*A D U N I Y A T A* 🌎 *_H U G U M A_* *Arewabook:Huguma* __________________________ *_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_* *lace* *kowanne nau'in shaddodi* *yadika na maza da mata* *mayafai* *lafaya* *takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana* *sarqoqi da agoguna* *under wears* *abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza* *_Akwai group na musamnan saboda nasu buqatar kayan kitchen HUGUMA UTENSILS UNIVERSE_* https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub *_Duniyar kwatalle kitchen din amarya da uwargida_* *_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?,sallah tana matsowa,azumi na tunkarowa?_* https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz __________________________ Page 01 *_The gateway_* "Maaaam.......don Allah maama,abbee bashi da lafiya sosai kin sani maama......idan kika tafi waye zai kula damu?,idan kika tafi maama waye zai kula da abbeee?" Muryar yaron da gaba daya bazai haura shekara goma sha uku ba kenan take fita cikin wani irin sanyi da matsanancin rauni wanda koda ba'a gaya maka ba.....koda kuma baka kalli fuskarsan nan dake jiqe da hawaye ba.....koda baka kalli hannuwansa dake rawa ba wanda ke tallafe da mujinyacin dake zaune tsakanin cinyoyinsa ba zaka fahimci yana cikin matuqar kaduwa razani tare da zallar firgici. Idanunshi qur bisa kanta yana fatan jin qididdigaggun kalmomin "Na fasa tafiya" daga bakinta,duk kuwa da cewa ba wani abu guda daya tal da ya bashi alama komai qanqantarta da take nuni da zata iya janyewar. A maimakon haka ma,sai sake gyara yafen mayafinta dake saman kanta tayi,ta duqa tana cusa ragowar kayanta da basu samu gurbi ba cikin baqar jakar gabanta. "Don Allah mariya.......ba don ni ba......ko don yaran nan,kiyi haquri......ki zauna ki rungumesu,ni tawa me sauqi ce,ina da tabbacin kwanaki qalilan ne suka ragemin,su din dai sune abun dubawar......" Mutumin da rashin lafiya da kuma talauci sukayi gamayya da matsin rayuwa suka yiwa kowanne sashe na halittar jikinsa illa. Yayi maganar da qyar yana fidda numfarfashi kaman numfashin nasa zaya qwace daga tsakanin qirjinsa zuwa hunhunsa. Dauke dubansa yayi daga kan fuskar mutumin da yake MAHAIFI a gareshi ya maida kanta zuciyarsa na narkewa da wani irin tausayin kansu gaba daya idan ka debe ITA!. Bugun zuciyarsa na sake daduwa da tsananin tashin hankali da tausayin na daban kamar zai fasa zuciyarsa ta tsage. Ya jima yana begen jin fitar wasu kalmomi daga bakin mahaifinsu wanda a qalla yau kusan kwanaki goma cif kenan baya um baya um um. Ya kashe darare masu yawa yana kasa kunnen yaji wani abu daga bakinsa.....sai gashi a yau bakin ya budu,amma kuma sun budu ne saboda tsananin bala'i da firgici da take shirin jefa rayuwarsu,bawai ya budu bane da zummar musu magana da kyawawan kalmomin nan da baya rabo dasu a kansu. Idanunsa cike da fatan zuciyarta zata rusuna daga kalaman mahaifinsu.....kodon kalmar mutuwa daya ambatarwa kansa wadda ta zama daya daga cikin dalilan da ya sanya yaji inama baiyi maganar ba,inama shuru yayi da bakinsa duk da tarin buri da begen yaji yayi maganar wanda ya cika zuciyarsa. Yana tsaka da wannan shawagin cikin zuciyar zato da fata ya sake jin busashiyar muryar mahaifin nasa mara amon sauti yana sake tattara dukka juriyarsa yana fadin "Mariya......idan kika tafi waye zai kula dasu?" A fusace ta waiwayo ta watsa masa wani irin kallo tana rataya jakarta bisa kafadarta "Dasu nazo?,ai dama a nan na samesu kuma a nan din zan barsu,dan da uwarsa ke mutuwa ma randa ta haifeshi yanzu haka suna rayuwa sunfi miliyan bare wadanda suka kai shekara sha uku da takwas" tana kaiwa nan ta soma daga qafafunta tana baiwa dakin takun bankwana,abinda ya bashi tabbacin da gaske fa take! Ba zata rusuna ba!. Da alama kuma ba abinda zai sanyata rusuna din!. Baisan wanne tunani ya kamata yayi ba,don a sannan qwaqwalwarsa tayi qanqanta da daukan dukka wadannan abubuwan bare har ya rarrabe hukuncin daya dace da wanda bai dace ba,sai ya tsinceshi a gabanta,riqe da qafafunta yana qaramin kuka da iya dukka qarfinsa a shekarunsa. Dubansa tayi kaman zata qwace qafar,sai kuma ta saka hannu ya dagoshi ta maidashi ta zaunar tana cewa "Nan din shine dolenku,a nan zaku zauna da dadi ba dadi,da wuya ko babu,idan nace nima zanci gaba da zama,dukkanmu ni daku za'a yi haihuwar guzuma ne ni kwance ku kwance babankun ma haka,gwara na matsa kadan,wataqila rabon yana a gaba". Cak maganar ta yiwa zuciyarsa tsaiwar mashi. Idanuwansa suna iya hangen mahaifinsa yana runtse idanunsa. Sai ya zare nasa idanun yana maidawa kan yaron daya yunqura zaibi bayanta bayan fitarta qofar dakin. Wata gigitacciyar tsawar data girmi shekarunsa ya daka masa "Dawo ka zauna!......zamu rayu.....zamu rayu da mahaifinmu!.......zamu rayu da wuya ko da dadi!.......zamu rayu da farinciki ko babu!.......mu din dolen junanmu ne yanzu!......bamu da kowa sai kawunanmu sai mahifinmu!" Ya qarashe maganar yana numfarfashi qirjinsa yana dagawa sama da qasa. Cak ta tsaya,ta kuma waiwayo,idanunsu suka sarqafe guri guda. Ba sanin shekara daya ko biyu tayi masa......ba kuma sanin shanu tayi masa ba.......tasan dabi'unsa dake zubi da dabi'un mutumin daya dauki wani dogon xango xamani ko kuma qarni cikin sararin duniya...... dabi'un da sukan jefata duniyar mamaki a wasu lokutan..... Amma ko a shifcin qwaqwale bata taba tunanin fitar wadannan kalamai masu tsananin zafi daga harshensa ba. Kalaman da suka jeru da kyau!. Suka kuma isar da saqo tamkar dai ya jima yana ajiyarsu......kamar kuma rubuta masa su akayi ya dauki dogon lokaci yana gwajin yadda zai furtasu. Yadda ta zare idanunta daga kanshi haka ya zare nasa. Sai ya maida dukka yunqurinsa wajen qoqarin kwantar da mahaifinsa yadda zayaji dadin kwanciyar. Jikinsa ya qara nauyi ya kuma sake sosai. Saidai duk da haka numfashi na fita ta qofofin hancinsa,abinda ya sanya sam tunaninsa bai kai kan komai ba. Bashi da wani sauran FATA a kanta......amma kuma hankalinsa ya gaza daukewa daga kanta,yana lissafe da takun takalminta sanda take ficewa daga cikin gidan nasu. Fitar da har yanxu ta kasa barin qwaqwalwarsa. Fitar da har yanxu take masa matsanancin ciwo......fitar daya alaqantata da sila kuma MABUDIN afkuwar kowanne irin tsanani da matsin rayuwa. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A*🌍 *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 02 Idanunsa da suka qanqance suka kuma sake shigewa ciki saboda tsananin kuka tashin hankali da firgici ya bude. Ya jefa idanunsa gefansa hannun hagunsa,ya kuma aza idanunsa saman shimfidaddiyar lamusashiyar shimfidar. Shimfidar da kwanaki uku kenan da matuwar mamallakiyarta, shimfidar da kwanaki uku da suka gabata iwar haka suna tare da me shimfidar. Kaka a garesu,mahaifiya ga mahaifinsu wadda ta zame musu bango jigo kuma majingina a garesu bayan rasuwar mahaifinsu. Har yau ya kasa sanya hannu ya tattare shimfidar,hakanan babu wanda ya damu ya dauke ta. Yo ina aka damu dasu ma ballantana abinda ke cikin gidan?. Su din ba wasu bane,basu da abinda zasu bawa jama'ar zaman makoki,basu da gata basu da wani tsayayye da zai tsaya ya tayasu jimamin rasa kakar tasu da suka zauna da ita shekaru uku cikin tsanani da kuma zazzafar gwagwarmaya irin wadda ke xamantoww tsere ne tsakanin tsanani da kuma sassauci cikin tsananin. Hawayen nan daya kasa yankewa daga idanunsa ne suka sake bullowa. Har yau gani yakeyi wasa ne,har yanxun gani yake JADDA zata dawo. Shudewarta ya dawo masa da mikin rasuwar mahaifinsa,sai yakejin kamar yau ne ya rasu,kamar a yau ne yayi bankwana da duniyar,kamar a yaune MAAMA ta sanya qafafu ta fice ta barsu,tafiyar data xama wani yanki na tunzura yanayin rashin lafiyar abbee......tafiyar kuma data zaman kamar ta tafi da ruhi da kuma rayuwarsa. Hannunsa daya ya sanya ya riqe wuyansa da kyau kamar yana shirin shaqe kansa. Wasu murtuka murtukan jijiyoyi suka fito bisa saman kansa da goshinsa sukayi layi rad'a rad'a. Kalar da idanunsa yayi ya sake ninkuwa da kalar jaa ainun,kuka da hawaye me zafi ya sake yanke masa,matuqar maqurar qiyayyar jinin mahaifiyarsa yana tsartuwa cikin kowanne sashe da lungu na gangar jiki da zuciyarsa. "Hamma.....ham" yaron daya fado dakin ya dakata da kiran da yake jera masa. Cikin wannan yanayin ya waiwayo yana kallonsa,sai yaron ya dan ja da baya,don ya tsorata ainun da yadda yaga fuskarshi ta sauya. Yanayi ne dake sanya masa tsoron hamman nasa sosai da sosai,duk sanda ya ganshi a irin haka sai ya dinga ganin kamar ba hamma dinsa ba. Ya lura da hakan shima,wannan ya sakashi zare hannunsa daga wuyansa yana tattaro wani irin yawu me tauri da kauri yana hadiyewa da qyar kamar me hadiyar duwatsu. Yakai zuciyarsa cen nesa,ya kuma gyara harshensa sannan ya jefa masa tambaya "Menene?" Murya da jikinsa suna danyin rawa ya soma fadin "Abba ne......abbansu farouq ne yace kazo yana soro" idanunsa ya sauke yana jin wani kaso na rahama da sassauci suna sauka a zuciyarsa. Mutum qwaya daya tak a duniya da ganinsa ko jin kiransa yake shaida masa zuwan alkhairi sauqi sassauci ko rangwame daga dukkan wani hali da suke ciki. Yana tafe amma yana jin kaman ba'a kan qafafunsa yake tafiya ba,yana tafe yana jin kamar tsakanin sama da qasa yake,saboda tashin hankali yunwa harma da qishi. Ko sau daya bayan rasuwar ya gaza kai qwayar abinci bakinsa daga abincin da maqota ke saka musu jifa jifa. Yana daddafe da bango yana wulga idanunsa ga sararin tsakar gidan nasu daya zama kamar filin sukuwa......ya zama fetal ya sake fadi,abinda ke alamta masa cewa lallai sun sake rasa wani bangon kuma madaafa. ******Dattijo me cikar kamala wanda duka duka shekarun haihuwarsa a duniya ba zasu haura arba'in da biyar ba. Amma alamu sun nuna muraran shi din me ginanne kuma lafiyayyen jiki ne dake iya cinye shekaru. Yana sanye da yadin kufta da yasha aikin hannu wanda ya qara masa cikar kamala. Ya tura hularsa baya,qafarsa sanye da slipper dan madina,wanda ke zamantowa daya daga cikin dabi'unsa a lokuta da dama idan zaya fito guraren da bai wuce masallacin cikin unguwa ba ko wata unguwata kurkusa a cikin abun hawansa ko a qafa. A raunane suke kallon juna shi da shi,ganinsa sai ya sake sakawa zuciyarsa wani raunin,yana shirin duqawa ya gaidashi ya tallabeshi "Tashi tashi......sannu da qoqari,sannu da haquri......akwai wai abu da kuke buqatar dauka ta cikin gidan?" Ya tambayeshi yana dubansa. Bai gane komai abban yakeson fada ba,don haka ya dubeshi sosai. "Gida na zan wuce daku,ba za'a barku ku dinga kwana kuna tashi gidan da ba kowa a cikinsa ba saiku kadai" Muryar nan data nuqu qwarai cikin wahala da gararanba ya bude "Sai kayan sawarmu" "Dauko abinda ya sawwaqa a kulle gidan" yayi maganar yana kama hannun qaramin qanin nasa dake kusa dashi. Sanda yake hada kayan kudu da yamma gabas da arewa na zuciyarsa a cakude yake da tunani. Zasu koma gidan abba?. Gidansu farouq?. Tabbas su farouq 'yan gata ne gaba da baya,saidai wani irin gata suke samu dake da wani wawakeken gibi da kuma naqasu. Gatan daya rasa wani bango kuma jigo a cikinsa,gatan da wani lokacin yakan juya musu da wani irin launi mara armashi. Wani gata da bai amsa sunansa ba a lokuta masu yawa,su din sukan zama har sun darasu samun wani abu guda daya,duk da tarin nasu naqasun rashin wadata da sukunin rayuwa. Sun darasu samun 'YANCI SAKEWA DA KUMA WALWALA. kenan zasu rayu tare da momy?,zasu zama qarqashin inuwa da mulkinta kamar sauran yaran?. Sakin ragowar kayan hannunsa yayi ya sulale ya zauna a qasa. Iya wannan tunanin kadai ya karya duka sauran guntun karsashinsa. Tunaninsa ya dinga rarrabuwa,a haka dai gatane suka sameshi saboda abban wani irin dattijo ne me fafutukar taimakawa da tallafawa sukkan me rauni. Tun zamanin da mahaifi da mahaifiyarsu ke rayuwa tare hannuwansa da aljihunsa harma da lokacin cikin hidimta musu suke. Shudewar uba a garesu ya sanyashi sake ninka alkhairinsa. Ya sanya hannu bibbiyu ya tallafi rayuwarsu data jadda,a yanzun kuma yana shirin maida nauyin kacokam bisa wuyansa. "Idan ba zaka iya shirya kayan ba fito hakanan a barsu zuwa gobe ko?" Muryar abban ta baqunci kunnensa,wanda dole ta sanyashi miqewa ya debi iyakar abinda zai iya. Ya janyo qafafunsa yana fita daga dakin,idanunsa na rarrabuwa a sassannin da suka qaraci dabdalar rayuwarsu suda jadda bayan shekaru uku da rasuwar mahaifinsu. Abinda ya dunqule waje guda ya bashi adadin shekaru SHA BIYAR a duniya. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A*🌍 *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 03 https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr ______________________________ Yana riqe da hannunsa tsam cikin nasa cikin tausayi da nuna kulawa. Yayin da yake biye dasu a baya,rungume da kayansu jikin qirjinsa, wanda ke dauri a wani yalolon mayafi. Duk taku daya yana yinsa ne tare da bugawar zuciyarsa,wani irin shakkun shigarsu gidan yana mamayar zuciyarsa,dukkan sarewa da kuma rauni tare da rashin tabbas suna cikashi. Daidai sanda abban ya waiwayo a nutse,lokacin da suka kawo bakin gate din gidan. Murmushi ya sakar masa a hankali da mufin kwantar masa da hankali,ya fahimci akwai anunuwa da yawa dake kai komo a zuciyar yarin game da shigarsa gidan. Shigarsa gida wani tsohon labari ne daya jima da shudewa,a qalla shekaru kusan biyu cur kenan yanzu ake magana. "Ka saki jikinka,hakan shine zai sanya dan uwanka shima ya saki jikinsa,ka dauka a ranka tamkar mahaifinku ne ya dawo,zan zame muku uba bango kuma majingina muddin numfashi yana yawo a gangar jikina,kasa a ranka a yanzun baku da sauran matsala ko maraici kaji?" Abba ya furta yana dora hannunsa saman kanshi,qauna da tausayinsa yana ratsashi. Ya jima yana kallon yaron a mabanbantan ranaku lokutta da kuma gurare cikin unguwar. Ya jima da sanin cewa yaron ya fita daban cikin sauran yara,komai nasa na dabanne,nutsuwa da hangen nesansa kawao zai sanya kayi tunanin ya girmewa shekarunsa. Bai taba ji ba,bazai kuma taba iya tuna wani lokaci da yaji wani yayi kusa dashi cikin unguwar bisa rashin gaskiyarsa ba,muddin kaji wani koke a kansa to lallai ba shakka taboshi akayi,an shiga gona ko huruminsa. Duk sanda ake irin wannan case din a mafi yawan lokuta yana tare da mahaifinsa,yakance "Ka barni nayi masa hukunci koda shine da gaskiya,ya cika zafin rai,ya fiya taurin kai da kafiya,wannan duka ba dabi'u bane masu kyau,ya kamata ya sauya saboda rayuwa". Murmushi abban yakan saki,ya kuma maida dubansa ga fuskar yaron kafin ya bawa mahaifinsa amsa "Ka godewa Allah,ba'a taba kawo maka qararsa akan rashin gaskiyarsa ba,koda kuwa an kawo qarar zaka sameshi ne ame gaskiya,shin me kake nema ko fata sama da haka?". Mahaifinsu mutum ne me tsananin kawaici,kanshi kawai yake kawarwa yana murmushi. Abban ya wuce komai a wajensa,maqoci ne me nagartar da samun irinsa yake wahala,don haka ne yake bashi dukkan girma,ba kuma wai don arziqi ko dukiyan daya mallaka ba,a'ah,don kawai ya cancanci hakan. "Kana jina?" Abba ya sake fada don maido hankalinsa kansa,sai ya gyada kansa a nutse shima yana duban abban "Yauwa,muje ciki,dukka su saddiq ma suna ciki na tabbatar yanxu" Bai musa ba yayi gaban abban yana biye dashi yana tsokanar dan uwan nasa daya sake sosai,farinciki ne ma kwance akan fuskarsa,da alama quruciya da rashin sanin cikakken ciwon kai ya sanya ko kusa ko alama baya hasashe ko hangen abinda kan iya faruwa,ko a kusa ko a nesa,me kyau ko akasinsa a kansu da rayuwarsu dama DUNUYARSU gaba daya. Ci gaba sukayi da tattaki cikin harabar gidan,yalwatacciyar haraba dake shimfide da interlock. Kana ma gidan kallo daya zakasan akwai sukunin rayuwa a cikinsu,duk da ba zaka kirayeshi da wani MAHAUKACIN ME KUDI BA amma tabbas yana cikin jerin MASU KUDI ARZIQI DA WADATAr daya tserema neman komai na biyan buqatar rayuwa,kamar yadda ya tserema RASHI ya masa tazara irinta HAIHATA HAIHATA. "Bude mana" Abban ya furta sanda yaga yaja ya tsaya ba tare daya buda qofar falon da zata sadaka da ainihin cikin gidan gaba daya ba. Matsawa yayi gaba kadan,ya murda qofar ya kuma tura,sannan ya saka qafafunsa cikin falon dake gauraye da sanyin Ac. Ita dince dai,itace mace ta farko da idanunsa suka fara tozali da ita. Bai sani ba,tsabar yadda ya washeta ne,yake kuma qyamatar shiga cikin dukkan lamuranta ne kamar yadda take nuna qyamata da qin jininsu qarara a fili?,wannan shi ya sanya ta zama mutum na farko daya fara gani?. "Kai dakata!,ina zaka je?,wajen wa kazo?,wai ban hanaku shigowa gidan nan haka gaba gadi ba kamar gidan tsohonku?,me ma ya kawowa da wasu tsummokara a hannu?" "Nine na kawoshi" Abba dake bayansa ransa na quna da jin kalamanta ya furta. Sak ta danyi,duk da bawai ta razana bane da jinsa,sai tsabar baqinciki da kuma zato daya soma zuwa ranta "Lallai kawai bala'i cikin gidan nan" Ta raya a ranta tana sake tattara dukka girarta waje daya ta hade,babu rahama ko qanqani saman fuskarta. Yaron dake zaune a rakube daga qasan carfet din ya sake tattare jikinsa waje daya,alamu dake bayyana lallai ya shiga taitayinsa da sauyawar yanayin nata. "Laaaaa......kaine kuma yau?ashe zaka sake shigo mana?" Yaron dake fitowa daga kitchen din gidan ya furta,fuskarsa na juna tsantsar farinciki,kamar yadda ya bada dukka hankalinsa akan wanda ya jefawa tambayar,hannunsa dauke da tray,daga hannun nasa har zuwa qafafunsa ya tattare bakin wando da kima rigar tasa. "Kai me yasa baka da hamkali ne?,zaka zo ka ajjiyemin ko kuwa?" Hamshaqiyar matar dake zaune saman kujerun falon ta sake ma yaron tsawa,wanda tamkar ma ya manta da abinda ya fito dashi daga kitchen din,kaf hankalinsa ya tafi ga baqon yaron daya shigo din,wanda a idanu shekarunsu tamkar daya suke. Juyawa yayi xuwa gareta don aje mata tray din,hakan bai isheta ba ta bishi da wani mummunan kallo,idanunta kamar zasu ciro su fado qasa "Shashasha,kamar wani wanda yaga qanin ubansa,sai nayi maganinku" Ta furta cikin fushi. Daga baya baya kadan ya ajiye tray din yana fatan kada hannuwanta yakai kansa,duk da yasan hakan zaiyi wuya,ko don wanzuwar mahaifinsu a wajen "Musaddiq......maza karbi kayan hannunsa ku wuce dakinku dukkanku" Zumbur yaron dake a zaune rakube tsakanin kujerun ya miqe. Bai jira kowa ba a cikinsu yayi hanyar dakinsu,saidai yana tafe yana dan waiwaye. A sanyaye ya sakarwa musaddiq kayan hannun nasa,yana qoqarin maida masa martanin murmushin da yaketa faman yi masa tunda sanda yayi tozali dasu "Muje ko?" Ya sake fadi yana kama hannunsa. Bai musa ba ya soma bin bayansa,don zamansa a falon yayi imanin sam bazai yiwu ba koda abba bai basu umarnin wucewa ciki ba. Zazzafa kuma tozartaccen kallo take binsu dashi,zuciyarta na mata wani irin suya,bacin rai da takeji kamar zata yi aman zuciyarta. Debe idanuwanta tayi daga kansu tana jan qaramar qwafa qasan zuciyarta,ita daidai take dasu,babu wanda ta shirya bari ya takura rayuwarta ko ya quntata ta. Duk wani motsi nata yana karance da ita,har zuwa sanda ya daidaita zamansa saman kujerar sannan ya dubeta yana kiran sunanta "Asama'u" Kallonsa kawai tayi ba tare da tace komai ba "Ga yara nan na kawosu,yara ne kuma da kin sansu bawai baqi bane a wajenki,kin kuma san basu da wata matsala ko aibu ko wani abun fada cikin unguwar nan......alqawari ne da na yiwa kaina tsakanina da ubangijina,na kuma cika alhamdulillah,ina fatan zaki tayani riqesu bisa amana ko don maraicinsu". Wani kallo takeyi masa ranta cike fal da mamaki,ta karkace tana dubanss tare da tattara abinda zata ce masa "Yanzu bayan naka yaran har yaran maqota kakeyimin kalensu?" Ta aje maganar tana jin zafi cikin ranta da zuciyarta. Tana jin ta quna bata tsoron qauri,ta soma gajiya ta kuma soma qosawa tare da debe haso hadi da tsammani na samun shimfidaddiyar rayuwar data jima tana mafarki gami da shimfidawa cewa zata samu cikin gidan..... *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* *PAGE 04* A nutse ya daga kai ya watsa mata wani irin kallo. Yau ta fara fadin hakan,amma kuma ya dade yana karantar hakan daga dukka ayyukanta da motsinta. "Nayi tunanin akwai dattako fahimta da kuma qaunar juna a tsakaninmu da har yarana sukafi qarfin kice riqonsu kikeyi,na zaci cewa kina ji a jikinki da zuciyarki kina rainkn 'ya'yan da kika haifa ne a cikinki?" Wani abu ne yazo yayi mata tsaye a wuya,ta juya kanta gefe guda tana tattaunawa da zuciyarta kan "Har abada 'ya'yan riqo ba 'ya'ya na bane,'ya'yan wasu ba zasu taba zama 'ya'yana ba.....banda qaddara me zai hadani da riqon 'ya'yan wasu?" . Idanunsa a zube fes a kanta,ya gyara zamansa sosai yana sake ci gaba da kallonta "Inaso ki cire a ranki riqo kikeyi.....ba 'ya'yana na cikina bama.......hatta yaran dana kawo yanzu,inaso ki ji a ranki Tamkar suna rayuwa ne cikin gidan mahaifinsu a gaban uwa da kuma ubansu". Dukka haqurinta ya qare,ya tuqeta ta kuma kai bango,tana jin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraronsa ba,don haka ta miqe tsam,ta kuma gegara ta gabansa tana barin falon. Da ido ya bita har zuwa sanda take shirin bacewa ganinsa. Ya jima yana ganin alamun da suke alamta masa akwai matsaloli masu yawa cikin rayuwar su farouq,amma yayita qaryata hakan gudun kawo damuwa da matsala cikin zaman uwar wani da d'an wani wanda keda wuyar sha'ani,sai gashi a qanqanin lokaci komai yana bayyana kansa daki daki. Numfashi ya zuqa ya fesar yana rufe idanunsa,qoqari yake ya saita kansa yana tunanin hanyar da zai daidaita komai. Tray din da faruqee ya ajjiye yabi da kallo,a dawowarsa daga lagos wannan karon ya fahimci kamar ma suke yiwa kansu girki harma su hada da ita idan ta kama,babu sakewa babu walwala sam tattare dasu. Ya lura da raguwar kuzarinsu kyara da kuma hantara daga gareta,saidai dukka ya kauda kai don bai kamaci a karon farko ya fidda soyayyar yaransa kai tsaye daga zuciyarsa har haka ba,bayaso yabar wani tabo ko targaden da zai kasa gyaruwa tunda wurwuri haka. Da idanu kawai yake bin dakin da kallo sanda Faruqee yaketa masa bayani zuciya da fuskarsa cike da zumudi da farinciki. "Kayi shuru?,ka tsaya a bakin qofa,ko dakin baiyi bane na gayawa abba a qaro wasu abun?" Faruqee ya fada jikinsa yana sanyaya da yadda yaga fuskarshi. Don a yadda ya zata zayaga farinciki sosai a fuskarsa kaman kwatankwacin nasa farincikin na dawowarsa cikin gidansu,farincikin samun aboki me hankali irinsa,farincikin samun aboki da yayi daidai da shekru da hankalinsa,ba aboli irin qaninsa ba da sam.baya gane wsu abubuwan saboda sabanin mizanin hankali da fahimta dake tsakaninsu. Karon farko yayi qoqarin sake fuskarsa da kyau yana kallon faruqee. Dakin gata kuma dakin yaran gata irin wannan da shi din bai taba samun kwatankwacinsa ba ta yaya zaice baiyi masa ba?. Dukka alatu da yayi saura a dakin bashi yake daukarsa ba.......duk da qarancin shekarun daka iya dakusar da tunanin yaro a sannan......amma shi sun bawa qwaqwalwarsa damar budewa da yin tunani me nisan zango akan "Wacce irin rayuwa zasu fuskanta a matsayinsu na agola bayan su kansu tsatson gidan basu tsira ba?,mene ne makomarsu?,meye farko da kuma qarshensu?" Tarin tambayoyin da baisan ta ina zaa fara sauke masa su ba "Nayi murna farouq" Ya furta a sanyaye,sunan da shi daya yake furtashi daidai yadda yake,don har yau bai taba kiransa da faruqee ba. Yadda qanin nashi ya zuba masa idanu ya sanyashi qoqarin sakewa,ya qaraso ainihin cikin dakin kamar yadda sauran suka kai ga shigowar. Qoqarin kauda komai ya dinga yi daga zuciyarsa,yana zaune daga falon yana iya jiyo muryoyinsu sama sama,saidai har yanzun baiji tashi muryar ba. Baiyi mamaki ba,don ya sani,yadda komai nasa ya fita daban daga cikinsu,haka dabi''arsa da halayyarsa ma ta zama daban. Abincin yaja ya soma ci bawai don cin abincin yana masa dadi ko yana burgeshi ba. Tunaninsa yayi zurfin da har ba komai dake wakana cikin falon yake ganewa ba,bai taba zata ba,bai kuma taba kawowa rabuwa da rabi'atu zai iya zame masa qalubale ba sai yanzun da dukkan alamu suka fara bayyana kansu. A karon farko har yaji ya fara tuhumar kansa da kansa,tare da nacin son gano meye ainihin laifin rabi'atu ne har ta cancanci a saketa?. Baici da yawa ba ya ture,ya miqe yana irgen lokaci,sai ya juya ya fara takawa zuwa dakin yaran. Dukkansu sunyi shirin bacci amma bandashi,yana zaune gefe daya na gadon farouq,ya goye hannayensa a qirjinsa tamkar wani babba da yayi nisa cikin nazarin wani abu. Motsin abban ya sanyashi waiwayowa,da sauri ya sauke hannayensa yayi qasa da kansa yana niyyar zamowa daga saman gadon "Yi zamanka me babban suna......tunanin me ka zauna kana yi?,duk 'yan uwanka sunyi shirin kwanciya banda kai?" Farouq dake zaune tsakiyar gadon yayi hanzarin karbar maganar dama tana damunsa tun dazu "Abba yaqi ya canza kaya,na bashi kayan bacci yaqi ya saka tun dazu" Hannu kawai abban ya miqawa farouq din,sai ya saka masa kayan baccin dake gefansa. Kayan abban yabi da kallo yana jujjyasu a hannunsa,sannan ya maida dubansa zuwa jikinsu dukka su ukun dake sanye da wasu kalolin kayan. "Amma faruqee ban gaya muku a bada kayan nan ba dukansu?,ina kayan dana kawo muku wancan tafiyar da nayi?" Ya qarasa tambayar yana maida idanunsa kan saddiq qaninsa. Har wani juyawa saida cikin saddiq din yayi,saboda tunawa da yayi da kakkaifan warning din da suka samu daga wajen matar gidan akan batun. "Abba,dukka mama ta karbesu,ta kuma gargademu kada mu sake mu sanar dakai,idan ba haka ba saita tsoma kawunanmu a ruwan zafi" Ba abba kawai ba,hatta me babban sunan saida maganar ta ratsashi duk da qananun shekarunsa,amma zuwa yanzu ya dade da yiwa kansa karatun qalubalen da suke shirin fuskanta "Ruwan zafi?" Abba ya furta cikin tsananin kaduwa da mamaki,sai faruqee ya gyadawa abban kai. Maganar ta ladabtar d abba ta sanyashi samun waje ya zauna. Yana tsoron ci gaba da wannan tafiyar tasu......yana tsoron garin neman lada ya rufta ya buge d wucewa jahannama,ya debo marayun Allah da nufin basu rayuwa me inganci,muddin Mariya bata goya masa baya ba meye makomar yaran?,ya gobensu zata kasance?. Tambayoyin da suka dinga karafkiya kenan a kansa. Indai haka ne ya zama dole yayi jan ido,ya zama dole yayi wuta wuta akan gidansa da iyalinsa. Ya sauke dukka nauye nauye haqqunan da suka zama wajibi dama wadanda basu zama wajibi bs,ya zama dole to itama ta bishi yadda ya kamata. "Ba komai,tashi me babban suna ka shirya,idan kun kammala ku kashe kayan wuta gaba daya kuyi addua ku kwanta" Yayi maganar ne yana sake nazartar dakin tare da kallon guraben da ga siya ma yaran abubuwa da dama ya ajjiye saboda jin dadin Rayuwarsu a yanzu ba komai a wajen sai gurbinsu. Sai daya kammala komai daga ainihin dakinsa sannan ya zarce dakin mariya. Ta gama shirin kwanciya tsaf tayi rub da ciki tsakiyar gado tana latse latsen waya. Fuska a hade ta daga kai ta kalleshi sau daya saita dauke kan nata ta maida ga wayarta tana sake tsuke fuska. "Tashi zamuyi magana" Ya fada cikin yanayin dake tabbatar mata da gaske yake,da kuma zafinsa ya shigo. Sai da tayi kamar ba zata tashi ba sannan ta miqe ta zauna sosai tana gyara wuyan rigar baccinta tare da tsuke fuska da kyau. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 05 last free page "Asama'u" Ya kirayi sunanta da wani irin yanayi da har cikin zuciyarta ta tabbatar cewa......dukka maganar da zata gita yanzu haka daga bakinsa ,yankakkiyar magana ce wadda babu janyewa a cikinta ko kuma wani sauyi bare sassauci "Ban rabu da mariya ba don na auro wata matar tazo ta azabtar min da 'ya'ya ba,ina tsananin qaunar 'ya'yana fiye da soyayyar da nake yiwa kaina,duk soyayar da zaki gwadamin bata da alfanu rana ko kuma fa'ida a gareni muddin ba zaki so 'ya'yana ba......asama'u,na rantse da Allah,dai dai da rana guda na samu wulaqanci cin amana ko tsanantawa diyoyina bisa ganganci bawai kuskure ko ajizanci irin na dan adam ba bazan raga miki ba"..... Wani dum taji har tsakiyar kabta,batabtaba kawowa dukka maganganunsa zasu kai har wannan iyakar ba,bata tana tsammanin abun yayi zurfi haka haka ba,da ake gaya mata yana da son yara batabtaba kawowa yakai har wannan bigiren ba. Zuwa sanda zatakai qarshen tunaninta shi din ya jima da miqewa yana kallonta "Bazan fasa tafiye tafiye na wajen neman halak da neman abinda zan rufawa kaina da iyalina asiri ba......ba kuma zan kwashe diyoyina na kaisu wanin guri ba,gaki gasu nan asamau,dukkan abinda kika qudirta yi kada ki fasa koki sauya ra'ayi" Ya qarashe fadi yanajin wani irin daci saman harshensa,bai kuma dakata ya saurareta ba ya juya a nutse yana barin dakin nata. Har sanda ya bacewa ganinta bata dauke dubanta daga bakin qofar dakin ba,ta qanqance idanu tana kallon qofar tare da jin dacin kalamansa suna gauraya kowanne sashe na jikinta. A taqaice dukka bayanansa suna auna mizani da kuma adadin iya matsayinta kenan a wajensa?. Bata shigo gidansa don ta fita ba,don muhallin dame muhallin duka sunyi mata,amma kuma bata shigo bautar d'an kowa ba,hakanan bata shigo don a takata ko aci mata zarafi ba bare kuma a hanata sakewa. Shawara take buqata kawai a yanzu hala,don gaba kura ne baya sayaki,ta kula dasu ko ta barsu komai ta fanjama fanjam?,to amma fisabilillahi zai yiwu kuwa ace ta buge da bautar d'iyoyin da ba ita tayi Jigilar daukar ciki da kuma rainonsu ba?. Matsawa tayi kusa da wayar landline dake gefan gadonta,ta latsa lambobi tana fatan sashen kamfanin sadarwar ya sadata da matar data kira take mararin magana da ita. Ba'a dauki dogon lokaci ba sukayi mata hakan,saita qarasa sauke dayar qafar tata qasa tana zama sosai yadda zatafi jin dadin amayar da abinda ke cikinta. Yanayin yadda suka gaisa kadai zai gaya maka akwai shaquwa me zurfi da tsohuwar sanayya a junansu. "Ya nake jinki haka sama sama?" Daga saya bangaren ta tambayeta. Sai data aje dogon tsaki sannan ta fara magana,zuciyarta cike da wannan bacin ran da batasan ranar da zai wanke daga zuciyarta ba "Barni kawai......dukka shirina har yanzun bai tafi a yadda na jima ina tsarawa ba" "Wani abunne kuma?" Kai ta rausayar tana jin kamar ta qifta idanuwanta ta budesu ta tarar babu kowa tsakiya da gefannin rayuwarta da mijinta,daga ita saishi "Yarannan haleema......bayansu ya sake kwasomin riqon marayu,bayan wadannan din har yanzu ban gama da matsalarsu ba......" Daki daki ba tare data rage komai a abinda yake faruwa ba ta shimfida mata,sannan ta dora da fadin "Inajin kamar naje gurinsa ayita ta qare haleema,na meye zaa dinga doramin nauyin da bai zama wajibi a kaina ba?" Ajiyar zuciya haleeman ta sauke "Ashe qarya kikeyi,baki shirya zaman auren ba" Haleema ta katsi numfashinta sanda taji tana shirin sake dorawa da wata mitar "Kamar yaya?,ya zakice haka bayan kinsan komai?" Ta tambayeta tana tsuke gira tare da mamakin amsar data bata "Eh to ai dole nace haka,wani lokaci sam baki da wayo asama'u,yaransa biyu da yake mutuwar so ki gaza riqesu?,bakisan ta hanyar riqon da zaki musu bane zaki samu fiye da abinda kike hange ko hasashe daga jikinsa?" Ta qarashe maganar da sigar tambaya,tambayar data dauki dukka tunanin asama'u ta jefashi wani guri me nisa "Amma haleema,saina zama baiwar yara har hudu?" Ta yiwa haleema tambayar tana jinjina girman abun,tamkar wadda aka dorawa nauyin wanke kashinsu da fitsarinsu gami da ci dasu tsahon kowacce rana da wuni na rayuwarta "Bance haka ba,ban kuma goyi bayan hakan ba,yaransa sune dolensa,su zaki kama ki riqe,saura kuwa wannan baida hurumin tilasta miki zama dasu,idan ma baki riqesu ba bakiyi laifi ba,kedai yaransa su zama makamin zamanki a gidan,yo asama'u kona ganin ido ne ke ba zaki iya ba?.......". Dadewar da sukayi saman waya sa haleema iya adadin karatun data samu daga gareta,ta kwanta ne tana juyawa tare da tauna yadda zata dauki shawarwarin haleema tayi aiki dasu,ta yaya zata danne zuciyarta da dukka wani abu da takeji tayi yadda haleema ta kwatanta mata?. *_W A S H E G A R I_* Dukka su hudun suna zaune a gabanshi,yana jansu da hira cikin yanayin da zakayi tsammanin shi din wani babban yayane a garesu bawai uba ba. Da idanu yake karantarsa,har yanzu dai bai sake ba kamar yadda ragowar 'yan uwansa uku suke a sake. Har yanzu a darare yake,dararewar data sanyashi yaji a ransa akwai abinda ya hanashi sakewar. Har cikin rai da gangar jikinsa a yanzun da suke gabansa yake jin kamar dukka su hudun mallakinsa ne,shine ya haifesu. Inda yana da iko tabbas zai maida agogon rayuwarsu baya ya mantar da al'ummar da suka sanshi dama na unguwar cewa shi din ba shine ya haifesu su biyun ba. Tun daga nesa da take takowa cikin falon idanuwanta yake kansu. Sunyi wanka dukkaninsu sun kuma shirya cikin shaddodinsu masu kyau,wadanda tayi imani cikin sabbin kayan daya saba tahowa da yaranne. Sake maida idonta tayi a kansu,a nutse yake qwarai fiye da dan uwansa,ba wani karsashi a tare dashi ko kuma rawar kai,saidai kuma haka siddan takejin muguwar matsananciyar tsanarsa shi da dan uwansa. Ta yaya tun bata aje nata yaran ba ace wasu yaran sun shigo sun sake cinye gurbi da muhallin mutum biyu bayan gurbin mutum biyun da yaran gidan suka cinye?. A yanzun idan har ta soma aje nata yaran kenan saidai su tashi daga na biyar?,ya za'ayi ta bari haka ta kasance?. Sai data iso dab dasu sannan ta iya controlling kanta tayi sallama. Dukkansu suka daga kai suna dubanta banda abba da ya kauda nasa kan kadan gefe don da haushinta ya kwana. Qoqarin gaidata sukayi,ta amsa tana binsu da kallo daya bayan daya,wannan ya sanya kowa ya sake kama kanshi a cikinsu,bansa me babban suna wanda tun daga kallon farko bai sake daga kansa ba bangaren da take. "Ina kwana abba?" Ta gaidashi cikin matuqar qoqarin daidaita kanta idanunta zube kan kayan breakfast dake gabansu. "Lafiya lau" Ya amsa mata a taqaice yana rufe plate din fried egg din daya gama ci. "Yau nayi bacci me nauyi ban samu tashi na hada abincin safe ba" "Eh laraba tayi.......don dama fita nakeso muyi" Ya amsa mata yana miqewa. "Ina haka da safiyar nan?" Tayi masa tambayar cikin son sanin komai "Makarantarsu Faruqee,inason na yiwa su me babban suna registration,next week idan Allah ya kaimu su koma tare baki daya" maganar tayi mata kama da almara ko kuma ba zata. Tana tantamar akwai hikima ko hankali kuwa cikin maganganun abban?,ta yaya zai dauki yaran maqota ya kaisu makaranta me kudade masu ciwo haka?,makarantar dako yaran cikinsa da taji nawa ne school fees dinsu saida taji kishi da baqincikin abun?,ta kuma bashi shawara a fakaice ya kusa sau biyar akan ya sauya musu da wadda bata kaita ba.... Ko don yadda shima wani lokaci ta lura kaman yawan school fees din yana dan takurasa?. Abinda ya darsu a ranta me girma ne,tana da abubuwan da takeson ta fadi masa amma girman bacin rai da kuma abinda ya tsaya mata a wuya ya hanata cewa komai har suka tarkata suka fice daga falon. Idan nace ta samu nutsuwa tun daga fitarsu har dawowarsu to zance ne kawai. Sanda suka tashi dawowa din kuma sun dawo da dukka tarkacen kayan amfani na buqatar rayuwa na yau da kullum. Komai hurhudu ya siya,amma kaf cikin siyayyar bataga tsinke nata ba "Somin tabi kenan hatsin gara a buta......tun yanzu?" Wani sashe na zuciyarta ya ayyana mata. Ai juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Tun a rana ta farko ta soma karantar iyakokinta?,dukka kuma akan yaran da suka kasance tamkar wata tsintacciyar mage?. Yaran da basu da GATA ASALI ko wani GALIHU?. Ita kuwa asama'u yaushe?,yaushe zatayi wannan SAKEN?. Muddin bata bazama su ba lallai anyi asarar haihuwarta,muddin bata ganar dasu kuskuren maida UBAN WANI NASU BA bata cika MACE BA.... *_BAN TABA KOMAI BAFA CIKIN LABARIN......BAN FARA KOMAI BA A CIKI_* *_zazzafan labari ne tsakanin SABREEN DA MUHAMMED FU'AD_* *_BANBANCIN RA'AYI TSARI DA AQIDA_* *_MUMMUNAN ZATO DA GURGUWAR FAHIMTA_* *_TA YAYA RUWA DA WUTA ZASU HADU GURI DAYA?_* *_ZALLAR QIYAYYAR MAHAIFIYA HALITTA MAFI SOYUWA A DUNIYA_* *_BAHAGUWAR BIYAYYA BISA TILASHIN ZUCIYA BA DON RAI YANA SO BA_* *_GWANA KUMA QWARARRIYA WAJEN SACE ZUKATA DA ALJIHUN MAZAJE DAMA ASUSUNSU GABA DAYA_* *_KARKI SAKE AYI BABU KE_* *_WANNAN SALON YASHA BANBAN DANA SAURAN_* *DUNIYATA(MUHAMMAD JADDA)* *DUNIYATA(SABREEN)* _GA HANYA MAFI SAUQI DA ZAKI KASANCE DA ZAFAFABIYAR FAMILY IN SHA ALLAH_👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 06 ___________________________ *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾 *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* __________________________ Tayi zaune kawai saman kujerar falon tana duban kowa d'ai d'ai da yadda yaran keta walwalarsu da sabgoginsu. Ta yita juya zancan haleema a ranta,anya zata iya kuwa?,zata iya jurewa?,daga bisani data tabbatar muddin taci gaba da zama a wajen zata karya dukka tsarinta saita yunqura kawai ta miqe tana bar musu falon. Cikin satin ya tabbatar yayi musu dukkan abinda ya dace,ya kuma sauke duk wani abu da uba zai saukewa 'ya'yansa,tun daga suturunsu xuwa takalmansu,kayan makaranta hadi da jaka takalmi da duk wani abu daya zama dole ga dan makaranta. Zai iya cewa Kansa da kansa sauyi ne na dare daya yazo cikin rayuwarsu,duk kuwa da cewa har yanzun.....daidai da second dayahasashe,koda da wasa irin na qwaqwalwa zuciyarsa bata taba hasashen ta manta da abubuwa guda ukun nan da suka shafi rayuwarsa ba......suka shigeta da wani irin yanayi,yanayin daya tilasta canzawar zubi da kuma tsari na dukkan feeling na zuciyarsa da gangar jikinsa. Abbansa Jadda Da kuma uwa uba mahaifiyarsa da zuciyarsa ke mata wani irin bahagon kallo. Halitta mafi girma da daraja cikin rayuwarsa......amma kuma dukkan wani matsayi da girman suna da halittar ta mallaka baya jinsa ko dis cikin jininsa da zuciyarsa. Eh tabbas......a tsukin kwanakin rayuwarsu tayi wani wawan sauyi,saidai nashi sauyin ya tsayane cak iya zahirinsa. Darare da yawa suna wucewa cikin idanunsa. Alfijir dake cikin kowacce asubahi da Ubangiji ya halittama kwanakinmu sun sha ketowa ta cikin qwayar idanunsa. Ta tsakiyar qwaqwalwarsa yana jin kamar an tsatssagarta da wani abu me kaifin tsini "Me yasa maama taqi zama damu?,me yasa ta kasa jurewa lalurar Abbey?" "Saboda bashi da komai yanzun,saboda shi talaka ne" Amsar da kullum yakeji ana rada masa kenan cikin kunnuwansa. Sau tari yakan sanya dukka tafukan hannayensa ya toshe qofofin kunnuwansa wai ko zasu daina jiyo masa wannan amsar......waiko amsar tambayarsa zata iya sauyawa?.....saidai aah,koda wasa bai taba jin amsar nan ta sauya ba. Tun baya daukar gaskiya ake rada masa ana kuma sake jaddada masa har zuciyarsa ta gamsu da hakan. "Indai haka ne maama ita tayi silar mutuwar Abbey......indai haka ne maama itace tayi ajalin jadda" Abinda yake gayawa kansa kenan a duk sanda ya kalli fuskarsa dake dauke da qananun shekaru "Amma ta yaya ta kashesu?" Tambayar da daya kasa lalubo amsarta,saidai yasan koda duniya zata taru ta hanashi wannan tunanin bazai taba kankaruwa daga qwaqwalwarsa ba har ABADA. ******* Safiyar litinin ce dake dauke da yawaitar hazo da kuma lullumin sanyi daya soma tun a daren shekaran jiya. Cikin dakin nasu a cikin su hudun kowanne shirin tafiya makaranta yake yiwa kansa don ba wanda baya iya yiwa kansa da komai da komai a cikinsu,daga su Faruqee da suke 'yan gidan,har su da suke baqi ko kuma ace 'YAN RIQO. Kusan za'a iya cewa banbancinsu dasu Faruqee din shine,mamarsu da babansu dukkansu suna a raye,sannan komai tsanani suna da gatan dangi da kuma muhallin da zasu kwana a ciki. Amma ta fuskar samun cikakken gata da kulawa na iyaye,sun tashi kusan a mizani guda,don sun rasa kaso tamanin a cikin dari sanadiyyar RABUWAR AUREn mahaifansu. "Ya kamata kayi ka gama,wannan laqai laqai din naka ba abinda zai haifar mana sai bata lokaci,kasan dai abba ya koma a motan haya zamu je yau" Faruqee dake saba school bag dinsa yace da saddeq dake kurba shayin da Faruqee ya hado musu dukkansu suka gasa cikinsu. Kusan ya zame musu jiki,duk randa mahaifinsu ya sanya qafa ya koma Lagos lunch box dinsu yakan koma hoto,zancan breakfast kuwa saidai da tsananin rabo Faruqee ya faki idanunta ya hada musu tea susha su wuce kaman yau. Tasha kamashi bayan anyi hakan,tasha gargadarsa amma a banza wai man kare,gobe ma sai ya qara. Tun tana hukuntashi ta hanyar duka har yakai shekaru sha biyar. Tayi niyyar masa wani wawan duka,amma da yake ance qashin namiji dana mace ba daya bane saita samu targade a hannun nata madadin shi yaji rauni. Yayi dariyar ranar kaman ba gobe,ya dinga maimaitawa qaninsa "Alhakina ne". Hakanan taji jiyyar hannun nata ba tare da kowa ya sani ba. Tun daga ranar ta canza kalar horo,saita hadashi da aiki me tsanani,kota hanasu abinci a ranar gaba daya. Irin wannan horon yafi mata dadi idan ya zamana abba baya gari,idan kuwa yana nan abubuwa da dama saidai tayi haqurin dole ta tarasu sai randa ya wuce. Saddiq da musaddiq ne a gaba,sai shi da Faruqee a bayansu. Kana musu kallon farko zasu burgeka,ka kuma dauka set din tagwaye ne guda biyu,don dukkansu kusan sa'annin junansu ne. Yanayin zubin kyan halitta da suke dashi,ga kuma wadatacciyar tsaftar uniform da Faruqee bai yarda wahalar cikin gidansu ta sanyashi qazanta ba. Ba wanda gabansa bai fadi ba cikin su ukun bayan ratsowarsu ta falo da zummar fita daga gidan idan ka dauke me babban suna da ya dauke idanunsa daga kanta tuntuni. Qafarta daya saman daya tana karkadata a hankali,kamar yadda ta zube musu idanunta tana binsu da kallo kamar qwayar idanun nata zasu zuba a waje. A darare dukkansu suka gaidata,saidai idanunta suna kanshi ganin yadda ya gaidata hankali kwance,sam kuma kwata kwata babu wannan razani da kuma d'ar d'ar dake kwance a fuskokin 'yan uwansa dake takawa cikin sanda suna fatan wucewa daga falon lafiya. "Zo nan dan qaruna!" Ta furta da wata kakkausar murya tana sake jin haushi da tsanar yaron. Dukkansu suka waiwayo,ta sake binsu da ido "Duk ku dawo nan" Ta kuma fada tana gyara zamanta. Ba wanda ya musa mata suka tako dai dai da dai dai suka zube saman carfet din "Kai don ubanka waye yace ka shiga kitchen ka taba madarar gidan nan?" Ta jefawa Faruqee tambayar tana watsa masa zagi da hannayenta. Kiran uban da tayi shi ya sauka har tsakiyar zuciyarsa ya sosata. UBA wani abu mafi daraja da yake ganin kimarsa cikin DUNIYARSA fiye da uwa,ubansa da kuma ABBAN Faruqee mutane biyu da basu da tamkar da bayajin zai iya jurewa zaginsu. Idanunsa ya maida ya lumshe yakuma yi qas da kansa yana hadiyar wani abu me tauri da zafi tamkar shi mama ke tambaya. Wai haka iyaye mata suke ne marasa tausayi?,marasa imani?,me yasa iyaye maza yaketa gani da tambari da dukka wani tabo na tausayawa 'ya'ya?,me yasa kalmominsu suke tsauri akan 'ya'ya cikin rashin tausayi da kyautatawa?. "Makaranta zamuje,kuma yunwa mukeji" "Ubanka nace......saboda ubanka ne ya kawo madarar shine kake ganin kana da right na shigarmin kitchen yadda kakeso?" *_Dukkan godiya sun tabbata ga Allah_* *_yadda muka fara lafiya Allah yasa mu gama lafiya_* *_kusa kurai da zaa gani a ciki ajizanci ne irin na dan adam,da fatan za'ayi afuwa a kau da kai_* *_Don Allah don Allah ina roqo da fatan zaku zama masu uzuri a gareni,saboda yanayin sabgogin rayuwa,kowa ya sani yau da gobe tana iya sauya bawa daga ainihin yadda aka sanshi_* *_duk sanda kuka samu wani sauyi tattare dani game da tsaiko na posting,tsahon pages da sauransi,ina kyautata muku zaton soyayyarku gareni zata sanya ku zama masu yimin uzuri_* *_ina godiya qwarai game da yadda bakwa gajiya da bibiyata,da bibiyar zafafa biyar gaba daya_* *_alkhairin Allah yakai muku a duk inda kuke,tare da fatan ubangiji zai tsareku kuma daga dukkan abunqi_* *_na gode qwarai,kuma in sha Allah a duk sanda dama ta samu zaku samu komai fiye da yadda kuke so ma cikin wannan tafiya ta DUNIYATA_* *_LABARIN ZAI TABO BOYAYYAR MATSALAR DA MUKE FAMA DA ITA,na muku alkawarin nishadi da sassanyar soyayya kan bigiren salon da kukafi so😍🥰_* *MU KASANCE TARE IN SHA ALLAH DAGA FARKO HAR QARSHE* *HUGUMANKU CE* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Read My Book "DUNIYA TA🌏" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ________________________ Page 07 Dif sukayi dukkansu,ba wanda ya iya tanka mata a cikinsu. Daga can qasan zuciyarsa yake jin wani irin zugi fushi da kuma radadi,don meye zata dinga zagin iyaye a gaban 'ya'yansu?,shi abban me yayi da har ya cancanci a zageshi?. "Badai makaranta zaku ba?,ku tashi ku bacemin da gani". Kaman dama suna jiran wannan umarnin ne daga gareta dukkansu suka miqe din kusan lokaci guda,kowa yana yunqurin barin gabanta kamar yadda ta buqata " Harda su kaza a cin danqo?" Ta furta tana kama haba idanuwanta a kansa "Kai dan qaruna ina zakaje?" "Makaranta mana maama,ko kin manta tare muke zuwa?" "Na manta uban masu gida,saika karanta min,don ubanka da can makarantar suka damu da zuwa?,shine yanzu saboda wuce gona da iri da samun waje har suke rawar jikin tafiya?.to wallahi kuda makaranta saidai idan anfi qarfina" Ta fada tana kada hannu da kyau cikin hargagi tana nunasu da yatsa. Hukuncin nata yazo masa a bazata,don bai taba tsammanin zatayi hukunci me tsauri har irin haka ba. Yaji abun ya taba ransa qwarai,domin a yanzun bashi da wani buri daya rage masa saina KARATU. KARATU shine cikar burinsa qwaya daya tal daya rage bai qarasa mutuwa daga zuciyarsa ba,yana jin zai iya bada kominsa don yayi karatu,zai kuma iya jure dukkan wata wahala tsanani ko tsangwama saboda karatu. Ko a yanzun yana daya daga cikin abinda ya sanya zuciyarsa ke qarfafa,tana sake jadda masa zai dauki komai ya kuma jure komai din saboda ingantaccen ilimin da yake hangowa zaya samu. Dole ya daga idanunsa da suka fara sauya launi ya kalleta dasu "Kalleni da kyau......ba wani karatu da zakuyi cikin gidan da ba na ubanku ba,idan kuma kallon mamaki kake yimin ai uwarka yafi kamata ka yiwa wannan kallon,ita kanta ta kasa jurewa zama daku sai ni da bani da galihu akeson hadani da alaqaqai,to wallahi yadda ban samu yadda nakeso ba,haka kuma ba zaku samu ba......." "Me kikeso ayi mama?" Ya furta tana aje numfashinta daga tijarar da takeyi. Tsananin mamakin yaron takeyi yadda yakeyin komai cikin dakiya da taurin rai dana zuciya "Ko baka tambaya ba ai zan gaya maka kuma dole kabi,ka sauke wannan munafukar jakar ku wuce ciki,sudai da babu yadda zanyi dasu gidan ubansu ne saisun dawo,a sauka lafiya" Ta fadi tana nunawa su Faruqee hanya da yatsa. "Mama.....amma" Zakayimin shuru ko sai ka jawo kuma na hanaku?" Wani dunqulallen abu ya hadiye can qasan ransa yana jin kamar ana masa suya "Kudin mota" "Kudin ubanka dai,sayyadarku zaku taka sisi bazan bayar ba" Ya fada tana zazzare masa idanu hadi da dukan hannun kujerar da take kai "Ku tafi Faruqee don girman Allah" Ya furta da rinannun idanunsa da kuma muryarsa da tayi laushi qwarai yana duban Faruqee din,don kunnuwansa sun soma gajiya da jin zagin da take nausawa bawan Allahn da baisan hawa ba baisan sauka ba. Kallon kallo suke ma juna shida Faruqee din,kowanne cikinsu zuciyarsa cike take fal da zallar bacin rai daya haurawa shekarunsu. A zahiri tausayin me babban suna shi yafi rinjaye a zuciyar Faruqee. Ba yau ba ba kuma jiya ba ya sani......muddin ka ambaci kalmar UWA ko mahaifiya a gabansa takan zame masa kamar tabo ko kuma ciwo koda ba dashi kake ba,ballantana a yanzun da aka kirata muraran. Abun ya jima da zame masa kamar wani ciwo,tunda zancan ya bulla cikin unguwa sai ya zama abun yamadidi da magana tsakanin maqota da mazauna unguwar. Sam baa tallafi rayuwarsu ba,ba'a agajesu ba,ba wanda ya waiwaya ya dubi tsanani bayan tsananin da suke ciki,ba wanda ya bawa rayuwarsu tallafin da zai rage musu radadin da sukeji,a maimakon haka,sai suka debo DAFI na cecekucen maganganu akan rayuwarsu suka sake watsawa ciwuka da raunukan dake ciki zukatansu shi da d'an uwansa. "Kaje Faruqee" Ya sake maimaita masa yana tsareshi da ido. Ya karanci komai ta cikin idanunsa,ya karanci abinda yake nufi da maganarsa,don haka bai qara koda minti daya ba ya kama hannun musaddiq suka suma takawa suna barin falon. "Na dawo gareka" Ta furta cikin izza da dagawa tare da jinta can saman qololuwar isa da kuma 'yanci "Ka koma ka zare wadannan kayan,don basu dace da agola irinka ba,tabbas da 'ya'yan da mahaifiya zata wofantar dasu,ta tsallakesu ta gudu ta barsu to ba'a banza ba......don haka banga dalilin da uwar data haifeku bata tausaya muku ta zauna daku ba ni zan tausaya muku ba......tunda kun iso inaga ya kamata me mana wanki da guga ya tafi hutu hakanan,ka shiga dakin ajiyar kayan wanki ka debo duk kayan da ka gani ka fita dasu bayan gida wajen fanfunan can ka wankesu......wallahi wallahi kace zaka saka iskanci a aikin kaga ikon Allah,banaso kuma azahar tayi maka baka kammala ba". Baice komai ba yakau da kai ya soma takawa yana komawa dakinsu ranshi yana wani irin tafasa da suya. Tsanar maama tana sake wani mahaukacin tasiri cikin ransa. Inda bata tafi ta barsu ba duk tsanani duk wuya,komai girman talaucinsu sunfi gaban a goranta musu,don da iyaye ake ado,sune abun adon diyoyinsu. Me yasa ta aikata hakan?,me yasa ta kasa jurewa?,tsabar son kai ne irin na jinsin DIYA MACE da ya tabbatar a yanzun haka halittarsu take?.ko kuma son duniya da qyale qyalen cikinta ne ya rudeta?. Me yasa batayi haquri ba kaman yadda Abbie ya dinga kira mata?. Har yau har kwanan gobe sashen qwaqwalwarsa da ya nadi muryar Abbie ta qarshe.....magiyar Abbie ta qarshe akan roqarta ta zauna ya gaza goge su......ya gaza goge wannan rarraunan sautin nasa daga nemory dinsa. Abinda ke sake aza masa wata mahaukaciyar wuta,tare da dasa masa fara kallon halittar diya MACE a baibai. Yana cire kayan saddiq yana kallonsa,a duk sanda zuciyar dan uwansa ta motsu shine mutum na farko dake fara fahimtar hakan. Ya kammala cire kayan tsaf ya musanya dana gida sannan ya juya ya adana na makaranta yana musu kallon tsanaki,dukka ruhinsa da zuciyarsa tana makarantar,yana wassafa malami na farko ya fita zuwa yanzu,malami na biyu kuma na dab da shiga ajin komai yana ciki. Hannu ya sanya ya share fuskarsa yana qoqarin lanqwasa zuciyarsa. Farat daya qaunar da yakewa karatu ya ninku a zuciyarsa ganin abba ya bashi dukkan wata dama da zaiyi karatun,sai gashi farat daya tana nema ta zama silar da zaiyi nisa sosai da MAFARKINSA?. _________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* _________________ *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 08 __________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* ___________________________ "Hamma" Ya tsinkayi muryar saddiq tana kiransa,sai ya waiwaya ya zubawa qanin nasa ido "Wai sai yaushe maama zata dawo?,yaushe za'a daina yi mana gori?" Tambayar ta tsinka zuciyarsa sosai ta kuma sake yi masa tabo. Ya zuba masa idanu sosai,kamar bazai ce komai ba sai ya motsa labbansa "Duk tsanani duk wahala.....kada ka sake zancanta sadiq,ta tafi kenam,ba kuma zata sake waiwayomu ba.....ni zan tsaya dakai a kowanne yanayi da.mataki na rayuwa,bazan bari kasha wahala ba in sha Allahu,bazan bari ka zubda hawaye irin wanda na zubar ba.....kayimin alqawari ba zaka sake zancan maama ba?" Ya qarashe maganar yana ritsashi da idanu. Kai ya jinjina a sanyaye yana maida jikina ga bango ya jingina,wani abu sosai yaron yakeji da baisan yadda zai fasalta shi ba "Ka cire uniform din" Ya bashi umarni ya sanya kai yana nufar qofa bayan muryar mama ta karade ilahirin gidan ta cimmasa har dakin nasu "Yaaya zan tayaka wankin" Sadiq ya fada a gaggauce "Aah banaso,kayi zamanka" Ya amsa masa yana qarasa ficewa. Tun daga wannan rana ta sauya lokutan zuwansu makaranta zuwa lokuta na bauta da wahalar ayyukan gidan da basu ratayu a wuyansu ba. Duk wani aiki ta kallafa masa,har takai ta bawa ainihin masu gudanar da aikin hutu tace saita nemesu,hutu ba tare da an yanke musu albashi ba. Dukka yawa da azabar aikin aikin banza ne a garesa idan aka kwatantashi da maganganu masu dafi da take jifansu dashi. Duk kalmarta guda daya me tsananin guba ce tana kuma same zuba masa dafi da guba me daci ne cikin zuciyarsa. Rashin ko inkula dinta a kansu da dukka dabi'unta basi fiya bashi mamaki ba,saboda ya riga da ya yiwa mata kudin goro gaba daya,tunda ya fara ganin sample daga kan mahaifiyar data tsugunna ta kawoshi duniya kuma. MATA BASU DA IMANI,BASU DA KIRKI,BASU DA TAUSAYI,BUQATAR KANSU CE A GABA DATA KOWA. Wannan shine rubutaccen abu daya zauna radam cikin kwanyarsa da zuciyarsa,wanda baya jin akwai lokacin da zaizo wanda wannan zai wanke daga cikin kundinsa. Duk yadda Faruqee ke cikin tsananin fushi da daukar alwashin sai ya gayawa abba idan ya dawo,in yaso ta kamashi ta gutstsira namansa ta kacalcala amma me babban suna ya danneshi ya kuma haneshi "Maama ma data haifemu ta gujemu,ta gaza tausaya mana?,ta kasa haquri damu?,ina ga mama......mu din ba dolenta bane Faruqee,iya abinci da take sawa ana bamu da gurin kwana ma kawai tayi qoqari" "Abincin nata ne?,ko gurin kwanan nata ne?,sannan shi kansa abincin waye yake qoshi?,bayan store din gidan nan cike yake da kayan abinci?" Qaramin murmushi ya saki. Duk da qarancin shekarunsa amma kwanyarsa tana aiki yadda ya kamata. Dukka wannan bai cika masa ciwo bafa,abinda maama tayi ya danne dukka wadannan ciwo da zafi da kuma tsaiwa a zuciya. Abu daya ne yakejin yana dab da kasa jureshi,hanashi zuwa makaranta......yana qaunarta yana qaunarta yana qaunarta har baisan iya adadi ba. Abu na biyu indai saddiq dinsa yana lafiya to komai me sauqi ne. A haka suka debi wata guda cur babu abinda ya sauya. Yadda kowacce safiya da ubangiji zai bullo da ranarsa haka zata fidda wani sabuwar muguntar don quntatawa cuzgunawa a garesu. Duk fushi zafin zuciya da rashin daukar raini irin nashi bai taba daga kai ya kalleta bare ya tanka mata ba,yana duba cewa ta girme masa,gaba take dashi,a qalla ta ninka shekarunsa sau biyu. Duka duka shekarunsa sha shida basu kai adadin shekarun da zai tsaya yana jayayya da babba ba. A hakane ALHAJI HAMZA KIBIYA ya waiwayo gida cikin iyalansa. Yaran suna ranshi matuqa,babu kuma ranar duniya da zata bullo ta bace bai tambayeta su ba idan suna waya,amsar kuma daya ce suna lafiya lau. Koda ya buqaci magana dasu tana gabatar masa ne da wani uzurin a kansu. Wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi. Sanda ya sanar da dawowarsa kaf ta hadasu ta musu mummunar jankunne data tsoratasu ainun. Saidai ko kadan shi bai tsorata ba,don ba komai yake bashi tsoron ba,bare a yanzun da zuciyarsa ke qarasa bushewa da qeqashewa akan komai na rayuwa. Yadda aka saba haka ta sakar musu,sukaci gaba da zuwa makaranta abba yana kaisu da kanshi kamar yadda yakeyi idan har yana gari. Ya tsumu sosai,zuciyarsa kuma ta cika da takaici da bacin rai me yawan gaske sanda ya isa class dinsu yaga yadda aka tsere masa a karatu. Kusan ranar duka ya qarar da ita wajen bibiyar dame dame akayi da baya nan?,ya karbi note books na classmate dinsa da dama ya taho dasu gida . Da yake abba yana nan akwai isashen lokaci 'yanci da kuma hutu,babu tarin aikace aikacen nan marasa dalili marasa kuma tushe ballantana makama,sai ya zauna ya qarar da dukka wuninsa a daki wajen ganin ya daidaita karatunsa dana 'yan uwansa. Bashi da matsala da saddiq,don ajinsu daya da musaddiq,kuma duk sanda suka dawo gida Faruqee yana hadasu su sake maimaicin karatu tare ta yadda zai zamana ba'a wuce saddiq din ba. Yana da wata irin baiwar basira ta gasken gasken,sharp brain dake da saurin koyo da kuma riqe abu tun yana dan mitsitsinsa ballantana a yanzun da yake shirin fara shiga shingen samartaka,danyan jini yana zagayawa da gudu a jikinsa. Wannan ya taimaka cikin sati gudan da abba ya musu hutu ya gama kammala komai,ya kuma tarar dasu tamkar dama dashi ake karatun. Sai a sannan ya samu sukuni ya soma dawowa daidai. Saidai kuma a satinne qarshen satin,a yammacin juma'a abban ya tattara ya koma lagos,abu guda daya dake alamta musu zasu koma RAYUWAR GIDAN JIYA kenan cikin gidan. ********* *_MONDAY_* Tushen aiki,bai sare ba ya shirya tsaf kamar yadda su Faruqee ke shiryawar,yana shirin Faruqee na rantse rantse da cewar ba abinda zai hanasu fita a makaranta yau din. Ya lallaba kitchen ya hada musu tea kaman yadda ya saba ya dawo ya bawa kowa,saidai ya tsallake me babban suna don yasan bazai sha ba,don kuwa tun daga wancan ranar data zagi abban bai sake ci ko shan wani abu da Faruqee zai dauko musu ba,ya tsani zagin iyaye matuqa,mutum ne kuma me fushi da gudun zuciya,wannan ya sanya yake takatsantsan,akan komai bai fiya zura jikinsa ba. Fitowa sukayi kamar wancan karon,saidai a yauma sun sameta hakimce a falon. Idonsa yadan lumshe yana addua daga qasan zuciyarsa. Ya tabbatar wannan zaman ta yishi ne saboda su,son a lokutan da abba yake gari kwata kwata nasa ganin qyallinta sai kusan shada zuwa sha biyu na rana. "Eh......wato akuyar daure an samu sake,to kuzo nan" Faruqee ne na farko daya fara cakewa guri daya,amma ya kama hannunsa ya jashi suka qarasa wajen. "Me zakuyimin ku?,tunda kuna da uba ya daure muku gindi?,ku tashi kuban waje,ku kuma ku koma ta inda kuka fito a cire uniform azo a kama aiki ko?" Cikin tsananin bacin rai Faruqee ya miqe yana nufar hanyar fita yana kuma qananun maganganu qasa qasa "Zagina kekeyi farouqu?,ka kuskura ka zageni ubanka zanci wallahi la'ada waje" Ta furta da hargagi tana nunashi da yatsa sanda suke kusa da ficewa daga falon. Abinda ya sanya me babban suna miqewa yana jin nauyi da kuma zafin zaginnan. Ko meye zatayi me ya gamo da iyayensu?,me su sukayi mata idan su din masu laifi ne a gareta?. "Don Allah mama ki barmu muje muma,idan mun dawo zamuyi miki duk aikin da kikeso" "Kai.....wasa nakeyi dakai?,zaka tashi ka bani waje ko sai na zagi uwarka mara daraja da ubanka dake qarqashin qasa?" Kamar saukar mashi haka kalamanta suka soki zuciyarsa,har sai daya kasa jurewa ya waiwayo yana dubanta. "Don Allah mama ko meye,ko meye mukayi miki ki mana hukunci ba tare da zagin iyaye ba......" "Ubanka da uwarka,shegen yaro me tsaurin ido,kaci ubanka" Ta fada har tana zullo tare da watsa masa daquwa. Ta jima da tsanar dama wannan kamewar tasa,ta jima da tsanar yadda yake da dauke kai da rashin hayaniya akan komai da zatayi masa,duk yadda takai ga tama masa wajen bashi baqin kashi da baqar wahala don ya magantu dukka ya shanye sai a yau din. Cikin qasa da minti guda launukan idanunsa suka sauya,baice qala ba amma kunnuwansa suna suna iya jin zafafan muggan kalaman da take jifanshi dasu. Ya tako a nutse ya iso gaban saddiq dake durqushe a gabanta ya sanya hannu ya damqi hannunsa ya tasheshi tsaye,abun sai ya masa kamanceceniya da sanda saddiq din ke tsananin roqon mahaifiyarsu akan kada ta tafi ta barsu. Bai waiwayeta ba,bai kuma dakata ba ya durfafi qofar fita daga falon kanshi tsaye,ba tsoro ba shakka ba kuma shayi "Ina zakaje,bance ba zakuje makaranta ba?" Ta furta da qaqqarfan sauti. Bai dakata ba bai kuma waiwayo ba ko ya nuna yasan tanayi har ya fice daga falon. A yau ta rushe dukkan wani ragowar kara da dagin qafa da yakeyi mata. Baya wasa da kalmar UBA sam a rayuwarsa,IYAYEN MA guda biyu,abba da Abbey. https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ________________________ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 09 Ko Faruqee baisan da zuwansa makarantar ba sakamakon banbancin abinda kowannensu yake karanta,har sai sanda aka fito break. Har a sannan ranshi a jagule yake,bacin rai kowanne second yana sake motsa zuciyarsa. Faruqee ya sameshi daga bayan makarantar zaune qasan bishiya saman rairayin dake wajen,hannunsa riqe da busashen siririn reshen bishiyar yana tona qasa dashi,ya kafe qasar da idanu kamar me nazarin samar da wani abun amfani daga gareta. Ta gefansa ya zauna,yayi masa tambayar duniya akan ya akayi ya taho makarantar amma ya gaza cewa komai. Na Faruqee ba,tunda ya shiga class din baiyi manana da kowa ba,don bayajin koda ya bude bakinsa akwai wasu kalmomi da zasu iya fita daga cikinsa. Dole Faruqee ya haqura ya kuma tayashi zaman shurun,don dukkansu dama babu me 'yanci ko damar yin break,to inama kudin?,dukka dana transport din da komai ta hada ta kalmashe. Sai a hanyar komawa yaji komai daga bakin saddiq. Qwafa yaja yana girgiza kai "Duk yadda kake tunanin matar nan ta wuce nan,duk kuwa yadda zan fasalta maka,ta samu sassauci ne daga garemu shi yasa take abinda taga dama,ace mutum ya shiga shekara ta sha biyar,kana girma amma baka da 'yanci?" Shikam baima iya cewa komai ba har zuwa sanda qafafunsu suka maidasu gida. Sai da suka gilma ta gaban gidansu kafin su cimma gidan RIQOnsu a yanzu,idanunsa zube bisa fuskar gidan dake garqame da kwado. Take yaji wata matsananciyar kewar gidan da kewar Abbie da jadda suka saukar masa. Duk da suna rayuwa ne cikin matsakaicin matsayi na rayuwa,amma rayuwarsu rayuwa ce me 'yanci da kuma dadi. Duk da suna rayuwa da maama cikin wani baqon hali da murdaddiyar dabi'a.......hakan yafi musu sauqi a kan rayuwarsu ta yanzun cikin gidan RUQO. Ya janye idanunsa sanda ya dubu daidai wajen da mahaifinsa ya dogaro da qyar ya biyo bayan maaman yana cike da fatan zata dakata daga aiwatar da qudurinta nayin nesa da rayuwarsu,wani zafin akan na dazu ya sake yunqurowa ya mamaye zuciyarsa. Daga saman balcony din da zata sadaka da ainihin falon suka sameta a zaune ta hakimce. Faruqee ne a gaba,musaddiq yana biye dashi,sai me babban suna da ko qaunar hada idanu da ita bayayi. Zuciyarsa yadda take a zafafen nan tana ayyana masa abubuwa masu dama a kanta. "Idan ka kuskura ka qaraso na saina sanya an maka dukan tsiya......baka isa ka shigamin gida ba tunda kai din tantiri ne mara kunya.....nan gaba kadan shaye shaye zaka farayi da daba,kaga kenan ka samu hanyar da zaka hallakani a banza" Ta fada tana miqewa tsaye. Dukka su hudun sukayi carko carko suna dubanta da jin kuma wani sabon bala'in daya tunkarosu kuma bayan na dazu da safe. "Kai har ka isa na fadi magana ka sabamin bare ka maidamin?,don an zagi uwarka da ubanka,su su waye da ba za'a zagesu ba?,wato gaka kai me zuciya ko,to an zagesu din na kuma zagi banza da wofi". Da qarfi ya damqi hannun saddiq ya kuma soma ja da baya yana janye jikinsa daga wajen " Yauwa gwara daka fahimta,don wallahi kabar gidan nan kenan,tun yanzu kana tsayarmin ina ga nan gaba idan ka gama zama balagagge?". Da sassarfa Faruqee da har ya isa bakin qofar falon ya soma saukowa yana takowa zuwa garesa ganin suna nufar gate din fita daga gidan yana qwala masa kira da niyyar tsaidashi "Aisai ka bishi kaima don ubanku,na fiku iskanci qananun balagaggu" Ta furta tana komawa saman kujerar ta zauna "Bar nan gurin" Ta kwatsawa musaddiq daya mace a wajen saboda tsoro da mamaki tsawa,baiyi wata wata ba ya juya shima yabi bayan 'yan uwansa. Bai iya tsaidashi ba har sai da suka isa qofar gidansu dake garqame. Sai sukayi carko carko suna kallon kallon shi dashi. A yadda ya hangi kwantaccen fushi da bacin rai akan fuskar me babban suna sai ya rasa da wadanne kalmomi zai iya shawo kan me babban suna?,wacce kalma ce zatayi masa aiki?. "Kayi haquri kazo mu koma,tunda gidan abba ne ba nata ba bata isa ta hanaka zama ba,yau ko kasheni zatayi saidai ta kasheni" Wani irin kallo ya yiwa Faruqee,ga mamakinsa murmushi ya gani ya subuce masa. Da wani irin zafi ya waiwaya ya dauko dutsen dake yashe gefan malalen simintin dake gaban gidan nasu,har tsoro ya kama Faruqee yaja da gefe,sai yaga ya doshi qofar gidan,ya kama kwadon dake jiki ya fara bugeshi baji ba gani. Tsakiyar azahar ne,wannan ya sanya ba yawaitar jama'a a layin bare a samu me dakatar dashi. A yanayin da yakejin zuciyarsa da kansa a ciki,bayajin akwai ma wanda ya isa ya dakatar dashi din sai MUTUM DAYA TAK A DUNIYA.....ALHAJI HAMZA KIBIYA. Zare kwadon yayi ya watsar gefe,kansa tsaye kuma ya soma cusa kai cikin gidan ba tare daya damu da yana datti ko qurar data lullube qofar ba. Wannan shine mafarin komowarsa gidansu......tushensa......asalinsa da yaji yafi masa kwanciyar hankali sau dubu akwan kwanansa cikin babban bedroom din gidan alhj hamza dake dauke da wuta 24/7 da kayan alatu na rayuwa. Tun a asalin halittarsa shi jajirtacce ne tsayayye da bai yarda da faduwa ba......sanda komai ya dinga faruwa kuma daki daki,sai zuciyarsa ta qara qeqashewa ta kuma tsaya kyam......ya karantawa kansa da kansa cewar shine uwa kuma uban kansa da dan uwansa sadiq.......shine gatan kawunansu,ya fidda kowa daga cikin zuciya rayuwarsa dama hasashensa. Wannan ya sanya tun rana ta farko da suka dawo gidan bai kuma karbar koda ruwa daga gidan alhj hamza ba. Duk da yadda ran Faruqee ke baci da yadda yake wofantar da komai da ya kawo musu din kuwa koda ruwan sha ne. Da kansa ya tsaya,sadiq na debo ruwa shi kuma yana wanke komai da yayi saura na gidan wanda zasu iya amfani dashi. Cikin kwanaki uku kacal ya fara Qwadago. Duk wani aiki da zai samar masa kudi......komai wuyarsa kuwa muddin halas ne yana karba yayishi hannu bibbiyu. Da wannan din ya dogara.....da dan abinda yake samu din ya dauke musu abinci dama abin sha......idan faraga ta samu harda kudin transport na makaranta koda na zuwa kadai ne banda na dawowa. Sauyawar yanayi da kuma tsarin rayuwarsa ya sake canxashi gaba daya. Yana tsananin son karatu kowanne iri ne,na addini dana boko gaba daya *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾 *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* ________________________________ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 10 Baya wasa da islamiyya,amma wahala da nauyin kansa dana saddiq ya sanya ya sallamawa zuwa islamiyya. Duk da haka bai sare ba,ya lalubi makarantar magariba ta manya ya soma zuwa don karantar litattafan addini,duk kuwa da nisan zangon tafiya dake a tsakaninsu. Su kansu ba 'yantattun 'ya'ya bane cikin gidan mahaifinsu......amma duk da wannan ya gaza barin me babban suna yakuma qyaleshi kamar yadda ya fuskanci yana da muradin hakan. Duk da basu da 'yanci ko fada aji a gidan......amma hakan baya hanashi dauko abinci daga cikin nasa kwanon data qayyade musu cikin gidan ya kawo don suyi tarayya suci tare,amma koda wasa me babban sunan bai taba dangwala yatsarshi a ciki ba. Abun yana ma Faruqee zafi da ciwo matuqa,har daga qarshe hakan ya sanya suka samu sabani "Don mama tayi maka laifi ai ba abincinta bane,abincin abba ne wanda har yanzu a nasa zaton kuna cikin gidansa ne cikin aminci bisa kulawarta,iyakarta da abincin nan tazo ta diba itama taci,don ko dafawa ba ita ke dafawa,larai ce......kuma ita ke qaramin yawan abincin a boye ba tare da saninta ba,to indai bawai nima gaba da fushi kakeyi dani ba banga abinda zai hanaka ci ba.....idanma kai ba zakaci ba....kada ka sake hana saddiqu yaci,kai ka zauna haka can ta matse maka". Busashen murmushi ya saki yana jin yadda cikinsa ke qugin yunwa,don yau ba wani abun kirki ya samo a aikin ba,wannan ya sanya basu wani qoshi ba wunin ranar sur.....ga kuma tafiya makaranta a gabansu gobe juma'a. Yadda Faruqee yayi fushi ya kuma dauki zafi da abun ya sanya yake barin saddiq din suna hadaka dashi. Shikam yasan bazai taba iya sanya abincin cikin bakinsa ba. A duk sanda yayi yuqurin hakan sai maganganunta su dawo musu kar kar cikin qwaqwalwa "Tunda uwarka ta zube ku ta tafi ta barku,banga uban da zai iya zama daku ba......uwarku ma ta barku ballanta wani?" Aduk lokacin da zai tuna da irin wannan maganar a take yakanji komai ya fita a kansa ne,tsananin baqinciki ya mamaye walwalarsa,wata irin wuta me zafi na taso daga qasan zuciyarsa da ruhinsa dangane da imaninsa. Ta wani fuskar da mama da sauran 'yan unguwa dake jifansu da muggan kalamai sai yaji sam baya jin zafinsu ko kadan,da uwa da uba da kuma dangi ake ado,su kuma basu da ko guda daya!. Ya tabbata lallai su din cikakkun marasa gata da galihu ne,kuma kowanne suna aka kirayesu dashi sun cancanta. Yayi imani inda har jadda tana raye.....koda sunfi kowa talauci da matsin rayuwa......to babu shakka zasu zamo na sahun gaba gaba wajen zama yaran da sukafi kowa samun gata na kulawa da soyayyar kaka. Saidai Allah baya barin wani don wani yaji dadi,ya tabbatar haka ubangiji ya tsara musu tasu DUNIYAr,haka kuma yaso ganinsu a cikinta. A wannna tafiyar abba yayi nisan kiwon da ya jima baiyi irinsa ba. Yana rayuwa bisa yaqinin lallai gidansa da marayun Allahn daya dauka riqo suna lafiya,tunda duk sanda zaya kirata hakan take gaya masa,sannan lokaci bayan lokaci tana hadashi da musaddiq,shima kuma "Lafiya qalau muke abba" Shine amsar da yake bashi bisa jagorancin mummunan gargadi da idanuwa da maman take aike masa duk sanda suke wayar. Faruqee ne bata taba yarda ta bawa wayar ba,sai a wani yammaci da abban yace ya jiyo muryarsa ta hadasu. "Lafiya amma ba qalau ba amma.....muna buqatar ka dawo a kusa abba" Bata iya barinsa ba ta fusge wayar daga hannunsa cikin hanzari ganin yana niyyar sauka daga layi. Maganar ta tsayewa abban a rai,ta kuma sanyashi yaji dukkan hankalinsa yana tarkatowa yana yowa gida. Duk kuwa da akwai sauran abu daya tsara zaiyi a can din,amman sai yaji komai ya fita a kansa tahowarsa gida ce abu na farko da yake kwana yana tashi dashi. *******Kusan dukkansu jan qafafunsu sukeyi,zafin rana yunwa ga gajiya dake tattare dasu. Akwai nisan tazara me dan dama tsakaninsu da makarantar wanda suke shanyeta a qasa daga tafiya zuwa dawowa. Babu ranar hutu a garesu idan ba asabar ko lahadi ba. Ga me babban suna kuwa,baya gane asabar ko lahadin cikin rayuwarsa da DUNIYARSA. Rayuwar tasa gaba daya a birkice take,bashi da wata dogon hutu daya wuce makaranta zuwa neman kudin abinci. Yayi wani irin duhu,dukkan hasken fatar nan da suka gado babu shi,ya rame daga ainihin halittarsa zuwa wata halitta ta daban. Tun daga nesa ya soma hangen wani abu da yayi matuqar girgiza hankali da kuma tunaninsa,ya sanya dukkan wani tunani nashi ya fara sauka daga kan layi,ya kuma daina gane me Faruqee daketa faman bashi labari yake fadi. Wata qurace take tashi daga wani sashe na gidansu gami da qarar zubewar bulalluka. Gefe guda akwai tsaiwar tsirarun mutane da kuma yara wadanda basa raina abun kallo,hakanan basa bari abun kallon ya wucesu kamar qanqantarsa. Zame hannunsa yayi daga jikin na Faruqee,a gaggauce da kuma hanzari ya soma tattaki har zuwa inda aikin ke gudana. "Gidanmu ne fa.....me yayi ake rusheshi?" Ya furta bayan ya tabbata ya tsaya gaban mutanen dake gabatar da aikin futu futu cikin qasa da qura. Dukkansu suka waiwayo suna dubanshi,kafin daga bisani wani dan tsamurmurin mutum dake sanye da milk riga da wando na shadda,da kuma babbar riga ta koriyar shadda gami da baqaf hula daya karkatata gefe ya qaraso gabansa yana dubansa. Bakinsa cike da gashin baki,kai kace daya daga cikin qabilun da suka shude ne shekaru aru aru. "Yaro me kake cewa?" Ya fadi yana saba babbar rigar da a zahiri an tafka babbar asara wajen ware shaddar aka masa rigar da ita gaba daya,don kuwa yadin ya masa yawa,alamu ma suna nuna kamar rinjayarsa takeyi "Gidanmu ne nace,me yasa kuke rushe mana gida?" Ya sake jefa tambayar ga mutumin yana tsareshi da ido da zummar jin ba'asin maganar. Qaramar dariya yadan saki yana sosa gashin bakinsa da alama qaiqayi yake masa. "Yaro man kaza......kai!bakasan tsohuwarka ko ince uwarka ta karbi rabin kudin gidan daga hannun matata ba sanda zata bar garin?". Fuska da idanu gaba daya me babban suna ya yamutse yana duban mutumin cike da zallar mamakin da kwanyarsa ta gaza dauka. " Ko da yake ma.ba fahimta ai zakayi ba,wannan zancan na babanka ne inda yana raye,ba abinda zaka gne yaro" Yana kaiwa nan sai ya juya yana dubañ mgainan "Kuyi ku raba ku zagaye mana haqqinmu" Da hanzari yasha gaban mutumin jin kalaman da yake sake maimaitawa "Kada su sake taba mana gida,don nan vidan ba gudan mamata bane da zata saidashi,gidan mahaidinmu ne daya ginashi da guminsa,ta nemeta ta biyata kudinta amma mu ba ruwanmu" Tsaiwa yayi yana qanqance idanu hadi da duban me babban suna "Kai wannan yaron da alama zakayi tsaurin idanu,da alama dai abinda ake fadi a kanka gaskiya ne......to ai ko kai yanzu ba zakace ga inda uwar data haifeka take ba,tunda ta bazama yawon duniya ta watsar daku.....". Kalmar ta sokeshi qwarai kamar kowanne lokaci. Duk a iya adadin fadar da akeyi bai taba yunqurin kare musu jifan da ake musu da kalmar ba,amma a yau din sai yaji koda sau daya yana da sha'awar huce musu wannan takaicin shi da saddiq.......yana da marmarin maida martani koda sau daya ne tak......amma baya sha'awar bata kariya ko wanketa daga muggan kalaman mutane a kanta,don bashi da abun cewa a kanta,kwata kwata dukkan wata soyayya qauna ko tausayi na fil'azal a tsakaninsu yanxun baya jin akwai burbushinsa,abinda ya sani kawai ya kare kansa ya kare saddiq dinsa "Ba abunda ya shafemu da inda taje ko inda take.......kaman yadda ba ruwanmu da karbar kudinku da tayi don nan gidan mallakin mahaifinmu ne mallakinmu......abinda muka sani kawai shine mu din halastattun 'ya'yane da aurar ya samar......" Daya daga cikin ma'aikatan wanda kuma gidan su yake ta qarshen layinsu wanda ke tsaye gaban tsani ne ya bushe da dariya "Dame kwado yafi gaya ku da shegun?,dame kuka fisu?" Yana kaiwa nan ya dauki qatuwar gudumar da suke dukan saman ginin da ita ya soma taka matattakalar tsanin yana hayewa da zummar ci gaba da aikinsa na ragargazar ginin da mahaifinsu ya kwashe lokaci yana zuba kudadensa wajen qawata musu shi. Ya sadaukar da kudi da qarfinsa wajen samar dashi,ya sanya burinsa akai na ganin sun rayu a cikinsa cikin aminci da kwanciyar hankali. Kwata kwata kasa jurewa yaji yayi da mummunar kalmar da yaji ya jefesu da ita. Sanda ya daga gudumar zai doka......daidai lokacin ba tare daya ankara ba ya sanya hannu ya fusgoshi sai gashi qasa warwas!. Abinda ya sanya dukka jama'ar dake tsaitsaye a gefe tun dazun basuyi magana ba yunqurowa,masu salati sunayi masu yunqurin tayar da babba magini sunayi. Wani irin mamakin sauyar rayuwa da mutanen dake rayuwa a cikinta ya kamashi. Da idanu yake binsu *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾 *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* *D U N I Y A TA* *_H U G U M A_* PAGE 11 _____________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* ___________________________ Daga sanda ya jawoshi ya maidoshi qasa......daga sannan yaga iya yawan adadin mutanen dame wajen wanda sam baiyi zaton sunkai haka ba,bai dauka suna da yawa haka ba.....amma duk da wannan yawan nasu babu wanda yayi yunqurin yin wani anu guda daya sanoda ceton rayuwarsu da cetin ginin gidan dashi kadai suma!mallaka a rayuwarsu wanda zasu nuna suce ya fito daga jini da gumin mahaifinsu?. Me yasa al'umma ta sauya?,ya dinga duban fuskokin masu luguiguita zancan da kambama abinda ya aikata din,dukkansu suna tsaye sanda ake himmar rugurguza mafaka guda daya tasu da tayi saurs,ba wanda ya tallafa,ba wanda ya dakatar. Kusan dukkansu fuskokinsu bayyanannu ne a idanunsa,fuskokin daya saba gani sunzo neman taimako wajen mahaifinsu,wanda bai taba gazawa ba da taimaka musu da abinda Allah ya hore masa,amma yau tsantsar butulci irin na dan adam sune suka juye suna masu tsaiwa suna kallon wasy na shirin zaluntarsu. A sanda yayi nisa da wannan tunanin a lokacin babba yayi amfani da wannan dama yakai masa duka,dukan da yazo masa a bazata banda jin hucin wucewarsa da yayi da hucin hannun Faruqee daya tare masa dukan. Yaja baya yana maida hankalinsa jikinsa,sai ya taka dutse ya kuma yi taga taga ya fadi da baya,wannan ya sanya babba ya sake yunquro masa da nufin turmesheshi cikin baraguzan ginin gidan da suka fara saukewa,sai Faruqee shima ya taso ya rufa masa baya da zummar baiwa me babban suna din dauki. Cikin zafin nama fushi da kuma taurin kai gami da kafiya da taurin zuciya Shima ya yunqura ya miqe yana jiran qarasowar babba. Idanunsa a lullube suke da bacin rai,baya hangen nisan tazarar shekaru da kuma girman jiki dake tsakaninsa dashi. "Kai.....kai......dakata.....meye hakan?" Muryar nan me cike da kamala tausayi da dattako ta ratso gurin. Kowa ya tsaya ya waiwaya yana duban saukowarsa daga motar zuwa takowarsa cikin fusassun duwatsun gurin. Alhaji hamza kibiya ne idanunsa na kai kawo tsakanin Faruqee me babban suna da kuma ginin gidan nasu. Mutum ne me cikar kamala da dattako,wanda ya riqe mutuncinsa da kyau. Yana daya daga cikin dattijan unguwa dake bada Umarni ko shawara abi,musamman da yake yana da abun hannunsa wato kudi abokan tafiya. Kunya tadan kama manyan dake wajen da basu hana ba sai tsaiwa kallo da sukayi,wanda sun tabbatar idanuwansa sun gansu gaba daya. Bai tsaya sauraren barka da zuwan da suke masa ba,sai qoqarin qarasawa gabansu kawai da yakeyi bayan yace da saddiq da musaddiq su tsaya daga baya,wanda dukansu suka tsorata tun farkon rigimar,to amma basu dame kawo musu dauki bare suyi hanzarin garzayawa su kirashi ko zai cecesu. Ta gefan babba dake tsaye yana kade jikinsa cikin jin nauyi yana kuma huci qasa qasa ya wuce,ya qarasa inda me babban suna ke zaune warwas ya miqa masa hannu ya tasheshi tsaye. Yana tsaye a gabansa ya bashi handkerchief yana karkade jikinsa. Idanun alhaji hamza a tsaye sosai jikin uniform din nasa da suka fara alamta masa wani abu. "Me yake faruwa a nan ne?" Ya watsa tambayar ga tsamurmurin mutumin daya lura kusan shine baquwar fuska a wajen. Baiyi qasa a gwiwa ba ya kwararowa alhaji hamza bayani kaman yadda ya yiwa me babban suna,bayanin da maimaicinsu yake sanyashi jin kamar ya rufe idanunsa ya budesu ya ganshi ba'a wajen ba,kamar ya rufe idanu ya kuma budesu ya tsinci kansa haihuwar wata uwar daban ba maama ba......kaman ya tsugunna qasa ta hadiyeshi ya huta. Sai daya kammala bayaninsa gaba daya sannan alhaji hamza ya gyada kai "Nine a matsayin wakilin yaran nan,kuma bana nan,yanzu haka shigowata garin kenan,inaso a dakatar da aikin nan,ka kuma sameni gobe mu zauna muyi magana akan batun da kazo dashi,ina da buqatar qwaqwarar shaida da hujja ka taho da ita,idan ya tabbata da gaskiyarka,zaku fadi iya kudin data karba zan biya na fansarwa yaran gidan da suka gada,idan kuma aka rasa daya daga ciki kasan qarshen case din basai na qarasa ba" Abba yayi magana yana janye hannun me babban suna sunayin gaba. Ko daya bai amsa maganar mutanen ba,wanda ba abinda ransa keyi game dasu sai baci da soyuwa. Rayuwa ta lalace,DUNIYA ta zama wani abu na daban?,babu me kawar da barna?,babu me rungumar dan wani?,kowa nasa ya sani. A baya suka bishi yana riqe da hannun me babban suna ba tare da yace komai ba. Motarsa ya qaraso da ita bakin gate din gidan nasa sannan ya kulleta,ya soma takawa zuwa ciki yana kiran Faruqee. Cak ya tsaya daga gate din gidan shida saddiq suna kallon abba Faruqee da musaddiq suna wucewa zuwa ciki. "Me babban suna" Abba ya ambata sanda ya sanya qafarsa ta farko cikin gidan "Abba baya shigowa gidan mu yanzu" Musaddiq ya fadiwa babban qasa qasa yana tsoron kada mama dake can ciki ta jiyoshi. A mamakance ya kalli musaddiq sannan ya waiwaya ya kalli me babban suna dake tsaye daga baya kansa a qasa. Yana jin nauyin abba qwarai,yana kuma jin nauyin saba umarninsa,amma bayajin qafafunsa zasu sake taka wannan gidan har abada kamar yadda yaci alwashi. "Faruqee meye haka?" Abba ya tambayi farouq cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa "Abba ya koma gidan su,mama ta koreshi". Wani abu yaji ya sauka tsakiyar kansa har kaman qafafunsa suna neman yin rawa. " Ya salam ya Allah" Ya fada a fili,tun yaushe ta aikatawa.marayun Allah haka?,ashe shi yasa hankalinsa yayi qololuwar tashi sanda ake taba ginin gidan nasu tunda yana kallonsa a mafaka guda daya duk duniya data rage musu?,ashe shi yasa yaji ya kasa samun nutsuwa kwata kwata a kwanakin?. "Muhammadu" Abba yakirayeshi kai tsaye da cikakken sunansa da ba kasafai yake kiransa dashi ba. Kansa ya daga,suka hada idanu da abban da idanunsa da suka jajur "Zoka wuce muje ciki" Ya sake bashi umarni nakai tsaye. Umarninsa dai dai yake da umarnin mahaifinsa da yayi silar kawoshi duniya,tabbas idan zaiyi musu da gardama wa mahaifinsa to la shakka zai yi wannan wa abban. Amma fa tabbas inda ya san abban zai ankara d wuri akan baya biye dashi,allai da yayi nisa da gurin tunda wuri,tun gabanin yayi masa umarnin shiga gidan irin haka. A gaba ya jeresu yana biye da bayansu har zuwa sanda suka isa ainihin falon gidan. Daidai sanda take fitowa daga kitchen hannun ta dauke da jug data tanadarwa abban lemo,haka kuma tasha ado da lace bakinta ya cika taf da lipstick ja shar dashi. Har cikin zuciyarta takejin bala'i da masifa suna tsarga mata. Yau kam dukkan juriyarta da karar da take masa ta qare muddin dai yace dawowa yayi da yaran nan masu zubin mayu. Iya zamanta da yaranshi ma ya isheta jarrabawar rayuwa bare ya qaro mata yaran da batasan matsayinsu a gidan ba,suba agololi ba,su kuma ba yaran masu gida ba. A gaggauce ta isa dining ta ajjiye jug din idanunta bisa fuskarsu "Ku kuma daga ina?,daga dawowarsa shine kuka biyoshi saboda tsabar maita?" Ta furta tana zazzare idanu hannuwanta riqe da qugunta. "Ya isa da Allah asama'u" Abba ya fada da hanzari yana daga mata hannu,don wasu maganganun bai dace ace an yisu gaban yaran ba,koda saddiq da musaddiq basu da shekaru sosai,ai Faruqee da me babban suna zuwa yanzun sun fara kammala hankalinsu tunda sun shiga shekara ta goma sha biyar. "Ku wuce dakinku ku canza uniform" "Ba inda zasu a gidannan dai wallahi,basu da daki kuma basu da matsugunni tunda dai bakai ka haifesu ba.....danginsu ma sai watsar dasu wai ballantana kai abba?" Ta fada tana sake matsowa hanyar da zasu wuce zuwa dakin "Abba babu kayansu ko daya a gidan nan fa.....baka dade da tafiya ba ta koresu,tunda.ka tafi suma suka koma kwana a gidansu" Faruqee ya fada gaba gadi,yana jin cewa shima yau yakai bango,komai ta fanjama fanjam. "To baqin munafuki,na koresu din,kuma wallahi wallahi koni ko su a gidan nan" Maganar faruqee ta dagawa abba hankali. A cikin gidan da bashi da maraba da kango suke kwana?,gidan dake cike da memories na iyayensu da suka gushe?,ta yaya suke iya bacci su biyu rakkin wanda har zuwa yanzu ba wanda yakai shekara sha bakwai ma bare sha takwas a tsakaninsu?. "Abba abinci ma aiki me babban suna yakeyi a tasha kullum yana kawo musi gari ko dan wanke" Musaddiq ya fada a dan tsorace yana satar kallom fuskar mama bayan ya riqe hannun mahaifinsa da kyau yana boyewa a jikinsa. Sosai maganar ta dakeshi,zaka fahimci hakan ta yadda kalolin idanunshi suka sauya duk kuwa da tarin haqurinsa. Farat daya yaji asama'u ta fita a kanshi gaba daya. Duk matar da zata iya yiwa maraya haka tabbas ya sani nashi yaran ba zasu tsira ba wadanda suke da uwa da uba,Allah ne kawai mafi sanin haqiqanin abinda su kansu su musaddiq din suke kwankwada daga hannunta idan baya nan. Bai taba barin garin ya tafi gurin neman kudinsa hankalinsa a kwance ba tun daga ranar daya saki mariya. Tun daga ranar daya rabu da mariya bai sake samun nutsuwa cikin gidansa ko aminci akan 'ya'yansa ba. "Asama'u?,bakya tsoron fushin Allah kike cutar da marayin Allah?" "Ni babu abinda Allah zaiyimin,don su din ba dole na bane,wadanda ma suka zame musu dole sun yakicesu sun zubda bare ni da aka tsinceni da haqorana talatin da uku.....don haka wallahi bazanyi riqonsu ba,yaranka dai ba yadda na iya dasu saboda ubansu nake aure" *_TAFIYA DA GWANI ME DADI_* *ZAFAFA BIYAR*❤‍🔥🥰 *zafafa biyar*❤‍🔥🥰 *ZAFAFA BIYAR*❤‍🔥🥰 *A DADE ANAYI SAI GASKIYA* _FITATTUN GWARAZAN MARUBUTAN LITATTAFAN NAN NE MASU DAUKE DA SALON LABARAI IRIN DABAN DABAN BISA TSARIN TAFIYA DAYA SUKA SAKE YUNQUROWA☺️😇_ _WADANDA SUKA SABA GABATAR MUKU DA QUNSHIN ZAFAFAN LITATTAFAI DA LABARAI MASU TAFIYA DA HANKALI DA TUNANI_ *_IRINSU_* BURI DAYA INAYA AMEENATU DALAAL BAQON MUNAFUKI KAIMIN HALACCI TSUTSAR NAMA WUTSIYAR RAQUMI BAQAR INUWA SIRADIN RAYUWAR BILKISU TABARMAR QASHI KUFAN WUTA *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ___________________________ PAGE 12 "Qarya kike,wallahi tallahi yarana dinma ba riqonsu kikeyi ba,koda basu taba gaya min ba amma na tabbatar ba irin riqon uwa da 'ya'yanta kike musu ba.....irin riqon da mukayi alqawarin zakiyi musu" Qaramar shewa tadan saki tana tafa hannuwanta hadi da qare masa kallo tsaf ido cikin ido "Dama waye yace maka uwar wani zata iya riqon dan wani tamkar nata?,au ashe bakaji abinda bahaushe ya fadi ba kenan,riqon uwar wani da dan wani ai sai Allah" Mamakinta ne ya qarasa kasheshi,ransa yakai qololuwar bacin da har ya mance da yara ma a wajen "Haka kika ce?,to bari kiji na gaya miki......muddin ba zaki riqe wadannan marayun ba saidai kisan inda dare yayi miki" Idanu ta fidda tana kallonsa cikin maqurar mamaki,wato ya fifita matsayin yaran a kanta kenan?,ta yaya zata ma zauna ta karbi wannan fifikon?,ya za'ayi ma tayi sake har yaga warginta haka?,a gaban yaran ya kafa mata irin wanna sharadin?,ai duk yadda taso ga son zama dashi ba zata karba irin wannan mulkin qarfa qarfan ba. Hannayenta ta sake hadawa ta tafa ta kuma riqe qugunta da kyau tana dubansa "Wallahi kaji na rantse bazan riqe su ba,har nakanma na gaji ai bamuyi abinda zanzo nayi kenan cikin gidan nan ba" "Tunda kuwa kikace haka saidai ki qara gaba" Gabanta yadan fadi,amma batajin zata bari ya gano lagonta "Hakan shi yafi sauqi,amma bazanje nayita zama da dakon aurenka ba,ka gayan meye matsayin tafiyar tawa idan na yita?" Ta kuma tambaya tana watsa hannuwa "Na sakeki saki biyu" "Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" Me baban suna ya furta yana saka hannuwansa dukka biyu ya toshe kunnuwansa,sannan ya koma ya sulale yana zama tsakanin kujerun falon. "Tafi nono fari,sai me?,dadin abun ai ba kai kadai bane namiji" Ta qarasa fada tana ture kujerun dining din ta sauka a gaggauce zuwa dakinta gabanta yana wani irin bugawa da sauri da sauri. Daga su har abban ba wanda ya iya cewa komai,falon ya dauki shuru kawai sai motsinta daga can uwar daki tana hada kaya gami da sakin maganganu wanda basa iya jin ainihin me take fadi. Mintuna goma kacal ta fito janye da akwatunta da qaramin mayafi yafe a kafadarta. Daga inda yake ya daga rinannun idanunsa yana kallonta. Abba ya saketa ne saboda su,me yasa abban zai saketa saboda dalilinsu?. Fitowarta sai tayi masa kama da fitowar mahaifiyarsu sanda take shirin barin gidan mahaifinsu. Me yasa ake tafiya ne ana barinsu?,farinjini ne basu dashi ko kuwa?,ko wani maqalalle kuma boyayyen abune dasu?,me yasa iyaye mata basa tausayinsu saidai maza?. Baisan yaushe ya yanke wannan hukuncin ba,shidai ya tsinci kansa a gaban mama ne,cikin matuqar tashin hankali da karyar da muryar yake fadin "Don Allah mama kiyi haquri,kada ki tafi saboda mu......" "Na rantse da Allah zan zabga maka mari idan baka bani hanya ba,munafukan banza da wofi wadanda babu alkhairi sam a jikinsu sai masifa da balai nau'i nau'i,ai daya sakenin sai ku ya aureku,gaku nan gashi,kara da kiyashi daukan mara sani" Sai ta wuce abinta ta barshi da zafafan maganganun daya gaza mancewa dasu. "Dawo ka zaun me babban suna,waye yace maka ka bata haquri?,waye yace maka zan iya zama da ita bayan bata sonku?,ba zata iya zama daku ba?,ba zata iya haquri daku ba?......in sha Allah na muku alqawarin dawowa da mamanku nan da sati guda kacal" Maganar data Haifar da wani irin farinciki mara misali a zuciyar faruqee musaddiq harma da sadeeq din da baima mamansu musaddiq din farin sani ba. Yayin da me babban suna yake binsu kawai da idanuwa,don kunnuwansa da zuciyarsa harma da qwaqwalwarsa sunyi nisa qwarai da abinda ke wakana a falon. Jarin maganganun mutane masu tsananin dafi daya soma girma da jinsu yaketa aunawa. Kullum kwanan duniya wayewar gari zuwa faduwar rana sai yaci karo da wata mummunar kalma da zata zamewa zuciyarsa tabo wadda ta shafesu da mutuncinsu,duk kuma MAAMA itace sila,dama uwa tana iya zama silar bacin suna da rayuwar 'ya'yanta?. Tambayar da amsarta ta kasa samuwa a gareshi kenan,musamman lokacin da MARIYA mahaifiya ga faruqee da musaddiq ta dawo ainihin dakin aurenta da zummar riqe yaranta harma da marayun Allah MUHAMMAD DA ABUBAKAR SADDIQ *************** Faffadan tsakar gida ne ma'abocin yalwa da kuma tarin dakuna da zasu nuna maka yawan adadin mazauna gidan dake cikinsa. Tun daga qofar gida,zauruka guda biyu masu girma har zuwa farfajiyar gidan da wani filin tsakar gida da gidan ya mallaka zakasan cewa asalin ginin gidan anyi gine na masu wadata a wani qarni can baya daya shude. Duk kuwa canzawar siffar ginin zuwa zubin ginin daya dauki shekaru,amma yanayin yadda akayi zuba ginin da kyakkyawan tubali hakan ya hanashi muguwar lalacewa ko muzanta daga suffar kyau zuwa ta tsufa. Dakuna guda hudu manya manya gidan ya mallaka lailaye da siminti da tsakar gidan ya wadatu dashi da fulasta wadda ke nuna yau ta jima da samuwa a jikin ginin gidan. Kafin idanunka yakai ga duqurqusar matakalar bene dake qarshen qofar daki na hudu a jerin dakunan gidan. Rijiya ce da aka dan dagata kuma aka rufeta da murfi na langa langa. Idan ka sake kai dubanka kuma can zuwa sashen hannun hagu na gidan,bayan ka wuce bishiyar mangwaro data samu muhalli na dindin da Tsakiyar gidan,kai tsaye kana iya hangen qofar da tafi kama data makewaye,da kuma qofar babban kitchen na gidan daya hada kowa da kowa. Akwai gurabe daga jikin bangon gidan da zai sanyaka ka fahimci a baya akwai wasu shuke shuke da sukayi zamani daga bangwayen gidan,saidai yanzun babu ko wanne tsiro idan ka cire bishiyar dake a Tsakiyar wadda gushewarta ita din ba abu bane me sauqi. A tsaftace gidan yake ba laifi,wanda kusan gado ne da kuma asali da tsafta daya samo cikin gidan koda kuwa bayan gushewar me gidan da rasuwar mace daya cikin matan aure uku da ma gidan ya mallaka a lokacin rayuwarsa. Safiya ce sosai,kusan qarfe bakwai da rabi na safe agogo ya nuna a daidai lokacin. Kowacce qofa ta gidan a sakaye take,sai wata qofa guda daya qyaure ta ya banbanta da sauran qyamaren gidan kafataninsu. Ba zaka gama fahimtar yadda banbancin yake bai tsaya daga qyauren kawai ba.....aah,har sai ka samu nasarar kutsa kanka cikin ainihin falon dake hade da uwar daki kaman kowanne daki na gidan. Kyawawan labulaye ne da aka yiwa dakin qawanya dasu ruwan toka wadanda sukayi daidai da sofas guda biyu dukkansu 3sitter da aka gewaye falon dasu hakanan suka dace da lallausan daddumar da aka shimfida a tsakaninsu qirar qasar turkiya. Akwai lausasan pillow guda hudu manya dake zube a qasa dukkaninsu kala daya da labule zuwa kujerun. Daga bangon dakin ta fuskar hagu kuwa,bango ne da yasha wallpaper me kyau aka kuma yiwa TV plasma me matsakaicin girma da reciever dinta mazauni na daban. Gaba kadan dasu 'yar madaidaiciyar AC ce ta tsaye wadda ke amfani da hasken rana da aka yiwa kafatanin dakin wayarin dinsa. Wannan ya sanya koda babu wuta ko ina cikin gidan,koda babu wuta ko ina a unguwar wannan dakin baya rabo da ita. Akwai freezer madaidaiciya itama data dace da tsarin dakin,sai manyan frames masu daukan hankali biyu masu sunayen Allah da ayoyin tsari,biyu kuma masu dauke da zanen nature me kyau. Sassanyan qamshin turaren icce dake zama a daki ya kama labulaye da kujeru da kyau falon yake fiddawa ya zarce kuma har uwar dakin,wanda ya cakuda da qamshin turaren daya zamewa mazauniyar dakin lazim amfani dasu. Labulen bedroom din aka daga,sannan kuma a hankali ta bayyana hannunta riqe da hijabin yarinyar dake tsaye cikin uniform. Matashiya ce wadda duka duka a qiyasce shekarunta ba zasu haura ashirin da biyu ke takowa a kasalance. *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾 *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* __________________________ *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 13 ___________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* ________________________ Sanye take cikin lallausar doguwar rigar bacci me kauri me gajeran hannu off white wanda ta tsaya daidai idon sawunta. Zaka iya kiranta doguwa saidai ba cancan ba,irin tsahon da yayi daidai da tsahon da za'a iya kiran diya mace doguwa,wanda siririn jikinta ya sake taimakawa wajen bayyanar tsahonta,muddin kuma ta samu damar mujewar jiki ko ta dan qara qiba to tsaf tsahon zai shanye da ba lallai a iya ganinsa ba. Tana da wani irin launin fata,fari me cakude da sirki sirkin ja,fara ce tas irin hasken fatar da kana kalla zakasan ba zallar hausa fulani bace,lallai ita din ruwa biyu ne halittarta ya hada nasaba da wani yaren(half cast). Ma'abociyar yalwataccen gashi me santsi da tsahon da kana iya hangensa ta cikin hular bacci dake kanta,a cukurkude kuma a daure cikin siririn band. Yanayin zubin idanunta shike fusgar hankalin maza da dama,bama maza kawai ba,harda mata 'yanuwanta suke kallonta a matsayin me tsananin kyau,duk kuwa da cewa ita din kanta ta sani,ba wata me mugun kyau bace na azo a gani,amma batasan meye yake janye hankalin mutane haka a kanta ba?. Tun tana mitsitsiyarta wannan abun yake tare da ita,FARINJINI ....wanda a sanda take da gatan uwa mahaifiyarta ke yawaita tofeta da addu'a ko yaya ne idan zasu fita. Mata ukune cikin falon,matashiya ta biyu wadda shekarunta zasu iya kaiwa sha shida na zaune dirshan saman lallausan carfet din nasu daya wadatu da tsafta,hannunta riqe da cup na tea,daga gefanta kuma bowl ne dake cike da chips. Sanye take da uniform irin na sauran 'yan uwanta dake alamta maka ta kammala nata shirin zaman tsimayinsu take bayaga breakfast data kasa kammalawa har yanzu. Yanayin yadda take cin abincin kawai zai gaya maka bawai dadin abincin takeji ba,idanma ba haka bane to lallai akwai abinda yake damunta. Ta biyun na gefan kujera tana qoqarin saka fara qal din sucks dinta. A qiyasce nata shekarun na haihuwa zai wahala ya wuce sha uku. Sannan qaramar data isa gareta tana gyara hijabin hannunta tana qoqarin sanya mata fuskarta shimfide da wani sassanyan murmushi nata shekarun tsakanin tara zuwa goma suke. Idanunta akanta da wani irin kallo na tausayi da rahama,zuciyarta na sake narkewa cikin tausayinsu gami da jin qwarin gwiwar basu kariya da samar musu da komai na buqatar rayuwa duk rintsi,komai wuya komai dadi. Wanzuwarsu a yanayi na farinciki yafi komai dad'ad'a mata rai da sanyata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk kuwa da irin birkitacciyar rayuwar da take fuskanta,wadda bata da dadi sam sam ballantana ban qaye. "A'ah.......kaga haneefata anyi kyau" Ta fadi da sassanyan muryarta me wani irin amo me dadi da daukan hankali idanunta saman fuskar yarinyar data kira da haneefa......yarinyar da ake cewa duk cikin qannenta ba wanda ke kama da ita irinta,duk da ansha cewa haneefan ta fita kyau,hasken fata kawai zata darata dashi. Dariya haneefan ta saki ta daga hannunta zuwa ga 'yar uwartata alamun su tafa,sai ta daga nata dogayen yatsun ta bata suka tafa din. Batasan wanne irin son karatu Allah ya dorawa qannen nata ba,wadda karatun bai fiya damunta ba huda ce,saidai a sannu da tayi tsaiwar daka a kanta yanzun abun ya shiga jikinta itama. Hudan ma bawai karatun bane bataso,a'ah,kawai hankalinta yafi karkata zuwa ga wasu bangarori. Kaman koyon abubuwa na qirqire(creatives),irinsu zane zane,dinki,decorations da sauransu. Bata jin akwai wanda zata matsawa kan abinda yakeso yayi muddin bai kaucewa hanya ba.....to amma kafin sannan tana da buqatar suyi karatu.......tana da buqatar su karantu da kyau ta yadda koda bayan ranta sun zarcewa raini da wulaqanci......tana da buqatar suyi karatun da duniya gaba daya zata tabbatar sun gagari rainin me raini ta fannin ilimi.....tanaso suyi irin nau'in karatun da hattana da maqiyi babu yadda zaiyi zai sallama cewa eh lallai......jinin hindu sun zama wasu taurari na daban a cikin familynsu gidansu dama unguwarsu gaba daya......zata nunawa wadanda suke ganin ba zasu iya ba.....ba zasu kai ba......zasu tozarta cewa......zasu iya iya.....za kuma sukai labarin da su basu kai ba. A nutse ta waiwaya ta kalleta. Tadan zuba mata idanu na second tana nazarinta. Tun tuntuni ta fahimci akwai kwantacciyar damuwa a qasan ranta,kasancewarta mutum me wani irin kakkaifan hange da saurin gano abu. Kaifin fikirarta ya fita daban dana dukkan wani yaro dake cikin gidan,don haka take saurin fahimtar kowanne motsi taku da kuma sauyawar yanayin qannenta. "Huda......wai baki duban lokaci?" Batace komai ba huda din,saita zare cup din bakinta ta direshi tana niyyar miqewa,abinda ya sakata maida idanunta ga cup din kenan. Ko rabin tea din bata sha ba,ta sake maida kallonta a kanta "Kin qoshi kenan?" Kai ta jinjina mata kafin tace "Banajin yunwa dama kwata kwata" Kyawawan idanun nata masu wani irin shape ta lumshe,can qasan zuciyarta tana furta "Alhamdulillah,astgafirullah" A duniya daya daga cikin sauti da take matuqar son ta yita ji kenan daga harsunan qannenta "BANA JIN YUNWA" Sauti mafi dadi kenan daga bakinsu zuwa kunnuwanta. Waiwayawa tayi gefanta ta kalleta sanda ta kammala saka takalmi da socks dinta "Nadra......shiga daki gefan katifata ki daukomin jakata na sallameku......yau din kamar babu me laka a jikinku" "Tom" Ta amsa tana saukowa daga saman kujerar da saurinta ta wuce dakin. Sanda take maido dubanta cikin falon sai suka hada idanu da hudan. Huda ta janye daga kallonta,sai ita din taci gaba da kafeta da kallo tana dubanta "Huda" "Naam" Ta amsa mata ba tare da sun hada ido ba "Wai meke damunki?" Ta jefeta da tambayar tana kebe baki......harta bude baki zatayi magana ta dakatar da ita a tsaurare "Karki soma cemin ba komai.......na gani a idanunki da motsinki......" "Gida......" "Ba damuwar mutanen gidan nan ba?" Ta jefa mata tambayar tana duban idanunta,a yanzu akwai sirkin bacin rai kadan a maganarta da idanun nata "Yaushe kika fara saka maganarsu cikin ranki?" Ta kuma tambayar tata tana kallonta "Ashe har yanzu baki saba da halayyarsu ba?,bakisan yadda zaki zauna dasu ba?,huda ina duk qoqarin da nake a kanki ke da kike babba ki fahimci yadda zaki zauna da kowa a cikinsu?" "Anty bakisan me suka ce ba a kanki.....bakisan me suke fada ba kullum" Ta qarashe maganar muryarta tana raurawa sosai da alamun zuciya da ruhinta gaba daya sun sare. "Kome zasu fada huda su fadi,indai a kaina ne karki azawa kanki damuwa.......kome ma zakiji sun fada,ba wani baquwar kalma da zakiji daga bakinsu ko sabon abu.....me yasa sai yanzu zaki fara sawa kanki kina damuwa?" Ta qarashe da sigar tambaya. Qasa tayi da kanta ba tare data amsa mata ba,ita kanta batasan me yasa sai yanzun abun ke damunta ba duk da sun share shekaru dasu a haka. Daidai sanda nadra ta qaraso ta miqa mata kyakkyawar hand bag din nata fara tas me adon brown duka jikinta dake dauke da tambarin kamfanin Gucci. Idanunta masu sheqi ta juya zuwa ga nadra,ta saka hannu ta karbi jakar tana qoqarin zugeta. "Anata kiran wayarki tunda na shiga" Nadra dake goya jakarta ta fada. "Okay,barta" Ta amsa mata a taqaice,don ta tabbatar a cikin mutum biyu daya ne yake kiranta,tafi kuma gasgata zatonta akan dayan. Zip din da take ajiye canji ta zuge,ta fidda kudin ta lissafa daidai yadda tasan zai ishesu break da kudin mota,saboda yau din basuyi abinci yadda suka saba ba kasancewar kayan abincinsu ya qare. Daga bakin qofar falon nasu tayi tsaye hannayenta goye a qrijinta tana dubansu har suka kammala ficewa daga gidannasu,sai taja Qaqqarfar ajiyar zuciya tana sauke hannayen nata ta juya a hankali don komawa falon don kwata kwata bata samu isashen bacci ba a jiya,tanaso ta runtsa sosai sannan ta shiga kasuwa tayi musu saye saye *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 14 ________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* _________________________ Saidai dai dai sanda ta saki labulayen da zummar shiga ciki din taji sallamarsa ta karade tsakar gidan. Qaramin tsaki taja,tabbas tunda aka jishi da sassafen nan kamar haka to ba a shakka wata tijarar yazo yi,ko kuma akwai abinda ya hadoshi da wani. Idan da sabo zata iya cewa sun saba da halayyarsa,macce daya ce cikin gidan suke dasawa har baka iya jin kansu. Har gwara ita tasan maganinsa,ta kuma san ta yadda take bulloma tsiyarsa,duk da bata taba tsaiwa ta kulashi ba anji muryarta a matsayinsa na qanin mahaifi a gareta. Sakaya qofar kawai tayi ta sake zuge labulen sosai sannan ta wuce uwar dakin ta yadda ba zata tsaya bata lokacin jin meke faruwa a tsakiyar gidan nasu ba,domin ita din tana cikin jerin sahun irin mutanen nan ne dai basa shiga abinda bai shafesu ba,wanda ya shafesun ma sai tura takai bango,bata da magana sam sam bare hayaniya. Wannan hali nata da siffarta ta sanyi da sauqin hali da kuma yauqinta ya sanya da yawa suke mamakin WANNAN DABI'A TATA......Dabi'ar da har yanzu su kansu basu da cikakken yaqinin a kanta,duk da cewa suna kallon gamsassun hujjoji ai sun gama bayyana a fili a game da ita. Babban bedroom ne qwarai wanda iya dauke gado da wardrobe guda bibbiyu,sai dressing mirror guda daya. Duk da cewa wai daga bacci aka tashi amma dakin neat yake,komansa akan tsari,ga kuma wani sassanyan qamshi da yake fita kaman dai yadda falon yake. Daya gadon da yake shine qarami ta nufa,wanda ke lullube da lallausar shimfida da tattausan blanket peach color. Tun batakai ga zama ba rurin da wayarta keyi ya cika mata kunnuwa,sai ta haye saman gadon ta lalubo wayar ta cirota daga gefan pillow dinta. Iphone 15 ce dake dauke da wata irin cover me kyau data dace da wayar da kuma me wayar gaba daya,ta zubawa sunan dake yawo saman screen din idanu *_ibraheem_* ya nuna mata. Wani gajeran murmushin gefan baki ta saki dake cakude da wani emotion. Siririn tsaki taja saman harshenta,ta fara qoqarin rejecting kiran "Done and dusted.......an gama da shafinka tun a jiya" Ta fada qasan ranta tana tuna yadda al'amura suka tafi mata successful kaman yadda aka saba. Sai data tabbatar tayo blocking ta kuma shafe duk wani abu daya shafeshi cikin wayar,bata bar hujja ko qarama ba da zata nuna tsohuwa ko sabuwar alaqa ko kuma mu'amala tsakaninta dashi ba. Ta sake bin wayar ta tabbatar komai ya koma kaman da,sannan ta duba wata ma'ajiya ta daban ta lalubi wata number ta kira ta kara wayar a kunnenta. Bugu biyu aka daga ana sallama cikin zaquwa da zumudi "Ina fatan saqon ya riskeki?" Tayi tambaya zuwa ga daya sashen "Ya riskeni qwarai kuwa tun a daren jiya.......ina godiya......na gode sosai,ina me baki haquri kuma akan sabanin Fahintar da nayi miki a farko.....gashi kuma ko sunanki ma ban sani ba" "Ba buqatar hakan......infact ma daga yau ba zaki sake samu na ko jin muryata ba......abinda na baki kiyi qoqarin tattalashi,ki kuma boyeshi daga sanin mijinki.......abu na qarshe saiki tayashi jiyya.....kinsan yadda zaki sanya masa tawakkali cikin zuciyarsa,don nayi imani ya zuwa yanzu zaiyi wahala bai zauce ba,na barki lafiya" Ta yanke kiran ba tare data barta tace komai ba,duk da tarin abubuwan fada masu yawa da take dasu take kuma son gaya matan. Itama goge number dinta tayi ta kuma sakata a sahun sauran tarin lambobin dake akwatin katangewa dake cikin wayarta. Layinta layi ne dake da wani irin tsaro na musamman,wanda ba kowacce number da bata yarjewa bace take iya samunta. Tana da ire irensa sunfi guda ashirin,duk kuma sanda take da muradi ra'ayi ko kuma buqatar hakan ya taso tana iya sauke wanda taga dama ta dora wani. Tana shirin shigewa duvet ta kwanta wani kiran ya sake shigo mata. Batason takura sam,sai taja tsaki tana kallon fuskar wayar. Shine din dai,batasan me yasa ya matsa da yawa ba,bataso a yanzun akwak enough kudi a hannunta,tanaso taje hutu koda na taqaitaccen lokaci ne kafin ta fada zuwa wani agenda din. "Tsautsayi da alama keta kiranka" Ta furta qasa qasa ta jawo wayar tana rejecting kiran shima sannan ta kashe kiran gaba daya ta jefar da wayar. Kanta ta mayar ta qudundune sosai cikin blanket din,saidai ko minti biyar bata yi ba cikakke ta miqe zumbur kamar wadda aka tsikara,ta sauko daga saman gadon tana qoqarin daure gashinta me santsi dake rufe gefan fuskarta. Kyakkyawar drawer dinta ta bude banqaran hijabs,ta fidda wani qaramin farin hijab cikin jerin hijban da take amfani dasu a lokaci irin haka idan zata shiga wanka. Sama kanta ta zurashi,wanda wannan ya fidda kyakkyawar fuskarta tsakanin hijab din,ya kuma fidda wata sihirtacciyar kama akan fuskar tata. Towels dinta ta nufa ta zari guda daya,sannan ta matsa gefan daya drawer dinta ta jawo ta can qarshe ta fidda set na kayan wankanta dake cikin wani dan kyakkyawan kwando kaman kwandon kaba,ta rataye toweldon saman kafadarta ta fara takawa a hankali tana fita a dakin tare da sake gauke fuskarta da kyau wanda kusan haka dabi'arta take duk sanda zata fita zuwa ainihin tsakar gidan nasu,duk da dama ita din ba matum bace data cika fara'a. Duka duka mutanen dake sabgarsu a safiyar ranar cikin sararin tsakar gidan ba zasu wuce mutum biyar ba. Dukkaninsu kuma mata ne da a shekaru suke qasa da nata shekarun idan ka dauke mutum daya dake ta bakin kitchen dinsu,zaune saman kujera 'yar tsuguno tana ta kokawa da wutar ice da take qoqarin kunnawa hayaqinta yana dawo mata cikin idanu yana sake tunzurata da hasalata. Duk wanda suka hada ido dashi sai ya janye dubanshi daga kanta kamar yadda itama kusan haka take musu,duk kuwa da cewa wasunsu suna son tankawa a gareta kaman yadda a wasu lokutan yake kasancewa,saidai wanzuwar ta bakin kitchen din ya sanya ba wanda yayi gigin aikata hakan a cikinsu. Bata dakata ba har ta isa bakin makewayensu da ko yaushe yake cike da tsafta da kulawa,ta xare towel din wuyanta ta azashi saman qofar bandakin idanunta nakan shaheed,yaron da aka kawoshi yaye daga gidan mahaifansa zuwa gidan kakanninsa. Yaron yayarta ne,yayarta ta kusan biyar,d'iya a wajen gwaggo mace ta biyu a wajen mahaifinsu. Ido suka hada da yaron,sai ya sakar mata murmushi,a hankali itama ta motsa bakinta tana maida masa martani. Tana da wani boyayyen soyayya ta yara a zuciyarta,saidai zuwan yaron sai ya zame mata kamar wani mabudi ko kuma wanzuwar sabon abu da bata saba gani ba cikin gidan wato murmushi kowacce safiya a tsakar gidan mahaifinta wanda ya jima da shudewa tun bayan gushewar mahaifiyarta. Tanason yiwa yaron magana,amma tayi imani rayuka zasu iya baci daga qarshe,dole ta kauda kai,ta sirka ruwan zafin data fito dashi ta fada wankan. Kafin ta kammala taji masu buqatar shiga bandakin da yawa,masu qananun mitoci da qorafi duka sunayi,wasu su juya wasu su zauna suna dakonta gami da ci gaba da yasar da maganganun da tayi imanin da biyu suke yinsu kamar yadda suka saba. Zuwa yanzu ta fara tunanin yadda zata maida qaramin dakin dake kusa da dakinsu toilet. Daya daga cikin dabi'a daya ta gidansu data tsana kenan,sharing toilet. Gini ne irin na da wanda duk yawan jama'ar gida suna hadaka ne a bandaki qwaya daya tal!. Zata iya cewa da sauqi nasu tunda akwai wadatar tsafta. Ko data fito babu wanda tabi takai,sai data kammala uzurinta na daura alwala a nan bakin famfo sannan ta tattaro kayanta tana barin wajen. Sai a sannan ta kallo mata biyun dake zaune daga bakin bishiyar. Daya ta girmi daya a shekaru,saidai dayar ta dara dayan jiki. Sun kalleta sun kuma dauke idanu kamar basu ganta din ba. Ba abinda ya dameta da hakan "Ina kwananku?" Ta furta da muryarta me laushin nan tana yin gaba ba tare da tayi koda yunqurin tsaiwa ba da salon gaisuwar da duk safiyar duniya bata daukewa kowacce cikin su ukun ba muddin zasu hadu a farfajiyar gidan. Amsa mata sukayi kaman yadda suka saba din,can qasa suna kuma binta da wannan kallon dake dauke da tarin ma'anoni can qasan ransu,wasu. sun furta su sun kuma bayyana,wasunsu kuwa an barwa zuciya AKWATIN SIRRI. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* PAGE 15 A nutse take ratsa falon harta cimma uwar dakin nasu. Duk takunta guda daya sauke qafarta da dauketa zuciyarta cike take da kewa. Wata qatuwar kewa data zamewa kowanne motsi na rayuwarta lazim. Kewa ce da zaiyi wuya ita iya barin gangar jiki. Kewar mahadin rayuwa jigon rayuwa mahadin numfashi wato MAHAIFIYA. Duk yadda lokaci yakai ga wulwula gudu,duk yadda zamani yakai ga fara yin tsaho da nesanta bawa daga dukkan tunani radadi da damuwoyin abubuwan da suka shude amma ya gaza yin nasara a kanta ta wannan fannin. Mahaifiya daban take cikin rayuwar 'ya'yanta,babu ma ya mahaifiya irin tata......jajirtacciyar uwa data zamewa maraicinsu sutura,ta zame musu bango abun dafawa,ta hana musu kuka akan rashin mahaifinsu.....sai gashi a yanzun suna kuka.....irin kukan da kunnuwa ba zasu iya ji ba,idanuwa ba zasu iya gani ba.......ta saka dukkan wani qarfi da iyawarta ta tare wannan shingen maraicin......tozarta da wulaqantar rayuwa dake shirin danne musu numfashi har ya zuwa lahirar duniyarsu.......tallafewar data sabbaba mata tarin ciwuka.......nauyi me yawa a qirjinta da rayuwarta......ya kuma bude mata qofofi masu fadin gaske cikin rayuwarta......ya maida JARUMA a mafi yawan lokuta.....wani lokacin kuma MAFARAUCIYA dake bude dukkan qarfin qwanji dana zuciyarta don cimma burikanta. Ya dasa mata abubuwa masu yawa cikin ZUCIYARTA ya kuma sanya dolen dolen ta sauya akalar rayuwarta ta fanni da dama. Ta koma tamkar tarwada me wahalar kamawa cikin ruwan da take ninqaya. Ta kuma koma tamkar hawainiya dake canza kala a duk sanda taso hakan,ta bace ta kuma saje da duk yanayi ko launin da takeso ko kuma taga dama. Tana da tarin sunaye masu yawa da a duniya a yanzun bayan ainihin sunanta na yanka SABREEN. Sunayen da ba'a yiwa yanka ba don tabbatuwar samuwarsu a kanta. Akwai idanuwa bakuna da hankula masu zafi da batasan adadinsu ba a kanta. Kowanne kuma da irin nashi kallon.....hasashen da furucinsa dangane da ita. Karon farko ta sakarwa fuskar nan tata murmurshi data fito tawai bisa fuskar madubin dame gabanta duk kuwa sa siririyar qwallar dake kwance cikin qwayoyin idanunta masu sheqi kaman an diga ruwan zaiba. Karaya da kuma qwarin gwiwa na karakaina tsakanin qirjin nata,saidai ko sau daya bata aminta ta dauki FADUWA TSORO ko kuma ja da baya ba. K'aramin towel da yafi kama da handkerchief ta sanya ta tsane qwalla don kada ta bata daman fitowa,ta miqa hannu ta jawo stool ta zauna a kai tana saka hannunta tana kokawar daure sassalkan gashinta dake qoqarin kwancewa daga daurin farko datayi masa. A nutse ta jawo set na kayan shafarta da take amfani dasu. Skin care product ne da suke mahadi da shower gel cream da sauran tarkace,wanda kudinsu duka zai tasamma dubu arba'in. Kudi ne me nauyi da ciwo a wajen me qaramin qarfi,to saidai ta wajenta amfani dasu sun zame mata jiki kaman yadda suka zame mata wajibi. Tana son ado,tana qaunar tsafta da qamshi,wanda da a baya bata basu muhimmanci ba,saidai daga bisani ta gama karantunta tsaf......ta fahimci kowanne taku a rayuwa akwai abokin yinsa.....akwai sauyawar yanayi da ta zamewa jiki da rayuwa dole......dole sai an aiwatar da wasu abubuwa ake samun wasu abubuwan,dole sai an gusa koda da taki daya ne sannan ake samun wasu sabbin damarmakin suke shigowa rayuwar dan adam. Gayunta na daya daga cikin abinda ya sake sama mata MUMMUNAR SHAIDA da kuma mummunan zato daga bakunan mutane da dama. Zaton daya kamata ya qona mata rai.....ya sanyata fidda qwalla masu zafi.....a maimakon hakan saidai kawai ta murmusa,ta kuma motsa ta barka a wajen da salon abun nan dake nuni da BANI DA LOKACINKI/KA. Tsaf ta duk wani shafe shafe nata,ta kuma gyars gashinnan me tsanani yauqi sheqi da tsaho,ta dameshi cikin ribbon me dan girma,abinda ya sake bawa ainihin kamanninta fita ras kenan. Koda ta bude ma'ajiyar kayanta tsaiwa tayi tana tunanin suturar da zata dace da jikinta a wannan lokaci. Shaqe take tafff da tarin suturu na alfarma,masu tsadar da koda ba'a gaya maka ba kai kanka ka sani. Suturun da a tashin farko xakasan sunfi qarfin wanzuwa cikin wannan wardrobe din.....kaman sunfi qarfin ma ace akwai wani cikin gidan daya mallaki masu darajarsu. Juya zagayyayun idanunta tayi tana dan lumshesu kadan zuwa bangaren abaya. Sai data gama nazarinta sannan ta jawo daya daga ciki. Egyptian abaya ce me asalin daraja da kuma kyau wadda kudinta ya tasamman dubu arba'in da 'ya'ya. Sam sutura me tsada ba damuwarta bace,tana iya mallakarta a duk sanda tayi marmari ko kuma muradin hakan. Da sanyinta dinnan da yake cikin halittarta take daura belt din da abayan yazo dashi bayan ta saka ta farko ta kuma dora alkyabbar da abayar tazo da ita. Siririn mayafi ta zaba daya dace da rigar tayi rolling me kyau da ma'ana,take zagayyar fuskarta ta fito cif tsakiyar veil din,sai ta kuma duba handbags dinta dake rataye sama da goma sha biyar kowacce da takalminta mahadi a qasanta. 'Yar qarama ta dauko qirar kamfanin D&G da takalminsa,ta natsa gaban madubi ta dauki turarenta ta bintike kan ta feshe jikinta dashi,sannan ta zari wayarta ta jefa a jaka tana duba agogon dake daure a tsintsar hannunta ta doso falon. Jakar ta ajjiye tana jawo tea flask dinsu tana qoqarin budewa. Bata fiya son cin abinci da wurwuri da safe ba,to amma kuma tana tunanin zaiyi wahala idan ta fita din ta iya tsaiwa taci komai tasan halin kanta da kanta sarai. A tsaitsaye take kurba kyawawan idanunta zube fes saman qaramar waya me keypad data dora saman cinyarta tanata qoqarin kiran wata number. Bugu biyu aka dauka,muryarsa ta bayyana cikin wayar da wani irin shauqi da doki "Da wacce irin saa yay na wayi gari ne?,ya Allah" Ya fadi yana zama gefan gadon bedroom dinsa. Taqaitaccen murmushi me qaramin sauti ta sake tana kai cup din bakinta,can qasan ranta wani abu yana yawo gami da kai kawo a ciki. Gaba daya ta manta da rayuwarsa,taso kuma ta gogeshi a babin rayuwar tata gaba daya,to amma data tuna wani abu,sai take ganin ya kamata ko yaya shima a bashi darasi. "Ina kika shiga don Allah,ina kika boye hanan?" "Dukka wadannan tambayoyin basu kamaceka ba,tunda dai gani din na kuma kira ai sai ka ajjiyesu ko?" "Haka ne ranki ya dade" Ya amsata da sauri ba tare daya damu da yadda matarshi ke tsaye saman kanshi tana dubansa cike da qunar zuciya da kuma takaici ba. "Zaka iya samuna nan da mintuna goma a gaban flavours na gadon qaya?" Ta jefa masa tambayar tana ajiye cup din hannunta,daidai sanda yaron ya daga labulen falon bayan ya turo.qofar ya shigo. Washe mata baki yaron yayi,abinda ya sanyata murmusawa tana miqa masa hannunta dake daure da agogon fatan daya kwanta a jikinta sosai,gefe guda kuma tana sauraron amsarsa "Ko mintuna biyar kika ce zanyi qoqarin kawo kaina" "Yayi,saika qaraso" Ta amsa masa tana dan kauda wayar ba tare data kashe kiran ba. "Wace tayi kiranka?,ina zaka je?,wallahi baka isa ka fita a gidan nan ba" Sautin muryar matar ya ratso ta cikin wayar. Lafiyayyen zagin da taji ya fita a bakinsa ya sanyata datse kiran ba tare data shiryawa hakan ba,ta lumshe ido tana jin yadda qirjinta yake quntata "Har yanzu yana nan a yadda yake......har yanzu babu wani abu daya sauyashi" Kalaman dake karakaina a kwanyarta kenan "Am sorry.....am sorry" Ta fada murya can qasa tana motsa labbanta. Sanyin hannun yaron daya taba nata hannun ya sakata bude idanunta. Har ya qaraso inda take ba tare data ankara ba "Antyn huda" Ya kira ta da sunan daya saba kiran nata "Kaci abincin safe?" Ta tambayeshi tana dubansa. Girgiza kai yayi da sauri,sauta juya gefanta tana masa nuni da doguwar yatsarta "Dauko wancan plate din ka cinye duk abinda yake ciki na barmaka" Da zumudinsa ya juya din yana nufar wajen. Zama yayi sosai bayan ya bude yaga abinda ke cikin,soyayyen chips da ragowar soyayyen qwai,ya fara kaiwa bakinsa yana murmurshin jin dadin garabasar daya samu. Qananun surutai da muryarsu tun kafin sukai ga isowa falon shine yaja hankalinta. Ta kafe qofar falon da kallo har zuwa sanda suka yaye labulen suka bayyana,yana gaba tana binsa a baya...... *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾 *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* PAGE 16 ___________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* _________________________ Idanunshi a kanta sanda yake shigowa zuwa cikin ainihin falon da yake da banbamci da sauran faluka dake gidan. Itama shi take kalla,kaman yadda suma bambanta a kamanni da mahaifinta haka suka bambanta a halaye da kuma dabi'u. "Kai....kai,ubanka.....cireshi daga bakinka......tashi!" Matar dake biye dashi a baya ta furta a zabure bayan shigowarta dakin,idanunta kuma suka fada akansa sanda yake cin Chip's din hankalinsa kwance. Debe idanunta tayi daga kansu ta maida kan yaron da ya tsorata sosai saboda yasan halinta,ba shiri ya miqe tsaye har farantin chips din dake saman cinyarsa ya fadi,tsirarun dankalin ciki da yayi saura ya tarwatse a wajen. Gewayesu yayi da gudu gudu zai fice yana matsawa daga wajenta amma duk da haka bai tsira ba,bayan uwar harara da take narka masa sai data bishi da ranqwashi tana cewa "Bansan inda ka dauko kwadayi ba don ubanka,saidai daga can bangaren uban naka,don mu nan ba makwadaita bane,masu kwadayin ma addu'ar shiriya muke musu.....ba zaka jazamin masifa ba......cin abincin da aka da kudin haram?,ina zamana lafiya?,to muddin zaka ci gaba da shigowa dakin nan kuwa sawuna a likkafa zan maidaka gidan naka uban" Tayi maganar tana daga tsaye tana kallon qofar da tuni ya riga ya fice daga ita. Dauke dubanta tayi daga kanta,don gugar zana irin wannan tash ba kasafai ta fiya damunta ba. Idan d sabo ta jima da sabawa da ita din,ta kuma zame mata jinin jiki. "Ni zan fara gaidaki ko kece zaki fara gaidani?" Muryarsa ta dawo da hankalinta daga duniyar tunanin data fara nausawa. Fararen idanunta ta aza a kansa,mutumin dake a mazaunin mahaifi a gareta.....wanda ya kamata a ce a yanxun basu da tamkarshi,koda baiyi ya mahaifin nasu ba.....amma ya zamana ya toshe wani babban kaso cikin gibi da rayuwarsu zata samu. Qaramin bakinta ta motsa wanda sauri yakan kira da shegen bakin rashin d'a da rashin mutunci,da wannan muryartata da sautinta ke cike da sanyi da nutsuwa tace "Ina kwana kawu?" "Lafiya qalau na kwana,sai uban baqinciki da takaicinki dake shirin hallakarmin da rayuwa" Ya furta cikin hargagi tamkar dama yana jiran ta gaidashinne. Har yantsu dogon yatsanta yana saman labbanta,yayin data kafe mutumin data kira a dazu da kawun nata da idanunta,tana dan motsa yatsan nata saman lebenta tana kuma nazarin fuskarsa furucinsa dama motsinsa. Ko sau daya bata taba ganin mutunci kima da martabarsa ba......daidai da misqala zarratin bata taba daukarshi da wani babban matsayi ba......abu daya ta sani,komai lalacewar fura tafi kashin shanu......komai kashinsa da zabgewa gami da lalacewar martabarsa a idanunta sunanshi kawunta kuma qani ga mahaifinta. Maida idanunta tayi ta lumshe kawai kaman yadda ta saba masa a yawancin lokuta......tasan me ya sanyashi wannan zuwan,wani boyayyen buqatarsa ne dake a qasan rai da bai samu biyanta ba. Ta tuna haduwarsu ta qarshe dashi a wancan satin daya wuce. Dama ta sani ba zai haqura ba.....shine zai fake da wasu abubuwa wanda shi kansa ba kubuta yayi daga su ba.....yazo ya samu wannan matar da qiyayyarsu ta jima da yin tsiro da jijiyoyi a cikin jikinta. Takai qarshen maganar sanda take bude idanunta saman fuskar bibo. Haduwa idanunsu sukayi waje daya da nata,ta juya qwayar idanunta tana watsa mata wani kallo "Ki dain kallona da wadannan tsayyayun idanun naki na rashin kunya masu kama da idanun mage.......kai ya kamata ka tsaya a kanta saboda tana jawowa bawan Allah zagi,wanda ya jima da mantawa ya zauna a duniyar.....amma ina kyautata zaton kullum ta Allah sai mala'iku sun tadashi zaune sun nuna masa qazantar da d'iyar cikinsa ke aikatawa. Ya rasu yabar yara sama da goma sha takwas amma ba wadda ke hana masa kwanciya lafiya a kabarinsa sai ke?,ai wallahi Allah wadai da haihuwar d'iyoyi irinki.....indai haka haihuwar take gwara mutum ya zauna a haka" Tana maganar tana jujjuya hannunta guda daya gami da yarfeshi,idanunta a kafe saman fuskarta,kaman yadda itama tunda ta fara maganar ko sau daya bata dauke dubanta daga kan bibo ba. Maganganun nata sunkai mata iyaka,tana jin ta gama daukar iya abinda zata dauka a iya wunin yau,saboda haka a nutse ta sauke qafafunta qasa ta miqa hannunta ta dauki handbag dinta ta miqe tsaye tana gyara rolling din mayafinta "Fita zanyi,kuma ina da buqatar na kulle mana dakin kafin na fitan,idan ba damuwa ko zamu koma tsakar gida mu qarasa maganar a can?" "Kaji ko?......dama ai na sani,babu wani sauran wanda take gani da kima a duniya.......yau koda fadima zata dawo duniya bata isa ta juyata ba bare alhaji" Tayi saurin cafe zancan. Wani irin juyowa tayi gareta ta zube mata manyan fararen idanunta "Kaman bakiji me nace ba ko?,nace muje tsakar gida mu qarasa......bankai ga furta cewa banda lokacin sauraro ba" Ta mata maganar dalla dalla tana kallonta. Sosai bibo ta kafeta da kallo,har yanzu babu abinda zai sauyata......wannan rashin shakkar da rashin tsoron suna nan rubuce baro baro cikin ayyukanta da dukka motsinta,dakiyarta da shariyarta da daukan abu me zafi ta wulwulashi ta sauya masa mizani idan taso. "Idan ta fito kawu qofar kawai zakaja jam lock din zai shige,ka sameni a qofar gida muddin baka wuce minti biyar ba" Tayi furucin sanda take takawa zata fice a falon tana riqe da vail din abayarta daya zame tana qoqarin mayar da rolling dinta yadda yake. "Tashi muje na sameta a waje din inji da wacce hujjar zata kare kanta kuma" Ya furta dukka jikinsa na nuna zumudi da qaguwar yaga ya bita. Da kallo bibo ta bishi tana daga zaune a kujerar ba tare data motsa ba baqinciki yana kasheta. A yau tana jin kaman ta tashi ta rufe rufa'i da duka. Yau ya tabbata mara amfani kwata kwata a garesu gaba daya. "Ko nayi gaba kya rufe musu dakin?" A zafafe ta miqe tana gyara daurin dankwalinta "In zauna inyi me a nan?,Allah ya sawwaqe,ai ni tawa son zuciyar bai fara sauka har takan kayan haramun ba" Ya jita sarai,ya kuma san da biyu take maganar,saidai a yanzu baya jin yana da lokacinta,dukka tunaninsa yana ta'allaqe akan sabreen. Yasan halinta sarai,muddin ya haura mintunan data dibar masa,yayi imanin da gaske zai iya zuwa ya tarar ta wuce din abinta. Tana rungume da hannayenta sanda take tsaye a qofar gidan nasu ta bashi baya. Fuskar nan dake shimfide da wani irin kwarjini yau din cakude take da ninkin rashin fara'a da walwala na tun asali da aka santa dashi. Har tsakiyar zuciyarta takejin wani abu yana tsikarinta duk da yadda iskar dake yawo sararin subhana ke kada doguwar riga da dan mayafin saman kanta tana watsa daddadan qamshin turaren dake tashi a jikinta. Turaren da ita kanta yake sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali,dadinsa ya sanya ta zabeshi a matsayin turarenta na dindindin,duk da batayi tunani matsayinta zaikai a nan kusa ta mallakeshi ba. Ta kalli agogon hannunta,yaci mintuna hudu cikin minti biyar din data bashi,don haka ta fara takawa sannu a hankali tana matsawa daga gaban gidan nasu. Tun batayi nisa ba ta jiyo taku da kuma muryar kawun nata,bata da buqatar kallon fuskarsa ko doguwar magana ta hadasu,buqata gareshi zata sallameshi.....kamar yadda tun tale tale.....kaman yadda tun can baya bashi da amfani a garesu a yanzun ma bata tunani akwai wani sauran amfani da yake dashi a rayuwarsu,don haka ta sabule jakarta,ta zuge ta zaro wani abu daga cikin kudin da yayi saura a ciki ta dunqule a hannunta tana jiran isowarsa "Ke sabreena......sabreen" Ya hada da qwala mata kira tamkar ya bata bashin kudi tana kuma shirin gudar masa dashi. Ranta ya sake baci,ta tsani kwakwazo,a banza ma idanun 'yan unguwar da dukka kunnuwansu harma da hankulansu suna kanta,kowanne motsi ko taku nata a biye suke dashi,sauraro suke.....jira sukeyi na samuwar dukkan wata dama da zasu samu abun magana a kanta. Wannan ya sanya tadan saurara daga tafiyar da takeyi tana dakon isowarsa. Ko a sannan tana iya ganin idanun tsirarun mutanen unguwar da suka samu sararin fitowa da safen kamar ita yana karakaina a kanta. Irin wannan kallon nasu gareta ya zama tamkar jarrabi ko masifa cikin rayuwarsu. Akwai abubuwa da yawa tasan da akeson gaya mata amma babu wannan fuskar. Bataga dalilin zallar rashin adalci irin nasu da suke gwada mata ba suke kuma gwadawa rayuwarta ba. Sun sany hannu dukka da qafafunsu sun tankwabeta sun kuma tankwabe rayuwarta a sanda take da tsananin buqatarsu......a yanzu kuma data yankema kanta bata da buqarsu.....a sannan su kuma suke qoqarin dawo da ita su dankwafar da ita.....suka kuma fidda makamansu da harsunansu wajen illata mata gangar jiki da zuciya. "Me na samu?" Ya iso gareta yana tambaya sanda motar da take da tabbacin waye a ciki ke dab da isowa inda take. Kowanne mutun da zatayi mu'amala dashi ko kuma tayi mu'amala dashi din......sau daya tak take masa wani karatu a taqaitaccen lokaci.......fahimtar waye kai?......meye qudurinka.......meye motsinka?.....mene manufarka......da sauran dukkan wani abu daya shafi rayuwarka yana zama RUBUTACCE cikin shafin qwaqwalwarta. Bata fiya manta abu ba,haka bata missing target saidai idan bata nufaci abu ba. Ta baya ta miqa masa kudin sannan ta fara takawa zuwa ga motar da tuni ta iso inda suke harma ta samu wajen tsaiwa. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 17 daga inda yake a zaune din yakejin kamar gilashin window din motar ya masa shamaki daga kallonta duk da yadda yake tarwai yake kuma iya baka daman gano komai dake ta wajen motar......duk da haka yana jin kamar ya rage ma idanunsa armashin kallonta,don haka ya kasa haqurin isowartata,ya sanya hannu ya sauke dukka gilashin nasa qasa. sau daya tak ta taba ganinsa ido da ido,amma ta haddaceshi tsaf,tun daga abun hawansa har zuwa halayya da kamanninsa....... Kakkaura kuma faffada da zaka iya kiransa me jiki saidai bai cancan ba. Maabocin iya ado sosai da murza hula ta zauna a kansa kamar shi yake saqa ma kansa ita. Yadda turarensa da shigarsa keda kyau da tsari haka ma kalaman bakinsa,saidai kash!.....daidai da wucewar daqiqa guda bata taba jin wani abu me kama da SO K'AUNA KO BEGE nashi ya tsartu a ranta ba. Waishin mcikina meye SOYAYYA ne?. Ita kanta jerin kalmar SOYAYYA da yadda mutanen duniya suka daukaketa na daya daga cikin abinda ke sanyata dariya koda bata shiryawa hakan ba. SHIRME shine cikakkiyar ma'anar da take ganin yafi dacewa da a kirata ko kuma CUTA,idan akwai sunan da yafi haka lalacewa ma a nata ganin daidai ne a kirata da wannan sunan. Yadda yake tsareta da kallo ya sanya qirjinta ya dinga suya duk kuwa da cewa ta saba da irin wannan shegen kallon. Kwarjininta na daya daga cikin abinda ya sanya take tsira daga guba da dafin MAZA duk kuwa da cewa ita da kanta take tsalle ta afka tsakiyar tarkon bisa tsananin lissafinta,ta kuma samu sa'a da nasarar zame kanta cikin SALO da kuma qwarewar iya wasa. Da hanzarinsa ya fito ya zagaya don bude mata qofar motar,hakan ya bawa kawu dake lafe yana kallon komai qare masa kallo. "Iya shaddar jikin yaronnan kawai ta isheni jari wallahi,wannan tsinanniyar yarina,yanzu meye aibun wannan da ba za'a aureshi ba?" Ya tambayi kansa da kansa yana naniqe da kudin hannunsa. Idanunsa ya aza a kanta bayan ya bude mata motar,sai ya sakar mata murmushi,tadan lumshe ido tana qaqalo nata murmushin cikin dauriya da son maida masa. Gefe guda zuciyarta na cike fal da qarin wani mamakin akan D'A NAMIJI. ta tuna kalamansa akan matarsa dazun dazun nan,amma a yanzun gashi a gabanta ita kamar zai narke. Ta yaya zata yadda tayi aure a duniya?,ta yaya zata bari zuciyarta ta kamu da soyayyar wani namiji?,yaya za'ayi ta banzatar da lafiyar zuciyarta cikin soyayyar wani?,soyayyar halittar da babu tausayi ko jin qai a tare dasu?,halitta mafi son kai cikin halittun duniya gaba daya?,halitta me tsananin mugunta da son cutar da halittar mace 'yaruwarta?. Ba zata iya sadaukar masa da murmushinta na dogon lokaci ba,duk kuwa da cewa fake smile ne,don haka ta zame jiki ta shige cikin motar ya mayar ya kulle yana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk duniya ba wanda ya kaishi sa'a a yau din. Yana jin kamar duka ranar tashi ce. A kujeran driver ya zauna yana qoqarin tayar da motar amma duka ido da hankalinsa yana kanta "Ina muka nufa my life?" "My life?" Ta sake jaddada maganar a ranta "Ko ina ya baro matarsa ta sunna da har ita ya danqara mata wannan sunan?" Wannan ba baqon abu bane a wajenta,saidai har yanzun mamaki da lamarin maza bai gama sakinta ba. "SAMHG store" Ta amsa masa a nutse tana gyara agogon hannunta daya goce "An gama ranki ya dade" Ya fadi cikin zumudi yana tayar da motar. Sun jima akan hanya yana tauna abinda zaice da ita,don a taqaitaccen saninsa da ita.....mutum ce me matuqar tsari,nutsuwa da aje komai a bisa gurbi da muhallinsa. Bayaso ya kwafsa kaman waccan karon,bayaso damarsa ta sake kubce masa,duk da cewa har kawo yanzun baisan me ya aikata daya rasa wancan damar a wancan karon ba. Yaji babu dadi ainun saboda ya qwallafa rai sosai a kanta. Ta yiwa zuciyarsa wani mahaukaci kamu a ganin farko. Yayi tsammanin kudinsa da ajin mataki na rayuwa zai saya masa ita cikin qanqanin lokaci,sanin da ya yiwa 'yammata kenan a yanzun,ballantana ita dake da kyau da aji irin wannan. Sanda yake wannan tunanin nata nazarin da karatunsa duka a kansa yake. Yadda yaketa rejecting kiran dake fama shigowa wayarsa a jejjere. Duk kiran da zai shigo sai ya katseshi. Tuni hankali da kuma jikinta ya bata wanda ke kira. Idanunta tadan lumshe,koda yaushe su dinne dai,cikin wahala,qasqanci,tozarta da kuma wulaqanta zaune cikin gidajen aure. Ko meye kuma zai fito yaje yazo su din yake afkawa. "Zan iya cewa wani abu?" Ya tambaya a ladabce yana murza steering motar cikin qwarewa "Kafin sannan ya kamata ka daga wannan kiran ko?" Ta fada idonta akan fuskarsa. Motsawa kadan yayi yana duban wayar ta qasa idanu,bai zaci ma ta lura da hakan ba. Haushi ya soma kamashi akan kiran da take masan babu qaqqautawa. Yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,tunda bai jima da fita a gidan ba,yasan kuma abinda ya fito ya baro a gidan "Tarin damuwa ce da matsaloli kawai take dauke dashi" Ya furta yana jan siririn tsaki. Har tsakiyar ranta taji saukar maganar,ta lumshe ido kadan tana budesu. Yana nan din a haka,yana nan yadda ta karanta. Tayi qoqarin tureshi daga shiga layikanta,tayi qoqarin hanashi shiga cikin tarkonta don baya cikin irin mazan data zana bisa layi da gurbin rayuwarta,taso ta barshi ya samu me hukuntashi a gaba.....amma tunda har ya sake dawowa cikin rayuwartata cike da karsashi da zumudi,to tayi imani hukuntashi yana cikin qaddararta ne. Ba kuma zata qyaleshi ba,a wannan karon saita hukuntashin yadda ta saba hukunta maza irinsa. Maza irinsa basa tsira daga tarkonta......basa tsira daga kamunta,hakanan basa tsira daga hukuncinta. Cikin salo na dabarar da yake gani kaman ba zata gane ba ya latse wayar,ya kuma jefo mata maganar da tafi damunsa "Hanan.......wannan karon bazan bari ki kufcemin ba" "Nima bazan bari ka tafi ba" Ta furta,a bakinta bisa mizanin ma'ana qwaya daya tak da hankali zai iya fahimta,amma kuma an aje ajjiyayyar ma'anar da ake nufi da maganar can qasan zukata. Wani irin dadin daya sabbaba masa lafiyayyen murmushi ya ziyarceshi. Bai taba kawowa ko kusa a ransa samun wannan gwaggwabar nasarar a kurkusa haka ba,amma kuma,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa "Duk kyau ko matsayinta zata sauko......a yanzun fa mata ke neman mazan aure idanu rufe" Hudubar data shiga kunnensa kenan,kuma ya yarda da hakan dari bisa dari. "Amma hanan banga alama ba......bansa inane mazaunin da kike rayuwa ba,gida unguwa da sauransu" "Gaggawar me kakeyi?,kada ka samu damuwa" Ta amsa masa tana jin ya ginsheta gaba daya,tana jin ta damu qarshen zamansu yazo,ta qagu su isa SAMHG store ya ajeta ya bata sarari. A hankali ya kutsa motar babbar harabar kantin saida dukkanin kayan buqatar rayuwa,wanda zaifi kyau ka kirashi da kasuwa a sauqaqe amma kuma a zamanance. Ba abinda basu hada ba na kayan buqatu,tun daga tufafi zuwa kayan masarufi. Wajen nada matuqar girman da idan ka kirashi da duniyar siye da siyarwa. Girmansa ya sanya yake da mashigu daban daban da kuma guraren fita mabanbanta. Cikin tafkekiyar harabar wajen ya aje motarsa,ya kasheta cikin mutuwar jiki da kasala yana waiwayowa inda take zaune tana qoqarin rataya jakarta gami da daukar wayarta ta riqe wadda ke aje saman cinyarta. "Idan ban damuwa zan dan tayaki tattaki zuwa ciki......don naga wajen kamar cike yake da maza da yawa......ni kuma ina kishin na barki ki fita ke daya a kallemin ke" Ya furta cikin kulawa da wani irin narkakken so dake ragargazar zuciyarsa. Da wani sassanyan kallo ta jefeshi,qawataccen murmushin nan dake qawata fuskarta da kuma labbanta ta sakar masa. Ta rausayar da kanta gefe tana juya idanunta. So take ta sallameshi a iya haka,bata buqatar doguwar damuwa. A lokaci irin wannan da takai qarshen mission dinta,ko fita unguwa ba kasafai take damunta ba sai idan buqatar haka ta taso. To amma hakanan taji akwai buqatar ta fita din,akwai kuma buqatar ta fita tayi musu siyayya. "Baka da damuwa akan duka wannan......wannan hanan din ba komai idanunta ke kalla ba ballantana su burgeta" Ta bashi amsa a nutse. Murmushi ya saki yana qara narkewa a sonta,yana ji cewa zai iya yin komai don ya mallaketa,yana jin cewa muddin ya sake barinta ta subuce masa a wannan karon ya tafka babbar asarar da bazai iya maida madadinta ba,baya jin ma zai bari hakan ya faru dashi sam sam.....kai koda tuna hakan na iya faruwar bayason yayi. "Na ga zahiri......na kuma tabbatar wannan halittar ta daban ce......gamu cikin neman sa'ar kasancewa da ita" Ya fada yana lumshe idanu. Kai ta kawar amma tana murmushin yaqe. Ya numfasa bayan ya gama qare mata kallo cikin shauqi ya dauki wayarsa dake aje tun sanda ya maidata silent ya bude. Tarin miscall a qalla guda goma kyawawa daga gareta. Ya jawo maballin sama ya sharesu yana sakin tsaki can qasan ranshi tare da wucewa mobile app na banking da yake ajiyar kudadensa. Sosai ta jingina da makarin motar idanunta a lumshe sosai,sai kayi tsammanin bacci ko kuma gajiya ne sukayi mata yawa,saidai a cikin biyun duka babu ko daya a ciki. "A taimaka a karantomin account number na dan bada wani tukuici" Idanunta ta janye daga saman wayar nasa,saita tashi ta zauna sosai tana dan sakin murmushi "No need" Ta amsa masa a yangance kaman yadda ta saba magana "Please.......ba wani abu bane me yawa.....just tukucin bani damar ganinki da kikayi a yau ne" Bata sake ce masa komai ba,sai ta zura hannunta cikin jakarta,wani dan siririn card me ruwan zaibar gold ta ciro ta aje a gefansa. Ta dauke kai tana qoqarin bude murfin motar wanda ita kanta tasan ba zata budu ta sauqi ko dadin rai ba......ta kwana da sanin meta aiwatar mata. Cikin qasa da minti daya taji ya furzar da iska daga bakinsa gami da cewa "Done.....ina fata zakiyi appreciating" "Why not?,godiya me kima......godiya nake qwarai......but motarka tana nema ta riqeni fa" "Da zatayi hakan data taimakeni ai" Ya amsata yana sake lafewa jikin kujerar. Kyawawan sexy eyes dinta ta waro waje kadan,sai kuma ta daga hannunta tana duban agogo "Akwai alqawari da nayi,bana so kuma na saba......idan ka sani na saba kuma......next time kafin na baka daman sake haduwa dani....." Katseta yayi yana dariya ta hanyar hada hannayensa biyu waje daya sannan ya saukesu ya juya yana buda side dinsa "Lemme check meye ya riqemin amaryata haka". Da lumsassun idanunta ta bishi da kallo har zuwa sanda yake zagayawa gaban motar zuwa daya side din da take zaune. Yayi dukan dabarunsa amma hakan baiba,don haka ya zagayo yana fadin " Bansan me yake faruwa,lafiya lau qofar yake,bari nasa a duban.....am really sorry" Ya sake apologizing yana hade hannuwansa. taka Kai kawai ta daga masa tana irgen lokutan cikar target dinta. Cikin saa kuwa ya juya ya fara takawa yana barin wajen,wanda hakan ya bata damar janye kallonta sannu a hankali daga kansa,ta kuma maida saman wayarsa dake ajiye a wajen tana bada haske,tabbacin yunqurin hanata komawa key yayi daidai kenan,saita katse kiran da takeyi daga tata wayar zuwa tasa don sanya wayar awake. A nutse ta jawo wayar ta wuce zuwa ga maballin kira. Tarin miscall dinne kuwa ta samu kamar yadda tayi zato,dukka kuma daga number dake ajiye cikin wayar da sunan MOM SUHAIL. "SUHAIL" Ta ambata a fili,idan har bawai ta manta ba suhail din shine sunan first born dinsa kamar yadda T.j ya tabbatar mata. Wani irin tausayin matar da batasan ko wacece ba ya fara ratsa ta. Tana shirin karkata akalar binciken nata zuwa wani sashe na daban saqon SMS ya shigo wayar. MOM SUHAIL kamar yadda yake a rubuce ta bangaren kira. Bata tsaya dogon jinkiri ba ta bude,gajeran saqo ne kamar haka. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 18 _Nayita kiranka baka dauka ba,kome meye mukayi da kai kafin ka baro gida ai ya kamata ka tsaya kaji dalilin kiran da nake maka babu qaqqautawa,bayan ka fito ciwon suhail ya tashi,a yanxu haka muna asibiti,amma babu ko sisi a hannuna,baka barmin komai ba,already kuma account dina yana buqatar naje banki na gyara bare nayi hidimata da kudina yadda na saba_. Wani abu me tauri taji ya tsaye mata a wuya,ta zura hannu a jakarta ta ciro wayarta,tanason taga nawa ita ya kashe mata?,nawa ya saka mata alhali ko sisi matarsa bata amfana dashi ba?. Naira dubu dari ta tarar. Wani matsiyacin tsaki ta saki,cikin dukkan arziqinsa ya rasa da meye zaiyi mata kyauta sai naira dubu dari?. Bata tsaya batawa kanta lokaci ba ta sauka ta koma mobile app dinsa da bai jima da fita a kai ba. Daga password har username dinsa fes cikin kanta,tamkar hadaka ko gamayya sukayi dashi wajen creating dinsu a sanda zai bude manhajar. Cikin qasa da second goma komai ya bude,tarin miliyoyin kudaden dake kwance cikin account din nasa suka bayyanarwa idanunta,sai ta koms ta jingina da kujerar motar tana kallonsu,kamar ma bata tsoro ko shakkar dawowarsa. Numfashi take fitarwa d'ai d'ai qirijinta na sake quntata. Tarin zallar rashin imanin maza yana sake tabbatar da kansa a zuciyarta. "Yana da wannan kudin ya fita yabar matarsa babu ko sisi?,yana da irin wadannan kudaden yabar yaronsa cikin halin ciwo?,yana da wannan kudin ya gaza siya masa abun hawan da idan lalura irin wannan ta taso baya kusa zata kaisu zuwa ga asibiti cikin gaggawa?. Tsanar MAZA tsanar SOYAYYA da kuma tsanar AURE suka sake linkuwa cikin ranta. Irin wannan shaidojin na gani da ido ta din saidai ta bada labarinsu. Shi din ma ba komai bane a cikin maza......bata kuma san namiji na nawa bane shi din da a yau xai shiga makarantarta.......a yau zata sanyashi ya koyi darasi kaman sauran,saidai nasa darasin yazo ne a gaggauce saboda gamawa da babinsa da tayi,da kuma dadewa da tayi da sanin shi din wayeshi?. Beneficiaries dinsa ta duba,cikin sa'a tun batayi nisa ba taci karo da sunan da yayi daidai da sunan matar *ameena mu'azzam*. Kai tsaye ta saka amount din da yayi mata ta kuma karkatasu zuwa ga account din. Daidai lokacin data hangi tahowarsa,ta daga hannunta ta zare wania abu daga jikin qofar,sannan ta maida hankalinta kan wayar kamar ba me wayar ne yake dosota ba. Hankali kwance ta koma ta goge alert massage din da kamfanin sadarwa suka aiko,ta kuma koma zuwa ga email a gaggauce ta goge nashi tayi minimize ta maida wayar mazauninta tana karanta sunan banking da yake amfani dashi,sannan ta zaro tata wayar tana duba ma'ajiyar lambobi dake cikin wayar. Sunayen dake ajjiye cikin wayar ta fara bi,cak ta tsaya saman wani suna da yayi daidai da sunan banking nasa,ta danna malatsi na tura saqonni,ta kuma aika da saqon a gajarce "Done" Ta jefa wayar a jaka daidai sanda ya iso bakin window din suna sake yunqurin buda motar. Ja daya bakaniken ya yiwa murfin ya bude,sai ya waiwaya yana dubansa cikin mamaki,wanda shima cikin manakin ya iso "Oga ina tunanin kaine baka jawo ta da kyau ba" "Kai amma nayi mamakin faruwar hakan" Ya matsa yana kama hannun motar ya matsashi har sau uku. Mamaki yadan sake kamashi,amma kuma kiransa da tayi d nuryarta me laushi ya dauke hankalinsa daga nan. "Okay na gode to" Ya fadiwa bakaniken yana cirar wani abu a aljihunsa adan gaggauce saboda kiran nata. Bude mata qofar yayi,ta sako qafafunta ta fito tana gyara zaman abayar jikinta. Cikin nuna kulawa yake fadin "Da alama motar bata gaji dake ba,kamar yadda me motar shima bai gaji da kallin wannan kyakkyawar surar ba......don Allah ayimin lamuni a bani exact gurin da zan sameki.......da gaske nake,banzo da wasa ba,ni din ba irin sauran samarin yanxu bane......da niyyar aure nazo" Ya qarasa maganar yana lanqwashe murya. A nutse ta watsa masa idanunta da suke sake narkar dashi. Batajin daga rana irin ta yau ma zai sake samun damar tsaiwa da ita a muhalli daya irin yanzun. Wannan itace dama ta qarshe kuma lokaci na qarshe a wajensa tsakaninsa da ita. "Ba damuwa......ka samu number dina ai.....komai zaizo da sauqi?" "Are you sure?" Ya tambayeta yana kallonta cikin kokwanto. Saboda shi kansa yasan samunta din abune me wahala.....ta subuce masa wancan karon.....hakanan haka ya qaraci karakainarsa da nemanta amma ko me kama da ita babu ballantana ita karan kanta din. Kai kawai ta gyada masa sannan ta juya ta soma takawa tana barin wajen gami da cewa "Godiya nake......fatan alkhairi" "Nike da godiya kyakkyawa" Ya fada murya a lanqwashe yana binta da kallo da zazzafan so,yana jin kamar ya saceta ya gudu da ita ya mallakawa kansa ita. A nutse take taka kowanne step da zai sadata da ainihin makeken store din. Murmushi ne kwance saman fuskarta ita daya,duk da bata juya ba amma ta tabbatar yana tsaye ne yana kallonta,tana hasaso yadda fuskarsa zata koma a sanda ya laluba asusun bankinsa ya taras da barnar datayi masa,tana hasaso yadda wannan tattausan kallon zai koma zazzafan kallo da kuma zurfin tunanin TA YAYA AKAYI HAKA YA FARU?. Yadda take daukan hankula da idanuwan wasu daga cikin jama'an dake sabgoginsu a waje da cikin shagon bai dameta ba,don ba wani baqon abu bane a wajen ta. Itadai ta sani,akwai dubbai zuwa miliyoyin mata da suka zartata a kyau.....don bata tana daukan kanta ta sanya a sahu ko jerin kyawawan mata ba,amma batasan mene a tattare da ita me matuqar jan hankali irin haka ba. K'annenta sune gaba da komai da kuma kowa. Buqatunsu kuma sune gaba da nata buqatun. Don haka duk list na abinda suke buqata ta fara dubawa. Tana tsinta tana jefawa a cart. Ta kwashi a qalla minti ashirin tana nasu siyayyan sannan ta fara nata. Siyayyarta bame sauqi bane,tana da tsari tana zabi,ba komai yake burgeta ba kaman yadda a rayuwarta na zahiri ba kowa ke burgeta ba,komai nata yana da tsari,don haka ta bata lokaci sosai akan nata kayan,ta saki jiki kuma kamar ba zata bar shagon ba. Sai data gama tsaf sannan ta gangara bangaren kayan maqulashe. A duk sanda ta samu kudi irin haka bata rabo da siya musu kayan taba ka lashe,harda ajiye wasu ma cikin daki. A duniya idan akwai abinda taqi jini shine taji sunce BABU ko BANI DASHI ADDA....kalma ce da bata yarda a yanzun ta shiga tsari da babin rayuwarsu sam sam. Sashe ne dake danqare da chocolate kala kala da kuma biscuits. Masu tsananin tsada da kuma masu matsakaicin kudi. Da ido ta dinga bisu daya bayan daya,wani lokaci can baya daya shude bata isa ta sanyasu cikin idanunta ba,wani lokaci can baya daya shude sunfi qarfin tabawar hannuwanta ballantana akai ga batun sanyasu a bakinta.....wani lokaci can baya daya shude saidai ta hangesu......hangema daga nesa.....wannan ya sanya tayi alqawari......ta kuma ci alwashin muddin tana raye ba zasufi qarfin rayuwar 'yan uwanta ba. Tana cikin dubawar ta hangi favourite chocolate dinta,ta kasa jurewa sai data daukota ta bareta ta jefata a baki,daidai sanda taji anyi kiranta da daya daga cikin sunayenta data mallakawa wani.....sunayen da suke zama tamkar tag ne ga kowanne namiji daya taba shiga rayuwarta. "Basma" Iya sunan daya kira tun kafin ta waiwaya ya gaya mata waye. Duk wanda ta bawa sunanta wannan sunan nashi ne shi daya,wannan sunan shita mallakawa shi kadai.....wannan kuma ya zame mata stamp kuma alama ta kowanne mutum daya taba shiga DUNIYArta. Murmushi ta saki tun kafin ta juya tayi tozali da wanda yayi kiran. