Search
You have no alerts.

    ABDULKADIR

    ABDULKADIR NA LUBNA SUFYAN

    SHIMFIDA

    Alhaji Ahmad Bugaje shine yaro na farko a wajen Alhaji Auwal Bugaje da Hajiya Sa’adatu da suke kira da Daada. Asalinsu yan garin Bugaje ne da yake karamar hukumar Katsina, tsatson su fulani ne,da suke kira da Daada. Asalinsu yan garin Bugaje ne da yake karamar hukumar Katsina, tsatson su Fulani ne, duk da ba sai an fada maka hakan ba. Yanayin jikin su da hasken fatarsu ma kawai idan ka kalla ya wadatar. Cirani ya kawo kakanninsu garin Kano, da niyyar siye da siyarwa, kafin daga baya su fada harkar canji, harkar da ta zame musu kamar gado a cikin zuri’ar su, dan kuwa itace silar arziqin su.

    Shi kanshi Alhaji Auwal itace sana’ar shi, kafin rasuwar shi kuwa, Allah ya azurta shi da samun yara takwas da tilon matar shi Hajiya Sa’adatu. Ahmad, Sani, Hamisu, Talatu, Sadiya, Maryama, Ali, sai Hafsatu. Sun sami wadattaccen ilimin addini dana boko, wanda a cikinsu daga Sani sai Ali ne suke aikin gwamnati, dukkan su sana’ar canji sukeyi, ko bayan da sukai aure suka hayayyafa. Bayan rasuwar Alhaji Auwalu, an raba musu gado a bisa tsari na addini. Ya kuma bar musu tarin dukiya mai yawa, dan a lokacin da wahalar gaske ka kira Bugaje ba’a samu wanda yasan shi ko ya taba jin sunan shi ba, saboda ana damawa dashi a cikin attajiran dake garin Kano. Ita kanta Hajiya Sa’adatu bata rasu ba sai bayan ta aurar da yaran ta mata gabaki dayan su.

    Gidan shi da yake nan Gadon Kaya, a garin Kano, Alhaji Ahmad ne ya gaje shi. Gidane babba, musamman daya kara gyara shi, manyan bangarori ne guda hudu a cikin gidan, sai wani bangare daya shima da yake daban. Ko harabar gidan kanta abin kallo ce. Ya kuma ji dadin kasancewar gidan mallakin shi, dan duk a cikin yaran Alhaji Auwalu shi kadaine ya auri mata har hudu, dukkan su tazarar shekara bibbiyu a tsakanin su, gashi yayi auren wuri saboda tashen kudi da yakeji a lokacin.

    1. Matar shi ta farko, uwargidan shi Hajiya Hasiya da duka yaran suke kira Hajja tana da yara takwas tare dashi:

    Muhsin
    Yazid
    Khadija
    Mubarak

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!