bikin. Ya dinga godewa Allah da aka yi hidimar bikin bayan an yi sulhu dan ya tabbatar su Hamida ba zasu zo ba da ba'a yi sulhun ba. A ranar da zai tafi ya durkusa gaban Baba ya ce "Baba Allah ya saka maka da alheri, Ubangiji ya karbi hidimar da kake yiwa zumunci. Na gode da auren Bilkisu na gode da komai Allah yasa ka gama lafiya". Baba ya ce "Allah ya tsare ya dafa maka ya taimakeka akan girman da ya hau kanka. Ka zama mai hak'uri ka ninka juriya akan komai. Tawa ta k'are ko yau ma mutu na bar dukkan yaran nan a hannun Allah da hannunka. Ka yi hak'uri da kowa dan Allah". Dukkansu hawaye suke yi cikin alhini. Haka ya tisa iyalinsa suka tafi cikin kewa. Bai kuma bar garin ba sai da aka dasa harsashin fara gina masa tamftsetsan gida da zai dinga sauka shi da iyalinsa a Funtua. Shi kam ba zai dawo Funtua gabad'aya ba. Amma idan ya yi retire zai yawaita zaman garin. Idan ya gaji ya koma Abuja a haka har rayuwar ta kare. Watanniin su Aysha shida da aure Bilki ta haifo lafiyayen danta a birnin Newyork din Amurka. Tare da oga Asad da kuma Alti. Alti dai ana ta keta hazo. Don bata jima da dawowa daga aikin Hajj ba. Bilki ta roka mata oga ya biya Mata. Shi Kuma ganin yadda take masa hidima da yara gabad'aya babu banbancin ya sanya ya biya babu gardama. Da yake cikin hutu ne sai aka kai yaran Funtua tare da y'an aiki don su kula da tagwaye da suke tafiyarsu ko ina. Sun tafi da Alti me dan ta kula da jariri da Kuma Bilki. Ba yadda za'a yi ka kalli Alti ka ce yar aiki ce. Don suturar mai kyau take snayawa, haka nan Bilki bata mata iyaka da cin abin da take so a gidanta ba. Sai aka yi sa'a ita kuma tasan ya kamata tana yin komai cikin nutusawa bata tsallake iyakarta. Idan Bilki ta ce mata jira take yi danta Faruku ya girma ta danka masa ita Sai ta ji hawaye tana godewa Allah. Don da kansa ya kawo mata d'auki da ya hada ta da Bilki ta zame mata komai ta hana ta zubar da hawayen rashin y'aya' da dangi. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:39] Abida ta dinga mamakin haihuwar Bilki don boye mata cikin ta yi tunda ba gari daya suke ba. A bikin su Aysha kuma bai wani fito ba. Kunya take ji domin ta tuna sadda suke gulmar Rukayya ita da Abidan na ta saki jiki tana ta haihuwa rututu babu hutu har suna fadin namiji take so ta haifa ko su ce so take ta tara magada. Ashe ashe ra'ayin mijinta take bi. Gata itama ta shiga ciki tsundum. Sati biyar da haihuwar suka sauka a Kano daga nan suka isa Funtua dan kaiwa su momi yaron da ya ci sunan oga Asad ya kuma biyo kammaninsa tamkar dai tagwaye. Daga nan kuma su kwashe yaransu su wuce Abuja. Kafin ta bar Funtua ta yi order din maijego package a wajen Bojuwa herbs Kano don matuƙa da gaske ta yarda da kyaun kayan da ingancimsu ga sauk'in farashi. Tunda Abida mai kyankyanmi ta yaba kyaunsu. Ta gamsu da packaging dinsu da sabbin containers ne ai ba wanda zai kushe kayan ko ya ce ba masu kyau ba ne. PAGE 29 Shekaru uku a gaba. Zuwa Yanzu Amal Noor da Farha me a gaban Bilki. An an aurar da Bilkisu shekarar da ta gabata tana zaune a kasar Italy da mijinta. Amal ta kammala sakandire tana ajiy daya