A D U N I Y A T A 🌎
H U G U M A
Arewabook:Huguma
Page 01
The gateway
“Maaaam…….don Allah maama,abbee bashi da lafiya sosai kin sani maama……idan kika tafi waye zai kula damu?,idan kika tafi maama waye zai kula da abbeee?” Muryar yaron da gaba daya bazai haura shekara goma sha uku ba kenan take fita cikin wani irin sanyi da matsanancin rauni wanda koda ba’a gaya maka ba…..koda kuma baka kalli fuskarsan nan dake jiqe da hawaye ba…..koda baka kalli hannuwansa dake rawa ba wanda ke tallafe da mujinyacin dake zaune tsakanin cinyoyinsa ba zaka fahimci yana cikin matuqar kaduwa razani tare da zallar firgici.
Idanunshi qur bisa kanta yana fatan jin qididdigaggun kalmomin
“Na fasa tafiya” daga bakinta,duk kuwa da cewa ba wani abu guda daya tal da ya bashi alama komai qanqantarta da take nuni da zata iya janyewar. A maimakon haka ma,sai sake gyara yafen mayafinta dake saman kanta tayi,ta duqa tana cusa ragowar kayanta da basu samu gurbi ba cikin baqar jakar gabanta.
“Don Allah mariya…….ba don ni ba……ko don yaran nan,kiyi haquri……ki zauna ki rungumesu,ni tawa me sauqi ce,ina da tabbacin kwanaki qalilan ne suka ragemin,su din dai sune abun dubawar……” Mutumin da rashin lafiya da kuma talauci sukayi gamayya da matsin rayuwa suka yiwa kowanne sashe na halittar jikinsa illa. Yayi maganar da qyar yana fidda numfarfashi kaman numfashin nasa zaya qwace daga tsakanin qirjinsa zuwa hunhunsa.
Dauke dubansa yayi daga kan fuskar mutumin da yake MAHAIFI a gareshi ya maida kanta zuciyarsa na narkewa da wani irin tausayin kansu gaba daya idan ka debe ITA!. Bugun zuciyarsa na sake daduwa da tsananin tashin hankali da tausayin na daban kamar zai fasa zuciyarsa ta tsage. Ya jima yana begen jin fitar wasu kalmomi daga bakin mahaifinsu wanda a qalla yau kusan kwanaki goma cif kenan baya um baya um um. Ya kashe darare masu yawa yana kasa kunnen yaji wani abu daga bakinsa.....sai gashi a yau bakin ya budu,amma kuma sun budu ne saboda tsananin bala'i da firgici da take shirin jefa rayuwarsu,bawai ya budu bane da zummar musu magana da kyawawan kalmomin nan da baya rabo dasu a kansu.
Idanunsa cike da fatan zuciyarta zata rusuna daga kalaman mahaifinsu.....kodon kalmar mutuwa daya ambatarwa kansa wadda ta zama daya daga cikin dalilan da ya sanya yaji inama baiyi maganar ba,inama shuru yayi da bakinsa duk da tarin buri da begen yaji yayi maganar wanda ya cika zuciyarsa. Yana tsaka da wannan shawagin cikin zuciyar zato da fata ya sake jin busashiyar muryar mahaifin nasa mara amon sauti yana sake tattara dukka juriyarsa yana fadin
“Mariya……idan kika tafi waye zai kula dasu?” A fusace ta waiwayo ta watsa masa wani irin kallo tana rataya jakarta bisa kafadarta
“Dasu nazo?,ai dama a nan na samesu kuma a nan din zan barsu,dan da uwarsa ke mutuwa ma randa ta haifeshi yanzu haka suna rayuwa sunfi miliyan bare wadanda suka kai shekara sha uku da takwas” tana kaiwa nan ta soma daga qafafunta tana baiwa dakin takun bankwana,abinda ya bashi tabbacin da gaske fa take!
Ba zata rusuna ba!.
Da alama kuma ba abinda zai sanyata rusuna din!.