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 19 ________________________ *_Katafaren sansanin UMMUMAHNOOR LUXURY,TA SHIRYA TSAF DON SAMA MUKU TSALA TSALAN KAYAN ADO DA SUTURA NA KECE RAINI IRIN NA 'YA'YA MATA,IRINSU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries ___________________________ Iya sunan daya kirata dashi ya bayyana mata kanshi tun kafin takai ga waiwayowa. Sanda ta juyo din yana tsaye daga bayanta,ya kafeta da wadannan jarababbun idanun nasa data sanshi dasu tun a lokacin,idanuwan data tsana fiye da kowanne ido a duniya,idanuwan da kuma tafi tsana bayan baqin mugun halayen dake rataye da jiki da zuciyarsa. "Malam nasiru....kana lafiya?" Ta fada calmly tana dauko wani box na chocolate din ta jefa cikin kwando. Takowa ya soma yi yana sake kusantota,har yanzun dai bai dauke idanunsa a kanta ba. Sake daga kai tayi ta kalleshi,sai ta fara tura kwandonta gaba "Kana mamaki ne?.....kayi tunanin bazan iya shaida ka ba ko?" Ta tambayeshi da murmushi a saman wannan miskilar fuskar da zaiyi wahala kaga fitar murmushin daga samanta. "Wannan basman bata manta fuskar mutanen da suka taba shigowa cikin rayuwarta.......hakanan wannan basman bata manta fuskar mutane irinku......hope kana lafiya ko?" Ta sake tambayarsa tana tafiya a nutse,tana kuma ci gaba da zaban abinda yayi mata tana jefawa a kwandon. Tarin mamaki ne ya lullube masa zuciya ainun......tsahon lokutan yayi tunanin duk ranar da sukayi haduwa ta farko da ita zata razana......zata kuma tsorata,idan da yiwuwar ma ta nemi guduwa duka zatayin duba da girman laifin data aikata masa. "Tana da wayo......tana kuma da hadari......da alama akwai abinda ta taka" Maganar abokinsa kenan ta dawo cikin kansa bayan wani zama da sukayi dashi,wannan ya sanyashi Maida hankalinsa jikinsa sosai,ya kuma tattaro bacin rannan da ta dasawa zuciyarsa wanda har yanxu a cikin bala'i da masifar data sakashi yake "Idan kika mantani ai baki cika 'yar halali ba......ai dama idan kere na yawo zabo na yawo dole wataran zasu hadu" Ya farta cikin fushi. "Yar halak?" Ta furta a sarari,sai ta dakata da abinda takeyi ta waiwayo ta zuba masa idanu "Akwai bashi ne tsakaninmu da kake nema na har kalmar kere da zabo zata gitta tsakaninmu?" Kansa ya daure tamau,zallar raina masa hankali da tayi yaga ta fito muraran. Ji yayi bashi da sauran abinda ya rage illa ya fiddo mata makamansa. "Kina iya cewa komai,amma kafin sannan shawara daya zan baki.......ki maido min dukka kudade na da kika samfe daga account dina sawunki a likkafa.....ko kuma hukuma ta matsaki ki fito dasu" Idanunta ta watsa masa tana sakin murmushi "Kasan a inda kudadenka suke?,za kuma ka iya zuwa karba din idan na gaya maka?" A tunzure cikin fushi da yadda takeson maida maganar wata mara alfanu ko muhimmanci ya kalleta "Duk duniya akwai wanda ya isa ya hanani karbar haqqina?,akwai wanda ya isa ya cimin haqqina ban karba ba?" "Kwantar da hankalinka mana...." Tace dashi still tana murmushi,saita dafe kwandonta ta soma takawa tana nufar ficewa daga gidan kuma tana fadin "Gidan marayun nan......a wannan ranar kowanne yaro ya rabauta da duk wani abu na buqata da bashi dashi,suttura kayan ado na 'yanmatan da kuke sakawa ana musu dauki d'ai d'ai cikin dare ana kai muku su gidajen shaqatawarku da hotels kamar yadda ka gayyaceni nima zuwa naka dakin hotel din......kana iya zuwa ka karbi komai dake hannunsu ka sanyashi a kasuwa ka maido kudinka......muddin kuma ba zaka iya hakan ba,to ina baka shawarar ka fita daga rayuwar SABREEN......ka kuma daina bibiyarta......idan bakaji ba kuma......zan sake sakaka fidda wasu kudaden masu ciwo da baka shirya fitarsu ba kamar dai wancan lokacin" Ta qare maganar tana kaiwa qarshen wajen ta karya kwana tana niyyar bacewa ganinsa. Daya biyu uku yahada dukka yaga basuyi masa daidai ba. Wani sashe na zuciyarsa ya soma zugashi da "Ta yaya kana tsaye qaramar yarinya me qarancin shekaru zata nemi raina maka hankali?". Ya samu kansa da kansa da tuhumar kansa tare da ganin tsananin baike da wallensa. Wannan tunanin kadai ya qara masa qaimi,ya taka qafafunsa cikin azama da qwarin gwiwa ya soma rufa mata baya lokacin da takeji a ranta ta kammala siyan duk wani abu da suke da buqata ita da 'yan uwanta,wanann ya sanya ta nufi gurin biyan kudin kai tsaye "Inda zan baka shawara......zaifi kyau ka koma ka tafi sabgaka...." "Saboda ke kike nema na bani ke nemanki ba?,saboda nine mai laifi bake bace?" Hankali kwance ta maqale kafada tana sakin siririn murmushi "A'aha.....ba don dukka wadannan dalilan bane suka sanya ni na baka wannan shawarar ba......na baka ita ne don gudun kada ALLURA TA TONO GARMA" "Ni dake zanga wanda allurarsa zata tono garma......" "Ba laifilaifi malam naseer....." Abinda tace dashi kenan tana ci gaba da tattaki a bayanta. Yau yanason ganin qarshen gudun ruwanta......yanason yasan ita din wace?......da waye take tare?,su waye suka dauki nauyinta?. Waye ya turota?,maqarqashiya ce ko kuma hadin baki?. Hakanan yaci gaba da rufa mata baya tamkar me tsaron lafiyarta ko wanda aka bashi aikin kula da ita. Har cikin zuciyarsa yakejin yau zai nuna mata shi waye,zai kuma tabbatar mata tayi mahaukacin gangancin kuskure data shiga hanyarsa. Mutum biyu suka samu ana lissafa kayansu jikin qaramar na'urar dake da alhakin qididdige fitar kaya cikin katafaren shagon. A hankali ta tsaya daga bayan matar wadda bata iya ganin ainihin fuskarta,saidai shigar atamfar chiganvy gold mix match da wani irin danyen lafiyayyen lace da aka yiwa qawataccen dinkin buba da zani ya fito da kamalarta da kuma cikar siffarta. Tsaye yake daga gefanta,matashin da duka duka shekarunsa ba zasu haura ashirin da takwas ba. Ya bata dukka hankalinsa yana sauraren maganar da takeyi dashi cikin muryarta dake bayyanar da tsantsar kamalarta da cikakkiyar nutsuwar ruhi data halitta. Yanayin yadda ya rusuna ya bata hankalinsa yana saurarenta kadai zai bayyana maka zallar ladabi da kuma ganin girmanta da yakeyi,akwai kuma tag idan ka lura sosai daga gaban aljihunsa dake bayyanar da cewa shi din ma'aikaci ne a wani guri na daban. Mai matsakaicin tsaho ce,hakanan me jiki ce saidai ba qiba me yawa cancan ba,ta lullube saman kanta da 4D Vail me asalin kyau da aka zubawa duwatsu masu daraja akayi adon jiki dasu. Sassanyan qamshinta ya dinga tasowa a hankali daga jikinta zuwa hancin sabreen dake tsaye daga bayanta tana kallon tulin kayan siyayyar da aketa jera mata cikin ledar dake dauke da tambarin store din. Hannunta dake dauke da wasu kyawawan banguls masu sheqi ta miqawa ma'aikacin gurin tana cewa "Bansan me yasa suke son mu'amala da wannan katin bankin ba,duk sun lalace da lamarin cashless" Murmushi ma'aikacin ya saki cikin tsananin girmamawa "To ai hajiya yafi sauqin sha'ani ne" Kai ta gyada a hankali tana furta "To Allah ya kyauta". A nutse ta maida dubanta ga saurayin,tun kafin tace wani abu ya sake matsowa a ladabce yana bata hankalinsa "Ka kiramin wancan yawalen da kuma wancan acicin suzo mu wuce kafin rana ta sake dagawa" "Okay to in sha Allah" Ya amsa mata yana zaro wayarsa daga gaban rigarsa,yayin da ta fara takawa cikin nutsuwa tana ficewa daga gurin hadi da gyara yafen mayafinta dake qoqarin zamewa. Wucewar tata ya bawa sabreen damar matsowa gaba don a lissafa mata nata kayan "Ji mana.......zaki dawomin da duk abinda kika san kin sace ko kuma saimun dangana da hukuma?" Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da ficensu hankali kwance. Yana da ban mamaki......saidai ita din ta fishi abun mamaki. Inda yasan meta taka a kansa......inda tasan cewa kafataninsa.....zahirinsa da badininsa a tafin hannunta yake da baiyi gigin matsawa rayuwarta ba har ya matso gareta har haka ba. A nutse ta waiwayo ta zube masa farare tas din idanunta masu matuqar jan hankali da fusgar tunanin me tunani "Kana sha'awar yin gaba da gaba da hukumar ne?" Ta masa tambayar idanunta a tsaye car tsakiyar nashi. Idan ya kira kansa gogaggen cikin duniya baiyi qarya ba.....muddin kuwa ya kasance hakan yana ganin mugun ganganci ne zaiyi ya gaza samun fikirar karantar mutum daga yanayin kallo zuwa lafuzan bakinsa ba....... "Kina tunanin abune me wahala a gareni?" Ya amsa mata yana mamakin yadda wannan mugun kwarjinin nata yake taka masa burki,kaifin idanunta ke hanashi daukan mataki tare da aiwatar da abinda yayi niyya.......abinda zuciyarsa ke shawartarsa. "Ko daya....daidai ne kuma" Ta amsa masa tana dauke duba da hankalinta daga kanshi tana maidawa ga ma'aikacin wanda ya kammala lissafin yana gaya mata adadin abinda zata biya. "Okay" Ta furta hankali kwance tana maida dubanta ga daya daga cikin ma'aikatan dake taimakawa da wadanda sukayi siyayya me yawa kamarta "Ko zaka fitamin dasu gate na biyu?" "Okay hajiya" Ya fada yana ajjiye qaramar calculator dake hannunsa yana qarasowa gurin tare da jira a gama sanya dukka kayan cikin leda. Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci yakai matakin qarshe a iya haqurinsa "Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai ka kawo qafafunka duk da gargadinka da tayi?" "Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a maimakon basma shi ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani. "Zai biya duka bill din.....na gode sosai" Ta fadiwa ma'aikacin "Naga uban wanda zai sakani biyan kudin nan......na fahimci na sakar miki fa da yawa" Ya furta da zafi sannan a zafafe ya biyo bayanta. Ya tsammaci zata nemi guduwa ko ta gudu dinma,amma ga tarin mamakinsa tun bai qarasa isowa gareta ba taja cak ta tsaya tana sauraron isowarsa. "Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin ruwan dake tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar wannan sirrin da jami'an tsaron dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman ruhi?". Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan burki. Kallonta yakeyi da madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?. Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan binciken da ya bata damar gano birnannen sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki daya bata sani ba?. "Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta qarashe maganar tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen. "Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta katseshi daga bin burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan kudin yana sauke wani irin gauron numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki da tsoro. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 20 ________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_ingancin kaya da kwalliyar mata shine muradinmu_* __________________________ Iya sunan daya kirata dashi ya bayyana mata kanshi tun kafin takai ga waiwayowa. Sanda ta juyo din yana tsaye daga bayanta,ya kafeta da wadannan jarababbun idanun nasa data sanshi dasu tun a lokacin,idanuwan data tsana fiye da kowanne ido a duniya,idanuwan da kuma tafi tsana bayan baqin mugun halayen dake rataye da jiki da zuciyarsa. "Malam nasiru....kana lafiya?" Ta fada calmly tana dauko wani box na chocolate din ta jefa cikin kwando. Takowa ya soma yi yana sake kusantota,har yanzun dai bai dauke idanunsa a kanta ba. Sake daga kai tayi ta kalleshi,sai ta fara tura kwandonta gaba "Kana mamaki ne?.....kayi tunanin bazan iya shaida ka ba ko?" Ta tambayeshi da murmushi a saman wannan miskilar fuskar da zaiyi wahala kaga fitar murmushin daga samanta. "Wannan basman bata manta fuskar mutanen da suka taba shigowa cikin rayuwarta.......hakanan wannan basman bata manta fuskar mutane irinku......hope kana lafiya ko?" Ta sake tambayarsa tana tafiya a nutse,tana kuma ci gaba da zaban abinda yayi mata tana jefawa a kwandon. Tarin mamaki ne ya lullube masa zuciya ainun......tsahon lokutan yayi tunanin duk ranar da sukayi haduwa ta farko da ita zata razana......zata kuma tsorata,idan da yiwuwar ma ta nemi guduwa duka zatayin duba da girman laifin data aikata masa. "Tana da wayo......tana kuma da hadari......da alama akwai abinda ta taka" Maganar abokinsa kenan ta dawo cikin kansa bayan wani zama da sukayi dashi,wannan ya sanyashi Maida hankalinsa jikinsa sosai,ya kuma tattaro bacin rannan da ta dasawa zuciyarsa wanda har yanxu a cikin bala'i da masifar data sakashi yake "Idan kika mantani ai baki cika 'yar halali ba......ai dama idan kere na yawo zabo na yawo dole wataran zasu hadu" Ya farta cikin fushi. "Yar halak?" Ta furta a sarari,sai ta dakata da abinda takeyi ta waiwayo ta zuba masa idanu "Akwai bashi ne tsakaninmu da kake nema na har kalmar kere da zabo zata gitta tsakaninmu?" Kansa ya daure tamau,zallar raina masa hankali da tayi yaga ta fito muraran. Ji yayi bashi da sauran abinda ya rage illa ya fiddo mata makamansa. "Kina iya cewa komai,amma kafin sannan shawara daya zan baki.......ki maido min dukka kudade na da kika samfe daga account dina sawunki a likkafa.....ko kuma hukuma ta matsaki ki fito dasu" Idanunta ta watsa masa tana sakin murmushi "Kasan a inda kudadenka suke?,za kuma ka iya zuwa karba din idan na gaya maka?" A tunzure cikin fushi da yadda takeson maida maganar wata mara alfanu ko muhimmanci ya kalleta "Duk duniya akwai wanda ya isa ya hanani karbar haqqina?,akwai wanda ya isa ya cimin haqqina ban karba ba?" "Kwantar da hankalinka mana...." Tace dashi still tana murmushi,saita dafe kwandonta ta soma takawa tana nufar ficewa daga gidan kuma tana fadin "Gidan marayun nan......a wannan ranar kowanne yaro ya rabauta da duk wani abu na buqata da bashi dashi,suttura kayan ado na 'yanmatan da kuke sakawa ana musu dauki d'ai d'ai cikin dare ana kai muku su gidajen shaqatawarku da hotels kamar yadda ka gayyaceni nima zuwa naka dakin hotel din......kana iya zuwa ka karbi komai dake hannunsu ka sanyashi a kasuwa ka maido kudinka......muddin kuma ba zaka iya hakan ba,to ina baka shawarar ka fita daga rayuwar SABREEN......ka kuma daina bibiyarta......idan bakaji ba kuma......zan sake sakaka fidda wasu kudaden masu ciwo da baka shirya fitarsu ba kamar dai wancan lokacin" Ta qare maganar tana kaiwa qarshen wajen ta karya kwana tana niyyar bacewa ganinsa. Daya biyu uku yahada dukka yaga basuyi masa daidai ba. Wani sashe na zuciyarsa ya soma zugashi da "Ta yaya kana tsaye qaramar yarinya me qarancin shekaru zata nemi raina maka hankali?". Ya samu kansa da kansa da tuhumar kansa tare da ganin tsananin baike da wallensa. Wannan tunanin kadai ya qara masa qaimi,ya taka qafafunsa cikin azama da qwarin gwiwa ya soma rufa mata baya lokacin da takeji a ranta ta kammala siyan duk wani abu da suke da buqata ita da 'yan uwanta,wanann ya sanya ta nufi gurin biyan kudin kai tsaye "Inda zan baka shawara......zaifi kyau ka koma ka tafi sabgaka...." "Saboda ke kike nema na bani ke nemanki ba?,saboda nine mai laifi bake bace?" Hankali kwance ta maqale kafada tana sakin siririn murmushi "A'aha.....ba don dukka wadannan dalilan bane suka sanya ni na baka wannan shawarar ba......na baka ita ne don gudun kada ALLURA TA TONO GARMA" "Ni dake zanga wanda allurarsa zata tono garma......" "Ba laifilaifi malam naseer....." Abinda tace dashi kenan tana ci gaba da tattaki a bayanta. Yau yanason ganin qarshen gudun ruwanta......yanason yasan ita din wace?......da waye take tare?,su waye suka dauki nauyinta?. Waye ya turota?,maqarqashiya ce ko kuma hadin baki?. Hakanan yaci gaba da rufa mata baya tamkar me tsaron lafiyarta ko wanda aka bashi aikin kula da ita. Har cikin zuciyarsa yakejin yau zai nuna mata shi waye,zai kuma tabbatar mata tayi mahaukacin gangancin kuskure data shiga hanyarsa. Mutum biyu suka samu ana lissafa kayansu jikin qaramar na'urar dake da alhakin qididdige fitar kaya cikin katafaren shagon. A hankali ta tsaya daga bayan matar wadda bata iya ganin ainihin fuskarta,saidai shigar atamfar chiganvy gold mix match da wani irin danyen lafiyayyen lace da aka yiwa qawataccen dinkin buba da zani ya fito da kamalarta da kuma cikar siffarta. Tsaye yake daga gefanta,matashin da duka duka shekarunsa ba zasu haura ashirin da takwas ba. Ya bata dukka hankalinsa yana sauraren maganar da takeyi dashi cikin muryarta dake bayyanar da tsantsar kamalarta da cikakkiyar nutsuwar ruhi data halitta. Yanayin yadda ya rusuna ya bata hankalinsa yana saurarenta kadai zai bayyana maka zallar ladabi da kuma ganin girmanta da yakeyi,akwai kuma tag idan ka lura sosai daga gaban aljihunsa dake bayyanar da cewa shi din ma'aikaci ne a wani guri na daban. Mai matsakaicin tsaho ce,hakanan me jiki ce saidai ba qiba me yawa cancan ba,ta lullube saman kanta da 4D Vail me asalin kyau da aka zubawa duwatsu masu daraja akayi adon jiki dasu. Sassanyan qamshinta ya dinga tasowa a hankali daga jikinta zuwa hancin sabreen dake tsaye daga bayanta tana kallon tulin kayan siyayyar da aketa jera mata cikin ledar dake dauke da tambarin store din. Hannunta dake dauke da wasu kyawawan banguls masu sheqi ta miqawa ma'aikacin gurin tana cewa "Bansan me yasa suke son mu'amala da wannan katin bankin ba,duk sun lalace da lamarin cashless" Murmushi ma'aikacin ya saki cikin tsananin girmamawa "To ai hajiya yafi sauqin sha'ani ne" Kai ta gyada a hankali tana furta "To Allah ya kyauta". A nutse ta maida dubanta ga saurayin,tun kafin tace wani abu ya sake matsowa a ladabce yana bata hankalinsa "Ka kiramin wancan yawalen da kuma wancan acicin suzo mu wuce kafin rana ta sake dagawa" "Okay to in sha Allah" Ya amsa mata yana zaro wayarsa daga gaban rigarsa,yayin da ta fara takawa cikin nutsuwa tana ficewa daga gurin hadi da gyara yafen mayafinta dake qoqarin zamewa. Wucewar tata ya bawa sabreen damar matsowa gaba don a lissafa mata nata kayan "Ji mana.......zaki dawomin da duk abinda kika san kin sace ko kuma saimun dangana da hukuma?" Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da ficensu hankali kwance. Yana da ban mamaki......saidai ita din ta fishi abun mamaki. Inda yasan meta taka a kansa......inda tasan cewa kafataninsa.....zahirinsa da badininsa a tafin hannunta yake da baiyi gigin matsawa rayuwarta ba har ya matso gareta har haka ba. A nutse ta waiwayo ta zube masa farare tas din idanunta masu matuqar jan hankali da fusgar tunanin me tunani "Kana sha'awar yin gaba da gaba da hukumar ne?" Ta masa tambayar idanunta a tsaye car tsakiyar nashi. Idan ya kira kansa gogaggen cikin duniya baiyi qarya ba.....muddin kuwa ya kasance hakan yana ganin mugun ganganci ne zaiyi ya gaza samun fikirar karantar mutum daga yanayin kallo zuwa lafuzan bakinsa ba....... "Kina tunanin abune me wahala a gareni?" Ya amsa mata yana mamakin yadda wannan mugun kwarjinin nata yake taka masa burki,kaifin idanunta ke hanashi daukan mataki tare da aiwatar da abinda yayi niyya.......abinda zuciyarsa ke shawartarsa. "Ko daya....daidai ne kuma" Ta amsa masa tana dauke duba da hankalinta daga kanshi tana maidawa ga ma'aikacin wanda ya kammala lissafin yana gaya mata adadin abinda zata biya. "Okay" Ta furta hankali kwance tana maida dubanta ga daya daga cikin ma'aikatan dake taimakawa da wadanda sukayi siyayya me yawa kamarta "Ko zaka fitamin dasu gate na biyu?" "Okay hajiya" Ya fada yana ajjiye qaramar calculator dake hannunsa yana qarasowa gurin tare da jira a gama sanya dukka kayan cikin leda. Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci yakai matakin qarshe a iya haqurinsa "Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai ka kawo qafafunka duk da gargadinka da tayi?" "Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a maimakon basma shi ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani. "Zai biya duka bill din.....na gode sosai" Ta fadiwa ma'aikacin "Naga uban wanda zai sakani biyan kudin nan......na fahimci na sakar miki fa da yawa" Ya furta da zafi sannan a zafafe ya biyo bayanta. Ya tsammaci zata nemi guduwa ko ta gudu dinma,amma ga tarin mamakinsa tun bai qarasa isowa gareta ba taja cak ta tsaya tana sauraron isowarsa. "Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin ruwan dake tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar wannan sirrin da jami'an tsaron dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman ruhi?". Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan burki. Kallonta yakeyi da madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?. Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan binciken da ya bata damar gano birnannen sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki daya bata sani ba?. "Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta qarashe maganar tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen. "Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta katseshi daga bin burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan kudin yana sauke wani irin gauron numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki da tsoro. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* PAGE 21 https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz __________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* ____________________________ Sanda take sallamewa saita samu kanta da zama sosai a inda ta idar da sallar tana irga tasbihi da yatsun hannunta,yayin da kunnuwanta kadan kadan ke jiye mata tasbihin matar dake yinsa can qasa qasa,saidai lokaci lokaci yana qwacewa ya fito,har zuwa sannan bata waiwaya ko sau daya ta kalli fuskarta ba,amma daddadan turarenta bai fasa silalowa zuwa cikin hancinta ba. Wayarta ta matsa haske ya bayyana ta duba lokaci. Tasan ko busari bai iso ba to dab yake da isowar,ta maida wayar ta ajiye tana kallon sararin cikin masallacin da babu kowa saisu uku. Daidai sanda zata dauke idanunta dai dai sannan taji matar dake gefan nata taja wani irin qaqqarfan salati numfashinta yana yayyankewa. A tsorace ta waiwaya gefan damanta... Hannuwanta dukka biyun na tallafe da qirjinta,tana kuma daga kanta sama tare da qoqarin maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Saidai tana kakkamota ne da qyar saboda yadda numfashin yake son qwace mata. Da hanzari ta miqe,hanzarin daya sanyata cilli da wayarta dake saman cinyarta. Jikinta dukka yana rawa a gaggauce ta matsa jikin matar "Lafiya?,me yake faruwa?" Ta furta cikin matuqar tsoro da kuma rudanin ganin yadda take kaman shirin rasa numfashinta. Bata iya amsa mata ba,wannan ya sanya sabreen zama sosai ta tallafeta da kyau zuwa jikinta tana sake maimaita tambayarta a rude "Ina ganin kaman asthma attack ne" Mace guda dayan data rage a cikin masallacin ta furta bayan ta iso wajen itama tana dubanta "Asthma?" Sabreen ta furta a gigice tana jin wani abu yana dukan zuciyarta. Shine ciwo guda daya da kullum taji sunansa sai zuciyarta ya tsinke,ciwo qwaya dayan da kullum takewa mummunan kallo,ciwo guda dayan da yayi silar wasu jigo na rayuwarta,har ila yau ciwo qwaya daya da yake wujijjiga rayuwarsu. Da sauri ta finciko jakarta bayan da tunaninta ya dawo,ta zugeta da hannu daya daya hannun yana tallafe da ita,ta daga jakar ta zazzage duka tarkacen dake ciki,cikin matuqar sa'a ta hangi inhaler dihta. A gaggauce ta dauka ta kara mata,hannuwan matar dukka rawa suke sanda ta dora nata hannun saman na sabreen kamar tana son tayata matsa inhaler din,kamar tanason nuna mata tsananin buqatarta da takeyi. Cikin mintuna qalilan ta fara samuwa,saidai har yanxun bata daidaita yadda ya kamata ace ta daidaita din ba. Oily eyes dinta sun cika taf da qwalla "Kamar asibiti tafi buqatar a kaita" Ta kasa haquri har sai da bakinta ya furta hakan "Zaifi kyau dai gaskiya don da alama tana buqatar iska sosai". Dai dai sannan wayarta data watsar ta dauki ringing. Matar ce ta matsa ta miqo mata,ta sanya hannu ta karba tana fadin " Na gode" Tana duba me kiran. Busari ne,ta latse wayar tana karawa a kunnenta "Na qaraso,ina dab da bakin masallacin" "Ka karba kayana wajen me gadi,gani nan fitowa asibiti zamu wuce" Bata tsaya sauraren abinda zai fada ba ta katse kiran. Idanunta ta mayar saman fuskar matar. Wani abu taji ya taba zuciyarta,sai takejin kamar umminta ce ta dawo,sai takejin tamkar lokacin data rasa umminta. A duk sanda take mutum me dauke da irin ciwon tsananin tausayinsa yake kamata,duk da itama abar tausayin ce. Duk sanda taga babbar kaman haka yana fafutuka da wannan ciwon sai ta dinga tuna umminta. Su biyun suka tallafeta don taji qwarin jikinta,suna takowa a hankali da ita har suka fito zuwa inda Kekenapep din yake "Zan samu face mask a wajenka?" Ta tambayi busari. "Eh hajiya" Ya amsa mata da sauri yana bude aljihun motar ya fidda shi sabo fil ya bata. A kusa da ita ta zauna tana riqe da face mask din,saita sauke idanunta qasa tana jujjuyashi. "Zan saka miki wannan saboda iskan mota,motan bana gida bane". Idanunta saman fuskar yarinyar,har zuciyarta tana jin qauna da jinjina taimakonta a kanta,ta lura tana d'anjin wani nauyi da kuma rashin sakewa. Qaramar yarinya haka me zuciyar taimako?,sai abun ya qayatar da ita. Mintuna ashirin daidai suka qarasa private hospital din,wanda a nan file nata dana qannenta dukka yake. Tuntuntuni ta sallama asibitin gwamnati,yana daya daga cikin muhallan da suka samarwa rayuwarta gibi,yana daya daga cikin guraren da suka dasa qaton tarihi a rayuwarta,suka kuma ajiye mata wani tabo na har abada,shi ya sanya daga sanda ta samu dama ta nisanta kanta da dukkaninsu daga asibitin gwamnati. Private hospital ne daya amsa sunanshi,babu nau'in wata kulawa da mara lafiya baya samunta,saidai kuma kudi ne zasu fita sosai daga aljihun majinyaci ko ahalinsa. Private room suka bata,cikin mintuna goma sha biyar kacal suka bata dukkan taimakon daya dace,bata samu nutsuwa ba sai da suka shafe awa guda taga bacci sosai ya dauketa tana sauke numfashin a hankali ta cikin oxygen din da suka maqala mata saboda yadda taso galabaita sosai. Zama tayi kawai gabanta bayan taja kujera,ta maqale hannunta a qirji bayan ta zube idanunta a kanta tana dawo da bayanan da likita yayi mata a kanta. "Ta samu mummunan attack ne,tana samun kulawa sosai to amma kuma kaman yanayi ya nuna ba'a kiyaye wasu dokoki na masu ciwon,sannan kuskure ne ta dinga fita hakanan ba tare da inhaler ko wani a kusa da ita ba". Idanunta ta qanqance sosai tana ci gaba da nazarin maganganunsa. Hakanan sai taji ranta yayi matuqar baci,indai har mace me irin wannan shekarun bata samu kulawa ba sai yaushe?,indai har ba za'a kula da dokokin da aka bata ba meye amfanin makusantanta?. Dukkan alamu sun nuna,tun daga suturar jikinta da komai nata ma cikin wadata da sukunin rayuwa take ainun,to meye zai hana su su bata kulawa su ahalin nata?. Idan zata iya tunawa mutum daya ne ta gansu a tare a tsaye cikin store din,har tana bada umarnin a kira mata wani data kira a cici da kuma yawale. Yawonsu kenan yafi musu kasancewa da ita?,yanzu haka fa mahaifiyarsu ce amma sun gwammaci tafiya yawo akan su bata kulawa?. Iska me zafi ta sake fesarwa ranta yana sake tunzura musamman bayan data duba agogon hannunta. Aqalla awa daya harda rabi da barowarsu store din amma har yanxun basu biyo address na asibitin data barwa wancan matar sun biyo bayan baiwar Allahn ba?. Sake juya wayarta tayi su huda suna fado mata a rai. Ta tabbatar zuwa yanzun sun dawo gida,suna can kuma zaune su daya a daki. Karon farko da taji kaman ya kamata ta siya waya ko qwaya daya ce ta ajiye cikin dakin saboda lalura irin haka,ko ba komai ba zata barsu cikin zulumi ba,zata kira taji lafiyarsu suma suji lafiyarta,duk kuwa da cewa komai runtsi a gida takeyin magrib. Daidai sanda tunaninta yakai nan taji an murda handle na qofar. Kyakkyawan matashin ne ya fara bayyana. Dogo me matsakaicin haske. Kai tsaye idan kace masa kyakkyawa bakayi kuskure ba,yana da cikakkiyar suma me santsi tun daga kansa zuwa habarsa. Yana sanye da dakakkiyar shaddar getzner Neautaral color daketa yauqi da sheqi. Yanayin dinkin da aka yiwa shaddar yayi masifar dacewa da structure na jikinsa. Dinkin zamani dake nuna zallar gogewa da wadatar arziqi na wanda suturar ke kwance a jikinsa. Yadda shaddar ke walqiya hakanan hular kansa,wadda koda ba'a gaya maka kudinta ba zakasan cewa bada qaramin zare aka saqata ba. Qafafun sanye cikin takalmin Batozzi,hakanan cikin qasa da second biyar dakin ya gauraye da sassanyan qamshin turarensa. "Hamma mun sameta,gata tana bacci" Ya furta da kwantacciyar muryarsa da alama kuma yana magana ne da wani a wayar dake manne a kunnensa,dukka hankalinsa da idanuwansa suna kan matar dake kwance cikin mazari yana d'okin isa gareta. "Okay hamma......in sha Allah" Ya sake fadi da sauri sannan ya jefa wayar a aljihunsa yana isa inda take kwancen ba tare daya damu ya kashe wayar ba. Rusunawa yayi sosai a gabanta yana riqe da hannunta da dukka hannayensa biyun. Yayi wani irin laushi,don idan ka kalli hannunsa da kyau kana iya ganin yadda suke danyin rawa. Dauke dubanta tayi daga kansa haushinsa yana saukar mata,saita maida kallonta akan wanda suka shigo din tare. Shine dai wanda ta gansu cikin store din tare wanda ta bari ya biya kudin siyayyar da tayi. "Kamar kece kika kawota ko?" Ya fadi saboda hada idanu da sukayi. Maganar tashi taja hankalinsa,yadan sassauta riqon da ya yiwa mara lafiyan ya kuma waiwayo da dukka nasa idanun yana dubansu,don shi sam sam bai ma lura da kowa ba a wajen. Kamar yayi mata susa ne a inda yake mata qaiqayi,sai ta miqe a nutse tana saqala Jakarta a kafadarta,haushinsu yana sake turniqeta "Eh nice bayan kun yasar da ita kun kama gabanku ba?,waishin kunsan muhimmancinta kuwa?,kunsan yadda ciwonta ke buqatar a dinga yawan kulawa da ita musamman ita da shekarunta suka fara yawa?. Ji yayi maganganunta sunyi girma ainun,tasan wace ita din a wajensu har da zataga gazawa da kasawarsu?. Saidai bai datseta ba saboda yadda yaga hawaye suna cika idanunta "Mutane da yawa basusan muhimmancin iyaye ba sai sanda suka rasasu......amma ku sani cewa......yadda suka baku kulawa a sanda bakusan muhimmancin rayuwa ba.....ba komai bane don kun basu kulawa a sanda sukasan muhimmancin nasu rayuwar......ba kowa a kusa da ita.....ba inhaler.....yanzu inda numfashinta ya katse fa?" Ta qarashe fada adan tsawace hawayen na fara gangarowa ta idonta qwaya daya,sai tayi hanzarin kauda kanta gefe ta dauke hawayen da yatsanta. Su kadai sukasan yanayin da suke shiga idan ciwon ya tasar musu shi yasa babu me fahimtar abun sai wanda ke cikin yanayin "Kuji tsoron Allah ku kula da ita yadda ya dace,don yadda muke amana a hannun iyaye haka suma amana ne a hannunmu,kuma Allah zai tambayemu game da yadda muka kula da tsufansu" Tana kaiwa nan ta soma takawa tana ficewa daga dakin. Gaba daya mamakinta ya cikashi,yadda take haqiqancewa ba tare da tasan komai a kansu ba. Mahaifiyarsa itace rauninsa har abada.....wani abu guda daya me matuqar tsada da muhimmancin da ba madadinta. Har ta fice ya kasa tsaidata kaman yadda yaso har sai data bacewa ganinsu. "Bita ka tsaidata......a qalla ko godiya ya kamata muyi mata,sannan kuma muji yadda za'a maida mata kudaden data kashe tunda na samu an biya bill na komai" "Okay" Ya furta a girmame yana juyawa ya fice a dakin. Kamar wayar dake aljihunsa yaji yana motsi,ya dafe wayar sai kuma ya sanya hannu ya fiddota da sauri. Mamaki ya kamashi,ya akayi bai kashe wayar ba. Hamman ne har yanzu akan layi,duka mintunan da sukayin wayar na a kunne,sai ya maida wayar kunnensa "Waye yake mata fada saman kai?" Ya furta nutse "Wanda ta kawota ne daga can store din" "Don ta kawotan take ma mutane fada?" Ya furta adan harzuqe "No hamma...." Ya fadi da sauri. Numfashi yaja yana ware idanunsa sosai "Stop......banason a sake mata hayaniya a wajen nan....if not ran kowa zai baci" "In sha Allah hamma" "Idan ta farka ta dawo daidai give me a call" "Done" Ya fada a taqaice kafin ya yanke masa waya,yana gama fadin kuwa yaji qit ya gintse wayar,saiya cireta daga kunnensa yana girgiza kai. "Hamma.....hamma" Ya maimaita sau biyu. Koda cewa tayi fada cikin yanke hukunci akan abinda bata sani ba.....bata da yaqini amma shi baiga laifinta ba,ya mata uzuri......hasalima ta burgeshi qwarai,dukkan alamu yana nuna tasan darajar dan adam ne,sai ya maida hankalinsa akanta yana duba shiga da fitar numfashinta. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 22 __________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* ____________________________ Batasan me yasa ba,batasan dalilin da ya sanyata takejin bacin rai sosai akan abun ba. Ta dinga fidda numfashi me dumi a hankali daga baki zuwa hancinta. Cikin nutsatsen takun nan nata take nufar inda tabar busari yana jiranta. Takun da yayi matuqar tafiya da hankali da tunaninsa baya ga zubin mamallakin takun. "Wai har yanzu akwai irin mata masu wannan ajin?" Ya furta qasa qasa ba tare da yasan a waje yayi maganar ba,tana ta'allaqa dubansa a kanta,yana jin tana tafiya da gaba daya kuzari tunaninsa dama hankalinsa gaba daya. Tamkar an zungureshi ko kuma anyi masa qaimi,sai ya saka hannu da wani irin hanzari yana bude murfin motar. Sam gaba daya ya manta da dalilin daya kawosu asibitin,ya kuma manta ma da waye yake tare,burinsa guda daya tal! A yanzu,ya samu isa gareta,yakuma samu daman yin magana da ita. Sallamar tashi ta ratsa kunnenta a sanda take dab da isa wajen da Kekenapep din yake. Ta lumshe idanunta a nutse tana riqe masaqalin jakarta da kyau. Dama tasan hakan zata iya faruwa duba,zaiyi wahala a kallon farko da tayi masa ya iya tsallake halaye da kuma dabi'uj data hanga kai tsaye daga gareshi. "Assalamu alaikum.....don Allah....." Ya katse maganar tashi da kan kanshi lokacin da yasha gabanta idanunsu suka gauraya waje daya. Wani kwarjini na musamman,wani yanayi ya tsarga masa irin wanda bai taba jin irinsa ba. Nashi idanun ya janye a hankali yana qoqarin daidaita kansa tare da zallar mamaki yana kuma tambayar kansa "Meye haka?,ita din wace?". Baisan iya adadin kalar matan daya gani ba tun da ya fara zama cikakken namiji zuwa yau. Baisan adadin matan da yayi mu'amala dasu ba daga jinsin yare daban daban,amma yau daya wata mace da baya tunanin ta rufa shekara ashirin da biyar a duniya na neman yi masa kwarjini?. "Lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsuke fuskarta tare da sake bada tazara tsakaninsu. Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi,sai ya sake mata murmushi hadi da gyara tsaiwarsa sosai a gabanta,yana jin ba wata mace da zata iya kaucewa tarkonsa muddin ya d'ana shi. "Ba lafiya ba......maganar gaskiya kenan.......akwai gagarumin tashin hankali" A mamakance take duba fuskarsa tana yamutse tata tare da qoqarin sakeyi masa sabon karatun da baisan tana yi ba "Amma fa a zuciyata" Ya qarashe maganar yana dafe qirjinsa. Numfashi taja sosai har cikin huhunta sannan ta fesar tana kauda kanta gefe hadi da juya qwayoyin idanunta. Ba shine mutum na farko data taba gamuwa dashi me irin wannan salon ba,don haka tafiyar dashi bazai bata wahala ba. Dukkan wani d'a namiji da zai ratso rayuwarta tayi imanin QADDARARSA ce a nan.......da kuma zallar tsautsayi. Mafi rinjaye daga cikinsu kuma SON RAI da SON ZUKATA. Ba kasafai ta fiya bada kai ta farat daya ba,koda ta tsara amsarka,don tuni ta fahimci duk wani abu da akeson yayi daraja.....kar a bari samuwarsa ta zama ta sauqi. Don haka ta soma tattaki da zummar kubcewa daga gabansa. A gaggauce ya sake tare mata gaba yana dubanta cikin marairaicewa "Ranki ya dade.......na tabbatar girmanki yafi gaban a tsaidaki a hanya....to amma muddin na barki kika wuce din nayi imanin sa'ata ta rayuwa ce ta kubcemin gaba dayanta......ki tallafeni ki sammin minti uku kacal" Ya furta yana nuna yatsunsa guda ukun. Juyowa ta sakeyi a karo na uku tana kallonsa. Ya fiya zaqin baki da yawa,maza irinsa suna da wani hali da dabia da tuni ta gama karatunsa. Tabbas akwai wani abu tattare dashi da wata qila take nema......tana hasashen yiwuwar samun wata qaruwa me girman gaske. Taga irinsa ba daya ba.....ba biyu ba....ba uku ba,har ba zata iya tantance adadi ba. Duk da wannan hasashen amma bata yarda ta nuna masa komai ba. Sai ta sake kau da kanta tana yamutsa fuska "Matsawarka daga hanyata kamar zaifi zame maka alkhairi akan ci gaba da tsaiwar......ina da tarin abubuwa a gabana....." "Bansan ko me ke jiranki ba......amma na tabbatar koda baikai wannan tsaiwar tamu alkhairi ba bazai wuceta ba" Ya fadi a zaqe da fatan samun nasara "Na roqeki kada ki watsan qasa a idanu,ki wofantar da wannan kyakkyawar damar a garemu gaba daya" Ya fadi yana marairaicewa tare da miqa mata wayar hannunsa yana kasheta da idanu gami da karyar da wuya da raunanar da idanun nasa. A nutse ta sauke kallonta akan wayar ta kalla. Tsaleliyar iPhone 16 wadda kana dubanta zakasan bata wani jima da baro dumin kwalin da aka qerata ba. A yangance ta dauke kanta daga kai ta sake maidawa gefanta bayan. Wani numfashi ya fusga da qyar bayan ya gama sauraren jerin lambar wayarta data karanto masa. Sautin muryar nata yana masa wani irin amsa kuwwa a kunnensa. Karon farko daya yadda cewa muryoyin wasu matan kadai suna iya haddasa fitina a zukata da gangar jikkunan maza. Sai yakejin yana sake zurfi ason ya kasance a tare da ita "Sai nakega kaman girma da martabarki ya dara kihau napep.....da zai yiwu da kin sadaukarmin da wannan tsadajjen lokacin na saukeki a gida....." Yana ajewa tana daga masa hannunta,sannan ta fara takawa tana wucewa cikin abun hawan da busari ke jiranta. Har ya bawa napep din wuta suka fice daga harabar asibitin yana tsaye a gurin. Sai daya tabbatar sun qwacewa ganinsa sannan ya buga qafarshi yana yarfar da hannunsa,wani shu'umin murmushi yana kubce masa. Ba shakka ita din ME ZAFI ce,ta kuma cancanci dukkan wannan dagawar da kuma jan ajin. Yana da makamai a hannunsa masu tarin yawan da zai iya yaqar zuciyarta yakuma yi nasara ba shakka ko kokwanto. Makami guda daya da dukkan namijin daya mallakeshi yake iya sanya kaza ta kwanta ta yanka masa kanta ta gasa ta kuma kawo kanta da kanta har inda yake don biyan buqatar ranshi. Iya wassafa samuwar nasara kadai a gareshi ya sanya murmushi ya subuce masa. Ya sake buga qafa yana wassafa irin yadda zai tsikari rayuwarsa da tsinke yadda ya kamata "Dole na qarawa kaina kusanci da dukkan qofofin da zasu budemin manya manyan qofofin taskokin da zan miki hidima dasu don mallakar muradina" Ya furta a sarari yana qanqance idanu,muradinsa yana sake ninkuwa,burikansa suna sake fadada. Daidai qofar gidan nasu busari ya ajiiyeta bayan ya fiddo mata dukan kayan daga cikin motar. Cikin farfajiyar gidan ya ajiiyeta mata kayan sannan ya juya yana komawa ciki. Tsaye tayi a farfajiyar gidan da iskar la'asar ke kai kawo. Ba wadatar yara sam,wanda koda ace akwai wadatar nasu tasan cewa ba kowa ne a cikinsu ke aikuwa ba. Kayan sun mata nauyin da ba zata iya dauka ba,tana tsaka da wanna tunanin ta hangi fitowarfitowar nadra,haneefa na biye da ita. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 23 ___________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* __________________________ Nadra,haneefa na biye da ita Dukansu suka watsar da abinda ke hannunsu sannan suka nufota. Fuskokin dauke da madaukakiyar fara'a wadda har tsakiyar zukatansu ta ratsa. Ita daya ce HASKE GIDANSU.....ita daya ce FARINCIKINSU hakanan ita kadai ce BAQINCIKINSU. Rashinta a kusa dasu yakan debe dukkan wata walwala da sakewa tasu,duk da tarin jamaar dake rayuwa a gidan amma duk sanda bata nan din suna jin gidan kamar babu kowa a ciki saisu. Cikin jikinta ta rungumesu kaman yadda ta saba,sannan nadra din ta soma jan daya daga cikin ledojin. Duqawa haneefa tayi itama zata dauki guda daya nadra din ta tsaidata "Bafa zaki iya dauka ba" Cak ta tsaya tana turo baki "Anty wai da gaske bazan iya ba?" Murmushi ya qwace mata saboda hangen farincikin da tayi daga idanuwansu. "Zaki iya auta" Ta furta tana bude ledar,jakankunan maggi da suka qarawa ledar nauyi ta ajjiye a gefe sannan ta daure mata ledar tana cewa "Bismillah auta aiba raguwa bace" Hakan ya faranta mata rai,ta sukunya ta dauki ledar tana cewa "Ita yaaya nadra kullun komai sai tace bazan iya ba,batasan na fita qarfi ba" Daga sabreen din har nadra data riga tayi gaba suka saki dariya. Idonta a kansu har suka mata nisa sannan ta tsugunna a nutse ta kwashe maginta,ta fara takawa tana binsu zuwa Qofar da zata sadasu da babban tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye tana hangen haneefa daga nesa. Ta sake sakin boyayyen murmushi,akwai jarumta me yawa dangane da yarinyar,da alama zuciyarta dakakkiya ce kuma a tsaye take. Dab da zata shiga din su kuma suna yunqurin fitowa su biyu. A hankali taja da baya tana basu hanya bayan ta sauke idanunta qasa,saidai duk da hakan da tayi bai sanya ta tsira daga garesu ba. Qasan ranta akwai haushi takaici da kuma fushin rashin samun nasarar da batayi ba a safiyar dazu. "Ke ya kamata mu bawa hanya ta wuce ai......gagara" Ta furta tana qanqance idanu idanun nata fes akan Fuskarta da kuma abinda ta riqo a hannayenta. A hankali daada dake tsaye daga bayan bibo din ta gewayo ta gefanta tana cewa "Muje mana bibo,yamma tana sakeyi" "K'nnnn,gaskiya dai,fitar dare ai 'yan kwalta" Ta fada tana zakudawa tare da bin bayan daada bayan ta waiwayo ta ajewa sabreen wani kallo. Da kallon itama ta bisu,sam ko kadan daada bata nuna ta santa ko tasan da zamanta......nata da sauqi don kome za'ayi a kansu baka taba jin ta tofa nata........batasan wanne matsayi zata aje daada ba a kanta cikin gidan,ta bibo kuwa fitacciya ce ainun,muddin magana ce a kansu,Ala cuta ala magani har abada bare ya fiye mata su,koda kuwa wanne irin nau'in alkhairi zasuyi mata ko zasu kowa cikin gidan. Ajiyar zuciya ta saki tana ci gaba da kutsa kanta cikin gidan tana ta qoqarin kauda abinda takeji a yau yana taso mata qasan zuciyarta. Abune da take ganin bai kamata ta damu ba......ita din dai tasan kanta,ta yarda da kanta,sannan tasan wacece ita?,to me ya rage?,me take nema da shaidar mutumin yau?,mutanen dake rayuwar a DUNIYARta sam basu cancanci ta basu damuwarta ko tayi yunqurin gamsar dasu game da WACECE ITA?. Da sallama a bakinta ta sanya qafafunta cikin falon nasu,komai a tsaftace a kuma tsare,madaidaiciyar iska me dadi tana kai kawo tsakanin falon ta wutar sola dake maqale a dakin. Sanda take zubewa saman kujera daidai lokacin haneefa ke isowa gabanta da school bag dinta da wani.littafinta a hannu "Anty munyi C.A,a cikin talatin na samu ashirin da takwas......sannan an bamu assig....." "Kai haneefa haba" Nadra ta fasa tana hade fuska. Murmushi ta saki,saita dagawa nadra hannu "Qyaleta,zo.nan auta" Ta kirata sanda huda ke qarasowa ta aje mata ruwan pure water me sanyi guda biyu "Ki aje komai sai zuwa anjima zan duba,duka yau tare zamuyi assignment din kinji?" Kai ta daga tana murna ta cilla da gudu ta koma bedroom dinsu da jakar. Sai data bula ruwan sannan ta kalli huda "Me yasa baku wuce islamiyya ba?" Gyara zamanta kadan tayi sannan tace "Jiran dawowarki mukeyi" Rabi tasha ruwan ta ajjiye tana sake karantar wani yanayi na daban daga huda din "Sai na dawo sannan zakuje Islamiyya huda?,yaushe aka fara wannan tsarin a dakin nan?" Tadan furta a zafafe tana dubanta. Qasa da kant huda din tayi,ba kasafai take ganin fushi ko fada dava Fuskarta ba,to amma duk sanda tayi din ya tabbata laifi sukayi mata babba. "Kiyi haquri.na tsaya dora abinci ne" Sassautowa tayi kadan tana sauke boyayyen numfashi. Bata qaunar abinda zai zaunar dasu cikin gidan ko kadan ballantana idanuwa ko kunnuwansu suji ko suga abinda rayuka zasu baci. Hakanan koda wasa bata qaunar suyi wasa da makaranta. Tana jin ciwo idan ta tuna iya inda matakin karatunta ya tsaya a shekaru ashirin da daya hudu da take dashi a duniya,wanda a yanzun kimanin shekaru hudu kenan rabonta da wata bawa wai makaranta. "Ku shirya ku wuce,duk da lokaci ya fita amma baiyi nisa ba ai" Ta fadi tana duba agogon hannunta sannan ta fara zareshi daga hannunta. Tana zaune dukansu suka gama shiryawa cikin fari qal din uniform da baqar doguwar riga daga sama. Hankalinta bai dawo daidai ba sai data tabbatar sun fita a gidan. Kai tsaye ta rage kayan jikinta ta zura sassauqar riga sannan ta wuce kitchen din dake falon tana duba girkin da huda ta fara yi. Komai yayi daidai,dole ta sanya huda ta koyi girki tun batakai minzali ba. Tana fita ta bar mata nadra da haneefa,tun bata san ya zata kula dasu ba har ta koya. Ko a yanzun idan huda tayi girki,itama tayi sai na huda ya dara nata. Sai data kammale komai sannan ta daura alwalar sallar la'asar,sanda ta idar idanuwanta sun fara nauyi,tana zaune daga saman abun sallar tana dan murxa idanunta. Ba baccin take buqatar yi ba a yanzu,tana son magana da jib ne. A yawancin lokuta a irin wannan lokacinne take samun tattauna maganganu ire iren wadannan,sam bata yarda tayi komai bisa idanunsu,bata taba bari ta rab'a lamarin rayuwarsu da nata rayuwar,komai tana tsaidashi ne iya muhallinsa. Hakanan tana hamma ta miqe ta koma daki. Locker gefan gadonta ta jawo,ta fidda madaidaiciyar baqar jaka dake dauke da mini laptop dinta,sannan ta zaro wayarta dake cikin jaka ta sake dawowa cikin falon. Kalmomin sirri ta sanya ta bude laptop din,sanna ta maida hankalinta akan wayarta tana barin laptop din ta daidaita. Maadanar lambobi ta shiga bincikawa har ta kawo kan sunanshi,ta danna masa kira tana aza idanunta akan screen na laptop din tana duban hoton daya mamaye fuskarta. Hoto ne da bata gajiya da kallonsa,duk sanda ta dubi hoton sai taji kamar tana tare da ita,kamar zata kirayeta ta amsa,kamar zata iya jin kadan daga radadin da take fuskanta,kamar zata damqi hannunta su fuskanci wannan JUYAYAYAR DUNIYAR su kuma kutsa cikin birkitacciyar rayuwarta su kawo daidaito. Daga wayar da akayi shi ya katse mata tunaninta,ta daidaita idanunta da suka fara zugi kadan kadan da alamun son tara ruwan hawaye "Aikin jeeb ya taso?" Boyayyen murmushi ta saki tana gyada kai "Sosai......ka zama kusa da na'urarka......inason sanin wayeshi" "An gama" Ya fada a taqaice "Aikin dazu fa?" Ta sake tambayarsa "Adda ya zama tsohon tarihi......bashi ba......ko bankinsa basu isa susan ya akayi kudin sukayi fiffike ba bare inda suka sauka" "Yayi" Ta amsa masa a taqaice tana sauke wayar daga kunnenta. Sake duba bagaren kira tayi a nutse har ta iso number wayarsa. Ta tsaya kadan tana kallon numbers din. Daga yanayinsa da yanayin shigarsa ta tabbatar ba qaramin mutum bane. Amma ko daya batajishi koda a gefan zuciyarta bama bare a shiga wani batu na daban. Hasalima yadda yaso bata mata lokaci ne yafi bata haushi,kalaman bakinsa kuwa aqalla taji masu kamanceceniya dasu a bakin gomman maza......maza iri daban daban,masu mabanbantan halaye da dabi'u. Tana jan system din kira yana sake shigowa. Ta dora zagayayyun idanunta ga fuskar wayar tare da zubawa numbers din idanu kamar me nazari. Batasan wadanne irin zukata suke dasu ba.......a sanda sukaso abu suna zamewa tamkar wadanda ba zukata a qirjinsu,tamkar wadanda hankulansu ke zamewa daga gangar jikinsu,idanuwansu da dukka kunnuwansu suna rufewa ruf izuwa ga cikar muradinsu. Dukka layukan da tasan zasu zame mata damuwa ta ciresu kwanaki biyu kenan,ta kuma tabbatar akwai masu nemanta da yawa. Qaramin tsaki taja ta saka hannu ta jawo wayar,ta daga tana karawa a kunnenta *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 24 ____________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* ____________________________ "Ranki ya dade.....girmanki ne ai" Idanunta ta lumshe sannan ta budesu,shima dai kaman sauran,gwanayen dadin baki da iya tsara mace,abinda basu da masaniya akai....ya zuwa yanzu babu wani d'a namiji da yake burgeta duk duniya. Sunan soyayya kawai da labarinta tana daukanshi a mazaunin wani wasa ne.....wasa da qwaqwalwa da wani salo na batawa kai lokaci. Ya'aqoub,daya daga matasan mazan dake sharafinsu,kuma giyar soyayya da ta sha'awar sabreen suka yiwa qawanya. Daya daga cikin mazan da sukejin zasu iya kashe komai......zasu iya bada komai,hakanan zasu iya salwantar da komai saboda ita "Ayimin afuwa nasan wataqila nazo da takura......ba wani abu nake bida ba illa a bani dama zan turo dan saqo da aike" "Ka wuni lafiya?" Ta katseshi ya hanyar tambayar lafiyarsa. Wani boyayyen numfashi ya aje,daya daga cikin dabi'unta da suka banbanta dana sauran matan da ya sani wadanda suke rayuwa shigen tata......dabi'arta guda daya dake tsundumashi a kokwanto da tunanin WACECE ITA?,YADDA ZAHIRINTA YAKR HAKA BADININTA YAKE?. Yana da tarin buqatu da yakeson gabatar mata dasu,saidai kwarjininta da wani irin shakkarta yakan daki zuciyarsa a duk sanda yayi yunqurin hakan. Ta sha bashi damar haduwa sama da damarmakin da take bawa kowa......hakan kuwa baya rasa nasaba da yadda yake kame kansa a gabanta "Lafiya qalau.....saidai tsananin kewarki......na iso qasar nan da burin ki zama mutum ta farko da zan fara tozali da ita....... Amma inajin nauyin tambayar hakan don kada na aza miki abinda ranki baiso" "Banayin abinda baniso......hakanan bana yin abinda zan takura" Ta fadi mishi kai tsaye kaman yadda halayyarta take. "Na sani nadeeya" Ya amsa mata da karsashinsa,har sai da boyayyen murmushi ya kubce mata. NADEEYA shine stamp din ya'aqoub,kaman yadda muhseena yake stamp din MASHKUR,mashkur din da tayi imanin zuwa yanzun qila ya kusa zaucewa da rashin samunta a waya da bayayi. Shi kansa ya'aqoub din wata irin saa ya taka a sanda yayi katarin samun number wayarsa. Dashi da mashkur dukkansu ta hadu dasu ne a rana daya,saidai kuma a mabanbantan gurare da lokuta. "Zaa yimin wannan alfarmar?" Ya tambayeta yana langabar da kansa tare da sassauta muryarsa da kyau "Zan duba" "Zuwa yaushe please......zuciyata a jigace take nadeeya.....i beg you karki sakamin lokaci da nisa....." "Baka da damuwa" Ta sake bashi amsa a gajarce "Dan saqo na yana iya isowa?" "Sharada yahaya gusau road,najbil road" Ta fadi a nutse tana yanke kiran. Wayar ya cire a kunnensa yana binta da kallo. Ya zaci inda yayi mata aike wancan karon wannan karon ma can za'a kai mata?. Iska ya furzar daga bakinsa,bata da wuyar canzawa tamkar waya hawainiya. Har yanzu bashi da wani yaqini ko tabbaci a kanta. Baisan komai a kanta ba banda suna da kamanninta. Yana da buqatar abubuwa masu yawa game da ita amma bata bashi dama ko qanqani a kanta ba. "Allah yakai damo ga harawa" Ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa. Ya miqe a hankali yana ture kyakkyawan mulmulallen table na glass dake gabansa cikin qawataccen falon nasa da ya tanada domin hutawarsa yana laluben number wayar babban yaronshi. Yanason saqon ya isa gareta da wuri,don yanason ya sanya qaimi ya matsa da kyau don samun kyakkyawan kusanci tare da ita. A yadda ya ganta baiyi tsammanin za'a dauki wani dogon lokaci ba tare da ya samu abinda yakeso ba. Saidai duk sanda ya tuna yanayin jin kanta,miskilancinta da shariyarta,sai yaga eh.....ba abun mamaki bane,mata irinta daban Allah yake halittarsu. Baki ta tabe tana ajjiye wayarta a gefe,sai kuma taja dan siririn tsaki tana sake bada duka hankalinta akan system din. Folder da takanyi rubuce rubuce ta adana a duk sanda zuciyarta ta buqaci abokin hira ta shiga,ta budeta,sannan ta fara rubutun daga dukkan abinda taji tana da buqatar amayarwa. Wata irin rayuwace da babu qawa ko aminiya......babu aboki ko amini......qawayenta sune qannenta da suka fito daga tsatso guda......saidai har kwanan gobe bata bari sun zame mata aminai ba.......saboda batason tunaninsu da hankulansu su gurbata ya zuwa wani tunani na daban. Tana jin itace dole.....kuma tilashin daukan alhakin komai yana a wuyanta. Awa guda harda qarin wasu mintuna ta dauka kafin ringing na wayarta ya janye hankalinta. Ta dauke idanunta da suka dan sauya launi tana mayarwa kan wayartata,daidai sanda take iya jiyo hayaniya da ifce ifcen wasu daga cikin jikoki da yaran gidan. Bame son hayaniya bace sam,zata iya rayuwa cikin muhallin da babu motsin kowacce halitta sai ita......tana da wannan damar ta samarwa kanta irin wannan muhallin da kuma wannan rayuwar......amma qaqqarfan dalili guda daya tal zaya hanata kaiwa zuwa ga wannan burin nata,tna buqatar tsira da sauran burbushin MUTUNCINTA tana son ta sake tabbatarwa da kowanne me zargi abinda yake zargi a ransa yaji haka ne?,ko kuma ya sauya bigiren ra'ayinsa a kanta. A nutse ta karanta sunan dake saman screen din,sai ta tattara dukka hankalinta akan kiran ta ture system din tana jingina sosai da makarin kujerar tata. A nutse tayi mata sallama "Wa'alaikumussalam" Aka amsa daga daya bangaren cikin matuqar nauyin jiki dana murya. "Lafiya kike titi?" Sabreen din ta tambaya murya a sanyaye itama. Tana jin dukka wata gaba ta jikinta tana yin sanyi "Alhamdulillah sabreen.....,saidai......" "Aisha ko?,ayshatu?" Kai titi take jinjinawa tana qoqarin hadiye abinda yake taso mata. Saita kass cewa da sabreen din komai,bataso ta bijiro mata da abinda take da tabbacin itama yafi qarfinta......bataso ta bijiro mata da abinda zai hautsina nutsuwarta,duk kuwa da tarin qoqarinta.....sadaukarwa da tsaiwar dakanta akan yarinyar "Titi ki fadamin me ya faru?" Ta sake jefa mata tambayar tana jin kamar ta tashi a daren ta iskesu a inda suke "Ki nutsu sabreen.....Allah yana sane da halin da take ciki......kinyi iya yinki......kinyi kuma iya abinda zaki iya,mu barwa Allah komai" "Titi ki fadamin!" Ta furta adan tsawace,tsawar ma da batasan ta yita ba "Sabreen.....naira million takwas suke da buqata wajen aikinta" Wani qaramin jiri taji tana niyyar kayar da ita tana daga zaunen. Tayi luuu da idanunta tana son furta addu'a ko qwaya daya ce amma bakinta ya kasa lalubota. "Tabbas titi akwai abinda kika boyemin......baya rabuwarmu wani abu ya biyo baya amma titi baki gayamin ba......tabbas" Ta fadi muryarta tana rawa. Tana ji har tsakiyar zuciyarta da ruhinta tausayin aisha kamar zai kasheta. "Wannan wacce irin DUNIYA ce dake cike da al'umma masu tsananin son kansu?,duniyar da kowa kansa ya sani?" Ta fadi a sarari tana iya jiyo kukan titi wanda takeson boyewa. Kasa riqe kanta itama tayi,sai kawai ta tsinke wayar,ta dora Fuskarta saman hannun kujerar da take kai. Ba zata iya riqe quncin da takeji saman qirjinta ba,ciwo nauyi da kuma radadin ya mata yawa. Abinda ta saba kamar kullum shi tafi buqatar yi a yanzu wato KUKA. KUKA abu guda daya daya zame mata solution na dukka matsalolinta,duk da ta dade da sanin kukan baya maganin komai. A hankali take rera sirin kuka wanda take kokawa rayuwar su da rayuwar aisha. Tsananin talauci da rashin galihu ya sanya ta tsinci kanta a halin da take ciki yanzu. SON ZUCIYA da rufewar idanuwa da tsananin zallar rashin imani ya sanya yayi mata silar zamowa daya daga cikin mutanen dake ziyartar asibiti domin ganin LIKITAN ZUCIYA.....ciwon da yakai minzalin da take buqatar TIYATA don ceto rayuwarta *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 25 __________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* ____________________________ Ita kanta batasan yawan lokacin data dauka a wajen ba,batasan kuma ta jima a wajen ba sai data fara jiyo muryoyin yaran gidan cikin wadanda ke zuwa islamiyya sannan ta tuna da HUDA NADRA DA HANEEFA. Ta tabbatar muddin suka shigo suka sameta a irin wannan yanayin sai hankulansu ya tashi. Wani irin soyayya da kulawa suke mata,wadda sam sam basa qaunar abinda zai tabata komai qanqantarsa. Da azama ta miqe tana leqa fuskarta tsakanin labulen falon zuwa filin tsakar gidan. Tanaso ta fita ta wanke fuskarta ta kuma daura alwala,amma bataso taci karo da kowa ballantana su tunzura hali da yanayin da take ciki. Idanunta ta maida ta lumshe muryar titi tana mata amsa kuwwa a kunneta. Cikin duhuwar idanuwanta tana hangen aisha da wannan innocent face din nata. Har yanzu bata huce ba daga abinda azzalumin ya aikatawa aishan ba.....duk da burinta ya cika na danganashi da gidan kaso da tayi. Har yanzu tana jin kamar hukuncinsa yafi qarfin wannan hukuncin da akayi masa a yanzun. Lokaci guda taji hankalinta yana neman tashi "Million takwas" Sautin adadin kudin ya ratsa kwanyarta. Ta ina zata soma nema?,ta ina kuma zata samu?. "Mashkur" Zuciyarta tayi mata hasashenshi farat daya. Tsam tayi da ranta tana juya sunan cikin zuciyarta. A hankali sai kuma ta dinga gyada kanta,tana bawa kanta da kanta tabbacin yes......a jikin mashkur yafi cancanta a hada wadannan kudaden,iya wannan tunanin ya sanyata juyawa zuwa dakin nasu da gaggawa tare da mantawa da niyyar fita zuwa tsakar gida da takeson yi. Zama tayi sosai saman gadon daga gefe. Locker gadon dake hannun damanta wadda ba kasafai ta fiya budeta ba ta bude. Tarin tarkace ne a idanun mai kallo,amma a wajen sabreen wasu ajiyayyun abubuwa ne dake da tarin muhimmanci da amfani a wajenta a mabanbantan lokuta. Har ma idan ka tambayeta a wani lokacin tana iya ce maka SUNE SABREEN. mitsitsiyar akwati ce wadda bata fi girman akwatin sanya zobe,ta saka hannu ta daukota sannan ta bude. Wani qaramin layi ta ciro ta rufe akwatin ta maidata,sannan ta dauki wata farar qaramar Samsung's ta bude gefanta ta zura layin ta maida wajen ta rufe sannan ta danne madannin dake gefen damanta. Take ta kawo haske,bayan bayyanar tambari da sunan kamfanin komai ya dawo daidai yadda ya dace. Batakai ga danna komai ba saqonni suka fara turmutsutsun shigowa. Tsai tayi da idanunta tana kallon notifications din har suka gama jerin gwanon shigowarsu suka qare. Kaman ta sharesu ta isa kai tsaye ga abinda zai sadata da mashkur sai kuma ta sauya tunani. Ma'ajiyar saqonnin ta shiga,ta fara bin sunayen mutanen da suka aje mata saqon daya bayan daya don bata jin tana da isashen lokacin da zata tsaya budewa da karantawa. Kamar yadda ta zata,ta samu saqonnin mashkur da yawa fiye dana kowa,saita wuce kowanne saqo ta tafi saqon daya tura mata na qarshe kwanaki biyu da suka wuce. Sallamarsa kadai ta amsa,ta tura masa ta maida wayar ta aje saman locker tana bin fuskar wayar da kallo,zuciyarta na shirya mata yadda komai zai tafi. Ta jima da ajjiye mashkur saboda yadda zalamarsa ta fito a fili. Ta jima da ganin ta barshi a gefe saboda yadda halinsa yasha banban dana kowa cikin mutanen da ta taba tarayya dasu cikin rayuwarta. To amma yanzu silar matsalar aisha tana ganin wannan shine right time da zata koya masa darasi shima yabi sahun sauran mazan da suka shude cikin rayuwarta. Agogon dake manne saman kanta ta kalla tana qoqarin dawo da nutsuwarta waje guda. Zuciyarta ke wani irin rawa tamkar dai ta soma gajiya da al'amuran da suke tunkarota cikin rayuwa. Wasu su shude,wasu kuma suna ci gaba da fuskantarta da babbar BARAZANA. kamar mintuna goma sha biyar sun qaru akan lokacin dawowarsu daga islamiyya na ainihi. Aje dubanta tayi saman hijabinta na sallah,saita miqa hannu ta dauka tana miqewa da zummar duba inda suka maqale. Bata wasa da duk wani abu da ya shafesu musamman fita da dawowarsu gida. Duk da su din kwata kwata basu san ko ina ba idan ka dauke hayoyi da layukan dakan sadasu da makarantarsu. Kaman jira akeyi tayi taku uku daidai wayar ta dauki ringing. Duk da ta jima bataji ringing din wayar ba amma babu abinda ta manta daga sautinta. Taku ukun ta sakeyi ta dawo tana duban wayar bayan zuciyarta ta gama ayyana mata waye din me kira "Mashkur" Kaman yadda ta aje number dinsa. Siririn murmushin da bata shirya ba ya subucewa labbanta. Tana tsaye tana ci gaba da duban wayar har ta qaraci burarinta ta yanke. Bata da niyyar daga kiran kwata kwata a yanzun,don ba tsarinta bane samun komai daga wajenta cikin sauqi ba. Ta yardarma kanta tana da tsada,tsadar data sanya kowanne namiji da zai ratsa ta cikin DUNIYARTA yarda da hakan,ya kuma bita da tsarinta a yadda ya sameta. Kaman yadda ta zata bazai kira sau daya ya bari ba haka taji wayar ta sakeyin qara,salin alin ta koma ta maidata silent,sannan ta jawo Locker ta wurgata ta rufe ta kuma soma takawa hanyar falonsu tana zura hijabin saman wuyanta. Shimfidadden kwarjinin dake boye bayan fuskarta ya sake bayyana sosai tamkar ta sanya hijabin ne don ado ba domin biyan buqatarta ba. Slippers dinta masu taushi ruwan hoda dake daga bakin qofar da zura ma fararen qafafunta,ta murda handle din qofar ta bude ta tura ta fito. Fayau tsakar gidan nasu yake da wadataccen filin nan da baya rabo da tsafta duk da iyalin da gidan ke qunshe dashi. Kamar kowanne lokaci kamar kuma yadda suka maidata ABUN KALLO. Kowanne motsinta yana saman idanun mafi yawa daga cikinsu,bawai don su bata kulawar data dace ba....bawai don suyi mata gyara idan tayi kuskure ba......badon kulawa ta qauna ba.......saidai don wani radin kansu da biyan buqatar qashin kansu. Tana da wani irin kaifin nazarin fahimtar meke kai kawo a kewayenta. A zaune take ko tafiya take?. Wani yanayi da a baya baya cikin dabi'unta,kuma bata dashi,amma yanayi da salon rayuwa ya tilastata kasancewa hakan. Dab da rijiyar gidan wadda daga ita sai hanyar da zata sadaka da ainihin farfajiyar gidan ta ganta. Tsaye gaban rijiyar dauke da cup da alama ruwa ta gama sha. Sanye take da atamfa classic da aka yiwa dinkin zamani riga da skirt daya zauna daidai jikinta. Kanta ba dankwali wannan zai baka damar hango baqar sumarta me sulbi da suka gada ainihi daga mahaifinsu. Idanunsu cikin na juna na wasu sakanni,sai ta fara janye nata duban daga kanta tana ci gaba da nufar soron. HADIYYA......Idan har a baya za'a gaya mata rayuwa zata ajeta a bigiren da suke kai a yanzun ita da ita zata qaryata......idan har a baya za'a gaya mata rayuwarsu zata koma kaman yadda take a yanzun zatace mummunan mafarki ne mara ma'ana....wanda bashi da tushe ballantana makama. Hadiyya 'yaruwar haihuwarta,wanda mahaifi yayi silar zamowarsu jini daya......hadiyyan da suka taso qarqashin rainon mahaifiyarta......cikin daki guda saman shimfida guda,duk da murdadde kuma zazzafan kishin da mahaifiyarta ke bazawa.......amma hakan bai sauya komai ba na kusancinsu. Sai gashi a yanzun sunyi irin rabuwar hannayen riga. A yanzun haka tana nata karatun cikin makarantar koyon aikin jinya bisa daukar nauyi da kulawar yayan mahaifiyarta......yayin da tata rayuwar tayi matuqar shan banban da ta hadiyyan.......take neman ta nutse cikin neman dauki da tallafin data gaza me kawo mata,har sai da tayi wani irin wawan tsalle da batasan zata sauka a daidai ko kuma garin saukar tana iya gamuwa da karaya da tarin raunukan da zasu zamewa rayuwarta tabo?. Takai qarshen tunanin sanda takai bakin qofar farfajiyar gidan ta farko,saita aza tafin hannunta saman fuskarta tadan shafi fuskar. Tasan bawai kuka takeyi ba,don a yanzun batajin cikin qwayar idanunta akwai sauran ruwan hawayen da suka rage da zasu bata hadin kan yin kuka. Kawai huci da dumin da fuskarta ya dauka takeso taji ya huce,idanunta sake mata dan zugi zugi tanason rage musu adadin iskar dake shiga cikinsu. Karo sukayi da huda sanda take shirin fita shigowa su suna shirin shigowa. Suka ja baya dukkansu hudan tana dan riqe goshinta "Ke kuma ina kuka tsaya haka dukka ku ukun har ana shirin kiran salla?" Ta jefa mata tamabayar tana tsareta da ido. Kafin huda tace komai haneefa ta tsinke da dariya "Anty.......yaa nadra muka tsaya jira......bata bada hadda ba sai malam ya tsareta" Idanunta ta mayar kan nadra wadda fuskarta ke a daure "Garin yaya?,kin soma wasa da haddar ne?" Kai ta girgiza da sauri,tana shirin magaa hudan ta rigata "Kallo suka tsaya yi jiya da daren bayan kin kwanta" Fuska a daure ta sake maida kallonta a kansu "Ashe?,yau zaku jawa kanku,sai na tsinke kowanne cable na kallo dake dakin nan" "Ah wai.......ni abunnan yana dauremin kai?,wai lalatacce shike tarbiyya" Murya bibo ta ratsa kunnuwanta sanda take dubansu nadra. Dukansu ido suka azawa bibo din lokacin da take kutsowa cikin gidan. Kaman yadda suka fita ne dazu,ita da daada,saidai kaman dazun ma daada ratsewa tayi ta wuce abinta ba tare data tsaya yiwa bibo tayin su wuce ba kamar dazun. Motsawa kadan huda tayi wanda motsinta kadai ya sanar da SABREEN abinda take shirin yi. Yatsarta ta kada mata sautin da ya sanyata tsaiwa can tare da hadiyar wani abu me tauri a wuyanta *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 26 __________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* __________________________ "Ku wuce muje" Sabreen tace dasu,suk sai sukayi gaba tana biye dasu a baya. Nadra ta hadawa kayan duka ta wuce musu dashi daki. Ita tayi tsaye dasu kowacce ta gama buqatarta suka daura alwala suka wuce daki. Sallah sukayi bayan sun sauya uniform. Har a sannan tana ankare da yadda huda din keta hadiyar zuciya. Ta sani muddin tace zata saki huda tayi abinda takeso zaman bazaiwa kowa dadi ba......tafi huda zuciya nesa ba kusa ba......tafi huda dabi'ar take yanke.....amma me?,daga baya ta fahimci me irin wannan dabi'ar ba kasafai yake nasara ba. Sai data kammala sallar magariban sannan tabi takan wayar. Ta samu miscal biyar hade da wasu saqonnin daga gefe. Tabi number tasa da kallo,sai a yanzu takejin ta shirya saurararsa. Kamar yasan tana riqe da wuyar saiga wani sabon kiran ya sake shigowa,don haka ta miqe a nutse ta koma daki tana matsawa daga inda su nadra dake cin abincin dare suke. "Laifin me nayi dana cancanci wannan uqubar fateema?" Numfashi ta saki wanda sautinsa ya isa har kunnensa "Ki gayamin ko meye nayi a shirye nake da na nema afuwa" Shuru ta sakeyi tamkar bata layin,saidai tana sauraren dukka maganganunsa "Fateema" Ya sake kiranta da sunan da shine nasa STAMP din,sunansa ne shi daya,duk duniya shi ta mallakawa wannan sunan "Naam" Ta amsa a karon farko tunda ya fara maganar "Kinsan irin rayuwar dana tanadar miki?,kinsan irin gatan da nakeson miki?,kinsan yadda nakeson maidaki tauraruwa a cikin mata?,kinsan yadda nakeso ki koma tamkar sarauniya?" "Dukka wadannan dama abinda ka lissafa basu nake da buqata ba" "Me kike da buqata fateema......ki gayamin,a shirye nake na mallaka miki su......" "Zamu iya haduwa?" Ta jefa masa tambayar "Ko a ina nake a duniya a yanzun haka kika ce kina buqatar ganina zan wanzu a gabanki" Maida idanunta tayi ta lumshe sannan ta budesu "Mu hadu yanzu fateema?,ko dan kadanne inaso naga fuskarki" "Alright" Ta amsa masa a taqaice,abin da yazo masa a bazata,don haka a rude yace "Venue?" "Zan gaya maka,i will call you" Bata sake bashi daman cewa komai ba ta yanke kiran. Wayar ta riqe a hannunta tana juyata a hankali bayan ta zubawa guri daya idanu. Lissafi ne fal Qwaqwalwarta,dole kafin ta samu abinda take nema saita yi haquri ta sake masa,dole ta dinga bashi mabanbantan gurare har zuwa sanda tsarinta zai fada aikinta zai cimma nasara. A nutse ta miqe tana wassafa yadda zata fita yau din da dare,abinda sam ba dabi'arta bane saiya zama mugun dole,ba kuma zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ya taba faruwa da ita ba,amma yanzun dole ta fitan,tanason ta amintar dashi sosai a kanta. Kai tsaye ta wuce ma'ajiyar kayanta tana duba suturar da zata dace da ra'ayinta a wannan lokacin. Da idanu ta gama qare musu musu,daga qarshe ta tsaya saman wasu Turkish dress masu strip skirt long sleeve shirt da doguwan kinomo sai madaidaicin veil da zai lullube saman kanta. Sam bata da ra'ayin sutura me matse jiki duk kuwa da yadda mutane da yawa suke kallon ita tafi dacewa da irin wannan shigar. Tsaf ta shirya cikin kayan kalolin navy blue da gray color. Sanda ta gama nada veil din a kanta sai data sake duban kanta sosai ta cikin madubin. Tayi wani irin sassanyan kyau me matuqar daukar hankali. Ta miqa hannu a nutse ta dauki turarenta ta feshe jikinta can qasan ranta tana jin fargaba kadan kadan kan haduwarta da mashkur,saidai kuma wani sashe na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwar ba komai,wannan ne haduwan farko,nothing will happen. Asalin wayarta ta jawo tana lalubar number JIB. bugu daya tak ya dauka,tadan motsa bakinta a nutse "Ina fatan kana available kuma free" "Ko ba hakan bane ai ya zama dole nayi creating time wa ke.....me kike buqata?" "Connection" Ta fada a gajarce " A daren nan?" "Haka abun yazo,mashkur......mashkur alqali abdulkreem" "Done.......wancan aikin ya kusa kammala......akwai ragowar information dana kasa accessing.....but...." "Karka damu.....mu sanya wancan a mala.....wannan din shine yafi muhimmanci a yanzu" "An gama.....bani code......let me write it" Ya fada yana dan riqe wayar kadan kafin yace "Okay.....karanto" A nutse ta karanta masa wasi gajerun lambobi guda uku sannan ta katse kiran. Ta jawo locker madubinta ta ciro Bluetooth tayi danne danne saman wayar tata ta bada wasu sakanni sannan ta maqala a kunnenta. Saita aje wayar,ta dauki wancan Samsung din ta kunnata sannan ta fara yunqurin kira. Bugu daya tak tayi aka daga,ta kalli wayar da mamaki sanda yake cewa "Am ready to go princess......ina zaune a mota nida driver a parking lot na gida" "Yayi.....but if possible ka taho kai daya mana" "An gama" Ya amsa mata cikin farinciki hankali kwance. Tana kammala saka takalma huda na shigowa dakin. Kallo daya tak tayi mata taga yanayinta ya sauya. Hudan tadan ritsata da idanu tana dubanta,saidai tun kafin takai ga tambayarta ta bata amsa "Zan dan fita kadan amma yanzu zan dawo" Iya abinda ta gaya mata kenan ta fara takawa zata fice. A jikinta taji yarinyar kallonta take,a jikinta taji tana tsaye ne kawai har yanzu,don haka ta tsaya cak sannan ta waiwayo. Ido suka hada,sai a sannan hudan ta kauda kanta. Iya hakan ya gayawa Sabreen maganganune sosai cikin zuciyarta,wataqila girma da kimarta kadai zai hanata ta furta mata su. Taku hudu tayi ta iso gaban hudan "Dole ce ta saka zan fita huda......amma bazan wuce awa daya ba,idan na dade biyu" "Amma anty...." Hudan ta furta fuskarta fal damuwa. Yatsanta ta dora saman lips tana duban hudan,sai kuma daga bisani ta dauke yatsan tana aza dukka hannuwanta saman kafadarta,ta kuma zaunar da ita saman stool na madubin dakin "Ke daya ce tal cikin mutanen da sukasan wace Sabreen gaba daya baya,kada kiyi tunanin na canza......ban canza ba huda.....kuma har abada bazan canza ba.....nayi alqawari......mommu da abba dake qarqashin qasa bazan bari suyi kaico dani ba" Kai ta gyada a hankali tana kallon Sabreen kamar yadda itama ita din take kallo. To amma a hankali tana rasa wannan yardar wanda tasirin maganganu daga kowanne saqo da lungu na layinsu dama unguwarsu ke kai kawo a kunnuwanta "Don't lose hope huda......alqawari na.....bazan karyashi ba,ki kula da nadra da haneefa" Ta fadi mata daga qarshe ta juya tana fita a dakin. Nata ruhin yana motsuwa. Har abada ba zata daina zargin maraici ba......har abada ba zata daina kuka dashi ba......a wani sashen na duniya,a irin wannan lokacin,diya kamarta tana qarqashin kulawar mahaifanta ne guda biyu.......ko kuma qarqashin kulawar wasu amintattun mutane da zasu zame mata makwafin iyayen.......sai gashi tata DUNIYAR ba haka bane,dukka kafadunta dauke suke da wani irin nauyi dakeson fin qarfinta ya kaita qas. Daga baya baya ta sanya busari ya ajeta kafin akai ga shiga gurin a yanayi salo na kula da takunta kanta dama dukka wani motsi nata. Sallamar busari tayi tace zata nemeshi idan hakan ta taso,sannan ta fara takawa a hankali tana nufar wajen. A hankali take ratsa wajen cikin nutsuwa data zame mata dabia,tana takawa a hankali qamshinta da kuma yadda shigar ta amsheta kadai suka soma jan hankulan matasa da yawa wajen. Guri ne da yakan hada matasa maza da mata,wayayyu da suke da gogewa a fannin rayuwa kudi da kuma ilimi. Wajene kebantacce da yawansu suka maidashi gurin nishadi da kuma debe kewarsu,wasunsu a duk daren duniya,wasu kuma jifa jifa. Yadda take daukan hankulansu haka kwarjininta ke dukansu,wannan ya sanya duk wani dakeson kawo mata caffa ya gaza yin hakan,saidai tazo ta ratsashi ta wuce shi kuma ya bita da kallo. Tun daga nesa ta hangeshi,ya fita yayi tsaf cikin wani lafiyayyen jeans da shirt da suka dace da takalmin qafarsa. Kanshi pcap ce daya sauko da ita tadan rufe masa fuska. Hannunsa dauke da wayarsa yana latsawa a hankali ba tare daya damu da abinda ke kai kawo a wajen ba. Ta sani,hankalin gomayyar 'yan mata dake wajen tabbas suna kanshi. Mashkur din ba irin mazan da mace me muradin jinsin maza irinsu zata kall sau daya bane ta iya kauda kai kota wofantar,kusan zata iya cewa ya hada dukkan komai,abubuwa da dama da mazan da suka taba ratsa rayuwarta ba wanda ya gama cikasu irin haka. Yana da kyau daidai gwargwado wanda kudi suka sake qawatashi,yayi karatu har zuwa matakin degree,hakanan dan wulaqanci ne shi,wulaqancin daya zame masa ado a idanun mata marasa kamun kai. Idanunsa a bude suke tarwai,yana da wata irin wayewa data zarta shekaru da kuma iliminsa,wanda hakan baya rasa nasaba da fita qasashen waje da yake yawan yi,musamman qasashen turawa. Dab da zata iskeshi ya daga kansa sai suka hada ido. Zumbur ya miqe yana zube mata idonshi,har cikin zuciyarsa yana jin wani abu daya qarasa mamaye gangar jikinsa. Karon farko daya soma jin ra'ayinsa akan mace na neman canzawa. A yanzun kallo daya tak.....cikin qasa da minti daya kacal ya soma ji a ransa kamar ya aureta shine abinda yafi dacewa dashi da ita gaba daya. Kamar alaqar daya shirya da dangantakar daya shirya ginawa a tsakaninsu ba ita ta dace ba,duk da har yanzu gaza fuskantar AINIHINTA....a wanne mataki na 'yammatan wannan zamanin take?. Wasu abubuwan nata na masa kama da dabi'un mace ta musamman.....amma wani motsin nata a wani lokacin sai ya sanya masa shakku akan haka. Kamar dai yanzun,yadda duk da duhun dare ya lullube sararin subhanana amma hakan bai dasa mata shakku ko ya zama dalilin qin fitowa su hadu ba. A maimakon kujerar daya ja mata don ta zauna saita matsa kujera ta gaba,saidai kuma fuskarta a sake tana maida masa martanin murmushinsa. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 27 _________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* _________________________ Duk da a qasan zuciyarta ba haka bane. Idanunsa a kanta kaman bazai iya daina kallonta ba yana nashi seat din ya zauna "Finally dai after wasu watanni......har na debe tsammani sai gashi......" Ya fada yana dan watsa hannayensa irin na gogaggun samari "Me ma bahaushe yake cewa?.....me haquri ko?" Ya aza mata nauyin amsa tambayar ta hanyar kallonta da idanunsa. Qaramin murmushi kawai ta saki tana maida bayanta ta jingina sosai da kujerar da take kai din,yayin data daba hankalinta gida biyu. Wani a gurinsa,wani kuma yana kan yanayin wajen dake cike da 'ya'ya mata. Tayi imanin dukkaninsu uwaye ne suka haifesu,koda ace akwai na gaba da fatiha to kadanne. Son rai son zuciya kwadayi su sukayi musu jagora zuwa ga turbar da suke kai a yanzu?. Ko kuma suma kamar ita dinne?. "Yauwa......thanks" Taji ya furta,saita maido dubanta kanshi. Idanu ya kashe mata cikin salon jan hankali me zafi,ya kuma sake matsowa sosai har yana rungumar table din da suke kai zuwa qirjinsa,sannan ya aje manual din da aka kawo ta hannun waitress. "Choose babe" Ya fadi yana lanqwashe murya kamar wani mace gami da kanne mata idanu. Manual din da ya tura mata ta sauke idanu a kai. Tarin abinciccika ne iri daban daban,wanda ko kaffara ba zatayi ba idan ta qiyasta maqudan kudaden da za'a lasa ta sanadiyyar cinsu. Sai data qare musu kallo gaba da baya,yayin da shi da waitress din ke jiransa ba tare da sun qosa ba,saita maida ta ajiye saman table din. Ta motsa bakinta zatayi magana kenan sallamar da akayi da wata raunanniyar muryar taja hankalansu. Dukkansu shi da ita suka maida dubansu ga wajen. Matashiya ce mai matsakaicin haske wadda idan ka kalleta a qiyasin da zaka fara yi mata duka duka shekarunta ba zasu haura ashirin da bakwai zuwa da takwas ba da haihuwa. Sanye take fallen zanin atamfa da kai tsaye zaka kirata da atamfa leda ko roba,duba da yadda ta cukuikuye a jikinta saboda tsufa da rashin quality da kuma yanayi na dan busawar iska data hadu dashi. Qasan zanin a cinye yake abinda zai wassafa maka kenan shekarun da atamfar ta dauka a duniya ana amfanarta. Hijabi ne a jikinta daya fara gajiya da rayuwa,tsananin sussuqewarsa ya sanya ya baiwa me kallo daman hango yaloluwar rigar dake a jikinta. "Ke kuma fa?,daga ina wa kike nema?" Mashkur dake dubanta sama da qasa da wani irin qasqantaccen kallo ya jefa mata tambayar. Rusunawa qasa tayi cikin matuqar taushi da karyar dakai ta hade hannuwanta biyu waje daya "Taimako nake buqata yallabai......don Allah ka taimaka min da duk abinda Allah......" "Wait.....wait mana" Ya fada a tsawace har hakan ya sanyata miqewa ta tsaya saman qafafunta. Waiwayawa yayi zuwa ga waitress din "Yaushe wajen nan naku ya lalace?,yaushe kuka fara bawa mutane irin wadannan daman shigowa gurin nan.....wait.....wai bakusan kowa na zuwa irin nan bane don ya huta ya kuma yi uzurin gabanshi ba tare da kowa da komai yayi disturbing nashi ba?". Duk joint din da basusan fuskar mashkur ba to tabbas ba cika joint ba......imma darajar wajen tsada da kuma darajarsa batakai ba......ko kuma dai kawai wajen bai cikin tsari da ra'ayinsa. Wannan abun ya sanya cikin rudewa ta soma bashi haquri tare da qoqarin nesanta matar daga wajen,duk da yadda kuwa take roqon su taimaka mata. A nutse Sabreen ke kallon matashiyar zuwa ma'aikaciyar ma gaba daya. Yar uwarta nace ke qoqarin rabata da gurin don dai kawai kada ta batawa customer rai ta hanyar da babu girma arziqi ko darajta dan adam. Yanzun inda ace cikin kyakkyawar shiga take.....inda ace cikin dressing me kyau take......inda ace jikinta a gyare yake......inda ace zata koma hakan tabbas basai ta tsaya bagging a taimaketa ba. Ta cikin ruwan sanyi matasa dama manyan ire iren wadanda ke zaune yanzu haka a wajen zasuyita miqo mata buqatunsu,wanda yadda ta karba da hannu bibbiyu......kwatankwacin hakanne zata samu nata biyan buqatar. "Dakata......barta ta dawo" Sabreen din ta samu kanta da furtawa idanunta da suka canza launi suna saman fuskar waitress din. "Kamar yaya?,ki barta......" Mashkur ya furta yana maida idonsa ga matashiyar data fara takowa a hankali zuwa inda suke din "Nooo" Ta amsa masa da wani sauti da yake tafe da wani irin zafi da ya motsa mata zuciya. Ganin matar kawai ya tuna mata abubuwa masu yawan gaske,ganinta ya fama mata wani babban ciwo,sai ta sanya hannunta cikin mitsitsiyar handbag dinta sannan ta zaroshi da dukkan kudin dake cikin jakar ta miqa mata. Cike da mamaki take kallon fuskar sabreen din. Saita motsa kanta tana mata nuni da kudin. Wani irin karyewa zuciyar matar tayi,sannan ta sulale da wani irin qarfi ta tara hannuwanta tana amsar kudin. Jiki da muryarta dukka rawa suke sanda ta fara jera mata addu'a da godiya "Ya isa jeki" Mashkur din ya fada yana fatan ta gusa ta basu waje ba tare data bata masa budget ko ta bata masa lokaci ba. Cikin jikinta taji cewa ita din mashkur yake kallo. Ta lumshe idanunta tana qoqarin daidaita mode dinta,sai kuma daga bisani ta sauke mata wannan kallon nata dake saurin waftar hankali "Are you okay?" Ya jefa mata tambayar cikin matuqar nuna kulawa. Sai da ta danyi gyaran murya sannan ta gyada kanta "Am okay....." "Am sorry ko?,irin wadannan mutanen dear ki daina gaggawar amincewa dasu ko basu taimako.....they are wicked wallahi at so many times......yanzun kalli yadda ta bata mode dinki gaba daya?" Gyara zamanta sosai tayi tana maida qafarta daya ta dora saman dayar,sannan ta sarqafe yatsunta saman qafarta tana sake zuba masa idanu. Rashin tausayi rashin imani da kuma rashin bawa dan adam darajarsa yana fita fes a tare dashi,wanda hakan ya sanya taji a ranta yayi deserving ayi punishing dinsa qwarai da gaske fiye da yadda ta shirya yi a baya. Ya daddage yana sharhi akan baiwar Allahn da baisan wacece ba?,meye matsalarta?,meye damuwanta cikin sararin subhana?. "Is okay ya wuce" Ta amsa masa a taqaice tana kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannunta. Hankalinsa yadan dauko kadan,a duk sanda yaga tayi hakan alama ce dake nuna tana dab da yin layar zana,layar zanan da idan tayin baka isa bincikota ba sai sanda taga damar bayyanar maka. "Times up?" Ya fada yana qureta da ido. Kadan ta saki murmushi "Eh.....kusan haka ne" "Ban yarda ba.....dole kici wani abu" "Nop......banjin wannan.......zan wuce.....but soon zamu sake haduwa" "Am......bamu tattauna komai bafa......if possible a qaramin minti goma kacal.....in sha Allah bazan haura haka ba" Hannuwanta ta aje daga daukan handbag dinta da tayi niyya,ta koma ta sake harde qafafunta tana kallonsa. Shima idanun ya zuba mata yana jin yadda kowanne sashe na jikinsa yake da buqatarta "Wai sai yaushe zaki soni kaman yadda nake sonki fateema?" Ya tambayeta bayan ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya. Dukka girarta guda biyun ta dage tana sake nazarinsa ta cikin qwayoyin idanunsa "Ta yaya zaka zargeni da abinda ba haka bane?" "U mean......kina sona kaman yadda nake sonki?" Sai data lumshe ido kadan as usual sannan ta gyada kai "Okay,prove it" Ya fada da wani irin zumudi yana gyara zamansa sosai tare da rinjayar da gangar jikinsa zuwa zuwa mazauninta. Ido tadan juya,reaction na fuskarta na nuna masa bata fahimta ba,a nutse ta motsa labbanta "Like?....." "Dis week nakeson zuwa dubai nayi annual leave dina......zanji farinciki fiye da yadda baki tsammani.....zanyi alfahari dake zan kuma mallaka miki komai da kike buri cikin rayuwarki......." Sai ya bude wallet nashi dake aje gefe,ya zaro wani qaramin littafi me abun rubutu a gefansa,ya buda tsakiyar littafin ya sanya biron,sannan ya aje mata shi a gabanta yana cewa "Write it down.....,ko meye.....komai girmansa kada ki gaza rubutawa,and zai kasance ne as you wish" Fararen idanunta ta dora akan littafin kamar me nazarin launin takardar "Musayar mutunci" Zuciyarta ta raya mata hakan. Wani zafi taji har cikin qwayar idanunta,saita dauke idanunta dama kanta daga wajen ta maidasu gefe. Cikin qasa da second biyar zuciyarta ta gama tsara komai,don haka ta waiwayo ta fuskanceshi sosai sanda yake fadin "What happened fateema?....." Yana leqen fuskarta. Murmushin da ta fuskanceshi dashi ya sanya yaji relief,fatan samun nasararsa daya soma zagwanyewa duk sai yaji yana dawo masa. "Nothing......kawai gani nayi kazo da qaramar buqatar da bata buqatar dogon sharhi da roqo har haka......kaman ma bata buqatar tafiyarmu wata qasa......nan ma zata iya zama dubai dinmu" "Really?" Ya tambayeta da wani irin excitement a jikinsa dama fuskarsa. "Yes" Ta amsa tana daga masa kai da nata guntin murmushin daya tsaya iya labbanta. "Thank god.....thank you fateema......ban taba tunanin it gonna be easy kaman haka ba" "Why?" Ta tambayeshi tana dubansa "Ba zaki gane ba.....your are so unique fateema......alright.....now" "Not now......am tired.....inason na koma gida na kwanta.....see you next time saimu qarasa tattaunawa" "When?,ina gudun ki kufcemin fa?" Bata amsashi ba sai data gama gyara zaman rolling dinta "Wannan ma kai kayi finding dina out ko nice" "You are the one" "Tom" Ta fada kawai tana shirin daukar jakarta,saidai kuma shi din ya rigata ta hanyar jawo jakar gabansa. Duk da bata saka ido da kyau ba,amma idanunta sunga tamkar takardun kudin waje ya saka mata "Thanks" Ta furta a gajarce ba tare da taga qima ko farinciki da kudin ba ko qanqani. Ya sani,daya daga cikin rules nata shine baa yi mata rakiya idan zata tafi,don haka a nan yayi tsaye goye da hannayensa yana kallom nutsasen takunta har ta fice daga gurin. Ko daya bata jin me busari yake fadi sanda suke tafiya a hanya. Gaba daya tunaninta yayi nisa zuwa wata duniyar ta daban. Lissafe lissafe ne fal kwanyarta,tama rasa da wanne zata fara?,daga ina zata fara?,a ina kuma zaren lissafin nata zai katse. Zuciyarta da idanunta sunason zuwa ganin aishatu,to amma kuma bata so taje ta ganta a halin da take ciki alhalin bata tanadar mata da komai da zaya fiddata daga wannan yanayin ba. Jib ya kirata,ya tabbatar mata aiki duka ya kammalu daga bangare biyu,amma ta gaya masa ya saurara ta isa gida tukunna. Goma saura busari ya ajiyeta daga gaban gidan nasu,ta sauke hand bag dinta ta zuge don masa ihsani kaman yadda ta saba,duk da shi din bai kawo komai cikin balance din da ha kamata ace ya kawo din ba amma bata damu ba. Sai data zura hannunta a jakar ta tuna bata da komai sai irin kudin da mashkur ya zuba mata. Tadan jawo kudin gaba kadan tana dubansu,sabbin US dollar ne qar dake qyalli da qamshin sabunta,saita maida dubanta a kanshi "Zan saka maka wani abu busari ta account,ka bayarma inna kace tayimin addu'a,saida safe" "Kinfi gaban haka......Allah ya bamu alkhairi" Ya fada yana dan bin bayanta da kallo. Yana mamakin kirki irin nata......duk da ita din zuma ce a wani lokuta idan bataso ba,ga zaqi ga kuma harbi. Ya tayar da napep din yana janyeshi da qofar gidan,qasan ransa kuma yana qididdige adadin alkhairinta a tattare dasu. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 28 Sanda ta isa falon dukkansu ta samesu qudundune saman kujera,kowacce nannade da blanket dinta. Huda ce kadai zaune saman carpet nannade da hannayenta tana kallo a tashar Arewa24. Tayi mata sannu da zuwa ta amsata tana wucewa ciki don rage kayan jikinta ta sauyasu zuwa da na bacci,gashinta ta kama ta daureshi waje daya ba tare da tasa komai ba,don bata fiya son abinda zai takurata ba duk sanda zata kwanta,ta shafe jikinta da daddadan turarenta me sanyin qamshi data wareshi ne kawai don kwanciya ta dawo falon. Tsam huda ta miqe ta gabatarata da abinci,saidai bat jima da fara cin abincin ba wayarta ta dauki tsuwwa. Jib ne,qaramin tsaki ta saki,a lissafinta ta gama amsa kowanne kira don bacci take da buqatar tayi,tanaso gobe ta shiga wajen aysha taga yadda jikinnata yake. Abun ya tsaye mata a rai,tana jin cewa idan tana da dama a rayuwa zata sauya rayuwar Yarinyar ne gaba daya. A kasalance ta kara wayar a kunnenta bayan tayi sallama ya amsa "Ya akayi?" Ta tambayeshi "Komai ya kammalu" Ya gaya mata kai tsaye. Dan shuru tayi tana saurarensa,daga yadda yake mata magana ya tabbatar mata fuskarshi qunshe take da fara'a duk kuwa da bata iya ganinsa. "Okay.....meye result?" "Bari na fara da abinda yafi damuna yafi kuma yimin dadi......da farko dai zan iya ce miki congratulations.......ina kyautata zaton indai zakiyi amfani da damarki sosai yadda ya dace,kin kusa fara shiga jerin sahun mata masu arziqi......kawai dai" Ya fada yana dan sauke qaramin numfashi "Wani lokaci duk wani opportunity sai naga kamar kina shuresu ne da gangan......" "Jib...." Ta ambaci sunansa "Ina tare da ke,sai na yita tunanin fa me yake damunki?" Yadda yayi maganar a wani sanyaye ya sanyata murmushin dole. Tasan me yake buqata a nashi son rai ace tana yi "Ka rasa wani abu ne?" Kai ya girgiza "Ko kadan.....kawai daman da kike samu ya zarta yadda kik amfani da ita......" "Bani labarin aiki na" Ta zabi shafe wancan maganar gaba daya,don ba me amfani bace a wajenta kamar yadda nashi hasashen yake bashi. Ajiyar zuciya ya sauke,har tana iya jinsa ta cikin wayar "Congratulations once again.......daga mashkur har mika'il.....suna daya daga cikin mutanen da suka mallaki manya manyan dukiya........sunyi tarayya ta wajen hali da dabi'a.........amma ta gurin source of income nasu sun sha banban" "Ehnnnn" Ta fadi tana juya abincin gabanta da spoon ba tare da takai ko loma guda bakinta ba tun bayan kiran nata da yayi "Mashkur dan kasuwa ne kamar yadda yace.....yana aiki tare da mahaifinsa......mika'il kuma wani babba ne a wani babban kamfani daya boye sunansa......don kamar yana cikin policy na kamfanin ma'aikata irinsa su dinga exposing kansu da rank dinsu cikin company din......saidai iya abinda hangena yakai......company ne babba dake samu da kuma biyan kowanne ma'aikaci albashi me matuqar tsoka" Yakai qarshe yana sauke numfashi tare da sararawa. Ajiye spoon din tayi tana gyara zamanta, bayanan sun mata dadi sosai,kuma su suka haska mata akwai nasara akan mission nata. A hankali tadan aza dubanta akan huda,duk da hankalinta yana ga kallo,to amma kuma bata bari tayi dukkan wata magana data shafeta a gabansu "Good job......na gode.....akwai sauran bayanai nasan,ina da sauran tambaya da qarin haske.......amma......bari zuwa gobe mayi waya" "Alright.....to hakan yayi" "Allan ya tashemu lafiya" Ta fada tana gintse kiran. Wayar ta sauke tana bin fuskarta da kallo,tunani ne cinkus cikin zuciyarta. Fuskar matar dazu kawai ke mata yawo a idanu "Meye amfanin dukiyar da bazaka bayar da ita ba fisabilillahi saidai qarfi ya qwata?" Ta furta a qasan ranta tana tambayar kanta da kanta. Daga mashkur har mika'il tayi imanin cikin budin da Allah yayi musun,inda zasi fidda abinda suka mallaka su dinga narkasu cikin nutsuwa a hanyar data dace......dubban jama'a zasu samu sauqi da radadin da yake damun zukatansu da gangunan jikinsu. "An kawo miki saqo" Taji muryar huda daga gefanta tana fada. A nutse ta daga kai tana duban hudan kafin ta maida dubanta ga akwatin data jawo gabanta. Zuba masa idanu tayi tanason tuna daga ina?. A hankali sai kuma abun ya fado mata,ita sam ta manta sunyi dashi ma zai bada saqon "Kaishi daki" Ta fada tana maida kanta ga waya. Wata number ta lalubs a gajarce kuma ta tura mata gajeran saqon karta kwana "Received......thanks". Shi daya ne cikin qawataccen falon da aka qawatashi da dukkan wani nau'in kayan alatu da qawa na rayuwa. Madaidaicin falone wanda ke da saurin janye idanun me kallo da kuma sauqin shiga rai lokaci daya ya kuma dace da kowanne mode da mutum yake ciki. Shi daya ne tal cikin falon,sanye yake da shirt me gajeran hannu sky blue,sai gajeran wandon da duka duka iyakarsa gwiwarsa. Yana a tsaye ne yana fuskantar qatuwar t.v plasma dake zaune dirshan saman kyakkyawar tv stand suna haska wasan qwallon qafa,saidai fiye da rabin hankalinsa baa wajen yake ba. Bayan gilmawar kowanne minti ko second sai fuskarta ta dawo masa. Ya lumshe idanunsa sanda aka buga qwallo na qarshe cikin tazarar bada sa'a game rabo wato penalty,ya daga ragowar tsadajjiyar giyar data rage a qasan glass cup din hannunsa ya qarasa kurbeta,ya dire cup din yana fidda iska daga bakinsa. Tsakanin awannin daga dazu zuwa yanzu ya gama tsara yadda zai baibaye rayuwarta da tsadajjiyar rayuwa......yadda zai narkar mata da zuciya da masu gidan rana......yadda zai maidata tashi shi kadai......yadda kuma zai siye mata zuciya da kuma rayuwa da kudi wadanda yayi imanin a wannan lokacin da muke ciki sune maganin kowacce matsala.....suke iya siya maka dukka nau'in macen da kakeson ka mallaka.....don babu yaren da matan sukafi ganewa irin yaren LUXURY LIFESTYLE. Kallonsa ya mayar saman system dinsa dake kunne,yana jiran kirane daga wajen CEO na JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES (JDCR). A duk sanda sunan ya fado masa a rai,ba abinda yake fara zuwa ransa sai GIDAN KUDI. wanna shine sunan da yafi kiransa dashi......wannan shine full definition nashi da yake ganin ya dace dashi gaba da baya. Sake matsawa yayi ya gani koda ya nemeshi?,amma ba wani saqo ko kira kai tsaye ta yanar gizo. Mamaki yadan kamashi,saboda sanin da yayi masa na zamantowarsa mutum me girmama lokaci tare da bawa lokaci muhimmanci,yasan tabbas akwai abinda ya riqeshi ne hala. Baiso yasha komai ba har sai sun kammala duka maganganun da zasuyi through video call. Yasan halinsa,yana da tsananin zafi yana kuma da masifar kaifin karantar mutum,wanda banda shima ya zama mutum me tsananin iya takunsa yayi imani da tuni labari ya jima da shan banban. Yaci wuya ya kuma tsallake turaku gwaji da jarrabawoyinsa sosai kafin yakai matsayin da yake kai a yanxun. Saidai kuma tsakanin jiya zuwa yau burinsa ya fara fadada. Ya fara jin cewa yana buqatar budawa a harkokinsa fiye da wannan da yake ciki a yanxu,yana buqatar qarin kusanci da CEO fiye da wannan kusancin........yana so matakin da suke kai sufi haka shi da shi na qullewa da kusanci tare da sakar masa ragamar komai na kamfanin fiye da yadda yake kai a yanzu. Sai ya zagayo saman kujera ya zauna saboda yadda yaji jikinsa ya fara week,alamu dake nuna abinda yasha din ya fara tasiri a jikinsa,duk da giya ce me tsadar gaske da yake kashe kudade masu kauri wajen siyota,bata bugar dashi buguwar da zata sanyashi fita daga hayyacinsa gaba daya. A sannan sai yaji bashi da wani sauran muradi daya wuce yaji muryarta,gaba daya taswirar qwaqwalwarsa ita take hasko masa cikin shiga da dressing daya dinga ji kamar yayi fiffike ya kamo ta,don haka ya jawo wayarsa ya fara gwada number dinta. A karo na uku kenan daga dazu zuwa yanzun da ya fara kiran nata bai samu isa gareta ba,saidai a yanzun cikin sa'a......har ya fidda rai da tsammani......dab da zata tsinke sai aka daga. "Kin barni da kewarki ko?" Ya fada murya can qasa. Shuru tayi tana sauraren yadda muryar tashi ke fita kafin ta motsa bakinta a hankali "Ka wuni lafiya?" "Ba lafiya ba......nayita kewarki ne kamar na zauce.....don Allah.....ki bani daman ganinki koda zuwa gobe ne MEENAL". Wani siririn murmushi ta saki,irin wanda take saki din a duk sanda wani cikinsu ya kirata da stamp name dinsa " Ba yanzu ba" Ta bashi amsa,amsar da a zahiri da gaske take,ta fito ne daga qasan zuciyarta. Ba kasafai take baka damar ganinta ba a sanda ka damu da ka ganta din,muddin akwai mission a kanka saita kaika matakin da take da buqatar kaje din. "Zan katse kiran,bacci ne a kaina,zan sauka saida safe?" Tayi furucin da sigar tambaya,bawai don tana da buqatar amsa ba. Bai samu sararin cewa komai ba t gintse kiran tana aje wayar a gefanta tare da bin wayar da kallo "Mika'il" Ta sake maimaita sunan tana gyada kai. Shima bin wayar yayi d kallo kaman sakarai "Zatayi girman kai,zatayi izza tun a ganin farko na sani......amma kuwa zuwanki hannu bazaiyi wahala ba 'yammata" Ya fada a sarari yana lashe baki hadi da sakin wani shu'umin murmushi. Yana shirin aje wayar wani kiran ya shigo masa. Mato sunan dake rubuce da number dake kiran nasa. Wani zunkudawa yayi sanda ya gama hada haruffan me kiran nasa saboda yadda kanshi ya fara nauyi,ya daga wayar ya sakata a hands free ya ajiyeta,sannan ya koma da baya ya jingina yana saurarensa "Sai ogaaaaaa.......sai bosssss" "Ya akayi mato......nasan kiranka alkhairi ne da kuma samuwa" "Ba kadan ba kuwa.......na samo mana wani sabon zone na caca.......harka ruwa ruwa.......kudi faca faca.......A wanki gara......abun kuma babu kama" Gyara zamansa yayi sosai yana bashi hankalinsa. Baya wasa da harkar caca kwata kwata,suna daya daga cikin abinda ke kawo masa maqudan kudade bayan kamfanin jadda DIAMONDCHORE da ya zame masa lamba daya "Kaman yaya?,yimin dalla dalla,don wutata ta kusa daukewa" Ya fada muryarsa tana dan rangaji. Yasan waye ciki da bai dinsa,tunda ya fadi hakan kuma ya gama fahimtar abinda ke faruwa,don haka ya tattara bayanansa ya gyara zamansa yana cewa "Wani gurin caca wanda na tabbatar a wajenka me gida local ne......akwai 'yan wasa na haqiqa amma kuma kai tsaye na fahimci cewa gidadawa ne.......basu da wani wayewa kwata kwata a cikinta.......akwai kudade amma fa a qasa,na tabbatar a bugu daya zaka tarwatsasu ka kuma yi gaba da duk wani abu da suka shigo cacar dashi" Wata shu'umar dariya ya saki "Mato nawa" Ya furta maganar mato din na masa yawo saman kai,saidai gajimaren da yahau ya hanashi tsaiwa su qarasa maganar,don haka ya sanya hannu ya katse kiran kawai yana furta "Munkaila bisa kansu" Cikin mutuwar jiki da kasala. *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* _________________________ *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 29 *SOUTH KOREA* *_THE CAPITAL OF SOUTH KOREA (SEOUL)_* *_Yanghwa-ro to hongdae geori_* Yanghwa-ro daya daga cikin lafiyayyun street dake da wani irin daddaden yanayi a kowacce safiya cikin anguwar hongdae dake tsakiyar south Korea. Yanayi ne me me dadi dake wanzuwa a kowacce safiya cikin street din dake da wani irin shuru da nutsuwa gami da nisanta da kowacce irin hayaniya daka iya damun ruhi ko matsantawa nutsuwar dan adam. Ga duk ma'a bocin fitowa da sassafe tsakanin yanghwa-ro zuwa hongdae geori zai zame masa abu me wahala baisan baqin fuskar matasan Nigerians din guda biyu ba. Zaratan matasa masu wani irin kyan zubi na halitta da kuma ajiyayyen kwarjini da kuma haiba. Yaya da qaninsa wanda fitowa jogging kusan kowaccw safiya ya zame musu kamar al'ada. Muhammed FU'AD,da kuma musaddiq hamza kibiya wanda yake daga gefan Muhammed FU'AD din. Idan yayi kamar zasu daidaita wajen sassarfa me kama da gudun da sukeyi sai ya zame har sai FU'AD din ya wuceshi yana fadin "Eheennn......don't stop.....don't stop" Da wata iriyar husky voice da Allah ya huwace masa wadda ke cakude da nishi kadan na gudun da suka dauko. Yayi kaman zai tsaya din ya kusa sau biyar......hakanan shima yake zaburar tashi har zuwa sanda suka iso daidai wani guri. Guri ne da kusan kowacce unguwa take da nata wanda aka tanadeshi aka killaceshi domin hutawar jamaar unguwar cikin wasu kujeru da shimfidaddun tsirrai da suka wadatu da tsafta suke kuma samun kulawa yadda ya kamata. Ruku'u musaddiq yayi yana cakewa a wajen,ya kama gwiwoyinsa da hannunsa yana sauke nishin wahala gumi yana fita daga sumarsa zuwa goshinsa. "Oh shit" FU'AD ya fada yana jan birki,sannan yayi reverse yayo kwana da hanzari yana dawowa daidai inda musaddiq ya cake. Baice masa komai ba ya kama wuyansa ya cafka yana tadashi tsaye sosai saman qafafunsa,abinda ya sanyashi sakin wata qaramar qara yana matse kafadunsa "Sorry hamma......am really tired wallahi......i try hamma......kusan minti talatin tunda muka fito muke wannan gudun.....ko doki hamma sai haka" "Shut your mouth.......malalaci kawai......da wanna halin da dabi'ar naku meye marabarku da mata?,inajin mun kusa baku jilban da dankwali kuna daurawa ko?". Sosai dariya taso murqushe musaddiq,amma yasan bai isa ya yita a gabansa ba. Duk wani training nasa suna shanyewa amma yanzun don ya gaza cikashe mintunan gudunsa shine ya zama malalaci har zasu fara dauka zani?. Zanin da ya sake tunawa ya sanya dariyar da yake boyewa ta qwace masa da gaske,don ba wanda ya hango daure da zani sai saddiq. Sakin qeyar nashi FU'AD yayi yana watsa masa wani irin kallo da lumsassun idanunsa dake da wani irin kaifaffen kallo me kashe duk wani zarra ta mutum "Are you laughing?,da gaske baka gaji ba......zamu qarasa gida a haka,ko sau daya kuma ka sake tsayawa kasan sauran......salary dinka na wannan watan zan saka abba yayi sadakarshi" Ya fada yana gyara doguwar socks din qafarshi daya rufe mass har gwiwarsa. Kayan motsa jiki ne a jikinsa,amma yadda sukyi masa kyau zata tsammaci ya sanyasu ne don ado. Sun fidda duk wata qirar qarfi da Allah ya bashi,murdaddun muscles dinsa zuwa shaffen cikinsa da qirjin yafi cikin dagowa. "Hamma......wallahi Allah ba abinda kake tunani bane" Ya fada cikin karya wuya da sanyaya murya "......Allah hamma kawai musaddiq na hango daure da zani da dankwali......" Sai ya qarasa fadi yana bushewa da dariyar data sanyashi ya murmusa dole. Dariya yake sosai yana kuma kallon fuskar fu'ad din. "Iyakarshi kenan" Ya furta a ransa. Murmushi shine maqurar dariya a wajensa ko yaya kuwa abu yakai. Kai ya girgiza kawai qasan ransa yana tuno wasu abubuwa na sadiq da musaddiq din. Suna da wani irin wasan da inda ace shima irin farouq ne baya jin yaran zasu shuka abun arziqi idan ba shiririta ba. Har kullum abba na jin dadin jajircewarsa a kansu,don shima din sun maidashi kakansu qarfi da yaji,yayita masifa yayita masifa amma a banza,maganae mutum guda ce take ratsasu.....zancan mutum daya ne yake zama daram saman kansu shine zancan muhammad fu'ad. Bai sake ce masa komai ba sai ya miqe yana zaro wayarsa dake aljihun wandonsa. Iphone 16 sabuwar qira wanda babban hoton wata kyakkyawar matashiya ya mamaye ilahirin fuskar wayar. Kyakkyawar bafulatana me wani sassanyan kyau,cikin kamilalliyar shiga data qarawa hoton da Fuskarta kwarjini. Dududu shekarunta da suka nuna cikin idanunta da kuma fuskarta goma sha takwas ne.....sha takwas din da aka soma gangarawa cikin sha tara. Kalmomin sirri ya sanya ya bude wayar,sannan kai tsaye ya tafi zuwa ajiyayyun lambobin da basu da yawa cikin wayar. Akan wata number dake dauke da sunan ABBA NA ya tsaya,ya danna kira sannan ya maidata aljihunsa yana gyara zaman Bluetooth guda daya dake manne a kunnensa yana bada hasken qyallin wuta time to time. Sai kuma ya fara takawa a hankali ba tare daya cewa musaddiq komai ba,wannan ya bawa musaddiq din daman biyo bayansa a nutse can qasan ransa yana murnar yadda aka haqura da jogging dinnan haka. "Shi ya dauka kowa kamarshi ne me jikin qarfe da baya gajiya da motsa jiki......idan na hada qarfi ina zan kaishi" Yayi gulmarsa a ransa yana biye dashi tare da qare ma bayansa kallo. Shi kansa yadda yake da ginannun muscles yana burgeshi yana kuma bashi sha'awa,amma bashi da juriya da qarfin halin da zai building muscles ma jikinsa kamar nashi. "Abba ka farka?" Ya fada cikin matuqar nuna kulawa bayan yayi masa sallama. "Okay gamu nan qarasowa" Sai ya katse kiran ta jikin Bluetooth din nasa sannna ya dan soma sassarfa yana cewa musaddiq "Oya.... Mu qarasa gida" Kaman zaiyi kuka hakanan ya taka ya soma bin bayansa. Kafin su qarasa gidan sai da yaji kaman zai zube,cikin ransa yake ganin gaskiyar sadiq ashe da yakanyi ciwo ko ya qirqiro uzurin qarya duk sanda ya tasheshi ya rakashi jogging. Har gwara ku shiga gym room dashi,wannan idan suka faki idonshi sai su zabi machine daya su haye su kasheshi ko su rage gudunsa sosai. A hankali suka qarasa hongdae geori cikij estate din dake unguwar. Gida me lamba ashirin,yayi tsaye yana danna bell yayin da qirjinsa ke dagawa sama da qasa yana fidda Zazzafan huci daga bakinsa. Ya jiqe sharkaf da gumi,musaddiq kuwa tuni ya zube saman step biyu dake bakin qofar gidan yana numfashi da sauri da sauri. A hankali qofar ta bude,dattijon mutumin nan Alhaji hamza kibiya ya bayyana cikin wata lallausa kuma kyakkyawar abayar qasar morocco ruwan zuma. Ba abinda ya sauya tattare dashi sai shekaru da suka fara bayyana kansu a jikinsa.....bayyana ba me muni ba saboda daular rayuwa da kuma jin dadin da yake ciki daya zarta ya kuma ninka na shekarun baya ta hannun zaratan yaransa guda hudu dukka maza. Da murmushi a fuskarsa kamar kullum yake kallonsa "Ina dayan me babban suna?" Alhaji hamza ya tambaya saboda idanunshi basu hango musaddiq ba sam sam. Da baki ya yiwa abba cunensa,abban ya dora hannu saman baki yana bushewa da dariya "Kai......taso dalla.....dama babu me maganinku ai sai me babban suna......tashi nace mace kawai.....koni nan da shekaru suka fara turamin ina gudun nan,kuma ka gani da idanunka.....ina zakuyi qwarin damu uwayenku mukayi?,baku da aiki sai hawa mota sai ciye ciye da shaye shayen banza" Abban ya fada yana wurga hannu. Kai ya daga da qyar yana duban abban "Abba wallahi.....bazan iya tashi ba da gaske,qafafuna kamar zasu tsinke.....gudun fanfalaqi yau hamma ya saka mukayi" Yadda yace gudun fanfalaqin ya tilastawa abba sakin dariya,yayin da FU'AD ya girgiza kai kawai. Suna ganin iskanci a gidan wajen sadiq da musaddiq,kullum kaman basa girma,kullum kallon kansu sukeyi kaman qananun yara. "Tunda ba zaka tashi ba ai idan wancan qadangare ya shige maka riga ai ka nema hanyar gida" Wani mugun tsalle ya doka sai gashi a tsaye kyam "Yauwa.....dan nema ja'iri,zo ka wuce kaji me babban suna" Abban ya fadi yana komawa ciki fuad yabi bayansa yana dariya qasan ranshi. Har yanzun musaddiq yana tsoron qadangare kenan tun yarinta?,abun ya dinga bashi mamaki don shi baiga wani abun tsoro a qadangare ba. Suna shiga yana biyo bayansu yana dube dube yana fadin "Wallahi abba ka kusa sakani na saki fitsari a wando......yanzu inda a gaban nasreen......" Tsaf ya kame bakinsa ba tare daya qarasa ba saboda kallon da FU'AD ya jefeshi dashi,ya sosa kanshi ya sauya akalarsa zuwa kitchen da kake iya hangensa tarwai ta falon. Saman kujera ya zauna a nutse yana warware takalman qafarsa,abban ma ya koma inda ya tashi ya zauna yana daukar mug tare da ci gaba da kurbar zazzafan tea din dake ciki. "Sannu da gida abba" Ya sake fada yana dan jingina bayansa da kujera "Sannu fuad shugaban 'yan motsa jiki" Abban ya amsa masa da murmushi tare da maida dubansa ga takalmansa daya cire. Duk abinda ya cire ko yayi amfani ddashi yasan ya killace shi,zaiyi wuya kaga ya watsar da kaya ko wani abu makamancin hakan. Ya tabbatar hakan baya rasa nasaba da matsananciyar tsaftarsa da kuma yadda rayuwarsa ta ginu a shekarun baya,cikin gwagwarmaya da daukar nauyi da lalurar kanshi. Yana da bala'in tsantsami shi yasa abubuwa da yawa ya gwammaci ya tsaya ya yiwa kansa. Idan ka ganshi a kitchen yana hada breakfast ko yana dafa tea zaka rantse da Allah ba shine dan marayan zakin nan ba mamallakin kamfanin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ba,wanda jaridu zuwa mujallu kullum kwanan duniya ke zumudi da rububin yin rubutu a kansa ba domin samun daukakarsu da qaruwarsu. Duk wani rubutu ko labari da wani gidan tv jarida ko radio zasu fitar akan MUHAMMAD FU'AD tamkar daukaka ce a tare dasu. Matashin mamallakin kamfanin haqar ma'adanai na diamond ne da makamantansu. Kifi daya a ruwa da manyan masu sarrafa gwalagwalai da diamond na duniya suke saka fatsarsu domin kamo kaya daga kamfaninsa saboda inganci da kyansu. Diamond guda daya daya taba tsinta a sanda yake tsakiyar bautar qasa can cikin jahar kogin nigeria. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 30 Dan bautar qasar da bai wuce sati biyu a camp ba.....wanda ya fita yawon ganin gari shida shaqiqin aboki amini kuma dan uwansa farouq hamza kibiya. Haka kawai yayi sha'awar bin daya daga cikin matasan da farouq ya saba dasu a teburin me shayi wanda duk dare sai yaja fu'ad koda kuwa bayaso,suje su zauna su sha hira suga yanayin gari da mu'amalar mutanensu. Da fari fu'ad baya so,daga bisani ne ya sake a hankali bayan da yayi tunanin wannan karin maganar ta bahaushe "Tafiya mabudin ilimi". Ba yadda zaiyi ya samu ilimin muddin yana nade a camp da kuma dakin. Abinda yafi damunsa yake hanashi fitar yadda 'yammatan camp din nasu harma da cikin garin suke da son wasa da wargi gami da son shigewa mutum. Shi kuma abu guda da yafi tsana kenan kaf fadin rayuwarsa. MACE halitta guda daya da ba kasafai yake mata uzuri ba a rayuwa.....halittar da yayi amanna ya kuma saddaqarwa kansa su da KUDI tamkar rai ne da bugun numfashi. Halittar da ya gama karatunta cewa tafi bawa KUDI muhimmanci sama da komai.....kwadayyar halitta me son kanta.....mara tausayi kuma mara imani koda akan dan cikinta ne kamar dai MAAMANSA. Farouq yaso hanashi binsu inda suke haqar a sirrance saboda sanin tsananin risk din dake wajen. Bawai iya barazanar fadowar rami bisa kan me haqa ba.....a'ah.....hatta na a tsakaninsu suna iya farde wanda ya tsinta din suyi kashe mu raba da abinda ka samu. "Farouq......ragon namiji shike tsoro.....faduwar gaba asarar namiji......ba'a haliccemu don mu kwanta ko mu zauna iyayenmu su dinga bamu suna mana wahala ba.....an halicci Muhammad fu'ad don yayi gwagwarmaya ya kuma fuskanci challenges a rayuwarsa.......na fara gwagwarmaya tun daga sanda na fara fahimtar Muhammadu sunana ne......na fahimci kuma MAAMA itace ta haifeni......" Ya qarasa maganar wani abu yana tsirgawa daga tsakiyar muryarsa har cikin qwayoyin idanunsa "Wai anni bata hanaka zancan maama dinnan ta haka ba?" Farouq yace da fu'ad a sanyaye. Wani malalacin murmushi ya saki ya sunkuya yana ci gaba da daura boot din qafarsa da kyau. Ta yaya MAAMA zata bar zuciyarsa wai?,ta yaya?har abada sai randa qasa ta cike idanunsa. "Na shirya zan wuce sai na dawo" Ya fada yana miqewa tare da zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban farouq. Harara ya watsa masa sannan ya miqe da hanzari "Ina zan barka ka tafi kaje ka bace ka jamin jarfa a wajen abba......qafata qafarka.....idan ma zamu bata mu bata tare" Yayi maganar yana miqewa. Miskilin murmushinnan nasa ya saki ya juya yana kada kai. Ya sani shine dai kawai a gaba kafin abba da yake qorafi akai,kawaidai bazai iya barinsa ya tafi bane ya barshi,wanda wannan daya daga cikin danqon qauna da 'yanuwantaka dake a Tsakaninsu. Yana shiryawa yana mita har ya kammala suka sulale suka fice daga gidan da aka musu masauki ba tare da kowa ya sani ba. "Ni bansan me zakayi da wata mahaqa ba.....dukkanmu abba jira yake mu kammala wannan service din ya bude mana namu kasuwancin" "Ta yaya zaka zama cikakken dan kasuwar da yasan daraja da kimar dukiya baka iya gwagwarmaya ba?.kana daga zaune ba tare da ka tara komai ba?" Fu'ad ya masa tambayar yana kallon hanya kawai ha tare daya kalli farouq din ba "Gwagwarmaya cikin wadannan qedarun?,don kawai Samuel ya gaya maka za'a je da kai?,suna da hadari fa fu'ad?" Murmushi ya kuma saki hankali kwance,har yanzu kuma bai kalli farouq din ba ya sake bashi amsa "Muhammad fu'ad dan arewa.....ya fisu hatsari.....zaka gane hakan idan sukayi yunqurin yin wani abu". Maganarsa ta tabbata kuwa a wajen farouq. Tun isarsu gurin komai ya fara bayyana. Da wani irin kallo ayarin suka fara binsu saboda ganinsu baqin fuska kuma 'YAN AREWA dake yara yaran hausa. A haka aka soma tafiyar har zuwa kebantaccen wajen da suke haqar ba dare ba rana don samo ma'adanai. Samuel shi ya dauki dukkan wani risky ya shige gaba aka barsu har suka isa gurin cikin wadanda aka aminta da shigarsu wajen. Duk inda fu'ad zai motsa farouq yana biye dashi,sam wajen shi baiyi masa ba,hakanan a tsorace yake da wajen,shi sai ya zamana kamar me gadin fu'ad ne a wajen. Duk wani motsi da za'a yi a wajen ko wani da zai tunkarosu hankalinsa yana wajen. A hankali ya tura kansa ramin da fu'ad ke ciki wanda yayi zurfi "Mutanen nan fa hankalinsu a kanmu yake,duk wani motsinmu suna ankare dashi" "Karka damu" Kawai yace dashi saboda wani abu daya fara hanga wanda ya dauki hankalinsa matuqa. "Farouq" Fu'ad ya kirayeshi da wani sauti me jan hankali wanda yaja hankalin wanda ke ramin daura dasu ya kumayi tsai yana jiran jin dalilin kiran. Tura kansa farouq din yayi yana cewa "Menene" "Na samo.....na samo" Ya fada da wani irin excitement,yayin da zuciyarsa da kwanyarsa suka cika da mamakin samun abinda bai taba zaton zai samu ba koda kuwa a mafarki. Har a qasan zuciyarsa ya gwada zuwa wajen ne kawai don samun experience da karantar yanayin yadda irin rayuwar yake. "Duba ka gani farouq" Ya fada yana miqo masa. Farouq din da hanzari ya dira ciki yana toshe bakin fu'ad "Keep quit fu'ad.....ka tono masifa" Ya fadi a tsorace. Da wani kallon mamaki yabi farouq din "Kaman ya?" "Kamar yadda ka sani.....kowa dake nan wajen abinda yake zuwa nema kenan kwana da kwanaki.....kana baqo wanda aka yiwa alfarma.....zuwan farko kayi kacibus da abinda yake dukkansu shine burinsu?. Akwai shugaba a cikinsu wanda duk wanda ya samo sai yabi qarqashin umarnin shugaba......zai kuma danqashi a hannunsa....." Tsaki fu'ad yaja saboda dokokin rainin wayo da yaji farouq yana karanto masa wanda shi baisan dasu bama,don ya fishi zama da hira da Samuel "Su sukamin wahalar?,ko an gaya maka nazo nan dinne don na yiwa wani qaton zindiqin arne aiki?.....let's go mu wuce gida" Ya fada yana kama ramin tare da nufar hanyar fitowa. Sanda yayi tsalle ya qarasa fitowa baima lura da wadanda suka kewaye ramin ba,har sai daya gama karkade jikinsa yaji sadiq daya fito daga bayansa ya zungureshi. Lafta laftan yare masu mummunar siffa tun daga halitta zuwa zuciya. Mutumin da alamu suka nuna shine shugaban yana tsaye a gaba. Ya sake matsowa gaba kadan ya miqawa fu'ad hannu.. Sarai ya fahimci abinda yake nufi,amma yadda yake kallonsu da dukkan wani motsi nasa cikin izza da nuna isa ya sanyashi jin har cikin ransa bazai taba iya bashi abun ba. Ballantana abinda yake wahalarsa kuma guminsa ne. Ko daya babu me haqqi a ciki bare yayi tunanin cinyewar zai zama laifi har a wajen Allah. "Ban gane ba" Fuad din ya furta cikin dakiya da jarumta "Ka miqo diamond din daka samu aka ce...!" Daya daga cikin wadanda ke daura da ogan ya furta murya a kausashe yana sake matsowa dab da fuad din saboda nuna masa tsananin buqatar abun da suke da,da kuma nauyi da girman abinda yake dauke dashin. Cikin qasa da second biyar ya gama fahimtar motsi da niyyar kowa. Tabbas!.....tabbas babu abinda yafi dacewa dasu muddin yana da buqatar tsira da wanann abun face tserewa "Ka shirya farouq.......ka shirya gudun tsira da rai.....ko mu ko su,ka qarfafa zuciyarka da gangar jikinka" Ya furtawa farouq qasa qasa tare da damqe hannunsa da kyau. Kaduwa sosai farouq yayi da abinda yaji fu'ad din yana fada.....yasan halinsa muddin ya fadi sai ya cika.....amma kuma abinda zasu aikata din mugun ganganci ne da zai iya zama ajalinsu. Bai gama sauke wannan tunanin ba yaji qarar wani abu timmmm sannan yaji an finciki hannunsa. Sanda zai duba sai ya samu fuad dinne ya kaiwa ogan nasu mummunan naushi har sai da yakai ga zubewa qasa war was,da wannan ya janye hankalinsu suka tsallakesu,saidai ko taku uku basuyi ba aka samu wadanda suka rufa musu baya bayan fusatacciyar tsawar da ogan nasu ya buga musu wadda har yanzu yana zaune a qasa "Catch them!!" Ya fada qarajin hasaso asarar dake tallafe dashi tare da tsoro da razanin rasa abinda yake tamkar shine cikamakin burin rayuwarsa. Wani irin gudu tamkar a indian film fu'ad ya dinga yi,abun har yaso yafi qarfin farouq banda shi dinma yaci sunan me sunan. "Mu tsaya fu'ad.....harbi sukeso su fara" "Wa ya gaya maka ana gudu da waiwaye?......just run!!,run kawai.... Kada ka sake waiwayawa". Ganin kamar farouq din ya fara karaya ya sanyashi yin wani juyi ya maida farouq din gaba shi yana biye dashi. Da gaske dai suka fahimci zaratan samarin 'yan arewan guda biyu na niyyar kufce musu,sai kawai suka fara harbi,harbin da ya gigita farouq qwarai da gaske ya kuma dinga kiran sunan fu'ad akan su maida musu abinsu. "Basu isa ba....don ba abinsu bane,arziqi ne na ubangiji daya shimfida a qarqashin qasa saboda bayinsa,ba don su kadai Allah ya ajjiyeshi ba" Ya fada a zafafe cikin yanayin gudun yana sake fusgar hannun farouq da kyau. Wani irin samfurin gudu da fu'ad din keyi riqe da hannun farouq sai daya zama abun kallo a wajen farouq din. Bai taba tsammatar iyawa ko qwarewa haka a tare dashi ba wajen sanin kurdawa tsakanin manyan dutsuna da qananunsu ba sai a sannan. Bayan shafe dogon lokaci suna fafatawa Allah ya basu nasarar kufce musu "Park zamu wuce mu kwana a can daga can muyi gida......ba park na kusa da nan ba,ta gaba da nan" Fu'ad ya fadi yana kallon farouq "Ya zamu bar camp kuma bamu dauki komai namu ba......sannan kuma......" "Kana tunanin sun qyalemu ne?,kana zaton idan muka koma can din zasu barmu mu kwana da ranmu?" Fu'ad ya tambayi farouq wanda da alama baisan girman ta'addanci irin nasu ba. *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* ________________________ *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 31 ___________________________ Wani murmushi ya saki "Ai basu ba,ko jamaa da muke tare dasu sukasan abinda muke dauke dashi sunanmu matattu......maganar diamond da gold akeyi farouq.......kasan nauyi da girman ma'adanin dake jikinmu?......mutanen nan sun wuce duk sani da tunaninka.....ni kaina da na yarda mubi Samuel da shirina,na san kuma cikin su waye zan shiga,kaine nake zaton bakasan irin girman wajen da muka shiga ba.....banda saa tana tare damu bamu isa mu shiga wannan wajen bama bare akai ga samun abinda muka samu kuma har mu gudo lafiya lau dashi......daga yanzu har zuwa sanda zamu koma qasarmu rayuwarmu na cikin hadari......take care dude...." Ya fada yana bugun kafadar farouq da ya gama mutuwar zaune. Bin fu'ad kawai yakeyi da kallo yana mamaki. Yasan girman hatsarin fiye dashi amma yayi kaman bai sani ba?,ko a yanzun wannan uban wahalallen gudun ceton ran da sukasha shi kaman ma baiyi ba?. A yadda ya sanshi da I don't care manner da rashin shiga abubuwan rayuwa sosai bai taba zaton ya iya daukar risk da tarar aradu da ka ba sai a yanzu. Tun daga tashar da suka samu mafaka sukasan lallai an baza nemarsu,a daren suka haye motocin kaya dake lodin arewa suka wuto gida.......wanda sai daga bisani abba yasan komai. Yayi fada yayi fada kaman zai ari baki......ya kuma yi musu fadan da bai taba musu shi ba,musamman me babban suna da yake girmama sunansa yake kuma qaunar yaron har cikin ransa. ANNI ce ta sanya baki aka samu ya lafa sannan aka fara tunanin yadda zaa yi da abinda ya haqo din,tunda ya riga ya shigo hannu ba batun ace za'a maida musu. Bisa dukkan dokoki da tsare tsare kan tsaftatacciyar hanya aka tsara komai ya zama dukiyar da a yanzun suke juyata shida farouq dinsa. Abban kuma ya zame musu jagora madubi.....ma'adanin kuma ya zama shine kasuwancinsu.....babbar masana'antar karbar haqaqqun ma'adanai su tace su gyarashi su fiddashi xuwa manyan qasashe,irinsu china,south Korea japan UK da manyan qasashen dake hulda da cinikayyar ma'adanan qasa masu tsada da daraja. A nahiyar africa JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ya zama kamfani na daya da qasashen ke rububin karbar kaya a hannunsu bayan doke Coregeo mining company din da yayi. Kamfanin daya jima yana murza zarensa da kyau,sai gashi rana tsaka JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES yazo yasha gabansa ta ba zata,al'amarin daya haifar da takun saqa me girma a zuciyar kamfanin. Duk da fu'ad yasan da wannan......amma ya dauka normal competition da kishi ne da kan iya faruwa tsakanin kowanne kasuwanci,saidai ga mamallakin kamfanin JOE abun ba haka bane. *_D A W O W A_* Dubansa abba yayi bayan ya aje mug din hannunsa "Kwanaki nawa ya rage mu tafi ne me babban suna?" Zama yayi sosai yana goge gumin fuskarsa da dan qaramin towel din da magaji(hadiminsa) ya miqo masa. "Ba zamu wuce sati daya ko kwana biyar ba abba,hankalina yana kan anni......jikintan nan ya fiya matsawa da yawa" Yayi maganar alamun abun yana tabashi ya bayyana har saman fuskarsa. Idanu abban yadan zuba masa,har a ransa yana cike da zallar mamaki na yadda me babban suna ke damuwa da anni da rayuwarta fiye da dukkansu su ukun. Annin da abban yake ganin ba itace halitta ta farko data cancanci samun wannan qauna da kulawa daga gareshi shi din ba......annin da yake ganin kulawar da yake bata baifi ya bata kaso hamsin cikin dari ba.......ita kanta wasu lokuta tana sanya damuwa a ranta game da inda yafi karkatar da kulawar tasa sama da daya bigiren da shine dolensa,.....kuma akafi buqatar hakan daga gareshi. "Yanzun haka ma nan da awa daya zan fita,zamu gana da ceo na Labrilliante company,zan miqa musu iya abinda zasu samu.....don abba wannan karon tunanina ya fara sauyawa" Maganar fu'ad cikin tatacciyar nutsuwar nan tasa da wani irin jan aji kamar mace ya dawo da Alhaji hamza daga tunaninsa "Wanne tunani ne fu'ad?" Zamansa ya gyara sosai yana bawa abba dukkan kallo da hankalinsa "Abba......a yadda mutanen nan daga kowacce qasa suke rububin siyan resources namu da muke fiddowa daga qarqashin qasar da Allah ya shimfida mana kadai ya isa ka fahimci suna amfani damu ne suna kuma amfani da damarsu......yanzu haka a daren jiya kafin na kwanta sai dana karba kira daga wani company dake japan bayan ainihin kamfanin da muke kaiwa kaya......suna taya kayanmu akan farashin da wancan kamfanin basa bamu......wannan shi yasa nayi wani nazari......abba ya kamata qasarmu ta amfana da wadannan ma'adanai masu tsada da daraja,wanda mu Allah ya mallakawa su.....abba inda a qasarsu wadannan ma'adanai suke,babu wani baqar fata daya isa ya sameshi.....it's hardly ka iya isa wajen......nayi tunanin bude babban company da zai dinga sarrafa wadannan ababen zuwa kayan qyale qyale na mata.....don dama company daya muke da na alhaji rayyan(dangantakar zuciya),shi kuma duwatsu masu daraja suke sarrafawa ba gold ko diamond ba". Shuru abba yayi yana girgiza kai. Tabbas fu'ad din yazo da tunani me kyau daya kamata ace tuntuni sun yishi "Na yarda da wannan tunanin naka.....to amma fu'ad qarqashin haka akwai tarin matsaloli da qalubale......" "Na sani abba......insecurity na qasarmu ma kawai qalubale ne......amma a hakan.....ya zama dole mu raya qasarmu da kowanne qaramin chance da muka samu a rayuwarmu......tsoro da tunanin asara ko faduwa shine abinda zaici gaba da kasheta kowacce rana......bayan tsoron dauko shi akayi aka dasa mana shi a zukatanmu......kuma ake da buri da fatan ganin ci gaba da wanzuwarsa har zuwa rayuwar na bayanmu" "Best son ever" Abban ya furta yana sakin wani irin murmushi tare da jin qarin alfahari da fu'ad din,gefe guda kuma yana taya ainihin mahaifinsa murnar samun nagartaccen yaro mara tsoro irin muhammad fu'ad din. Qas yayi da kansa cikin girmama abban "A tayamu da addu'a abba" "Kullum cikinta muke" "Allah yaja kwana,ya qara lafiya me amfani" Ya masa addu'ar da yake jinta har cikin zuciyarsa. Agogon dake manne a bango ya kalla,sai ya miqe a nutse yana cewa "Zan qarasa ciki abba na shirya kada na sabawa lokaci" "Hakan yayi kyau" Abba ya fada fu'ad din yana sake burgeshi saboda yadda ya dauki alqawari da matuqar muhimmanci kaman yadda yake girmama lokaci. A nutse ya tura qofar dakin da sallama a bakinsa,duk kuwa da yasan ba wanda zai taras a ciki. Dakine da duka duka basufi sati guda a cikinsa ba......amma har ya kama ya kuma rine da sassanyan qamshin nan nasa dake iya bawa zuciya nutsuwa da kwanciyar hankali koda cikin radadi da qunci take. Towel din hannunsa ya rataye,ya kuma matsa gaba kadan ya ajjiye takalmin motsa jikinsa wanda daga ranar da suka tasamma barin Korea sunansa shara. Baya yawo da kaya,kowacce qasa zaije,koda kwana nawa zaiyi single yake tafiya abinsa,saidai yana sauka a qasar komai da zai buqata na amfani zai sanya a tanadar masa,yana gama amfani dashi kuma a nan zai barshi ya qara gaba. Matsawa gaba kadan yayi gaban wata mini dispenser da tafi kama da tulun zamani wadda ke zaune saman wani kyakkyawan table kusa da mirror,ya dauki disposable cup ya matsi ruwan dake da madaidaicin yanayi ya fara sha a hankali bayan yayi tsaye gaban madubin idanunshi a kai kamar me karantar yadda yake zuqar ruwan zuwa cikinsa. Ya gama ya ajiye saman madubin yana fidda siririyar iska yana ci gaba da kallon fuskarsa a madubin. Kyakkyawar sumar kansa data wadatu da tsafta ya taba sannan ya gangaro zuwa madaidaiciyar qasumbarsa data hade da gemunsa wadda ta zamawa fuskarsa wani lafiyayyen ado daya qara fidda zahirin kyawun fuskarsa,ta kuma qara masa wani mahaukacin kwarjini. Gemun da qasumbar daya zama topic of discussion a wajen 'yammatan da suka marmace a kansa. Kusan kowacce tana gayawa kanta namiji babu gashi a fuska ai mace ne,bata taba ganin qasumba da gemu da yakai kyan nasa ba......tsabar macewa a soyayya ne.....ko kuma zallar tsagwaron gaskiya suka fadi?. Rigar jikinsa ya yaye zuwa sama sannan ya zareta ya ajjiyeta saman gadon,wannan ya bawa Ginannun muscles din jikinsa bayyana muraran. Muradden jikin da zai gaya maka adadin lokutan da aka bata ana bashi kulawa ta fannin lafiya da cin lafiyayyen abinci me gina jiki. Yayi taku daya don dauko bath set nashi zai wuce toilet sai ya fasa,ya dawo da baya ya dauki wata farar samsung dake ajjiye saman mirror din. Yaga miscal amma sai ya fara maida hankalinsa ga dalilin daukar wayar,ya latsa ya fara lalubar magaji. Umarni ya bashi na abincin da zai hada masa kafin ya fito,saiya maida wayar yana shirin ajeta kira ya shigo wayar. Cak ya tsaya yana kallon sunan dake tsalle saman wayar. MOM kaman yadda farouq ya dauka da hannunsa yayi masa saving. Kafe sunan yayi da idanuwa,wayar tana kadawa hade da zuciyarsa. Sunan yake tuna ma'anarsa da kyau cikin kwanyarsa.....wadda aka maqalawa sunan ta cancanci wannan sunan kuwa anya?......ta dace data karbi sunan?,nata ne sunan da gaske?. Kamar bashi da idea akan yadda ake daga waya,haka yaci gaba da kallon wayar har ta qaraci ringing ta katse. Ya sake daga qafarsa zai wucs kiran ya sake shigowa. Kamar dai dazu a yanzunma haka ta gama kadawa ta katse,kira na uku kuma ya sake shigowa immediately,saidai akasin dazu,yanzu sunan daya fito akai ya banbanta dana dazu. Lovy dovy shine sunan daya bayyana,sai ya saki qaramin murmushi yana dawowa baya kadan. Kafin ya daga sai daya kalli lokaci,tabbas ya tsaya saurarenta ya tabbatar saita kwakwashe masa duka mintunan daya tsara zaiyi a gidan ya fice zuwa Labrilliante amma hakan bai sanya ya fasa dagawa ba,ya sanya wayar a kunnensa. Da siririyar baby voice dinnan nata tayi masa sallama. A nutse fuskarsa a sake ya amsa "I will call you back habibty.....nan da one hour haka?" "Yes habibee.....byeee" Ta fada cikin rashin damuwa da kuma fahimtarsa a duk sanda ya sako mata uzurinsa. Wayar ya mayar ya ajjiye yana murmushi,daidai sanda a daya BANGAREN......... Ta daga kai ta kalleta sanda take zaune a gabanta "Waya yake amsawa hajiya" Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta bayan computer ta gaya masa ana amfani da layin ta hanyar amsa wani kiran *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 32 ___________________________ Waya kuma ake amsawa?” Ta tambaya cikin wata irin isa sa ginshiri tana qanqance idanunta,qwayar idanun nata suna kan wadda tayi maganar. Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci “Eh haka ne”. Juyawa tayi ta zauna sosai tana fesar da iska me zafi daga bakinta. Ta qanqance idanu sosai tare da zubawa guri daya idanu,abinda zai baka tabbacin akwai wani radadi me yawa da take ji daga cikin zuciyartata “Alamu kenan suna nuna yaga kiran,nice dai…….nice dai da bazai amsa wayata ba,nice dai da bazai saurareni ba sai a sanda yaga dama ko kuma aka bashi umarni?” Ta qarashe maganar ta hanyar yiwa kanta da kanta tambayar. Tambayar da bata haifar mata da komai ba sai qarin qunci da bacin ran da ya sanyata miqewa tsaye. Hannunta ta dunqule ciki juna,ta fara kai kawo tana naushin tafin hannunta da daya hannun data dunqule waje guda. Ba shakka tayi sake ba dan qarami ba,ba shakka kuma hajiya mariya tana son jefa kanta tsakiyar shingen da ba nata ba. A baya tayi tarin ayyuka game da hakan,amma idan har tace taga nasara tattare da hakan to tayi qarya me yawa ma,zata iya kiran ayyukanta na baya da JIYA I YAU,tana tsaye a waje daya babu sauyi ko qanqani,zata zuba idanu ne abubuwa mafiya daraja da kima a rayuwarta…..kuma mallakinta amma ace suna ci gaba da subuce mata?,suna ci gaba da zama haramiya a gareta?,shin zata yarda da zamowa ‘YAR RAKIYA ko kuma taci gaba da wanzuwa a mazaunin ‘yar kallo?. “Ba zata sabu ba!” Ta furta a zabure sannan ta juya da sassarfa tana daukan mayafinta dake yashe saman kujera “Tashi samira muje” ta bawa hadimar tata umarni,wadda ke zaune tun dazu guri daya tana duban kai komo da maganganun da takeyi ita daya “Ina hajiya?” Ta tambayeta murya a lanqwashe. Tayi imanin tunda har ta buqaci fita irin wannan afujajan ba shakka ba alkhairi a cikinta sam “Gidan alhaji hamza!” Ta bata amsa a tsawace da salon abun nan da ake cewa haushin kaza huce kan dami. Tsam ta miqe tana gyara daurin zaninta sannan ta wuce da sassarfa zuwa shiyyar dakunansu don dauko hijabi. Cikin jerin amintattu kuma lafiyayyun dakunan da mansion house din na alhaji hamza kibiya ya mallaka. Zaune take tsakiyar wani lallausan rug dake a gefe daya na dakin wanda aka masa rukuni da lausasan sofas qwaya uku da suka zamewa wajen tamkar wani dan qwarya qwaryar falo ne na cikin bedroom. Wani irin lafiyayyen daki ne da ba zai barka kasan safiya ko dare ba,zafi ko sanyi,damuna ballanta rani ba muddin ka kasance wanzajje a dakin. Daga saman rug din take zaune saman abun salla da zai baka tabbacin bata jima da kammala sallar walaha ba. Salla ceda bata taba wuceta a rayuwa muddin ba wani qaqqarfan dalili ya gifta ba,tun zamanin quruciyarta har kawo yanzu da girma da shekaru suka hau kanta. Shine kuma ya same mata sila da tsani na dawowa rayuwa hamza a shekarun baya,a sanda ta yanke zato da tsammani daga sake rayuwa dashi da kuma yaranta da suka zame mata sanyin idaniyarta. Wataqila nutsuwa da kamalar da fuskarta ta wadatu dashi yana da alaqa da wannan din,yawan ibada,yawan bautar Allah,yawan azumin tadawwu’i da babu wanda yayo gadonta a wannan fannin qafa da qafa irin muhammad fu’ad. Akwai haske sosai saman fuskarta,tana saye da atamfar chiganvy gold mekauri kyau da asalin tsada. Jikinta lullube da mayafi me kauri,yayin da yatsarta ke maqale da qaramin carbi irin na ma tsawa. Daga gefanta saitin kafadarta shine a kashingide,kana kallonsu zakasan magana sukeyi,magana kuma irin ta da da uwa,hira cikin nutsuwa qauna da kuma kulawa “Nikam saddiq……sake kiramin wayata mana,jakata tun ranar da akayi asibiti dani ban sake ganin gilmawarta ba,akwai muhimman abubuwa a ciki,harda kudaden Amna data bani ajiya” idanu ya zaro sannan ya miqe yana zama sosai “What?,anni?,dollars fa?” “Wallahi sadiq” ta fada a nutse. “To Allah ya tsananta rabo,don auta ta saka buri akan wannan ajiyar,naji tana lissafin abinda zatayi dasu idan ta dawo” ya fada yana cusa hannunsa a aljihu yana laluben wayarsa. Fuskarta anni ta shafa tana fadin “Idan har ba’a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane bawa”. Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din…..din,sautin dake gaya musu lallai kiran ya isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar. Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa kunnuwa zuwa kwanyarta. Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana tasowa can qasa qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin. Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen idanunta da suka qara girma saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me tsaho data rufe rabin fuskarta baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta zauna sosai tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin yake fita. Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin safe kaman yadda suka saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace dai kawai su buda jakarta su dauki kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun fita. Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta ta tattare gashinta ta qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo mata,wadda ko samun damar budeta batayi ba. Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma bata yin awanni masu yawa kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman qaramin carfet data sanya musu daga gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi ta daura sannan ta miqe tana isa gaban luggage din. Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta sautin ke fita,jakar ma da gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba. Hannu ta zura tana laluben meye yaketa qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta zazzage jakar gaba daya saman gadon. Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar wanda ta tabbatar duka nata ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa ta jawota,ta dagata a hannunta tana jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar anason sanar mata da amsar duka tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya sake kadawa daga cikin jakar. Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila da take da alaqa da mamallaki ko mamallakiyar jakar. Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa gudun kada kiran yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar suka biyota suka fada saman cinyarta hade da qananun hotunan passport. Ba wannan bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba sunan dake yawo saman screen din wayar MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba sunan da kyau tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta daga kiran ta Kara wayar a kunnenta "Alhamdulillah.....an daga anni" Musaddiq ya fada yana sanya wayar a kunnensa. Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin daga bisani sallamarsa ta maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa bakinta da tata siriryar muryar tana amsa sallamar. "Barka da warhaka" Ya fada a nutse. "Yauwa.....barka" Itama ta amsa masa a taqaice "Don Allah idan ba zaki damu ba zan iya tambayarki wayar nan ta waye?" Banbarakwai taji tambayar tazo mata,har sai data sake duba sunan dake jikin wayar,amma yanayin yadda muryarsa ke nuna kamalarsa da nutsuwarsa ya sanya tayi gyaran murya daban "Kaman sunan me kiran dana gani akan wayar yana da alaqa me qarfi ko kuma mafi kusanci dame wayar ko?". Murmushi ya saki,yadda tayi maganar cikin fasahar harshe da tsari sai yaji ya burgeshi,hakanan kuma a karon farko ya gano muryar,yakuma dago ko wacece "Hakane ranki ya dade.....idan na canka dai dai.....kamar mutuniyar kirkin nan kuma baiwar Allahn nan data ceci rayuwar mahaifiyarmu ko?" Dan jim tayi tana son gano ma'anar zancansa,don tuni rayuwarta taci gaba daga inda ta tsaya,tuni ta shiga wani babin kuma na daban,ta manta abinda ya faru dazu jiya bare shekaran jiya. Haka policy na rayuwarta yake. Ba kasafai take bawa komai gurbi cikin rayuwarta ba bare ta hadu da traffic akan dukka plans nata da kuma tunaninta ba. "Dattijuwa me asthma a masallacin HGMS store?" "Oops....." Ta furta a hankali,yanayin daya sanya musaddiq sakin murmushi don ya fahimci abun ya kwanta mata "Kayi haquri don Allah,ka kuma nawa mama haquri,na hada da purse dinta ne a cikin kayana bisa rashin sani,bansan ma da ita din ba sai yau da aka kira" "No....karki damu......mune ma muke fata Allah yasa bamu takuraki ba....." "Zaku iya karbanta a jambulo third gate.....link 5" Abinda ta furta kenan ta yanke wayar,daidai sanda anni ta miqa hannu da zummar karbar wayar su gaisa. "Ya ka katse wayarwayar inaso mu gaisa nayi mata godiya da ban gajiya" "Daga canne anni ta yanke......" Ya bawa anni amsa yana duban wayar tare da mamakin yadda take magana da bada amsa haka cikin taqaice komai "Babu matsala.....amma zanso sake ganinta ko magana da ita......zanso nayi mata godiya sosai,dukan wanda yayi saving rayuwarka ai baka da sama dashi.....mutum ne me matuqar kima da martaba cikin rayuwarka.....har yanzu ina iya jin sanda ta rungumeni sosai a jikinta kamar ta sanni......sai na dinga jin kamar amna ke riqr dani......ta damu sosai kamar mahaifiyarta ce a cikin halin" Ta qarasa maganar tana duban fuskar musaddiq,fuskarta kuma na nuna abubuwa da dama da zuciyartata taji. Zamanshi sosai ya gyara yana murmushi. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* PAGE 33 "Ni kaina anni ina iya hango sanda taketa masifa da fada da gaske wai mun banzatar da rayuwarki,bamusan illa da kaifin ciwon ba......amma fa anni kaman ina zaton.....anya bata da ciwon itama ko wani nata?" Yayi tambayar yana duban anni kamar annin tasan zahirin maganar. Cikin isa izza da jin cewa takai kowanne qololuwar mataki na rayuwa ta ratsa babban falo kuma na farko na gidan,ta ratse dukkan wasu hadimai da kuma masu aiki na farkon gidan,falon farko har ta dangane da falo na biyu. Kowanne taku idan tayi idanunta suna sauke zazzafan kallo ne akan kowanne alatu da kuma jayan jin dadi na rayuwa dake kowanne muhalli na falon. Kowanne abu da idanunta zaya sauka akai tana debe kallonta ne daga kanshi cikin jin wani irin zafi da quna gami da radadi idan ta tuna cewa MUHAMMAD FU'AD ne ya yishi tare da gumin dan uwansa MUSADDIQ. Da wannan tunanin ta tsaya tsakiyar falo na biyu hannayenta riqe da qugunta tamkar qaramar yarinyar da take ganiyar fitsara da kuma jin cewa tana daidai da kowa. Ko ita dinma a yanzun kusan hakan take. Tsaiwarta a falon qiris ya rage dukkan wani ganuwar haquri nata kawaici da yakana da takeyi su qare,haquri da kawaicin da take ganin tunda tazo duniya bata taba yiwa wata halitta irinta ba "Amina nakeson nayi magana da ita" Ta fadi kanta tsaye sanda daya daga cikin hadiman dake da alhakin kula da wannan sashen ta qaraso. "Eyeee?" Me aikin ta tambaya cike da mamakin yadda ta kirayi sunan dattijuwar data zame musu baya goya marayi haka gatsal,babu sayawa ko qanqani,duk kuwa da cewa zasuyi sa'annin juna,amma a garesu kiran ainihin sunanta wani baqon abune da yake jimawa bai faru ba "Nace AMINA nake buqatar gani.....uwar farouqu da saddiqu" Ta maimaita a wannan karon da madaukakiyar muryar data sanya hadimar maida hankalinta ta hanyar dubanta da kyau,sai kuma taja baya kadan tana cewa "Inji wa zaa ce mata?" Ta tambayeta tana sake kallonta sosai "Kice mata uwar Muhammadu da musaddiqu" Sunayen data furta din ya saka hadimar sake dubanta da kyau,saidai bata ce komai ba don bata da hurumin cewa komai din,ta taka a hankali ta kama stairs tana hawa a hankali don isar da saqonta ga anni. Kafin anni ta furta nata hasashen knocking dinta ya dakatar da firar tasu. Firace da yawancin lokuta musaddiq din yakan qaraso har quryar bedroom din anni ya tayata don debe mata kewa lokaci lokaci da hanata zaman kadaici. Duk da cewa gidan cike yake da hadimai wadanda suka aiki qarqashinta ta kowanne fanni da take da buqata na rayuwa. Hatta hirar akwai masu tayata cikin masu aikin,wadanda aikinsu kenan,gwanaye ne wajen iya hira da mutum,debe masa kewa da sanyashi nishadi......musamman FU'AD ya daukesu aiki saboda haka kawai,amma ko kusa ko alama hira dasu bai kama qafan hira da yaranta ababen soyuwarta ba. "Waye?" Musaddiq ya riga anni tambaya "Badawiyya ce" "Bismillah qaraso" Anni ta bata umarni tana gyara zamanta saman lallausan abun sallarta. A nutse kuma cikin girmamawa ta qaraso cikin dakin. Ta tako a hankali zuwa gaban annin ta tsugunna "Baquwa kikayi anni" Ta fadi kanta a qasa "Baquwa kuma?,daga ina?" Tayi tambayar cikin dan mamaki,saboda yau din ba ranar ganin baqi bane,tana cikin ranakun hutunta,sannan tun bayan dawowarta ma daga asibiti fu'ad ya hana kowa ganinta,yace saita murmure ta huta tukunna. "Ban dai kai ga gane fuskarta ba.....tadai ambaci asalin sunanki,tace kuma a gaya miki babar fu'ad da musaddiq.......kuma...." Tadan fadi tana daga kai kadan ta dubi fuskar musaddiq da ya tattara dukka hankalinsa akan waya,har sai da yaji sunansa ya fito cikin zancan ".....suna dan yanayi da yallabai musaddiq kadan". Dukkaninsu daga ita har musaddiq din kowannensu ya fahimci wace......kowannensu ya gane wace take nemanta. Fuska annin tadan saka kadan tana murmushi " Banda abun badawiyya,ai ba baquwa bace 'yar gida ce itama.....ki gaya mata ta hauro.....ta qaraso zuwa falon sama". "To anni" Ta amsawa anni din a ladabce tana miqewa don isar da umarninta,saidai kuma a can qasan tata zuciyar mamaki ne kwance. Mamakin yadda annin ta bada umarnin qarasowar matar zuwa falonta na qarshe wanda daga shi sai dakunan baccinta.....matar da sam bataga ruwa ko alamun kirki a tattare da ita ba,tun daga yanayin kallonta har zuwa lafuzzan bakinta,to amma menene ALAQARSU DA YALLABAI FU'AD DA KUMA MUSADDIQU?,tambayar da bata da amsarta kenan daidai sanda ra qaraso falon. Tana nan a tsaye inda ta barta,kamar dazun ba abinda ya sauya daga yanayin tsaiwarta a cikin falon,zuwaira na daga gefanta bayan tayi amfani da sakannin hawan badawiyya sama da saukowarta ta sake yiwa zuciya da ruhinta wani karatu da sake dorata akan wani bigiren. "Tace ki qaraso saman" Badawiyya ta furta a ladabce kaman yadda tsarin aikinsu yake cikin gidan girmamawa ga duk wani baqo da zai sanya qafafunsa cikin gidan alhaji hamza kibiya,walau me dogon zangon zama,ko kuma me gajeriyar baquntar da bata wuce awanni zuwa mintuna Kai ta jinjina,eh yana da kyau hakan,ko ba komai a karon farko idanunta zasu ganeta komai da kyau......idanunta zasu gane mata yadda akayi amfani da kudi da jini da kuma quruciyar d'iyanta don shimfida kyakkyawan rayuwa ga wasu. Cikin jin isa taqama gami da izza take taka kowanne step na stairs din,idanunta na sake qididdige mata adadin dukiyar da aka narkar wajen ginin gidan tare da qawatashi da kayan alatu dana alfarma na kecewa sa'a. Irin alatun da ita shine nata mafarkin,irin qawar da shine burinta DUNIYARTA. Yau ga komai a kusa......komai a dab da ita da sunan mallakinta.....amma wani taqi da kuma taku kadan sun hanata isa ga wannan bigiren. Iya lallausan carpet din da aka mamaye ilahirin stairs din dashi aka lullube tsadajje marbles din dake shimfide don kada anni taji sanyi cikin jiki da qashinta......duba daya zakayi masa kasan asalin tsadar da yake dashi. Wani abu ya dinga taruwar mata yana tsaya mata a wuya,wutar bacin rai taba taso mata kamar ta hallakata. Sai da badawiyya ta fice daga dakin sannan anni ta janye idanunta ta maida kan musaddiq. Suna hada idanu sai ya janye dubansa daga kan annin ya mayar ga wayarsa. Ta tabbatar yaji komai kuma shima ya fahimci wacece tazo din. A karon farko kenan data fara tsomai qafafunta cikin gidan tun bayan data sake bayyana cikin rayuwarsu karo na biyu. Yanayin yadda ya share din kamar baisan meke wanzuwa ba yadan sanyata murmusawa. A sannu a sannu hali da dabi'ar dan uwansa tana masa naso cikin jiki. Saidai bata da tabbas din shima dama yana da dabi'ar ne ta iya shariya dayin kamar baiga abu ba?,ko kuwa kuma daga bayane zama da madaukin kanwa ya sanyashi koya?. "Musaddiq" Ta kira sunansa kai tsaye "Na'am anni,akwai wani abu da kike buqata ne?" Yayi tambayar badon haka bakinsa yakeso ya fadi ba. Kai ta girgiza har yanzu tana duban fuskarsa. Cikin ranta tana jin inama wannan dukka tarin kulawar,.....wannan nuna damuwar da bata muhimmancin zasu rabata ko yaya yake da matar da suke kira MAAMA?. Saidai ta sani,TUN RAN GINI tun ran zane.....bakin alqalami kuma ya riga ya bushe......dawo dashi bisa zarafin aiki da damshinsa don gamsar da buqata kuwa aiki ne ba na yanzu yanzu yau ko gobe ba "Ba buqatar komai......amma bakaji wadda tazo bane?" Ta sake tambayarsa "Naji anni.....maama ce" Ya amsa mata kai tsaye. Kai ta sake jinjinawa,ta buda baki zata sake magana amma ya rigata "Maama ce.....kuma bani da tabbacin alkhairi ya kawota" Ya sake fadi idanunsa na nuna akwai wani abu daya taba zuciyarsa. Fuska annin ta sauya tana rage adadin saketa da tayi a baya tadan tsuketa kadan "Wato kaima kanason bin sahun dan uwanka kenan musaddiq?" Ta Tambayeshi cikin tsuke fuska. Kai ya jinjina sannan yakai hannunsa ya ture hularsa baya yana shafar sumarshi "Ba haka bane anni.....akwai wasu abubuwa da wasu lokuta suke iya tasowa dan adam a matsayinsa na dan adam din,duk kuma yadda mutum yaso ya ture ya goge ko ya shafesu ba zasu taba barin zuciya da ruhi su huta ba". " Ya isheni......tashi muje" Ta fada tana yunqurawa sannan ta miqe tsaye tana gyara lullubinta. Tana sanya qafarta cikin falon qofar bedroom din anni dake falon ya bude. Anni ce a gaba musaddiq da ya bude mata qofar yana daga bayanta. Kyakkyawan kallo ta sauke musu a sanda take tsaye tsakiyar falon tana kallon yadda dukiya ke magana da kanta cikin falon. A iya rayuwar da tayi.....a iye shige shige gami da fadin tashin da tayi cikin duniya tasan abu me daraja......tasan abu me tsada kamar yadda tasan abu me aji,don haka bata buqatar batawa kanta lokaci wajen sake nanatawa kanta a nan dukiyar da yaronta ya mallaka take tafiya,da gaske ne.....ba sharri bane.....hakanan ba cikin labarai na qanzon kurege bane. Sanda suke takowa zuwa falon yana biye da anni saita gaza dauke idanunta a kansu. A hankali taji tashin hankalinta yana sake qaruwa. Kana musu duban farko a yadda suka fito shi da anni din baka isa duk masifarka kace ba diyan cikinka bane. Musaddiq ne.....musaddiq din da tun farar safiyar jiya bata sake sanyashi a idanunta ba bayan zaman jiransa data dinga yi na yazo suci abincin rana ko dare tare,abincin da ta yiwa tanadi na musamman,ta barar da kudade sosai a kanshi duka zai gashi ya tashi a tutar babu,sai gashi a yanzun tare da matar ya zame mata tamkar wani body guard a sanda nata idanun suke mararin son ganinsa tun jiya. "Bismillah mana maama ku zauna" Anni ta fadi fuskarta lullube da murmushi sanda musaddiq yake dauke mata pillows din dake saman kujerar saboda taji dadin zama. Tana jin kamar ba zata zauna ba,to amma kuma wani sashe na zuciyarta idan bar bata zauna daidai da nata zaman da tayi saman kujerun da tayi imani da dukiyar d'anta aka siyesu ba....lallai ta sake zama me daraja a kanta. A nutse ya qaraso gabanta ya kuma rusuna har qasa a ladabce yana gaidata "Barka da safiya.....mun tashi lafiya?" "Lafiya qalau......ya mukayi da Kai jiya?" Ta jefa masa tambayar tana son boye fushinta don kada amina ta fahimci tarin galabarta a kanta ta kuma karanci rauni da ciwon da ta haifarwa zuciyarta. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 34 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 34 "Kiyi haquri......jiya mun fita da hamma farouq ne,mun samu baqi masu yawa a company,so kuma nike kula da fitar da kayan da kamfani ya sarrafa dole na tsaya har dare muka kammala muka sallamesu". Dubansa take sosai,sam harkar kayan gona da kayan abincin da yakeyi batayi mata ba,gani take kamar akwai wata maqarqashiya da shiri cikin abun. Taso ace shima kamar dan uwansa harkar diamond da gold yakeyi......ga kayan masarrufi da ma'adanai me zaa tsinta a kayan abinci?. "Kai wai me ya hanaka bin sawun dan uwanka ne ma?,bayan duk duniya kaine mutum na biyu bayanni da bashi da kamarka?,don me zaka tsaya kamfani harkar kayan abinci?,kana zaune a Nigeria ya dauki bare ba dangin iya bana baaba ya tsallaka dashi yana nuna masa manyan harkoki kai kana zaune kana fama da sabgar shinkafa?". Boom yaji furucin nata ya masa tsawa saman ka,sai yakejin kamar ta samu ruwan zafi tana kwarara masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafukan qafafunsa.. A dabarance ya jefa idanunsa sashen da anni take,sai yaga kwata kwata hankalinta da idanunta baa kansu yake ba,ta aza dukka idanunta ga makekiyar tv plasma din dake aiki suna watso labaran abinda ke faruwa da mutanen Palestine. Yasan sarai taji,tana da wani irin matsanancin kara,ba sanin jiya ko yau ya yiwa anni ba......ballantana tana zaune a falon.....da zazzafa kuma kakkaifar muryar da maama take magana zaiyi wahala ace koda a bedroom dinta take ace bataji komai ba. "Kalleni nan" Ta fadi cikin nuna zafinta ainun tana karantar yadda yake kaffa kaffa da kunnuwan anni "Ka tashi ka bani guri,kuma indai ni na dauki cikinka.....nayi naqudarka,na kuma haifeka to tabbas anjima inason zama dakai.....dole nasan me kuke ciki don ba wani ya haifamin ba" "Wannan gaskiya ne.....ai ita uwa tafi gaban komai" Zuwaira ta fadi tana satar kallon musaddiq daya miqe. Kallo daya yayi mata ya wuce yana yin gaba don bashi da lokacinta,hasalima baisan fuskarta ba baima gane wacece ita ba.....duka bama wannan ke damunsa......zafafan kalaman da ta soma fesarwa gaban anni su sukafi sanya masa damuwa,tun yanzu kenan?,me zata fada a gaba?,me kuma tazo dashi?. Wannan tunanin ya tilasta masa jan burki akan rukunin kujerun dake dab da qofar sauka daga stairs din. Yana jin kamar ya zama dole ya tsaya din,kamar idan ya tsaya din zai iya tsaida wata barnar da dukka zata fito daga bakinta. "Musaddiq......sauka zuwa qasa" Anni wadda tana kallonsa cikin qasa da second biyar ta karanci abinda yake shirin aikatawar. Idanunsa ya zubawa anni,ta karanci yana roqon ta barshi ne amma saita wofantar da roqon ta sake maimaita masa "Ka wuce zuwa aikinka.....Allah ya bada sa'a,ka dawo lafiya" Ta furta a nutse kaman yadda ta sabawa kowannensu addu'a a kowacce rana,a fili ko kuma a boye. Idanuwan mutum uku ne suka rakashi har sai daya kufcewa ganinsu. Nata idanun ta janye tana jin suna mata yaji yaji. Wato abun har yakai matakin da ita bata isa ta basu umarni ba subi?,abun yakai lalacewar da maganar wata itace gaba da tata maganar?. "Barka da shigowa mariya.....fatan mun tashi lpy". Anni ta furta fuskarta qunshe da murmushi. "Ba gaisuwa ce ta kawoni ba.....zuwa nayi na tambayeki sai yaushe zaki sakarmin yara na su dawo gareni kamar kowacce UWA?" Sautin kalmar uwa din yadan bada amsa kuwwa kadan cikin falon yayin daya dauke kowanne motsi da yake gilma falon na wasu sakanni. Tamkar me nazari haka anni ke kallon fuskokinsu ita da zuwaira,sai kuma ta gyara zama tana cewa "Gwara da kika ce UWA baki ce MAHAIFIYA BA......wanne abu aminatu tayi kuma?" Tayi tambayar hankalinta kwance,tamkar yau ce rana ta farko data fara sanin wata me suna mariya kaf rayuwarta. Idanu ta zuba mata kamar yadda itama ta zuba mata nata idanun. Babu komai cikin tambayar annin face zallar rainin wayo da kuma rainin hankali. Tana cewa yanzu yanzu tayi mata tambayar amma buqatar maimaici takeyi kenan?. Tattara dukka nutsuwarta tayi da kuma tarin kalaman dake cike fal a bakinta,tanaso a yau ko yaya ta fanshe haushi da takaicin anni dake kwance a ranta.....haushi baqinciki da kuma Takaicin da suka jima suna ci mata rai. "Zuwa yanzu ya kamata ace kinsan cewa da Muhammadu da musaddiq nice na haifi abuna ba kece kika haifamin su ba......zuwa yanzu ya kamata ace kin warware duk wani qulli da kikayi a kansu....kibarmin yara na na moresu kamar yadda kowacce uwa ke morar 'ya'yanta......yanzu har takai matsayin da ni zan daga kira na kira fu'ad yaqi dagamin kira saboda baqin kilbibinki da qullinki ameena?" Qaramin murmushi anni ta saki tana dan motsa idanunta sannan ta waresu akan maama. Tana mamakin maama din sosai a yadda take da qarfin halin lissafo abubuwa irin haka. Kamar ma dai ta manta ita din WACECE. Kamar ta manta su waye yaran da take ikirari gami da!kiransu da sunan 'YA'YANTA. A dukka zancanta babu wani abu daya dameta ko ya bata mata rai,don bawai yau ko jiya tasan mariya ba,ba kuma shekaran jiya ko waccan shekaran jiya ta gama fahimtar duk wani karkataccen saqo shagube da jirwaye da kamar wanka da mariya ke aike mata a fakaice ba. Saidai ko da wasa bata taba daga mata hankali kota dadata da qasa ba,tunda ta sani cewa tun ran gini tun ran zane......hakanan mariya din ta riga tabar kari tun ran tubani,duk wani da zatayi a yanzu bazai zame mata damuwa ba,don akwai idanun data sanya take kallonta dasu. Abu daya ne da taji bataji dadinsa ba shine abinda fu'ad din yayi. Qin daga kiranta,wanda ita kanta ba zata daga masa qafa ba akan hakan,kuskure ne babba wanda yana daya daga cikin abubuwan da take yaqi dasu da son canzasu akai zuwa wani abu na daban,saidai akance mahori ya riga mabada hali. "Wannan tsohon zance ne da duniya ta riga ta shaidashi......meye abun daga hankali,tada jijiyar wuya ko wahalar da baki wajen maimaitamin shi mariya?,fu'ad danki ne halak malak da ya fito daga tsatsonki,haka ma musaddiq.......qaddara ta jefosu hannuwana da taimakon salon taki rawar da kika taka,shin meye laifin ameenatu a ciki?,rubutacce ne wannan,duk wanda yayi lissafinsa ba daidai ba dole idan yazo kwashewa ya diba ba daidai ba......ba wanda ya tayaki lissafin bare kiyi tunanin shi ya miki dungushe" Sosai martanin anni ya tabata. Ta sani magana ce take maida mata a kaikaice wadda bata buqatar dogon bayani ko kuma fashin baqi. Murmushi maaman ta saki tana kada qafarta "Shi lissafi idan akayishi ba daidai ba......akwai hanyoyin gyaransa don a samu a diba yadda ya kamata,akwai rance akwai ciko akwai kuma bashi.......mariya nake har yau har gobe ameena" Idanunta anni ta janye daga kanta tana sakin murmushi. Mariya na daya daga cikin halittun dake bata mamaki a rayuwarta kaf.....saidai ta wani fannin sai taga lamarinta ba abune daya cancanci a tsaya ana masa mamaki ba. Landline dake kusa da ita ta jawo ta soma latsa wasu lambobi wanda bugu biyu kawai aka daga. "Kiyimin kiran amna kice ta kiramin yayansu tace ya kirani yanzu yanzu" "An gama" Aka bata amsa a gaggauce cikin zaquwa da son isar da buqatarta. Kife wayar tayi tana duban maama hankali kwance "Kada ki tsananta sanya damuwa a ranki mariya......komai juyin lokaci da zamani fu'ad da farouq ba zasu taba canzawa daga sunan 'ya'yanki ba......" ".....na jima da sanin hakan" Ta katsi numfashin anni tana miqewa "Kada ki tsammaci cewa gazawa kasawa ko kuma rashin isa ta sanyani bi ta hannunki don nayi magana da fu'ad......a'ah.....nayi hakanne don ki sani.......daga rana irin ta yau hakan ba zata sake faruwa ba.....don zaki rasa dama irin wannan ne har abada.........a sannu zaki manta da cewa kin taba sanin wani me suna fu'ad ko musaddiq......wannan saqon nakeson isar miki". Yadda bata motsa ba hakanan bata ce da ita komai ba,har zuwa sanda ta juya tana ficewa zuwaira tana biye da ita a baya. Duk da ranta baqiqqirin yake amma ta wani fannin tana jin wani farinciki yana shigarta. Ko banza,ko kuma yaya ne ta amayar mata da wani sashe na maganganun da suke cizo zuciyarta. Cikin miliyoyin maganganun da take buri da fatan amayar mata yau din ta fesar mata da kadan daga ciki,saidai kuma ta kasa samun salama ko qanqani cikin ranta,musamman sanda take ratsa stairs tana saukowa tana ratsa falon farko na anni din. Bata da wani buri a rayuwa daya wuce dukka wannan daula dukiya da kuma mulki su dawo qarqashin kulawarta,su dawo qarqashin mulkinta,su dawo qarqashin umarninta. Tunda ya sauko ya kasa wucewa yabar gidan kamar yadda anni ta umarceshi,kawai sai ya samu kansa da samun waje ya zauna saman tsadaddu kuma lafiyayyun sofas din da suka zamo ado wa falon. Kujeru ne na musamman kaman yadda kowanne falo na gidan ke qawace da nashi kalar kujerun. Ba komai yakeyi ba,kawai yana zaune ne hakanan,saidai kuma zuciyarsa tayi nisa da gangar jikinsa. Tun yana da shekaru biyu a duniya yasan wacece ita,yasan abune me matuqar wahala ta iya zama da anni ta sauko lafiya qalau ba tare data gasa mata maganganu masu ciwo ba. Damuwar anni damuwarsu ce,sukan gwammace ciwo bacin rai damuwa ko jarrabawa ta samesu amma tabar musu anninsu ta zauna lafiya. Motsi da alamun takun mutum da yaji yaja hankalinsa,ya waiwaya da sauri daidai sanda ta kammala sauka daga stairs din take doso ainihin falon ta yadda zata cimma qofar fita waje. Da idanu ta kafeshi har zuwa sanda ta cimmasa a inda yake tsaye goye da hannayensa. "Ka gaza tafiya ko saboda kada kabar wajen na bata ran qanwa ko yayar ubanka!" Ta furta a zafafe. Kadan zuwaira ta matsa hannuwanta "Da ruwan sanyi ma saika dafa dutse......kiyi a hankali" Ta furta mata qasa qasa. Kalamanta sun samu gurbi a zuciyarta saidai basu samu damar sauketa daga fushinta ba gaba daya,don haka taci gaba da kallonsa a sanda yake tsaye a gabanta ba tare da yace komai ba. Kimanin mintuna biyu kafin ta furxar da iska daga bakinta sannan ta juya tana barin falon zuwairan na biye da ita. Sanda suke ratsa farfajiyar farko ta gidan zuwa na biyu.....duk da maganganu da zuwaira keyi wanda duka akan abinda ya faru cikin gidanne amma hakan bai dauke hankalinta daga tarin zalla zalla kuma galla gallan motocin dake ajiye qarqashin sashen ajiyar motoci na gidan ba. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 35 Ta sauke wata qatuwar ajiyar zuciya me nauyin gaske "Bugatti,rolls Royce,Lamborghini Aventado,Brabus G_wagon,Mercedes Benz,BMW......zuwaira?" Ta qarashe lissafin jerin motocin da idanunta suka gani din tana waiwaya ga zuwairan "Na'am?" "Kinsan adadin lissafi da qiyasin kudaden wadannan motocin kuwa?,kinsan waye da waye matsayi da matakin rayuwa suke cillashi zuwa ga mallakarsu?,kinsan wanne me tsananin sa'ar ne cikin duniya yake da rabon samun wadannan motocin?.....zuwaira ace d'ana keda su amma ya rasa a gidan da zaya barni sai a wannan wulaqantaccen gidan?" Ta fadi da mugun zafi tana nuna gidan da suke tsaye a gabansa da yatsa. Kamar yau ne zuwairan ta saba ganin gidan,kamar ba cikinsa take kwana take tashi ba,ta daga kai tana duban gidan da maama din ke kira da wulaqantacce. Kyakkyawan gini ne da aka yishi madaidaici me dauke da madaidaiciyar harabar dake dauke da mota qirar range Rover guda biyu duka don biyan buqatar matar gidan. Wadatacciyar haraba dake dauke da dogayen katangu da kuma yalwataccen gate dake qarqashin kulawar mutum daya wato malam saidu. Akwai qaton kitchen da aka zuba masa dukka kayan tasarrufin girki kamar kitchen din 'yar bana bakwai,kitchen din dake maqale da store dake danqare da kayan abincin da yafi qarfin cikin mutum ashirin da zasu shekara kullum suna ci kuma ana kyauta dasu. Babban falo me dauke da dining area......bedrooms guda hudu da kowanne aka qawatashi da kayan gado 'yan turkey masu asalin kyau da tsada,kaman yadda aka qawata falon da kayan turkey din hatta da curtains da carpet kuwa. Wuta 24hrs,engine wanki dana guga,Ac hade da fanka,me aiki guda daya a cikin gida,da kuma me kula da farfajiyar gidan namiji baya ga me gadi malam saidu. Albashin naira dubu dari duk wata ga mamallakiyar gidan. Nisan buri......zurfafa da kuma zarmewa a son zuciya.....take laifuka,dannesu da manta abinda baya ta haifar ya lullube idanunsu su dukka biyun "Indai zaa yi qiyasi bisa irin nau'in arziqin fu'ad.....idan dai zaa yi duba da gidan daya sanya wadancan mutanen wanda idan aka sanya gidanki cikin nasu baifi matsayin boys quarters na gidan ba......tabbas ya wulaqanta haqqin haihuwa......hakanan ire iren wadannan gidajen kinfi qarfin zama a cikinsa saidai kiyi kyautarsa ga irinmu" "Zuwaira" Ta kira sunanta cikin jaddadawa "Na'am" "Ki rubuta ki ajiye.....muddin ban raba tsakaninsa da aminatu ba tabbas ban haifu 'yar halak ba...." Maganarta ta qarshe kenan da tayi ta kutsa kanta cikin gidan tana jin gaba daya gidan tafi qarfin wanzuwa a ciki. "Subhanallah......innalillahi wa'inna ilaihi rajiun" Malam saidu ya furta yana dire qaramar radio din dake hannunsa yanata kokawar kunnata. Sake maimaita salatin yayi,kansa yana sake daurewa sosai. To amma meye ya kawo wannan cin ALWASHIN?. Me ya kawo wannan CIN BURIN. Saita rabashi da anni?,rabuwa ta har abada?,sai ta mallakeshi?,MALLAKA kamar wani miji?. Shin me ya kaita alwashi akan DAN DA BA NATA BA?,wanne rashin imani ne zata tasamma shiga tsakanin UWA da D'A?,shin mene ne alaqarsu?,wacece ita a tsakaninsu?. Kasa kunna radio din yayi,yayi shuru tamkar yana nazarin wani abu dake shirin tunkarowa. Ya gaza fahimtar tsakanin ita da ANNI WACE MAHAIFIYAR?,WACE KUMA UWAR?. Cikin nutsatstsen takunsa ya miqe daga zaman da yayi saman sofa bed yana sanya rufaffun takalmansa na fata berluti brand da suka dace da suit da lafiyayyen suit dinsa *hugo Boss* brand da sukayi fice wajen fidda luxury suit daga zare da yaduka gami da auduga mafi daraja a duniya. Tsaye yayi gaban mirror yana cirar madaidaicin comb da yake amfani dashi wajen taje kwantacciyar sumar dake fuskarsa qasan habarsa da kuma kansa. Sumar da ko yaushe cikin sheqi take da asalin santsinta da wani irin darkness da gashin yake dashi nuturally. Sosai fuskarsa ta sake fresh,cikakkiyar eyebrows dinsa da eyelashes dinsa masu baqin gashi sun sake fidda ainihin kyawun fuskarsa,sun kuma sake taimakawa kyakkyawar qasumbarshi wajen sake qawata fuskarsa da wani irin ajiyayyen kwarjini. Sai daya feshe jikinsa da sassanyan turarensan nan na din din din sannna ya kalli lafiyayyen agogon fatar dake kwance luf saman fatarsa. Lokaci ya cika daidai kamar kullum da zaici wani abu,ya taka a nutse yana isa inda dan kyakkyawan silver tray din ke ajiye wanda komai ke ajiye samanshi bisa tsarin da akasan wanda zai mu'amala da tray din yake dashi. Har ya miqa hannu zai dauki glass mug din dake da murfi sai ya dakata saboda qarar wayarshi dake side pockets na suit nasa. Hannu ya zura ya zarota yana duba me kiran. Sunan nan dai na dazu ya sake bayyana "Amna....amna" Ya fadi sau biyu a hankali yana motsa jajayen labbansa da sukayi wani fresh suka sake fidda red color nasu kamar me amfani da wani kebantaccen abun shafawa labba Sai daya koma a nutse ya zauna saman sofa sannan ya daga kiran "Hamma......" "Amna......i will be busy today fa" "I know fa yaaya......anni ce kawai tace na gaya maka ka kirata" "Lafiya dai ko?" Ya tambaya yana dan motsa fuskarshi "Hamma......waye yasan tsakaninka da anni kuma?" Wani qaramin qasaitaccen murmushi ne ya subuce saman labbansa,wanda ya fidda kyawun fuskarsa sosai "Jealous girl" Ya furta a hankali. Siririyar dariya ta kufcewa amna din,ya latse wayar yana laluban number annin. Tunda ya tashi da sassafe kafin ya fita yayi kiran layin nata har sau biyu saidai ba'a daga ba,sai ya bada uzurin banbancin tazarar lokuta dake tsakanin nigeria da South Korea din wala'alla tana nata baccin ko don yanayin jikin nata ma. Tana gaban mirror tana fama da tazar doguwar sumarta. Wani abu guda daya da taqi jini shine duk abinda zai taba mata kai. Tun tana qarama daya daga cikin dabi'unta bata qaunar kitso kwata kwata,wannan ya sanya har sai da ummunta ta taba aske gashinta,saidai kowanne bawa da irin halittar gashinsa,don babu jimawa wata sumar ta fara taruwa ta kuma sake cika kan da yalwarta da santsinta har taso tafi ta baya da aka aske. Sake runtse idanunta tayi sanda ta sanya comb din a tsakanin gashinta,daidai sanda ta sake jin daddadan sautin nan irin na dazu. Ta wurga fararen idanunta saman purse din dake ajjiye saman madubin. Idanu ta zuba mata,kaman zata dauka sai kuma ta share taci gaba da abinda takeyi,wannan ya bawa wayar daman ci gaba da kadawa har ta gaji ta tsinke. Wayar ya sauke daga kunnensa yana duban fuskar wayar. Sai ya sake gwada kira yana mamaki kadan cikin ransa,don tunda yake da annin bai taba kiran wayarta sau biyu ba ba tare data daga ko ta biyo kiran ba,sai gashi yau kira na biyar kenan zaiyi mata,duk da annin da kanta tace ya kiratan zasuyi magana. Kodai akwai laifin da yayi mata?,ya tambayi kansa duk kuwa da yasan ba haka bane. Abune mawuyaci ka batawa annin rai,musamman su din sanyin idaniyarta guda hudu. Sake leqa fuskar wayar tayi a karo na uku kenan da ake kiran wayar. Suna daya ne dai MUHAMMADU. Siririn tsaki taja tana jawo wayar gabanta,cikin tarin abubuwan data tsana harda maimaita kiranta a waya koda kuwa kiran me muhimmanci ne. Ba wayarta bace amma ranta taji ya baci data duba taga miscal shida kenan harda na dazu,don haka dab da wayar zata katse ta daga adan zafafe ta karata a kunne. Karamar ajiyar zuciya ya saki Lokacin daya fuskanci an daga wayar,a hankali ya maida hankalinsa ga daukan kiran da akayi,cikin jikinsa sai ya dinga ji kaman ba anni bace. Koda cikin bacci anni ta daga kiransa zaya fahimta ballantana idanushi biyu. Kamfanin wayar ya fara irga sakannin da akayi ana riqe da duka layukan biyu,mamaki yaji yadan fara kamashi,yayin da a nata bangaren kuma ranta ya ninka baci akan na dazu. Ansan ba'a da abun fada aka addabi mutane da kira ba qaqqautawa?,an daga kuma zaa bar mutane da riqon waya a hannu?. "Idan ba wani abun fadin zaa ajjiye wayar" Ta fada tana cije lips dinta na qasa saboda haushin da takeji cikin ranta. Daga wayar yayi daga kunnensa yana duba number still duk da yasan number anni ce ba kuskure a ciki. Amma baquwar muryar me kama da muryar babies itace ta daure masa kai. Sai ya dakata daga takun da yakeyi don dauko mug dinsa,ya soke hannunsa a aljihun trouser na suit dinsa tamkar me jin sanyi "Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye "Ina me wayar?" Ya sake jifanta da tambayar "Bansan me wayar ba.....koma wace me wayar wayan baya hannunta......ka jira idan ya koma hannunta ka sake kira" Ta amsa masa a taqaice tana gintse kiran. Sautin Din din din na yankewar kiran ya sakashi janye wayar a kunnensa mamaki yana kashesa "Who's she?" Ya furta a fili yana trying na sake kiran layin,saidai ya taras da na'ura tana gaya masa wayar a kashe take. Sosai ransa yayi qololuwar baci,wacce irin yarinya ce haka mara kunya wadda bata iya magana dana gaba da ita ba?. Maida akalar kiran nasa yayi ga musaddiq zuciyarsa na masa wani irin zafi. Bayan magana da take fadi kanta tsaye harda katse masa kira?,wayan nata ne?,ko itace tayi kiransa da zata katse masa waya?. Daidai sanda yake zaune a falon tun bayan wucewar maama da zuwaira kiran muhammad fu'ad ya shigo masa. A kasalance ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa,yana tsammanin driver manu ne ya gaji da jiran fitowarsa yayi kiransa. Sunan da ya gani a rubuce jikin wayar ya sanyashi sauke ajiyar zuciya gami da daidaita zamansa. Ya jingina bayansa da kujerar yana kara wayar a kunnensa. A ladabce yayi masa sallama "Wa'alaikumussalam.....wace mara kunyar kuka bari wayar anni taje hannunta.....har tana katsema mutane kira?" "Turqashi!.....anzo wajen" Musaddiq ya fada qasan zuciyarsa. Ya sani kowanne bayani zaiyi masa ma ba lallai ya fahimta ba. Ya tsani ya kiraka ka katse masa waya har sai idan shi ya buqaci hakan. Bashi da abun ce masa don haka muryarsa a raunane wadda tayi laushi saboda tarin tunane tunanen dake kanshi yace "Kuskure aka samu hamma......kayi haquri....bari na hadaka da annin" Ya fadi yana miqewa tsaye. Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,ya koma saman sofa bed din ya zauna yana jawo mug din yana duban dafaffiyar tumeric fresh milk din ciki kamar yau ya saba ganinta. Da sassarfa ya soma kowawa ciki,dab da zai isa stairs din yaja ya tsaya saboda annin dake saukowa a nutse zuwa qasa *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* Page 36 "Dama baka tafi ba?" Anni ta jefa masa tambayar a nutse tana jifansa da kallon tuhuma. Kalar tausayi ya koma yana karya wuya "Bazan iya tafiya bane anni na barki" "Saboda kana tsoron kada ta cinye nama na?" Ta sake tambayarshi cikin salo na gatse. Ya gama fahimtar gatsen take masa amma sai ya basar yana binta da wayar lokacin data wuceshi tana zarcewa saman kajurun falon ta zabi daya ta zauna "Anni......hamma ne yakeson magana dake" Ya furta yana rusunawa a gabanta "Kiraminshi......wataqila yayita kiran layina bai sameni ba" Ta fada tana daukan remote hadi da sauya tashar dake aiki cikin tvn. Sipping yakeyi na madarar yana irga yadda agogon dake facing dinsa yake bugawa. Ranshi a bace yake amma yana qoqarin danne hakan. Qarar wayar ya sanyashi waiwayawa inda ya gangarar da wayar yana kallon kiran musaddiq. Yasan ba kiran qashin kansa bane.....na anni ne,don haka bai barta tana burari ba ya jawota ya daga yana sakata a kunne. Da wannan calmness din nashi yayi sallamawa anni. Itama ta amsa masa har cikin zuciyarta tana jin wani farinciki yana saukar mata da jin tasa muryar dake bayyanar mata lafiya qalau yake. "Barka da warhaka anni" Ya fada yana dan rusunar da kanshi tamkar yana a gabanta. Yana jin wannan respect din har cikin zuciyarsa "Barkanka me babban suna....." "Kin tashi lafiya?,ya jikin naki anni?.....ina fatan ba wani matsala ko damuwa?" Ya tambaya cikin kulawa. Ajiyar zuciya ta sauke hade da furzar da numfashi "Ba ciwo,sai damuwa da kukeson sakani kai da musaddiq". Maganar ta dukesu duka su biyun,har musaddiq dake zaune a gefe ta sanyashi daga kai cikin hanzari yana dubanta. " Subhanallah......subhanallah anni kiyi haquri.....me mukayi?" Ya furta yana jin damuwa sosai cikin ranshi tare da tuhumar kansa akan sanya damuwa ga ruhin da kullun burinsa ya kyautata musu?. "Fuad.....yau ka gaida maama daga safen nan zuwa yanzu?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi dauke wuta,sannan a hankali ya hade labbansa guri daya ya kuma amsa mata a hankali da "A'ah". "Me yasa?" "Ba komai" Ya amsa mata kai tsaye,saboda shi din mutum ne da bai iya qarya ba sam komai girman laifinsa kuwa "Me ya hanaka daga wayarta sanda ta kiraka?" "Anni......fargaba kiranta yake sanyamin,anni banason ganinta tana kirana.....anni bana buqatar mu'amala da ita......nafiso taci gaba da nisantarmu anni kaman yadda tayi a baya......bama buqatarta......duk sanda zan ganta anni sai naji wani abu a kanta.....inama zaku fahimci laifi mafi girma data aikata mana wanda yafi tafiya ta barmu girma muni ciwo da kuma girman zunubi?" Wadannan sune abinda so samu ya kamata ya cewa annin,amma kuma bakinsa ya gaza furta hakan,sai shi kadai daketa jujjuya maganganun cikin zuciyarsa. Ya rasa waye zai zayyanawa su,ANNI dince,to amma bayaso yabar mata wani abu da zaya yi mata tsaye a zuciyarta ko kuma a rayuwarta. Damuwa itace abu na qarshe da yayi alqawarin tarewa anni shigarta,kamar yadda ta sanya duk wani qarfin iko na jiki dana aljihunta ta tare ma rayuwarsu kasancewa da wanzuwa cikin damuwa har kawo bigiren da suke kai haka a yanzu. Wannan tunanin ya sanya ya zabi bawa anni amsa ta hanyar cewa "Ba komai". " Ban tsammaci haka daga gareka ba Muhammadu,kanaso abbanku yaji ba dadi a ransa shima kamar yadda naji?" Ta fadi cikin tausa murya tamkar tana magana da qaramin yaro. "Ko kadan anni.....kema da muka sanya kikaji ba dadin yanzu haka kiyi haquri ki yafe mana......za'aci gaba da kokawa da zuciya,kuma zaa gyara in sha Allah". Murmushi ta saki tausayinsu yana narka mata zuciya. Lallai duk dan da baiyi sa'a da dacen uwa ba abun tausayi ne shi. "Bakuyimin laifi ba muhammad.....illa dai lahirarku da kuma fagen rayuwarku da nakeson na sake share muku ita tas". Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa ta karaya......inama ana canjen uwa?.......inama ace anni ita ta haifesu kamar yadda ta haifi Sadiq da farouq?. " In sha Allah anni bazai sake faruwa ba" "To Allah ya yiwa rayuwarku albarka,ya tsaremin ku daga dukkan sharrin me sharri" "Kinyi addu'a me kyau anni" Ya furta qasan ransa,don sai yaji kaman ta nemawa kanta tsari ne daga dukkan wani matakin da maama keson kutsawa dashi cikin rayuwarsu. Ya jima yana juya wayar a hannunsa,tunani da dama suna kutsawa kwanyarsa. Sai yaji gaba daya madarar da duka breakfast din da aka kawo din ya fita a ransa,don haka ya maida mug din ya ajiye,ya miqe ya jawo bedside drawer ya zari dukka abinda yake da buqata ya taka a hankali yana fita a dakin jiki da zuciyarsa duka babu walwala da karsashi. Sannu a hankali motar dake dauke dashi zuwa companyn ke tafiya busa qa'idoji da dokokin qasar,yayin da shi kuma yake kwance jingine sosai da back seat din na motar. Wayarsa ya sake cirowa cikin rashin walwala ya budeta,bangaren kira ya shiga yana duba adadin miscals na wayar nashi. Miscall dinta shine na qarshe a jerin kiraye kirayen daya rasa cikin wayarsa. Ya bude numbers din yana kalla tamkar me qoqarin haddace numbers din. Tsahon wasu sakanni sai ya dauke duban nasa ya mayar ga titi da yake ita hangowa tarwai ta glass. Haka kawai yake jin bayason kiran,gaba daya bashi da wani hope ko marmari akan dukka wani abu da ya shafeta,ta kashe komai ta kuma qonashi murqus tun a shekarun baya da suka shude,ME YAYI SAURA?. Amsar da kullum take biyowa baya shine BABU. Da wani dan qaramin hanzari ya danne zuciyar tasa ya danna maballin kira,kiran kuwa ya tafi direct kai tsaye,wanda cikin qasa da sakan goma kiran ya isa ga wayartata. Duk da jerin dinner abincin daren da me hidima da ita keta faman jere mata a gabanta amma ba wani abu daya daya burgeta ya ko ya bata sha'awa. Sai yanzu ta fahimci dawowa DUNIYARsu da kuma shiga DAULARSU ba shine kadai iya abinda take buqata ba. Ba shine kadai iya abinda ruhinta da zuciyarta suke da muradi ba. Lallai tana buqatar wani abu da yafi wannan muhimmanci a tattare da ita. Ta juya a hankali tana duban zuwaira data cika plate da pepper chicken tana ci hankali kwance. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta "Zuwaira....." "Asama'u" Zuwairan ta amsa mata da bakinta daya cika da zallar tsokar kazar gwamnati(broiler). "Me yake faruwa dani ne?......wa kaman ba nice ma'u ba?,kamar ba nice asama'u ba?,koda karin maganar nan da hausawa keyi ne yakeson tabbata a kaina?,lokaci shekaru da zamani suna son maidani wata lusara?......indai hakan ta kasance bazan taba yafewa kaina ba......bana ma fata hakan ta kasance,dole yarana su dawo qarqashin iko na kamar kowacce uwa.....dole su kasance qarqashin shimfidaddun dokokina.....suyi abinda nakeso na sakasu....su kuma bar abinda na hanasu......suso wanda nakeso.....suqi wanda bana so.....su kyautatawa wanda naso su rabu da wanda bana so.........dole na rabasu da aminatu.......dole Alhaji hamza ya zame musu babban abokin gabar da babu irinsa......zuwaira.....wannan karon burina da muradina me girma ne.....inaji kuma ina ganin kamar girman buqatata a wannan karon ya shallakewa aikin MADUGU.....Ina buqatar wanda yafi madugu zafi.....ina buqatar aiki da zafi zafinsa" Idanun zuwaira suna kanta har ta kammala,sai zuwairan ta nisa ta ajiye plate din naman hannunta ba don ya isheta ba,sai don gano damarmarki masu girma da yawa a gabanta.....da wata siririyar qofa da take hangota da fadin gaske daga can ciki. "Akwai BAHAGO bayan madugu din......bani da kokwanto ko tantama a kansa.....tun ba yau ba......tun kina kogi na miki sha'awar zuwa wajensa amma kika qi bada hankali.....na tabbatar inda kin aminta da hakan da yanzu ba wannan matsalar a gabanki.....da tuntuni kin jima da tsallake wannan babin.....saidai kina da buqatar kudade..... Kudade masu kauri.....kaman yadda aikinsa yake da zafi haka yake da karbar kudi,saidai ribar da zaki samu yafi abinda duka zai amsa daga gareki". Zamanta ta gyara sosai tana duban zuwaira. Ta sani ita din gaba take da zuwaira ta fannin abubuwa masu tarin yawa.....zuwaira bata isa ta hada kanta da ita ba indai ta wannan bangarenne......amma kuma komai qasqancin bawa akwai ta inda yake iya wuce maka "Tunanin da ya fara zuwa kaina kenan.....abun nan yana min ciwo.....kamar ni zuwaira?" Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta "D'ana......mamallakin jadda diamondchore resources amma bazan iya kallon mutum nayi masa kyautar million biyu zuwa sama ba?,zaman me nakeyi a duniya zuwaira?" Ta qarashe fada da wani irin zafi da take jin ya ishe mata har qasan zuciyarta "Komai ya qare idan kinbi a sannu.......idanma baki da wannan jumurin zirga zirgar ai kina dani,driver kawai zaki yiwa umarni......fu'ad kuwa danki ne.....muddin kuma yana neman albarka.....dole ya biki" Ta fadi tana tallafar farantin namanta da nufin ci gaba da kaiwa cikinta. Daidai Lokacin kiran ya iske wayar dake yashe a gefe guda. Tare suka kalli wayar,sai zuwaira da tafi kusa da ita ta miqa hannu ta jawota tana dubawa. Baki ta tabe sannan ta furta "Tabdijan" Ta matsa gaba tana ajewa maahmah a gabanta "Qarshen sakaci......qarshen toxarci......tabbacin akalar duka yaranki suna hannun aminatu.....tabbacin steering dinsu yana damqe a hannunta kenan......sai yadda taga dama zata juyashi......an bada umarni kuma ya karba da gaggawa gashi ya zartar" Maganganun zuwaira kamar saukar ruwan dalma tsakiyar tsokar zuciyarta take jinsu. Tamkar tana yiwa ciwonta fami ne,sai ta gaza cewa komai,ta ja wayar tana daga kiran ta sakashi a hands free ta ajiye saman cinyarta "Assalamu alaikum" Nutsatstsiyar muryarsan me nuna zallar kwarjini da nutsuwar mamallakinta ta bayyana tana karade falon "Amen......sai yanzu kaga damar kirana bayan da aminatu ta baka umarni ko?" Tayi maganar cikin tsananin daci da bacin ran dake damfare a zuciyarta. Idanuwansa ya lumshe kana ya budesu duka Lokaci guda. A duk sanda yaji sautin muryarta abubuwa da dama take tunasar dashi wadanda suka jima da shudewa. Yana jin kamar tana bankada babi babi na wata rayuwarsu ta baya da a yanzu yaketa kokawar binneta tana sake boqarewa gami da son bayyana kanta. "Am sorry" Ya tattara kalmar da qyar yana gaya mata. Shuru ne ya wanzu a tsakaninsu,kowa da abinda zuciyarsa ke raya masa,kowa kuma yana qoqarin controlling kansa ya fuskanci dan uwansa "Barka da dare.....kin yini lafiya?" "Da ban wuni lafiya ba zaka ganni fu'ad?,ko kana jiran labarin baqincikinka kai da Musaddiq ya kwantar dani ya kasheni?" "Ya salam" Ya furta a hankali har kalmar ta shiga kunnuwanta da kyau,abinda yada karya lagonta kenan tayi shuru bata sake cewa komai ba. Shurun da tayi ya bashi damar sake cewa "Am really sorry.....naso kiranki to amma kuma ban samu zama ba......" Qaramin tsaki taja me sauti,ita sam a yanzun ma ba wannan bane a gabanta,kiransa ko akasinsa......hanyoyin biyan buqatarta sune abinda take da muradin riska "Ba wani matsala ko?,ba abinda kike da buqata?" Yayi mata tambayar data zama lazeem a kansa a duk sa'ilin da zaya kirata ta waya ko zaiyi tattaki zuwa inda take "Akwai matsala......kuma ina da buqatun da zasu zama tamkar abun kunya a tattare da kai ace uwa ta mutum irinka sunfi qarfinta" Murmushi yaso qwace masa,duk da koda a gabansa kake ba zata fahimci hakan ba. Ya riga ya fara harbo layin da ta soma hawa,don haka furucinta bai dagi hankalinsa ba ko kadan. Ya bata dukkan wani jin dadi ta fannin sutura.....muhalli abun hawa lafiya,abinci da abun shan da kaf gidan daga ita har masu aiki a qarqashinta babu wanda ke ta'ammali da wani ruwan sha idan ba ruwan gora ba. Ya bata kulawar da babu yadda za'a girka abinci cikin gidan ba tare da nama ko kifi ba. Ba irin nau'in nama ko kifin da babu shi cikin gidan muddin musulunci ya halasta cinsa.....hakanan babu nau'in cima da babu ita a gidan muddin halas ce cikin addininsa.....kamar yadda abun sha ba nau'in da babu.......ana kuma sake shiga da wani duk qarshen kowanne wata ba tare da damuwa da cewa akwaisu bila'adadin ba bash kuma qare ba "Maahma?......wanne abu ne yafi qarfinki?" Ya tambayeta murya a tausashe yana son ya kaita muhallin da yayi imani can takeson zuwa "Kudi fu'ad.......a matsayina na mahaifiyarka......bani da wani abu da zai shiga tsakanina da kai sai dubu dari a wata?" Ta furta tana jin ciwon abun sosai cikin zuciyarta. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 37 Ya riga ya sani tun kafin ta fadi,yasan abinda zata fada din shine burinta na qarshe da zai kaita ga cikar muradinta. Yana da cikakken sani na haqqin uwa.....yana da cikakken sani na duk wani haqqi da yake wuyansa daya zamewa rayuwarsa tilas ya saukeshi......a ciki kuma babu wani abu guda data rasa sai KUDI. Kudin kuma da yakejin ba zaya iya mallaka mata sama da abinda yake bata din ba saboda wani babban dalili. Inda zai yiwu cikin abinda yake batan ma zayaso ya zama qasa da hakane ke shiga hannunta. Barin kudi a hannunta GANGANCI NE. Barin kudi a hannunta KUSKURE NE da ya tabbatar aikatashin zai zamana babu wani abu da zai goge wannan kuskuren. "Am sorry maahma....." Ya fadi da lallausar muryarsa data karye. Shi daya yasan abinda yakeji a qirjinsa idan ya daga idanu ya kalli maahma a matsayin mahaifiyarsa.....shi kadai yasan abinda yakeji idan ya tuna dalilin da yasa take neman kudade haka masu yawa daga hannunsa. "Idan akwai wani abu ba wannan ba da kike buqata.....ko musaddiq kina iya shaidawa.....am sure zaiyi handling komai.....na barki lafiya" Ya qarasa maganar yana zame wayar daga kunnensa. Zazzafar iska ya fitar a bakinsa sanda ya zubawa titi idanu......ya tabbatar duk yadda ubangiji ya ni'imta rayuwarka.....tabbas akwai jarrabawa da ba'a raba ruhi da rayuwa dasu. "Sadiq" Ya kira sunansa a hankali,sai sadiq din dake zaune a gaban motar yana fama shirya bayanai kan yadda ganawar su da kamfanin zata kasance yadan waiwayo "Na'am" "Banaso mu wuce awa biyu a kamfanin nan.....inaso kome mukeyi cikin satin nan mubar Korea......gida nima nakeso mu koma" "In sha Allah hamma" Ya amsa masa cikin girmamawa sannan ya daidaita zamanshi yana ci gaba da aikinsa. Sai data tabbatar ta kammala gyara gashin tsaf,ta saka siririn ribbon ta daureshi. Sosai fuskarta ta fita tarwai,silky skin din nan nata kaman tana amfani da wani abu daban na gyaran fata. A nutse ta taka don dauko wayarta dake saman gado,idanunta ya sake sauka kan luggage din da har yanxu ta kasa budewa,sai ta koma ta zauna sosai saman dan madaidaicin rug na gaban gadonta,ta jawoshi jikinta ta soma zugewa Tsala tsalan abayas ne suka fara mata sallama. Abayas masu tsananin kyau da tsadar da suka amsa kudinsu na qasashen dubai da oman da Morocco. Kowacce abaya da shoe din daya dace da ita wanda yawanci takalman kamfanin Gucci Hermes kitton da tom Ford ne. Tsala tsala agoguna na kerewa sa'a data tabbatar kudade ne ba qanana ba aka zuba aka siyesu. Sai wasu siraran abun hannu masu shining da sukafi mata kama da na gold,daga gefensu kuma turaruka ne turmus masu mabanbantan qamshi da kuma tsada. Dan aljihun dake jikin luggage din ta zura hannunta,sai ta fiddo kyakkyawan kwalin,ta juyashi kadan a hannunta,tun bata bude ba ta fahimci kwalin waya ne,saita zazzage ledar kwalin ya fado. A nutse tayi unboxing wayar data jima da sanin kudinta. Aqalla kudin wayar ya tasamma miliyan hudu,sabuwar Samsung 3screen da bata gama fita hannun jama'a ba. Ta riqe wayar a hannu tana juyawa tare da duba qaramin takardar dake nuna a qasar da aka qerata da zafi zafinta acan Ya'aqoub ya siyeta. Ajiye wayar tayi a gefe tana bin kayan da idanu,kaya ne masu tsada dukansu,siyayya ta masu aji masu ji da naira. Babu abinda baiyi kyau ba a ciki amma sam ba abinda ya burgeta. Idanunta ta lumshe zuciyarta tana motsawa. Ta tuna mata da yawa,a daidai yanzun 'yammata nawa ne kamarta suke can suna neman yadda xasu tsira da mutuncinsu?,'yammata nawa ne suka rasa darajarsu saboda neman yadda zasu rufawa kansu asiri?,mata nawa ne suka hadu da abubuwa marasa dadi saboda an rasa me taimakonsu?,bayan al'ummarmu cike take da mawadata irinsu Ya'aqoub din,wanda kyautar dubban daruruwa zuwa miliyoyi ba komai bane don su fita da aljifansu?. Zuciyarta ta tabu sosai,ta shiga tuna wasu shekarun baya da suka shude da rayuwarta,shekarun da sukaso girgiza duniyarta,sukaso jefata wani baqin duqununun ramin da inda ta afka babu rana ko wata na fita daga ciki ko tsere masa?. Sautin qarar daya daga cikin wayoyinta ya katse mata tunaninta,ta bude idonta tana wurgawa inda wayar take,ta miqa hannu a kasalance ta jawota. Mk kamar yadda tayi saving number dinshi haka ya nuna mata. "Mika'il" Ta furta sunan muryarta qasa qasa,yayin da zuciyarta ke wassafa abubuwa da dama a kanshi. Ci gaba tayi da kallon wayar,batayi yunqurin dagawa ba har zuwa sanda wayar take dab da tsinkewa. A kunnenta ta kara wayar,sannan ta maida idanunta ta rufe gami da jan bakinta ta tsuke. "Hi" Ya furta cikin zamudi tamkar ya mance gurin da yake a zaune. Qaramin tsaki taja qasan zuciyarta,ta motsa labbanta a hankali "Assalamu alaikum" Ta fadi a nutse.....sallamar da ta sanyaya masa jiki,ta kuma jefa shakku a cikin zuciyarsa. Itace macen da yakewa kallon bariki ta farko da take matuqar masa kwarjini. Itace ta farko da yake hangen wasu kalan dabi'u da suke jefa shakku da kokwanto cikin zuciyarsa. Baisan kala da adadin matan da yayi mu'amala dasu cikin rayuwarsa ba,amma sai take neman zame masa ta daban. Dan gyaran murya yayi sannan ya amsa mata da "Wa'alaikumussalam.....afuwan.....banyi sallama ba ko?,na matsu da naji muryarki ne.....na kwana da kewa na kuma tashi da ita......ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da tasha qamshin nan nata da yake a halittarta sannan ta amsa masa "Lafiya qalau......" "Naji dadi dajin hakan.....yaushe za'a bani damar sake ganinki?" Yayi mata tambayar abinda yafi damunsa kuma cikar burinsa a kanta. "Sai lokacin yayi......idan yayin da kanshi zai kawoka gareni". Sam ba haka yaso ba,sai kuma yake ganin kaman daga gareshi ne,ya kamata ya gyara wasanshi. "Zan iya haqurin jiranki koda na shekara nawa ne......amma inaso kisan akwai zuciyar da tayi matuqar mutuwa a kanki take kuma da buqatar soyayyarki....." "Mika'il......" Aka kira sunanshi daga gefe,muryar ta fusgi hakalinsa,yadan waiwaya kadan ya dube kamilar fuskar nan,daya daga cikin fuskoki biyu dake masa kwarjini cikin kamfanin "Am sorry......zan yanke kiran,ina fatan samun wayarki a bude zuwa anjima,ba kamar yadda nasha wahala jiya ba" Boyayyen tsaki ta saki tana yanke kiran hadi da zame wayar daga kunnenta. Ta wurga fararen idanunta gefe tana sauke qaramar ajiyar zuciya. Wato namiji akan mace tamkar mayen qarfe ne da qarfen kansa?,musamman idan zaki bashi abinda yakeso?,ko kuma yana hasashen samun wata riba ko ganima a kanki?. A nutse ya zuba masa idanunsan nan yana kallonsa lokacin da yake jefa wayarsa a aljihu yakuma iso bakin zagayayyen table din da yake zaune a kai. Muhammad fuad jadda CEO abinda ke rubuce kenan jikin wani dan siririn katako dake zaune sosai saman table din daga gaba gaba. Saidai a maimakon muhammad jaddan,farouq hamza kibiya ne zaune saman kujerar yana duban mika'il da kyau har ya zauna kujerar dake fuskantarsa. "Sassaucina fiye da oganku kamar yana son jawo sakaci da aikinku ko?" Ya jefawa mika'il tambayar yana debe dukkan wani wasa da haba haba da ya saba yi dasu dake saman fuskarsa. Shafar kansa kadan mika'il yayi cikin rusunawa "Sorry sir.....urgent call ne shi yasa....but hakan bazai sake maimaituwa ba" "Mituna nawa nayi ina kallonka ba tare daka sani ba,hankalinka baya jikinka?,ka kuwa san girma da matsayin position da kamfani ta baka mika'il?" Ya sake masa tambayar yana riqe habarsa da yatsarsa guda gami da kafeshi da idanunsa sosai. Yanayin ya tabbatarwa mika'il na gaske ne,a irin wannan lokacin da yake buqatar kusanci na sosai da JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES bai kamata ya bari BOSS muhammad ya dawo ya samu wani shaidan banza a kansa ba "Sorry sir.....it will never happen again" Kaman bazai daina kallonsa ba sai kuma ya fesar da iska daga bakinsa,ya tura masa wani folder yana cewa "Ruwanka ka riqe aikinka da kyau,ruwanka kayi wasa dashi.....daga rana ita yau ba zaka sake ganina a company dinku ba,wataqila saidai ziyara......ka kuma fini sanin waye boss dinka" Ya qarashe maganar yana tashi daga saman kujerar. Yadda hankalinta yayi kan zuwa duba aysha yasa gaba daya ta manta da batun wayar da ta bada address din aje a karba. Gaba daya ta manta ma da zaman wayar cikin dakinta. Sai data tabbatar su huda sun dawo daga boko sun wuce islamiyya sannan ta shirya cikin wani dinkin atamfa doguwar riga data bude sosai daga qasa ta zauna mata daga sama cas jikinta,ta kuma lullube kanta da Chantilly veil,takalmi da jakan D&G su suka zama cikamakin adon nata. Kamar ko yaushe tsakar gidan nasu zuwa farfajiyar gidan bata rabo da kai kawon jama'a jifa jifa. Kamar kullum haka ta ratsasu a nutse ta fice ba tare data damu da idanun dake zube a kanta ba. Kamar dai kowanne lokaci,abinda ta baro cikin gidan shine a waje. Yawan idanun jama'a dake kanta ko kadan basu dadata da qasa ba. Tun asali mutum ce me damuwa da lamarin gabanta. Abubuwa da dama da suke cikin zukatan mutane a kanta bata isa ta gogeshi ba. Abune da tun yana damunta ya zame mata jiki. Suna mata kallon biri ne tana musu kallon ayaba. Anyi walqiya me hasken data haska mata abubuwa masu tarin yawan da suke boye cikin hijabin idanuwan jama'a da wani irin shamaki da tsinkaye da idanuwa basu kaiwa wajen. Wasu mutanen a riga kawai suke mutane.....wasu dattawan a suna ne kawai kuma a baki.......wasu jama'ar da ake tunanin suna gyara ko bada gudunmawar gyaruwar al'umma su din GUBA ne,guba ce wadda bata da magani,guba ce me d'aid'aita komai da wargaza komai. Daidai sanda takai qarshen tunaninta sai ta fidda eye glasses dinta da ba kasafai ta fiya amfani dashi ba ta manne qwayar idanunta. Daya daga cikin abinda ya sanya suke mata mummunan kallo da mafi munin fassara. Eye glasses ne me duhu dake qarawa fuskarta kyau da kuma kwarjini,yake kuma iya hana mutane ganin ainihin qwayar idanunka. A nutse takai bakin titi,saidai yanayin kai kawon abun hawa kadai zai gaya maka akwai qarancin motocin haya "Ki siya mota kawai ki huta sabreen" Ta tuna kalamin qawarta qwaya daya da take da ita duk duniya wato haseena. Karon farko tun wayewar garin ranar ta saki murmushin da batayi niyya ba,abinda ya sanyashi tsaiwa da motarsa cak. Duk da cewa ta daki zuciyarsa tun daga nesa daya hangeta,amma sai gashi farat daya ta sanyashi tsaiwar da baiyi niyya ba. Taga gilmawar farar motar amma saita dauke dukka wani hankalinta zuwa wani sashen,qasan zuciyarta tana fatan bawai ya tsaya bane saboda ita,don a yanzun bata da buqatar qaruwar kowanne namiji cikin rayuwarta. Tana da tarin matsalolin da takeson ta kammala dasu tukunna,mazajen dake cikin rayuwarta kuma a yanzun ta sallami kowa da kalar sallamar data dace dashi kafin ta sake sabon zubi. A hankali motar ta dawo daidai gabanta ta kuma tsaya cak,sannan aka sauke glass din motar,abinda ya bawa sassanyan sanyin ac din dake gauraye a motar damar fitowa waje ya kuma daki fuskarta. Sallamar da yayi mata ta tilastata waiwayowa ta dubeshi. Nutsatse kuma kamili a ido,wankan tarwada wanda ko bai miqe tsaye ba ta tabbatar dogo ne. Zagayayyar Fuskarshi da gemu ya yiwa qawanya,sai idanunsa dake saye a cikin glass. "Bai dace ace zafin rana yana dukan wannan kyakkyawar fuskar ba.....shigo don Allah na rage miki hanya". Jin kai da miskilanci cikin jininta yake,duk daga yanayin kamalar data gani a fuskarta ya mata kwarjini amma saita sake dauke kai ba tare da tace masa kanzil ba. Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana bude mata motar "Ki shigo domin Allah". Ya furta yana tsareta da idanu har zuciyarsa yana jin tayi masa. Duk da cewa akwai wani irin kwantaccen kwarjini akan fuskarta wanda bayajin cewa ita kanta tasan tana dashi. Kaman yadda magiyarsa ta dauki hankalinta haka bullowar kawu ta dauki hankalinta. Duk da cewa daga nesa yake amma ta zuba masa idanu da kuma wannan komar tata dake saurin karanto lissafin me lissafi. Cikin qasa da minti daya ta gama karantarsa,zaiyi wuya ace ba ita yaje nema gida ba bai sameta ba ya fito. Batayi shawara ta biyu ba ta juya a hankali ta kama murfin motar ta bude ta shige ta maida ta rufe,daidai sanda motar ke tashi ya iso gurin. "Kaga shegiyar yarinya?,ni zaki gudarwa?,don ubanki ai duk tantirancinki dai idan dare yayi gidan adamu kike dawowa ki kwana ko?,to mu zuba dani dake.......meye amfaninki muddin ba za'a moreki kudi ba?,ai amfaninki kiyita kawo mana kudi tunda hanyar da kika zabawa kanki kenan" Ya fada yana yarfe hannuwa shi daya a gefen titi,kai kace ya samu matsalar kwanya. Juyawa yayi da zummar barin wajen,saidai taku biyu rak yayi wayarsa keypad dake aljihunsa ta dauki kururuwa. "Kai jama'a......Allah yasa ba bala bane.....kash.....shine wallahi" Ya fada yana qoqarin danna madannin wayar da yayi tsananin tauri saboda ganin rayuwa da yayi. "Hel.....helo bala.....don Allah kar ka damu.....ai in sha Allahu ina me tabbatar maka damu za'a shiga wannan cacar.....yo ta ina zamuyi wasa?,bayan kai da kanka ka tabbatar min mutumin nan attajiri ne......ai ina maka rantsuwa da Allah baka bina bashin rantsuwa wannan karon arziqi ne yake kiranmu....inata buga buga naga na samu adadin abinda akeso a shiga cacar dasu....kada ka damu,zuwa nan da dare in sha Allahu zaka jini,yauwa na gode" Ya fada yana sauke wayar,ya soma laluben aljihunsa don maidata ciki yana sake magana a fili. "Idan ma Allah ya taimakeni na haye da wadannan kudaden ina zaki sake jina?,ai nima na zama attajirin kaina don ubanki" Sai yaja qwafa sannan tsaki ya biyo baya,ya juya yana sauya hanya. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 38 Sau biyu yana sake juyawa yana kallonta. Tun bayan sallamar da tayi yayin shigowa motar bata sake cewa wani abu ba. A nutse take da dukkan nutsuwarta,nutsuwar data sake janye ra'ayinsa a kanta matuqa. "Erhmmm" Ya danyi gyaran murya kafin ya dora da "Na gode qwarai da baki wofantar da magiyata ba.....hakan ya nunamin kinsan darajar dan adam....." Maganarsa ta sanyata dawowa tunaninta tare da tunasar da ita a inda take. Batace masa komai ba,tadan dai motsa kadan alamun tana saurarensa,hakan ya bashi damar ci gaba da magana. "Da farko dai sunana alhassan.....ko zan iya sanin sunan malamar?" Sunan daya kira kanshi dashi ya sanyata juyawa kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga kwaltar da suke bisa kanta. Kaman ba zatace komai ba sai kuma ta motsa bakinta "Sunana....." Sai tayi hanzarin dakatawa. Shima kaman sauran?,yana buqatar a bashi stamp?,yana buqatar personal suna nashi tamkar dai sauran 'yan uwansa jinsinsa?. Eh yana buqata,saidai shi din bata jin zatayi wani doguwar mu'amala dashi da har zai buqatu ya zuwa stamp na musamman "Da alama sunan nan me tsada ne ko?,sai na siyeshi?" Ya fadi yana dan satar kallonta kadan fuskarsa dauke da murmushi. Kai ta girgiza a hankali "Sunana sawwama" "Nice and good name.....me azumi kenan?" Ya fadi yana dubanta kadan. Kafada ta daga,koma meye ma'anar sunan bai zame mata damuwa ba,kawaidai ta bashi sunan ne don shine sunan da yazo kanta. "Ma sha Allah......gashi mun iso inda kika cemin,kuma ina da tarin abubuwan fadi don inason alaqar tamu tayi nisa,tafi haka zurfi,za'a bani wani abu kaman number waya ko adress nazo na sameki?" "Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta kai tsaye daidai sanda yake tsaida motor din a inda ta nuna masa. "Waya ba guarantee adress aishi zai zama babban guarantee ko?....me yasa kikace baki da adress?" "Saboda bamu da gida" Ta sake bashi amsa kai tsaye sanda take dubansa da fararen idanunta masu sheqi da hasken rana ya qara musu qyalli,abinda ya sake daukan hankalinsa kenan. Murmushi ya saki yana jin tana sake burgeshi "Alright.....nasan dai ba dan adam din dake rayuwa a titi.....amma bazan takurawa zabinki ba......zaki iya bani dama ta uku?,damar yin magana dake a nan?" Numfashi ta sauke a hankali tana jin ya takurata da yawa,ta daga hannunta dake daure da agogo ta kalla sannan ta sauke tana juya idonta daya sashen alamun qosawa "Mintuna biyar kawai" "Na gode" Ya fada yana gyara zamansa sosai. "Bari na tafi kai tsaye kada na cinye mintunana ko?" Ya furta yana sake sakin murmushi. Batace masa komai ba still,saidai ta kafe idanunta ne saman qofar gidan dake gabansu kadan. Tunaninta yafi karkata akan gidan,tana tunanin me zataje ta taras?,wanne abu zata samu cikin gidan. "Tunda na ganki sawwama naji zuciyata ta kwanta dake.....ta kuma kamu da sonki......naji kuma a raina na samu matar aure.....ina fatan zaki bani dama....." Statement dinsa na qarshe data samu fahimta kenan. Waiwayawa tayi ta dubeshi,shima idanunsa yana kanta,da alama ya gama dukkanin bayanansa ita yake da buqatar jin ta bakinta. Dauke duban nata tayi,sannan ta saka hannu ta bude murfin motar ta zura qafafunta ta fito. Da mamaki yake binta da kallo har zuwa sanda ta maida masa murfin motar ta rufe,tadan rage tsaho kadan tana dubansa da shiny eyes dinta "Na gode da karamcinka......amma kayi haquri.....babu aure a rubuce cikin rayuwata.....na barka lafiya" Ta motsa labbanta a hankali sannan ta janye jikinta daga motar. Soma takawa tayi a hankali tana barin wajen,AURE na daya daga cikin abinda take mantawa dashi a rayuwarta. Aure yana cikin abinda yake a lissafin qarshe cikin abubuwan da suke ba dole ba a rayuwarta. Aure yana daya daga cikin abinda take masa wani irin kallon da batasan ajin data zubashi ba.....babu shi ko kadan a dictionary dinta,idanma anyi zancensa,tana masa kallon wani baqon abu wanda batasan ranar da zata saba da ji ko ganinsa ba,bare azo da batun wanzuwarsa akan kanta. Ko kadan bata damu da tsaiwarsa a wajen ba,abu daya ta sani.....kaman sauran mazan,yadda basu da masaniyar daga inda ta fito......hakanan bata basu qofa ko qanqani game da sanin inda zata ko inda zata shiga. Don haka bata kutsa kanta cikin gidan ba sai data kadar masa da hankali,ta kuma tabbatar ya bar layin. Da sallama a bakinta ta shiga madaidaicin tsakar gidan dake shimfide da sabon simintin da bata jima da sanyawa ayi musi shi ba saboda jin dadinsu. Yara ne aqalla kusan guda biyar wadanda shekarunsu bazai haura goma zuwa sha uku ba. Biyu daga cikinsu wanki sukeyi,daya kuma tana wanke wanke,yayin da guda dayar take jawo ruwa a rijiya tana zubawa a babban mazubin ruwan da suke amfani dashi a gidan. Sallamarta ya sanya kowacce ta watsar da abinda takeyi,suka kuma rugo da gudu suna rige rigen isa inda take. Kyakkyawar fuskarta ta fadada da fara'a itama ta buda hannunta tana tarbarsu,daidai sanda muryar matar ta iskesu "Ku da waye haka?" Ta bayyana tare da qarashen tambayarta tana qoqarin daura dankwali saman kanta. Murmushi ne ya wadaci fuskarta itama,kakkaurar matar ma'abociyar tsaho da qiba,saidai alamu sun nuna yanayi na rayuwa ya sanya qibar zubewa sai saura data zama halittarta ce ba zata iya rabuwa da ita ba. Baqace wannan ya sanya dukka kamanninta sukafi karkata ga kamannin babarbariya. "To ku barta ta qaraso mana" Ta fadi tana juyawa cikin dakin da ta fito,dukansu sai suka bi bayanta harda sabreen daketa jefawa yaran tambayoyi. Tare suka zauna da yaran saman shimfidaddiyar dardumar da matar ta shimfida saboda sabreen din,daya daga cikin yaran ta miqe ta fice sai gata da ruwa adan qaramin jug da cup,yayin da sauran sukaci gaba da zama a kewayenta. "Ina Ayshatu?" Tambayar farko da sabreen tayi mata bayan sun gama gaisawa,tambayar data sanya yaran suka miqe daya bayan daya suna fita a dakin. Bata ce komai ba matar saita miqe tana dosar wata qofa dake maqale a falon,itama batace komai din ba ta miqe ta biyo bayanta. Yalwataccen daki ne dake wadace da tsafts,ba komai a qasan sai wata lamusashiyar katifa guda daya yashe a qasa. Daga samanta idan ka duba da kyau mutum ce a kwance data lulluba duka jikinta. A sanyaye sabreen ta qarasa gaban katifar,ta saka hannu ta yaye rufar bakinta yana rawa ta kira sunanta "Aishatu?" A hankali ta ware idanunta akan sabreen din,sai kuma wani busashen murmushi ya subucewa kyakkyawar fuskar yarinyar "Aunty....kece kika zo?" Ta tambayeta da siririyar muryarta. Kasa riqe kanta tayi,sai kawai tayi qasa da kanta hawaye yana diga daga idanunta. Tana jin tausayin yarinyar kamar zai fasa zuciyarta,tana jin kamar zata narke a wajen,tana jin inama ace tana da ikon fidda ciwo ta farat daya daga jikin mutum a yanzu yanzu basai anjima ta cisgeshi daga jikin ayshatu "Ko baki da ikon cire mata shi yanzu yanzu.....kina iya sama muku dama ke da ita na samo mata lafiya a duk inda lafiyar take a fadin duniya" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsar data motsa mata wani qwarin gwiwa daga can qasan zuciyarta. Wannan ya sanya ta sake daga idanunta tana kallon aysha. Allah ne kadai yasan bila'adadin mata da yaran da suka shiga irin yanayin da ayshatu ke ciki duka sanadin TAIMAKO. Lalacewar al'ummarmu abune me matuqar ban mamaki da daure kai. FYADE ba'a daukeshi da wani muhimmancin da me aikatashi zai fuskanci hukunci mafi tsananu ba a tsarin doka. Tana iya tuna yawan kudaden data kashe,shige da ficenta da kai kawo data dinga yi kafin ta samu ayiwa azzalumin hukuncin da doka ta tanada. A abinda ya yiwa aisha,ba hukuncin daurin shekaru take da buqata ba......lahira yafi kamata ya baqunta yaje ya hadu da hukuncin mafi iya hukuncin masu hukunci. Sosai ta bawa zuciya da gangar jikinta qwarin gwiwa,ta zauna sosai ta yiwa yarinyar komai. Ta bata abinci ta kuma dinga hilatarta,har suka dinga hira tana saurarensu murmushi yana subuce mata. Hakan ya sanyaya ranta kafin su kebe da ummaa ta sake mata bayanin data yi mata a waya. "Waje nakeson a fita da ayshatu,inason ta warke sumul taci gaba da rayuwarta,duka duka shekarunta sha uku,ya kamata ta rayu kamar kowa" Ta fada zuciyarta tana mata zafi. Allah ya dora mata tausayin yaran da matar kanta da batasan asalinsu ba,amma dukka dawainiyarsu kusan kaso tamanin cikin dari tana a wuyanta,hatta da hayar gidan da suke zaune a ciki kuwa,banda abinci da ma karantarsu rayuka shida. Da idanu ummaa take bin sabreen. Tasan cewa dukkaninsu babu wanda suka hada dangantaka a tsakaninsu,amma suna jin juna kamar 'yan uwa,suna kuma ci gaba da tsananin shaquwa da juna.....kuma a yanzun sune 'yan uwan kawunansu. "Sabreen......kiyi iya abinda zaki iya mu barwa Allah sauran.....samun maganin ayshatu a gida Nigeria ma miliyan nawa ya kama bare ayi batun fita da ita waje?,kinsan miliyoyin kudin da za'a cajemu?,daga visa passport masauki abinci da zaman asibiti zuwa kudin magani?" Shuru sabreen tayi tana saurarenta,tana jin zuciyarta na wani irin ciwo,irin ciwon da mutum kanji a duk sanda yake tsananin son abu amma babu ikon samuwar wannan abun gareshi. Numfashi taja sosai ta aje tana duban maama "Allah zaiyi cikin iko da isarsa......na tabbatar Allah bazai taba wofantar da bayin da aka zalunta ba" Kai ummaa ke jinjinawa tare da yaba tauhidi da yaqinin sabreen. Ta jima dasu saidai hankalinta yana kan asibiti,don haka lokaci kadan ta qara akai tayi musu sallama bayan ta aje musu kudi kaman yadda ta saba da basa wuce cefane da zirga zirgar makarantar yaran. Tana hanya zuciyarta kamar ta fashe,hakanan ta sake jinta a rikice bayan fitowarta daga asibitin bayan taji bayani daki daki na yadda zata fita da ayshatu waje ayi mata aiki. Kudade ne masu kaurin da a yanzun bata dasu bata kuma bawa wani ajiya ba. Batasan tayi farautar kudi don ta ajiye ta tara abun duniya ba......tana farautarta ne don ta raba a tsakanin mabuqata marasa galihu irinta,yanzun ka buqata ta taso mata wadda take da girma da muhimmanci a rayuwarta. Sai taja numfashi mai nauyi,tabbas a yanzun zatayi FARAUTA ta ainihi,tsakanin MIKA'IL YA'AQOUB da kuma MASHKUR waye zaiyi aman wadannan maqudan?. _tofa zamuji waye,komarta zatayi kamu ko kuma wannan karon ita zata shiga komar?_ *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 39 Tun a hanya har takai gida zuciyarta na karakaina ne tsakanin sunyen mutum ukun MIKA'IL MASHKUR KO KUMA YA'AQOUB. Da sallama ta shiga parlor din bayan ta tsallake tarin idanun da a kullum suke da tuhume tuhume da zarge zarge a kanta masu tarin yawa. Ta samesu suna hada uniform dinsu guri guda nadra zata wanke. Huda kuma na kokawar kammala abincin dare,don da alama basu jima cancan da dawowa islamiyya ba. Takan samu cikakkiyar nutsuwa a duk sanda ta dawo gidan ta samesu lafiya lau kaman yadda ta fita ta barsu. Haneefa ta zaburo da gudunta ta daneta tana mata sannu da zuwa "Auta na gaji.....mu zauna". Ta fada tana direta saman kujera itama ta zauna a gefanta. Jakarta ta bude ta fiddo alawa cikin wadanda ta siyawa su aishatu ta musu tsaraba ta miqawa nadra da haneefa "Karbi huda" Ta furta sanda huda din ta gama goge qasan tiles din inda suka zubda ruwa. A nutse ta tako,ta zauna a hannun kujera ta miqa hannu tana karba din idanunta akan fuskar Sabreen. "Komai lafiya ko?" Sabreen din ta tambayeta tana kallonta ganin kallon da huda din ke binta dashi. Kai ta gyada tana kauda dubanta daga kanta "Lafiya lau anty" Da idanu sabreen din ta rutsata tana kallonta,kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta buda baki a hankali "Ko yauma kunnuwanki sun sake ji miki wani magana daga bakunan mutanen gidan nan da kika sakashi a ranki?" Ta mata tambayar tana tattara hankalinta a kanta. A hankali ta girgiza kai alamun aah "Huda" Sabreen ta kirayi sunanta kanta tsaye. Daga kai tayi ta kalleta sai kuma ta qara sadda kanta qasa "Dawo nan ki zauna" Ta fada tana nuna mata gefanta zuciyarta tana bugawa fiye da yadda ya kamata ace ta buga din. Ko kadan bata qaunar taga sauyawar yanayi daga motsin kowannensu. Duniya da mutanen cikinta tsoro suke bata matuqa.....irin tsoron da babu shi a cikin FARAUTARTA amma tana dashi cikin DUNIYARTA data 'yan uwanta. Sune dukka rauninta a rayuwa,sune tsoronta kuma sune kwanciyar hankalinta. Kamar yadda ta buqata haka ta zamo ta zauna a gefanta,saidai har yanzu bata yarda sun hada idanu ba "Huda.....kalleni nan" Ta fada tana kausasa muryarta. Yadda ta bata umarni kadai ya gaya mata bada wasa take ba,ta furta umarnin ne tun daga tsakiyar zuciya da kuma ruhinta,don haka ta dago din ta dubeta kai tsaye kaman yadda tace "Zan maimaita tambayar dana miki,kuma ina buqatar ki bani amsarta kafin nadra da haneefa su sake dawowa dakin nan......mene a ranki?,meye damuwarki?" "So nake ki daina fita yaaya......ki zauna a gida kaman kowa" Ta fadi muryarta tana rawa. Idanunta sabreen ta maida tadan lumshe kana ta budesu. Fargaba tadan saukar mata,yau huda ce ta fara tararta da wannan maganar,gobe sai nadra jibi sai haneefa?. Tambaya ta yiwa kanta amma kuma tana baiwa kanta yaqinin abinda zai faru kenan a zahiri. "Kina zargi na ne kema huda?" Tayi mata tambayar takai tsaye tana kallon qwayar idanunta. Kamar maganar ta daketa sosai hakan ya sanyata daga kai da hanzari ta kalleta tana girgiza kai,sai kuma ta sake sauke kan nata qwalla tana gangaro mata. "Yaushe kika soma zare audugar dana baki ki sanyawa kunnuwanki akan zancan mutane?,yaushe kika samu cikakken zaman saurara da fahimtar maganganun mutane?,yaushe hankalinki ya fara kaiwa nan huda?" Ta furta idanunta suna qanqancewa,wanda hakan zai nuna maka zallar radadin da takeji a zuciyarta. "Ina nan yadda kika sanni huda.....babu kuma abinda zai canzani......gwagwarmaya da fadi tashin da nayi a baya bai sauyani ba bare yanzu dana 'YANTU.....karki bari zargi shakka ko kokwanto a kaina ya ratsa zuciyarki har ya samu gurbi......bazan iya zama ba huda......bazan kuma iya daina fita ba,don haka ki cire damuwar wannan daga ranki" Ta amsa mata tana miqewa a nutse daga saman kujerar,saidai dukka gabbanta sun saki da gajiya da kuma damuwar data saukarwa ruhinta. Ta qasan idanu take bin sabreen din da kallo har ta shige dakinsu. Ta janye idanunta tana sanya hannunta gami da dauke qwallar dake tsiyaya daga idanunta. Anya ta kyauta idan har ta sanya zuciyar data sadaukar da komai nata saboda farincikinsu da ingantuwar rayuwarsu.....ta kyauta idan tayi silar sanyata a damuwa?. Babu kyautawa ko kadan,idan har ta aikata hakan kenan bata da maraba da sauran gama garin jama'ar gari?. Bata da banbanci dasu?,tafi aminta dasu kenan akanta?. Nadama taji tana saukar mata a hankali. Bawai tayi komai bane da gangan,kawai ta kasa controlling din kanta ne akan batun,ta kasa jure abubuwan da takeji take kuma gani kulliyaumin,ita daya kuma tasan yadda takeji a duk sanda akayi magana akan yayartata halitta mafi soyuwa a gareta. Tana zaune a wajen tana feeling guilty akan maganar,har sabreen ta sauya kaya zuwa wasu riga da wando silk me dogon hannu,rigar tadan sauko mata har saman cinyoyinta,yayin da wandon ya sauka har saman qafafunta. Tayi alwala ta dawo ita da haneefa,nadra na daga waje bakin fanfo tana dora nata ta kalleta "Ki tashi kiyi alwala,ko kina fashin sallah ne?" Tayi mata tambayar cikin basarwa tana qoqarin zura jilbab dinta. Kai ta girgiza,ta miqe tana takawa a sanyaye tana ficewa. Sanda nadra ta shigo sai tace ta sanya hijab su jira huda din ta shigo sai suyi jam'i kamar yadda sukeyi lokaci lokaci. Zama tayi gefan kujerar falon kafin shigowar hudan tana duba saqonnin cikin wayarta. Tana jimawa bata duba saqon sms ba don bata fiya bashi muhimmanci ba. Sama sama ta fara jiyo hayaniya daga tsakiyar gidan nasu,saidai bata wani bada hankali ba,don ba baqon abu bane cikin gidan nasu musamman lokaci irin wannan. A hankali hayaniyar ta fara yin yawa,sai kuma ta fara jin kamar muryar huda cikin hayaniyar. Abinda yaja hankalinta kenan,ta daga kanta daga wayar tana duban nadra da itama tayi kasaqe tana sauraro,saidai batace komai ba,ko wala'alla itama tanason gane cewa muryar hudanne ko ba ita bace. Baqon abune ga dan dakinsu wato yin hayaniya ko daga murya kaman haka. Basu da abokin fada ko adawa,kamar yadda har mahaifiyarsu tabar duniya bata da abokin fadan,saidai kai kayi dasu idan kaso hakan. Hudan ce ma mai dan zafin rai wani lokaci da kuma rashin dagawa duk wanda ya shiga gonarta. Sabreen ta shafeta sosai......amma yana da wahala ka gano haka saboda miskilanci da rashin son shiga shirgin mutane. A sannu ta tanqwarata ta koya mata hadiye fushi,a dole kuma sukaci gaba da tafiya kan wannan bigiren har kawo inda yanzu rayuwa ta ajiyesu. "Dubamin.....kamar muryar huda nakeji" Sabreen ta fadi tana duban nadra. Da hanzarinta nadra din ta miqe,don dama abinda take jiran ji kenan daga sabreen. Bin nadra tayi da kallo har ta fice,saidai kafin dawowar nadra dakin kunnuwanta sun bata tabbacin huda ce,saita ajiye wayarta gefe tana duban haneefa "Auta qarasa karatunki.....kada ki fito ina zuwa" Kai haneefa ta daga idanunta a raunane tana bin sabreen da kallo har ta fice. Kusan duk wani ahali na gidan dake cikin gidan yana tsaye a tsakar gidan banda mace qwaya daya.....mace guda daya tak da koda mutum zaa dafa a gidan sai tayi niyya ko ra'ayi zaka ga gilmawarta a shiyyar tsakar gidan ma bare akai ga farfajiyar gidan. Tun kafin ta qarasa idanuwanta suka gane mata da wadda akeyi. Huda da hadiyya......suna tsaye tsakiyar mutane kowaccensu tsamo tsamo a jiqe da ruwa,ruwan da bata raba dayan biyu ruwan wankin da hadiyyan takeyi ne da kuma wanda ke zuba yanzu haka daga famfo. Kwalar huda na hannun hadiyyan cikin zafi da zafafa "Zanga uban daya tsaya miki cikin gidan nan.....kibar ganin kamar kun isa kun bunqasa......kun riqar da ba'a saku ba'a kuma hanaku......ni bariki da duk wanda ke cikinta baya bani tsoro wallahi" Ta fada tana waro idanunta waje. Idanu sabreen tadan runtse kadan tana jin wani abu me zafi yana saukar mata. Ta sani yau Allah kadai yasan adadin tarin maganganun da kunnuwansu zasu amsa cikin gidan. Maganganu ne da aka tarasu cikin qiraje ana neman ranar zubda su,amma ba'a samu ba saboda kiyayewarsu da shiga hurumin kowa sai nasu......yau kam da dama ta samu ba shakka sai iya abinda sukaji. Bata cewa kowa komai ba sai kutsa kai cikin mutanen data dinga yi a nutsenta sanye da hijabin sallarta,abinda ya dinga jan hankalin kowa da fitowarta kenan. Bata tsaya ba har sai data isa tsakiyar inda suke abun,a sannan ran huda yayi bacin da itama ta cakume hadiyya. Abinda ya tunzura hadiyya kenan ta daga hannunta a zafafe ta saukewa huda lafiyayyen marin daya sanya huda din sakinta ba shiri. Cikin tsananin fushi hudan ta zabura don maida martani sabreen ta iso tsakaninsu "Karki soma" Sabreen din ta fadi duk da ita kanta tasan marin da hadiyyan tayi shiryayye ne da ko waye aka yiwa shi sai yaji matuqa a jikinsa. "Barta.....barta.....ta tsammaci ni din sa'arta ce,batasan ko yayartata da take kallon kanta jan wuya ba ni nasha gabanta wallahi faufau" ".....yaaya.....kina jin abinda take fadi?,kina ganin abinda tayimin?" Huda ta fadi muryarta na rawa,kuka yana shirin qwace mata amma bataso tayi kukan don bata shirya yinsa a gaban wadannan azzaluman ba. Mutanen da babu rahama tausayi jin qai ko imani a zukatansu a tattare dasu. Mutanen da d'ai basa kallon maraicinsu basa kuma kallon komai a tattare dasu face zallar sharri da mugun fata tare da mummunar makoma. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 40 Idanunta ta lumshe tana gyada kai "Ya isa huda.....ki wuce daki.....karki sake tsaiwa a nan" Ta fadi tana duban idanun huda. Kai hudan ta jinjina,da alamu umarnin sabreen din ya mata nauyi da yawa,da alama a yau ta bata umarnin da takejin matuqar nauyin bi da dauka.....umarnin da zuciya ke raya mata kamar ta takeshi "Aikin banza aikin wofi.....ni wallahi na riga na tserewa mutum.....duk iya barikinsa saidai ya ganni ya qyale,ba wanda nake tsoro ko shakka,hakanan babu wanda zan dagawa qafa" Hadiyyan ta fadi tana jujjuya jiki cike da jin taqamar ta daki hudan a bulus. "Ke meya kaiki ma kulasu?,mutumin da yake kan hanyar samun kwalin degree a fannin likitanci?" Cewar bibo tana bin bayan sabreen da harara wadda tuni ta fara takawa tana barin wajen "Qyaleno bibo....wani lokaci ajjiye karatun akeyi ai ka nunawa mutum kaima fa ka iya barikin nan ehe...tarbiyya ke sawa kake dage qafa" "A'ahhh.....akul,zuba ruwa ki kurkure bakinki,'yar nan meye hadinki da bariki?,bariki fa?,suma jaza musu akayi.....don ko yaya ka taba bariki dai dole a samu me gado kota nono sa zuqa" Cak ta tsaya daga tafiyar data fara yi zuwa daki,bugun zuciyarta nason qara yawa dajin lafazin bibo "Aikuwa dai an tafi lahira an bar musu gado mara amfani wallahi" Hadiyyan ta fadi tana gyara daurin zaninta tana gatsina fuska. Lafazin hadiyyan ya sanyata waiwayowa,wani irin zafi takeji yana sauka mata a qirji,ranta yana wani irin mummunan baci "Akul hadiyya.....kul dinki......hawainiyarki ta kiyayi ramar iyaye na...." Kammala daura zanin tayi da gaggawa ta maida hannunta ga qugunta duka tana riqe dasu,fuska da bakinta cike fal da isgili rashin mutunci da wulaqanci,idanunta tsakiyar na sabreen "Idan naqi ji fa?,kina da sauran wani abu da zakiyimin ne sabreen?". Kai ta dauke sabreen din,tana hadiyar wani yawu me tauri tamkar dunqulallen dan waken da ya tsaya a maqogaro. Kamar ba zata tanka ba kafin ta waiwayo,a nutse ta kalli idanunta tace "Ki gwada qinjin gargadina mana hadiyya koda na minti guda ne kiga abinda zaya faru?" Ta qarashe maganar cikin jin zuciyarta da ruhinta sun taurare. Akan batun iyayenta kuma komai tana iya aikatashi muddin hakan zai sanya ta kare mutuncinsu daga baki da aibantawar mutanen da basusan me ake nufi da daraja da kuma kimar dan adam ba "Hadiyya.....rabu da ita.....karki sake ce mata komai don ke din tsatson mutunci ce......kuma muddin hassada tana dawainiya da mutum akan ci gaban daka samu da kulawa ta iyaye komai ma zai iyayi maka don ganin kun dawo daya kai dashi" Kalmar HASSADA ta sanya sabreen waiwayowa ta kalli hadiyyan da bibo din gaba dayansu. Banda yadda ranta yakai maqurar baci da babu abinda zai hanata murmusawa. Wata kalma ce da take daidai da hali da kuma abinda ke cin zuciyarsu a kanta,shine sukeson sanya dukkan qarfinsu su juyar da ita zuwa kanta. Tana jiyo bibo tana ci gaba da soki burutsunta,sai bata bi takai ba,ta dinga takawa a hankali abinta har ta wuce zuwa dakin su. Wani zafi da zugi zuciyarta takeyi mata. Wani irin radadi data jima bata ji irinsa ba saboda kawar da kanta daga harka da sabgar kowa a gidan. Tana kallon yadda huda ke zaune tana kuka amma batace mata komai ba. Tasan kukanta guda biyu ne,na tadda hadiyyan taci mutuncinta dasu gaba daya amma sabreen din ta hanata maida martani. Ita nadra da haneefa sukayi sallansu,don har suka idar huda din tana zaune tana kuka. A hankali ta maida idanunta kan hudan,tana jin tausayinsu dukka yana kamasu. A hakan a sanda rayuwa ta fara musu kyau. A hakan a sanda ta jajirce akansu.....a sanda basu nemi komai a gurin kowa ba......a sanda asirinsu yake a lullube ba tare da sunyi ROKO ko bara ba.....ba kuma tare da sun nema komai a wajen kowa ba......ya rayuwa zata kasance musu a sanda dukka babu wadannan ababen data lissafa?. "Ki tashi ki dauki pure water kiyi alwala cikin kitchen" Tace da ita tana ci gaba da sauke kanta qasa. Abubuwa ne cunkus masu yawa qasan ranta. Har tayi sallar nadra ta zuba musu abinci daga ita har hudan ba wanda ya samu damar sanya komai a cikinsa. Ta kama haneefa ta tsefe mata kanta,don ba abinda take bari suyi cikin unguwar,bata bari kowacce kalar mu'amala ta hadasu da kowa,tana kaffa kaffa da komai nasu,ta nesanta su da mu'amala da kowa don kiyaye jinsu da kuma ganinsu,tana dubansu tace musu "Gobe zamu fita kitso,ke nadra kece me nauyi,bazanyi jira ba me yawa don da wuri zamu dawo gida in sha Allah". "To" Suka amsa mata gaba daya. Ta miqe a nutse ta barsu a falon,don tasan ba zasu kwanta yanzu ba har sai sun gama kallon film din da ake haskawa. Numfashi ta sauke me nauyi sanda ta zube ruf da ciki saman gado tana lumshe idanunta,sai takejin fitar numfashin tamkar raguwar radadi ne daga zuciyarta. A haka idan ka kalleta zaka dauka bacci takeyi,amma idanunta biyu tana ci gaba da sauraron motsin su nadra jifa jifa daga falon. Radadin da rayuwa ke tafe dashi take tunawa daki daki. Ba wani majibancin al'amari da zata sanya kanta saman kafadunsa tayi kuka.....ba wanda zata amayarwa da irin radadin da takeji.....ba abokin shawara.....ba abokin raba dadi da akasinsa,sai nauye nauye dake aje saman kanta masu tarin yawa. Har suka kammala komai sukayi shirin bacci suka kwanta tana jinsu,sai da kusan bacci ya daukesu sannan ta miqe don samawa kanta abinda zataci,daidai lokacin taga motsawar huda. "Huda?" Kai tsaye tayi kiran sunanta don ta tabbatar batayi bacci ba kenan. Abinda kuma ke alamta mata bacin ran da take ciki ne har yanzu yake nuqurqusarta. Qasa qasa ta amsa mata,sai ta umarceta ta tashi ta zauna. Ba musu ta yaye abun rufar ta miqe ta zauna tana dubanta. Takawa tayi zuwa gaban gadon ta zauna idanunta a kanta. Ta zuba mata idanu na wasu mintuna ta zuba mata,abinda ya yiwa hudan nauyi tayi qasa da kanta,ta buda bakinta a hankali tana jin tsanar gidan dama duka mutanen ciki "Kiyi haquri adda" "Yanzu meye ribarki huda?,wace riba kikaci bayan kin tsaya kin biyewa hadiyya?,shikenan kalaman da kunnuwanki keson ji daga bakinsu kinjisu hankalinki ya kwanta?". Hankalinta taji yadan tashi,tsanar rayuwar gidan tare da ci gaba da rayuwa ma a cikin gidan duka tana saukar mata. Ta girgiza kai idanunta suna tara qwalla me yawa "Ba haka bane adda......bakiji abinda suke fada a kanki bane?,bakiji mummunan jifa da qazafin da sukeyi miki ba?" Ta fada hawaye na saukar mata. Yawu itama ta hadiya tana qoqarin hana nata qwallar fita,duk da ba qaramin abu bane yake sanya fitar hawaye daga idanunta ba "Ki barsu suyita fada mana huda?,meye zai gutsireni?,mene ne kena zai gutsireki?......shin kin manta su din su waye?,ko kin manta ne huda?" Kai ta girgiza qwaqwalwarta na tunano mata abubuwa da dama daga halaye da dabi'un mutanen gidan. "Wannan ya zama lokaci na qarshe da zaki sake maida kai cikin shirginsu" "Kiyi haquri" Ta fada bayan ta gyada kai "Ya wuce......ki kwanta hakanan" Ta fada tana dan taba kafadarta. Dukka wayoyinta ta dauka harda ma wadanda ta basu hutu na satittika dana watanni,sannan a nutse ta wuce zuwa falon. Bata zauna ba sai data zuba abinci,duk da cin abincin nata har kullum tamkar wasan yara yake. Takan tuna umminta duk sanda ta zauna irin haka zataci abinci "Kedai saidai addu'ar shiriya sabreen.....yarinya kamar mage?,ki dinga lasar abinci?,zakici ba zakici ba?,shi yasa kikejin jiki idan ciwonki ya tashi". Numfashi ta sauke,ta saka hannu tana goge qwallar data cika mata idanu. Babu wani lokaci ko yanayi da zaizo bata tuna umminta ba. Ba wani dan qaramin sakan ko minti da zaizo ba tare da tuna umminta ya sanyata zubda hawaye. Bangwaye guda biyun da zubewarsu ya sauya rayuwarsu daga wani abu izuwa wani abun na daban. Kunna wayoyij tayi gaba dayansu ta kuma jeresu a gabanta,ta jawo abincin tana qoqarin tilastawa kanta ci,idanunta na yawo tsakanin fuskokin wayoyin. Haske kusan dukansu suka dinga yi alamun shigowar saqonni zuwa gareta kena. Ta saba da irin hakan duk sanda ta baiwa wayoyinta hutu toba shakka zata samu saqonnin da basu da adadi. Da yawansu tana gogesu ne ba tare da tako duba ba,d'ai d'aiku daga ciki take tsaiwa dubawa *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *_Arewabooks:@Huguma_* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 __________________________ PAGE 41 Kusan a tare wayoyi uku suka dauki ruri dake nuna alamun ana kiranta. Mashkur mikail da ya'aqoub,abubuwan farautarta da batasan waye a ciki zai fada komarta ba. Ta dinga bin sunayen da wayoyin da kallo cikin canki cankin wanda zata fara daga wayarsa a ciki har sai da suka katse,sai ta barwa ranta wanda ya soma sake kira. Saidai kuma cikin rashin sa'a sai ga mashkur da mikail suna kiranta lokaci guda. Plate din hannunta ta ajiye,ta sanya hannu tana daukan kiran mikail. A lissafinta shine mutum na farko da takeson saukewa daga layinta. Dukka wani binciken halayya nasa suna gwada mata tsantsar dacewar ya karbi sakamako da horo yadda ya dace. Ita kanta batasan adadin abinda zata diba daga gareshi ba,saidai ko banza ta sanya zata sanyasu a muhalli da guraben da suka dace. A jirkice yayi mata sallama da muryar data sanya ta saka masa ayar tambaya. Ta daga wayar daga kunnuwanta ta duba fuskar wayar tana mamaki "Bayan neman mata harda caca da harqallolinsa harda shaye shaye?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,sai ta maida wayar kunnenta kawai tana saurarensa. "Sai yaushe zaki bani dama ne?......ina tsananin kewarki......ina son kasancewa dake" Abinda ya fada kenan yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Katse wayar tayi tana jan dogon tsaki. Baci kawai takeji ranta yana yi kota ina tare da azalzala mata akan mikail. Sai ta jawo wata qaramar waya daga gefanta wadda bata hasken komai ba ta turawa JIB qaramin saqo. Tana jin ya kamata aikinta ya fara ta kansa. Yadda mashkur yaketa kiranta ba daga qafa ya sanya ta share kiran ya'aqoub ta daga nashi. Kiran ya'aqoub din ma bata mata rai yakeyi,ta tabbatar dukkan wani magidanci me mata irinsa a yanzun yana cikin gidansa ne koda a dakinsa ko a sassan yake. Taga maza da yawa da halayensu,daya daga cikin halayyar tasu kuma da tafi baqanta mata rai take tunzurata shine wannan. Wai ta yaya ma zatayi Aure?,bayan bataga komai ba a tattare da mazan sai munanan dabi'u dake girgiza zukatan matan su haifar musu da muguwar illar hawan jini ko ciwon zuciya?,ko mummunan zawarcin da har ki mutu bazai fita a tarihinki ba?. Har abada tana kallon zaman 'ya mace me cikakken 'yanci a yayin da ya kasance babu igiyar wani a kanta. "Saura kadan ki kashemin raina muhseena......hala bakisan girman soyayyar da nake miki ba har yanzu?......kinsan Allah?,banqi a daren nan ace an daura aurena dake ba?" "Aure?" Ta furta a hankali tana jin kalmar tayi mata girma da yawa. "Yes aure muhseena....." Ya maimaita fada yana gyara zamansa cikin tattausar sofa din da yake kai. Yana fatan samun gamsashen amsa tare da mamakin kansa yadda yarinyar ta sauya masa tsari gaba daya. "Gaskiya ne" Ta amsa masa a taqaice tana aje numfashi. Hira ya dinga qoqarin janta dashi,duk da ita din bame doguwar hira bace amma ta dan sake masa,don itace hanya guda daya da take dashi da zata haska mata hanyar gano gurbin da zata dasa bomb dinta. "Kiyimin alfarma daya mana......ki gaya min credit dinki na yimin rakiya dubai for just one week......ni kuma nayi alqawari zan biya ko nawa ne" Ya fada yana sake jin kowacce gaba tasa tana narkewa da sha'awarta da sonta. Yanajin koda bata shirya aurensa ba......zai kashe mata ko nawa ne suyi irin rayuwar da yake muradi......idan da yiwuwar ta zama tashin a gaba sai ta zama.....idan ma hakan bata samu ba yana ganin duk inda ta kwana sha ne muddin ya tsira da abinda yake qulafucin samu. "Zan baki dama kiyi tunani......sannan ki yanke ko nawa kikeso muhseena.....ko nawa ne muddin raina zaikai ga muradinsa". Maganarsa t qarshe kenan data sake sanyawa sabreen mummunan zato ga maza......maganarsa ta qarshe data sanyata ta kusa raba dare tana kuka......ta kuma dinga godewa Allah ta wasu fannin. Mashkur din data tura masa mabanbantan mabuqata da buqatar neman tallafin da duka duka baikai ko digo cikin abinda ya mallaka ba yasa aka koresu?......yace bashi dashi?.....yace bazaya bada ba?......wannan mashkur din yau shike bada damar a nemi ko nawa ne zai iya mallaka mata bisa rashin sanin WACECE ITA?. Hakan tamkar wata dama ce a gareta kenan da zata samu dukka kudaden da takeso......amma bisa sharadin sadaukar da abinda yafi komai mutunci a tare da ita?. Koda ta saba ko tana da damar accepting masa abinda yazo dashi.......tabbas ba zata lamunce ba......tanaso ta debi kudadensa ta hanyar data saba azabtar da sauran.......tanaso ta debesu ta hanyar da zaiji ciwon da bazai kankaru ba a zuciyarsa.......tanaso ta debi kudin da zai tsaye masa a rai......yayi masa ciwo fiye da yadda rayuwa da zukatan matan da ya fadawa mutuncinsu sukayi musu ciwo......tanason bashi darasi me girma a rayuwa.......tanason shima ya girgiza girgizar da zata tsaida masa komai na rayuwarsa cakkkkk koda ba tsaiwa bace ta har abada......to amma kuma ta sani.......babban plan da yake buqatar nutsuwa da tsare tsare masu yawa. Don haka da safiyar washegari ta tura JIB wani saqon da sunan mutum biyu. Tana tsaye tana shan ruwan dumin da takesha duk safiya kafin shigarta wanka saqo ya shigo wayarta. Sanda ta duba sai ta samu alert na kudi daga wajen ya'aqoub. Five hundred thousand ce,sai ta gyada kai a hankali tana sakin murmushin takaici. Don kyauta yana da kyauta ya'aqoub ba daga baya ba......abinda bata da yaqini shine haka yake a cikin gidansa?,ko shima fankan fayau ne?. Saqon godiya ta tura masa a gajarce,ta aje wayar tana shirin wucewa wanka wani saqon ya sake shigowa "Patiently waiting for you" Share saqon tayi hade da sauran. Tasan me saqonsa ke nufi a gajarce. Kowacce safiya izina ce a gareta,kowacce rana kowanne sati da kuma kowanne wata cikin rayuwarta yana bude mata babi na abubuwa da yawa cikin rayuwarta. Waishin akwai ragowar NAGARTATTUN MAZA kuwa?,tambayar da kullum idan ta yiwa kanta ita take bawa kanta da kanta amsa da BABU. Kanta tsaye take takawa cikin tsakar gidan nasu ba tare data daga kai ba bare ta lura da waye a hagunta ko damanta?. Ba tare data damu da kallon nan nasu data tabbatar a safiyar yau zai ninka ko ma ya canza salo saboda abinda ya faru a jiya. Dab da zata sanya qafarta a qofar toilet din nasu dake da sassa biyu bathroom da toilet ta jiyo muryarsa yana koda sallama. Sallamar da muddin ya yita duk wani dake da hadin kai dashi take masa dadi......duk wani wanda yake da qulli dashi Kuma yake neman yin ta kansa,mutane kuma kamar ita sukejin kamar su turashi ya koma muhallin da ya fito. Koda taso tayi shigewarta toilet din ta tabbatar sai ya ganta don ya iso dab da wajen. Don haka ta tsaya a nutse tana bude toilet din ta hanyar murza handle,abinda ya bashi damar qarasa shigowa farfajiyar tsakar gidan. Da ita ya fara hada idanu kamar yadda nata idanun suka zube a fuskarsa. Kamanni dai da mahaifinta har kullum sune,bata kuma fasa ganinsu shimfide a fuskarsa,saidai nisan tazarar halayya da dabi'un sun kai girman tazarar dake tsakanin sama da qasa. "Yauwa alhamdulillah......ai gwara dana sameki cikin gidan.....zuwan dama naki ne" Kallonsa kawai tayi ba tare da wani mamaki ba,dama wanne zuwa ne zaiyi gidan ba nata ba?,koda yayi zuwan daba nata ba to lallai daga qarshe sai ya zama nata ko kuma ya hado da ita a abinda bai zama damuwarta bama bare y shafeta. Amma tun a jiya tasan tabbas dama zayazo,shi yasa taso su fice kitso da wuri yazo ya taras da sararinsu kawai. "Ina kwana kawu?" Ta fada cikin girman nan da bata fasa bashi shi kaman yadda kowa cikin gidan ke bashi duk kuwa da farin sanin da tayi na waye shi?,sanin da kaf gidan tayi yaqinin ba wanda ya masa shi......sanin da a qa'ida ya cancanci ta rainashi......amma sai kuma batayi hakan ba.......sanin da ko yaushe ta tunashi dashi take jin kaico da bacin rai da rashin sanin son ganin gilmawarsa. "Lafiya qalau......idan kin baro bandakin ki sameni a dakin bibo" Ya fada yana saba babbar rigarsa yana wucewa ciki tare da jaddada sallamarsa. Da kallon takaici ta bishi,tasan dama zaa rina,ba wani abu da zai fari cikin gidan ya kwana ya hhantse baije kunnuwansa ba.......yana kuma zuwa kunnuwan nasa ne ta hanya guda daya rak wato BIBO. Idanma akwai ta biyunta to bata bayyana ba tukunna. Cikin rashin damuwa da lamuransu gaba dayansu ta kada kanta ta wuce bandakin. Babu wani abu da zai sanyata gaggawa a zuwa kiran data tabbatar babu alkhairi sam sam a tare dashi. Wannan ya sanya ta kammala wankanta a nutse,takuma tsaya gaban madubi ta shirya tsaf kamar yadda ta saba. Tun bata kammala ba ya aiko kiranta ya kusa sau biyar. Ana shidan ta tsaida nadra da taji tana gaya musu cewan kaya take sanyawa "Kace gani nan zuwa" Ta fadima usman daya aiko. Rigar lace tayi niyyar sakawa,don haka ta fara sanya 'yar cikin rigar ta yane kanta da mayafi ta zura slippers dinta tana cewa "Ku kammala shiryawa ina dawowa zamu wuce" Ta qarasa fada tana sanya qafafunta a waje,huda kuma ta bita da kallo. Sam bataso ace sabreen din taje da kanta kamar yadda kawu ya buqata ba,ta tabbatar da cewa ba wai wani abun arziqi zai aiwatar ba face tsantsar son zuciya da son rai kamar yadda suka saba. Ba wani lokaci da abu irin haka zai taso cikin gidan ya zamana anyi hukunci cikin adalci da sanin ya kamata. Hankali kwance ta daga labulen dakin bibo gami da sallama. Su uku ne cikin falon,kawu bibo sai hadiyya dake zaune saman daya daga cikin kujerun. Qafarta daya saman daya tana kadata a hankali. Tako ina tana jin kishin wanzuwar komai dake tattare da sabreen din. Kowanne abu tana yinsa ne don kawai ta samu daqile sabreen din. Ba haka takeso ta bude idanuwa ta ganta ba. Wani qaqqarfan abu ya dasu a ranta game da sabreen din. A haka mutane ke raina matakin da take kai.....suke mata kallon wadda ke tafiya bisa baragurbin bigire......amma ita a nata idanun ta sani cewa sabreen din tayi mata wani irin nisan tazara me tarin yawa. Bataso ta ganta a haka.....ba'a haka take da muradin ganinta ba,tana son ta sauya daga matsayin da take kai a yanzun,shine abu daya da zai gamsar da ita..... *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *_Arewabooks:@Huguma_* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ________________________ PAGE 42 Janye dubanta tayi daga kan hadiyya,sai ta nemi hannun kujerar dake daga bakin qofa ta zauna akai,wayarta a hannunta tana qoqarin sakata a silent. Ta manta yaushe ne lokaci na qarshe data shigo wannan dakin,bama shi ba,dukkan wani daki dake cikin gidan ba muhallin shigarta bane. "To da kika shigo kikayi mana derere saman kujera ai sai ki sauko ko?" Muryar bibo ta rasa kunnenta. Dauke dubanta tayi daga saman wayar ta aza a fuskarta. Abubuwanta sun fara mata nauyi akai,tanason ta fara shige huruminta. Tana ganin kima da martabarta a matsayinta na macen data taba kasancewa mata a wajen mahaifinta,amma ta lura da sam sam bata kula da wannan. Dauke idanunta tayi daga kan bibo din,tana ji a ranta lokaci ya kusa da zata sassauta wannan girma da martabar da take bata,tunda har ita din ta gaza riqo dasu yadda ya kamata "Gani" Ta fadi kai tsaye tana duban kawun. Zamansa ya gyara yana wani hakimcewa. Jira yake su kammala da maganar da aka tattagoshi a kanta ya gabatar da nasa batun wanda shine yafi damunsa "Yanzu ke......wani irin baqin hali gareki ne?.....kin fita ZAKKA ke kadai?,kin addabi kowa kin damu kowa?,a gidan nan kaf babu wanda yake da matsala sai ke?" Duk da tasan qarshen zancan,ta kuma san abinda ya sanyashi debo dogon zance har haka amma sai maganganun nasa suka bata mamaki. Banda tsabar rashin son zaman lafiya na mutanen gidan......a yanayin yadda ta tsara rayuwarta dana 'yan uwanta,ya kamata ace tana cikin sahun jerin mutanen da za'a mance da wanzuwarsu cikin gidan. Zaka jima baka ga gilmawarta ba,zaka jima baka ganta zaune a farfajiya ko filin tsakar gidansu ba.....zaka jima baka ganta a tsaye tana magana da kowa ba,to wai shin me ta tsarewa bibo da ire irenta cikin gidan?. "Wani abu akace maka ya faru?" Tayi tambayar tana tsareshi da idanu. Fada yakeso rufeta dashi kamar yadda bibo ke buqata.....amma kuma yana duba da tunanin kada hakan ya sarayar da samuwar tashi buqatar. "Yo har sai ance miki ma wani abu ya faru cikin gidan nan banda raini?.....me ya kaiku shiga hurumin yarinyar nan banda neman tada zaune tsaye?,yarinyar da babu abinda ta sanya a gaba banda karatunta?,inajin kaf cikin yaran marigayi babu kamarta ko akwai?" Ya qarashe tambayar yana maida dubansa kan bibo da taketa cika tana batsewa. Dukka salon fadan daya dauko babu wanda yayi mata "Ina fa?.....mu irin karatu ne,kuma karatu shine a gabanmu" Ta fada tana gyara daurin dankwalinta. Da idanu kawai take binsu tamkar bata fahimtar koda kalma daya daga cikin maganganunsa,har zuwa sanda yakai qarshe ya kuma jona da tambayar bayyana fifiko me yawa tsakaninsu da hadiyya. Tsam ta miqe tana duban kawun "An gama?,inaso na fita ne" Ta fadi kai tsaye ba tare da tayi duba ga sashen da bibo ke zaune ba. Dukkaninsu idanu suka zuba mata su ukun,yayin data juya a hankali tana nufar qofa ganin kawun bai iya cewa komai da ita ba. Cikin tsananin jin zafi gami da yunqurowar wani boyayyen zazzafan kishinta a kanta ta sauke qafafunta tana aje wayar hannunta gefe "Kin gani ko bibo?,ai dama na gaya miki......wallahi bata kunya ko shakkar kowa......ni nasan kawu ba matakin da zai iya dauka a kai....." "Ke!.....yimin shuru,rashin kunya zakiyimin?" Ya fada cikin fadan nan nasa yana rarraba idanu. A duniya idan akwai abinda ya tsana itace kalmar YA KASA KO YA GAZA "Aah dakata sule......" Bibo ta fada tana daga masa hannunta daidai sanda kunnuwan sabreen sukayi nisa daga jin cecekucensu. "rashin kunya har takai wadda waccen figaggiyar gantalalliyar yarinyar tayi maka.....tambadaddiya da ka kasa saitota cikin yaran dan uwanka......kaf dinsu yara mata goma sha tara amma ita daya ta fita ZAKKA?,to kada kazo kace zaka zaqemin akan yarinya......me laifi daban wanda za'a huce a kansa daban?". Ransa ya baci sosai,don shi din irin mutanen nan ne da basa son raini ko wargi ko qanqani. Banda ma bibo din da taga wallensa......kaf yaran gidan tsoro da shakkarsa suke idan ka cire SABREEN din "Ke hajara......dakata,hawainiyarki ta kiyayi ramata......kibar ganin ina daka ta taki.....wallahi ina nan yadda kika sanni......kawai ina duba wasu abubuwa ne nake rama miki halacci da halacci......amma tunda iskancin naki a kaina zai sauka a gaban qaramar yarinya irin wannan......to shikenan......ni na zare hannuna daga sha'aninki cikin gidan nan......" Ya fada yana miqewa cikin hargagi gami da kakkabe babbar rigarsa. "Haba sule.....zauna mana kaji......ba haka nake nufi ba.....ni dadina dakai wannan masifar taka da jarabar". Tsaiwa yayi yana hade rai gami da dubanta "Ba haka kike nufi ba hajara gayamin abinda kike nufi". Sai kuma ya waiwaya sashen da hadiyya ke zaune "Tashi ki bawa mutane guri kin zauna kina raba idanu a gabansu" Ya fadi mata cikin tsawa kamar zaibi ta kanta. Wayarta ta dauka sumi sumi tana yin hanyar shigewa bedroom din bibo din,qasan ranta cunkushe fal da baqinciki. Baiyi mata yadda takeso ba,ba kuma haka takeso ya yiwa SABREEN ba. Batasan dame sabreen din ta fisu ba da har tauraruwarta tafi tasu haske cikin gidan,duk da tayi yaqinin ko meye sabreen din zata juya ta kuma nunawa duniya shi to ba shakka ya samu ne daga dattin ZINA da kuma dattin BARIKI. Ba abu mafi daure kai irin mazan dake karakaina a kanta tamkar su sadaukar mata da rayukansu......amma ta gaza cafke koda guda daya ta maisheshi mijin aure?. "Mazan bariki dama suna auren macen da suka hadu da ita a bariki?,ai saidai su tsotseta tas.....su musaya wannan zaqin da gardin da suka samu daga gareta da 'yan kudaden da zasuyita mata barinsa......daga sanda buqata kuma ta biya su tattarata su watsar su qara gaba zu zabi wata". Sai ta tuna maganar da sukayi taba yi da bibo wadda ke kamaceceniya da kalmomin maleeka roommate dinta. Juyi tayi kadan saman gadon,tana da burika masu tarin yawa akan karatunta,wannan ya sanya ta sadaukar da rayuwarka akanshi. Tana so ta ganta tana fantamawa,tanason ta ganta tana haskawa tamkar sabreen da dukkan wani alatu da jin dadi......tanaso taga maza suna mutuwa a kanta sama da sabreen......amma dukka ta hanyar karatunta da kyawun sura da Allah ya bata. Tana cikin sahun jerin farko farko da 'ya'ya masu kyau a gidan......ta tabbata ko wannan ya isheta jari wajen zaben kalar mijin da take buri da muradi idan aka qara da karatunta da takesa ran kammalashi ta kuma riqi kyakkyawan certificate mafi girman daraja a idanun mutane. Ta samesu a zaune sun gama shiryawa sanda ta koma dakin. Kai tsaye ta wuce can ciki ta jawo rigarta ta sama ta zura,ta hada igiyoyin ta daureta ta zauna dai dai jikinta,abinda ya bawa rigar daman fidda kyakkyawan shape din nan nata da ba kasafai ya fiya bayyana ba saboda ita din ba ma'abociyar sanya damammun kaya bace. Sai data sake goge jikinta da sassanyan oil perfume dinta sannan ta fara rolling dan kwalinta saman kanta idanunta akan fuskarta data bayyana tarwai ta cikin madubin. Maganganunsu taketa tattaunawa ita da zuciyarta. Dabiar kawun dama bibo gaba daya. Yadda tsahon lokaci da zamani bai sanya kowannensu ya sauya ba. Ranta da zuciyarta duka ba dadi. Ta iya rigima tuburan idan taso......ta iya surutu har kayi zaton ma ba ita bace......hakanan ta iya fada musu da kuma taurin kai......amma daga sanda rayuwa ta soma Karantar da ita wasu darussa sai ta gane basu take buqata ba,don haka ta tattarasu ta aje a gefe. Jakar da zata dace da shigar da kuma yanayin ta dauko. Kaman yadda ta saba duba jaka kafin takai ga fita da ita haka ma wanna,a nan taci karo da kudaden da mashkur ya bata. Maidasu jakar tayi da zummar damqawa suraj su,daidai lokacin haneefa ta shigo tana kiranta "Kizo inji kawu sule" "Kawu kuma?" Ta tambayi haneefan tana duban idanunta "Eh" Kamar ba zata mata komai ba,sai ta fesar da iska daga bakinta. Tasan dukkan abinda zai sanyashi shigowa wajenta baya taba zame mata abun alkhairi face tarin matsaloli fadace fadace da fadin maganganu barkatai da zasu yamutsa DUNIYARTA tana zaune salin alin "Kice masa gani nan" Ta bata amsa tana juyawa sashen ajiye takalmanta ta fara dubawa. Takalma ne kala kala masu mabanbantan shape kudi da kuma kaloli. Wani adadi ne me yawa ma'ajiyar takalman taci,wanda dukkansu idan ka kalla babu takalmin qasa sa dubu goma. A duk sanda ta kalli sashen suturar data mallaka a yanzu,a karan kanta mamakinta yana sake ninkuwa ne. Suturu na alfarmar da yaran masu hannu da shuni ke taqamar mallaka ko jin isar cewa sun kai. Daya daga ciki ta zaro,ta aje a qasa ta zura a qafafunta sannan ta debi wayoyinta ta jefa a jaka tayi hanyar fita tana ji a ranta ko sisi a yau din bazai samu daga wajenta ba muddin abinda ya shigo dashi kenan. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 43 ___________________________ GROUP 1 https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz *_assalamu alaikum warahmatullah_* *_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_* *_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_* *_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_* Shadda Laces Atamfa Kayan yara English wears dana jarirai Qawatattun handbags Mayafai Abayas da jallabiyas Inner wears Huluna na maza da mata yara da manya socks Takalma na maza da mata yara da manya Lafayas Sarqoqi agoguna banguls da rings _kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_ _bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_ *_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_* *_masu manyan qarfi da matsakaita?_* *_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_* *_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_* *MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA* *_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_* *_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_* *_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽 GROUP 2LINK https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr _________________________ Samunsa tayi zaune dirshan saman carfet yana karakaina da kwanukan da suka gama breakfast. Ya buda flask din da suka zuba dafaffen naman kai wanda sukaci suka bar sauran sai zuwa dare. Yana cikin ire iren siyayyar da take musu lokaci bayan lokaci dukka a qoqarinta na ganin basu rasa komai ba......basu nema komai sun rasa ba......hakanan komai din bai gagaresu ba. Tana da buri me yawa akansu,tana da mafarki mai fadi......tana kuma fata da sanya ran wataran zata basu rayuwa fiye da wadda sukeyi a yanzu haka. Daga kai yayi yana dubanta sanda yake tauna naman,zaqin maggi yana ratsashi. "To zauna mana banda abinki,kikayi wani dogogo saman hannun kujera?" Ya fadi saboda yadda ta kame a hannun kujerar rungume da hannayenta. Sam batason ya bata mata lokaci ta kuma fahimci zuwa yayi yaci mata lokacin "Kawu ai ina tunanin wancan maganan mun gama da ita ko?,fita nakeso nayi ne ana jira na" Ta fada tana duba agogon hannunta. "Kefa kin fiya tsiya da hurwar banza da wofi,ayita tattaroki kina wargajewa?,har sai kin jawo magauta sun jimu?" Shuruuuu tayi tana me zuba masa idanu tare da mamakin fitar kalamin daga bakinsa. Wai magauta,ji kuma na nawa?,ko yana tunanin cikin gidan yana da wani magauci a tsakaninsu da ya wuce shi karan kansa?. "Tunda sauri kike bari nayi a gaggauce" Ya fada yana sude hannunsa daya nado romon naman kan,ya gyara zamansa sosai yana kallonta. "Kinsan hausawa sunce ko kana gudu haifi ka yar.....kuma ita haihuwa rana gareta" Yayi maganar cikin sigar kwantar da murya da jan hankali. Bata ce masa ta tafasa ya sauke ba,tadai ci gaba da kallonsa yana bayanansa tare da son jin inda zantukansa zasu tuqe "Wato wata gwaggwabar mu'amala ce ta taso mana,wadda cikin ikon Allah take buqatar adam zuba wasu kudade kuma a kwashe da riba me tarin yawa.......to kinsam harka ta samu dai ba'a wasa da ita a lokaci irin wannan,duba da yadda al'amuran qasa suka yamutse....to na duba na dubo......na laluba na lalubo kaf 'yan uwa na kusa dana nesa......ba wanda zai rufan sittira ya bani kudin nan aro ko bashi banda ke diyar albarka" Ya qarasa maganar yana addu'a qasan ransa. Ya santa sarai.....yasan aikinta,yasan kuma abinda zata aikata da wanda ba zata yi din ba. Ya jima baiga yarinya mai zubin matsorata ba,wadda kuma a zahiri zuciyarta a tsaye take carrr babu tsoro ba irin sabreen din. Tsam ta miqe abinta bayan data fahimci cewa yakai aya a maganarsa "Bani da wasu kudade kawu.....zan fita sai na dawo" Ta fada kanta tsaye tana gyara chain din hand bag dinta. Daga zaunen ya tada kai yana dubanta "Wai baki fahimci abinda nake magana bane akai sabreen?" Qaramin murmushi ta saki. Ta sani,idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba,zaije yayi caca ne.....abar da ya jima yana tabawa da taimakon mahaifinta ta soma sakinsa,sai gashi a yanzu gushewar me masa saiti ta sanya ya dawo da dukka wasu tsaffin dabi'unsa da ake sanya ran yayi adabo dasu. Duk da hanyar da take samar da kudadenta.....amma tayi imanin ba zata iya diba ta bashi ya buga caca ba. Inda wajen wata lalurar dabanne,ita a karan kanta lokaci bayan lokaci tana miqa mass,shi kansa yasan tana sahun mutane na farko farko da hannunsa ke yawan amsa daga garesu koda bataso haka ba. "Naji kawu...kayi haquri bani dasu" Ta sake fada hankalinta kwance,don sam case dinta bai daga mata hankali ba,don abu daya data sani shine,ko sama da qasa zasu hadu ba zata iya bada silai tata ya sanya a caca ba,bayan tarin buqatu da lalurori dake zayyane cikin littafin ayyukanta da takeson wanzarwa. Tana da babban mafarki akan mutanen da take rayuwa dasu,tana son kowanne ta daukeshi ta dora rayuwarsa bisa wani gurbi ko matakin da koda bayan ta gushe tasan tayi dashen daya baza rassa sassa da kuma jijiyoyi masu inganci da qarko. "Bari dai na miqe don kiga iya adadin tsahona,sannan ki tabbatar da gaske dai nake" Ya fada rai a bace yana miqewar kamar yadda yace. Kallonsa ta sakeyi sosai,a nutse tsaf ta janye iidonta. Ranta yana baci mamaki yana sake mamayarta. Bai taba nuna damuwa ko yaya akan yadda suke rayuwarsu ba,sunci?,basuci ba?,lafiya suke ko akasin haka?,yaya karatunsu lafiyarsu da sauransu,amma a yanzu qarfi da yaji so yake ya dinga qaqaba mata lalurorinshi wanda koda ya sauke su baya gani baya kuna darajta hakan bare ya qimanta su. Fara takawa tayi a nutse tana dosar qofar waje "Idan ka gama zan rufe dakin kawu,dukkanmu zamu fita ne" Ta fada masa a ladabce tamkar ba ita ta hana masa abinda ranshi yakeso ba tana qarasa fita a falon,don ta tabbatar idan ba haka sukayi dashi ba zai yita zama yana jawo zantuka kala kala da daga qarshe zai barta da qunar zuciya da zubar hawaye mai zafi. "Indai ni kika tozarta sabreen zaki gani......na tabbatar inda ubanki ne yazo da buqatarsa ba zaki taba tozartashi ba,ba komai,badai ni kika wulaqanta ba?,to in sha Allah......in sha Allah,sabgar dai da bakiso za'a yita,kuma sai ta kawo arziqin da baki tunani mara mutunci kawai" Ya fada daidai sanda yake sanya qafarsa a waje. Baya taja kawai batace masa komai ba,har ya zura takalmansa yayi gaba yana sababi kamar ya ari baki. A hankali take takawa huda na gefanta,haneefa na daya gefan tana riqe da hannun haneefan cikin nata,sai nadra dake a gabansu da yake tana da sauri a tafiya ba laifi. Dukka su ukun sanye suke da atamfa iri daya kamar yadda mayafansu suke iri daya. Duba daya zakayi musu kasan suna samun kulawar rayuwa daidai gwargwado. Ba yunwa wahala ko jigata a tattare dasu,wanda duka hakan ya samu garesu ne ta sanadiyyar YAYA ME KAMA DA MAHAIFIYA da suka samu. Kaffa kaffa take dasu da rayuwarsu sosai tun daga lokacin da duniya ta gama bude mata dukka fuka fukai da lokunanta da saqonta.......tun daga sanda duniya ta soma yi mata wani karatu wanda a sannan ba'a taba yi mata karatun da yakai gefan wannan ba.....tun daga sanda ta fahimci DUNIYA cike take da ababen tsoro da mutane MAFARAUTA masu banbancin hali da dabi'a cikin abun farautarsu. A haka suka kai qarshen layinsu suka kuma sada kansu da bakin titin unguwarsu. Tsaiwarsu da duka mintunan da basu haura uku ba motar ta karyo daga cikin layinsu da yunqurin hawa bisa babbar kwalta,idanunta suka sauka akan matuqin motar. Za'a iya cewa ido hudu sukayi,shi ya fara gaggawar janye nasa idanun yana gabansa yana faduwa,sai itama ta janye nata tana jan wani dogon siririn tsaki. Bata jin har abada......har numfashinta yabar gangar jikinta zata iya manta wannan fuskar tasa.....yana daya daga cikin mutanen da ba zata taba iya mancesy ba bare akai ga mance fuskarsa......mutumin da had kullum idan ta tunashi take gayawa kanta shekaru hamsin da takwas dinsa a duniya ya yita ne a banza da wofi ba tare data qara masa komai ba......hakanan arziqinsa bai qareshi da komai ba sai dulmiya cikin sabon Allah kaca kaca. Da wannan tunanin ta sanya hannu ta tsaida musu empty keke napep me tahowa,don zai yi wahala ta fita ta hada abun hawa da wani ko wata,ta saba da daukan drop duk inda zata muddin ba busari zai dauketa ba. A mu'amalarta da 'yan uwanta kuwa bata lamunci susan kowa ba ko kuma kowa ya sansu ba,duk fita indai dasu ne abun hawa na haya take dauka duk da aminta da tayi da busari din dama JIB,amma ta sanya a ranta kowanne cikin su akwai iyakarss,aikin da yake mata kuma sam bai shafi 'yan uwanta ba,basu da alaqa sam dasu,ko fuskokinsu cikin su ukun babu ta guda daya da zasu iya shaidawa. Cikin motar dake girke daga nesa kadan daga shagon. Motar da aqalla ta dauki tsahon kwanaki tana sintiri a titin,tana kuma daukan dukka sa'o'in a wanni a fake a wajen ba tare da kowa ya damu da su waye a ciki ba?,meye kuma yake kawosu ba?. Dai dai sanda suke sauka daga napep din,ta biyashi ta kuma sanyasu a gaba suna nufar babban shagon wankin kan gyaran fuska da kuma yin kitso na noor's beauty parlor,daidai lokacin ya dauke idanunsa daga kan wayar hannunsa,idanun kuwa sukayi kyakkyawar sauka a kansu su dukka hudun. Da wani irin hanzarin samun damar cimma abun FARAUTAR ya tabo dan uwansa dake kashingide yana lumshe idanu,da alamun gajiya ta fara sanyashi jin baccin dole. "We found her......" Ya fada da wani irin karsashi da qwarin gwiwa,wanda bai bashi damar jiran abokin nasa ya kammala zama gaba daya ba yayi swapping da sauri zuwa kakkaifar camera dinsa ya soma daukan hotonsu bayan zooming camera din da yayi daga bakin window din,ya kuma bada hoto me kyau duk da 'yar tazarar dake a tsakaninsu. Kafin su shiga ya samu hotuna guda uku kyawawa da suka yalwata farincikinsa. Yayin da abokinsa dake zaune daga gefe bakinsa ya kasa hutawa daga furta "Well done" Ba. Harara ya juya ya watsa masa bayan ya tabbatar ya adana hotunan "Dole kace well done tunda ka kwanta kana shirin yin bacci" Ya fadi masa da gurbatacciyar hausarsa da zata gaya maka shi din ba ainihin bahaushe bane. Dariya ya saki yana cire hular kansa tare da karkadeta ya maida saman kansa "Da gaske na cire tsammani duba da satittikan da muka shafe muna zuwa wajen nan babu wani alamun nasara ko alamun ganinta.....amma yau dai komai ya fara hawa saiti,meye target na gaba?" Ya tambayi abokin nasa yana kallonsa. Haka kawai ta dinga jin wani yanayi yana mamayarta na rashin sukuni da kuma sakewa tun daga sanda suka sauka daga motar har zuwa sanda take zaune saman kujerun da aka qawata wajen ana kitse lallausar sumar nadra da haneefa me tsaho da santsi wadda dukka da tsahonta batakai tata yawa ba. Wayarta ce a hannunta tana duba wasu bayanai da JIB ya tura mata......amma sai takejin kamar akwai wata mantuwa ko kuskure da tayi. A karo na kusan shida ta daga kanta tana duban nadra da fuskarta t fito tayi kyau sakamakon kitson da aka kusa gama mata. Cikin qasa da minti biyu gabanta ya yanke yayi wani mummunan faduwa "Nayi kuskure.....nayi ganganci" Ta fadawa kanta da kanta can qasan zuciyarta tana jin wata qaramar fargaba tana mamayeta. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 44 ________________________ GROUP 1 https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz *_assalamu alaikum warahmatullah_* *_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_* *_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_* *_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_* Shadda Laces Atamfa Kayan yara English wears dana jarirai Qawatattun handbags Mayafai Abayas da jallabiyas Inner wears Huluna na maza da mata yara da manya socks Takalma na maza da mata yara da manya Lafayas Sarqoqi agoguna banguls da rings _kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_ _bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_ *_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_* *_masu manyan qarfi da matsakaita?_* *_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_* *_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_* *MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA* *_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_* *_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_* *_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽 GROUP 2LINK https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr __________________________ Duk wani da zatayi mu'amala dashi......yadda bata yarda yasan daga inda take ko inda zata......hakanan take nesanta tare da barin duk wani muhalli da suka taba haduwa ko ya taba ganinta a can din. Cikin tsarinta bata sake mu'amala ko huld da gurin......tana kuma nisantar wajen da duk abinda zai sanya ta ratsa wajen ko tayi hulda da gurin. Wannan gurin shine guri na qarshe da suka hadu da alhaj naseer.......shine kuma gurin data sauya saboda wankin kai wankin qafa da gyaran fuska da takanyi time to time. Batasan me ya dauke hankalinta ba ta sake dawowa gurin ba,ta karya dokarta da kuma tsarinta da kanta,ya akayi tayi mantuwa irin wannan?,haka kawai saita kasa samun nutsuwa,ta maida wayarta jaka ta ajeta gefe,ta hada hannayenta guri daya sannan ta harde qafarta daya saman daya tana sauraren gilmawar kowanne motsi dake kewayen wajen,tana kuma karantar kai kawo da aikin kowa dake wajen cikin nutsuwarnan tata da kaifin sansano abu. Yawan rashin nutsuwarta ya qara yawa,tilas ta miqe a hankali sanda aka kama kan huda wadda ita daya ta rage sai ita din karan kanta da zaa wankewa kai "Madam saura ke" Daya daga cikin ma'aikatan ta fada tana kallonta sanda take takawa a hankali tana nufar bakin qofar wajen "No......inajin sai zuwa wani lokaci ni na dawo,a kammala dasu dai" "Okay to" Ta amsa mata tana tattare kayan gyaran gashin data baza. Cikin tsanaki ta riqe curtain din wajen. Ta sanya idanunta a nutse tana qarewa titin kallon cikin nazartar kowanne abun hawa dake kai kawo a wajen. A qalla ta kusa kashe mintuna goma a tsaye ta cikin shagon wanda babu lallai kai da kake waje ka iya ganinta. Idanunta basu iya gani ko hangen komai da zata iya sanyashi cikin zargi ba,zargin da zai iya alaqantuwa da wala'alla yanayin da takejin jikinta da zuciyarta a ciki ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana matsawa da baya a hankali cikin ainihin shagon. Ranta yana raya mata wala'alla don ta fito ne da dukkansu shi yasa ta kasa sakewa,sai taji gaba daya ta qagauta a gamawa hudan su wuce ba tare data damu da cewar ita din ba'a yi mata komai ba. "Ta koma?" Ya tambaya daga daya sashen cikin tsananin farinciki,hankalinsa kwance a yau din saboda samun damar kama bakin zarensa da kyau "Eh,ta koma" Suka bashi tabbaci daga inda suka janye motartasu suka ajeta. Wani shu'umin murmushi ya saki,yayi taku biyu yana jan wata dunqulalliyar kujera ya zauna akai "Na gaya muku....tana da matuqar wayo fiye da zaton me zato.....amma ku sani....muddin aikinku ya tafi da kyau.....ya kasance kamar yadda na tsara.....ina me muku albishir din qari akan abinda mukayi yarjejeniya daku" "Aikinka kamar anyi an gama shi ne" Ya maida masa amsa cikin zallar nishadi "Take care.....ina sake maimaita muku.....ku kula" Daga haka ya yanke sadarwar dake tsakaninsu,don baya yarda suyi wayar data wuce minti daya dasu. *******Sanye take cikin daya daga cikin suturu na alfarmar da suma zame mata abun sawarta. Walau fita zatayi?,ko kuma tana zaune ne kawai a gida saboda gwada qarfin izzarta tare da son nunawa duniya matsayinta da kuma kashe qarfin kwadayin izza da kwadayin sauran kayan qyale qyale na rayuwa. Ni'imtaccen falon nata da takejin qarfin iko da isarta sun zartasa a killace yake tsaf kamar yadda dabi'arta take na mace da batason qazanta sam sam,yana gyare ne tsaf bisa jagorancin masu aikin da suke duk wata hidima ta gidan ba tare da tayi cas ba bare as idan ka dauke bada umarni. Ta kasa hankalinta ne gida uku,daya yana ga bada umarnin yadda takeso a tsara table din don zuwan musaddiq cin abincin dare gidan,daya yana ga duban cikar lokacin da zai iso din,yayin da dayan yake kan zuwaira tana sauraren zantukanta da a mafi yawan lokuta sukafi gama da banbadanci. Sake gyara zamanta tayi tana daidaita zanin embroidery vlisco atamfa din dake jikinta wadda kudinta ya tasamma dubu sittin. Ta zube idanunta akan zuwairan karo na uku "Duk yadda zanyi zuwaira.....kome meye ne zai faru dole zan dauki mataki fa.....ba irinmu ake zuwama da irin wadannan abubuwan su bari ba.....komai tsiya musaddiq da fu'ad 'ya'yana ne halak malak,babu wanda ya isa duk duniya ya kankare wannan matsayin" Ta fada har cikin zuciyarta tana jin zafi tsana da qyamar anni......tana jin a duniya ita da alhaji hamza sune manya manyan maqiya kuma abokan gabar da bata da sama dasu. Sake duba agogo tayi,yadda taga lokaci yana ta ja ya sake sanyawa ranta ya baci "Zuwaira yanzu haka yana can ta riqeshi har sai sanda tayi masa izini zai taho gurina?" Kyabe baki zuwairan tayi tana tallafe kanta da hannunta tare da dogarashi jikin kujera,sannan ta karkatar da kanta tana kallon wani sashen,tabbacin abun yana mata matuqar ciwo kenan "Kema ai kinsan kwanan zancen.....ai kinyi sake maryam ba dan qarami ba kuwa". Maganganun zuwaira suka sake zame mata tamkar allura,taja wata doguwar qwafa bacin ranta yana ninkuwa,a take taji duk wani danshi na maqogaronta ya bushe ruwa take da buqatar sha. Kamar ko yaushe a tsawace tayi kiran sunan me aikinta,ta nufota a gaggauce,ba tare data bari ta qaraso ba tace da ita "Koma ki bani ruwa......banason kowanne sai swan.....karki maimaita kuskuren jiya". Jikinta yana ruwa ta amsa mata " In sha Allah ba za'a samu matsala ba" Ta juya da hanzari hanyar kitchen. Su biyu ne kadai zaune saman lafiyayyen dining din na wata iriyar mulmulalliyar kwalba me garai garai. Komai na gidan an zubashi ne bisa nunawa kudi iyakarsa,komai me kyau ne me kuma asalin tsada,kamar yadda komai aka zubashi bisa tsari. Anni ce saman daya daga cikin kujerun,jikinta sanye da wata sassauqar cotton abaya 'yar asalin moroco wadda ta dace da jikinta da kuma shekarunta. Kanta sassalkan dan kwali ne da yazo da rigar,tana riqe da waya da alama wani kira take amsawa da ya janye hankalinsu su duka ita da musaddiq dake zaune saman kujerar dake fuskantar tata. Idanunshi akan annin yana dariya saboda yana iya sauraren abinda siririyar muryar ke fadi ta wayar. Jikinsa na sanye da yadin senate me asalin tsadar. Sosai yadin ya kwanta masa a jiki ya kuma dace da kyakyawar hularsa dake aje saman table din daura da plate din abincin da yaci rabi yana riqe da cokalin yana sauraren wayar anni. "Don Allah anni kice mata ta zauna kin yafewa nanna ita" Ya fada qasa qasa yana boye dariya da muryarsa don bayaso ta jiyoshi. Annin ta jishi sarai,murmushi me sauti ya kubuce mata,saita cira wayar daga kunnenta tana cewa "Ga qaramin yaaya zai baki saqo" Ta aje masa wayar a gabansa taja nata plate din a hankali taci gaba da diban abincinta tana ci tana kuma saurarensu. Idan daru ne tsakanin amna da musaddiq a gidan ba wanda baisan da zamanshi ba. Saidai kuma akwai shaquwa me tsananin qarfi tsakaninsu da ba wanda ya isa ya taba daya a gaban dayan. Wani sabo da 'yan uwantaka ce me zurfi a tsakaninsu wadda tadan sha banban da wadda ke tsakaninsu da FU'AD da kallon UBA kusan sukeyi masa. Tana jin yadda suke fafatawa da yace mata an barwa nanna ita,ya dinga kwasarta yana dariya anni na zaune kawai tana murmushi har sai daya tabata sosai sai ya yanke kiran,daidai sanda farouq ke shigowa falon. Sassanyan matashi,cikamakin barin zuciya ruhi da rayuwar mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources muhammad fuad jadda. Kaman twin brother dinsa fu'ad yadda ake kallonsu kenan,illa banbancin career da kowanne yake dashi.....yana da wani ajiyayyen kyau nutsuwa da haiba. Su biyun kam sun zamewa duniyar 'yammata da yawa jarabawa,ba'a maganar 'yammatan da karansu baikai tsaiko ba.....yammatan da basu da damar nuna yatsa ko tsaiwa a dandamalin da kowacce diya da take ji da gata da kudi zata tsaya......yammatan da saidai su gansu jikik TV mujallu da jaridu da kuma sauran kafafen sadarwa......aah.....wannan fagen na 'YA'YAN GATA ne,yaran da iyayensu da kuma su kansu suka ci suka kuma tayar da kai,yaran da suke da chance 50 to 60 percent na ganinsu,walau a gidajensu ko a guraren ayyukansu,ko tafiya ta hadasu a filin tashi da sauka na jirgin sama a kowacce jaha dake Nigerian,ko kuma su hadun cikin qasashen da aiki ko kuma hutun da sukan tafi dukka family din alhaji HAMZA KIBIYA zuwa wasu daga cikin kebantattun qasashen da sukanyi quri'ar zuwa. Wata irin nutsuwa suke da ita,wanda kwata kwata harkar mata bata gabansu. Har gwara gwara farouq din,akwai wasu banbance banbancen dabi'u da kuma halaye tsakaninsu da fu'ad. Tun asali farouq mutum ne meson comedy ko yaya ne,abinda zai sakashi dariya da nishadi,yanason yaga ya tsokani mutum abinda ya sanyashi yasha wahala qwarai a hannun mariya......sabanin sadiq da yake da tsoro da kuma tsantseni. Saidai dukkansu a yanzun girma ya sauya wasu daga cikin halayensu. Raino na uwa da Allah yayi musu alfarma suka sake samu,sai dukka wannan tsoron na sadiq ya gushe,ya koma tsaiwa da jajircewa akan komai,saidai kuma ua biyo halin fu'ad na matsanancin miskilanci shariya da kuma maida kansa kamar baya fahimtar abinda kake aiwatarwa. Dauke kai da banzatarwa akan abu idan baiso ba,zaman kadaici da rashin son hayaniya ko doguwar magana. Farouq yana nan da halinsa,saidai ya ragu sosai,kusan dukka sakewarsa cikin gidan ne,idan ya fits waje ya koma boss saidai cikin abokai kuma. Shi dinma ya samu abokin tayi wato musaddiq,wanda shine copy dinsa,idan suna a gidan maida anna suke kamar kakarsu,abu daya ne yake bata salama idan fu'ad yana nan,tofa nan daya,sunsan qaryarsu tasha qarya,dole su shafa mata lafiya subar bakinta ya samu salama. A boye musaddiq da sadiq suka fara zuwa zance abinsu. Ba wanda ya sani sai ranar da fu'ad ya fahimta. Da wannan salon hukuncin nasa ya ritsasu a falo,kowanne ya rasa da bakin da zai masa bayani,amma koda anni ta iskesu ana shari'ar goya musu baya tayi "Ba wanda bazai iya riqe mace ba a cikinsu,tunda sama ta kasa,ai bai kamata qasa ta gaza ba" Ta bawa fu'ad amsa. Ya fahimceta sarai,ya kuma fahimci anni dasu take shida farouq......kai tsaye ma idan an tashi shi din za'a ce,don dama farouq din dab yake da bayyana nemansa gasu annin,shi dinne bashi ga tsuntsu bashi ga tarko,bai kuma san ranar da zaiyi tsuntsu ko tarkon ba,don a yanzun baya jin duk yarinyar da yace zaya aura din zai iyayi mata adalci,don a qasan ransa ko digo baya jin marmarin aure,baya ma taba hange ko hasashen gashi da macen auren ko gashi a sunan magidanci......duk da cewa shi kansa shaida ne akan jikinsa yakai geji yakai iyaka ya kuma kai maqurar buqatuwa zuwa ga diya mace......duk da tarin yanayin da yakan tsinci kansa a ciki.....shi kansa yasan kowacce irin lafiya ake da buqata yana da ita,don ba'a maganar cikakkiyar lafiya ma ga mutum ma'abocin motsa jiki. To amma baisan dalili ba.....ko kadan sabgar bata gabanshi,hasalima!,zai.iya cewa bai taba jin soyayyar wata 'ya mace a zuciyarsa ba......bai taba daga idanu ya kalli wata mace yaji ta burgeshi ba......bai taba zama koda da minti daya ba....kaf rayuwarsa tunda ya mallaki hankalinsa wai yayi imagining aure cikin rayuwarsa ba. A yanzu ya sake gina rayuwarsa bayan ginin da yayi mata shi yafi sawa a gaba,aikinsa kasuwancinsa da sana'arsa sune budurwarsa kuma matarsa,baya da wani buri a yanzun illa ya sake zama gwani ta fannin ayyukansa gaba daya. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 45 ________________________ https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX *_assalamu alaikum warahmatullah_* *_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_* *_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_* *_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_* Shadda Laces Atamfa Kayan yara English wears dana jarirai Qawatattun handbags Mayafai Abayas da jallabiyas Inner wears Huluna na maza da mata yara da manya socks Takalma na maza da mata yara da manya Lafayas Sarqoqi agoguna banguls da rings _kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_ _bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_ *_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_* *_masu manyan qarfi da matsakaita?_* *_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_* *_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_* *MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA* *_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_* *_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_* *_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽 __________________________ Yana da matuqar karsashi da qarfin zuciya......da kuma fuskantar dukkan wani goal nashi har sai ya cimmasa ya kaishi qasa. Baya taba bari buri tsoro ko fargaba suyi masa iyaka ko shamaki......faduwa kuma bata sanyashi yayi giving up,wannan shine sirrin nasarar da kullum yake dada samu. Za'a iya cewa kai tsaye farouq hannun damanshi ne,don haka ba wani motsi ko mission nasu da dayan bai ganewa koda bai gayawa daya ba,duk da cewa ma babu boye boye gaba daya a tsakaninsu. Wannan ta sanya farouq ya jima da fuskantar fu'ad,idan magana kake ta aure ko soyayya to kada ma ka fara kiran sunanshi a ciki,domin baya gane komai ta wannan bangaren. Yakan jima yana dubansa cikin mamaki,ya bawa kasuwancinsa lokacinsa da rayuwarsa fiye da komai baya ga familynsa,wato shi sadiq musaddiq anni da abba,kullum lissafinsa da target dinsa moving forward.....moving to the next step. A hankali ya fara zolayarsa don gane gejin yadda idanunsa basa gane kowacce halitta da ake kira da DIYA MACE,sai ya sake karatun nasa da kyau yadda ya kamata,har daga qarshe ranar yakai kusan biyu na dare saman system yana duba wasu sabbin diamond da aka samu nasarar cirowa,yadda zasu sarrafashi da kuma kamfani mafi dacewa da zasu kai. Shi kam har yayi bacci ma kai na biyu ne,ya fito main parlor na sassansu ya sameshi zaune dungurgur saman sofa yana fama da zazzafan coffee don hana idanunsa kamuwa da bacci. Farouq din da mamaki yake kallonsa,saidai baice masa komai ba har sai da yaje fridge ya ciro ruwa me sanyi ya dawo gefansa ya zauna "Sannu bawan kasuwanci" Ya fada cikin gatse,gatsen da bai damu fu'ad ba saima maida idanunsa kan ruwan hannun farouq din da yayi. Har ya dauke idanunsa kamar bazai magana ba cikin dabi'ar nan tasa ta shariya da banzatar da abu,sai kuma ya dawo da dubansa kanshi. "Kana da jarabar son aure.....amma kana kashe kanka da abubuwan banza da wofi.....kana namiji me yake hadaka da kayan zaqi da sanyi?" Yayi masa tambayar fuskarsa a hade yana duban idanunshi. Qaramar dariya farouq din ya saki yana qoqarin bude gorar hannunsa "Kasan me?,nifa bazan iya rayuwar da kakeyi ba,duk wani abu me dadi ka haramtawa kanka ci sai d'ai d'aiku,ka tattaro abubuwan da sam basu da dadi ko dandano a harshe kullum dasu kake mu'amala......yanzu kalla don Allah" Ya fada yana nuna tray din gaban fu'ad da awannin baya kadan ya gama amfani dashi. "Gasashen zaitun.....hadin salad me man zaitoon,shayin ginseng,wolf Berry smoothie.....meye mai dadi a ciki?" Ya fada yana yamutsa fuska. Idanu kawai fu'ad ya zuba masa har yakai qarshen zancan. A nutse ya saki wani qaramin murmushi da bai bayyana ba yana dauke idonsa daga kan farouq "Dukka abinda ka lissafa yanxun kaje kayi binciken amfaninsa ga jiki da lafiya" Ya amsa masa yana jawo wata takarda dake aje a gefansa yana son hadesu waje daya da stapler. Kai ya girgiza yana tabe baki "Wanne amfani zan tsaya dubawa abinda basu da dandano ko kada......kaifa a taqaice ko?,bakasan meye dadi ba kwata kwata wallahi" "Tashi don Allah ka tafi mr ciye ciye karka cikamin kai da bayanai.....kaci gaba da ciye ciyenka yadda kake da hazaqar son kayi aure,auren zai baka amsarka". Dariya ta kubcewa farouq din harda buga qafa tamkar ba dare ba " To mijin aljana.....don dai na tabbatar zaiyi wahala kaidai idan aka kira me ruqiyya yayi maka ruqiyya inajin mata hudu gareka cikin jinsin aljanu". Duk yadda yakai ga pressure dinsa hade rai ko salon miskilancinsa farouq kadai ke saukeshi. Ya addabeshi wasu lokutan har yaji kamar ya makeshi amma ba yadda ya iya dashi,don kaf duniya baya gashi ba wanda yake masa karan tsayen da yake masa irin haka. Ko a yanzun ma sai da yayi silar fitar murmushi daga kyakyawar fuskarsan nan ma'abociyar tsukewa da ba kasafai ta fiya fidda fara'a "Kaga bakina alaikum na huta ai.....don wadannan matan na bil'adama......." Sai kuma yayi shuru ba tare da ya qarasa fade ba. Ba kasafai ya fiya son tona abinda ke danqare a zuciyarsa ba,baisani ba ko Allah ya nufeshi da rahama daya zare son aure ko son mallakar mace kwata kwata daga zuciyarsa ba?. Dan kadan farouq ya kalleshi ta gefan idanu ganin ya dauko magana ya kuma katseta,sai shima yayi shuru kawai bai sake cewa dashi komai ba. Tun daga wannan lokaci idan yaso masa tsiya da shaqiyanci yakan kirashi da mijin aljana. Anni tayi tayi ya daina amma ina,lamarin farouq sai a hankali,mugun shakiyyi ne idan yaso,idan kuma ya sakaka a gaba ka saku kenan......amma kuma tamkar hawainiya yake,idan yaso canzawa zaka rantse da Allah bashi bane matsokanin nan ba. Kusan a tare suka amsa sallamar farouq din "Kana nan dama?" Farouq din ya fada sanda ya qaraso dining din yaja kujera dake tsakiyarsu ya zauna yana tattare long sleeve din shirt din jikinsa sama. "Yana nan sunatayi shi da mutuniyar" Anni ta bashi amsa tana dariya qasa qasa. Baki ya tabe yana bubbude warmer din dake jere kan dining din "Wannan autar taki anni taci kai wallahi.....wai ita an gaya mata zama zamuyita yi da ita a gidan nan?,baka gaya mata gaskiya wallahi" Ya qarasa maganar yana duban fuskar musaddiq cikin salo na harara. Dariyar ta kubcewa musaddiq ya kalleshi da kyau yana daidaita zamansa idonsa akan farouq "Yanzu don Allah BB(big brother suke masa abbreviation),so kake ayita kada mata hanjin ciki?,duka duka amna nawa take?" "Allaaaaahu akhbar.....kaga masuyi don Allah,dama kana cikin masu lalatata a gidan nan......don Allah kayita gaya mata damu zata rayu.....Allah ka sakata ne kawai a keken bera......itafa har yanxu bata da hankali na lura......na godewa abba ma da yace sai taje ta raka nanna......tafiya duka duka sati biyu kawai amma ta cika mutane da qorafin yhan yhan yhan......itafa gida zata dawo waye ya mutu waye ya tashi.....shi kuma wancan mijin aljanar yana can yana sake daure mata qarqashi...." "Farouq?" Anni ta tsaidashi tana dubansa "Sunan nan bazai fita a bakinka ba ko?" Ta sake jefa masa tambayar tana dubansa. Gyara zamansa yayi yana wani tsuke gira,shi ala dole yana son zama serous. "Allah dai ya bada haquri anni......amma shima ai anni ba sunan da yafi dacewa dashi sai wannan.....banga alamar lafiyarsa qalau ba" Ya qarasa fada qasa yana fara serving kanshi da abincin da yafi so. Idanu anni kawai ta tsura masa tana kallonsa ba tare da tace komai ba,ita kanta yadda fu'ad keyi da lamarin yana tabata,ko a fuska ko kuma a aikace bai taba damuwa da ganin dukansu su ukun suna shirin yin aure ne su barshi ba,yana shiga dashi akayi dukka maganganun da zaayi da iyayen yara,amma shi yana zaune ba wani damuwa a gabanshi,saima lissafin yadda zaici gaba da juya kwabo ta koma dari. "Kaga MAN.....ka koma gaya mata gaskiya,aurar da ita zamuyi da wurwuri.....ba zancan yin PHD a gidan nan.....munason ganin jikokin 'yar uwarmu mace". Daga anni har musaddiq ba wanda farouq din bai bawa dariya ba ganin yadda yayi maganar da gasken gaske har yana tabo hannun musaddiq din don ya jishi da kyau,ya kuma basar ya soma cin abincinsa. Na anni kawai idanu,tana tsarkake girman ubangiji da yadda yake halittar bayinsa da mabanbantan dabi'u da kuma halaye. Yara hudu,mace cikon ta biyar amma kowanne da nasa halin da dabi'ar. Ta sauke boyayyar ajiyar zuciya kunnuwanta suna sauraren hirarrakinsu. Bahaushe yayi gaskiya da yake cewa DA D'A DA DUKIYA BA'A YI MUSU MUGUNTA,DON BA'ASAN ME MORARSU BA SAI ALLAH. tana tuna wani lokaci can baya.....shekaru da suka shude,sanda ta tsoma qafafunta da sunan kome gidan tsohon mijinta alhaji hamza. Yadda tasha baqar wuya kafin ta daidaita lamuran gidan ta kuma maida kowa cikin hayyacinsa. Me babban suna tafi shan wuya akansa akan kowa,tasha gwagwarmaya kafin ta samu nasarar cire wannan fushin baqin rai da kuma mummunan fenti da ya yiwa kusan kowa da yake kewaye dashi idan ka dauke 'yan gidan nasu. Rashin yarda da rashin sakewa da jama'a wanda har yanzu tana fuskantar ragowa da kuma tasirin wannan dabi'ar tattare dashi da bata gama barin jikinss ba. Wani irin yanayi me ban tausayi da har yaso taba karatunshi.....boyayyen kuka duk dare da rashin bacci. Ta dauki dogon zango cikin musu addu'a da neman daidaitar rayuwarsu. Tofi rubutu da addu'a dukka kafin lamuransa su fara daidaita. Sai ta fuskanci kyara tsangwama ga duk macen da zata dososhi koda qanqanuwar yarinya ce. Bata fuskanci yadda abun yayi musu!mugun tasiri ba sai bayan wasu shakaru data haifa musu Aminatu amna me sunanta kenan.....haihuwar data tabbatar matsanancin rabo ne,don ko a wasa bata taba tunanin wai zata sake wata aba wai ita haihuwa ba. Da fari tsakaninsa da amna idanu ne kawai,baya ma zama.inda take bare daukarta,ta fahimci kaman wata kakkaifar gaba ce tsakaninsa da jinsin mata,ita kadaice mace cikin miliyoyin mata da take samun kulawa da qauna daga gareshi wanda ita dinma sai da suka debi shekaru yana dari dari da ita. Bata tsananta tuhuma ba,tasan incident din daya faru dashi a baya akan mariya da mariya sune suke hunting dinsa. Wannan abun bai karye ba tsakaninsa da amna din har sai sanda ta fara laulayin haqori. Kashin haqori matsananci daya sanya mata amai da zawo da yaso wucewa da rayuwarta. A ranar a kuma daren har sun fidda rai da ita,tayi wani suma a hannunsa. A ranar taga gigicewa mai tsanani a tattare dashi,shi daya ne yake da qwarin gwiwar daya dinga mata wasu abubuwa don dawo da mumfashinta,sai gashi cikin ikon Allah ta dawo. Tun daga wannan ranar kulawarsa a kanta ya zama na dabanne,sabo ya shiga tsakaninsu,ta tashi ta ganshi a matsayin yaya kuma uban da bata da kamarshi. "Kamar akwai inda zakaje ko?" Anni ta tambayi musaddiq da suke hira da farouq *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 46 ____________________________ https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX *_assalamu alaikum warahmatullah_* *_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_* *_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_* *_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_* Shadda Laces Atamfa Kayan yara English wears dana jarirai Qawatattun handbags Mayafai Abayas da jallabiyas Inner wears Huluna na maza da mata yara da manya socks Takalma na maza da mata yara da manya Lafayas Sarqoqi agoguna banguls da rings _kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_ _bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_ *_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_* *_masu manyan qarfi da matsakaita?_* *_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_* *_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_* *MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA* *_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_* *_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_* *_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽 _____________________________ Tana tsareshi da ido. Duba daya ya yiwa annin ya fahimci tambayar ta yita ne kawai bawai don tana son sanin amsa daga bakinsa bane....aah,ta yita ne don tanason tunasar dashi wani abu "Kamar zan fita din......amma kuma banason fitar" Ya fada yana kallon qatoton agogon dake manne a bango. "Amma dai ina fata kana sane da girman umarnin uwa ko?,sannan kana sane da girman alqawari......haka kuma uwa uba baka manta dashi ba?" Dukka jikinsa ne yayi sanyi,sai yadan sadda kansa qasa kadan. Lallai ba shakka inda ace dukka iyaye haka suke tamkar anni da zaiyi wuya.....za'a tirza,hakanan za'a sha fama kafin a samu baragurbin yara cikin al'umma. Kai ya jinjina,sai ya soma ture plate din gabansa,ya dauki wayarsa ya sanya gaban aljihunsa ya miqe yana fadin "Sai na dawo" "Allah ya kiyaye......" Anni ta bashi amsa tana satar kallonsa. Tako ta ina ba alamun jin dadin zuwan da zaiyin,ba wani sukuni walawala ko farinciki irin na da a sanda zai hadu da iyayensa. Da kallon tausayi ta bishi dashi har ya bacewa ganinta. Ta janye idanunta tana sauke zazzafar ajiyar zuciya,sai suka hada idanu da farouq dake zaune yana cin abinci a hankali. "Daga musaddiq har muhammad tausayi suke bani har yanzu,har yanzu wannan tabon da aka barwa rayuwarsu yana tare dasu bai goge ba". Kai farouq ke gyadawa yana duban anni "Gaskiya kika fada anni......musaddiq nashi me sauqi ne,ba wanda abun ya yiwa illa matuqa yake kuma taba halayensa da dabi'unshi har yanzu irin fu'ad......akwai fushi saurin daukan zafi da yawa cikin halayensa......shariya rashin son yin magana ko hira da kowa,wanda yawancin lokuta idan irin hakan ta faru nasan abinne ya motsa masa,shi yasa sau da dama nake maida kaina wani iri a wajensa saboda na sama masa farinciki duk qanqantarsa". Kai kawai anni ke jinjinawa,har cikin zuciyarta tana jin ba dadi,abun kuma yana tabata. Wani gauron numfashi ta sauke tana ajiye wayarta data dauko wadda ta kasa juriya tana shirin kiranshi kenan. Kacokam ta aza idanunta ga bakin qofa tana tsumayin qarasa shigowarsa tana jin yadda yake gaisawa da ma'aikatan gidan faran faran. Irin sakewa da ta tabbata idan ya shigo ciki baya iya irinta da ita. Da sallama ta yaye kakkauran curtain din dake bakin qofar ya shigo. Ganinsa kawai da tayi,zuciyarta kuma na ayyana mata cewa wannan din d'anta ne halak malak sai taji wata izza ta sake daduwa cikin kanta "Kina da wannan kadarar.....kina da wannan damar don me yasa zaki bari a qwace miki su cikin sauqi haka?" Ta yiwa kanta da kanta wannan tambayar. Gyara zamanta tayi sosai sanda ya iso ciki,ya zauna saman daya daga cikin kujerun yana dan tsagaita dubansa daga inda take "Barka da dare" Ya furta a nutse,har yanzun baya jin wani sabo shaquwa ko soyayya nata a tattare dashi,yana jinta kamar kowacce baquwa......yana kuma jinta kamar kowanne baqon abu na rayuwarsu. Qoqarin wadata fuskarta da fara'a tayi kaman yadda zuwaira ta shawarceta don samun isa ga burika da muradanta cikin sauqi "Ai na cire tsammani da zuwanka musaddiq......wai dama haka duniya take?,......na zaci komai girman laifin uwa d'a yana iya yafeshi ko?" Ta fada murya a sanyaye. Idanunsa kadan ya daga yana kallonta,ya kasa gamsuwa da ita har yanzu,yana jin inama ace yadda ta furta wadannan kalaman a bakinta haka suke har cikin zuciyarta?. "Kibar wannan maganar maamah,abune daya riga ya shude,kin wuni lafiya?" Ya maida maganar da tambayar lafiyarta "Alhamdulillah.....saidai yayanka ya watsar dani musaddiq,ya barni cikin buqatar rayuwa da abubuwan da a zahiri ya cancanci ace nafi qarfinsu amma suna neman fin qarfina" Ta fada a karye. Mamaki sosai ya sake lullubeshi har ya gaza jurewa sai daya daga idanunsa ya qarewa suturar jikinta da kuma falon da take ciki kallo. Tana cikin ni'ima da wadatar da babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa amma tana kiran abubuwa da dama sunfi qarfinta?. Anya kuwa da kyakkyawa da kuma tsakakkiyar zuciya ta dawo cikin rayuwarsu?,anya wannan tsohon maqalallen halin baya tare da ita?. Shine mutum na farkon da yafi kowa sanin cewa hammansa baya wasa da ci sutura sha muhallinta da lafiyarta,bayan ya dauke duka wannan kuma da wani ajiyayyen salary na dubu dari duk wata,duk da aqa'ida ba wata qwaqwarar buqata guda daya da ashekarunta ta yima rayuwarta saura. Hatta da man fetur da ake zubawa motocinta guda biyu bai daukewa kansa ba,to me take nema sama da wannan cikin dukiyar da aka sameta a sanda ta nisancesu?,cikin dukiyar da aka sameta a sanda ta gujesu?,cikin dukiyar da aka sameta a sanda take can cikin duniya tana kalar rayuwar data zaba?,kalar rayuwar data fifita sama da ta rayu dasu?. "Bana jin akwai sauran abinda hamma ya rageki dashi maamah" Ya gaza jurewa sai daya fadi mata idanunshi tsar a kanta zuciyarsa kuma cike da mamakin furucinta. Idonta itama takai kansa tana kallonsa "Yanzu a naka tunanin a matsayina na mahaifiyar mutumin da ya mallaki kamfanin sarrafa diamond......mutumin da yake da harqalla da manyan kamfanoni da suke a qasashen waje.....qasashen wajenma manyan qasashen da suka tumbatsa ta fannin tattalin arziqi da qarfin mulki da iko.....mutumin da yake noma kaso mafi tsoka na dukka abincin da Nigerian dama Africa gaba daya suke ciyar da al'ummarsu amma ace abinda zai iya cira ya bani na zallar kudi shine dubu dari?" Ta aje masa tambayar ranta yana fara mata zafi amma tana danneshi. Ci gaba yayi da kallonta yana fahimtar abubuwa da dama tattare da ita,a yau kuma a yanzun sai yaji shima ya shirya tambayarta "Idan har ya miki kadan kuma hamma bai kyauta ba......wacce buqata kike da ita da zakiyi da kudi?" Tambayar sak irin ta dan uwansa kenan......amsar kuma da ba zasu taba samunta a bakinta har abada "Musaddiq......yanzu bayan ci sha sutura da biyan duka sauran buqatu da zasu taso Shikenan iya abinda nake da buqata a matsayina na 'yar adam?,bayan ina da d'an da a kullum idan zai bani kyautar million daya bazaiji komai ba a jikinsa daga abinda ya mallaka?" "Maamah......kin taba zuwa da wata buqata kinaso ayi miki kaza?,ko a yiwa wane kaza wanda ba zallar kudi zaki amsa ba da hamma ya taba qinyi miki?" Ya jefa matar tambayar yanason gane ainihin gaskiyar da takeson lullubewa "Kai musaddiq.....kalleni nan......dukkanku ke da fu'ad nina haifa abuna......banyi lalacewar da don zaku yimin wani abu sai na zama tamkar almajira a wajenku ba....." "Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki" Ya fada kawai don kawo qarshen zancan. Can qasan zuciyarsa babu gasgatawa ko yarda da ita ko kadan. Idan yayi rantsuwa ko kaffara bazaiyi ba,ba haka siddan hammansa yaqi yarda ya sakewa maamah tsurar kudi ba,ya yadda dashi dari bisa dari,yana komai bisa bayyananniyar hujja da kuma dalilai. Kawai dai mutum ne shi me tsananin zurfin ciki da miskilanci,wannan ya sanya idan ya aiwatar da abu babu lallai ka fahimci don me yayin?,kuma bazai taba zama yayi maka wani bayani ba game da hakan. Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna,tanata qoqarin controlling kanta don har yanzu bata kai ga cimma burinta na abinda takeson taji ba. Ta furzar da iska kadan sannan ta fara kiran daya daga cikin masu aikinta. Kamar ko yaushe da sassarfa ta iso saboda tsoro da gudun sabawa umarninta. "Ki sauke kayan abincin nan a nan....ko dining din zaka hau kaci?" Ta tambayeshi tana dubansa. A zahirance so yake ya gaya mata ya qoshi,baya buqatar cin komai,amma ya tabbata fadin ba abinda zai haifar sai wani rigima da tashin hankalin,don haka yadan gyara zamansa "Ta kawo nan din" Sai ta juya ta watsa mata kallo "Kinji ai abinda yace". Suna zaune ta dinga sauke kwanukan abincin. Warms na alfarma masu tsananin tsadar da ko a gidajen masu sukuni sai wane da wane. Da kanta maamah din tayi serving nasa don buqatarta shine ya saki jiki yaci sosai ta yadda zata samu daman yin magana dashi ta kuma samu duka information din da takeso. "Bismillah sauko" Ta fada da salon bada umarni nakai tsaye. Bai musa mata ba ya zamo ya sauko din,sai ya fara kai hannunsa ya dauki glass cup na lemo yana juyashi a hannunsa. Spoon ta dauko ta qara a plate din,ta kalleshi da murmushi "Muci tare ko?" Kai ya gyada kawai yana duban kwanon. Komai yayi masa banbarakwai. Ko a shekarun baya da suke da qananun shekaru ya iya abinda qwaqwalwarsa zata iya riqewa baya jin sun taba zama kwano daya,sai yanzun da ya zama cikakken mutum?. Ko a baya sanda bai kammala iya cin abinci ba idan ta zuba musu ta tura musu ta shiga sabgar gabanta hamma ne ke zama ya bashi komai zafinsa har sai ya qoshi. Hira take sako masa a hankali a hankali,tana cin abincin yana juya cokalin kawai a ciki bayan ya dire cup din lemon. Sai bayan data soma karantar kamar sakin jiki tattare dashi sannan ta aje nata spoon din tana dubansa cikin murmushi "Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 47 "Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta kanka da kalar sana'arsa ka maida kanka baya ta hayar sanya jikinka a al'amura ta harkar gona?,bayan sana'ar ba taka bace,gadon gidan Alhaji hamza kibiya dinne zasu daukeka su cusa ka?,sannan su raba dansu da fu'ad kai su tsigeka daga gareshi?,wanne irin ragon azanci ne wannan shirme da shashanci?,sannan wannan kadai ya isa ya nuna akwai mummunar manufa da qulli cikin zuciyar amina da manufa aka shirya wannan". Maganganunta sunyi masa girma qwarai,mamaki kuma ya lullubeshi har sai daya tsaya kawai yana duban yadda maamah din ta haqiqice. ".....bazan yarda ba a rabamin kan yarana,bayan a mahaifa guda suka kwanta......don wannan zalunci ne kawai,duk yadda zakayi ka nema komawa sashen da dan uwanka yake aiki,shima kuma zan masa magana kaji?" Sai ta qarashe kuma cikin kwantar da harshe saboda magana ta gaba da takeson yi. "To" Kawai ya iya cewa da ita,ya sani basai an gaya masa ba,maamah din tayi nisan da batajin kira,hakanan dukkan wani bayani da zaice zaiyi mata yana zaman bata lokaci ne kawai a wajenta. "Yanzu bayan kamfanin diamond ai ina sanya ran zuwa yanzu addu'ata ta cicciba Muhammad izuwa mallakar wasu boyayyun mafanunnukan ko?" Ta fada tana murmushi tare da tsare musaddiq da kallo. Dubanta yayi sosai,yana ji har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa bai gamsu xa yanayin tambayar tata ba,don haka girgiza mata kai kawai yayi "Bansan komai a kanshi ba maamah tunda ba sashe daya muke dashi ba" Wani abu ne ya tsaya mata a wuya,amma sai tayi qarfin halin danneshi ta amsa masa da "Haka ne......amma dai baka ce bakasan qarfi da nauyin kudaden da suke shigo masa ba ko?" Sake daga kai yayi yana dubanta zarginsa yana sake tabbata "Bana ce ba maamah.....abune da ya shafi sirrinsa kuma ba a qarqashinsa nake aiki ba.....ni ina qarqashin farouq" "Eh to.....maganar gaskiya sai yanzu na fahimci kimiyyar da ta sanya amina tayi kutin kutin din cusa danta wa Muhammed kai kuma ta rabaka dashi.....kana jininsa wanda bashi da na biyunsa a duniya amma bakasan komai nasa ba?.....wanda ni nayi imanin a yanzun inda zan zaunar da shi saddiqun nayi masa ire iren tambayoyin da nayi maka din yana da amsar kowacce fes?.....wannan itace hanya mafi sauqi da zata samu salwantar da fu'ad da dukka abinda ma ya mallaka". Idanunsa ya runtse yana jin zafin mummunan zaton da maamah din ke jifar 'yar tahalikar dashi.....matar data zame musu bango majingina,matar data zabi farincikinsu akan nata.....matar da silarta ne a yau suka zama dukkan abinda suka zama din.....suka kawo izuwa matakin da suke kai a yanzu......matar da banda ita da yanzu shi da muhammad din duka da take taqama dashi ba'asan a wacce shiyya nahiya ko yanayi suke ba. "Maamah..." Ya fada yana bude idanunsa a kanta ba tare da ya shirya tsaida maganarta ba. "Duk yadda kike tunanin anni fa ba haka take ba.....idan baki godewa anni ba bai cancanci ki jefeta da mugayen zato ba......kamfanin nan da rayukanki suke baci akai asalin diamond din da aka samu ba hamma bane kawai ya sameshi ba.....a lokacin suna tare da BB farouq......" "Amma shi ya haqo shi kuma ya samu nasarar tsira dashi.......ka dauka bansan dukka wannan ba?" Tayi maganar tana tsareshi da idanunta da suka cika da bacin rai. Lallai sai sun nuna mata fifikon matar can akanta?,bayan bata da masaniya akan sanda ta dauki cikinsu bare kuma haihuwarsu?. "Eh hakane.....amma shi BB farouq baida sha'awar harkar diamond noma yafi so shi yasa......" ".......shi yasa aka fidda haqqinsa aka bashi nasa kason......dukiya ta zama ta muhammad sh kadai......amma duk da haka basu qyaleshi yana amfana da abarsa shi kadai ba.....saboda nasa kason da nasa bangaren na haqar ma'adanai yafi noma albarka da kawo samu,shi yasa suka tattare shi suka kuma dora masa dukan lalurarsu suna zuqeshi sannu a hankali.....suka kuma nesantaka dashi.....suka haramta maka sanin komai daya shafeshi ta cusa danta" Ta qarashe maganar da wani irin ciwo da emotiona daga zuciyarta "Maamah....." Ya kira sunanta yana son dakatar da ita. Baya qaunar ko kadan wadannan kalaman marasa dadin sauraro suna fita daga bakinta zuwa kawunan mutanen da suka yiwa rayuwarsu tsaiwar da babu wani mahaluki daya taba yinta "Ni na zabi fannin noma da kayan abinci......basu suka sani ba....ba wanda ya bani shawara....." "Musaddiq!.....ina fada kana fada duk akan mutanen can?,to waishin ko zaka koma cikin aminatu ta sake haifarka a matsayin danta bani mariya ba?". Maganar yaji tayi tsauri da yawa,kuma ya sani uwa uwa ce komai lalacewarta,hakanan ba'a canzawa tuwo suna,don haka ya miqe tsam,don dama a qagare yake da wannan zaman da baiga ma'anarsa ko alfanunsa ba. Ya dauka zasuyi hira ne irin ta d'a da uwa?,ya dauke zata tambayeshi bayan ta barsu yaya suka rayu?,ya dauka zata nuna nadaman barinsu da tayi sun basu gama zama mutane ba?,sai gashi gaba daya hasashenta da hangenta ba'a nan yake ba?,da gaske ne abinda zuciyarsa take raya masa ta biyo DAUKAKARSU DA DUKIYARSU NE?. "Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki,sai da safe.....na barki lafiya" Ya fada yana juyawa a hankali yana fita daga falon zuwa farfajiyar gidan. Da kallon takaici ta bishi,shi kansa me sukuni da wadata ne wanda zai iya kashe mata ko nawa take buqata ballanta a gangaro kan muhammad,mahaukatan kudade ke shigo musu daga harkar noma kayan abinci da sauran kayan masarufi da sukeyi,kuma su rabasu cikin qasashen Africa dama qasashen qetare. Tana da dukka information daidai gwargwado a kansu.....amma sai gashi wadatar kowannensu yanason zame mata hoto. Yadda ranta yake a bace sai zama ya gagareta,takai ta kawo kusan sau uku tana ji har cikin zuciyarta ya dace ta gaggauta daukan mataki,ya kamata tayi wani abu akai kada komai yaci gaba da tafiya a haka. Daidai sanda takai dab da qofar taji horn na mota da kuma shigowarta farfajiyar gidan,bata bi takai ba amma zuciyarta tana mamakin baqon daren da sukayi. Mintina uku kawai tayi sallama cikin falon. Sallamar data sanya maamah din waiwayowa tana amsa mata fuskarta babu walwala. Sanye take cikin wani lafiyayyen lace ruwan zuma. Kallo daya tak zakasan cewa ba na qananun mata bane,ba kuma qananun kudi aka sanya aka mallakeshi ba haka dinkin boubou din da aka zuba masan. Zagayayyen dauri ne saman kanta da zai gwada maka adadin wayewarta da kuma zurfinta a sanin data yiwa duniya. Mayafinta na yafe a kafada daya,daga hannayenta har zuwa wuyanta adon sarqa zobe da bangles ne da babu ko tantama da shakka na gold dinne. Ita din idan ka kalleta baifi ka bata shekaru arba'in da biyar ba,saidai kuma ta dara hakan,don a yansu tana dosar cika shekaru sittin ne a duniya. Daga bayanta wata macece wadda duka ba zata haura shekara arba'in ba. Riqe da wata kyakkyawar handbag wadda babu ko tantama jakar matar dake gaba ne saboda dacewa matuqa da tayi da kayan jikinta. Maimaita sallamar tayi a karo na biyu tana duban maamah fuskarta a sake. Wannan ya sanya maamah din tayi qoqarin sakin tata fuskar gami da sakaya damuwarta a gefe,cikin mamaki da tarba me kyau ta matsa gareta tana tararta "Hajiya......isowar yaushe?" Ta tambayeta tana murmushi "Tun shekaran jiya fa?,gajiya nayi ma na gudo,amma ason dan ahalan sai farkon sabon wata zamu dawo" Ta furta tana neman wajen zama. Zaman itama tayi a kujerar dake fuskantar tata "Da kyau.....ai ya kyauta wallahi,ko yanzu aikin huta ko?" "Yadda ya kamata kuwa.....wai nikam musaddiq nake gani yana fita sanda nake shigowa da mota?". Dan tabe baki kadan maamah din tayi sannan ta amsa cikin salon rashin bawa maganar muhimmanci "Shine mana" "Hala bai ganeni ba,don baiyimin magana ba" "Ko ya ganekin ma babu lallai ya miki magana ai harira" Ta amsa mata boyayyar damuwar fuskarta tana bayyanar da kanta. Kallon tsanaki hajiyar mamallakiyar sunan harira ta yiwa maamah kafin tace "Ban gane me kike fada ba mariya" Qarasa bawa sauran boyayyar damuwarta qofa tayi ta fallasa kanta,don tambayar sa harira tayi mata ta zama tamkar susa ce tayi mata akan ciwonta "Ina da damuwa harira.....ina da damuwar da har kwanan gobe na gaza gano maganinta". A nutse hajja harira ta waiwaya ta dubi 'yar aikinta,wadda ke tsaye daga gefe,tunda suka shigo taketa faman gaida maamah din amma bata ma jita ba bare ta amsa " Ajiyemin jakar ki fita daga waje ki jirani" Ta fadi mata. A ladabce ta ajiye jakar sannan ta juya da hanzari tana ficewa,abinda ya bawa hajja harira damar maido hankalinta ga maamah "Nayi tunanin kawo yanzu kinyi nisa daga dukkan wani abu me suna damuwa daga randa dan cikinki ya zama mamallakin kamfanin diamondchore?" "Daga sannan sabuwar damuwa ta fara hajja harira" Maamah din ta furta ranta yana matuqar quna "Idan na kalli yadda kike fantamawa hajja sai na sake tabbatarwa kaina lallai akwai aiki a gabana......aikin kuwa shine YADDA ZAN MALLAKE 'YA'YANA". Wani irin duba hajja hariran take mata,sai kuma ta kyabe baki "Keda wanne baccin kikeyi da baki aikata hakan ba mariya?,wanne gangancin ya kaiki?,bakisan daga ranar da Allah ya yiwa 'ya'yanki arziqi ba.....akwai tarin mutane da dama da suke marmarin juye matsayinki su haye kai ba?.......kin ganni nan mariya?,kaf 'ya'yana babu wanda ya isa ya aiwatar da wani abu komai girmansa kuma komai qanqantarsa ba tare da sanina ko yardara ko sahalewata ba.....ke koda matansu ko 'ya'yansu zasu yiwa kuwa sai da sanina da yardaya,a cikinsu babu wani gida da bansan me yake gudana a cikinsa ba 24hrs......yanzu haka katafaren gini na sanya sukeyi na bai daya duka zamu zamana a muhalli guda....." Kai kawai maamh ke gyadawa,a yau ta yarda ta miqa wuya ta kumayi surrender kan cewa harira ta fita shu'umanci,iya yadda tae bada.labarin cike da izza da alfahari kawai ya isa gaya maka gaskiyar haqiqanin zahirin abinda ke faruwa kenan......jikinta ya isa ya sake qarfafa maka zancanta.....tsanin alfahari da takeyi yayin bada labarin kuma zai gaya maka yadda take jin dadin yadda take tafi da rayuwarta. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 48 "Inaso na zama uwa mafi gata a duniya harira,inason na zama uwa mafi izza akan yaranta......inason na zama uwa mafi zama abar alfahari abar nunawa a duniya....inason 'ya'yana su dawo qarqashina.....na mulkesu kaman yadda ubangida yake mulkar bawansa......su zamana a tafin hannuna kamar yadda jariri sabuwar haihuwa yake zama a hannun mahaifiyarsa". Wani murmushi hajja harira ta saki tana duban maamah "Lallai mariya burinki me girma ne......amma dai kinsan ki baro kari tun ran tubani ko?,ko mu da muka raini yaran har suka girma muka aurar dasu,bamu gusa ko nan da can ba muna gabansu suna gabanmu sabunta ayyukanmu mukeyi akai akai.......munayi matansu sunayi,wanda keda nasara shike samun rinjaye.....ballantana ke,yaranki ina da tabbacin suna buqatar gagarumin aiki kafin samun saituwarsu akan bigiren da kikeso". "Abinda ya wuce ya wuce hajja harira.....yanzu meye abinyi?" Gyara zamanta tayi sosai tana bawa maamah dukkan hankali da nutsuwarta "Akwai plans guda biyu,plan A da plan B......idan A baiyi aiki ba zamu wuce zuwa na biyu" "Kamar?" Ta tambayeta cikin matsuwa da jin bayanin komai "Yauwa......na farko akwai wajen mutumina da zan kaiki wanda shi yakemin aiki akan komai da kowa......" "Kai....kai.....amma kin gama min komai" Maamah ta fada tana gyara zamanta da kyau fuskarta na washewa da madaukakiyar fara'a,saboda ta hangi zuwan nasararta a nan kurkusa......ta hangeta tana fantamawa fiye da yadda hajja harira ke fantamawa din. "Ba komai fa.....zaman tare ai ba qarya bane....zaki zayyane masa dukkan abinda kike da buqata wanda nake da imani a kansa mallaka sai yadda kika juyasu.....akan mansur ya fara yimin aiki,lokacin da yayi aure sai na fuskanci wani abu,maganata qasa take da maganar matarsa,dukkan umarni da zabi nata ne sai abinda taga dama sai kuma abinda tace.....a sannan na farga,amma in gaya miki inayi yarinyar nan tana nata har daga qarshe na hadu da DAN DUMA....tuni na saka ya qara mata wuta a gidan,mansur ya saketa tayi gaba,tun daga ranar dukkan wanda zaiyi aure a cikinsu nice nake zaba masa yarinyar da nakeso ya aura din,wadda zan cimma buqatuna ta hanyarta,wadda zan juyata ba musu ba kuma damuwa......to kema wannan shine plan B dinki idan na farko yaqi aiki" Shuru maamah tayi tana jinjina kai,lallai duk iya yadda take ganin mulki da isa da kuma izzar hajja harira ta wuce nan. Wannan shine cikakken ma'anar HAMSHAQIYAR UWA ko kuma CIKAKKIYAR UWA. Idan so samu ne tana son kamar haka ko sama da haka "Amma banajin musaddiq zai qara watanni shida ba tare da yayi aure ba" "Ko yau yau zaa daura auren kina iya ruguzawa,ki maye gurbinta da wadda kikeso" Ta fada kanta tsaye cikin confidence. "Waye babbar damuwarki a cikinsu?,muhammadu?" Kai ta jinjina. Tafi damuwa da kamashi a hannu fiye da musaddiq. Tasan waye fuad din,yana da tsauri da tsananin da ita kanta tayi imanin mafi rinjayen aikin a kansa zaa gabatar "To ki manta da batun musaddiq me sauqi ne" "Haka ne wannan" Ta fada tana murmushi,tana jin cewa qarshen matsalarta yaxo,tana jin cewa lokaci yayi da zata cika muradanta "Yaushe zamu tafi zuwa wajen DAN DUMA?,kinsan ba'a bori da sanyin jiki" Ta karkata tambayarta ga hajja hariran cikin zumudi da farinciki,tana jin bacin ranta yana zagwanyewa. Tunda suka fito daga wajen a cikin jikinta kawai takejinta uncomfortable. Haka kawai take jin kamar akwai wani abu,tayi dukkan research da idanunta hankali da kuma tunani bata ga wulgin kowa ba,hakanan bataga alamun ana bibiyarsu ko wani abu da yayi kama da hakan ba. Saidai har suka soma nisa da wajen bata samu nutsuwa ba,abinda muddin ta soma jinsa a jikinta zaiyi wahala idan baby afkuwar wata matsalar. "Me napep idan zaiyuwu ka kaini madabo.....zan qara maka wani abun" Tacewa me abun hawan. Malam ne yaketa fado mata a rai,dattijo kuma kamilallen mutumin,ma'abocin nutsuwa karamci da kuma ilimin addini. Asalin haduwarsu ta fara ne a ranar da zasu rabu da ameen,daya daga cikin mazan da suka taba shiga rayuwarta dama tarihinta. Abun yaso ya kwabe mata har ameen din yaso fahimtar ainihin wace ita ba tare da takai ga fita daga layin ba. Ya sanya aka biyo sahunta tiqa tiqan qattin dake gadin qofar gidan nashi harda rakiyar karensu guda daya. Malam din shi ya musu kaca kaca,ya kuma hada harda ameen din daya tako da kansa,ya nuna masa daraja da martabar mace,sunaji suna gani yayi saving nata a hannunsu ya wuce da ita sukaci gaba da takawa a qafa har titi. Ita dinma a hanya bai qyaleta ba,ya dinga yi mata fada bawai don ya fahimci wacece ita ba?,ko ya fahimci ainihin abinda ya hadosu. Donme tana diya mace zata bari takai gefin magriba a irin wannan unguwannin?. Haka kawai taji ranta ya nutsu da dattakonsa da kuma addininsa,rana ta farko da wani ya taba yi mata fada irin wannan tun bayan shudewar iyayenta. A daren ranar tayi kuka tayi kuka,kukan kuma kukan dadi ne na yadda yau aka samu mutum qwaya daya daya tsaidata da zuciya daya yana mata fada kanshi tsaye. Tun daga wannan ranar malam din ya zame mata daya daga cikin mutanen da suke da martaba a idanunta. A duk lokacin da kudi suka samu takan dauki wani abu tayi tattaki taje ta gaidashi,ta kuma bayar wa almajiransa tace ayi ma iyayenta da suka rasu sadaka. Matarsa tana da matuqar kirkin da ta dauketa kamar diya kaman yadda malam ya dauketa diya a wajensa. Duk sanda zataje gidan bata gaza fahimtar wasu abubuwa daga sabreen. Macace mai matuqar hikimar da sai da takai daga qarshe ta karanci wace sabreen din,sai ya zamana itama bata fiya boyewa inna komai ba muddin ta tambayeta din,gidan sai yake zame mata wajen samun nutsuwa a wadansu lokutan. Unguwar madabo,daya daga cikin tsaffin unguwanni dake birnin kano,wadda take da dadadden tarihi. Hakanan ta tara malamai da masana addini masu yawan gaske. Tsukukun loko ne da ko adaidata sahun a matse yake shiga,wannan ya sanyata ta nemi ya ajiyesu daga bakin babban lokon da zaka karya ka shiga qaramin. Ta bude jakarta ta sallameshi,sannan suka fara takawa ita dasu zuwa ciki. Tun a rumfar dake qofar gidan ta tabbatar malam baya nan,don babu tabarmin karatu,hakanan daliban nasa sai jifa jifa kowa yana sabgar gabansa,don haka kai tsaye suka wuce zuwa ainihin cikin gidan. Da sallama a bakinta suka kutsa kai,gidan yana nan kamar kullum cike da tsafta. Ba kowa a filin gidan sai hayaqi dake fitowa daga kitchen da alamu ana gab da kammala tuwon dare. Yaransu bakwai da malam,maza hudu mata uku kuma dukkansu sun aurar dasu,don haka inna ce kadai ke rayuwa cikin gidan,sai babbar jikarta da aka kawo mata don ta tayata zama. Sake sallamar tayi,kusan lokaci daya aka amsa mata daga kitchen din da kuma rumfar dakin inna. Cikin qasa da second daya wadda ke kitchen din ta fito. Matashiya ce da duka duka bata wuce sa'ar huda ba,murmushi sosai take saki,ta baro cikin kitchen din tana goge hawayen fuskarta da hayaqi ya sanya mata tana takowa "Adda sabreen.....kece yau a gari?" Miskilin murmushin nan nata ta saki "Inji maqi baqo ko rumasa'u?" Sai ta saki 'yar dariya tana kamo haneefa "Muje yau inna taga su auta,tanata zancanku tace kwana biyu shuru,gashi batasan muhallinku ba bare ta binciki ko lafiya?,layinki Kuma kwata kwata baya shiga" Ta qarasa maganar tana riqe da hannun haneefa wanda tuni sukayi gaba zuwa dakin innar. Sai a sannan da rumasa'u tayi zancan layinta baya shiga ma ta tuna yana daya daga cikin layukanta da suka tafi hutu,sai ta taka a hankali tana bin bayansu zuwa ainihin falon innar. Dare dare ta samu haneefa gefan cinyar inna. A duniya gidan yana daga cikin gidan dasu haneefa din keson azo,don sai ya kasance musu kamar wani gida daya qwaya tak na 'yan uwansu da suke iya ziyarta su kuma sake,sakewar da basa iyayinta cikin ainihin gidan mahaifinsu. Da murmushin tambayar da taji innar na yiwa haneefa ta qarasa shigowa ciki "Wa'alaikumussslam.... .ina nan ina tuhumar amaryata me takeci naga tana ta tsaho?,kunyi nisan zango wannan karon AMEENATU(real name dinta kenan)". Murmushi ta kuma saki,a duk sanda innan ko malam sukayi kiranta da sunan ba wanda ke fado mata a rai sai mahaifinta. Shike yawaita kiranta da sunan,sunan da ya kasance na qanwa ga mahaifinsu guda daya tak da aka haifa a tsakanin su maza su uku,tazo kuma ta rigasu rasuwa a wajen haihuwa tabar nata yaran mata duka su uku. "Kuna raina inna....abubuwa ne suka sha kaina" Ta fada tana zama itama. Gaisawa sukayi sosai ta tambayeta malam "Malam yau duka bai zauna ba,ya tafi kasuwar qauye,amma yana hanya nasan in sha Allahu". Kamar kusan kowanne lokaci idan sunzo gidan,komawa take 'yar kallo,nadra haneefa harma da hudan suke sabgoginsu. Lumshe idanunta tayi tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Ta tabbatar yau ta faranta musu ta kuma rage musu kewa qunci da takurar zama waje daya. Tana so ta dinga kaisu guraren da zasu dan sha iska,amma tana tsoron koda da kuskure suga wani abu da zai iya affecting tunaninsu. Suna matuqar son a zo gidan,amma kuma duk dadewar da za'ayi ba'azo din ba ba zasu taba tada mata zancan ko suyi qorafi koda kuwa sau daya ba,har sai ranar da sukazo din. A nan sukayi sallar magariba,sukaci kuma tuwon dare. Suna haramar tafiya malam din ya dawo. Sosai shima yaji dadin ganinsu,ya bude kuma duk abinda yazo dashi din kama daga rake,gyada,quli kabewa,dinya da sauransu ya diba musu. Walwalarsu ta dadu sosai a sannan,duk sai da suka fice da zummar zasu tafi ya rage saura Sabreen din,ta xuge jakarta ta fiddo kudi ta aje gaban malam "Malam ayimin sadaka,sannan ayi mana addu'a". Kudin ya kalla sannan ya kalleta. "Zan miki addu'a aminatu koda baki bada komai ba....." "Malam bakai na bawa ba,yaran malam na bawa" "Idan kin fita waje ki raba musu da kanki kamar yadda aka saba" Ya tareta "Malam don Allah kayimin alfarma ko rumasa'u ta raba musu,tabbas don dare yayi ne da bazan karya maka tsarinka ba,malam kai kemin fadan kaiwa dare a waje" Ta fada murya a karye. Tanason masa ihsani,amma mutumin yana da wani irin kamewa da gudun duniyar data tabbatar bazai karbi komai nata ba "Shikenan,Allah ya karba.....kici gaba da kula da qannenki da kanki" "In sha Allah malam" Ta fada tana yin qasa da kanta kunya da nauyinsa suna kamata. Tana jin kamar inna ta gaya masa wani abu a kanta ko zata gaya masa,saidai ta sani ko daya innar nada cikakkiyar kamalar da bazata taba fadin sirrin wani ba. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 49 Tunani ne kala daban daban cikin kanta sanda suke abun hawa har suka isa gida. Banda hadiyya data samu tana zance a farfajiyar gidan nasu bata hadu da wani babba ba sai yara dake dan kai kawo a tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye take bude musu qofar dakin. Wannan shine tabbacin basu da wani sauran gata.....ba wani wanda ke tsaye yana jiran dawowarsu......babu wani da zai tambayi ina sukaje?,me yasa suka dade wuni sur a waje?,ba wani me musu barka da dawowa,dasu dawo da kada su dawo duk daya.....ire iren wadannan abubuwa ke qara mata wata qaqqarfar zuciya tare da jin cewa.....ZATA SADAUKAR DA TATA RAYUWAR don samarwa rayuwar qannenta gobe me kyau.....zata zame musu makwafin uwa da uba,dukkan wuya da dadi.....zata hanasu dandanar duk wani kalar baqinciki na rashin gata dama rashin abun kulawa da rayuwarsu. Dukansu a qoshe suke kuma a gajiye,don haka basu jima ba kowacce ta nema wajen kwanciya,don dama ita haneefa suna shigowa ta bingire a wajen. Sau biyu tana yaye labulen tana duban tsakar gidan nasu. Wanka takeso ta fita tayi saboda yadda gajiya kebin jikinta,uwa uba ma kuma ita din tun asali mutum ce data saba da yin wanka da dare kafin ta kwanta,saidai kuma daga baya abun ya zame mata qalubale babba,saboda kallon da ake mata da wasu idanu na daban. Yadda ta fita dinnan ta wuni a waje ba zata iya kwanciya haka ba,don haka taci gaba da dabuwa. Akwai daukewar qafafu sosai,wanann ya bata daman cire kayan jikinta ta daura zani ta kuma lullube sassalkan gashinta da babban towel,ta dauki kayan wankanta. Tana shirin fita nepa suka kawo wuta,don haka ta tsaya ta kashe solar din dakin ta maida musu nepa sannan ta fito. Ta tsaya daga bakin famfonsu tana tarar ruwa. Tsakar gidan tarwai da haske,kuma tsaf tsaf dashi,dabiar gidan qwaya daya tal dake burgeta,wanda idan ka dauke wannan babu wani abu dake burgeta cikin gidan dama jama'ar gidan gaba daya. Allah yasa har ta gama tarar ta wuce wankan ba wanda ya fito. Ta kammala ta nade jikinta da zanin ta dauro towel din a sama ta fito. Tana duqe baqin famfon tana daura alwala. Bude toilet din wankan da akayi ya sanyata daga kai. Sukayi idanu hudu da ita,saita miqe sosai ta tsaya maimakon dazun da take duqe tana daura alwala. Kallon bibo din takeyi kamar yadda itama ita take kalla,tun daga qafafunta har zuwa kanta da yake lullube da towel. "Ha'illallahu.....mahammadurrasulillahi......ke duniya ina zaki damu?,aah?yanzu wankan ma sai kinzo gida?" Bibo taja qaramin salati sannan ta kama haba tana sake qarewa sabreen kallo. Wani abune yazo ya yiwa sabreen tsaye a wuya,ta lumshe idanun takaici. Ta gama fahimtar zahirin abinda bibo ke nufi......ta kuma gama fahimtar abinda inda ta dosa,saidai kafin ma ta sake daga qafarta ta sake jin muryarta "Kiji tsoron Allah 'yar nan......ki daina sanyawa mala'iku suna tsaida iyayenki cak cikin kabarinsu......yanzu wannan wankan....." A fusace da kuma wani irin zafin nama ta waiwaya tana duban bibo,abinda ya sanya towel din kanta zamewa sumarta ta fito. Bata qarasa ba itama sai tabi kan nata da kallo. A bushe yake ba kuma alamun damshi ko lema,hasalima ta nannade doguwar sumar tata da tayi gado ta uwa da uba a tsakiyar kanta ta cusata guri guda,wannan ya sanya bibo din hadiye abinda taso fada din. "Ke zaa cewa kiji tsoron Allah,kuma zan maimaita miki kiji tsoron Allahn" Ta fadi da ita a nutse sannan ta fara takawa tana dosar dakinsu. Idanma tace zata riqe zafin da qirjinta yakeyi da suya to tabbas ta yiwa kanta qarya,don haka ta sulale saman kujerar falon ta saki wani marayan kuka. Bibo na daya daga cikin qalubalen rayuwarta,bibo na daya daga cikin mutane na gaba gaba da suke mata wata irin adawa mara fasali ba tare da tasan meye ne ta tsare musu ba. Ta jima a wajen tana kuka har sai da fuskarta tayi wani pink pink,sannan ta samu ta sauya kaya taja jikinta zuwa kan gadonta ta kwanta tana rufe idanunta tare da sauraron bugawar jini daga kanta wanda keson komawa ciwon kai. Sassanyan ringing dinnan shine ya sakata bude idanunta. Shaf ta mance da batun wayar sai yanzu da tayi kuka. Tunawa tayi tayi alqawarin kai wayar a yau,kada ma su tsammaci ko ta gudu da sune,wannan ya sanya ta miqa hannunta qasan pillow din data ajeta dazu ta dauko da nufin dagawa ta basu uzurin gobe in sha Allah aje a karba. Bata wani tsaya bata lokacin duba me kiran ba,tunda tasan koma waye zai kira a irin wannan lokacin tabbas makusanci ne,don haka ta shafa ta daga ta kuma Kara a kunnenta. "Assalamu alaikum anni?" Ya furta cikin husky voice dinsa dake cakude da wani irin nannauyan sauti dake nuna izza da zatin mamallakin muryar. Yayi sallamar a sanda yake tsakiyar system da kuma tarin tarkacen takardun dake dauke da plan na ginin sabon kamfanin samar da kayan qyale qyale na mata mafi tsafa da daraja da za'a dinga qawatashi d wani yanki na diamond d gold. Wani yankewa gabanta yayi ya fadi,zuciyarta kuma ta buga sosai har tana jin sautin bugun cikin kunnuwanta. Batasan dalili ba batasan kuma me yasa taji hakan ba,sai ta buda bakinta a hankali da muryarta da tayi nauyi saboda nauyin dake cike a qirjinta "Ba ita bace". Shuru ne ya biyo bayan fitar sautin nata. Ita tana bawa kanta tabbacin wancan mutumin ne daya kira duba da shurun da aka sakeyi mata kaman dazu,shi kuma kwanyarsa tana son alaqanta sautin da muryar mara kunyar yarinyar nan data dag masa waya. Kusan a tare suka daga wayar daga kunnuwansu. Ta samu tabbacinne ta hanyar karanta sunan dake yawo saman screen din. Sauke wayar yayi daga idanunsa,yaja siririn tsaki yana kashe wayar. Sautin tsakin yakai mata har kunnenta,wani mummunan baci taji ranta yayi. To ita meye nata a ciki da har zai bita da tsaki?,waye wannan daya cika izza haka?,wanne irin mutum ne me izgili da rashin sanin daraja da martabar dan adam?,don kawai a bisa kuskure wayarsu ta fado cikin kayanta sai ta zama abar wulaqantawa?. Samun kanta tayi da latse wayar kawai ta kasheta gaba daya ranta yana suya,cikin ranta kuma tana yiwa kanta alqawarin a gobe wayar ba zatakai sha biyu na rana ba a hannunta zata kira busari yakai musu duk inda suke. "Wanne irin wulaqanci ne da rashin sanin abinda kukeyi da zaku ci gaba da barin wayar anni a wani wajen?" Fuad din ya furta daidai sanda ya kira musaddiq. "Kayi haquri hamma,ta fadi inda za'a karba anje ba'a samu ba,anyita kiran wayar kuma ba'a dagawa". "Koma meye banason na sake kira naji muryarta.....kuyi magana da ita idan wayar takeso ta sauke layin daga kai,ka sanya ayima annin swapping a dauki wata wayar a hada mata". " Ka kwantar da hankalinka me babban suna,banjin yarinyar tana da niyya ko nufin riqe wayar nan,akasi kawai dai aka samu da ajizanci irin na dam adam......tana da kirki qwarai,ita ta kaini asibiti ta kuma zauna dani har sai da musaddiq ya iso". Wata sassanyar iska ya saki daga bakinsa,sai yanzu ya tuna inda yasan muryar "Itace mara kunyar yarinyar nan data tsaya tana yiwa mutane fada akai don ta kaisu asibiti?" Ya jefawa anni tambayar da nutsatsiyar muryarsan nan. Murmushi ne ya subucewa annin. Tasan halin fu'ad qwarai da gaske. Yana da tsananin kamewa da rashin son shiga sabgar kowa "Ba rashin kunya tayi ba muhammadu......fada ta yiwa musaddiq,kuma ai ta fadi gaskiya ne,ta kuma yi daidai,sun tafi yawonsu sun barni,a jikina kuma babu inhaler kwata kwata,a nata ganin indai hakan taci gaba da kasancewa komai ma yana iya faruwa". Shuru ya ratsa tsakanin bayanin anni,yana ji kawai annin tana son bata kariya ne saboda halinta na bawa kowa uzuri komai girman laifin da ya aikata mata "Is okay....." Ya fada yana sauke siririyar ajiyar zuciya a qoqarinsa na fesar da bacin da ranshi yayi "Ya jikin naki anni?" "Jiki alhamdulillah na warware" "Suna kula dake kuwa?" Ya sake tambayarta da wannan seriousness din nashi. Murmushi ta saki kadan "Qannenka suna qoqari sosai,ina samun kulawa tamkar kana nan.....saidai kewarku,ina fatan komai yana tafiya kaman yadda aka zata?,kowa kuma yana lafiya?" Murmushi ya saki,wanda mutum uku keda wannan baiwar sakashi murmushin koda baiyi niyya ba,anni abba da farouq kada ma farouq din yaji labari. Abune me wahala ka tsinci murmushi akan fuskarsa,akwai mutane da yawa dake da tambayoyi da yawa a kansa Anya kuwa ya taba dariya? Wannan kuwa yana murmushi?. Wasu tambayoyin na isa kunnensa ta harshen farouq,wasuma kam baisan ana yinsu ba. "Ba zamu wuce kwanaki hudu ba anni in sha Allah". Farinciki ya wadaci fuska da zuciyarta "To ma sha Allah.....amma baka shaidamin ba me babban suna?,banda na tambayeka da ba zaka gayamin ba ko?". "Aah anni......banason na sanyaki wannan hidimar me yawa" Murmushi ta sake saki "Hidima ai bata qarewa Muhammadu muddin akwai rai a jikina.....fatan da zakuci gaba da yi mana shine Allah ya qara mana lafiya....." "......da nisan kwana me amfani" Ya qarashe fadi. Qaramar dariya ya sanyata a wannan karon "To da nisan kwana me amfanin mu daku gaba daya". Koda suka gama wayar baiko motsa ba a wajen,yayi zaune da wayar kawai a hannu yana juyata. Duk yadda zai fasalta anni a rayuwarsa da zuciyarsa bazai kwatantu ba. Ita din uwa ce data amsa sunanta na uwa. Wadda tayi sadaukarwa da yawa cikin rayuwarsu,sadaukarwar da tayi musu ba qarama bace,sadaukarwa ce da UWA kadai ke iyayi wa danta. Asthma dinta bata taba hanata taba ruwa saboda su,asthma dinta bata taba hanata sammakon tashi koda da sassafe ne a lokacin da hazo da sanyi suka lullube sararin samaniya......a yanayin da kuma yafi zama barazana ga masu lalurar......asthma dinta bata hanata tsaftace musu muhallin kwanansu......bata hanata dafa musu abinda zasuci *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 50 koda ita din bataci ba,bata kuma hanata kulawa da lafiyarsu koda ita din bata da cikakkiyar lafiya. Har tsakiyar zuciyarsa yana jin wata qauna me girma tana tabashi game da anni,tayi musu abinda baki bazai iya fadi ba,zuciya da ruhi ba zasu iya mancewa ba. Ta musu hidima da jikinta da kudinta da lokacinta harma da lafiyarta,irin hidimar da ya debe tsammanin zasu sameta,irin hidimar da suka buqaceta a yunwace daga wajen wadda tayi silar zuwansu duniya amma ta gagaresu.....kulawar da baiyi tsammanin zasu sameta ba daga gurin kowacce mace a duniya. Baiga abinda zai samu a duniya ba da zai manta da anni.....baya tunanin akwai abinda anni zata nema daga gareshi ta rasa. Yana shirin sauke wayar tasa don ya tattara tarkacensa ya wuce daki ya samu bacci koda na awa biyu ne kafin zuwan lokacin sallar asuba sai kiranta ya shigo. Kamar ko yaushe ya zubawa kiran idanu,a duk sanda zata kirashin sai ta tuna masa da abubuwa masu yawa. Aduk sanda kiranta zai shigo wayarsa saita tada masa wani abu daga can qasan zuciyarsa. Bashi da wani zabi da ya wuce ya daga din,sai ya sake zama sosai ya ya dauki wayar yana karawa a Kunnensa, Cikin jin isa da izzar cewa ta haihu.....cikin isa da jin izzar ita din a yanxu wata abace cikin duniyar.....cikin jin izzar ta isa takai qololuwar gata a cikin jerin iyaye mata ta amsa sallamarsa. "Barka da dare.....an wuni lafiya?". Maimakon ta amsa masa saita sake daidaita kanta,a dake take masa magana "Yanzun ace bankai kima da martabar da a kullum zaka kirani kaji ya na kwana ya na tashi ba?" Ta maida masa gaisuwar da qorafin abinda me masa suya a qirji. "Afwan.....kiyi haquri" Ya zabi furtawan. Har cikin zuciyarsa,har kuma tsakaninsa da Allah kirantan kaman yadda take buqata wani baqon abune cikin rayuwarsa dama lokutansa. Yadda ta zamewa rayuwarsu baquwa haka dukkan wata mu'amala da zaiyi da ita take zama baquwa a wajensa. Koda yayi niyyan yin hakan saboda sauke nauyi da haqqin haihuwa dake wuyansa sai ya manta sam sam,tunda abune da aka fareshi bada dadewa ba,sabo dashi kuwa zai dauki lokaci kafin ya shiga jiki da zuciya,bayan haka ma......kwata kwata mu'amalar dake a tsakaninsu wata irin tattaurar mu'amala ce da babu taushi a jikinta bare ta shiga zuciya da kyau ta tsayema tunani. "Koda baka nemeni ba ni bazan zubewa duniya ku ba.....ku zama inuwar giginya na nesa kasha dadi...." Ta fadi tana watsa hannuwa ba tare data tuna da kuskuren rayuwarta na farko ba. Numfashi ya aje,maganartata ta zama tamkar wani tuni ne daya dace ace kanta da kanta ta yiwa shi "Ba zata zubewa duniya su ba....." Baisan zubewa ta nawa ya rage tayi musi ba,kalamanta a kullum sake haska masa ita yake,yayi imani yana kuma sake samun gamsuwa da dalilai masu tarin yawa dake bayyana masa lallai AKWAI DALILIN dawowarta cikin rayuwarsu......lallai ta dawo ne bawai da sunan nadama ba ko gyaran kuskure......AKWAI DALILI AKWAI KUMA HUJJA. Wasu yana kallonsu shimfide a zanen tafin hannun qaddararsa,wasu kuma baisan daga inda zasu soma bullo musu ba. "Ba'a canzawa tuwo suna Muhammad,kuma ko ma meye ka zama sai dana haifeka sannan ka zama din......mahaifiya daya ce kuma ni dince dai". Idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kafin ya samu budesu. Ba abinda maganganunsa ke haddasa masa sai sake jagula duk wata qanqanuwar nutsuwa tasa da yake qoqarin samarwa kansa. "Kiyi haquri" Ya sake maimaita mata kalaman da ta dade da haddacesu daga bakinsa. "Yaushe zaku dawo?,idan ba nan kusa bane dawowar taka ka sanarmin......don nasan sai yadda akayi dakai,sai kuma abinda aka shimfida maka". Yaji saukar kalamanta sosai har saman zuciyarsa. BATA SON AHALIN ALHAJI HAMZA KIBIYA ya dade dayin wannan karatun a qanqanin lokacin data duro cikin rayuwarsu......ya kuma san halinta tun daga sanda ya fara rarrabe abubuwa har zuwa sanda ta fice daga rayuwarsu. Idan batason abu bata sonshi kenan......dadi ko wahala basa sauyata akan abun. Idan taqi taqi kenan.....hakanan idan taso taso kenan......bata ja da baya akan duk abinda ta sanya a gaba......bata rasa ABUN HARINTA komai dadewar lokaci. Wadannan abubuwan ya sanya ya sanya dukkan wata nutsuwa da karatu nasa a kanta......ya sanya duk wani nazari da dogon hange da tsinkayensa a kanta,yasan wacece......sanin da ita kanta batasan bata kuma yi zaton yakai zurfin haka ba. "Ba zamu wuce satin nan ba in sha Allah" Ya amsa mata kamar yadda ya amsawa anni a dazun. "Har sai ankai sati?" Ta masa tambayar a zaqe,har abun yadan so bashi mamaki,don sam salon tambayar nata baiyi kama da ta zaqu ko tsahon kwanakin sun mata yawa da zasu bayu ga ganinsa ba,tabbas yasan akwai dalilin tambayar a qasa. "In sha Allah" Ya bata tabbaci yana jiran dalili na gaba "Kudi nake buqata ka turamin ta account dina akwai amfanin da zanyi dasu......kada suyi qasa da million daya" Tayi maganar kanta tsaye cike da karsashi da qwarin gwiwa kaman yadda hajja ta kwatanta mata. Mamaki kadan ya kamashi.....saidai ya ajeshi a gefe "Akwai abinda baki dashi?,cikin gidan ko sutura ko wani abu makamancin haka?,ko akwai wanda kike da buqatar ayi masa wani abun?" "Duka babu ko daya.......shin waima sai ina da wannan buqatun zan buqaci kudi daga wajenka?,yarinya ce ni qarama ko kuwa?,ko banyi isar da zaa dauki tsabar kudi a bani ba har sai akwai dalili ko hujja?" "A'ah......" "To dakata......ba sharhi nakeso ba......kayi abinda nace daga yau zuwa gobe". Sai yaji alamun yanke kiran,abinda ya tilasta masa sauke wayar daga Kunnensa yana binta da kallo. Yatsunsa kawai ya dora saman goshinsa yana murzasu a hankali,kadan kadan yake furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas yasan da akwai wani abu......akwai wata a qasa...... Wanzuwar kudi a hannunta kwata kwata ba alkhairi bane,kuma ko yanzun bayajin alkhairi ne ya sanya ta nema. Cikin lokaci qanqani yaji jijiyoyin kansa sun qara adadin gudunsu da kuma harbawarsu,abinda ya haifar masa da fara jin alamun ciwon kai. Bayason hayaniya......bayason matsala kwata kwata,wannan ya sanya yake nesa da mutane da al'amuransu,banda kasuwanci daya daukoshi tsundum ya jefa cikin mu'amalantar mutane qarfi da yaji. Ba wani karsashi ko qwarin gwiwa ya dauki dukan abinda yasan yana da buqata,a maimakon tattare takardun nasa gaba daya da yayi niyyar yi ya kuma shiryasu kamar yadda ya saba. Yana da wani irin tsafta da duk abinda yayi amfani dashi zai wahala ka sameshi ba'a killace ba. Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya tura qofar dakinsa idanunsa akan dakunan abba da saddiq daya tabbatar zuwa lokacin sun jima da yin bacci,wani lokacin sai ya dinga ji kamar su kadai ne basuyi sa'ar rayuwa ba.....sai ya dinga ganin kamar kowa ya dace da rayuwa me kyau amma banda su. Duk sanda irin wannan tunanin ya fado masa yakanyi qoqarin korar shaidanne daga ransa. A gefan gadon ya zauna,ya miqa hannu ya kunna bedside lamp,dan siririn hasken da baida takura da yawa ya bayyana. Hannunsa ya zura qasan drawer din da fitilan take kai,ya ciro wani mini wallet dinsa,ya bude ya sake zaro wani qaramin hoton dake ciki. Duk da hoton baida cikakkiyar kala amma fuskar mutumin ta fita sosai,kamannin nan nasa da murmushinsan nan da idan ya kalla sai yaji kaman idan ya kirashi zai amsa. Wani abu ya tsaya masa a wuya,yayin da idanunsa suka sauya launi,gefe daya wani qaqarfan abu da ya jima yana kokawa dashi akan maamah din ya fara taso masa,sai ya fara hadiyar zuciya kadan kadan yana qoqarin hadiye bacin ranshi,tamkar me hadiyar lomar abinci,don daga inda inda kake kana iya hangen Adams Apple dinsa daya zamewa wuyansa dama fuskarsa ado yana kaikawo daga sama zuwa qasa. A duk sanda ya kalli fuskarsa cikin hoton sai yaji duk duniya ba wanda ya kaisu maraici......a duk sa'ilin da zai kalli wannan jarumar fuskar sai yaji zuciyarsa ta cika da qiyayyar kowacce d'iya mace a duniya idan ka debe anni da manal......wata irin wuta ce take ruruwa a zuciyarsa a kanta......har yakanji kamar bazai iya sake kusantar muhallin da take bama ballantana yaci gaba da accepting nata ko kyautata mata a matsayin uwa. Fuskar abban wata fuska ce da a kullum take tunasar dashi gwagwarmaya da ainihin ma'anarta.....fuskar tasa fuska ce dake karanta masa tare dayi masa bitar cusgunawa....uzzurawa da azabtarwa irin ta diya mace. Kowanne hoto nasa da abinda yake karanta masa.....hakanan da abinda yake tunasar dashi. Ko kusa ko alama....ko sau daya.....hakanan koda wasa bai taba sha'awar aure ba ballantana wata diya mace. Yana kallonsu a wasu halittu ne na daban da babu imani ko tausayawa cikin lamuransu. Sanadin ciwon abban....da silar data sanya ya dinga ci gaba abune da bayason tunawa,abune dake dake tilasta zuciyarsa juyawa MAAMAH baya da dukkan abinda ya danganceta. Koda ya tuna da abin a sanda take daura dashi yakanji baya buqatar kallon fuskarta ko kuma sauraren muryarta,yanaji cewa ba abinda zai bashi sukuni face yayi nesa da ita. *_AKWAI WANI SIRRI.....AKWAI WANI BOYAYYEN SIRRI CIKIN DUNIYARSA_* *******Sannu a hankali take tafiya cikin daya daga cikin layukan da suke zame musu turba kuma hanya ta isarsu gida a duk sanda suka rasa samun abun hawa ko kuma kawai jin rikici irin na dalibin dakan qirqirarwa kansa tafiyar qafa haka siddan. Ita daya a hanya amma tanata mamakin yadda yau aka raba musu lokacin tashi daga makarantar alhalin tunda suka fara tsahon shekarun tare ake tashinsu. Ta cika tayi fam akan yadda nadra din da haneefa sukayi gaban kansu suka taho gida abinsu ba kamar yadda suka saba ba abinda basu taba yi ba. Gefe daya kuma na zuciyarta ya cika da saqe saqe tare da tunanin yadda zata qarqare haddace ayoyin qarshe na shafin da a yau zata bada haddarsa a islamiyya. Kaman daga sama,babu zato kuma ba tsammani taji an finciki qaramar jakar da take dan cillata a hannunta wadda ke dauke da muhimman abubuwa da dama. Sanda ta daga kai kuwa a firgice barawon ya soma nisa da ita yana gaya mata "Idan kina da gata,ko kina da me qwatoshi ki turo shi" Sai ya juya cilla sassarfa ya fada wani lokon dake daura dasu. Ko wanne sashe na jikinta rawa yake,tayi wata irin tsorata da bata taba yin irinta ba. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 51 Abune da bai taba faruwa da ita ba koda wasa,ta waiga gabas da yamma kudu da arewa,ba kowa a layin,babu gicci ko wulqawar kowa,ko cutas da ita zayayi zaiyi ne hankali kwance,abinda ya sake kada mata hankali kenan,ta soma yunqurin tattara dukkan qoqarinta wajen ganin tabar layin. Taku uku tayi ya shawo kwana. Hannunsa riqe da jakartata da yanzu yanzu aka wafceta. Birki taja ta tsaya,gudun zuciyarta yana sake qaruwa kaman zuciyarta zata fito ta bakinta. Ta qura masa idanu tana kallonsa kaman yadda shima ita yake kallon. Guduwa takeson tayi amma ta kasa kaman an kafeta a wajen. Duk taku daya da zaiyi yana sake ganin kamanni na jini da kuma yanayinta da SABREEN din. Yana mamakin yadda ta iya boye komai nata,yadda ta iya bad da bami,ta iya nutsewa da narkewa cikin sararin duniya ba tare da ka iya gano daga ina take fitowa ba ina kuma take komawa?. "Karkiji tsoro......ni ba cutar dake zanyi ba.....jakarki na karbo miki,nazo wucewa naga abinda ya faru,karbi jakarki" Baya taja kadan,bata jin aminta dashi sam sam a zuciyarta. Wani irin raino da horo sabreen ta yiwa kowannensu na rashin yarda da baquwar FUSKA muddin sunanka NAMIJI. "Da gaske nake miki.....ba cutar dake zanyi ba,idan kuma baki yarda ba ga jakarki nan" Ya fada yana ajiyeta a tsakaninsu sannna ya juya ya fara takawa yana barin wajen fuskarsa shimfide da murmushi,qasan zuciyarsa kuma fes cike da murnar samun CIKAKKIYAR NASARA da kuma tabbacin DAUKAN FASA mafi ciwo a gareta. Sai data tabbatar ya bada tazarar da koda ya juyo zuwa gareta zaiyi wahala ya cimmata sannan ta taka ta isa ga jakar,ta tsugunna ta dauka,ba tare data damu da datti da qurar data debo daga qasa ba ta rataya tana maida idanunta kansa. Tafiyarshi yakeyi baiko waiwayota ba,ta kalli jakar ta kuma kalleshi,sai ta buda bakinta a hankali tana furta "Na gode". Cak ya tsaya tamkar dama yana dakon martaninta ne,sai ya waiwayo yana sake fadada fara'ar fuskarsa "Nima na gode.....sunana....." Dakatawa yayi kadan saboda tuna wani abu da yayi _"Tana da wayo,tana da hadari.....da alama kuma akwai abinda ta taka_ kalaman suka dawo masa kai fes "Sunana BASSAM....kefa?" Ya furta yana murmushi tare da samun gamsuwar lallai sunan zaifi saurin isar da saqo a maimakon ainihin sunansa na NASEER. Bashi da buri baya kuma fatanbta fahimci komai har sai zuwa sanda komai din ya kammala......har sai zuwa sanda shi da kansa zai mata bayanin komai. A lokacin da yake buri da kwadayin jin sheshsheqar kukanta......a yanayin qunci baqinciki da kuma tarin damuwa da yake fatan ta hallakata......koda bata hallakata ba yana fatan tayi mata mummunar illar da koda gaba ba zata qara gigi kasada ko gangancin shiga shingen mutane irinsa ba. "Kefa 'yammata?" Ya tambayeta cikin lanqwasa murya da tausasa harshe gami da sanya wani amo me sanya nutsuwa ga duk me saurare. Lokaci daya ta danji ta samu nutsuwa kadan,sai ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bashi amsa "Huda" Ta furta a nutse tana jin wani iri da kiranta da sunan 'YAMMATA da yayi,karo na farko cikin rayuwarta da wani ya taba kiranta da wannan sunan. Murmushi ya sakar mata yana gyada kanshi gami da lumshe ido yakuma budesu a lokaci guda "Nice name.....duk wanda ya baki wannan sunan ya iya zaben suna". Maganar tasa ta sanya fitar murmushin dole a saman fuskarta. Tadan murmusa kadan,abinda ya sake sanyashi ganin kamanninta muraran da sabreen. Wutar daukan fansanshi ta sake ruruwa cikin ransa. Kai ta jinjina a nutse tana dan sadda kanta qasa kadan "Autyna ce" Ta samu kanta da bashi amsa "Antynkin nan tana ja da yawa.....ta iya zaben sunaye" Ta fada da ma'ana biyu,a zahirance kuma da harshen da ba kowane zai fahimci boyayyen sirrin dake qasan zuciya ba. Dagowa tayi a karo na biyu ta sake kallonsa,sai taji wani dadi zuciyarta tana saki kadan. Duk wanda zaya so sabreen a wajensu basu da kamarshi......kaman yadda suke nisantar wanda zai kawo suka a kanta ko wanene. "Nadan rakaki kadan ko?,ki fita daga layin nan,don har yanzu ban gamsu da sahihancinsa" Ya fadi yana duban gefe da gefansa bayan ya zube dukka hannayensa cikin aljihu. Tayashi duban itama tayi gabanta yana dan faduwa,ta yaya zata iya jerawa dashi wai?. Amma ko kafin tace komai ya fara takowa zuwa inda take tsayen yana jifanta da murmushi,tadan ja baya kadan dole ta fara takawa ya rufa mata baya "Kada ki damu,bawai zamu jera bane,ba wanda zaisan tare muke......kawai dai zanyi gadinki har ki aminta" Kalmar aminci daga bakinsa ta sanya taji ta sake,sai taci gaba da tafiya,shi kuma yana biye da ita da 'yar nisan tazara a tsakaninsu. Duk wani taku nata guda daya yana lasafta yadda komai zai wakana......a yanzu bayan wutar daukan fansa dake ransa,wata wutar daban ta soma rura kanta da kanta a zuciyarsa.......bayajin koda ba komai tsakaninsa da sabreen zai iya qyale wannan danyar 'yar shilar ta wuceshi. Duk da bata qarasa 'yar uwarta ba a komai.......amma zata sama masa nutsuwa yayi yaqinin hakan ko yaya take kaman yadda ya dade yana tsara zai samu daga yayartata. Bai tsaya ba har sai da qafafunta suka isa babban qofar gidan nasu,sai ya samu waje nesa kadan saboda gudun bacin rana da bacin aiki,ya tsaya kawai yana jifanta da wani mayataccen kallo tamkar mayunwacin zaki. Har ta sanya qafafunta sai ta dakata ta waiwayo,suka hada idanu abinda ya bashi damat jifanta da wani shu'umin murmushi. Itama murmushin ne ya subuce daga bakinta tana jin cewa ya kyautata mata matuqa,abinda ba kasafai suke samunsa daga wajen al'ummar da suke kewaye dasu ba,don haka wannan din ya qawatar da ita. Bakinta ta bude a hankali ta furta kalmar "Na gode sosai". Duk da tasan ba lallai ya iyajinta ba,amma zai karanci bakinta. Ya kuma karanta din,sai ya daga mata kai don haka ta juya tana shigewa cikin gidan. Haka kawai murmushi ke fita a fuskarta tana tuna yadda komai ya kasance. Badan shi ba Allah ne kadai yasan abinda zai faru da ita a wannan qonannen layin da babu kowa. Ba yadda kuma zatayi,nan dinne dai hanyar wucewarsu tilo guda daya,inda da wata hanyar tabbas ba abinda zai sanyata ta sake bi ta nan wajen. "Ke dawa kike murmushi ke daya?" Sabreen dake tsaye gaban fridge dinsu tana duba adadin pure water da lemon daya rage musu a ciki ta fada hannunta dafe da murfin fridge din. Cikin sauri ta gyara yanayin fuskarta tana qoqarin adana takalmanta data shigo dasu "Ba kowa adda...." Idanunta ta zube mata sosai tana son karanto wani abu amma bata samu nasarar gano komai ba,saidai duk da hakan haka kawai takejin bata nutsu da irin amsar huda din ba. Emotions ke sauya yanayin fuskar mutum,walau na farinciki ko baqinciki,dole idan ya nuna saman fuska to akwai wani labarin a qasan zuciya. Sakin fridge din tayi bayan ta rufeshi tana takowa tsakiyar dakin "Wacce irin tafiya kukayi ne yau ke dasu nadra?,kinsan dai banason kuna raba tafiya ko?" Ta fadi tana zama idanunta still akan fuskar huda din. Fuska ta bata ba kaman dazu ba tana duban sabreen "Wallahi dama nace zamu hadu dasu.....kawai adda ina fitowa na samu wai sun wuce gida?,yau bansan me yasa aka rarraba mana lokacin tashi ba" Ta qarasa maganar fuskarta a bace da gaske. Idanunta tadan dauke daga kanta tana sauke numfashi "Banason irin wannan tafiyar,kome raba lokacin su dinga jiranki" Cikin ranta tana jin abun kwata kwata baiyi mata ba. Qaramar dariya ya sakarwa kansa bayan ta shige gidan. Fara takawa yayi hankali kwance yana barin layin. Tabbas shima zai buga nasa wasan yadda ya dace,zaiyi wasa da rayuwarta da kuma hankalinta yadda ya kamata......zai gigita mata rayuwa ya dagula dukkan wani lissafi nata......zai guntule dukkan wani farinciki nata kaman yadda ta gurgunta ta kuma dagula rayuwa da nutsuwarsa. Yanaji a ransa abun zai bashi nishadi qwarai,zai kuma qarasa goge baqinciki qunci da takaicin data qunsa masa. ********Cikin nutsuwar nan tasa yake saukowa daga matakalar jirgin riqe da kyawawan briefcase guda biyu. Tasa data Alhaji hamza kibiya. Biye yake da dattijon,yana aje tasa qafar a duk muhallin da ya cire. Kamilallen dattijon da adadin furfurar dake baibaye a fuskarsa da kuma gashin kansa suka sake tabbatar da dacewar sunan dashi. Cikin kamala yake komai nashi,sanye da shadda dinkin babbar riga da maroon hula dara sak ainihin shigar marigayi malam aminu kano. Muhammad fu'ad jadda,mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources wanda ke biye dashi a baya. Sanye cikin dinkin kaftan da yayi matuqar qara masa kwarjini da wani irin haiba me cika idanun me kallonsa. Idan ka kallesu shida Alhaji hamza kibiya din zakayi tsammanin shine ainihin mahaifi gareshi saboda yadda tsahonsu yake kusan daya da kuma murjewar jikin. Bayansa kuma sadiq ne janye da luggage dinsu. Shikam t.shirt ne jikinsa da trouser,ya lullube qafafunsa da lafiyayyen boots ba kaman fu'ad ba dake sanye da wani lafiyayyen halfcover ba dan qasar itali da aka samar dashi da dinkin hannu(sau da dama mu a nigeri muna raina takalman hannu,amma a qasashen qetare babu takalma masu daraja da tsada irin handmade shoes,wani ma kana ce masa handmade ne ka bata show din😂,nija my nation 🫡😂). Tare suka jero kafada da kafada shi da Alhaji hamza din zuwa muhallin da farouq yafi tsaiwa a duk sanda yazo daukosu daga tafiya irin wannan. Ko a yanzun da suke nufar mota don isa gida ma duk hirar akan kasuwanci ce. Abun yana bawa Alhaji hamza mamaki. Duk qwarewarsa da qaunarsa da kasuwanci fu'ad din ya shallakeshi. Kowacce rana kowacce safiya,kowanne dare da wuni plan din rayuwarsa da komai nasa yana kan kasuwanci. Me za'a bunqasa?,me za'a qirqira?,me kuma za'a gyara?,ina ne nasara take a bunqasata?,ta ina faduwa take ayi hanzarin bawa gurin kulawa da kariya?. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 52 Yana jingine da motar yana kallonsu,idanunsa fes a kansu. Yana masa dadi yana kuma sanyawa ya manta cewa fu'ad ba dan uwansa bane na jini a duk sanda ya ganshi kamar haka da Alhaji hamza din. Yana alfahari yana kuma qara ninka alfaharinsa akan muhammad fu'ad din. Shi kansa ya sallama......jajirtaccen mutum ne da jajircewa take a cikin jinin jikinsa. Ya maida idanu a hankali akan yanayin takunsa. Tafiya ce me cike da ginshira gami da cikakken kuzari da karsashin da zai bayyana maka adadin cikakkiyar lafiyar da yake da ita. Daga abban har fu'ad din hankalinsu baya wajen,yana duba wani qaramin takardu da suke dauke da bayani da taswirar burinsa na gaba wato ginin katafaren kamfanin samar da kayan ado na sarqoqin mata da zai dinga amfani da wani sashe na ma'adanan da yake haqowa. Tun daga fitowarsu gaba daya security guards dinsa da ya bari a gida kowanne ya koma kan aikinsa. Dukan inda ya ajiye qafarsa nan suke maida tasu. Murmushi ya subucewa farouq,ya dawo kenan,kuma yanzun za'a fara. Bayaso abba ne ya tilastashi daukan guardsmen duba da yanayin qarancin tsaron da ake fama dashi. Uwa uba ma zaiyi wahala a nasibin rayuwa daya samu......da irin mu'amalarsa ace ya zauna haka gayansa yana yawo babu masu tsaron lafiya tattare dashi. Wani lokacin idan yaso yana kubce musu ne yayi fitarsa shi kadai a mota yasha iska ya dawo. Ba kasafai ya fiya son fita qasashen waje sai idan harka haka ta taso takai kayan da sunyi yawan yayi wakilci......amma yanzun ya koyi fita din lokaci bayan lokaci haka siddan ma don ya samu ya sarara yayi rayuwarsa shi kadai. Mutum ne da bayason matsi,bayason takura,zai iya rayuwa me dogon zango shi kadai a wani muhalli na daban,shi yasa ko a yanzun a sassansu gini ne me zaman kansa dake dauke da bedroom and parlor da toilets kowa shi kadai. Saddiq da musaddiq sun hade dakunansu saboda kowa nashi apartment din ya masa girma. Amma oga fu'ad shi daya ne a nashi,hakama farouq,sai shi farouq din da lokaci bayan lokaci yakan dawo sassan fu'ad din yayi kwanaki yana kwana a nan sannan ya koma wajensa. Kullum ya hangi fu'ad din daga nesa ba abinda yake tunawa sai wannan matashin dan bautar qasar,mara tsoro kuma mara shakka,cikakken jarumin daya shiga yankin daba nasa ba,yayi abinda koda haifaffen yankinne ya aikata bazai sha ba.....ya kubuta da tarin nasara. Farouq yadan sake murmusawa yana tuna yadda yaci wahala bayan uban gudun da sukayi,ya tuna yadda fu'ad din yayi jinyarsa tamkar ba dashi akayi gudun ba "Ba abinda nakeji man.....ni dakai ba daya bane,sau nawa ana gaya maka ka dinga gym saboda yuwuwar samuwar irin wadannan lokutan na qwatar kai?,sai kuyita zama kaman mata,baku da wani banbanci dasu?" Ya tambayi farouq din a wancan lokaci yana dage masa dukka girarsa bayan ya bashi maganin ciwon jiki yasha. "Yanzu wannan pain killer din da kake fana dashi......da warm water da fenugreek kake sha da yafi maka amfani". Harara ya balla ma fu'ad din yana dubansa "Ba zaka qarasa kasheni ba da wadannan home remedies din naka ba" Sai ya juya ma fu'ad din baya yana sauke numfashin wahala yabar fu'ad din da sakin siririn murmushin nan nasa me tsada. Miqewa yayi yana dauke cup din "Idan home remedies bai kasheka ba......son jiki da rashin exercise....aci a kwanta duka ya kasheka......naga wanda zai aureka da qaton tumbi" Ya qarasa maganar yana jefa kwalin lemo a dutsbin. Duk da farouq na cikin yanayi a sannan saida murmushi ya qwace masa.....fu'ad mahadin rayuwarsa ne kuma mahadin zuciyarsa ne kaman yadda ya tabbatar a wajen fu'ad dinma haka yake. Kafadarsa y Ta dama yaji an daka "Murmushin me kake kai kuma?" Sassanyar muryar nan tasa sake cakude da wani deepness ta shiga kunnen farouq. Kallonsa ya dora saman fuskar fu'ad din yana jin yawan kewarsa da yayi "Ina nan ina kallon gujajjen dan bautar qasar nan da bai kammala service dinsa ba sai a garin kano". Murmurshin nan da shi daya ke iya fidda masa shi daga kan fuska ya saki kadan yana sake kaiwa kafadarsa duka. Dariya kadan ya saki shima farouq din "Ina hasaso yadda zasu cinye namanka danye duk sanda suka fahimci daga ma'adanin qasarsu ne aka samar da attajirin nan mamallakin jadda diamondchore company........" Murmurshin ya sake sanyashi saki,sai ya saka tafin hannunsa saman wuyansa yana dan karyar da wuyan kadan "Naman muhammad jikan jadda yafi qarfin cinsu umaru...." Ya bashi amsa da anihin sunansa,abinda ya sanya farouq din sakin dariya sosai. Kafadar fu'ad din yadan bubbuga "Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri ne......tun daga ranar da mukayi temple run dinnan na sake yadda da hakan..." "A nan zaku gama hirar ne?,idan ku baku gaji ba ku tallafa ku kaini naga aminatu na" Muryar abba ta sauka kunnuwansu. Fu'ad ne ya waiwaya don farouq yana fuskantar abban ne. Dan murmusawa kadan fu'ad yayi ya matsa yana yunqurin budewa abban qofa,amma farouq ya rigashi "Dukkanku kai da abban yau qarqashin hidimata kuke....baqinmu ne ku daga South Korea". "Sannu sarkin noma.....godiya muke" Shima abban ya fada cikin barkwanci bayan ya shiga motar. Dashi da farouq din baya suka shiga bayan ya bawa shugaban security dinsa umarnin su bisu a baya. Kusan duka a hanya ma dai tattaunawar ta kasuwanci ce. Farouq din yana bawa abban labarin yadda abubuwa suka kasance bayan tafiyarsu "Amma tabbas sai ka sake sanya idanu akan mika'il.....ina suspecting wani abu tattare dashi,duk da bana ce gashi ba,amma nasan kai din zaka fini fahimtar komai" Farouq din ya furta. Idonsa fu'ad ya dauke daga kan wayar hannunsa,wanda saqon mika'il dinne ya shigo,mutum na farko daya fara masa saqon barka da dawowa kafin kowa. Bai cewa farouq komai ba,amma kuma maganar tasa ta samu gurbi sosai a zuciyarsa ta zauna,sai ya gyada kansa a hankali yana sake maida dubansa ga wayar. **"Anni an gama komai" Ta furta sanda take saukowa daga saman tsararren dining area din daya dauki kyakkyawan family dining table na wani mulmulallen tangaran kai kace an samar dashi ne daga burbushin diamond ko gold da kamfanin jadda ke wankewa su fiddashi. Fara ce tas,mai matsakaicin tsaho,saidai bata da qiba ko qanqani. Yanayin sumar gaban kanta kawai zai fada maka akwai suma me yawa a saman kanta wadda bata da duhu ta danyi brown kadan bame yawa ba. Yanayin yadda ta datsi daurin dankwalinta daga tsakiyar kanta shi zai baka daman ganin hakan sosai. Straight gown ce a jikinta ta atamfa me igiyoyi hagu da dama wadda ta daureta daga gefen qungunta guda daya. "Ma sha Allah.....sannunku da qoqari....sun wuce ne?" Anni data daga kanta daga tab din hannunta da take duba wasu addu'o'i ta fada. Fuska tadan yamutsa kadan tana zama kujerar gefan annin gami da ajiye qaramin towel din hannunta a side table sannan ta dauki wayarta dake ajiye akai tana qoqarin budeta "Kowa ya wuce......yanxun abba da hamma kawai muke jira" Ta qarasa maganar murmurshi yana subuce mata. "Umhummm......wato shi saddiq shine marainin wayonki da baki ta tasa ko?" Anni ta fada tana maida idanunta ga addu'o'inta . Fuska ta yamutsa,duk da bata kalli annin ba amma ta amsa "Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba dalili......hamma takurawarsa me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko wayar nan yanzun ya shigo yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa ta kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X. Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon daman daukan shuru na wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni kallo sai ta saki dariya "Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin annin dake wani yauqi da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin green,bashi da nauyi ko kadan "Saikin fada 'yar kasuwa......" Ta amsa mata ba tare data dubeta ba "Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk dogayen rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa qasa tana qunshe bakinta da hannu. Kadan ta dubeta ta harareta "Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza tana qoqarin maida kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta "Babu anni.....anni ta abbanmu". "Amna.... Qoqarin maidani kakarki kike ko?" "Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta "Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi zamanki a can". Kyabe fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka "Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da sister?....." "Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai kinfi jin dadi". Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni "Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta "Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa hawaye tana juyawa annin baya "Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi dama yaa farouq kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake zan yita zama". Yadda tayi maganar zata yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya amma ta dake "Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta. "Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai matsa miki.......i swear" Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta. "Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana daidaita zamanta saman kujerar. Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe "Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun arziqi kai tsaye a gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana duban musaddiq dake dariya qasa qasa. "Eh anni.....su abban basu iso ba?" "Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don tun dazu suka tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata da yake miqa mata. Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta zuge jakar cikin rashin tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai ta samu komai a muhallinsa ba tare da an canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data nuna low battery da alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge. "Ikon Allah" Ta fada,abinda yaja hankalin amna da musaddiq kanta "Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da mamaki idanunta cikin jakar "Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko akwai wani abun daban ba" "Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu "Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake yiwa godiya?" "She's not natural fa anni" Ya fada a taqaice "Kamar yaya?" Ta tambaya cikin rashin fahimta. "To nidai anni ko qyallinta ban gani ba,a bakin wani waje wani ya tareni ya bani,baicemin komai ba ya juya,nima haka na juya da kan motata na dawo gida" "Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin ba.....na kasa manta damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a ranta. Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin da suke da tabbacin baqinsu sun iso "Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 53 Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa tsaye tare da dakon qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata da kyau tana dariya idanunta saman fuskar fu'ad "Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi yana subuce mata "Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba". Abban ya fada yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da murmushinsa "Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da fu'ad din tana karbar briefcase dinsa "Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta bayansu abban. Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska "Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South Korea kun yar dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe. Ba wanda maganar bata bawa dariya ba a cikinsu "Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai" "Allah bazan nemi wannan ba....." "......me qarya?" Saddiq ya datsi numfashinta yana fadi idanunsa a waje "Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran quruciya a tare da ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske. Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon. Ta rusuna tana masa sannu da zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya. Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai a wajen annin. Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito. "Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa". Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni "Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me aiki "Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu "To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana nufar qofa "Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba. Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki "Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari". Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan "Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......" "Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin juma'a". "Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko a sirrance akayi shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu qwarara......matsalar kawai har yanzun ni kaina bansan color na macen da kakeso ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan duka sai daya qame,don maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba. "Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar" Ya fada yana jingine masa luggage dinsa daidai qofofin sassansu "Tafi nono fari" Fu'ad din ya fada yana zura key ma qofan sassansa yana budewa,saidai fuskarsa kwance take da murmushi yana juya halin farouq din. Shi daya farouq din yakewa haka.....kamar yadda shima farouq din kawai ke akwai 'yar hakan a tsakaninsu. "Alhamdulillah" Ya furta a sarari murya can qasan bayan ya isa ainihin bedroom dinsa,yana jin ma'anar godiyar daga qasan zuciyarsa. Tarin godiya ce fal zuciyarsa game da ubangijinsa,godiyar da har wani lokacin ya dinga jin baisan ta yadda zaiyiti ba takai gurbin da akeso. Ubagijinsa ya gama masa komai.....ya kyautata rayuwarsa fiye da yadda yake tsammani. Komai na sashen nasa a killace a kuma tsaftace akan tsari fiye ma da yadda yakeso. Wani irin qamshi ke tashi,abinda ya sanyashi sakin wata nannauyar ajiyar zuciya data sanya yaji wani nauyi ya ragu sosai daga saman zuciyarsa. Yana yiwa qamshi wani jarababben so,a duniya qamshin yana daya daga cikin jerin abubuwan da yafi qauna. Qamshi yana sanyashi maqalewa waje,kaman yadda akasinsa ke sanyashi rabuwa da waje. Yana iya baiwa farouq dinsa komai amma indai ta fannin abinda ya shafi turare ne to zaka iya jin musunsa dashi. Bai yarda ba a taba masa turaruka,gwara ka zaba ko na nawa ne ya siya ya baka kyauta. Kayan jikinsa ya dinga zarewa har sai daya rage saura fara qal din vest din jikinsa da gajeran wandon da bai qarasa gwiwarsa ba. Muradadde kuma ginannen jikinsan nan dake dauke da wasu lafiyayyun muscles dake alamta ainihin qarfi na siffa ta zahiri da badini ya bayyana,lullube da wadatattun gargasa ta ko ina. Wankan yakeson yayi amma shigowar kira ya hana masa hakan,tilas ya samu saman sofa bed ya zauna yana amsa kiran. Amsa kiraye kirayen ya daukeshi lokuta masu tsahon da har musaddiq ya dinga zuwa dubashi zasuci abinci. Daga qarshe ya basu excuse akan suci din idan ya kammala zai fito. Fitowar da bai samu daman yi ba kenan,don sanda ya fito a wankan gaba daya kasala da tsohuwar gajiya ce ta saukar masa,dole ya haye gadonsa bayan ya maida da dakin dark ta sakin dukka manya manyan curtains dinsa,ya kuma kashe kowacce fitila da zata iya bashi haske don baya son bacci a duhu sam sam. Koda baccin yakeyi kana kunnata ka tasheshi. Sunsha fafatawa da farouq akan hakan,don shi mutum ne da kwana cikin haske bai dameshi ba. Wannan dalilin yasa ko a yanzun yafi sha'awar kowa ya zauna a sassansa,ba kasafai ya fiya son takurawa mutum da salon tsarin rayuwarsa ba. *****Su biyun dukansu suna zaune ne saman buzu na fatar dabbar da basusan wacce iri bace. Kaman yadda dukkaninsu jikinsu ke sanye da sutura ta alfarmar da zaka fahimci rayuwa ta basu sukuni yadda ya dace,saidai tasu salon miqa godiya wa mahaliccinsu da suka munana hanyarta. Daga atamfar jikin hajja har lace din da maahma ke sanye dashi wanda ya darawa atamfar hajjan tsada isashen jari ne ga mutane masu yawan gaske. Kaman yadda jakar maahma din da takalman data sanyawa qafafunta suke wani jarin me zaman kansa ga wasu mutanen. Takalmin da fu'ad din yayi mata order dinsa da kanshi tun daga qasar Italy. Kusan yadda ta bawa mutumin dan duqurqushi me zubin wada hankalinta hajja bata bashi nata haka ba. Daya daga cikin qoqunan gabansa da suke kife ya daga,qoqon da babu komai amma saiga haske ya cikashi. Tafukan hannayensa ya saka yana rufe qwayar da hannunsa nasa. Idanunsa ya runtse,wasu irin maganganu ya dinga furtawa da ba'a gane abinda yake fadi,tun yana fada a hankali a hankali har ya fara furtawa da sauri da sauri da kuma qarfi har muryarsa tana amsa kuwwa. A hankali jikinsa ya fara wani irin kakkarwa tamkar wanda aka jonawa shocking. Da wani irin sauri yan fusge hannayensa daga saman qwaryar yana yarfar dasu kamar wanda wuta ta taba,sai kuma ya sake maidasun yana canza salon yaron da yakeji ba irin na dazu ba. Ya kusa minti biyu a haka,wata irin zufa da basusan daga ina take ba ta gama jiqeshi sharkaf.....a hankali a hankali ya soma sassauta muryarsa sannan ya fara daidaita yanayinsa kafin ya bude idanunsa da suka ninka ja akan asalin jan da suke dashi. "Matso!" Yace da maamah a tsawace. Tsoro ba kalma bace da ta santa ba kaf ray uwarta......qafafunta sun taka gurare da dama amma a yanzun saita samu kanta cikin shakka da d'ar d'ar har ta matso zuwa inda yake mata nuni "Ba shine wannan ba?" Ya fada da qarfi yana nuna mata qoqon. Fu'ad ne kwance saman gadonshi yana baccinsa hankali kwance kaman yadda ya kwanta a ainihin dakinsa dake gidan Alhaji hamza kibiya. Mamaki ya qarasa cikata,ba shakka fu'ad ne,kuma dakin ya mata kama da dakunan gidan Alhaji hamza,sun dawo kenan kaman yadda yake shaida mata dazu da sassafe kan suna hanya?. Daga ita har bokan ba wanda ya samu cewa wani abu dif hoton dake cikin qwayar ya bace kaman an dakeshi harda tartsatsin wata wuta. "Kin gani ko?,ba mutumin da muka sha wahalar kawoshi zuwa garemu saishi......baya ga haka kinga yadda surarsa ta dauke da gaggawa......abinda ke bamu tabbacin aikinsa yasha banban da dukka ragowar aiki da muka taba yi a baya......akwai tashin hankali......akwai wahala.......akwai kuma qalubale!!!" Ya furta da kakkausar muryarsa mara dadin amo da sauti bare sha'awar saurare. Dukkan kayan aikin nasa ya tattara ya zuba cikin qwarya daya daga cikin qorai biyu dake gabansa,take suka bace bat tamkar ba'a taba halittarsu ba a wajen. Jajayen idanunsa da babu rahama,musulunci ko imani a ciki ya daga ya kalli maamah dake dubansa babu ko qiftawa. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 54 Idanu yadan zuba mata na wasu mintuna da har sai data dan sha jinin jikinta. Sai kuma ya saki wani busashen murmushi da yafi kama da kukan jaki yana kallonta "Ba shakka kin haifi jarumi......kin haifi yaron da taurarinsa suke da tsananin hasken da ba kasafai ake samun galaba ayi kutse a cikinsu ba ko asha kansu.......yaronki yana tattare da abubuwan al'ajabi da baiwarwarki masu yawan gaske wadanda ko ke uwar da kika haifesa bakisan yana dasu ba......cikin mutane dubu guda daya ake iya samu irinsa......". Kai kawai take jinjinawa tana sauraronsa. Tun sanda ta haifi fu'ad din tasan daban yake da sauran yara,to amma a yanzun kalamansa daga mata hankali sukeyi,kamar sunason shinshina mata rashin nasararta ne......kamar suna shinshina mata rashin yiwuwar aikinta?. Maganarsa ta gaba ta bata amsa ta kuma yanke mata dukkan zatonta "Aiki a kansa ba qaramin abu bane me girma......akwai tsari a jikinsa......yana da addu'a sosai tare da kare kowanne abu da musulunci yayi umarni akai.....baya shan giya.....baya zina.......baya kallace kallacen abubuwan haramun......hasalima azumin da addininku yace a dinga yi litinin da alhamis baya wuceshi.....abinda zai bada mamaki banda wannan uwar goyon nasa da uban goyonsa ba wanda yasan yanayin wannan azumin koda farouq makusancinsa......." "Kana nufin yanzu mallakar da nakeso ayi masa.....da shiga tsakaninsa da iyayen goyonsa bazai yiwu ba kenan?" Ta dawo dashi zuwa ga ainihin amsar da takeso taji. "Zaki iya samun biyan buqata.....zaki kuma iya samun faduwa......biyan buqatarki ya ta'allaqa da adadin sadaukarwar da zakiyi da kudaden da zaki ajiyewa shaqiqanmu don suyi miki yadda ya dace......amma fa....." Ya fada yana daga yatsa "Tabashi abune da zai iya zuwa da hadari......mafi qarancin sakamako shine a gaza yin nasara a kansa......muddin rashin nasarar ta zarta haka kuwa.....dani da dukkan wani shaqiqi da mukayi aiki dashi zamu iya samun nakasa,harda shudewa daga rayuwa ma idan ta dauro,saboda haka......aikinki aikine me tsadar gaske " Yayi maganar yanayin muryarsa daga qarshe yana canzawa alamu dake nuna saukar mutanen boyen da yake aiki tare dasu a kansa. Tsoro yadan shigeta kadan amma ta dake "Kamar nawa zai kai?" Ta fada a dokance "Kalli nan!" Taji an furta daga bakin mutumin amma da mabanbantan muryoyi marasa dadi da batasan mutum nawa bane suka hadu suke maganar. Waiwayawa tayi tana duban inda ya daka,saiga lambobi a jere wanda data dubesu da kyau suka bayyana kansu a matsayin million goma. Sosai adadin ya daketa,duk da tasan a qa'ida tana cikin arziqin data bawa wannan adadin baya amma kuma batakai ga samunsu ba zuwa yanzu. Ta waiwaya ta kalli hajja dake zaune tana kallon komai,don dokarsa shine me matsala dashi yake magana. Da idani ta mata tuni da tsarinsa,baya yanka kudi a nemi ragi.....daya daga cikin kusakuren da zaka iyayi wanda zai tunzurashi kenan. Kamar wadda wuyanta ya qage ta maido dubanta gurin,saidai zuwa sannan lambobin da hasken da suka nuna mata yawan abinda zata biya din ya shafe daga wajen ba komai. Ta maida kallonta ga duqurqushin bokan da kamanninsa suka juye,saita gyada kanta "Na karba na aminta" "Karki qara minti daya a wajen nan......kizo da sadakin aikinki kuma nan da kwanaki uku kacal" Daga haka ya bace shi da dukkan sauran tarkacen dake wajen,sai gurin ya rage daga ita sai hajja din. Zumbur suka miqe kaman yadda ya umarta,suna riqe da hannun juna suka fara fitowa daga sarqaqiyar har suka cimma inda suka faka motarsu. Sau biyu hajja tana juyawa tana kallon maamah wadda ta kafe kwaltar da driver ke zabga gudu akai. Tunda suka fito daga wajen bata ce komai ba,magana bata hadasu da kowa ba. Tun a dazun ta fahimci tayi nisa ne qwarai a tunani,kaman ta qyaleta amma sai ta kirayeta don tanaso taji ta bakinta "Banji kince komai ba tunda muka fito?" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta dora idanunta akan na hajja din "Daga yanayin ayyukansa,da kuma bayanansa kawai na gamsu cewa aikinsa me zafi ne......abinda kawai ya tsayemin a rai yanzu shine ta yadda wadannan kudaden zasu samu" Tayi maganar alamunta suna nuna lallai lallai a matse take da buqatar mafita "Danki ne,dole ki bashi umarni yabi don babu wata uwa sama dake......idanma hakan bai yiwu ba,cikin kadarorinki ki saida wani abu.......ko kice masa wasu zaa yiwa wani abu da kudin da zarar yasa anyi abun ki saida abun kiyi zarafin gabanki". Ajiyar zuciya ta sauke ranta yana mugun baci "Yanzu har takai idan ina da buqatar abu a wajen dana saidai nayi qarya ko na biyo ta wata hanyar?" Ta yiwa hajja tambayar. "Biyan buqata ai yafi dogon buri,kome ya faru.....kuma kome kika saida,wuyarta aiki yayi yadda akeso......sai kin maida ninkin baninkin da bakisan adadinsa ba......sai kin karba kin gaji......saikin tara fiye da yadda kike buri......saikin zame musu tamkar abun bautarsu wajen yi miki biyayya.....a yanzun da zan kira auwal dake wata qasar,nace masa ya dawo nigeria yau yau inason ganinsa.......na rantse miki da Allah a qasar nan zai kwana,koda babu jirgi bazai kwana a gida ba saidai a airport.......saidai idan nice nace masa ya koma gida ya kwanta ya taso gobe......koda ya koma bashi da cikakken nutsuwa har sai gari ya waye ya kawo kansa gareni......bari yau zan nuna miki qarfin ikona ki gani da kanki" Ta fada tana fiddo wayarta daga jakarta. Kai ta jinjina kawai tana dubanta,tana jin inama ace itace hajja?.....tana hasashen ranar da wannan damar zata samu a hannunta?.....tabbas saita sanya aminatu kuka da idanunta........sai ta sanya zuciyar aminatu da hamza sun buga da qasqancin da zasu gani daga yaran da su suka rainesu har suka zama abinda suka zama a yanzu (Tabbas gaskiya ne da akace ka guji sharrin wanda ka kyautatawa.......me makon jin dadi kyakkyawan fata da kyakkyawan mu'amala ta shiga tsakaninsu da mutanen da suka maida mata 'ya'ya mutum.....amma ga nata salon sakamakon,Allah kayi mana tsari daga sharrin dukkan wani abu me sharri mutum ko aljan,me rai ko maras rai ameen ya hayyu ya qayyumu). Bugu daya tak aka daga kiran da hajjan tayi,muryarsa ta fito tarwai yana gaidata. Cikin kulawa ta amsa masa sannan tace "Kaga yahaya.......naje unguwa ne sai na sallami driver da xummar zan tuqo kaina na dawo gida......." "Me yasa hajja?,ta yaya zakiyi tuqi da kanki?" Ya fada a tsananin firgice kaman wanda akace masa ta hallaka. Murmushin qasaita ta aje "To ai yanzu ma gashi na kasa dawowa din da kaina duk kasala ta rufeni...." "Bari na kira driver din ya dawo ya maidaki" Ya furta da hanzari "Kaga dakata.....wanne irin driver?" Ta fada tana bata rai "Yi haquri hajja,me kk so?" Ya sake fada a rikirkice "Matarka nakeso ka turomin ita zata maidani......kace ta kirani na bata kwatancen inda nake yanzu haka ina jiranta......kada kuma ta batamin lokaci" Ta fada tana bata rai "An gama" Ya fada zuciyarsa na rawa. Ta rigashi ajiye wayar ta waiwaya tana kallon maamah cikin murmushi "Kinsan matar da nace a kiramin?" Kai maamah ta girgiza tana shakkar yiwuwar wanzuwar umarmin da hajjan ta bada yanzu yanzu "Matarsa ce......itace taso dagamin yatsa taso tayi fito na fito dani,a zatonta tana da malaman da xasuyi mata aiki fiye da nawa......tanaso ta mallaki yahaya ta mallakeni.....har na sanya ya saketa na sakashi ya dawo da ita don tazo taga iyakarta......taga iya mizanin nawa aikin.....don tazo ta banbance tsakanin aya da tsakuwa,ta sake kuma fahimtar da gaske fa shi ruwa ba sa'an kwando bane......ita kanta a yanzun sai yadda nace mata,duk dana fahimci kanta yana fusga wani lokaci kaman wasu abubuwan idan nayi mata tana jin ciwonsu,shi yasa nakeson na qarasa horata da kyau" Kai kawai maamah take jinjinawa,abun yayi mata da kyau.....salon kuma ya burgeta yahau mizani da gwargwado na abinda take hasashen shimfidawa kanta. DA FUAD DA MUSADDIQ DAMA MATAYEN DA ZASU AURA SU ZAMA QARQASHIN IKONTA. wannan shine cikakken iko da isar UWA. Ta fada a ranta "Wannan shine cikakken iko da isa.....ki katange komai kaman yadda sanda kk sha wahalar komai din ke daya kk sha" Hajja ta fada tana jinjina kai "Indai ni na haifi fuad ya zama tilas ya fidda kudaden nan ya bani.....zan motsa masa qwanjina.....zan kuma banbance masa uwa da mahaifiya a wannan lokaci karo na farko" Maamah ta sake fada a ranta. Ya jima riqe da wayar bayan gama waya da mahaifiyar tasa yana juya wayar a hannunsa. Sassa biyu na zuciyarsa kowanne na qalubalantar dan uwansa. "Tayi daidai,ko mutuwa hajja tace muyi daidai ne......ai ta isa....girmanta yana da yawa,to laifin me ma tayi?,koni ta kira zuwa zanyi bare matata,komai tayi a kowanne lokaci ko yanayi daidai yake" Daya sashen yake fadi,yayin da daya sashen zuciyarsa yake cewa "Ta yaya tana tsaka da hidimar gida,ya tabbatar yanzu haka tana can tana yiwa hajjan girkin rana daya zama wajibi aka kowacce matar danta tayi mata shi kulli yaumin rana da dare ba fashi......(tsarin girkin abincin gidan tsarin girki ne na bai daya,duk da irin girma da wadatar gidan tukunya daya ake dafa abincin safe rana dana dare,raba girki ne a tsakanin faccaloli tamkar kishiyoyi,kowacce zatayi kwana biyu 'yar uwarta ta karba,hakanan a tattare a babban dining room dake dauke da family dining table akecin dukka abincin. A nata fadin don a tattala mata dukiyar 'ya'ya,kuma dukkansu zasu samu sauqin kashe kudi a gidajensu,tunda kome zaa siyo hadin gwiwa zaayi a kawo......amma kuma ta gefe daya.....tsabar nuna isa izza da mulki ne,da kuma dabarar karantar motsin kowa cikin gidan ba tare data shiga sashen kowa ba don ta tattaro kowa din waje daya. A yanzun ya tabbatar tana can tana wannan hada hada.....bama wannan ba......fita haka katsam a lokaci guda ba shiri?. Wannan sashen dake hango masa rashin dacewar shine sashe mafi rauni a zuciyarsa,don haka wancan bangaren ya rinjayeshi ya danna mata kira kanshi tsaye. Sanda maamah ta bude baki da zummar sake magana kira ya shigo wayar hajja. Ta daga wayar tana kalla,sai ta sake wani murmushi me sauti "Naja'atu ce" Ta fada cikin nishadi,saita daga wayar tana sanyata a hands free "Salamu Alaikum hajja......daddynsu arfat yace kina buqatar nazo daukarki......kina daidai ina?" Fuska ta tsuke tamkar ba itace ta gama dariya yanzu ba "Ke banason hauka......haka akeyi daga kiran waya ba gaisuwa ba komai?,duk kinzo kin gaidani dazu da safe amma yanzu mecece?,la'asar fa muke dosa?" Shuru yadan biyo baya kafin muryarta ta sake bayyana a karye "Kiyi haquri,ina wuni?.....kin yini lafiya?" "Lafiya lau" Ta furta a dake "Ina 'yan kaba,kizo daidai bakin kasuwar turawa ki jirani" Daga haka ta katse wayar. Dubanta maamah tayi tana mamaki "Hajja me kuma zai kaimu 'yan kaba?,ai sam ba hanyarmu bace" Zamanta ta gyara tana sake sakin shu'umin murmushi "Eh mana.....ai so nake ta sake gane girman izzar tawa......sai bayan mun isa gidan ki zaki fahimci sauran aikin". Sosai maamah ke duban hajja din,lallai dole tasha kan kowa da komai,dole ta murxa kambunta yadda takeso. Sai yanxu take tambayar kanta ya akayi tayi sanyi haka ta sake?,hajjan da a baya a wajenta take daukan courses na abubuwa amma yanzu nema take ta zama malamarta qarfi da yaji?. "Kina mamaki ne mariya?" Ta tambayeta tana kallon hanya "Ai duk wanda yayi bacci a wannan zamanin zaiga bacci.....ba yara na ba ba surukaina ba.....hatta da jikokina.....yara da manya dukka sai abinda hajja ta shimfida"........ Ji yayi tamkar an daka masa tsawa tsakiyar baccinsa ana kuma masa umarni da ya farka. A nutse ya farka saidai kuma yanajin wani irin sauti mara dadi yana amsa kuwwa cikin kunnuwansa tamkar dai a mafarki akayi masa tsawar. Idanunsa ya lumshe a hankali yana son tuna abinda ya faru din,amma kansa blank bai iya hasaso komai ba "Hasbiyallahu la'ilaha illa huwhuw,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya furta a hankali bakinsa yana motsawa. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 55 Tsam yayi da ransa yana jin yanayin jikinsa yana sauyawa daga ainihin yadda ya kwanta din a dazun. Numfashi ya aje a hankali ya yaye blanket din ya miqe,ya zauna sosai saman gadon. Duk da knocking din da akeyi din hakan bai hanashi hada hannuwansa guri guda yayi addua ba,ya shafa saman fuskarsa a nutse sannan ya zuro qafafunsa qasa ya miqe. A nutse yake takowa zuwa ainihin falon nasa dake cike da nutsuwa,shuru tamkar ba cikin gidan yake ba,komai komai cikin matsananciyar tsafta a killace kamar yadd yakeso koda yaushe ya dinga ganin komai a hakan. Yana ci gaba da jin jikinsa da wata 'yar maqalalliyar kasala har ya isa qofar falon,ya murza key ya bude qofar amma bai murza handle ba,ya barta a haka yana komawa da baya hadi da bada umarnin a shigo. Tun bai zauna ba ta sako qafafunta falon,dauke da wani kyakkyawan kwando me qananun tayoyi,yana da mariqi tamkar na luggage ko trolley da zaka iya rageshi ko ka qarashi sannan ka jashi yadda kakeso. Da sallama a bakinta da qanqanuwar nutsuwar nan da take samar da ita a gabansa. "Wa'alaikumussalam" Ya amsa yana zama saman daya daga cikin qawatattun sofas din da suka yiwa falon qawanya masu tsananin taushi da kyau na gaske,yasa hannunsa yana lalubem remote na A.c din falon don ya rageta. Shi din ba kasafai ya fiya son ac ba ko ya qureta har haka ba,wannan din sai oga farouq,a nan ma zaka iya jin kansa dashi. "Hamma barka da warhaka". Ta fada cikin shagwabarta da marairaitar nan tata data zama a halittarta. Labbansa ya motsa kadan da wani yanayi da yafi kama da murmushi "Habibtyn hamma" Ya furta a nutse kaman yadda tsoron qarewar haruffan bakinsa. Sunan daya kiratan dashi ya sanyata ta sake rakwarkwabewa. Ta tabe fuska tana kallonsa "....hamma na dauka ka daina yayi na......BB farouq yacemin ka samo wadda ta sace zuciyarka.....tunda ta sace zuciyarka wai kuma tayi snatching naka a wajen kowa....she owns you ita kadai". Qaramin murmushi ya sake subuce masa wanda yafi na baya. Rigimar amna yawa ne da ita,har yau bata girma baisan kuma sanda zata girma din ba,yafi tunanin aure ne kawai zai kawo mata wannan hankalin da girman. Gefe daya farouq,shikam a duniya yanaso yaga ya tubura amna din,wani lokacin yana yi ne kaman hankalinsu daya,abinda kuma bazai taba zama hakan ba "Zo nan" Ya fada yana yafitota da hannu gami da nuna mata gefansa. Sai ta tako din a hankali ita da kwandon nata har ta iso gabansa ta zame ta zauna sosai "Baki gaya masa tare zaku zabi mata da hamma ba?,baki gaya masa sai wadda kikace tayi kinaso sannan hamma ya aura ba?" Yayi mata tambayar yana kallon qwayoyin idanunta abinda ya qara mata karsashi da qwarin gwiwa. Murmushi ya subuce mata data tuna da wannan "Na gaya masa hamma sai ya tabe baki,kasan me yace?" Kai ya girgiza yana qara girmama quruciyar amna din,tabbas auta ba wasa ba,ko yaya sai wannan quruciyar ta tabashi "Wai ita soyayya ba ruwanta da jiran lokaci ko dacewa,sace zuciya takeyi ko an shirya ko ba'a shirya ba....." Ta qarasa maganar daidai sanda farouq din yayi knocking hadi da turo qofar yashigo gaba daya,don yaji muryarta alamun suna zaune daga falonne. Tsaf kalaman nata da suka fito daga bakin farouq din duka zauna masa akai,sai ya daga kai yana dubansa sanda yake takowa falon. Ya bude baki zai fara mata tsiyan nashi fu'ad din ya tari numfashinsa "Kai kakeso ka lalatamin kunnuwan qanwa?.....kai kake karanta mata yadda soyayya take ko?". Wani dariya ya saki yana saka hannu ya dauki green apple guda daya cikin apple din dake ajiye cikin wani dan kwando nan saman fridge din dake kusa dashi yana takowa falon "Har yanzu kallon jaririya kuke mata ba?.....zakusha mamaki sanda ta kawo wani tace itace shi takeso,aure takeso kuyi mata". "Hamma....." Ta fada idanunta suna yin rau rau tana duban fu'ad. Hannu ya daga mata alamun tayi shuru kada tace komai,sai ya maida dubansa ga farouq din "To sai me?,idan ta fada dinma ai daidai ne". Yana zama a gefansa yace "Ni zanfi kowa murna da hakan ai......tashi ki bamu waje" Farouq din ya fada yana komawa serious dinsa. Duk sanda yayi irin hakan ta tabbatar Lokacin wasa ya fita kenan,don haka bata musa ba ta tsugunna tana rage plates da bowls din da tasan fu'ad ya gama amfani dasu saboda ta sanshi bai fiya son tarkace a waje ba,yanzun saisu sanyashi fasa cin abincin gaba daya. Spoon ya dauka kawai ya saka a plate din fu'ad din bayan fitar amna,wannan din ba wata sabuwar dabi'a bace,kusan sun saba cin abinci kwano daya,tun daga wancan lokacin da suke fafutukar rayuwa da samarwa kawunansu 'yanci,har zuwa yanzun da suka zama cikakkun mutane kuma 'yantattun 'ya'ya. A nutse suke cin abincin kuma ci gaba da tattaunawa akan tafiyar tasa. Har suka kammala basu tashi a gun ba,sai da kiran anni ya shigo masa waya. "Ka shiga wajen maamah kuwa?" Tambayar data fara yi masa kenan "Zan shiga dai anni....." "Kome kake ka barshi,ka shiga ka gaidata tasan da dawowarka" "In sha Allah anni" Ya fada a nutse,sai ta katse wayar shima ya sanya hannu yana sauka daga bangaren kiran gami da fidda siririyar iska daga hancinsa. Miqewa farouq yayi abinda ya sanya fu'ad din daga kai daga zaune ya kalleshi. Kafin yakai ga tambayar shi ya rigashi magana "Na jima ban shiga abuja ba,ina jin gobe ko jibi zan shiga din......." "Safe journey" Fu'ad din ya fada a taqaice yana miqewa shima. Siririyar dariya farouq din ya saki yana tsare fu'ad din da ido wanda alamu ke nuna yana Neman hanyan wucewa ne daga wajen "Kar muyi haka dakai.....karka canza kuma daga yadda na sanka......ko da da sau daya baka taba yimin kara ka rakani wajen fannah ba.....kayimin alqawari next time idan na tashi zuwa tare zamuje......." "Yanzun daga daukomin dogon sharhin nan farouq.....cewa nayi bazani ba?.....kawai dai kasan ba abu bane me sauqi gajimare ya gama yawo dani na sake komawa wani tsakanin kwana daya ko biyu kawai......infact ma kasan yanzun shirye shiryen dake gabanmu ai.......ba cikakken lokacin batawa a irin wadannan abubuwan.....but duk da haka bazan karya alqawari ba.....if zaka iya jirana na kammala sai muje din". Dariya ce taso qwacewa farouq din amma ya maze,ya san dama zaa rina,kuma wannan dogon bayanin da yakeyi duka yana neman hanyar guduwa yaqi zuwa ne. Bai taba ganin mutumin da soyayya bata taba burgeshi ko d'ad'ashi da qasa ba ko yaya takai ga bawa jama'a sha'awa ba irin fu'ad din. Bawai ya tsani mata bane......aah......amma yadda yake nesa qwarai da al'amuransu kai tsaye idan kace bai jituwa da shirginsu bakayi laifi ba. "Kanka tsaye kacemin yanzun ma ba zakaje ba.....kacemin ka shirya nunawa fannah iyakata....ni din ba kowan kowa bane a wajenka" Ya fadi yana hade rai sosai idonsa akan fuskarsa. Kallon idanun farouq din yayi,bai wani damu ba yasan halin kayansa sarai,yasan ya fada ne don ya motsashi,don haka ya daga kafadunsa "Ka fada soyayya ne at wrong time......har yanzun kana da sauran lokaci da ya kamata ace kana gina kanka ne bawai soyayya ba......ita soyayya idan lokacinta yayi zata kawo kanta da kanta" "Kaiii.....inaaa......a wannan lokacin da mutum ke bacci da qyar?,am against you fa har abada indai ta nan wajen ne.....kaidai da waccan aljanar tayi maka shigar sauri zamu ci gaba da nema maka magani......" Bai qarasa ba yaji saukar spoon a kafadarsa,ya goce spoon din ya fadi qasan marbles,sai ya soma sauka daga dining area din yana dariya abinsa gami da cewa "Tafiya abuja dole ce......zan siya ticket harda kai......alfarma daya zan maka zan daga zuwa next week cikin weekends din" Yana kaiwa nan ya fice abinsa daga parlor din. Kai kawai ya girgiza yana murmushi qasan zuciyarsa. Bazaice ko sau daya ga sanda suka taba samun sabani da farouq ba ko wani ya bata ran dan uwansa. Wani hadi ne daga buwayi gagara misali,idan kaga musaddiq da Sadiq zakayi tunanin sune uwayensu daya,kaman yadda da yawa ake tunanin shi da farouq din twins brothers ne da suke da kamanni daban daban. Baiyi mamakin jin ba ruwan zafi a toilet kaman yadda ya saba samu koda yaushe ba,don dukka ma'aikatansa da sauran masu masa hidiman sassansa ya basu hutu na satittikan tafiyarsa south Korea,don haka ya kunna heater ya dawo cikin bedroom din sannan ya wuce kai tsaye yana fita daga ciki. Qofa ce qwaya daya tak wadda batakai duka sauran doors din falon fadi ba,ya budeta ta hanyar key din dake maqale a jiki ya turata a hankali ya shiga. Dakin yana da dan duhu don haka ya laluba makunni ya kunna fitila take haske ya gauraye dakin *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 56 A yadda qofar dakin take daga waje,ba zakayi tsammanin taras da yalwataccen daki me wani irin tsari da kyau ba kaman haka. Ci gaba yayi da kunna kowacce fitila ta cikin dakin,kama daga ta bango zuwa kyawawan table lamps masu wani irin kyau me daukan hankali. Wani irin guri aka tsaga daga sashen nasa da yayi Linkin da ainihin farfajiyar gidan bangaren da duk yawan taro ko hayaniyar jama'a da gidan zaya tara zaiyi wuya ka iya jinta muddin kana wajen. An qawatashi da wasu irin shelves da drawers masu mugun kyau da daukan hankali da aka tsara takardu documents zuwa litattafai nau'i daban daban daga yarukan duniya daban daban da yake iya fahimta yake kuma iya magana da wasunsu. Ragowar bangunan kuma manyan frames ne masu asalin kyau da tsada na qasar turkey da dubai da aka kashewa kudade masu ciwo aka tsara sunayen Allah da ayoyin qur'ani masu girma da wani irin ruwan gold daya sake baiwa frame din kima kyau da daraja. Akwai kyakkyawan table din daya zama cikon ado wa home office din nashi da yake hade da kujerarsa,sai kuma wasu cushions da aka zuba gajajjeru da ba zasu bata tsarin wajen ba,daura dasu kadan kuma wani board ne dake dauke da rubuce rubuce barkatai da baya rasa alaqa da tsare tsare na abubuwan da ya sanya a gaba zaiyi. Komai na room din neutral color ne kaman yadda dayan bedroom dinshi yake,abinda zai bayyana maka kenan normally bayason kaloli masu hayaniya can can can. Da gaske a yanzun target dinsa shine bude kamfanin......babban burin da a yanzun bashi da wani sauran abu daya rage masa kamar shi,saidai abune daya tabbatar yana buqatar qarin jajircewarsa da kuma aiwatar da komai cikin sirri har sai an kai gabar da ya kamata komai din ya bayyana. Ba alaman qura ko datti ko qwalli daya,don duk wanda ke aiki dashi yasan tsarinsa da kuma dokarsa. Waje ne da ba wanda yake bari ya shigar masa sai family dinsa,anni farouq amna saddiq sai musaddiq......sai kuma amintaccensa mutum guda daya me sunan malam. Ya bude lockers da yawa,ya kuma jona abubuwa da yawa kafin ya daidaita komai ya juya yana fita a dakin da zummar zuwa sanda zai dawo komai ya zama normal,don yau din aiki yakeson yi sosai kafin ranar Monday ya isa kamfani ya duba yadda ya barsu. Fes ya fito a shirye,sanye da lallausan yadin filtex fari qal mai qarancin nauyin da har kana iya hangen farar vest din jikinsa data lafe takuma saje da yadin sosai saboda tsananin haskenta. Sassanyan qamshin nan nasa dake da daukan hankali yake fitarwa sannu a hankali,fuskarsa tayi fresh cikin yanayin da zai nuna maka cikakkiyar nutsuwar zuciya da ruhi da yake da ita. Sabanin wasu lokutan,yanzun kanshi saye yake da hular data dace da yadin jikin nasa,sai half covers din daya sakaye doguwan qafansa a ciki. Komai rashin nisan waje bazai taba iya taka qafarsa ba tare da ya sanar da anni ba,yanzunma sassanta ya bulla,yana tafe yana amsa waya har ya cimma sassan nata. Bai iya ci gaba da amsa wayar ba sanda qafafunsa suka shiga ainihin falon,sai ya zare wayar daga kunnensa sakamakon sautin karatun qur'ani dake fita daga speakers din dake daura da qatuwar plasma din dake girke saman mulmulallen tv stand din. Karatu ne cikin muryar babban malaminsa sheik abdurrahman assudais,qira'ar dake balain kashe masa jiki tare da saukar masa da nutsuwa koda yana cikin bacin rai. Falon anni na dabanne,badai ka shigo ka samu ana kallace kallace marasa ma'ana ba bare akai ga batun jin kida ko waqa,kusan duka haka ta azasu akai,suma kuma haka suka taso. Lokaci irin wannan magariba ke kan hanyar qarasowa,zaka sameta zaune cikin kamala tana wani abun da zaya amfani lahirarta,imma girkin abba ita da amna,ko ka sameta da carbi,ko tana sauraren wani karatun addinin. Yanzunma suna tare da amna din,wanda daga gefan amnan kadan wata baquwar matashiyar ce da zata girmewa amna din da aqalla shekaru biyu ko uku. Yana shigowa ta sanya remote tayi qasa da karatun sosai tana murmushi. Ya qaraso a nutse ya zauna daga gefanta yana tanqwashe qafafunsa tamkar ba wanda yayi shirin fita ba,sai kuwa ta tareshi "A'ah miqe....ai sai ayi magariba kana zaune a nan.....kaje ka dawo.....don abincin dare ma yau banda kai a gidan nan" Girarsa duka biyun ya daga alamun mamaki,yanayin daya qarawa fuskarsa wani irin kyau,ya kuma fusgi hankalin matashiyar qwarai da gaske "Anni yau din nayi wani laifi ne....?" Ya fada calmly idonsa akan annin. Kai ta girgiza "Ko kadan......kawai nasan idan kayi dinner a daya gidan naku hakan zai farantawa maamah sosai,zai kuma sake bada fahimtar juna da shaquwa a tsakaninku". Tayi maganar cikin kwantar dakai itama tare da fatan kaishi zuwa ga abinda takeso din. Kansa yadan motsa kadan,har yanxu anni kaman bata fahimci daga ina ainihin tushen matsalarsu ya fara ba?,har yanzu kuma kamar annin bata fahimci menene yake riqe da matsalar tare da sake wanzar da ita ba?,wanne fahimtar juna da shaquwa a yanzun ake nema tsakaninsu ne?. "Saika dawo......kace ina gaidata" Ta fada tana daukan remote zata qara volume,abinda ke alamta masa ta gama fadin bayaninta kuma batason yayi sharhin komai akai "Hamma....." Amna ta kirayi sunansa tana murmushi idonta a kansa. "Lovy dovy" Ya fada yana xuba hannunsa a aljihun rigarsa yana jin karsashinsa da duk wani walwalarsa yana ja baya tamkar wanda aka tura gidan kaso. Murmushi tayi,tsokanarsa takeso tayi amma kwarjinin nan nasa ya taso ya danneta "In fada hamma?" Tayi masa tambayar tana dubansa "Say it amna....." Ya maida mata cikin caring din daya kusa sanya matashiyar narkewa. Bata taba zato koda a mafarki yana da wannan siffar ta kulawa haka ba......bata taba hasashen akwai dabi'a ta sauqin kai a tattare dashi har haka ba "Muhammadu.......yi tafiyarka......ku wuce ciki keda unaisa ku wankemin bottles dinnan,suna kitchen basu da yawa". Duk da yaso ya wuce din kamar yadda anni tace amma dole sai daya dan tsaya a farfajiyar gidan suka gaisa da ma'aikatan gidan,sannan kuma me sunan malam yayi masa tattaki suka fice daga gidan bayan ya shaidawa security dinsa ba nisa zaiyi ba baya buqatarsu. Yana takawa a nutse yana sake fuskantar gidan wani yanayi yana riskarsa,abubuwa masu tarin yawa da suka saba dawo masa a duk lokacin da zai gifta ko ya shiga gidan.....al'amura masu nauyin dake iya motsa zukata qwarai da gaske. Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya yake janye jiki da rayuwarsa sosai daga gidan. Duk da komai na fasalin gidan ya canza,ba wani abu da yayi saura dangane da ainihin ginin gidan na baya,to amma dai wannan filin....wannan gurbin da wannan muhallin da aka aza tubalin ginin gidan har yanzu dai shine a wajen. Har yau har kwanan gobe idanunsa basa mantawa da tsarin gininsu na asali,wannan ya sanya idan ya kalli wasu guraren sai ya tuna da JADDA sai kuma ya tuna da ABBANSA,duk da guraren a yanzun sun sauya sun koma wasu abubuwan na daban,amma tambarinsu yana nan kafe qasan ransa da zuciyarsa. Cike da girmamawa,martabawa tare da kallon Cikakkiyar kima da darjtawa malam sa'idu yake miqewa sanda ya fuskanci dosowarshi gidan. "Barka da zuwa yallabai.....sannu da zuwa" Malam sa'idu yake fadi cikin mutuntawa. "Barkanmu da warhaka baba.....mun sameku lafiya?" Fuad din ya furta shima cikin tsananin bada girma. Malam sa'idu bawai me gadi bane kadai a gareshi,yana da wani role da yake takawa da kuma wani ajiyayyen matsayi da fuad din ya bashi ba tare da sanin kowa ba. Malam sa'idun da asalinsa me saida kayan marmari ne a bakin titin tsohon layinsu,wanda a yanzun layin ya koma tacan katangun gidansu yake,qofofin sun dawo bayan gidansu na asali,inda kusan gaba daya fuad din ya siye layin sai tsirarun gidajen da suke mazauna ciki suna da buqatar zama a ciki. Tun asali bayan layin nasu suna kiransa ne dama da layin 'yan gayu,don kusan manyan gidaje ne ata wajen,kamar yadda kusan mafi rinjayen unguwar tasu layinsu ne kadai keda qananun gidaje jifa jifa. To a yanzun layin duka ya zama qarqashin kulawar fuad da wani irin kwalta da aka zuba,gate a farkonsa da qarshensa da manyan fitilu jere reras.....cctv cameras da masu gadin layin saboda tsaron dukiyar mazauna layin da rayukansu. Bayajin malam sa'idu zai iya ficewa daga tarihin rayuwarsa ko zuciyarsa. Yadda mahaifinsa baya iya cin komai haka malam sa'idu zai hada fruit ya bashi daidai qarfinsa lokaci bayan lokaci duk sanda Allah yakai wucewar fuad ta wajen,ana tsaka da haka malam sa'idu yaje ganin gida,bai kuma dawo ba har sai bayan wasu shekaru. Bai manta da yadda malam sa'idu ya nuna jin ciwon rasuwar abbansa ba,wannan ya sanya ko da rayuwa ta kawosu inda suke a yanzun ya nema malam sa'idu. Kyautata rayuwarsa yayi da gasken gaske ba tare da mutane sunsan da hakan ba......amma sai ya ajeshi a mazaunin me gadi bisa shawararsu da amintarsu shi da malam sa'idu din,kuma hakan bai hana ya bashi albashi ba duk wata,saidai ba irin albashin da ake jifan gamagarin masu gadi ba. Malam sa'idu baisan wace maamah ba bare anni,tun a baya wajen sana'arsa yake lazimtar zama,bai tara jama'a bare gulma dayi da gidajen alumma ya shigo ciki har yasan abinda gidan wani ke ciki,abu daya ne dai da har yau bai fahimta ba,jaddada gadin gidan da kula da shige da ficen matar gidan daya kasa tantance matsayinta a wajensa. Da yake bame damuwa da abinda bai shafeshi bane bai taba tambaya ba,yana dai aikinsa yadda akace,duk kuma abinda muhammad din yake da buqatar sani yana sanar masa. "Mu zauna daga nan" Fuad ya fada yana neman wajen zama saman bencin da malam sa'idun kan dan kashingide akai wani lokaci. "Aa haba yallabai.......ai sai ka bata kayanka kuma......bari a dauko maka kujera daga cikin gida kafin mutanen gidan su qaraso" "Yi zamanka" Ya fada cikin ko in kula. Mamaki ya sake kashe malam sa'idu. Duk uwar dukiyar daya mallaka,kyau....ilimi duk basu sanyashi jin ya bambamta da sauran jama'a ba. "Ita kadai ta fita?" Fuad din ya tambayeshi yana zaro wayarsa "A'ah....su biyu ne" Ya amsa masa kai tsaye,don ba tambayar da zaiyi masa da zai boye masa wani abu. Kai ya daga yana duban malam sa'idu din jin ya ambaci ita da wata.....Allah yasa abinda yaketa qoqarin kaucewa da fatan kada ya faru ba shine ya soma faruwa ba "Sun jima da fita?" "Eh ya kusa awa biyu zuwa uku haka" Ya sake amsa masa. Idanu yadan zubawa malam sa'idu din kamar yanason fahimtar wani abu daga gareshi,sai kuma ya janye idon yana fesar da iska daga bakinsa,sai ya samu kanshi da Maida wayar aljihunsa kawai ya miqe daga zaman da yayi niyyar yi da,ya dawo gaban gidan ya tsaya sosai jikin realer da aka yiwa gaban gidan adon flowers da ita,idanunshi bisa hanya zuciyarsa na karanta masa abubuwa iri daban daban. Tun dazun tunani da hankalin maamah yana kan hajja,har zuwa lokacin da mintuna kadan suka rage musu su isa ga unguwar "Yarinyar can fa hajja kin kaita wata unguwar tana jira". Murmushi hajja ta saki da qaramin tsaki a hade "Bari ki gani" Ta fada tana daukan wayarta daga saman cinyarta. A hands free ta saka wayar,bugu daya ta daga. Akwai qaguwa sosai cikin muryartata,amma kuma bata isa ta nuna hakan ba koda da wasa kuwa "Hajja na qaraso" "To yayi.....na bar wajen,zan turo miki address na inda zaki sameni,na gaji gida nakeso na wuce,kada ki wuce minti biyar baki iso ba" "To hajja" Ta amsa mata a sanyaye. Katse kiran tayi,murmushi na subuce mata ta kalli maamah "Yanzu nan zata zo cikin minti biyar?" Maamah ta tambaya cikin mamaki "Kuma mijinta shi zai maidani gidanma a gabanta ba....da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne". A gajarce ta tura mata adress din,sannan ta fara qoqarin kiran yahaya daidai sanda suke karyo kwanar da zata sadasu da shimfidadden jadda street din dake rubuce jikin wani qaramin allo dake kafe a farkon layin. Tunda ya hangi motar ya ganeta kafin takai ga isowa. Yaci gaba da bin motar da idanu har ta qaraso qofar gidan,tayi kuma yi tsaiwar bawa malam sa'idu umarnin bude mata hanyar shigewa,sai a sannan ya sauke hannayensa yana duban tayoyin motar da sukayi bududu abinda zai shaida maka ba qaramar tafiya akayi da motar ba,tafiya me tsaho kuma cikin guraren da basu da shimfidadden titi ya saka kai yana wucewa ciki kafin malam sa'idu ya kammala bude musu gate din. Kansa a qasa yake takawa cikin gidan,haka kawai zuciyarsa yakejin bai gamsu da yanayin fita da kuma shigowar motansu a yanzu ba. Cikin falon ya yiwa kansa gurin zama. Ba kowa a ciki,don dama muddin idan bata nan din bata aminta da masu aikin nata su kusanci falon har sai ta dawo. Tun tsaiwarsu bakin gate din ta ganshi,wannan ya sanya driver yana aje motar qasan rumfar aje motocin ta bude ta fito "Ya da sauri haka ko duk gajiyar ce?" Hajja ta tambayeta sanda take tattaro jakarta "Yaroncan Muhammadu na gani,yana ciki yana jira,bansan tun yaushe ya shigo gidan ba.....banyi zaton jirgin safe zasu biyo ba" Ta fadi hankalinta yana yin cikin gidan. Da kallo hajja tabi maamah din ganin yadda duka hankalinta yayi cikin gidan,sai kawai ta jinjina kai ta soma yunqurin fita a motar itama tabi bayanta. Qafafunsa na harde cikin juna yayin daya jingina bayansa da makarin kujerar,ya zube idanunsa duka a bakin qofa yana jiran ganin shigowarta. A wannan yanayin ta murda qofar ta shigo,tanata qoqarin azawa fuskarta rashin sukuni da gasken gaske. A wannan karon batajin zatayi masa da wasa akan dukka buqatun da zata bijiro masa dasu.....dole yayi yadda takeso wanda shine zai zama cikamakin burin MALLAKAR 'YA'YANTA. Duk yadda taso tayi diban watsin tsiya dashi amma sai kwarjininsa yakeson bugar da ita. Hausawa sukace kuma wanda yayi me kyau ya sani haka wanda yayi maras kyau. Idanun da yake binta dashi sai ta dinga jin kamar yanason karantar daga ina take?,me kuma taje yi?. "Sannu da zuwa" Ya fada a nutse yana zare qafafunsa daga cikin na juna daidai sanda take aje mayafinta da jakarta "Ai kaine da sannu" Ta fada a taqaice tana ta tattalin fushinta da bacewar fara'a daga fuskarta,saidai kuma wani bangaren na zuciyarta yanata saka mata tsarguwa da kuma shakku. Hada ido sukayi a karo na uku,sai ta kasa jurar kallon da yake binta dashi din "Kana mamakin na baka umarni baka bi ba kazo na sameni a raye ban mutu ba ko?" Ta fake da wannan,don batasan da abinda zata iya qalubalantar kallon nasa dake mata wani irin nauyi da kwarjini ba. Idanun nasa ya sauke a qasa yana girgiza kansa,baikai ga cewa komai ba ta sanyo kai da tata sallamar. Ita dinma dashi suka fara hada idanu,saidai nata kallon yafi na maamah tsini a nata idanun da zuciyar. Kwarjininsa ya cikata fal,hakanan alfaharin ganin farko wa mamallakin jadda diamondchore resources ya cikata. Sunansa ya jima da shiga kundin nata lissafin,saidai a dukka hasashenta bata taba tunani ko zaton samunsa a nan kurkusa ba.....bata taba kawowa cewa yana da wata alaqa ta jini me kusanci irin haka da tsohuwar qawa kuma aminiyarta mariya ba.....bata taba hasashen mariyan tana da nasibin haifar babban mutum har kamar Muhammad jadda ba. "A'ah.....yaron namu ya iso kenan......maraba" Ta fada tana sauya reaction na fuskarta cikin qasa da second biyar tare da takowa cikin falon a hankali. Akaikaice yake dubanta da wani irin kallo,sam baisan fuskarsa ba......bai kuma tuna ko yaya a inda ya santa ba,ta yaya ita din akayi tasan wayeshi?,yaya akayi tasan daga tafiya ya dawo?. "Bana jin zaka iya shaidani.....shi ya sanya banyi mamakin musaddiq daya kasa ganeni ba.....ga yayansa ma ya gaza shaidani?" Ta fadi tana sakin fara'ar da bata kai ga qarasawa ainihin zuciyarta ba,yayin da kwarjininsa ke barazanar hanata samun abun fadi. Still dai baice komai ba yana ci gaba da dubanta. Ko dis baiji matar tayi masa ba,bai hangi dattako ko kamala da sukayi daidai da shekarunta ba a tattare da ita,sai kawai ya dauke kallonsa daga kanta don baiga amfanin maida hankali tare da son qoqarij fahimtar abinda ya tabbatar daga qarshe bame amfani bane,amma ina suka fita har na tsahon awannin ita da maamah din?. Tambayar data maqale masa kenan,bashi kuma da amsa. Qafarsa kawai ya miqa ya zira takalmansa ya miqe "Lokacin sallah ya kusa,zanyi salla na dawo" Ya fadi yana juyawa a nutse yana fita a falon. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 57 _________________________ https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy Assalamualaikum Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule?? Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen?? To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen. Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki. Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina. Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy ____________________________ "Yaa huda.....yaa huda?" Muryar haneefa ta ratsa kunnuwanta dai dai sanda take kwance qudundune cikin bargonta. Kusan idan bawai dare ne yayi ba hakan ba dabi'arta bace,amma a yanzun yana neman ya zame mata dabi'ar da sabreen ta fara karantar hakan. Batakai ga ce mata komai ba,don ba abinda ta gani behind kwanciya din da take yawan yi,sai ta barshi kawai a zuwan yanayi ne da yakan sauyawa kowanne dan adam. A yanzu ma gaba daya hankalinta yana kan ayshatu.....ciwonta gaba yake qara yi,ga mika'il a gefe,ga mashkur shima daya sanya wuta da yawa a kanta. Ya'aqoub ne kawai me dan sauqi saboda bai cika zafafawa ba. Dukkansu batason kowa ya subuce mata a daidai wannan lokacin da shirinta ke qara zurfi a kansu,kuma tafi hangen samun nasara da wuri akan mika'il da mashkur,don shi ya'aqoub a yanzu tunaninsa yafi karkata kan yadda zai shawo hankalinta ta aminta ta aureshi,abinda kuma bataga ranar yiwuwarsa ba. Wai mema zata tsinta ne a auren?,bayan tana ganin yadda su mazan suke?,tana ganin kuma yadda matan ke komawa?,ko hanyan aure yanzu mutum yayi mata ai bai qaunarta ballantana ace mata tayi. Duka tsari da halayyar mazan baiyi mata ba ballantana ta cusa kanta a sabgarsu da nufin zama tsakaninta da waninsu zama na din din din?. Miqewa tayi a dole tana duban haneefa,sai haneefa din ta miqo mata takarda tana cewa "Wani ne wai a waje yace a baki...." Da sauri ta fiddo mata idanunta waje sanda muryar sabreen wadda ke amsa waya take dosowa cikin dakin. Yadda suka daga kai suka kalleta duka su biyun ya sanyata janye wayar daga kunnenta tana kallonsu "Lafiya?" Tayi tambayar tana sauya yanayin fuskarta. Wani faduwa gabanta yayi,cikin tsoro tsoro ta girgiza kanta tana qaqalo murmushi tace "Ba komai.....ina kwance haneefa ta tsoratani,na dauka wani abune da naji tanata tashina". Idanu ta sake zuba mata na daqiqu sannan ta amsata tana zama gefan nata gadon " Ko bata tsorataki ba dama ai yaci ace kin tashi,an kusa kiran sallah.....uniform dinku nadra ta wanke tunda kin koyi laziness......kije kiyi alwala ki dawo ki kwashe abincin tukunya a flask a wanke sauran abinda ya rage". "Tom" Ta fadi tana matse takardar a tsakiyar hannunta tare da tunanin yadda zata miqe da takardar ba tare data lura da ita ba,to amma kuma ci gaba da zama dinma tunanin mafita tamkar tana bata damar dora ayar tambaya ne a kanta. Aljihun skirt dinta ta tuna dashi,cikin dabara ta cusa a ciki,sannan ta zame ta sauko tana gyara inda ta kwanta din,ta daura dankwali saman doguwar sumarta ta juya tana fita a dakin. Dauke idonta tayi daga kan tab dinta ta bita da kallo. Haka kawai ta gagara samun nutsuwa kwanaki biyun nan,duk motsinsu a kan idanunta yake,kuma da gaske tana ganin dan sirkawar wani abu kadan tattare da huda din. Bandaki kawai ta wuce kai tsaye tana fata da zumudin budewa taga meye a takardar?. Sai data samu guri cikin toilet din ta zauna sannan ta ciro takardar ta kuma warwareta. Kaman yadda ta zata shi dinne,sunansa kawai data gani sai bugun zuciyarta ya qaru da kaso hamsin cikin dari. Yau kwanaki uku kenan,ya rakota daga hanyar makaranta har dab da gidansu kamar yadda ya saba a kowacce rana......tun tana gocewa har ya fara zame mata sabo ba tare da sanin nadra ko haneefa ba wadda yanxun aka banbanta musu lokutan tashi qarfi da yaji ba tare da kowa yasan dalili ba. Ya zame mata kamar abokin rakiya a yanzun.....tun tana dari dari da tsoro har hakan ya fara gushewa daga zuciyarta. A ranar alhamis tayi matuqar mamaki yadda ya tsaya suna tsaka da tafiya,ya kuma kafeta da idanu "Lafiya kake?" Ta tambayeshi da mamaki "Ke kyakkyawa ce" Ya fadi yana jin wutar sha'awarta na ruruwa a ransa tamkar yadda ya dinga jin ta 'yar uwarta. Yana jin kamar ya dauketa a yanzun ya wuce da ita ya aikata abinda ya tanadi aikatawa,saidai kuma bazaiyi haka ba,yanason komai ya kasance a daidai sanda zatafi jin ciwo da radadin da zai iya zama ajalinta,ya kuma tarwatsa farincikin da take musu tattali. Yanason idan ya tashi ya tarwatsata tarwatsewar da ba zata taba dawowa ta gyaru ba ballantans ta koma yadda take. Idanu ta waro tana dubansa,yadda yake yawan kambata da kurantata ya sanya kusan kullum sai ta kalli madubi......kusan kullum sai ta kalli kanta da kanta taga wannan kyan da yake magana a kai......wannan budurwar da yake yawan kiranta dashi. Tun bata ganin abinda yake fada din har ta fara ganin,amma tana ganin kaman bata ca canci kowacce rayuwa ba a yanzun......karatu shine yafi da cewa dasu kamar yadda yaa sabreen ke gaya musu "Ina sonki huda.......ina tsananin qaunarki tun daga ranar dana fara ganinki.......zuciyata tana miki wani mahaukacin so da bansan iya adadinsa ba......wallahi inaji a zuciyata tamkar zanyi hauka saboda ke huda......ki soni don Allah......ko baki sona ni zan koya miki yadda zaki soni din". Kalaman da suka tsoratata suka kuma razanata kenan. Kalaman kuma da Naseer din ya shiryasu ne kawai don ya soma wasa da tunaninta da qwaqwalwarta,plan na biyu kenan daga cikin tsarikansa. Baya taja tana girgiza kai,tana jin tsoro yana shigarta. Wacce irin soyayya a shekarunta?,duka duka nawa take?,koda yaa sabreen bataga ta kawo kowa tace shi zata aura ba,bataga wani yazo qofar gidan da sunan zance wajenta ba.....koda abinda ake maganarshi a kanta da nasu idanun basu taba ganinta cikin motar wani ko tsaye da wani ba har zuwa yanzun da take tsaye a gabansa. Ko rakota da yakeyi kullum kwanan duniya a tsorace take......wani lokaci zuciyarta tana raya mata idan sukayi kacibus da yaa sabreen fa?,sai kuma zaqin bakinsa da daddadar hirarsa ta yaudare tunaninta da kunnuwanta. Tayi mugun tsoratar data dinga ja da baya da baya tana girgiza kai. Yana tsaye ya kafeta da idanu,abun yana masa sugar sosai. Irin hakan yafi buqata don ta haka ne sabreen din zata fuskanci girman nasa aikin. Ya samu sabon ruhi sabon gangar jiki da baisan komai ba game da rayuwa......zai hurewa zuciyar kunne,sannan ya mori gangar jikin yadda yaso ya kuma watsar da ita tamkar wani yasashen abu maras amfani. Yana tsaye harta gudu a layin ta bacewa ganinsa,sai ya bushe da dariya. Hakan da tayi ya tabbatar masa qwaila ce,ya kuma bashi tabbacin baa taba gaya mata kalmar so ba sai a kansa "Allah sarki......gashi baki fara da jin kalmar ba a sa'a......anyway......ko mene ya faru dake 'yar uwarki ce taja miki" Ya fada yana juyawa don barin layin ya qarasa inda yaransa ke cikin mota suna jiransa. Hannunta har rawa yake sanda take warware takardar. Tsakanin alhamis jumaa asabar da kuma yau lahadi ba wasu mintuna biyar kyawawa da suka wuce ba tare da tunanin abinda ya faru tsakaninsu ya dawo kanta ba. Duk juyin da zatayi sai kalamansa sun dawo mata,kallonsa murmushinsa da kambamawarsa. Fuskarta kam ta kalleta yafi sau adadi tana sake duba kyawun surarta da yake yawan jaddadawa. A yadda take gani ba mace me kyan yaa sabreen dinsu......ashe itama to tana da kyau dinne da gaske?,ko kuma yana fada ne kawai?. *_Hello me kyau,fadin azabtuwar da idanuna da zuciyata sukayi saboda rashin tozali dake ba abu bane me sauqi......ina fata zaki daure a gobe ki barni naga wannan kyawawan idanun da zuciyata ta mutu a kansu.....idan ba haka ba.....zan iya rasa numfashina_* Da sauri ta duqunqune takardar ta kuma jefa a toilet ta bita da flushing zuciyarta na bugawa sosai. Tsoro zumudi fargaba da mamaki dukka suka hade mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi. Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja qofar ta bude ta fito ba tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura alwala tayo dakin nasu. Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe abinci tayi zaune saman kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi kitchen. Yanzunma da kallo sabreen ta bita har ta shige kitchen din. To wai me yake samun huda take wasu wasi haka?. Bata sani ba,sai ta girgiza kai ta taka hannun kujerar tana dauko babbar dardumar da sukan shimfida suyi magariba da ishai akai suyi bitar karatun makaranta ta taimaka musu da wanda zata iya. Da ruwan zafi sosai tayi wanka bayan wucewar hajja saboda ciwo da jikinta yake mata sakamakon zaman mota data jima batayishi kaman haka ba. Ta shirya kanta cikin fafi indian abaya me laushi,ta yane kanta da mayafin abayar daya kasance medium cotton kaman yadda jikin dogon rigar yake. Cikin falon tayi zaune bayan ta kirayi me aikinta ta canza mata channel. Qafafunta a miqe saman side glass table din,hannunta dauke da glass cup dake cike da lemon raspberry tatacce me asalin tsadar. Babu wani abu da zata ci ko tayi amfani dashi cikin gidan da yake da qaramin kudi. Komai nata me tsada take zaba,hatta da ruwan da zata sha kuwa ballantana akai ga sutura ko wayar hannunta. Ko a yanzun haka ta gaya masa tana buqatar ya sauya mata iPhones din hannunta guda biyu. Iphone 15 da wata tsaddadiyar waya sabuwar qira da kamfanin Samsung's. Duka duka wayoyin ba wadda tayi wata uku,to amma garin gane ganenta ta hangi wasu sabbin fitar,su kuma takeso ta riqe. A komai tafison ta zama cikin sahun mutane na farko da ake ganin komai sabo a wajensu. Inda tana da iko komai zai zamana ana ganinsa ne ta wajenta,sanda zai soma zagayawa hannun masu kudi irinta ita ta dade da cin zamaninta. Ta sani,a dukiyar da d'anta yake dashi yana da qarfin kudi da mulkin da zai iya sanyawa a qera mata duk abinda take buqatar ya kasance nata ita kadai daga kowanne kamfani a fadin duniya,to amma ta fahimci rayuwarsa baya daidaitata dai dai data sauran masu kudin irinsa. Ba kuma haka takeso ba.....ba haka take muradi ba......tanaso ta gansu suna rayuwa daidai da matakin arziqinsa. Ta fahimci yana cikin sawun mutanen da ba kasafai suke bayyana arziqinsu ba,sai abinda ya riga ya bayyana ba yadda zasuyi dashi. Aka idar da magariba akayi ishai shuru. Tun tana tattalin maganganun da zatayi dashi har wasu suka fara bace mata. Ta daga kai ta kalli agogon dake shirye saman tv din falon takwas da rabi na dare,to shin sai yaushe zai shigo?,sai yaushe wannan abun zaizo qarshe?. Sannu a sannu sanda taga an doshi tara na dare babu alamunsa,wayoyinsa dukka a kashe shida musaddiq din da zata sanya ya kira mata shi a duk inda yake. A ranta ta dinga jin cewa hadin baki ne......a ranta kuma ta dinga ji aminatu ce ta hanasu.....a yanxun haka qila suna can gabanta......ta zaunar dasu sai abinda tace musu. Wannan tunanin ya dugunxuma mata zuciya,har taji bata da wani sauran zama cikin gidan. Dakinta ta wuce kawai bayan ta ajiye kofin lemon,ta shiga zaro takalmi cikin jerin takalman alfarma dake adane a shoe rack dinta. Cikin zuciyarta takeji yau din Alhaji hamzan zata tunkara......tanaso taji shine yayi mata cikin yaran ko ubansu?,tana so taji da ita dasu wai waye ahaqqu dasu?. "Nazo muje ne?" Zuwaira ta tambayeta sanda taga tana dosar qofar fita daga falon "Zauna basai kinje ba" Ta amsa mata a gaggauce tana fita a gidan. Mugun bugun da takewa tafekeken gate din gidan ya fusata securities din gidan,saidai kuma lokacin da suka duba wadda ke bugun ta na'uarar tsaro dole kowannensu fusatarsa tayi nata guri. Basusan ainihih matsayinta ko ita wacece ba......amma yadda suka fahimci girmamawar da take samu daga mazauna gidan ya basu alamar cewa tana da nata matsayin na daban. Ko kallo security din daya bude mata qofar bai isheta ba ballantana tabi takan welcoming nata da yakeyi tare da bude mata qofa ta biyu da zata sadaka da farfajiyar gidan. Daga nan wasu security din su sake marabtarka kashi na uku kenan kafin kakai ga ainihin cikin gidan ka zarge qofar da zata sadaka da babban falon anni na farko. Bata taba tunanin zata sake takowa cikin gidan ba karo na biyu.......don duk lokacin data tako din alatun gidan yakan zame ma idanu da zuciyarta barazana. Tana jin kamar kowanne abu idan ta kalla a gidan yana mata izgili ne tare da gaya mata da dukiyar danki aka samar dani......baki kuma da wata izza ko power ta mallakata. Kowanne taku daya idan tayi cikin gidan ranta quna yake......sak fasalin yadda takeso gidan da zata rayu ya kasance sai gashi kacokam a yau din irin wannan dream house din nata mallakin aminatu ne.. Wasu mutane da basu da masaniyar sanda ta dauki cikin fuad har ta haifeshi. Qofa ta qarshe da zata bata daman shiga falon annin nanma sai data jinkirtawa na'ura sannan ta bata izinin shiga,ta dauke kanta ranta yana suya da wani irin fushi. Tafi qarfin ta tako gidan alhaji hamza har abada.....inda sun bata girma da martabarta da a yanzun ba shakka ita ake zuwarma haka neman gindin zama. Tana sane da yadda mabuqata ke yawan ziyartar gidan karbar taimako a duk sati......taimakon da ta tabbatar daga fuad ake rabashi.......sai gashi ita duk yadda taso ta dinga cina farfajiyar nata gidan da mabuqata,tana raba musu kudi a envelope yadda taso abun bai samu yadda takeso ba. Bai hana taimako,amma saidai ta rubuta list na mabuqatan ya hadasu dana gidan alhaji hamza a raba musu taimakon tare. Bata samu yin sallama ba,sai Allah ya sanya tana sanya qafafunta a falon idanun anni dake kashingide cikin lausasan sofa ya sauka a kanta. "Ikon Allah" Anni ta furta tana miqewa daga kashingidar da tayin tana sauke qafafunta qasa idanunta akan maamah "Da kinyi zamanki ma.....don ni ba wajenki nazo ba kaman yadda na alqawarta zuwa na na qarshe gidan nan......wajen hamza nazo" Maganar tata tazo qarshe dai dai sanda amna ke fitowa daga kitchen ta zuba abincin dare,don tace yau zaman cin abincin abban yayi dare da yawa,ba zata iya jiransa ba da wuri takeso ta kwanta. Kallon kallo sukayi tsakanin maamah din da amna. A kallon farko ta fahimci wacece duk da wannan shine karon farko da ta fara ganin yarinyar ido da ido. Autar alhaji hamza kenan,yarinyar da ake gaya mata irin sabon dake tsakaninta da fuad......yadda take ji dashi da yadda shima yake ji da ita "Idan har kikayi da wasa kina zaune zakiji ance 'yar gida akayi.....wannan matar zata aura masa autarta..... Kinga shikenan komai ya qarasa watsewa" Muryar hajja ta dawo mata akai cikin tattaunawar da sukayi da hajjan a dazu dazu kan hanyarsu ta dawowa gida. "Ke amna......dubamin abbanku idan ya kammala,kice maza maza yayi baquwa" "To" Ta fada tana ajiye plate din sannan ta miqe tana nufar qofar da zata sadata da sassan abban nasu ba tare da tabi ta ainihin farfajiyar gidan ba. Tana tafe tana waiwayen maamah,itama ta lura da hakan,sai taja wani tsaki me matuqar qarfi abinda ya sanya amna din maida kanta tana yin gaba. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 58 ___________________________ https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy Assalamualaikum Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule?? Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen?? To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen. Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki. Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina. Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy _________________________ Farfajiyar gidan ba kowa sai qofar dakin malam saidu da yake iya hangowa wanda yake a bude. Juyawa yayi zuwa sassan da spare din famfo dake bawa shukokin gidan ruwa yake,ya xame takalminsa,ya kuma xare agogon hannunsa ya jefa aljihu sannan ya matsa ya kunnashi. Dukkan hannayensa ya tara yana kallon saukar ruwan,sai yaji wasu kalamai suna dawo masa a ka _"ka mutu mana......ai ba a kanka aka fara mutuwa ba,kuma ba'a kanka zaa daina ba......talauci da fatara tafi mutuwarka yimin barazana......ta kuma fi mutuwarka dagamin hankali"_ Wani abu yaji ya tsaye masa a tsakanin numfashinsa daya sanya ya cire hannayensa daga famfon. Wasu daga kalaman maamah kenan a can shekarun baya a bakin famfo tamkar irin haka,daidai sanda abban nasu yake daura alwalar sallar magariba. Takalmansa kawai ya mayar yana jin bazai iya ci gaba da xama a cikin gidan ba. Ire ire wadannan abubuwan da ba wanda ya sansu saishi,.....koda musaddiq kuwa......suna sanyashi yana jin kamar numfashinsa zai fita a wasu lokutan. "Ko buta zaa baka ranka ya dade" Muryar malam saidu ta ratsa kunnensa sanda yake dab da qofa. Kansa kawai ya gyada masa yaja ya koma ya zauna,ba jimawa ya dawo da butar,ya karba ya fara dora alwalar a gaggauce,ya gama ya bashi ya karba ya maidata wajenta "Zo muje malam said" Fu'ad ya fada yana ware hannun rigar sa. Tare suka jera shida malam saidu din,duk da yadda yaso ya zuqe saboda girmamawa,me sunan malam kuma yana daga bayansu kadan ta yadda bazaiji wani abu da suke tattaunawa ba "Magana zamuyi" Ya fada a nutsensa "To....to" Ya fadi da hanzari "Tambayoyi ne amma sai bayan mun idar da sallah zan saurari amsoshinsu" "To ba laifi ai" Ya amsa masa,don ya saba lokaci lokaci dama yakan masa tambayoyi game da gidan ya kuma buqaci amsarsu. "Waccan matar da suka shigo da hajiya meye sunanta?,wace ita a wajenta?,yaushe ka fara ganinta a gidan?,sannan kamar sau nawa ta taba zuwa ko take zuwa?,ita kadai ce koda wasu?,tana dadewa cikin gidan?,suna yawan fita tare ko aah" Yakai qarshen dukkanin tambayoyin nasa sanda suka kai bakin masallacin,don haka yayi shuru yana adduar shiga masallaci a madadin tarin tambayoyin. "Lallai na sake yarda da maganar bokan can.....lallai akwai aiki qwarai akan yaronkin nan" Hajja ta fada duk da nata yaron da matarsa data shanya a waje kowanne cikin motarshi yana jiran fitowarta. Labba maamah ta cije kadan sannan ta saki sanda take maida riga maras nauyi a jikinta "Ni kuma cewa nayi miki zan qyale wannan aikin ya cimmani?,na zuba idanu naga iya gudun ruwansa na yau kawai......amma duk abinda yakai gobe zakiji kirana......a gobe nakeso mu koma a fara aikinnan" "Ai da zafi zafi akan bugi qarfe....." Hajjan ta fadi zuciyarta na saqa mata abubuwa masu yawa. Har bakin gate din farko ta tako tana yiwa qawartata godiya da ban gajiya. A nan suka gaisa da yahaya da matarsa. Yadda ta samesu a jere kowanne da mota yana jiran dakon fitowar hajjan ba tare daya isa yabar wajen ba ba bisa umarninta ba ya sake ninka kwadayinta itama na kaiwa wannan bigiren,sai taji kamar ta jawo wadannan kwanakin da tayi imanin suna dab da zuwa......ranar ea zata nunawa aminatu da hamza cewa ruwa ba sa'an kwando bane.....hakanan koda giwa ta fadi tafi qarfin wawa. Haka siddan?,daga maqotaka?,ba sidi ba sadada a kama mata yara a musu muguwar mallaka?,bayan ko sanda ta tafinma suna da wayon da zasu iya kula da kansu?. Da wannan qananun mitocin ta isa cikin gida. Ya kusa minti ashirin yana fuskantar gate din gidan,harde da hannayensa kawai yana duban qofar kwanyarsa tana digesting maganganun da sukayi da malam saidu daga hanyar masallaci zuwa dawowarsu. Baisan a wanne matsayi zai ajjiye maamah din ba.....karo na uku da wani abu ya sanya yake tunanin ANYA ITA DINCE TA HAIFESU?,anya ita din UWACE?,akwai zuciya irin ta uwaye a qirjinta kuwa?. Me yasa kullum DUNIYA itace a gabanta sama da komai?,yayi tunanin shi da kowa ma zata canza ko kuma ta canza din.....amma sai kuma akasin tunaninsu ya biyo baya.....akasin tunanin da shi kadai gani na zuciya da lura da bin takunta sannu a hankali suke karanta masa komai a kanta....karatun da idanuwa kadai sunyi kadan su iya fahimta ko ganeshi. Hannayensa ya sauke jikinsa a mugun mace,baya jin zai iya komawa cikin gidan nan,idanma yace zai koma din abinda zai wanzu tsakaninshi da ita bame dadi bane. Ko haduwarsu na 'yan mintuna kadai ya sake wani karatun. Ya dawo lafiya?,wacce nasara ko qalubale ya riska?,duka ba damuwarta bane......damuwarta shine KUDI.....me yasa bai turo ba?. Abu guda daya da bai taba faruwa tsakaninshi da anni ko abba ba......basu taba neman anini taro ko sisi daga hannunshi ba.....a hakan take neman kudin da zata rabashi da Alhaji hamza da aminatu?,mutanen da su suka bashi RUHI na rayuwa da yake yawo a jikinsa a yanzu?. Kansa ne yaji ya sara,sai ya sake qara azamar barin qofar gidan ya juya zuwa nasu gidan. Gidan da a baya shine gidan maqota a wajensu amma a yanzun basu da gidan daya kaishi. Tun a gate ya sallami kowa,ya gaya musu da wuri zai kwanta don gobe zasu fita da wuri,duk da baida yaqinin goben a yadda zai tashi saboda wani nannauyan ciwon kai daya saukar masa yanzu yanzu. Tun bai qarasa sassansa ba ya kashe duka wayoyinsa,yabi ta qofar baya don bayason kowa yasan ya shigo din ya wuce sassansa. Bai kunna kowanne fitila na sassansa da zai bada alamar yana ciki ba,sai ya wuce a hankali kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki zuwa study room dinsa,ya tura qofar ya shiga ya maida ya rufe. Zaune kawai yayi saman sofa idanunshi a kulle,yayi nisan nazarin da shi kansa baisan wane zare a tunanikansa zai kama ba. Abu daya ne da yafi daure masa kai da dagula masa lissafi,qoqarin da takeyi da gaske na sai ta raba tsakaninsu,indai haka ne wannan fitar tasu tana da alaqa da qudurinta.....indai haka ne kudin da take nema lallai yana da alaqa da qudurinta......indai kuma haka ne tabbas wannan BAQUWAR FUSKAR akwai tata rawar cikin mission din......duk da yasan wannan din tsohon quduri ne dake ranta.....amma dukkan alamu sun nuna ta samu MAKAMASHI. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 59 Shuru ne ya biyo baya tsakaninsu,babu wanda yace da dan uwansa komai tsakanin ita da anni din. Daga yanayin tsaiwarta da yadda take bin komai da wani irin kallo ta tabbatar ba alkhairi bane ya kawota,don haka taci gaba da abinda takeyi din ba tare data ce komai da ita ba. Baifi minti biyu ba kacal sai ga amna ta dawo "Yace gashi nan...." Ta bata amsa tana sake binta da kallo tamkar a tsorace,sannan ta qarasa ta dauki plate dinta ta koma kusa da annin ta naniqe ta zauna tana ci gaba da satar kallon maamah din. Da sallama ya shigo falon cike da kamalar nan tasa dake shimfide saman fuskarsa,sanye yake da jallabiyya ruwan qasa,kansa sanye da qaramar hula tashi ka fiya naci. Amna da anni ne suka amsa sallamar tashi,yayin da maamah ta dubeshi kadan kafin ta dauke kanta "Mariya ce?,....bismillah......zauna mana" Ya fada yana zama kujerar dake daura data anni. Kamar tace ba zata zauna ba,to amma kuma zaman yafi kamata tayin,don tanason daga qarshe ta gasa masa maganganun da indai ya haifu zai fara janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta fu'ad dama rayuwarsa gaba daya,yabar mata 'ya'yanta kamar yadda kowacce uwa keda iko da nata yaran. "Muna lafiya.....ina fata kuma lafiyar ko?" Gyara zamanta tayi sosai tana dora qafarta daya kan daya,sannan ta saka idanunta sosai cikin nasa "Wajenka nazo hamza" Ta fadi kanta tsaye,abinda yaja hankalin anni kenan tadan daga kai ta dubeta,sai kuma ta saukar tana son kwashe hankalinta sam sam daga kansu. "To ai gani.....Allah yasa lafiya" Fuska ta qanqance tana dubansa idanunta a ciki. "Al'amarinku yana bani mamaki hamza yana kuma dauremin kai.........duk duniya ban taba ganin inda ake irin haka ba sai a kanku,hankaka mai da dan wani naka?......amma mu ajjiye wannan batun......tunda kun zab lallai sai na zama maqasqanciya a gabanku akan 'ya'yana?......ba laifi don komai da ka gani a rayuwa lokaci ne.....kuma iyaka gareshi......" Ta furta qasan ranta tana hangen iya adadin lokacin da ya rage musu wanda alaqar uwa da uba zata wanzu a tsakaninsu.....da tazarar lokacin da alaqar zata juye zuwa alaqar gagarumin abokin adawar da duk duniya fuad din zai wayi gari bashi da abokin adawa irinsa. Burinta shine ta bude idanu taba tsabtsar gaba da adawa mai qarfin gaske ta qullu tsakaninsu......irin adawar da zata bawa kowa mamaki ta kuma shiga sahun tarihi......tabbas saita fanshe dukkan wani baqinciki da suma cusa mata......hakanan ba zata qyale ba sai sunyi aman duk wani da sukaci daga cikin arziqin fuad......koda kuwa wannan gidan da suke ciki yana cikin jerin sahun mallakar fu'ad din. "Wai nikam hamza.......ban sani ba ko cikin duhu ne a sannan?......hadaka da kuma gamayya kukayi da ubansu fu'ad yayin samuwar cikinsu?,ma'ana tare kukamin cikinsu ko kuwa?" Ba alhaji hamza kibiya kadai ba,hatta anni dake zaune daga gefe ba tare da shiga shirginsu ba sai data cira kanta da sauri maganar tana dukanta "Subhanallahi.......innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Alhj hamza ya fada zallan mamaki yana saukar masa,idanunsa akan fuskar amna wadda ta yunqura tana miqewa ba tare data tsaya daukan plate din abincin ba saboda yadda maganar ta girmimi kunnuwanta. "Mamaki kukayi?,to ai ba abun mamaki bane duba da yadda kuka qanqame min rayuwar 'ya'ya hamza" Ta kuma fadi cikin izza ba shakka ko d'ar a cikin idanunta. "Mariya cikin hankalinki kike kuwa?" Anni ta gaza jurewa ta fada tana kafeta da idanunta. Wurga kallonta tayi zuwa ga annin "Kinga ina iface iface ne ko yage yage da zakiyimin wannan tambayar?" "Shin mene marabar dambe da fada mariya?,ai hauka nau'i nau'i ne.....nakin ina kyautata zaton ta wannan fuskar yazo" "Kamar yadda cutarwarku tazo da sigar yaudara da damfara ba.......na rantse da Allah a yau inda fu'ad yana a faqirinsa bashi da komai da tuni kun watsashi shi da dan uwansa........." "Kaman yadda zamantowarsu halittar da zaki iya mora ta sanya kika dawo cikin rayuwarsu ba?....bayan kin watsar dasu a sannan kina zaton su din ba masu amfani bane,nauyi ne kawai a wuyanki?". Anni ta maida mata amsa ta hanyar katse numfashinta bacin rai yana fara nuna alamun tasiri cikin muryarta "Ya isa aminatu......ban yarda ki sake cewa wani abu ba" Alhaji hamza ya fada yana daga mata hannu. Ya gama karantar akwai abubuwa masu tarin yawa a bunne cikin zuciyar maamah din,biye matan da annin zatayi shi xai bata damar furzar da maganganun da idan suka qyaleta basu tanka mata ba har ta mutu saidai ta mutu dasu a cikinta. Dole ta ninke dubban maganganun da suke tsinkulinta a rai kawai don ta bawa abban girmansa,amma bawai don abinda take da shirin furtawa itama ya qare ba,ta kauda kai tana hadiye fushinta ba tare data sake jefa baki a maganarsu ba "Ka gaya masa ya bini.....domin kuwa duk duniya ba wanda akace aljannarsa tana qarqashin qafarta face ni.....komin lalacewata......ka taimaka ka sakar masa mara ya rabu dani lafiya kaman yadda na tabbatar ka rabu da naka lafiya......ka shaida masa yazo ya bani kudin dana buqata a hannunsa.......bawai alfarma nake nema ba......ka gaya masa dole ne yayimin...." Tana kaiwa nan ta miqe tsam,idanunta akan anni da tayi kaman batasan da wanzuwarta a wajen ba. Taso ace annin taci gaba da ja,don tana da tarin maganganun da takeso ta amayar mata "Wallahi duk d'an da ya hana uwarsa bacci.......shima bazai huta ba" Ta furta tana juya hankali kwance tana barin falon. Shuru ne ya biyo baya,duk kuwa da cewa ta gama ta kuma fita daga gidan ma gaba daya "Hasbunallahu wani'imal wakil" Alhaji hamza ya furta gauraye da wata ajiyar numfashi me nauyi idanunsa na kallon waje daya. Baisan wanne irin abune yake dawainiya da mariya ba......baisan kuma wanne girman laifi sukayiwa rayuwarta haka da take musu kallon wasu manya manyan abokan adawarta ba. Anni batace komai ba kaman yadda shima bai buqaci tace ba,tanata qoqarin sarrafa bacin ranta da ganin ta hadiyeshi ba tare data barshi ya mata tasiri ba "Ina muhammadu?" Alhaji hamza yayi tambayar yana duban annin "Bansan ina yayi ba.....mun rabu dashi a dazu kan zai shiga wajenta" Ta amsa masa a taqaice. Karkacewa yayi ya ciro wayarsa daga aljihun jallabiyyarsa ya soma trying number din fuad din. Sosai yayi nisa cikin tunani,a haka idan ka ganshi zaka dauka bacci yakeyi,saidai ba ko guda daya. Wasu mintina ne daketa wulga masa tsakanin bacci da ido biyu wanda a ciki baisan ainihin abinda yakeyi ba A silent wayar take,amma hasken da take fitarwa ya ratsa rufaffun idanunsa a cikin duhun dakin. Kamar bazai bude idanun nasa ba amma sai ya budesun a hankali yana saukesu akan wayar. Yayi tsammanin ya kashe duka layukan,sai a sannan ya lura guda daya ya kashe. Sunan daya gani saman wayar ya sanyashi sauke qafafunsa a hankali yana maida hankalinsa a kanta,ya miqa hannu ya daukota daga inda take ajiye yana qoqarin dagawa. Sallama yayi amma muryarshi ta maqale,yadanyi gyaran murya sanda yajiyo muryar abban yana masa sallama "Ina ka shiga ne?" Alhaji hamza ya tambayeshi "Ina cikin gida abba" "To fito......inason ganinka.....ka sameni falon anninka" "To abba" Ya amsa masa a ladabce. Remote ya laluba ya dauko ba tare daya tashi a gun ba ya maida hasken dakin. Take yayi tarwai da haske kaman yadda ainihin dakin yake "Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla.....wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" Ya furta muryarsa can qasa,yana jinsa gaba daya ba kuzari,tun daga zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa. Bai wani bata lokaci ba ya sauya kayan jikinsa sannan ya wuce sassan annin. Sallama yayi hankalinsa na kaiwa fuskar anni. Tun bai zauna ba jikinsa ya bashi akwai wani abu,don ba kasafai kake ganin fuskar annin a haka ba. A nutse ya qarasa shiga ciki,kai tsaye kuma ya nufi inda Alhaji hamza yake,wanda bai motsa ba daga wajen tunda maamah din ta fita ta barsu. "Bismillah.....zauna" Alhaji hamza din ya masa nuni da kujerar dake kusa dashi. Sanda ya zauna din ita kuma anni ta miqe da zummar barin wajen,abban ya maida dubanshi kanta "Zama kema zakiyi......ina zakije?" Duban abban tayi,kaman zatayi magana sai kuma ta fasa,ta koma ta zauna ba tare data sake cewa komai ba. "Muhammadu" Abba ya kira sunanshi kai tsaye,abinda ba kasafai hakan ke kasancewa ba. Mamakin ya hanashi amsawa saidai ya daga kai kawai yana duban abban. "Muhammadu ya ina yabonka sallah zaka kasa alwala?" Abban ya sake fada idanunsa still akan fu'ad din,tausayinsa kuma yana ratsa zuciyar abban. "Abba....." Fu'ad ya motsa labbansa a hankali da zummar yin magana "Me dame mariya tace maka tana da buqata wanda bakayi mata ba?" Ya masa tambayar Kai tsaye don sauqaqe masa wahalar tunani. "Abba.....ba wani nauyi ko haqqi daya kamata na bawa maamah wanda bana bata shi......bana tunanin akwai wani abu da ya zama nauyi ko haqqi da ubangiji ya doramin wanda na gaza dauke mata shi". Har cikin zuciyarsa abban ya gamsu da wannan,saboda shi kansa ganau ne bawai jiyau ba akan hakan "Na sani Muhammadu......amma don me yasa idan tana da buqatar kudi daga hannunka kake hana mata?". Sam baima kawo wannan zancan bane,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana sauke kanshi qasa. Rashin amsawarsa ya bawa abba amsar tambayarshi "Me yasa kusan ko yaushe matsalarka da ita akan tana neman kudi ne ka hanata?,bayan Allah yayi maka wadatar da zaka iya bata ko nawa ne Muhammadu?" Ya qarashe maganar ta sigar tambaya idanunsa a kanshi,can qasan ransa yana mamakin abinda ke kawo musu matsala akan abinda yasan ya jima da fin qarfinsa. Km *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 60 "Ka sani cewa......duk d'a aljannarsa tana qarqashin qafar iyayensa?,kuma haramunne jayayya dasu bare su buqaci abu aqi ayi musu?" "Na sani abba.......amma bazan iya bawa maamah ko sisi ba". Sosai maganar ta bawa abban mamaki,har anni dake zaune daga gefe itama ta daga kai tana kalleshi "Akwai abubuwa masu yawan da baka gama saninsu ba abba akan maamah......akwai boyayyun sirrikan dana ajewa cikina abba.......akwai wasu abubuwa masu yawa wadanda ba zasu fadu ba......amma koma meye cinta shanta lafiyarta dama suturarta wani abu ne da bazan taba iya hana mata su ba ko don albarkacin haihuwa da Allah ya bata........amma batun kudi abba........bazan iya bata ba" "Dalili?,dalili nakeso naji Muhammadu" Abba ya sake tambaya cikin tsananin mamaki. Bai taba umartarsa da abu ba ya saba.....sai gashi s yau yana qoqarin bijire masa.......tabbacin akwai wani qaqqarfan dalili da kuma hujja kenan "Abba...." Ya kirayi sunansa yana jin nauyin abinda zai furta din. Shurunsa ba abinda zai harfa tsakaninsa dashi sai gurguwar fahimta,bayaninsa din kuma bawai abu bane me dadin ji ko sauraro ba. "Kasani Muhammadu.....koda baka bayar ba ni zan dauka na bata da kaina" "Zan bayar abba.....zan bata amma bawai don zuciyata tana so ba......" "Zuwa yaushe kenan?" Ya sake tambayar sa "Zan yiwa sadiq magana,zai saka mata" "Kirashi yanzu yanzu" Ya sake bashi umarni kai tsaye. Dole ya fidda waya ya turawa sadiq din saqon umarnin fidda kudaden,sannan ya aje wayar yana duban abban "Zai sanya mata in sha Allahu". Ajiyar zuciya abban ya sauke. Shi kansa yasan akwai qalubale masu tarin yawa cikin rayuwarsa,to amma ko meye zaiyi yana yine saboda kyautatuwar rayuwa da kuma gobensu. Kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci baya gajiya da yi musu nasiha dukkaninsu,yanzunma nasihar ce dai yayi masa. Haka kawai sanda yake barin falon yaji hankalinsa bai kwanta ba. Muddin maamah tazo gidan to ya tabbatar akwai wani abu maras dadi daya biyo baya. Ko mene kuma ya farun yasan babu me gaya masa cikin gidan,daga amna sai musaddiq wanda baya gidan. Yana takawa a farfajiyar gidan yana lalubar number amna din. Bugu daya ta daga tana amsa sallama a nutse "Fito waje inason magana dake" "To hamma" Ta amsa masa tana sauke plate din hannunta data gagara cin abincin ciki. Wayar tabi da kallo har yanzu muryar matar tana amsa kuwwa a kunnenta. Maganganunta sun girmi kunnuwanta,batasan komai a kanta ba amma tana ganin rashin kirki qarara daga dukkan wani motsi nata. A tsaye ta sameshi idanunsa saman qananun shukokin dake bawa wajen iska me kyau da yanayi me dadi "Zauna" Yace da ita yana nuna mata kujerar dake gabansa tare da qoqarin karantar fuskarta. Ba musu din ta zauna tana jin jikinta yana qara sanyaya daga kallon da taga yana yi mata "Akwai baquwar da tazo gidan nan dazun?" Ya tambayeta yana kallon tsakiyar idanunta. Kallonsa itama tayi sai tayi qasa da kanta tana tuna gargadin da anni tayi mata "Ba ruwanki da abinda tazo ta fadi,wannan ba abinda ya shafeki bane.....ba'a gaban kowa kuma akayi ba saike kadai...... Kada na soma jin zancan nan ya fita" Gargadin annin kenan bayan ta bar falon ta isketa a kitchen. "Ehnnnn......kina nan sanda ta shigo na tabbatar......akwai wasu abubuwa data cewa anni da abba?" Ya sake tambayarta yana kallon fuskarta. Ba zata iya kallonsa kuma tayi masa qarya ba......hakanan ba zata iya saba maganar anni ba,don haka ta zabi sunkuyar da kanta ta kuma girgiza masa kai. Qaramin murmushi ne ya subuce masa wanda ba komai cikinsa sai bacin rai "When kika fara yiwa hamma qarya amna?" Tambayar tasa saita rudata gaba daya,taji bata da sauran zabi illa ta shaida masa gaskiya. Tambayar farkon data jefawa abban ita ta sanya fuad jan kujera shima ya zauna wani nauyi yana saukar masa. Ya ilahi.....wannan wacce irin jarabawa ce?,me yasa UWA take jin tasu jarabawar rayuwar?. "Tashi kije" Ya bata umarnin daya sanyata miqewa da sauri tana barin wajen. Tafin hannunsa ya sanya yadan daki goshinsa yana lumshe ido. A mizanin hankali da tunani da sanin ya kamata......yayi zaton maamah zata kasance ne cikin sahun farko na mutanen da ko kansu sukan sanya a gaba suka yanka ba zata ce komai ba. ****A hankali take takawa cikin layin zuciyarta na bugawa a hankali a hankali. Bugun zuciyartata ne batasan meye ainihin dalilin faruwarsa ba. Tsoron ganinsa takeyi ko kuma shauqin ganin nasa?. Tun daga wancan ranar daya aike mata wasiqa ta qarshe bata sake jinsa ko kuma ganin motsinsa ba,har kawo yau da suke shirin cinye satin gab daya a kuma shiga sabon sati. "Assalamu alaikum" Sautin sallamar daya sanya zuciyarta wani irinn bugawa ta ba zata,mamaki kuma da tsoro suka hanata amsawa saboda yadda taji alamun muryarta a shaqe take. Kasa waiwayawa tayi har zuwa sanda ya tako yana cimmata a inda take,ya zagaya kuma yana yiwa kansa matsaya a gabanta dab da ita. Yanayin kallon daya rutsata dashi ya hanata janyewa baya kaman yadda takeyi a duk sanda ya tsaya kusa da ita kamar haka "Banga alamar kinyi kewata ba......inacan soyayyarki zata kasheni?" Ya furta yana karyar da wuya tare da komawa kalar tausayi ainun. Idanunta ta fiddo waje tana dubansa "Me ya sameka?" Ta samu bakinta da subucewa gami da tambayarsa kai tsaye. "Ciwon sonki" Ya fada wani mayaudarin murmushi yana subuce masa. Nasararsa yake hange muraran daga idanun yarinyar,ya tabbatar yana dab da cika burinsa......yana kuma gab da daukan fansa. Wata ajiyar zuciya taja tana sauke numfashi "Bakiyi kewata ba huda sam sam" Ya sake fadi yana kalmashe wuya idanunsa cikin nata,yanason ya sake dasa mata dafin da zaiyi wahalar gogewa daga ranta. Yanason ya cimmata sosai,ya kuma nutsar da ita cikin tafkin qaunarsa fiye da yadda yayarta ta jefa masa qugiyar da har yanzu ya gaza zameta daga ruhinsa. Baya jin akwai wata mace da zata iya kashe masa qishirwarta. A kanta yakejin komai kuma ita kadai zata iya sama masa da wannan nutsuwar. Saidai kuma ya karanci hakan wani abu ne da bazai taba samunsa ba.....don haka gwara yayi daukan fansan da zata gwammace bashi rayuwarta yayi yadda yaga dama da ita. "Don Allah me kyau kice wani abu mana" Ya fada yana marairaice mata "Nayi kewarka mana....." Ta samu kanta da furtawa. Yadda ya fidda idanu yana gwada mata mamakinsa ya sanyata jin kunya gami da mamakin kanta. Wani abu ne da yake faruwa da ita karo na farko a rayuwarta da bata taba tunanin zuwansa a nan kusa ba "Da gaske kike?" Ya fadi har yanzu idanunsa a waje,sai tasa hannunta kawai ta lullube fuskarta dasu tana sakin qaramin murmushi,abinda ya sake fidda kamanninta sosai da sabreen. "Don Allah yau daya ki bani aron mintunanki biyar" Ya fadi yana hade hannayensa waje guda. Mintunan biyar din da yake sanya ran a cikinsu zai qarasa dashen da ya dauko. "Don Allah karkice aah,bazan sake neman wata alfarma ba daga wajenki ba daga wannan" Ya sake maganar yana qara marairaicewa da kyau. Rabuwa biyu zuciyarta tayi,wani sashe na zuciyar tata yana cewa ta bashi damar.......yayin da wani sashen kuma yake cike da tsoro,tsoron da kusan kullum a cikinsa take. Batasan yadda akayi ya shammaci rayuwarta har ta soma sabo dashi take kuma jin wasu baqin abubuwa a kansa ba,irin abinda bata taba jinsa akan kowa ba,koda kuwa cikin duniyar mafarkinta ko kuma hasashe. Cikin qasa da mintuna biyar din daya dauka ya qarasa wargaza duk wani tunani nata. Sanda take takawa zuwa gida dauke da kalamansa masu nauyi.......ji ta dinga yi duniyar tamkar ita daya ce mace a ciki......dama haka zukatan dake da masu furta musu kalamai masu dadi sukeji?. Yau daya ta gasgata kalaman daya taba furta mata "Har yanxu ke yarinya ce.....ba zakisan dadin rayuwa ba sai kinso kin kuma bada dama an soki......kowacce rai tana da buqatar wanda zai sota.....a lokacinne zaki karanci martaba da darajarki da kuma zamowarki cikakkiyar mace duk da qarancin shekarunki. Hannunta takai tana shafa qaramar wayar daya bata wadda ke dauke da layi da kuma number dinsa. Ita kanta batasan adadin yawan roqon da yayi mata ba kafin ya karya zuciyarta ta aminta da karbar wayar ba "Zanyi tafiya me nisan xango,a qalla zanyi watanni biyu ban saki a idanuna ba......bazan iya jurar rashin ganinki ba......" Kai take girgizawa a tsorace "Yaa sabreen......" "Ita kike tsoro?,zanje na nema dama a wajenta,kada ta rabani da abinda raina yakeso,zan roqeta ta barni na dinga jin muryarki....." "Baka da hank......" Taji bakinta ya subuce da fadi.....sai kuma ta yiwa kanta waigi daga furta abinda tayi niyyar fada din a mugun tsorace. Yaa sabreen din da kullum kwanan duniya cikin kwatanta mata ta kaucewa sauraren kowanne d'a namiji har sai ta isa minzali?,yaa sabreen din da bata lamuncewa kowa mu'amala dasu ba komai kusancin dake tsakaninsu?,shine a yanzun yake neman kai kansa da kansa gabanta?. "Huda......zan iya komai a kanki.....zan kuma iya komai saboda ke,ni kadai nasan zafin sonki da nakeji a raina.....don Allah ki karbi wayar nan......muryarki kawai xanji,daga gaisuwa idan kinso ki kashe wayar" . Ido ta zuba masa a mamakance jikinta kuma yana yin sanyi,wai dama haka soyayyar take?. Qwallar data gani shimfide a idanunsa suka karya duk wani qwarin gwiwa nata,kafiya da kuma dagiya,ta karbi wayar ba tare da tana da masaniyar ta karbi shiryayyen abu da zai wargaza musu rayuwa ba dukkaninsu...... Sake dafa wayar tayi sosai,qasan ranta tana jin qarin tausayinsa yadda yake faman marairaice mata,da alama soyayya ba qaramin kamu tayi masa ba. Dama wannan itace soyayyar?,dama haka akeji?,dama haka take iya canza mutum daga ainihin yadda ka sanshi?. Ita kanta mamakin kanta takeyi yadda ya iya canzata gaba daya cikin qanqanin lokaci haka,amma kuma hakan fa yana nufin nan da shekara daya ko biyu kenan aure zatayi?. Tayi aure kuma yana nufin tabar yaa sabreen?,tabar nadra tabar haneefa?. To wai ta yaya ma zata fuskanci yaa sabreen din da shi?,tace mata me?,bayan tsahon tasowarta idanunta basu taba gwada mata yaa sabreen din tana soyayya ba da kowa ma ballantana aure?,kullum zancanta yadda zasuyi zuzzurfan karatu kuma su zama wasu a gaba......wannan qudurin zai cika kuwa?. Eh.... Wata zuciyar ta bata amsa daga wani gefan "Shi karatu ai baya hana aure......kaman yadda aure baya hana karatu" Ta tuna da wata hira data jiyo 'yammatan ajinsu sunayi,abinda ya sanyata sakin murmushi kenan dai dai sanda take sanya qafarta cikin falon nasu. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 61 Dai dai lokacin sabreen din ke aje wayar mashkur wanda ya sanyata a lissafin yadda komai zaya kasance. Shine mutum na farko daya matsanta mata da son ta bishi wani guri wajen garinsu. Da fari yaso ace dubai suka wuce,saidai tayi duk wata hikima tata ta kansile tafiyar da a baya ya tayar dayi musu shirinta gadan gadan. Baisan wace ainihin sabreen ba.....shi yasa ya gaza fahimtar dukka wadannan shirmen basa gabanta. Taqi kadan take jira ta yasar da qwallon mangwaro ta huta da quda. A matse take.....kuma cikin matuqar buqatar kudaden saboda aikin ayshatu data tabbatar gab zuciyarta take ga kaiwa ga matakin da zata daina moruwa. Ko a jiya data ziyarci gidan jikinta yayi sanyi.......ta kuma sare sosai da yanayin jikin nata,har sun fidda rai da ita a wunin ranar,amma da yake shi rai idan yana da sauran shan ruwanshi a gaba to tabbas fa sai ya sha. Motsin shigowarta ba tare da sallama ba ya sanyata daga fararen idanunta ta zubesu a kanta. "Meye hakan kuma yau?" Tayi mata tambayar tana duban fuskarta wani abu yana darsuwa a ranta. Fuskarta da fara'a ta juya tana fadin "Au.......mantawa nayi wallahi" Saita tsaya daga qofar tana yin sallamar kamar yadda suka saba. Sai data danyi jim kadan sannan ta amsa mata,ta bude labulen ta shigo,sabreen ta bita da kallo can qsan rabta wani abu yana kai kawo "Sannu da gida" Ta fada tana nufar hanyar dakinsu,don sam ba'a sake take ba,Allah Allah take ta samu waje ta yiwa wayartata ajiya me kyau. Tasan halin yaa sabreen din qwarai da gaske,tana da mugun fikira da saurin dago wani abu dake a boye,a yanzun haka kallonta da takeyi din gani takeyi kaman tana kallon wayar ne tarwai bisa idanunta. Bata iya amsa mata ba,tadai bita da kallo har zuwa sanda ta wuce dakin. Janye dubanta tayi daga bakin qofar dakin tana sauke numfashi. Bataso taji kokwanto ko shakka ko kadan akan 'yaruwarta......to amma haka kawai jikinta yake bata wani yanayi daban wanda bata saba jinsa ba akan huda din. Duk da tasan ba kowa a dakin amma hakan bai hanata kallon gabas da yamma hagu da dama na dakin ba kafin ta ciro wayar daga aljihunta,ta kuma daga katifarsu daidai inda tafi kwanciya ta jefa wayar. Tana dagowa sabreen na daga labulen dakin ta shigo hade da sallama. Wani mummunar faduwa gabanta yayi,ta amsa da sauri tana kuma waiwayawa,sai suka hada idanu da ita. Tsoronta ya qaru,ta dinga ji kamar ta ganta ne sanda take ajiyar. Kanta da taga ta dauke shine abinda ya bata relief,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya ta fara fidda uniform din jikinta. "Huda" Tayi kiran sunanta sanda ta zauna bakin gadonta. "Na'am" Ta sake amsa mata tana sakin rigar uniform dinta data kama zata fidda. Idanunta ta zube mata,kafin tace komai haneefa da nadra sun shigo,wanda already sun rigata dawowa harma sun sauya uniform dinsu zuwa kayan gida "Gashi yaa" Nadra ta fada tana miqa mata Leda "Kuje falo a samu plate a juye yasha iska,gani nan fitowa" Ta amsa musu tana binsu da idanu har suka fice kafin ta maida dubanta ga huda "Zo nan huda" Ta umarceta tana ci gaba da karantarta. Ba musu ta ajjiye dan kwalin hannunta sannan ta tako ta zauna a inda sabreen din tayi mata nuni. Zuba mata idanu tayi tamkar yau ta fara ganin fuskarta,abinda ya sake sanya ma huda fargaba da shakku "Kinsan na tsani nayi tambayar meke faruwa?,akwai matsala?......a bani amsa da babu komai....bayan kuma da matsalar.....akwai kuma abinda yake faruwar" Ta qarashe maganar idanunta har yanzu cikin na hudan. Har cikin qashinta taji tambayar tata tamkar taba hango komai tar tar,saidai kuma wani sashe na maganarsa ya bata qwarin gwiwa tare da hikimar kaucewar tuhumarta "Tunda har akwai tsoron yaa sabreen a ranki,bai kamata ki bari a yanzu tasan muna tare ba,har sai mun sake shaquwa da junanmu.....ta yadda koda ta tashi rabamu,tausayin yadda mukeson junanmu zai sanyata ta haqura......akwai lokacin da na ware da zamu sanar mata......kinga koda kuwa na girme mata nesa ba kusa ba.....amma dole nayi mata biyayya kema na tayaki yi mata biyayya ko ba haka ba?" Wasu daga cikin kalamansa da a yau suka sake sanyawa ta sake masa. Yadda ya mutunta mata yayar da duk duniya bata da abu mafi girman daraja irinsa.....bata jin zata kasa sonshi a ranta. "Me yake faruwa huda......kome qanqantarsa kada ki boyemin" Ta furta tana kallonta. Kanta ta girgiza tana narke fuskarta "Me kika gani yaa sabreen......?" Itama kanta ta kada zuwa gefe guda gami da cije lips dinta na qasa,daga qasan zuciyarta ana gaya mata lallai akwai wani abu da ba dai dai ba. "Canji nake hangowa dan kadan huda......wanda kowanne canji cikin rayuwa daga kadan kadan yake farawa" Ta amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana. Zama tayi sosai hudan tana dubanta "Ba komai yaa sabreen fa.....idan ma akwai din ni bazan boye miki ba" "Kin tabbata?" Ta jefa mata tambayar da wani nannauyan sauti dake tabbatar mata tambayar me girma ce dake dauke da tarin fassarori da ma'anoni. Kalamansa sukaci gaba da bata confidence,har ta daga kai cikin tabbatarwa "Na tabbatar" Ido ta lumshe tana gyada kai "Shikenan" Sai ta miqe itama tana daukar daya wayar tata wadda ita ta shigo da ita dakin. Mika'il takeson tabowa.......tana da buqatar fara kawar dashi daga layin,koda kudin visa passport da bill na asibitin ta samu daga gareshi,idanma so samu ne ya zamana komai ya fita daga jikinsa,ta yadda duk abinda zai samu daga bangaren mashkur din zai zamana tamkar ribar qafa ce. Akwai abubuwa da yawa da yake list dinta wannan karon da takeson yi,wanda kuma yana da buqatar muquden kudade. Akwai mutane da yawa data kwana biyu bata gansu ba,tanason a wannan karon ta jiqa kowa yadda ya kamata. Kaman yadda ta saba kebe kanta a dukkan lokaci irin haka da ya shafeta. Yanzunma can farfajiyar gidansu ta wuce bayan ta rabbatar ta sallamesu da dukkan abinda ya kamata. Me home work yana yi,me bita da hada haddar da zaya bayar a islamiyya ma yana nashi. JIB ta kira,kamar ko yaushe layinta layine na musamman da ita kadai ke kiransa dashi,hakan ya sanya baya missing call,don muddin yaga kiran yasan akwai abu me muhimmanci. Gaisuwar ban girma yayi mata kaman yadda suka saba sannan suka shiga tattaunawa kai tsaye akan ayyukan da takeso ta gama dasu "Ka sani,ba kasafai nakeson dadewa da mutum ba.....nafison nayi na gama a wuce gurin ya sake sabon lale.....ciwon aishatu shine abinda yafi dagamin hankali najeeb......banason sanadiyyar wani ayshatu ta rasa ranta......inason sama mata lafiya tare da mata tanadin rayuwa da zata manta abinda ake kira da tsanani talauci ko wahala". Can qasan ransa yake hadiye wani abu,yana cika da mamakinta ako yaushe,tana yawan sanya ranta da kanta a risk,bawai don saboda jin dadinta ko walwalarta ba......aah......tana yin komai ne kawai don jin dadin wasu. "Zamu kammala da izinin Allah......amma a wannan karon indai komai yayi kyau,adadin kudaden an samesu daidai ya kamata kema ki inganta rayuwarki sama da yadda kike a yanzu". Dan qaramin murmushi ne ya subuce mata,har jib yana iya jiyo sautinsa kadan "JIB.....kune a gabana......har yanzu inajin mutanen dake tare dani ban kaisu matakin daya dace sukai ba". Zuciyarsa ce ta karye girmanta na dada qaruwa a ranshi "Ko yanzun ma me ya rage?,kinyi mana komai,tunda muna iya tsaiwa da qafafunmu......mu ya kamata mu tallafeki kikai inda ya dace kikai din.....kusan dukkanmy burinmu ki samu nagartaccen miji......" "Mubar wannan maganar jib yanzu" Ta katse numfashinsa. Murmushi kadan ya saki,shima kansa yasan ya taba inda batason aje. Sau tari yakanyi mata uzuri......koda shine yaga abinda ta gani,yaji kuma abinda taji ba shakka iya hukuncin da zaima rayuwarsa shine nisantar kowacce diya mace,saidai kallo daga nesa,indai ba qaddara me qarfi da zata hada tarayyarsu guri guda ba. "Zakibi mashkur abuja bayan mun gama da mika'il" Ya furta a nutse bayan shurun daya gifta a tsakani na wasu 'yan mintuna ".....banason tafiyar nan jib" "Itace hanya guda daya mafi sauqi da zamu kammala komai hankalinmu kwance......na sani baki taba bin kowa ko ina ba......amma a yanzun zakije,na miki alqawarin ba abinda zai faru,zan baki kariya da support harki dawo,zan bi bayanku idan ta kama......kwana daya tal zaki bani zan kammala aikinsa.....mashkur din nada tsananin wayo fiye da yadda kike tunani......amma kuma kinsan kutsa kai asusun mika'il yafi na mashkur hadari da kuma tsauraran matakai da sai an masa shiri na gasken gaske?" Shuru tayi tana son fasa maganganunsa daya bata su a cure. Kanta har ya soma dan hargitsewa,sai ta gyara zamanta kadan tana cewa "Ka rudar dani jib......mashkur nada wayon da lallai sai an bishi qafa da qafa kafin cimma nasara......mika'il sassauqan wayo ne dashi......amma nasu account din yana tattare da tsaro sosai haka ne?" "Exactly boss lady" Ya fada yanason jefa raha cikin zancan. Ya jefawa fuskarta murmushi kadan kuwa,sai taja dan qaramin tsaki "A ajjiye wasa jib.....na soma gajiyawa da wadannan hadarurukan......inason muyi babban aikin da zan huta nima hakanan na kula da rayukan dake gabana da kyau" "Haka nakeso miki nima......bari na qara miki wani bayani kadan......mika'il yana riqe da ragamar babban account din dake mallakin wani kamfanin sarrafa diamond......kamfani ne ne matuqar qarfin jari da huldodin kasuwanci da qasashe daban daban.......kusan rabin kudin wannan kamfanin asusunsa mika'il yana da access dashi.....hakanan duk wani kudi da zai shiga ko ya fita yana da access da hakan.....a bincikena na lura yana wadaqa da kudin yadda yakeso,saidai kuma yana bi ta hanyar lura da saka tsantseni ta yadda ba lallai a gane hakan ba,saboda mahaukaciyar riba da matsiyatan manya manyan kudaden da kamfanin ke samu a kowacce rana....." "Matsiyata.....manya manya?" Ta jefawa jib tambayar. Qaramar dariya ya saki "Sorry......maqudan kudade" "Okay......naji kana amfani da wasu kalmomi ne.....eheeen......kaga kenan komai zaizo mana akan daidai?" "Haka nake tunani......amma ki bani kwana uku,zan duba yadda zamu kutsa cikin asusun.....amma shima dole ku hadu a ranar Koda na awa daya zuwa mintuna talatinne......ki sassauta riqon tsaurinki kiyi kaman kin sakar masa komai....." "Mtseewww....ya isa don Allah" Ta dakatar dashi,don zuwa yanzun abubuwan sun fara barin kanta,tana ji kawai lokaci ya tunkarota da zata maida kai sosai ga 'yan uwanta. Dukkansu girma suke qara yi,kuma suna da buqatar attention dinta sosai fiye da wanda take basu a baya. Jib na 'yar dariya yace mata "Shikenan......cikin kwanaki ukun zaki iya jina koda wanne lokaci,kibar wayar a bude,ki kuma fara shirin zuwa abujan.....nima zanyi nawa shirin" *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 62 "Yayi" Ta amsa masa a taqaice tana katse kiran. Shuru kawai tayi tana jin yadda iska ke kai kawo a farfajiyar wajen. Yadda iskar ke kadawa sai take jin kamar kwatankwacin yadda tata rayuwar ke garawa kenan,daga hagu zuwa dama,daga dai dai zuwa rashin daidai,amma a yanzun cikin ranta takejin lokaci yayi da zata tsaida komai.....ko a iya haka ta tabbatar tayi qwarin da rayuwarsu ba zata tagayyara ba. Tunda ta tabbatar ta fita zuwa farfajiyar gidan ta rufe qur'aninta,ta kuma miqe da hanzari ta wuce zuwa cikin dakinsu. Cikin mintuna qalilan ya cire dari darin da take na amsa wayarsa da takeyi cikin dakin. Tun tana a tsaye tana kai kawo da kuma leqe tsakanin labulayen dakin har ta koma ta zauna sosai a gefen gadon tana sauraren kalamansa dake da wani irin dadi suke kuma sake samun matsugunni me kyau a zuciyarta. Yadda dukka kalamansa suke a tsaftace,ba wani kalma ko furuci maras kyau ya sanya take sake jinsa sosai cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma yana yabawa kamalarsa da kamewarsa. Ba wani abu me muhimmanci da zaman zaiyi mata,don haka ta yanke duka tunanin tana miqewa daga inda take din tana nufar cikin gida don komawa dakinsu. Tun daga nesa kadan dab da qofar da zata sadaka da ainihin tsakar gidansu ta hangi hadiyyan. Ta ganta sarai zance takeyi,wanda dama takanyi din lokaci bayan lokaci. So samu tabi ta wata hanyar da bazata hada numfashi da ita ba,to amma kuma babu hanyar,saidai tabi zabi guda daya daya rage mata,ta koma ta zauna ta jirata har ta gama zancan tabar wajen. Wannan abunne kuma takejin ba zata iya ba,duk abinda ta niyyaci ko nufaci yi ba kasafai take bari dalilin wani ko wata ya sanyata ta juya da baya ba. Tunda ta doso gurin ta fuskanci hankalinsa ya dauku a kanta. Ba baqon abu bane a wajenta saurin gane motsi ko manufar d'a namiji a kanta daga kallo daya tak. Dauke hankalinta da idanunta tayi daga wajen kamar bata san da zamansu ba tana wucewa ciki. "Wannan 'yar gidanku ce itama kenan?" Ya maida hankalinsa ga hadiyya yana tambayarta wadda tuntuni idanunta suna a kanshi,cikin wani irin banzan kallo da bacin ran yadda yake kallon sabreen din "Eh 'yar nan dince.....sai akayi yaya kuma?" Ta bashi amsa a matuqar fusace har sabreen dake gab da wucewa tana ita jiyota. Kanta ta girgiza kawai tana sakin siririn murmushin nan nata maras sauti me dauke da tarin ma'anoni masu yawa. Itakam daga hadiyya har dukkan wani gajan baqo da zayazo wajenta bata tunanin akwai wanda ya isheta kallo a cikinsu. "Ina kuma hudan?" Sabreen ta tambaya tana kallon sararin da tabar hudan a zaune kafin fitarta "Ta shiga daki" Haneefa ta bata amsa. Labulen daya sakaya qofar shiga dakin tabi da kallo "Daki kuma?,me takeyi a ciki?" "Ban sani ba wallahi.....naga dai ta shige" Nadra da aka miqawa tambayar ta amsawa sabreen cikin rashin taqamaimen amsa "Tun yaushe ta shiga din?" Ta sake tambayar nadra wannan karon qasa qasa. "Baki jima da fita ba" Ta bata amsa itama da yanayin yadda tayi mata tambayar. Bata son saka ko darsa wani abu a ransu,don haka tadan sake rantabrana kallon nadra "Rufe littafin data bari a bude din" Batayi gaggawar shiga dakin ba don kada ta barwa zuciyar yaran wani hasashe,saita koma ta bude fridge ta dauko ruwa,ta qarasa gaban first aid box dinsu dake ajiye cikin falon t dauki paracetamol ta taka zuwa dakin. Daidai sanda ta shaqi wani sassanyan numfashi daya cika fal da farinciki da kuma shauqin soyyayya,daidai lokacin ta daga labulen dakin tana takowa zuwa ciki. Mutuwar kwance tayi sanda idanunta suka ga shigowarta,sai ta kasa ci gaba da maganar da taso ci gaba da yi. Tana iya jinsa yana cewa "Hellooo.....my love.....hello" Amma ta kasa kowanne motsi. Duk sautin maganarsa qwaya daya ji takeyi kamar zata saki fitsari,don tana ganin yadda sabreen din ke matsowa tsaf zata iya jin sautinsa. "Me kikeyi a kwance bayan sallar magariba?.....kuma na barku ne kuna karatu?" Ta mata tambayar tana kafeta da idanu,gami da zama saman drawer dake tsakanin gadajen nasu. Shuru yayi daga inda yake zaune yana bin sakannin da suka kwashe da ita akan waya suna qara gudu,yana kuma sauraren sautin muryar sabreen dake ratsowa ta cikin wayar zuwa kunnuwansa tare da sake tuna masa abubuwa masu yawa da suka shude tsakaninshi da ita. Numfashi taja ta sauke,lokaci daya yadda zata sauya daga ainihin yanayinta yazo mata,saita bata fuska "Banajin dadi ne". Inda hankalinta cikin jikinta yake a lokacin ba shakka babu abinda zai hanata jiyo sautin fitar murmushinsa. Ko iya hakan yana gwada masa samuwar matakin nasara daga gareshi. Ta yadda ya bibiyi diddigin rayuwarsu.....a yadda bincike ya fito masa.....basa iya boye mata komai.....komai girman laifinsu ko gaskiyarsu.....komai tsanani ko maslaharsu.....ba wani abu da suke iya lullube mata shi,yau gashi ya fara taka matakin nasara......ta koya qarya saboda shi. "Me yake damunki haka nan da nan?" Cikin qwarewa wajen iya bankado abinda ke lullube ta tambayeta. Tambayar data sanyashi jingina bayansa da kujera yana jiran jin amsa ta biyu "Kaina ne yake ciwo" Sai ya tsinci muryar sabreen din tana bada amsar da hudan ce ya kamata aji haka daga bakinta. Yadda ta bada amsar ya sanya huda daukewar numfashi daga jikinta na wucin gadi,tare da sanya Naseer tattara hankalinsa akan wayar,kadan kadan fargabar kada ya zamana ta gano meke lullube tana son saukar masa. "Ga magani tashi kisha" Ta sake cewa da huda tana miqa mata kofin ruwan dake hannunta tare da satches na maganin. Ruwan da maganin duka tabi da kallo,ta fara motsawa kadan sannan ta miqe da sauri ta zauna tana sakin wayar. Santsin pillow din ya sanya ta zame ta kuma sulale ta sauka a gefen cinyarta saita matsa kadan tana qarasa danneta. Ci gaba tayi da dubanta har zuwa sanda ta balla maganin tasha,sai ta miqa hannu ta karbi rayuwar ruwan da maganin itama ta balla ta sanya a bakinta tabi da ruwa "Ba abu mafi sauqin fade irin ciwon kai.....amma ki sani,yawan kiran sunansa yana iya jawoshi koda babu shi a wajen" Ta fadi tana qarasa sauke idonta a kanta. Tsoro da fargaba ya sake cikata,saita lumshe idonta tana son dasa gaskiyarta a zuciyarta "Nima zamana kenan na jishi ya saukar min,na dauka nadan lokaci ne xai sauka idan na kwanta" "Allah ya sawwaqe" Ta fada a taqaice tana takawa a hankali hadi da ficewa daga dakin. Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fidda idanunta waje,tana iya jin yadda bugun zuciyarta ke kai kawo wanda ta tabbata tsoro razani da kuma firgici ne ya haifar mata dasu. *****Tsakanin asabar da kuma lahadin yana da isashe lokacin da zaiyi shirin komawa bakin ayyukansa zuwa litinin,wannan ya sanyashi maido da dukan ayyukansa da suka tsaya sakamakon tafiyar da yayi. Shi kansa yasan satin da zasu shiga din ba satin zama bane,babu hutu sam a tattare dashi. Aikine me yawan gaske,don bayajin zai zauna ya huta har sai yakai ga gacin kammala komai ya kuma bude kamfanin da a yanzu shine cikar burinsa. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 63 Sassanyan yammaci ne dake bada wata irin iska me dadin shaqa da samar da nutsuwa ga zukata,hakan ya sanya zaman wajen yayi masa dadi ,wanda tun bayan sallar azahar ya zauna a nan din. Yau din zama sukayi sosai da mu'allim,wanda shi yake kula da bangaren masu buqata ta musamman da kuma neman taimako. Ya karba list na mutane masu yawa,ciki harda list din anni dana maamah wanda ya jima yana kallonshi. Sunaye na mutane barkatai,wanda yafi kyautata zaton an shirya sunan ne kawai an kuma shigar. Ya karba takardar da zummar zai duba din,don hatta da numbers na wayoyinsu dake a jiki kallo daya yayi musu yaji sunfi masa kama da lambobin bogi. A yanzun ya gama shigar da komai cikin laptop dinsa da kusan zaiyi wahala ka ganshi ba ita. Tana dauke da muhimman bayanansa da kuma sirrika sosai a ciki. A yanzu da yake zaune yana karbar kira ta kai tsaye ta cikin system dinsa. Video call ne da daya daga cikin kamfanin narka gold da wankeshi daga qasar china,farouq ya tako yana isowa farfajiyar. Kujera yaja ya zauna,sannan ya fidda wayarsa yana duba saqonnin WhatsApp da tun daxun ya sauka da zummar zai koma din. Hira sosai suka shiga yi da fannah,don kusan duka saboda ita din ya hau. Jifa jifa yana mata gajeran voice note don kada ya janye hankalin fu'ad da baqonshi. A nutse ya kammala amsa kiran,yayi disconnecting sannan ya maida dubansa ga farouq. Idanu yadan zuba masa,yana mamakin yadda yakejin dadin soyayya gaba daya,wai shin mene a cikinta har haka da take iya maida mutum wawa ne?. "Ya dai?" Yaji muryar farouq din yana katse masa tunaninsa "Am just wondering...." "For what?" Farouq ya katse masa magana yana maida masa tambaya murmushi dan kadan yana fita a fuskarsa "Yadda mutum me hankali yake komawa kaman soko.......wannan abar farouq It doesn't make sense wallahi" Ya fadi iya gaskiyarshi,gaskiyar da har saman fuskarsa zaka hangeta kwance quru quru. Dariya ce sosai ta qwacewa farouq har yana duqawa,abinda ya sanya fu'ad tsaiwa ya zuba masa ido yana kallonsa. "To abun kuma ya fara cin qarfina,to be sincere ka fara bani tsoro sama dana baya.......nafi tunanin kuma yanxun bawai aljana bace ta aureka ba,tunda koda aljana ce saida soyayya ai ko?" "Kai ka sani qaton banza" Fu'ad din ya fada yana jifansa da wata harara data sake sanyawa farouq ya fashe da dariya,don irin wannan hararar kawai yake iyayi masa idan ya quleshi ya kaishi bango. Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi don kada ya jawowa kansa jagwal ko yaqi bashi hadin kai akan batun da yazo masa dashi,ya sani sarai kadanne daga aikinsa ya murje idanunsa,musamman yanzun da har ya shiga gonarsa ya kuma tsokaneshi. "Mu ajjiye wannan batun.....ina nan dai inayi maka addu'a.......na saka a duba mana ticket zuwa abuja Saturday in sha Allah......already ma nayi payment zai mana printing ne kawai" "Bazanje ba" Ya bashi amsa kai tsaye yana qoqarin shutting down system dinsa idanunsa saman screen din. Fuska farouq din ya narke yana koma masa kalar tausayi "Sai na tafi ni kadai.....amma kuma idan ta tambayeka,zan bata labarin ka saba Alqawarin da mukayi da kai ne" Yakai qarshe yana zuba ma side na fuskarshi idanu. Shuru yayi kawai bai sake cewa komai ba,wanda alamu ke nunawa farouq zaiyi wahala yace bazaije din ba. Sau tari shuru a wajensa alamu ne na accepting abubuwa,idan baya so kai tsaye zaice baiso kuma bazaiyi ba kaman yadda yanzu ya fada mishi da farki,yana sane kuma ya sanyo zancan cika alqawarin......don ya sani shi din mutum ne da ba abinda ya tsana irin qarya sam sam,idan kanaso kaga tunzurarsa ko fadansa to kayi masa qarya. "Ya ake ciki maganar ginin?" Farouq ya sanyo masa maganar da yasan yanzun itace a gabansa sama da ko wacce. Sai kuwa ya qarasa kashe system din ya rufeta yana dora fararen idanunsa akan farouq din. "Ending month dinnan nake sanya ran gini zai kammala,sai preparation kawai na budewa wanda shima banaso ya wuce watanni biyu.....duka engines da sauran kaya next week zasu iso in sha Allah" . Kai farouq yake jinjinawa,yana matuqar yabawa da hazaqa da qoqari irin na fu'ad din. Tun farko yasan idan don ta shine bazai iya ba......don haka ma ya saki wannan ragamar kawai ya miqawa fu'ad din,don tunda shi ya faro barota shine zai iya. Qaramin murmushi farouq din ya saki,fu'ad ya dage masa gira alamun tambaya "Ba komai.......kawai na tuna temple run dinka ne......rigimammen dan bautar qasar da yaje garin wasu ya musu barna.....ya kuma gudo da abinda suke ta buri da nacin samu......Allah inda a zamanin yaqe yaqe ne zakayi barna da yawa fa" Maganar dole ta sanya murmushi kubcewa daga fuskar fu'ad,ya zauna sosai yana sake duban farouq "Mazantaka a zuciya take farouq......sannan dukkan namiji muddin zai amsa wannan sunan dole kalmar TSORO ta fita daga dabi'arsa......bai halatta ba sam sam namiji ya zama me tsoro ba..... Idan hakan kuwa ta kasance a matsayinsa na shugaba kuma jagora,dole al'amura su lalace..... Adinga ganinsu kuma ba'a yadda suke ba". Duk da tsananin gajiyar dake a jikinta bayan dawowarsu daga wajen boka DURGUJI amma hakan bai sanyata zama ta huta ba bare akai ga batun kwanciya. Kai kawo kawai takeyi tsakanin kitchen da dakunanta cikin sabgar dafawa da saukewa. Wani tsari da takeson fara qirqiro dashi a yau din,don shine hanya guda daya da zata samu ayyukan da aka tsara mata su tafi yadda takeso. Ta bata lokaci sosai tana son tuna wanne abinci da wanne abinci sukafiso ta dafa musu lokacin quruciyarsu?. Da qyar ta dinga tuna wasi abubuwan da suma shafesu saboda yadda ruhi da zuciya suka jima da yin nisa daga rayuwarsu dama komai daya shafesu. Tayi lissafin abubuwa guda hudu duk da tasan sunfi hakan,saidai sauran ta barwa ranta zata nemi ganin ma'aikatansa da yake yawan rayuwa dasu don samun wasu amsoshin. Anni ce tasan wadda zata samu amsar kai tsaye daga gareta,saidai zuwa yanzun tana jin cewa tafi qarfin anni ballantana ta sake neman wani abu daga wajenta akan 'ya'yan da ita tayi cikinsu ta kuma haife abinta. Alwashi taci......tana nan kuma riqe dashi......hakanan ba zata runtsa ba ba kuma zata huta ba har sai ta samu cikar wannan alwashin nata. Tana aikin masu aikinta suna mamakin shigarta kitchen yau da kanta. Duk kallon da suke binta dashi bata samu nasarar tantancewa ko kuma kula ba,saboda hankalinta yayi matuqar nisa akan maganganun da suka tattauna da durguji. _"sau daya nakewa mutum aiki na gama dashi.....muddin kuma nayi aiki baici ba yana da wahala na sake na biyu indai ba sa'a ka taka ba......aikinki me hatsarin gaske ne......duk abinda kikaji ko kika gani kada ki wuce wata guda kacal baki dawomin ba"_ Ita batun sake aiki da rashin sakewar duka ba damuwarta bane,tunda ta riga data sani kudi suke juya akalar kowa su kuma sauya tunaninsa. Muddin zata zube masa kudi ta tabbatar duk taurin kansa sai ya sake waiwayarta. Kawai abinda yake damunta a yanzu shine yadda zata samu dawowar hankulansu a kanta,ta yadda cinsu da shansu zai dawo qarqashinta,wanda wannan shine abu guda daya tal da zai sanya aikinta ya tafi yadda ya dace. Tana kammala white rice sai ta kasa haquri ta fita a kitchen din. Dakin gadonta ta wuce ta samu saman sofa bed ta zauna tana latsa wayarta. Number fu'ad din ta fara kira,daidai sanda yake zaune suka ci gaba da tattaunawa da farouq yana nuna masa tsarin taswirar ginin kamfanin. Fararen idanunsa ya daga yana azawa saman wayar. Zubawa wayar idanu yayi yana kallon yadda sunan ke wucewa ta saman screen din. A duk sanda zaiga shigowar kiranta sai yaji wani abu tun daga qasan ransa har tafin qafafunsa. Inda yana da iko bazai daga wayar ba sam sam,to amma wata fuskar tafi gaban mari "Ina zuwa" Yace da farouq yana daukan wayar ya daga ya saka a kunnensa. Cikakkiyar sallama tayi da kwantacciyar murya da zai iya cewa ya manta rabon da yajita daga bakinta,wani abu guda daya sake jan hankalinsa,saidai bai hanashi amsa sallamartata ba hadi da dorawa da fadin "Barka da yamma" Dan murmushi ta saki kadan "Yauwa barka kadai Muhammadu" Ta fada cikin nuna kulawa "Ka wuni lafiya kai da dan uwanka?,tunda har yanzu ban cancanci a kullum naga lafiyarku ba......hasalima kamar kuna mantawa ne da rayuwata" Yadda tayi maganar ya taba ransa kadan,yaji sautin da amon da ya jima baiji daga gareta ba "Kiyi haquri ba haka bane" Ya maida amsa wani abu yana kai kawo a ranshi "To idan ba haka bane yaya ne Muhammadu?,kamanhar yanzu kun kasa manta abinda ya faru ne kawai" Idanunsa ya lumshe kawai yana saurarenta. Zuciyarsa nadan qara bugun da takeyi yana jin wani abu sosai can qasan ransa da kuma wani sashe na zuciyarsa "Idan zaku iyayimin alfarma,inaso ana gama sallar ishai ku shigo kai da musaddiq....inason ganinku duka ku biyun" "In sha Allah" Ya amsa mata kai tsaye. Wayar na a kunnensa har ta yanke Kiran,sai shima ya zame wayar daga kunnensa yana kallon screen din. Sanda ya daga idanunsa sai suka hada ido da farouq,murmushi farouq din ya sakar masa kawai. Har yanzu bai taba saka baki ko shiga lamarinsa da maamah ba,infact ma shi bai taba masa magana a kanta ba,ko yaushe shida sadiq suna qoqarin kiyaye iyakokinsu ne. Wani irin murmushi ta saki bayan ta ajiye wayar idanunta akan qofa tana jin wani farinciki yana shigarta. Nasara ce a kusa take shanshanarta......kuma jikinta yana bata komai yana kusa da qofarta. Plan dinta guda uku ne qwarara,ta fara da wannan na farkon,idan yayi aiki shikenan,idan baiyi ba zata wuce plan B,idan shima yayi aiki shikenan,idan kuma shima baiyi ba tana da plan C......wanda shine tsororuwar shiri mafi tsauri da tauri.....plan din data tabbatar zai yamutsa hazo iya yamutsawa........ita kuma zata saki dukkan wata iyaka da ikon da Allah ya bata don ganin tabbatuwar plan din da kuma wanzar dashi. Ranta fes,Zuciyarta wasai ta ajiye wayar ta koma kitchen tana shirye shirye shirye gadan gadan. Haka kawai yakejin yanayinsa wani iri,jikinsa da zuciyarsa dukka ba'a sake suke ba,a haka ya shirya cikin Moroccan abaya ne sulbi ya wuce zuwa sallar magariba. Kafin ya isa masallacin suna hanya shi da farouq musaddiq da saddiq suka biyo bayansu. Wannan din wata kyakkyawar al'adarsu ce da anni ta renesu a kai. Muddin suna garin ko suna qasar,hakanan ba wani babban uzuri ko aiki bane ya riqesu a kamfani,to zaka samesu a gida duk inda magariba tayi. Kwata kwata basusan yawon dare ba,farouq ne ma medan sha'awar fitan daren,to sukan fita jifa jifa su zaga a mota su dawo. A nan zasuyi sallar magariba suyi ishai,suyi dinner tare me uzuru ya wuce nasa uzurin. Sanda yake sabule tattausan flip flops din qafarsa yace da musaddiq ba tare daya waiwayo ba "Bayan ishai ku shirya kaida saddiq zamu shiga wajen maamah" Dan kallon yayan nasa kadan yayi,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya amsa da to. Tun bayan magariba ta sallami kowa tare da kafawa kowa sharadi da dokar bataso kowa ya sake tako mata parlor sai gobe idan Allah ya kaimu. Ta duba doormat din bakin qofar falon yafi sau goma daga zamanta,ta kuma tabbatar komai yana nan intact kamar yadda ya kamata ace ya kasance din,sai ta koma ta zauna tana sauya tashar Tv din zuwa mbc Bollywood bawai don tana jin dadin kallon ko yana burgeta ba,dukkan hankalinta yanzu da nutsuwarta shine takowarsu cikin falon,su zauna kuma su cika cikin su da abinci da abin shan da ta tsumashi ta kuma tanadashi musamman saboda su. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 64 Saddiq da musaddiq dinne a gaba shi kuma yana biye dasu a hankali a hankali,hakan ya sanya suka dan masa tazara kadan. Wayar Mika'il yake amsawa,wanda yakeso ya tabbatar komai ya zama daidai zuwa ranar Monday da zai koma office. Yanason ya gabatar masa da dukkan wasu mu'amala na kudi da banking ya samu bayan tafiyar tasa,komai na shige da ficen kudi. Yana wayar ne amma hankalinsa yana kan saddiq da musaddiq,tamkar 'yan biyu kamar yadda kowa yake musu kallo hatta da makarantun da sukayi. Suna hira abinsu ne cikin wani irin shaquwa da jituwar jini. Malam saidu ne ya bude musu qofan da kanshi,ya rusuna kuma yana miqa masa gaisuwa sai ya gyada masa kai hadi da daga masa hannu saboda wayar da yakeyi din,ya taka a nutse yana bin bayansu. Dab da zasu isa steps din da zasu sadasu da ainihin falon yaji gabansa yayi wani mummunar faduwa "Zamu qarasa anjima" Yace da Mika'il a gaggauce yana katse wayar ba tare daya jira amsarsa ba "Kai saddiq" Ya furta da muryar da taja hankalin maamah dake falon,wadda dama dukkan tunaninta yana fa farfajiyar gidan tana sauraren kowanne motsi. "Saddiq kuma?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance,sai ta tuna kuma bata da sauran lokacin batawa,don muddin ta bari wani bayan yaran nata ya taka wannan shirin akwai matsala,don haka ta zabura tayi zumbur ta miqe ta kuma nufi bakin qofar falon da sassarfa. Wancakali tayi da doormat din,ta sanya hannu ta dauke abun da yake qasan,sannan ta finciki tsintsiya dake ajiye a can wani gefe daban ta fara tattara sauran abubuwan da suka rage. "Kunyi addu'a ne?" Ya fada yana tsaresu da idanu duka su biyun. Juna suka kalla shi da musaddiq din "Hamma ai daga masallaci muke" Saddiq din ya fada dukkaninsu suna sauke qafafunsu daga saman steps din da suka fara dorawa "Kuyi addu'a kafin ku shiga.......haka musulunci ya koyar damu,kome zakayi akwai addu'ar da akeyi masa" Ya fadi idanunsa akan musaddiq "To hamma" Suka fadi sannan suka maida qafafunsu kowa bakinsa yana dan motsawa. Da kallo ya bisu zuciyarsa cike da wani wasi wasi da baisan daga inda ya samo asali ba. Sosai hankalinsa yana kan musaddiq da ya tabbatar baisan komai akan shirin maamah nason raba tsakaninsu da iyalin alhaji hamza ba. Shi kansa abban baisan komai ba akai,shi daya yake juya maganar tsakanin qirjinsa da zuciyarsa. Dan ja sukayi suka tsaya sanda suka sameta duqe tana tattare wani abu da basusan meye shi ba. Ta daga kai tana dubansu,wani irin bacin rai ya cika mata zuciya fal. Ta yaya banda sun raina umarninta zata ce tana buqatar ganinsu su biyu su rakito mata wani?. Fushin yanason yayi galaba a kanta amma tanata qoqarin danneshi. Yanzun ba lokacin nuna fushi bane ko fada..... Lokaci ne na sauke kai da maida komai ba komai ba muddin nasara take da buqata,wannan shine abinda hajja ta gaya mata. Dole ta qirqiro murmushi tana cewa cikin nuna kulawa a garesu gaba daya "Maraba da 'yan samari na" Saita zubda abun cikin kwandon shara ta kuma taka zuwa ciki tana fadin "Ku qaraso mana". Sai da suka fara shiga sannan yabi bayansu yana kula da hagu da damansu "Ina ma'aikatan suka barki kina shara?" Fuad ya furta da nutsatsiyar muryarshin nan yana zama hannun kujera hannunsa goye a qirjinsa yana kuma qoqarin karantar komai dama motsin komai dake a falon. Dan murmushi ta saki tana zama saman daya daga cikin kujerun alfarma dake falon "Ina buqatar kebewa da 'ya'yana,nayi sirri dasu irin na uwa da 'ya'yanta,shi yasa na sallamesu yau da wuri". Maganar tata sai ta kasance kamar ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse guda,don haka saddiq sai ya rusuna kawai yana gaidata. "Lafiya alhamdlh saddiq......ya mutanen gidan?" "Suna lafiya maamah" "Ma sha Allah,don Allah kace ina gaidata da kyau da kyau" "Zataji in sha Allah......hamma zan qarasa,saikun fito" Idanu fuad din ya zube masa,yayin da maamah ta bata fuska tana cewa "Ina kuma zaka daga shigowarku ko zama bakayi ba?". Dan murmushi yayi yana saukar da kansa qasa cikin girmamawa "Gida zan qarasa,jibi zamu koma company ban kuma gama shiryawa ba,kinsan kuma hamma......bazai dagan qafa ba idan aka samu kuskure" Tabe baki tayi kadan ta yadda ba lallai bane su fuskanta,qasan zuciyarta kuma cike fal da baqinciki da bacin rai,amma kuma a fili saita saki murmushi "Gaskiya ne,to Allah ya taimaka,ka gaisheta" "In sha Allah" Ya fadi yana waiwayawa gefan musaddiq ya bashi hannu yadda suka saba yana yin gaba. Shiru falon ya dauka sanda saddiq ke ficewa,cikin ranta take gayawa kanta da kanta saura kadan komai yazo qarshe.... .watan watarana saidai ya gifta katangun kamfanin ya ratse ya wuce ta bayansu,komai na wata dama ta shiga cikin kamfanin baida ita. Sai daya kammala ficewa tsaf sannan ta maida dubanta garesu,dukansu ta fahimci kamar hankalinsu baya tare da ita,don haka ta danyi gyaran murya,gyaran muryar daya sanya dukansu suka dubeta,sai ta saki musu murmushi. Amsa gaisuwarsu dukka su biyun tayi,a yau sai take jinta kamar a aljannar duniya,sai takejin kamar burinta ya gama cika duk da an samu matsala a karon farko,amma akwai tafiya ta gaba,ta tabbatar ba zasu tsallakewa abincinta ba. Tanaso a yau tasan abubuwa masu yawa game da rayuwarsu,tanason tasan adadi da zurfin dukiyar da kowannensu ya mallaka,koda batasan duka ba,tanason ta karanci kaso me tsoka. "Ina fata dukkaninku kuna lafiya" "Alhamdulillah" Suka fada kusan a tare kowa ba karsashi a tattare dashi. Ta fahimci hakan,don haka ta gyara zamanta tana fadada fara'ar fuskarta "Ina fatan zaku cire komai daga zuciyarku,kuci gaba da kallona a matsayin mahaifiyarku,komai zai wuce mu fara gina sabuwar rayuwa tsakanina daku.....ina buqatar 'ya'yana a kusa dani kamar yadda kowacce uwa take da buqatar 'ya'yanta. Inaso na kasance daku tamkar komai bai faru ba,nayi alqawarin baku farinciki da kariya kaman yadda kowacce uwa ke bawa 'ya'yanta" Ta qarashe maganar cikin matuqar raunin zuciya da karyewar murya kamar wadda ke shirin sakin kuka. Dukkaninsu dubanta suke,kowannensu da mabanbancin feeling a zuciyarsa,saidai kuma dukkaninsu akwai mamaki danqare qasan ransa. Ci gaba da dubanta fu'ad yayi mamakinsa yana qaruwa. Tunda ta fara magana baiji inda tace tayi nadama ba......nadama koda qwaya daya akan abinda ta yiwa abbansu ba,su din basu da buqatar ta nema yafiya ko afuwarsu,tunda itace ta haifesu,tayi silar kowasu duniya.....ba wani abu da zasuyi mata wanda zasu saka mata da iya wannan aikin......amma kuma abban fa?,kota manta cewa itace silar komai?,ta manta itace silar faruwar komai?. A yanzun ya Fatimid tafi buqatar hankalunsu a kanta da abinda suka mallaka sama da nadama neman afuwa ta zahiri da yafiya daga mutumin da aka zalunta wanda yanzu haka yake kwance a qarqashin qasa. "Banaso ku dinga nesa dani suka nesanta kanku dani,bani da wani abu dana mallaka a yanzu sama daku.......ina zaune ni kadai,idan mutuwa ma nayi kenan saidai kuji labari daga wajen bare?" Ta maida tambayar kan fuskar musaddiq. Kanshi ya girgiza mata yana sauke kan nasa qasa. Har yanzu idanunsa da sauran tunaninsa sun kasa goge masa komai,ballantana hammansa daya tabbata komai yana rubuce ne a allon zuciyarsa. A duk sanda ya kalleta sai ya tuna ruwan data watsa saman fuskar majinyacin mahaifinsu sanda ya buqaci ta bashi ruwa,shine ya zame masa rumfa yaje ya kwanta a samanshi da zummar kareshi saboda sanyi da yadda ya jiqe din sosai,a sannan ta taka ta fice a dakin hankalinta kwance tana waqe waqe abinta. "Don Allah koda abincin dare ne ku kasance tare dani ko na safe... Ku bani koda awa daya kowacce rana mu zauna ni daku nasan na haifi 'ya'ya nima kamar kowacce uwa.....don Allah" Ta sake fada da muryar roqo sosai,raunanniyar muryar daka iya sauko da tausayi a zuciyar wanda baisan manufar me magana ba. "In sha Alla" Kawai fu'ad din ya furta. Ya sani koma me zaice yanzu ba maslaha zai kawo ba,ba kuma zata taba fahimta tunda akwai banbancin manufa a tsakaninsu. Kowanne a cikinsu abinda ya ajjiye a zuciyarsa daban. "Muje ga abincin dare can na shirya muku.....abinda nasan kunfi so sosai" Ta fada tana murmushi ranta yana mata dadi da yadda suka karbi request dinta suka amince da xuwan nasu. Ba wanda ya musa mata,suna dai binta da ido da kuma hankulansu har xuwa sanda ta jawa kowannensu kujerar zama tana fadin "Bismillah" Inda ta kasance daga kujerar dake facing dinsu. Serving nasu komai da komai tayi,tana yi tana jansu da hira tare da qoqarin tuna musu wani abu na daga quruciyarsu. Shidai fu'ad idanu ne kawai nashi ba tare daya iya maida komai ba,har ta kammala tana fadin "Gashinan kowa ya dauki nasa". Duban abincin yayi da kyau,gaskiya ta fada batayi kuskure ba,a baya baida abincin da yakeso irinsa,amma tun daga ranar data dafa abincin cikin gidansu,ta kuma yiwa mahaifinsu haramiyar abincin a sanda yake kwance yana jinya.....yunwa take sake take rawa wajen galabaitar dashi,ta hana masa abincin,abinda yayi silar kwanansa da yunwa,tun daga ranar har kawo yau bai sake saka irin abincin a bakinsa ba,daga ranar ya fita a ransa,fita ta har abada wadda har yau bai sake dawowa zuciya da rayuwarsa ba. "Shikam hamma ai maamah yanzun wannan ba cimarsa bane......nima kuma kin manta dama ba kasafai na fiya ci din ba?" Musaddiq ya fada yana shafa kanshi idanunsa cikin na maamah din. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 65 Wani abu ne yaso ya tsaye mata a rai,tunzura takeso tayi amma kuma tana gayawa kanta ba yanzu ba......idan ma basuci na yau ba ai na gobe yana nan,muddin kuma zasu ci gaba da taka qafarsu cikin gidan yau ko gobe nasara tana nan tare da ita. "Yaushe Muhammad ya daina ci?" Ta yiwa musaddiq tambayar sai kuma ta maida dubanta ga fuskar fu'ad din a mamakance,saidai kuma sanda suka hada idanu dashi sai komai daya faru a wancan ranar ya dawo mata a take,amsar tambayarta ta fita kamar budewar shafukan littafi. Wani abu taji me nauyi wanda sam baiyi kama da kunya ko nadama ba,tabbas a baya din don ba cikin daidanta take ba.....ba yaran bane a gabanta ballantana abinda ya shafesu da har zata lura da meye ya damesu da wanda bai damesu ba.....amma tabbas sai yanzu ta tuna,tun daga ranar yake bar mata kwanonta gaba daya yadda ta zuba. "To amma bai kamata ace bakuci komai ba koda lemo ne" Ta sake fadi tana jan jug din gabanta tare da qoqarin raba kofunan ta zuba musun kada ya zamana komai da komai ma tayi asararsa a yau din. Idonsa still a kanta,ya miqa hannu ya jawo gorar ruwan daya tabbatar a kulle take ya soma budeta,qarar budewar ya sanya ta daga kanta zuwa gareshi tana dubansa "Ruwa kuma muhammadu?,ga lemo dai" Ta fada tana tura masa wanda ta zuba "Maamah dare ya soma yi.....idan kuma dare ya fara bana iya cin komai...." Dubansa ta sakeyi kadan sai kuma ta dauke kanta tana qirqiro murmushi "Kowa time table zai bani na abinda yakeso yaci kullum har sati guda koma sati biyu.....masu girki na musamman zan ajiye muku.....burina naga kun kusanta dani......na maida tsohuwar alaqar dake a tsakaninmu" Ta qarasa maganar tana duban cikin idanunsu. "Fu'ad" Ta sake kiran sunansa,ya daga fararen idanunsa da suka fara rusuna saboda gajiya da zama a wajen,sam baya jinsa comfortable sam sam "Me yasa kabar musaddiq tare da farouq......duk da ba laifi bane.....amma kaman zaifi cancanta ya kasance tare dakai qarqashin naka kamfanin" Shuru ya biyo baya na second uku,sai ya maida idanunsa ya kulle yana jan boyayyen numfashi. Shikam yayi imanin ba zata canza ba,ya tabbatar abune me wahala da girman gaske da zai sauya mata hali farat daya. Wannan ya sanya kowanne taku ko motsi nata yake sanya masa ayar tambaya,wani lokaci idan tayi wani move din sai yaji gaba daya kanshi ya juye yana tambayar kansa anya da gaske maamah din itace uwa ta asali a garesu?. "Kowanne bawa da abinda yafi shaawar yi yafi qwarewa a rayuwarsa......yadda abba ya ginemu shine kowa ya dauki zabinsa da ra'ayinsa a rayuwa muddin bai kaucewa hanya ba....inda kikaga farouq da musaddiq su suka zabi wannan sashen duk kuwa da cewa tare da farouq mukayi gwagwarmayar samar da abinda na gina din a yanzu.....ba wanda ya zaba masa ko ya tursashi gashinan maamah ki tambayeshi" Juyawa tayi tana duban musaddiq ranta duka a jagule,bata son kowa ya rabi fu'ad a duniya idan ba dan uwanshi ba,batason kowa yasan sirrin dukiyarsa idan zaiyuwu sai ita daya,wannan tunanin ya sanya ta yanke shawarar sanya ido me tsananin a alaqar fu'ad din da amna......don ba zata taba yarda amina ta dauki d'iyarta ta qwaquma masa ba su qarasa nadeshi. "Shikenan,Allah ya taimaka" Ta fadi tana sauke numfashi bawai don ta haqura a zuciyarta ba. Kawai tana ganin tunda komai yana kan turba bai kamata ta bata lokacinta tana dogon zance dasu ba,lokaci kadan take jira ta soma bada umarnin wanda zai shiga ko ya fita daga rayuwarsu. "To yaya sunan surukar tamu musaddiq?....koda wasa baka taba attempting kawota ta gaida mamarka ba?" Ta yiwa musaddiq tambayar tana dubansa da murmushi,cike da zaquwa da son jin kalar matan da suke shirin kawowa rayuwarsu. Wani babbab abu da yake cikin tsarin abubuwan da takeso ta yiwa garambawul idan damar da take tsimayi ta samu,tanason surukanta su zama qarqashin ikonta fiye da yadda hajja ke juya nata mulkin a gidan. Murmushi kadan ya saki,karon farko da yaji 'yar kunyarta ta sauko masa "Minal bata iya zuwa ko ina,daga makaranta sai gida.....zata zo wataran in sha Allah". Ba haka takeson ji ba,don haka ta gyara zamanta tana sake sakin fuskarta "Aah wataran yaushe kenan?,ina buqatar ganinta mu tattauna ka shaida mata mamarta nason ganinta......" Ta fadi din don da gaske tanason ganin wace ita?. Zuwan nata kuma a nan ne zata samu amsoshin tambayoyib data tabbatar ba zata samesu daga bakin musaddiq ba. "In sha Allah" Ya fadi a taqaice yana auna yadda abun zai kasance. "Kai kuma fa?" Ta waiwaya tana duban fu'ad daya tattara hankalinsa duka saman wayarsa tamkar ma baya jin abinda suke fadi. Gajiyayyun idanunsa dinnan ya daga ya kalleta,sai kuma ya maida dubansa ga musaddiq. Kan musaddiq din a qasa yana satar kallon fu'ad din ta qasan idanunsa,boyayyan murmushi nason qwace masa. "Me maamah?" Ya tambayeta da sautin muryarsa da tayi laushi sosai. "Wa ka daukomin a matsayin suruka?" Ta sake maimaita tambayar tata. "Babu fa maamah...." Musaddiq ya fadi muryarsa na nuna murmushin da ya boye. Debe kallonta kacokam tayi ta maida kan musaddiq tanason sake samun tabbacin hakan "Kamar yaya kenan?" Satar kallon fu'ad yayi sannan ya dubi maamah,yayi qasa sosai da muryarsa,duk da yasan dole ya jishi don yana da wannan baiwar ta kaifin ji "Ba wata budurwa.....tsoronsa ma suke......ba wadda take iya tararsa maamah tace tana sonshi" "Very good" Ta fada qasan zuciyarta. Tsananin farincikin da taji ya bayyana har saman fuskarta,tadan danne tana hada rai "Garin yaya?.....har yanzu halinka dinnan bai canza ba?" Ta watsa masa tambayar . Karon farko kenan da magana kwatankwacin wannan ta taba hadasu,don haka ya rasa ma da abinda zai bata amsa illa cewa da yayi "Ba yanzu ba....lokaci baiyi ba.....in fact ma da sauran lokaci" "Lokacin lokaci na ne,yana kuma tafe" Ta bawa kanta da kanta amsa a zuciyarta,amma a fili sai tace "Allah ya nuna mana lokacin". Duka hirar ba wani armashi gareta ba,amna haka suka sadaukar da lokacin har zuwa sanda ta basu izinin tafiya sukayi mata sallama suna ficewa. Suna tafe ne kawai suna dosar gidan,daga shi har musaddiq din ba wanda yace da dan uwansa komai. Sai da sukazo mabanbantan qofofin sassansu,fu'ad din ya murza key yana bude qofarsa yace da musaddiq "Shigo ciki ka zauna muyi magana" Ba tare daya dubeshi ba,ya gama budewa ya shige musaddiq din yabi bayanshi. Zaune kawai tayi tana duban kwanukan abincinta da suka barta dashi,banda ruwan gorar dukkaninsu ba abinda suka taba ko qanqani. Lemon data zuba ta turawa musaddiq din ma tana saka ran zaiyi koda kurba daya ne amma baiyi din ba shima sai ya buge da shan ruwa. Ta fahimci yana bin sahu tare da matuqar kwaikwayo ga fu'ad,iya wannan ya isa ya bata amsar cewa,muddin ta samu fu'ad ta samu musaddiq......wanda kuma wannan din shine babban qalubalen da aikin data sake amanna ba qarami bane. Furzar da iska tayi me zafi daga bakin ta,kusan komai data tsara ya wargaje babu shi,dan abinda ta amfana dashi daga zuwan nasu bai taka Kara ya karya ba. Akwai damuwa sosai a ranta da take da buqatar abokin tattaunawa,don haka ta sauka daga dining area din zuwa ainihin falon ta dauki wayarta ta lalubo hajja. "Musaddiq" Ya kira sunanshi kai tsaye sanda yake zaune saman wata qawatacciyar kujera da irinta qwaya daya ce tal cikin falon. "Na'am" Ya amsa masa. Shuru kaman bazaiyi magana ba,sai kuma ya zauna sosai yana goye hannuwansa a qirji "Inaso ka zama me takatsantsan sosai......inaso kuma ka zama me kula.....bazan hanaka zuwa gidanmu ba duk sanda kake da muradin hakan......amma kayi aiki da hankalinka da kyau......yanzun kai ba yaro bane.....ba wannan musaddiq din da ko yaushe sai hammansa yana gefansa bane don ya kula da abinda zai cutar dashi ko ya amfaneshi bane.....abubuwa sun yiwa hammansa yawa......kula da rayuwarsa yana hannunsa". Wadannan kalaman na hamman su suka dinga juyawa cikin kanshi. Duk da bai fito qarara ya masa bayani a bayyane ba,amma kamar yadda yace din shi ba yaro bane yanzun,hakanan shi a karan kansa hankalinsa ya fara dauko masa wasu abubuwan a iya zuwansu gidan yau kawai. Haka kawai ya kasa bacci a daren,har yanzu musaddiq baisan ainihin wace maamah din ba. Iya matakin da idanuwan basira da hankalin musaddiq kadai ya kaishi bai sadar dashi da ainihin wacece maamah ba........meye zata iya yi?,da wanda ba zatayi ba.......dole koda a fakaice ne ya sake nesantashi da tunkudeshi daga dukkan abinda yake ganin zai iya zama cikas a rayuwarsa. Bugu biyu tak hajja ta dauka,hakan ya yiwa maamah dadi,sai ta miqe da wayar tana nufar bedroom dinta "Na zaci kinyi bacci ai" "Aah inadai shirin tashi.....labaran ne ya zaunar dani muna lissafin abinda kamfaninsa ya samu na shekara". Ido maamah tadan fiddo cike da mamaki "Kamfaninsa fa?,yanzu lissafin shima tare kukeyi?". Dan qaramin murmushi me sauti hajja ta fidda tana aza hannunta saman kan budurwar dake kwance saman cinyarta tana amsa waya itama "To meye a ciki?,nice uwarsa fa?,akwai wani abu da suka isa su boyemin?,koda cikin gidajensu akayi abu koda da darene da safe kuwa rana bata bullowa bansan komai ba......ke banda ma ina taka birki ma wasu abubuwan......ai hatta sunnar aure da matansu sai sanda na bada iznin a yita,kuma idan anyin sai an fada min" "Innalillahi......ke hajja?" Maamah ta furta cikin tsananin mamaki "Ke?.....zauna kina wasa da lamarin yaran yanzu,kina sake musu hanya sai linzaminsu ya koma hannun matansu,keda wahalar raino da daukan ciki amma wata ita keda d'an,kin zama 'yar kallo,sai abinda tace a tsakuro a sammiki.....tun daga kan yahaya na fara daukan izina.....ban kuma zauna ba har yau har magajin gobe" . Duka mamaki ya gama kashe maamah,amma kuma bayanan hajja din sai suka gamsar da ita,ta kuma yarda cewa gaskiya ta fadi,gashi yanzun ita tana fafutukar karbar 'ya'yanta daga hannun wata ma tun basuyi aure ba?. "Yanzun ya ake ciki?,komai ya tafi dai dai ko?" Ajiyar zuciya maamah ta saki tana maida hankalinta ga hajjan "Hajja ba abinda sukaci fa?.....duk wahalar nan kin ganni da kayana suka barni....." "Karki gaggawa,idan ba yau akwai gobe,idan ba gobe akwai wani satin" "Haka nake gayawa kaina......kana iya target din abu amma shekara goma gaba kake hangowa.....zamu zuba dasu in sha Allah......wannan karon banga abinda ya isa ya hanani ko ya dakatar da burina ba" Ta fadi har qasan zuciyarta tana jin confidence akan wannan. "Sirrin samun nasararmu dama itace jajircewa naci da kafiya". Hajjan ta qara mata qwarin gwiwa. Sun tattauna sosai har na kusan mintuna talatin kafin su yanke kiran. Hajjan ta sauke wayar wani murmushi na fita daga fuskarta,tadan tsuke bakin ta lissafinta yana tafiya da nisa sosai. "Mommy ga adeel zaku gaisa" Budurwar ta fadi tana daga kanta daga saman cinyarta hadi da miqa mata wayar. Sai data kalleta sannan ta amsa wayar ta sanya a kunnenta. Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar nashi,ba jimawa sukayi sallama ta miqawa yarinyar wayar tana kallonta. Kallon hajja kawai a garesu yana da fassarori,don haka tayi masa sallama ta katse wayar ta ajiyeta a gefe tana kallon hajjan "Momy lafiya?" Numfashi ta ajiye tana dubanta duba na kai tsaye "Ina sake gaya miki......nayi miki tanadi,kada ki kuskura ki zurfafa a soyayya da kowa....don kowa a cikin rayuwarki temporary ne......akwai target dina.....kuma bazanyi missing target dina ba tabbas" Tayi maganar da sautin da zai gaya maka tayi maganar ne da gasken gaske daga zuciyarta,ta kuma yi maganar tana kafe autartata da idanu don ta sake jaddada mata girman maganar. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 66 Itama duban momyn nata take yi,ta sani tabbas momy din nata tana matuqar ji da ita.....kaman yadda ta sani taci buri sosai a kanta. Duk da hakan tana da buqatar qarin haske a maganarta,don haka ta motsa kadan "Momy.....wanne irin buri ne?,ta yaya zan iya sallamar dukkan kuma wadanda muke tare dasu yanzu?" "Bance ki sallamesu yanzu ba,tukunna dai.....amma dai abune da kika sani cewa.....ke din ba kalar qananun maza bace....ban haifeki don wani me jaririn arziqi a hannunsa ya aureki ba.....plan dina kuma idan lokaci yayi zakiji....don ku yaran yanzu kwata kwata bakusan me ake nufi da sirri ba". *****Ta jima zaune gefan gadonta tana juya wayarta a hannu. Mikail takeson kira,ta kuma shirya haduwarsu kaman yadda ta tsara zata kammala da babinsa ta kuma rufeshi kwata kwata cikin shafukanta kamar yadda ta binne maza masu yawan gaske. To amma haka kawai duk sanda tayi attempting na kiran nashi sai taji kaman kada ta kira din. Wani sashe na zuciyarta na bata qwarin gwiwar ta kira "Ya cancanci ya fuskanci komai......ya kuma cancanci kowanne irin hukunci,jin kunyar mara kunya asara ce!" Ta sake jin wani sauti daga can qasan zuciyarta yana rada mata maganar har zuwa kunnuwanta. Danna kiran tayi,ta kuma tattara dukka nutsuwarta akan wayar tana sauraren yadda Kiran ke tafiya kai tsaye zuwa layin mika'il din. A kasalance yake shiryawa,kasancewar daren jiya ya shawu. Duk da ya tsagaita shan ma,bai wani sha yadda yakeso ba,saboda ya sani safiyar yau din litinin tana cikin ranaku masu muhimmanci da zai gana kai tsaye da CEO. Mutum na farko kaf rayuwarshi dake masa wani irin kwarjini,kwarjinin daya tabbatar yana da alaqa da kamewarsa......da yadda fara'a ko murmushi sukayi nesa da fuska dama rayuwarsa gaba daya. Ya jima yana so ya shiga rayuwarsa fiye da matsayinsa,amma kuma ya gaza samun wannan fuskar. Mutum ne da idan ya zauna aiki kawai,baya daukan wata magana da ba cikin aiki take ba,kamar yadda baya daukan wasa ko kuma wargi. Yadda dukkan ma'aikatan dake aiki qarqashin kamfanin suke da iyakoki......haka nan dukkan wata magana da zaiyi dakai akwai iya adadin lokacin da yake baka. Qarar wayarsa ta ja hankalinsa sanda take saka links na rigarsa,sai ya dakata cak daga abinda yakeyi din cikin tsananin mamaki yana kallon wayar. "What a wonderful day" Ya fada qasa qasa yana daukan wayar ya zauna gefan kujera. Wani mamakin yana sake kasheshi da idanunsa suka tabbatar masa eh itace take kiransa "Yau kuma da kanta?,da wanne irin sa'a na tashi?" Ya yiwa kansa tambayar yana daga kiran ba tare daya tsawaita dogon tunani ba. Kamar kowanne lokaci tayi masa sallama wadda shikam ba kasafai yake iya tunawa da ita ba. Sai yadan daburce kadan kafin ya amsa sallamar ya dora da fadin "Good morning queen....nayi kira nayi kira har na gaji anqi a dagamin waya.... Kwatsam sai gashi na tsinci wani abu da ban taba kawowa zai faru ba". Murmushi ta saki kadan wanda ko kusa da gefen zuciyarta bai kai ba,yayin da shi kuma kunnuwansa yaji kaman zasu narke da fitar sautin sassanyan murmushin nata. Kowanne tsiga na jikinsa sai ta shiga tashi "Ka sani ko yanayin alaqa da dangantakarmu ne suka dauko hanyar sauyawa?" "Da gaske!" Ya fada da wani irin murna daya kasa boyuwa yana fidda idanunsa waje "Eh mana....." Ta amsa masa a taqaice. "Yes!" Ya sake fadi da wani irin dadi yana mamayarsa "Indai haka ne kiyimin proving mana......" "Kamar?" Ta jefa masa tambayar da zazzaqar muryartan nan,don wajen da takeso azo kenan tana tunanin kuma ana gab da zuwa din,saidai ita ba zata iya requesting ba har sai ya nema da kanshi "Mu hadu yau.......don Allah kada kicemin aah". Shuru tayi cikin salon jan aji,kaman bataso "Please mana.....please,kice to" Ya fadi murya a raunane cike da fatan samun amincewarta "Shikenan" "Oh god......" Ya sake fadi yana dukan kujera da hannunsa,yana kuma ji duk duniya ba wani d'a namiji da yakaishi sa'a yau dai a duniya. Yana nashi bidirin amma nata qasan zuciyar a quntace. Wani mugun tsanarshi take ji da haushinsa. Da gaske wannan din dabi'arsa ce bazai kuma taba canzawa ba,ko shin mata nawa ya lalata da kalar wannan mummunar dabi'ar tasa?. "Bansan da wanne irin yare zan gode miki ba....amma zakiga godiya a aikace har saikin rasa da meye zaki maye min gurbin hidimata a gareki......tabbas zan ninka darajarki.....zan daukaka martabarki a idanun duniya......zan maidake tauraruwa cikin mata....zan miki ado da gold irin adon da sai 'yar gata...." "Thank you......thanks" Kawai tace dashi don tanaso ya dakata daga zubo wannan dogon sharhin nasa. Tana tausaya masa a daren yau irin barnar da zatayi masa,ta tabbatar wadannan maganganun da yake jerowa a yanzu saisun koma sumbatu. "Zan shiga company akwai lissafin da zamuyi da boss dina.....duk inda la'asar yayi koda bamu gama ba zan dauki excuse......zan kama mana daki a Bristol,zan tura miki details da komai da komai". Baki ta tabe tana jin wani haushi yana cikata. A daren yau bashi ba,hatta da boss din nasa saita sakasu a lissafin da babu fita. Tanaji a jikinsa ma shi da boss din basa zaiyi wahala idan ba zamuje ta tadda muje mu ba. A yadda yakan bata labarinsa lokaci bayan lokaci......irin kudaden da yake wasa dasu da kuma shekarunsa talatin da bakwai a duniya amma ace ba macen aure?,to idan ba sheqe ayarsa yakeyi ba me yakeyi kenan?. Ture wannan tunanin tayi daga zuciyarta don a halin yanzu bashi da amfani,abu guda daya ta sani ba sassauci,kuma a yau din takeso mika'il ya zama tarihi cikin rayuwarta,shi kuma ta bashi darasin da zai sanya rayuwarsa tayi laushi da kyau. "Ba laifi...." Ta amsa mass,bata kuma jira cewarsa ba ta dora "Ina fata kasan rule din.....zaka rigani isa gurin da wasu mintuna......kuma bana buqatar kowa yasan muna tare ne da kai" "Dukka dokoki da qa'idojinki kisa a ranki an gamasu......ranki ya dade.....da zaki bani dama da kin fadi inda zan aiko driver ya daukomin ke.....don bana buqatar kiyi wahala" . Wani sirrintaccen murmushi ta saki "Na maka uzuri saboda baka jima cikin rayuwata ba bare ka fahimci wacece ni......zanzo da kaina,bana buqatar kowanne driver" "As you wish.....saidai zan saka kudin transportation.......please karkice min aah" Idanunta ta lumshe sannan ta budesu,har ta fara gajiya da dogon hirarsa "Alright....byee" Ta furta a taqaice tana tsinke wayar. Ajiyeta tayi gefe tana furzar da iska daga bakinta. Inda ace dukka haka mazan aure suke ba shakka a jiya da kunnuwanta basu jiye mata abinda taji ba saman dogon layin masu lalurar ciwon zuciya dake dakon ganin likita......tabbas da idanunta basu gane matan auren da hawan jinin bacin rai da baqincikin d'a namiji ya jefa musu hawan jinin daya juye musu zuwa ciwon zuciya ba......da bataga matar data yanke jiki a wajen ta fadi ba......wadda daga qarshenta gawarta aka fitar a asibitin 'yaruwata na kuka dukka sanadin baqinciki namiji. Ita kuwa me zatayi da aure?......wanne tsautsayi ne zai kaita damqa rayuwarta hannun d'a namiji guda daya yayita hajijiya da rayuwarta ba gaira ba dalili?. Abubuwan data gani din dasu ta kwana,su suka yita yiwa kunnuwa da idanuwanta gizo,kuma suka hanata komawa duba ayshatu.....suka kuma sanyata jin ta matsu ta kora mika'il mashkur harma da ya'aqoub din daga rayuwarta gaba daya. Kafin tabar wajen taji alamun shigowar saqo. Koda ta duba alert ne daga banki da sunan mika'il wanda ya sanya mata 1mil a matsayin kudin mota kawai. Ta juya wayar a hannunta,ta sake juyata,sai kuma ta saki siririn tsaki tana ajeta a gefe. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 67 Kamar kowanne lokaci,yakanyi breakfast dinsa ne a sassansa,saboda duk wani abu da zaiyi breakfast dashi yasha banban da cimar mutanen gidan. Wannan ya sanya ya aje cook dinsa daban wanda yasan tsare tsare na cimarsa. Koda a ranar baida ra'ayin cin abincin cikin gidan,nashi cook din zai masa irin abincin da yayi dai dai da ra'ayinsa,zai shiga ne kawai ya taya anni zaman cin abincin. Yau din ranar litinin ne daya tsara abubuwa da yawa da zaiyin. Bakwai da mituna goma sha shida ya murza handle na bedroom dinsa ya soma takowa a nutse zuwa ainihin parlor dinsa. Yayi wani sassanyan kyau cikin tsadajjen yadin Qiviut fabric me tsananin taushi da kuma rashin nauyi,daya daga cikin favourite yadiddikansa duk da tsadar da suke dashi amma baya jin wannan. Metro blue ne da yayi matuqar haska fatarshi,ya kuma fidda sura haiba da cikar kamalarshi. Fuskan nan a dinke kaman ko yaushe,wanda kusan duka safiya anni ko abba ne ke jefa murmushi a kanta,sai kuma fitinannenshi farouq musamman idan a sassan ya kwana,to fa kafin su rabu kowa ya wuce wajen aikinsa sai ya addabeshi har ya zare wannan yanayin daga kan fuskarsa din.. Yau din budadden takalmi ya sanya,abinda ya bawa zara zaran yatsunsa daman fitowa kenan cif da cif cikin takalmin da ya soma zareshi daga qafansa sanda ya iso dining area dinsa. "Good morning sir" Cook din nasa daya kasance yaren igala ya furta cikin girmamawa yana rusunawa "Morning ameh.....how are you?" Yana jan kujera zai zauna "Fine sir...." Ya amsa masa yana matsowa da sauri gami da kama aikinsa na serving nasa komai. Wannan kuma shine ya bashi daman duba wayarsa da yaji tana vibration,wanda kusan koda yaushe idan zai kwanta bacci yana barinta ne a hakan gudun takura. Sunan daya gani ya sakashi dan furzar da iska kadan daga bakinsa. Duk da cewa a yadda suka rabu jiya bayajin yau zata kira ta assasa wata matsalar ko damuwar,shidai baisan me yasa duk sanda zaiga kiranta hakanan ba sai wani abu ya tsirga masa ba. Daidai sanda Ameh yake barin gurin ya daga wayar,ya ajeta daga gefansa bayan ya sakata a handsfree yana jawo mug din da ya zuba masa dafaffiyar madarar da aka watsa mata turmeric guda guda,wannan yadan sauya mata kala zuwa yellow kadan. "Barka da asuba" Ya fadi cikin nutsuwar nan tasa. Murmushi ta saki daga daya sashen,cikin son nuna zallar kulawa tace masa "Barka kadai.....kira nayi naji lafiyar d'ana ya ya tashi?,na kira dan uwanka wayarshi a kashe,ina fatan komai lafiya?" Kaman ko yaushe,duk wani motsi nata yana masa banbarakwai,yanzun ma haka ne,sai ya aje mug din yana hade hannayensa waje daya "Mun tashi lpy alhmdlh.....da fatan kema haka......musaddiq ban fita cikin gidan ba tukunna,bamu hadu dashi ba". Fuska tadan yamutse,amma bata bari sautin muryarta ya canza ba "To yayi ba damuwa.....amma ya kamata dai ace kasan kwananshi da tashinsa......banason yadda kuke nesa nesa da juna fa?". Sai yaji maganar kamar ta saukar da murmushi cikin zuciyarsa,murmushin dake nannade da mamaki,amma sai ya basar "In sha Allah" "To hakan yayi.....nace ba?" Ta fada don janyo hankalinsa "Ina tare dake maamah" Ya amsa mata tana duba agogon hannunsa da kuma qaramar wayar dake ajiye a gefe,wanda kiran saddiq yake shigowa "Cewa nayi bari nayi muku tuni,dinner by 8pm yau......ina fatan zaku cikamin burina na kasancewa tare daku duk dare?". Idanunsa ya sake lumshewa,tsananin rashin gamsuwa da tsarij yana tsarga masa. Da can da waye da waye taci gaba da kasancewa duk daren a sanda ta tattarasu ta baiwa duniya kyautarsu?. Bayajin a stage din da ake kai yanzun zai yarda da ita ko ya gasgatata. Furucinta da kuma alaqarta da hajja harira ba zasu taba barin zuciyarsa ta nutsu da ita ba "Okay.....we will be there in sha Allah" "To yayi na gode.....sai na ganku" Ta fadi tana yanke kiran. Wayar yabi da kallo,har tayi maganar da tafi damunta,ta fadi kuma dalilin da ya sanya ta kirashi suka kammala wayar baiji addu'a guda daya daga bakinta ba. Yaja numfashi me nauyi yakaishi xuwa cikinsa,ya tabbatar babu yadda za'ayi anni ta kirashi......walau yana qasar nan ko yana wata qasa su kammala maganar su bata bishi da kyawawan addu'o'in da ko yaushe yake jinsu har cikin tsakiyar zuciyarsa ba. Addu'a da tsaftaccen niyya da kuma manufa na alkhairi. Hasken wayar ya sanyashi maida dubansa gareta,sai ya daga itama ya sakata a handsfree yana sake janyo mug dinsa yaci gaba da kurba "Saura mintuna goma lokaci ya cika hamma" "Gani nan......Moses ya qaraso?" Ya tambayeshi yana bude daya plate din dake gabansa "Muna tare dashi" "Okay.....get ready" Ya fada yana katse kiran tun kafin saddiq din ya katse nasa. Kamar kowacce safiya,ya shiga wajen annin cikin nutsuwa mutuntawa da kuma qaunar daya tabbatar daga ubangiji take....irin qaunar da yayi imanin Allah ne ke sanyata cikin zukatan bayinsa aduk sanda yakeso. Ta gyara lullubin laffayarta tana masa addu'a,addu'ar data sanya rauni me yawa a zuciyarsa,raunin da yaso nunawa har sanda yake cikin motar da dagashi sai saddiq sai driver,sauran guards suna gabansa wasu a bayansa cikin wata motar ta daban. Wacce irin rayuwa ce hakan wai?,wanda zai hafoka daban?,wanda zai gina maka rayuwa da kyakkyawan fata da kuma addu'o'i daban?. Wannan shine abinda ya dinga yi masa yawo akai,har daga qarshe ya samu ya yakice komai a ransa kafin su isa kamfanin. Kamar kowanne lokaci isowarsa cikin kamfanin kadai yakan sanya kowa shiga hankalinsa. Hakan kuma yana da nasaba da rashin daukan wasansa da yadda yake daukan komai da muhimmanci. Wannan ya sanya duk wanda ke aiki dashi yake shiga taitayinsa yake ajiye komai a gefe sai idan ka fita wajen kamfanin. Babban office ne dake dauke da kusan sashe biyu a cikinsa,wanda kusan kowanne sashe zaman kansa yakeyi. An qawatashi cikin tsari da nau'in kalolin da yafiso ya kuma fi ta'ammali dasu. Komai cikin tsari yake da tsananin tsafta tamkar wankewa da gyarawa kawai akeyi ba tare da ana shiga ba. Yadda mamallakin office din ya zama na daban,haka office din nasa ya zama na musamman. Hularsa ya zare ya ajiye su saman mulmulallen table din yana hadawa da wayoyinsa da system dinsa daya karba daga hannun ahmad,wanda shike jigilarsa tun daga sanda zai shigo kamfanin har ya fita. Idanunsa na ga wasu files daya tarar saman table din,amma kunnuwansa na sauraren bayanin taheer. Baice komai ba sai da ya gama sannan ya kalleshi "Ina mika'il?" Yayi tambayar hankali kwance yana daga wasu takardu dake gefe "Bai qaraso ba tukunna" Saddiq dake qoqarin kashe tab din hannunsa ya bawa fu'ad amsa. "Alright.....trading manager da laboratory technician.....su da sauran staffs dake qasansu dukka ka shirya mana meeting.....one hour thirty minutes kawai,akwai meeting da zanyi da sababbin ma'aikatan da muka dauka kafin nayi wannan tafiyar" "Done" Ya fadi cikin rusunawa da girmamawa. Daya bayan daya yake duba duka aikin daya bari da wanda suke zaman jiransa. Wadanda yake buqatar qarin haske ya turawa saddiq komai ta email nashi,don shine yake da alhakin kula da komai daya shafeshi,kaman yadda komai din sai ya biyo ta hannun saddiq din kafin ya iso gareshi. Duk da cewa yasan shi din mutum ne da baya saba lokaci ko karya magana,amma hakanan ya samu kansa da duba agogonsa. Yau din gaba daya hankalinsa baya a jikinsa,yana jin cewa yau zata kasance babbar rana a gareshi wadda zata kafa tarihi cikin rayuwarsa da kyakkyawar yarinyar da ya tabbatar koda cikin bariki samun irinta abune me wahala. Duk da 'yar hira da tattaunawa dake gudana tsakanin ma'aikatan hankalinsa shi ba'a wajen yake ba yayi nisa wajen wassafa yadda zai rayu da ita,yayi nisa wajen tsara yadda zai more rayuwarta da kyau.....ya kuma yi nisa wajen tsara yadda zai jiqata da kudi.....yadda zai sake maidata tauraruwa.....da kuma yadda zai maisheta abar kallo. Muddin ya sameta yayi imanin zaiyi zarra cikin duniyar bariki,zai kuma tayar da hankulan abokan adawa da yawa,hakanan zai zama wani na daban daya mallaki babe din da baijin akwai sauran irinta. Miqewar da ma'aikatan sukayi daga saman kujerun zamansu dake zagaye da kyakkyawan table ya sanyashi dawowa hayyacinsa. Miqewa ce taban girma ga CEO din nasu,wanda yake takowa cikin hall din cike da takunsa dake sake nuna zallar kamala da nutsuwar da Allah S W T ya hore masa. Lafiyayyen kwarjinin nasa dake sake saka kowa shiga taitayinsa yana kwance saman fuskarsa. Basu zauna ba har sai daya basu izinin zama sannan shma ya zauna din. Yadda suka saba gabatar da meeting irin wannan haka suka fara yanzun ma. Mataki bayan mataki,matsayi bayan matsayi. Yana biye da bayanan kowa ta sigar da idan ka kalleshi a haka zata tsammaci kaman baya fahimtar bayanan,don babu system ko abun rubutu ko daya a hannunsa,illama yatsun hannunsa daya sarqe cikin juna yana kallon duk wanda bayani yazo kansa. A gaban mika'il din akwai mutane da sai sun kammala miqa nasu bayanan kafin azo kanshi. Duk sai yaji ya matsu,tamkar ya nemi a daga masa qafa tukunna ya fara gabatar da nasa bayanan. To amma ko giyar wake yasha yasan hakan bame yuwuwa bane,don waje ne da ba'a daukan irin wannan wargin. "Ina neman afuwa,lokacin da na tsara zamu zauna din ina ganin kamar sai mun wuceshi.....zamu sake qara awa daya zuwa biyu......akwai me wani uzuri kaman na abinci?,shiga bayan gida da sauransu?". Yayi maganar cikin harshen turanci da wani irin daddadan accent,karyewa da lanqwashewar halshensa kawai ya isa ya gaya maka gwani ne wajen iya yaren. Cikin rashin jin dadi mika'il din ke rarraba dubansa akan fuskokin staff's din,yana cike da fata da burin samun wanda zaice yana da uzuri shima ya zama na biyu da zai furta haka. Saidai kaman yadda zuciyarsa ke raya masa ba wanda ya nemi wannan excuse din,hasalima daya daga cikinsu cewa yayi "Koda duka awanninmu na yau zaka qarar sir mun sadaukar maka dasu" Sauran suka shiga gyada kai. Kowannensu da wani irin qawa zuci da qauna ta gaske yake zaune dashi,duk da ba'a rasa qananu matsaloli da kowacce tafiya bata rabo dashi,amma ya gina wani irin qaunarshi a zukatansu da sadaukarwa me tarin gaske,wanda shi kansa baisan ya gina din ba. Saidai kuma abune sananne,duk wajen da ake samun kulawa tausayi da kyautatawa dole qauna ta biyo baya. Fada ce ta ma'aiki,an gina zukata abisa son wanda ke kyautata musu da qin wanda ke munana musu. "Alright.....na gode" Ya fada da salon daya sake sanyawa kowa nutsuwa da qaunarsa a zuciya. Boyayyar ajiyar zuciya mika'il din ya saki,gumi yana fara tsatsatsafo masa. Yafi kowa son samun kusanci da jadda......yafi kowa son ganin yafi kusancin dashi,yanaso yafi kowa samun fada da dama,don haka shi yafi cancanta ya nuna zallar biyayyarsa ga boss din ba wasu ba,don haka ya saki wani murmushi "As you wish sir.....mu duka muna qarqashin cewarka ne". Kadan fuad ya waiwaya ya kalleshi,sai ya gyada masa kai ba tare da yace komai ba. Gyara zamansa yayi saman kujerar kamar tana mintsininsa ne,yana jin kamar babbar asara tana shirin samunsa ne,kaman zai rasa wannan babbar damar ne a yau,wadda muddin ya rasata din baisan ranar da zai sake samunta ba. Sake danna wayarsa yayi ta kawo haske,lokacin da suka tsara zasu hadun yana dab da cika. Wajen SMS ya shiga,ya rubuta gajeran saqo ya tura mata,idanunsa suna kan wayar yana fatan samun amsa daga wajenta,duk da kuwa yasan abune me wahalan gaske. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 68 Tunda suka dawo daga makarantar hankalinta yana kan wayar,dama kawai take nema da sabreen din zata fita ta samu ta fidda wayar. Ta tabbatar yayi kiranta har ya gaji,yanzun haka qila yana cike ne da kewarta. Sunyi hira me tsaho dashi jiya cikin toilet,wanda ta dinga mamakin yadda yasan wasu abubuwan a kansu,saidai amsar daya bata ta cire dukkan wani zargi nasa daga ranta "Indai zakiyi mamakin yadda akayi nasan rayuwarki huda ashe son da nake miki ma baikai nan ba......kina wasa da kalar soyayyar da nakeyi miki ko?" Idanunta ta lumshe har cikin zuciyarta tana jin a yau din bayan yaa sabreen din ta sake samun wani barin zuciyar wanda ya damu da rayuwarta ya kuma damu da damuwarta. Har yake iya sanin wacece ita a rayuwa ba tare data sani ba saboda tsananin son da yake mata "Inason na daukeki daga gidanku huda.....na killaceki daga rayuwar da kike ciki......na hana kunnuwa da idanuwanki ji ko ganin duk wani mummunar kalma duk don saboda yaa sabreen....". Ta riga tayi amanna yasan komai kawai a kansu har akan sabreen din,don haka sai ta lumshe ido zuciyarta tana karyewa "Ba rayuwar da tafi rayuwar aure daraja da martaba a wajen mace.....qila idan yaa sabreen dinki taga zakiyi aure itama tayi" Ya fada cikin salon karya harshe dason nuna yadda zuciya ta karye,saidai a gefe guda yana sone kawai ya cusa wani kakkaifan abu a zuciyarta. "Banji dadin shaidar dana ji daga bakunan mutane a kanta ba.....don nima a yanzun ina daukarta kamar yaya take a gareni". "Hameed....." Ta katseshi cikin rauni. "Muyi kowacce magana dakai amma banda ta yaa sabreen,don zuciyata me rauni ce a kanta,ita din komai namu ce....." "I know huda.....i know,but inason na killaceki huda na daukaka darajarki.....inason ta silarki ya sabreen dinki ta zauna waje daya,ta samu martaba irinta....." Sai kuma yayi shuru bai qarasa ba,shurun da itama hudan da zuciyarta ke mata zugi ta zabi yinsa. "Zamuyi waya anjima idan kin samu lokaci.....i so much love you....please take care" Ya fadi yana katse kiran ya barta da yawa a hannu. Zare wayar tayi daga kunnenta jikinta yana yin sanyi. Kenan kowa ma yana dora tuhuma akan yaa sabreen?,kowa ma yana da zargi a kanta?. Idan dai har Hameed da yake baqo a unguwar dama rayuwarsu gaba daya zai iya samun wani abu a kanta to ya kenan sauran jama'a suke kallonta?. Shin gaskiya Hameed yake fadi?,tayi aurenta kawai ko hankalin yaa sabreen dinta zai dawo daidai?. To shin me yasa yaa sabreen din ba zata zauna kaman kowacce mace ba?. Me yasa bayan ta samu kudaden da sun isa ta riqe musu rayuwa?.....me yasa ba zata haqura ba?....me yasa?,meye dalilinta?,idan a baya tana da hujja tana da dalili yanzun meye dalilinta?. Wadannan tarin tambayoyin su suka dinga yi mata kai kawo,sannu a hankali sai taji kaman tana da ja akan sabreen din,tana kuma qalubalantarta duk da harshe ko aikinta bai nuna ba....... Amma tun daga sannan can qasan zuciyarta wutar hakan tana ruruwa sannu a hankali. Kamar wadda ke ciwon jiki haka ta dinga aiwatar da komai. Duk da tana da daukan lokaci wajen wanka da shirinta amma a yau din sai abun ya sake ninkuwa. Ta gyare gashinta ta kuma dameshi cikin band madaidaici,ta gama shafa cream dinta na musamman dake qarawa fatarta glowing cikin kowanne yanayi,amma kuma saita kasa ci gaba da yin komai. Bata taba ayyukan da suka tsaye mata a rai takejin ta takura ba irin aikin Mikhail dana mashkur da cikin qarshen satin nan zata yishi. Batasan dalili ba......amma ta alaqanta hakan da canzawar salon aikin. Ma'ana kowannensu zata kasance dashi cikin dakin hotel daga awa daya har zuwa sanda aikin zai kammala. Shin tana da tabbacin kubuta daga hannun miyagun kurayen da dama dama suke nema irin wannan?,mutanen da suke kallon diya mace cikin idanuwansu da wani irin duba kwatankwacin duban da mayunwacin zaki kewa nama a yayin da sukayi arangama?. Tana zaunen amma tana lura da yawan shige da ficen da huda keyi tsakanin falon zuwa dakinsu. Kaman zatayi mata magana sai kuma ta basar,don tana da wani irin dabi'a nabin komai da idanu har sai sanda ta samu cikakken hujja ko makama a kanshi. Qarar yar siririyar wayar da tasan kiranta na dabanne shine ya dauki hankalinta. Wanda ta zata din shine kuwa,Jib ne,sai ta daga kiran tana rage volume na kiran. "Hello jib?" Ta furta daidai sanda huda ke ficewa a dakin. Samun kanta tayi da jan qaramin tsaki can qasan ranta. Jib?....ko waye kuma da wannan sunan?,zai iya yiwuwa wannan shirin da takeyi ma fita zatayi,kuma wajensa zata je,idan mace da namiji suka kebanta a waje daya kuma me zai biyo baya?,idan taje gurinsa me zasu aikata?..... Tambayar data yiwa kanta kenan ta qarshe data sanya bugun zuciyarta qaruwa,saita samu kanta tana saurin dakatar da kanta daga wannan tunanin tana furta "A'uxubillah" Wani sashen na zuciyarta kuma yana gaya mata "Yaa sabreen ce fa?" Idanunta ta lumshe tana son sake jaddadawa kanta eh.....ya sabreen ce,amma wani sashen kuma yana qoqarin maidata baya. "Yadda kika tsara abun bazai yiwu ba sister.....dole ya kasance kuna tare nan da awa guda......mafi kyau kuma ku isa wajen tare koda xaku shiga ta qofa daban dabanne......don na bincika a yanzun kamar suna dakin meeting da boss dinsu..... Meeting din kuma zai zamana sun tattauna muhimman abubuwa.....na lissafa zasu soma lissafi na kudaden da company ke dashi a qasa......zasuyi musayar documents da bayanai,zaa tashi ba tare da sun kammala ba don bayanan yana da yawa,kuma owner na kamfanin jadda baya saba lokaci......wadannan bayanan da zasu kasance tare dashi ina da buqatar wasu abubuwa a ciki da zasu sauqaqamin kutsa kai cikin account din muyi aikinmu da wurwuri mu gama.......inaso kuma aikin na gamashi ne a daidai lokacin da masu kula da komai nasu suka tafi hutun fitowa daga meeting din....idan zaiyiwu ki samu kaiwa office dinsa,akwai wani ajiyayyen code cikin files na office din da zaki ciromin,kin fahimta?" Dukkanin bayanan sa ta fahimta ta kuma gamsu,to amma kimarta fa?. Bata saba yin magana ta dawo ta warware ta ba "Kada kiyi tunanin komai.....wannan ce rana ta qarshe tsakaninki dashi.....kuma wadannan sune awannin qarshe da aishatu keda chance na tsallakewa siradinta". "Ba damuwa" Ta bawa jib amsa a taqaice tana yanke kiran. Wayar ta aje a gabanta kawai tana kallonta tare da tunanin da yadda zata sake requesting wa mika'il din su kasance tare tun yanzu?. Kaman ana jira ta yiwa kanta tambayar saiga shigowar saqonsa. Tana duba saqon tana jin sanyi da yadda komai yazo mata a sauqaqe. Duk da hakan ya faranta mata amma saita ajiye wayar bayan ta gama dubawa,ta miqe kawai ta isa wardrobe dinta tana laluben suturar da zata dace da jikinta da kuma yanayin. Shurun nata da rashin samun amsarta ya qara masa yawan rashin sukuni. Ya dinga duba wayarsa duk bayan wucewar wasu mintuna,har sai daya kasa jurewa ya sake tafa massage dij har sau biyu ya tura mata a jere. Saqon ya shigo mata sanda take daura agogon hannunta ne,tun taga sunan tasan shine,bata bi takai ba sai data gama daurawar,ya qara barima a kunnenta tayi Rolling mayafin Turkish dress din,ta kuma jawo kimono din kayan da suke zuwa tare da shirt me dogon hannu da skirt din ta aza saman kayan sannan ta dauki wayar ta bude tana maida masa amsa "What's the adress?.....zan taddaka har inda kake don farincikinka". Sai data maimaita karanta saqon kusan sau hudu,tana mamakin yau itace da kanta zata turawa wani d'a namiji saqo da yayi kama da wannan?. Ji tayi kaman ba zata iya turawar ba,ta aje wayar saman madubi tana furzar da iska daga bakinta "No way out" Taji zuciyarta na gaya mata,dole ta tura muddin tanason cika mission din. Tana so ta rabu ne da mikail.....ba kuma zata iya barinsa salin alin ya wuce hakanan ba,sai ta miqa hannunta ta sake bude wayar,ta danna send sannan ta maida wayar ta ajiye. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 69 Bayan maimaita karanta saqon da yayi,har sai data kaishi ga murza idanun nasa don ya tabbatar daidai ya gani ko kuwa akasin hakan?. Jikinsa har rawa yake wajen maida mata reply,har bai lura da yadda Muhammed jadda ya zuba masa idanu ba yana karantar yanayinsa. "Mr mika'il" Ya kirayi sunansa da husky voice dinsan nan dake ratsa zukata su kuma maida hankalin mutum zuwa jikinsa. "Yes.....yes sir" Ya fada adan daburce yana qoqarin tattara masa nutsuwarsa bayan ya tabbatar da isar saqon zuwa wayarta. Bawai address kawai ba,harda code da zata samu zarafin bude office dinsa ta shiga ta zauna tayi tsimayensa. Murmushine ya subuce mata da ganin yadda ya bata komai in details. Ba wani shakka ko kokwanto. Wato shi namijin bariki akan mace susutacce ne?.....sannan fiye da rabin maza ta fuskanci ba kasafai suke iya mallakar kansu ba idan batu ake na mace. Wani zaka hangi fuskarsa cike da kamala amma muddin aka raba masa mace a nan dukka rauninsa yake bayyana. Bai tsoro shakka ko kwanton ita din fa baquwa ce cikin rayuwarsa gaba daya?. "Good job mika'il" Ta fadi murya can qasa tana forwarding ma JIB komai. "Kana tare damu?" Muhammad jadda ya sake jefa masa tambayar yana dage girarsa dukka biyun "Yes.....yes sir" Ya fadi yana sakar masa murmushi don ya amintar dashi. Idanu yadan tsareshi dashi kaman meson karantar wani abu,wanda duka duka cikin mintuna biyar ya dauke idanun yana cewa "Bismillah" Tare da maida idon nasa saman farar takardar gabansa da daya daga cikin ma'aikatan ya gabatar. Sai da yayi namijin qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya fara gabatar masa da komai daki daki. Sai data buda qaramar handbag dinta ta tabbatar ta sanya komai a ciki sannan ta fiddo dubu biyu a ciki ta miqawa huda dake tsaye a gabanta "Masu kamfanin pure water zasu kawo ruwa....ki basu wannan idan sun kawo.....naso saikun wuce islamiyya kafin na fita.....amma it's urgent.....kiyi qoqari ku fita da wuri kada kuyi latti" "A dawo lafiya" Ta fadi bayan ta karbi kudin. Qasan ranta fal farinciki,a yau din zatayi hira da hameed yadda ranta keso,don zata saitawa su nadra hanya zuwa islamiyya ne ita kuma ta baje kolin soyayyarta yadda ranta yakeso. Gaban haneefa ta qarasa tana sakin murmushi,itama haneefa din murmushi ta saki,hannunta ta dora saman sumarta data cirewa dankwali. A kullum fuskar haneefa ba wanda take tuna mata dashi sai umminsu. Akwai shaquwa da sabo me tsanani tsakaninsu.......amma duk da haka saida mutuwa tayi aikinta ta raba tsakaninsu. "Ayimin addua auta....zan kawo miki abun dadi" "A dawo lafiya yaa sabreen........amma yau kam sabuwan teddy nakeso ki sayamin" "Ke kuwa ki rasa abinda zaki zaba sai Teddy?" Nadra ta fada tana qyalqyala dariya "To madam tsokana.....ba ruwanki" Sabreen tayi hanzarin katse nadra data wuce daki tana ci gaba da dariyar tsokana din hadi da yiwa sabreen a dawo lafiya. Tana takawa don fita daga layinsu ta isa bakin titi amma tunanin qannen nata ne a ranta. Batason ko kadan yadda kullum sai ta fita ta barsu,wani lokaci su fita tare saidai su rufe dakin,harma wasu lokutan su rigata dawowa. A yanzun huda tafi tsaye mata a rai,tunda har ta cika shekara sha biyar ta shiga ta sha shida tana da buqatar sanya idanunta a kanta,don mataki ne da komai daga nan yake farawa daga rayuwar yarinya. Duk da inda ace ita din me gata ce,ita dinma tana buqatar kulawa ne tare da qarasa rainon tarbiyyarta. Ko kusa ko alama bata lura dashi ba,don tayi nisa a tunaninta,sai muryarsa taji daga gefanta. "Um uhmmm......sai ina kuma haka?" A nutse ta waiwaya tare da sake rage yanayin tafiyar tata tana kallonshi. Tsaf yake kallonta,ya turo hula gaban goshinsa yana mata wani irin kallo. Idanunta ta dauke don bata buqatar yanayin kallon da yake binta dashi. Ta sani haushinta yakeji qwarai,tun waccar ranar data hanashi kudi. Wannan duka ba damuwarta bane,don idan da sabo ta saba,sai ta watsar da wannan batun kamar kullum tace dashi "Barka da warhaka kawu.....an yini lafiya?" "Ras na wuni.....ko kin dauka zan mutu ne saboda kin hanani kudinki?,to kisha kuruminki 'yar nan......cikin satinnan da yardar me duka arziqi zai fashemin......sunana zai fantsama a duniyar masu arziqi......daga sama'ila zan koma alhaji ismai'il sha maka Allahu". A mamakance take kallonsa,tadai sani bashi da wata sana'a data wuce caca,kuma muddin ka jishi yana lissafin maquden kudade irin wannan to wata caca za'a buga kuma yake sanya ran zai cinye. "Allah ya bada sa'a.....amma dai kawu.....caca" "Akul naji bakinki.....dani dake ai dan juma ne da dan jummai... Ke har gwara ni duk tsiya". Kanta ta dauke tana hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya,bata sake tanka masa ba sai ta fara takawa tana barin wajen. Har tayi taku hudu qwarara ya qwala mata kira da ainihin sunanta "Aminatu" Dakatawa tayi don ba zata iya ci gaba da tafiya ba,ba'a canzawa tuwo suna,duk duniya kawu sama'ila ubanta ne. "Ke wato baki jin ko dar idan an miki gugar zana ko?,to miqomin wani abu nan,ki rubuta shi a lissafi duka cikin satin nan zan biyaki" Ya fada yana miqa mata hannu tamkar ya bata ajiya. Idanu ta xuba masa,sai kuma ta sanya hannu tana sauke jakarta daga kafada,ta zuge ta fidda dubu dubu guda hudu ta miqa masa. Karba yayi yana juyasu alamun a raine suke a wajensa,sai ya yatsina fuska "Ki rasa abinda zaki ban sai wannan?,kai Allah ka dawo mana da arziqinmu za'a sha kallo wallahi......" Daga haka ya juya yana cusasu a aljihu tare da barin gurin bai kuma sake bi takan inda zataje din ba. Kasa ci gaba da tafiya tayi har sai daya bacewa ganinta,ta kada kai ta na yin gaba kamar kullum zuciyar nan cike da nazarin rayuwa . Tun daga rasuwar mahaifinsu har ta mahaifiyarsu bai taba miqo komai yace musu gashi ba wai don su rayu.....amma ita ba zata iya qirga ko lissafa adadin sau nawa ya karba daga hannunta ba,kuma a raine,ba godi bare na gode. Ya riga ya bata shaidan da zata nuna na cewa shi take nema,wannan ya sanya bata samu matsalar shiga kamfanin ba tun daga gate din farko gate na biyu,ta zarce zuwa main entrance,ta ratsa reception da sauran guraben da kamfanin yake dashi kai tsaye kuma ta isa ga office din. Tayi amfani da code din ya kuma bude mata successful. Ta tura qofan a hankali kamar me tsoron shiga qaramin murmushi na sauka saman fuskarta "Quda a wajen kwadayi akan mutu" Ta furta qasa qasa tana sanya qafafunta cikin office din. Har ta fara takawa sai kuma ta tsaya cak tana wurga idanunta sassa sassa na qawataccen office din da aka narka kudi akayi masa wani irin lafiyayyen tsari me daukan hankali. Tabbas tasan babu yadda za'ayi guri irin wannan ya rasa CCTV camera,indai kuma hakanne ta yaya zata iya gudanar da komai ba tare data samu wata matsala ba?. Dan wani abu cikin kunnenta ta matsa,muryar JIB ta bayyana,sai ta danja da baya kadan ta raba qafa tsakanin office din da veranda din da jerin gwanon office din yake don bataso ta fito gaba daya ko ta shiga gaba daya don kada camera din ya samu damar nunata "Ni dakai duka bamuyi tunanin CCTV ba jib?". "Ya salam" Ya fadi yana aje wani numfashi "Haka ne......wasu lokuta dama kece ke mana hasshen irin wadannan abubuwan......ba matsala bane,manyan kamfanoni irin wadannan akwai irin cameras din da suke amfani dasu,katseshi ba zaiyi wahala ba nasan takan irinsu sosai......yanzu ki tsaya daga nan inda kike...kafin ki shiga ki gano mana daga wanne saiti camera din yake shikenan kawai" "Okay....." "....karki datse connection daga nan har mu gama aikin" "So kaji komai tsakaninmu kenan bayan sirri ne?" Ta fada cikin dan salon zolaya da wani lokaci takeyi masa. Dariya ya qyalqyale da ita kadan yana fadin "Tuba nake....Allah yabar soyayya". Sai kawai ta saki murmushi kadan tana tura qofar hadi da sake qarewa office din kallon tsaf. Cikin qasa da minti goma ta gano komai suka kuma katse sadarwa da tsaida aikin camera din. Da dan hanzari ta ajjiye hand bag dinta. Tanaso tayi komai ne ta gama kada damar ta subuce mata yazo ya shigo. Sai data tattara dukka hankalinta da nutsuwarta ta karanci inda komai yake ajiye a office din,gudun kada ta taba wani abu ta kasa maidashi daidai inda yake hakan ya nuna masa alamar tayi masa bincike. Hatta da biro dake ajiye qwaya daya tal saman teburin sai data karanci a yadda yake ajiye din,ta dauka ta kuma gwada maidawa ta tabbatar ya zauna kaman yadda aka ajiyeshi. Wayarta ta fidda,ta sake yiwa office din qaramin video komai da komai sannan ta maida wayar jakar,ta kuma shiga aikin bincika komai daki daki. Baya ga abinda suke nema taga abubuwa da yawa cikin office din,irinsu condom dake nuna mata lallai riqqaqqen dan bin mata ne,taaba irin masu tsadar nan da sauran abubuwan maye. Abinda ya sake darsa mata mugun tsanarsa kenan,wutar kuma ta tabashin ta hanyar kwakwashe masa komai tana sake ruruwa cikin ranta. Ya zama dole ta durqusar dashi,durqusarwar da bazai sake tashi ba. Maida komai tayi kaman ba wani abu daya faru a office din,ta tattare duk abubuwan da take nema din tayi musu ajiya ta musamman cikin jakarta. Hatta da wani qaramin ledar cake da akaci aka barshi sai data tabbatar ta maidashi yadda yake,ta gyara rolling dinta da kyau tana sauke numfashin samun nasarar kammala komai ba tare daya dawo ba. Maqoshinta taji ya bushe tana da buqatar ruwa,sai ta taka tana nufar kyakkyawan fridge din dake girke waje daya. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 70 Turus tayi tana kallon yadda aka maqare gidan farko na fridge din da wasu kalan kwalabe da bata saba ganin irinsu ba. A hankali take dubasu har ta fahimci kwalaben na meye?. Kwalaben giya ne tabbas,ta maida idanunta ta lumshe tana furta "Innalillahi" Can qasan harshenta. Sai kuma taja jikinta baya a hankali tana matsawa daga jikin fridge din don batajin zata iya shan wani abun sha daya fito daga fridge din komai halascinsa. Zuciyarta ke qara bugawa da tsanarsa haushi da kuma takaici. Shikam mikail dame zaiji?,abubuwan ai sunyi masa yawa,sun masa yawan da batasan wanne a ciki zai iya dauka ba. Kaman ana son bata amsar tambayarta sai qofar tayi qaramar qara alamun ana budeta ne,ba jimawa ya bayyana cikin office din yana dubanta da murmushi "Am so sorry dear......ina fata banyi keeping naki da yawa ba......boss ne idan ya tashi aikinsa tamkar engine.......baya gajiya,na samu na kubota da qyar". Idanunta ta dauke daga kan files din da yake rungume dasu,wanda ta tabbatar a cikinsa sauran bayanan da take nema suke. Ta kalato dukkan dauriyarta ta jefeshi da qaramin murmushi "You deserve it ai....." "Wow......serious?" Ya fada da wani irin zumudi da zakwadi yana qarasowa gabanta dab da ita ya zauna har yana neman hade gwiwoyinsu guri guda. A dabarance ta miqe da sauri,sai ya bita da kallo. Taji a jikinta yana kallonta ne don haka ba tare data juyo ba tace "Bari nayi fitsari kadan" "Oh....okay to dear" Ya fada yana dora files din saman table din cikin ransa yana qissima yadda a yau din zai gwangwaje,a yau din zai kashe duk wata qishirwa tasa dake damunshi a rai.....a yau zaiyi morewar da bayajin ko daren amarcinsa zaiyi wannan. Gaban madubij toilet din ta tsaya tana sauke numfashi idanunta akan fuskartata. Muryarta can qasa tace "Please jib.....muyi komai mu gama da sauri......banason ganin fuskarshi kwata kwata" "I know.....zanyi iya qoqarina......amma please kada kice zakiyi halin hawainiyar nan taki" Dan murmushi ta saki,yasan halinta sarai,koda nawa aikin zai basu idan ta motsa mata tana iya cancel dinsa "Zanyi qoqarin nima" Ta amsa masa tana kunna famfo sai ta bige da daura alwala. Mutum hudu ke biye dashi sanda yake takowa cikin veranda din idanunsa saman takardar dake hannunsa yana sake karanta abinda take dauke dashi. Can qasan zuciyarsa akwai wani kokwanto da mamaki,kusan zaman yau da suka fara yi da mikail wanda ba'a qarqareshi ba saboda quracewar lokaci ya karanci kamar hankalinsa ba gurin yake ba sam sam. Yana karance da kuma bibiye da motsinsa. Duk muhimmanci da girman takardar a wajen kamfanin gaba daya amma har ya iya mantota cikin dakin taron,wannan ya sanya ya yanke biyoshi da kanshi ya kawo masa don ya sake alamta masa muhimmancin takardar. "Wait here" Ya fadi a nutse ga mutanen dake bayanshi yana sanya code na qofar office din Mikhail din ta bude ya murza handle din yana turawa can qasan ransa yana jin kamar bai kamata yayi hakan ba ba tare daya nema izinin shigar ba. Duk da kowanne office a qarqashinsa yake amma bai shiga office din kowa,hakanan baya taba bada damar a bude maka office muddin baka nan,amma haka kawai yau din yaji yayi hakan. Sanda ya murda handle din yake shigowa da sallama cikin husky and deep voice nashin nan,dai dai sannan itama ta bude qofar toilet din ta fito tana qoqarin maida rolling na mayafinta. Idanunsa kan mikail daya miqe a rude cike da tsananin mamakin ganin boss din nasa yau da kanshi a office dinsa gabansa yana faduwa,yayin da nata idanun suke kan fu'ad fuskar fu'ad din tana dubansa qasan ranta tana jin kamar tasan wannan fuskar. Baikai ga lura da ita ba ya miqa masa takardar "Keep it......." Ya furta da wani irin yanayi idanunsa cikin tsakiyar qwayar idanun mikail wanda hakan kadai ya isa ya gaya masa wani gargadi yake aika masa da kuma muhimmancin da takardar ke dashi "In sha Allah sir" Ya amsa yana karbarta da hannu biyu. Juyawa yayi da zummar ficewa a office din,dai dai sannan idonsa ya sauka a kanta. Idanunasu suka gauraya waje daya,sai tayi saurin zare dubanta daga kan fuskar tashi gabanta yayi wani irin faduwar da batasan meye dalili ba. Dan zuba mata ido yayi na sakanni tamkar zaiyi magana,sai kuma ya fasa,ya juya ya kalli mikail sannan ya maida dubansa kanta sai kuma ya juya yana ficewa a nutse daga office din. Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke. Allah ya sanya ba zuwa yayi ya samesu cikin wani yanayi ba da dukka sauran gaskiyarsa da yakeson tabbatarwa boos din a yau babu ita. Yasan an jima ana kai masa tsegumin halinsa,amma kasancewar shi din ba mutum bane me daukan qananun maganganu ya sanya abun bai wani tasiri ba. A yadda yake jinsa a dan rude sai yaji yana buqatar giya don daidaita nutsuwarsa. Ya tafi zuwa fridge din yana fadin "Boss......bashi da sauqi kwata kwata,idan har wani kuskure ya faru tsaf zaka rasa aikinka,a wajensa wannan din ba wani abu bane me wahala". Batace dashi komai ba kaman yadda bata kula da abinda ya dauko yakw sha ba,ta qarasa wani sashe na dakin ta tayar da sallah kawai don lokacinta ya shiga. Tunda ta tayar da sallar har ta idar yaba zubawa cikinsa barasa. Sanda ta sallame din saita kafeshi da idanu kawai. Ranta cike fal da mamakin yadda dan adam da hannunsa zai dinga durawa cikinsa abinda yasan zai cutar dashi?. Waiwayowa yayi sai suka hada ido. Ta hade fuska da kyau tana miqewa "Banason wannan abar sam... Muddin kanason mu kasance tare kuwa saidai ka rabu da ita" Tayi maganar duka tana jin wani iri har cikin ranta "Am sorry dear.......indai wannna ne kada ki damu na ajiye". Tana maida takalmin qafarta tana tunanin yadda zata samu ta duba takardar da boos din nasa ya kawo masa yanzu?. Ta kalleshi tana gyara zamanta bayan ta gama saka takalmin "No water no drinks?" Murmushi ya sake mata "Akwai mana.....gasucan a fridge sai kalan wanda kikeso" Kai ta girgiza "Ba wani abu da zai fita a fridge dinnan na sha shi" "Why?" Ya tambayeta yana zare ido "Na tsani shaye shaye" Ta bashi amsa kai tsaye,amsar data sakashi sake zaro idanu "Duk kyan nan naki babe?,kinsan yanzun macen bariki bata gama cika ba sai ta hada da cakewa?". Ido ta dan rufe kadan tana budesu,kalmar MACEN BARIKI da yayi amfani da ita a kanta tana mata quna sosai cikin rai "Cikar wannan kyan naki babe ki dinga taba wani abun da zai sanya ki dinga jin kanki very high......Ni zan dauki nauyin baki komai mai tsada wanda ba kowacce yarinya ce ta isa ta samesu ba......sai irinku matan da kuke da gata a wajen partner dinsu......like kaman wannan giyar.....bata bugar dani,saidai nayi bacci na awa daya shikenan idan na farka zan jini fresh......please ki koya sha ko kadanne akwai dadi,saikin gwada zaki gayamin" Yayi maganar yana qoqarin sake zuba wata a cup da alama kuma ita yake da niyyar baiwa idan ya zuba din. Tsam ta miqe tana jawo jakarta dake a gefanta tana ratayawa "Ya haka kuma?" Ya tambaya yana dubanta "Zan wuce gida" Da sauri ya diro daga saman kujerar da yake kai "Haba babe.....me yayi zafi?,bayan baki cikan alqawari na ba......kinsan dakin nawa na kama mana a Bristol kawai saboda yau?" Idanunta ta juya tana ajiye numfashi "Banga alamun ka dauko wannan hanyar ba......kana yimin maganar abinda babu shi a tsarina.......baka iya saukar baqo ba sam......na nema abun sha kana min sharhin da lokacinka yake ci maka......idan lokacin dana diba ya cika zan tafi koda ba komai daka samu" "Ba za'ayi haka ba" Ya fada da hautsine jin zaiyi asaran abinda ya qwallafa rai a kai,ya ajjiye komai na hannunsa ciki harda takardar da yanzu yanzu aka jaddada masa muhimmancinta yayi hanyar fita daga office din. Wannan shine ya bata cikakkiyar damar qarasawa,ta fidda wayarta tayi snapping takardar ta turawa JIB kai tsaye ta share komai ta koma mazauninta tana jiran dawowarsa. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 71 Kai tsaye ya wuce saman sofan dake ajiye bangare daban na office din yana zame takalman qafarsa. Already sunyi sallan azahar bayan fitowarsu daga hall din,don haka ya maida bayansa kadan ya jingina da sofa din. So yake ya huta kadan kafin ya fita yaje yaga baqinsa,to amma tunani ya hanashi hutawar,don maamah ce ta fado a ransa,sai ya fidda waya yana kiran musaddiq idanunsa akan agogo yana qirga yawan awannin da suka rage da zasu maidasu gida su duka. Ko kadan bazai bari musaddiq yaci gaba da mu'amala da gidan maamah haka kai tsaye ba,ko mu'amala da dukkan wani abu daya shafi gidan game da abinci ko abun sha ba. Don sam hankalinsa bai kwanta ba bazai kuma taba kwanciya ba,don ta kashe dukkan wani abu da zai bashi nutsuwa tattare da ita. Bugu daya ya daga,muryarshi ta fita cikin girmamawa. "Qarfe nawa zaku bar company yau din?". "Zamu dan jima yau,saboda akwai sabbin fertilizer da aka muka fitar,zamu gabatar dashi ga manoma" "Yayi kyau,idan kun kammala kafin ka fita a company din ka sanarmin" "In sha Allah" Ya fada a girmame. Katse wayar yayi yana sanya hannu zai jawo file din daya shigo dashi sai kuma abun ya fado masa. Ya tsaya cak yana juya ganin da yayi mata. Daga toilet ta fito,jikinta duk damshi da lema da yake nuna ta taba ruwa,to me yakai mace office din mikail?. Ya jima yana jin maganganu iri iri akan mikail din,to amma shi din ba mutum bane ke daukan qananun maganganu shi yasa bai taba bi takai ba. Hakanan bai fiya zafafa bincike da bin al'aurar mutum ba. Amma yau haka kawai yaji maganganun da yakeji a kanshi din yana dawo masa. Muqamin da Mikhail yake dashi a company din bashi da alaqa sam da hada hadar jama'a karbar baqi ko mu'amala dasu ballantana yace harkar kasuwanci ne ya kawota wajensa. Qaramin tsaki yaja yana qoqarin watsar da maganar. Ta iya yiwuwa irin watsatsun 'yammatan nan ne dake yawon bin maza office office dinsu don kawai son abun duniya. Muddin ko haka ne shi bazai bari wannan ta faru cikin kamfaninsa ba. Dukiya yake nema ta halal me cike da albarka,dole duk wanda yake qasansa ya kiyaye dokar Allah lokacin mu'amalarsu,bayan kuma mutum ya fita daga kamfanin saura ya rage nashi. Zancen ya maqale a ransa duk da ya bude file yana dubawa,qananun shekarun daya fuskanta tana dasu su sukafi tsaye masa a ido duk da ba qare mata kallo yayi ba,yana tsoron kada ya zamana yaudarota yayi ya kawota office dinsa?. Wayarsa ya zaro ya laluba number saddiq da ya baro a first floor yana ganin ma'aikatan da suke da buqatar dauka kafin shi ya gansu yayi final interview dasu. Ringing biyu ya daga,sai ya zauna sosai ya sake tambayarsa inda yake duk da yasan a inda yake din "Muna qasa.....na kusa kammalawa dasu" "Alright......kasan me nakeso da kai?" Ya tambayeshi yana shafa baqar kwantacciyar sumar dake gefan fuskarsa zuwa habarsa "Aah hamma" "Mikail......ina buqatar kowanne motsi nasa daga yanzu ya zama ana min monitoring nasa" "Done hamma" Saddiq din ya fada cikin qwarin gwiwa. Sosai wannan aikin da hamman ya bashi yayi masa dadi,don ya jima yana ganin abubuwan zargi masu yawa tattare da mika'il din,to amma baida cikakkiyar hujja da zai gabatarwa da hamma,shi kuma hamma koda kana da hujja sanda zaka gaya masa magana sai ya bincika ya tabbatar da gaskiyar maganarka. Minti talatin ya sake duba agogonsa. Yana shirin miqewa saddiq din ya shigo,ya gabatar masa da komai ya ajiye masa duka takaddun "Well done" Fu'ad ya fadi bayan ya tabbatar da komai ya tafi daidai. "Kira me sunan malam.....wanne time ya bawa mutanen nan?" Ya gayawa saddiq daya kasance executive assistant dinsa wani lokaci ya juya ya zama P.A dinsa,har muqamin me sunan malam dinma yana hawa wato scheduling coordinator ma gaba daya. Hularsa ya dauka da agogonsa daya jiye a gefe,ya qarasa ya sanya takalmansa daidai sanda executive Porter dinsa ya shigo Shi ya dauki sauran kayan da yasan zai iya fita dasu din,yabi bayansa,yayin da musaddiq ya tsaya don ya qarasa killace komai ya kashe sauran electronics dake kunne,don yasan ba lallai su sake dawowa ta kamfanin sai kuma gobe. Yana fita suka hadu dame sunan malam din,sai yabi bayansa suna takawa a nutse yana gaya masa sauran schedule dinsa na yau duka "Amma sir.....sai nakega kaman abubuwan sunyi yawa.....ko akwai abinda zaa rage ko a sauyashi a kaishi gobe?". Kansa ya girgiza sanda saddiq ya matso yana scanning keycard jikin designated elevator din da shi daya yake amfani dashi cikin company din. "Kada ayi cancel komai.....zamu kammala in sha Allah komin dare.....make sure kowanne ka sanar masa da exact time da zamu hadun" "Yes sir" Me sunan malam ya fada yana bawa guards dinsa waje,daya daga cikinsu yayi gaba don tabbatar da lafiyar elevator din duk da anyi keeping nata waje daya kuma don saboda shi,muhammad jadda yabi bayansa sauran guards din suka shiga hadi da saddiq. Cikin ransa ya shirya sake maida kanshi busy fiye da kima,bama wai shi kadai ba,hadda musaddiq don kaucema duk wani tsari da plan na maamah har sai yaga iya inda gudun ruwanta zai kaisu. Ya shirya sadaukar da dukka lokacinsa ya tafi dashi a aiki fiye da yadda yakeyi a baya,duk da ko a bayan shi din ba wani cikakken lokaci gareshi ba. Sau tari anni tana yawan yi masa fadan yana tsaurarawa rayuwarsa da yawa,ya kamata ya fiddawa kansa lokaci da zai dinga hutawa. Bashi da wani time qwaqwara daya ware don yaje hutu,idan ka ganshi yana hutawa to tabbas umra yaje wadda duka duka baya haura sati daya yake dawowa. Suna yawan ware qarshen kowacce shekara suje dukansu suyi umra,daga nan abban ya zaba musu qasashe guda biyu dake da wani tarihi cikin addini ko rayuwa suje su qarashe qarshen shekararsu a can. Sau tari shi din baya tafiya tare dasu,saidai ya biyosu daga baya,wanda ana kammala umra dinsa yake dawowa kan kamfaninsa,bai fiya binsu tafiye tafiyensu da suka tsara ba. Direct suka nufi private parking garage dinsa wanda aka tanada kawai saboda ajiye motocin da yake kai kawo da kuma hidima dasu. Wajene da yasha banban da sauran duka parking lot na company din,wanda aka qawatashi aka kuma cikashi da tsaro na cctv da kai kawon security. Dukka sauran guard nashi suna tsaye suna jiran qarasowarsa. Isowar nashi yasa da sauri CSO dinsa ya qaraso ya bude motor din da zai tafi a cikin ta ya matsa yana bashi guri,ya shiga saddiq yabi bayansa. Sanda motocin ke motsawa suna barin wajen zuwa ainihin hanyar da zata sadasu da gate na farko na kamfanin,daidai lokacin ya gyara zamanshi yana bude wani guri a side na kujerar da yake kai don ciro earpiece da zaiyi using nasa wajen amsa kiran daya shigo wayarsa. Kaman fitar kibiya idanunshi suka fada parking lot na sauran staff da suke da matsayi na biyu cikin kamfanin. Kan mikail idanunshi suka fada,ya bude mata murfin motar yana jifanta da wani mayen murmushi,yayin da nata fuskar yake kadaran kadaham tana sanya jikinta cikin motar *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 72 Zare Idanunshi yayi daga kansu yana jin wani quna a ransa. "Tun yaushe mikail yake irin wannan abun?" Yayi maganar a hankali ba tare da yayi tunanin saddiq zai jishi ba. Dan dubansa sadiq din yayi kafin ya rusunar da idanunsa "Hamma yana dan taba harkokinsa dama,amma kuma banajin a cikin company,yanayin komai ne a wajen company" "Idan har a wajen company yakeyi in zanyi wani abun bazai wuce tunasar dashi kawai da gyara masa kuskurensa da take wuyan kowanne musulmi,ya kuma wajaba a kansa ya zama dole a addini da wajen ubangiji yayi akan dan uwansa musulmi a sanda ya fahimci kuskure ko gyara cikin al'amarinsa.....amma kuma muddin yana shigo min da wasu abubuwa da basu dace ba muhallin neman halal dina.....lallai lallai zan dauki mummunan mataki ne a kansa". Yayi maganar da sound din da zai nuna maka da gasken gaske yake. Tunda suka shiga motar take jifanta da wani irin narkakken kallo. Yanaji jikinsa yana macewa kasala yana saukar masa kamar ko yaushe idan yasha barasa,shi yasa yaso ta bashi hadin kai ko hannunshi yadan fara kaiwa jikinta guraren da suka tsone masa idanu amma ta qiya. Yana kuma tsoron suna isa Bristol zaiyi wahala baiyi baccin nan nasa ba na wajibi,wanda muddin baiyishi ba bazai iya hasala komai ba yadda ya kamata. Ta gaya masa tana da qa'ida da kuma dokokin da dole ya kiyayesu muddin yanason rakiyarsu tayi tsaho. To sai yaga hanzarin ma na meye?,ya qyaleta mana?,don dai jiran awa daya kacal me zai cishi?,shi da ta tabbatar masa a yau din wuni guda tana tare dashi?. "Babe......muddin a yau kika bani hadin kai yadda na jima ina mafarki.....zan baki fara sheet da ba komai a ciki ki rubuta komai da yazo kanki kike burin mallaka......idan nace komai ina nufin komai fa,komai tsadarsa ko yawansa.....ina tare da lalitar jadda diamondchore" Ya fadi yana sakin qaramin shu'umin murmushi,don ya hango irin barnar da ganimar da kwasa cikin account din. Kadan tadan dubeshi sai ta dauke kai,tana maimaita sunan kamfanin da tun shigarta ta tabbatar ba qaramin kamfani bane gama gari da kowa ya saba gani ba......to amma sai taji ba abinda ya burgeta tattare dashi. Ta tabbatar tunda har mamallakin kamfanin zai danqawa mutum irin mika'il ragamae tasarrufi da dukiyar kamfanin duk kanwar ja ce,ba yadda za'ayi mikail din ya dinga irin wannan fantamawar yana wasa da kudadensa ba tare da masaniya ko daurin gindinsa ba. Ta yaya ma cikakken namiji kamar wannan daya mallaki dukiya ke dimbij yawa,kadarori kala daban daban ciki harda private jet amma ya gagara aure?,bayan a shika shikan aure bai rasa komai ba?. Qaramin tsaki taja qasan ranta hoton fuskarsa yana dawo mata tana jin kimarsa da haushinsa suna kwaranyewa daga idanunta,saboda haka batajin daga shi har mika'il sun cancanci tausayawa. Saidai ta sani,kudaden da suke da zummar kwasa din ba qananun kudade bane.....kudade ne da ta tabbatar ita kanta sunfi qarfinta dama duk wanda yake tare dasu,saidai kuma yawan masu buqatan kudi da muke dasu suke kuma kewaye da idanunta sun isa su lashe komai cikin zama mawadata da zasuci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin salama,ta soma hango wasu daga cikinsu suna rayuwa irin rayuwar da takeson ganinsu sunayi,wannan tunanin ya sanyaya sakin sassanyar ajiyar zuciya. "Bakice komai ba" Mikail ya fadi yana dan waiwayowa ya dubeta kadan,don tsananin rudewa da firgicewa cikin farinciki da dimuwa da yake ganin wasu matan a ciki idan ya musu irin wannan albishir din sam sam baiga koda kamannin haka a wajenta ba "Idan kuma hakan baiyi miki ba ki zabi kome kikeso a rayuwa......indai zaki bani rayuwarki zan baki komai da kike da buri" Ya sake fada cikin qoqarinsa nason gamsar da ita kalamansa. "Baka da damuwa" Ta amsa masa cikin salon miskilancin nan nata,don maganganunsa sun fara isarta,bata fiya son doguwar magana ba. Juya kalmar ta bashi rayuwarta takeyi cikin ranta. Har yanzu ta kasa sabawa da kalaman maza 'yan bariki,har yanzu mamakin wannan halittar ta d'a namiji ta kasa sakinta,su koda yaushe kansu sukeso?,kansu suka sani?,ko yaushe yaya zasuyi su samu jin dadinsu daga wajen 'ya mace?,ba tare da sun damu da yadda tata rayuwar zata kasance ba?. Basu da wannan asarar,suna iya sanya qafa suyi fatali dake duk sanda wannan halin nasu ya motsa na BUTULCI,aurenki sukeyi ko zaman bariki kuke?. Tayi imanin halin D'A NAMIJI A JININSA YAKE,dan kunama ne shi da gaske,tana kyautata zaton babu wani d'a namiji da bashi da wannan halayyar,saidai na wani ne ya d'ara na wani kamar yadda take gani take kuma kan gani din. Wannan hasashe da karatun da tayi musu shike nesanta zuciyarta kullum daduniyarsu,takejin ba abinda yafi dadi a wajen mace irin ta rayu ita kadai ba tare data raba kowanne namiji cikin rayuwarta ba bare ta bashi wani matsayi da zai zameta lalura qunci ko quna nan gaba cikin rayuwa.......gwara ta rayu ita daya shine zata zama me cikakken 'yancin da bata dame bata mata rai. Nisa da zurfin da tayi a tunani ya sanya har suka iso Bristol bata sani ba. Yayi parking na motar ya fito yana takawa da qyar saboda yadda jikinsa yake qara nauyaya,ya zagaya side din da take zaune ya bude mata qofar sai ya miqa mata hannu alamun ta taho. Hannun nasa ta kalla sannan ta kalli fuskarsa. Ta gama ganin zallar mayen giyar da yasha yana narkewa a jikinsa "No need" Ta fada tana girgiza kai sannan ta dauke dubanta daga kanshi. Baya yaja kadan yana furzar da iska daga bakinsa. Gulmarta yakeyi a ranshi,jin kanta yayi yawa,tana da wata izza da wani irin jan aji da kamewar da bai taba gani a wajen matan titi ba sai a kanta,amma ba komai,yaci alwashin a yau dinnan sai ya banbance mata aya da tsakuwa,dukka wannan jan ajin garawar da wahalar dashi data dinga yi sai ya fansheshi a yau. Tana gaba yana bayanta kamar ma ba tare suke ba har suka wuce ciki. Bata sake gasgata da gaske yayi booking ba......da gaske lamarin namiji abune me bada mamaki da daure kai ba sai da suka shiga babban dakin daya kama musu,wanda duk kwana daya a yadda ta gani cikin jadawalinsu naira dubu tari takwas da hamsinne. Komai an jere na kayan abinci,isowarsu kawai ake jira. Ya fada saman lafiyayyen gadon da yafi kama da gadon da ake shirin cin amarci a kai yana dubanta qasa qasa. "Komai da kike buqata akwai an tanadeshi.....amma inajin sai kinyimin alfarma na matse baccin nan ko na awa daya ne cakal.....kiji dadinki yadda kikeso.....idanma akwai wani abu da kike da buqata ga waya can ki musu magana zasu kawo miki" Yayi maganar muryarsa tana maye ita kanta,da alama baccin yayi mugun cin qarfinsa. Sanda ya miqe yana shirin sabule wandonsa da riga sai ta kau da kanta tana jin yadda zuciyarta tayi wani irin bugawa. Irin wadannan abubuwan take gudu shi yasa bata taba yarda ta biyo kowa wani kebantaccen waje ba,sai gashi haka kawai jib ya takura mata sai tabi mutum biyu don samun cikar aikinsu. Yif taji ya koma ya fada saman gadon,koda ta maida dubanta sai taga bai iya cire komai a jikin nasa ba,kawai kokawar banza ya gama yi ya koma ya fadi cikin bacci. Minti goma qwarara ta bashi sannan ta taka ta isa gabansa. Yayi sadidan a baccinsa,taja da baya a hankali tana jin faduwar gaba tace "JIB yayi bacci" "Good" Ya fada yana jawo dukka kayan aikinsa. "Stay tuned.....minti talatin ya wadatar......ki kula da duk abinda zanyi requesting" "Okay" Ta fada tana jin sanyin jiki da faduwar gaban da batasan dalilinsu ba. Ganin mintuna arba'in suna niyyar shudewa ba wani labarin nasara,ga mikail yana motsawa lokaci bayan lokaci ya sanyata magantuwa "Jib.....ya ake ciki?" "Wannan aikin yayi tsauri da yawa adda.....akwai tsauraran matakai da shinguna masu zafi a kai,yanxun haka abinda na soma fahimta kamar wani abu ya fara alerting nasu anason musu kutse cikin asusun nasu" Ya fadi shi kansa kamar yanajin qarfin gwiwarsa yana son sarewa. Duk inda ya zaci zai samu nasarar balla account din nasu da dukkan hanyoyi da dabaru amma sai yaga abun kamar ya wuce nan. Daidai lokacin da yake tsaka da meeting da investors din da suka jima suna da shaawar sanya hannun jarinsu a kamfaninsa na jadda diamondchore resources da yake a lagos da kano.....da kuma sabon kamfanin da yakeson yabude din a yanzu na jewelry da sauran dangin kayan ado da qawa na mata. Daga saman system dinsa wani abu ya fara harbawa. Alamace da take nuna masa DANGER. Sosai ya zubawa alamar idanu,sannan da hanzari ya jawo system din gabansa ya soma bibiyar abun "What?,scammers?" Ya furta qasan ransa,sai ya kalli baqin nasa yana miqewa tsaye gami da daukan wayarsa "Excuse me" Yana daga musu hannu tare da takawa a hankali yana matsawa nesa dasu. Sadiq dake can nesa dashi ya kira "Call the security team na kamfani......ka gaya musu akwai alamun shirin yin kutse su kula". "Done" Ya fada kaman yadda ya saba gaya masa. Juyawa yayi yana komawa wajen baqinsa,ya koma mazauninsa ya zauna yana jawo system din gabansa. Hankalinsa ya raba biyu,yana saurarensu yana kuma duba yadda suke samun progress na sake kutsa musu. Alama ta qarshe daya gani ta sanyashi lumshe idanunsa hadi da ture system din gefe kadan ya maida dukka hankalinsa dari bisa dari akan baqinsa. "Done adda!......done,millions of naira sunyo dropping" JIB ya fadi da wani irin sautin farinciki,yana jin sukuni yana ratsashi na samun cikar mafarkin mutanen da suke rayuwa ruhinsu a jikkunansu. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* Page 73 "Zan iya tafiya?" Shine abu na farko data tambayeshi ba tare da tabi takan adadin kudin da suka samu cira ba "Yes adda.... Zaki samu me napep a corner farko na street din yana jiranki gudun samun delay". Katse kiran kawai tayi,ta miqe tana daukar jakarta ta jefa wayar hannunta da sauri tana dan duban yadda mikail yaketa motsawa,alamar koda kowanne lokaci yana iya farkawa,saita wuce kai tsaye ta bude qofar ta fice. Sai data tsaya da lobby din ta daidaita nutsuwarta da kyau gudun zama suspect a idanun security na hotel din,sannan ta fara takawa a nutse tana qarasa ficewa. Hankalinsa a tashe yake dawowa wajen fuad din,yama gaza kiransa a waya kaman yadda shi ya kirashi a daxun. Ta bayansa ya qaraso,yadan rusuna don sanar dashi halin da ake ciki "Na sani.....jeka jirani mu qarasa mu wuce gida" Ya dakatar dashi ba tare da ya barshi yace komai ba. Da dan mamaki sadiq yake dubansa ganinsa zaune hankali kwance. Duk da yasan yafi gaban hakan amma wannan din ba qaramin abu bane da ya kamata ya ganshi haka a zaune calmly ba yana tattaunawa da investors,to amma bashi da sauran zabi illa juyawa ya tafi din kamar yadda ya buqata. Tana tafe a hanya tunane tunane cinkus cikin kanta da qwaqwalwarta. Haka kawai taji ta kasa isa gida,sai kawai ta bawa me napep din umarnin suna da wajen da take so ya kaita. Guri ne very quite,ba cikar jamaa,kuma kowa sabgan gabanshi yakeyi. Hakanan gurin yana da yalwa da fadin da zaka zauna a guri wani ma da yake nemanka bai ganka ba. Order din lemo da ruwa kawai tayi don batajin zata iya cin komai. Batasan me yasa ba.....ba yaune karon farko da haka ta fara faruwa ba amma wannan din yanason tsaye mata gami da sanyayar mata da jiki. "Eh ba shine na farko ba......amma kuma yafi kowanne nauyi da girma......baki taba samun kudade masu tsananin kauri da yawan wadannan ba,sannan kamar an shiga lalitar wadanda baki taba koda magana dasu ba.....kaman akwai nasu haqqin a ciki". Wani sashe na zuciyarta ya fara tunasar da ita. Wanda qarar ring na wayarta ya katse mata tunanin. Sunan titi data gani shi ya dauke hankalinta daga dukkan tunanin komai,ba jinkiri ta daga wayar suka fara magana "Da sauqi.....amma sumanta biyu yau" "Komai ya qare in sha Allah" Ta bawa titi amsa a taqaice saita katse kiran. Dukka karsashinta taso dawo dashi,ta fara lalubar wata number da jib ya bata. Ayyuka biyu tayi a wajen da suka qara kashe mata kusan awa daya da rabi. Ta tura dukkan abinda mutumin ya buqata don yiwa titi aishatu da dan rakiya daya visa na fita qasar india da ita da komai da komai da zaa buqata na asibiti lafiyarta da sauransu wanda ya lashe maquden kudin da suka ninka kudin da akayi hasashen zaa kashe din. Abu na biyu kuma ta zauna ta datse ta share ta kuma sake toshe kowacce hanya ko kafa da zata sake sadata da mikail.....sai data tabbatar ta sanya kowanne shinge da zai nesantata dashi nisa na har abada sannan ta tattare komai nata tana fita daga wajen. _hmmm,anya kuwa kayan Muhammed fuad jadda zasu tabu 'yammata?,to muje zuwa dai muga yadda wasan zai kaya FUAD dinne keda nasara?,ko SABREEN?_ Karo na farko a rayuwarta da taji shigowar sabreen cikin gidan dama dakin gaba daya amma ta shareta kamar ma bataji ba. Tayi lakur saman gadon tana ci gaba da kwanciyarta. Hirarsu da hameed yau ta dasa mata abubuwa da yawa cikin zuciyarta dangane da yayartata. Tayi amanna ta kuma yarda hameed mutumin kirki ne na qwarai,daga yadda yake yawan mata nasiha da wa'azin ta kare mutuncinta......ta guji yawace yawace da yawan fita barkatai.....don duk yarinyar data fiya fice fice,qafafunta basa zaman gidan tabbas akwai ayar tambaya a kanta ko taqi ko taso,alamar kamewa ga mace shine ta lazimci zaman gida. A yau din ayoyi qwalli biyu da hadisai guda biyu suma daya karanto mata sunja hankalinta. Itakam hameed yayi mata,a yanzu dukka burinta shine tayi aure......tayi aure ta matsa daga rayuwar da take sake Fahimtar yaa sabreen din tana yi.....ta auri hameed tayi nesa daga cakwakiyar gidansu.....baqaqen maganganu zallar gori da habaice habaice. Ta tabbatar zata samu irin rayuwar da takeso daga wajen hameed,zai killaceta kaman yadda yake fadi din. Tayi mamaki sosai da taga qofar tasu a bude,sanda ta shiga kuma falon sai ta tabbatar akwai wani a ciki,sai ta aje jakar hannunta ta kutsa uwar dakin. Gaban gadon hudan ta qarasa tana kiran sunanta. Da farki sai tayi banza kamar bataji ba,har sai data saka hannu ta yaye bargon da take ciki "Lafiya huda?" Ta tambayeta tana qoqarin son ganin fuskarta "Lafiya qalau" Ta samu kanta da bata amsa kai tsaye. Wani irin mamaki yaso kasheta a tsaye,amma sai ta cinye wannan. Hudan a yanzun ta fara zama budurwa,shekara sha biyar ta fara hawa bigiren kaiwa yammatanci,tabbas zata iya faskantar canje canjen halaitada dabi'u a tattare da ita kaman yadda ta tabaji mamanta ta fadi a sanda take cika tata shekara sha biyar din,wanda a yanzun shekara biyar daidai kenan "Idan har lafiya lau huda me zai hanaki zuwa makaranta kuma uhmmm?". Kamar ta bude bakinta ta gaya mata aure takeso,kamar ta bude baki tace ta bawa hameed ita,kamar tace mata ta gaji da ganinta kullum tana fita babu sahihin inda take zuwa,ba makaranta ba ba kasuwa ba,amma sai tace "Gajiya nayi,amma zani gobe" "Gajiya?" Ta maimaita qasan ranta,amma a sarari sai tace "Allah ya kaimu" Ta juya zuwa sashen kayan sawarta tana fidda kayan jikinta don sauyawa da wasu. Can qasan ranta zuciyarta ta kasa samun nutsuwa,sake gaya mata takeyi "AKWAI MATSALA.....DOLE KI NINKA SANYA IDANUNKI" da wannan tunanin ta kammala canza kayan sannan ta juya ta koma falon don duba me dame akayi da bata nan. Da kallo ta bita har ta fice,sai taja qaramin tsaki qasan ranta zuciya da shaidan suna ayyana mata ko dame dame ma tayi sanda ta fitan?,caraf kuma wani sashe na zuciyartata ya kwabeta *D U N I Y A TA* *_H U G U M A_* PAGE 74 Kaman kowanne lokaci ya bawa kowa daman yayi order na abinda yakeso qarqashin kulawar sadiq da shike handling kusan komai. Shi daya ya ware kansa a wani table da corner na daban,ya fidda system dinsa da ya sanya sadiq dauko masa ita. Ranshi a tsananin bace yake,amma kuma yana da wani irin abu,ya iya boye fushinsa idan yaso,ya iya kuma danne abinda yake damunsa,dole da rayuwa sun sanyashi iya controlling anger dinsa. Yana da matuqar sani da zafi gami da kaifi ta bangaren computer.....ya koma da baya daga baya cikin karatunsa,ya zabi computer science ya kashe lokaci akai har sai daya zama qwararre kuma cikakke akan fannin,saidai ba kasafai ayyuka da cushewar abubuwa ke bashi daman practicing karatun nasa ba,amma komai nasa zaka sameshi a tsare da burbushi da alamu dake nuna yasan kan computer sarai. A nutse ya soma bin komai daki dai cikin matuqar qwarewa tare da sanin makamar komai. Ba jimawa musaddiq ya iso wajen,sai yayi masa alama yayi joining sadiq kawai. Juyawa yayi yana matsawa daga wajen don tunda ya ganshi a hakan ya bawa system nutsuwarshi yasan akwai abinda yakeyi me amfani. Ya samu sadiq din yana waya wanda ya kasa jurewa ya kira security team din da kansa. Ranshi a bace shima yake wayar,duk da abincinsa dake ajiye gabansa baiko bi ta kansa ba. Dan zuba masa ido musaddiq yayi kafin ya zauna,jikinsa kuma yana bashi lallai akwai wani abu. Jawo tray din yayi yana bude komai tare da warware spoon da fork din dake nade cikin tissue,ya sanya musu cikin abincin ya saita musu komai saidai still hankalinsa yana kan saddiq din. Kusan mintuna goma sha biyar da isowarsa kafin ya kammala wayar,ya kasheta ya ajiye yana jan tsaki. "What's going on?" Musaddiq ya jefa masa tambayar yana dage giranshi. Cup din daya zuba musu ruwa ya jawo yana kurba "Scammers......hackers.....me ma zance ne musaddiq?". Idanu musaddiq ya waro waje yana kallon sadiq "A'ina?Meye ya faru?" "Sun diba maquden kudade daga cikin asusun company dazu........security team dinmu sun kasa aiwatar da komai......hamma fu'ad kuma baisan wanne matsaya ya dauka ba.....duk da nasan bazai qyale ba amma sai naga kaman ya dauki abun da sanya.....ina dai kyautata zaton yanzun yakebin kadin abun kamar ba kudi masu yawa aka diba ba" Saddiq yayi maganar yana maida hankalinsa ga fu'ad dake dan nesa dasu wanda baya iya ganinsa sosai da sosai "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Musaddiq ya soma maimaitawa yana rasa abun fadi kwata kwata. Sannu a hankali ya soma bude idanunsa har ya gama budesu gaba daya "Wayyo......." Ya furta yana miqewa sosai saman gadon yana jin yadda kanshi da idanunsa sukayi fresh. Komai ya sakeshi kenan,babu wani sauran burbushin giyar a tattare dashi,komai kuma zai tafi daidai yadda ya dace. Idanunsa ya fara wurgawa cikin dakin bai ganta ba,sai ya barwa ranshi tana toilet ne tana shiryawa,don haka ya jawo wayarsa yana yana duba time "Kai!" Ya fada a mamakance ganin irin baccin da yayi na kusan awa uku maimakon awa daya kacal kaman yadda yace zaiyi. Jikinsa ya danyi sanyi ganin yadda baccin yayi tsaho,zuciyarsa ta raya masa yarinyar nada wani irin aji da wahalar samu tamkar tarwada cikin ruwa,anya zata zauna duka wadannan awannin tana jira?. "Da kuwa na tafka babbar asara" Ya furta a sarari gabanshi yana faduwa,sai ya jiye wayar ya miqe da hanzari ya nufi toilet din. Duka bandakin ya duba ba ita ba alamar ta,sai ya fito ya soma duba dakin har zuwa balcony dake gaban dakin,lobby da sauran gurare,hakanan ya dawo zuciyarsa na harbawa da tsananin baqincikin kufcewar wannan damar a garesa "Wai me yasa ma nasha barasa duk da sunan farinciki?,wannan tsinannen baccin......" Ya katse zancan bayan ya zauna gefan gadon yana dafe kansa da hannayensa bibbiyu. Yadan jima a haka yana karatun asarar da yayi,da kuma wassafa yaushe zai sake samun irin wannan damar?. Tsaki yaja sanda yaji wayarsa tana qara. Ya waiwaya yana duban me kiran,john ne chief of security team. "Ubanshi zan masa......ya barni naji da asarar da nayi" Ya fada a sarari yana rejecting kiran. Sake kira yayi bayan sakanni biyar kacal,hakan ya sake qufular dashi,don daga yanzu har wayewar gari har kwana uku bayajin zai huce daga asarar da ta sameshi. Sake rejecting yayi,bai haqura ba ya sake kiransa a karo na uku. Wannan karon da niyyar cuccusa masa ashar ya dauki wayar,tunda a tsakaninsu kar tasan kar ne,saidai yana dagawa ya jefeshi da tambayar data sanya ya shiga tunani "Kana tare da wayarka kuwa?,kasan me yake faruwa?,bakasan anyi kutse account din kamfani ba?". Dif wuta ta dauke masa,sai kuma ya bude bakinsa " Kai john banason iskanci.....ka sanni na sanka,idan giyarka ka shawo ka daina gigin kirana ka bari ta sakeka tukunna,wayata tana hannuna......kuma ba wani abu daya faru,na sani fa ka dade kana harin muqamina,to qaryarka tasha qarya......in kanaso sai ka jira sai sanda matsayina ya qara daukaka a jadda company sai ka shiga takarar neman tsohon matsayi na" Daga haka ya katse kiran yana mitar shi baisan abinda yake damunsa ba zai qara masa damuwa. Yankewa yayi kawai ya kirata ya lallasheta ya kuma sake shawo kanta,tunda kudin kwana biyu ma ya biya,ya samu ko wuni dayan gobe tayi masa tunda ya tabbatar ba zata taba dawowa a yau ba. Saqon da idanunsa suka gane masa daga banking da kamfanin nasu ke ta'ammali dashi ya kusa sanya gudawa da fitsari duka yanke masa lokaci guda. Yayi wani mugun gigicewa sanda ya shiga saqon idanunsa suka haska masa adadin kudaden da aka zare daga asusun. Wani irin abu yaji yana tsirga masa daga kowacce kafa ta gashi dake jikinsa. Gangar jikinsa yakejin kamar ba tashi ba ballantana ayi batun qafafunsa su samu daman iya daukansa,don haka sai kawai ya sulale ya zube ragwab a wajen yana jin kamar numfashinsa zai qwace masa. Meye ma zaiyi ne?,ihu ko kuka?,hauka zaiyi ko mene?,kudade maqudai?,kudadenma kuma na kamfanin jadda?,kudaden da akansu yau suke lissafi zasu kuma gama lissafinsu a gobe?. Shin waye ya aikata hakan?,waye yake da alhakin aiwatar da hakan?. Yaushema abun ya faru?,wa zai soma kira ya tambaya bayan daga bakinsa ya kamata a fara ji?,wai yaushe ma abun ya faru ne?. Ko sanda ya duba time na faruwar abun,da sanda John ya fara kiransa sai kawai ya saki wayar ya dora hannu saman kai yana fadin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da qarfin gaske,wanda kalmar ma sam batazo bakinsa ba sai sannan. Yana dire kalmar farko hawaye suka fara bin kuncinsa. Daidai sanda kuma kira ya shigo wayar tasa abinda ya sanyashi zabura kafin yakai dubansa ga wayar. Sir sadiq daya gani a rubuce ya sanya fitsarin dole kubce masa duk kuwa da yadda yaso ga riqeshi. Ya shiga uku ya lalace,yasan tunda yaga kiran saddiq din magana ya gama isa kunnen boss. Da wanne baki zai kare kansa?,idan suka buqaci kuma ya biya a ina zai samu?,ta ina zai samosu?. Yayi imanin koda danginsa zai siyar bazai hada wadannan kudaden ba. Zuciyar dake da Allah a cikinta......hakanan zuciyar dake da yawan ambaton Allah ce kadai ke samun nutsuwa a sadda bala'i ya durfafo ta,don haka dukka wata dabara da kuma nutsuwa sukayi qaura daga gareshi. Ya dinga zirya yana kai kawo,ya kasa aiwatar da komai,ya kuma kasa kamo bakin zaren komai. A haka lokutan sallah duka suka shude masa,hakanan qarar kiraye kirayen mutane suka yita shiga kunnuwansa suna fita ba tare daya iya rabar inda wayar take ba. Duk wani kira da zai shigo wayar tsoro yake bashi,baya qaunar koda rabar inda wayar ma take gaba daya. Sai kusan bayan sallar ishai ya iya fusgo tunanin baiyi sallah ba,ya miqe yana hada hanya ya nufi toilet don cire jiqaqqen wandon jikinsa daya jiqe da fitsari ya dauraye jikinsa ya kuma daura alwala. Har a sannan sam tunaninsa bai kawo masa sabreen ba,ya mance sam sam da itama saboda tsananin rudanin daya shiga. "Don't call him again......ka barshi,inason naga iya gudun ruwanshi......kafin sannan ni na gama nawa" Fuad yace da sadiq wanda ke shirin sake kiran mikail din karo na biyu "Okay" Ya amsawa fuad din yana maida kansa ga titi. Ring na wayarsa ya katse shurun daya gilma cikin motar. A hankali ya maida kallonsa kan screen din. Anni ce,sai a sannan ya manta bai kira ba bai kuma sanya an kirata ba wunin yau. Zuciyarsa tadan saki daga quntatar da take ciki,ya daga wayar yana sanyata a kunne. Kusan tare suka yiwa juna sallama ita dashi,sai suka amsawa juna sannan tace "Nace dai Allah yasa lafiya......daga ku har abbanku yau duka kunyi dare a waje" "Lafiya lau anni.....ayyuka ne suka riqemu,wasu al'amura kuma suka taso wadanda su suka shagaltar dani daga kiranki" "Babu komai......kada ka damu,tunda dai dukkaninku kuna lafiya to alhmdlh......farouq yace min kuna tare da musaddiq ko?" "Eh muna tare anni" "To Allah ya tsare,ya dawo daku lafiya" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ya amsa mata zuciyarsa na sake cika fal da qaunarta da qarin ganin kimarta. Tana taka muhimmiyar rawa qwarai da gaske wajen cike musu wawakeken gibi da ramin dake zukata da kuma rayuwarsu. Tun da aka kirayi sallar magariba ta gama shirya komai,sannan ta sallami masu aikinta kamar jiya. Tsaf ta shirya cikin embroidery holland gold atamfa da keta sheqi da nuna ainihin tsadar sutturar. Tayi kyau abinta,kai ba zakace itace ta haifi zabgegen saurayi irin muhammad fuad da musaddiq ba. Ita din ba baya bace wajen iya kula da jiki da tattalin fatarta da dukkan abinda zaya qara mata lafiya da kuma quruciya. Parlor ta koma tayi zaune bayan ta kunna tv ta kuma saita tashar da take ra'ayi. Ta kame saman daya daga cikin sofas din falon tana kallon hagunta da damanta. Kujerun take kallo,a ranta tana wassafa ranar da zatayi gwanjonsu. Duk da tsadarsu da kudaden da aka kashe wajen mallakarsu sam ita bata tuna wannan. Abu daya dake sake tsaye mata a rai shine,labarin katafaren ginin daular data samu cewa yana yi cikin garin abuja. Batasan ainihin wacce unguwa bace,amma me kawo labaran ya shaida mata cikin jerin unguwanni mafi daraja da tsada a garin abuje yake ginin,kamar yadda yakejin qishin qishin din yana nan yana tamfatsa wani a lagos. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 75 K'aramar qwafa taja,muddin da gaske wannan villa din yake ginawa.....indai da gaske hoton da me dauko rahotonta ya nuna mata fuad dinta ke ginawa.....to kuwa koda zatayi yawo tsirara ba zata taba bari ameena da hamza su sanya qafafunsu cikin wannan daular ba. Wayarta ta dauko ya kira hajja harira,a nan suka bata lokaci me tsaho suna sake tsara yadda komai zaya kasance. Batasan ma lokaci yaja haka ba sai da suka gama waya da hajja harira din. Ta kalli agogo tana mamakin rashin shigowarsu gidan,fargaba na saukar mata na kada fa yau ma a maimaita abun jiya?. Bata samu fuad ba,amma ta samu musaddiq,ya amsa mata da zasu shigo,don shima baisan fuad din ya gama shirya yadda zasu cinye daren a waje ba. Ci gaba tayi da duba lokaci mintuna bayan mintuna,saidai duk sanda ta kalli agogon sai ranta ya sake baci,haka ta sake jawo waya da xummar sake trying number musaddiq amma ta kasa samunsa. Ranta ya sake baci qwarai,dama ta sani samun number fuad ba abu bane me sauqi,sau tari xaka iya kiransa ka kasa reaching dinsa,saboda ba da gama garin wayoyi yake amfani ba don dalili na tsaro da kuma matakin rayuwa da yake kai dole yana buqatar tsari akan komai nashi. Dukka number dinsa taci gaba da gwadawa,number ta qarshe data kira taji alamun kiran ya soma tafiya,saita samu gefen kujera ta zauna tana furzar da iska me zafi daga bakinta ranta yana tafasa. Kaman jira ake ya gama wayar wani kiran ya shigo. Kamar ko yaushe bayyanar sunanta saman screen din fargaba da kokwanto yake sanyashi. To amma ba yadda ya iya,dole ya daga kiran ya mata sallama kaman yadda yake a dabi'arsa. "Wa'alaikumussalam.......me yasa har yanzu baku shigo bane fuad?,ka manta da alfarmar dana nema kenan?" Ta fadi tana qoqarin tausar zuciyarta ta yadda kalaman zasu fita da taushi daga bakinta. Komai qanqantar motsi tsakanin anni da maamah sai yaga tarin banbance babance. Da fari anni lafiyarsu kawai takeso taji kafin komai......amma ita nata uzurin su shigo suci abinci shi ta fara gabatarwa,abincin da ta tabbatar koda basuci a wajenta ba zasuci ako ina nema,amma kuma lafiya fa?. "Ayyukane suka tsaremu yau dukkaninmu,yanzu haka ma wani guri zan qarasa......amma in sha Allah i will do my best". Shuru ta danyi wuta tana dauke mata,yanzun qarfe tara harda rabi na dare,yaushe yaje wani waje,yabaro gurin kuma yazo wajenta?. " Okay,ina jira" Abinda ta fada kenan tana jin kamar ta bude masa abinda ke ranta. Bala'i da masifa takeson lullubeshi dashi,to amma ko dazun suna waya da hajja harira sai data gaya mata "Me garaje ba kasafai ya fiya cin nasara ba a dukka lamuransa,saikin saka haquri juriya da kauda kai kaman bakiga komai ba". Wayar ta cillar gefe,ta hada tafukan hannayenta cikin fuskarta. Wata irin tsanar anni da alhaji hamza tana mata masauki a zuciya tana kuma qara samun hauhawa cikin ranta. Inama ace yau zata budi idanu taga babu su cikin rayuwarsu?,da kowacce dama tazo mata yadda takeso. Iya tafiyar da sukayi cikin motar bawai zaman shuru kadai yayi ba,zuciyarsa ta gama nisa akan matsalar iya balla shingen asusun ajiyarsu har kuma a debi wani abun?. Ba shakka koma waye ya aikata hakan yana da alaqa me qarfi da kamfaninsu,yana kuma da alaqa ta kusa kusa da mika'il. Dole ya zamana yana da alaqa da mikail.....ko shi kansa mikail din ma gaba daya. Dalili......dukan abinda zai basu daman yin kutse kai tsaye da samun nasara haka a sauqaqe yana tare da mikail din. Dazu dazu ya danqa masa komai,cikin qasa da awa biyu kacal kuma ace komai ya faru?. "Muje gida" Ya bawa driver din umarni,wanda ba wanda ya binciki dalili tsakaninsu ukun suka sauya akalar tafiyar tasu. A tsaitsaye ya leqa anni sannan ya wuce zuwa sassanshi. Ya samu sassan nasa neat kamar ko yaushe kaman kuma yadda yake buqata. Ba duhu ba kuma haske me yawa sai matsakaicin hasken da bai fiya takurawa idanuwa ba. Ko ina qamshi yake fiddawa da wani irin moderate yanayi. Takalmanshi ya sabule daga bakin qofa yana sauya wasu lausasan flip flops,daya daga cikin hadimansa ya sunkuya ya daukesu yana adanasu cikin wani qawataccen ma'ajiyar takalma me daukan hankali. "Ku ajiye komai ku tafi,na sallami kowa.....sai da safe" Ya fadi musu yana takawa zuwa hanyar da zata sadashi da wani dan corridor da zai bashi daman isa bangaren dakunan baccinsa. Daga zuciyarsa har gangar jikinsa basu da wani karsashi ko qwari,to amma kasancewar zuciyar jaruma ce ya sanya bata gaza ba,sai daya tabbatar yayi wanka yayi sallah ya sauya kayan jikinsa sannan Kai tsaye ya dawo falon da babu kowa a cikinsa,saidai ya tabbatar security tako ina suna kai kawo cikin gidan dama wajen gidan. A nutse yake ratsa falon hannunsa zube a aljihun boxers din daya sanya tamkar wanda ya boyeshi saboda jin sanyi ko baya buqatar aga hannun nasa. Light blue kalan kayan sun masa wani irin kyau,saidai kuma fuskarsa tadan fada kadan wanda baya rasa nasaba da stress din yau daya tsinci kansa a ciki. Dining ya wuce kai tsaye,komai yana shirye cikin tsafta. Bayajin a duniya bayan anni akwai wanda yakai ameh sanin tsarinsa akan abinci. Yasan duk abinda ya bude cimarsa ce,kuma abinda yakeso ne,saidai kuma bayajin akwai wani sauran space da cikinsa zan dauki abinci,wannan ya sanya ya bude royal glass bowl din da tun bai bude ba yana iya ganin abinda yake ciki. Lafiyayyen fruit salad ne da aka samar dashi daga dukkan nau'in kayan marmari na nan qasar dama wanda bamu dasu a nan din. Baya rabo da fruit sam,don haka masu shirya masa store da fridge dinsa sunsan duk inda zasu samar masa da nauin fruit da cimar da yakeso din. Yadan diba da yawa,sai ya sauka a hankali ya duba ma'ajiyar shayinsa. Bayashan coffee sai idan dole ta kama,amma yasan sirrin shan black tea da ake masa hadi na musamman da abubuwa masu amfani ga lafiya irinsu cinnamon cardamom scent leaves da sauransu. Da kansa ya shirya komai saman tray ya nufi wata yar kyakkyawar books shelves ta ainihin gogaggen katako dake bangon gabas na parlor din. Hannu daya ya sanya ya murza wani abu da ba lallai ka iya lura da zamansa jikinta ba,sai ya sakeshi yasa hannu ya juyashi take qofa ta bayyana daga baya abinda ba zaka taba tunanin samuwarsa a wajen ba,ya taka ya shiga a hankali yana maida qofar yadda take. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 76 Daki ne da yakan jima bai shiga cikinsa ba sai muhimmin aiki irin haka ya taso. Saidai duk da haka komai a tsaftace yake. Wani irin table ne na musamman ya jawoshi gaban main table dake dauke da nau'ikan na'urorin computer iri daban daban,ya aza tray din hannunsa a kai,ya taka a hankali ya kunna kowanne lantarki dake dakin,ya bada haske sosai. Komai na dakin bisa tsari yake,da nau'o'in kalolin green masu qarawa idanu qwarin gani. Idanunsa saman systems din daya kunna guda biyu yana jiran su gama saituwa. Kadan kadan kuma yana kurbar black tea din da qamshinsa ke qara masa nutsuwa,kafin ya ajiye ya soma shan fruit salad din,daidai sanda komai na system din ya daidai ta,sai ya sake jawo kujerarsa gaba yana bata dukkanin hankalinsa. Cikin tsananin nutsuwa da qwarewa yake bin komai. Ya kusa kashe a qalla awa biyu cikakku kafin ya dakata,ya tura kujerarsa baya yana zubawa allon computer idanu yana duba abinda ya samu a tsahon zaman da awannin da ya kashe. Iska kawai yake furzarwa daga bakinsa,mamaki yana sake cikashi da samun bayanan duk da bai qarasa samun ragowar baya nan ba,amma ko iya wadannan bayanan da zaman da zaiyi da mikail sun isheshi samun kan komai. Ya dinga murza tafin hannunsa cikin na juna tamka ma jin sanyi,kanshi yana sake cakewa. "Jibril usman" Ya maimaita sunan idanunshi nakan sunan da bai samu damar samun ainihin fuskar me sunan ba. Tabbas ko wayeshi din mayen computer ne,kuma qwarrare a sanin fanninta,saidai duk da haka qwarewar tasa akwai saura,don akwao gurare da abubuwa daya gani wanda shi Jabril din da ya samu rufesu to ba shakka shi kansa yanzun bazaikai ga isa ga bayanan ba. Qaramin masanin computer zai iya saluting jibril,amma shi da mutane ire irensa zasuyi murmushi ne kawai,a karon farko kuma su fahimci saura taqi kadan yakai inda ya dace yakai din. Gefe daya ranshi ya sake ninka baci,duk wanda yaga aka zare kudin zaiyi tsammamin manyan hackers gagarumai wanda suka gagari duniya system dinsu ta hadu dashi......wannan kadai ya isa ya sake zaburar dashi lallai lallai yana buqatar yin garambawul wa security team dinsa,amma kafin sannan mikail shine mutum na farko daya dace ya dauki mummunan mataki a kansa,saboda shi da kansa ya yiwa tsaron company dinsu aiki,ya saka abubuwan da duk qwarewarka idan ba samun wani information mutum yayi ba zai wahala ya samu isa ga inda suka samu isa din. "Ina yaje?,waye ya bawa sirrinmu?" Wadannan sune tambayoyi guda biyu da yake buqatar ji daga bakin mikail din. Kodai yaci amanar company......ko an nemi rayuwarsa an masa barazana....kota dalilin sakacinsa bayanan sun fita. Washegari kaman kullum,yabi tsarin jawadalinsa na kullum tun daga gida har zuwa office. Qarfe shida da rabi yake kammala motsa jikinsa ya wuce wanka,idan ya fito yakan dan bar bathrobe jikinsa ya karbi newspaper da magazines ya duba,yadan duba saqonnin email da WhatsApp dinsa ya hada da shan ruwan duminsa ko dafaffiyar madarar shanunsa me tumeric. Sai bayan kammala dukka wadannan hidindimun sannan yake shiryawa,yayi breakfast ya wuce office. Kamar ko yaushe yau dinma bakwai da rabi ya fito daga toilet daure da bathrobe dinsa. Yanaso yau ya fita da wuri ne fiye da yadda ya saba fitan. Don ko da safe daya tashi ya sami missed calls din maama din kusan guda goma,wanda ya tabbatar tun na daren jiya ne. Yawan kiran nata kadai da takeyi yana sake bashi tabbaci ne a kanta. Ya jawo wayar ya turawa musaddiq text akan zuwa takwas ya shirya zai aikeshi wani guri,sai ya cire toilet slippers din ya sanya wasu tausasan rufaffun takalma ya soma takawa yana fita don riskar parlor ya duba newspapers din yau. Ba kowa parlor din sai ameh daketa zirga zirgar shiryawa ogan nasa dining,sai me sunan malam dake zaune saman lallausan turkey carpet din da aka qawata tsakanin kujerun. Me sunan malam din na daya daga cikin amintattunsa da basu da shamaki wajen samun daman isowa parlor dinsa. "Good morning sir" Ya fadi yana rusunar dakai "Morning me sunan malam.....mun tashi lpy" Ya amsa masa yana zama saman wata sofa guda daya data banbanta da sauran duka kujerun parlor din yana kai hannunsa saman dan qaramin table din da aka zube masa sabbin newspaper din bayan an kwashe na jiya. "Lafiya alhamdulillah sir" "Ma sha Allah" Ya furta yana bude page din farko na jaridar ba tare daya tsaya karanta bangonta dake dauke da title na labaran ciki ba. Labarin farko suka wafci idanunsa. Ya sake dawowa da baya bayan ya karanta layin farko da akayi da manya manyan zane. Bai tsaya bata lokaci ba ya koma bangon don sake duba title din da ya tsallakeshi a dazu. Tabbas duka abu guda suke nunawa cikin harshen turanci *_GAGARUMAR SATA.....AN WAWASHE KOMAI DAGA ASUSUN JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES/AKWAI YIWUWAR DURQUSHEWAR COMPANY DIN NAN DA WANI DAN LOKACI_*. Jaridar ya juya tamkar ma ya manta wanne gidan jarida ne suka kafe labarin. Sai ya maidata ya ajiye yana dauko newspaper ta gaba. Ita dinma kaman wancan,bangon farko abinda yake rubuce kenan a jiki,ya sake juyawa shima ya duba gidan jaridar sai ya maidata itama din ya ajiye,ya sake daukan ta uku. To ita dinma babu wani canji,duka dai labari guda daya ne,abinda ya bashi tabbaci da yaqinin wannan shine labari na farko da zaiyi trending kenan yau a duniya kasuwanci. Idanu kawai yaci gaba da zubawa rubutun kamar wanda kwanyarsa ta kasa gano komai,ya daga idanunsa a nutse da suka fara sauya launi ya kalli ameh daketa goge dining din da kyau don kawar da qura datti ko maiqo komai qanqantarsa daga muhallin cin abincin boss din nasa da ya sani da tsananin tsafta da rashin son qura ko datti komai qanqantarsa "Ameh......dauki waya ka kira sassan saddiq.....i wanna see him yanzu yanzu". "Yes sir" Ameh ya amsa masa yana sakin komai,sannan ya gangara a hankali yana nufar inda wayar take girke. Daidai sanda ameh ya gama shaidawa saddiq saqon fuad farouq yayi knocking daga can first door sannan ya turota a hankali ya shigo. Yana sanye da kayan motsa jiki da alama fitowarsa kenan daga dakin motsa jiki na gidan,wanda dama kusan kullum shine qarshen shiga,fuad kuma na farko,saddiq da musaddiq ke binsa daga baya. Dauke yake da jaridu har guda uku a hannunsa,kallo daya fuad yayi masa ya karanci shima labarin ya gani kuma shi ya shigo dashi. Fuskarsa a dinke ba walwala ya samu kujerar dake fuskantar fuad din,wannan ya sanya me sunan malam ficewa ba tare daya gabatar da abinda ya kawoshi ba,hakanan ameh shima ya wuce ta kitchen ya bulla ta baya yabar sassan. "Tun jiya naketa qoqarin ganinka.....duk da dare yayi sanda kuka dawo nayita nemanka ban samu ganinka ba........yanzu da safe kuma sai naga wannan" Ya fadi yana zube masa jaridun hannunsa. Binsu yayi da kallo sannan ya maida dubansa kan fuskar farouq "Nima haka na tashi na gansu farouq" "How comes fuad?" Ya furta tsananin bacin rai yana cin zuciyarsa. Kanshi ya motsa kawai yana girgizashi kadan "A lot of things farouq......bansan ma ta inda komai ya fara ba......na kuma rasa ta inda zan kamoshi......inajin kamar ana warwaremin tunani na ne......da farko wawashe asusun kamfani ta sigar da ba wanda zai iya yinta sai na kusa ko wanda yasan sirrin asusun......ina cikin aikin kamo zaren kuma sai ga wannan......wannan fantsamar labaran tabbas shiryayyen abune koda kwashe kudin ba shiryayye bane.......zakafi kowa fahimtar anyi ne don a yiwa kamfanin illa......ta yaya babban kamfani kamar namu da yake da hannuwan jarin manyan 'yan kasuwar duniya ace saboda tsananin rashin tsaro har za'a iya kutsa kai ciki a debe kudin mutane?......wanne tabbacin tsaro muke dashi da zamu baiwa dukkanin wanda yake da buqatar kasuwanci damu?,wannan shine tuhumar da xamu fara fuskanta daga wajen al'umma......waye ya fidda labarin cikin qasa da awanni uku,har ya zamana labarin da kowanne shafin jarida suka maida bangon labarinsu?". Kai farouq ke gyadawa cikin zuzzurfan nazari,ya daga Idanunsa ya sake duban fu'ad "Shi kansa kwashe kudin nan baka tunanin aike ne?,ture ne?,kuma suna da alaqa da wanda ya fidda labarin?". Mintuna kusan uku fu'ad din baice komai ba,kansa yana sake qullewa,sanda ya bude baki zaiyi maganar sadiq ya shigo sanye da jallabiyya hannunsa riqe da system. Kallo daya dukansu sadiq din yayi musu ya fahimci sunga komai,tun da sassafe kiraye kirayen wayoyi suka tasheshi,kusan fitar labarin su suka hanashi fita motsa jiki tun daga sallar asuba daya koma. Yana tunanin ta yadda zai iya sanarwa da fu'ad din abun,amma kuma yasan zai wahala awannin safiya su wuce bai sani ba tunda shi din ma'abocin bin shafukan jarida ne. "I hope abba baiji komai ba ko bare anni?" Fu'ad yayi tambayar tsananin fuskar farouq da sadiq. Junansu suka kalla kafin farouq ya amsa "Zai wahala abba bai sani ba,tunda kasan yana bibiye da kafafen yada labarai,annin dai ita zaka zatarwa haka" Kai ya girgiza yana yin qasa da kan nashi,yasa hannunsa yadan shafi qasan wuyansa. "Yanzu mene abunyi?" Farouq ya tambayeshi yana kallonsa. "Dole komai ya kasance cikin hikima da kuma tsanaki,hakanan for now dole mu zama cikin takatsantsan da sanya ido akan kowa,faruwar wannan kadai ya sake gayamin tabbas akwai wasu qofofi dana bari a bude......akwai wasu bayanai namu tabbas da suke fita.....akwai wanda kuma yake dauka yakai din......sadiq " Fu'ad ya fadi yana dubansa "Na'am hamma" "Inaso kabar kowa a haka,kada ka sake amsa waya ko maganan kowa.....amma ka shiryamin meeting na sirri,koda me sunan malam banason yasan da zaman.....ka tsara awannin da zamu zauna din zuwa tashi,zai fara daga goma na safe har sai sanda na buqaci tashi......general meeting nake buqata" "Okay hamma" Ya fadi yana sauke system din saman cinyarsa cikin qoqarin duba schedule dinsa na yau yayi cancelling wasu ya kuma gyara time na wasu koda akwai yiwuwar zai iya gabatar dasu. Sun jima da farouq a wajen suna tattaunawa kafin farouq din ya miqe ya wuce nasa sassan da zummar shiryawa,don yanason ya bishi zuwa kamfanin. Sai qarfe tara saura suka fito,kaman ko yaushe ya taka zuwa sassan anni. Kowacce safiya takan zauna a parlor har sai taga ficewar kowa zuwa wajen sana'arshi. Yau dinma tana zaune cikin riga da zani na lallausar atamfar super exclusive me ruwan sararin samaniya da ratsin ruwan ganye. Ta lullube jikinta da tattausan mayafi dan turkey daya dace da atamfar,dukka hannayenta siraran awarwaro ne masu daukan idanu da suka dace da fatarta da batayi komai na darajar kulawa nutsuwa da kwanciyar hankalin da take ciki. Kamar kullum kuma kaman ko yaushe ya duqa gabanta suna gaisawa. Yau din bata ja zance dashi ba saboda ta karanci kaman gaggawar fitar sukeyi. "Muhammadu" Ta kirashi sanda suka gama sallama ya juya zasu fice *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 77 A nutse ya waiwayo sannan ya amsa "Na'am anni......akwai wani abunne?". Kai ta girgiza tana jin tausayinsa hakanan yana tsarga mata. Tasan cewa akwai abubuwa da yawa da suke damunshi cikin zuciya,amma shi din wani irin mutum ne me masufar zurfin ciki. Zai wahala kaji ya b'ara ko kaji kukanshi. "Kaman akwai wani abu ko?" Ta jefa tambayar gareshi don batason fitowa kai tsaye ta Qureshi da tambayoyinta "Ba komai anni" Ya fada cikin bata tabbaci,don yayi imani ya nuna mata akwai damuwar,to yinin yau gaba daya haka zasu barta cikin rashin sukuni. Kai ta gyada ba don ta yarda ba,sai don tasan koma meye idan ya dace ta sanin shine mutum na farko da zai fara gaya mata "Ubangiji ya kauda dukkan abunqi,Allah yayi jagora" "Ameen ya hayyu ya qayyumu anni,na gode" Daga haka ya juya yana fita. Har cikin ransa yakeji irin wannan addu'o'in nata,duk kuwa da cewa bawai shi daya takewa adduar ba kowannensu ne,amma yakanji a ransa kamar tasa ta dabance. Bai shiga mota daga parking lot na gidan ba,sai yace su fiddo motocin su sameshi waje. Ya soma takawa a nutse suna jerawa shida farouq suna tattaunawa kadan kadan har suka fito a gidan. Sanda suka doshi gidan nasu yayi tsammanin farouq zai dakata daga yi masa rakiya amma sai yaga yaci gaba da binsa har suka isa bakin gate. Sun gaisa da malam saidu cikin girmamawa sannan suka kutsa kai ciki,guards dinsa guda biyu dake biye dashi suka dakata suna jiran fitowarsa. Tunda ta wayi gari ta kasa tabuka komai,tana kwance kawai a daki tana kwancewa da saqawa bayan doguwar wayar da sukayi da hajja harira. Anya kuwa nasarar da take sanya ran samunta zata cimmata?,zata ma iya haqurin kwana ukun da bokan ya deba mata kuwa ba tare data koma ta sanar dashi komai ba?. Maida tunaninta tayi tana sarrafa shawarar da hajja hariran ta bata. Bata jin cewa shawarar zatayi aiki har ta lanqwaso mata me babban suna yadda takeso?.....anya bazai zama doguwar hanya me wahala ba?. "Waye ne?" Tayi tambayar cikin izza sanda taji an nace da knocking mata qofar bedroom "Nice hajiya.....yallabai ne yazo" Me aikin ta furta a qasqance "Yallabai?,fu'ad kenan?" Ta tambaya a mamakance tana duba lokaci "Eh shine" Ta sake amsawa a ladabce. Cike da mamaki ta kalli agogo. Wannan ba shine lokacin da suma saba shigowa gareta ba,me ya kawoshi yau da safe?,ko dukka cikin dabaru da salon son kauce mata ne?. "Ina zuwa" Ta amsa mata sannan ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon. Tun daga nesa ta zuba idanunta a kansu,hira suke qasa qasa da wani irin kusanci da emotion da zaka tsammaci su din tagwaye ne da ska rayu qarqashin mahaifa guda daya. Bata ga wani banbanci ba ko kadan tsakanin danta muhammad jadda mamallakin kamfanin haqa da sarrafa diamond ba.....da kuma farouq hamza kibiya me kamfanin saida tsabar abinci da taki ba!. Meye ribar suna da yayi?,meye amfanin salon banbancin kasuwanci tsakaninsu muddin a idanu zaka dinga hangar yanayin sukunin rayuwa iri daya tsakaninsu?. Kamata yayi ace ana hangen tazara tsakaninsu,kwatankwacin tazarar dake tsakanin bawa da uban gidansa. Wani irin abu yayi mata tsaye a wuya,amma dole ta saita yanayin fuskarta sanda ta isa gabansu "Wato farouq kayi wuyar gani,har gwara sadiq ya fika kirki anfi ganinka" Dukkaninsu ba wanda zancanta ya kwantawa,saidai kawai sun bita da irin yanayin da tazo musu dashi. Wannan faran faran sa sabuwar maraba da iyalan Alhaji hamza kibiya sabuwa a idanunsu da basu taba ganinta ba.....koda kuwa sanda ta dawo ta iske iyalinta cikin kyakkyawan rayuwa qarqashin jagorancinsu da tallafawar rayuwarsu. "Wanne irin aiki ne ya riqeku jiyan kaida dan uwanka kuka saka halartar kira na?" Tayi masa tambayar daketa cin ranta,don har xuwa lokacin bata gamsu wai aiki ne ya riqeshi ba Yana murza yatsun hannunsa idanunsa samansu,zuciyarsa na wani irin motsa cikin yanayi maras dadi. Koda yaushe maganarta babu komai ciki sai zallar son kanta a ciki......ba wani sauti alama ko yanayi na kulawa ko nuna damuwa......ba wannan shaquwar da maganadisu dake tsakanin uwa da danta da har zata iya karantar yanayin damuwa walwala ko farinciki da yake ciki,abinda dukka ta rasasu anni kuma ta haye kansu ta zauna sosai. "Yanayi ne na aiki da zai iya rutsawa dakai ako wanne yanayi ko lokaci" Ya amsa mata a taqaice don bawa kansa kariya . "Yau kuma fa?" Ta sake fadi tana tsareshi da dukka idanunta "In sha Allah" Kawai ya fada shima nan a taqaice. Duka duka zaman bai wuce na mintuna goma zuwa sha biyar ba suka wuce. Mintuna goman da suke da matuqar tsada da daraja a wajensa......don ita din itace.....yana jin ya wajaba ko yaya ya bata wadannan mintunan don tserewa tuhumar ubangiji. Fadin ma yanayin daya kwana a cikinsa a wannan ranar dare har ya zuwa safiya bata baki ne. Duk sanda ya waiwaya ya sake duba wayarsa sai ya dinga jin abun kamar mafarki......kaman baccin daya kwanta shi yakeyi,kaman har yanzu idan ya farka zai samu komai ba gaske bane. Daga sallar magariba har ishai saida safe ya hada da asuba ya ramasu. Gaba daya ya wani firgice ya fita hayyacinsa a tsakanin. Ba abinda yake iya tunawa sai wanene Muhammed jadda da kuma irin hukuncin da zai iya dauka a kansa. Duk yadda yaso ma ya yiwa kansa hasashen ta inda zai fara kare kansa a gaban mutumin da a fagen aikinsa baida maraba da zakin daya fito farauta sai yaga sam zantukan daya tsara ko kadan basu hau kan saiti ba,basu kuma dace da hankali ba. Tsananin tsoron da firgicin ya sanyashi kashe wayoyinsa gaba daya,saishi kadai cikin dakin tamkar tsohon mahaukaci. Ba abinda kunnuwansa ke gaya masa sai sautin sallamar talauci cikin rayuwarsa,an debi kudin da ya tabbatar baida abun biya koda kuwa zai saida komai daya mallaka shi da danginsa su koma yawo tsirara. Taku biyu yayi don shiga toilet ya rage gudawar da yake fama da ita tun faruwar abun idanunsa suka fada kan dan kunnen. Gabansa yayi wani mummunar faduwa sanda kwanyarsa ta haska masa wani abu lokaci guda tamkar haskawar walqiya cikin duhun dare. Tsugunnawa yayi ya dauki dan kunnen.....sai yanzu ma ta dawo kwanyarsa,sai yanzu tunaninsa ya soma haska masa wani abu "Fateema?" Ta maimaita ainihin sunan da shine nasa STAMP din data bashi. Komawa yayi ya zauna saman kujerar dake daura da qofar bandakin yanason tuna yininsu na jiyan a tare. Yayi dukkan wani flash back daga qwaqwalwarsa zuwa zuciyarsa da kuma idanunsa,ba wani motsi nata guda daya daya bashi alamun rashin gaskiya a tattare da ita "To amma me yasa na farka na nemeta na rasa?" Ya jefawa kansa tambayar data sanyashi miqewa ba shiri,ya jawo wayarsa da baiyi shirin kunnuwa ba ya kunnata,cikin ransa yana jin gamsuwar tabbas ita ta aikata ko kuma tana da hannu wajen afkuwar komai. Sanda wayar ta daidaita sai ya fara yunqurin kiranta,saidai a duk sanda zai kirata din sai computer ta datse kiran ba tare da an masa bayanin komai daga danganci network ne babu a area din da take?,ko kuma wayarce dungurun gum a kashe?. Ci gaba yayi da gwada kiran babu qaqqautawa,har sai daya sare,energy dinsa yayi qasa,ya tabbatar bazai cimmata a waya ba. "Sai kayi tattaki ka sameta a inda take" Wannan shawarar ta sakashi zabura ya miqe,ya zura takalman qafarsa a gaggauce,saidai yana daukan key din motarsa komai ya tsaya masa cak "A ina take?,a ina kuma zaka sameta din?