a jami'a a Riyad tare da Amrah suana hannun Abida da Sulaiman da suka Koma k'asar Saudiya shekaru biyu da suka wuce. Yayin da Noor take ajin biyar a sakandire Farha na aji uku. Bilki ta ta sake haihuwa bayan Mai sunan Asad da suke kiransa da Sadik. Yanzu mace take shayrwa Har ta yi wayo Mai sunan Momi. Tuni Faruku ya kammala sakandire yana karatunsa a jami'ar alkalam d take Katsina. Ba yadda oga bai yi ba ha zo Abuja ya yi ko ya tafi waje ya bada hak'urin said zai yi masters zai zo. Ammar ya kammala masters d'insa a Birmingham Na k'asar biryani ya dawo ya rungumi kasuwanci babansa Na canji a Abuja. Maganarsa da Amrah ta nuna da zarar ta kammala karatunta za'a yi biki. Shirye shiryen cikar Baba Babba shekaru tamanin da biyar a duniya suke yi. Wata irin liyafa aka shirya mass. Dukkansu yayan gidan sai da suka baro k'asashe da garutuwansu suka dira a Funtua. Kowa d'auke da kyautukan girma daban daban. Abida da y'arta ta zo mai sunan MAMI tana yawonta ko ina. Taro ya kai taro. Ya'ya sun girma sun zama manyan k'asa. Farincikin Baba baya misaltuwa. Ba abinda ya saka shi hawaye irin yadda shi kad'ai yake ganin yadda y'ay'ansu suka zama zarata masu rik'e da mukamai daban daban. Baba K'arami bai ga hakan ba. Aysha da Hafcy sun zo kowacce da goyonta. Bayan an gama ciye ciye tare da yanka kawataccen cake din deenasnakck and more Kano. Da Hamida ta zo da shi tare da snacks dinsu masu dadin gaske. Cikin nutsuwa aka dinga yin hotuna. Sai da ya jasu sallah. Kowa ya nutsu gaban Ubangiji. Sannan Baba ya juya garesu gabad'aya yana mamakin yawansu su da y'ay'ansu. Ya yi gyaran muraya tare da yi musu sallama. Suka amsa dukkansu a sanyaye don kuwa lallai Baba nasiha zai yi musu mai shiga jiki. Ya ce "Na yi farincikin ganinku gabadaya. Na samu nutsuwar ba zaku kaskanta ba don kuwa kun hada kai kowa kuma yana neman na kansa. Ina yi muku nasiha ku ji tsoron Allah, ku yi ibada, ku tsare ya'yanku daga fitowa a social media suna bayyana tsaraicinsu da sunan wayewa. Ku guji barci mai yawa don kuwa mabudin lalaci ne, lalaci kuwa yana haifar da dauwammen talauci. Ku guji shirka don cinye imani take yi tamkar yadda wuta ke cinye karmami. Shirka kala kala ce. To ku kula don da yawa mutanen yau suna cikin halakar sun kafirta basu ankara ba. Da yawa idan tsautsayi ko azal ya samu mutum ko jarabawa sai a jinginawa wani tare da gasgata sa hannuna ko wanene ya yi mini shihiri ko sammu. Duk abin da kuka ga same ku mai kyau, to ku jinginawa Allah. Ku yi masa godiya mai yawa. Idan marar dad'ine ku jinginawa jarraba da k'addara da ta same ku kai tsaye da aka rubuta cikin littafin k'addararku. K'addara kuwa bata sauyawa amma tasirin addu'a yana dakushe kaifinta. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:50] Kada ku ci kudin ruwa don Annabi ya la'anci mai cinsa. Ku guji sauya halitta Annabi ya ce tsinannunu masu feke hakori don su yi wishirya da masu aske gira. Manyan malaman addini sun ce masu sauya halitta daga bak'i zuwa launin fari da masu k'ara girman mazaunai ko kirji duk sun shiga cikin tsinuwar. Kunsan kuwa ko LIMAMIN unguwarku ne matuƙar mumini ne ya tsine muku ai kun yi hannun riga da yin albarka bare ma'aikin Allah. Ku yi iyakacin k'ok'arinku akan tarbiyar yaranku, ku kula da wa suke mu'amala. Ku guji hassada don kuwa durk'ushe mai yi take yi. Ku guji yanke hukunci cikin tsanani don yana janyo nadama. Ku guji b'arin zance don tuntuben harshe yafi tuntuben k'afa zafi. Ku kame daga yawan surutu marar amfani, ku yawaita istigifari. Ku dinga nazarin yadda aka yi mana kunnuwa biyu, idanuwa biyu amma baki daya. Ba dan komai ba ne illah jinmu da ganinmu su fi furucinmu yawa. Ku guji zina, ku nisance ta don kuwa tana kan gaba wajen gadar da talauci bayan haka kuma naso take yi cikin zuri'a tare da cinye imani. Annabi ya ce zina bashi ce. Ku tsare kanku, ku tsare bayanku daga fad'awa tarkonta. Ku guji yada bacin rai. Ku dinga boye laifin wanda suka saba muku don yada shi yana haifar da gaba. Ku yawaita yiwa magabatanku addu'ar rahma. Ku yiwa kanku tanadin lahira tamkar yanzu zaku tafi. Haka nan ku nemi duniya tamkar ba zaku mutu ba. Kowa ya nemi na kansa kada ku dogara da mutum guda. Duk zuri'ar da ta zubawa mutum d'aya ido take jiran tallafinsa da wuri zasu dirkake don kuwa Allah ne kad'ai zai iya da bukatunku babu gajiyawa. Ku nunawa ya'y'anku muhimmanci dogaro da kai. Kowa ya nemi na kansa sai zumunci ya yi dad'i. Duk zuri'ar da kowa yake neman na kansa suke karatu zasu yi karfi su d'aukaka zasu daina zubawa mutum d'aya da ya yi shura a cikinsu idon ya yi musu hidimar dole da bata dole ba, idan bai yi ba kuma, sai a tisa shi a gaba da kushe da gaba. Mafi yawa irin wadannan sun yi iyakacin kokarinsu yau da gobe ce ta sanya suka gaza ko suka daina yi. Amma idan kowa na da sana'a komin ƙanƙantarta za'a samu sauk'in zarmewar da ake yi na jiran wane ya bayar. Masu kud'in ma a yanzu da rayuwa ta tsananta nemansa suke yi kasuwanci suke yi iri iri, ya'yanasu ma sana'a suke yi don su samu kudin, to akan me za'a yi ta zuba musu ido a kullum su bayar?" Daidai nan ya yi shiru yana nazarin yadda jikinsu ya mutu tub'us wasu ma k'walla suke gogewa. Ya nisa ya cigaba da fadin ku rarraba ya'yanku su karanci fanni daban daban ta yadda duk wata kafa kuna da k'afa. Ku yi kasuwanci, ku yi Nima Annabi ya ce arzikin Duniya na kasuwa da gona. Ku yawaita istigifari don mabudin alheri ne. Duk abin da ya yi muku tsanani ku yawaita zubar masa istigifari Allah zai warware muku cikin hikimarsa. Kada ku tsangwami wanda kowacce ta samu jinkirin aure don wannan ikon Allah ne. Duk saurin mai sauri sai ya jira ikon Allah. Aure, haihuwa da mutuwa lokaci ne ba'a yinsu sai lokacinsu ya yi. Annabawa uku a jere da Allah ya ambacesu cikin suratul Maryam. Ilyas Yahya da Isa (A.S.). Basu taba aure ba. Amma rashin aurensu bai hana a basu annabta ba kenan idan mutum a kame yake rashin yin aure ba tawaya ba ce, tunda ko a shari'a ma ba farilla ba ce, sunna ce mai karfi. Nana Aisha bata taɓa haihuwa ba, ita ko bari bata taba yi ba, amma sunanta ba zai shafe ba a doron kasa ba, don kuwa sai aka azurta ta da ilimin da ta yada shi ciki al'umma. Rashin haihuwarta bai hana miji ya sonta fiye da kowa cikin matansa ba. Allah