Baisan wanne tunani ya kamata yayi ba,don a sannan qwaqwalwarsa tayi qanqanta da daukan dukka wadannan abubuwan bare har ya rarrabe hukuncin daya dace da wanda bai dace ba,sai ya tsinceshi a gabanta,riqe da qafafunta yana qaramin kuka da iya dukka qarfinsa a shekarunsa.
Dubansa tayi kaman zata qwace qafar,sai kuma ta saka hannu ya dagoshi ta maidashi ta zaunar tana cewa
“Nan din shine dolenku,a nan zaku zauna da dadi ba dadi,da wuya ko babu,idan nace nima zanci gaba da zama,dukkanmu ni daku za’a yi haihuwar guzuma ne ni kwance ku kwance babankun ma haka,gwara na matsa kadan,wataqila rabon yana a gaba”.
Cak maganar ta yiwa zuciyarsa tsaiwar mashi. Idanuwansa suna iya hangen mahaifinsa yana runtse idanunsa. Sai ya zare nasa idanun yana maidawa kan yaron daya yunqura zaibi bayanta bayan fitarta qofar dakin.
Wata gigitacciyar tsawar data girmi shekarunsa ya daka masa
“Dawo ka zauna!……zamu rayu…..zamu rayu da mahaifinmu!…….zamu rayu da wuya ko da dadi!…….zamu rayu da farinciki ko babu!…….mu din dolen junanmu ne yanzu!……bamu da kowa sai kawunanmu sai mahifinmu!” Ya qarashe maganar yana numfarfashi qirjinsa yana dagawa sama da qasa.
Cak ta tsaya,ta kuma waiwayo,idanunsu suka sarqafe guri guda. Ba sanin shekara daya ko biyu tayi masa......ba kuma sanin shanu tayi masa ba.......tasan dabi'unsa dake zubi da dabi'un mutumin daya dauki wani dogon xango xamani ko kuma qarni cikin sararin duniya...... dabi'un da sukan jefata duniyar mamaki a wasu lokutan..... Amma ko a shifcin qwaqwale bata taba tunanin fitar wadannan kalamai masu tsananin zafi daga harshensa ba. Kalaman da suka jeru da kyau!. Suka kuma isar da saqo tamkar dai ya jima yana ajiyarsu......kamar kuma rubuta masa su akayi ya dauki dogon lokaci yana gwajin yadda zai furtasu.
Yadda ta zare idanunta daga kanshi haka ya zare nasa. Sai ya maida dukka yunqurinsa wajen qoqarin kwantar da mahaifinsa yadda zayaji dadin kwanciyar. Jikinsa ya qara nauyi ya kuma sake sosai. Saidai duk da haka numfashi na fita ta qofofin hancinsa,abinda ya sanya sam tunaninsa bai kai kan komai ba.
Bashi da wani sauran FATA a kanta......amma kuma hankalinsa ya gaza daukewa daga kanta,yana lissafe da takun takalminta sanda take ficewa daga cikin gidan nasu. Fitar da har yanxu ta kasa barin qwaqwalwarsa. Fitar da har yanxu take masa matsanancin ciwo......fitar daya alaqantata da sila kuma MABUDIN afkuwar kowanne irin tsanani da matsin rayuwa.
D U N I Y A T A🌍
H U G U M A
Arewabooks:Huguma
Page 02
Idanunsa da suka qanqance suka kuma sake shigewa ciki saboda tsananin kuka tashin hankali da firgici ya bude. Ya jefa idanunsa gefansa hannun hagunsa,ya kuma aza idanunsa saman shimfidaddiyar lamusashiyar shimfidar. Shimfidar da kwanaki uku kenan da matuwar mamallakiyarta, shimfidar da kwanaki uku da suka gabata iwar haka suna tare da me shimfidar. Kaka a garesu,mahaifiya ga mahaifinsu wadda ta zame musu bango jigo kuma majingina a garesu bayan rasuwar mahaifinsu.
