489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Na ɗauka da wasa Mama take yi sai washe gari da safe bayan mun yi wanka na koma rage baccin da ban yi ba cikin dare saboda Kukan Al'amin ban jima da kwanciya ba Zainab ta tashe ni akan Mama tana kira na. A falon Abba na same ta, muka sake gaisawa sai Abba ya ce "Mamanku ta ce mijin ki yayi tafiya ko?" Ba tare da na kalle shi ba na amsa haɗi da gyaɗa masa kai dan haka kawai kuma kunyar Abban na ke ji yanzu, ni dai jiki na bai bani aka Baba Jummai bata basu labarin abin da ya faru ba yanda kuma suka mun…-
247.6 K • Completed
-
-
Ina ɗaki, hayaniyar yan dubiya duk ta cika mun kunne, tun da Anty Amina ta tambaye ni abinda za'a dafa da rana na nuna mata shinkafa da mai wanda su kaɗai suka suka rage mana a gidan, ina ganin Hajja ta shiga kitchen ɗin na fito na barsu. Ta biyo ni ɗaki tana tambaya ta sauran kayan girki nace mata iya abinda muke dashi kenan, zata yi magana Anty Aminan ta jata waje shikenan nayi zamana a ɗakin ban sake fita ba suma kuma babu wadda ta sake leƙa ni. Da yaron yana gurin su ma aka maido mun dashi…-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin na kai masa wayar ta yanke dan haka da na bashi ajiye ta ya yi ya cigaba da cin abincin ba tare da ya duba wanene ya kira ba. Duk yanda na so na mayar da hankali na kan Al'amin dake ƙananun rigima sai na kasa ƙarshe kawai na goya shi na yi tsaye ina kallon Bilal da ke cin abinci wayar sa na ƙara alamar shigowar wani kiran amma be amsa ba. Kamar me tsoron magana na ce masa "Ana kiran ka a waya fa" ya ɗago ya kalle ni kafin ya ɗaga wayar ya karata a kunnen sa lokaci ɗaya yana miƙewa tsaye.…-
247.6 K • Completed
-
-
A ƙaramar akwati na zuba mana duk abun da na san zamu buƙata a yinin, Baba Jummai ta goya Al'amin tana tsaye tana jiran na yafa gyale na da na ajiye a gefe. Zama na yi a gefen gado ina rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya, ta kalle ni ta ce "Ya kuma kika zauna? Tun da dai an kaiwa maƙwaftan nan abinci se ki tashi mu tafi kuma su ce zasu shigo yinin suna". "Baba ban gayawa Bilal ba" na faɗa ba tare da na kalle ta ba, "Naga abinda ya ishe ni ni Hasana, yanzu gidan ku ɗin da zaki tafi shine kike…-
247.6 K • Completed
-
-
Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama haɗa kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kashewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da jakar ta daga ɗaki ina kallon ta na ce "Kuma wlh karki gayawa kowa abin da ya faru, kawai…-
247.6 K • Completed
-
-
Washe gari da wuri na fara haɗa kayan mu dan komawa gidan Anty Labiba duk da jirgin dare su Mama zasu bi amma da wuri nake so na tafi can ɗin dan ko rakiya ba zan tsaya yi musu ba. Gaba ɗaya raina babu daɗi na tashi, na ɗauka Bilal zai sake kira na daga baya ko kuma da asuba amma shiru. Ina zuge akwatin kaya na Zainab ta shigo ta ce mun na zo na yi baƙi, na ɗora mayafin doguwar rigar yadin jiki na ina ƙoƙarin kawar da ɓacin ran dake kwance akan fuskata na fita falon. Turus na yi a bakin ƙofa…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Twenty
Washe gari har azahar banga Bilal kuma babu wani daga dangin sa se yan uwana da suke ta kaikawo a gurin. A ƙa'ida da safe za'a sallame mu tunda na cike awanni shida na ƙa'ida amma da likita ya shigo duba mu ya ɗauki yaron se yace akwai alamun jundice a tare dashi dan haka ba zasu sallame mu a lokacin ba se mun ƙara 12 hours under observation idan abun is not severe da zamu iya tafiya gida tohm. Nan da nan hankali na ya tashi saboda yanda nake jin labarin jundice ance yana kashe jarirai, shaiɗan da…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Twelve
"Idan har izini na kike nema ban yarda ba, ko da yake ai kin saba yin gaban kanki. Kiyi duk yanda kika so Halima lokacin ki ne dama kika samu". Abinda Bilal ya gaya mun kenan bayan dana same shi akan maganar posting ɗina zuwa garin Bauchi. Duk yanda kuma naso da ya zauna muyi magana ta fahimta yaƙi, ƙarshe ma barin mun part ɗin yayi gaba ɗaya ya tafi can part ɗin sa da falon kaɗai muke amfani dashi ina jin sa a daren ya gyara ɗakin tun da dama da hado da komai a ciki ya dawo ya ɗauki bedsheets da…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Three
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Ranar ina idar da sallar isha'i nayi bacci saboda ɓacin rai seda na farka da asuba sannan naga missed calls ɗin Bilal guda biyu ya kirani tun ƙarfe tara na dare. Duk yanda nake cike da haushin abinda yamun jiya amma haka nan zuciyar dake sonsa ta angiza ni nabi kiran nasa. Murya ƙasa ƙasa muka gaisa ya shaida mun yana masallaci idanya fita ze kirani. Ko yasan ina fushi dashi ne se gashi bayan ya fito…-
247.6 K • Completed
-
-
*Barkanmu da Sallah yan uwa* 🙏🏽 Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan shiga cigiyar inda Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wadda ban tantance hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko karɓi canji ba bayan na sauka na shige gidan a bakin ƙofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito daga falo kamar zata hantsila da Sharifa a hannunta ta…-
247.6 K • Completed
-
-
Banji komai dangane zaman da ya ce Hajja zatayi ba dukda nasan ba jituwa mukeyi da ita ba amma kuma abinda yake so ne kuma wanda zai faranta masa ni kuma burina a koda yaushe kenan. Har ya fita ya kirani a waya yace na shirya gashi nan dawowa zamu fita tare, da nace masa Al'amin fa kar lokacin tashin su yayi bana nan sai ya ce ai ba jimawa zamuyi ba dan haka nayi maza na canza kayana na shirya Sharifa ina jin horn ɗin mota na fita. Raina fes na kame a gaban mota ina jin wani farinciki na ratsani. Na…-
247.6 K • Completed
-
-
Ƙaddara da kwaɗayi haɗi da son zuciya irin nasa ya janyo masa faɗawa tarkon nadama. Dukda dai tsohon halin sa ne, a baya lokacin samartaka ya kan kwatanta domin rage zafi kamar yanda hakan yake ɗabi'ar dayawan Samari a wannan zamanin. Sun ɗauki hakan a matsayin wayo ko dabara a ganin su ai basu aikata Zina a zahiri ba sai dai suna mantawa da hanin ubangiji da yace kada a kusanci Zina ba wai kada a aikatata ba Aa kwata kwata kada a kusanci duk wani abu da yake da jiɓi da ita. Da yawan su sun ɗauki…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 19 20 21 … 46 Next