kuma da kansa ya ce yana jin nauyin wanda bai bawa haihuwa ba Ashe kuwa duk wanda ya tsangwamesu Allah yake yiwa isgili, ya jira kuma hukunci ta inda bai yi zato ba. Ku dinga rabon gado da wuri tare da iyakance dukiyar kowa ya hanyar rubutu. Wataƙila yaune had'uwarmuta k'arshe da wasu daga cikinku. Ina rokonku ku girmama manyanku, manyan kuma ku tausayawa kannenku, ku mu'amalancesu da kyautatawa. Allah ya taimakemu gabad'aya. Allah ya yi muku albarka ya rufa muku asiri duniya da lahira ". suka amsa da fadin ",Ameen Baba Allah ya kara maka lafiya da imani". Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:54] *DINGISHIN KWAD'O* PAGE 30 *Epilogue* Bayan shekara biyu. Ana ta Shirin auren Ammar da Amrah ta kammala karatun likitanci tana housemanship a specialist Hospital Abuja. Farha tana jikin Bilki ta ce "Mahmah kinsan me ya ya Faruku ya ce min?" Bilki ta jijjiga kai tare da fadin a a ". "Wai na tambaye shi budurwarsa ta alkalam ya ce abokiyar karatunsa ce. Farha ce matarsa. Na ce a ina take wai a Abuja gidan Mahmah". Mahma to dama Yaya da kanwa suna yin aure ne?" Bilki ta ce "Basa yi ". Daga haka ta shige wanka ta barta zaune a bakin gado. Ta koma d'akinta. Ta kira shi a waya. Yaya Faruku ka rikita ni fa. Kuma Mahma ta ce "no". Ya ce "saboda me to?" Saboda Yaya da kanwa basa yin aure mana". Ya ce "Ki ce mata da gaske nake yi dan haka mu za'a fara a kanmu.' Kwanaki biyu a tsakani ta sake tambayar Bilki. Mahma dan Allah ki fad'a mini wacece babar Yaya Faruku dan Allah? Don har cikin zuciyarta ga ni take yi sai dai idan ba shi Mahmah ta haifa ba amma ba ita ba kam. Bilki ta ce "Alti ce'. Farha ta rike kirjinta tare da fadin Ashe "Da gaske yake da ya ce ba ke kika haife shi ba. Allah sarki". Bilki ta wuce ta tana jin yanzu ya yi wuri da yawa. Tunda Bana zai kammala digirin dole ya wuce wata k'asar ko baya so don ba zata yarda ya damawa Farha lissafi ba. Zuwa yanzu Farha ta wasiwasi take yi akan su waye suka haife su ita da Faruku? Dole akwia wanda ba Mahmah ce ta haifa ba a cikikinsu. Haka kawia take fatan Allah yasa ita ta haife ta. Amma tana jin soyayyar ammi da su junior a ranta fiye da kowa a cikin daginsu. Sannan yadda take ganin soyayyarta a idanuwan Mahmah haka take gani a idanuwan ammi. Ana yin hutu Noor da Farha suka cewa Dady suna son tafiya Saudi gidansu junior daga nan su yi umrah. Bai k'i ya amince aka fara nema musu visa. Da zasu tafi sai da Abida ta matsa a tafi mata da ciccibi da kazar sababi tunda freezing dinsu ake yi ba zasu narke ba tunda ba doguwar tafiya ba ce. Sanyi flusher ne aka tafi mata da saiwowin tunda bojuwa herbs suna bayarwa sia ka dafa da kanka tunda ba'a shiga da abu mai ruwa cikin jirgi. Haka aka Abida ta matsa sai da aka yiwa maminta d'inkunan native wears don ta gamsu da k'warewar teler da Bilki take bawa dinkin Farha da take k'arama. ku wannan layin masu buk'atar su a dinga yiwa y'ay'ansu mata dinkuna irin na yan gayu y'anuwan masu kud'i. Sun isa lafiya, junior ya yi murna ganinsu kamar me. Mami kanwarsa dai bata kama da shi da Farha. Gana ganinta ka Ga Abida. Tafi kama da khadijan oga da