Har yau ya kasa sanya hannu ya tattare shimfidar,hakanan babu wanda ya damu ya dauke ta. Yo ina aka damu dasu ma ballantana abinda ke cikin gidan?. Su din ba wasu bane,basu da abinda zasu bawa jama'ar zaman makoki,basu da gata basu da wani tsayayye da zai tsaya ya tayasu jimamin rasa kakar tasu da suka zauna da ita shekaru uku cikin tsanani da kuma zazzafar gwagwarmaya irin wadda ke xamantoww tsere ne tsakanin tsanani da kuma sassauci cikin tsananin.
Hawayen nan daya kasa yankewa daga idanunsa ne suka sake bullowa. Har yau gani yakeyi wasa ne,har yanxun gani yake JADDA zata dawo. Shudewarta ya dawo masa da mikin rasuwar mahaifinsa,sai yakejin kamar yau ne ya rasu,kamar a yau ne yayi bankwana da duniyar,kamar a yaune MAAMA ta sanya qafafu ta fice ta barsu,tafiyar data xama wani yanki na tunzura yanayin rashin lafiyar abbee......tafiyar kuma data zaman kamar ta tafi da ruhi da kuma rayuwarsa. Hannunsa daya ya sanya ya riqe wuyansa da kyau kamar yana shirin shaqe kansa. Wasu murtuka murtukan jijiyoyi suka fito bisa saman kansa da goshinsa sukayi layi rad'a rad'a. Kalar da idanunsa yayi ya sake ninkuwa da kalar jaa ainun,kuka da hawaye me zafi ya sake yanke masa,matuqar maqurar qiyayyar jinin mahaifiyarsa yana tsartuwa cikin kowanne sashe da lungu na gangar jiki da zuciyarsa.
“Hamma…..ham” yaron daya fado dakin ya dakata da kiran da yake jera masa. Cikin wannan yanayin ya waiwayo yana kallonsa,sai yaron ya dan ja da baya,don ya tsorata ainun da yadda yaga fuskarshi ta sauya. Yanayi ne dake sanya masa tsoron hamman nasa sosai da sosai,duk sanda ya ganshi a irin haka sai ya dinga ganin kamar ba hamma dinsa ba.
Ya lura da hakan shima,wannan ya sakashi zare hannunsa daga wuyansa yana tattaro wani irin yawu me tauri da kauri yana hadiyewa da qyar kamar me hadiyar duwatsu. Yakai zuciyarsa cen nesa,ya kuma gyara harshensa sannan ya jefa masa tambaya
“Menene?” Murya da jikinsa suna danyin rawa ya soma fadin
“Abba ne……abbansu farouq ne yace kazo yana soro” idanunsa ya sauke yana jin wani kaso na rahama da sassauci suna sauka a zuciyarsa. Mutum qwaya daya tak a duniya da ganinsa ko jin kiransa yake shaida masa zuwan alkhairi sauqi sassauci ko rangwame daga dukkan wani hali da suke ciki.
Yana tafe amma yana jin kaman ba'a kan qafafunsa yake tafiya ba,yana tafe yana jin kamar tsakanin sama da qasa yake,saboda tashin hankali yunwa harma da qishi. Ko sau daya bayan rasuwar ya gaza kai qwayar abinci bakinsa daga abincin da maqota ke saka musu jifa jifa. Yana daddafe da bango yana wulga idanunsa ga sararin tsakar gidan nasu daya zama kamar filin sukuwa......ya zama fetal ya sake fadi,abinda ke alamta masa cewa lallai sun sake rasa wani bangon kuma madaafa.
Dattijo me cikar kamala wanda duka duka shekarun haihuwarsa a duniya ba zasu haura arba’in da biyar ba. Amma alamu sun nuna muraran shi din me ginanne kuma lafiyayyen jiki ne dake iya cinye shekaru.
