489 Results in the "Hausa Novels" category
-
HALIMA Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce, "Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki…-
247.6 K • Completed
-
-
Nayi mamakin yanda Bilal bai musa ba lokacin da nayi masa maganar service. Nayi sa'a a lokacin ana dab da fara registration dama, ranar da aka buɗe kuwa banyi wasa ba na je na yi a matsayin mara aure saboda ko da na gaya masan ya ce toh nayi zaton zai je ya fitar da certificate of marriage da domicile letter waɗanda zan buƙata amma har ranar ta zo bai ce mun komai ba nima kuma banyi masa magana ba dan ina gudun kada ya canza ra'ayi. Posting ya fito aka kaini, ban wani damu ba tunda ba nesa bane nasan…-
247.6 K • Completed
-
-
Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da…-
247.6 K • Completed
-
-
Kwanaki biyu da suka biyo baya nayi su ne cikin taimakon ubangiji domin a kowacce daƙiƙa ji nakeyi tamkar numfashi na zai iya yankewa. Babu abinda yake shiga cikina banda ruwa da paracetamol da nake ta banka saboda azababben ciwon da kaina kama, ikon Allah kaɗai yake riƙe dani akan ƙafafuna hatta yaran ma game game kawai nake musu duk abinda hannu ya kai nake haɗawa na basu su ci. Nayi kuka har hawayena sun ƙafe ya zama sai na zuci nakeyi, a duk sanda na tuna abinda naji kuma na gani dangane da…-
247.6 K • Completed
-
-
Amirah ta ɗaga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu. "Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa "Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace "Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace "Toh lafiya dai?" "Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana…-
247.6 K • Completed
-
-
Madallah da mutane masu karamci. Nagode ƙwarai dagaske, ina lafiya wani aiki ne ya ɗauke ni tsayin kwanaki amma Alhamdulillah mun kammala na kuma gode ƙwarai da haƙurinku ina fatan har mu kammala babu wani uzuri da zai sake gifta mana 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 *KURA A RUMBU littafin kuɗi ne 800, yake mai jira nayi posting ki fitar kiji tsoron Allah dakw da wacce take jira ki turo ta karanta a bati ku guji haƙƙin komai ƙanƙantarsa. Duk wacce ta shirya sauke nauyi ta tura mun kuɗi na a asususun…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Thirty
Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba. "Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin. Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Thirteen
Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Ten
Ɗaki na koma dan bazan iya karyawa ni kaɗai ba na fara sabawa tun da mukayi aure da Bilal bamu taɓa raba kwano ba, yanzu bama na jin cin abincin raina duk babu daɗi. Tun ina sauraron jin ya buɗe ƙofa ya fito har bacci ya kwashe ni a kishingiɗen da nake. Ban farka ba se da naji ana ƙwala kiran sallar azahar, nasha mamakin irin baccin da nayi. Se da sake watsa ruwa saboda jiki na da naji duk ya ɗaure sannan nayi alwala na fito ina jina fayau ciki na a rarake. Sallar na farayi sannan na gyara…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Sixty
Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Sixteen
*Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri* Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Six
Duk nazarin na ban hango abin da take ganin na rashin dai dai ba. Rashin yi mun kyauta ne aibun sa ko kuwa rashin kammala ginin da be yi ba da kuma zancen lefe? A cikin ukun sune abin da nake ganin Anty Labiban take emphasizing se dai ni a ganin ta wannan ai ba komai bane ba. Bilal nake so ba abun hannunsa ba. Iya kar ƙoƙari yana yi gurin ganin ya kammala in da ze ajiye ni kuma ba a ɗaura auren nan an ga be yi mun lefe ba balle su ce wani abu. Ni duk wani lefe da wasu bidi'o'i basa gabana duk da dai ba…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 20 21 22 … 46 Next