twins. Farha ta daure ta tambayi Abida da ta ga Noor na barci, akan wacece ta haife ta ita ko Mahmah? Abida ta murmusa ta ce itace mamanki mana. Shi kuma Alti ce ta haife shi". Abida ta shige daki ta fashe da kuka. Sulaiman ya diririce ya ce "menene?" Ta ce "Tsufan da bana so ne yake sake shirin yanko mana ni da Bilki. Tunda aka saka auren Amrah nake ta rarrashin zuciyata kada na yi kuka. Sai kawai yanzu Farha take tambayata wacece ta haife ta, wacece ta haifi Faruk don ya ce yana sonta. Har y'ar Farhar nan ma girman ya zo kenan?" Kuka take yi bilhakki. Ya jijjiga kai ya yi dariya tare da fadin Abida duniya Farha na shirin kammala sakandire kina fadin yar yarinyace. Kuma wa ya ce tsufa zai yanko muku? Ni fa har yanzu kallon ki nake yi tamkar MAMI. Diyarsu mai shekaru hud'u. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:57] Dad'i ya kamata ta goge hawayenta tare da fadin "Har na ji sanyi da nutsuwa." Ya k'yalkyale da dariya tare da mamakinta. Farha ta sake tambayar Sulaiman akan wacece ta haife ta a tsakanin Mahmah da Ammi dan Allah? Kaitsaye ya ce mata Ammi ce ta haife ki. Amma Mahma ce mamanki don tun kafin ki zo duniya da shekeru goma ta bata ke". Farha ta yi shiru. Ta ce "Kenan kaine Dadyna?" Ya yi mata shiru. Ta rike hannunsa ta ce "Ashe shiyasa nake jin ku tamkar yadda nake jin Mahmah a raina?" Ya murmusa ya ce "Amma dai Bilkina ce uwarki, Abida ta haifa mata ke". Ta ce "Har abada kuwa Dady". Tunda ga lokacin bata sake tayar da maganar ba. Bata taɓa nunawa Bilki ta gane ba, tunda ta k'i yarda ta fad'a mata ba ita ta haife ta ba. Ba ma zata sake tambayar ba tunda ta ga bata so. Shikenan ta sakawa zuciyarta Faruk ne mijinta tunda yana sonta ita ma tana sonsa. Alti kuwa tunda Faruku ya fad'a mata ta dinga kula masa da Farha shikenan take taya shi yaki. Komai ta ga ni sai ta siya ta bawa Farha tana fadin toshi ne. Har gobe bai son ya Dade a Abuja. Ko da Amrah yanzu bata nan ya daurewa zuciyarsa yana zaune a gidansu tare da Babansa. A yanzu da ya fara hankali sosai yake tallafawa a cikin gidan tunda asusunsa baya rasa kud'i masu auki sosai. Oga ya tura masa. Mai sunansa ya tura masa. Hatta Ammar da yake kula da harkokin babansa a Abuja tura masa kudi yake yi. Yana sonsa don shine takwaran ABBAnsu na farko. Haka nan Bilki. Har gobe kuma suna tare da Alawiyya da take da yaranta. Tana zuwa gidan wajensa lokaci zuwa lokaci tana yi masa gyara. Sannan har Abuja tana lekawa wajen Bilki. *Za'a buga hard copy mai bukata sai ta yi magana a buga da ita* *Tare Littafin BAK'AR TA'ADA za'a buga hard copy Duk Mai so Sai Ta yi magana a yi da ita *. Tana zaune a falon oga Asad tana jin littafin Malamin bogi da da ake k'arantawa a tashar limamin tsakar gida. Gaskiya Maman Afra ta sanya ta dariya sosai. Daga nan ta tsallaka ainihin tashar tsakar gida tana jin Turken gida na marubuciya Janafty. K'iran Abida ya fado wayar ta amsa. Kaitsaye ta ce "Abida yau na yi dariya saii yau fa na kammala sauararon Malamin bogi na Maman Afra. Yanzu TURKEN GIDA nake bi." Abida ta ce "Hmm wani littafin nake ji yanzu yadda kika san almara kamar rayuwar