Yana sanye da yadin kufta da yasha aikin hannu wanda ya qara masa cikar kamala. Ya tura hularsa baya,qafarsa sanye da slipper dan madina,wanda ke zamantowa daya daga cikin dabi'unsa a lokuta da dama idan zaya fito guraren da bai wuce masallacin cikin unguwa ba ko wata unguwata kurkusa a cikin abun hawansa ko a qafa.
A raunane suke kallon juna shi da shi,ganinsa sai ya sake sakawa zuciyarsa wani raunin,yana shirin duqawa ya gaidashi ya tallabeshi
“Tashi tashi……sannu da qoqari,sannu da haquri……akwai wai abu da kuke buqatar dauka ta cikin gidan?” Ya tambayeshi yana dubansa. Bai gane komai abban yakeson fada ba,don haka ya dubeshi sosai.
“Gida na zan wuce daku,ba za’a barku ku dinga kwana kuna tashi gidan da ba kowa a cikinsa ba saiku kadai”
Muryar nan data nuqu qwarai cikin wahala da gararanba ya bude
“Sai kayan sawarmu”
“Dauko abinda ya sawwaqa a kulle gidan” yayi maganar yana kama hannun qaramin qanin nasa dake kusa dashi.
Sanda yake hada kayan kudu da yamma gabas da arewa na zuciyarsa a cakude yake da tunani. Zasu koma gidan abba?. Gidansu farouq?. Tabbas su farouq 'yan gata ne gaba da baya,saidai wani irin gata suke samu dake da wani wawakeken gibi da kuma naqasu. Gatan daya rasa wani bango kuma jigo a cikinsa,gatan da wani lokacin yakan juya musu da wani irin launi mara armashi. Wani gata da bai amsa sunansa ba a lokuta masu yawa,su din sukan zama har sun darasu samun wani abu guda daya,duk da tarin nasu naqasun rashin wadata da sukunin rayuwa. Sun darasu samun 'YANCI SAKEWA DA KUMA WALWALA. kenan zasu rayu tare da momy?,zasu zama qarqashin inuwa da mulkinta kamar sauran yaran?.
Sakin ragowar kayan hannunsa yayi ya sulale ya zauna a qasa. Iya wannan tunanin kadai ya karya duka sauran guntun karsashinsa.
Tunaninsa ya dinga rarrabuwa,a haka dai gatane suka sameshi saboda abban wani irin dattijo ne me fafutukar taimakawa da tallafawa sukkan me rauni. Tun zamanin da mahaifi da mahaifiyarsu ke rayuwa tare hannuwansa da aljihunsa harma da lokacin cikin hidimta musu suke. Shudewar uba a garesu ya sanyashi sake ninka alkhairinsa. Ya sanya hannu bibbiyu ya tallafi rayuwarsu data jadda,a yanzun kuma yana shirin maida nauyin kacokam bisa wuyansa.
“Idan ba zaka iya shirya kayan ba fito hakanan a barsu zuwa gobe ko?” Muryar abban ta baqunci kunnensa,wanda dole ta sanyashi miqewa ya debi iyakar abinda zai iya. Ya janyo qafafunsa yana fita daga dakin,idanunsa na rarrabuwa a sassannin da suka qaraci dabdalar rayuwarsu suda jadda bayan shekaru uku
D U N I Y A T A🌍
H U G U M A
Arewabooks:Huguma
Page 03
Yana riqe da hannunsa tsam cikin nasa cikin tausayi da nuna kulawa. Yayin da yake biye dasu a baya,rungume da kayansu jikin qirjinsa, wanda ke dauri a wani yalolon mayafi.
Duk taku daya yana yinsa ne tare da bugawar zuciyarsa,wani irin shakkun shigarsu gidan yana mamayar zuciyarsa,dukkan sarewa da kuma rauni tare da rashin tabbas suna cikashi. Daidai sanda abban ya waiwayo a nutse,lokacin da suka kawo bakin gate din gidan.
Murmushi ya sakar masa a hankali da mufin kwantar masa da hankali,ya fahimci akwai anunuwa da yawa dake kai komo a zuciyar yarin game da shigarsa gidan. Shigarsa gida wani tsohon labari ne daya jima da shudewa,a qalla shekaru kusan biyu cur kenan yanzu ake magana.
“Ka saki jikinka,hakan shine zai sanya dan uwanka shima ya saki jikinsa,ka dauka a ranka tamkar mahaifinku ne ya dawo,zan zame muku uba bango kuma majingina muddin numfashi yana yawo a gangar jikina,kasa a ranka a yanzun baku da sauran matsala ko maraici kaji?” Abba ya furta yana dora hannunsa saman kanshi,qauna da tausayinsa yana ratsashi.
Ya jima yana kallon yaron a mabanbantan ranaku lokutta da kuma gurare cikin unguwar. Ya jima da sanin cewa yaron ya fita daban cikin sauran yara,komai nasa na dabanne,nutsuwa da hangen nesansa kawao zai sanya kayi tunanin ya girmewa shekarunsa. Bai taba ji ba,bazai kuma taba iya tuna wani lokaci da yaji wani yayi kusa dashi cikin unguwar bisa rashin gaskiyarsa ba,muddin kaji wani koke a kansa to lallai ba shakka taboshi akayi,an shiga gona ko huruminsa.
Duk sanda ake irin wannan case din a mafi yawan lokuta yana tare da mahaifinsa,yakance
“Ka barni nayi masa hukunci koda shine da gaskiya,ya cika zafin rai,ya fiya taurin kai da kafiya,wannan duka ba dabi’u bane masu kyau,ya kamata ya sauya saboda rayuwa”.
Murmushi abban yakan saki,ya kuma maida dubansa ga fuskar yaron kafin ya bawa mahaifinsa amsa
“Ka godewa Allah,ba’a taba kawo maka qararsa akan rashin gaskiyarsa ba,koda kuwa an kawo qarar zaka sameshi ne ame gaskiya,shin me kake nema ko fata sama da haka?”. Mahaifinsu mutum ne me tsananin kawaici,kanshi kawai yake kawarwa yana murmushi. Abban ya wuce komai a wajensa,maqoci ne me nagartar da samun irinsa yake wahala,don haka ne yake bashi dukkan girma,ba kuma wai don arziqi ko dukiyan daya mallaka ba,a’ah,don kawai ya cancanci hakan.
“Kana jina?” Abba ya sake fada don maido hankalinsa kansa,sai ya gyada kansa a nutse shima yana duban abban
“Yauwa,muje ciki,dukka su saddiq ma suna ciki na tabbatar yanxu” Bai musa ba yayi gaban abban yana biye dashi yana tsokanar dan uwan nasa daya sake sosai,farinciki ne ma kwance akan fuskarsa,da alama quruciya da rashin sanin cikakken ciwon kai ya sanya ko kusa ko alama baya hasashe ko hangen abinda kan iya faruwa,ko a kusa ko a nesa,me kyau ko akasinsa a kansu da rayuwarsu dama DUNUYARSU gaba daya.
Ci gaba sukayi da tattaki cikin harabar gidan,yalwatacciyar haraba dake shimfide da interlock. Kana ma gidan kallo daya zakasan akwai sukunin rayuwa a cikinsu,duk da ba zaka kirayeshi da wani MAHAUKACIN ME KUDI BA amma tabbas yana cikin jerin MASU KUDI ARZIQI DA WADATAr daya tserema neman komai na biyan buqatar rayuwa,kamar yadda ya tserema RASHI ya masa tazara irinta HAIHATA HAIHATA.
“Bude mana” Abban ya furta sanda yaga yaja ya tsaya ba tare daya buda qofar falon da zata sadaka da ainihin cikin gidan gaba daya ba. Matsawa yayi gaba kadan,ya murda qofar ya kuma tura,sannan ya saka qafafunsa cikin falon dake gauraye da sanyin Ac.