gidanmu marubuciyar ta d'auko take rubutu komai tiryan tiryan tamkar a majigi. Zuciyata ta kasa nutsuwa na ce bari na kira ki ke ce mai gayyaar jama'a ko kinsan marubuciyar kin bata labarin mu ita kuma ta yi giggiwar rubutawa babu neman izinin kowa". Bilki ta ce ya sunan littafin da kuma marubuciyar?" "Dingishin KWAD'O Ita kuma sunanta Surayya Dahiru Gwaram." Abida ta amsa mata a takaice. Bilki ta ce "Na dai saurari littafinta HALIN YAU, Sabo da Kaza a Tsakar gida. Amma Gwaram din ba na ce ga inda take ba fa". Abida ta ce ni kam na karance su, kamar dai a Jigawa ne. Amma kaina ya kulle zan yi magana da Yaya Munira idan kuwa labarinmu ta ji, ta yi kuskuren yayatamu a duniya sai mun gurfanar da ita a gaban kuliya". Bilki ta kyakyace da dariya tare da fadin Abida kanwata. Amma bari nima zan bincika ya ma kika ce sunan labarin?" "Dingishin kwado kuma Maigado har na shiga paid group dinta tunda ta kammala a can na ji k'arshen labarin, amma duk da haka kullun sai na sauarari na tashar maisanyi. Kuma duk na danna mata likes a episode 1 10 don labarin ya ja hankalina k'warai da gaske ". Bilki ta ce "Nima zan koma na danna mata don ban yi ba, to ya batun gurfanar da ita kuma?" Abida ta yi dariya ta ce "ke na hak'ura idan ma labarin namu ne Allah yasa ya zama aya da gargadi ga masu hankali." Bilki ta ce "ameen." Suka yi sallama. Oga Asad ya kalli Bilki ya ce "Kuna nufin baku san Gwaram ba?" Ta ce "Eh". Ya jijjiga kai ya ce garinmu ne ni". Ta kalle shi ta ce "Ta ina Baban Bilkisu?" Ya ce tun shekarun baya mun je yiwa oganmu ta'aziyar rashin mahaifinsa a lokacin ina Calabar. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 16:00] Garin manya ne fa. Ai yanzu da zan ganta sai na yi saluting dinta don kuwa former I.G Sulaiman Abba Gwaram ba abinda da bai yi mini na alheri ba, ya taimakemu k'warai da gaske a lokacin da muke k'ananun y'ansanda. Wataran zan d'auke ki mu je ki gaishe shi bamu da nisa da shi, daga nan na wuce Maitama na kai ki gidan NEPA kacokan dan ki gaida tsoho mai ran k'arfe Eng. Hamza Gwaram da iyalinsa gabad'aya, wataƙila ma ki yi katarin ganin marubuciyar a gidan. Daga nan sai ki gane Gwaram tana da manyan mutanen da suka kai k'ololuwar mukamin da ba zai yiwu ace an fade ta ace ba'a santa ba. Idan mun je Kano kuma zan kai ki gidan sardauna marigayi Bello Maitama. Na wuce da ke gidan Justice Tijjani Abubakar Gwaram. Ke suna da yawa fa. Ban da ma mutuwa da bata barinmu da na kira miki G.m. Dahiru Nepa yanzun nan a waya. Ban da tsofaffin Y'an siyasar jiya Shugaban gwagwarmayar Nepu. Hon Sani Gwaram." Bilkisu cikin alhini ta ce "Allah ya jiƙansu da Rahama". Ya ce "Ameen Maigado.". Lallai ya kamata marubuciyar ta yi rubutu a garinsu tunda ta yi a Funtua, Toro da Bulkachuwa.". Koda yake ta ce saboda Justice Zainab Bulkachuwa ne ya sanya ta yi labari a Bulkachuwa." "Sannu a hankali zata yi a garin nasu tunda ta yi a garin wasu ma". Oga Asad ya fad'a a takaice. * Oga Asad ya shirya musu tafiya Shi da Bilki zuwa k'asr itali dan su dubo Bilkisu da ya haihu daga can su zarce Canada. A birinin rome take zaune dan haka a can suka yada zango. Kwanansu biyar a garin. Ta kaisu gidan Anty zaliha Maman safiyya. Don sosai ta zame mata uwa take kulawa da ita. Bilki ta dinga Godiya da fatan alheri ga anti zaliha. Daga Rome suka wuce birin suak shiga jirgin kasa zuwa birinin Caserta don kaiwa abokiyar karatunta a B.U.K. Aunty Fauziya Fiji ziyara. Sun samu kyakkwar tarba ta mussaman. Sun jima kafin su tafi bayan oga Asad ya yiwa yaranta alheri. Fatan alheri ga yayata Anty Fauziya Fiji da anty zaliha usman da iyalinsu gabad'aya da suke zaune a kasar Italy. Daga nan suka wuce k'asar Canada takanas don Bilkisu ta gaida takwararta Barr Bilkisu Garba Ibrahim. Duk yadda Maigado tasan barista mai karamci ce sai da ta gane ashe bata ga komai ba cikin karamcinta sai da ta je muhallinta. Saukar girma ta samu. Bilki ta dinga nazarin barista tana daukar kwas din sirrin gayu da kwalliya da kuma alheri da iya mu'amala. Fatan alheri gareki da iyalinki Barista. Allah ya shirya miki zuria ya kara arziki. Sun dawo gida Nigeria lafiya. Rayuwa ya cigaba da gungurawa kowa na hakuri da yadda k'addara zaba masa. Haihuwa dai ta tsayawa Bilki. Ta ce tunda da bakinsa ya ce tana yin 43 ta gama, yanzu da take 42 ma ai duk d'aya ne. Dole ya hak'ura ya k'yale ta. Sai baje kolin soyayya da tattala juna tamkar ba Hausawa ba. Tafiya ya same Shi da tawagar Shugaban kasa zuwa k'asar burtaniya. Kan dole ya tafi Babu ita. Bilki tsabar sangarta har da kuka wiwi. Yayin da ya dinga lallabata tare da bata hak'uri akan ba dadewa zai yi ba. Kwanansu daya ya k'irata. "I miss you Gwarzona." Balki ta faɗa cikin taɓara jikinsa ya mutu. "Na yi kewarki Balkina. tamkar na tsero na dawo. Shirya bari mu yi vedio call ko na rage Jim kewar nan ta ki." Ya katse wayar. Ta tashi ya shirya irin shirin da yake so. Ya k'irata kuwa suka gama sheke ayarsu tamkar ba oga ne yake zaro manyan kalamai masu nauyi ba. Cikin son ta sake narkar da zuciyarsa ta ce "Baban Bilkisu ina sonka, ina son na rayu da kai ina jin dadinka sosai". "Allah Maigadona? Ki ce zan samu tarba ta mussaman." Ta ce "irin wacce ba'a taba yi maka ba." Ya murmusa ya ce "Na gode Allah ya yi miki albarka." Ranar da ya dawo cikin dare ya sauka. A bakin k'ofar falo ya tarar da ita "Welcome back Gwarzona." Ta faɗa cikin wata irin murya. Ga mamakinta sai ji ta yi ya sunkuce ta zuwa cikin falon sannan ya dire ta. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 16:03] Ita kuma ta yi masa wani irin juyo don ya ga mutanen nasa da kyau. Don wata irin lalatacciyar riga ta sanya da ya fito da figure 8 ɗinta. Ya kidime ya jata jikinsa yana fadin "I really missed you Maigadona". A daddafe suka hau sama. Ya yi wanka ya ci abinci marar nauyi sannan aka shiga cin uwar sabada. Hankalin Bilki ya kwnata. Don oga Asad ya mayar da ita queen ta sosai a cikin gidansa. Dukkan niimar rayuwa Ubangiji ya yi mata. Hak'uri da juriya da ta yi ta ga sakamakonsa. Ubangiji ya yi sakayya a tsakaninta da Sahal don ko da basa tare tana sane da har gobe yana cin arzikinta. Ta tuna tsananin da ta shiga a farkon aurenta da oga Asad. Baba Babba ya yi ta jadadda mata kalmar ta yu6 hakuri, da ba ta