Ita dince dai,itace mace ta farko da idanunsa suka fara tozali da ita. Bai sani ba,tsabar yadda ya washeta ne,yake kuma qyamatar shiga cikin dukkan lamuranta ne kamar yadda take nuna qyamata da qin jininsu qarara a fili?,wannan shi ya sanya ta zama mutum na farko daya fara gani?.
“Kai dakata!,ina zaka je?,wajen wa kazo?,wai ban hanaku shigowa gidan nan haka gaba gadi ba kamar gidan tsohonku?,me ma ya kawowa da wasu tsummokara a hannu?”
“Nine na kawoshi” Abba dake bayansa ransa na quna da jin kalamanta ya furta. Sak ta danyi,duk da bawai ta razana bane da jinsa,sai tsabar baqinciki da kuma zato daya soma zuwa ranta
“Lallai kawai bala’i cikin gidan nan” Ta raya a ranta tana sake tattara dukka girarta waje daya ta hade,babu rahama ko qanqani saman fuskarta.
Yaron dake zaune a rakube daga qasan carfet din ya sake tattare jikinsa waje daya,alamu dake bayyana lallai ya shiga taitayinsa da sauyawar yanayin nata.
“Laaaaa……kaine kuma yau?ashe zaka sake shigo mana?” Yaron dake fitowa daga kitchen din gidan ya furta,fuskarsa na juna tsantsar farinciki,kamar yadda ya bada dukka hankalinsa akan wanda ya jefawa tambayar,hannunsa dauke da tray,daga hannun nasa har zuwa qafafunsa ya tattare bakin wando da kima rigar tasa.
“Kai me yasa baka da hamkali ne?,zaka zo ka ajjiyemin ko kuwa?” Hamshaqiyar matar dake zaune saman kujerun falon ta sake ma yaron tsawa,wanda tamkar ma ya manta da abinda ya fito dashi daga kitchen din,kaf hankalinsa ya tafi ga baqon yaron daya shigo din,wanda a idanu shekarunsu tamkar daya suke.
Juyawa yayi xuwa gareta don aje mata tray din,hakan bai isheta ba ta bishi da wani mummunan kallo,idanunta kamar zasu ciro su fado qasa
“Shashasha,kamar wani wanda yaga qanin ubansa,sai nayi maganinku” Ta furta cikin fushi. Daga baya baya kadan ya ajiye tray din yana fatan kada hannuwanta yakai kansa,duk da yasan hakan zaiyi wuya,ko don wanzuwar mahaifinsu a wajen
“Musaddiq……maza karbi kayan hannunsa ku wuce dakinku dukkanku” Zumbur yaron dake a zaune rakube tsakanin kujerun ya miqe. Bai jira kowa ba a cikinsu yayi hanyar dakinsu,saidai yana tafe yana dan waiwaye.
A sanyaye ya sakarwa musaddiq kayan hannun nasa,yana qoqarin maida masa martanin murmushin da yaketa faman yi masa tunda sanda yayi tozali dasu
“Muje ko?” Ya sake fadi yana kama hannunsa.
Bai musa ba ya soma bin bayansa,don zamansa a falon yayi imanin sam bazai yiwu ba koda abba bai basu umarnin wucewa ciki ba.
Zazzafa kuma tozartaccen kallo take binsu dashi,zuciyarta na mata wani irin suya,bacin rai da takeji kamar zata yi aman zuciyarta.
Debe idanuwanta tayi daga kansu tana jan qaramar qwafa qasan zuciyarta,ita daidai take dasu,babu wanda ta shirya bari ya takura rayuwarta ko ya quntata ta.
Duk wani motsi nata yana karance da ita,har zuwa sanda ya daidaita zamansa saman kujerar sannan ya dubeta yana kiran sunanta
“Asama’u” Kallonsa kawai tayi ba tare da tace komai ba
“Ga yara nan na kawosu,yara ne kuma da kin sansu bawai baqi bane a wajenki,kin kuma san basu da wata matsala ko aibu ko wani abun fada cikin unguwar nan……alqawari ne da na yiwa kaina tsakanina da ubangijina,na kuma cika alhamdulillah,ina fatan zaki tayani riqesu bisa amana ko don maraicinsu”.
Wani kallo takeyi masa ranta cike fal da mamaki,ta karkace tana dubanss tare da tattara abinda zata ce masa
“Yanzu bayan naka yaran har yaran maqota kakeyimin kalensu?” Ta aje maganar tana jin zafi cikin ranta da zuciyarta. Tana jin ta quna bata tsoron qauri,ta soma gajiya ta kuma soma qosawa tare da debe haso hadi da tsammani na samun shimfidaddiyar rayuwar data jima tana mafarki gami da shimfidawa cewa zata samu cikin gidan…..
D U N I Y A T A
H U G U M A
Arewabooks:Huguma
PAGE 04
A nutse ya daga kai ya watsa mata wani irin kallo. Yau ta fara fadin hakan,amma kuma ya dade yana karantar hakan daga dukka ayyukanta da motsinta.
“Nayi tunanin akwai dattako fahimta da kuma qaunar juna a tsakaninmu da har yarana sukafi qarfin kice riqonsu kikeyi,na zaci cewa kina ji a jikinki da zuciyarki kina rainkn ‘ya’yan da kika haifa ne a cikinki?” Wani abu ne yazo yayi mata tsaye a wuya,ta juya kanta gefe guda tana tattaunawa da zuciyarta kan
“Har abada ‘ya’yan riqo ba ‘ya’ya na bane,’ya’yan wasu ba zasu taba zama ‘ya’yana ba…..banda qaddara me zai hadani da riqon ‘ya’yan wasu?” . Idanunsa a zube fes a kanta,ya gyara zamansa sosai yana sake ci gaba da kallonta
“Inaso ki cire a ranki riqo kikeyi…..ba ‘ya’yana na cikina bama…….hatta yaran dana kawo yanzu,inaso ki ji a ranki Tamkar suna rayuwa ne cikin gidan mahaifinsu a gaban uwa da kuma ubansu”. Dukka haqurinta ya qare,ya tuqeta ta kuma kai bango,tana jin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraronsa ba,don haka ta miqe tsam,ta kuma gegara ta gabansa tana barin falon.
Da ido ya bita har zuwa sanda take shirin bacewa ganinsa. Ya jima yana ganin alamun da suke alamta masa akwai matsaloli masu yawa cikin rayuwar su farouq,amma yayita qaryata hakan gudun kawo damuwa da matsala cikin zaman uwar wani da d'an wani wanda keda wuyar sha'ani,sai gashi a qanqanin lokaci komai yana bayyana kansa daki daki.
Numfashi ya zuqa ya fesar yana rufe idanunsa,qoqari yake ya saita kansa yana tunanin hanyar da zai daidaita komai.
Tray din da faruqee ya ajjiye yabi da kallo,a dawowarsa daga lagos wannan karon ya fahimci kamar ma suke yiwa kansu girki harma su hada da ita idan ta kama,babu sakewa babu walwala sam tattare dasu. Ya lura da raguwar kuzarinsu kyara da kuma hantara daga gareta,saidai dukka ya kauda kai don bai kamaci a karon farko ya fidda soyayyar yaransa kai tsaye daga zuciyarsa har haka ba,bayaso yabar wani tabo ko targaden da zai kasa gyaruwa tunda wurwuri haka.
Da idanu kawai yake bin dakin da kallo sanda Faruqee yaketa masa bayani zuciya da fuskarsa cike da zumudi da farinciki.