yi hakuri ba da yau ba ta san inda wata kaddaran za ta sake jefata ba. Don ta riga ta gane duk inda ka je a duniya sai ka fuskanci k'alubale ka kuma yi hak'uri. Yin gaggawa yana nufin yin da nasani mai tsananin gaske. Shiyasa yadda a kullum take yiwa iyayenta addu'ar samun rahama haka take yiwa Baba Babba addu'ar ya gama da duniya lafiya don ya yi dukkan k'ok'arinsa akan aurenta da dukkan al'amarinsu gabad'aya. Sannan Yaya Faruku tana roka masa bene hawa na kololuwar masu daraja a cikin aljanna. Don ya yi mata zumunci iyaka, ya yi sadaukarwa mai yawa. Don haka tana masa kallon uba ne ba Yaya ba. Yana cikin kariman mutanen da ta ga ni a dukkan tsayin rayuwarta. Duk kuma nasarar da ta samu a duniya tana da tabbacin da tallafinsa a ciki, don ko auren nan na oga da take jin dad'insa a yanzu shine dai sila. Cikin dare tana kwance jikin oga. Ta yi ligi ligi ya k'ure mata jarumtarta. A tausashe ya ce "Na gode Maigado, kkin sabumta tsufana, kina bani shwarwari kina kula da y'ay'ana da gidana. Ke alheri ce." A kasalance ta ce "Ni ma na gode da kokarinka a kaina gwarzona" Yana Jin dadin gwarzon da take fad'a masa. "In sha Allhu, ba zan taɓa gazawa ba, ina roƙon Allah ya cigaba da bani karfin da ko da yaushe za ki ji kin gamsu da ni, Alllah ya yi miki albarka Allah ya kara ma Baba Babba Lafiya Allah ya ba ma Faruku aljannah, Allah ya jikan Baba karami da mami Allah ya haɗa mu da su a darusslam." "Amin Amin Gwarzon Bilki uban Bilki kuma I.G din gobe da yardar Allah." Balki ta faɗa kwalla na ziraro mata, ta dago tana kallonsa cikin wani irin shauki. Shi din gwarzone , namijin duniya ne na gaske. Mai adalci ne. Baya yiwa duk wanda ya dangance shi kwangen dukiyarsa bare kuma su iyalinsa. Ta ba shi lambar yabo a zuciyarta da idanuwanta. Ya rumgumo ta yana faɗin" Amin Amin my BABYY." Bilki ta kyayace da dariya, tana maimaita sunan, shima dariya yake yi, kafin su kama bakin juna suna sumbata cikin shauki da soyayya mai tsayawa a zuciya. *Tsokaci*. *Assalamu alaikum, barkanmu da yini ya iyalin?* *Allah ya taimakemu gabad'aya*. *Ina ta samun k'iran waya daban daban akan ingancin kiranyen da Abida ta yiwa Dr Sule*. *A gaskiyar magana na saka me don hi Shirin labarin*. *Don haka a daina tambayar fatawar ingancin, kawai duk addu'ar da za'a yi akan tsarin shari'a tare da cikkaken yaƙinin in sha Allah Ubangiji zai karɓa* *Bayan haka ina son na sanar da ku cewar gabad'aya labarin nan kirkirarren labarine(fiction) bai faru a gaske ba, bai shafe ni ba, bai kuma shafi wani nawa ba*. *Haka sunaye da garuruwan da na ambata duk kirkirarrune bana kowa ba ne".* *ALHAMDULILLAHI* *ALHAMDULILLAH* *Godiya ga dukkan waɗanda suka siyi labarin nan.* *Na gode, Na gode da hak'urinku Allah ya ya bar zumunci. Allah ya yiwa dukiyarkubda zuri'arku albarka*. *Yan comment section* *Ina matuƙar godiya a gareku gabad'aya*. *Mussaman* *Anty Maryam Saminu Sulaiman* *Sarauniyar sharhi*. *Da* *Anty Nana Bauchi* *Da dukkanku da ba zai yiwu na iya kama sunanku gabad'aya ba*. *Na gode Allah ya saka muku da alheri ya bar zumunci*. *Godiya ta mussaman ga* *Haj Rabi Sani madakin Gini*