“Kayi shuru?,ka tsaya a bakin qofa,ko dakin baiyi bane na gayawa abba a qaro wasu abun?” Faruqee ya fada jikinsa yana sanyaya da yadda yaga fuskarshi. Don a yadda ya zata zayaga farinciki sosai a fuskarsa kaman kwatankwacin nasa farincikin na dawowarsa cikin gidansu,farincikin samun aboki me hankali irinsa,farincikin samun aboki da yayi daidai da shekru da hankalinsa,ba aboli irin qaninsa ba da sam.baya gane wsu abubuwan saboda sabanin mizanin hankali da fahimta dake tsakaninsu.
Karon farko yayi qoqarin sake fuskarsa da kyau yana kallon faruqee. Dakin gata kuma dakin yaran gata irin wannan da shi din bai taba samun kwatankwacinsa ba ta yaya zaice baiyi masa ba?. Dukka alatu da yayi saura a dakin bashi yake daukarsa ba.......duk da qarancin shekarun daka iya dakusar da tunanin yaro a sannan......amma shi sun bawa qwaqwalwarsa damar budewa da yin tunani me nisan zango akan
“Wacce irin rayuwa zasu fuskanta a matsayinsu na agola bayan su kansu tsatson gidan basu tsira ba?,mene ne makomarsu?,meye farko da kuma qarshensu?” Tarin tambayoyin da baisan ta ina zaa fara sauke masa su ba
“Nayi murna farouq” Ya furta a sanyaye,sunan da shi daya yake furtashi daidai yadda yake,don har yau bai taba kiransa da faruqee ba.
Yadda qanin nashi ya zuba masa idanu ya sanyashi qoqarin sakewa,ya qaraso ainihin cikin dakin kamar yadda sauran suka kai ga shigowar.
Qoqarin kauda komai ya dinga yi daga zuciyarsa,yana zaune daga falon yana iya jiyo muryoyinsu sama sama,saidai har yanzun baiji tashi muryar ba. Baiyi mamaki ba,don ya sani,yadda komai nasa ya fita daban daga cikinsu,haka dabi''arsa da halayyarsa ma ta zama daban.
Abincin yaja ya soma ci bawai don cin abincin yana masa dadi ko yana burgeshi ba. Tunaninsa yayi zurfin da har ba komai dake wakana cikin falon yake ganewa ba,bai taba zata ba,bai kuma taba kawowa rabuwa da rabi'atu zai iya zame masa qalubale ba sai yanzun da dukkan alamu suka fara bayyana kansu. A karon farko har yaji ya fara tuhumar kansa da kansa,tare da nacin son gano meye ainihin laifin rabi'atu ne har ta cancanci a saketa?.
Baici da yawa ba ya ture,ya miqe yana irgen lokaci,sai ya juya ya fara takawa zuwa dakin yaran.
Dukkansu sunyi shirin bacci amma bandashi,yana zaune gefe daya na gadon farouq,ya goye hannayensa a qirjinsa tamkar wani babba da yayi nisa cikin nazarin wani abu.
Motsin abban ya sanyashi waiwayowa,da sauri ya sauke hannayensa yayi qasa da kansa yana niyyar zamowa daga saman gadon
“Yi zamanka me babban suna……tunanin me ka zauna kana yi?,duk ‘yan uwanka sunyi shirin kwanciya banda kai?” Farouq dake zaune tsakiyar gadon yayi hanzarin karbar maganar dama tana damunsa tun dazu
“Abba yaqi ya canza kaya,na bashi kayan bacci yaqi ya saka tun dazu” Hannu kawai abban ya miqawa farouq din,sai ya saka masa kayan baccin dake gefansa.
Kayan abban yabi da kallo yana jujjyasu a hannunsa,sannan ya maida dubansa zuwa jikinsu dukka su ukun dake sanye da wasu kalolin kayan.
“Amma faruqee ban gaya muku a bada kayan nan ba dukansu?,ina kayan dana kawo muku wancan tafiyar da nayi?” Ya qarasa tambayar yana maida idanunsa kan saddiq qaninsa.
Har wani juyawa saida cikin saddiq din yayi,saboda tunawa da yayi da kakkaifan warning din da suka samu daga wajen matar gidan akan batun.