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar data kusa tsaida numfashinsa "Na shiga uku" Ya fada yana jin dukka jikinsa yana rawa "Bansanta ba,bansan komai a kanta ba" Ya fadawa kansa da kansa idanunsa suna tara hawayen da babu makawa sai da suka yiwa kansu qofa "Garin ya akayi haka?" Ya sake tuhumar kansa da kansa,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna a wajen. Yafi qarfin awa biyu zaune ya kasa hasalawa kansa komai,kafin daga baya wata zuciyar ta bashi wata guntuwar shawarar data dan bashi nutsuwa kadan,har ya iya miqewa ya gyara rigar jikinsa ya maida hularsa ya lalubi qofar fita. Dukkan wani muhalli da yasan sun taba haduwa,cin abinci,shan ice cream,shopping da sauransu ba wanda baije ba. Saidai duk inda yaje din dogon bayani ne maras fa'ida ko kuma alfanu,domin ba wanda ya ganeta. Abinda bai sani ba shine......ita din tamkar tarwada take a cikin ruwa......tana da matuqar santsi da idan taje waje zai wahala ka sake samunta a nan... Muddin taje waje dakai sau daya ta kansile wajen kwata kwata cikin jadawalin rayuwarta,ba guri bane da take mu'amalantarsa ba a koda yaushe ballanta fuskarta ta zama sanniya a wajen mutanen dake yawan xiyartar wajen ko kuma ma'aikatansu ba. Tun yana zagayawa da qarfin gwiwarsa har ya sare. Zuwa sannan yanajin zai haukace ne idan bai gayawa kowa halin da yake ciki ba,don haka yana isa Bristol baiko koma dakinsa ba ya kira mato a waya. Tazarar minti ashirin kacal ya iso,ya shigo dakin yana cewa "Kai matsala ne dakai,wani lokacin sai ayita faman kiranka baka dagawa,tun jiya nake danna maka kira kaqi dagawa......gobe ne za'a zauna cacar nan fa......" "Shut up mato!" Ya dakawa mato din tsawa,don maganarsa a sannan daidai take da yana buga masa abu me qara a kunne. "Lafiya uban gidana?,me kuma ya faru?" "Mato na hadu da 'yar damfara......na hadu da gagarumar barauniyar data yasheni tas......bama ni ta yasheba tukunna......ta taba dukiyar kamfanin jadda ne!". Zaro idanu mato din yayi waje yana janye jikinsa baya da sauri kaman yaga wani abun tsoro tattare da mika'il din "Anya yau bakasha barasar da kanka baya dauka ba?,kasan maganganun da kakeyi?,barauniya fa kace,kuma macace?,sannan data tashi dukiyar Muhammed jadda ta kwashe?" Ya qarasa maganar kaman zaiyi ruku'u. Ba kuma ruku'u din zaiyi ba,kawai yayi hakanne don ya samu damar ganin fuskar mika'il dake zaune sosai,yanason kuma samun tabbacin maganar haka take ko kuma akasinta. "Duk yadda kaji ka sake kuma fada hakanne" Ya fada a galabaice yana tsananta fatan samun mafita daga wajen mato. Ga mamakinsa sai yaga mato ya juya yana neman hanyar fita daga dakin. Da wani irin hanzari mikail ya miqe ya damqo rigarsa yayi qarfin halin jawoshi baya sannan yasha gabansa "Ina zakaje kuma?" Kicin kicin yayi da fuska "Ka dauko bala'in da yafi qarfinka ai me gida,ni kuma bani da wani gatan da zan iya tareshi,kaga gwara na yiwa kaina qiyamulallaili nasan nayi". Sakinsa mikail yayi har yana taga taga kaman zai fadi. Cikin fusata da fushi yake duban mato,yayi taku biyu a gabansa sannan ya tsaya yana sake kallonsa *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 78 "Kai butulu......na dade da sanin alaqar bariki bata da riba.....kuma bata wanyewa lafiya qalau.....amma inaso ka sani.....ni mikail baka isa ka gwadamin wannan halin ba saboda yadda kaci a jikina,komai ka zama ta silata ne.....to ga hanya nan......kana iya tafiya......amma ka sani,wallahi.....wallahi duk abinda zan shiga zan bada sunanka da tabbacin tare mukayi komai". Ji mato din yayi kaman ya debo qarfe ya jibga masa saman kanshi,sai ya koma ya sulale ya zauna "Ya zakayimin haka oga?,kasan tun safe naga qishin qishin abun?,ya baza jaridu da jafafen yada labarai?,amma ban taba tunanin kaine a ciki dumu dumu ba?" "Mune dai a ciki,kuma zanyi maka haka muddin kaima kayimin hakan". Ya bashi amsa kai tsaye yana duban tsakiyar idonsa. Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana yin collapse. Nadama da dana sanin taba sanin mikail a rayuwarshi tana sauko masa. Shikam ina zai iya tarar case da Muhammed jadda?,wanne ganganci ne ma zaiyi saken da koda sunansa zai shiga list na sahun wadanda ake tuhuma. Shuru yaci gaba da wanzuwa a dakin tamkar dukkaninsu ba xasu sake magana ba kafin mato ya magantu "Ita yarinyar wacece ita?,zaifi kyau kabi sawayenta ka bincikota ka damqawa jadda ita a sauqaqe su tuhumeta". Wani banzan kallo ya watsawa mato "Inda nasan ita din wace da ta yaya ma zan batawa kaina lokaci ina neman shawarar butulu irinka?......tun haduwata da yarinyar na karanci tasha banban da sauran yammata dama mata gaba daya.....tun daga yanayin kyau siffa da kuma jan ajinta......bata sake shallake tunani ba sai a yau dana karade dukkan guraren da muka saba haduwa ko na saba ganinta amma na kasa zaqulota,......ta shafe dukkan wani footprint nata,bani da sauran hanyar da zan iya lalubota". Shuru mato yayi abun yana tsimashi shima. Duk iya yawan duniyarsa bai taba cin karo da abun mamaki irin wannan ba.......duk budewar idanunsa da kuma son duniyarsa baiga gangancin da zai sanyashi tunkarar fada ko jayayya da mutum irin muhammad jadda ba.....hakan daidai yake da saida rai.....daidai yake kuma da Rungumar mayunwacin zaki. Amma irin wadannan maquden kudaden kuma ace diya mace ce ta diba?. "Me afkuwa ta afku yallabai.......yanzu lokaci ya qure ya kuma matse da zaka tsaya nemanta da bayyanar da gaskiyarka.....don koda ka samota dinma ka gabatar musu da ita to ba shakka dole saika rasa aikinka.....na tabbatar zasu sallameka ne". Wannan maganar ta mato ta sanya gumi tsatstsafowa mika'il. Ya koma baya yana zama sosai tare da kamo habar rigarsa yana sharce gumin goshinsa. "Don ubanka mafita nace ka bani bawai ka dinga haskomin makomata ba" Ya fadi da mugun tsaron ci gaba da jin sautin xai rasa gurbin aiki da kamfanin jadda diamond rashi na har abada,bayan a nasa mafarkin yana hangoshi ne wataran a kujerar CEO din ma gaba daya yana juya nasa kamfanin diamond din. "Mafita kam na samota......amma sai idan ka amince.......zaka juya hankalin kowa kayi wasa dashi.......ka kuma binne batun kwashe kudin asusu ba tare da kowa ya fahimta ba". Kaman an watsa masa ruwan sanyi haka yaji rahama tana sauka a zuciyarsa,baisan sanda ya kama hannun mato ya riqe qam qam ba abinda bai taba yi ba tsakaninsu "Dama za'a samu irin wannan hanyar na kasa yarda da ita mato?,maza gayamin......gayamin don Allah". Hannunsa ya zame yana mamakin yadda yau masifa da bala'i suka sanya ubangidan nasa zama maqasqanci a gabansa. "Caca......a caca ne kawai zaka ciyo maquden kudaden da zaka iya cike babban gurbin da zai sauke fushin me jadda daga kaso dari zuwa ashirin". Ido ya zubawa mato alamun me gama Fahimtarsa ba. "Nasan baka gane ba ko?,me gida......kana da nasibin da muddin ka zauna teburin caca saidai ka kwashe badai a kwashe ka ba,tunda kake baka taba zama teburin caca an cinye ka ba tsahon shekarun daka dauka,saidai ma ka tashi da gwagwabar ribar dake lunka arziqinka.......wannan zaman da za'ayi a gobe babban zama ne......akwai manyan gidadawan masu kudin da basu gama wayewa a sabgarba.....basu kaika qwarewa ba,sun sanya mugayen kudade masu nauyi cikin cacar saboda romon bakan shigowarka cikinta da nayi musu da yawan kudade masu nauyin gaske.......kudin da kowanne zai zuba ba qarami bane me gida......kuma ina da tabbacin kaine zakayi nasarar wawashesu......ka zuba kudade sosai ka saki jiki don ka sarqafo dukkan abinda zasu zuba.....bana jinka.....nasan da qwarewarka.....na kuma yarda dakai". "Nima na yarda da kaina" Ya fadi kai tsaye cikin confidence da kuma yarda da cewa lallai ba shakka waraka tazo. Rungume mato yayi yana jin tsananin farinciki kafin ya sakeshi yana cewa. "Muddin muka gama da wannan,na rantse da sarki Allah saina nemo yarinyar nan......saina nuna mata cewa ita din ba komai bace cikin duniyar bariki,sai na bar mata tarihi,saina sanyata tayi danasanin zuwanta duniya!!". Tunda gari ya waye yake kwance kawai lamo,ita bame bacci ba hakanan ita ba idanunta biyu ba. Su biyu ne a dakin tun bayan wucewar nadra da haneefa makaranta,tana daga parlor huda na cikin uwar dakin qudundune a bargo da sunan bata da lafiya ba zata samu daman zuwa makaranta. Ta shirya hakanne don tana sanya ran sabreen din zata fita ta barta a dakin kamar jiya,tasha hirar soyayya da hameed dinta,wanda a yanzu duk duniya bata jin akwai sauti ko muryar da takai tasa dadi da daraja. Amma ga sabanin mamakinta yadda taga sabreen din kwance yana gaya matane ba lallai bane ta fita ba yau din. Tayi tsaki cikin bargon yafi a qirga,tayi juyi daga hagu zuwa dama sau ba adadi. Tana iya ganin yadda wayarta dake qasan filo keta haske alamun kiran hameed wato naseer ne yake shigowa amma tsoro ya hanata dagawa. A hankali a hankali ta dinga jin duk wata juriya tata tana qarewa,muradinta da burinta kawai shine yadda zata samu taji muryar hameed dinta. Sannu a hankali ta dinga jin hirarsu ta jiya tana dawowa _akan sonki bana tsoron kowa,zan kuma iya komai a gaban kowa saboda ke....zan iya sadaukar da komai a kanki,zan kuma iya rabuwa da kowa,kefa?,zaki iya?,ki gwadamin wataran_. Kalaman Hameed kenan ko yaushe a kanta. Muddin zai sadaukar har haka ita me zaya hanata ta sadaukar?. Tambayar data yiwa kanta kenan,abinda kuma ya cire sauran dan tsoron dake ranta ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta. Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sakar mata kamar qaramin yaro "Har na fidda rai.....huda kina azabtar dani,kullum kafin na samu jinki sai nasha baqar wuya?,sai na shafe awanni ina lalubenki?,bayan ni ko agaban waye bana iya wofantar dake huda?,koda waye a wajen zan ambaceki zan kuma yi waya dake.....me yasa huda ni bazakimin wannan sadaukarwar ba?". Yadda yayi maganar sai ya bata tausayi sosai,harma taji tana zargin kanta daqin daga wayar tasa tun dazu "Allah huda idan aka wayi gari na mutu sonki ne ya kasheni" Duk wata tsiga ta jikinta sai data zuba......son da yake mata wai da gaske ne har yakai haka?. "Kina mamaki kuma kina musu ko?,kinason tabbatarwa?" Cike da quruciya da rashin sanin kan rayuwa ta furta masa "Eh" "Nan da kwana uku xan dawo ya kama ranar Monday,zaki yarda na shigo makaranta na daukeki?.....zan kaiki inda zan nuna miki zallar soyayyata a gareki ki ganta quru quru.....kin yarda kinaso ki gani tawan?". Sai ta narke wuya zuciyarta na karkata gason ta gani din. Can qasan ranta kuma fal mamaki,tadai kusa ganin wannan soyayyar da yaketa faman zuguiguita mata ita......ta kusa ganin soyayyar nan dai da takeji anata magana a kanta. "Zan miki tanadi na musamman,zaki gani da idanunki.....daga ranar nasan ba zaki sake musu shakka ko kokwanto ba". Janta yayi zuwa cikin hirar sosai duk da sama sama take amsa masa a darare amma hakan bai dameshi ba,sake jan ra'ayinta kawai yakeyi,yana kuma sake dulmiyata cikin kogin qaunarsa. Kadan kadan takejin motsi daga dakin,to amma sai kunnuwanta sukafi tafiya zuwa tsakar gidan gidan nasu. Don ta tabbatar huda bacci takeyi ko sanda ta fito,ta share wannan maganar tana dauko wayarta ta lalubi number jib. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 79 "Allah dai yaja kwana hajjaju......our young hajiya" Jib din ya fadi cikin fara'a. Karamin tsaki taja tana kauda zancan,haka kawai ita batajin komai akan kudin,bata kuma jin wata walwala. Duk wani tsari da jib din yakeyi mata tana jinsa ne kawai,don nata lissafin duka ba'a wannan bangaren yake ba. Uwa uba shi Kansa jib din bataji ya tsarawa kansa komai ba,ita kuma yanzu su dinne a gabanta da sauran yara marayun nan da take kwana dasu ta kuma tashi dasu cikin ranta. "Ka sameni gidan marayun nan,zamu qaraso nida busari" Ta bashi saqon a taqaice "Okay to ba damuwa.....amma ke me kika warewa kanki?" "JIB....ajiye maganarnan haka a gefe,kada kabarmu mu jiraka please" "In sha Allah" Ya fada mamakin halayenta suna sake ninkuwa a ranshi. Kafin ta ajiye wayar tahau ta daya sim din data saba neman busari,ta tura masa saqo sannan ta ajiye wayar tana dan furzar da iska daga bakinta gami da zubawa labulen qofar falon idanu kamar me nazari akan yadda aka sarrafashi. Kadan kadan ta dinga jin kamar dai motsinne daga dakin da kaman sautin murya a can qasa. Tun tana basarwa har ta miqe,ta taka a hankali ta soma nufar dakin. "Eh" Kalmar da aka fadi qasa qasa ta shiga kunnenta sanda ta yaye labulen dakin. Hasken daya ratso falon zuwa uwar dakin ya ratsa blanket din da take ciki ya kuma alamta mata wanzuwar wani a dakin,sai tayi wata mutuwar kwance zuciyarta tana tsananta bugawa ta latse wayar tana turata tsakanin katifar da bagon gadon. Daqyar take iya hadiyar yawu saboda tsoro,tun yaushe nema aka shigo bata sani ba,kada dai ace ta jima a tsaye tana jinta?,wannan tunanin kadai ya sanya jikinta jiqewa da gumi kamar an watsa mata ruwa. Hannu ta sanya ta yaye bargon,sai ta runtse idanunta "Keda waye kike magana?" Sabreen ta jefa mata tambayar tana zube mata idanun nan nata masu kaifi. "Magana kikaji yaa sabreen?" Shuru tayi dajin tambayar datai matan,sai ta girgiza kai alamun aah bayan ta gama qare mata kallo "Wannan gumin fa?,ko zazzabi kikayi ya sauka?" Ta sake jefa mata tambayar amma wannan karon da salon son kamo abun farauta "Eh.....eh nima haka naji" Idanunta ta maida ta lumshesu sannan ta bude. Ta gama bata hint,ta kuma gama hada dukkan wasu abu da takeso,ta sanyata a ajujuwa kuwa tun daga sauyawarta zuwa yau,kuma ta fadi a kowanne aji......tana jin sunzo matakin qarshe ita da ita,sai ta sake mata blanket din,ta juya tana takawa a nutse zuwa inda take adana kayan wankanta ta diba tana fita a dakin. Da wani malalacin kallon ta bita har ta gama ficewa,haka kawai taji kaman akwai wani abu ba daidai ba "Idan ma akwai.....idanma kuma ta gane aiba wan sabon Allahn kikayi ba" Wannan tunanin ya bata qwarin gwiwa ta tabe baki,ta maida kanta filo tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai,daga bisani kuma ta koma tunanin hirarrakinsu da hameed kaman yadda ta saba. Cikin qanqanin lokaci suka isa babban gidan kula da marayu,wanda yana cikin gidajen da suke karban kaso mafi tsoka daga dukkan abinda ta samu. A yau din kabakin arziqin data kai musu ya faranta ran kowa. Hakanan list da tayi na abubuwan da zata aiwatar musun ya sanya kowa kokwanton anya da gaske take?. A duka shekarunta ina taga adadin wadannan kudaden?. Ayyuka ne da zasu canza fasalin gidan gaba daya ya canza cimarsu harma karatun yaran gidan. Tsari ne kuma data dauki sunayen 'yammatan ciki da suka isa aure suke da buqatar tallafin kayan daki da kayan kitchen harma da suturar fitar biki. A ranar gaba daya gidan a yamutse yake da tsananin mamakin ayyukan da tace zatayi din. Saidai daga bisani shigaban gidan ya basu nutsuwa ta hanyar fadin "Ta iya yiwuwa 'yar wani hamshaqin attajirin ce mu bamu sani ba ta bad da sawu,ko daga suturar jikinta da fatarta zakasan cewa kaman hakan zai yuwu,kudai godewa Allah daya turo me dauke mana damuwarmu koda yaushe,gashi a wannan karon bayan tallafin data saba bayarwa zata mana aikin da mutanen dake da ikon yi masu yawan gaske suka gaza yi mana......zata mana aikin dana tabbata muddin ya tabbata matsalolinmu masu yawa zasu kauce". Ta yita share qwalla me yawa a hanyar komawa gida,yaran suna mata gizo cikin idanuwanta. Wato maraya a wannan zamanin daidai yake da wani abu maras alfanu cikin al'umma muddin ba dukiya aka mutu aka bar masa ba?,hankula da idanuwan al'umma duka sun toshe?,me arziqi shine mutum?,me arziqi shike da amfani?,idan yau kana da abun hannu kowa qoqarin rabarka yakeyi?,kowa so yake ya hada dangantaka dakai komai qanqantarta?,kowa so yake ace kuna da alaqa kunsan juna?. Anya mutane a yau kuwa sunsan iya adadin bala'i da masifar zubar ruwan hawaye a idanun maraya qwalli daya tak a garesu?,anya suna tunawa da girman haqqinsa da ma'aiki yayi gargadi da jan kunne akai?. Bibo ta fado mata a rai,saita dinga juya kai kawai,matar tana daya daga cikin mutanen da zasu azabtar dasu tsananin azaba inda Allah ya qaddari mutuwa ta dauke ummeensu a sanda suke dukkaninsu qananu......arrahmanu arraheem ubangiji da baya hadawa bawa abu biyu......sai ya dauke musu sanyin idaniyarsu a sanda ita nata hankalin da qarfin ya fara kawowa. Ya sanya mata qarfin zuciya da kuma qarfin halin iya tare musu tashin hankali da masifa komai girmanta,ya sanya rainonsu da kulawa dasu a hannunta tun bata wuce itama a raineta ba. (YAKE BAIWAR ALLAH!....tabbas riqo yana da wahala.....riqo yana da daci yana da nauyi,amma kisani......DA KI RIQE YARO KI AZABTAR DASHI GWARA KI TUN FARKO KICE BA ZAKI KARBA RIQON BA yafi miki sauqi da mafita har a wajen Allah muddin kikasan zuciyarki ba zata iya jure da kiyaye wannan amanar ba.....AMMA WALLAHI WALLAHI WALLAHI kikayi kuskure kika karbi riqo don ki burge ko kada a zargeki,to wallahi idan nace KINA CIKIN MASIFA ma kadan ne.....ba zaki san girman bala'i da kike ciki ba sai ranar gobe qiyama......hatta ubangiji bayason kuka maraya shi da yayi kowa yayi komai ya kuma qaddara hukuncin maraici a kansa IDAN KINSAN akwai maraya yanzu haka da kike banbanta riqonsa dana 'ya'yanki.....to ki gaggauta yiwa kanki hisabi tun kafin ranar zuwan hisabin na gaske.......idan har kinsan akwai maraya yanzu haka a hannunki.....to ki gaggauta gyarawa kafin ki barwa 'ya'yanki masifa da bala'in da zaiyita bibiyar rayuwarsu,kiyi qoqari kifi qarfin wannan tsokar dake qirjinki wadda ake kira da ZUCIYA.....kiyi qoqari kifin qarfin wannan maqiyin naki wato SHAIDAN.....Allah ya bamu ikon fin qarfin wadannan ababe guda biyu ameen summa ameen). "Kaini gidan malam" Ta fadiwa busari a nutse,wanda bai musa ko ya tambayi ba'asi ba ya karkata akalar motar. Zuciyarsa shima cike take da farinciki,don yana cikin alherin tashi daga dan adadaita sahu,zuwa mamallakin shago sukutum da guda a babbar kasuwar kantin kwari nan da sati uku kacal. Kusan duk wanda ya kwana ya tashi a kamfanin yasan da faruwar komai. Yayin da sake fitar labarin boyayyar badaqalar data afku qasa da wasu awanni ya sake sanya mutane da yawa na kamfanin mamaki musamman wadanda basu san komai ba,basusan kuma abinda ake ciki ba. Kowa da kansa da kansa ya yiwa hisabi,don shigowar boss Muhammad kamfanin ya sake sanya kowa shiga taitayinsa. Masu zuba kunnen abinda zai faru da kalar matakin da zai dauka suka ci gaba da sanyawa,yayin da a nasa bangaren ya nutsa cikin bincike tare da tattaunawa da taimakon dan uwansa kuma shaqiqinsa farouq. Ganawa ce takai tsaye kuma da mutum na farko bayan shigarsa kamfanin da sukayi da manager din banking da yake mu'amala dashi,wanda suka iso su uku da biyu cikin nasu ma'aikatan. Hankalinsu kusan yafi na fuad tashi,don sun sani ba qaramar nasara bace ace kamfani kamar wannan yana da asusu dasu,hakanan kuma....gagarumar asara da faduwa ce ace a yau ya rufe account dinsa dasu sanadiyyar wannan. "Baku da laifi sir......coz kusan sai aka shigar da komai da ake buqata da zai bawa mutum damar accessing da account din sannan kuka bada damar fitar kudin......inda kuskuren yake shine......amount din da aka fidda din ya cancanci ace anyi alerting namu kafin a bada daman fiddashin.....saboda akwai hanyoyin da mukebi wajen fidda kudade masu nauyi irin haka........kuma kun san da hakan......anyway...sakacin security team namu yafi na kowa.......sai kuma ma'ajij company da yake number one" Ya qarashe maganar yana komawa ya zauna sosai yana gyara wuyan suit nashi. Matsowa sadiq yayi dab dashi a nutse ya rada mishi "Hamma......mun gaza samun mikail har yanzu mu shaida masa zaman da za'a yi yau din". Kansa ya gyada "Kar damu dashi......idan inason ganinsa ko ina ya shiga zan sanya ne a kawomin shi.......but nafison ya kawo kansa da kansa in a legal way.....ka rabu da nemansa" "Okay" Ya fadi cikin gamsuwa. Ya yadda da hamman nasa,ya sani ba ordinary mutum bane tuntuntuni......bayajin a yanzu ko farouq zai gaya masa wayeshi saboda kaf gidan yafi kowa kasancewa dashi cikin awanni masu yawa. Fara aiki dashi ya sanya kullum kwanan duniya yake sake shiga ransa. Baisan haka hamman nasa yake da shiga rai ba sai yanzu......baisan haka kyakkyawar mu'amala take yawo a jininsa ba sai yanxu da aiki yake hadasu adadin awanni masu yawa. Hannu ya miqa ya karba file din da suka iso masa dashi na dukka bincike da nasu bibiyar da sukayi. Kusan wasu guraren abubuwan da suka bincika yazo daidai da nasa,wani gurin kuma sun kasa accessing information din jibril wanda shi a yanzu haka yana da komai. Abu daya ya kasa yarda dashi shine......jibril bashi kadai yayi wannan aikin ba.....dole akwai wani a tare dashi......wanin kuma yana qarfafa zargin muddin ba mikail bane da kanshi ya dauki duka information din ya miqa musu da zummar cin amana ba......to na jikin mikail ne wanda yake tare dashi. Hannu ya bawa manager din sukayi musabaha "Mr Joshua mamallakin bankin yana miqa jajensa......yanzu haka yana hanyar zuwa kowanne lokaci,da fatan zaa karbi baquncinsa". Wani abu me kama da murmushi kawai yayi yadan dage kafadarsa,sukayi sallama dashi ya fice. Iska me zafi ya fitar a bakinsa,ya miqe yana zare suit din jikinsa na saman ya ratayeta a muhallin da aka tanada don ratayewar. Ya duqa yana zare takalmin qafarsa hadi da magana da saddiq "Awa nawa ya rage mu shiga meeting?" "Thirty minutes hamma" "Good......yanzun security team kawai nakeson gani,kayi cancel sauran staffs......infact ma banason susan da zaman.......ina da buqatar binciken sirri a kansu don dole mu nemo me fidda mana information......ka gayawa me sunan malam immediately after meeting inason ganinsa" *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 80 "Done" Ya fada kaman yadda ya saba. Daga kai farouq yayi ya kalli saddiq din "Kalleshi kaman mutumin kirki........ya addabemu cikin gida......sai yazo company sai ya zama wani me biyayya.....thank god da Allah ya hadaka da fu'ad......da nine da tuni ka kusa sakamin hawan ruwa" Ya qarashe maganar yana daukan gorar ruwan da fu'ad ya dauko musu saman table yana mamakin yadda qananun hidima na cikin office yake yi da kansa,duk da cewa yana da qarfin ikon da ko taka qasa yace bazaiyi ba akwai masu yi masa. "Bakasan mutane da yawa da suka fiya wasa ba suna da wani boyayyen talent?". "Talent a wajen wa wai?,wannan?,kawai dai Allah ya tattaro mana shi da taimakonka" Ya fadi yana bude murfin ruwan. Bai amsa ba fu'ad,yadai saki siririn murmushin da ba lallai ka iya fahimtarsa ba yayi bismillah can qasa ya soma zuqa a hankali. Kafin yakai ga dire cup din kira ya ratso wayarsa,saddiq yafi kusa da ita don haka yace "Hamma amna ce" "Kai dauki kace mata lokacin aiki ne yanzun" Kai fu'ad ya girgiza da sauri yana aje ruwan. Wayar ya miqa masa,ya sake duba kiran sannan ya daga "Good morning hamma" "Mornin lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki "Hamma ka tashi lafiya?,yau ka fita early kuma anni tace baka tambayeni bama" Ta qarashe fada da shagwabar nan tata data zame mata jiki. Murmushi ya saki "Ban tambayeki ba amma kina raina amna.....wani muhimmin abune ya taso.....kiyimin addua,ki gayawa anni ma idan tazo sallan dhuha tayimin addu'a.....but karkice mata wani abu ne ya taso,just kice munyi waya nace tayimin addu'a during salat of dhuha". "In sha Allah hamma.....Allah ya kula ya tallafa" Ta fada cikin kulawa "Ameen autan anni" Murmushin jin dadin sunan ta saki "Hala rival dina baya kusa hamma......yaji da kunnensa sunan dai nawa ne" "Karki bari na dawo gida na iskeki....." Saddiq dake gefan fu'ad ya fadi da sauri. Kai ya daga fu'ad din ya jefa masa harara "A gaba na?" "Sorry sir" Ya fadi yana shafa kansa. Abun ya yiwa amna dadi,yana iya jiyo qaramar dariyarta har ya katse kiran. "Baka hasko komai game da mikail ba?" Farouq ya jefa masa tambayar sanda yake qoqarin duba wani saqo daya shigo system din nasa daga department na wanke dukka diamond din da aka haqo don tabbatar da kyansa da ingancinsa. Fararen idanunsa kewayayyu da hasken system din ya qara haskewa ya daga ya dubeshi na wasu sakanni sannan yace "Kai me ka hango?". "Guy din bashi d gaskiya kwata kwata.....and ina kyautata zaton yana da masaniya akan komai koda bada saninsa akayi ba". "Na fahimci haka......but akwai wani abu ko wani behind him....." "It's true.....ni tun tafiyarka South Korea na karanci abubuwa masu yawa game dashi,bamu samu zama bane yadda naso har wannan abun ya faru......amma bari mu fita a meeting dinnan" "Yayi" Ya amsa masa yana duba lokaci. Wata irin zazzafar tattaunawa ce ta wanzu tsakaninsa duk wani dake under security team. Jiki da zukata sunyi laqwas da wani irin tsoro da kuma firgici. Bacin ran da suka gani a fuskar boos din nasu ya sanyasu cikin tashin hankali,domin kuwa wani abune da basu taba ganinsa a tattare dashi ba. Dukka bayanan da suka bashi kusan yazo iri daya akan nasa da wanda baki suka bashi,saidai akwai wasu sauye sauye cikin nasu "Na baku 2days to find full details na dukka team din da sukayi wannan aikin......na tabbatar ba aikin mutum daya qwal bane......team work ne tabbas!" Ya fadi yana doka file din saman table din da yake kai. Zuciya da qwaqwalwarsa duka a zafafe ya dawo office,yayi nufin yin alwala don yayi salat dhuha kaman yadda ya saba sai yaga lokaci ma duka ya qwace,duk da haka bai fasa daura alwalar ba saboda ita kadai tana saka masa sanyi cikin zuciyarsa "I need rest please.....duk meson ganina ka gaya masa sai after one hour......kayi shutting komai saina nemeku" Yayi magana da mutanen dake tare dashi. Da daya da daya kowa ya fice har saddiq. Farouq ya miqe a hankali "Ina zaka kai kuma?" "Zan bar CEO ya huta haka nan......da gaske brain dinka yana buqatan shuru na wasu lokuta". "Ko zan huta da ganin kowa banda kai farouq" Ya amsa masa yana jingine bayansa jikin sofan da ya canza mata siffa daga kujera ta koma qaramin gadon hutawa cikin sakan talatin. Murmushi farouq ya saki,sai ya kalli agogonsa sannan yace "Na sani.....but now dai dole farouq yadan matsa kadan Shima.....zanje nayi waya da fanna......yau duka ban kira naji lafiyarta ba". Kiran sunan fanna kawai da yayi ya sanya ya daga masa hannu ba tare da yace masa komai ba,sai ya sake sakin qaramar dariya yana takawa "Anyi zancan SOYAYYA zaka birkice.....bari na qara matsawa da hanzari......hala daya cikin matan naka ne ma zasu kawo maka ziyara". Yayi zancan yana kaiwa qofa. Maganarsa ta sanya fu'ad sakin murmushin dole duk da bai shirya ba,sai ya bude idonsa a hankali yana bin bayan farouq da kallo har ya qarasa ficewa,ya maida idon ya rufe bayan ya saita security na qofan nasa da wani qaramin remote a gefansa ta yadda babu me iya damunsa,duk da ya bada warning ma reception nasa da kuma saddiq. Shi a wannan ire iren situation dinma idan har yace soyayyar zaiyi baisan ta yadda zai fuskanceta ba.....baisan ma ta inda zai kwasota ba. Yasha ji daga bakin farouq rashin bada kulawa da bada lokaci yana kawo macewar soyayya.....shi kam ya tabbatar wannan shine dalili na farko da zai saka tasa soyayyar mutuwa murus. Ya tuna 'yammata biyu da farouq ya takura ya hadasu.....abinda dukka ya rabasu dashi shine lack of caring. Sometimes ma mantawa yakeyi da babinsu,koda kuwa ta hanyar tura tex bare kira bare aje gayin tattaki zuwa gidajensu. Da kansu suka fahimta baida lokaci,suka kuma samawa kansu salama zancan ya mutu murus,shima suka shafa masa lafiya. A hankali kekenapep din ke gangarawa da ita layin gidan malam din,ya kuma tsaya daidai gidan. "Na gode......kana iya tafiya,gobe idan Allah ya kaimu zan nemeka saimu qarasa komai,ka gaida ummaah da kyau" "Zataji in sha Allah....tace zatayi tattaki da kanta don miki godiya". Murmushi kawai ta saki tana sauka daga napep din,idanunta kan muhallin da malam ke bada karatu. Ba jamaa wajen,ta kalli agogon hannunta,da sauran lokaci akan lokacin daya saba xama,sai ta taka a nutse tana wucewa cikin gidan. Kamar kullum ta taras da rumasa'u tana aikace aikacen gida,matar malam na daga rumfarta a zaune tana tsince busashen zogale. "Maraba da diyata" Ta fadi cikin fara'a da murmushi tana sauke farantin zogalen daga cinyarta gami da karkade zaninta da ya d'an baci da kadan. Har qasan zuciyarta kuma tana jin dadin dawowarta da wuri,ba kaman wancan karon ba data tafi ta jima bata waiwayosu ba. Itama tata fuskar da murmushi tare da jin dadin yadda aka samu wasu halittu da suka damu da rayuwarsu ta qarasa shiga cikin rumfar,bayan ta zame halfcover din qafarta "Aah.....ina sauran jikokin nawa?" Ta furta tana duban bayan sabreen. Murmushi ta saki tana zama saman shimfidaddiyar daddumar da matar malam din ta shimfide mata "Ba daga gida nake ba gwaggo" Ta fada Kaman yadda taji rumasa'u tana kiranta wani lokaci. "Kash.....to ai naso ganin kishiyata haneefa ne ai" Ta furta tana dariya tare da yunqurin miqewa "Itama kullum zancanta kenan.....amma zan kawosu na kusa in sha Allah" "To Allah ya yarda" Ta amsa mata tana bude fridge din dake ajiye a rumfar gaban falonta ta ciro mata ruwan pure water me matsakaicin sanyi da lemon zobo,rumasa'u ta hado da kofi ta shigo mata dashi. "Nima inata sanya ido naga huda" Ta fada tana murmushi. Kiran sunan hudan ma ya sanya hankalinta dawowa kan huda din data barosu gida. "Zasuzo in sha Allah rumasa'u" Ta amsa mata cikin kulawa. Zama tayi suna dan taba hira,tana son su sabreen yarinyar,wanda su kansu basusan dalili ba,saidai ba ruwan ubangiji shi yakan sanya qauna da jituwa tsakanin bayinsa a duk sanda yaso hakan ya kasance. "Hala malam baya nan?" Ta tambayi gwaggo "Yana nan,yadan fita ne kasuwa,amma da wuri yau din zai dawo,yana da karatun dare na manya da yakeyi". Kai ta jinjina,tana jin dole zata jirashi har ya dawo,duk da tanason komawa gida da wuri,don a yanzun hankalinta bai bata ta dinga nisan kiwo ba. Jikinta da zuciyarta sun gaza samun nutsuwa sam sam akan huda,cikin jikinta takejin akwai wani abu ba daidai ba. Iya yadda tayi magana da ita dazun kawai ya isa gaya mata akwai wani abu,saita rufe babin wannan tunanin tana maida hankalinta tsakar gida hadi da taya su gwaggo amsa sallamar malam din. *Tsaye yayi kawai gaban madubi yana duban fuskarsa da kyau tare da son bawa kansa qwarin gwiwa. Yana buqatar cikakkiyar nutsuwa da kuma qarin tattara dukkan wani tsohuwar fasaha da qwarewarsa wajen ganin ya cimma nasara a cacar. Tunda yake bai taba caca mafi hatsari ba irin wannan. Caca ce da zata iya zuwa masa da sakamako guda biyu......nasara wadda zata wankeshi daga dukkan wani rudani da tashin hankali.....ko kuma faduwa wadda daidai take da daukan guduma ta kuma tarwatsa rayuwarsa gaba daya. Hasashen sunan faduwa kawai sanyawa zuciyarsa wani irin mugun bugu yakeyi,tuna sunan FADUWA kawai sai yaji kaman qirjinsa zai tarwatse,don haka a yanzu da yake tsaye gaban madubin ya daga murya don baiwa kansa da kansa tabbaci tare da qwarin gwiwa "Ba faduwa a hanyata,tabbas nike da nasara......ni zan cinye!" Ya fadi da wani irin qaraaji yana sake sanyawa ransa nasarar da gaske tasa ce. Qofar aka dan qwanqwasa,ko ba'ayi magana ba yasan waye,don haka ya waiwaya yana fadin "Gani nan,tayar da mota" Sai ya juya ya dauki waya da maqullansa ya fito. Baice da mato komai ba ya bude gaban motar ya shige,mato kuma ya bawa motar wuta,ya danna hon me gadi ya dage musu gate din suka fice. "Ina fatan yau baka shawu ba" Mato ya fada yana sake bawa motar wuta saman kwalta. Harara ya waiwaya ya maka masa kafin yace "Mahaukaci ne ni?,idan nasha ta yaya zan samu isa ga abinda nakeso?,......zan shawu iya shawuwa bayan mun dawo da talin himilin kudin da zan cike gibin asarata". Kai mato ya jinjina yana dan dukan steering " Inaji a jikina kam wannan nasarar tana hannuwanka......munkaila me da'ira?.....ka manta sunan naka ne?". Wata wawiyar dariya ya saki,sunan da mato ya tuna masa ya sake jinsa cikin alfahari......wani rubutaccen suna ne daya samoshi daga wajen abokan cacarsa. Muddin zai hau tebur din caca to ko kai waye ka zama nama,baisan iya adadin abinda ya tara ba da dukiyoyin al'umma shekara da shekaru,sai yau gashi dare daya wata qaqqarfar guguwa tanason yin gaba da tsohon arziqinsa?......inaaaa......ai bazaya bari ba,sai inda qarfinsa ya qare. Iya sunan da mato ya gaya masa ya sanya masa qarin karsashi tare da jin dokin isa wajen. "Ni kaina inaji a jikina lokacin nawa arziqin ya gabato,don gagarumar caca ce ina gaya maka me gida.......tsaffin 'yan caca za'a zuba wadanda suka sanya kudi masu ciwo......don Allah banda ganganci ina tsohon hannu zai kara da sabon jini?,yaro masanin dabaru da siddabarun kayar da mutum?" "Tsautsayi ne mato" Ya bashi amsa wani murmushi yana subuce masa,don nasararsa kawai yake hanga muraran. Tafiyar mintuna kadan suka isa gidan cacar,tun daga waje ya fahimci gidan a cike yake,abinda ya sake tabbatar masa da maganar mato. Ya fito a motar yana murmushi suka jera da mato zuwa ciki yana sake bashi bayani akan komai. "Amma me gida......nayi mamaki da me jadda bai nemeka ba". "Har gwara ya nemeni da wannan shurun da yayimin......shirunsa yana nufin komai mato......shi yasa nake bidar nasara a wannan karawar.......daga nan wajensa zankai kaina ayi a gama......bani da tabbacin a yanzun baida masaniyar inda nake.......tsaf yana sane da motsina duka zai iya yiwuwa". A mamakance mato ke duban mikail,tsoron girman izza da qarfin ikon Muhammed jadda tana sake saukar masa,saidai bai samu cewa komai ba suka qarasa ciki. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 81 Daga yadda yaga wajen ya sake amanna da maganganun mato din. Duba daya ya fahimci tabbas masu tsohon arziqi da kudin caca ne,kuma da alama a yau din kowa cikin buri yake,hakanan kowa yayi guzurin dukka wata dukiya da yake alfahari da ita. Saura kadan dariya ta fashe masa,don dukkaninsu shi a nasa idanun kallon gidadawa yake musu,kuma cinyayyu da zasu qare wasan cikin hasara da rashin nasara. Su biyu rak ke zaune daga wata kwana cikin farfajiyar wajen. Kawu kenan,wato kawu sama'ila shi da nasa aminin barau. Cikin nutsuwa da shegen kwanyar da yake dashi yake karance mikail da idanunshi sunkai kan kawo amma banda kan kawu din. A nutse yake karantar mukail,har zuwa sanda suka zauna da'irar da za'a zuba caca ta farko. "Me ka karanta ne sama'ila?,kayi shuru ko ka fasa ba zaka buga wasan ba?" Murmushi kawu ya saki yana tura hularsa gaba. "Tun bayan mutuwar yaya daya haramta min yin caca,ban qara zama gagarumar caca irin wannan ba.....inaji a jikina silar arziqina ne yazo.....bazan zauna ba har sai naga iya nashi takun......baka ruftawa wasa baka san yanayin hannun kowa ba" "To me ka fahimta sama'ila?" Barau ya sake tambaya idanunsa akan yadda wasan ya fara tafiya "Dan zamani ne fa wannan da zai kara da tsaffin 'yan wasa......gogagge ne kana kallonshi,kuma shima qwararre ne da irin tasa qwarewar,wanda idan kowa baiyi takatsantsan ba komai zai iya faruwa" "Shege sama'ila" Barau ya fada yana qyaqyacewa da dariya "Ka zuba ido kawai kayi kallo" Ya amsa masa yana maida hularsa daga gaban goshi zuwa qeya. A duk sanda yakeson samun nutsuwa ta qwaqwalwa da ruhi sararsa shine kwanciya,ya rufe idanunsa yayi kuma shuru a waje da muhallin da ba hayaniya ko kuma motsin kowa. Ko yanzun hakan yayi cikin office din,saidai qarar wayarsa ya sanyashi miqa hannu ya lalubota don yasan ring din na daban ya sakawa kiran don kirane da yake buqatarsa "Sir........yana gidan caca na green card" "Good" Ya fada a nutse yana bude idanunsa "Don't let him go.....ina buqatar information na wuninsa na yau gaba daya" "Yes sir" Ya furta cikin girmamawa. Wayar ya ajiye,sai ya miqe a nutse ya zauna ranshi na wani mahaukacin baci. Ga wani zargin ya sake shigo kasa akan mikail yanason kore uzurin da zuciyarsa keson bashi. Muddin ya kuskura bincike yazo masa caca yayi da kudinsa na halal tabbas!,zai nuna masa ainihin kalarsa......zai gane waye zahirin muhammad jadda. Dukiyar da aka tarata da gumin halak?,dukiyar da ake takatsantsan wajen jefa haram a ciki komai qanqantarsa?,kudin ruwa da ruba dukkaninsu haramtattu ne a cakudasu cikin dukiyarsa,amma yau din zanyi ganganci ko kuskuren zarar halalinsa ya jefa a qazantaccen guri irin wannan?. Tsam ya miqe,sai ya koma saman table dinsa ba tare daya sanya takalma a qafarsa,ya kunna system dinsa ya tattara hankalinsa akai. Karo na kusan goma barau ya kalli kawu sama'ila kaman yadda mato ke zaune yana murmushi daga gefan mikail yana kuma tayashi lissafin maquden kudade da dukiyar da yaketa cinyewa ta abokan bugunsa. "Sama'ila?,dama wannan shine hasashen naka?". Murmushi kawu ya saki yana karkacewa kaman abun ya masa dadi "Gaskiyar kenan barau.....amma barshi ya gama iya tasa dabarar......uwayensa na nan zuwa su koyar dashi darasi" Wata dariya barau ya saki bayan ya gama fahimtar abinda kawun yake nufi "Yanzu naji batu,amma ta yaya muna da kai zaka bari wannan jaririn yazo gidanmu ya cimu wasa?" Murmushi ya sake saki idanunsa akan mikail daidai sanda ya cinye alhaji wada miliyoyin kudi "Talala ce me kaman sake.....barshi ya gama karbarmin kudaden tukunna da gidajen" Dariya barau ya sake saki harda buga qafa. Cikin awa uku ya daurewa kowa jijiya a wajen. Cikin tumbatsa da izza mato ya miqe "Akwai wani sauran wanda zai kara da sarki?" Yayi shela yana ji a ransa sun gama da kowa,babu me sauran motsi. Shuru ne ya biyo baya,sai ya sake maimaita tambayar yana duban kowa d'ai d'ai "akwai" Barau ya fada da qarfin murya. Mato da mikail din duka suka waiwaya suna duban kawu dake qurya,sai suka dubi juna tsakanin mato din da mikail "Waye kenan a cikinku zai shiga?" Tsam kawu ya miqe yana nuna kansa "Nine" Ido suka hada sai suka bushe da dariya tsakanin mato da mikail "Qaraso mana dattijo....koda yake ba dattijo a nan......inajin akwai rabona a jikinka ne kaima.....ko giya ta kwana daya na sha da canjinka". Boyayyen dariya kawun ya saki,ya fara takowa zuwa wajen kowa ya zuba masa idanu yana mamakin qarfin halinsa,kamar ba'a gabansa aka cinye kowa ko ba amma shi zai jefa kansa?. "Dame zaka shiga?" Ya jefa masa tambayar a raine. Karkacewa yayi ya zaro wasu takardu yana dubansu. Takardun dake dauke da sunan alhaji aliyyu ahmad zaki......mahaifi ga sabreen..... Takardar dake matsayin mallakin magadan kuma marayan yaran da yayi Qundumbalar shiga cacar da ita,cikin jin cewa zata ciyo masa tarin maquden kudaden da zasu zame masa silar arziqinsa gaba daya. Saman teburin ya aza takardar yana kallon mikail,hannu ya sanya ya dauka ya duba ya karanta ya kuma tabbatar original ce wanda gidan ya haura miliyoyin kudi "Ashe.....kudinka baaba ai ya haura 'yan canji ma ai.......idan na samu nasarar cinye gidan nan ko?,rusheshi zanyi na maidashi gidan shaqatawa,ayita shigomin da 'yammatan unguwa ina hutawa dasu ina biyansu". Wani abu ne ya cakewa kawu a rai,ya tsani zina,ya tsani harkar neman matan banza,kaman yadda ya tsani shaye shaye,barshi kawai da cacarsa data zame masa masifa wanda dama tana da shiga jiki. Kai tsaye yaji tsantsar cin fuska ce ya tanadeta zaiyi musu wannan ya sake aza wutar qaimi a zuciyarsa,ya karkace kaman yadda yakanyi a yanayi irin wannan,ya kalli Mikhail da kyau "Idan dai har ya zama mallakin naka kana da wannan damar" Ya bashi amsar da wani irin kakkaifan kallon dake gaya masa kai tsaye na SAI NA BAKA DAMAR CINYE GIDAN SANNAN ZAKA AIKATA HAKAN. Izza da jin cewa zai samu nasara akan kawun ya sanyashi ninka abinda kawun ya zuba shima ya zuba cikin cacar aka fara buga wasan. Tashin farko kawun ya maido takardun gidan yayi tafiyar ruwa da kudaden da mikail ya zuba,abinda ya jawo hautsinewar wajen,hankula dukka suka komo wajen,aka fara yo dafifi,wadanda aka cinye suke alhini dukansu karsahinsu ya dawo,sai aka fara zuba sabon wasa. Da daya da daya ya dinga zuba abinda ya ciyo kawu sama'ila yana kwashewa. Duk abinda ya zuba kawun ya cinye shaidan zuciya da kuma mato saisu gaya masa ya sake zuba wani,zai iya yuwuwa ya samu nasarar dawo da abinda aka cinye masa a baya. Tafi tafi cikin qasa da awa biyu sai gashi yana tashi daga Mikhail me manyan kudi yana komawa asalin mikail dinsa kaman yadda ya shigo wajen. Cikar awa biyu cif komai ya qare!.kawu sama'ila ya wawushe duk wata kadara daya cinyo daga wajen wasu ya zuba!,ya koma tsurar yadda ya shigo musu a wajen!. Sowa ihu murna da tafi ya cika wajen,ainihin sunan kawu sama'ila na teburin ya soma dawowa bakunansu wato DA BANBANCI!. Kowacce tsiga ta jikin mikail zubawa takeyi. Idanunsa sun kada sunyi jazur,jijiyoyin kansa sun fito rada rada. Sosai yakejin ya muzanta,ya toxarta. Ta yaya zai bari wani qaramin alhaki tsohon daya bashi shekaru masu tazara ya kafa tarihi a kansa?,tarihin da muddin ya bari ya tabbatu a haka.....to ko shakka babu ya xubar da kimarsa da kwarjininsa a idanun abokan cacarsa dake bashi wani irin girma. Karon farko a rayuwarsa da wani yayi nasara a kansa,shi kuwa ta yaya zai bari haka ta tabbata?. "Ga wasu kudaden na zuba.....azo a sake zama!!" Ya furta da qarfi,sautin daya sanya wajen yin dif aka zuba masa ido. Da sauri mato ya kalleshi,ya kuma ja hannunsa da qarfi yana dubansa qasa qasa "Wanne kudi kuma ya rage maka indai ba motar da mukazo a ciki ba zaka saka?" "Qyaleni mato.....bakajin habaicin da suke yada min?,dole na aje musu tarihi,dole sunan mikail suma yaci gaba da wanzuwa a kunnuwansu da bakunansu da wajen cacarsu". "Wanne kudi ya rage maka?!" "Ragowar abinda aka bari a asusun jadda" Ya fada yana jin zuciyarsa ta qeqashe,kuma tabbas wannan kudin xai dawo da sauran kudin da duka narke,duk kuwa da yasan mugun gangancin dake cikin aikata haka. "Kada kayi haka!" Mato ya fadi a gigice. "Anma yi" Ya amsa masa ba fargaba ko shayi saboda ya bawa kansa tabbacin shine keda nasara. Wayarsa ya fidda yabi dukkan process yayi transfer kudin da suka rage zuwa account din wanda zai ajiye kudin,idan nasara tasa ce ta dawo masa,idan ta kubce kuma dukka kudi sun tabbata mallakar KAWU!. Daidai lokacin da akayi alerting mutum biyu fitar kudin,sai fuad dake zaune yana bibiyar komai ya lumshe ido yana sauke siririyar ajiyar zuciya,daidai sannan kuma kira ya shigo masa. Ko daya duba sai yaga daga department din da aka kira ya daga yana cewa "Just keep an eye on it,naga komai" Sai ya kife wayar yana maida dubansa ga allon system din yana qoqarin tracking account na wanda aka sanya kudin. *_TURQASHI....QAQA QARA QAQA,BAZANCE KOMAI BA😂😂.....amma akwai ZAZZAFAR TURKA TURKA FA.....MUJE ZUWA_* *HUGUMANKU CE* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* Page 82 A wannan karon......daga shi har kawu samaila sai da aka basu hutun mintuna ashirin,don kowannensu yayi iya shirin da zai qara yi. Magoya baya kuma jingima kawun ya samu,wanda kusan dukkansu suna murna ne da nasarar daya samu,don sun tabbatar cewa koda basu maida dukkan abinda Milakil yaci nasu ba,to tabbas kawun zai maida musu wasu abubuwa kasancewar shi din nasu ne. "Me gida......ka tsaya iya waccar asarar da kayi......kada kayi kuskuren sake yin wani ganganci......ka fini sanin waye muhammad jadda" "Sosai kuwa mato.....amma jikina yana bani nasarata tana tare dani wannan karon......bazan bari nayita asara ba" Ya amsawa mato cikin yanayin da yake alamtawa mato cewa mikail din yayi nisan da bazaiji kira ba. Cikar mintuna ashirin aka sake zama,zaman daya dauki sabon salo ya kuma dauki hankulan kowa dake wajen. Tsahon wasu mintuna ana fafatawa,inda daga qarshe komai yazo qarshe. Kawu samaila ya sake wawushe kudin,ya kuma bar mikail cikin wani irin yanayi tsakanin mutuwa da rayuwa. Dukka kururuwar murna da muryoyin abokan kawu samaila dake tashi a wajen baya iya fayyace komai. Abu daya kwanyarsa ke iya fahimta gami da maimaita masa "An qarasa cinye kudin jadda diamond resources,ba abinda yayi saura". Kowanne sashe na jikinsa ya dauki rawa da wani irin kalar tashin hankali mara misali. Yana jin komai ne tamkar yana mafarki.....yana ganin kamar xai farka ko zai tashi,yana ganin kamar ba haka bane har sai daya damqi hannun mato "Mato da gaske ne?,ko mafarki ne?" "Da gaske ne maigida......ai na gaya maka dama". Taga taga mikail din yayi zai fadi mato ya taroshi,jama'an dake kusa suka kuma karanci hakan suka kawo masa dauki ta hanyar tallafe masa mikail din suka zaunar dashi suna masa sannu "Kaima banda abinka oga ai kayi wauta.....hausawa sukace idan bakasan gari ba saurari daka......na tabbatar rashin sanin waye sama'ila ya sanyaka sakin jiki dashi kan teburin caca......amma ita dama yau gareka ne gobe ga dan uwanka,idan an sake wani zaman ta yiwu ka samu nasarar maido wani abun naka" "A wajen wa?......lallai garba ka manta waye sama'ila ne" Dan uwansa da suka kawo daukin tare ya fadi yana murmushin aikin gama ya gama. "Kaini gida mato.....mu fita daga nan" Mikhail ya fada kaman wanda ya hadu da ciwon makanta,don gaba daya sai yakejin wajen ya matse masa ainun,kai......kamar ma baya shaqar numfashi yadda ya kamata a wajen. Tsoro fargaba da mutuwar jiki suka saukarwa mato sanda ya tayar da motar da yake tunanin ita daya ce Allah ya mantar da Mikhail bai sanyata tsaiwa takarar na ciyo ko a cinyeni ba wato caca. Kuka rurus mikail ya fashe dashi. Yana ji har a cikin zuciyarsa bashi da wani sauran abinda ya rage masa,to wai shin idan baiyi kuka ba me zaiyi?. Yana hango kawai yadda zai qare sauran Rayuwarsa ne a gidan kaso......yana hango yadda me jadda zai qarasa murqusa Rayuwarsa bayan rasa dukkan wata dama daya fara jiyo qamshinta a baya. Ba shakka fateema ta cuceshi.......har a zuciyarsa yana jin inda zai iya ido hudu da ita a yanzu babu abinda zai hanashi hallakata. Sun dan dauki lokaci da malam suna hira tana ta juya yadda zata gaya masa batun tallafin data kawowa dalibansa da rabon jarin da takeson yiwa duk wanda ya isa munzali a cikinsu. Cikin kudaden tanaso ta yiwa malam din alherin kudaden da zasu taba rayuwarshi sosai. Sosai mutumin yake burgeta........namiji na farko baya ga mahaifinta da taji dabi'u da halayensa sun mata,namiji na farko da takeji nagartarsa ya mata......kuma namiji na farko da idan ta zauna suna magana dashi takejin kamar wani sashe na mahaifinta ne ya dawo duniya. Duba da yadda lokaci yake qara tafiya,ta tabbatar qanqanin lokaci ya rage ya fita don yin sallar magariba. Sai ta daure ta gyara zamanta. "Magana nazo muyi malam,saidai bansan yadda zaka karbi abun ba" Ta fadi kanta sunkuye a qasa. "To ina jinki mana aminatu.....lafiya dai ko?" Zamanta ta gyara tana jin nauyinsa da kuma kwarjininsa yana ratsata "Eh lafiya malam......akwai tallafi ne da wata qungiya ta sa kai ta kawo don a rabawa makarantun tsangayu..... To banyi qasa a gwiwa ba na sanya sunan makarantarka a ciki,don nasan akwai dalibai da qarfinsu ya kawo kuma suke da buqatar sana'a......hakanan kaima malam na saka naka sunan a ciki......an kuma dace sun bada kaso me tsoka" "Toooo.......ikon Allah" Ya fada a tsanake yana nazarin abun "To sannu da qoqari,Allah ya saka da alkhairi......to sudai yara ba za'a hana raba musu jari ba......saidai komai zai zama bisa tsari don kada su saka a gaba su cinye.......kuma tallafar Rayuwa ne don bakasan ta sanadin jarin abinda Allah ya hukunta wani zai zama ba......amma zaki raba musu da kanki......hakanan zaki rubuta da kanki......batun sunana da kika saka ni na yafe....na gode miki da dukka qoqarinki a kaina.......amma basai kin bani komai ba". Shuru gurin yayi,qasan ranta tana jin wani abu maras dadi. Har ga Allah malam uba ta daukeshi........tana masa kallo ne irin na d'a da uba......to amma kuma tasan halinsa,ba kasafai yake canza hukunci ko magana ba idan ya zartas "Lokaci yana gabatowa,zan fita na shaida musu su zama cikin shiri.....wanda kuma yasan baida sana'a kar ya shigo ciki" "Hakan ma yayi malam" Matar malam din ta amsa masa,sai ya dauki butarsa da rumasa'u ta cika masa da ruwa yana ficewa. Yammaci lokaci ne da kowanne ma'aikaci yayi handing over aikinsa na ranar......ya kuma tattara ya nasa ya nasa yayi guda ko kuma guraren da mutum keda ra'ayin zuwa. Company din yayi tsit.....don hatta da masu danyin late kafin subar office din a yau sun fice,ba kowa sai muhammad fuad......saddiq da musaddiq ke zaune saman sofa,jifa jifa yana daka kansa ya kalli muhammad fuad da yaketa aiki haiqan saman system tamkar a nan zasu kwana ko bashi da niyyar barin office din a yau. A hankali ya zare idonsa daga system din ya maida saman agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Mikhail ya fado masa a rai,sai ya jijjiga kai a hankali ya maida dubansa ga musaddiq. Idanu yadan zuba masa kadan yana jin tausayinsa yana saukar masa. Ya tabbatar a gajiye yake,kuma bashi da burin daya wuce ya wuce gida,saidai kuma komawarsa gidan a yanzu babban hadari ne ga lafiyarsa dama rayuwarsa. "Mu qarasa gidan malam muyi sallar magariba a can" Ya fada yana dan ture table din gabansa ya kuma miqe yana ware hannun rigar suit shirt dinsa daya nannade,sannna ya juya yana dauko suit din yana qoqarin maidawa. Suna hanya kadan kadan yana jin saddiq da musaddiq din suna hira abinsu jifa jifa.....yayin da shi kuma ya tattara nasa hankalin kan wayarsa yana rage saqonnin da bai samu dubawa ba. A zahirin gaskiya ya gaji,yana kuma buqatar hutawa ne daga gangar jikinsa har ma qwaqwalwarsa,to amma ya sani.....a cikin matsalolin dake cunkushe cikin kansa,muddin zai zauna na second biyar shuru tunanukane zasu addabeshi,wanda yayi imanin zasufi jigatashi fiye da gajiyar da yakeji yanzu haka a jikinsa. Kamar kowanne lokaci malam din bai taba karbar komai a hannunta ya eabawa daliban da kanshi ba,yau ma ita da manyan dalibansa ya bawa dama suka tattauna,ta kuma rarraba kudin da zata raba musun sannan aka tsimayi sauran wadanda basu kusa suka dawo aka soma hawa layin karbar tallafin. Har qananun cikinsu bata tsame ba,saidai kowanne tayi kudin girma girma,adadin na qananu daban,na manyan daban. Ita da rumasa'u suka fito zuwa rumfar gaban gidan malam din,rumasa'u na riqe da jakar tana miqo mata,ita kuma tana miqa musu. Duk wanda ya karba sai ya balbaleta da adduar data dinga sanyawa tana jin saukar wani irin sanyi cikin ranta,wannan ya qara mata qwarin gwiwa taci gaba da binsu da kudin daya bayan daya. Kaman yadda ya saba a kowanne lokaci ya sanya mota uku cikin motocin dame tsaron lafiyarsa tsaiwa su kuma jira fitowarsa daga ainihin bakin titin unguwar,motoci hudu harda tasa suka fara gangarawa zuwa ainihin layin gidan. Suna shiga yana ci gaba da duban tsari da yanayi da banbancin unguwanni da al'umma ke rayuwa a ciki. Unguwannin da suke buqatar tsari me yawa da kuma tallafi don samun daidaiton rayuwa. Kusan dukkan guard's dinsa har yanzu suna mamakin yadda yake zuwa unguwar lokaci lokaci. Ko tsoron lafiyarsa baya yi baya kuma duba girman matsayin da Allah ya bashi?. Saidai a nashi bangaren malam din tamkar wani jigo ne a rayuwarsa.......ya zame masa fitila me haska masa duhu.....domin shine mutumin daya shayar dashi ilimin addinin da a yanzu haka ya zamewa rayuwarsa haske da kuma garkuwa. Silalowar motocin da kuma nishin isowarsu wajen yadan dauki hankalin da yawa daga cikin almajiran. Saidai da yake daliban malam auwalu daban suke da sauran almajirai ba wanda yayi wani motsi na hayaniya ko fita daga tsari,saidai idanu da suke bin motocin dashi wanda ke qoqarin gyara parking a muhallin da suke ganin zasu iya tsaiwa. Idan ka duba da kyau fuskokin manyan cikinsu murmushi ya sake wadata,domin sun sani mutum daya ne tak me irin wadannan motocin sak....dake zuwa wajen malam,wanda duk ranar da yazo kuwa kakar kowa ta yanke saqa,duk da cewa qalilan daga cikinsu ne suka samu nasarar shaida fuskarsa. "Bari hamma na fita na duba ko yana ciki" Musaddiq ya furta yana duban fuad da ko sanda motar ta tsaya bai daga kanshi ba,hankalinsa still yana kan waya "Okay" Ya fada a hankali kaman wanda bayason yayi magana. A nutse ya bude motar ya fiddo qafarsa dake cikin rufaffen takalmin kamfanin Hermes. Ya qarasa fitowa daga motar yana gyara hannun rigarsa sannan ya fara takawa a nutse yana dosar rumafar malam din daya daga cikin guard yana biye dashi. Daga shigowar motocin har tsaiwarsu a wajen bata wani basu muhimmancin da zasu dauke hankalinta daga aikin da take ba,don Allah Allah take ta kammala ta wuce gida saboda yadda tunanin huda yaketa mata yawo saman kai abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba kenan. "Hamma malam fa idan ba da gaske akayi ba bazai koma sabon gida da makarantar daka gina masa ba" Sadiq da idanunshi kekan almajiran ya fada yana leqo kansa first set din da fuad ke zaune. A nutse ya zare lumsasssun idonsa akan wayar yana waiwayawa gefansa ya kuma aza idanunsa a muhallin da yake kyautata zaton a kanshi Sadiq yake magana. Saidai kuma duk da tarin almajiran daketa miqa hannu suna karbar wata takarda idanunsa basu sauka a ko ina ba sai a saman fuskarta. "Yanzu banda abun malam.....ga gini can a wadace,ga makarantar zamani amma yace sai yayi shawara?,har yanzu kuma bai gama shawarar ba?" Sadiq ya sake fada yana dariya qasa qasa,dariyar da bata samu isuwa ga kunnuwan fu'ad ba duk kuwa da cewa yana wajen. Sosai ya zuba ma fuskartata idanu bawai don tayi masa kyau ko kuma taja hankalinsa ba......aah.....sai don tuna a muhallin daya soma ganin fuskar duk da ba wani kyakkyawan kallo yayi mata ba. "Office din mikail......a ranar da incident din zai faru" Sashe mafi saurin harbawa cikin kwanyarsa ya bashi amsa *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 83 "Exactly....." Ya furta har labbansa suna motsawa,yayin da wani qaqqarfan tunani ya darsu a ransa. Bai dauke idanunsa daga sashen ba musamman ganin musaddiq ya doshi inda take kai tsaye......amma kuma kafin ya qarasa din ta juya tana takawa zuwa cikin gidan malam din,abinda ya sanya musaddiq da bai kula da fuskarta ba ya soma tambayar wanda yafi kowa girma a wajen kan ina malam?,kafin ma ya bashi amsa muryar malam din ta ruskeshi yana basu umarni su fara daura alwalar sallar magariba. "She's a suspect" Ya fadi a hankali yana zare idanunsa daga kanta sanda ta kammala shigewa malam ya bayyana. A nutse ya waiwaya ga sadiq yana kallonsa. "Kiramin jordan" Ya furta a nutse yana qoqarin bude side din da yake zaune. Baiyi wahalar komai ba ya janye dogon hannun rigarsa ya danna wani abu,cikin qasa da minti daya hotonsa tsaye jikin motar ya bayyana ta qaramin allon computer dake maqale a set din gaba fu'ad "Ka fita ka cewa malam gani nan shigowa.....ka cewa jordan din ya shigo". Ya danyi mamaki kadan da hakan,amma bai damu ba ya amsa masa yana bude murfin motar sannan ya fice yana gayawa jordan saqon boss din nasu. "come in" Yace ma qaqqarfan mutumin da yayi tsaye bakin motar cikin rusunawa. Cikin jin nauyin hada mazauni daya da boss din nasa ya shigo. Sai fu'ad din ya bashi umarnin rufe motar. Yayi kaman yadda yace din yana maido dubansa ga fu'ad din yana satar kallonsa. Duk yadda yakejin qarfi a ginannun tsokokin jikinsa a yanzu da yake zaune kusa da boss din nasa sai yaga ashe bai fishi da komai ba. "Kayi noticing wata girl a cikin yaran can tana raba musu wani abu?" Yayi tambayar kanshi tsaye,don yasan mutum ne shi me tsananin kula da motsin kowa "Yes sir" Ya gyada masa kai cikin qwarin gwiwa da confidence "Good.......i want every single details of her.....but don't forget.....make it secretly" "Done sir" Ya fadi a yanayinsa da muryarsa suna bawa fu'ad din tabbaci. Tun daga fitarsa a motar ya soma aikinsa,tun tana daga cikin gidan malam din fitowarta da tafiyarta hankali kwance saboda tasan bata da wani issue da kowa a nan area din......hasalima ba wanda yasanta a yankin don haka take tafiyarta a tsanake.......ya riga yayi waya da duk wanda ya kamata,don haka qarqashin kulawarsa take,tun daga abun hawan data samu zuwa isarta gidansu. Can qasan ran malam din yake mamakin dan dadewarsa wajensa a yau,duk da cewa ya maisheshi tamkar uba kaman yadda ya daukeshi d'a. Tun malam din yana tsoron asan cewa fitaccen mutum kuma attajiri irin muhammad fu'ad na zuwa wajensa har ya soma sakewa. Duk zuwan da zaiyi din kowa yana tsaiwa a waje ne amma shi da Sadiq ko musaddiq ko farouq idan tare sukazo suna zama ne tare dashi. Magariba dama ishai duka tare sukayi da malam din. Duka yana sane yana yi yana duba agogonshi bayan ya sanya musaddiq ya kashe wayarsa,tasa wayar kuwa dama shigowar kira yana bisa qa'ida ne so baida damuwa. Yadda zaman yaga ya miqa malam din yasa aka fito musu da tuwon dare daga cikin gidan. Yace a fito dashi dinne kawai saboda karamci irin nasa,bawai don yana sanya rai zasu iya ci ba. Saidai ga mamakinsa Sadiq da musaddiq din cin abinsu sukayi sosai,daidai lokacin shi kuma suke tattaunawarsu da fu'ad. Kudin daya saba bayarwa malam ya rabawa mabuqata duka wata ya ajiye,ya bada na malam din wanda kamar ko yaushe sai yayi kaman bazai karba din,yakance "Muhammadu......nikam bani da matsala ci sha sutura ko.muhalli,ina ganin a baiwa bayin Allah dake da tsananin buqata mana". Ko yaushe shi kuma yakan maimaitawa malam din. "Koda kullum zaka rubuta adadin mutanen da idanunka suke gani suna da buqata ta aikemin dashi malam za'ayi musu komai kuma hakan bazai hana ayi maka ba......a duk sanda ka hadu da mabuqaci kada kayi shayi ko shakkar alqawarta masa taimako,tabbas za'ayi masa dukan abinda ka buqata". Ko yaushe ya fadi haka malam ka jinjina kai. Girma da kimar malam a idanunsa tana da dimbin yawa,ya taka rawa me yawa a rayuwarsa,ya kuma tallafeshi da abinda baida abinda shi din zai iya saka masa dashi. Sai daya tabbatar tara na dare tana musu sallama sannan sukabar gidan malam din. Sanyin Ac din dake kadawa cikin motar ya sake saka masa kasala tare da taso da gajiyar jikinsa,saidai shi kuma ba wannan bane a gabansa yanxu. Gaba daya hankalinsa ya karkata gason jin komai daya shafi yarinyar,yana ji a jikinsa kamar akwai wani abu a qasa,kamar akwai wani abu. Ko sanda suka isa gida ma goma ta gota,saidai ya samu abba da anni zaune a falo da alama hira suke,duk da abban akwai takardu da yawa a gabansa yana rubuce rubuce. "Jiya da yau dai duka ba zama.....yarona ya rantse sai ya zama mutumin arewa na farko daya bawa 'yan kasuwa da masu arziqin arewa sample na kishin yankinsa" Anni ta fada tana murmushi. Shima murmushi ya saki,a koda yaushe yana alfahari da anni da kalamanta da suka zama sune qarfinsa. Bata tsareshi da yawa ba haka shima abban suka sallameshi ya wuce sassansa. Ta isa gidan bayan magariba da kadan,sanda tsakar gidan nasu ke cike da hada hadar ahalin gidan. Masu wankin uniform sunayi,masu zaman hira na zaune,masu kwashe tuwo da abincin dare kowa yana sabgar gabansa. Koda tayi sallama ba ta tabbatar babu wanda zai jita bare ya kalleta,idanma sun kalletan......zasu kalleta ne da mummunan kallon nan da tasan babu wanda ya isa ya wankeshi daga idanunsu sai randa ubangaji yaso,don haka ta zabi wucewa ciki salin alin ba tare data tankawa kowa ba,saidai duk da hakan bata tsira ba daga jiyo kalaman nan masu muni daga kunnuwan bibo "Hala yau barikin batayi ribaba.....dawa kuma batayi nama ba.....naga fuskar ba fara'a bare walwala......." "Ita bariki daman ai alalan gero ce......idan baka iya ba ta kwabe maka.......ta fara hangen wannan din inaji shi yasa ta soma yiwa 'yar uwar training......gashi an fara da fitar dare?" Yabi ta taya bibo din fada. Wata mummunar faduwa gabanta yayi,jikinta ya dauki rawa da jin kalamansu na qarshe,ta sanya hannu tana dauke hawayen daya silmiyo mata sanda taga daada na dauke flask din abincinta tana wucewa dashi dakinta. Hakan ya tuna mata da rayuwar gidansu,duk da yawansu abinci baya daya daga cikin matsala ko damuwar rayuwarsu,abinci na daya daga cikin abinda muddin kai haifaffen jinin gidanne ko maqoci ko abokin huldar arziqi tabbas kafi qarfinsa!. Abinci me kyau bawai irin abincin da za'a ci ba kawai saboda kore yunwa ko babu yadda za'ayi,yau sai gashi abinci ya zama matsalar gidan ta farko!,abinci ya zama damuwar gidan.....abinci kuma ya zama abu mafi wahalar samu garesu haka abu mafi daraja da tsada a gurinsu. Ji take kaman iska ke tafe da ita har ta sanya qafafunta cikin falon nasu "Ina huda?" Ta jefawa nadra da haneefa tambaya wanda suke zaune qasan carfet kawai. Sun tasa litattafansu a gaba bayan gama sallar magaribarsu kenan da alama. "Muna dawowa islamiyya ta ajiye jakarta ta fita" Nadra ta fadi da karyayyar murya tana tuna yadda ta daka mata tsawa sanda taga tana shirin fita din ta tambayeta "Inda kika aikeni makira sarkin tambaya!" Daga haka ta zuba mata manyan idanunta tana kallonta har ya fice. Ji tayi qafafunta kaman suna lanqwashewa don haka ta samu ta lallabo ta zauna kusa da haneefa da take kallonta da idanunta da tasha jin ana cewa irin nata ne sak,sai ta jawota jikinta tana duban nadra tare da qoqarin rarrashin zuciyarta "Bata gaya muku ina taje ba?" Kai nadra ta girgiza "Bata fada ba" "La haula wala quwwata illa billa" Ta fada muryarta nadan rawa kadan. Cikin qanqanin lokaci zuciya ta fara sawwara mata abubuwa masu yawa akan huda. Ina huda ta sani?,ina zata je?. A iya saninta huda bata da wata qawa illa nadra da haneefa,bata da wani wajen zuwa sai inda ita ta kaisu,bata da wajen zama idan ba dakinsu zuwa tsakar gida da farfajiyar gidansu ba.....to ina huda ta tafi?. Zame haneefa tayi daga jikinta ta miqe tana qoqarin saita kanta,ta wuce kitchen ta duba abinda suka dafa ta zuba musu "Kuci bari na shiga toilet" Saita fice zuwa tsakar gidan nasu. Dariya taji qasa qasa daga shiyyar da mutan gidan ke zaune,bata waiwaya ba haka batace komai ba,saidai jikinta ya bata tabbas da ita ake. Da qyar ta saita kanta ta cire pad din jikinta ta sauya wata sannan ta fito. Tana saka qafarta waje tana ganin shigowar huda wadda ta zarce dakinsu kanta tsaye. Tayi namijin qoqari qwarai da gaske wajen saita kanta ko don idanun jama'ar dake wajen tabi bayan huda a nutse zuciyarta kaman zata fado daga qirjinta. Sanda ta tabbatar sun isa falon dukkaninsu sai saitinta ya kwance gaba daya. Ta miqa hannu ta finciko huda dake qoqarin wucewa daki kai tsaye "Dawo nan......daga ina kike?" Ta jefa mata tambayar a tsawace tana dubanta da kyawawan idanunta da suka qara girma a yau. "Gid.....gidansu qawat...." Sai ta kasa qarasawa saboda tsoron daya kamata na ganin Sabreen ta daga hannu tabbacin lafiyayyen mari tayi nufin sauke mata. Tsit dakin yayi,a hankali ta maida dubanta sassansu nadra,saitaga sunyi tsumu tsumu suna kallonsu. Wani abune ya daki zuciyarta ya kuma karyata,abinda ya sanyata ja da baya wannan ya baiwa huda damar shiga dakin da sauri sauri. "Kuci abincinku ina zuwa.....babu abinda zai faru" Sabreen din ta fadi wani madaukakin tashin hankali yana saukarwa zuciyarta amma tana qoqarin tausar kanta,ta kuma taka da dan hanzari ta wuce dakin itama. Hijabin uniform dinta take qoqarin zarewa,sumarsu me tsaho da sulbi ta gado ta kwance,daidai sannan sabreen din ta miqa hannu ta sake jawota. Jikinta ta fara duddubawa,sannan ta sanya hancinta ta fara sansana jikinta,abinda ya sanya huda mutuwar tsaye zuciyarta tana wani irin bugawa tana bin sabreen din da idanu kawai ba tare da tasan ainihin ma'anar abinda takeyi ba. Bakinta ta kama ta matse tana duba harshenta,sanna takai hancinta tana shanshana labbanta. Bataji sauyin komai ba daga gareta,amma yadda zuciyarta ke bugawa ya tabbatar mata lallai akwai alamun rashin gaskiya a tare da ita,sai ta sanya hannu ta tunkudeta,kai tsaye ta fada saman gadon tayi zaman 'yan bori,tayi taku biyi sabreen din ta tsaya a kanta gab da ita "Ki gayamin daga inda kike tun muna mu biyu kafin duniya ta jimu!" Ta sake fada mata tana fidda idanunta da a yau suka qara girma saboda tashin hankali. "Ni fa ba inda naje adda......gidansu qawata" "Wacce qawar?,yaushe kika yita?,kuma a ina take?" "A islamiyya muka hadu...." Ta fadi tana jawo qarfin gwiwa bayan ta tsinto wasu maganganu daga kalaman naseer da yake a matsayin bassam a wajenta. Yadda tone din ta ya sauya farat daya yaja hankalin sabreen,saita gyara tsaiwarta "Islamiyya?.....inane gidansu?,me yasa ni bansanta ba?" Tashin farko sai taji ranta ya baci,karon farko kuma a rayuwarta taji kaman yau yaa sabreen ta raina mata wayo "To ai kowa ma yana da mutanen da yake mu'amala dasu,ba lallai sai uwa ko uba ko 'yan uwa sunsan da zamansa ba" Tayi maganar kai tsaye abinda ya zowa sabreen din a wata gigitacciyar ba zata *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 84 Dukkan wani motsi nata ya tsaya cak......cikin wani irin madaukakin mamaki take duban huda bugun zuciyarta yana canzawa da wani irin yanayi taji yana saukar mata na sanyin jiki tun daga saman kanta har qafafunta,wani irin sanyi jikinta yayi saidai duk da haka ta dawo da hayyacinta cikin jikinta "Huda?......" Ta kira sunanta da sautin mamaki. A wannan karon sai hudan taji abun yadan mata nauyi,ta kasa hada idanu da sabreen din,ta juya tana son qarasa cire uniform dinta. Kanta tsaye ta nufi gadon huda din,ta soma janye zanin gadon zuwa katifar tata. Sannu sannu a hankali ta soma birkice duk wani kaya na huda dake dakin,zuciyarta na raya mata akwai wani abu da huda kesha tabbas wanda shi ya canzata. Muddin kuwa hakan ta kasance batasan meye abu na gaba da zai faru tsakanin tata rayuwar data hudan ba. Cikin abinda ta tsana mafi girma da muni shine shaye shaye,bata samu relief ba sai data tabbatar bata samu komai daya danganci maye daga fannin huda ba. Hudan da tayi tsaye kawai tana bin yayar tata da kallo. Wato a yadda ta yiwa dakin nasu a yau tayi imanin banda takai wayar an canza mata babba,kuma data shigo da ita tana jikinta a maqale babu abinda zai hanata ganin abinda take boyewar. "Ki gyara dakin,idan kin shirya gayamin inda kikaje ki sameni a falo,idanma baki shirya ba duk daya" Ta bata umarni nakai tsaye tana takawa tana barin dakin. Qasan ranta ta riga ta gama yanke komai.....ta riga kuma ta gama yanke hukuncin da zata dauka akan huda din. Har suka gama dukkan wani sabgarsu a falon ko leqowa batayi ba ballantana ta fito har ta sameta da wani batu,ko abinci bataga tazo ta diba ba. Wanna ya sake qona ran sabreen matuqa da gaske,ya kuma sake bata tabbacin eh lallai da walakin goro a miya. Koda suka shiga dakin sanya nadreen da haneefa tayi suka kwanta,itama tabi sahunsu a nata gadon ba tare da ko tabi takan huda ba. Saidai a nata salon kwanciyar ta kwanta dinne bawai don tana da niyyar yin bacci ba,ta kwanta ne tana monitoring dukkan motsin hudan. Har ta gama juye juyenta,ta fita falo sha biyu saura na dare,shigarta kitchen da zaman cin abincinta ta gama ta maida kwanon tana jinta. Har zuciyarta tana son jin muryar bassam dinta.....amma wata zuciyar tana kwabarta,yau din bai kamata tayi waya dashi ba,don gaba daya jikinta da zuciyarta babu qwari. Sha biyu na dare yana zaune cikin kebantaccen dakin nasa,gaban system da tarin cups na shayi da yake canzawa daga wannan zuwa wancan. Aiki yakeyi sosai,aikin kuma yana tafi masa yadda yakeso,don yana sake samun wasu bayanai da yakeso. Wayarsa tayi qara alamun shigowar kira. Waya ce daya ware musamman saboda waya tsakaninsa da gurd dinsa musamman idan basa kusa ko basa tare. Jordan ya gani,sai ya dakata daga dukkan abinda yakeyi din ya daga wayar yana relaxing bayansa jikin kujerar da yake zaune akai din,don dama yana expecting kiransa daga wannan lokaci har zuwa asuba zuwa safiya. "Barka da warhaka sir" Jordan ya fadi da hausarsa da bata gama tsaiwa tar ba "Barka dai jordan......how far?" "Fine sir.....duk wani information ya kammalu" "Very good......" Ya fadi da nutsuwar nan tasa data sake qaruwa sakamakon bacci dakeson fara kamashi. "Tell me jordan......" "Immediately sir" Ya fada yana sake tattara hankalinsa akan boss din nashi. Idanunshi a lumshe sanda jordan ke sakar mishi bayanai dalla dalla akan sabreen din. Bayanai ne na bincike da yayi a kanta ta hannun mutane daban daban da suke da jibi da Rayuwarta. Ba abinda yake sauraro illa muryar jordan yana masa bayani dalla dalla har yakai qarshe. "Good job jordan......na baka hutun gobe.....ka kwanta ka huta sosai.....but idan ina buqatar wani abu daban zan kiraka" "As you wish sir" Ya fada cikin girmamawa. Da wani irin cakudadden yanayi na ajiye wayar gefansa yana furzar da iska me dumi daga bakinsa. Ba abinda yafi riqewa saman kansa irin kalaman jordan na biyun qarshe "A taqaice dai sir ana kyautata zaton KARUWA Ce ko kuma mayaudariyar maza......wadda maza da dama ke sonta suke kuma kashe mata kudade masu kauri,kuma daga qarshe abinda yake faruwa ba'a jimawa take rabuwa dasu......tana rayuwa ne ba uwa ba uba.....amma tsarin Rayuwarta da yadda takema kanta komai da 'yan uwanta.....koda d'a me uba da kuma tsananin gata sai haka......bata nemi komai ta rasa ba......sir......akwai wanda ya gaya min tana da hatsari.....tana da hatsari.....tana kuma da mabanbantan sunayen da ita kanta batasan adadinsu ba". Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke yana jin wani abu yana tokare masa a qirji. Ya miqe qafafunsa sosai tamkar zaiyi miqa yana jin wani irin ciwo a zuciyarsa. Qoqari yake ya sake tuno fuskarta ko zai iya banbance shekarunta da yayi imanin ba zasu wuce ashirin ba tsanani da daya. Abinda yaqi jinij yaji ko ya gani kenan koda cikin labarai diya mace ta lalace har haka. A dukka qananun shekaru irin nata ta iya zama mace me hadari har haka?,har ta iua bada jikinta zuwa ga wasu mazan don ta mallaki abun duniya?,har ta iya yaudara da damfarar wawayen maza irin Mikhail?. Wannan kadai ya isa ya bashi tabbacin tabbas ita ta shirya ko ta tsara ko ta jagoranta ko kuma ta bada gudunmawar faruwar badaqalar cikin kamfaninsu. "Ya Allah.....how?......diya mace da wannan aikin?,aikin fashi da makami fa kenan a miqaqqiyar hausa,fashi da makami na yanar gizo. Shi a yanzun ma idan yace zai kamata yace ya kama wa?,ya gayawa duniya kamfaninsa na tuhumar mace da kitsa shiga na'urarsu kuma suka kwashe kudaden asusunsu?. Tabbas ya bari hakan ta faru ba komai bane ga kamfaninsu face zallar faduwa da kuma sake nunawa duniya rauninsu muraran. To amma idan ya qyaletan kenan taci bulus?.....jadda company ya zama marainar wayonta?.....jadda company ya zame mata abun wasa?. Ya kamata ya dauki mummunan hukunci a kanta,irin hukuncin da ko sunan jadda kadai taji zai gigitata ya dimautata ya kuma sanyata a fargaba....ambatar sunan kadai ya zamowa kwanyarta da kunnuwanta baraza. Sai yaji gaba daya tunaninsa ya karkata kan fitar kudin kamfanin karo na biyu. Idan wannan ita ta aikata ya tabbatar ba zata sake dawowa ba a karo na biyu gudun kada a kama na'urarsu har a samu isa ga inda suke,tabbas wannan karon mikail shi ya aikata haka da kansa,don haka ya bude idanunsa yana sake jawo system dinsa. Yanaso ya sani,yanason yayi bincike ta yadda komai zai tafi masa a daidai. Cikin qasa da awa daya komai ya fito masa yadda yakeso. Ainihin wanda kudin suka koma account nashi daga account din wanda aka bawa ajiyar sunanshi ya fito baro baro da taimakon shigabannin bankunan da dukka suke amfani dashi,wanda yakan nemesu idan buqata irin haka ta taso "Rufa'i ahmad mu'azzam" Ya mamaita sunan yana zuba masa idanu. "Wayeshi?" Amsar da bashi da ita,babu kuma me bayar da ita sai mikail,kasantuwar hakan kuwa ya zama tilas a gobe mikail ya miqo kansa ko kuma shi yasa a kawo masa shi. Kadan yadan daki table din,sannan ya sake jawo wayar gefansa ba tare da duba da yadda dare yayi ba. Duk da daren hakan bai hana a daga wayar ba da bugu daya tak. "Barka da dare sir" Aka furta da muryar dake nuna kiranne ya tasheshi daga bacci "Barka abdus_samad....i have a work for you" "Okay sir...." Ya fada yana watsakewa daga baccin nasa. "Zan tura maka through email then sai muyi magana.....but ina buqatar bayanan as soon as possible" "Yes sir" Ya furta cikin matuqar bada girma. Kiran ya katse don duk wani abu me muhimmanci ba kasafai ya fiya magananshi ta waya ba,duk da layinsa yana da tsaro sosai......to amma ya sani a kowanne motsi akwai maqiya abokan gaba da abokan burmi. Komai ya tura masa,sai a sannan yaji idanunsa sun fara yaji yaji alamun suna da buqatar bacci,dole ya tattare komai ya tafi ya kwanta don yana da buqatar ya qarasa hada abinda dukka ya rage masa a gobe tunda jumaa bai fiya fita office ba,koda ya fitan baya dadewa sosai,ga kuma alqawarin tafiya abuja da ya yiwa farouq. Bayason ya sake karya alqawarin,duk da yasan farouq zai fahimceshi zai kuma bashi uzuri fiye da yadda yake buqata ma. A wannan yanayin kawai yaji ya kamata ya fara amfani da private jet dinsa,sai ya lalubi me haqqin kula da zirga zirgarsa ya tura masa bayanai sannan ya ajiye wayar yana nufar qofa bayan ya kashe komai ya kuma kwashe komai da yake da buqatar fita dashi. *******Duk wani motsi nata saman idanun sabreen din take yinsa. Tana sake karantar duk wani yanayi na huda din. Zuciyarta na sake tsinkewa yana kuma saukar mata da fargaba hakan. A duk sanda zatonta da zarginta ya bata akwai wani ne a rayuwar huda din?. Abu daya dake sake gigita tunaninta da sanyata jin ya zama tilas ta nuna nata salon maganar nan da ake cewa duk wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 85 Ba wata kalma data sake hadasu da ita,har suka kammala shirin makaranta,ta dauki jakarta kaman kullum,ta kuma fidda kudin transport dana break. Wannan karon nadra ta miqawa a maimakon huda "Ki kula sosai nadra......ana tashi kada ku tsaya ko ina" "to adda" Ta amsa mata tana kama hannun haneefa suka fara takawa zasu fice. "Nifa?" Huda da ta kasa fahimtar abinda sabreen din tayi ta tambayeta. Kai ta daga a nutse ta watsa mata kallo. Sai ta janye idonta daga kallon da takewa sabreen din saboda yadda idanun sabreen sukafi nata kaifi. "Na dakatar da zuwanki makaranta" Amsar data bata kenan ta miqe,amsar kuma data girgiza huda din. Ta dakatar da zuwanta makaranta kamar yaaya?. Dakatar da ita daga zuwa makaranta fa kenan yana nufin yankewar ganinta da bassam?. Idan haka ta kasance kenan sunyi bankwana da bassam?,saidai ta zauna ta zuba idanu tana ci gaba da rayuwa cikin wannan quntataccen gidan nasu da babu farinciki ko guda daya a cikinsa?. Bata sake bi ta kanta ba,dole kuma data gaji da tunanin taja qafarta tana komawa cikin dakin,yayin da sabreen taci gaba da kai kawo tsakanin falon da dakin,tana shirya zata kasance da huda a dakin tsahon wuni da kwanakin da zasu biyo baya. Ta tabbatar idan ta lazimci hakan dole koma meye huda take boyewa ya fito fili. Tayi juyi tayi tayi juyi har batasan iyaka ba. A duka hukuncin abinda yafi damunta shine yanke mata qofar fita. Fitar da itace hanya guda daya da zata bata damar samun bassam ta kuma shaida masa sabon dokan da adda sabreen din ta kafa mata. Ta yita zuba ido taga ko zata fita?,saidai yau qiyau miyau,banda toilet data fita tayi wanka ta dawo ba inda taje,haka suka wuni tana sabgoginta don ko tayin abinci batayi mata ba,sai data gaji don kanta tana rara gefe ta fada kitchen din ta diba taci ta koma taci gaba da kwanciyarta. Ko da akayi sallar isha'i tana jiyosu a parlor suna assignment da sauran bitocin karatunsu kaman yadda suka saba. Ba wanda yabi ta kanta a tsakanin su ukun. Gaba daya dakin dama gidan ya sake gundurarta ya kuma fice mata a kai. To wai shin ita adda sabreen dakeyi mata haka?,ita waye ya takurata haka?,waye ya dameta haka?,kullum Allah shike da kullum sai ta sanya qafa ta fita waye ya taba dakatar da ita ballanta ya sanya mata dokar fita. Miqewa tayi ta zauna bakin gadon nasu tana jan qaramin tsakin baqinciki. Tana masifar son gadonta da jin dadin kwanciya akai,amma yau gaba daya sai taji ta tsaneshi ya kuma fice mata a kai. Wayarta dake haske ta jawo ta buda tana dubawa. Wayar na cikin personal wayoyinta da ba kasafai take bari saqo ko kira a ciki ya wuceta ba. "Kina da tafiya on Saturday da mushkur......ina fata baki manta ba?" Saqon da jib ya tura mata kenan. Yatsunta ta cusa cikin sumarta tana yamutsawa kadan kadan. Har cikin jininta taji batason tafiyar,komai kuma ya fice mata a kai,to amma batasan dalilin da ya sanya wani sashe na zuciyarta ke zugata yana gaya mata BAI KAMATA TA BARI MASHKUR YACI BULUS BA,KODA DAGA KAN MASHKUR TA RUFE QOFA YA KAMATA YA DANDANI DACIN QWACE ABU DAGA HANNUN ME SHI. Idanunta ta juya ta kalli sashen dasu nadra ke zaune. A irin wannan yanayin ma da take qoqarin fuskantar inda rayuwar huda ke neman dosa,sam sam bata qaunar tayi nesa da kowannensu don sanya ido akan motsinsu "Ko ta buqaci friday?,gajeriyar rana ce......sannan kuma tana da tabbacin zai wahala ta rasa ticket din juyowa a ranar" Tayi zancan cikin ranta,don haka ta soma rubuta tex tana turawa kowa tsakanin mashkur da jib da zai kula da komai. Kamar jira akeyi ta kammala muryar ta mamaye ilahirin tsakar gidan nasu. Da wannan madaukakin sautin nasa da babu komai ciki face takura wulaqanci da kuma saukar azal akan duk wanda ta ratso dashi. "Yau kuma akan waye da waye ta fada?" Ta fada qasan ranta,don tasan wajibi sunanta a sahun farko. Bai taba shigowa gidan ya fita salin alin ba tare daya takalo wani abu da ita ba,wannan ya sanya ko yaushe take shiryawa zuwansa da ko wanne irin yanayi ma zayazo dashi. "Kowa da kowa ya fito,maza da mata,yara da manya,yau dai Allah yayi arziqin me arziqi ya dawo......rabon bawa da arziqi mutuwa......Allah ya lamuncemin nima......ku futo yau arziqin rufa'i ya dawo,wanda yayi biyayya aci dashi,wanda kuma ya bijire saidai yaga ana ci" Ya qarasa maganar yana bin dakunan da qofofinsu suke a rufe yana bubbugawa. A nutse ta maida idanunta kan su nadra da suma ita suke kallo. Tana iya hangen wani boyayyen murmushi akan fuskar nadra din,da alama idan so samu ne tanason fita ta ganewa idanunta kamar yadda ya gayyaci kowa ta kuma fara jin alamun suna fita din,don muryar bibo har nan inda suke muryarta zaqwai tana karadi. Batasan me yasa duk gidan nadra tafi kowa maidashi kaman kakanta ba. Ada muguj balain tsoronsa sukeyi,amma yanzu kwata kwata bata tsoronsa. Duk sanda ta kwasheshi idan yana tambotsansa ya dinga zaginta kenan amma ita ko a jikinta,hasalima dariya take binsa da ita,yayi dukan yayi dukan sabreen tayi fadan amma ko a hancin takalminta "Kada wanda ya motsa,ku gama aikin da yake gabanku" Ta dan hade rai tana fada. Idanunsu suka maida kan litattafansu suna ci gaba da aikinsu,saidai daga ita harsu kunnuwansu yana tsakar gidan suna tsintar wasu daga kalaman kawun. A qalla ya kusa mintuna arbain da shigowar gidan kafin suji an banko qofar dakinsu. "Barin hali sai mutuwa,miskili kafi mahaukaci ban haushi....halin ne ya motsa ko baqinciki ake da komawata mawadaci?" Ya qarasa maganar sanda yake sako jikinsa cikin falon yasha shadda dinkin babbar riga da 'yar ciki yanata bazata. "Ko daya kawu......ina maka murna.....amma Allah dai yasa ba daga aikin da abban ya hana bane...." Tayi masa shaguben data tabbatar kaf jama'ar gidan ba wanda ya isa ya gaya masa hakan,wasu saboda tsoronsa wasu kuma saboda kwadayin abun duniya. "Sannu ja'ira maras kunya.....ke harni zaki gayawa haka?,yo dani dake waye zaiwa wani gori?,Allah na tuba ba har gwara nawa kudin ba gwagwarmaya da fargaba nasha na kuma zuba nawa jarin kadan suka jawomin masu yawa?,ke nawa kika zuba kike samun naki kudin?" Ya fada cikin bambamin daya sanua huda dake daki kwance yin bakam tana jinsu,maganar kawun kuma ta sake tsaye mata a rai tare da sake jin wani baqon yanayi akan sabreen din da yafi kama da haushi haushi da son shinfida tata rayuwar......ita da aure ma zatayi?. A hankali ta sauke idanunta zuwa wayar hannunta,maganganun kawun suna mata wani irin daci cikin zuciya har zuwa saman harshenta. Ba wannan bane karon farko daya jefeta da magana irin wannan ba muddin zata sako masa zancan caca.....amma wannan din yayi mata zafi ne saboda ya ambata tsakanin su nadra da huda da taketa qoqarin gano bakin zaren matsalarta. "Kome meye dai sama'ila ya shallake......ba kuma zai sake zuwa tambayar komai a hannun kowa ba.....kuma daga yau har na mutu sunana mawadaci.....munyi hannun riga da talauci" Ya qarasa maganar yana wara hannayensa kaman me jiran wani yazo ya rungumeshi. Sai daya gaji ya sauke sannan ya gyara zamansa yana sake kallonta "Yauwa......batun kudadenki.....zuwa nayi muyi lissafin abinda kk taba bani na rage.....don bazan iya biya duka ba domin kuwa tattalin dukiya akeyi yanzu......yauwa". Badon yanayin daya jefa zuciyarta ba tabbas murmushi ne zai qwace mata,amma a yanzun sai kawai ta dubeshi ta dauke kai "Bana buqatar komai a ciki.....hasalima dama kyauta na baka ba bashi ba" . Washe baki ya fara yi yana shafa habarsa "Aah......kaga farar diya irin albarka.....diyar da babu kamarta kaf haife haifen da ahmadu yakeyi baiyi kamar taki ba har yabar duniya.....Allah dai yashi miki albarka" Ya fada yana sake sakin dariya. "To ni zan wuce......sai kunzo ganin hamshaqiyar fada ta tarewa nan kusa da kuma qarin auren mata ta biyu". Kadan ta dubeshi,saita kasa cewa dashi komai,har ya juya ya fice yanata sakin qarin bayani. Hannu ta sanya ta dafe goshinta kadan,abubuwa da dama suna mata kai kawo saman zuciyarta. Kwata kwata DUNIYARTA bata jinta daidai bata kuma kallonta daidai da duniya kowa. Akwai abubuwa da yawa da takejin suna ba daidai ba cikin rayuwarta......WAI SAI YAUSHE KOMAI ZAI DAIDAITA?. _Tambayar data yiwa kanta kenan da bata da amsarta,wadda batasan wannan din shine MAFARI na komai ba_ *******K'arfe goma na safe ne sanda yake takawa cikin farfajiyar gidan nasu. Sanye cikin farin lallausan yadi daga lallausar auduga mafi tsada da daraja. Fari ne qal yadin maras nauyi dake iya bayyana shatin fara qal din vest din jikinsa sama sama. Kusan komai da yayi amfani dashi a yau din fari ne,tun daga sutura takalmi da agogon fata me tsada dake daure a tsintsiyar hannunsa. A irin wannan rana ma ta juma'a motor din hawansa yakan canza zuwa fara duka don sabunta sunnar ta'ammali da farin abu. Hularsa tana hannun me sunan malam dake tsaye daga gefe bayan ya karbi news paper din daya kammala dubawa. Ameh ya sallama daya biyoshi da tray din teen da zaitun da kuma jan inibi da bai zauna yaci ba,ya juya yana duban me sunan malam "Ka shiryamin zama da shugaban gidan jaridu a gobe.....don yau din zamuje abuja.....but zuwa yammaci zamu juyo" "Okay sir" Me sunan malam ya furta,sai fu'ad din ya sanya hannu ya karbi hular ya juya yana nufar qofa,abinda ya sanya duka guards dinsa tsaiwa don sunsan inda zashi,mutum biyun daya saba tafiya dasu sukabi bayansa. Dab da zai fice a gate din farko yaji tana qwala kiran sunansa da shagwabar na tata "Hamma......hamma na". Tun kafin ya waiwayo murmushi ya subuce masa duk da bai shiryawa hakan ba. Yasan zaisha qorafi saboda haduwa da tayi wahala a tsakaninsu a kwanan nan. Barin hali inji hausawa sai mutuwa,tana isowa taja tunga kuwa tana tura baki gaba "Hamma.....kace kada na yarda da abinda BB farouq ya fada......kuma ni Allah alamun nake gani". Wani lafiyayyen murmushi da ba kasafai ake katarin ganinsa saman fuskarsa ba ya saki yana juya fuskarsa dama da hagu kafin ya tsaida dubansa saman fuskarta. "Amneeen hamma amneen anni......zaki yarda magauta su rabamu?" Kai ta girgiza da sauri tana sake fuskarta qasan ranta kuma tana fata inama saddiq yana kusa yaji yadda hamma yake ji da ita. "Kwana biyun nan school ya saki gaba.....nima duka aikace aikace sun tasomin......ko bakison mu bude company n jewelry sample din farko da zamu fara fiddawa ya zama naki......kinsan sunan da zamu bawa brand din?" Kai ta sake girgizawa cikin tsananin jin dadi "To sai kin kawo cin hanci zan gaya miki" Yayi maganar yana juyawa tare da ci gaba da tafiya. Da hanzari ta tattaka ta cimmasa sukaci gaba da tafiya tare "Please hammana.....ka gayamin cin hancin me kakeso?,kome kakeso hamma zan bayar" "No....ki canka da kanki kawai ki bada din sai na gaya miki" Shuru tayi tana zurfafa nazarinta na abinda ya dace ta bashin,dab da zasu fice a gidan tace masa "Yauwa.....hamma........zanyi maka mata ka huta da gorin yaa farouq akan kaqi nemo mata......na baka friend dita nasreen...." Dan rage speed na tafiyanshi yayi ya waiwayo yana jefa mata harara da fararen idanunsa. Ya yarda autanci da kuma quruciya suna damun amna din da gasken gaske,da alama fa da gaske take,don daga yadda tayi masa maganar tana zumudi tare da jij ta masa bajinta kadai zai gaya maka iya gaskiyarta kenan. "Wannan ba cin hanci bane......saidai ma ki jawo komawa ta biyu da za'a bawa product din" Hannu ta sanya tana rufe bakinta gami da zaro ido. Sai yanzu ta gane tayi wautar,ta tuna sunanshi da farouq ke gaya masa,ta kuma tuna shi lamarin yin budurwa ko zancan aure abune da bata taba gani ya zauna ya bashi muhimmanci ba. Kunnenta ta kama daidai sanda suke isa qofar gidan wanda sam bata ma kula da gidan da suke nufa din ba saboda yadda hankalinta ya dauku "Am sorry hamma.....please,wallahi idan ka fasa yaa saddiq zaiyimin dariya". "Ki canza wani abun.......but this" Sai ya girgiza mata kai yana maida dubansa ga muhallin malam Sa'adu wanda bai ganshi wajen ba da alama ko ya zaga ne. Tun daga shigowarsu gidan har takowarsu farfajiyar gidan idanunta yana bisa kansu. A yadda tasan hali da dabi'arsa ya akayi yarinyar ta samu sakewarsa har irin haka?,anya abinda take tunani kowanne dare kuwa bazai afku ba?. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 86 Ita kuwa ta yaya zata bari wani abu ya hada zuri'arta data hajiya amina?. Muddin da rai da ruhi da kuma numfashi a gangar jikinta.... Koda zata rasa komai data mallaka.......koda shine abu na qarshe da zata aiwatar cikin rayuwarta ba zata taba bari wannan tunanin ya wanzu a kwanyar kowa bama bare akai ga haifar tunanin a zahiri. Labulenta ta saki zuciyarta na mata wani irin suya. Kwanaki biyu kenan suna sanyata yin asarar komai data shirya domin su. Yaune cikar kwanakin da bokan ya diba mata,muddin a yau ma nasara ta qwace mata to lallai zancan bokan ya tabbata na cewa aikin aiki ne......muddin a yau bata samu yadda takeso ba batajin gobe warhaka zata kasance a bigiren da take tsaye akai a yanzu......dole ta tafi plan B da zafi zafinta kuwa. "Zuwaira.......maza leqa ki gaya masa ya qaraso ciki amma shi kadai......bana ko qaunar kallon fuskar yarinyar ballantana gangar jikinta ya shigomin cikin gida". Sosai zuwaira taji nauyin aiken saboda ba qaramin kwarjini fu'ad din yakeyi mata ba,amma ba zata iya musa umarnin uwar dakin nata ba. Da bismillah a bakinsa yake shirin sanya qafarsa a step na farko da zai sadaka da qofar falon zuwaira ta fito. Kai ya daga ya kalleta a nutse ganin kamar an jehota,sai tayi qas da kanta cikin tsananin qanqan da kai ba tare data iya hada ido dashi ba tace "Maamah tace ka qaraso ciki.....amma so samu tanason ganawa da kaine kai kadai". A nutse ya waiwaya ya dubi amna,suka hada ido sai ya zare idonsa daga kanta,ya miqa mata hularsa yana cewa "Riqemin yanzu zan fito" Bata musa ba ta sanya hannu ta karba,ta koma daga gefe ta zauna kawai jikinta a sanyaye,don inda ya barta gida zata koma,sai yanzu ta tuna gidan waye ta biyoshi?. Matar da totally ita tsoro take bata tun ranar data shigo gidansu ta kuma ga abinda tayi musu. Bai fasa duka addu'anshi ba kafin ya sanya qafarsa cikin matuqar kula da takatsantsan. Tana zaune saman sofa qafarta daya saman daya tana kadata a hankali. Ciki ciki ta amsa masa sallamar ba tare data masa wani dogon kallo ba. Ya qarasa ya tsugunna cikin girmamawa yana fadin "Barka da safiya.....kin tashi lpy?" "Koma ka zauna muhammadu" Ta furta kai tsaye wanda baice komai ba ya miqe din ya koma ya zauna sosai. "Wacece mahaifiyarka ne muhammadu?" Tayi masa tambayar da wani sauti dake cike da izza da kuma bacin rai. Kanshi ya daga ya kalleta suka hada idanu,ta tsareshi da ido sosai da kuma tarin abubuwa daya gansu kwance cikin idanun nata. "Kece" Ya amsa mata a gajarce. "To amma banga alama ba.......banga alamar hakan ba......yanzu ace samuwar farincikina daga gareku sai ya gagara?,yanzu ace samun kulawa da danuwarku a kaina sai ya zamemin aiki?" Ta jefa masa tambayar da ba abinda tayi tasiri a kai sai tuna masa da baya da tayi. Ta tuna masa sanda suke da tsananin buqatarta a daidai wannan lokacin ta tattara hankalinta zuwa ga wani waje daban. Ya tuna tun shekarunsa basu kai ya koyi wasu abubuwa masu yawa harda ma wadanda sukafi qarfinsa saboda rashin samun kulawarta. Ya tuna yadda yake kasa yiwa mahaifinsa dake jiyya abubuwa da yawa saboda bashi da qarfin da zai iya dagashi zuwa toilet da sauransu,saidai su zauna shi kuka shima kuka. Sau tari maganganunta da lafuzzanta sunfi masa kama da na mutanen da idonsu ya rufe......mutanen da buqatar gabansu kawai suka sanya a gaba,mutanen da ba ruwansu da damuwar kowa sai tasu......mutanen da ba wani burbushi na nadama a tare dasu ballantana dana sani. "Kiya haquri" Ya jefeta da kalmar da yakejin iya ita kadai kawai zai iya furta mata don bashi da wani sauran abun fada. Sake zube masa idanunta tayi tana sake jaddada zallar miskilanci da taurin fu'ad din. Ba wani alamun sarewa ko saukowa a tare dashi?,tamkar ma an sanya fetur da ashana an qone dukkan wata qauna ta mahaifiya dake zuciyar kowanne d'a. Anya ba zancan hajja harira bane akan hanya da take hasashen hadda farraqu hajiya ameena ta sanya akayi musu?. "Zanje abuja yau din.....nace bari na sanar miki,sai mun dawo" Ya furta bawai don yana sanya ran zata masa addu'a ko wani abu daya dace ba,don yana kaiwa qarshe ya miqe yana gyara hannun rigarsa. Dan runtse idonta kadan tayi tana hasashen yau dinma kenan babu nasara?. Da qyar ta iya controlling kanta da fadin "Sai ka dawo" Duk kuwa da tarin tambayoyin da takeson masa akan me zaije yi abuja?,yaushe zai dawo?. Binsa tayi da kallo har ya fice daga falon,taja wani mataccen numfashi idanunta na qanqancewa saboda bacin rai.....dole suje plan B bata kuma fatan su isa plan C don zaifi kowanne mataki wahala a gareta dasu gaba daya "Yaro baisan wuta ba sai ya taka.......yaro man kaza......idan kasan wata bakasan wata ba" Dukka ta furta a sarari tana daukan wayarta gami da kiran hajja harira. Cikin wani iri ya dawo cikin gidan. Saidai yayi qoqarin daidaita yanayinsa lokacin daya isa parlor din anni. Can babban dining area din dake parlor din ya samesu saman dining. Anni abba da farouq suna breakfast,yaja kujera kusa da anni ya zauna yana gaida abba da basu samu haduwa ba sai sannan. "Abba.....nace ya kamata ace tare muka fara hawa jet dinnan". Dan murmushi ya saki yana ciro tissue cikin tissue box. "Nikam wannan jumaar a kibiya zanyita me babban suna......indai muna da rai ai za'a yita hawa ko don zuwa ibada qasa me tsarki.......yanzu kam ku wuce sabgar gabanku.....saidai kads ku manta da addu'a,Allah yasa a shiga a sa'a,ya kauda dukka abunqi" "Allah yasa a fara hawa cikin sa'a,ubangiji yasa rai aka yiwa" Anni itama ta furta tana murmushi. Har qasan ranta tana jin dadi gami da jin alfaharin kasancewarta uwar goyo a gareshi. Koda muhammad bai kasance me dukiya da arziqi kaman haka ba.....shi din abun alfahari ne ga dukka uwa me hankali......yana da wasu nagartattu kuma kebantattun halaye na daban da ba kowanne dan adam yake samun baiwar mallakarsu ba. Da dukka zuciya da idanu ta takawa hasken idaniyar tata har zuwa sashen da kowannensu zai hau mota tana rakasu da addu'o'i na neman kariyar ubangiji da kuma tsarinsa. Abban yau sunyi kibiya shi da musaddiq,wanda dama kusan kowanne qarshen wata ko sati idan ya samu chance acan yake sallar juma'arshi,hakanan yakan tafi musu da tarin alkhairai daga arziqin da Allah ya wadatashi dashi bayan wasu daga cikin 'yan uwan da suke zaune a gidan. Wannan din wata dabi'a tasa ce dake qara masa farinjini da soyayya wajen al'ummar garin,domin kuwa alkhairinsa ba wai iya ga 'yan uwansa kadai ya tsaya ba......ya kewaye kowa da kowa. A saman idanunta dukka motocinsu suka tashi,sai gidan ya rage daga ma'aikata sai ita sai musaddiq.......sai mutanen dake can boys quarter da ba kasafai suke iya jiyo motsin abinda ke faruwa cikin ainihin gidan ba ko kuma su aji nasu. Idanunsa lumshe cikin jirgin,sanda yake lulawa dasu sararin subhana daga abujar birnin tarayya zuwa kanon dabo. Abujan da duka duka awa biyar sukayi cikinta suka fito. Acan sukayi sallar jumaa cikin centra mosque abuja,daga nan suka wuce unguwarsu fanna. Rashin sabo da wannan sabgar ya sanya mintuna talatin kawai yayi gidan ya cewa farouq zan dan kama masauki na wucin gadi da yafi kusa da airport.......zai tura masa location din sai ya sameshi a can su wuce. Shigarsa masaukin yayi arba da abinda ya sake tsuke tunaninsa ya kuma sake dora masa mamaki me azabar nauyi......ya shiga daidai sanda mashkur ne gangarowa daga sama riqe da wayarsa a mugun gigice yana cigiyar hotonta daya buda cikin wayarsa. Hoton da yakebin duk wanda ya gani da tambayar "Don Allah kaga wannan?,yanzun nan ta sauko daga dakina fa.......ta yasheni ta kwashemin komai daga accounts dina guda biyun". Da irin wannan bayanan ya tareshi sanda yake yunqurin kiran elevator ya haura dashi zuwa sama bayan yabar guards dinsa guda cikin reception din. Duba daya tak ya yiwa hoton ya dauke idanunsa a hankali ya maida fuskar mashkur da tayi wani irin hautsinewa.....da alana ta zare masa kudi masu yawan da tsaf zai iya taba rayuwarshi. Wacce irin hatsabibiyar yarinya ce wannan?,fu'ad ya yiwa Kansa da kansa tambaya sanda elevator din ya qaraso ya bude ya soma shiga. Har a sannan yana jin muryar mashkur dake bulayin neman wanda ya ganta. Lumshe idanunsa yayi yana jin wani mummunan bacin rai yana saukar masa. Yana buqatar qarin information a kanta abinda ya raya kenan a ransa,ya fiddo wayarsa yana neman Jordan,sukayi maganganun da zasuyi,dab da zai ajiye wayar kuma kiran abdus_samad ya shigo masa. Dukkan wasu bayanai ya karanto masa akan rufai ahmad mu'azzam. "Caca" Shine alaqar data hadasu da mikail?,ta yaya zai zama mutumin banza yana zaune kudinsa ya tafi ta qazantacciyar hanya irin caca?. "Thanks for your effort" Ya amsa masa yana gintse kiran. Still yana shiga dakin daya kama din kiran saddiq ya shigo masa "Hamma......mikail keta neman haduwa dakai......" Idonsa yadan lumshe kadan kana ya bude kaman yadda ya saba a duk sanda ranshi ya baci yake kuma qoqarin hadiyewa "Ya samawa kansa mafita.....koda bai kawo kanshi ba tabbas zan sanya a kawomin shi.......bani da time na ganinsa yanzu......sai zuwa Monday......ka tuntubi Easter kan investigation da na saka suyi cikin company" "Itama tayi dropping min massage.....tace in sha Allah zuwa Monday din komai zai kammala" "Alright" Ya amsa a taqaice kanshi yana sake shiga rudani. Wannan din shine abinda ya zurfafa tunaninsa cikin jirgin,har sai da farouq ya magantu "Wani abu ya sake faruwa ne?" Idanunshin da suka sauya launi ya bude a hankali sannan ya girgiza kai "Nothing.....kawai dai kaman akwai abubuwan da nake ganin ba haka ya kamata su tafi ba.....but everything will be fine". Kai farouq ya kada masa yana dubansa da kyau "Whenever you need assistance........kada ka manta farouq na side dinka.....am ready to be a good partner". Dan qaramin murmushi ya sakar masa yana gyada kai "Na sani tuntuni". Tun kafin sabreen tayi nisa da gida ta zura hijabinta zuwa gurin daya gaya mata ta duba zaya ajjiye mata sabuwar waya torch. Yadda ya kwatanta matan haka ta sameta a wajen,ta dauketa cike da murnar zataji muryar da tayi kewa qwarai ta wuce zuwa gida. Murmushi ya saki bayan informers dinsa dake wajen ba dare ba rana sun shaida masa abinda ya faru "Yadda zaki bare sabuwar wayar nan yarinya haka zan bareki nan da kwanaki uku kacal masu zuwa" Yayi maganar cikin shauqi da wassafa ta yadda a ranar zaici karensa babu babbaka,ya dauki tiyo dake maqale da bututun tukunyar shisha ya zuqi hayaqin har cikinsa ya fesar,sannan ya kalli matashin dake gefansa. "Aikinka na yau tunda ta dauki wayar zai fara da tura mata zazzafan saqo da zai nuna asalin kewa da shiga rudani da rashin jin muryarta" "An gama oga" Ya fada yana bude wayar ya fara abinda aka umarceshi,shine kuma kwangilar daya dauko takanas zai yiwa naseer din. Jikinta har rawa yake sanda ta kunna wayar saqon ya shigo. Tana gama karantawa taji idanunta sun cika da qwalla,tausayinsa ya cikata. "Allah sarki bassam.....bazan sake yarda adda sabreen tayi silar yin nesa dani ba" Tayi maganar yana yunqurin kiransa saiga nasa kiran ya shigo. A yadda ya marabceta a yau din sai da zuciyarta tayi narkewa da qwalla ta fita. "Tun daga ranar bani da lafiya huda.....fargabata na mutu ba tare dana cika muradan zuciyarmu ba....baqincikina kuma sai na jima a kushewata qilan kafin labarin mutuwata ya riskeki....." "Allah ya kiyaye.....in sha Allah ba zaka mutu ba" Ta fada muryarta tana rawa tana tuna yadda ta rasa abbanta da umminta,yanzu kuma sai ace shi?. "Ganinki ne kawai zai sanya na warke huda.....ki taimkeni muddin kinaso na farfado naci gaba da rayuwa kizo na ganki" "Bansan gidanku ba.....bansan inda zan ganka ba" "Indai zakizo din huda zan tura miki da adress....ki taimakeni kizo......amma karki takura kanki daga nan har zuwa litinin,har sai kin gamsu da kanki na cancanci kizo din na ganki.....". Ko kusa ko alama bata ji saukar damuwa saman zuciyarta akan mashur ba,wanda ta tabbatar ta masa gagarumar barnar da zaiyi wahala ya maida gurbinta. Wani tabbataccen labari data samu a daren jiya akan mashkur shi daya ya qara mata qwarin gwiwa da jin cewa ya cancanci ta rabashi da komai da yake sanya shi jin xai iya shiga ko bata rayuwar dukka diya macen da yaso a sanda yaso. Da confidence dinta take takowa zuwa cikin gidan nasu. Kamar ko yaushe bata damu d kallon me kallo ba......bata damu da hasashen me hasashe ba......hakanan bata damu da zunden me zunde ba,ta keta a hankali har ta isa qofar dakin nasu da tayi tsammanin samunshi a bude saboda lokacin lokaci ne da tasan suna makaranta a irinsa. Da mamaki hadi da wata cakudaddiyar fargaba ta murxa qofar ta tura ta bude tana shigewa,saita samu kanta da takawa a hankali har zuwa qarshen falon. Ba kowa,kuma wajen yana tsaftace kaman kullum,don haka ta juya tana sanya kanta cikin dakin tana mamakin waye yake magana haka kaman masu gulma?. "Nayi maka alqawarin xuwa ka ganni muddin ba'a wata qasa kake ba.....zanzo har inda kake don ka tabbatar da ingancin son da nake maka!". Qididdigaggun jimlolin da suka zamewa sabreen tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta. Wuta ce gaba daya taji ta dauke mata sanda take iya hasken waya a kunne huda. "Anya huda ce?,meye hakan yake shirin faruwa?,d waye take magana haka?. "Waya" Taji an rada mata cikin kunnuwanta,abinda ya sanyata xabura ta kuma sanya hannu ta yaye blanket din da hudan ke ciki,take ta bayyana kwance maqale da waya tana ta doka murmushin samun abinda zuciya takeso. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 87 Bayyanar haske cikin duhun blanket din ya sanya huda zabura,haduwar idanunta kuma dana sabreen ya sakata miqewa cikin matuqar kaduwa da zabura har wayar na neman subucewa,saidai kuma kafin yakai qasa sabreen din ta sanya hannu da zummar tarota,abinda ya bawa huda qaimi itama takai nata hannun don bawa wayar kariya. Sabreen din ta rigata samun nasara,batayi wata wata ba ta sanya wayar a kunnenta,lokacin da Naseer keta faman maimaita kalmar "Hello......hello baby?" Wani abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafafunta. Wannan muryar ba baquwa bace a wajenta da zata iya bacewa daga kwanyarta.......ba muryar naseer ba......maza da dama da suka taba shiga qaddarar rayuwarta,suka kuma ratsa ta DUNIYARTA bata wasa da komai daya shafesu bare ta bari ya bace mata "Nnn......" Tayi niyyar furtawa,sai kuwa ta dunqule maganar ta hadiye ta maidata cikinta,ta sauke wayar tana katse kiran sannan ta maida dubanta ga huda dake tsaye tana fuskantarta idanunta fes kan fuskar sabreen. "Ki bani wayata adda" Ta tattaro dukka qwarin gwiwar daya rage mata ta furta tana miqawa sabreen hannu. Saidai maimakon ta bata wayar yadda ta buqata sai ta maye gurbin hakan da ajiye mata lafiyayyen mari saman fuskarta,sanda take yunqurin maido hayyacinta cike da matsanancin mamaki ta sake sauke mata wani marin a daya kuncin nata. Gigicewa tayi duka ta sanya hannayenta ta dafe kuncin nata gaba daya,wannan baiwa sabreen din ba cikin matsanancin fushi ta turata ta koma saman gadon tayi zaman dabaro sannan ta bita tayi tsaye a kanta tana damqe hannunta a cikin matuqar dimuwa da gigita. "Kinsan waye wannan?,kinsan waye kike tare dashi huda?....kinsan hadarin da kike shirin jefa rayuwarki dama mu gaba daya?,kinsan waye Naseer?!" Taqarasa fada idanunta a waje sosai suna nuna girma da yawan bala'in data tarko musu. Gaba daya ido ta zubawa sabreen din tana mamakin maganganunta "Wayeshi din?" Hudan ta fada zuciyarta a tsaurare. "Ba sunanshi naseer ba,sunanshi bassam". Ta sake fada tana ji a ranta ya kamata itama tayi tsaiwar daka har sabreen din ta fuskanci nata zabin. "Basma......bassam.....innalillahi" Sabreen ta furta duka a tare tana komawa qasan dakin gaban hudan ta zauna jabar. "Tun yaushe kuke tare?,kun taba haduwa?,shine ya baki waya?,dame dame yake gaya miki?,tun yaushe kike waya dashi?!" Tayi maganar wani irin zafi yana taso mata daga qasan zuciyarta. Iya kallon da huda ke mata.....iya abinda take gani daga idanun hudan kawai sun isa bata amsar zuciyarta ta fara soyewa. "Dake nake magana huda!" Ta furta da wata gigitacciyar tsawa data ratsa hudan ainun ta cakude da radadin marin da baibar fuskarta ba har yanzu. "Ki barni yaa sabreen.....ki barmin zabina......bassam ya cancanta,shi nakeso kuma yayimin alqawarin bani kulawa kaman yadda iyaye ke bawa 'ya'yansu......banyi wani abu da ba daidai ba fa,kema kin tsara rayuwarki ne daidai yadda kikeso......kina kuma abinda kk ga dama a sanda kikeso.....ni ko nadra ko haneefa akwai wanda ya taba tsaidaki ko ya hanaki?,ni mene ma nayi?,abinda ban taba wuce layin bayan gidanmu ba?,ban taba zuwa hotel ko joint joint ba.....ba'a taba ganina da wani d'a namiji a cikin mota mun kebe b.......". Sake saukar wani lafiyayyen marin da yafi na dazu shi ya daukewa huda dukkan wata kalma da zata ci gaba da fita a bakinta. Marin da wannan karon ya jawo digar jini daga hancin hudan,muryar sabreen din kuma dake shaking tace "Huda?.....kinyi hauka ne?,eh idan ma haukar kikayi kisan wadanne kalamai zaki gayamin.......nice sabreen da na baki tazarar shekara kusan biyar cikin rayuwarki.....nice sabreen da na sadaukar da walwalata farincikina da martabata saboda kuji dadi!....nice sabreen dana hana muku kuka......nice sabreen dana hana muku jin yunwa da wulaqanta.....nice sabreen dana zame muku garkuwa......nice sabreen dana maye muku gurbin uwa da uba wanda kece ta farko daya cancanci ta zama shaida akan hakan......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu na shaawa ko burgewa a jikinki da d'a namiji zai gani ya burgeshi......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu da zaki amfana mini face zallar qauna da 'yan uwantaka fa fisabilillahi......wanne sauran kulawa kike buqata da ban baki ba?,wacce sauran qauna ce da tafi wannan girma da fadi?......soyayya huda?.....kin san wanne abune da yafi tarwatsa rayuwar diya mace?,kinsan wanne abu ne yafi zama girman nadama cikin rayuwar 'ya mace?,kinsan mene ne mabudin nadama......wahala da azabtuwa da zuwa da qaddarar da bata sauyuwa cikin rayuwar mace?......ba komai bana face SOYAYYA kuskure na gaba da rayuwar kaso casa'in dake afkawa shine AURE......namiji!.....bashi da imani......bashi kuma da tausayi.....namiji BUTULU ne dake iya bijirewa halasci komai girmansa.......namiji halittar data fi kowacce halitta son kanta cikin duniya.....halittar da babu imani cikin ruhinta ta fannin azabtar da ruhin diya mace.......samun salamar rayuwaki ki rayu ke daya.....baki saka kanki cikin sabga ko sha'anin kowanne d'a namiji ba......wannan wani karatu ne da rayuwa tayimin bayan gushewar abba da ummina.....mutum na farko da ya fara qoqarin bata rayuwata shine ALHAJI LAWAN......" Da wani irin kallo huda ta dubi sabreen,saidai ta kasa furta komai "Eh....alhj lawan maqoci kuma aboki ga mahaifinmu,......tun daga wannan rana na fara karatun waye namiji?,daki bayan daki kinsan komai kafin na fara sakaya wasu al'amuran daga idanunki saboda samun damar saituwar tunaninku.....huda!......dago kanki ki kalleni da kyau!" Ta furta da gasken gaske,abinda ya sabbabawa hudan duban nata da idanunta da suka hada hawaye masu yawan gaske "Ba suna kirana karuwa ba?,ba cewa suke ina yawon ta zubar ba?,ba cewa sukeyi nayi cikin shege yafi sau a qirga ba?,ina bin maza?,ina sata?,ba haka suke bada shaida ba?......to na barsu da Allah na kuma barsu da ranar da zasu tsaya gaban Allah su baida shaida akan hakan......ni aminatu ahmad na rantse miki da girman Allah ban taba bawa kowanne d'a namiji kaina ba.....ban taba sanin d'a namiji ba ban taba kwanciya da kowa ba,idan kuma na taba....." "Aah yaa sabreen" Huda da kuka ya kecewa ta fada da hanzari tana dora hannunta saman bakinta yayin da dukka hannayenta ke rawa. Wani qauna da tausayi na 'yan uwantaka ke tsirgawa kowannensu. Daga ita har huda din hawaye ne da kuka ya ballewa kowannensu har zuwa wani lokaci "Me yasa kika boyemin wani abu daya shafi rayuwarki huda.....bayan hudubata kullum a kanku itace.....komai girman matsala ko qanqantarta.....kome girman abu da qanqantarsa da kukaga alamun zai afka cikin rayuwarku.... Alkhairi ne a idanunku ko sharri ban yarda a boyemin ba?.....kinsan wayeshi?". Kai kawai huda ke kadawa ragowar hawayen idanunta suna sauka tana jin wani abu maras dadi cikin qirjinta "Sunansa na asali shine naseer bawai bassam ba......yayi amfani da sunan bassam ne saboda sunan dana bashi nawa shine basma a madadin sabreen......dila ne na qwayoyi da cocaine da dukkan wani nau'in kayan maye,yana dillancinsu da safararsu zuwa qasashe masu yawa ta wannan qazantacciyar hanyar ya tara duk wata dukiya da yake qafafa da ita. Ya qware ainun wajen ta'ammali da mata duk kalar wadda ranshi yayi mishi.....yarinya ko babba musulma ko Christian,koda kuwa ba harkarki bane idan wani abu a kanki ya darsu zai sanya a dauko masa yarinya yayi mata fyade......a irin haka muka hadu,kuma na zama sanadiyyar daya buga gagarumar asarar da har yau ya kasa murmureta bayan kuma ba haka ya tsara ba......yayi zaton ya samu irin matan barikin da zai kashema kudi ya gama da tenure dinsu ya sallamesu........tashi d'aya na bace masa bat......yana da balain naci da bibiyar da nayi imani ita ta bashi daman gano ni wace da inda nake......yayi nufin yin ramuwar gayya ne a kanki huda....saidai kuma naci alwashin sai nayi silar qarar da ragowar rayuwarsa a gidan maza tunda har bai daddara ba ya dawo cikin hurumina.......yaso kuma taba killataccen gold din da hannu vai isa yakai gareshi ba". Ta sani ta kuma dade da sani zantukan adda sabreen kamar rubutu ne saman dutse.......bata qarya komai runtsi komai wahala,don haka maganganunta akan waye bassam naseer sukayi matuqar tsoratata. Jikinta ya sake daukan rawa.....wannan shine dalilin da ko yaushe yake qoqarin yadda zai shirya haduwarsu tana rushewa?. "Ki rabu dashi don Allah adda.....kada ki sake jefa kanki cikin hadari.....". Bata saurareta ba ta jefa mata wayartata zuciyarta na mata wani irin ciwo da kuma son daukar fansa "Bakin alqalami ya riga ya bushe......kirashi ki jaddada masa zaku hadu da yammacin litinin,saidai kice kina tsoron kada a gane kin fita a gida.....kuna da event a wani guri dab da wajen acan kikeso ku hadun" Tayi maganar tana qoqarin yago paper cikin wani memo dake saman bedside din hudan tana rubuta mata sunan wajen. *_LITININ DIN DA MUTANE DA YAWA SUKA CIWA BURINTA.....LITININ DIN DA ZATA ZANA QADDARORI CIKIJ RAYUWAR WASU,WASU QADDARORIN KUMA DA SUKE ZAMA MABUDIN QOFOFI MASU TARIN YAWA GA RAYUWAR WASU.....MABUDIN FARA GWAGWARMAYA DA TIRKA TIRKAR DA ZATA JA MANA RAGAMA HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN.....ZAMU GANI WAYE LITININ DIN ZATA ZAMEWA FARAR RANA KO AKASIN HAKAN?_* _KUCI GABA DA BIBIYAR 'YAN MUTAN HUGUMA_🥰🥰🥰 *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *_Matsalarki inda zaki samu ingantattun kayan kitchen na kece raini cikin farashin rangwame da rahusa me kama da KYAUTA?_* *CHINA* *DUBAI* *INDIA* _Duk kasu a sanqame a waje daya,amintattun kaya nau'i daban daban masu daukar hankali don qawata kitchen,siyan daya ko sari_ *_Ko damuwarki kayan kitchen DESIGNERS na alfarma da kece raini?_* *_maza garzaya cikin gidan HUGUMA UTENSILS UNIVERSE,domin kuwa ta shirya tsaf dom share muku hawayenku da galla gallan kayan kitchen cikin qanqanin farashi_* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub __________________________ PAGE 88 Lokacin da motarsu ke shan kwanar layin nasu wayarsa ta dauki tsuwwa. Kaman bazai dauka ba amma sai ya miqa hannunsa,saboda duk kiran daya shigo ta wannan wayar yana da tabbacin yana da alaqa me qarfi dashi. Sunan Musaddiq ne ke yawo saman screen din. Ya sake zama sosai yana daga wayar sannan ya karata a kunnensa. Kafin yace komai muryar Musaddiq din da sautin sallama ya ziyarci kunnensa. Ya amsa masa a nutse. "Hamma kun dawo ne?" Ya tambayi fu'ad din "Muna dab da shiga gida.....wani abu ne?" Siririyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Hamma muna asibiti" Yanayinsa ne yadan canza kadan ya bude baki yana tamba cikin fargaba "Asibiti?,kai da wa?,waye ba lafiya?" "Maamah ce hamma......muna dawowa nida abba saiga kira da asibiti.....wai an kai ta ta fadi" "Ta fadi?" Ya maimaita kalmar cikin mamaki "Eh hamma" Shuru kaman bazaice komai ba,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya "Me ya sameta?,ko kuma me sukace yana damunta?". Kai Musaddiq ya girgiza yana sauke idanunsa akan hajja harira,sai ya miqe kuma a hankali yana tura qofa ya fice daga dakin. "Wasu bayanai likitan ya fara,saidai yace yana da buqatar ganinmu ni dakai a tare don yayi mana gamsashen bayani" "Alright.....zan shigo" Ya amsawa Musaddiq yana sauke wayar a kunnensa. Guri daya ya zubawa ido yana kallo qwaqwalwarsa na tafiya zuwa wani nazari. Ya bude bakinsa a nutse da zummar bawa driver umarnin wucewa asibitin,sai kuma ya lumshe idonsa yana tuna wani abu daya faru a shekarun baya wanda sai daya sanya shi sauke wani numfashi me nauyi,kana a hankali ya hadiye kalmarsa yana maida idanunsa ga gate din gidan da suke dosa. "Waye a asibiti ba lafiya?" Farouq da yake amsa waya sanda fu'ad ke wayar ya tambaya bayan ya kammala wayar yana duban fu'ad "Maamah ce" Ya bawa farouq din amsa a gajarce ba tare daya kalli farouq ba. "Maamah kuma?,amma inaga ya kamata ace mun juya akalar tafiyar tamu zuwa asibitin ko?" "Ba yanzu ba farouq.....na gaji,sai na huta tukunna......kaina kaman zai tsage da abubuwan dake cushe akai". "Duk da hakan bai zama hujja na kasa zuwa dubata ba.....ka huta din idan mun dawo......janar....." Ya qwallawa driver nasu kira wanda ya rage gudun motar saboda kawowarsu tafkeken gate din gidan alhaj hamza kibiya "Sir" Ya amsa masa a a ladabce "Juya motar nan mu koma titi" Ya bashi umarnin idanunsa saman wayarsa yana lalubar number wayar Musaddiq don yaji a wanne asibiti suke?,don ya tabbatar yace fu'ad zai tsaya tambaya zai bata lokacinsa ne kawai. "SAMHG hospital kuke?" Ya tambaya Musaddiq ga zaton suna can din. Kebantaccen asibiti ne da ake duba iyalin gaba daya bayan asibitinsu na cikin gida da fu'ad keson maidashi babba ya fadadashi sosai cikin sabon ginin mansion house din da yake musu yanzu haka "Okay.....turon address din" Ya fadi yana kashe kiran. A haka zakayi zaton kunnuwa da hankalinsa basa tare da farouq din,saidai kuma har yayi wayar ya gama yana saurarensa. Ta yaya za'a kaita wani asibitin da ba nan ne asalin inda kowa yake zuwa ba?. Tambayar da ya samu wani guri na musamman cikin kwanyarsa ya adanata. Kira farouq din ya sakeyi,a wannan karon anni ya kira. Dab da zata tsinke ta daga da cikakkiyar sallama da muryar nan tata ma'abociyar kwarjini da nutsuwa. "Mun dawo anni.....amma mun wuce asibiti dubiya,kada ki jimu shuru" "Waye ba lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa "Maamah ce" Ya amaa mata kai tsaye "Subhanallahi......amma ba wanda ya sani cikin gidan nan......ince ko jikin nata da sauqi?" "Ban sani ba anni,sai munje yanzun zamu gani" "To don Allah kuyi mata sannu,idan akwai wani abun kuyi gaggawar sanar mini" "To anni" Ya amsata yana sauke wayar. Dubansa yakai ga fu'ad,har yanzu waje daya yake kalla,yadda yayi dif kaman baya wajen,haka fuskarsa ta nuna kaman baisan me ake magana akai ba. "Fu'ad" Farouq ya kirayeshi sanda suka isa farfajiyar asibitin,guards dinsa kuma nata kai da kawowa wajen tabbatar da tsaron wajen kafin fitowarsa. Idanunsa dinnan masu bala'in kwarjini ya daga ya zubewa farouq su. Yanayin kallonsa yana da matuqar kaifi da saukar da dafi,idanun suka so yiwa farouq din kwarjini,saidai wannan din ba baqon abu bane a wajensa,abune da ya riga ya saba dashi tuntuni. "Ako yaushe ka dinga tuna cewa taci albarkacin kalmar UWA.....zata kuma ci gaba da cin wannan Al Farmar koda meye tayi maka" Idanunsa yadan ragewa kaifi kaman zai lumshesu sai ya fass,ya sake budesu sosai saman fuskar farouq din. Wannan maganar inda farouq din yasan mugun famin da ya yiwa ciwonsa da baiyita ba,har maqogoronsa sai da yaji yawu yana neman daukewa,ya tattara dukka wani yaqi da yakeyi da yanayinsa sannan ya bude bakinsa "Inda ace a yau za'a zare wannan kalmar tsakanina da maamah......da har abada ba zata sake ganin fuskar muhammad fu'ad ba muddin kuwa ya haifu daga tsatson jadda.....a lokacin daya miqa mata dukkan soyayya da yarda......a lokacin ta nuna masa cewa DIYA MACE MAYAUDARIYA CE.....BA KUMA ABAR YARDA BACE,bata barshi haka ba har sai da tayi silar......." Ji yayi bazai iya qarasawa ba.....ji yayi wannan sirrin bazai iya furtashi ga kowa ba,sai kawai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya zura qafafunsa yana fitowa ba tare daya jira me budewar ya bude masa ba. Tun bai qaraso bakin qawatacciyar balcony din da aka yiwa dakin ba musamman saboda shan iska da hutawar me lalura da me jinya ba ya hangeta zaune ta hasken fitilun da aka wadata wajen dashi. Kanshi ya dauke sarai,yana jin har qasan ransa ya washi matar. Ba zaya gaya mata gogayya da duniya ba.....kaman yadda bazai gaya mata sanin takan duniya ba. Bata tunanin akwai wani yanayi da zai nuna mata a yanzun da zai tunzurata ta janye rayuwarta daga cikin tasu har sai ta cimma nata gacin. "Sannu da zuwa.....ashe ka qaraso" Hajja harira ta furta cikin tsananin nuna kulawa tana miqewa daga saman kujerar da take kai. Kanshi ya dauke yana maidawa ga Musaddiq daya taroshi tun daga farkon balcony din "A nemo likitan......yazo da gaggawa don ina da abunyi" . Sosai maganar ta daure kan hajja harira wadda kwarjininsa ya hanata sake cewa komai. Lallai ya kamata kafin ta zurma kanta da yawa ta sake karantar kowanne taku da motsi nasa domin samun isar muradinta cikin sauqi. "Waye a cikin dakin?" Ya sake jefa tambayar ga Musaddiq. Saidai kafin wanda aka yiwa tambayar ya amsa hajja hariran ta rigashi amsawa cikin matuqar alhini "Basu barin kowa ya shiga don har yanzu ma bata farfado ba". Duba daya tak ya yiwa hajjan yayi taku uku ya isa gaban dakin,ba tare da jiran umarni ko bada dama ga kowanne likita ba ya murza handle din ya tura kansa ya shige. Daga bakin qofa ya fara tsaiwa,ya harde hannayensa a qirjinsa yana qare mata kallo. Tana kwance cikin lallausan blanket da aka rufeta dashi har zuwa qirjinta. Ba qarin ruwa babu na jini.....baiga oxygen ba,saidai akwai canola daya kula da ita a hannunta. Idanunta a rufe suke,a haka tafi kama da me bacci. Sake nutsa idanunsa sosai yayi saman fuskarta yana karantar fuskar bayan wucewar kowacce daqiqa har ya samu matsaya cikin zuciyarsa dangane da ita,ya sauke hannayen nasa yana sake qarasawa ciki,takun likitan kuma sai ya biyo nasa takun. Fasa qarasawa yayi bakin gadon,ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa ya waiwayo a nutse yana amsa sallamar likitan gami da zube masa idanunsa. Dan tsamurmurin likita sanye da lab coat,hannunsa kuma riqe da wani file,yayin da wuyansa ke rataye da abun auna gudun zuciya. Ta cikin farin gilashin idanunsa ya kalli fu'ad. Kallo qwaya daya tak daya mamayi zuciyar likitan da wani irin mahaukacin kwarjini tare da zallar mamakin wanzuwar muhammad jadda cikin asibitinsu. "Meye ya kawo mamallakin jadda diamond chore resources asibitin?" Ya tambayi Kansa da kansa tsoro da kwarjini suna cikashi. "Kada dai ace da gaske suke da suka gaya masa ita din mamarsa ce?" Wannan maganar ta sake tsarga masa wanda hakan ya sake sakashi jin rudani yana mamayarsa. Yasan waye muhammad jadda,bazaiso kuma fadawa matsala dashi ba,ba zayaso fadawa hurumin da ba nashi ba da karatunsa daya samu yake riqe kansa da iyalansa. "Shine likitan?" Fu'ad daya gama qarewa likitan kallo ya furta yana duban musaddiq daya qaraso daga ciki yayi tsaye gefan fu'ad din "Shine hamma" Ya amsa masa shima yana maida dubansa kan likitan. Duk wani qoqari nasa ya tattaro,ya kalato yawun bakinsa yana dora murmushi saman fuskarsa "Barka da zuwa asibitinmu yallabai.....munyi farinciki da shigowarka yau asibitinmu......hakan ba qaramin qarin kima da martaba bane ga asibitinmu damu kanmu gaba daya". Hannayensa zube a aljihun wandonsa,kamar yadda idanunsa suke a Kan likitan. "Madalla.....inason magana dakai if possible" "To......ba damuwa.....ba matsala hakan,muje ne ko a nan zamuyi?" Yayi tambayar yana raba idanunsa tsakanin fu'ad din da musaddiq. "Qaraso ka duba patience dinka". "Aah yallabai..... Ai ba za'a barka a tsaye kana jira ba.....hasalima ban jima da fita a dakin ba ai". A nutse ya debe dubansa daga kan likitan,sannan ya fara takawa a nutse yana fita a dakin musaddiq ya mara masa baya. A hankali yaci gaba da takawa yana fita a asibitin. Bai dakata ba har ya isa inda motarsa ke ajiye. Kafin ya qarasa daya daga cikin guard din ya zabura ya bude masa sannan ya jira isowarsa "Kada ka rufe.....zanga baqo" "Yes sir" Ya fadi yana barinta a bude kaman yadda ya buqata. Budewar data bash daman kallon likitan da kuma karantar kowanne motsi nasa cikin wani kallo da ba na kai tsaye ba wanda ke cike da hikima. Wani irin bugu zuciyarsa keyi musamman sanda ya tsinci kansa tsamo tsamo tsakanin Jordan da abdulbasit da suka kusa rufa tsahonsa. Ya daga kansa yana duban fuskokinsu da suke manne da baqin gilashin idanu. *D U N I Y A T A* *_D U N I Y A T A_* Page 89 ________________________ https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz *_assalamu alaikum warahmatullah_* *_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_* *_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_* *_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_* Shadda Laces Atamfa Kayan yara English wears dana jarirai Qawatattun handbags Mayafai Abayas da jallabiyas Inner wears Huluna na maza da mata yara da manya socks Takalma na maza da mata yara da manya Lafayas Sarqoqi agoguna banguls da rings _kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_ _bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_ *_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_* *_masu manyan qarfi da matsakaita?_* *_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_* *_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_* *MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA* *_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_* *_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_* *_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫶🏽🫶🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽 https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr _________________________ PAGE 89 "Enter" Jordan yace dashi yana jiyowa sosai gareshi gami da nuna masa cikin motar. Bashi da abunda zai ce don shi kansa yasan nan din ba wajen wasa bane,ya daga qafafunsa da yaji sun fara masa nauyi yana sanya jikinsa cikin motar,yana kuma jin yadda gumi yake tsargo masa daga kowacce kafa ta jikinsa. Set din dake opposite nasa ya masa nuni,hakanan ya zauna yana qoqarin gyara lab coat dinsa yana hadiye wani miyau me kauri. Idanu kawai fu'ad din ya sake zuba masa duban daya sanyashi kasa nutsuwa ya dinga gyare gyare,daga gyara agogo zuwa gyara rigar jikinsa da kuma hannun rigar. A nutse ya janye masa idanun,sannan ya motsa bakinsa "Ya sunan doctor din?" "Ni....Dr kamal......sunana Dr kamal". Kai fu'ad ya jinjina yana lumshe ido gami da budesa sanan ya maimaita sunan a hankali "Good Dr kamal,ina maka murnar samun damar zama likita ga mahaifiyata......am.....inaso nasan da meye da meye suka ce ka gaya mana a matsayin cutar dake damunta?". Sosai maganar ta rudashi saboda tazo masa a bazata,ya dubi fu'ad yana qoqarin nuna masa gaskiyarsa "Su waye?.....Ni ba wanda yacemin ga abinda zan fada sai abinda bincikena ya gano". "Kamal!" Fu'ad ya kira sunansa da wata irin deep voice dake dauke da amo me tsoratar da wanda ake magana dashi. "N...na'am" "Lookat me......" Ya sake fadi masa yana tsareshi da idanunsan nan da suke sanya Dr kamal jin kamar zaya narke. "Kayi haquri yallabai" Dr din ya sake fada kansa tsaye ba tare da fu'ad din ya sake cewa komai dashi ba. Wani irin rudani da firgici suna ratsashi.....gaba kura baya sayaki,yasan hajja harira ba sanin shanu ba,amma ta yaya zai yadda yayi jayayya da mutum irin muhammad jadda din?,wanda yayi imanin ita kanta inda hajja harira ta gama sanin wayeshi da kyau ba zata saka kanta cikin wannan wasan ba. "Yallabai......sunce zasu biyani bayan barazana da hajja harira tayimin......sunce na kwantar da ita kawai na saka mata ruwa wanda zai qara mata kuzari ne kawai...........sunce tabbas zakazo...idan kuma kazo din na kambama ciwo da kyau,na nuna muku zaman kadaici da kewa ce take damunta,wanda muddin ba'a kula da ita da kyau ba.....an samu wani cikin wadanda sukafi kusa da ita take kuma yawan ambatarsu su zauna tare da ita ba to tabbas zuciyarta zata iya bugawa ayi hasararta......sunce idan.....". Dakatawa yayi ba tare daya qarasa fadin abinda zai fada din ba saboda daga masa hannu da fu'ad yayi. Shuru ya ratsa motar,abinda ya sake ruda Dr kamal,ya sanya hannun rigarsa yana goge gumin fuskarsa bayan ya cire gilashin idanun nasa. "Sauka kaje....kaci gaba da riqeta.....zaka sallameta,but sai daidai lokacin da na baka umarnin yin hakan" "Okay sir" Ya fada da gaggawa yana juyawa gami da laluben hanyar fita daga motar,don zaman motar duk da laushin kujerunta da sanyin Ac da wani ni'imtaccen qamshi da yake fita......amma ji yakeyi kaman yana zaune ne cikin qabarinsa. "Dr" Ya sake kiran sunansa dab da zai sanya qafafunsa a qasa. Adan zabure ya waiwayo yana qoqarin saita kansa. "Banda wannan harqallar.....ka tabbatar babu wata sauran haramtacciya ko miyagun harqalloli da kakeyi a boye......don idan hakan ta kasance ka tabbata ba zaka tsira a hannuna ba" "Wallahi ranka ya dade ba ruwana......ni din mutumin kirki ne ka tambayi kowa ma" "In kuwa hakane ka kyautawa kanka". "Sauko malam" Jordan yace da Dr kamal din a dake cikin rashin son wasa. Jinsa ya dinga yi kaman zai kifa sanda yake komawa cikin asibitin. Inda ace yasan da gaske take ita din mahaifiyarsa ce ta yaya zaiyi wannan kasadar?. Fadan giwa da damusa waye yake shiga?,sai wawa sai mahaukaci,shi kam qaura zaiwa asibitin bazai sake shigowa ba sai gobe,duk da yasan bashi da inda zaije yace ya guje masa. Duk wani mamaki da maamah zata bashi a yanzu ya biyo bayan wanda ya gani a yanzu da shekarun rayuwarsa ta baya. Ko daya bai sake komawa asibitin ba,saidai kuma bai hana kowa zuwa ba. A kwanakin ma gaba daya yana qoqarin ganin ya gyara wasu abubuwa da yake ganin suna qoqarin tasowa can qasan kamfanin,wanda idan har ya bari matsalar tayi girma zata iya jawo asara mafi muni fiye data kudadensu da suka zirare. A cikar ranar lahadi kusan kowanne bayani ya kammala samunsa,ya shigar da komai cikin documents,sai la'asar ya kammala,don haka daga nan alwala yayi ya wuce masallaci. Daga masallacin ya sake dawowa gida,ya leqa anni da bata jima da dawowa duba maamah ba,sai ya zauna falon bayan ta sanya amna ta dama masa yoghurt da fura. "Muhammadu" Anni ta kirasa,sai ya dauke idanunsa daga tasha alhadath dake nuna yadda bani Israel ke dake ragargazar Palestinian,hankalinsa ya fara nisa kan hanyar da zai aika musu tallafi ya kuma isa garesu kai tsaye "Na'am" Ya amsawa annin yana dubanta "Jiya abbanku ke complain....ko sau daya ance ba'a ganka a asibiti ba......ni kaina ko sau dayan banji kace zaka je ba,sai zama da kaketa yi a sassanka?". Hannu ya sanya ya karbi kyakkyawan tray din da amna ta jero cups da bowl me kyau dake dauke da dammen yogurt din,ya aje gabansa yana cewa "Thanks lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki,ta juya tana komawa kusa da anni ta zauna. "Jikin nata da sauqi ai anni......infact ma tun ranar ta samu lafiya.....yau ma zasu sallameta". Ya amsa ba tare daya kalli annin ba,don yasan yana yin hakan zata dago wani abu "Duk da haka muhammad wannan din baiyi kyau da tsari ba....." "Yanzu daga nan can zanyi anni kiyi haquri". Kalmar haquri idan ya fadeta da gaggawa haka to tabbas baison bacin ran annin ne,ta gama karantar hakan. Jujjuya furar yayi sannan yayi bismillah yakai bakinsa. Fuska yadan bata ya daga kai yana duban amna "Yaushe kika koma sakamin sugar a abin sha?". Kai tadan langabe "Hamma.....kadan fa na saka maka wai don bakinka yayi taste" "Zoki dauke abarki" Ya fada yana dan ture bowl din. Da sauri ta miqe tana fadin "Ayyah hamma.....kayi haquri kada magauta suji kanmu....bari na hada maka wani wannan sai BB farouq yasha" "Kayi zaton amnan taka tayi hankali ne?,kaima kai ka sowa kanka wannan gallafirin......wai sai yaushe zaka fidda mace ne Muhammadu?,bakasan duk girman namiji aure shike cikashe wani gibi ba?,gibin da babu abinda zai cikeshi face auren?......ita kanta amna yaushe ta fara iya riqe abinda ya dace da itama ballantana ta riqe abinda ya dace da waninta?". Waiwayowa tayi tana duban annin kamar zata saki kuka "Wayyo anni.....yanzu duk qoqarin da nayi baiyi ba?,hamma don Allah ban canza ba?" Wani sassanyan murmushi ya kubce masa,ya maida kallonsa ga anni "Tsokanarki fa anni takeyi.....kin canza sosai amna ta,kinyi kuma hankali,yauma nasan akasi aka samu,ki dama min wata ki sakamin apple a ciki da grapes ki ajiyemin,idan na dawo zan sha". Tabe baki anni tayi tana kauda kanta " Ai daman.....indai abu da laifin amna duk girmansa saika maidashi qarami......da tashi kayi kaje ka shiryadinma da zaifi maka". Murmushi ya saki ya miqe a nutse. Duk wani jini na anni girmansa yake gani martabarsa yake gani hakanan qaunarsa yakeyi. "Hamma na shirya na rakaka?" Ta fada tana tallafe da tray din. Bayason zuwa da ita,saboda ya tabbatar ba zata samu marabtar data dace da ita ba,amma bazai iya cewa bazaije da ita ba,don haka yace "Ki shirya.....but be fast....banson jira" "Yanzun nan hamma" Ta fadi tana qara hanzarin barin wajen. Suna hanya tana cikashi da labarai kala kala wanda hakan yake masa dadi da debe masa kewa. Don amna din wajen quruciya da sakalci irin na autanni ba daga baya take ba. Koda suka isa cikin asibitin sai ya kalleta "Ko ki zauna a nan,ko na yiwa Jordan magana ya kaiki ki zabi duk abinda kikeso.....kina da 30 to 40minutes" "Yay!.....thank you hamma na" Ta fada da tsananin murna. Zaune take daga bakin gadon da kwata kwata cikin kwanaki ukun a duniya taji ba abinda ta tsana sama da kwanciya a kansa. Kwanciyar da babu alamun nasara a tattare da ita,kwanciyar da bata amfaneta da komai ba saima sake haska mata rashin nasararta muraran da ake sakeyi. "Ba alamun nasara hajja......zuciyata tafi karkata akan na tafi plan C.....a plan C ne kuma nakejin cewa koda sharadina zai zama silar rugujewar fu'ad wannan karon basan sassauta masa ba......a wannan karon a shirye bake na gindaya masa sharadin da nayi imanin bazai iya tsallakeshi ba.....a wannan karon hajja......ban yarda koda da darsawa a rai ba zuciyata ta darsamin wai bazanyi nasara ba.....dole dole dole nasara ta kasance a tsagina.....hajja a yau zan bar asibitin nan,ina da buqatar na huta saman gadona nayi bacci me lafiyar da zai bani damar tsara komai da kyau cikin kwanyata.....na kuma wayi garin litinin da wannan shirin". Kai hajja ke gyadawa tana kuma sake juys Plan C din maamah data tabbatar zaiyi wahala idan ba abinda take hasashe bane ba. "Hakan ma yayi,abun ni kaina ya soma shallake tunani na.....amma mariya anya shima baida hatsabiban da suke masa aiki?" Shuru maamah tayi,ko qwalqwalwarta bata kama muhammad yana biye biyen nan ballantana hankalinta. Tun daga haihuwarsa zuwa tasowarsa kawai tasan ya banbanta da sauran yara,quruciyarsa ma ta daban ce a cikin yara,zuwa sanda ya cika shekara goma cas a sannan ta sake ganin banbanci mabayyani a kanshi. Shigowarsa dauke da cikakkiyar sallama sai ta zama tamkar amsa ga tambayoyin hajja harira. Bakinta yana dan rawa tana kamo amsar sallamar da qyar ta hada kalaman tana amsa masa. A nutse ya tako ciki idanunsa akan maamah din data dauke kanta daga gareshi gabanta tana ji yana faduwa. Haka kawai ita kanta sau tari sai taji ya mata kwarjini,fargabar kada dai ace yaji wani sashe na tattaunawarsu yana cikata. Duk yadda hajja ke qoqarin ankarar dashi tana wanze a dakin ta hanyar jera masa sannu da zuwa amma ta gaza samun hankalinsa. Bawai kuma don baijita ba,aah haka kawai yakejin wani abu na daban game da matar,sannan kuma kwanyarsa a kullum idan ya ganta takan yawaita qoqarin tunata cikin jerin sahun mutanen da yaga gilmawarsu a shekarun da abbansu yake raye. Kaman bai lura da sauyawarta ba,yaja kujera gaban gadon ya zauna yana gaidata. Ta amsa masa tana hadiye bacin ranta. Fada takeson masa sosai ko zata samu sassauci amma kuma idan ta tuna a gobe akwai nata plan din dai ta danni zuciyarta,saidai duk da hakan sai data b'ara "Kasan ina nan amma fu'ad ka banzatar dani?,ko ka manta ba'a canzawa tuwo suna?" "Kiyi haquri" Ya jefeta da kalmar nan da har ta fara tsanarta saboda yawan fitarta daga bakinsa. Shuru yaci gaba da ratsa dakin ba tare da kowa yace da dan uwansa komai ba,kafin daga bisani aka turo qofar. Dr kamal ne,ya qarasa shigowa cikin takatsantsan da tsantseni,wanda dukkan me hankali yana kallonsa zai fahimci hakan. "Kwanciyar haka ta isa?,xaki iya komawa gida?" Ya tambayeta a tausashe saidai kuma kalamai ne masu harshen damo da yawa a ciki. Juyowa tayi tana dubansa maganar tana qoqarin fassara kanta da kanta cikin qwalqwalwarta. Ta zargi wani abu,amma kuma yanzun ba muhallin wannan bane,don haka ta dauke dubanta ta maida kan Dr kamal "Ina buqatar sallama Dr,naji qwarin jikina". " Yanzu in sha Allah" Ya fadi yana bude file dinta. Hannunsa yana dan rawa yayi rubuce rubuce ya maida ya rufe,sai fu'ad ya miqa masa hannu Kai tsaye,yadan kalleshi sannan ya miqa masa file din salin alin. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 90 *_MONDAY_* *_Tushen aiki,ko nasara na tsoronki_* Cike da confidence take shiryawa cikin tsadaddiyar dubai abaya budaddiya data lullube jikinta ainun. Wine color wadda aka qawata qasanta da kuma qasan wandon abayar da wasu irin stones da zare ruwan gold masu daukan hankali. Gaban madubi ta matsa tana saka brush tana sake kwantar da doguwar sumarta me yauqi da rashin cika sannan ta ware madaidaicin mayafin abayar tayi rolling dinsa saman kanta,abinda ya bawa kyakkyawan fuskarta daman fita tarwai ta kuma haska da wine color din abayar jikinta. Siririn agogo ta sanya gold me dan adon wine,wanda yake suwa set da komai nasa,ta taka a hankali ta matsa ta dauki purse dinta da wayarta ke ciki tanata haske. Kiran ta daga ta sanya a kunnenta tana aza idanunta kan huda dake zaune gefan gadon,kai kace mata ket ta zura da gudu "Okay.....gani nan fitowa" Ta furta tana maida wayar jaka sannan ta maida kallonta kan huda. Suna hada idanu boyayyun hawayen dake qasan idanun hudan suka yiwa kansu hanya. "Adda.....ina tsoro" Ta fada tana jin zuciyarta tana nauyi. Taku biyu Sabrina ta isa gabanta,ta kuma kamo hannunta "Duk duniya.....duk wanda yace zai tabaku bazan qyaleshi ba muddin ina da iko da qarfin hakan......ba yau ba,ba kuma sau daya ba ina jan kunnen Naseer yayi qoqarin fidda rayuwarsa daga kaina......ya sanyawa ranshi bai taba haduwa da wata basma ma ba amma baiji ba........a wannan karon ya kamata nayi masa general hukuncin da zai sanya a rage ire irensa baragurbi cikin mutane......kada kiji tsoro,babu abinda zai faru" Ta bata tabbaci tana matsa hannayenta. Iska me zafi maamah ta furzar daga bakinta sanda suka kammala zama saman qawatattun kujerun da aka zuba saboda zaman cin abinci ko shan wani abu ga baqi maziyarta wajen. "Wai nikam mariya.... Meye hikimar tattaunawarmu a nan?" Hajja harira ta tambayi maamah tana kallonta. "Harira.....gani nakeyi kaman akwai wani information nawa da yakeyin leaking.......yadda fu'ad yake samun damar kaucewa kowanne tarko nawa abun yana da matuqar daure kai......inaso mu koma gida da wuri don a yau nakeso A YITA TA QARE!" "Ina saurarenki" Hajja ta furta tana hade yatsunta guri daya tare da bawa maamah hankalinta. "Hajja......aure zanwa fu'ad!" Sosai maganae ta zowa hajjan a bazata,wanda hakan yaso hautsinata tare da haifar mata da fargaba......fargabar yiwuwar rushewar plan nata da rashin cimma interest dinta tsakanin wasan da ake murzawa yanzun. "Aure kaman yaya mariya?,ya samo matar auren kenan?" Kai ta girgiza tana sake matsowa kaman hajja din bata jinta sosai "Ya akayi kanki ya kulle hajja?,zanwa fu'ad aure da yarinyar da duk na zaba masa don ta zamemin tsanin MALLAKARSA". Shuru hajjan tayi wuta tana neman dauke mata. Ba wai kuma mamaki ta shiga ba,aah tanason adan taqin tayi tunanin amsar da zata bawa maamah wadda zata bayu ga tafiyar lissafinta daidai. Duk yadda taso kuma ta kwalkule maganar ta fiddata a daidai ta gaza,don harbuwar maganar zuwa kwanyarta tazo mata ne da wani irin katsuwar hanzari da gajere kuma tsukakken lokaci "Yimin bayani dalla dalla qawata". "Yanzun nan" Cewar mamah tana komawa ta zauna sosai. "Zan nema yarinyar da na tabbatar babu soyayya a zuciyarta sai soyayyar kudi......zan nema yarinyar da zata iya aikata komai indai akan kudi ne.....zan nema yarinyar da ba kasafai namiji ke burgeta ba kaman yadda kudinsa yake burgeta ba......za muyi contract da ita na auren fu'ad zuwa wani lokaci.......zata shayarmin dashi ta ciyarmin dashi daga dukkan wani abu da akeso yaci ko yasha da zai jawo min hankalinsa.......daga sanda buqata ta biya zan sallameta daga dukkan adadin kudaden da takeso tayi kuma nesa da rayuwarsa.....a sannan ne kuma tayimin tawa shimfidar da zan soma tawa tafiyar". Idanu hajja ta zubawa maamah sosai.....ga bikin zuwa kuma babu zanin daurawa.....tabbas wannan tsari nata yayi.....kuma komai zai iya tafiya ya kuma wanzu kaman yadda ta tsara din muddin akayi katari da kalar yarinyar da zatayi aikin. A jikinta takejin wannan aikin nata ne,wannan kuma su za'a yiwa.....wannan aikin JANAN dinta za'a yiwa ba kowa ba......zata soma tata shimfidar ne itama a sanda mariya ke tunanin zatayi tata.....a sannan zata wanzar da nata tsarin da zai kauda na mariya,dole ta tsaya kai da fata ta taya mariya fafutukar wannan tsarin ya tabbata,to amma ta yaya zaiyi accepting?. Yaron da yake da tsananin kafiya da tsaurin da bokansu ma ya gaza juya akalarsa?. "To amma ta yaya kike zaton zai karbi maganarki ta sauqi irin haka?" Hajja ta yiwa maamah tambayar da taketa cin ranta. Wani murmushi maamah ta ajiye tana goye hannuwanta a qirji,daidai sanda sabreen ke shigowa wajen tana takowa cikin nutsuwar nan tata me fusgar hankali,sai maamah din ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hajja ba tare data bawa ganin data yi matan muhimmanci ba,amma abu daya taji ya darsar mata a rai "Da mata masu kyau irin haka ya kamata ta yiwa fu'ad din fatsa.....domin su din suna da saurin kama zukatan mazaje". "Komai lalacewar uwa uwa ce.......hakanan komai lalacewar d'a yasan me ake nufi da uwa.....ballantana fu'ad da nasan me na haifa?,nasan iya matakin kaifinsa da kafiyarsa......wannan ba wani abun damuwa bane". Ba tare da jira ko neman izini ba taja spare kujerar dake gefansa ta zauna. Shimfidadden kyan nan dake fusgar zuciyarsa tunda can baya wanda ya jashi zuwa ga wanzuwar alaqa tsakanin su a yanzun sai yakega ya ninka yadda yake a baya. Fuskarnan a rubuce da dabi'ar miskilanci baro baro samanta. "Zuwa da kai ai yafi saqo ko?......ka nema qanwar ga yayar tazo da kanta.....zaifi kyau a sauka ta inda aka hau". Tayi maganar a jejjere da wani irin aji da kintsi daya qara kwarjantata a idanunsa. Zuciya da ruhinsa suna masa d'ari d'ari gami da gargadinsa a kanta,to amma kuma wani sashen na zuciyarsa na bashi tabbacin tabbas yaci wasan ne......lallai ta fuskanci cewa shike da nasara wannan dalilin ya sanya tsananin wayonta ya bata shawarar tayi gaggawar bada kai. Wata irin dariya ya kece da ita yana kallonta gami da gyara zamansa sosai "Haba 'yammata?,irin wannan karaya haka da sauri?" "Karaya kuma?......sabreen bata taba karaya ba.....hakanan ba zata karaya akan wulaqantaccen mutum maras daraja irinka ba". Mamaki ne ya lullube farincikinsa,a hankali yanayin fuskarsa ta sauya. "Daga yanzu zuwa sanda zaka isa gidan birsin ka fara qididdige yawan adadin haramtattun kudadenka da zasu salwanta bayan cafke jirgin da aka boye cocaine me nauyi,wadannan kudaden an samesu ne ta hanyar maida mutane zuwa dabbobi wajen basu gurbatattun magungunan bugarwa da sanya maye.....kaga kuwa garin banza a farau farau din banza yake qarewa". Wani irin shock ya shiga saboda kiran sunan jirgin da ayau yake sanya ran isowarsa. Ya lissafa yau a ranar sa'a a gareshi.....zai aike mata da sakamakon abinda tayi masa ta jikin 'yar uwarta......hakanan kuma zai maida gurbin hasarar da yayita jiran cikewar gurbinta. Bai qara koda motsi daya ba sautin takun ma'aikatan cikin sassarfa da hanzari ya karade gurin. Hankalin kowa dake wajen ya tashi yayin da aka soma kallon kallo a tsakanin juna. "Kada wanda ya motsa.....munxo kama me laifi ne.....kowa yana cikin aminci.....amma kada ku motsa har sai mun gama mun bada umarni" Daya daga cikin ma'aikatan da ba'a iya ganin fuskarsa yayi maganar a gaggauce. Ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yakeyi......wannan ya sakashi miqewa da zummar samun hanyar fecewa,saidai kuma tuni suka ankara suka masa qofar rago gami da fadin "U are under arrest!". Wadannan din ba irin ma'aikatan daya saba gani bane,rana dubu ta barawo,ya tabbatar idan har ya saba kubce musu to a wannan karon babu wannan damar,don haka ya tsaya kyam jikinsa yana kyarma har suka gama. "Koda ka sake samun rayuwa a nan gaba.....kayi komai da lura" Ta furta tana nuni da gefen kanta,sannan ta juya a nutse ta fara takawa "Thanks for the information" Daya daga cikin ma'aikatan ya furtawa sabreen din da ta fara barin wajen. Murmushi ta saki kadan "Wannan aikin kowanne dan qasa na gari ne" "Gaskiya ne" Ya furta yana saluting nata,yayin da suka waiwaya zuwa ga Naseer suka riqeshi sosai suka sanyashi a tsakiya suna fita dashi ta daya qofar cikin hararrami da tsaurara masa tsaro. "Keep calm......you're safe guys.....kowa yaci gaba da sabgarsa". Mutumin da yayi musu jawabin farko a yanzu ma ya fadi sanda yake bin bayan abokan aikinsa da sassarfa. "Tabbas akwai wata boyayyar fuskar a bayan wannan" Muryar hajja ta daki kunnen maamah wadda idanunta ke kan hanyar da sabreen ke wucewa. Dauke kallonta maamah tayi zuwa kan hajja "Kada dai ace tunaninmu yazo daya?" "Me kenan?" Hajjan ta cewa maamah tana dubanta "Na samota.....inaji a jikina zata iya.....inaji a jikina ba iya fuskar da muka gani yanzu ce kadai a tattare da ita ba.....zo muje" Maamah ta fada tana jan hannun hajja zuwa hanyar da sabreen tabi. "Inason insan wacece.....inaji munzo nan ne a yau domin cikar burina" Maamah ta fada tana jin wani irin nutsuwa da fuskar data gani din. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 91 Agogon fatar dake daure a hannunsa ya duba bayan yadan gyara shirt din jikinsa. Lokacin da yake hutu na mintuna ashirin zuwa talatinne a yanzu. Iska ya furzar daga bakinsa yana duba adadin mutane da jerin sunayen wadanda keson ganinsa ta qaramar computer gabansa wanda mutumin da yake kula da sashin da zaka soma tsaiwa kafin ka samu damar ganinsa ya tura masa wato mr abdulhaleem. Mikail shine mutum na farko cikin jerin sunayen,to amma baya buqatar ya fara da ganinsa,don hakan zai iya hasala fushinsa ya gaza ganin sauran mutanen dake da muhimmanci su ganshi din. Me sunan malam ya kira,ya bashi apple da strawberry sai ruwan dumi. Mintuna goma kacal ya bawa kansa sannan ya fara bada umarnin shigowar baqin. Duk wani mutum me muhimmanci sai daya kammala da ganinsa kafin ya bada umarnin shigowar mikail,wanda zuwa sannan yayi imanin inda za'a auna jininsa yakai dari biyi qila harda talatin ma. Sanda yake shigowar fu'ad din yana tsaye daga bakin book shelve din da aka yiwa wani kyakkyawan tsari cikin office din. Dukkan documents din da suka shafi case din yake cirowa a nutse yana qoqarin danne yadda ranshi yakeyi yana baci. Ba kaman kwanakin baya kadan da suka shude ba.... Lokacin da yake da daraja da martaba ta gaba gaba cikin kamfanin......a lokacin da zaiyi sallama cikin girma da mutunci cikin office din,ya tako kaman kowanne ma'aikaci da Allah ya tarfawa garinsa nono yake iya idanu biyu da muhammad jadda din kai tsaye ba tare da shamaki ba. Akwai dubban ma'aikatan dake kamfanin wanda basu taba idanu biyu dashi ba......amma shi yana cikin wadanda zasuyi tattaki har zuwa cikin office din su zauna saman kujerar da ake bawa kowa don ya tattauna da CEO din.....a yau din sai gashi a matsayin qasqantacce,me tarin laifukan da baisan ta inda zai fara kare kanshi ba. Ya fadi gaskiya?,wadda ya tabbatar fadar nata wata faduwa qasa ce wanwar......yayi qarya?,ita kuma ta zame masa alaqaqai da babbar matsala a duk sanda me jadda din ya gano ainihin matsalar. A nutse ya juyo abinsa ba tare daya kalli sassan da mikail ke gurfane saman gwiwoyinsa ba. Baice komai dashi ba sai daya koma saman kujerarsa sannan ya motsa bakinsa a nutse "Tsugunna kazo kayimin ko bayyana min gaskiya?....idan kuma duka ba wannan ba ka shirya amsa tambayoyin muhammad fu'ad?" Ya qarashe qarshen maganar yana dauke idanunsa daga kan file din yana zube masa su. Kallonsa kadai ka sanya razani a zuciyar mutum,ballantana ma mutum irinsa maras gaskiya ko qanqani?. "Na shirya sir.....don Allah kayimin rai" "Gaskiyarka kadai ita zata fiddaka.....am listening" Ya furta yana dora qafarsa daya kan daya,sannan yayi relaxing bayansa sosai da fuskar kujerar tana juyata a hankali,wanda banda motsa kujerar da yakeyi idan ka kalli kyakkyawan fuskarsar nan me shimfidadden kwarjini zakayi zaton bacci yakeyi. Bai boye masa komai ba......ya gaya masa komai yadda ya wakana......saidai statement dinsa na qarshe da harshensa yaso sarqafewa "Saidai.....daga b.....dag.....ga baya na gano da ita da wan....." "Da wancan tsohon dan cacan UBA NE DA 'YARSA BA ka gayyatosu suka taba dukiyar da gumin halal ya tarata?!" Ta furta da wata irin tsawar da hatta mutumin dake qofar farko bama reception na office dinsa ba zai iya jiyo tartsatsinta,bayan dukan table din da yayi da hannunsa abinda ya sanya wasu files din da takardun misplacing daga inda suke. Har cikin tsokarsa yake jin fushin yana masa tasiri.....bai taba ganin an raina masa wayo kaf rayuwarshi irin wannan lokacin ba. Sanda yake kammala binciken da sakamakon daya karba daga hannun wadanda yasa suyi nasu binciken ya duba yaga conclusion nasu yayi daidai da nasa.....saidai duk da haka zuciyarsa tana masa kokwanto. Ta yaya 'ya zata zama KARUWA?.....yar fashin YANAR GIZO.....MAYAUDARIYA ME SACE XUKATAN MAZA DON KAWAI TAYI AMFANI DASU?. Sannan kuma ace uba ya zama DAN CACA?,WANDA ZAI IYA ZUBA KOMAI A CACAR NAN DON NASARA TA ZAMA TASA CIKI HARDA TAKARDUN GIDAN DA MARAYU KE ZAUNE A CIKI?. Dukka jikin mikail bari yake kai kace wanda aka watsawa ruwan qanqara ne cikin hunturun matsanancin sanyi. "Kayi haquri yallabi.....tuba nake.....kayimin gafara kayimin aikin rai....wallahi banci komai a ciki ba sir.....ko sisi sai nawa kudaden ma da suka narke!" "Will you shut your mouth or not?!" Ya sake fadi da wata gigitacciyar tsawar data sanya fitsari balle ma mikail din,ya kuma koma yayi zaman dabas a qasa don ya gama sarewa.....ya kuma yi imani bashi da sauran mafita. "Ni zaku mayar dan iska?,dukiya ta halalina a gidan caca?,a wajen karuwai?,a wajen sabon Allah?.....ko an gaya maka ni ban san dadin rayuwa ba?,sai kai?......to daga kai har su wannan shine zai zame muku aikin ashsha na qarshe da zaku aikata.....daga kaina ba zaku sake marmarin sake aiki irin wannan ba......ka tashi ka fita ka bani guri.....zan nemeka.....idan kaso ka gudu duk inda kakeso" Ya fadi yana huci idanunsa da suka sauya launi akan fuskar mikail da yayi jalaf da gumi da fitsarinsa. "Na roqeka sir......kayimin duk kalar hukuncin da zakamin a yau basai wani lokaci ba......amma ka yiwa Allah kada ka koreni daga bakin aiki koda zaka sauyan matsayi". "Naci gaba da biyanka albashi kaci gaba da shan barasa da neman mata.....ka bacemin a wajen tun ban gama tunzura ba!' Ya amsa masa yana sake jin zuciyarsa tana hasala. Ajiyar zuciya gami da iska zazzafa ya dinga fesarwa bayan fitar Mikhail din. Ya sake komawa yayi relaxing sosai yana jin wani irin huci yana fita daga fuskarsa. Ya tsani dukkan wasu ayyukan ashsha......mikail yayi masa abu mafi muni....abu mafi munin koda dashi kadai ya kamashi cikin company dinsa zai iya zama silar korarsa ko rasa aikinsa....NEMAN MATA.....zina itace abinda yafi qyamata cikin rayuwarsa bayan shaye shaye,dukka rayuwar mikail ta dagula ta kuma gurbata cikin wadannan ayyukan. Wata qyama ta mikail dama yarinyar gaba daya suka sake kamashi,ya waiwaya fannin caca......abar data tabbata da nassi cewa haramun ce itama qarara..... "Wadanne irin ahali ne wannan?" Ya furta a fili qasa qasa zuciyarsa na masa wani irin ciwo. Baisan girman tsanar da ya yi musu ba....ko don ya taso ya samu nagartaccen mahaifinsa ko yaushe yana jaddada musu su guji su kuma nisanci wadannan abubuwa iya gudunsu?. Wanne hukunci ya dace yan yankewa mikail?,tsohon dan cacar da kuma 'yar kwaltar Yarinyar?. Wannan tambayar ce har ya gama zamansa a company na wunin ranar bai samo amsarta ba. Yau koda ya koma gida sai yaqi zaman sassansa.....ya zauna sosai sunyi dinner dukkansu kaman yadda suka saba a duk sanda dama ta basu irin haka dukansu su shidan. Sun jima suna hira tsakaninsa da abba,wanda anni na gefe tana jin gwarazan 'ya'yan nata. Qauna da kuma wani alfahari dasu yana ratsata. Sha daya saura ya sanya qafafunsa a sassansa,wanda kamar tunanin yana tsaye daga bakin qofa yana jiransa ya mamayeshi. Yaja dogon tsaki kamar zai tsinke harshensa......ya taka a hankali yana zarcewa toilet bayan ya sanya me sunan malam ya sallami kowa,masu kwanciya sun kwanta,masu kwana bakin aikinsu sun kama wajen tsaiwarsu. Shafa'i da wuturi yayi a kebantaccen wajen daya ware saboda ganawarsa da ubangijinsa. Koda ya idar sai yayi zaune saman abun sallar. Yana jan hasbunallahu da duk dare bata wuceshi qafa dubu da la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. Iya wadannan abubuwa guda biyu ya tabbatar suna taka rawa me yawa cikin rayuwarsa,sun kuma zame masa mabudin sirrin nasararsa. Har ya kammala ya kasa tsaida hukuncin da zaiwa kowannensu,har sai daya hau saman lalallausan gadonsa,ya dauki qaramin remote yana sauke rumfar gadon da ke tattare ba lallai ka lura ma da ita,kyakkyawan net din ya sauko ya lullube gadon ruf yana bada wani dim light da ke bawa bacci nutsuwa. Numfashi me zurfi ya sake ja yana jingina bayansa da pillow hadi da lumshe idanunsa kana ya budesu. Kamar wannan kawai ake jira yayi qwaqwalwarsa ta fara aiki. "Mikail ya dade da zama korarre daga dukkan wani aiki da yake da nasaba da jadda diamondchore resources company......kamfanin dake kano ko lagos.....koda kuwa aikin shara ne cikin kamfanin........mutumin da ake kira da samaila fa?,idan yace ya dawo masa da dukkan abinda yaci nasu horo ne me sauqi.....dole ya hada masa da wani abun....YARINYAR KUMA FA? . Jan duvet dinsa yayi yana lullube fuskarsa har zuwa kanshi. Koda a qasan zuciyarsa bayason tunata. KARUWA wani suna ne daya samu gurbi cikin kunnuwansa tun yana da shekara goma sha uku a duniya. _"mariya......bansan me yasa idanunki suke makancewa ba da barin daidai.......kina matsayin matar aure.....wadda ke auren sunna da yara har guda biyu,me zai hadaki alaqa da qawance da karuwai?" "Karuwai?,hmmmm.....bakasan a yanzu babu wanda yakai karuwa mutunci ba?,saboda zaunannun kudi gareta da zata yiwa duk wanda taso ihsani.....kyautar ban girma da ban mamakin da ke da kike qarqashin inuwar aure baki isa ki sameta ba.....kaga kuwa karuwanci ai ya biya su". Muryoyin dukansu su biyun da irin zancan da sukayi a sannan ya dawo masa tarwai cikin kwanyarsa abinda ya sake qarawa zuciyarsa wani irin zafi da radadi. Abbansa dake kwance a qarqashin qasa yanzu......da kuma maamah din da take rayuwa dasu a yanzun hakan itama. Wani yanayi ne da bayason tunashi......wasu abubuwa da binnesu yafi zama alkhairi a gareshi duk da yadda kullum suke qona masa zuciya da mafi zafin ciwo da suka. "Dole ta fuskanci hukunci me girma....." Ya fada yana bude idanunsa,ya dauki wayarsa ya aika gajeran saqo sannan ya koma ya kwanta yana qoqarin tilastawa kansa yayi bacci. Kwanaki ukun da ya dauka yana dakon jiran kira daga wajen Muhammed jadda sai suka zame masa tamkar me jiran ranar mutuwarsa ne. Komai ya tsaye masa cak.....wata iriyar nadamar sanin sabreen dake a mazaunin fateema a wajensa tana mamayarsa irin nadamar dashi kansa baisan yawanta ba. Ranar da saqo daga kamfanin jadda din kwana yayi yana zawo. A gobe jumaa....juma'ar da baisan yaya zata kasance masa ba. ****takardun gabanta ta jawo ta rufe a nutse tana maida dubanta kan fuskar hajja dake shan lafiyayyen nonon da aka zubawa madara aka kuma niqeshi cikin 'ya'yan itace masu dadi. "Na gode sosai qawata.....na gode qwarai da gaske......tabbas banda ke koda komai zai tafi zai kasance me wahala a wajena..... Banda abinda zan iya biyanki dashi,kedai Allah ya bawa autarki miji na gari". Wani qasaitaccen murmushi hajja ta saki tana Ajiiye mug din dake cike da furar idanunta akan fuskar maamah. Ita daya tasan me take tsarawa cikin zuciyarta,ita kadai kuma tasan me ke kai kawo a ciki "Ameen mariya......banda abinki mene ne amfanin amincin?,mene ranar amincin?......yanzu kawai abinda ya rage shine.....muyi tattaki har zuwa cikin gidansu don mu sake tabbatar da komai a kanta.....daga nan sai mu saka rana ta daban da zamu tunkari yarinyar.....komai ina ganin bazai mana wahala ba......ina ji a jikina zata karbi komai cikin sauqi da hanzari,tunda kudi ta fito nema......mu kuma biyan buqata kawai mukeso". Kai maamah ta jinjina farinciki yana lullubeta. Hasken nasararta da dukkan wata lamba ta nasara tana walqawa cikin idanunta. "A shirye nake na rasa komai don wannan abu ya tabbata" Maamah ta furta "Ba zaki ma rasa komai din ba.....don komai zai fito ne daga jikin wanda ake abun don shi" Hajja ta fadi tana sake sakin murmushi. "Ina jin me zai hana yau mu shiga gidan nasu?,tunda ga adress nan da komai jikin takardar?" Maamah dake sake duba takardun ta fadi "Da zafi zai haka?......" "Bakiji abinda bahaushe ya fada ba?,da zafi zafi ake dukan qarfe?" Maamah ta katse maganar hajja,sai kuma suka saki dariya dukkaninsu. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 92 Cikin wani dan banzan lace peach colour da torches na purple maamah din ta shirya,sannan tayi amfani da wani irin luxury veil me wani irin lafiyayyen jiki ta lullube jikinta dashi. Tun daga takalmi da jakar hannunta zaka sallamawa shigartata,ballantana azo ga sarqa da awarwaraye zuwa zobunan gold data sanyawa yatsunta guda hudu kowanne hannu bibbiyu. Cikin motocinta ta sanya driver ya fidda wadda bata fiya shiga ba,aka gogeta tas ainihin kyawunta da qyallinta ya sake bayyana. "Gaskiya kin fini gaggawa mariya" Hajja dake shiga cikin motar ta furta tana 'yar dariya. Ajiyar zuciya maamah ta saki tama girgiza kai "Mariya kenan,ba zaki gane yanayin da nake ji ba,saboda ke komai ya miki daidai cikin rayuwarki,yara biyu?,amma ba guda daya wanda zaka juya yadda kakeso?......zaiyi wahala idan har yarinyar tana cikin gidan ma ban nemeta ba......gwara mu yita ta qare hajja.....idan na samu yadda nakeso ma zuwa qarshen watan nan a gama komai ta tare na fara aiwatar da aikina.....don na samu labarin dab yake da kammala ginin wannan gidan da nake burin kasancewa a ciki ni da duk wanda naso naga dama". Kai hajja ta jinjina tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Tafi kowa buri da kwadayin wannan gidan,saboda bahaushe yace gani ya kori ji. Tayi yawo da qafafunta tsakanin katangun gidan,ta kuma samu ganin iya abinda Allah yayi tana da rabon gani,don hatta ginin da akeyi qarqashin kulawar security ne,so shiga ko fita din yana qarqashin kulawa. "Karki damu.....komai zaizo yadda muka tsara qawata" "Haka nake fata" Dukkaninsu sukayi maganar cikin ransu suna gamsar da kansu tasirin tasarrufinsu ba tare da sun tsarma kalmar IN SHA ALLAH a ciki ba. Idanunsu kaf cikin layin lokacin da motarsu ke gangarawa,suna lissafe da kowanne gida da suke giftawa har suka qaraso babban qofar gidan "Yauwa......tsaya a nan,shine wannan da alama" Hajja ta fadi tana baiwa driver din umarni. Tare suka fito kowa ta qofa daban daban,maamah ta soma gyara lullubin kanta tana duban gidan. Gida ne da kana masa kallon farko zaka fahimci a wani zamani da can mamallakin gidan yana cikin sahun masu arziqin wancan lokacin,to amma duk da hakan data fuskanta sai tadan tabe baki "Banda lalura da neman biyan buqata babu abinda zai sanya na nemawa fuad aure a irin wannan gidan........bari amma ba komai.....ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba,muddin komai ya kammala,xan sanya binciken qwaqqwafi sai na nema masa auren yarinyar da tafi kowacce 'ya gata a al'ummarmu.....sannan kuma wadda zata dace da tsarina". Murmushi hajja ta saki tana jin maamah tana motsa mata wani abu cikin ranta. "Qwarai kuwa qawata......dan gata ai sai 'yar gata,amma naji dadi da kika fahimci nema masa wannan ba matsala bace.....tunda AUREN WUCIN GADI NE AUREN BIYAN BUQATA". Ranta a sake tana murmushi suka fara kutsawa gidan suna magana da juna qasa qasa. Har suka dangane da babban tsakar gidan gidan basu hadu da kowa ba. A irin wannan lokacin lokaci ne da yara da sauran wadanda suka tasa cikin gidan suka jima a makaranta har wasu ma suna dab da tasowa,don haka ba kowa din sai tsakar gidan dake a tsaftace kamar kullum. "Salama alaikum.....gafaranku dai mutanen gida" Hajja ta ware muryarta ta kwarara sallamar idanunsu yana yawo bisa tsaftataccen tsakar gidan. A hankali ta bude idanunta dake a lumshe,kimanin awa guda tana kwance a haka saman doguwar kujerar falon tun bayan kiranta da JIB yayi ya shaida mata an rarraba wasu cikin kudaden a account din mutum dubu d'ari tsaffin 'yan pension da suka rasu da bashin banki,wanda hakan ya sanya ake cirewa daga cikin abinda gwamnati ke bawa iyalansu duk wata. Hakan ya tagayyara iyalai da dama,domin basu da qarfin biyan kudin bare su tsira daga zari d'ai d'ai da banki yake musu. Cikin ranta da jikinta takejin wani irin sanyi kamar ta aiwatar da wani wajibi da yake kanta. Ta zame ta kwanta cikin mutuwar jiki tana tuna yadda bashin bankin ya zamo silar shigarsu halin ni 'yasu bayan rasuwar abbansu,duk da cewar bashi yaci bashin ba ci masa akayi babu saninsa babu kuma yardarsa,rayuwar ta dinga qwallo dasu har zuwa sanda tasu mahaifiyar ta sake tafiya ta barsu da tsanani da uqubar rayuwar. A yau tasan iyalai da yawa zasu kwana cikin farincikin da take fata ya zama sanyi da haske cikin qaburburan mamatansu ciki harda iyayenta. Ta jima a kwancen tana tunanin me gobe zata haifar mata?,a wanne gurbi zata dora rayuwarta wadda daga rana irin ta yau takeso ta koma aminatu dinta ba sabreen fateema minal da sauran tarkacen sunayen data yita rabawa maza ba. Ta zauna taci gaba da kula da rayuwar qannenta dake da matuqar tsada da muhimmanci a gareta. Tanaso subar gidan,tanaso su bar kano ma gaba daya idan zaiyuwu,saidai kuma tana hasaso irin qalubalen da zata iya fuskanta a sanda ta koma rayuwa cikin wata al'ummar da basusan ainihin wacece ita ba. Wanne kallo zasuyi mata sanda take zaune cikin gidan da daga ita sai qannenta mata?,wannan ne kadai abinda yake sake taka mata burki,sai kuma ga sallamar ta ratso har dakinta. Sallama ta uku taji an sakeyi,dole ta miqe daga kwanciyar ta sauko da qafafunta qasa ta miqe tana takawa a hankali don amsa sallamar da kuma duba waye. Don tasan lokaci irin wannan da yawa cikin matan gidan suna bacci. Har ta sanya hannu zata yaye labulen muryar daada ta dakatar da ita,sai ta koma a hankali ta zauna a inda ta tashi tana jawo wayarta ta bude. "Wa'alaikumussalam" Ta amsa tana binsu da kallon rashin sani. Saidai kafin ita ko su su sake cewa komai bibo ta bankada nata labulen ta fito da buta a hannu. Itama sakin bakin tayi tana kallonsu,saidai ita tana musu duban farko ta karanto zallar wadatar da suke ciki da kuma arziqi. Atamfar jikin maamah ta kalla,saitaga tana mata kama da atamfar da sabreen ta saka rannan har musu ya barke tsakaninta da hadiyya,inda daga qarshe hadiyyan ta tabbatarwa da bibo kudinta ya kusan kaiwa dubu sittin da biyar idan ma baifi haka ba. Wannan abun data tuna ya sanyata saurin ajiye butar hannun nata sannan ta kawo fara'a da murmushi ta aza saman fuskar tata. Idanma arziqi ne kamata yayi ace kai ka fara tararsa a dakinka ya fara sauka "Marabanku sannunku da zuwa lale" Ta fadi cikin haba haba da tsananin kulawa. Hausawa sukace shimfidar fuska tafi shimfidar tabarma,wannan da suka gani ya sanya suka karkatar da hankalinsu akan bibo suna amsa mata,wannan ya sanya daada salin alin sakin labulenta ta koma ciki don ba kasafai ta fiya shiga shirgin da ba bata ba,musamman kuma data ga bibo din ta zaqe. "Ku shigo ciki mana,kwa tsaya daga nan?,ai baqonka annabinka" Ta fadi da sauri tana juyawa ciki. Idanu suka dinga bin rumfar bibo din dashi sanda take rawar jikin aje musu ruwan sha,akwai wadatar tsafta amma ba wadatar arziqin da yakai koda quarter din nasu. "Bismillahir rahmanirrahim" Ta fadi tana zama a gabansu. "Mu sake gaisawa ko?,ina wuninmu zaa ce?" Tayi zancan tana sake fadada fara'arta. Hajja da tasan takan duniya ta washe mata bakinta tana amsa mata itama cikin madaukakiyar fara'a da nuna sakewa. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 93 itama,tana hango qishi qishin halayen bibo da kyau daga yanayinta da idanunta dake nuna zallar wayo. Itama maamah data zurfafa a tunani ta sake waiwayawa suka gaisa,sai kuma dan shuru ya biyo baya na wani lokaci kadan kafin bibo ta kasa daurewa "Kuyi haquri fa bayin Allah,abubuwan da yawa,ban shaida ku ba" Tayi maganar tana basu hankalinta sosai. Murmushi hajja tayi tana gyara zamanta "Eh ai gaskiya ba zaki shaidamu ba,don bana jin mun taba gamuwa kam.....mu din baqi ne,sunana hajja harira.....wannan kuma mariyatu amma muna kiranta da maamah" Hajja ta fadi tana nuna maamah din da hannu "To....to ma sha Allah,ni hafsatu nake.....kuma nice mace ta uku cikin gidan nan.....duk da me gidan Allah yayi masa rasuwa,ya rasu ya bar kowaccenmu da 'ya'ya". Fuskokinsu suka nuna jimami suka masa addu'ar samun rahama sannan hajja ta dora "Muna tambaya ne akan wata yarinya da muke kyautata zaton itama 'yar gidan nan ce" Sake daidaita zamanta bibo tayi,zuciyarta tana zillo da fatan jin wacece "Mun sanya an biyo mana sawunta ne saboda muna son nemawa d'anmu ita". Murmushi bibo ta tsinke dashi hade da faduwa kuma da gabanta yayi. Wannan dan mutanen ko makaho ya shafasu yasan cewa tabbas masu arziqi ne,masu dukiya ne,ba kuma qananun mutane bane,akwai arziqi daula da dukiya a wajen,iya zamansu a wajen kawai qamshin turarensu ya cika wajen,wannan kawai ya isa ya gaya maka matsayinsu a rayuwa. Zuciyarta cike fal da fata take dubansu,don tana kyautata zaton ba wanda za'a nema haka cikin gidan cikin dattako haka irin d'iyarta dake karatun kiwon lafiya. "To......to ma sha Allah,ai kowa kukeso a gidan nan 'ya'yanmu ne dai.....wacce ce a ciki?,hadiyya?". Kai hajja ta girgiza tana kallon bibi "A'ah,Sabrina ce". Tamkar hajja ta kawo ruwan zafi ta watsa ma bibo a sassan jikinta haka taji,ta dinga jin wani abu yana tsarga mata tun daga saman kanta har tafin qafafunta. Wacce Sabrina din ga nasu 'ya'yan a zazzaune kamammu?,wadannan mutanen masu alamu na damshin arziqi sune za'a ce sun tattako neman auren Sabrina din?,wacce daraja ko kamala take da ita data cancanci wannan?. Ji tayi ba zata iya daurewa ba,tako wacce fuska sai ta barar da dan guntun mutuncin da qila dansu yaje ya musu qarya ya labarta musu tana da shi yarinyar,dole ta farke mata laya don ba zata iya bari wannan abu ya faru ba.....idan ma Allah ya bata sa'a ta musu nuni da tata kamilalliyar d'iyar. "Tofa......amma dai hajiya d'anku ya rufeku gaskiya,duk da bansan ko irin cikin mutanenta shima yake ba?". " Kamar yaya kenan?" Maamah ta jefa mata tambayar cikin fargabar kada ta kasance an kusa aurenta ne da wani,wanda muddin hakan ya faru sai inda qarfinta ya qare wajen baza dukiya har sai an fasa an dawo da abun kan fuad din. "Abinda nake nufi shine maganar gaskiya baku yiwa yaronku zaben macen aure ta gari kaman yadda addini ya shardanta ba......ni da kuka ce Sabrina ma abun mamaki ya bani,waye zai nemi auren wannan idan ba asharari ba?,danku dan gidan girma da dattako bai cancanci auren mace irin Sabrina ba......yarinyar da duk cikinmu ba wanda yasa sana'arta data wuce KARUWANCI.....sam bata kwana cikin gidan nan sai anci sa'a qwarai....ni nan da hannuna nasha tsareta amma ta tsallake ta gudu,rubutun shiriya ba irin wanda bata sha ba,fada duka ba wanda ba'a yi ba......ga sata kaman bera,yanzu haka kwanaki muna kyautata zaton cikin shege taje ta zubar,ba wanda take ganin mutuncin sa ballanta ta raga masa,dan tsoro irin na diya mace fa sam ita bata sanshi ba,gaba gadi take komai cike da rashin kunya da rashin albarka......son abun duniya a wajenta abun har ba'a magana......zata iya komai akan kudi.....idan nace komai ina nufin komai da komai fa......har kisa...." "Wadannan dabi'un su suka sanya mukeson aurenta da yaronmu". Maamah da dogon sharhinta ya fara isarta ta fada tana kallon bibo,dogon sharhin da yayi Mata dadi ma,don ya qara tabbatar mata da cewa tabbas zata iya.....Sabrina din ita tafi dacewa ta kuma fi cancanta da deal din. Idanu bibo ta gwalalo tana kallonsu maamah cike da zallar mamaki. "Amma ta yaya za'a aikoku neman aure kuje ku nema musu irin wannan baragurbin diyar?, bayan ga gaskiya kun gani daga bakin iyayenta sun gaya muku ba'a rufeku ba?,anya ku din ba kishiyoyin uwa bane zaku rufi uwarsa ku cutatar mata da d'a?,ku nema masa auren tantariyar hatsabibiyar KARUWA ba tare da saninsu ba?" "Ni nan nice uwarsa kuma mahaifiyarsa data dauki cikinsa wata tara ta kuma haifeshi ba tare da taimakawar kowa ba.....a haka nakeso ta zamewa d'ana matar aurensa,wannan din zabina ne!". Dukka sai aka gogewa bibo hadda,sun sanyata a rudani gaba daya ta rasa fahimtar komai. Uwa kuma?,uwa da kanta?,anya da gaske uwar ce?. Tana tsaka da wannan tunanin ta tsinkayi miqewarsu suna aje mata wasu adadin kudin data tabbatar ba 'yan kadan bane. "Ga wannan ki soma riqewa......ki nuna mana kawai dakinsu ko dakinta cikin gidan nan" Maamah data qagu ayi komai a wuce wajen ta furta tana duban bibo "Daki me kallon wannan dab da matakalar bene" Ta furta a sanyaye. "To mun gode fa" Hajja ta fadi tana bin bayan maamah da tuni ta fice. Zumbur ta miqe tabi bayansu tana leqensu ta tsakanin labule,salati da sallallami kawai takeyi zuciyarta na wani irin bugawa. Tunda take a rayuwarta bata taba ganin baragurbin iyaye ba irinsu,shin anya ma da gaske kuwa suke?. Tsaf nutsuwarta ta dauke,tana jin ba zata iya zama haka ba tare data labartawa kowa wannan zancan ba. Balaraba bata nan tun dazun ta fita.....bata jin kuma zata samu cikakken hadin kan yin magana da daada,don tasan ba kasafai ta fiya shiga shirgunan da ba nata ba,ballantana ma kuma lamarinsu Sabrina din. Wuf ta fito ta kuma fada dakin daada hankalinta a kansu sanda suke cire takalmansu suna shiga parlor dinsu Sabreen. "Lafiyarki meye haka bibo?" Daada dake zaune tana gyaran zogale cikin rumfarta ta fada idanunta akan bibo. "Muhammadur rasulillahi daada.....zo kijimin wata lalacewa....zo kiji wata almara,wai zuwa akayi neman auren yarinyar nan Sabrina?". Tayi zancan tana zama d'aid'ai a gaban daadan. "Wa'alaikumussalam" Sabreen ta fada a hankali tana daga idanuwanta zuwa ga bakin qofar falon nasu. Idanu ta zube musu sanda suke shigowa cikin falon,haka kawai taji gabanta yana faduwa akan baqin fuskar da batasan su waye ba. Sai ta samu kanta da miqewa tsaye tana fadin. "Sannunku da zuwa" "Yauwa sannu 'yar nan" Maamah ta furta cikin murmushi yayin da hajja ke qarewa sabreen din kallo wadda ke sanye cikin soft Egyptian bubu me mayafi,amma madadin mayafin sai ta sanyawa kanta hula wadda santsin gashinta ya hanawa hular zama daidai,kaman ma ta mata kadan sakamakon nannadadden gashin data daure a qeyarta. A nutse ta taka zuwa ga fridge dinsu tana lalubar musu ruwa,yayin da su kuma suka dinga bin dakin da kallo suna ganin zallar banbanci tsakanin falon da sauran falukan gidan,wanda hakan ya sake jaddada musu zarginsu. A hankali idanun maamah ya fada kan babban hotonsu guda daya dake kafe a falon. Sabreen a tsaye huda a zaune a gabanta,nadra da haneefa suna zaune daga dama da hagunta. Idanu ta tsura musu tana kallon yadda suke kamanceceniya da juna,tana mamakin kuma yadda sam sunan yaran bai fito cikin bincikensu ba. Gabansu ta ajiye ruwan sannan ta koma da baya ta zauna a nutse tana kallonsu. "Barka da warhaka" Ta fadi tana qoqarin karantarsu,don ta fahimci akwai wani kallo na daban qasan idanunsu da sukeyi mata ita da falon. "Yauwa sannunki 'yammata.....ya kike ya garin?" Hajja ta fada da murmushi "Alhamdulillah.....wa kuke nema?" Ta tambayesu kai tsaye,don itadai tasan dukan wanda yake alaqa ko mu'amala da ummensu na kusa kona nesa ya jima da sanin rasuwarta,tun suna zuwa wadanda basu sani ba daga baya har labarin ya game ko ina,kuma an jima sosai da sunan anzo wajenta. "Ke muke nema wajenki mukazo" Hajja ta sake fadi har yanzu tana murmushi "Ni kuma?" Ta tambayesu a mamakance "Eh ke" Hajjan ta jaddada mata "To gani,Allah yasa lafiya" "Lafiya qalau sai alkhairi......yaronmu mukazo nemawa yardarki ki zame masa matar aure" . Tamkar tana karanta tatsuniyoyin gizo da qoqi haka taji zuwan zancen kunnenta,daga inda take zaune ta daga idanu tana kallonsu,kalmar aure tana maimaituwa a kunnenta. "Aure kuma?,bam fahimta ba,ya sanni ne?,idan ya sanni munyi jarjejeniyar aure dashi?" "Kwantar da hankalinki,baki sanshi ba bai sanki ba.....hasalima mu muka shirya abun". Idanunta ta sake azawa sosai a kansu tana musu kallon masu tabin qwaqwalwa a wannan karon,kamar wasu qananun yara?,hadin aure kaman wasan 'yar tsana?. " Eh.....zakiji abun wani iri ko?...." "Da zaki daure ki tafi bayaninki kai tsaye da sai nafi fahimta" Ta furta a gajiye da zamansu a wajen,don bata fatan su huda su dawo su samesu cikin falon. "Dalla dalla zan miki yanzu yammata......auren KWANGILA ne,shi mukeso kiyi da d'anmu..... Wanda dukanmu mu dake zamu amfana gaba daya,zaku fimu samun moriyar abun ma,don ke da kanki zaki yanks adadin kudin da kikeso kafin aikin da kuma bayan aikin......ga mahaifiyar yaron da kanta zata tsara miki yadda takeso abun ya kasance". Da wani irin madaukakin mamaki ta maida idanunta kan fuskar maamah,uwa kuma?,uwa da nemawa d'anta auren kwangila?,wacce irin uwa ce wannan?. Mutuwa tayi murus a zaune sanda maamah ke karanto mata qudirinta,har ta kammala ta kasa janye idanunta a kansu. "Muddin komai ya tafi yadda nakeso......zaki zama wata abun kwatance cikin ahalinku......hakanan zaki gane a baya wahala kawai kikeyi.....zakiyi arziqin da me kamoki cikin danginki sai yayi da gaske,zaki samu kudin da rayuwar wadannan zata zama rayuwa mafi gata" Maamah tayi zancan idonta akan sabreen hannunta kuma yana nuni da hotonsu dake bango tanason ganin reaction din sabreen akan hoton.....don ta fuskanci wani abu kadan daga gareta. "Basu da alaqa da dukka wani aiki ko kwangila......ki sauke hannunki daga saman hotonsu" Sabreen ta furta da wani irin emotion idanunta itama tsaye cikin na maamah. Wani shu'umin murmushi maamah din ta saki,sai ta sauke hannunta a hankali,ta samo abinda takeson samowar,kuma tabbas lallai komai zaizo da sauqi. "Aure na gaske ko na wasa,na kwangila ko wanda bana kwangila ba baya cikin tsarina hajiya,bama wannan deal din ba.....koma meye a yanxu bani da sha'awarsa......bana buqatar komai bana buqatar kowa!" Tayi zancan da wani fushi fushi da kuma dakewar zuciya. "Koda wannan shine aiki na qarshe da zakiyi sai kin mana wannan yarinya......ina me baki shawarar ki kwantar da hankalinki kibi kawai......cikin sati daya ko biyu ma zuwa wata daya idan buqata ta biya kina iya tafiyarki.....kada ki yarda akan wannan ki jefa rayuwarki cikin hadari". "Bazanyi ba" Ta furta idanunta a lumshe kuma a nutse,saidai kuma batasan me yasa zuciyarta take wani irin tsananin bugu ba. Bawai barazanarsu bace ta tsoratata kota dameta ba,don ba kalar barazanar da bata gani ba,to wadannan su ko nasu qalubalen yasha banban da sauran?. "Zata iya yiwuwa" Zuciyarta ta gaya mata kafin muryar maamah ta sauke a kunnenta. "Kwana daya kacal kike dashi kan bayyanar yardarki......idan kika haura haka kuwa.....zamu tilastaki ki yarda koda baki so ba" Ta qarasa maganar tana matsawa gabanta ta ajiye kudi masu yawa da rubutacciyar number wayarta,sannan suka juya suna fita daga dakin salin alin. Dole ta bude idonta ta rakasu da kallo,ta rasa abinda take ji a qasan ranta,tsoro ko fargaba?,wanda dukkansu bata sansu ba,ko kuma shakka ce ko kokwanto?. Suna shirin sanya takalmansu su huda suka shigo,kallon kallon sukayi a junansu su hudan na mamakin ganin fitowar baqi daga dakinsu,abinda suka manta rabon dasu gani,ganin yadda baqin ke kallonsu sai suka gaidasu,suka amsa kuwa cikin fara'a,su suka wuce suma suka fada dakin. "Ban taba zato ku tunanin yarinyar nan zata watsar da damar samun kudade masu kauri irin haka ba" Hajja ta fada sanda driver ke tuqasu don maidasu gida. "Na fiki mamaki hajja,anya bayanan da muka samu a kanta babu na bogi?" *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 94 "Nima na fara wannan shakkar,saidai kuma na yarda da aikin hidima.....ya iya aiki fiye da zatonki,wannan ya sanya bamu rabu ba tsahon shekaru" Kai maamah ke jinjinawa "Ta yaro kyau take bata qarko.....a wannan karon zata fahimci duk wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi". **Duk wata jijiya dake harba jini a jikinsa kyarma take,kaman yadda ya jiqe jalab da gumi a sanda yake zaune saman kujerar cikin shaddarsa dataji aiki,kadan daga shigar yiwa talauci jan kunne daya fara yi a kwanakin kenan a cewarsa. Zaman MUHAMMAD JADDA a gabansa a yanzu sai yakeji kadan yake da banbacin zaman mala'ikan mutuwa a gabansa. Ya tsinewa Mikhail dake zaune a qasa da mato yafi sau shurin masaki,hatta da wanda ya shirya cacar ya tsine masa a ransa har baisan adadi ba. Wallahi inda yasan akwai wani daya jibanci muhammad jadda ma sam da baiyi kuskuren hada caca dashi ba ballantana akai ga karbar dukiyarsa,bai sani ba.....qaddara kuma ta rigayi fata. "Dukka wannan abubuwan daka lissafo malam rufa'i matsalarku ce.......abinda nakeson tambayarka shine.......nawa ta raba ta baka kayan ta qwamushe kudade daga account na kamfani na?" . Gigicewa ya sakejin yayi da saukar tambayar da baiyi zatonta ba ballantana tsammani. "Sabrina?" Sunan da yazo masa a cikin zuciyarsa kenan,saidai abinda bai sani ba ya zarce har zuwa saman harshensa sautin sunan kuma ya bayyana a kunnen fuad da Mikhail dake zaune a wajen. "Yes" Fuad ya furta yana yin relaxing bayansa a jikin kujerar yana kuma qarewa kawu rufa'i kallo tare da karantar duk wani motsi nasa. Salati kawun ya dinga debowa a tsakanin rude,daga sama zuwa qasa,daga qasa zuwa sama. Wani irin tashin hankali yakeji yana saukar masa,wacce irin masifa ce Sabrina din keson jefasu?. "Wannan yarinya anyi 'yar Allah bani......yallabai....wallahi wallahi bansan da komai ba.....gagararriya ce dama ta fitinemu,tunda uwarta ta sanya qafa tabar duniya shikenan yarinyar ta zama kangararriya........wannan aikin nata na kwashe kudaden akawunt na al'umma dama na jima inajin qishi qishin dinsa......batun zamowarta karuwa kuwa na jima da sani......" "Dakata" Ya tsaida kawun ranshi yana tsananin baci. Dukka komai ma akan yarinyar gaskiya ne kenan?,komai da komai ya gama samun tabbatattun shaidu da hujja.......a nata tunanin har takai riqar da zata shiga gonarsa?,idan har ta saba shiga shirgin wadannan tarkacen maza.....tana tunanin muhammad jadda zai tabu?. "Ba kowanne namiji take saurara ba......tana da girman kai da izza......sai namijin da taso tayi alaqa dashi.....koshi dinma yana gwaruwa kafin ya samu ta fara saurarensa......amma ni yallabai,ba abinda ya taba faruwa tsakanina da ita duk da naso hakan ya faru,amma aurenta naso yi,saidai kwata kwata aure baya gabanta,shine cikin jerin sahun lissafin abu na qarshe da take tunanin wataqil watan watarana idan tana raye zatayi,hasalima zancan aure dana fara mata dashi ya kawo rashin samun cikakkiyar fahimtar juna a tsakaninmu.....hakanan da sunan FATEEMA NA SANTA". ya tuna maganarsu da Ya'aqoub kenan a jiya bayan ya sanya an kawo masa shi a wani kebantaccen guri. Tashi yayi ya zauna sosai yana harde yatsunsa cikin juna gami da zube idanunsa akan kawun idanunsa a samansa,fuskar nan shimfide da wani lafiyayyen fushi daya cakuda da izza da kuma miskilanci. Yanaso ya tuna hukunci guda daya mafi tsaurin da zai musu......yanason ya musu hukuncin da zasuji a jikin su,saidai kuma yanaso hukuncinta yafi zama mafi tsaurin da ba zata sake gigin maimaita kusakuren data aiwatar a baya ba. "Rufa'i kake ko?" Ya jefa masa tambayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa. "Na'am yallabai.....labbaika" . "Inason kai da d'iyarka ku hadamin kudina nan da awa ashirin da hudu,ficika a ciki banaso tayi ciwo,naira biyar idan babu a ciki zata iya zame muku matsala..... Muddin kuwa ba haka ba......" Kawai sai ya girgiza kai ba tare daya qarasa fadin abinda zai fada din ba,ya maida bayansa ga kujerar yana jawo wayarsa ya fara latsawa hadi da bawa banza ajiyarsu shida Mikhail din. Yadda cikin kawo ya karta ya bada wani sauti zata zaci zai tsinke da gudawa ne,cikin kwanakin yaci kudin da baisan iya adadinsu ba,wanda maidasu a yanzun wani gagarumin tashin hankalinne da baisan ta ina zai tarosa ba. Uwa uba sabreen.....yarinyar dake da matsiyacin taurin kai da daukar kasadar da yasan ko sama da qasa zasu hade ba zata fidda abinda ya shiga hannunta ba. "Tana da taurin kai da kasada......wonderful" Ya qarasa maganar yana maida idanunsa saman fuskar kawu rufa'i ba tare daya motsa daga yadda yake a zaune ba. "To me zai hana ku bani aurenta a madadin kudin da kuka cimin kai da ita?". Tsananin mamaki da rudu ya sanya kawu rufa'i rikitowa daga saman kujerar sai gashi ya zube a qasa a gaban muhammad fu'ad " Wallahi tallahi yallabai mun baka.....na yarda munci sadakinta harma da sauran kudin hidimar aurenta....." "Oh.....da kana tunanin wani kudin daban zan lissafa na baku?" Fu'ad ya fada very calm yana dage dukka girarsa idanunsa akan kawun. "Inaaa yallabai.....wane mutum?,wane aikinsa?" Ya fada yana jijjiga kai da kalar mamakin daya kasa sakinsa. "Oya.....kaje ka shaida mata ka bada aurenta nan da sati biyu kacal masu zuwa" "An gama ranka ya dade" Kawu rufa'i ya miqa kaman babbar rigar jikinsa zata tadeshi ya fadi ya durfafi qofa,jordan ya bude masa ya fice babu ko waiwaye bare ya tuna da Mikhail daya bari a ciki. 🔅Idanun bibo akan su maamah har suka fice daga gidan,saita dawo a gaggauce ta sake zama gefan daada "Kin gansu can daada......don girman Allah daada ki dubamin zancan nan fa?". A karo na biyu daadan ta sake dubam bibo bayan ta dauke kai daga farantin zogalenta "To wai ke meye naki a ciki bibo?". Kaman ta harari dadar sai kuma ta daure " Haba mana daada,don ke yaro daya Allah ya baki yana can saudiyya baisan me ake ciki a qasar nan ba?,fisabilillahi ace duk kamammun 'ya'yanmu a rasa wanda zaa zo neman aure cikinsu sai wannan tambadaddiyar?" "Duk tambadar tata kin gaya musu,kuma sunce sunji sun gani,ke meye yayi miki saura a ciki?" Daada ta sake jefawa bibo tambayar. Bata da amsa amma kuma bata gamsu har yanzu da cewa ta zuba idanu wannan abun ya tabbata ba. Iya leqen da tayi qofar gida taga motar da sukazo a cikinta ya sake dasa mata kwadayin duk yadda zatayi ta tabbatar likita hadiyya ce ta shiga wannan ahalin,saita miqe ta fita da sassarfa zuwa dakin Sabrin. Duk su huda sun wuce ciki sunata qoqarin sauya uniform dinsu zuwa kayan gida,su kuma killace sauran. Tana nan zaune inda suka barta ta kasa koda motsawa wanda ita kanta batasan dalilin mutuwar jikinta da fargabarta ba. Ciki ciki ta amsa sallamar bibo din,don duk sanda ta ganta a dakin ba wani ba wata,ba tantama ba alkhairi bane ya kawota. "Ashe sun tafi.......lalatattu mutanen banza da wofi,haka ake zuwa neman aure?,mata ma da zuwa neman auren idan banda lalacewa?" Saita soma sakin kuka tana matse hawaye "Allah sarki rayuwa......Allah ya jiqan alhaji da rahama,mutuwa me tonon silili,banda baka wai yau shine har wasu matan ke takowa gidansa da sunan nemawa diyarsu auren dansu?,yaron da ba'asan asalinsa ba?". Idanunta sabreen ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda,tana jin muryar bibo har tsakiyar kanta ne "Don Allah ki fita.....banason hayaniya" Tayi zancan a nutse tana yamutsa fuska. Haba bibo ta kama,yarinyar dake da wannan halin tun yanzu inaga ta shiga gidan arziqi har haka?,tabbas ba shakka sai inda qarfinta ya qare "Wato abun arziqi ma bai karbi kare ba ko?,don inason kare haqqin zaman tare?,a gidan waye ya shigo miki bandani?,to kuwa muddin na haifu ga cikin sahura da labaran bazan sake shiga shirginki ba" "Da dai yafi miki" Sabreen din ta furta qasa qasa tana jan qaramin tsaki sanda bibo ke fita a dakin gwiwa ba qwari. Taso taji sauran bayani daga bakin sabreen din yadda suka dade a dakin,taso kuma taji meye matsayar yarinyar akan mutanen. 𝗗 𝗨 𝗡 𝗜 𝗬 𝗔 𝗧 𝗔 𝙃 𝙐 𝙂 𝙐 𝙈 𝘼 𝙋𝘼𝙂𝙀 95 Wani zuzzurfan numfashi sabreen ta sauke,tana jin yanayinta gaba daya yana sauyawa. Tun daga tunaninta bugun zuciyarta dama komai nata. Zuwan mutanen ya kasa barin zuciyarta da idanunta har ma da kwanyarta. "A ina suka sanni?,su waye su din ma tukunna?" Wadannan sune tambayoyi masu ban tsoro da kuma qara sanya mata firgici. Qasan ranta kuma zuwa yanzu takejin ya kamata tayi qaura daga ainihin inda aka Santa,ta koma wani bigire na daban wanda ba kowa yasanta a wajen ba don sake lullube kamanninta dama komai nata,tare da sake bad da sahu da dukkan wata alama da zata alamtawa masu farautarta inda take. Saidai kuma......wani hanzari ba gudu ba,har yanzu tana tattalin MUTUNCI,har yanzu kuma tana matuqar girmama kalmar MUTUNCIN MACE.....kalmar da tayi imani tayi adabo da ita daga idanun mutane da yawa. ******Dukkaninsu shuru sukayi kai kace ruwa ya cisu. Ba abinda kawu rufai yakeyi sai sharce zufa tare da mutsu mutsu kamar wanda wani abu yake cizo. Gefe guda mutumin dake kusa dashi ya sake sauke zuzzurfar ajiyar zuciya,ya kuma miqe ya zauna sosai yana tura hularsa baya. "Rufa'i.......baka da wata mafita akan buqatar muhammad jadda......" "Ina naga mafita rabi'u?.....aini godewa Allah kawai nakeyi nake kuma sakeyi.....don na tabbatar inda wa'adin biyan kudinsa ya sanya mana da mun bushe.....wallahi bani kadai ba ba kuma Sabrina ba......dukkan danginmu qwanmu da kwarkwatarmu......waye zai iya fada dame kudi?,wa ya isa yaja dame kudi?,wahala ma kenan rabi'u" . Kai babban aminin kawu rufa'i yake jinjinawa,banbancin ra'ayi wajen sana'a shi ya kawo nisan alaqa kadan tsakaninsa da rabi'u din. Sam rabi'u baya hanyar caca ballantana yayita,suna kuma yawan samun sabani da kawu rufa'i akan hakan,wannan ya sanya indai kaga kawu rufa'i yayi shawara da rabi'u to babban al'amarine dake neman nutsuwa da hankali irin wannan. "Yanzu abinda kawai yake damuna rabi'u......yarinyar nan Sabrina,bansan ta yaya zan bullo mata da batun maganar na bada aurenta ba......yarinyar ta fita zakka a cikin dangi kamar wadda akayi tsugunnon haihuwarta tsakanin fukafukan shaidan....." "A'uzubillahi" Rabi'u yayi saurin fada yana dakatar da kawun "Haba rufa'i......Sabrina fa 'yarka ce halak malak...." "Na sani rabi'u.....na sani,Kai dai kawai ka barni......na fika sanin wacece ita,wallahi duk taqadirancina ta dameni ta shanye yarinyar nan......yadda kasan me gani har hanji akan maza.....tana iya zuqe tattalin arizqin kowanne d'a namiji idan taso tana zaune daga gida.......ka bani shawara rabi'u,yau daya sai nakejin ina shakkar tunkararta". Shuru rabi'u yayi na wani dan lokaci sannan ya gyara zamansa "To a zahirin gaskiya dai aurar da Sabrina ba wani abu bane mummuna,asalima yin hakan tamkar taimako ne ka baiwa rayuwarta.....kuma a addinance kai din uba ne a wajenta da zai iya zaba mata mijin aure,to abinda nake ganin yafi kawai ka tunkareta da zancan.....sannan kabi dukkan hanyoyi na hikima ka kwatanta mata aure shine babban rufin asirin mace". Shuru kawu rufa'i yayi tamkar me shakka ko kokwanto akan shawarar rabi'u. "Har yanzu rabi'u bakasan yarinyar nan ba,kafaffiya ce me shegen taurin kai da rashin tsoro,idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya tanqwarata,bata tsoro shakka ko kuma shayi.....ba irin Sabrina bane ake zuwa musu da magana haka kai tsaye a hada da wa'azi da shawara ba kuma su dauka.......Sabrina rinduna ce da sai an fuskanceta da gayyar jama'a....amma dai kafin sannan zan gwada wannan din rabi'u " "Zata aminta in sha Allah,kuma komai zaizo da sauqi" "To Allah yasa" Kawu rufa'i ya furta ajiyar zuciya tana subuce masa. Shi kadai yasan kalar tashin hankalin da yake ciki,yayi nadamar sanin duk wani dan caca tun daga haihuwarsa kawo yau bare kuma har ta zame masa sana'a. *****Shi daya ne tal tsaye cikin kitchen din,sanye da fararen tanks top da joggers masu taushi. Kunnensa daya yana maqale da earpiece yana amsa waya. Daga gefe guda kuma yana tsaye ne gaban wani qaramin cabinet yana ciro ganyen zaitun,ginseng wolfberry da zai dafa tea dinsa na musamman dasu,sannna ya jawo wai qaramin plate din daban ya zuba dabino teen da busashen inibi da ake kawo masa shi tun daga china bayan anyi packaging nasa a wata jar leda mai kauri. Hankalinsa yayi nisa sosai wajen amsa wayar da dafa tea din,har baiji shigowar farouq ba,wanda ta qaraso dab dashi ya kumayi tsalle ya haye saman kitchen cabinet din kusa da plate din da fuad din ya zuba friut din,ya soma miqa hannu yana tsinta daya bayan daya yana jefawa a bakinsa gami da cilla qafafunsa yana duba wayarsa rabi da rabi,yayin da kuma lokaci bayan lokaci yakai kai dubansa ga fuad din. Daidai sanda ya gama amsa wayar tea din nasa ya gama dahuwa,ya jawo kebantacciyar ma'ajiyar kyawawan kofunan shan shayi na tangaran. "Nayi zaton baka shigo ba ai". Fuad dake zuba musu tea din ya furta ba tare daya kalli farouq ba. "Na shigo tun dazu......na tsaya duba wasu baqi ne da abba yace na sauraresu don yayi nisa". Kai kawai ya jinjina,yayin da farouq ya maida dubansa kan cups din da fuad ke zuba tea din "Amma dai bani ka zubawa ba ko?" Ya fada yana dan yamutsa fuska. Sai a sannan ya daga kai ya kalli farouq din. "Ba dole bane sai ka sha......" Yayi maganar shima yana hayewa saman kitchen cabinet din tare dakai cup din bakinsa a nutse hankali kwance yana sipping. Sosai farouq yake kallonsa kafin murmushi da yafi kama da dariya ya subuce masa "Ina mamaki idan na ganka a kitchen......zai zamewa 'yan jarida babban labari idan sukasan muhammad jadda dinnan yana shiga kitchen da kanshi time to time" "It's my hubby.........inason dafa tea dinnan da kaina.......na tabbatar bakasan amfanin wadannan ganyayyakin a jikinka ba da bazakayi wasa dasu ba". Yakai qarshen maganar yana sake maida cup din bakinsa. "Inaso na koya......but bakina yanason dadi.....harshena ba irin naka bane" Yayi maganar yana nuna damuwa akan fuskarsa. Sake cire cup din yayi yana balla masa harara "Ka zauna dadi ya kasheka......you know baka fini son girki me dadi ba......but lafiyanka a matsayinka na d'a namiji sama take da komai.....wait.....wai meyasa ma zan zauna inatayi maka wannan bayanin,do what you want,amma sanda kayi aure kada ka nemeni da shawaran komai". Murmushi ya sake kubcewa farouq,yana so yana kuma farinciki yaga ya sanya muhammad magana har haka,wannan dalilin ne ya sanya baya gajiya da tsokananshi,duk da ba kasafai yake biye masa ba. "Kaine na hannun daman ango.....so that kai ya kamata na fara nema kuwa......" "Baka da wani abu me muhimmanci ne da zaka fada?" Fuad din ya fadi yana kafe farouq da idanu. Dariya sosai farouq ya saki harda sunkuyawa kadan "Da alama aljanar amaryarka ta iso,taji batun aure....." "Farouq" Fuad yadan kirashi da husky voice dinsa. "Times up" Farouq ya furta yana daga hannayensa sama "I have something to talk about.......very serious" Farouq din ya fada yana gyaran murya kadan sannan ya maida fuskarsa serious,abinda ya sanya fuad shima ya bashi hankalinsa ganin ya koma umarul farouq dinsa na asali. "Tun jiyan zuwa yau nake zuba ido da kunnen ka nemeni ko kayimin qarin bayani...." "Akan me?" Fuad din ya tari numfashinsa. "Akan yarinyar daka nema aurenta ta hannun kawunta a office dinka......kwata kwata ban fahimci meye shirinka ba......in fact ma duk wanda ya sanka dole abun ya sanyashi mamaki......how and when ka fara sassautawa ra'ayin riqau akan aure?,when kasan yarinyar har soyayyar da za'a iya aure ta shiga?,.....anya auren tsakani da Allah zakayi kuwa dude?" Sassauta zamansa fuad din yakeyi,baisan murmushi ya subuce saman kyakkyawar fuskarsa ba. Murmushin da ya sanya farouq ya sanya masa qatuwar ayar tambaya ya sabbaba masa kafe fuad din sosai da ido. Bayaso fu'ad din yaje ya aikata wani kuskure,yanason koma meye su bishi a sannu "Banda kai dan rainin hankali ne dama ana auren wasa ne?.....da gaske aurena zaa daura mata,aure zan nema kaman yadda kuka nema kuke kuma neman naku....already ma gayawa wancan tsohon nata...two weeks ma nace masa badon ina nufin nan da 2weeks din nake buqata ba,zan daura mata igiyata kaman kowanne mutum......but....." Ya katse maganar yana durgowa daga saman cabinet din,sannan ya fara takawa zuwa bakin sink din kitchen din ya kunna tap yana wanke cup din. A mugun qagauce farouq yake kallonsa yana son jin qarshen labarin,ya sani tsaf zai iya qin qarasa masa ya barshi da guntuwar magana a ciki "But what fu'ad......tell me mana?" Farouq ya furta cikin damuwa,danuwar data taba zuciyar fu'ad din har ya waiwayoshi bayan ya gama wanke cup din. "I want her to lern the hard way.......she made a mistake data zabi taba kudin jadda company" 𝗗 𝗨 𝗡 𝗜 𝗬 𝗔 𝗧 𝗔 𝙃 𝙐 𝙂 𝙐 𝙈 𝘼 𝙋𝘼𝙂𝙀 96 Yayi maganar yana zube idanunsa akan farouq da mamaki ya fara saukar masa "To learn what?fu'ad?......sai ka aureta ne sannan zata koya darasin rayuwa?". Wani dan qaramin murmushi ya saki,ya miqe tsaye sosai yana goye hannayensa har yanzu idanunsa akan farouq din " Ba wata hanya me sauqi da zan sanyata ta barwa sauran mata masu irinta darasi sai ta wannan hanyar.....dole ta fuskanci hukunci.....dole ta gane yadda ta dauki kanta batakai can ba......dole ta karbi sakamakon mutanen data dinga sanyawa a masifa saboda rabasu da dukiyarsu data dinga yi ba dalili.....inason ta san meye rayuwa......tasan kokai waye kana da iya limit dinka a rayuwa.......abdus salam na tura mata amma tayi avoiding nasa........kaga inda tayi accepting dinsa da hukuncin zaizo da sauqi" Yakai qarshen zan can yana sakin hannayen nasa gami da juyawa yana nufar inda ya ajiye wayarsa. "Let her fu'ad......" "Am sorry bro....Definitely sai na nuna mata kuskurenta......na dauki wannan alwashin" Ya sake fada yana bude wayarsa. Shuru farouq din yayi yana wani gajeran tunani.....yafi kowa sanin waye fu'ad.....yafi kowa sanin halin tsaiwarsa da kafiyarsa akan komai ma.....idan yace zaiyi ba gudu ba ja da baya "Amma ta yaya zaka tunkari su abba da wannan maganar?". " Kaman yadda kowanne me neman aure yake sanar da iyayensa mana......akwai wani abu sabo ne a ciki?" Yayi zancan kanshi tsaye hankalinsa kuma kwance ba wani haufi. Duk da yasan waye fu'ad amma wannan karon mamaki yake sake bashi,yayi tsai da ranshi yana kallonsa kamar yadda shima shi yake kallo. "Da wani abu?" Fu'ad ya furta yana dage dukka girarsa biyun. Kai farouq kawai ya girgiza,yama rasa me zaiyi?,murmushi ko takaici?. "Idan naji wani abu daban daga wajen anni ko abba tabbas kaine" Fu'ad ya fadi ba tare daya kalli farouq ba daya sauko daga saman cabinet din shima. Harara ya watsawa fu'ad din kaman zai idanunsa zaso fado "Saika hanani fada din" Daga haka ya soma tattaki zai fice daga kitchen din "Karka damu,koda ka fada din ai ba wani abun bane.....zan koya mata tarbiyya ne na kuma koya mata wadatar zuci da kame kai daga dukiyar al'umma......kaga ko ba komai zan samu ladanta ko?" "Kai ka sani" Farouq ya fada yana qarasa fita a kitchen din,yanayin yadda yayi magana kuma ya sanya fu'ad sakin wani lallausan murmushi. *****Tamkar tsakanin hajja da maamah din babu wani me sauran abun fada sanda driver ke wulwula saura dasu cikin baqar range Rover din mallakin maamah. Ba wanda yace komai din har zuwa sanda maamah ta gaji da shurun ta gyara zamanta. "Amma hajja abun yazomin a bazata,ya kuma dauren kai matuqa". Juyawa gefanta hajja tayi tana duban maamah data tsinke mata zaren nata lissafin da take hadawa tare da qoqarin ganin amsar lissafin ya fito daidai. " A yadda bayaninta ya nuna......zata iya aikata komai muddin akan kudi ne.....hakanan kudin sune abu mafi daraja cikin idanunta......ya akayi ta wofantar da buqatarmu ta watsa mana qasa a ido?......duk da cewa ido ba mudu ba ai yasan kima.....duk wanda ya kallemu zai shaida irin daula da ni'imar da muke ciki". Wata ajiyar zuciya hajjan ta saki itama,ta zubawa waje daya idanu kafin tace "Ni kaina abun ya dauren kai,kuma iyakar tunani na bamu shiga mata da wani abu da ba daidai ba" Tayi maganar cikin 'yar damuwa. A wannan gabar ita kanta nasara take buqatar a samu.....nasara takeso tazo musu......yarinyar zata zame mata tamkar wani tsani me tsananin sauqin da zai ciccibata ya zuwa matakin tata nasarar. "Ba wani abun damuwa bane ba hajja......ita iya nata hasashen ta dojewa buqatarmu.....kina tunanin zan barta?" Ta jefawa hajja tambayar. Duk yadda hajja ta saka idanunta cikin na maamah din don hango plan dinta akan yarinyar ta gaza ganowa,don haka ta dora da tambayar "Wanne mataki kenan zaki dauka?". "Matakin da shine mafi dacewa da ita,ki zuba idanu kawai ki jira cikar kwanaki ukun dana bata.....da kanta zata budi baki tace ta amince" Ta furta sanda motar ke tsayawa a farfajiyar gidanta,don haka ta saka hannu da kanta ta bude murfin tana fita hajja ta mara mata baya zuciyarta cike da wasiwasi. Sun samu zuwaira ta kammala komai,ta cika table da kalolin abinci iri iri na alfarma,wanda duka cikin izzar maamah dince. Ba'a abinci kala daya a gidan,bata yarda wannan ba,daga breakfast lunch har zuwa dinner ana mata varieties of food ne taci wanda ranta ke ra'ayi tabar sauran. Daki na musamman da aka kebe ta sanya aka shigar da hajja don ta huce gajiya kafin itama ta watsa ruwa ta sauya wasu kayan ta fito. Kamanninta da musaddiq suna fitowa sosai sanda take fitowa daga dakinta sanye da wata bubu gown me tsananin laushi. "Yau nake sake ganin kamanninki da musaddiq fa...." Hajja ta fada tana murza awarwaro hannunta. Murmushi kadan ta saki tana jan daya daga cikin Kujerun dining din ta hau ta zauna "Tun duniya na kwance akance kamannina da musaddiq yafi yawa......shi wancan babanshi ya dauko.....ni kuwa ba?" Maamah ta hade zancan duka tana qoqarin daukan cup da zuwaira ta fara zuba musu lemo "Uhmmm" Hajja ta fada tana kallon maamah,can qasan ranta tana jin wani abu.....tana kwatanta irin izza gadara da mulkin da maamah din zata zuba a duk sanda haqarta ya cimma ruwa "Waya sani ma ko ta rufe idanu ta manta dake ta canza qawaye?" Wani sashe na zuciyarta ya jefo mata wannan tunanin. "Ni kuma bari zanyi hakan ta faru?" Ta bawa kanta da kanta amsa "Kinsan wani tunani da nayi" Maamah ta sake fada tana juya cokalin cikin abincin bayan barin zuwaira waje. Zuwairan da a yanzu tsananin kishi da tsanar hajja ke ruruwa qasan ranta,ganin farat daya hajjan ta rushe gwamnatinta,gwamantin da da ita aka fara fafutuka aka kuma dasa harsashin gininta. "Zanyi magana da fu'ad a yau ko gobe.....zan sanar masa ya fara shirin aurensa nan kusa". Kallo hajja ta bita dashi "Da wuri haka?,har yanzu bamu samu tabbacin amincewar yarinyar ba". Wani murmushi maamah ta saki tana saka lomar abinci na farko a bakinta. "Sabrin qaramar alhaki ce a wajena.....bata isa ta tsallakewa tarko na ba......amincewar fu'ad tafi zama abu me wahala a gareni akan amincewar sabreen.....na rantse miki da Allah.....muna nan zaune dake zata kira da kanta ta furta ta amince". Maganganun maamah din a yanzu daure kan hajja sukeyi. A kafe yarinyar take,ba wata alama ta amincewa a tattare da ita har suka baro gidan,to wanne abune haka zai sakata sauya ra'ayi da gaggawa?. "Indai kina da wannan tabbacin to tabbas tsarinki yayi". Hajja ta bata qwarin gwiwa,daga wannan kuma sai suka zarce da wata hirar ta daban. ******A hankali suke takowa ta tsakanin kyawawan shuke shuken da aka qawata kusan kowanne sashe na gidan. Baqin wando ne a jikinsa wanda bai qarasa idon sawunsa ba da kadan,sai shirt itama baqa me gajeran hannu,hakan ya bayyana murdadden damtsensa,kalar rigar kuma daya kasance baqa ta haska farara lafiyayyar fatarsa dake sulbi tamkar ta mace. Kadan kadan iska ke wasa da sumarsa daga hagu zuwa dama,wani lokaci yasa hannu yadan shafeta kadan. Ko daga ina kake muddin a daura dasu kake to tabbas hancinka zai iya dauko maka lallausan qamshinsa daya zauna sosai a jikinsa,ya kuma kama komai da yake mu'amala dashi,kama da wayarsa keys dinsa briefcase da sauransu. Shi da farouq ne bayan fitowarsu daga ainihin parlor din abba wato alhaji hamza kibiya. Karo na farko kaf tsahon rayuwarsa daya gabatar da wata d'iya mace a matsayin macen da yakeso ya aura. Har a sanda suke takawa yanayin anni ya kasa barin idanunsa,can qasan zuciyarsa sai yakeji anya ya kyautawa wadannan dattawan guda biyu da suka karbi lamarin auren hannu bibbiyu da zallar farinciki?. "Alhamdulillah.....alhamdulillah,Allah na gode maka daka gwadamin wannan ranar da raina da lafiyata.....wacce me sa'ar ce?,a ina take?,ya kuma sunanta?" Anni da qananun hawaye suma maqalewa ta fada tana kallonsa. Sunkuyar da kansa yayi,sam bai dauka lamarin aurensa ya zaune musu a rai ba har haka saida wannan maganar ta taso,ko da wasa bai taba qiyasta zasuyi farinciki har haka da zancan aurensa ba,tunda duk sanda farouq ya sanyashi a gaba game da lamarin auren cewa anni take "Ka shiga hankalinka fa......matar mutum kabarinsa.....komai komai nada nasa lokacin.....kar ka sake kiransa mijin aljana......yarona yana da ibadar da ba wata halitta data isa ta cutatar min dashi". "Sunanta sabreen......kuma marainiya ce" Abinda yaji kawai farouq ya fada kenan. Kallon gefan ido ya yiwa farouq din,a nasa zaton zai tona asirin plan dinsa......sai baiyi hakan ba......amma ya jishi kuma yana isar da wani zance da baisan sanda suka yishi da farouq din ba. "Dukkaninmu ya fimu iya shiri anni......yanason aje nema masa auren,kuma sati uku kawai yake buqata". Shuru suka danyi dukansu,don abun yazo musu a bazata. Sun dauka zaya jera ne tare da 'yan uwansa ayi komai lokaci guda?. "Anni......komai na gininku ya kammala......da bude company da tarewarku duka duka sati biyu ne ya rage......ayimin afuwa idan abun yazo muku a gaggauce......inason ku zama wakilai akan komai kafin mubar nan din". Yayi maganar cikin sunkuyar da kai tare da mamakin me yasa farouq yin hakan?. Bazai iya qaryata farouq din ba ko yace ba haka bane a gabansu annin,dole ta sanya ya dora da nasa bayanin. Baida wani plan na a daura auren sam a yanzu,yanason ya fara sanya mata shamaki ne ta hanyar maidata property dinsa. Shiga ko fita saida izininsa,hakanan yana buqatar kowanne motsi nata ya kasance qarqashin umarninsa,matakin quntatawa na farko kenan da yakeso ya fara aiwatar mata wanda zai sanyata jin ta qasqanta,kuma ita din batakai inda take tsammanin ta kai ba. Murmushi abba ya saki yana cewa "Banda abinka ko a yau iyayenta suka baka ita ai bai haramta a daura muku aure da ita ba......zan samu mamanka a sanar mata ko akwai wanda zai zama nata wakilin wajen zuwa neman auren......zanyi magana da bangaren mahaifinka suma,in sha Allah bazai wuce wadannan satikan ba". Har suka isa sashensa baice da farouq ci kanka ba,sai da suka isa falon. Qarasawa yayi gaban freezer a nutse ya bude,ya ciro ruwa me sanyi abinda yadan jima baisha ba,yau dole zaisha din saboda yadda tsarin farouq yazo masa a bazata,ya kuma busar masa da maqoshinsa. Sai daya gama sha ya dire robar saman dining,ya kuma fara saukowa daga steps din dining din cikin tafiyar nan tasa me cike da ginshira. Ba zato ba tsammani farouq yaji saukar waya sama cinyoyinsa,sannan fu'ad din ya tako gabansa ya tsaya hannunsa zube a aljihun wandonsa. "Tunda kai ka tsara komai ai sai ka qarasa aikinka......ka kirayi wancan tsohon ka gaya masa yadda ka tsara din,don bani da lokacin masa bayani......lokacin kawai nace ka shaida masa.......sadakin aure kudin sanya rana da sauran bidi'o'i ya lissafa ya cire cikin kudadena da suke kwasa,canjin ya rubutasu aci gaba da lissafi har zuwa ranar da zan fashesu gaba daya......don ba wanda zaici kudin jadda ta wannan hanyar ya tsira". Da idanu farouq yake binsa,dariya nason kamashi amma yana dannewa "Amma malam ya kamata ka koyi ladabin magana zuwa yanzu,ko ka manta yanzun suraki yake a wajenka?" . Harara ya watsa masa da fararen idanunsa yana zama saman sofa "Kaci gaba da gayamin haka,wataran zaka wayi gari da haqoranka a hannu" . "Zaka aikata.......ai gwara da aka saka ranar auren 3weeks,kafin aljanarka ta dawo ta sanyaka kace ka fasa.....kaini koma wanne irin aure ne fa gwara kayishi,a qalla addu'ata bata fadi qasa banza ba,zaa yiwa aljana kishiya.....naci nasara" . Duk da baijin dariya ko wani raha sam a ransa.......amma saida maganganun nan na farouq suka sanyashi sakin wani miskilin murmushi kafin kuma ya waske kaman bashi ba. Yana tsaka da cin abincin dare kiran ya shigo masa,ya daga wayar ya sanyata a hands free yana adduar koma waye ya kirashi Allah yasa alkhairi ne. Tunda farouq ya gabatar masa da kansa gumi ya fara yanko masa,gaba daya yaji abincin ya gundureshi ya fita a kansa,sai ya tsame hannunsa daga ciki ya miqe tsaye yana sauraron farouq jikinsa yana kyarma *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 97 "To.....to shikenan......in sha Allahu zan shaidawa dangin uwarta.....to Allah ya nuna mana....to godiya nake a gaida alhajin". Ya qarasa fada jikinsa yana rawa wayar kaman zata sulale ta fadi " Na shiga uku na lalace ni rufai" Ya fadi a sarari yana zama dabar saman Kujerun da kwana uku kacal da zubasu sumame daga jadda company ya riskeshi. A da mugun laushin Kujerun yake ji,amma a yanzu yana jjnsu tamkar kujerun da aka sarrafa da bishiyar qaya. Kansa kawai yake mirginawa daga hagu zuwa dama. Duk da ya iya tijira ya kuma iya tubura,amma wannan karon sai ya tsinci kansa da tsananin shakkar yadda zai tunkari sabreen din ya gaya mata ya bada aurenta a madadin kudin cacar wasu da yaci,da kuma nata kudaden data kwasa. Bata iya doguwar magana ko rashin kunya irin na 'yan uwanta ba.....amma idan tayi maka wani abun har sai ka gwammace baki ta bude ta gasa maka rashin kunyar. "Yanzu meye mafita?" Ya fada a sarari yana juya hannaye irin na wanda ya banu ya lalace,daidai nan matarsa umma asabe tayi sallama ta shigo dakin. Kusan duka wayar da farouq din keyi da kawu nashi hankalin yana kan news da suke hasko faduwa da tashin hannuwan jari a kasuwa a yau din. Yaji suna sallama da kawu rufai din,sai wayarsa dake ajiye a gefe ta dauki ruri. Kamar kowanne lokaci da bayyanar sunanta saman fuskar wayarsa ke sanyashi jin wani iri haka ma yanxun. Ya miqe ya zauna sosai yana sauke qafafunsa dake harde a dazun,ya daga wayar ya saka a kunnensa yana yin sallama. "Wa'alaikumussalam..." "Barka da dare" Ya fadi a nutse yana qoqarin saita kanshi. "Barka kadai......idan kana gida ka shigo yanxu inason yin magana da kai". Dan shuru yayi kafin ya amsa a taqaice da "Okay" Amsawar tasa ya bata daman katse kiran,ta ajiye wayar tana sake hada kalaman da zata tunkareshi dasu. Kaman bazai motsa ba sai kuma ya miqe,farouq ya miqa masa dayan wayan tashi "Mun gama magana......" "Ba wani abu me muhimmanci a ciki da saika sanarmin......ka riqe duk bayanansa zasuyi maka amfani wajen qarasa plan din daka tsara". Dariya farouq ya saki yana lumshe idonsa,ya kuma sake relaxing abunsa sosai cikin kujera "Hakanma ni yayimun.....zakaga kalar tawa ja'irartar". Bai amsashi ba ya soma wucewa inda flip-flops dinsa ke jere nau'i daban daban cikin wata ma'ajiyar takalma dake bakin qofar shigowa falonsa,ya miqa hannunsa kan wanda ya fara gani,ya zarosu ya sanya a qafarsa ya buda qofa ya fice yana jin wata fargaba haka kawai tana saukar masa wadda baisan dalilinta ba. Yau ma gidan ba kowa,banda malam saidu daya bude masa qofa suka gaisa ya wuce ciki. Ita daya ce hakimce saman lafiyayyun kujerunta,falon bai cika hask sosai ba sai haske fitilun da aka qawata ginin POP din dake saman falon. Da murmushi a Fuskarta ta amsa sallamarsa tana tashi daga kashingidar da tayi ta zauna sosai. Ya zare takalmansa ya barsu daga nan sannan ya qaraso ciki. Kaman kowanne lokaci,ba kasafai ya fiya zama saman kujera ba idan ya shigo falon yauma haka,sai ya samu daura da inda take zaunen ya zauna yana tanqwashe qafafunsa kamar me shirin fara cin abinci. "Bari na samo maka ruwa tukunna". Ta fada tana miqewa sannan ta wuce cikin kitchen. Bai dakatar da ita ba don gudun ballo wata rigimar daban kuma,saidai bayajin ko a gabansa akayi aikin ruwan zai iya aminta yasha shi. Kansa ya daga kadan yana kallon falon da ainihinsa nan din dakine na mahaifinsu ciki da falo......dakin da ya rayu yasha jiyya a cikinsa har ya koma ga mahaliccinsa.....dakin da nan ne waje na qarshe data sanya qafafunta ta tsallakesu ta fice......dakin da anan sukaci gaba da zama shi musaddiq da jadda cikin talauci har itama jadda ta tafi ta barsu. Yau ga dakin ya zama wata qawatacciyar duniya.....saidai wadanda suka cancanci suci arziqin abun sunyi qaura sun barwa wani sashe da basu da alhakin samun gajiyar abun. "Bismillah" Ta fada tana dire masa tray din sannan ta koma saman kujera ta zauna. Idanunsa ya lumshe da suke masa wani irin radadi sannan ya budesu,ya miqa hannu ya dauki gorar ruwan swan ya balleta ya tuttula a cup ya dauki cup din kawai ya riqe a hannunsa "Tashi ka koma saman kujera ka zauna sosai magana nakeso muyi dakai me matuqar muhimmanci" Tayi maganar tana soke yatsunta cikin na juna tana sassauta sakin Fuskarta zuwa daurewa. Kallo daya tak yayi mata,sai ya dire ruwan ba tare daya ce komai ba ya miqe din ya zauna saman kujerar dake fuskantarta. "Muhammadu" Ta kirashi kai tsaye da zallar sunansa,kiran da ya saka gabansa faduwa abinda ya mance rabonsa da yajishi "Na'am" Ya motsa tausasan labbansa ya amsa da wata murya can qasa. "Wacece ni a wajenka?" Ta jefa tambayar a gareshi tana kafeshi da idanuwa. Jin abun yayi yayi masa banbarakwai kawai,yana ganin amsace bayyananniya ai da ba sai anyi dogon neman amsa ba. "Mene ya kawo wannan tambayar maamah?" Ya fada a sanyaye "Akwai.....amma kafin sannan inaso naji amsa daga bakinka.....don komai da zai taso daga baya din yana da alaqa da kalar amsar daka bani" Qasa yayi da kansa ransa da zuciyarsa suna sake jaddada masa tabbas akwai wani abu. "Mahaifiyata ce ke" Kai ta jinjina tana jin alfahari,tana jin kalmar har tsakiyar ranta,zamowa mahaifiya ga mutum irin Muhammad jadda ba qaramar takar sa'a bace ga kowacce mace.....ba qaramin zamowa riba bace ga kowacce uwa me haihuwa.....ribar qafa ce ta kowacce bangare. "Shikenan......akwai buqatar da nake da ita daga gareka.......kuma umarni ne zan baka,bawai roqo ko neman alfarma nakeyi ba......ina magana ne da harshen uwa kuma mahaifiya........ba me cin alfarma ko darajar kowa ba cikin duniya......ina magana ne da baki na uwa wadda haihuwa ta karramata da wannan darajar..." Tayi maganar a jere cikin sauti da yanayin da ya sanya yaji kowanne noti na jikinsa ya qarasa kwancewa "Wacce irin nannauyar buqata ce haka?" Ya samu bakinsa da subucewa yana tambayarta ba tare daya shirya hakan ba don dai kawai kunnuwansa sun kasa jumurin jiran jin me zai fito daga bakinta. Gajeran murmushi ta saki tana gyara zamanta "Na godewa Allah da tun yanzu ka gane girman buqatar uwa akan d'anta.......muhammad" Ta sake kiransa da sunan nan dake masa girma da nauyi. "Ka jima kana bijirewa umarni na.....kana sabawa Maganata......ka dade ina fadin magana kana taketa,kana mata riqon sakainar kashi......ina dauke maka kai,ina maka kara ina maka alkunya......ina maka sassauci irin na uwa......ina da tarin buqatu......ina da tarin burika.....ina da mafarkai da yawa da nakeso na cikasu amma dukka ban samu wannan damar daga gareka ba.....a yanzu ina da wani babban mafarki akanka na samu macen auren dake sonka ba don dukiya ko abinda ka mallaka ba,macen auren data dace dakai ta gari wadda zata zauna da kai da zuciya daya......wannan damar da ita nayi amfani na laluba na kuma zaba maka nagartacciya guda daya......wadda nakeso kai tsaye ka karbeta saboda umarni ne nakai tsayen daga uwa zuwa d'anta!" Ta qarashe maganar da kakkaifan harshen daya sanyashi wata matsananciyar faduwar gaba da bai taba jin irinta ba "Ya ilahal aalameen" Ya furta a zuci da bakinsa murya can qasa. Wanne irin lamari ne haka katsam lokaci guda?. Matar aure fa take magana maamah din......maamahn da bata gama zama nagartacciyar uwa cikakkiyar garkuwa ga 'ya'yanta ba ta kowacce fuska?,yaushe zata samu nagarta fahimtar nagartacciya cikin mata?. "Maamah......aure ba abun wasa bane,aure ba tafiya ce ta yau kuma a kammalata gobe.....aure abune da akeso mutum biyu su gani su kuma aminta......" "Dakata Muhammadu!!!" Ta furta a tsawace tana daga masa hannu. "Ka manta a farkon zance na?,na gaya maka ba neman shawara nake ba?,hukunci na yanke ina gaya maka hukincin ne saboda kasan da wanzuwar abun.......zan nema dangin mahaifinka koda mutum qwara daya ne,da nawa ahalin mutum uku a ciki,su kadai sun isa suje neman auren.......bana buqatar komai naka a ciki......bana buqatar sisinka,zanyi komai.....abu guda daya tal nake buqata" Tayi maganar tana daga yatsanta dan manuni. "Ka kula da ita yadda zaka kula dani mahaifiyarka......ka bata kulawa ka tattalata kamar yadda kowanne d'a namiji yake tattala mahaifiyarsa da 'yarsa da matarsa......idan kanaso ka hadu da mummunan fushi na kuma kalar wanda baka taba gani ba......ka gwada tsallake wannan dokar" Wani irin mawuyacin hali yaji yana neman fadawa,lokaci daya taji tamkar an daga duniyarsa ne an kifata daga sama zuwa qasa,yayi qoqarin tattaro muryarsa a raunane yanason sake fahimtar da ita,don shi ba abinda ya fahimta a wannan abun face wani kitsatse kuma shiryayyen al'amari da muddin ya rufta ciki rayuwarsa kaf yana hango rugujewarta "Amma maamah......" "Muhammadu.......muddin kace zaka gwada bijiremin.... To ka jira tsinuwa daga gareni da zata biyo baya......zan daga maka nono......zan maka Allah ya isan nonona daka sha?!!". Qas yayi da kansa yana jin wata zufa tana keto masa,duk kuwa da wadatar ac dama pan dake kadawa a hankali. Jin jikinsa da kansa yakeyi gaba daya kaman ba nashi ba......yanajin kaman gini me hawa goma ne ya lafto saman kansa. Bakinsa yayi nauyi qwarai,yaji bashi da wata sauran kalma data rage masa. "Kiyi haquri" Ya fada a mugun raunane.....raunin da a sannan idan abokan adawar kasuwancinsa suna wajen zasu rantse da Allah ba muhammad jadda bane. "Naji......tashi kaje ka fara shiri" Abinda tace dashi kenan wani dadi yana ratsa qasan zuciyarta ganin alamun nasara baro baro a tare da ita. Zuciyarta fari tas sanda yake fita,tana jin wannan karon sa'arta ce,lokacin sa'arta yazo,sabreen kawai ta rage mata,sai kuma ta koma wajen boka ya hada mata dukkan kayan sa'a,ya bata kuma manya manyan bomabomai din da zata bawa sabreen ta shiga gidan dasu masu qarfin da sa'arta zata qarasa cimmata nan da nan. Da qyar yake jefa qasarka gaba yana nufar gidan ba tare da cikakkiyar fahimtar inda yake sanya qafar tasa ba. "Wannan wanne irin tashin hankali ne?,wanne irin shiri ne kuma daban wannan bayan shirinta nason ciyar da su da shayar dasu da kayan tsubbu da suka kaucewa hanya sunna da kuma koyarwar musulunci?" Ya yiwa kansa da kansa tambayar sanda yake zubewa saman kujerar falon kowanne sashe na jikinsa yana mutuwa. "Wanne shiri ne daya wuce ta ajiye maka wadda zata baka komai kaci ka kuma sha kai tsaye ba haufi?,wadda zaku rayu tare qarqashin rufi daya?,ta yadda komai zaifi sauqin kama ka?" "Yes!" Ya samu kansa da fada bayan dogon nazarin da kwanyarsa ta tafi me dogon zango. Ba shakka kusan duk wanda ya sani tare da maamah babu wani halin dattako ko na alkhairi sam sam tare dasu,ta yaya maamah din har zata iya cimma MAR'ATUSSALIHA da irin wannan halaye da dabi'u nata?. Tsaftatacce sai tsaftatacce fa haka qur'ani ya fadi Allah da kansa kenan yake bamu labari. "Wacce yarinya ce ke shirin jefa rayuwarta tsakanin runtsin da yafi qarfinta?,wacce yarinya ce wannan?" Yayi tambayar a fili yana qanqance idanunsa. Anaso ayi amfani da maamah ne ko kuma maamah din keson amfani da wasu?. Ya sake tambayar kansa da kansa yana sake zurfafa nazarinsa wanda yaji kaman kansa zai tarwatse,sai yaji me yasa bai tsaya ya nema cikakken sani akan wacece ba?,sunanta?,d'iyar wace?,a ina take?. Yanaso ya sani da gaske.......yana buqatar sani,amma kuma bayaso yayi kowanne motsi ko taku da zai sanya maamah ta sake tsaurara aqidarta a kansa. Tana a wajen tana juya girman nasara takun farko data fara samu ita da matar da takewa kallon aminiya wato hajja,ta kuma neman alfarmar ta shirya don rakata wajen boka nan da kwanaki biyu ko uku kafin masu neman auren sabreen sukai ga magabatanta saiga zuwaira ta shigo. "Alhaji hamza ne yake son magana dake". Sosai zancan ya bata mamaki,ta dauke wayar daga kunnenta tana kasheta gaba daya cike da madaukakin mamaki. Alhaj hamza yau a gidanta?. Bai taba tako koda qofar gidan ba koda kuwa da wasa tunda ta dawo gidan da zama karo na biyu......ko a baya ma ba zata iya tuna sanda irin haka ta faru ba sanda marigayi yana da rai ballantana yanzu. "Alhaji hamza kuma?" Ta sake jaddada tambayar ga zuwaira. "Eh shi". "Ce masa ya qaraso ciki,faduwa tazo daidai da zama......nima nemansa nake" Tayi maganar tana hade ranta da kyau tun Alhaji hamza din bai kai ga shigowa cikin falon ba,zuciyarta tana raya mata indai har daga fitar fuad ne yaje yakai masa qararta lallai sai ta saka sunyi nadama daga shi har fuad din. A wannan karon zata nuna masa shi da munafukar matarsa.....dama sauran dukkan munafukan dake gefe suna kallo cewa,itace fa ta haifi fuad harma da musaddiq......babu wani da yayi mata wahalarsu.......babu wanda kuma yasan ciwo da zafinsu sama da ita. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶H ̶U ̶G ̶U ̶M ̶A ◦•●◉✿PAGE 98✿◉●•◦ Cikin sallama da kuma cikakkiyar kamala ya shigo falon. Kujerar da tafi kusa da bakin qofa ya zauna tare da bismillah a bakinsa. Ciki ciki ta amsa tana gyara nata zaman gami da harde qafarta ta dorata daya bayan daya don nuna izza da tata isar. Bata jin zata iya gaidashi ko gabatar masa da wani ruwa ko lemo wanda mutumin dake da kima da martaba kawai akewa haka,sai ta jefa masa tambayar "Ina fata lafiya ce ta kawoka.....sannan ina fatan alkhairi ne ya sanyaka takowa cikin gida na?". Wani murmushi ya sake dake cike da kamala da dattako. Shi ba mace bane,saboda haka bayajin yana da wani lokacin bata lokacin gutsi gutsin maganganu "Batun d'anki kuma d'anmu shine ya taso dani....." "D'ana dai....." "Hakanma yayi.......jiya ya sameni da zancan samun matar aure da yake buqatar aje nema masa ita,kuma cikin qasa da sati uku yakeso a kammala komai". Wani murmushi ta saki tana kada qafarta,shuru na kusan minti daya sannan ta soma magana cike da izza. Malam hamza......ita kuma wacece?,a ina take?,shi yace yanaso ku kuma aura masa akeso ayi?.....koda yake duka wadannan tambayoyin basu da wani amfani......na yiwa d'ana mata.....kuma nan da sati uku in sha Allah ya zama magidanci,saboda haka ba wani batun wata yarinya da zan karba" Tayi zancan tana sauke qafafunta data harde. Cikin son hadiye dafin maganganunta ya dubeta da duba na tsanaki "Kin manta cewa a addinij islama muke ba wasu addinan na daban ba?.....laifi ne idan kin aura masa wadda yakeso shima ya auri wadda yakeso duka a lokaci guda mariya?". Yayi maganar hankali kwance yana tsareta da ido. Kallonsa takeyi itama,saidai kaifin nasa idanun ya shafe nata,don haka ta nanye dubanta a kansa tana jin sam sam bata aminta da wannan zancan nasu ba. Zuciyarta kawai tana bata wata qulalliyar ce.....sun nemo masa mata ne kawai bisa hadin baki suna son cusa masa don a samu damar cin dukiyarsa da lasisi (ni kuwa nace uhmmmm.....idan mutum yana aikata abu sai ya dauka kowa ma haka yake?🤔🤔....kaico da uwa irin maamah). "Koma wacece ni uwa ga Muhammed fuad ban karba ba ban aminta ba". Ta fada tana tura dankwalin kanta gaba. Shuru ya ratsa na wasu mintuna,tamkar bazaice komai ba sai kuma ya miqe tsam " Zai auri zabinki.....kamar yadda ba wanda ya isa ya hanashi auren zabinsa......abu daya ya rage miki ki bada komai akan yarinyar zamu binciki waye mahaifinta......idan har ta cancanta.....zai auri mata biyu a rana guda.....zabinsa da zabinki.....komai bazai wuce kwanaki hudu ba,don haka ki sanar da iyayensa bangaren danginki don a fita haqqin kowa dake kansa". Daga haka ya juya yana takawa a nutse yana fita a falon. Miqewa tayi tsaye tana bin bayan nasa da kallo,Zuciyarta na wata irin tafasa,ta yaya kansa tsaye da wannan confidence din yakeson nuna mata qarfi da iyakarta akan abinda duk duniya tafi kowa iko dashi?. "Ba zata sabu ba" Ta dauki wayarta da sauri tana kiran hajja. "Daga hankalin na meye?,koma wace muna da boka,fiddata bazai zama wani abu me wahala ba.....ki bashi kwatance gidan da sunan mahaifinta na ainihi.. ..kibi a hankali ki zuba masa idanu......wannan karon harshi sai munyi maganinsa" "Na gode aminiyata......duk duniya bani da masoyi kamarki" "Yiwa kaine ai" Ta fada da binnanniyar ma'anar da ita daya ta barwa kanta saninta. *****A mamakance yake riqe da takardu biyun a hannunsa yana dubansu. Gyara zamansa ya sakeyi sosai sannan ya daga kansa ya kalli anni dake zaune a gabansa "Abunne yaketa bani mamaki aminatu.....yarinya daya ce shi da mahaifiyarsa duka ke fatutuka fa". Dan muskutawa kadan anni tayi tana daidaita zamanta. "Ina cikin damuwa abba tun randa kace maamah ta zabawa fuad matar aure......bamusan ya zata kasance ba yarinyar.....to amma yanzu kuma na shiga rudani ne,ya akayi dukansu suke neman yarinya daya cikin rayuwarsa?". Shuru abban ya danyi,sannan ya ninke takardar ya ajiye a gefansa yana sake dubanta "Ina aminatu?" Dan murmusawa kadan tayi saboda shi kansa yasan wannan sarar tasa tana bata dariya "Gani abba" "Yauwa.....abu na farko da nakeso ba gaya miki shine......ki dinga tunawa mariya itace mahaifiyar Muhammadu na ainihi,ita ta dauki cikinsa tahaifeshi ta kuma reneshi na wasu shekaru kafin ya dawo hannunki.....dole haqqin dake wuyansa nata yafi naki.....sannan so na uwa daban yake,duk yadda kikeso ki kawar masa da abu me cutarwa akwai guraren da ba huruminki bane shiga cikinsa" "Abba nafi mariya qaunar me babban suna....." Wani murmushi ya saki yana girgiza kai "Kin fita sanin ya kamata ne,kin fita kuma tausayin dan adam da qaunar yara koda ba naki 'ya'yan bane.......mu ajiye wannan.....abinda nakeso dake......a baya kafin bincike ya zamaya ya fito daga gida daya nima ina da wannan shakkar da kokwanton,saidai kuma ba hurumina bane na hana.....bugu da qari na samu relief da naji shima itace yarinyar da yake nema din,koda mariya da tata manufar na hadashi da yarinyar.....to shi ba yadda za'a yi ya cutar ai da kansa da kuma tasa rayuwar......abun tambayar qwaya daya ne kawai dana gaza banbancewa........ya akayi dukkaninsu sukasan yarinyar?,kuma dukkansu suka afu a kanta?,wanda samun amsar shima na huruminmu bane.....don muhammad yakai munzalin baligi kuma aqili da bazai dauko abinda zai cutatar dashi ba". Kai kawai anni ke kadawa,maganganun abba suna gamsar da ita,daga bisani da saki nannauyar ajiyar zuciya "Haka dukka maganganunka suke abba....daga yau in sha Allah bazan gushe ba ina adduar idan akwai sharri cikin lamarin.....ubangiji al'arshi ubangijin sammai ya juyar dashi ya koma alkhairi,ya kuma tsare dukkan wani sharri" "Yau aminatu na......yanzu kikayi magana me kyau" Sai ta saki murmushi tana jin kunya tana dan kamata,don har yanzu girma tsufa ko shekaru basu sanya wannan kunyar dake a tsakaninsu ta gushe ba. ****Shudewar awanni uku kenan da wata murya tayi kiranta,ta kuma shaida mata cewa kirane nakai tsaye daga gurin hajiya mariya akan batun neman aurenta,ta aminta ko aje zuwa mataki na gaba?. Duk da batasan meye ainihin abinda suke nufi da mataki na gaba ba,amma hakan bai hanata sauke saqo da kakkausar murya ba. "Idan tana saurare shikenan.....idan kuma saqo zaki isar mata ki tsaya ki saurari komai dakyau don kada kiyi batan koda harafi daya wajen isar mata da saqona......ni aminatu sabreen ba haja bace a kasuwa da kowa zai iya tayata da farashin da yaga dama ya kuma siya,'yantacciyar diya nake ba baiwa ba wadda keda daman zabawa kanta komai da kuma kowanne yanayi na rayuwa......da ita da d'anta dama dukkan dukiyar da suka mallaka basa gabana koda kuwa zasu mallakamin dukkan abinda suka mallaka din.......ki gaya mata kada ta sanya ran wataran akwai abinda zai canza ni......ba wani abu da zai sauya tunani na akan maza......ba d'anta bama kawai.......har yau ba'a samu nasarar Haifa min wanda zai janye ra'ayina naji ina da niyya ko sha'awar ya zama mijina". Sosai kalaman suka daki maamah wadda ke zaune a gefe tana sauraron komai. Ba zata iya jurar jin wadannan nauyayan kalaman ba,don haka ta miqa hannu ta gintse kiran cikin wani matsanancin fushi,sannan ta dauki wayarta tana laluben wata number tana cewa "Zaki fahimci cewa komai yana da nasa iyakar". Numfashi ta zuqa tana duban agogo,sai tayi zumbur ta tashi ta zauna. Batasan yaushe lokaci yaja har haka ba,batayi sallar azahar ba don haka ta miqe tana sanya slipper ta nufi tsakar gidan nasu. Yadda taga kusan kowa da kowa cikin yara da jikokin gidan sun dawo sai ya dauki hankalinta. Su huda kusan sune sahun farko da sukafi kowa dawowa gida akan lokaci,ya akayi yau suka zama na qarshe?. Tun tana daura alwala take sanya ran shigowarsu amma shuru,ta kammala ta wuce daki,ta tayar da sallah ta kammala,sai tayi zaune a wajen tana zuba kunnuwa. Shuru maqatau,abinda ya sanyata miqewa kenan gabanta yana faduwa. Basu taba kai warhaka a makaranta ba,har gashi masu zuwa islamiyya cikin gidan sun fara wucewa,sai kawai ta dauki wayarta da key din dakin ta fito. Layukan nasu ta duba amma babu su,abinda ya tsananta faduwar gabanta kenan. Ta dauki wayarta zummat nemo busari yazo ya dauketa suje makarantar sai gabanta yayi wani mummunar faduwa sanda idanunta suka sauka kan number wayar da aka kirata dazu. Tunanin ya sake bnagazar Zuciyarta abinda ya sanya qafafunta yin sanyi qalau,ta sulale tana zama saman dakalin dake daura da ita hannunta yana yin sanyi qalau. Wayarta taci gaba da kalla tana kuma taya agogon dake fuskar wayar irga wucewar kowanne second,har zuwa sanda ya nuna mata qarfe biyar daidai harda rabi na yammaci sai kawai ta danna kan number ta kira. Kira ta dinga yi ba qaqqautawa amma ba'a daga ba,yayin da duhun dare yake sake kusantowa,yan islamiyya da wadanda na sukaje kasuwa sunata dawowa suna giftata kowa idanunshi a kanta don bash saba ganinta haka zaune a waje ba,wanda ita sam bata damu da hakan ba,har zuwa sanda kallon da yawan kiran suka soma quntata rayuwarta,saita miqe tana komawa cikin gida afujajan cikin matsanancin tashin hankali. "Indai tayi kuskuren sanya min 'yan uwa cikin harqallar da daga ni sai ita......tabbas sai na shayar da ita mamaki koda hakan shine abu na qarshe da zanyi a rayuwata" Ta furta a sarari ganin yadda duhu ke sake kutsowa ba'a daga wayar ba ba'a kuma biyo kiran ba. Sanda ake haramar kiran sallar ishai,sanda take zaune kan abun sallah ta bada faralin magariba cikin rashin nutsuwa da tashin hankali tare da zurfafa tunanin inda zata kamo bakin zaren kiran ya shigo wayarta. Duk da kirana ne da take ta dakon shigowarsa amma bata daga ba sai dab da zai tsinke. "Ki sakesu.....don su din basusan komai akan rayuwata ba". "Good......naji dadi nayi kuma farinciki,haka kwanyarki take ja da wuri?" Hajja harira ta fada cike da mamakin gaske kan yadda ta dauki haske da wuri. Lalle da gaske ne da akace musu tana da basira tana kuma da hadari. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶H ̶U ̶̶G ̶U ̶M ̶A ◦•●◉✿PAGE 99✿◉●•◦ Idanunta ta lumshe tana jan wani numfashi har cikin hunhunta,tana jin wani zafi baqinciki da radadi suna ratsa zuciyarta. "Ina sake maimaitawa.....kada kuyi involving innocent lives a cikin wannan deal din......ku sakesu safely". "Karki damu yarinya.....qannanki zasu dawo hannunki cikin aminci..... Munyi hakanne kawai don mu gwada miki banbancin tazarar dake tsakanin sama da qasa......don kuma mu nuna miki girman wutar da kikeson wasa da ita kike kuma tunkara ta hanyar bijirewa umarninmu" Sake lumshe ido tayi,maganganun hajja suna ratsata ranta yana sake baci "Ku sakesu" Ta sake maimaitawa muryarta cike fal da bacin rai. Ta nason fadin abubuwa masu yawan gaske,saidai kuma tana qoqarin tausar zuciyarta. Ta sani ta riga data shiga hannunsu,sun mata shigar sauri,sunyi mata kuma shigar ba zata,dole tabi komai a sannu,dole itama ta shammacesu kamar yadda sukayi mata suma. "Zamu sakesu amma bisa sharadin kin amince da buqatarmu?......" Wani yawu me tauri ta tattaro a bakinta ta hadiyeshi da qyar. Baya cikin tsarinta QARYA amma yanzu ya zama dole ta fara gwadata akan mutanen "Na yarda" Ta fada kanta tsaye. Murmushi hajja ta saki sannan ta sake cewa "Kada fa kiyi tunanin kin amince don ki yaudaremu mu sakar miki yan uwa haka siddan.....lalala.......kina iya karya alqawarin,amma ki sani daga wannan lolacin daga kuma rana irin ta yay rayuwarku tamu ce,ba wani motsi ko taku da zakiyi ba tare da munsan ina zaki ko ina kika nufa ba.....ko yaya muka sameki da laifin yunqurin karya wannan amincewa da kikayi daga yau har zuwa ranar da zaki kammala aikinki.....hukuncinki abune da bazai fadu ba,na barki lafiya" Daga haka kiran ya yanke. A hankali wayar ta sulale daga hannunta,wanne irin abune kuma ke shirin tunkaro rayuwarsu bayan tarkuna data tsallake masu tsananin girman hatsari?,su waye ne wadannan mutanen?,me suke nema da rayuwarta?,me yasa basu hango kowa ba sai ita?. Take idanunta suka sake dawo mata da fuskokinsu. Fuskar hajja a farko,ta tabbatar a yanzu haka ita uwar wasu ce......me yasa duniya ta cika da masu son zuciya da masu son rai?,a yadda take uwa tayi imanin ba zata taba bari wani aibu ko abu me cutarwa ya samu yaranta ba..... to amma me yasa su take qoqarin ingiza rayuwarsu zuwa ga wani bigire?,don ba itace ta haifesu ba?,kenan kowa dansa ya sani?,wai shin a duniya WAYE ZAI RUNGUMI MARAYA IRIN RUNGUMAR DA UWA KEWA DANTA NE?. A hankali kuma sai tunaninta ya hasko mata fuskar maamah. Har yanzu bata yarda ita din uwa bace ga yaron da take nemawa aurenta.......idan kuwa har hakan ya kasance da gaske ita uwarsa ce?tabbas tata lalacewar ta dara ta hajja. Me yasa take mata famfo akan danta ba zata tayata ta inganta masa rayuwa ba?,me yasa idanunta suke rufe akan cikar qazamin burin da batasan inda zai kaita ba. Wadannan tarin tunane tunanen su suka zaunar da ita adadin lokacin da bata sanshi ba. ******Dukkaninsu ta sanyasu cikin jikinta ta rungumesu tana sauke ajiyar zuciya a tare da hadiyar wani abu wani yanayi yana tsargawa a dukka sassan jikinta washegarin ranar da tayi zaune tana dakon ta inda zasu shigo. Dukkaninsu cikin abaya masu tsananin sulbi da tsada. Nadra da haneefa sun kasa daina bata labari tamkar wadanda sukayi balaguron alkhairi. Da alama zuciyarsu da hankulansu basu riski wani abu mara kyau ba a zahiri da zai ankarar dasu hadari suka fada ba. "Suna da kirki adda.....wannan kayanma su suka siya mana fa bayan kowa ya zabi irin wanda yakeso" Nadra da kanta ke jikin Sabreen ta fada "Munci kayan dadi sosai adda.......dakin da muka kwana me kyau sosai shima,harda Ac da komai da komai" Haneefa ta fada cikin zumudin gaske tana riqe box na chocolate dinta da kyau farinciki muraran cikin muryarta. Idanunta ta mayar kan huda,ita daya ce kawai a zaune ta zubawa Sabreen idanu,tunda kuma suka shigo itace bata ce komai ba a cikinsu. Duban tsakiyar idanun hudan tayi ta karanci lallai nata feeling din akan mutanen yasha banban dana 'yan uwanta,zataso taji meye a zuciyarta?,meye nata hasashen. Zataso tayi magana da huda koda ba zata fahimceta gaba daya ba,aqalla ta rage wani nauyi daga zuciyarta dama qirjinta. "Ku shiga ciki ku canza wasu kayan.....kema haneefa ki ajiye wannan chocolate din" . Tare suka miqe nadra tayi gaba haneefa tabi bayan ta suna maganganunsu. Da hannu Sabreen ta yafito huda,sai hudan ta taso tsam ta dawo gabanta ta zauna. Dukka hannuwan huda Sabreen ta kama ta sanya cikin nata hannun,suka fara kallon kallo a tsakaninsu,kafin wani lokaci idanun Sabreen din suka cika taf da qwalla. Tana jin kamar ta gaza.......tana jin kamar ta kasa basu kariyar data dace dasu,tana jin tausayinsu matuqa da gaske,tanaso suyi amintacciyar rayuwa yantacciya kamar kowanne yaro. Tana qyamatar dukka abinda zaya tabasu,to amma da alama a dan tsakanin nan wata qaqqarfar guguwa ke shirin tasowa,wanda bata sani ba zasu kubuta daga azabarta da kuma qurarta ko kuma dukkaninsu zasu fuskanci wani sakamakon da ubangiji ne kawai yasan yanayin qarshensa. "Inaji kamar na gaza huda.....kamar banyi aikin daya dace ba......" Tayi maganar qwalla cike a idanunta,muryarta kuma tana rawa sosai kamar zata saki kuka. Damqe hannunta hudan tayi tana girgiza kai "Kinyi dukkan qoqari adda.....kin bamu kowacce irin mafaka da kariya a rayuwarmu.....tundaga sanda suke daukemu jikina ya bani akwai matsala,duk kuwa da bamu fuskanci komai ba sai haba haba da maraba,sun bamu kowacce irin kulawa.....amma bamu sansu ba,bamusan su wayesu ba.....adda,abu daya suka gayan shine,dansu sukeso ki aura......me yasa ba zaki aureshi ba adda?,kaman alkhairi sukeson hadawa......me yasa bakison aure?". Kai Sabreen ke kadawa da sauri da sauri. "Ban shirya aure ba huda.....ban shirya auren kowa ba,koda zanyi aure sai na aurar daku gaba dayanku a hannun nagartattun mazaje.....saina aurar daku a muhallin da nasan koda mutuwa nayi bani da haufi......bani kuma da kaico....amma ba yanzu ba,ba a irin wannan yanayin ba huda....idanma auren zanyi.....bazanyi auren cutatarwa ba,dansu baimin komai ba,ta yaya zan aureshi kawai don na zama silar da mallakarsa?" Maganganunta na qarshe ne hudan bata gane ba,sai ta zuba mata idanu tana kallonta. Duk da tarin fargaba da yake ciki yake kuma kan fuskanta akan yadda zai tunkari Sabreen da maganar bada aurenta.....to qarshen tika tika tik inji bahaushe.........a yau shi rufai ahmad ya karbi komai na auren Sabreen din hatta da sadakinta bisa yanayin da bai taba zata ba. Abinda yasha kwana yana mafarki shine......daga shi har Sabreen din sun cinye dukiyar aurenta da hannunsu,tun daga kudin aure kayan lefe sadakinta dama komai da komai na kudin baki. Sai gashi a yau ya wayi gari da baquncin wasu attajiran mutane dauke dakkan wata dukiyar aure. Kama daga sadakin aure daya tasamma naira miliyan biyar.......maqullin mota qirar Ferrari da baisan inda ma zasu ajeta ba........da tarin goro daya kusa huhu talatin,kwalayen alawa da suka kusa kaiwa kwali hamsin da tarin dabino da baisan ina zai ajiyeshi ba. Ga wasu uban kudaden da shi kansa baisan miliyan nawa bane na amarya kyauta ta daban,shi kansa ga wata dukiyar da aka mallaka masa a mazauninsa na uban amarya,abinda ya sanya jikinsa dukka ya dinga bari......Allah yasa komai ya tafi a tsari bisa taimakon kamilin amininsa. Qarfe uku na yammaci motar da yasanya ta jido komai da komai ta tsaya a gaban gidan daya kasance gida ga d'an uwansa kuma uban riqonsa da yayi masa alkhairi masu tarin yawa a rayuwarsa. Yara masu wucewa ne suka fara tsaiwa kallo ganin mota shaqe da kayan kwali kamar ana shirin bude provision. Wannan ya bashi damar kiran yaran,kafin wani lokaci sai gasu sun cika wajen harda wadanda ba'a kira ba,suka fara hidimar diban kayan suna shigewa cikin gidan dasu. Hadiyya na daga bakin qofar famfo tana wanke uniform dinta na school of nursing,tazo gida ne weekend anjima kuma takeson komawa,yayin da bibo ke zaune saman kujera 'yar tsuguno daga qofar kitchen dinsu tana gyaran wake suna taba hira da shalelenta. Daada ce ta fito a daki dauke da buta don kama ruwa gami da daura alwalar sallar la'asar. Daidai sannan yaran suka fara layin shigowa "Kai.....kai daga ina?,ko.izzatu ce tazo?,izzatun alkhairi,don ita daya ce kaf gidan nan ke iya shigowa da kabakin arziqi haka" Bibo ta fada tana sakin murmushi "Kawu ne yace mu shigo dasu,ku gyara waje don suna da yawa,a ina za'a ajjiye?" Wani yaro cikin yaran wanda shekarunsa suka dan dara na sauran ya fada yana sauke kwalayen hannunsa. "Wai kana nufin rufai?" Bibo ta tambaya "Indai shine aje masa inda yace,kada yazo ya yiwa jama'a tijara,bansan ma masifar data sakashi kawo mana kaya gidan nan ba,shi abinsa da baya tabuwa,tunda kudin cacar nan suka samu mu kuma bamu da kwanciyar hankali". Taja qaramin tsaki daada na gaban famfo tana tarar ruwa wanda suka kusa daukeshi don haka da qyar yake zuwa. Tun tana irga adadin kwalin har suka fara yawa suka fara kuma shallake tunaninta. Tun daada na bandaki har ta fito tana daura alwalarta,sai bibo ta ajiya farantin waken tana cewa "Wai rufai sai ya cika mana gida hankalinsa zai kwanta?,wanne irin kwalaye ne haka na alawa da biscuit masu tsada kuma?,ko kantin siyayya zai bude ai sai haka ko?......hadiyya tsame hannunki ki leqa ki ganemin". Zubda ruwan kurkurar bakinta daada tayi,a karon farko tayi magana "Ke kin fiya ci da zuci wallahi.....wai shinma a kanki kayan zasu zauna?,koma meye ai zaiyi bayani ko?,tunda shima kinsan bakinsa baya shuru". "Adai dubo din daada abun ya fara wuce lissafi". Ko kafin hadiyya ta fita ta dawo kwalayen sun sake yawa,sai gata tana zare mayafinta "Aida saura bibo.....shikam yana can yanata bawa yara umarnin aci gaba da shigo dasu". Wannan karon har daada tsaiwa sukayi suna kallon ikon Allah,zuwa wani lokaci da faffadan tsakar gidan nasu yayi hani'an da kaya,muryar nan tasa dake iya tada mutum a barci ta karade tsakar gidan,ta kuma ratsa har kunnuwan Sabreen da haneefa dake riqe da hannun juna a daki. "Me bacci ya tashi......wanda kuma idonsa yake biyu ya bani hankalinsa ta nan......me aiki ya ajiye aikinsa saina kammala bayani na" Ya qarashe maganar yana saba babbbar rigarsa gami da jawo botikin fenti ya haye sama yana harde qafarsa daya kan daya. "Lallai ba'a daya a dangi.... Kuma gado ba karambani ba......yau ta tabbata cikin diyoyin dan uwana akwai wadda tayo gadon arziqi irin namu.....ta fita zakka diyar albarka haihuwar asuba" Yayi zancan yana dukan tafin qafarsa daya dora saman gwiwarsa. Harara bibo ta galla masa tana jan qaramin tsaki "Kai ka fiya sarqa zance,ba yadda za'a yi kayi magana miqaqqiya......akan meye kake magana?akan kuma wace?" Tayi zancan gabanta yana faduwa,saboda tsoron kada zuwan matan nan a wancan kwanakin yana da alaqa da wannan uban kayan da kwatankwacinsu basu taba shigowa cikin gidan ba. "Akan waye kuwa nake magana idan ba'a kan Sabrina ba?......akwai wata me qashin arziqinne sama da ita cikin gidan nan?". Sosai takeso ta rufe kawu da balain yadda yake ware 'ya'yansu,yana abu kamar su ba haifarsu sukayi ba,to amma kuma tana buqatar taji kan zancen sosai. "Sabrina kamar yaya?" "Sabrina?" Huda itama dake daki ta maimaita sunan tana maida idanunta akan fuskar Sabreen din data tabbatar itama taji sautin futar sunanta daga tsakar gidan nasu da yake tamkar sansanin yaqi wasu lokutan. Wuf tayi zata miqe,Sabreen tasan fita zatayi taji ba'asin sunanta da aka kama,don haka ta jawota ta zaunar da ita tana girgiza mata kai idanunta cikin nata. "Sabreen fa......cikin ikon Allah yau na bada aurenta ga hamshaqin attajirin nan da basai ba gaya miki sunansa ba.....zaki gani cikin IV" Baki duka suka saki suna dubansa,banda daada data nufi dakinta tana cewa "Allah ya tabbatar da alkhairi" "Ameen hauwa'u....ke da yake baki iya doguwar magana ba" Fara takawa yayi yana nufar dakinsu Sabreen din yana cewa "Bari naje na fito" Yayi maganarsa gaba gadi yana dosar dakin. Page 100 Yau din da cikakkiyar sallama ya shiga falon,wanda duba daya Sabreen tayi masa qirjinta taji yayi wani mummunan faduwa. Ta dauke idonta a kansa tana amsa sallamar ta dubi huda. "Ki wuce ciki ku zauna keda su nadra.....kada ki bari haneefa ta fito" A sanyaye huda din ta miqe,tana jin kamar ta zauna taji da meye kawun yazo dashi. Abune me wahala ya shigo dakinsu da alkhairi,koda yaushe idan kaga ya shigo akwai wani tashin hankalin da yake tafe dashi. "Yar arziqi......yarinyar kirki,haihuwar albarka,kedai Allah yayi miki albarka,farar haihuwa,ubangiji ya jiqan mahaifinki da mahaifiyarki,ba abinda zamuce da haihuwar diya irinki sai sambarka,kin zame mana marufar asiri,kin zama kuma silar kawo mana hamshaqin attajiri cikin salsalarmu" . Dukka yayi maganar ne yana kallonta,bakinsa cike fal da fara'a. Wani irin duba take masa,don gaba daya bata fahimci inda maganar sa ta dosa ba. "Nasan ba zaki fahimci komai ba,amma yanzu zan miki bayani......ungo wannan" Yayi maganar yana ajiye damin sabbbin 'yan dubu dubi din a hannun kujerar da take kai "Duba tsakar gida daga nan idan zaki iya hangowa....goro alewa da biscuit din na aurenki......wannan kuma" Yayi maganar yana nuna kudin dake kusa da ita. "Ki cire million biyar kudin aurenki kenan,sauran kuma kyauta suka baki tukuicin auren dansu da zaki yi,kome kike buqata kuma ki samu takardar kiyi list......karki cuci kanki idan da hali ki siyo full scape masu yawa ki raba dare kina lissafawa ba abinda zaifi qarfinsu don akwai.abun fiye da tunaninki". Cikin kanta da zuciyarta taji tana tantama,anya mafarkin yin arziqi bai soma haukata kawu rufai ba?. Kaman yaji me take tunanin,cikin murmushi yace mata "Kina kallona kamar na tabu ko?,to wallahi koke na gaya miki wanda ya biya sadakin aurenki saikin zabure.......da farko dai kuma a taqaice na bada aurenki ga Muhammad jadda......mamallakin jadda diamond chores resources LTD....ga sadakinki nan......sati biyu masu zuwa zasu zo da waliyyansa da naki a tara shaidu kowa ya shaida". Wani wawan duba take masa a kaikaice kamar taga wani tuburarren mahaukaci,yayin da gagarumar jayayya da yaqi ya barke tsakanin bangarori biyu na zuciyarta. Sashen farko ya cika da fargaba da kuma zulumin komai fa kawu yana iya yi indai akan kudi ne.......kada ya zamana zancansa gaskiya ne.......yayin da wani sashen na zuciyarta kuma kewa abun kallon zancan shifcin gizo ne kawai. Ta yaya zai bada aurenta haka?,sai kace wata diyar 'yartsanar roba ko abun wasan yara?,a haka ake bada aure bada masaniyar kowa ba sai tasa masaniyar shi kadai?. Sam sam kanta ma bazai dauki wannan shirin film din na kawu ba,saidai batasan me yasa takejin muguwar faduwar gaba da wani irin tashin hankali dake cakude da fushi ba,ta zuba masa idanu yayin daya ci gaba da zuba mata bayanan da sam ita bama fahimtar me yake fada takeyi ba. Abu na qarshe data fahimta shine,wayarsa daya ciro yana cewa "Kawunki na senegal abdulk'adir ya bani damar karba.....yace kuma idan na shigo na hadaku kuyi magana". "Uncle abdulk'adir?......tashin hankali!" Maganar tayita qasan zuciyarta zuciyartata na wani irin bugu mara misali. Uncle abdulk'adir.....zazzafan mutum me tsananin tsauri da kafiya......me zafin zuciya da kafewa kai da fata wajen gaskiya.....mutumin da ako da yaushe take kaucewa haduwarsu......mutumin da ko yaushe take qaranta yin waya dashi,mutumin da har yanzu bata yarda yasan ainihin number wayarta ba gudun bin diddigi tsanani takura da kuma sanya idanu......yau shine kawu rufai ke ambata a gabanta?. Da gaske bakin alqalami ya riga ya bushe tunda har sunan kawu abdulk'adir ya fito cikin batun!!!!. "Kinga ban sameshi ba,dama dazun yacemin yau jumaa sai yammaci yake fita a masallaci.....qila ya kashe wayar da zai shiga,amma ba matsala anjima saina dawo na hadaku". Batasan takai hannu ta watso kudin qasa daga hannun kujerar ba saida taga kawu na binsu yana tarosu. "Yaushe mukayi dakai zaka aurar dani ga wani da bansan waye ba?,saboda son dukiyarka da kwadayin abun duniyarka kawu?......" Saita saki wani murmushi daya sanya hankalin kawu ya tashi "Bari na baka shawara......tunda wurwuri.....tun komai da duminsa kaje ka warware abun nan.....wallahi wallahi wallahi ba wanda ya isa ya auraminshi ko wayeshi kuwa,bansan da wannan zancan ba haihata haihata,ba kuma abinda ya shafeni bane" "Za kuwa kiyi kaffara aminatu......" Muryar kawu ta isa kunnenta sanda take yunqurin shigewa daki abinta don batason taci gaba da zama awajen. Yadda yayi furucin da wani qwarin gwiwa ya sakata waiwayowa. Yana tsaye kawun riqe da kudaden "Zakiyi kaffara.... Don baki da kudin da zaki iya biyan me jadda kudaden kamfaninsa da kika sace......hakanan bani da kudin da zan biyashi kudinsa da na ci a caca cikin rashin sani......ke din fansar kudadensa ce......cikin dattako da kuma alfarma irin tasu duk da haka suka sake biyan wasu kudaden saboda aurenki.......kin shirya yaqi da fito na fito da mamallakin diamond gold da azurfa?". Qafafunta taji suna yunqurin kayar da ita,maganganun kawun suna mata girma akai dama sassan jikinta tamkar bata da jarumta da qwarin gwiwar iya dauke dukkan bayanansa. 𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙛𝙪'𝙖𝙙 Idanunsa zube cikin na farouq sanda yake masa bayanin yadda komai ya kasance. Yayi relaxing sosai abinsa,yayin da ya miqe dogayen qafafunsa saman table din glass dake gabansa yana sipping ruwan wolf berries da wasu daga cikin 'ya'yansa cikin qaramin cup na glass. A nutse ya ajiye cup din,me sunan malam ya dauka yana ficewa dashi daidai sanda farouq ya kammala duka bayaninsa. Yatsunsa ya sarqafe waje guda idonsa akan farouq "Duka wannan hidimar wa ya aikeka tsarata?.....bakasan already ta debi kudin aurenta ba?". Qaramar harara farouq din ya watsa masa yana dora qafarsa shima daya saman daya " Duka wannan kai ka sani......abu daya nake da matsaya akai......daga gidan dattako muka fito....so dole neman aurenmu da kuma matayenmu susha banban da na kowa......that's all" Kai fuad yake jinjinawa da wani qaramin kwantaccen murmushi can qasan fuskarsa. "Tunda kuka sake basu dukiyata dole na tsaurara matakan tsaro.......kuma tamkar kun sake lafta musu bashi ne.....don already na sallamesu,nace su lissafa cikin abinda suka dauka su zare kudin komai da komai". Girgiza kai farouq yayi,wai me yake damun fuad ne akan wannan batun?. Duka duka abinda aka basun ma baikai koda kaso daya cikin goman abinda yake fiddawa kusan kullum ana rabarwa mabuqata ba. Gyara zamansa yayi ya sako masa zancan da yafi damunsa tunda suka dawo din......ya kuma tsaye masa a rai. "Abu mafi muhimmanci da kuma ban mamaki ma.....kai da maamah ashe gida daya.....kuma yarinya daya kuke nema". A nutse ya daga idanunsan nan da wani lokaci suke fita gada gada,wani lokaci kuma su kasance lumsassu kamar wanda bacci ya kama ya zubawa farouq su "Ba wadannan idanun nace ka watsamin ba......na gaya maka wani abune da yaban mamaki". Dan murmushi yaja kadan,idan bai manta ba farouq ya taba gaya masa bai fiyason ya watsa masa idanunsa ba,don wani lokaci suna masa wani iri da dan sakashi jin kamar ba me babban sunansa ba. "Maamah tana da nata plan din......kamar yadda nima nake da nawa plan din......so an samu haduwar target duka akan abu daya". Zuba masa ido farouq yayi yana jin zuciyarsa na sake cika da shakkar halin matar,duk kuwa da cewa mahaifiya take a wajen dan uwan nasa kuma rabin jikinsa. Saidai duk inda akaje aka dawo shi din me qoqarin saita fuad ne,musamman akan mahaifiyar daya fahimci shi da ita duka zukatansu sunyi nisa akan abinda suka saka a gaba. "Kada kayi mummunan zato ko zargi akan yarinyar daka zaba don ta cikashe maka rabin addini da rayuwarka.....hakanan kada ka dora zargi akan mahaifiyar da tayi silar shigowarka duniya". Wani murmushi ya saki yana sauke qafafunsa qasa,sannan ya miqe ya zauna sosai yana duban farouq "BB farouq.....har yanzu sai nake ganin kamar baka gama sanin waye Muhammad fuad jadda ba.....any way......komai ina sane dashi,zan kuma ji dashi daidai da yadda ya dace...." "But....." "But what?" Ya katsi numfashin farouq. "Don't make....." "Ba abinda zai faru dude" Ya sake fadi kawai yana miqewa daga zaman alamun yakai qarshen maganarsa dama hukuncinsa. Yaji wani irin abu tun daga saman kansa har tafin qafarsa a sanda ya kammala bincikensa kan wacce maamah keson hadasu. Kenan ba wani guri daya kuskure wajen fahimtar hatsarin yarinyar?,zallar rashin tarbiyyarta?,qwarewa wajen iya taku tare da buga kowanne irin wasa da qwaqwale zuciya dama dukiyoyin jama'a?. Kenan ya tabbata itama jan wuya ce tunda ga hadin gwiwa nan ya tabbata tsakaninta da maamah?. Abu daya ne tak! Da baikai ga ganowa ba.....hakanan duk wasu 'yan bincikensa suma basu kai ga ganowar ba shine.....KAN WACCE IRIN KWNGILA SUKA GINA ALAQAR?......MEYE LULLUBE QARQASHIN BATA AURENSHI?. Shidai yasan tasa agenda din.....TO MECECE TASU?. "zaki gane baki da wayo.....i will teach you a lesson........ You'll learn through experience" Yayi zancan yana fitar da wani siririn murmushi. Cikin ranshi yake tsara wanne hanya zaibi don ya fara gwada mata nashi salon izzar?,tasa isar?....da kuma qarfin ikonsa tun daga yanzu?". Dakatawa yayi daga tafiyar da yakeyi,yadan waiwaya kadan sashen da farouq yake "Kace ba?,kunkai sadaki ko?" Ya yiwa farouq tambayar data dan sashi maida hankalinsa akanshi "Yes.....haka na bawa abba shawara kuma hakan akayi". "Good boy" Ya fada yana dan murmushi "Ka gaya musu.....cinta shanta dama fitarta dukka yanzu suna qarqashina......kada ta sake fita muddin ba da sanina ba". " What kind of madness......" "Tell them ko ni na kirashi da kaina....you know ina da number wayarsa ko?". "Oh sheet" Farouq ya fada yana kama goshinsa. "Wai meye damuwanka?......bakason komai.....but kana bibiyan komai why?" Juyowa yayi sosai yana duban farouq din,wannan karon murmushinsa yadan bayyana "Wickedness" Ya amsa masa a taqaice. "Bai kamata a dinga qyale irinta ba haka suna ci gaba da abinda sukaga dama......punishing nasu ya kamata ayi ta hanyar da zasu ji har cikin tsoka da jinin jikinsu" Balcony dinsa ya isa kai tsaye hannayensa zube a aljihun wandonsa,yana bin dukka tsirran dake shuke daga gaban wajen da ido. Haka kawai yakejin interest dinsa yana qaruwa akan ya hora yarinyar. Abinda ya karanta maza sun badasu da har ta raina ajawalinsu haka da yawa,so dole ta fahimci nata kuskuren. *_SABREEN_* Jadda wani dadadden suna ne daya jima yana shiga kunnenta lokaci bayan lokaci,saidai ta tantance wayeshi yadda ya kamata abune da bazata iya ba. Tun daga fitar sunan daga bakin kawun har zuwa shudewar daqiqa sittin kallon kawu din kawai takeyi,kafin daga bisani qarar wayarsa ta katse wa kowa saqar da yakeyi cikin zuciyarsa. Sau da dama bayyanar number farouq cikin wayarsa wani abune dake zame masa kama da ZAK'I DA MADAC'I,daidai ga gaurayar farinciki da kuma dimuwa a lokaci guda a kuma muhalli guda. "Ga iyalin gidannan.....bismillahir rahmanir rahim" Ya ambata kafin daga wayar kaman yadda amininsa ya bashi shawarar yi domin amintar da kunnensa daga jin abinda zai dinga daga masa hankali har a samu a qare maganar auren. Sai daya zauna sosai sannan ya daga kiran,ya bada kunnensa yana sauraren bayanin da farouq ke masa,wanda duka bayanin yana yinsa ne yadda kawun zai fahimta.....ya kuma gwammace ya dinga isar da saqon fuad ne gudun kada ya bayyana halinsa.....ko aljanar daya sake haqiqancewa akwaita ta sanyashi yin wani baqon halin da mutuncinsu zai zube idanun surukai,duk kuwa da cewa shima dama a karan kanshi dan kai tsaye ne,dan gaba gadi.Page 101 "To.....to in sha Allahu ranka ya dade.....godiya muke qwarai da gaske....Allah ya qara arziqi" Yayi zancan yan a kashe wayar,sannan ya maida dubansa ga sabreen da tuntuni baqinciki ya qarasa kasheta a wajen,ta kuma koma ta zauna tun kan ya gama wayar,badon bata gaji da zamanta a wajen bane.....aah....don tana da sauran abun gayawa kawun,saidai kafin ta fara nata jawabin shidin ya rigata "Saqo ne daga mijinki......yana me umartarki daki lazimci zama a gida......yace a gaya miki baya buqatar daga yau har zuwa randa zaa tara shaidu a shaida daurin aurenki ki sake leqawa ko ina.....amma dan uwansa yace idan kina da buqatar fita ki sanarmin a kawo mota da masu tsaron lafiyarki......zasu kaiki duk inda kikeso a qasar nan ko a wata qasarma idan kina buqatar haka" Yayi bayanin fuskarsa wasai farinciki yana nuna kansa muraran a fuskar tasa. Idanunta ta lumshe tana son tilastawa kanta fahimtar ma abinda kawun yake cewa. Shigar maganar kunnenta daidai take da wasan kwaikwayon yara. "Miji?,ita sabreen?,mijin kuma yana iqirarin hanata fita saida izininsa?,wai shin yaushe ma akayi daren har garin zai waye?,yaushe ta yarda da wannan wasan kwaikwayon nasu da har zai tunanin ta amsa sunan MATARSA?. Shi a matsayin wa da zai tilasta ta aureshi?". "Ko baka qarasa bayanin komai ba tsaf na fuskanci dalilin da ya sanya ka bada amanna qulla auren nan......kawu......har yanzu ba'a haifi me arziqin da zan aureshi don dukiyarsa ba koda ina da manufar yin aure......ballantana sam sam aure shine abu na qarshe cikin jerin lissafin wajibai na rayuwata.......kawu......ka rubuta ka kuma ajiye,wannan abu tamkar sabreen bata taba sanin ya wanzu ba......ba wani qato daya isa ya hanani fita a sanda naso a kuma duk lokacin dana ga dama.....ruwanka kawu ka maida musu dukiyarsa ruwanka ka riqe......abu daya na sani....kudin dani sabreen na taba na tafi dasu ta hanyar da nake ganin tayimin daidai.....kuma yayi adabo dasu har abada saidai ya sake sabon zubi da lale" Daga haka ta miqe tana yunqurin shigewa daki tana jin kwanyarta kaman zata birkice. Me yasa qaddarorin qulluwar aure suke ta yawo a kanta cikin qasa da sati daya kacal?. Ta gama laluben hanyar gamawa da issue din wadancan matan?,yanzu kuma sai ga wannan?. "Idan dai har kina ganin zaki iya ja dame jadda ga fili game doki nan" Abu daya da kawu yace da ita kenan ya miqe yana ficewa abinsa yana barin sabbin kudaden dake a mazaunin sadakinta yashe a qasa. ᎷᏬᎻᎯᎷᎷᎯᎠ ᎰᏬ'ᎯᎠ "Hamma?......hamma?" Ya jiyo muryar amna dake cike da shagwaba tana kiransa da alama nemansa takeyi. Wata iska ya zuqa me yawa yana dauke dubansa daga saman furannin da yake kalla cikin balcony dinsa tun dazun,ya juya a nutse yana fadin "Am here lovy dovy". Dan murmushi ta saki tana qanqame paper din hannunta da wani tsadajjen biro me garai garai,ta taka a hankali ta isa balcony din inda yayi tsaye goye da hannayensa a qirji yana jiran isowarta. "Hamma wajenka nazo" Tayi maganar hannunta boye a bayanta. Murmushi ya saki yana mata nuni da daya cikin lausasan kujerun dake ajiye a wajen. Ta taka a hankali ta zauna tana kallonsa da murmushi,fuskarta na nuna wani irin excitement "Hamma.....zuwa nayi ka gayan favourite colour da kakeso a sawa matarka a lefe......and then ka fadi dame dame zaa zuba?,lissafin anni ya qure,tace nazo na sameka naji naka ra'ayin". Ido ya lumshe yana sakin murmushi,ya fuskanci sun daukaki abunnan,da gaske suka dauki komai,kuma da alama gagarumin shiri sukeyi. Dukkan abinda suka aiwatar shi ko daya ma baizo kansa ba,ya manta dasu cikin ma hidimar neman aure,ko ita kanta yarinyar yana mantawa da zamanta sai idan wani abu ya gilma ko sun tada zancan. "I don't have anything to say......the choice is yours" Ya fada da tsararren accent din nan nasa dake nuna gwanancewa wajen iya sarrafa harshe. Murmushi sosai amna ta saki tana gyara zamanta cikin nuna doki "Thanks hamma......bari na zabawa addana classy kaya" Ta dora hannunta saman paper din ta soma zana list. Da sauri yaja baya sanda yake yunqurin fitowa daga dakin,idanunsa akan bibo wadda ta afko dakin kamar an tunkudota. Fadowarta dakin bai hana sabreen maida kanta taci gaba da takawa zuwa cikin dakin a nutse ba. Maganganun bacin rai ne fal zuciyarta da zataso amayarwa da kawu rufai din,to amma tanata dannar zuciyartata saboda yiwuwar wanzuwar tata manufar. Sassauta fuskarta tayi tana fuskantar kawun sosai idanunta cikin nashi "Banda abun rufai......ai ba'a yiwa 'ya'yan yanzu dole......tunda dai yarinyar nan tace batayi bataso ka qyaleta mana,gida cike fal da 'ya'ya......nan nan hadiyya idan kace ita zaka bashi.....wallahi tsaf zaa katse karatun nan duk da muhimmancinsa.....duk kuma yadda take sonsa....ai aure shine gaba da komai a wajen yarinya". Tayi zancan tana jaddada masa muhimmancin maganar da kuma gaskiyar abinda take fada. Hannu yasa ya kama habarsa yana dubanta "Wato har yanzu dai ba zaki daina hali ba bibo?,kin saurari komai kenan?" "Kaga rufai kada kayimin mummunar fassara.....saboda Allah don kawai yarinya ta nuna batayi......na bada shawarar kada a shiga haqqinta saika nemi canzamin magana?". Karon farko kawu rufai din yaji jikinsa ya sanyaya da bibo din,ya kalleta sosai cike da mamaki "Bibo" "Rufai" Ta amsa masa da sunansa kamar yadda shima ya kirata da sunanta "Bari kiji na gaya miki......sabreen suka nema ba wata 'ya cikin gidan nan ba..." "Suka nema ko kuma ka nemo Mata?" Tayi zancan tana yada kanta gefe cikin salo na watsa habaici. Wata dariyar takaici kawu rufain ya saki "Gwara ki fito kai tsaye ki fadi abinda yake ranki bibo......ki saurareni da kyau kiji.......sabreen bani na nema mata miji ba.....farinjininta da qashin arziqinta daga Allah ne,don haka bani da hurumin musanya musu da wata.....saiki dage da addu'a kema Allah ya azurta taki 'yar da koda yaron mijin Sabrina ne". Maganar tayi masifar sosawa bibo rai,harta kasa masa shuru sanda yake qoqarin fita daga dakin. Ta saki shewa ta daki cinyarta "Ahayye......lallai sai yau na sake yarda kai din dan kunama ne.....kuma ka cika cikakken butulu......to bari kaji,ka tsallake yaranmu kaf ka tafi nemowa wancan tsintacciyar magen miji saboda tsabar qwarewa wajen munafurci da tsugudidi.....wallahi indai ina da rai na ci maka alwashin sai hadiyya ta auri mijin daya kerewa na sabrin" "Allah ya bada sa'a......ko mafarki kikayi hakan ta faru lallai kin cika me sa'a" Ya bankada labulen ya fadi mata sannan ya juya abinsa zuwa tsakar gidan don ya sarrafa kayan da aka shigo dasu din. Ta gefe daya ya dauki dukka maganganun sabreen ya azasu akan mizanin abinda baida muhimmanci sam sam,saboda shi din yasan waye muhammad jadda.....kuma duk inda takai ga kafiya da jin kanta to la shakka daidai yake da zamaninta. Idanunta ta lumshe tana qoqarin daidaita fitar numfashinta,yayin da idanuwansu dukka su ukun yake zube a fuskar yayar tasu. "Kiyi haquri adda" Haneefa dake tsaye sosai a gaban sabrin din ta fada fuskarta kamar zata saki kuka. Duk da ba komai ta fahimta ba,amma kusan ta saba da hayagagar kawun,wanda duk sanda ya yita cikin falon nasu to wani fada ne ko tashin hankali......tun bata fahimta har ta gane komai sannu a hankali. Cikin zuqar numfashi daya ta dawo da dukka jarumtarta tana sake gayawa kanta. Ita din 'yantacciyar 'ya ce.....ba property din kowa ba ballantana a ajiyeta a sanda akaga dama a inda kuma akaso.....sannan a janyeta ko a sauyata a duk sanda buqatar hakan ta taso. Murmushi ta saukewa fuskarta,ta miqa tattausan hannunta tana shafar kumatun haneefa din "Komai bai faru ba auta.....ku koma parlor ku kunna tv,nasa an gyara muku receiver din". Kai ta gyada a sanyaye,ta waiwaya ta kalli nadra da huda,sai ta juya tana ficewa suma suka bi bayanta,duk kuwa da cewa fuskokinsu sun nuna sam zuciyarsu bata gamsu da abinda ta fada ba. Kanta ta cusa sosai cikin lallausan pillow dinta,ta shaqo qamshin ciki tana fesarwa ta baki. Wacce irin qaddara ke bibiyarta haka?,ta kowacce fuska barazana rayuwa takeyi mata da lamarin aure?,tabbas ko sama da qasa zasu hadu ba zata taba aminta da wannan shirin wasan kwaikwayon na kawu ba......kamar yadda ta gama shirya komai don bacewa wadancan azzaluman matan. Kamar ana jira takai nan wayarta ta dauki qaramin sauti tana haske......ta daga kanta a nutse ta zubawa wayar idanu. A nata zabin bata da sauran wani dangantaka ko dalili naci gaba da sauraronsu.....to amma yaqi dan zamba ne.....wannan wata rubutacciyar magana ce data jima da haddaceta tare da adanata cikin dictionary dinta. Sai data zauna sosai sannan ta daga wayar ta sanya a kunnenta tana cije labbanta. "Salamu alaikum" Tayi sallama da muryar nan tata da tun randa ta fara furta mata manufarta a kanta ta haddaceta tsaf......sannann ta sakayata a gurbi na musamman da take ajiye dukkan wasu abubuwa da suka zame mata dole takatsantsan dasu. Cikin wannan miskilancin nata daya zame mata jinin jiki ta amsa mata. Hakan sam ba damuwar maamah bane.......tana da tarin abubuwa da takeson sake sani tsakaninta da fu'ad. "Ina fata zuwa yanzu dukiyar auren d'ana ta ruskeki?". Tadan shiga mamaki kadan,kamar zata tambaya amma miskilanci ya hana,sai ta zabi ci gaba da yin shuru har zuwa sanda maamah ta fahimci ba zatace komai ba.102 "Magana nakeso nayi dake masu tsananin muhimmanci.....naso ta kasance fuska da fuska.....to amma inason dauke idanu da hankulan mutane daga kan plan da dukka ma wani tsare tsare namu......na tsinci cewa yarona da nake nemawa ke shima ke yake nemawa kansa......abune me matuqar mamaki da daure kai.....nayi mamaki kaina ya kuma daure akan ya akayi hakan ta faru?.....ban samu wani tsoro ko kuma fargaba ba......saboda dukkan wata alama da zata bani cewa auren soyayya ne ake shirin qullawa babu shi......ya akayi kikasan muhammad jadda?.......meye naku shirin akan aurenku..... Duk da ba lallai ne na sani ba......amma zan gaya miki abu guda daya a taqaice......koma meye kuka shirya ke dashi ki tabbatar shirinku baici karo da nawa ba". Sosai kanta yayi wani irin daurewa,sai taji kamar ta fara daina gane komai. Tana nufin ita din mahaifiya ce ga.......ya salam......." Ta furta cikin zuciyarta da murya qasa qasa. Wai su din wadanne irin mutane ne wadannan?,da d'a da uwa dukkaninsu kowa da irin kalar tasa alqiblar?,da d'a da uwa kowannensu nada karkatacciyar manufa?,kuma duka ba'a kan kowa ba?,a kanta?. "Ina fata kin fahimta?" Maamah ta tambayeta ganin koda tarinta bataji ba. "Akwai wani abu me muhimmanci daya dace ki fadan ki fadi ba?" Ta motsa labbanta a nutse tana tambayar maamah duk da yadda kwanyarta da zuciyarta suke cakude da rudani. "Shikenan.....qaramar magana ce kuma gajeriya,amma me matuqar muhimmancin daya kamata ayi mata riqon tsauri" Qaramin murmushi ta saki me sauti,sautin daya ratsa ta wayar ya isa kunnuwan maamah. Wai ta yayama ita zata tsaya a dinga tambulin da rayuwarta tsakanin UWA da DANTA?. Ta yaya ma zata tsaya ta zuba musu idanu suna yin yadda sukaga dama rayuwarta?,rayuwartata da ba mallakin kowa bace ba kuma wanda yake da iko da ita?. Rayuwar da aka fusgeta da qyar?,tsananin kuma nisan kwana ya kawota inda take zaune a yanzu?. Isar murmushin kunnuwan maamah ya haifar mata da 'yar fargaba kadan,saidai kuma lafazin sabreen din ya danne dimuwar "Baki da damuwa.....ki qirga kwanakin kawai da kike jiran komai ya kasance" "Da kyau.....naji dadi dana sameki ame saurin cika alqawari.....sati uku.... Sati uku kadai ya rage ki zama daya daga cikin familyn jadda......nasan kuma bakisan wanne irin family zaki shiga ba......cikin qasa da sati daya kafin sannan ina buqatar ganawa dake don ki karbi jadawalin tsarin yadda nakeso komai ya kasance". Idanu ta lumshe ta kuma budesu lokaci daya tana gyada kai. Karon farko a rayuwarta da tasan murmushi yana iya fita daga fuskar dan adam a yayin da yake cikin bacin rai. "Baki da matsala" Ta furta da ma'anoni daban daban. "Okay.....inason ki saki jikinki.......bayan hidimar dashi da uban goyonsa zasuyi miki......karkiji nauyin tamabayata komai......ko nawa kike da buqata a shirye nake dana kashe miki shi......inaso surukata tafi kowacce suruka daga cikin surukan sanannu kuma attajiran families.....biki zamuyi na kerewa sa'a.....irin bikin da zai kauda zato da kuma dukkan zargin me zargi a kanmu". "Ba damuwa bane....na fahimci komai,amma ina buqatar hutu........zamuyi magana wani lokacin" Ta qarasa fada tana yanke kiran ba tare data jira cewar maamah din ba. Gefe tayi jifa da wayar tana nutsa hannunta cikin sumarta "Ya ilahi.....ya akayi dukka haka ta kasance?ya akayi komai yazo a daidai?" Tayi zancan a fili "Kiyi aurenki adda......kiyi aurenki" Taji muryar huda dake rawa,wadda ke tsaye daga gefanta. Hannayen nata ta zare daga sumar,ta daga kanta a hankali tana duban huda dake tsaye. Idanunta cike fal da hawaye,ta qaraso da sauri ta tsugunna gaban Sabreen gami da riqo hannayenta "Adda....." "Shshsh" Ta dakatar da ita tana dora yatsanta akan lips dinta. "Nayi aure a wannan situation din kike fadi huda?.....na kaiku ina?.....waye zai kulamin daku?" "Allah......Allah ne adda" Ta amsa mata har yanzu muryarta na rawa. "Na sani huda.....na sani,amma kinsan wanne irin aure ne wannan auren nawa?.....rayuwar addanki sukeson jefawa cikin wani game da ake bugashi tsakanin D'A da UWARSA.game din da ba wanda yasan meye ainihin ma'anar bugashi,zasu tsoma rayuwar aminatu a ciki bayan bata cancanci ta fuskanci raba uqubar rayuwar kowa ba.....me nayi da zasu nemi na zama silar cutar da dayansu?". Tana kaiwa nan sai ta samu kanta da kecewa da kuka,wani nannauyan kuka me siririn sauti,irin kukan data dauki sama da shekara shida tana tarashi a qirjinta,don bata da kafadar da zata kwantar ta fiddashi ta rage wannan radadin. A yau hudan ta zame mata wannan kafadar,har ta zama jarumar data dinga sharewa sabreen hawaye dukka jikinta yana rawa "Daga yau zamu dinga raba wannan tsananin da quncin adda......ba zaki sake kuka ke kadai ba....kiyi haquri kada su nadra su jiyoki" "Ba wanda zai rabamu huda.....dole na nemana muhallin da zamuyi nisa da dukkan wannan qullin.....bazan fuskanci wannan abun ba". Tayi maganar tana zare kanta daga kafadar hudan,ta miqe tsaye kai tsaye tana dosar bakin gadonta. 𝙒 𝘼 𝙎 𝙃 𝙀 𝙂 𝘼 𝙍 𝙄 *******Daidai lokacin da su huda suka wuce tahfeez a safiyar asabar din. Ta shirya kanta tsaf cikin turkey dress da suka maidata tamkar daya daga cikin kyawawan 'yammatan turkey din. A nutse take rufe qofar parlor dinsu,ta zuge qaramar jakar hannunta ta jefa key din duk da yadda takeji a jikinta akwai idanuwa masu yawa a kanta cikin jamaar dake zazzaune a tsakar gidan. Tsakanin jiya da yau din ta karanci an samu yawaitar jama'ar dake zama a tsakar gidan nasu. Wani irin zama da yake kama da zaman gulma tsurku da kuma zunde.....a wani yanayin kuma yafi kama da zaman jajantawa da kuma jimamin da batasan ma sunayi ba. A nata ganin dukkan kai kawonsu bazai wuce akan tatsuniyar qirqirarren aurenta da kawu ya gabatar cikin gidan ba,labarin daya girgiza kowa cikin gidan harda 'yan uwanta da suke uba daya wanda suke aure a wani gidan.....lamarin da inda suna da yadda zasuyi suka tsige mata shi me yiwuwa ta sanyasu cikin jerin masoyanta da bata da kamarsu. Idanuwa sunyi yawa a kanta sanda take ratsawa tsakar gidan,idanuwan dake cike da hassada da jin haushinta,sannu a hankali ta samu ta isa ga soronsu ta bulla farfajiyar gidan da zata danganata da gate na qarshe na gidan. Motar dake lullube cikin tempol qarqashin rumfar data kasance ma'ajiyar motor mahaifinsu sanda yake raye idanunta suka fada..... Ido ta dauke daga kanta tana jin wani zafi yana ratsa zuciyarta. Da gaske yake kawun kan lallai saita karba komai harda motar da anata idanun daidai take da motar daukan gawa. "Komai ya kusa qarewa" Ta fada qasa qasa sanda take gifta motar,tana buqatar isa inda tayi niyya don shirya yadda zata nesanta kanta da qannenta da wannan Cakwakiyar da ake shirin tsomata. "Ke.....ina zuwa?,ina zaki haka?" Muryar kawu rufai ta ratsa dodon kunnenta,kawun dake tsaye qofar wani daki dake can qarshen katangar gidan. Dakine da ashekarun baya mahaifinsu kr jibge kayan abinci a ciki. Duba daya tayi masa ta kauda kai taci gaba da takawa abinta don fita. Ya fahimci maganarsa sam bata dadata da qasa ba,hakanan sautinsa bazai taba dakatar da ita ba,don haka ya saki aikin gyara kwalayen da yasa akeyi ya tako da sassarfa cikin burin cimmata.103 Har ta murda hannun qofar ta bude sai kuma ta dakata saboda wani tunani da yazo mata. Tsaf kawun zai iya binta waje ya tara mata jama'a,don shi din bai ita magana qasa qasa ba. "Ina zaki nace ke aminatu" Yayi tsaye a gabanta yana fada idanunsa a kanta yana daure fuska. "Kin tambayi mijinki?,da izininsa koda saninsa zaki fita?" Ya sake jefa mata tambayar da gaske yana adan tsorace. "Mijinki" Kalmar tayi wani amsa kuwwa cikin kunnenta. A duk sanda taji ya ambaci wannan Kalmar sai abun ya zame mata wani irin baqon abu. "Bazan hanaki fita ba.....amma sai na tabbatar da izininsa kika fita din,don a yanzu ke amana ce a hannunmu,bazan Kuma yi wasa sa wannan amanar ba har sai na tabbatar ta fita daga hannu na". A nutse ta daga ido ta kalleshi,abun yana bata mamaki gaba daya,wai yau kawu shike haqiqancewa haka akan lamarin da ya shafeta?,wai yau shike tambayarta ina zata fita?,lallai kudi sun zamewa rayuwar wasu bayin jarabta. Abune da bata taba sanyawa cikin kanta ba......wai akwai wata rana da zata zo har wani ya damu da inda ta fita ko kuma ina zata je?. "Ki sanar dashi sannan kije duk inda kikeson zuwa din" Ya same maimaitawa yana tura qofar da qafarsa. "Oh......inda ranka kasha kallo....duniya juyi juyi wai kwado ya fada ruwan zafi......dama idan bakayi sharar masallaci ba ai kayi ta kasuwa,kudi shu'umai......iska kuma na wahal dame kayan kara.....ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta". Wannan jerin gwanon habaicin suka fito daga bakin bibo wadda ta iso daura da wajen don zubda sharar sa ta kwaso daga dakinta. Waiwayawa kawu rufai yayi yana dubanta "Wai dukka wadannan gayyar gamayyar haibaicin akan waye kike?,indai da Sabrina kike aikin banza kikeyi,kinfini sanin halinta,uwa uba kuma a yanzu ita din me arziqi ce.....me arziqi kuwa baya fada da talaka......ni kuwa kinsan warki nike daidai qugun kowa.....to saiki banbance". Tsaiwa tayi sannan ta waiwayo tana zabgawa kawu harara,wani irin tsanarsa da haushinsa suna cikata "Magana kakeyi ne ko bakinka ne a haka?,aini rufai na jima da sallamaka cikin lamurana.....ashe da gaske aboki yana iya juyewa ya koma maqiyi?,dadin abun ba'a fimu iya 'yan shige shigen nan ba,to na meye ma zan damu banda abinka rufai?" Ta qarasa maganar tana yarfe hannu cikin son boye damuwarta da lamarin. "To barkanki.....gwanda da kika gyara zancanki kika samawa kanki salama....". Kunnuwanta ba zasu iya ci gaba da sauraron wannan quruciyar ta kawun da bibo ba,wanda har yanzu suka kasa dainawa,duk kuwa da cewa kansu da bakinsu a hade yake,yanzun ne abun duniya yake shirin hadasu,don haka suna tsaka da sa'insarsu ta tajuya tana takawa da nutsatsiyar tafiyarta dinnan da 'yan bani na iya suka sawa suna "Maciji me tafiyar mutuwa" Nutsuwarta a tafiya a cewarsu sam bai dace da halinta ba a tasu fahimtar. A falo tayi wurgi da jakarta ranta yana susa,tun komai baiyi nisa ba har kawun ya soma!shiga gonarta da kuma nuna mata iyakarta?. Dankwalin kanta ta zame sassalkar sumarta ta zare daga ribbon din data matse gashin,ta koma da zafi zafi ta zauna saman kujerar tana furzar da iska daga bakinta "Ta yaya ma zata zauna a maida rayuwarta haka?,ya zata zauna ta rayu kaman haka?,dole ta matsa qaimin tattare komai dama kowa nata zuwa bigiren da zata ci gana da gudanar da rayuwarta cikin 'yanci kuma a yanayin duk da takeso. Idanunta dama kunnuwanta gaba daya suna a tsakar gidan nasu,tana bibiye da kowanne motsi na gidan. Jira takeyi kawai kawun ya matsa daga gidan ya tafi tashi sabgar itama ta fice nata. Kaman yadda takeji koda sama da qasa zasu hade ba zata taba daga waya ta kirayi mutumin da bata taba jin burbushin muhimmancinsa cikin rayuwarta ba......hakanan fitarta a yau ta zama wani abu na tilas don laluba yadda zasu gusa daga wannan muhallin zuwa wani 'yantaccen gurin. Tana ji a jikinta idan bata aiwatar da hakan ba a yau tamkar bata da wani sauran lokaci da ya rage mata,kamar lokaci ya riga ya qure mata,kamar yaune kawai damar data rage mata. Saidai duk yadda take zirga zirga da sanya idanu,kowanne motsi sai ta juyo muryar kawun ko gilmawarsa. Tun lokacin dawowar yara daga makaranta baiyi ba har yayi. Ba nutsuwa a tattare da ita sanda suka shigo,don ko abinci bata dora musu komai ba,burinta kawai kawun ya matsa ta samu ta fice,amma qemem wunin gaba daya yau a gidan ya yishi. Bata samu ya bar gidan ba sai kusan biyar na yammaci,tasan kuma yayi hakanne saboda yasan ita din bamai fitar dare bace,saidai a wannan rana ta karya record dinsa,ta shirya a gaggauce ta fice abinta. Cikin nasara ta kammala komai,saidai hakan ya dauketa har zuwa bayan sallar ishai,tanata fargaba ta shigo gidan,ta wuce kai tsaye cikin dakinsu,wanda tana sanya qafa shima ya sako tasa qafar,saita zarce bedroom kawai,don tasan dole zai fahimci ta fita,koda bai fahimta ba a cikin gidan nasu ba zaa rasa masu gaya masa ba,a yadda suka canza su kansu,komai yana shirin canzawa gaba daya. *******K'arar wayarta shine abinda ya farkar da ita daga nannauyan baccin daya dauketa,hannunta daya mata nauyin ta miqa ta jawo wayar tana duba me kiran. Ganin sunan titi ya sanyata miqewa ta zauna sosai tana amsa wayar. "Anjima da yammaci jirginmu zai tashi zuwa qasar India,najeeb ya gama komai" "Alhamdulillah" Ta furta a sarari tana jin kamar an cire mata daya daga cikin nauyayan duwatsun dake danne saman zuciyarta. Ciwon aishatu shine cikar burinta na farko da take fatan gani kowacce rana. "Zan shigo naga aishatu.....zan shigo da wuri titi in sha Allah" Ta fada tana jin farinciki yana ratsata . Murmushi titi din tayi "Koda baki shigo ba sabreen kin gama yiwa aishatu komai ai,tsakaninmu dake sai fatan alkhairi". Idanunta ta maida kan agogo bayan sun gama wayar,takwas saura na safe. Tayi mamaki da motsinsu huda bai tasheta ba,suma kuma cikinsu ba wanda ya tadata,sai ta jawo dan qaramin farin hijab dinta data cire sanda zata kwanta ta aza saman kanta ta zuro qafafunta qasa ta sauko tana fitowa falon. Dukansu sun gama shirinsu,kowa sanye da uniform,fitowar tata taja hankalinsu,suka soma gaidata sanda take zama kusa da haneefa,saita karba saka mata socks din tana cewa "Auta ta daina neman me saka mata socks yanxu ko?,girma yanata zuwa" Dariyar jin dadi tayi tana cewa "Amma adda kullum ya nadra cewa takemin yarinyar nan...." "Rabu da ita,harda ke za'a raba aiki idan muka koma sabon gida" . Furta sabon gidan da tayi sai dukansu suka zuba mata ido,bata bada hankali ba sai data gama sawa haneefa socks din. "Adda......wani gidan zamu koma?" Haneefa ta riga 'yan uwan nata tambaya fuskarta na nuna farinciki sosai. "In sha Allah.....gobe.....kaman ko yaushe bana buqatar masaniyar kowa,idan an tashi daga school yau ba islamiyya.....koda kun dawo baku sameni ba zan shiga duba aishatu,ku fara shirya kaya huda cikin manyan bags din can kafin na dawo" "Tom" Huda ta amsa mata saidai nata jikin a sanyaye yake. A nata hasashen tana ganin kaman idan addan nata tayi auren shine zaifi dacewa da ita......auren zai zama wata hanya ta wanketa daga dukkan zargi da mummunan kallo da society din da suke rayuwa a ciki suke mata,bataga alfanun ture wannan auren ba.....duk da tayi mata nata bayanin gwargwadon yadda zata fahimta. Addua ta musu na dawowa lafiya,saita jawo wayarta tana son taba JIB ya qara mata bayani akan wanda titi tayi mata,sannan shima suyi handing over akan komai.....tana buqatar sabuwar rayuwar da babu kowa cikinta daga ita sai qannenta da kasuwancin da takeso ta fara wanda shi take sanya ran zai zame musu madogara _ni kuwa nace ummmm inji me ciwon haqori,anya kuwa sabreen?,haka siddan zakici bagas?😂,to bari dai mu gani_ Wayar bata shiga ba saiga nadra da haneefa sun dawo cikin dakin,ta ajiye wayar ta maida hankalinta a kansu tana shirin tambayarsu lafiya huda itama ta shigo. Tsoro sosai saman fuskarta,ta qaraso cikin falon tana dubanta. "Adda.....ina tsoron faruwar wani abu" "Me kenan?" Sabrin ta tambayeta tana tattara hankalinta sosai a kanta "Wasu manyan qatti ne guda biyu a qofar gidan nan.......duk wanda zasu shiga ko zai fita su zasu bude masa qofa.......nayi qarfin halin tambayarsu su waye amma ba wanda ya amsa min a cikinsu". Shuru sabreen tayi tana qanqance idanunta cikin alamun zurfafa a tunani. Kwanyarta ta gaza cafko komai,sai ta maida dubanta kan haneefa. "Akwai wani alamu na cutarwa a tare dasu?,hayaniya tsawa ko wani abu daban?". Kai ta girgiza "Ba daya,kawai zasu kalli fuskarka ne sannan su bude maka qofar" "Haka kowa yake fita daga cikin gidan?.....akwai wanda kukaga sun hana fita?" "Kowa yana fita,amma cikin tsoro,ba kuma wanda suka hana". Sosai ta jijjiga kanta zuciyarta tana d'arsa mata wani abu,saidai kuma bata tunanin hakan zata kasance. " Ba damuwa,ku wuce kuma ku fita kaman kowa,basu da alaqa daku". Cak sukayi suna kallonta,da alama dukkaninsu itace damuwarsu,kada ma huda taji labari saboda sanayyarta da abubuwa da yawa da sauran basu sani ba. Tattausan murmushin nan nata dake tsananin qara mata kyau ta saki tana girgiza kai "Karku damu......muna da yawa a gidan,ba abinda zai faru damu,a dawo lafiya" Tana ganin yadda suka kama hannun juna da kyau kaman kowa na shirin karewa dan uwansa wani abu me cutarwa,wannan sai ya tsinka mata zuciyarta sosai,ta sake jin ruwa da iska zata ci gaba da zamewa rayuwarsu garkuwa har abada. Tana dauke idonta daga kansu kankatsin salatin bibo ya rusketa "Daada.......tani......wai bakuga yau kuma bala'in da muka wayi gari dashi bane yau?,karta kartan garada sun tsare mana qofar gida kamar gidan tsaffin 'yan damfara.....koda yake biri yayi kama da mutum.....kuma sai da karen gidanka kake ganin na wani gidan......wannan masifa da take shirin afko mana gida ya ubangijin Allah ka tsaidata iya kan wansa ya jajibota....." "To wannan balai mudai bamu taba ganin irinsa ba tsahon rayuwarmu da mijinmu sai a wannan karon" Tani da suke dan juma da dan jummai wani lokaci ita da bibo kafin su hautsine kuma ta fada tana tafa hannuwa "Yo kome zamu gani aisaidai mu nemi tsari.....wanna masifa duk yadda akayi silar wannan gafalallen auren ta samemu.....wai daada ba zaki fito bane sai an cimmaki?". "Me zan fito nayi?,ina ruwan biri da gada?,tunda dai basuce ni suke nema na ina ruwana ni dasu?,maza ku zafafa damuwa dasu sayi awon gaba daku idanma zuwan nash ba naku bane ku jawa kanku da shegen bakinku" "Bakinki ya sari danyen kashi wallahi,.....saboda abun arziqi bai karbi kare ba,daga abun arziqi sai ki juye mana da fatan tsiya?,sha zamanki idan an cimmaki wani cikinmu aka cimmawa" "Ke kika sani" Daada da bata fiya jurewa dogon cece kuce ba ta fada. Tana danna number jib kunnuwanta suna saurarensu. Wannan dabiar tun bata mallaki hankalin kanta gaba daya ba tasan bibo da ita,har kwanan yau kuma ba abinda ya canza a tattare da ita. Waya sukayi da jib din ta minti talatin kacal,daga nan sai ta soma shirin shiga wanka. Ta dawo daki ta tsane jikinta da towel,ta shirya cikin glitter wax me tsananin kyau data dace da kalar fatarta da kuma yanayin qirar jikinta,dinkin half bubu da straight skirt da aka tsaga bayansa,ta dauki Chantilly veil me asalin tsadar peach color adon jikin atamfar,ta hada da plate shoe da hand bag dinsa bagco. A tsaitsaye ta hada tea da biscuit tasha,ta yafa mayafinta ta daura agogon hannunta don buri take taje taga farincikin dake kwance fuskar aishatun. Hankali kwance take takawa a harabar gidan nasu tana nufan qofa,tana jin ta gama da dukka wata matsala yanxu dake gabanta,so saura ya rage na wadanda suka gayyatota cikin matsalar susan yadda zasu warware qullinsu. Tana taba handle din qofar taji an budeta,sai ta daga kanta a hankali ba kaman dazu da yake a qasa ba tana kallon gabanta. "Good morning madam" Kakkaurar muryar ta fada cikin tsananin girmamawa har yana rusunar da kansa duk kuwa da cewa ya ninkata a tsaho da shekaru,girman jiki kuwa sam ba'a maganarsa don bata kawo koda gefansa ba. "Good morning madam" Ta sake jin wata muryar ta daban a daya gefan nata shima ya fada a girmame.104 Da idanu ta sake binsu,murdaddune a tsaye,wanda babu alamun tsoro ko shakka a tattare dasu,zubin tsayayyun masu damarar nan da akan samu akan hanyar shiga fadar shugaba wasa,wanda rana ko ruwa basa sanyasu motsawa ko canzawa daga muhallin tsaiwarsu. Sosai ta tattaro dukka dauriya da qwarin gwiwarta,ta azawa fuskarta wani mugun daurewa,tasa hannu tadan tura qofar tana amsawa ciki ciki da "Morning" Tana sanya qafarta zuwa waje "Sorry maaa........kiya haquri ki koma ciki..... Isn't allowed maaa". A mamakance ta dakata gami da ja baya saboda yadda yayi bake bake a gabanta,bataga ma hanyar wucewar ba komai qanqantarta " Isn't what?......waye kai?" Tayi masa tambayar kai tsaye saboda bata da lokacin batawa tayi wani dogon nazari. "My name is abdulgafar......ni da abokin aikina kuma duka munzo ne don tsaronki" Ya fada da matuqar girmamawa kansa a qasa,baya iya wani cikakken hada ido da ita. Haushi da mamaki duka suka hadu waje daya suka tsaya mata a wuya "Tsarona like how?.....ni na buqaceku?" "No maaa.....bake bace......umarni ne daga wajen boss" Dayan da baiyi magana ba sai yanzu ya fada da tasa girmamawar "Who's boss?" Ta fadi da mugun fusata saboda ta fara shanshano wani abu "Sir muhammad jadda....." "Enough......ya isa.....ku bani hanya na wuce,daku da boss din naku da gadin nawa duka matsalarku fe ba tawa ba". Rusunawa kadan yayi yana hade hannayensa waje daya "Am sorry maaa......ba'a yarda mu barki ki fita ko ina ba har sai boss ya dawo". Kadan ya rage bakinta ya furta kalmar ashar saboda tsananin mamaki,sai tayi tsaye kawai tana kallon baqar fuskar mutumin mamaki yana zagayawa da ita duniyar tunani,yayin da shi kuma yake ci gaba da furta mata kalmar rarrashi da kuma ban haquri duka a cakude cikin harshen hausa da karyayyen turancinsa. A wannan karon tana jin tura takai bango,ta inda kuma aka hau ta nan ake sauka,bata kuma da sauran lokacin batawa tayi sa'insa da yaranshi,don haka ta juya a mugun fusace zuwa cikin gidan. Tana tafe da dan sassarfa tana neman number kawu Rufai,abinda ta manta rabonta dayi kenan,saidai shi ya kirata idan neman abun duniyarsa ya motso,shima din ba kasafai ba,don yafi ganewa yayo tattaki suyi ido da ido. Wata muguwar guda taji an sake mata data ratsa har tsakiyar kanta sanda take taka tsakar gidan nasu,ta runtse ido gudar bibo tana sake birkita mata kwanya,tana so taji da matar nan,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata tukunna dai ba yanzu ba,wannan qurar data taso miki a yanxu ita tafi cancan ta a kasheta. "Yar arziqi irin albarka......kiranki alheri ne.....yanzu haka ina cikin layin naku ai,gidan zanzo akwai bayanin da zan miki" "Basai kazo ba kawu... .Amma inaso ka kira wancan mutumin da kake iqirarin ka bashi aurena......ka shaida masa yayi gaggawar janye wadancan gumakan daya dasa mana a qofar gida da zummar hanani fita sabgogina" "Kajimin shashasha.....macen da aketa tattali amma ta kasa gane hakan......banda abun ki wacce macace kaf unguwar bama gidan ba ta samu darajar samun masu tsaron lafiyarta idan bake ba?,ke wannan kawai bai isheki alfahari ba?" "Kawu!" Yau din ta kirashi da dan tsauri a muryarta saboda yadda ranta yakai maqura a baci "Fadi abinda kikeso ki fada......gani nan ma na shigo gidan" Ya qarasa fada yana datse kiran. Da kallo bibo data maida yanzu zaman tsakar gida sana'arta qarfi da yaji ta bishi dashi "Allah ka rabamu da mutuwar zuciyar da 'ya'yan cikinmu zasu dinga juya mu" Ta fada qasa qasa,yaji tana magana amma bai fahimci me take cewa ba,don shi a yanzu hankalinsa nakan lamarin sabreen da me jadda,bazai samu cikakken bacci ba sai ranar daya tabbatar an miqa musu ita. A tsaye take don ta kasa zama,ba abinda zuciyarta ke maimaita mata sai kalmar "Wai waye wannan muhammad jaddan?,me ya dauki kansa?,wa yafi?,wa ya damu dashi?". Koda kawu ya shigo kallo daya yayi mata ya tabbatar lallai abubuwa sun fara cabewa. A yadda yayi mata farin sani fuskarta kawai ta gaya masa lallai ta fara cika,kuma dab take da fashewa,fashewar kuma da yayi imanin ba zata taba zame masa alkhairi ba musamman shi,bata da tsoro,tana iya yin komai idan har ta tsara zatayin,gwara tun wuri yayiwa tufkar hanci......ya gayyato masu tayashi yaqinnan don ya samu ya tsira da mutincinsa da sauran 'yan canjinsa. "Ka kirashi ka gaya masa......idan ba haka ba zan gaya masa ta hanyar da bazata yiwa kowa dadi ba kawu!" Ta sake maimaita maganar da sautin da zai tabbatar maka kai tsaye daga zuciyarta maganar ke fita. "Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin gumi yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani sakashi a masifa ba. Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci. Number da a kullum kiranta yake yawan sakar masa da fargaba da kuma faduwar gaba ya kira,duk da ya fuskanci cewa mamallakin number mutum ne me tsananin sauqin kai da kuma fahimta qwarai,hakanan kiran number wayarsa yafi masa sauqi akan kiran wancan mutumin da yake jinsa tamkar wani mala'ikan daukan rai a wajensa. Daidai lokacin da yake tsaye cikin malam aminu kano international airport,zagaye da guard nasa,gefe daya kuma farouq ne da yayo masa rakiya. Kusa da kusa suke tsaye sosai shi da farouq din,da alama akwai magana me muhimmanci da sukeyi shi dashi din. Hannunsa ya zura kawai cikin aljihun kaftan dinsa ya zaro wayar,ya maida dubansa ga fuskar fuad dake qoqarin sanya wayarsa a silent,don ba kasafai ya fiya son kiran waya ba "Surukinka ne yake kira" Yayi maganar qasa qasa ta sigar zolaya da muryar da iya su kadai zasu iya jin maganar. Kadan yadan daga fararen idanunsa ya jefa masa harara,sannan ya maidasu kan wayar yana ci gaba da abinda yakeyi din ba tare daya ce dashi komai ba. Idanunta suna lumshe,amma kuma yadda kawun yake wayar cikin matuqar girmamawa kai kace sune sama dashi sai bacin rai ya sake zuwa mata wuya......ba wannan bane a gabanta,abu mafi muhimmanci shine ya sanya wannan qattin su janye daga qofar gidansu,don haka ta saka kunne sosai tana sauraron muryar farouq dake fita tar tar ta speaker din wayar kawu,wanda ya sakata ne a speaker don ta samu tabbaci kan duka hukuncin da ya yanke a kanta. Haka kawai cikin ranta takejin bashi bane yake magana,daga yadda farouq din ke magana adan sake ya sake baya yaqinin haka. "Yallabai din yana kusa?,akwai saqo da aka bani zan isar masa....." "Yana jinka uncle......bari na saka a speaker......though dai zaiyi kusan two weeks idan ya wuce.....zai dawo one week before the wedding". Kansa fuad ya sake dagawa ya watsawa farouq wata harara,don me zai zauna yana bayani musu akan abinda shi kadai ta shafa "To ma sha Allah......ma sha Allah.......dama sabrina ce ke neman izinin rage masu tsaronta......sannan kuma a yau din tana buqatar ya bata izinin fita.....". "Ban yarda taje ko ina ba....koda kuwa qofan gida ne". Wannan dakakkiyar muryar tasa dake cike da ginshira ta ratsa wayar ta kuma samu kyakkyawan damar isar da saqo ga kunnuwanta. Kaman ya yarfa mata ruwan zafi haka taji. Tsam ta samu kanta da miqewa,ta zauna sosai tana zubawa kawu rufai idanu wanda zuwa sannan har ya fara haramar rufe maganar hanyar fadin "To in sha Allah.....in sha Allahu ba damuwa......". Bai ankara ba,baisan kuma ta yaya ba sai tsintar wayar yayi a hannunta,kai tsaye ta zare wayar daga hannun kawun ta maidata kunnenta cikin wata fusatacciyar murya "Ina fatan kana kan waya!" Sautin da yaja hankalin farouq da wayar ke hannunsa,da kuma shi kansa fuad daya soma takawa zai wuce ciki don ya isar da saqon da yakeson isarwa din. Taku uku farouq ya cimmasa,sai ya zura masa wayar kawai a aljihun gaban rigarsa yadan matsa gefe yana karantar yanayin fuad din "Ban nema izini ba......hakanan bance a nema min izinin komai daga wajenka ba......umarni ne kawai kan ka janye wadancan halittun da babu sanin kimar dan adam ko daya a tattare dasu......kafin su tafi kuma ka tabbatar sun karbi komai naka daka bada da sunan dukiyar aure" "Au haba?" Ya fada da wani irin calmness zuciyarsa da kwanyarsa na qidddige wasi cikin halayenta. "Ashe bayan qwamushe girman kai harda rashin kunya kika hado?.......abun yayimin daidai......i salute you ma'am........zaki ci gaba da zama cikin gida har na tsahon sati biy cur ba tare da kin taka koda qofar gida ba.......wannan shine punishment mafi sauqi a gareki". "But....who are you?" Ta tambayeshi a zafafe tana jin zallar rainin wayo cikin maganganunsa. "Relax mana.......so soon haka?,saurin me kikeyi nason jin waye muhammad fuad?,bayan sanin nasa suine babban barazana a rayuwarki?". Yakai qarshe yana ajiye numfashi,bai kuma barta ta sake cewa komai ba yace "Kina zaton zan barki ba masu tsaremin ke.....don nasan kadan daga aikinki ki fecemin da dukiyar aure na.......wannan wasan zaiyi dadi sosai.......but......kisan dawa zaki bugashi......idiot!". Qit ya katse wayar,ya kuma zarota a gaggauce daga aljihun nasa. Abu daya zai sanya ya buga wayar a qasa,ta fito daga wajen mutum me matuqar girma da mutunci a rayuwarsa. "Don't ever never try it.......kasan bana shiri ko jituwa da mara kunya......wayarka taci saa data kasance taka ce,da daga yau ba zata sake amsa sunan waya ba" Sai ya sake masa wayar shi kuma ya cafe,yayin da ya qara gaba yana wucewa cikin kaman yadda yayi niyya. Yadda ya qara zafin nama cikin tafiyarsa kadai zai gaya maka zuciyar 'yan maza ta motsu sosai,ya bishi da kallo sosai. Yadda yayi doguwar magana haka yau cikin fada,ya tabbatar koda ya bishin bazaice komai dashi ba. Kasa bawa kawu wayar tayi har sai daya sake kwatsa mata tsawa "Bani wayata nace!" Saita miqa masa wayar wanda miqawar ya hadu da silalowar siraran hawaye daga fuskarta. Da gudu gudu ta qarasa shigewa dakin,tana jiyo sababin kawun da yaketa yarfa ruwan masifa kamar xai ari baki "Kinsan wayeshi?,kin kuma san matsayinsa da har kika gaggaya masa magana haka?,kinsan idan ran mutumin nan ya baci ya kama duka danginki ya kulle basu da saidan me fiddasu?". Maganganun kawu ba sune suke dawo mata akai ba,yadda ya dinga yaba mata magana kalma bayan kalma kuma murya a kwance.....hankalinsa ma a nutse shine yafi mata matsanancin ciwo. Wunin ranar haka ta dinga juyi cike da baqinciki da takaici,tanaso tayi kuka amma tana hana kanta,tana ganin tafi qarfin tayi masa kuka(ni kuwa nace anya sabreen?,ba girin girn ba tayi mai). Tana daga kwancen tana irgen yadda awanni suka shuda suka kuma zama silar tafiyar ayshatu india ba tare data yiwa yarinyar kallon qarshe kamar yadda taso ba. Da wannan juyin ta qarar da wuninta kaf da tunaninta na yadda zata samu zullewa tsakanin qattan garadan nan ta fice a gidan,ta kuma nisanci kowa ta yadda zai kasance kafin zuwan sati biyun da ya ambata saidai ya dawo ya tarar ta zama tarihi a garesu gaba daya. ********"kai jama'a,qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un,mudai mun hadu da masifa,wannan bala'in har ina?,kai da gidan mijinka amma duk shiga ko fita wani qato yana tsaye,shi xai bude maka qofa shi xai rufe maka?". Muryar bibo kenan dake sakin buhun data dawo dashi daga kasuwar saitin dakinsu sabreen din,don tana so dukka maganganun da zata fada ya samu wajen zama na din din din a kunnenta. A kwanakin sam bata da aiki sai fadin baqaqen maganganu da kuma tarin habaice habaice,tana neman duk wata hanya ne da sabreen zata kulata ta lanqaya mata sharrin da har masu gadin nata zasuji su kuma isar dashi ga uban gidan nasu,wataqila hakan ya zama silar fasa auren. Sosai auren ya tsaye mata a rai,ta laluba ta kuma bincika inda zata sake ganin matan nan don ta sake jaddada musu 'YAR BARIKI fa dansu zai aura.....amma bata samu ma wanda ya gansu ba ranar da sukazo unguwar ballantana ya tayata neman su. Ita din a yanzu tsoron taba sabreen din takeyi,duba da iya mutanen da suke gadin gidansu ma gaba daya ba ita sabreen din ba,wannan dalilinne kawai yake taka nata birki akan abubuwan data qulla aiwatar mata. Abu daya take jira shine ranar da zaa ce zaa kawo lefe,tana sanya ran ranar ta zame mata ranar nasara tunda ba wani daya danganci sabreen,a ranar sai tayi mata tonon silili cikin jamaar kawo lefen,ta tabbatar za'a tafi da ita a baki,kuma dole saqo zaikai kunnen wadanda suke da iko da hana abun ko aiwatar dashi.....randa zasuzo karbar kayan aurensu kuwa tasan dukka yadda zatayi.....koda tsiya koda bala'i ta juya abun ya koma kan hadiyyarta.105 A wannan lokacin sabreen din na kwance saman doguwar kujerar falon nasu,a kwance take rigingine tana kallon ceiling,saidai kuma manyan idanunta dukkabiyun a rufe suke kai kace bacci takeyi. Banda yar qaramar fankar dake bada iska me dadi a falon ba zakace akwai wutar nepa ko sola cikin dakin ba. Ta kashe tv ta kashe dukkan wani qwai da zai iya bada haske. Kwanakinta shida kenan tana irin wannan kwanciyar,musamman lokaci irin wannan da yara suka wuce makaranta. Zuwa yanzu kwanyarta da tunaninta dukka sun gajiya kan yadda zata sanya wadannan qattan subar qofar gidan,abinda zai bata damar sakewa kenan ta qarasa aiwatar da plan dinta. Ta lura daidai da second basa gusawa daga qofar gidan bare ta samu wata qaramar dama ma da zata gifta. Dukkan wani tunani nata ya soma gajiyawa,hakanan ta fara gajiya,bataga wani alamu na samun cikar nasararta na nesantasu da wannan gidan ba. Kulli yaumin Allah shine da kullum sai kawu ya shigo dakin ya sameta a haka,qarfi da yaji ya zama me wa'azi yayin da ita kuma ta zama kurmar dole. Ta sake qaranta magana da wawalwalarta,ta sake zama miskila sosai,sai yayi maganarsa ya qare ya tashi kan wa'azin biyayyar na gaba da muhimmancim aure bata ma bude idonta ba bare tace dashi ta tafasa a sauke ba. Wannan abun da take masa yana sake razanashi,yasanta cikin miskilai ma nata halin na daban ne,wannan ya sanya ya dauki matakin da bata taba zato ko kawo cewa zai dauka din ba......don a daidai sannan kunnuwanta suka jiyo mata sallama da wata murya da take kyautata zaton ta santa......ta mata kyakkyawan sani ba in general. Daga sallamarta ta farko har zuwa ta biyu dukansu suna ji,amma tsananin mamaki ya saka suka kasa amsawa har sai data sake bayyana sosai a gabansu. Bahijja........matar da a yanzu haka suka shafe shekara goma sha daya basu sanyata a idanaunsu ba.....haihuwar haneefa......haneefa daa yanzu girma da shekaru suke bayyana kansu a tattare da ita. Kasa kowanne motsi tayi,saboda tana jin komai ne a mazaunin mafarki,sai kawai idanuwanta data bude ta zubawa qofa idanu tana sauraren isowarta don taga da gasken itace?. Daga cikin al'ummar gidan da suka shaidata suma kallon mamaki suke binta dashi. Fuskar da ta bace musu tun wani zamani baya. Da idanu take qarewa gidan kallo kawai tare da al'ummar gidan da ba wanda ya iya fusgar sunanta sai daada. "Ikon Allah.......kina nan bahijja?". Murmushi ta saki "Ina nan daada...." Ta amsa mata dashi tana ji a jikinta lallai akwai tarin qalubale masu yawa. Kasa daidaita nutsuwarta tayi lokacin da take sallama zuwa cikin falon nasu. Ta sauko gaba daya daga saman kujerar cikin wani irin hanzari tana dosarta. A murya tana jin tamkar ummenta ce ta dawo,haka nan wani sashe na kamanni,duk jikinta rawa yakeyi,hawaye kuma suka balle mata,irin hawayen nan da suke zama tilas zubarsu a idanu. Cak komai nata ya tsaya sanda ta fada jikinta tana sakin kuka lokacin da muryar uncle abdulk'adir. Muryar data sake sanya kowanne sashe na jikinta rawa,ta zare jikinta daga na bahijja ta daga kanta kaman me ciwon wuya tana ware fararen idanunta da suka sauya kala akan uncle abdulk'adir din dake takowa zuwa cikin dakin. Yana nan dai kaman yadda suka sanshi,giant dashi me yawan daurewar fuska. A wancan lokutan basu da shekaru sosai,wannan ya sanya basu fiya fahimtar rashin sakin fuskar nasa ba saboda yana da fara'a ga yara. Sai ta riqe bahijja sosai wadda suke kira da didi,itama ta kama nata hannun tana shirin zaunar da ita. ◦•●◉✿ "Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin gumi yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani sakashi a masifa ba. Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci ✿◉●•◦𝘽𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙖𝙬𝙖 𝙪𝙠𝙪 ✿◉●•◦ Dukkanin wani kuka a yanzu a kuma wannan lokacin ta yishi,kukan faduwa da rashin nasararta da kuma rashin hango galaba qarara daga kaucewa wannan birkitaccen auren da yafi kama da auren bauta. "Ba abinda zaki mana.....ba abinda zakiwa kanki ki kyautatawa kanki da rayuwarki sai aure......a wannan shekarun zaman me kike tunani zakiyi?,har kice bakison aure?,idan bakison aure me kikeso sabreen?.....kisa a ranki idan har bakiga afkuwar auren nan ba to daya ne a cikin ku biyu ya mutu.....ko ke ko shi". "Ya Allah......kasa ya mutu.......ya Allah ka sanya wannan tafiyar da yayi ya yita kenan" Ta samu kanta da furtawa a zahiri. Adduar data baiwa kowa mamaki a wajen banda kawu rufai dake zaune daga gefe. Gigitacciyar tsawar da uncle abdulk'adir ya sake mata ya sanyata runtse idonta kawai ba tare data motsa ba tana sauraren bugun zuciyarta,ko qas zuciyarta bata rusuna ko ta canza ba game da adduar data masa,saita dinga ninks wata can qasan zuciyarta tana maimaitawa akan Allah ya kawo duk wata sila ko hanyar da zaiyi nisa da rayuwarta ya barta ta huta kamar kowacce 'yantacciyar d'iya. "Wai ina amanar da nake yawan tambayarka akai rufai game da yaran nan?,ya akayi ka bari sabreen ta zama haka?". Wani lafiyayyen gumi ne ya yanko masa,baisan iya adadin qaryar sunan nan lafiya qalau da ya yiwa abdulk'adir ba......baisan iya adadin saqon da ya aikowa yaran ya handame ba ba tare da yabar kowa yasan ma anyi aiken ba. Idanunta kawai taja ta rufe lokacin da didi keson jin ko tana da wata matsala ko kuma damuwa ne game da auren bayan kasancewar ita ce batason mijin?. "To ta cewa didi me?,ta gayawa didi mamarsa tana da manufar aurawa danta shi?,while shi kansa batasan me yasa ya nemi aurenta ba da kanshi?. Tana jin bata da sauran option a yanxu illa ta tsaya ta zuba idanu kawai a buga wannan wasan da ita.......waye zai zama WINNER?.....WAYE KUMA LOSER a tsakanin mutum ukun?. 𝐒𝐚𝐛𝐫𝐞𝐞𝐧 𝐌𝐮𝐡𝐚𝐦𝐦𝐚𝐝 𝐟𝐮𝐚𝐝 𝐌𝐚𝐚𝐦𝐚𝐡 𝙜𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝐇𝐚𝐣𝐣𝐚 𝐡𝐚𝐫𝐢𝐫𝐚 Daga gefe da nata shirin da KO MEYE SHI?. Abu daya ne zata ce ya sanya wani dan siririn haske da sanyi cikin mummunan yanayin da take jin kanta a ciki.....shine samun wani haske a dakin da ya zama tamkar makwafin uwa a garesu. Yadda haneefa huda da nadra suka sanya didi a gaba tamkar ummensu ce ta dawo. Ita kuma tana tsakiyarsu,hira sukeyi tamkar xasu kwana a zaune ita dasu,su din kamar zasu koma cikinta,yayin data rungumesu da kyau itama kasancewar Allah bai bata haihuwa ba.....dangin mahaifinsu ko a wancan lokacin na rasuwar yayarta musamman kawu rufai su sukayi tsayin daka suka hanata koda haneefa da take qarama a sannan,sai haqura tayi badon zuciya bata so ba. Kwana da wunin da sukayi da sabreen ba wani abu daya canza daga yanayinta. Ta riga tayi giving up tun bayan da kawu abdulk'adir ya wuce yabar didi bahijja da zummar zata zauna dasu a nan har sai lokacin biki yazo za'a share biki da ita sannan ta koma.....komai ya qare kenan!,abinda ya rage mata daya ne shine......ta maida kanta kan tsara yadda zata maidawa kowa aniyarsa......amma har yanxun tana jin abun kamar ba gaske bane.....tana jin kamar a mafarki ne.....yaya akayi wadannan mutanen suka mamayeta har haka?,suke shirin juya rayuwarta dare daya daga wani bigiren zuwa wani......bigiren da bata taba tunanin zata tsinci kanta a ciki ba har abada. ✿◉●•◦𝙎𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙣𝙖 𝙯𝙪𝙬𝙖......✿◉●•◦ Isowar akwatinan auren muhammad jadda zuwa gidansu sabreen ahmad kadai ya sake gigitar da tarin jama'a na cikin gida dana waje. Wasu irin qasaitattu kuma lafiyayyun luxury akwati kala daban daban da suka tasamma jimillar akwatuna talatin da shida wato dozen hudu dalla dalla inji munafukai da 'yan gaza gani akwatina d'ai d'ai har arba'in da takwas kenan. Iya kwati set qwaya daya tal kawai idan aka fiddata aka saidata banda kayan cikinta sun isa musulmin jarin cikakke ga mutum a qalla goma sha kyan kyan. Wasu sabbin designers akwatuna da sabreen din ta zama mutum na farko cikin jerin ahalin iyalan masu arziqi data mallakeshi. Fadin irin tarin dukiya da suturun alfarma dake ciki ma bata baki ne. Lefe ne da aka zubawa kayan ado na gold da diamond a ciki kamar yadda yake shine ainihin sana'ar muhammad jadda,wanda duk wanda ya gani sai ya tabbatar lallai sun cika kayan aure daga wajen mamallakin kamfanin diamond da gold. "Anya bayan wannan sana'ar kuwa baya yankan kai?,suna kyautar mota kaman suna kyautar sweet.....bayan motar da aka hado mata da ita a kayan aure yanzun guda biyu suka sake sakawa akai kayan lefen fa,wai kyautar uban ango da uwar ango.....nabeela wannan wacce irin baqar rana ce?" Hadiyya da labarin lefen ya hanata zaune ya kuma hanata tsaye cikin dakin hostel din nasu ta fada da idanunta da sukayi jajur don kuka. Wadda ke zaune a gefensu ta saki murmushi "Kina wasa da bariki.....ai indai kin cika macen bariki me wayo to tabbas kafin ta bare dake kike kama kanki.....ki samu wani alaj din kiyi wuf dashi ki shige daga ciki abinki....." "Muffy.......motocin millions of naira fa kaman ana bada biscuit?" Hadiyya ta sake maimaitawa. Tsaki wadda suka kira da muppy din ta saki tana jawo kwalbarta "Har yanxu na yarda da sauranki baki waye ba.......wai shin kinsan waye muhammad jadda kuwa indai da gasken shi zata aura?.....to bari kuji.....ni ina samun labarinsa ta bakin mata da 'yammatan dake cudanya cikin manya manyan Billoniers din da muke dasu.....kusan burin kowacce mace a cikinsu ta samu kutsawa koda gefen inda yake......amma inaa....saidai hange daga nesa,baya shan koda taba ballantana akai ga giya......bai daga idanu ya kalli d'iya mace ballantana har ta burgeshi akai ga batun nemanta.......abu me tsananin daure hankali da tunani kenan. Koda kyau ne da namiji a yanzun irin na jadda zai wahala kaga baya neme nemen mata ko shaye shaye.....ballanta shi ya hada duka,ga kyau ga masu gidan rana baja baja tamkar ganyen bishiya.......bai shaye shaye ba neman mata,ya rufe wadannan hanyoyin guda biyu wadanda sune suke saurin sawa a cimma d'a namiji.......budaddun qofofi masu saurin isar da sharri rayuwar d'a namiji" Tayi zancan da confidence dinta ganin yadda dukkansu suka bata hankalinsu. Ita kanta tana jin dadin106 Ita kanta tana jin dadin bayar da labarin qwarai.....don har a qasan zuciyarta tana jin muhammad din winner ne na gaske daya tsallake tarakunan da matasan masu kudi da yawansu basu iya tsallakewa,idanma basa yin duka to zaka samu sunayin daya daga ciki tabbas!. "To.....ko muna da rabon samun irin wannan mazan ko sai a aljanna?" Maganar daya daga cikinsu kenan data bawa kowa dariya duk da suns taya 'yar uwarsu ne jimami. Su kansu a karan kansu sun sani.....samun irin muhammad din sai mace me tsananin sa'a,kowacce cikin zuciyarta kuma ba tare data bayyanawa hadiyya ba ji takeyi dama itace sabreen din,duk da cewa hadiyyan ta gaya musu cikakkiyar KARUWA CE. Duk yadda bibo ke fama da habaici a ranar kasa komai tayi. Wani irin baqinciki ke nuqurqusarta kaman ta hadiyi zaciya. Inda tasan lalacewar sabreen ba wani abu bane da zai zame mata illa ba ya hanata auruwa da tuntuni ta dade da sanya hannu a lamuranta ta kadata tayi nesa dasu bare yau taga wannan abun takaici. Lefe ya kasa dauke qasan?,sai babban falon marigayi mahaifinsu na sama aka kaishi aka zube a can?. Didi ta sanya muqulli ta rufe don sunyi yawan da za'a ce wai anzo kallo an zauna an bisu daya da daya an kalla kamar yadda aka saba ganin lefe. Wanda gulma ta qarewa kuwa saidai ya leqa ta windo ya kalla,iya Kalllon bayan akwatin kawai ba tare da ankai ga budesu ba wani abu ne me qayatarwa a idanun me kallo. Tana kwance kamar kullum har akayi didifniyar ajiye lefen dama komai da komai,idanu take budewa kawai lokaci bayan lokaci ta kalli su huda. Ba wata damuwa sam sam a tattare dasu,sai take hangowa ma kamar farinciki suke ciki. Sun samu didi da yanzu duk inda ta motsa suna wajen ta zame musu uwa na wucin gadi. Tausayinsu takeji qwarai,a ina zata barsu randa aka maqala mata wannan maqalallen auren?. A yanxu kam akwai walwala me yawa tare dasu saboda qishirwar UWA da suke kasheta tare da didi din. "Anata hidima anata hidima......amma mu har yanxu bamuga qyallin ango ba,bamuga yazo gaisuwa ko ganin amaryarsa ba bare akai ga batun gaidamu iyaye" Irin lafazin da ya fita daga bakin me biwa bibo kenan bayan ta yaye labulen dakin suna gaisawa da didi. Dan murmushi didi da tasaki,duk da itama abun yana ranta,bata taba ganin ya kirayi sabreen din ba duk da tasan zai wahala ta daga wayar a yadda ta kafe dinnan bataso......bata taba jin ance gashican yazo ba koda ba zata fita ba "Danku ne fa?,me kike ci na baka na zuba?,ai har sai kun gaji da ganinsa" "Aiyo to......naga mun aurar amma ba haka mu muka saba gani ba,koda yake sha'ani me arziqi daban dana talaka" Daga haka ta saki labulen tana wucewa don saqo ne takeson ta isar ta kuma tabbatar ya kai inda take da muradi. Sanda didi ke zaune saman kanta tana jefa tambayar kanta,sai ta mayar da idanunta kawai ta rufe tana cewa "Ki tambayi kawu" Tana ganin shike da cikakkiyar amsar bada ita ga wulaqantaccen aure irin wannan. A duniyar auren hadi.....a kuma duniyar auren dole bata taba ganin kalar nata auren ba......ki sau daya bai taba tako qafarsa unguwarsu bama bare akai ga isowarsa qofar gidan mahaifinta da zummar nemawa kansa ita kamar yadda kowanne d'a namiji yakeyi. Sai damunsu akeyi da kawo dukiyar data tabbatar tamkar magana ce a fakaice ake gaya mata na sun zabi kudi ga kudi nan.......kawu yayi mata abinda ba wani mahaluqi daya isa yayi mata shi,hakanan ba wanda ya kwatanta yi mata hakan sai shi. A kullum kalmar UBA da Allah yabashi wannan take dubawa take dauke masa qafa da idanu akan wasu abubuwan,banda haka bata tunanin akwai wanda zai mata hakan ta lamunta. 𝘼𝙡𝙝𝙖𝙟𝙞 𝙝𝙖𝙢𝙯𝙖 𝙠𝙞𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙤𝙡𝙙 𝙧𝙚𝙨𝙞𝙙𝙚𝙣𝙘𝙚 "Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa tana shafa hannunta saman fuskarta bayan ta kammala sallar ishai a ranar. Rana ce data zama ta hidima sosai a garesu kai kace bawai lefe kadai aka kai ba......tamkar bikin ake gudanarwa a ranar. Gefe guda kuma cikin hidimar tashi suke daga gidan,akwai 'yan uwa sosai da abokan arziqi da kowa ke zaban furniture din da yakeso a sassan nata. Har qasan ranta takejin farinciki idan ta tuna kwanaki bakwai kacal suka rage muhammad dinta ya zama magidanci kamar yadda kullum take da mafarkin wannan ranar. Abu daya ne ya tsaye.mata a rai,yake sake sanyata a shakka da kokwanto duk kuwa da abba hamza yayi qoqarin nusasheta tare da yi mata bayanin ta fidda abun a ranta wato batun mariya. Komai da mariya akeyi,ayyukanta duka suna gwada yadda take dama dama da auren nan. Ta yiwa mariya farin sani,ba sanin jiya ko yau ba kawai......banza bata kai zomo kasuwa,hakana nan mariyar ungulu ce bata jewar banza......ta kasa aminta da haka siddan mariya keson abun nan ba wata adawa kaman yadda ta saba.....uwa uba kuma neman yazo daidai dana fuad din. A haka dai take kallon abubuwa amma kuma tanata qoqarin gamsar da kanta all is well kaman yadda abba ya shawarceta. Sallamar musaddiq da farouq bayan sunyi knocking ta basu izinin shigowa su saka sanyata gyara zamanta yadda qafafunta zasu miqe sosai. Kaman ko yaushe tana dubansu bisa alfaharin samun 'ya'ya irinsu suka qaraso. "Larai keson magana dake akan dakincan,tana tambaya shima zaa fitar da kayan ciki?,nace mata dai su kwashe kawai" Farouq ya fada yana shafar sumar kansa hadi da zama gefan annin musaddiq kuma ya yiwa kansa mazauni saitin qafafunta. Haka suke duk sanda suka sameta zaune koda su hudunne sai su sakata gaba a tsakiya kamar wasu yayayyu ko masu shan maama,sa. Basa ganin girmansu gaba dayansu indai suna gabanta ne. "Eh yayi hakan....tashin nan ina jinsa kamar wasa wallahi" Anni ta fada tana alhinin bari muhallin da suka dauki shekaru a cikinsa,duk da cewa bawai sun barshi kenan ba.....nan dinma zaa sake zuba sabbin furniture da komai da komai cikin satin nan,idan sun gaji da waccan unguwar sai ta taho nan ta zauna......saidai ko kusa ko alama wannan gidan bai isa ya hada kafada da wannan din ba. "Lokaci anni.....zakiso wancan gidan fiye da wannan fa" Kai ta kada "Kayya.....ku yara kune qyale qyalen rayuwa ke mugu gardi.....faruqu......inason magana da surukata,ko zaka kiramin ita?" Ta tambaya farouq. Zamansa ya gyara ya ciro wayarsa yana budeta "Banajin ina da number surukar nan taki anni...." Ya fada a ransa yana tunanin fuad dinma baida ita,bayason kuma su fahimci hakan "Amma bari nasa a turo sai na kira miki". Kawu kawai ya kira kanshi tsaye ya nema number daga wajensa. 𝙎𝘼𝘽𝙍𝙀𝙀𝙉𝙉 Jujjuya wayar kawai takeyi a hannunta tana cije lips dinta zuciyarta na sake quntata. Tunda suka gama waya da matar da har yanzu ta kasa yarda wai ita din mahaifiya ce ga wancan dan rainin wayon ma'abocin girman kan mamaki yake sake cikata. Wayar mintuna talatin amma ta sanyata zaman minti ashirin tana tariyar kowacce magana data fita daga bakinta "Duk abinda kikaga baiyi ba kiyi magana.....duk kudin da kike buqata ki nemesa a wajena zaki sameshi........burina guda daya tal shine ki cikamin burina da kuma manufar da ta sanya na nema miki auren d'ana.......wannan shi zai baki damar zama cikin jerin sahun masu kudi masu arziqi.....kuma shine zai zama kariya daga rayuwar 'yan uwanki.....domin har yanzu suna a hannun mu duk da kuwa mun sake miki su". Kai ta jinjina tana sake cije lebe.....har yanxu matar bata santa ba......batasan wacece Sabrina da iya adadin abinda zata iya aikatawa ba......inda ace ta sanya harsashin wasan tsakanin ita da ita ne data nuna mata tata zallar qwarewar......to amma inaaaa......bisa rashin sa'a ta sanyo da rayukan da suka zama sune K'ARFINTA kuma sune RAUNINTA dole tayi komai bisa lura da kuma tsari. Bataji nauyin gaya mata kai tsaye ba.....ta shaida mata cewar "Bani buqatar ku nunawa duniya ni.....duk wani events bani da sha'awar zuwa.....koda kin tsara hakan dani ki cireni a ciki" Amsar data bawa maamah sanda ta bata daman shirya duk kalar events din da take da buri ko mafarkin gudanarwa koda kuwa wasu qasashen take so ayi jigilar qawayenta don gudanar da komai a can. Ta bude mata komai ne don a nata karatun.....gogaggiyar mace kaman sabreen da tasan dadin kudi da bariki.....tabbas zataso cikin manyan burika dama mafarkanta tayi kalar bikin daya zarce na kowacce yarinya dake tashe ko kuma take jin kanta ko ubanta wani ne. "Ma sha Allah.....alhamdulillah,to Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa....gata bari na bata" Muryar didi kenan data shigo dakin riqe da wayarta "Ga surukarki.......karbi mana" Didi ta fada tana miqawa sabreen wayar. Kanta ya daure,wacce surukar tata kuma?,wata dabance bayan wadda ta gama tumasanci yanzu ko kuwa?. Yadda didi ta tsareta da ido......ba wani sauran abinda zatayi saita saka hannu ta karba din. "Assalamu alaikum warahmatullah" Anni tayi cikakkiyar sallamar da wannan muryar tata data cika da nutsuwa da dattako,muryar data tsarga tun daga zuciyar sabreen din ta sace wani nauyi da fushi daketa kai kawo a qirjinta cikin mintuna qalilan ba tare data ankara ba "Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ta samu kanta da amsawa da wata nutsuwa data sameta ba tare da tasan daga ina bane. "Allah yasa zaki iya shaida wannan mamar taku,ina fatan ya gaya miki komai a kaina?" Anni tai maganar da sautin murmushi a muryarta. Dif tayi don batasan me zatace mata ba.....me zai gaya mata mutumin da ko fuskarsa bata gama tantancewa ba bare duk wani abu daya shafeshi. A taqaice anni ta yiwa sabreen bayanin matsayinta. Bayanin daya dinga zillo saman zuciyar sabreen yana sake rikita mata lissafi,iyayensa biyu?,masu mabanbantan dabi'u da halaye,wadannan sune kawai abinda tafi riqewa tanason kuma tantancewa amma kawo yanzu kanta ya tsuke gaba daya. "Ki daukeni tamkar mahaifiyarki sabreen.......duk wani abu da uwa kewa 'yarta zaki sameshi a tare dani in sha Allah". Kalmar data daki qirjinta ta kuma saukar da wani abu me sanyi saman ranta "Suna da banbani" Taji ana gaya mata daga can saman kanta bayan ta sauke wayar da suka gama da ita. Tana tariyar maganganun data gaya mata cike da harshe me hikima da fasaha.....sam babu hadi ko a iya kalamai tsakaninta da waccan dake iqirarin ita ta haifesa "Zanso nasan wacece uwar ta gaske" Ta fada qasa qasa tana duban didi dake shigowa. "Saiki kintsa kanki.....don tace zatayi aiken me gyaran jiki da zasu fara aikinsu daga gobe har zuwa ranar da zaa daura aure.......amma sabreen" Didi ta fada tana neman wajen zama gefan sabreen din ba tare data damu da damuwar da batun gyaran jikinta ya saukar mata ba. "Mamarsa nada kirki har haka?.....me yake tsananta damuwarki......duk wani motsi nasu yana alamta su din mutanen kirki ne.......wanda dukiyarsu bata rufe musu idanu ba.....don Allah ki kwantar da hankalinki......tabbas ina kyautata musu zato" "Ba zaki gane ba didi,abinda kike gani a zahiri ba shine a badini ba.......to waima wanna jikin zaa gyara?" Tayi dukka maganar ne idanunta a kulle,amma wannan ta qarshen ta ware idanunta ne akan didin. Kallonta didin takeyi tana jin kamar sabreen din bayan matsalar miskilanci da yake damunta harda matsalar jinnu. "Wanne jikin kike dashi bayan wannan nakin?,ko kinaso kiyi ma dattijuwar matar me tsananin karamci gardama?" Ido ta tsurawa didi tana jin kamar fa bai kamata tace mata bataso ba ko?,to amma ai sam gyara jiki ma baihau ba a wannan bigiren da take kai ita,don haka ta mayar da idanunta ta rufe tana motsa labbanta "Da zaiyiwu shine abunda nafiso ta janyemin". Didin ta jima a zaune tana kallonta mamaki yana sake kamata,sai data gaji don kanta kawai ta miqe tana cewa "Allah ya kyauta" Ta fice a dakin. "Anni da suruka.......Muryar nan kamar na santa anni" Musaddiq ya fada yana kallonta. Sai a sannan ta iya dauke kanta daga fuskar wayar kamar sabreen dince a gabanta,batasan me yasa ta jarabtu dason yarinyar da bata taba ganin fuskarta ba hakanan "Ba mamaki ka taba rakiyar zance a boye ko jinsu suna waya da hamman naka" Dariya ta subuce masa "Anni wannan soyayyar waye yasan sanda aka qullata?,banda ansan gidan su da sai nace mijin aljana ya bishi da gaske aljanar xaya aura" "Ungo nan.....wato wannan dan kaniyar yayan naka ya koya maka ko?,maza ka fadi yaji,idan shi yasha a hannunsa kaidai kasan sauran" "Tuba nake" Ya fada yana rufe bakinsa da hannunsa yana qoqarin boye dariyarsa. ********Tana kukan zuci qwarai da gaske wanda ke tattare da zargen abubuwa masu yawa data tanadi tunkarar kowa da komai......amma hakan bai hana zuwan me gyaran jikin da take aikinta da wata irin qwarewa tamkar zata sauya fatar jikin ta ta ainihi da wata ta daban ba. Komai ta kawo idanu ta xuba masa kamar dai komai nata ya daina aiki.....saidai fa wannan kwanyar......wannan zuciyar suna nan suna aikinsu daidai. A daidai sanda komai yake tafiya,shirye shirye suna nisa,kwanakin qulla auren da zai zamewa rayuwarsu 𝙈𝘼𝘽𝙐𝘿𝙄n tafiya bisa wata turba da basu taba kawowa zata bude musu......a wannan lokacin shirye shiryen maamah sukayi nisa itama. Ta narka kudaden da batasan adadinsu ba wajen bokanta.....wanda ta saida tsaffin kadararrta ta narkasu zuwa kudin da zasu isheta aiwatar da komai. Kowacce rana da gari zai waye,yana waye mata ne da tsananin farincikin ganin kusantuwar cikar burinta........sanin wacece yarinyar wacece SABREEN adan gamayyarsu ta qididdigaggun lokuta ya sanya ta gabatarwa da boka SUNANTA don tana buqatar aiki a kanta na musamman. 𝙏𝙪𝙧𝙦𝙖𝙨𝙝𝙞......𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙠𝙞𝙣𝙖 𝙩𝙪𝙣𝙖𝙣𝙞 𝙝𝙖𝙣𝙜𝙚 𝙠𝙤 𝙝𝙖𝙨𝙖𝙝𝙚𝙣 𝙖𝙗𝙞𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙪 𝙥𝙖𝙧𝙩 2 𝙣𝙖 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙣𝙖𝙣 𝙩𝙤 𝙠𝙞 𝙜𝙖𝙜𝙜𝙖𝙬𝙖𝙧 𝙖𝙟𝙞𝙮𝙚 𝙝𝙖𝙨𝙖𝙨𝙝𝙚𝙣𝙠𝙞.....𝙙𝙤𝙣 𝙗𝙖 𝙡𝙖𝙡𝙡𝙖𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙚 𝙘𝙖𝙣 𝙢𝙪𝙠𝙖 𝙣𝙪𝙛𝙖 😁😄 𝙄𝙙𝙖𝙣 𝙗𝙖𝙠𝙞 𝙨𝙖𝙢𝙪 𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣𝙩𝙖 𝙥𝙖𝙧𝙩 𝙤𝙣𝙚 𝙗𝙖 𝙠𝙞𝙮𝙞 𝙝𝙖𝙣𝙯𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙢𝙖𝙨𝙝𝙞 𝙠𝙞 𝙗𝙞𝙗𝙞𝙮𝙚𝙨𝙝𝙞 𝙙𝙖 𝙠𝙮𝙖𝙪......𝙙𝙤𝙣 𝙜𝙪𝙣𝙙𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙮𝙖𝙣𝙖 𝙖 𝙜𝙖𝙗𝙖 𝙕𝙖𝙯𝙯𝙖𝙛𝙖𝙣 𝙩𝙪𝙜𝙜𝙪 𝙈𝙖𝙠𝙞𝙧𝙘𝙞 𝘿𝙖 𝙬𝙖𝙩𝙖 𝙞𝙧𝙞𝙣 𝙗𝙖𝙝𝙖𝙜𝙪𝙬𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙗𝙞𝙧𝙠𝙞𝙩𝙖𝙘𝙘𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙨𝙤𝙮𝙖𝙮𝙮𝙖 𝘼𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙡𝙖𝙨𝙩 𝙥𝙖𝙜𝙚 𝙙𝙖 𝙣𝙖𝙠𝙚𝙨𝙤 𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙠𝙖𝙧 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙭𝙖𝙢𝙖 𝙢𝙪𝙧𝙛𝙞 𝙜𝙖 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙏𝙤 𝙖𝙢𝙢𝙖 𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙢𝙖 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙗𝙖𝙣𝙞 𝙙𝙖𝙢𝙖 𝙗𝙖 𝙯𝙖𝙢𝙪 𝙝𝙖𝙙𝙚 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙡𝙡𝙖𝙝 𝘿𝙪𝙠 𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙣 𝙦𝙤𝙦𝙖𝙧𝙩𝙖 𝙣𝙖 𝙝𝙖𝙙𝙖 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙨𝙝𝙞 𝙞𝙣 𝙨𝙝𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝,𝙙𝙤𝙣 𝙯𝙖𝙞 𝙯𝙖𝙢𝙚 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙈𝘼𝙉𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼. 𝙃𝙐𝙂𝙐𝙈𝘼𝙉𝙆𝙐 𝘾𝙀. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 1 𝘼𝙢𝙗𝙞𝙩𝙞𝙤𝙣 & 𝙨𝙪𝙘𝙘𝙚𝙨𝙨 𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙛𝙪'𝙖𝙙 𝙟𝙖𝙙𝙙𝙖 "Hustle until you no longer need to introduce yourself,push your self because no one else is going to do it for you". Kalamansa na qarshe kenan da tarin mayan attajiran da sukayi meeting na qarshe dasu wanda keson saka share dinsu cikin sabon kamfanin da kwanaki bakwai suka rage masa ya budeshi. Kalamai ne da suka dauki hankulan mutanen dake wajen,wanda dasu aka kammala zaman. Sanda yake sallama dash fiye da rabin hankalinsa yana kan wayarsa da tun dazun ya lura tana haske. Sai da gurin ya rage saura shi daya da hudu daga cikin guard dinsa da wannan karon dasu yayi tafiyar wadanda ke nesa da inda yake,ya miqa hannu a nutse yana jawo wayar gami da fesar da iska me dumi daga bakinsa. Cikin kowanne motsi yana jin farinciki na yadda al'amuran bude kamfanin ke gudana da dukkan wani haske qyalli da kuma alamu na nasara,bai taba qwallafa rai akan wani abu kaman haka ba,baisan me yasa dukka tunaninsa da hankalinsa suka raja'a wajen son ganin cikar wannan mafarkin nasa ba. Tunda yazo samu cikakken zama na awa biyu cur ba,saidai idan dare yayi ya wafci wasu awanni ya tilastawa kansa kwanciya ya huta. Kowanne minti idan ya shude da amfaninsa a wajensa,ko baya din dama shi mutum ne me girmama lokaci tare da bashi muhimmanci qwarai. Sunan farouq kawai daya gani ya sakashi gyara zama yana furta "Ya salam" Qasa qasa fuskarsa nason fidda wannan sihirtaccen murmushin nasa da ba kasafai ake samun dacen ganinsa ba. Wani sirri ne kwance cikin murmushinsa dake qara masa haiba da kwarjini da fitar asalin kyan da ubangiji ya huwace masa. Yasan zayasha qorafi ne kawai wajen farouq din......don yace masa zai kirashi har baisan adadi ba......hakanan bazai ma iya tuna awar qarshe da sukayi waya ba. "Hala baka da wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka sama da business dinka?" Kalmar da farouq ya fara jera masa kenan. Boyayyen murmushi ya saki yana daga dogayen qafafunsa ya aza saman dunqulallen table din gabansa me azabar kyau. Wani irin shaquwa da fahimtar juna ce tsakaninsu dake sanyasu iya fahimtar mode din juna koda basa kallon fuskokin juna. Yasan zaiji fiye da haka ma a bakin farouq din,don muryarsa a dake take da alama har kan fuskarsa akwai alamu na qosawa "Idan ka cire ku family na.......tabbas ba abinda ya fishi muhimmanci cikin duka kaf rayuwata". "Aurenka da yarinyar su a wanne muhalli ka sakasu?....." Ya sake masa tambayar kansa tsaye cikin salo na kaiwa maqura da son masa titsiye. "Aure?....yarinya?" Ya maimaita maganar har ga Allah cikin son neman qarin haske. "Eheeennn" Farouq ya fada a taqaice,cikin ransa yana jin rainin hankalin jadda yana neman fin qarfin tunaninsa muddin ya gaya masa ya manta da lamarin auren dake gabansa. "Mmtsewww......au" Fuad ya furta wani siririn murmushi yana sake qwace masa. Sai a yanzun kwanyar tayo masa tariyar karatun baya na abinda ya baro a nigeria. Kusan gaba daya sabgar ta shafe daga tunaninsa,abinda ya sanya a gaba ya mamaye tunanin komai daga kansa. "Am sorry......kasan halin......" "......halin mijin aljana.......zata sakashi ya aikata fiye da haka ma,saidai alhmdlh.....duk abinta a wannan karon munci qarfinta,kuma in sha Allah dan uwana bazai mutu babu aure ba". Dariya sosai ta qwace ma fu'ad din ganin yadda farouq din ke maganar very serious,abinda ya jima baiyi ba,ya rasa abinda yasa suka damu da auren nan......ya fuskanci gaba dayansu murna suke dashi.....ya karanci dukkaninsu sun daukeshi serious kuma da gaske suke lamuran baki daya.....ciki harda MAAMAH duk da akwai qatotuwar ayar tambaya a kanta......don ya sani,koda yaushe ita ungulu bata jewar banza. "Ka duba email dinka na sauke maka saqo......ka duba urgently" "Alright" Ya amsa masa suna katse wayar dukansu. Yasan tsaf xaya iya mancewa idan bai duba saqon yanzu ba kaman yadda farouq ya buqata. Don haka kanshi tsaye ya bude email dinsa. Baibi takan sabbin saqonni da ya fahimta kaman akwaisu ba,kanshi tsaye ya bude saqon farouq din. Daya bayan daya yake bin hotunan daya turo da kallo ba don yana fahimta can can ba. Hotuna ne na style readymade na kayan maza masu azabar kyau da aji da wani fitaccen kamfanin fidda readymade suturu ke samarwa. Company ne da sanya suturar data fits daga cikinsa sai wane da wane......sai mutanen da suka amsa sunan shegu ne su ta fannin kudi da dukiya. A idanu kayan sunyi kyau,saidai shi baisan me zaiyi dasu ba,don haka ya jawo daya wayar tashi ba tare daya dauke dubansa daga kan hotunan kayan ba ya dannawa farouq din kira. "Am coming" Abinda yaji farouq din ya fara fadi kenan da alama yana magana da wasu ne daga gefe "Have you seen it?" Idanunsa ya lumshe kadan sannan ya budesu "Yes I have.....but bansan me zanyi dasu ba......hala ka fara preparation na bude garment company ne?". Wani qululun takaici ya tsayewa farouq a wuya,seriously mutumin nan da gasken gaske yake ya fara mantawa da cewa aure zaiyi. Duka ya sakar masa ragamar komai a hannunsa ba tare da damuwa ko tambayar ya ake ciki ba ko meke faruwa ba. "Na rantse da Allah sa'arka daya baka kusa dani......shin wai ka manta yarinyar mutane da zaka aura wadda ka kaiwa sadaki?,in all likelihood ka samu memory formation right?" . Wannan karon ma saida sautin dariyarsa ya isa har kunnen farouq ''Calmdown mana dude......abun yayi zafi ne har haka?" "Yama fi haka zafi" Ya fada yana jin ya tuqewa halin fu'ad din. "To am sorry......amma dai ka sani......ina da abubuwa masu muhimmanci da yawa a gabana.....kai din kuma wakili nane a ko ina......duk abinda ya dace ka zartar ka zartar....na baka wuqa da nama" Ya fada calmly,don bayason ya sake tunzura farouq din,tunda yana ganin yana iya bakin qoqarinsa a abinda shi a nasa ganin baikai muhimmanci da suke bashi ba. Dan shurun da farouq din yayi da yadda ya sauke numfashi ya tabbatar masa fushinsa ya sauka,dama ko can basa wani dogon fushi da juna,da farouq ya zazzage abinda ke cikinsa shikenan,shine dama me yawan kauda kai.....zaka jima kana masa abu amma miskilancinsa bai bari ya nuna maka har kasan kana masa ba daidai ba,har sai sanda ya gama taraka tukunna. "Kayi magana dasu abdulghafar......for now ya kamata su sassauta tsaronsu akan yarinyar" "For what reason?" Fu'ad ya maida masa kanshi tsaye yana gyara zamansa sosai saman lallausar kujerar da yake zaune akai. "Ina ganin kaman ya kamata ta sake.....duk da dama dole ka bata security da guard,ko don yanayin halin tsaro da qasar ke ciki,sannan zuwa yanzu ta zama part of us......wanda duk xai d'amfara da sunanmu dole a bashi tsaro" "Forget about it farouq......she's gonna be able to do what you....." Sai kuma ya fasa qarasawa yana jan siririn tsaki. Shi sam sam koda sau daya bai taba jin wani abu da yayi kama da yarda ko gasgata yarinyar ba.....akwai abubuwa da yawa da uake suspecting a kanta,wanda ya sake qaruwa tun daga lokacin data bayyanar masa a mazaunin ZABIN MAAMAH. "Do you have concern about her actions?" Farouq ya tambayeshi yana tattara masa hankalinsa. "Manta kawai......mu ajiye wannan,baka tambayeni akan komai ba dude?". Yayi maganar calmly kaman zancan business din yafi bashi peace akan batun auren. "Akan komai?,akan business dinka?,wannan shine kadai damuwarka?" "Wani abu daban daya kamata na damu dashi sama da haka?". Numfashi sosai farouq yaja,yana tsoron yadda fu'ad gaba daya baya bawa harkar nan muhimmanci,yana tsoron faruwar wani abu......careless din yayi yawa har haka,yana jin kamar ya kashe wayar kawai,to amma ya sani wannan shine abu na qarshe da zaiwa fu'ad ya bata masa rai,ya tsani a kashe masa waya sam sam. Yadda yake masa bayanin nasarorin da sauran abinda ya rage ya sake bashi tabbacin business dinsa shine gaba da komai. Sunyi magana har ta kusan awa guda kafin su yanke sadarwar dake tsakaninsu. Sanda yake qoqarin minimizing email din idanunsa suka sauka kan wani sabon adreshin email din dake dauke da sabbin saqonni guda uku,kamar zai share ya wuce sai baiyi hakan ba,ya danna ya budeshi ya fara bin saqonni da kallo. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 2 Kallon farko zaka fahimci ya bada dukka hankalinsa akan abinda yake ganin gilmawarsa cikin wayar tasa. Saqonni ne kusan guda uku,kala daban daban,saidai kuma kowanne saqo daya yakeson isar masa. _mr muhammad jadda,You hereby warned to stop all activities related to lunching your company_ saqon farko kenan. A nutse ya sauke idonsa zuwa ga email na biyu _Not heeding this warning may put your personal and professional assets at risk_ . Sake matsawa yayi zuwa saqo na uku shima still dai kakkaifan jan kunne ne zalla a cikinsa. _Ignoring this warning may lead to financial losses and reputational damage_ still dai qasansa shima wani saqonne _Proceed with caution,as this may have unintended consequences_. Tsam yayi da ransa,yana sake bin saqonnin daki daki yana bitarsu. Wannan wanne irin barazana ce haka me girma?,daga wanne sashe ta bullo?,su waye keda alhakin aiwatar da hakan?. Ya jima da sani......ba sanin jiya ko kuma yau ba.....sana'arshi sana'a ce dake dauke da tarin hamayya gogayya da kuma abokan adawa na sarari dana boye,wani irin matsayi ne da Allah ya bashi wanda bai taba tunanin samuwarsa a qananun shekaru irin nashi ba. Akwai tarin mutanen da suka fishi jimawa cikin harkar.....saidai har yanzu basu samu irin nasibin daya samu ba. Gyara zamansa ya sakeyi da kyau yana furzar da iska daga bakinsa. Ya sani,zai iya bincike akan ainihin adreshin,saidai kuma yasan zai wahala ya iya reaching komai akai koda yaso samun haka. Beside ma,isn't the first time daya fara samun ire iren wadannan saqonnin,wanda daga qarshe yake cimma daga wanne waje suke?. Ba abinda ya taba girgizashi ko ya daga masa hankali kwata kwata,amma kuma hakanan yaji wannan saqon ya tsaye masa a rai. Bai sani ba.....ko don saqon yazo masa ne a daidai sanda yake da burin aiwatar da abinda ya qwallafawa ransa na cikar burinsa?. Yadda yake a tsaye a siffa da zati me taba zuciya,haka zuciyarsa take a tsaye. Ba komai ke bashi tsoro ko firgitashi ko sanyashi yaja baya akan abinda ya fuskanta ya kuma qudira zai aiwatar ba.....don haka wannan saqon ma sai ya sanyashi cikin sahun sauran saqonni marasa muhimmanci,wadanda ba komai bane a ciki face zallar barazana maras muhimmanci a wajensa. "Hasbiyallahu wa ni'imal wakil,hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya furta a nutse,take taji zuciyarsa tana sake samun nutsuwa da aminci. Komai ya tattare yana duba lokaci,cikin jikinsa yake jin ya gaji,yana buqatar cikakken hutu kafin gobe,so samu yabar qasar nan da kwanaki biyar,to amma ya fahimci zai wahala dama ta bashi hakan. Sanda suke takawa da guard dinsa zuwa mazaunin motocinsa guda biyu kira ya shigo wayarsa. A gajiye ya zura hannunsa a side pocket dinsa ya zaluqota. Taku biyu baya sukayi dukkaninsu,wanda wannan kuma sabonsu ne,don basu tsaiwa a waje muddin zai amsa waya,saidai idan shine ya buqaci hakan. Sosai ya zubawa sunan ido yana kallonsa,yayin da zuciyarsa ta cika da wasi wasi da saqe saqen abinda kunnuwansa zasu iya jiye masa daga bakinta. Yaci gaba da irga bugawar da wayar keyi,wanda yake jinsa kamar daidai da bugawar numfashinsa. Ko a tarihi,ko kuma a labari yana kyautata zaton shi din yana cikin mutane sahun farko da idan labarinsu zai fita a kundin littafin al'ajabi zai ja hankalin mutane da dama. Kiran uwa na daya daga cikin kiran dake sanya dukkanin yaro alfahari.......kiran uwa na daga cikin kiran da kowanne yaro ke fatan gani a kowacce rana.....kiran uwa kira ne dake iya juya zuciyar kowanne yaro daga baqinciki zuwa farinciki.....amma banda su......banda tasu mahaifiyar......banda kuma nasu kiran wanda ba komai a cikinsa face zallar ko kwanto da didibniya tsakanin lalubo alkhairi ko sharrinsa. Yana daga cikin motor qafafunsa suna waje ya zauna,yana qoqarin lalubo nutsuwarsa da yakan rasa a duk sanda kiranta ya riskeshi ya daga wayar. Alamun daga kiran ya sanyata sake hada nutsuwarta waje daya,gami da dagawa hajja furaira hannu wadda ke lissafo mata tsare tsare na abubuwan da suka shirya gudanarwa a wata shimfidaddiyar farar takarda. Tsit wajen yayi,bakajin motsin komai da kowa,abinda zai sanya wanda ke nesa irin fu'ad din xaya dauka ita kadai ce wanze a dakin. "Barka da warhaka" Ya furta da muryar nan tasa dake da tasirin kwarjini me yawa da haiba a ciki. "Barka kade.....ina fata kana lafiya?" Ta masa tambayar data zamo abu mafi dadewa baiji ba daga bakinta. Duk da zuciyarsa ta kasa yarda haka siddan tayi kiransa amma ya hadiye wannan.....ko yaya yaji dadin tambayar cikin ransa koda kuwa da manufa aka yita "Alhamdulillah.....Allah yasa kuma hakan" Dan murmushi ta saki,zuciyarta tana ayyano nesanta zuwa kusa da ita. "Lafiyarmu qalau,sai shirye shirye da muke yi gadan gadan". Bai wani fahimci shirye shiryen da take magana a kansu tashin farko ba......har sai data dora da nata bayanin. " Na kiraka ne don na shaida maka.....ina buqatar wasu kudade da zan qarasa duk hidimomin da suka ragen.....ta bangaranka da kuma bangaren ita kanta amaryarka......don kasan hidimar biki ba qaramin abu bane,......bare ni da zan aurar da dan fari......kuma ita kanta yarinyar ya kamata ace ita,danginta da dukkan wani dage da jibi da ita yasan cewa tabbas da gaske mamallakin diamond company zata aura.......banason harkar qaranta......ya kamata duniya kanta ta shaida d'ana zaiyi auren fari". Kusan koda yaushe fitar kalmomin bakinta suna zame masa tamkar makaranta ne......ya jima da sanin maamah din macace me son izza da nuna isa.......ya dauka wani tsohuwar dabi'a ce a tattare da ita.....amma xuwa yanzun ya sake amanna mutuwa ce kadai zata iya samun nasarar rabata da wannan halin. "Me ake buqata?" Ya tambayeta kai tsaye.....don shima da nashi plan din. Zuwa yanzu yana kallon komai ne tamkar a tafin hannunsa ake shiryashi,abinda ya rage masa ya sani kuma kadanne da bayajin zai zame masa me wahalar riska. "Kudi nakeso ka sakamin......sannan ka sakawa amaryarka......kamar million......." "Kiwa saddiq magana......zan gaya masa ya saka miki adadin abinda kike buqata" Ya yanke bayanin da taso yi masa da adadin kudaden da duk da yasan ya jima da fin qarfinsu........amma kuma ana nemansu ne a muhalli da gurbin da babu buqatar yawan wannan adadin. Murmushi ta saki tana jin wani dadi yana ratsa zuciyarta,tun a yanzu tana sake samun tabbacin nasarar dake bibiyarta,tana kuma fara jin qamshi da dadin da uwa keji a yayin da take gwada girman izzarta akan yaranta suke kuma bibiyarta sau da qafa akan duk wani buri ko quduri nata "Allah yayi maka albarka" Ta fada tana murmushi. Kalmar ta dinga masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa,sai ya dinga jin kamar ba daga bakin maamah ta fito ba. Idan yace bazai iya tuna ranar data fadi wannan kalmar a kansa baiyi qarya ba. A hankali sai yaji kaman zuciyarsa tana rugujewa. Inama ace ta fadi kalmar ne domin cancanta da kamatar ta fadeta a kansa?,bawai don duniya ko wani abu dake cikinta ba?,bawai don son rai ko biyan buqatar rai ba. Da wannan murmushin dake sake yalwata saman fuskarta a kowacce rana ta ajjiye wayar saman table din gabanta. Qasaitaccen table ne da yazo cikin set na kayan furniture din da aka qawata sabon gidan nata data riga kowa tarewa a ciki. Gida ne datake jin zata kece biki na alfarma a ciki......zata daga sunanta da kuma martabarta a idanun qewaye dama duniya gaba daya. "Kowanne motsinsa sai ya dangantani da saddiq hamza kibiya" Ta fadi tana duban idanun hajja,har cikin ranta tana jin wata wuta tana ruruwa tare dason gaggautowar ranar da zata saka kakkaifar wuqarta ta yanke wannan alaqar da tafi mata kama da baqar alaqa. "Hanzarin na mene mariya?,saurin me kikeyi ne?,saura kwanaki nawa duka duka?" Hajja ta bata qwarin gwiwa tana cike da kwadayi da son jin abinda ya faru tsakaninta da fuad din. Kai maamah din ta jinjina tana son dawo da walwalarta kaman daxun. "Bai tsaya jin koma nawa nake buqata ba......kawai yace nayi magana da saddiq,shima zai masa magana na karbi abinda zan karba din......kinga zan karbi kaso biyu kenan......da nawa dana yarinyar can,zan san mata wani abu a ciki ne kawai.....sai na cire abinda zan cira a ciki.......zan ware na boka donshi kansa yawan kudin dana qara masa akan wanda ya buqata na fahimci ya qara masa azamar aikin nan.....hajja" Ta qarash da kiran sunanta da wani irin sauti dake nuna gajiya da zallar zaquwa. "Inaso yayimin aiki irin aikin da bai taba yin irinsa ba tunda ya fara harkan nan......inason yayimin kalar aikin da ba fuad ba......ko tsuntsun gidan fu'ad sai ya zama me biyayya a gareni........inason yayimin aikin da sabreena zata koma tamkar bawa da ubangidansa a hannuna........bansan me yasa yarinyar ke yimin kwarjini ba,bansan me yasa nakeji wani abu daban ba idan ta kalleni......inason dukka wadannan abubuwan su shafe daga idanuna". Wani murmushi dake dauke da tarin boyayyun ma'anoni da rufaffun qudurori dake amsa kuwwa da amon nawa burin yana sama da naki hajja tayi,sannan ta harde qafarta tana cewa. "Dukka wannan qanqanin aiki ne a wajensa,kuma ko iya haka aka tsaya zaki bawa wani labarin zafin aikinsa......isassun mata kawai ke iya aiki dashi,matan manya da iyayen manyan mutane irinki,saboda daga sadakin aikinsa kawai zaki fahimci ba gama garin boka bane.....don haka ki rubuta ki ajjiye.....dukkanin wadannan burirrika naki tamkar sun gama cika ne......saidai banji share dita a wannan kasafin naki ba". Rausayar da kai maamah tayi tana sakin murmushin jin dadi. A qasan ranta tana mamakin son kudi tsantsa irin na hajja din,duk kuwa da cewa lullube take cikin wadata me tarin yawa.......saidai wadatar yaranta idan kaf idan aka hadesu batakai kaso daya cikin ukun abinda fuad ya mallaka ba shi kadai......amman duk da hakan bata raina kudi komai qanqantarsu(tabbacin zuciya ta zarme da yawa dason abun duniya,Allah ka kiyashemu). "Baki da dukkan wata damuwa hajja,kina da million uku a ciki,kafin alqalami ne kawai......kuma somin tabi,nan gaba kadan ke zaki dinga bada wannan adadin a matsayin taki kyautar" "Qwarai da gaske kuwa mariya" Hajjan ta fada kanta tsaye tana duban idanun maamah da wani irin confidence daya sanya maida hankalin maama duka a kanta. Wannan ya sanya ta sassauta kaifafa harshenta da nuna dukkanin qwarin gwiwar dake kan fuskarta. "Yaronki ai yarona ne mariya...ni nasan bani da haufi....ba zaki taba butulcemin ba" Ta sake yiwa kalamanta ado da wasu kalmomin "In sha Allahu" Maamah ta amsa tana rausayar dakai har yanzu murmushin na saman fuskarta,ta kuma jawo wayarta tana fadin "Bari na nemi musaddiq ya nemo yaron can,don da zafi zafi ake dukan qarfe......gobe nakeso muyi sammakon tafiya hado dukka ayyukan dama sauran bayanai......bikin nan da gaske tahowa yakeyi,kwana shida kacal ya rage......inason tasan da zaman kowacce doka qa'ida dama sharadi kafin ta samu lasisin karbar igiyoyin auren d'ana a kanta". Da wani kallo hajja ta bita kawai ba tare da tace komai ba.....saidai kuma can cikin wani saqo na zuciyar magana ce me yawa nauyi da kuma dogon xangon da bazai yiwu baki ya furtata ba. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 3 Daure da babban towol da kuma da kuma wani babba data lullufe jikinta kirif tun daga saman kanta take takowa daga cikin toilet din dake manne da falon tana dawowa cikin ainihin falon daya zama sansaninta a yanzu. Nan din wani kebantaccen guri ne cikin gidan nasu,da asalinsa ya zama muhalli ne na mahaifinsu,wanda tun bayan shudewarsa ba wanda yake ta'ammali da wajen,don gidan nasu ya wadaci kowa,kawai sai saman inda falon nasa yake ya zama wajen da akan bude ne kawai a share,sai idan wani taro ya tashi kuma cikin gidan sannan akan zauna a ciki har ayi a gama. A yanzun saman ya zama kusan nata,tunda aka fara mata aikin gyaran jikin ko qasan gidan bata saukowa. An killace muhallin da komai da zata buqata,kaman yadda aka ajiye mata cima kala kala wanda sam basu taba birgeta ba koda qanqani. Hasalima ita a yanzu cin abinci ya zame mata daya daga cikin horon da mamma bahijja keyi mata. Koda kuwa ta kauda kai ta kuma kafe akan ba zataci ba,mamman bahijjan data tsaya a bigiren da akan buqaci uwa saita nemo wani abu daban ta bata,takance "Aure zakiyi fa sabreena,gidan miji zakije,anata gyaran fata amma can cikin ko oho?,kinsan yadda yunwa ke kassara ni'imar mace kuwa?" A duk sanda ta furta hakan sai sabreen taji kaman wani abu ya shaqe mata wuya. Wai halan basu kula kuma basu lura da dukkan komai?,sunata magana akan auren da ba komai a cikinsa face zallar rudani?,rarrabuwar burika da kuma tarin biyan buqatar rayuka masu yawa a cikinsa?. A yanxun data dawo daga dauraye jikinta da tayi daga gyaran jikin da kullum kwanan duniya takeji kaman ana mannawa fatarta wuta.....duk inda ta gifta kota zauna wani irin fitinannen qamshi take barwa gurin. Wani irin mayen qamshi me matuqar naci da mannewa jiki dama dukkan wani abu da mutum zaiyi mu'amala dashi. Qawatattun idanun nan nata da a yanzun suka koma rusunannu ta daga a nutse tana duban me gyaran jikin dake faman gyara wutar da zata sake turareta da ita. Ta zama wata kurmar qarfi da yaji,magana na mata wahalar gaske,kwanyarta da nazarinta harma da dukka tunaninkan da takan raba dare tana yinsu.....dukkansu sunfi ta'allaqa da kuma rinjaye akan YAYA WASAN ZAI KAYA?......wa zata fuskanta cikin fuskoki muryoyi dama ruhikan dake zagaye da wannan game din?. Idan ta tuna da mariya maamah.......tana jin wani abu sosai qasan ranta......jikinta kuma yana bata wani lamari me nauyi da batasan mene shi ba,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata ita din ba komai bace......tayi ganganci ne ma kawai data kutso kanta cikin rayuwarta......batasan wacece sabreen ba da gaske da bata aikata hakan ba.......bata kuma san meye da meye zata iya aikatawa ba. Motsawar sunan muhammad fu'ad kawai cikin kwanyarta shine abinda yafi sanyawa wani tsagi na zuciyarta damuwa.........lalata dukkan wata alaqa da kuma dangantaka cikin aurensu shine abu mafi sauqi da zata iya aiwatarwa......to amma kuma saki fa?.....A HANNUNSA YAKE!,amsar da akowacce rana take qara yawan adadin fargabarta. Lumshe ido tayi taja iska sosai cikin huhunta sanda muryoyi biyu suka sauka a tsakiyar kanta "Turaren ya hadu kona miqo miki ki zauna akai da kanki....." Cewar basudaniyar me gyaran jikin,yayin da nata maganar ya cakuda dana mamma bahijja data miqa mata wani bowl na tangaran "Bata din.....kafin hayaqin ya gama bin jikin ki saiki qoqari ki shanye wannan". Dara daran fararen idanunta ta daga tana kallon mamma bahijja kafin ta maida dubanta kan abinda take miqo mata,itama ita take kallo wannan ya hanata katabus na musanta mata,sai kawai ta miqa hannu ta karba,saidai kuma data fakaici ta juya,saita maidashi daga gefanta ta ajiye. Sanda tururin hayaqin ke ratsa sassan jikinta haka kowanne lungu da saqo na zuciyarta ke qoqarin bata mafita a lamarin dake tunkarota nan da kwanaki biyar masu zuwa. Zuwan mamman bahijja ya zame mata wani babban katanga daya hanata aiwatar da kowanne shiri da zai nesantata da auren.....duk da tarin bayanan da kawu yayi mata na ba inda zata shiga a duniya ta iya tserewa me jadda........saidai ta dauki.maganar tasa a wasan yara ne. Koshi waye.....ko kuma da meye yake taqama tayi imanin saidai idan bata sakashi cikin plan dinta ba..... "Adda baki sha bafa" Muryar huda da ke zaune gefanta ta fada,wadda kusan kowanne shirye shirye da ita ake aiwatar dashi. Maida idanunta tayi ta sake lumshewa muryar huda na dawo mata,ta fahimci dari bisa dari ba wani me adawa da auren,kusan kai tsaye ma zata iya cewa dukkaninsu maraba suke da abun,duba da irin walwalar da suke ciki gaba dayansu. "Ki nutsu sabreen.......ki nutsu.....karkiyi abinda zargi zai dawo kanki......karkiyi abinda su mamma bahijja xasu kasa karbarki da wankeki daga laifi duk sanda kika kammala da wancan game din kika dawo musu" Wata murya daga can qasan zuciyarta ta soma gaya mata. Idanunta ta bude ta aza kan huda har sai da hudan tadan sha jinin jikinta. Sunyi mata farin sani,daga kallonta kawai suna iya karantar umarni da kuma hani,amma ga sabanin tunaninta sai tayi mata nuni data miqo mata abun. A hanzarce kuwa ta ajiye littafin hannunta ta miqe ta dauko ta miqa mata. Tsure abun tayi da kallo wanda batasan da meye da meye aka hadasu ba,to amma koda meye aka hada din,ta tabbatar mamma tana asarar kudinta ne kawai,don haka ta kafa kai ta soma kurba a hankali gardin abun yana ratsa kunnenta duk kuwa da bakinta ba taste,haka zuciyarta a quntace take. *******Doguwar tafiya,hawa da kuma sauka,kutsawa cikin surquqi dukka ba damuwar maamah bane. Fatanta da burinta ta dangana ga mubata.160 data miqawa al'amarinta gaba daya,ta kuma sanya hope me yawa a kansa. A yanayin data ganshi a yau ya sake saka mata tabbacin samun cikakkiyar nasara. A hargitse yake yau din cikin zafin ayyukan mutanen da suka zabi ya zame musu abun dogaro kuma hanyar samun duniyarsu ba tare da damuwa da meye makomarsu ta lahira ba?. Bayan shafe shafensa da buge bugensa,ta hautsina dukkanin kayan aikinsa da yayi,ya kalleta da jajayen idanunsa qananun ainun dake cike da rashin tauhidi da kuma zallar sabo fajirci da fasiqanci. Dubane daya sake tabbatar mata ba rahama ko tausayi ko misqala zarratin a cikin ransa "Akwai tarin sarqaqiya......akwai tarin qalubale......akwai al'amura da yawa da zasu iya wanzuwa ko su biyo baya........ita din taurarinta nada tsananin haske da wahalar kutsa kai a cikinsu........tana da wahalar sha'ani na gaske......tabata kuma abune da zai iya zuwa da nasara da akasin haka.......kaman zan iya cewa KINYI KUSKUREN ZABINTA.......to amma kuma ba wani tauraro da zai iya shiga nasa taurarin sai natan......tamkar itace mahadi masarrafi kuma barin nasa taurarin......taurarinta sune abokan tafiyar nasa.........sunyi matuqar dacewa da juna.......wanda hakan shine zai bada damar tafiyar umarninmu da haninmu a kansa......kusan komai nasu suna matuqar kamanceceniya dana juna......ITACE TA DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMI GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA......saidai na gaya miki.....kamar akwai alamun KUSKURE DA NADAMA.......akwai babban waqeee'a......juyewar komai da lullubewar mayanin duhu bisa faifan qaddara". Tunda ya fara maganar gabanta ke wani irin faduwa. Hajja da suka gama sauraron bayanan a tare ta dora hannunta a kafadar maamah da zummar yin magana da ita da neman qarin bayani......saidai da sauri maamah ta zame hannunta daga kafadarta......tayi nisan da batajin zataji kira......zuwa yanzu nasara take nema ta kowacce fuska,ta kuma kowanne yanayi......bata buqatar tsaiko fashin baqi ko qarin bayani a yayin da take dab da cimma nasararta........bayan kuma a baya ya bata tabbacin ta wannan hanyar ce kawai nasara zatazo mata babu ko kwanto "Amma dai akwai hasken nasara ko dan kadanne?". Kansa dake cike da wasu irin gasussuka ya jinjina ba tare daya koda dubi idanunta ba. Cikin samun qwarin gwiwa tace "Nasara duk nasara ce komai qanqantarta,baa canza mata suna daga nasarar dai,hakanan daga qaramar nasara ake cimma babba......ayimin komai da ake da iko a kansa.......a sakamin yarinyar a tafin hannuna kafin samuwar fu'ad.......itace tsanin......ita zan fara mallaka don ta zama hannuna tsani na kuma idona zuwa ga wancan babban burin nawa!". Ta fadi muryarta na raunana tana tsoron jin akasin abinda zuciyarta ke muradi. "An gama!" Ya fada da wata kakkaurar murya maras dadin amo. Saita sauke ajiyar zuciya tana yi relax ganin yadda ya soma maida hankali akan aikinta. Boyayyar ajiyar zuciya hajja itama ta saki. Ba haka taso lamarin ya kasance ba,taso tana kuma so taji cikakken fashin baqi da qarin bayani daga bakinsa. Wacce irin sarqaqiya ce? Wanne irin duhu ne?. Wani irin baqin lullubin mayafi ne haka?. Wacce nadama ce zata biyo baya?. Meye kuskure a cikin zabin nata?. Dukka wadannan amsoshin tana buqatar saninsu ne don tasan daga ina zata dasa nata harsashin?. Daga ina tata TAFIYAR zata fara?. Ta wacce fuska zata saita tata DUNIYAR?,ta aza duniyar SHALELENTA?. Bata data cewa ko wani motsi,ta sani cikin aikinsa ba shishshigi,ke me rakiya kuma baki data cewa......hakanan baki da damar yin komayya kiyi tambaya akan aikin daba naki ba.....wannan kadai ya kashe mata jiki,ta zurfafa a cikin saqe saqe har ya kammala aikin maamah,ya kuma shaida mata su wuce zasu tadda komai cikin motarsu da qarin bayani. Bata sake gasgatawa da imani da zancansa ba saida suka samu komai a mota a ajjiye kaman yadda yace. Ta sake tsinkewa da lamarin aikinsa,inda da wani suka je wajen.....ko akwai gilmawar dan adam ta wajen sai tace an ajiye musu ne. "Kings abun mamaki hajja?,kullum mutumin nan sake dauren kai lamarinsa yakeyi" Ta fada tana juya kayan tsatsubar dake hannunta. "Kina zaton gurin qaramin mutum na kawoki......amma mariya?,me yasa kikaqi tambayarsa dukka qalubale da matsalolin daya hango miki?" Hajja tayi tambayar da tafi tsaya mata a rai. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 4 A nutse ta daga kai tana kallon hajjan "Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan matsayin da nake kai a yanzu......me zanyi da ita ballantana na buqaci sharhi a kanta?,bana buqatar dukkan wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan cikar burina a yanzu.......inaji a jikina da raina cewa......zan iya kauda kowacce matsala da zata tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin da muke kai a yanzu......da qwanjina....da kuma fikirata". Jinjina kai kawai hajja keyi.......tanason taji wanne tanadi da tsari tayi akan hakan?,amma kuma bataso ta zafafa tambaya akai har maamah ta zargi wani abun,saita tattarewa ranta komai tana jiran lokaci.....domin kuwa ta san cewa qwace goruba a hannun kuturu ba abu bane me wahala ba. ********Abune sananne a wajen kowa......sharar biki da yawan maganarsa a bakunan mutanen mu ya ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko zuri'ar da za'a gudanar da bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES. Daga qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda tabbacin ya samu ne daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza kibiya sukewa bikin shiri na gasken gaske. Daga abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan labarin ya fara kewaye kowacce kafar sada zumunta. Duk da a qurataccen lokaci labarin ya fasu.....to amma labari ne me dumin gaske daya bawa mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin 'yammata da dama......musamman yaran masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar sonshi......suke kuma da qaqqarfan hope din samun shiga a wajensa kodon matsayi da mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa......ko kuma kasancewarsu abokan kasuwancin gold da diamond dinsa. A gefe guda kuma wajen 'yammatan da suka hada duk wata sura kyau da isa.....wadanda sukasan basu da wani tsanin isa zuwa gareshi......saidai sunyi mutuwar murus akan mayatacciyar soyayyarsa......abun ya sake bude musu topic of discussion......qarqashin kowanne posting na labarin bikin dake dauke da qawataccen IV na bikinsa da aka qawata da zallar ruwan gold,yake kuma wani irin sheqi da daukan idanun da zai gaya maka bikin ba na yaro bane......tarin cincirindon comments ne da mabanbantan kalamai masu yawan gaske. Da yawansu suna fatan inama zasu samu hotunan amaryar?,ina free wedding pics da sauransu,saidai ko daya basu samu ba face kunji kunji da shaidar zur daga wasu daga cikin commentators na qarya,sai luguden labba da tsabar kyan IV din bikin da aka kashesu dashi.......sai videos na lefen da aka samu wadda ta qwarewa gulma da munafurci ta ba bajesu dashi......abinda ya sake hura wutar tattaunawar. Sam wadanda ake abin dominsu basusan anayi bama......daga angon har amaryar ba ma'abota social media bane........idan kaga ta qulla abota da waya to akwai sabon mission a gabanta........data gama ta ajiye wayar dama layukan da tayi aikin dasu,wani ta karya ta zubar.......wani kuma sai bayan wani zamanin.......yayin da oga fu'ad sam sam ayyukansa basa ma bashi damar tunawa da wani media......koda WhatsApp dinsa idan ka ganshi akai wani abune ya kama da lallai yake da buqatar hawa yayi a can din. Koda yana free ma ko yana annual leave dinsa.......yanayin tsaro da dukka rayuwarsa ke buqata ya sanya ya sake nesa nesa da duk wani harkoki irin wadannan......don komai nasa a matakin rayuwar daya taka yanzu yana buqatar privacy. A daren da ya rage ayyuka sosai......abu daya tak ya rage masa ya kammala yabar qasar. Yana zaune saman bean bag chair,daga gefansa ruwan wolfberry ne me dumi yake sipping yana kuma chewing berries din idan sun shigo bakinsa. Haka kawai yayi shaawar shiga yaga me duniya ke ciki don duka schedule dinsa na yau ya kammalasu. Da wani personal account yake amfani,wanda bai taba ba baya kuma wallafa komai a ciki bare ka iya gano waye mamallakinsa. Akwai account na company dinsa kala daban daban dake qarqashin kulawar ma'aikatansu dake kula da wannan fannin,so amma ko su baya bi ta kansu tunda yayi imanin zasuyi handling dinsa ya dace da abubuwan da ya kamata ace an sanya din. "Ya salam" Ya fada yana miqewa daga relaxing din da yayi cikin bean bag din yana kallon yadda hotunan katinan daurin auren ke shawagi cikin media. Da farko ma bai fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita jeho masa ire iren posting din.....kamar sunayi da gayya sunsan shike da alhakin abun har sai da hankalinsa yakai. Shuru yayi yana sauka gami da furzar da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne wannan farouq saddiq da musaddiq,sai amna ta hudunsu. Kamar jira akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana dubawa......farouq ne,kusan tun randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa yadda za'a sameshi ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call. Ta signal ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke ta'ammali dashi saboda samun cikakken tsaro. Shigan farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa. "Hey...." Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad "Don't tell me baka ma taso ba?" Yayi masa tambayar yana tsuke fuska tare da bata fara'ar fuskarsa "Zuwa ina kuma dude?.....bakaga abinda kuka jawo ba?,baka ga abinda ke trending ba?" Ya masa tambayar shima hana dan bata fuska kadan. Kai farouq ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu "Am asking you seriously fa.....where are you?" "Ask media users......farouq,you take it very serious fa.....wannan fa auren ba wani abu bane da za'a damu dashi har haka ba.....ba wani babban abu bane da zai zama ya yada ko ina ba......it's just a temporary......." "Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact ma idan ka matsa da yawa zan fiddo komai.....just ka dauko hanya gobe kawai......if not,bazan gaya maka abinda zai faru ba". Datse kiran farouq din yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba tare daya motsa daga inda yake ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi sosai,shi yasa yayi masa abinda yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa ne,shi sam baiga me yasa zai damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun daurawa kai hidima har haka ba......already sun gama diban kudin komai da komai uban da 'yar,daurin aure kuwa ko aike yayi cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan da zai ajeta ko ba yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan ya gama sabgogin gabanshi,for god sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?. Bai sake bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu bane me dorewa ba. Saidai yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan me zaya faru ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni ya sameshi. Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din hannunsa,ya koma gefan table din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga wayar. Cikin nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi masa sallama cikin tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar. "Barka da warhaka anni......anni ayyuka sun sani gaba,ayimin afuwa" Yayi riga malam masallaci wajen fada. Murmushi ta saki cikin nutsuwa tace "Anyi maka Muhammadu........ya aikin?,fatan komai yana tafiya daidai?" "Alhamdulillah anni.....komai alhamdulillah,saidai muna buqatar qarin addu'a" Ya furta maganar jerin saqonnin daya gani shekaran jiya suna fado masa. Ba'a raina kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa. "Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi......amma nayi zaton samun baquncinka a yau......tuntuni mun sauka a sabon gida.....duka duka jibi ne daurin auren nan......ga baqi a gidan kowa kai yake tambaya". Hannu ya sanya ya shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano abinda yasa suka daukaki sabgar nan haka.....har wani taron gayyar jama'a anni itama tayi kenan bayan ta maamah?. "Jibi din zan shigo in sha Allah anni" "Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya kamata....private jet ne,baida buqatar samun wani issue ko ya kawo excuse" Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo masa. Murmushi ya saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da anni kenan?. "Bani shi anni please" Ya fada da sauri,bata ce komai ba ta miqawa farouq wayar tana murmushi. Drama din fu'ad da farouq babu me shiga,idanma kace zaka shiga din kunya zakaji. "Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da anni......ka canza hali wallahi" Ya fada yana dan daure murya. "Kome zaka fada ka fada.....ina nan ina jiranka" "Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai zan daurawa auren nan da yarinyar......tunda naga ka damu da lamarin ta da yawa" Daga haka ya katse kiran yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah dinsa sai Allah. Haka kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida hankalinsa qwarai kan qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa nigeria kaman yadda ya alqawarta. Hannu anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita. Duk da mitar da yakeyi din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta fahimci akwai lauje cikin nadi.....boyayyen manufa da qudurin data hana fu'ad damuwa da dukkan wani lamari daya shafi auren. "Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends dinmu gobe zasu iso.....amma ace shi yana can neman kudi?.....har yau ya kasa sanin kalmar hutu a rayuwarsa?.....ta yaya zai kula da diyar mutane?" Murmushi anni ta sake,yadda farouq din keta mita ke bata dariya "Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya iso fa.....sannan tunda kaga haka din ba yadda zai taho dinne,da yau gobe da jibin dukka na Allah ne,kuma kaman yau ne.......ina da saqo ma da nakeson ka miqawa d'iyata...." Anni ta fada tana yunqurawa ta miqe. "Ina amna ta shiga ne?" Farouq ya tambayi anni dake qoqarin bude wani side na wata qawatacciyar cupboard ta daban dake cikin aljannar duniyar bedroom din nata. "Tana bangaren beauty spa" 𝘿𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖 𝙩𝙖 𝙣𝙖 𝙠𝙪𝙙𝙞 𝙣𝙚. 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 5 "Okay" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda yaga alamun ta dauki bikin kamar yafi yadda kowa a gidan ya dauka. ******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma bugawar agogo sake kusantar da ita kawai yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda ke shirin faruwa da ita. Sannu sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin da da yawansu ta manta da kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin rasa mahaifinsu mamallakin gidan gaba daya,yau sai gasu da daya da daya suna bullowa da sunan halarta taron bikin da tayi imanin ba wani bane ya gayyacesu. Dondai mamma bahijja ba wata mu'amala ke tsakaninsu ba,hasalima ba sanin kaso casa'in da tara a cikinsu tayi ba. Ba sanin jiya ko yau ta yiwa duniya ba,ta sani....kusan mafi rinjaye a cikinsu sanin waye yake shirin aurenta shi ya kawosu bikin,bikin da babu wani abu guda daya da take da masaniyar ita ko mamma bahijja ta tsarayi,koda an tsara din ta tabbatar aikin kawu rufa'i ne,wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye,komai yana gaba gaba a kai,hakanan ya saki kudi anata hidima cikin gidan. Yanayin yadda ya saki bakin aljihunsa ya dasawa sabreen qaqqarfan yaqinin kudade ya samu ko ya karba daga wajen mutanen daya sadaukarwa da ita. Bata cewa da kowa komai ba,amma tana karance da kowanne motsi na cikin gidan. Yadda bibo tayi uwa tayi makarbiya,a rana takan hauro saman da zummar dubasu har babu adadi,saman da a baya sai da akasha dambarwa da ita kafin ta daga qafan kasancewarta a can,sai da sukayi baram baram da kawun,ya wanke mata zanin mutuncinta tas tare da buga mata gori nau'i daban daban,yau din sai gata tana zarya tsakanin hidimar da ba tata ba bata kuma shafeta ba. Sanye take da wata simple dubai gown me rangeamen nauyi da sassauqan ado me daukan hankali,cotton ce me yankakken hannu da ya tsaya iya damtsenta,sai siririn mayafinta data maidashi tamkar dankwali ta yane sassalkan gashinta dake zube gadon bayanta ba tare data daureshi da komai ba. Cikin jikinta sam babu qwari,tana jin kamar iska zata iya dibanta ta kayas da ita,hakan kuwa ta sani baya rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk da dama can ita din ba ma'abociyar cin abincin bace. Ta samu huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban. Goshinta ta dafe tana zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma bahijja na magana da qannen mahaifiyarta da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa jibi gobe kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a. "A zuba miki adda?" Huda ta tambayeta cike da fatan ta amsa cewa zataci din. Hannuwan huda da sukasha lalle tabi da kallo. Ko nata hannuwan farare suke sidik da zara zaran yatsunta dake dauke da dan baqin lalle dan kadan saman farcenta,ragowar lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu baya da suka shude. "Zuba......amma kada kisa miya.....mai zaki saka da dan maggi kadan" Ta yiwa huda bayani a taqaice tana zare idanunta daga sashen da suke. Sauka idonta yayi kan wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta ma don batajin zuwa yanzu tana da wani uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran mutanen da takejin sun Ta'allaqa a wuyanta kadai zuciyarta ke mata amsa kuwwar ta nemesu.......tayi sallama da kowannensu.....saidai kuma wani sashen daban yana bata qwarin gwiwar bata da buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani gajeran balaguro ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da bai wuce misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata cewa wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu.....kwadin me kwadayi......burin me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta.....sannan ne ita kuma zata aiwatar da nata shirin hankali kwance( nikam nace uhmmm....qaddara dai ta rigayi fata🥺😊). Da plate huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen tasan duka tayi ne don taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan ta mata roban yaji da magi daban. Da kallo kawai tabi plate din,don tasan yafi qarfinta koda duniya ma tana kwance bare yanzu da wani abu waishi abinci baya burgeta. Sallamar kawu rufa'i da sautin muryarsa kadai ya sanya abincin data sanya a bakinta ya tsaya mata cak a maqogaronta,sauran na bakinta kuma taste dinsa ya canza mata,har tana jin ba zata iya taunawashi ba,har sai data tattara dukkan juriyarta sannan ta tauna ta turashi zuwa maqogaronta wanda ta samu ya wuce da qyar,sai kawai ta yanke hukuncin ajiye abincin. Idanunta ya sauka kan kawun sanda take ajiye plate din a qasa,wanda yake jaye da wata mini luxury luggage me azabar kyau da kuma daukan idanu. Koda bakasan me duniya ke ciki ba,koda bakasan darajar abinda yake janye dashi ba tabbas zata fahimci luggage ne me tsada da madaukakiyar daraja. Wajen zama mamma bahijja tayi masa tana sanya nadra ta ajiye masa drink da ruwa. "Ya hidima ya kuma shirye shirye?" Kawun ya furta da muryar dake nuni da zallar farincikin da yake ciki "Alhamdulillah.......ai kune da hidima,tunda mu nan ba abinda zamuyi" Kai kawu rufa'i ya girgiza yana satar kallon sabreen da tunda ta gaidashi bata sake koda kallon sashen da yake ba. "Allah ya yiwa yarinyar nan taurin kai bahijja......idan kinga abubuwan da sukaso gabatarwa zakisha mamaki......har yanzu quruciya ke dawainiya da ita,inda tasan girman matsayi da darajar mutumin da zata aura,na rantse miki saita qare rayuwarta tana godemin.....attajirin matashin da babu irinsa a wannan qarnin da muke ciki?" Dan murmushi kasan momma bahijja tayi,adan zamanta ta fahimci kawun yana sa son abun duniya "Duk bama wannan ba rufa'i,indai har bincikenku ya tabbatar da nagartarsa ai magana ta qare.....dukiya wannan wani abune na daban ai" "Habawa.....idan ana batun nagarta ma da dattako har ayi magana wadannan dattijan?" "To alhamdulillah.....haka akeson ji...." "Yanzu haka ma aike ne......saqo ne na musamman daga surukarta......kaya ne tace a kawo mata da zata sanya a gobe kenan" "Tofa.....ikon Allah,kuma dai?,basa gajiya?"Momma bahijja ta fada duba da irin kudaden da aka narkar,tun daga dukiyar aure har izuwa batun lefen dasu kansu har yanzu basu gama sanin komai da komai dake cikin akwatunan ba. Tana qara ganin girman qaunar da suke gwadawa sabreen din,a gefe guda har ranta tana jin tamkar sabreen din tayi sa'ar inda zata rayu cikin qauna da kulawa. "Wai wai.....ma sha Allah" Momma bahijja ta furta tana daga lafiyayyen applique lace da kudi suka koka qwarai wajen siyensa. Daga qasanshi kuma wata bazin ce data amsa sunanta sai super Sheraton da iya ado da gayu da kashema kai kudi irin na momma bahijja bata taba katarin ganin irinta ba. Daga qarshe set ne na banguls earrings da sarqa da zobensu duka na danyen gold me matuqar daraja(nikam nace masu abu da abinsu). Ko qwaqwqqwaran motsi sabreen batayi ba ballanta ta daga kanta ko zata nuna alamun tasan bidirin da akeyi,har sanda hadiyya tayi sallama tana shigowa falon da guntuwar fara'arta. Sunan kayan kawai ya gaya mata darajar abinda aka sako a ciki saidai hakan bai dadata da qasa harta daga kai ta basu darajar kallo ba,don batajin zata iya rabasu a jikinta. Komai daya fito daga hannunsu duhu yake mata,baya mata haske ko kadan.....musamman da take kyautata zaton kayan sun fito ne daga hannun waccar matar maras daraja. Still shigowar hadiyya bata sakata daga kai ta dubeta. Can qarshen zuciyarta danqare da mamaki,yadda kudi ke iya sauya dabi'un mutanen duniya cikin qanqanin lokaci,duk da wannan karatun ta jima da haddaceshi......kusan shi ya zama sila na sauyawar DUNIYARTA. Hadiyyan ta sauya kamar ba ita ba,abinda bata taba tsammanin zaya faru nan kusa ba. Bata zaqe da yawa ba wanda tasa tasirin karatu ne wala'alla da salon gogewa......hakanan kowanne taku kadan tana yunqurin kutsa kai jikinsu ne. Hadiyya ita ta qarasa daga kayan matsanancin mamaki yana sake kasheta. Hidima sosai suke gwadawa sabreen din kaman rijiyar kudi garesu. Ba wanda yakai me kudi sanin darajar kudi,saidai ga wadannan bataga alamun hakan sam daga garesu ba. "Gashi zakiyi magana da surukarki" Momma bahijja ta fada tana sauke wayarta daga kunne gami da miqawa sabreen. Dan turus tayi tana sauke fararen idanunta akan fuskar momma bahijja din. Muddin wannan matar ce sam bata da sha'awar wata magana da ita. Komai nata bisa gadara ne iko izza da kuma nuna qarfin dukiya,don me zata zauna tana gwada mata tata izzar bayan ba ita ta gayyaceta cikin rayuwarta ba. Idanu sunyi yawa a kanta,don haka ta sanya hannu ta karba tana kauda fuskarta daga kallon idanuwan. Sallamarta kadai ya gaya mata ba wadda take zato bace,cikakkiyar sallamar data saukar da duk wani zafi da zuciya da kuma halshenta suka dauka,saita amsa mata a nutse matuqa "Kina yini lafiya diyata?" Anni ta fada daga nata bangaren jin sabreen din tayi shuru. Karon farko sai taji nauyin matar ya saukar mata,batasan me yasa a iya waya kawai takejin girma da kwarjininta ba......shin itace asalin mahaifiyarsa ko yaya?.....itadin wacece a wajensa?,waccan ma wacece a wajensa?. Iya wannan tambayoyin da bata da amsa kadai suna sakata a jikinta tana jin tabbas akwai wani gagarumin abu birne a qasa.....duk da zuciyarta tana gaya mata ba wani babban abu bane da zai gagari sarrafawarta ba. "Barka da yamma.....lafiya alhamdulillah" Ta hade gaisuwar da amsar tambayarta. "Ma sha Allah" "Naga saqo,na gode" Tayi hanzarin fada,don a cikin ranta takejin bai kyautu ba har sai ta magantu. "Ba komai......inaso ne kawai kiyimin alfarmar sanyasu a duk sanda zaki shigo ahalinmu" Tayi maganar a tausashe cikin kuma nuna kulawa,kulawar data bayyana kanta sosai cikin sautin muryarta "In sha Allah" Ta sake amsa mata "Ina fatan hakan ba takura?" "Ba komai....in sha Allah" "To alhamdulillah......ina roqon ubangiji ya tattara dukkan alkhairanku ga junanku......ya kauda kowacce irin fitina da abunqi a tsakaninku". Batasan me yasa ma......amma har tsakiyar qirjinta taji saukar addu'ar......batayi kuskure ba idan tace kunnuwanta itace mutum ta farko data fara jin addu'ar daga bakinta,sai taji labbanta sunyi nauyi bare su tallafeta ta amsa.....yayin da anni tayi zaton kunya da kawaici suka hanata amsawar......a haka tace ya baiwa momma din wayar. Zuciyarta tayi nisa qwarai da zurfi wajen tunani,har batajin ma meke wakana cikin falon,sai kawai ta yanke nesanta kanta dasu ta hanyar komawa daki kaman yadda ta maida hakan dabi'arta. Bata jima cikin duniyar dakin data maida mazauninta ha nadra ta shigo dauke da wayarta a hannu. "Ana kiranki" Ta fada tana miqa mata wayar. Kamar tace mata ta koma da ita sai ta fasa,ta saka hannu ta karba tana daga kwancen tana duba me kiran. Sunan data gani ya sanyata miqewa ta zauna sosai babu shiri,hannunta na gaggawa wajen amsa kiran ta sakashi a kunnenta "Kicemin kun dawo titi don Allah,kicemin ayshatu ta warke" "Na warke adda......na samu sauqi" Muryar yarinyar ya saukar mata a kunne. Wani hawaye me sanyi ne ya kubce mata,kullum da lamarin yarinyar take kwana take kuma tashi,daga yadda taji muryarta tasan cewa tabbas lafiya cikakkiya ta samu a gareta "Muna cikin sabon gidanmu yanzu aunty.....na gayawa titi bazan yarda na fara ganin kowa ba sai ke". "Yanzu kuwa zaki ganni ayshatu" Ta bata amsa kai tsaye kaman ta manta a wanne yanayi ita din take.....kaman ta manta rabonta da taka qasar waje wasu kwanaki ne masu yawa. Da wani irin excitement ta ajiye wayar,ta zura qafafunta qasan gadon da hanzari zara miqe da nufin shiryawa,sai kuma ta dakata cak saboda dawowa hayyacinta da tayi. Tayi imanin wadannan mutum mutumin har yanzu suna tsaye a qofar gidansu suna gadinta,yawan mutanen dake kai kawo a gidan bai sanyasu sun tafi ba......don ko dazu ita iya jiyo baqin tsagin abbansu suna tambaya a kansu. "Saina fita kota halin qaqa wannan karon......ko meye zai faru saidai ya faru" Ta fadi tana qarasa saukowa,ta kuma fito kai tsaye zuwa ga falon tana nufar doguwar veranda din dake saman wanda tacan zata samu hanyar gangarawa qasa ta koma ainihin dakinsu. _DUNIYA TA na kudi ne_ 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 6 Page 06 Batasan gidan ya fara daukan mutane ba sam sai data sauko din. Gomayyar idanuwa sukayi kanta caaa ana qare mata kallo. Kowa da nashi tunanin cikin ranshi,wasu na kallon tsantsra kyan data qara saboda gyaran jiki na musamman data samu tsahon kwanaki daga wajen qaararriyar me gyaran jiki......wasu kuma na mata kallon sha'awa suna fadin inama su ko 'ya'yansu keda wannan sa'ar ta auren irin mijinta?,yayin da wasu nasu kallon na bin qwaqwafi ne hassada da tarin tambayoyin ta yaya KARUWAR GIDA.....WADDA TA GAMA RABA MUTUNCINTA WA MAZAN TITI TA SAMU BABBAN MUTUM.IRIN MUHAMMAD JADDA DIN?. Miskilanci da shariya kusan cikin jininta suke,don haka tayi kaman bata gansu ba ta wuce dakinsu kai tsaye.....ballantana kusan dukansu tana cike dasu. Ba wanda yabi takan rayuwarsu.....qaqa suka kwanta qaqa zasu tashi?,amma sai gasu yanzu zube da sunan sunzo auren yarinyar da basusan yaya ta girma ba?,me taci har takai wadannan shekarun?. A gaggauce ta shirya cikin wata luxury Egyptian abaya datayi masifar karbarta,wadda inda cikin nutsuwarta da hayyacinta take itama ya kamata ace taga yadda rigar ta karbeta. Tun daga nesa kana iya ganin mugun kyan da fatarta tayi,wani irin haske da glowing kawai takeyi,saika rantse da Allah diyar wani hamshaqin ce. Qaramar handbag kawai ta dauka ta jefa wayarta a ciki da dan canjin da zata riqa saboda mota,ta fito daga dakin a nutse tana isowa falon,daidai sannan momma bahijja ta shigo rungume da dinkakkun atamfofin da tasa aka dinkawa su haneefa duk da tarin suturunsu. "Ina zuwa kuma?" Momma din ta jefa mata tambayar tana kallon yadda take komai a gaggauce. Batasan da wanne harshe zata yiwa momma bayanin aysha da muhimmancinta a wajen ta,don haka a taqaice tace "Dubiya zani momma...." "Zuwa ina?.....kuma dubiya a irin wannan lokacin?" Kai ta langabe kadan tana fargabar kada momma din ta hanata fita,don a irin wannan lokacin ita kadai takejin zata hanata fitar ta hanu "Ba niss momma.....ba jimawa zanyi ba". "Nadra ta rakaki,kuma kada ki wuce awa daya" Ta fada tana qarasawa tana zube dinkunan hannun nata saman kujera. Mayafi kawai ta figowa nadra,ta sanya wasu plate shoe nata sannan suka fito. Sam bata damu da yadda idanuwa keci gaba da binta da kallo ba,har wasu na qoqarin gaisawa da ita,a haka ta doshi qofar gidan nasu tana tsara yadda zata kaya tsakaninta da qedarun da aka tsaida a qofar gidan. Tana takawa zuwa qofan tana jin fargabar yau dame zasu zo mata?,don dai yadda takeji a ranta yau koda sama da qasa zasu hade sai ta fita.......don ba wani mahaluqi daya taba saka mata dokar zama cikin gida har haka tsahon rayuwarta......sai yau gashi sama ta ka wani mutum can da baisan ciwonta ko darajarta ba......yanason yayi amfani da giyar kudi ya yiwa rayuwar karan tsaye. Tana tura qofar yana riqeta kana aka qarasa budeta. Fuskar kakkauran mutumin ta bayyana har abun yana bawa sabreen mamaki. Bata taba kawowa a lokacin irin wannan zata sameshi tsaye bakin qofar ba kamar wanda aka tsaiguntawa zata fita......waisu basa zama?,ko basa hutawa da jiddin suna tsaye suna gadin duk wani motsinta. "Good evening madam" Abdulgaffar ya furta cikin matuqar girmamawar nan da suka saba mata magana da ita saidai kuma a dabarance yana matse kowacce hanya da zata iya rabawa ta fice daga gidan. Ta gama karantar motsinsa kaf.......bata wani damu da gaisuwarsa ba ta azawa fuskarta wani irin halakakken bacin rai da kuma d'aurewa "Kiramin boss dinku" Ta bashi umarni nakai tsaye da wani irin sauti da babu wasa ko kadan a ciki. Tanaso ta gwada musu girman abinda zata iya aikatawa.......tanaso ta gwada musu basu ba......koda boss dinsu ma bata daukeshi da wani tarin muhimmanci ba. "Bani da connection dashi......idan zan kirashi saina jira anyimin iso kafin na samu magana dashi......amma ga jordan zai kira miki shi" Abdulgaffar yayi mata bayanin cikin girmamawa yana matsawa da baya. Can qasan ranta mamaki yake kamata,wanne irin girman mulki da izzar kudi gareshi da har yaransa ma ba kowa da kowa keda daman magana kai tsaye dashi ba "Good evening madam.......kiyi haquri ki jira kadan,yanzu in sha Allah zai amsa" Jordan ya fada yana rusuna mata. A ranta tanaso ta gaya musu ne a fili "Qattin banza.....kun zauna kuna yiwa mutum qwaya daya bauta saboda yana da dukiya" Abinda zataso gaya musu kenan ganin yadda jordan ke lalubar muhammad fuad jadda cikin girmamawa. A lokacin yana tsaka da hada duk wasu muhimman abubuwa nashi da kanshi,ba tare da ya bari hidiminsa ya masa ba wato me sunan malam. Akwai wasu abubuwan da da kanshi yake yinsu,duk da tarin hadiman dake gareshi. Yana sanye da fara qal din t.shirt me laushi Vshape neck,hannunta iya dantsensa wanda hakan ya sanya murdaddun damtsensa dake nuna girman daga qarfe da yakeyi suka bayyana,wandon jikinsa ma farinne duka duka tsahonsa iya qaurinsa,sai lausasan fararen flip-flops masu tsananin haske da taushi. Cikin kowanne irin yanayi tsarinsa na dabanne,kai tsaye zaka iya cewa gayu ya ratsa jikinsa da gasken gaske.....koda kuwa bacci zai shiga zaka sameshi neat....komai nashi kuma completed kai kace ba bacci zai kwanta ba. Yadda yake a nutse cikin wani irin tsari haka komai nashi yake kasancewa,waya.yake amsawa wadda ya sakata a hands free ya ajiye saman wani zagayayyen kujera me siffar qwallo dake a gefe. Kadan ya kalli wayar,sai ya fahimci kiran jordan keson shigowa amma yana buqatar izinin haka,don haka ya katse wancan kiran ya bawa kira jordan din dama "Barka da wannan lokaci sir" Jordan yayi maganar cikin girmamawan data bata ran sabreen,ta cika fal da mamakin wanne irin ban girma ne haka kaman yana a gabansa?,ya kasa miqewa da dukka tsahonsa ya amsa wayar. "Yauwa Jordan......ya akayi?" Ya tambayeshi kai tsaye. Sai daya dan daga idanu ya kalli sabreen din da idanunta ke cike tab da fushi,sannan qasa qasa yace "Madam daka tura a yiwa aiki ce keson magana dakai sir" "Madam?" Ya tambaya yanason tuna abun don ba komai yake baiwa muhimmanci ba "Eh sir....." "Bata wayar" Ya umarceshi kai tsaye don ya tuna inda zancan ya dosa. "Ka matsa a wajen idan ka bata" Ya sake fadiwa jordan don bayason yayi involving yaransa cikin abinda bai shafesu ba.....hakanan yana ganin ba girmansa bane su fahimci komai ba. Kaman ba zata karba wayar ba don tana jin kamar ta zuba a qasa data nema magana dashi......saidai kuma girma da martabar inda zataje din ya shafe komai a idanunta,don haka ta sanya nadra ta karbo wayar daga hannunsa sannan ta karba a hannun nadra din,ta taka a nutse tana dan komawa ciki duk da jordan ya matsa daga inda zai iya jinta. A kunnenta ta kara wayar,saidai har kusan shudewar mintuna guda tim ba wanda ya cewa da dan uwansa komai. 𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀 𝐓𝐀 𝘓𝘪𝘵𝘵𝘢𝘧𝘪𝘯 𝘬𝘶𝘥𝘪 𝘯𝘦 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 7 Tana tsananin buqatar ta fita,ta kumayi imanin wadannan gumakan ba wanda zai musu magana suji sai wanda ya turosu.....tana jin kuma faduwar fara yin magana dashi. Sanda taji ya motsa da bisa alamun ajiye kiran zaiyi,a nutse ta bude baki ta soma magana dashi da qaramar muryar nan tata me wani irin tone "Ban kasance daya daya daga cikin hajojin kamfaninka ba ballantana ka sanya min masu tsaro na......'yantacciyar d'iya ce kamar kowa,hakanan mutum ce dake da nata tsarin da qa'idojin da ba komai take jurewa ba......ka yiwa wadannan gumakan magana da suyi gaggawar matsawa subar qofar gidanmu". Tsayawa yayi cak da abinda yakeyi,ya harde hannayensa a qirji yana sauraronta da muryar dake nuna tamkar gargadinsa kawai takeyi kai tsaye. Idanunsa ya lumshe kai tsaye na sakanni sannan ya budesu,yana ci gaba da jin qaramin sautinta dake magana cikin yanayi na tsiwa har sai data qarasa maganarta. "Bakisan waye ni ba.....i can't tolerate it,dole ki koyi manners......bawai na zama dani kawai ba,manners akan komai ma,tabbas kina buqatar tarbiyya,Your attitude needs a serious adjustment.....and im not going to put up with anymore nonsense,I won't tolerate any more of your nonsense,its time to get in line" Yayi furucin harshly muryarsa cike da seriousness. Din din din da taji wayar nayi shi ya tabbatar ya yanke kiran. Ta sauke wayar daga kunnenta tana jin wani irin daci yana taso masa tun daga cikin maqogoranta har zuwa saman harshenta. Tabi wayar da kallo ranta yana mugun baci,tana jin maganganun daya gasa mata suna yawo cikin kunnuwanta. Tana jin kamar tayi cilli da wayar ko zata samu sauqin radadin dake cisgar zuciyarta......to amma saita tuna idan tayi hakan bata kyautawa ainihin me wayar ba,wanda shima da alama komai nasa yana yine bisa tsoro da kyakkyawan bin umarni ba tare da sabawa ba. "Kai mishi wayarsa" Tace da nadra tana miqa mata wayar,sannan ta miqe tana gyara jakarta tabi bayan nadra zuwa qofar gidan,tana jin yau saita nuna masa iyakarsa ta hanyar fita,idan yaso ya tashi duniyar a yau kowa ya huta. Nadra ta rigata isa,ta bashi wayar dake ringing,yana duba me kiran yayi hanzarin dagawa tare da matuqar rusunawa yana fadin "Hello sir" Idanunshi suna sauka kan sabreen,sai ya miqe yana sauraron umarni daga wayar yana kuma kallon sabreen wadda ke tafiya cikin tsananin fushi,har kuma ta samu nasarar sanya qafafunta a qofar gidan. "......idan naga sabanin haka ka kuka da kanka" Qarshen maganarsa kenan data jawo hankalinsa zuwa ga sabreen wadda ta dauki hanyar barin layin sosai bata tsaya koda waiwayarsa ba ballantana wayarsa da yakeyi,tana jin bata da lokacinsu gaba dayansu. Da sassarfa abdulgafar ya jefa wayar a aljihunsa ya juya da sassarfa yabi bayanta. Daga yadda yau boss din ya masa magana ya tabbatar akwai magana a qasa. He's speaking seriously,yasan abinda ya fada da gaske yake. "Madam.....ah.....am,madam sorry......listen please" Ya furta bayan ya cimma bayanta. Nuna ma tasan yana biye da ita a wajenta bata lokaci ne,bata da lokacin batawa ta saurareshi daga shi har boss din nasa "Madam please ki tsaya ki saurareni,am going to loose my job.....please listen to me". Maganar ya taba mata zuciya........yanzun nar rashin imaninsa yakai ace ya kori mutum bakin aikinsa saboda wani abu daban ya faru?. Daga yadda yake maganan kawai ya gaya mata da gaske yake fadi,don haka tadan sassauta tafiyar ba tare data kalleshi ba tace "Ina jinka" "Please madam ki koma gida.....kiyi haquri ba yadda muka iya.....haka boss ya tsara......" "Wannan kuma bazai yiwu ba,idan baka da abun fada ka koma yafi maka sauqi" Daga hakan taci gaba da tafiyanta. A nutse take ratsa layin,yayin da idanun 'yan sanya ido ya soma yin caa a kanta. Ba yadda zaka kalleta ita da abdulgaffar din kace ba body guard dinta bane,saboda yake take mata baya yana maida takunsa duk inda ta dauke ba tare da sunsan abinda ya sanya ya biyota ba,take tsegungumi suka fara tashi,masu rade radi akan irin mijin da zata aura a yau suka samu tabbacin hakan Da alama zazzafa ce itama tamkar boss din nasu,ya hanga ya hango babu wani sauran abinda ya rage masa illa ya kira oga farouq,don haka yana biye da itan yayi kiransa,yayi kuma bayani a taqaice. "Turawa hood location ta watsapp...zaizo da mota ya kaita.....idan yazo din give me a call.....zanyi magana da ita" Yayi maganar haushin fu'ad yana kamashi. A ganinsa tunda batu ake na aure koma meye ya kamata ya ajiyeshi a gefe,batun aure ya wuce wasa.....ya kuma wuce tunanin mutum. Wani irin aiki ne da ake yinsa da umarni da kuma doka. Iya tsaiwar da tayi tana jiran ababen hawan da batasan dalilin da yasa duk wanda ta tsaida sai ya wuce ba.....wanda qwarewar aiki irin na abdulgaffar ya sanya yake musu alama me nuna gargadi kan tsaiwar tasu,take suke wucewa abinsu. A hankali motar ta rage gudu tana qarasowa gabansu,wanda tun kafin takai ga qarasowar abdulgaffar ya ganeta. Motocin da dukka suka jibanci familyn muhammad jadda da kuma gidan alhj hamza kibiya ba boyayyu bane,don hatta da plate number dinsu na dabanne da wani irin kebantaccen tsari na daban. Bai bari motar ta qaraso gabansu ba ya kirayi farouq din,sai komai yazo a daidai,isowar motar gabansu da kuma matsawa da yayi daura da ita ya saka wayar a handfree yadda idanunta zasu iya ganin wayar "Ranki ya dade......Allah ya taimakeki,tuba muke,kunyi magana da boss yana cikin fushi ne.......ayi mana alfarma kiyi haquri,ga driver da mota nan ya iso,ki shiga ya kaiki duk inda kikeso,tuba muke,tuba muke" Ya maimaita har sau biyu yana hade tafukan hannayensa guri daya. Batasan me ysaa ba,amma sai taji tasss ta sauka daga fushin da takeji. Yanayin maganarsu dama komai nasu ba daya bane,batasan kuma waye ba......sannan batasan nasabarsa dashi ba.....amma da iya lafuzan bakinsa kadai ta tabbatarwa kanta yasha banban dashi tako ina. Batace komai ba ta soma takawa tana nufar motar da tuntuni suka wagale mata qofar suna tsaye suna jiran isowarta,tadan dubi security din kadan ta kauda kai tana tabe baki. Su kuma a haka rayuwarsu zata qare?,basa da aiki sai ta'ammali da murda murdan garadan da babu rahama akan fuskarsu?,idan kuma suna tsaye sai kace gumaka?,wacce irin rayuwa zata shiga ne?. Da wannan tambayar ta shiga cikin motar suka maida murfin suka rufe. Duk da yadda ranta yake a bade,zuciyar kuma bata tare da komai amma hakan bai hanata fahimtar banbancin inda ta shigo ba. A hankali ta kalli wani sashe na motar,cikin ranta tana jin zallar tsagwaron banbanci. Batayi kuskure ba idan tace tsahon rayuwarta bata taba tsammanin da gaske akwai mota irin wannan a nigeriar mu ba,cikin motar bai mata kama da komai ba saida wani qawataccen madaidaicin falo na alfarma,idan ba yaye labulen window din kayi ba zata ko dan jirin motsin motar kadan ba saika tsammaci cikin wani killataccen falon kake. Taja numfashi a boye tana saukeshi,duk da ita kadaice a nan amma saita killace ganinta. Bangare daya zuciyarta tana bugawa da samun tabbacin lallai da gasken da kawun ke fada su din ba qananun mutane bane......amma ta yaya suke bibiyan rayuwarta?,me yasa sai ita?,me suke tunanin tana dashi wanda zata iya basu?. Amsar dai kamar kowane lokaci.....hasashen kaman na kowanne lokaci shine AKWAI WANI ABU A QASA. Da wani irin makirin narkakken murmushi ta maida murfin qawataccen akwatin ta rufe bayan ta gama ganin suturar alfarmar da aka tsumata da wasu tsatsube tsatsube na musamman da suke a mazaunin matakin farko na fara tunkarar shirin data yiwa rayuwar mutum biyun.......sanadin wato sabreen.....da kuma maqasudin wato muhammad fu'ad. "Komai yayi hajja........suturar million biyu kam baa kashe kudinsu a banza ba.......yanzu zuwaira za'a aika?.....inajin kamar nayi tattaki naje nakai Mata da kaina,don inaso ta fahimci muhimmancin sanya suturar nan" Tayi zancan da wani irin muhimmanci cikin sautinta,tana tuna bayanan bokan da bata dana biyunsa a yanzu haka _".......tana sata a jikinta ta fara zuwa hannu fa hajja......hakanan shi Kansa fu'ad kallon farko da zaiyi mata da suturar zai jarabtu da sonta,abinda zai bada damar gudanar da aikinmu cikin sauqi,zai karbi komai daga hannunta yaci ya kuma sha ba tare da wani matsala ko tangarda ba"_ Murmushi hajja ta saki tana dora qafarta daya saman daya "Tafiyar zuwaira ita daya yana nuna aiken bame daraja bane,hakanan zuwanki da kanki zai jefa shakku a idanun mutanen da hankulansu ke kanmu irin aminatu hamza kibiya......wannan saqon babbar aminiya kuma amintacciya ya kamata ta isar dashi" Murmushi me sauti ya qwacewa maamah,ta bawa hajja hannu suka tafa tana fadin "Allah yabar mutum da nasa.......bari na yiwa usama magana" Ta fadi tana dauko wayarta dake ajiye gefe ta fara lalubar number wayar usaman. Zuwanta wajen aysha da dawowarta....farincikin data samu na ganin yarinyar ta dawo cikin cikakken hayyacinta da wata lafiya data sanya kumatunta cikowa shine ya haifar da sakewar fuskarta,ya kuma saka mata farincikin da ta kusa mantawa da abinda ke tunkararta a gobe. Kallon masu kallo da idanun masu sanya idanu tun daga qofar gidansu da lafiyayyar motar ta ajiyeta bai dadata da qasa ba,har zuwa sanda ta isa tsakar gidan,ta kama matakala tana haurawa zuwa saman nasu. Tana sanya qafarta sukayi kacibus da momma dauke da tray da lemuka da ruwa akai. "Yauwa yanzu nake shirin kiranki......kina da baqi suna qasa,ki hanzarta ki samesu" Ta gaya mata tana rabata zata wuce "Baqu momma?,su waye?,daga ina kuma?" "Kinga duka wadannan tambayoyin ki adanasu idan kinje kyayi musu.....me lalle ma ke take jira tunda kika fita". Ambaton sunan me lalle saiya fara dagula mata lisssafi,bayan dirje fatar da aka dameta dashi na kwanaki kusan goma yanzu kuma wani me lalle ne na daban zata zauna yi?,salon a bata mata hannu da qafar da bata shirya diga musu komai ba?. Ganin momma tayi gaba har tana gangarawa qasan stairs din ya sakata itama ta laqume dukka tambayoyinta tana wucewa ciki. Zuciyarta fal da saqe saqe ta sauya abayar jikinta zuwa wata sassauqar doguwar Riga cotton me gajeran hannu data zauna daidai jikinta,ta dauki qaramin hijab daya tsaya mata iya kafadu ta maqala ta juyo tana saukowa. Dukkansu su biyun suka amsa mata sallamar idanunsu a kanta "Tubarkalla ma sha Allah" Zuwaira da tayo rakiya ta qarfi da yaji don ba haka Hajja taso ba ta furta kyan sabreen yana bugar da ita. Duk yadda take jin hira da yadda aka tsara komai bata taba kawowa kyan yarinyar yakai haka ba,ta dauka maamah din nada tsananin wayo......zata dauko yarinyar da bata da cikakken siffa gudun juyewar reshe da mujiya. A iya sanin data yiwa halittar 'ya'ya maza masu jarabtuwa da kyakkyawar mace komai kamewarsu kuwa. Sanda suka iso gidan batayi tunanin gidan masu matsakaicin qarfi da gata irin wannan yana qunshe da kyakkyawar sura har haka ba,taci gaba da qare mata kallo yadda shape me qirar Coca-Cola ya fita sosai ta cikin rigar ta wajen qugunta. Duk kallon da zuwaira ke qare mata hankalinta baikai ba,saboda hankalinta daya tafi akan hajja da suka fara hada idanu. Ta yaya zata manta fuskar matar?,bayan tana a wajen sanda sukazo da tallar qazamtacciyar hajarsu?,kuma kusan itace tafinta a wajen matar dake iqirarin mahaifiya take a wajensa. Yadda sabreen din ta tsareta da idanu tana zama a dosane a hannun kujera irin yadda takeyi idan zuwan mutum magana ko mu'amala dashi baiyi mata ba "Sannu ko?" Hajja ta fada tana qaqaro murmushin dole. Wani irin kishi me girma ya sauko mata akan Sabreen din. A haduwarsu da suka taba yi qwaya biyu hankalinta bai taba kaiwa kan sassanyan kyan da yarinyar ke dashi ba. Wani irin halakakken kyau dake boye a kowanne sashe da kuma halittarta. Anya wannan ba kuskure bane?,idan har tayi saken daya fadawa sonta rabasu kuwa zai zama abu me sauqi kuwa?. Tabbas bata taba kula da wannan kyan ba,wanda inda tasan dashi tana da dukkan makaman da zata rusa tafiyar........a yanzu bayan komai yayi nisa ta yaya zata katse wannan wasan da bata taba ganin abinda maamah ta ciwa buri a kansa har haka ba. "Yauwa sannu" Sabreen ta maida mata da salon yadda tace da ita. Haka kawai taji ba zata iya gaida matar ba,tun a waccar ranar duk wata kima martaba da kuma mutunci da ake ganin dan adam me girma da shekaru nasu duka su biyun suka kwaranye mata. "Ya gida ya shirye shirye?" Hajjan ta sake dauriyar fada yadda sabreen din ke shan qamshi yana qara qona mata rai,amma duka wannan ba komai bane......tasan s nan kusa zata fahimci wace ita?kuma su waye su. "Alhamdulillah" Ta sake amsa musu. Kai tsaye hajja ta gabatar da abinda ya kawosun,da dukkan alamu sun nuna ba'a maraba dasu ata nan din "Saqone daga mamarki" Hajja ta fadi tana turawa zuwaira akwatin,ita kuma tana sadar dashi xuwa ga sabreen dake binsu da idanu. 𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐓𝐀 𝘭𝘪𝘵𝘵𝘢𝘧𝘪𝘯 𝘬𝘶𝘥𝘪 𝘯𝘦 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 8 Page 8 Duniya ta Sai data qarewa akwatin me ruwan gold kallo,sannan a nutse ta aza kallonta akan hajja,don tayi yaqinin itace jagorar tafiyar kamar wancan karon. Kallon kallo ne dake nufin ina buqatar qarin bayani. Da yake hajja din 'yar gari ce har ta fahimci ma'anar kallon,ta saki wani qaramin murmushi sannan tace "Kusan duk inda akace ana arziqi tsiya guduwa takeyi.....lallai ba shakka kina cikin matan da sukazo duniya a sa'a da har tarihi zai baki daman kasancewa matar muhammad jadda.......wannan suturan ta lashe miliyoyin kudi.....kuma an tanadeta ne kawai saboda ki sanayata a ranar da za'a miqa ki zuwa gidan fuad,wannan shine burin uwar mijinki da kuma umarni na farko da takeso ki fara dauka cikin tafiyar ku......lallai ne muddin kika kasance me biyayya ina miki busharar keda sunan talauci kinyi adabo.... Aiki ne na qididdgaggun watanni,amma ribarsa zaki ci gaba da cin gajiyarta har qarshen rayuwarki data zuri'arki". Idanu ta lumshe a nutse sannan ta budesu. Tana jin wani murmushi yana taso mata daga qasan zuciyarta amma kuma batason bayyanarwa hajja dashi. Shin sun dauka ita din wawiya ce da har zata aminta da komai daya fito daga garesu?,sunyi tsammanin shirunta galaba ce a tare dasu?,ko sauraro da dakonta a kansu suna tsammanin alkhairi ne?. Zamowa tayi a nutse daga saman kujerar ta zauna a gabansu gaba daya tana langwashe qafarta. Idanunta tsakiyar na hajja ta soma magana da nutsuwar nan tata dake qarawa maganarta kwarjini da fahimta a muryar me sauraro "Ina zaton aikin data nema daga gareni zaya tsaya ne kawai iya kan danta.......aiki kawai tace zanyi mata na wata uku ko hudu......bata da hurumin komai cikin rayuwata.....kama daga cima ko sutura......" Ta tsaya iya haka tana maida numfashin bacin rai. Ranta ya fara dugunxuma na ganin yadda suke qoqarin maida rayuwarta tamkar gare gare tsakanin uwa da d'anta da suka zamo tsatso daya......abinda sam ba zata lamunta ba kenan,ita tayi mata......danta ma yayi mata?,shin ummeeenta su ta haifawa su?. A mamakance hajja ke binta da kallo,bata taba zaton haka daga gareta ba,kallon hajjan ya isheta hakanan,dom haka ta miqe cikin rashin damuwa tana gyara lullubin kanta tace da ita "Ki gaya mata damuwarta ta tsaya iya kan aikinta kawai......indai tace zata hada da shigar da rayuwar sabreen......komai bazai tafi yadda take tunani ba.....ni din tamkar wahainiya nake a wasu lokutan.....sawun keke da gane gabansa yake da wahala koda a wajen gwanaye". *MAAMAH* Idanunta ta runtse bayan hajja ta jera mata dukkan wadannan bayanan da sabreen ta aiko mata dasu ba tare data rage komai a ciki ba.....koda ta manta wani abun zuwaira dake gefe tana taso mata dashi. Ta bude idanunta cikin bacin rai tana duban akwatin da iya shi daya kawai kudi ta zuba masu yawa,banda kayan banda kuma aikin da akayi akan kayan. "Yarinya ce qarama tabbas.....amma na yarda da gaske tana da hadari........tana kuma da wasu boyayyun abubuwan da bamusan dasu ba......iya kalmominta na yau sun sake zaburar dani akan dole na ninka shirina a kanta......amma ba wannan ba.......asarar data sani nayi tun a matakin farko yafi damu na....." "Kada ki damu.......akwai mataki na biyu da nayi imanin ba zata tsallakeshi ba......saidai shi na biyun bangare daya ya qunsa.......bangaren cusa soyayyarta a zuciyar fuad ya saraya,saidai a samo masa wata hanyar ta daban". Ajiyar zuciya maamah ta saki tana jin sassaucin tashin hankalin dake sauko mata "Wannan dinma wahalar da nayi a kansa bazai tafi a banza ba.....koda bataso sai tayi amfani dasu,ta hanyar da takeso ko ta hanyar da bataso bata kuma shirya mata ba". Daga haka ta jawo akwatin ta cusashi qasan lafiyayyen gadonta. 𝙈𝘼𝙁𝘼𝙍𝙄𝙉 𝙏𝘼𝙁𝙄𝙔𝘼𝙍...... 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 Tamkar jira akeyi su kammala sauka daga jirgin,wayarsa dake riqe hannun daya daga cikin guard dinsa da tun tafiyar zuwa yanzu shike da alhakin riqe masa ire iren wadannan kayan nasa. "Sir.....oga farouq" Ya sake matsowa kadan bayan fuad yana fadi cikin rusunawa. Baice komai ba ya miqa masa hannun shi kuma ya dora masa wayar,ya dawo da wayar fuskarsa yana duban kiran farouq din yana ci gaba da takawa yana fita a wajen. Boyayyen murmushi ya saki,tun jiya ya kashe wayarsa dama duk wani hanya da farouq din zai sameshi,yasan tabbas idan ba haka ya masa ba bazai shafa masa lafiya ba,zai birkita masa lissafi ne kawai. "Idan baka da niyyar dawowa ne malam ka yiwa mutane magana.......awa uku kadai suka rage awannin daurin aurenka su cika......amma still ace baka iso ba?". "Who told you dude?.....mu hade a Bristol,banason hayaniya" Daga haka ya kashe wayar ya miqa masa yana magana dashi ya tura masa number dakin da yayi booking already. Yana da gidajen da zai iya sauka a cikin su,saidai sam sam baya shaawar ya sauka a can din gudun kada a cimmasa a dameshi da damuwa. Abinda bai sani ba yayi gudun gara ne,don kusan mafi yawan abokansu da sunzo ne don farouq a Bristol din sukayi masauki. Sanda saqon yakai wayar farouq shafa kansa kawai.yayi,yaci alwashin sai ya rama wasa da hankalin da fuad din yayita yi masa. Ya ajiye wayar yana kiran musaddiq kan ya fiddo mota yanason kai yakai ga fitowa su ruskeshi a can. Yayi mamakin ganin motocin jadda har guda biyar a wajen suna jiran isowarsa. Bai gama wannan mamakin ba farouq ya fito cikin daya daga cikinsu yana qoqarin rufe wayarsa ya jefata a aljihu. Wani kallo me kama da harara ya watsama fuad din wanda ya jingina kawai jikin daya daga cikin motocin yana kallon qarewar fushin farou a kanshi. Ya sani shi ko farouq din babu me iya fushi da dan uwansa.....duk wani abu da daya daga cikinsu zai fadi burga ce kawai da cika baki,da zarar sunyi face to face yake wucewa tamkar bai faru ba. Koda ya iso duka yakai masa ya goce yana wannan tsadajjen murmushin nasa "Haka kawai ka nakasani bayan banyi komai ba?" Ya furta murmushin yana shimfide a fuskarsa "Sa'arka daya wallahi......yau babbar rana ce" Farouq ya fadi yana buda masa murfin motar da kansa. Sai daya shiga sannan yabi bayansa,yana zama wayarsa kuma ta dauki tsuwwa ya ciro yana amsata. Tunda suka taho a hanya farouq ke amsa wayoyin mutane iri iri. Yana ankare dashi amma baice komai ba,ko a iya haka ya samu alama da shaidar lallai gayyar jama'a farouq din yayo. "Kada kacemin tsayawa kayi ka batawa kanka lokaci kayita kiran mutane?" Yayi maganar yana tabe baki cikin rashin bawa abun muhimmanci. Wani kallo ya watsa masa "An gaya maka kowa irinka me wai?,kai abinda ka dauka daban.....yadda mu muka dauka......aure komai lalacewarsa sunansa aure.....barema ba lalataccen koda na bariki ne". "K'nnnnn" Kawai ya fada yana zamewa gami da yin relaxing sosai jikin motar "Nidai muyi mu qarasa,bacci ne a ido na,kwanakin duk da nayi acan ba wani bacci na samu ba". " Mutuwa zakayi ba bacci ba" Farouq ya fada cikin harzuqa. Kallo daya ya yiwa farouq din ya lumshe idonsa yana cewa "Allah ya baka haquri" Daga haka bai sake cewa komai ba kaman yadda bai kuma bude idonsa ba har sukaje. Da lallausan farin towel ya fito daga toilet din dakin daya zame masa masauki daure a qugunsa. Ya qarasa gaban madubin dakin yana duban yadda farouq ya zube masa duk wani kayan shafawarsa. Duddubasu yayi kawai ya ajiye yana mamakin yadda farouq ya dauki auren nan serious. Sai ya jawo stool ya zauna akai yana kallon kyakkyawar fuskarsa ta cikin madubi gami da sanya qaramin towel yana tsane ruwan kansa. Koda ya gama sai ya aje towel din,ya soma lalubar wayoyinsa. Sunyi da larab zai kirashi don ya tabbatar an gama design na hall din dake cikin kamfanin inda za'a gabatar da taron budeshi a jibi kaman yadda ya tsara. Gajiya yayi da dube dubensa,sai ranshi ya bashi farouq ya kwashesu. Qaramin murmushi ya saki,yasan zai aikata,kuma duk zaiyi hakanne don ya tilastashi shiryawa. Duk da abun ba wani muhimmanci gareshi ba a wajensa.....amma farouq ya tattara duka lokacinsa akan komai dason ganin komai ya tafi daidai din,ya qarasa gaban madubin ya sake zama yana bude lotion dinsa na dindindin ya fara shafawa. Yana tsaka da taje sumarsa me tsananin daukan hankali aka murda handle din aka turo,bai motsa ba don yasan mutum daya ne zai masa haka. Ta cikin madubi ya hangoshi ya shigo. Sai ya samu kansa da dan qare masa kallo. Yayi kyau cikin wata irin danyar shadda dake nuna nauyin kudaden da aka narkar domin siyenta,aka kuma keta alfarmar nera tare da nuna mata iyakarta wajen tsara mata dinkin jikinta. Farar hula ce saman kanta da aka yiwa nadin farin rawani,wanda aka saki jelar rawanin ya zubo ta qirjinsa daga gefan kafadarsa ta dama. Iya abinda ya iya gani kenan,amma fadin yadda shigar ta qarawa farouq din kwarjini ma ba'a magana. "Kayi kyau ango" Ya fada da sigar zolaya yana maida idanunsa saman mirror table din yana aje comb din hannunsa tare da lalubar hair spray. "Kaima yanzu zakayi naka kyan.....don komai namu iri daya zai kasance". Da sauri ya daga kai ya kuma juyo gaba daya yana dubansa hadi da fiddo sexy eyes dinsa sosai zuwa waje,abinda ba kasafai ya fiya yi ba "Wanne irin rigima ne wannan farouq?,kafi kowa sanin banason manyan kaya basu dameni ba......for god sake zakace babban riga zan saka harda wani qarin rawani kamar nine zan jagoranci sallar juma'a na yau din?". Watsa hannuwansa farouq yayi "Kai ka sani" Ya fada a gajarce yana nufar inda kayan suke ya soma ware masa. 𝐃𝐮𝐧𝐢𝐲𝐚𝐭𝐚 𝐧𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐧𝐞 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 9 Page 9 Duniya ta Tsaye yayi ganin da gaske farouq din yake,daga qarshe baida wani zabi illar amsar kayan daya dinga yi da daya da daya yana sanyawa. Komai nashi fari ne qal yayi amfani dasu,tun daga undies har zuwa complete suturar jikinsa. Qerarren handmade half shoe din me ainihin tsada da kyau gami da daukan idanu dan asalin qasar italy,da agogon rolex me asalin daraja da ya samu ado daga wani yanki na gold din da kamfaninsa ke sarrafawa. Gurin saka rawanin akaso asha daru,amma shigowar ahsan cousin din farouq ya raba gardaman. Shi ya karba ya nada masa shi tsaf saman kansa "Ya subhanallah......ya Allah,na taba ganin wanda rawani ya yima kyau kaf tsayin rayuwata kuwa irinka?.....amma ban taba ganinsa dashi ba farouq" Ya maida tambayar kan farouq sanda fuad ke tsaye gaban madubin yana kallon yadda fuskarsa ta fita fes kamar an sauya masa ita. Wani annuri shi kansa yaga tana futarwa wanda bai taba gani ba,da gaske manyan sutura suna qarawa mutum kwarjini,karon farko yaji manyan kaya suna sake burgeshi. "Lokaci yayi" Yaji farouq yana fada ba tare da yaji amsar da ya bawa ahsan ba. "Ya salam" Ya fada sanda suke yo tattaki shi da farouq da ahsan zuwa ma'ajiyar motoci na Bristol din. Yawan matasan masu jini a jika daya gani kowa cikin shigar fararen kaya da babbar riga ya bashi mamaki. Abokan da da yawa ya manta dasu,wasu kuma haduwa tayi wahala,saidai kowa a cikin su yana cikin jerin sahun matasan da suke wasa da kudi som ransu saboda samun cikakken sukuni da arziqin rayuwa. Parking lot din ya cika gaba daya da motocinsu,ta wannan tana wane wannan,a haka ya qaraso gurinsu da natsattsen takun nan nasa kamar namijin talo talo. Daya bayan daya yake basu hannu suna gaisawa,wasu su zolayeshi wasu suyi masa qorafi. Da yawansu bashi da abun cewa,musamman yadda yaji gabbansa sunyi sanyi da ganin mutanen da farouq din ya tara masa duk kawai dondai su shaida daurin auren da bai gama gamsuwa da yiwuwarsa ba. Ba wanda shigar fuad din bata dada da qasa ba,don ya dace da shigar ainun,harma tafi karbarsa sama da farouq din. A nan suka kashe wasu mintuna kusan sha biyar ana rudu irin na abokai,gaba daya wajen ya dumame da qamshin turaruka masu tsananin tsada,daga bisani suka fara shiga motocinsu suna tashi daga wajen. Convoy sosai suka hada da jerin gwanon motoci masu tsayi,kusan daurin auren sanannen labari ne daya karade kowa,don haka duk inda zasi gifta sai ya zamana kamar suna sake bada sanarwar afkuwar abun. Duk inda suka gifta saisun wafci hankula da kyawun motocin,kowanne traffic suka je ba jinkiri ake daga musu qafa motocinsu su wuce tas,don haka basu wani kashe lokaci sosai a hanyar ba suka isa inda suka nufa. Bai sake ji a jikinsa komai da gaske bane sai sanda suka isa alu avenue dake nasarawa,masallacin alfurqan inda acan aka tsaida don shaida daurin auren. Jikinsa yayi wani irin sanyi sosai,yana ganin da gasken gaske komai yake wakana lallai. "Ya salam.....ya subhanallah" Kawai yake fada a ranshi. Irin taron dafifin al'ummar daya gani bai taba zaton zai samu irinsu a gurin ba........manyan mutanen daya samu a wajen bai taba koda kawowa zai samesu a wajen ba.....duba da ba wani mutum daya daya gayyata da bakinsa. Manyan 'yan kasuwar duniya daga qasashen duniya daban daban......manyan 'yan siyasa da qusoshin gwamnati......shugaban qasa da attajirai gami da duk wani me fada aji,don kusan kowa qarin martaba ne a tare dashi halartar daurin auren. Basu ma kai ga samun damar isa cikin masallacin ba saboda yawan al'ummar dakeson ganinsa tare dayi masa fatan alkhairi. Baisan iya dadin yawan manyan mutanen daya jima bai gani ba amma yau daurin auren ya tattarasu waje guda ba.....baisan kuma adadin su nawa ya gaisa dasu ba,har zuwa sanda kunnuwansa suka jiye masa ta lasifiqan cikin masallacin data fito waje tana fadin. "Mun shaida daurin auren matashin attajirin dan kasuwar gold MUHAMMAD FUAD JADDA da amaryarsa AMEENATU AHMAD MU'AZZAM". "AMEENATU?.....why?. Me yasa aka sanya mata wannan sunan?" Ya furta can qasan ransa. Ta yaya zai zamana tana da suna me matuqar martaba da mutunci a idonsa irin wannan?,why..... Full name din da aka kirata dashi bai tuna masa komai ba sai kawun nata rufa'i,ranar daya samu fill details nashi da wannan sunan ya sameshi. Ya saki siririn tsaki yana jin ranshi yana baci. Inda mutane sunsan ko su waye su da basu bata kudadensu ba wajen siyan ticket na jirginsu sun cika jingim wajen shaida daurin auren ba,ya sake jan qaramin tsaki yana juyawa tare da neman nesanta kansa da hayaniyar wajen,guard dinsa da duk hautsinewar wajen basu yarda sun matsa ba suka biyoshi a baya. Can wajen motocinsu ya koma,sai daya shiga ya zauna sannan yace musu "Don't.....karku gayama kowa ina ta nan idan ba farouq bane ya tambaya". "Yes sir" Suka amsa a matuqar ladance suka maida murfin suka zuge masa. Rawanin duka da babbar rigar ya cire ya ajiye gefe,sannan ya koma ya zauna sosai yana nazarin wajen ta cikin motar. Abinda ya lura dashi,bawai farouq kadai ba,hatta da abba ya dauki abun very serious,yaga mutanensa a wajen har baisan adadinsu ba......haka anni,yaga familynta sosai,tamkar tana auren farouq ne,sai ya maida idonsa ya kulle yana son tuno waye da waye ya gani daga bagaren maamah?. Bai samu nasarar kaiwa qarshen tunaninsa ba knocking da aka yiwa glass din motar ta sakashi bude ido,ya ganshi farouq ne,yana daga kwancen ya danna remote ya bude mass murfin. Dubansa yayi sanda yake qoqarin shigowa "Reception zamu wuce.... Already wasu sun fara yin gaba,musaddiq da saddiq tun dazu suna ta wajen". Shi sai a sannan ya tuna ma.baiga kowa cikin su ba,ason ranshi farouq din ya barshi ya koma masauki ya kwanta ya rama baccin dake.kansa,ya kuma rage hayaniyar mutane da yakeji har cikin kansa,saidai kuma ya sani koda yace zai masa bayani ma farouq din ba fahimtarsa zaiyi ba,yadai fadi abu daya "Ina fatan daga can duk wata hidima ya qare baku qirqiri komai ba kuma......don bazan iya jure zuwa wajen komai ba". " Wanda baisan halinka bane zai wahalar da kansa shirya wani abu......walimar.ma saboda cika sunna ne da neman albarkar auren" Farouq ya amsa masa yana daga kiran abokinsa da yake gaya musu sun isa wajen "Muma muna dab......ka jirani" Yace yana sauke wayar. Siririn murmushi kawai fuad ya saki,farouq.....farouq..... Idan ba farouq babu shi.......kaman yadda yasan idan babu shi babu farouq din. Tunda momma bahijja ta tilastata tayi wanka,ta kuma shirya cikin wata sabuwar atamfar Hilton wax. Cikin kayan da momma ta zare cikin lefen ta bayar aka dinka ba tare da sanin sabreen din ba. Tun tana shiryawa taji shigowar uncle abdulhakeem da tun jiya suka iso suka kwana a tahir guests palace. Zancan duka ya shafi aurenta ne,wanda duk kalma daya da zata fita daga bakin uncle din nata sai taji kanta ya wani sara mata. Zazzafan mutum ne da ta jima bataga mutum me zafi da kafiya akan gaskiya ba irinsa. Ta jima tana tunanin idan ta kammala deal dinta ta tashi matsawa daga gurbin da take zuwa wani ta yaya zata bacewa idanunsa?,ta kuma zullewa duk wata tuhuma tashi?. Taji ya ambaci sunan su huda da nadra da tafi sati tana tunanin ina za'ayi da rayuwarsu?,amma tasan tayi kadan ta tsaya gabansu ta musu wannan tambayar,bata kuma samu jin abinda suke cewa ba sanadiyyar hayaniyar yan tafiya daurin auren data qaru. Ta gama shiryawar taji wani zazzabi ya sauko mata bayan ciwon kanta daya dinga gaba gaba saboda tunanin data matsawa kanta dashi,sai kawai ta lallaba can gadonsu nadra dake qarshe ta haye can ta qudundune. 𝐃𝐮𝐧𝐢𝐲𝐚𝐭𝐚 𝐧𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐧𝐞 𝟎𝟖𝟏𝟖𝟕𝟐𝟓𝟓𝟖𝟔𝟐 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 10 Page 10 Can cikin tsakiyar kanta maganganun mutane ke mata yawo sanda motar ke tafiya cikin nutsuwa saman lafiyayyar kwaltar dake shimfide a kanta. Muryoyin mutane daban daban da sukayi mata fadan shiga gidan miji wai a cewarsu "Allah yasa dai ki iya zama......don zaman aure daban da zaman bariki,zaman gidan miji daban da yawon bariki" Muryar bibo kenan da nata salon fadan da yafi kama da turun mutuwa "Da dadi ba dadi kiyi haquri ki zauna......Allah yasa mutuwa ce zata raba,kiji kiqi ji,ki gani kiqi gani" Muryar daada kenan wadda ta kama hannuwanta tana fada muryarta a sanyaye. Ko da can ba zatace ga wani mummunan abu da daada ta taba musu ba,ita dai barta da shariya da rashin shiga lamari da sabgar kowa cikin gidan. Idan ka ganta kuwa a ciki to tabbas abu yaci tura,amma bibo da yaabi koda dan wani akeyi suna iya ara su yafa tun usul. "Mommaa......nadra.....haneefa.....huda" Sunayen data iya kirawa momma kenan sanda take yunqurin sakata a cikin motar da zata yi musu jagora zuwa inda zasuje. "Ina sane dasu......kuna su din ba nauyinki bane" Ta amsa masa a tausashe. Ta cikin lafayar jikinta take iya hangen yadda motar ke tsala gudu abinta,amma saboda lafiyar motar da irin tsarin da akayi mata zaka rantse ba gudun takeyi ba. Ta maida idanunta ta lumshe,wasu hawaye da batasan sanda suka taru ba suka biyo kuncinta suka diga bayan hannunta dake ajiye saman cinyarta. Har yanzu dai ta kasa gasgata abinda take gani,har yanzu ta kasa gasgata abinda kunnuwanta da zuciyarta ke nanata mata. Da gaske mutumin nan yaci galaba a kanta da dukka tsarikansa.....da gaske shike da nasara ba ita ba.......da gaske ya cinye wasan a wannan gabar.....saidai kuma hakan baya nufin zaita nasara kenan a kanta,hakan baya nufin ta fadi kenan har abada.....lallai zata canza labarin......zata canza qaddarar da dukkan iyawarta. "Gidan mamarshi zamu fara shiga.......sai gidan riqonsa,kamar haka matar data shigo dazu tace ko?" Daada ta fadi tana dan duban momma bahijja da hannun sabreen yake cikin nata. "Eh haka ne" Ta amsa mata idanunta sauke kan faffadan sabon gate din gidan maamah dake nuna zallar dukiyar dake narke cikin gidan. A nutse jerin gwanon motocin suka cusa kai makekiyar harabar gidan data kasance mafarkin maamah na shekara da shekaru,gidan daya dauki hankula da bakunan dukkan jama'arta dake hulda da ita. Gidan da a cikin ranta ita kanta ta gamsu da dukiyar daya lashe,amma zuciyarta bata gama nutsuwa da hakan ba saboda har yanzu gidan alhj hamza kibiya da iyalinsa yafi nata girma yalwa da kuma tsari,ba tare data duba yawan da suka darata dashi ba,da kuma yawan al'umman da gidan ke dauka suke riqo a yanzu haka. Tunda motar ta tsaya a parking lot na gidan gabanta yake wani irin faduwa,ta maida idonta ta lumshe tana sauraren bugun da zuciyarta keyi da bata taba jin irinsa ba,sai taji bugun har kusa da maqogoronta. Sake runtse idanunta tayi sanda momma bahijja ke fadin ta fito,tana jin bugun zuciyar na sake daduwa amma kuma ta rasa me ya kamata ta karanta?,wacce addu'a ce ta dace da irin wannan yanayin da takejin kanta a ciki?. Riqon hannunta da momma din tayi shine ya sassauta mata abinda takeji kadan,ta sake riqe momma din itama da kyau ba tare tasan ta yadda zata gaya mata abinda takeji cikin qirjinta ba. A dan hanzarce ta shigo dakin nata,sannan ta maida qofar ta kulle ta kuma murza key. Da dan hanzarin still ta isa gaban madubin nata dake manne da wasu lafiyayyun lockers. Ta murza daya daga ciki ta bude ta,sannan ta saka hannu ta ciro baqar ledar dake a ciki ta dora saman madubi. Ko ina a jikinta amsawa yakeyi da wani irin doki da son fara aiwatar da nata aikin,a yau batasan sau dubu nawa tana addu'ar samun wannan sa'ar ba......batasan sau nawa ta roqi samun nasara a wannan ranar ba,nasarar da indai ta rasata kamar wadancan kwanakin ta tabbatar komai zaizo mata da wahalar gaske.....batasan kuma ta yadda zata tari abun ba. Kusan leda shidda ce,kowacce sai data kunceta sannan ta saka hannu ta fara ciro kayan ciki. Kusan tarkace ne a idanun me kallo,amma a wajen maamah gwara rashin million dubu da rasa daya daga cikin kayan. Wasu kwalabe ne masu dauke da wani irin baqin abu a ciki,wani kuma kore kore ne,saidai yana da dan qamshi qamshi kadan a ciki mara qarfi. Ta bude kowanne ta tsiyaya cikin tafin hannunta,ta kuma mulke hannun nata da kyau kamar yadda aka umarceta da tayi,sannan ta maida komai muhallinsa kamar bata taba komai ba cikin dakin. Gaban madubin ta tsaya tana qoqarin controlling kanta da daidaita nutsuwarta. Idanun ta fes cikin fuskarta tana maganar zucci da kanta da kanta,wanda batayi wani nisa ba knocking din da ake mata ya isa kunnuwanta. Adan fusace tace tambaya don bata buqatar doguwar mu'amala da kowa har sai wadda tayi shirin saboda ita ta iso "Zuwaira ce" Ta bata amsa a tsanake. "Sun iso,suna falon qasa sun......." "Gani nan" Ta tari numfashin zuwairan ba tare data jira sauran bayaninta ba. Ba sauran bayaninta take da buqatar ji ba,tunda taji abinda take buqatar jin,ta waiwaya tana zura takalmanta data cire tare da kallon tsadajjen mayafin data lullube jikinta dashi ta tabbatar ya zauna a jikinta......ya sanyata tayi kwarjini da wata irin kamala da sam zai wahala ka kawo wani abu me muni a kanta. Kyanta ya bayyana.....kamanninta da musaddiq sosai,yanayin jin dadin da kulawar data samu wadda take rainawa ta sake sanyawa jikinta ya murje sosai,hutu da quruciya sun bayyanar mata. Murmushi ta sakarwa kanta da kanta,sannan ta juya a hankali tana fita a dakin. Tun daga saman stairs din take raba idanunta tana son hangota. Bata wani sha wahala ba,ta hangeta zaune saman lallausan carpet din da aka qawata tsakiyar falon dashi. Qafafunta a tanqwashe suke,kanta a qasa cikin shigar laffayar da tazo mahadin lace din da aka zauna akyi dukka adon jikinsa da hannu(handmade lace),kamar yadda lafayar jikinta itama duk wani zare da duwatsun jiki da hannu aka gameshi. Abune na masu dashi,ba wani cikar jama'a masu yawa ko cinkoso,kowa yana zaune a nutse,yayin da gaisuwa ke wakana tsakaninsu momma da jama'ar da suka samu cikin falon. Da wani irin kirki na gasken gaske saman fuskarta,faffadan murmushi da fara'a me nuna tsantsar maraba da baqo ta iso rukunin kujerun tana furta "Lale maraba......sannunku da zuwa......sannunku da qoqari" Da murmushi a fuskar momma ta amshe maraban tana duban maamah tsaf tare da karantar yanayinta. "Bari na zauna kusa da diyata" Ta fadi tana zama kujerar dake kusa da sabreen din. Gaisuwa akayi cikin mutunci dason nuna ainihin zallar kirkinta,suka gabatar mata da amanar sabreen tare da dan qaramin jawabin girmama kowa ga sabreen din "Itama diyata ce ai tunda yarona take aure,kuma in sha Allah zakuyi alfahari da hada alaqa damu,Allah ya bada zaman lafiya,shi kuma Allah ya tayashi riqo" Maamah ta furta cikin zaquwa da gajiya da bayanan. So take kawai ta isa ga muradinta. "Am nace ba.....idan ba damuwa inason ganin diyata a kebance,minti biyar don Allah" Maamah ta fada tana murmushi. Ba tare da tunanin komai ba ko kawo komai ba momma bahijja tace "Bismillah mana......haba hajiya ai diyarku ce" Daada ta fadi yadda momma din ta karbi sabreen yana burgeta. Duk da tayi gaba zuwaira ke mata jagora zuwa wani daki na daban a saman benen.....amma saita dinga jin wani irin yanayi yana bibiyar gabobinta. Kasa zama tayi,tana a tsaye sanda taji zuwaira taja musu qofar ta fice. "Zauna mana.....ki yaye wannan lullubin kan naki......don fahimtata nakeso kiyi sosai tamkar yau ne karon farko da kika fara fahimta ko haddace wani abu a rayuwarki" Tayi maganar cikin jerarrun kalmomin da kana jinsu zakasan ko meye zata fada yana da matuqar muhimmanci a wajenta. Sai data fara janye lullubin nata baya,sannan ta sulale a wajen ta zauna. Tana jin kamar babu wani sauran qwarin gwiwa daya rage mata a rayuwa,duk da yadda take kokawa da zuciyarta da qoqarin qarfafawa kanta gwiwa. "To alhamdulillah.......komai ya kammala,kuma komai yazomin da sauqi fiye da yadda nayi zato ko kuma tsammani........ina fata baki manta meye manufar aurenmu ba?" A nutse sabreen din ta daga kai sannan ta zube mata idanunta saman fuskarta. Kallonta tayi na second kusan goma sannan ta gyada kai "Da kyau.....da farko abinda zan fara gaya miki shine abinda na maimaita miki a baya.......qaidar contract dina na farko shine sirri.......inason sirri,don muddin aikin nan ya fita daga da'irar sirri zuwa wata da'ira ta daban.....to tamkar kin wargaza rayuwarki da hannunki ne......bayan taki rayuwar da kika wargaza kuma......kin wargaza ta 'yan uwanki suma...." Daga ma maamah hannu tayi da hanzari tana zare idanunta daga kanta "Ki tsaya iya kan ameenatu kawai......huda,nadra da haneefa,tabasu ko sako sunansu cikin sabgarki da ameenatu tamkar ganganci ce" "Da kyau!" Maamah ta furta tana sakin murmushi,abubuwa biyu zuwa uku suna jan hankalinta. Gyara zamanta tayi tana ci gaba da murmushi "Ashe ameenatu ce....abu yayi kyau..ameenatu ta bata,wata ameenatun zata gyara,wannan abun yayimin dadi.......qwarin gwiwarki da rashin sarewarki ya burgeni......kariyar da kike bawa qannenki tana da yawa,kuma ita dai ta isa ta bani yaqini da tabbacin ba zaki bari a samu failure ba ko don saboda su......." "Shiga maganarki kai tsaye" Sabreen ta fadi mata tana kauda kanta zuwa wani sashe na daban. Idanu maamah tadan zuba mata har yanzu tana murmushi,sai kuma ta miqa hannu ta zaro wata paper da abun rubutu ta ajiye a gabanta. "Inaso ki rubuta adadin kudaden da kike da burin mallaka a rayuwarki......ni kuma zan mallaka miki su a madadin sadakin aikinki,zan kuma qara miki kwatankwacinsu muddin komai yayi daidai". Fararen manyan idanunta ta daga ta watsawa maamah su,karon farko da idanun suka yiwa maamah din wani kwarjini da bata taba jin irinsa ba. Murmushin da ya subuce kuma a fuskar sabreen ya sanya mata kokwanto "Ki fadi magana me muhimmanci saboda mutanen dake zaman jiranki a qasa" . Maganar tata tadan daure mata kai,a nata ganin ba wata magana da zata zama me muhimmanci a wajen sabreen sama da maganar kudin aikinta,wanda take ganin shi kadai ya isa ya bata azama akan aiwatar mata da komai. To amma akance......shi yaqi dan zamba ne,don haka ta gyada kai 𝗗𝘂𝗻𝗶𝘆𝗮𝘁𝗮 𝗻𝗮 𝗸𝘂𝗱𝗶 𝗻𝗲 𝟬𝟴𝟭𝟴𝟳𝟮𝟱𝟱𝟴𝟲𝟮 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶𝗕̶𝗢̶𝗢̶𝗞 ̶𝟮 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 𝟭𝟭 𝗣𝗮𝗴𝗲 𝟭𝟭 "𝗡𝗮𝗷𝗶 𝗱𝗮𝗱𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗶𝗸𝗮 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗺𝗲 𝗹𝘂𝗿𝗮 𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶,𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘇𝗮𝗶 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶 𝘆𝗮𝘇𝗼 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝘂𝗾𝗶........𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗲 𝘀𝗮𝘂𝗾𝗶 𝗻𝗲 𝗶𝗱𝗮𝗻 𝗸𝗶𝗻𝗯𝗶 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗰𝗲 𝗺𝗶𝗸𝗶,𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻𝗻𝗶 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗻 𝗺𝗮 𝗸𝗶𝗻𝗮 𝗶𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗺𝗮𝗹𝗮𝘄𝗮 𝗸𝗶 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗮𝗯𝗶𝗻𝗸𝗶,𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶 𝗻𝗮 𝘀𝗮𝘄𝗮 𝗮 𝗮𝗯𝗶𝗻𝗰𝗶,𝘀𝗮𝗶𝗻𝗮 𝗿𝘂𝘄𝗮𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮,𝘀𝘂 𝗸𝗲𝗻𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗸𝗲 𝗱𝗮 𝗯𝘂𝗾𝗮𝘁𝗮𝗿 𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗰𝗰𝗲 𝗿𝗮𝗻𝗮 𝗸𝗼𝗱𝗮 𝘀𝗮𝘂 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝗻𝗮𝗰𝗶𝗻 𝘆𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻𝘀𝗮,𝗻𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮𝗻 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝘀𝗮𝗻𝗰𝗲 𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗿𝘂𝘄𝗮𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮,𝗶𝗱𝗮𝗻 𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘀𝗮𝘂 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝘁𝗮𝗸 𝗮 𝗿𝗮𝗻𝗮 𝗺𝗮 𝘆𝗮 𝘄𝗮𝗱𝗮𝘁𝗮𝗿. 𝗜𝗻𝗱𝗮𝗶 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂 𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗲 𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗮𝗹𝗯𝗶𝘀𝗵𝗶𝗿 𝗱𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗻𝗮 𝗰𝗮𝘀𝗮'𝗶𝗻 𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘂𝗸𝘂 𝗸𝗮𝗰𝗮𝗹 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶 𝘇𝗮𝗶 𝘀𝗮𝘂𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗶𝗱𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗸𝗲𝘀𝗼......𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗿𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗸𝗶𝗻 𝘇𝗮𝗺𝗮 '𝘆𝗮𝗻𝘁𝗮𝗰𝗰𝗶𝘆𝗮.....𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶 𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻,𝗴𝗼𝗯𝗲 𝗯𝗮𝘀𝗮𝗶 𝗷𝗶𝗯𝗶 𝗯𝗮 𝘇𝗮𝗻 𝗮𝗶𝗸𝗼 𝗮𝗺𝗶𝗻𝘁𝗮𝗰𝗰𝗶𝘆𝗮𝘁𝗮,𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘁𝗮𝘆𝗮𝗸𝗶 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗻𝗮 𝘄𝗮𝗱𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗻𝗮𝗸𝗶𝗻 𝗮 𝗺𝗮𝘇𝗮𝘂𝗻𝗶𝗻 '𝘆𝗮𝗿 𝗮𝗶𝗸𝗶 𝗵𝗮𝗿 𝗸𝗶 𝗸𝗮𝗺𝗺𝗮𝗹𝗮 𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻𝗸𝗶 𝗸𝗶𝘆𝗶 𝗴𝗮𝗯𝗮........𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗸𝗶 𝘇𝗮𝘂𝗻𝗮 𝗱𝗮 𝗳𝘂𝗮𝗱 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘇𝗮𝗯𝗶𝗻𝗸𝗶 𝗻𝗲.......𝘀𝗮𝗶𝗱𝗮𝗶 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘇𝗮𝗻 𝗴𝘂𝘁𝘀𝘂𝗿𝗮 𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗻 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗵𝗮𝗹𝗮𝘆𝗲𝗻𝘀𝗮 𝗱𝗼𝗻 𝗸𝗶 𝗸𝗶𝘆𝗮𝘆𝗲 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶 𝘆𝗮𝘇𝗼 𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝘂𝗾𝗶......" "𝗕𝗮𝗯𝘂 𝗯𝘂𝗾𝗮𝘁𝗮" 𝗧𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮 𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲,𝘀𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘁𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲 𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗴𝘆𝗮𝗿𝗮 𝗹𝘂𝗹𝗹𝘂𝗯𝗶𝗻𝘁𝗮. 𝗪𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗺𝗮𝗺𝗮𝗸𝗶 𝗸𝗲 𝗵𝗮𝗷𝗶𝗷𝗶𝘆𝗮 𝗱𝗮 𝘇𝘂𝗰𝗶𝘆𝗮𝗿𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗮𝘂𝗸𝗼𝘄𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝘀𝗮𝗺𝗮𝗻,𝗯𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗳𝗲𝗻 𝘀𝘁𝗮𝗶𝗿𝘀 𝗱𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗹𝗮 𝗮𝗹𝗹𝗮 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝗶𝘆𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗱𝗲𝘄𝗮. 𝗔𝗻𝘆𝗮 𝗸𝘂𝘄𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗱𝗶𝗻 𝗨𝗪𝗔 𝗖𝗘?,𝗨𝗪𝗔 𝗖𝗘 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗵𝗮𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗿 𝗯𝗶𝗹'𝗮𝗱𝗮𝗺𝗮?,𝗸𝗼 𝗸𝘂𝘀𝗮 𝘂𝘄𝗮 𝗰𝗲 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗷𝗶𝗻𝘀𝗶 𝗸𝗼 𝗵𝗮𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮 𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗯𝗮𝗻?. 𝗕𝗮𝘁𝗮𝘀𝗮𝗻 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗯𝗶𝘆𝗲 𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮 𝗯𝗮 𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗮𝘁𝗮𝗷𝗶 𝗺𝘂𝗿𝘆𝗮𝗿𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗲 𝘁𝘀𝘂𝗴𝘂𝗻𝗻𝗮𝘄𝗮 𝗴𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗺𝗼𝗺𝗺𝗮 𝗯𝗮𝗵𝗶𝗷𝗷𝗮 𝗱𝗼𝗻 𝘁𝗮𝘀𝗮𝗻 𝘁𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗮𝘀𝗼. 𝗕𝗮 𝘇𝗮𝘁𝗼 𝘁𝗮 𝘁𝘀𝗶𝗻𝗰𝗲𝘁𝗮 𝗮 𝗴𝗮𝗯𝗮𝗻𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗶𝗻 "𝗟𝗮𝗹𝗹𝗮𝗶 𝘆𝗮𝗿𝗼𝗻𝗮 𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗰𝗲,𝗻𝗮𝘆𝗶 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻𝗰𝗶𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂𝗻 𝘀𝘂𝗿𝘂𝗸𝗮 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻....𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮" 𝗧𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗮𝘀𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗮𝘇𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗸𝗮𝗻 𝘀𝗮𝗯𝗿𝗲𝗲𝗻 𝗱𝗮 𝘀𝗶𝗴𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮. 𝗬𝗮𝗺𝗺𝗺𝗺 𝘁𝗮𝗷𝗶 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗮𝗯𝘂 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗯𝗶𝗻 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘀𝗮𝘀𝗵𝗲 𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗸𝗶𝗻𝘁𝗮. 𝗖𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗵𝗮𝗿𝗯𝗮𝘄𝗮 𝗷𝗶𝗻𝗶 𝗱𝗮𝗸𝗲 𝘇𝗮𝗴𝗮𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗴𝗮 𝗷𝗶𝗷𝗶𝘆𝗼𝘆𝗶𝗻𝘁𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝘀𝗮𝗾𝗼 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝘂𝘆𝗲 𝘀𝗮𝘂𝘆𝗲 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗮 𝗮𝗳𝗸𝘂𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝘀𝗮𝘂𝗿𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗴𝗮𝗴𝗴𝗮𝘄𝗮 𝗺𝗲 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲 "𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗺𝗶𝗸𝗶 𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮" 𝗧𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗺𝗮𝗶𝗺𝗮𝗶𝘁𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 𝘀𝗮𝘂 𝘂𝗸𝘂 𝗱𝗼𝗻 𝘁𝗮𝗻𝗮𝘀𝗼𝗻 𝗮𝗱𝗮𝗱𝗶𝗻 𝘀𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗶𝗻 𝘀𝘂 𝗰𝗶𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗳𝗶𝗻 𝘁𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗲 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻 𝗻𝗮𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝘀𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮 "𝗔𝗺𝗲𝗲𝗻 𝘆𝗮 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵......𝗮𝗺𝗲𝗲𝗻 𝘆𝗮 𝗿𝗮𝗯𝗯𝗮𝗹 𝗔𝗮𝗹𝗮𝗺𝗶𝗻" 𝗠𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲𝗻 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗸𝗲 𝗮𝗺𝘀𝗮𝘄𝗮 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶. 𝗛𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻 𝘁𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗲 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮,𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝘄𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗱𝘂𝗸𝗸𝗮 𝗯𝗶𝘆𝘂𝗻 𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗼𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗳𝘂𝘀𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮𝗿𝘁𝗮 "𝗧𝗮𝘀𝗵𝗶 𝗸𝗶 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝗸𝗶......𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗻𝗮𝗻 𝗸𝘂 𝗸𝗮𝗶𝘁𝗮 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗸𝗮𝗶 𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲......𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗵𝗶 𝘆𝗮 𝗿𝗮𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗰𝗲 𝘁𝗮𝗷𝗲 𝗱𝗶𝗻.....𝗸𝗶𝗻𝗷𝗶 𝗱𝘂𝗸𝗸𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗮𝗶𝗻𝗮 𝗸𝗼?" 𝗦𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮 𝘁𝗮𝘆𝗶 𝗱𝗮 𝗴𝘆𝗮𝗱𝗮 𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗸𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗺𝘂𝗴𝘂𝗻 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗶𝗻 𝗷𝗶𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗯𝗮 𝗷𝗶𝗻 𝗶𝗿𝗶𝗻𝘀𝗮 𝗯𝗮,𝘀𝗮𝗶𝘁𝗮 𝗷𝗮𝘄𝗼𝘁𝗮 𝘁𝗮 𝗿𝘂𝗻𝗴𝘂𝗺𝗲𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗺𝗮𝘁𝗮 𝘄𝗮𝘀𝘂 𝗮𝗱𝗱𝘂'𝗼'𝗶𝗻,𝗮𝗯𝗶𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝘁𝗮𝗷𝗶 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝘀𝗮𝗿𝗮𝘄𝗮,𝘁𝗮𝗸𝗲 𝗰𝗶𝘄𝗼𝗻 𝗸𝗮𝗶 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿 𝗺𝗮𝘁𝗮. 𝗦𝗮𝘂𝗸𝗲 𝗹𝗮𝗯𝘂𝗹𝗲 𝗮𝗺𝗻𝗮 𝘁𝗮𝘆𝗶 𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗼 𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗯𝘂 𝗮𝗱𝗮𝗱𝗶,𝘀𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘁𝗮 𝗺𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗻𝗮𝗿𝗸𝗲 𝗳𝘂𝘀𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗶 𝗸𝘂𝗸𝗮 "𝗔𝗻𝗻𝗶 𝗱𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗮 𝘆𝗮 𝗿𝗶𝗴𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶,𝗵𝗮𝗿 𝘆𝗮𝗻𝘇𝘂 𝗯𝗮𝘀𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗼 𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮 𝗯𝗮.....𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮𝗮 𝗺𝘂𝘀𝗮𝗱𝗱𝗶𝗾 𝘆𝗮𝗰𝗲 𝘀𝘂𝗻 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗺𝗮𝗮𝗺𝗮𝗵....𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗰𝗮𝗻 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘀𝗮𝗶 𝗻𝗮𝗻". 𝗔 𝗻𝘂𝘁𝘀𝗲 𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝘇𝗮𝗿𝗲 𝘄𝗮𝗿𝘄𝗮𝗿𝗮𝘆𝗲𝗻 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘁𝗮 𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗲𝘆𝗶 𝘁𝗮 𝗺𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗺𝗻𝗮 "𝗠𝗲 𝗸𝗶𝗸𝗲 𝗰𝗶 𝗻𝗲 𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗸𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘇𝘂𝗯𝗮 𝗮𝗺𝗻𝗮?,𝗰𝗶 𝗱𝗮 𝘇𝘂𝗰𝗶?,𝘆𝗮𝘆𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗰𝗲 𝗳𝗮?,𝗵𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗶 𝗸𝗶𝗻 𝗴𝗮𝗷𝗶 𝗱𝗮 𝗴𝗮𝗻𝗶𝗻𝘁𝗮 𝘄𝗮𝘁𝗮𝗿𝗮𝗻𝗮.....𝘄𝗮𝘁𝗮𝗾𝗶𝗹𝗮 𝗱𝗮𝗿𝗲 𝗻𝗲 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗺𝘂𝘀𝘂 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮,𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮 𝗺𝗲𝘆𝗲 𝗻𝗮𝘀𝗮𝗻 𝗵𝗮𝗺𝗺𝗮𝗻𝗸𝘂 𝘇𝗮𝗶 𝗸𝗮𝘄𝗼𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗯𝗯𝗮𝘀 𝗸𝗼𝗱𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮 𝗻𝗲" . 𝗧𝗮𝘆𝗶 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘀𝗼𝗻 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗿𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗮𝗺𝗻𝗮 𝘁𝘂𝗻𝗮𝗻𝗶𝗻 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶,𝗱𝘂𝗸 𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮𝗺𝗮 𝘁𝗮𝘀𝗼 𝗾𝘄𝗮𝗿𝗮𝗶 𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗼 𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮𝗻,𝗱𝗼𝗻 𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗴𝗮𝗻𝘂 𝗺𝗮𝘀𝘂 𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗲𝘀𝗼 𝘁𝗮𝘆𝗶 𝗱𝗮 𝗶𝘁𝗮. "𝗔𝗺𝗺𝗮 𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘆𝗮𝘂𝘀𝗵𝗲?,𝗻𝗶 𝗸𝗼 𝗴𝗼𝗯𝗲 𝗻𝗲 𝗴𝗮𝗻𝗶 𝗻𝗮𝗸𝗲𝘆𝗶 𝘁𝗮𝘆𝗶 𝗻𝗶𝘀𝗮" "𝗦𝗮𝗶 𝗸𝗶𝘆𝗶 𝗳𝗶𝗳𝗳𝗶𝗸𝗲 𝗸𝗶𝗷𝗲 𝗮𝗶 𝘀𝗮𝗿𝗸𝗶𝗻 𝗴𝗮𝗿𝗮𝗷𝗲" 𝗦𝗮𝗱𝗱𝗶𝗾 𝗱𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗼𝘄𝗮 𝗿𝗶𝗾𝗲 𝗱𝗮 𝗹𝗲𝗱𝗮 𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘀𝗵𝗶 𝗱𝗮𝗸𝗲 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗲 𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗺𝗯𝗮𝗿𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗯𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻 𝗸𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘀𝗵𝘂𝗵𝘂𝗿𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗮 𝘀𝘂𝘁𝘂𝗿𝘂 𝗻𝗮 𝗺𝗮𝗻𝘆𝗮𝗻 𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲. 𝗝𝘂𝘆𝗮𝘄𝗮 𝘁𝗮𝘆𝗶 𝘁𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗲𝘀𝗵𝗶 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗯𝗮𝘁𝗮 𝗿𝗮𝗶,𝘀𝗮𝗶 𝘁𝗮 𝘁𝘀𝘂𝗸𝗲 𝗯𝗮𝗸𝗶 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝘁𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝘇𝗮𝘂𝗻𝗮 𝗯𝗮 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗰𝗲𝘄𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶 𝗯𝗮,𝗱𝗼𝗻 𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻 𝗺𝘂𝗱𝗱𝗶𝗻 𝘁𝗮𝗰𝗲 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗮𝗿 𝘇𝗮𝘀𝘂 𝘆𝗶𝘁𝗮 𝘀𝗮'𝗶𝗻𝘀𝗮 𝗻𝗲 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗱𝗱𝗶𝗾,𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗾𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮. "𝗔𝗻𝗻𝗶 𝗸𝗲𝘆 𝗻𝗮 𝘀𝗮𝘀𝘀𝗮𝗻 𝗕𝗕 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾,𝘆𝗮𝗰𝗲 𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮 𝗺𝘂𝘀𝘂 𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶,𝗵𝗮𝗺𝗺𝗮 𝘇𝗮𝗶𝘇𝗼 𝘆𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮". 𝗪𝗮𝗶𝘄𝗮𝘆𝗮𝘄𝗮 𝘁𝗮𝘆𝗶 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗯𝗮𝘄𝗮 𝗮𝗺𝗻𝗮 𝘂𝗺𝗮𝗿𝗻𝗶 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗻𝘂𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗮 𝘁𝗮 𝗮𝗷𝗶𝘆𝗲𝘀𝗵𝗶. "𝗕𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗸𝗮𝗷𝗲 𝗳𝗮 𝘀𝗮𝗶𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗺𝗮𝗹𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗻𝗮 𝗿𝗮𝗸𝗮𝗸𝗮 𝗸𝗮 𝘆𝗶𝘄𝗮 𝗮𝗻𝗻𝗶 𝘀𝗮𝗹𝗹𝗮𝗺𝗮......𝗱𝗼𝗻 𝗯𝗮 𝘇𝗮𝗸𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗮𝗻𝗶 𝗸𝘄𝗮𝗻𝗰𝗶𝘆𝗮 𝗱𝗮 𝘄𝘂𝗿𝗶 𝗯𝗮 𝘆𝗮𝘂......𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗻𝗮 𝗴𝗮𝗷𝗶 𝗱𝗶𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗯𝗮𝗰𝗰𝗶 𝗻𝗮𝗸𝗲 𝗯𝘂𝗾𝗮𝘁𝗮 𝗺𝗲 𝘁𝘀𝗮𝗵𝗼.....𝗸𝗼 𝗳𝗮𝗻𝗻𝗮 𝗵𝗶𝗱𝗶𝗺𝗮𝗿𝗸𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗷𝗶𝗻 𝗺𝘂𝗿𝘆𝗮𝗿𝘁𝗮" 𝗙𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝗿𝗶𝗾𝗼 𝗳𝘂𝗮𝗱 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝗲 𝗾𝗼𝗾𝗮𝗿𝗶𝗻 𝘄𝘂𝗰𝗲𝘄𝗮 𝗸𝗮𝗶 𝘁𝘀𝗮𝘆𝗲 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮. 𝗪𝗮𝗶𝘄𝗮𝘆𝗼𝘄𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗹𝗶 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻 "𝗗𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗶 𝗸𝗮𝘀𝗼.....𝗸𝗮 𝗮𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗸𝗮𝗻𝗸𝗮 𝗵𝗶𝗱𝗶𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗸𝘄𝗮𝘁𝗮 𝗸𝘄𝗮𝘁𝗮 𝗯𝗮𝘁𝗮 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝘁𝘂𝘀𝗵𝗲 𝗸𝗼 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶.....𝘄𝗮𝗶 𝘄𝗮𝗶𝘁 𝗺𝗮......𝘁𝘂𝗸𝘂𝗻𝗻𝗮 𝗸𝗮𝗻𝗮 𝗻𝘂𝗳𝗶𝗻 𝗻𝗶 𝘇𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮 𝗮 𝗴𝗮𝗯𝗮 𝗸𝗮𝗸𝗮𝗶 𝗰𝗮𝗻 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻?" "𝗪𝗮𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶 𝘄𝗮𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶 𝘀𝗮𝗶𝗸𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗮𝗻𝗴𝗼,𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘀𝗮𝗶𝗻𝗮 𝗸𝗮𝗶𝗸𝗮 𝗵𝗮𝗿 𝗰𝗶𝗸𝗶" 𝗬𝗮𝘆𝗶 𝗴𝗮𝗴𝗴𝗮𝘄𝗮𝗿 𝘆𝗮𝗻𝗸𝗮𝗿 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮 𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮,𝗱𝗼𝗻 𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗰𝗲 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶 𝘆𝗮𝘀𝗮𝗻 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗮 𝗳𝘂𝗮𝗱 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗮𝗯𝗶𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲𝘀𝗼 𝗱𝗶𝗻 𝗯𝗮 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝗷𝗮𝗻 𝘇𝗮𝗻𝗰𝗲 𝗯𝗮,𝗸𝗮𝘀𝗮𝗻𝗰𝗲𝘄𝗮𝗿 𝗱𝘂𝗸 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮 𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘀𝘂 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗾𝗼𝗾𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗮 𝗱𝗮𝗻 𝘂𝘄𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗿𝗮𝗻𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮𝗿. 𝗜𝗱𝗮𝗻𝘂 𝘆𝗮 𝘇𝘂𝗯𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮,𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿 𝘇𝗮𝗶𝘆𝗶 𝗺𝗮𝗴𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗶 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮 𝗳𝗮𝘀𝗮,𝘆𝗮 𝗷𝘂𝘆𝗮 𝘇𝘂𝘄𝗮 𝘀𝗮𝘀𝗵𝗲𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗮𝘄𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗻𝘂𝘁𝘀𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗻𝗮𝗻 𝘁𝗮𝘀𝗮. 𝗖𝗮𝗸 𝘆𝗮 𝘁𝘀𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗯 𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮,𝗺𝘂𝗿𝗺𝘂𝘀𝗵𝗶 𝗺𝗲 𝗾𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝘀𝗮𝘂𝘁𝗶 𝘆𝗮 𝘀𝘂𝗯𝘂𝗰𝗲 𝗺𝗮𝘀𝗮,𝘆𝗮 𝘄𝗮𝗶𝘄𝗮𝘆𝗮 𝘆𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗶 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻 "𝗪𝗮𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶 𝘆𝗮𝗿𝗼𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗸𝗮 𝗿𝗮𝗶𝗻𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘄𝗮,𝘄𝗮𝗶 𝗸𝗮 𝗺𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗸𝘄𝗮𝗻𝗮 𝗱'𝗮𝗶 𝗱'𝗮𝗶 𝗵𝗮𝗿 𝗯𝗮𝗸𝘄𝗮𝗶 𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗸𝗮.....𝘁𝘂𝗸𝘂𝗻𝗻𝗮 𝗺𝗮 𝘄𝗮𝗶 𝘄𝗮𝘆𝗲 𝘆𝗮𝗰𝗲 𝗺𝗮𝗸𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗻𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶 𝗻𝗲?,𝗮𝘂𝗿𝗲𝗻 𝗱𝗮𝗻𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗿𝗮𝘄𝗮 𝘀𝗮𝗶 𝗿𝗮𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻 𝘁𝗮𝗿𝗯𝗶𝘆𝘆𝗮 𝗱𝗮 𝘇𝗮𝘀𝘂𝘆𝗶?" "𝗚𝗶𝗱𝗮𝗻 𝘁𝗮𝗿𝗯𝗶𝘆𝘆𝗮?" 𝗙𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻 𝘆𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗱𝗮𝗿𝗶𝘆𝗮𝗿𝘀𝗮,𝗱𝗼𝗻 𝘁𝘂𝗻 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗻𝗮𝗻 𝗵𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝗯𝗮𝗿𝗼 𝗳𝘂𝗮𝗱 𝗱𝗶𝗻 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮𝘀𝗼𝗻 𝘆𝗮𝗴𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗮𝗯𝘂 𝗺𝗲 𝗸𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝘀𝗮 𝘀𝗮𝗺.....𝘆𝗮𝗻𝗮𝘀𝗼𝗻 𝗶𝗱𝗮𝗻𝗺𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗻 𝗮 𝗺𝗮𝘇𝗮𝘂𝗻𝗶𝗻 𝘄𝗮𝘀𝗮 𝘀𝗼 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝘆𝗮𝗷𝗶 𝘀𝗼𝘀𝗮𝗶 𝗮 𝗿𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗮𝘂𝗿𝗲 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗺𝗮𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻𝗰𝗶. "𝗧𝗼 𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗯𝗮 𝗹𝗶𝘀𝘀𝗮𝗳𝗶 𝘆𝗮𝗹𝗹𝗮𝗯𝗮𝗶" 𝗬𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘁𝗮𝗻𝗮 𝗷𝗮𝗻 𝗵𝗮𝗻𝗻𝘂𝗻𝘀𝗮 𝘀𝘂𝗻𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗮𝘀𝗮𝘄𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶. 𝗗𝗮𝗴𝗮 𝗾𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲 𝗱𝗮𝗶 𝗱𝗼𝗹𝗲 𝗶𝗱𝗮𝗻𝘂 𝘆𝗮 𝘇𝘂𝗯𝗮𝘄𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻,𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘄𝗮𝗻𝗸𝗮 𝗱𝗼𝗻 𝗱𝗮𝗺𝗮 𝘀𝗮𝗯𝗼𝗻𝘀𝗵𝗶 𝗻𝗲 𝗱𝘂𝗸 𝗱𝗮𝗿𝗲,𝗯𝗮𝗿𝗲 𝘆𝗮𝘂 𝗱𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝘄𝘂𝗻𝗶 𝘇𝗶𝗿𝗴𝗮 𝘇𝗶𝗿𝗴𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗯𝘂 𝗴𝗮𝗶𝗿𝗮 𝗯𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮𝗹𝗶𝗹𝗶 𝗱𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝘆𝗮 𝗮𝘇𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮. 𝗬𝗮𝗷𝗶 𝗱𝗮𝗱𝗶𝗻 𝗷𝗶𝗸𝗶𝗻𝘀𝗮 𝘀𝗼𝘀𝗮𝗶,𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝘆𝗮 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗼 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶. 𝗞𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗱𝗮𝘇𝘂 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝘆𝗮 𝗱𝗶𝗻𝗴𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘆𝗮𝘄𝗮,𝘀𝗮𝗶 𝗴𝗮𝘀𝗵𝗶 𝘆𝗮 𝗳𝗶𝘁𝗼 𝗳𝗲𝘀 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗼𝗹𝗶𝘃𝗲 𝗰𝗼𝗹𝗼𝗿,𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗵𝘂𝗹𝗮 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗹𝗳 𝗰𝗼𝘃𝗲𝗿 𝘀𝗵𝗼𝗲 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗮𝗻 𝗽𝗮𝗹𝗲 𝘀𝗮𝗴𝗲 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗰𝗲 𝗾𝘄𝗮𝗿𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝗼𝗹𝗶𝘃𝗲 𝗰𝗼𝗹𝗼𝗿 𝗱𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗺𝗮𝘁𝗰𝗵𝗶𝗻𝗴. 𝗗𝗮𝗴𝗮 𝘀𝗵𝗶 𝗵𝗮𝗿 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝘀𝘂𝗻𝘆𝗶 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗯𝗮𝗹𝗮'𝗶𝗻 𝗾𝘄𝗮𝗿𝗲𝘄𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗶𝘆𝗮 𝗵𝗮𝗱𝗮 𝗰𝗼𝗹𝗼𝗿 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝘀𝘂𝘁𝘂𝗿𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘇𝗮𝘂𝗻𝗮 𝗮 𝗷𝗶𝗸𝗶. 𝗗𝘂𝗸 𝗱𝗮 𝗮 𝘆𝗮𝗻𝘇𝘂 𝘀𝗵𝗶 𝗯𝗮𝗶𝗱𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗹𝗼𝗸𝗮𝗰𝗶𝗻,𝗱𝗼𝗻 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮 𝗽𝗿𝗼𝗳𝗲𝘀𝘀𝗶𝗼𝗻𝗮𝗹 𝗰𝗹𝗼𝘀𝗲𝘁 𝗼𝗿𝗴𝗮𝗻𝗶𝘀𝗲𝗿 𝗱𝗮𝗸𝗲 𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗶𝘆𝗶 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮𝘀𝘂 𝗻𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗵𝗼𝗻 𝘀𝗮𝘁𝗶𝘁𝘁𝗶𝗸𝗮,𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗮𝗷𝗶𝘆𝗲𝘀𝘂 𝗻𝗲 𝗮 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗴𝘂𝗿𝗮𝗿𝗲𝗻 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗶𝘆𝗮 𝘇𝘂𝘄𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘀𝗮𝘁𝗶 𝗸𝗼 𝘀𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮,𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗮𝗹𝗯𝗮𝘀𝗵𝗶𝗻𝘀𝗮 𝗱𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗸𝗼𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻𝗻𝗶 𝗯𝗮𝗶𝘆𝗶 𝗮𝗶𝗸𝗶𝗻𝘀𝗮 𝗯𝗮. 𝗦𝗮𝗶𝗱𝗮𝗶 𝗱𝘂𝗸 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗱𝘂𝗸 𝗿𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗺𝘂 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮 𝗵𝗮𝗱𝗮𝘄𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗱𝗿𝗲𝘀𝘀𝗶𝗻𝗴 𝘁𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗮𝘁 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗸𝗲 𝗴𝗮𝗻𝗲𝘄𝗮. 𝗬𝗮𝗮𝗮𝗻 𝗵𝗮𝗹𝗶𝗻𝘀𝗮,𝗺𝗮𝘆𝗲 𝗻𝗲 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗶𝘆𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗿𝗮𝘄𝗮 𝗷𝗶𝗸𝗶 𝗮𝗱𝗼 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻𝗰𝗶 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝘁𝗮𝗸𝗮 𝗺𝘂𝗵𝗶𝗺𝗺𝗶𝘆𝗮𝗿 𝗿𝗮𝘄𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗳𝘂𝘀𝗴𝗮𝗿 𝗵𝗮𝗻𝗸𝘂𝗹𝗮𝗻 '𝘆𝗮𝗺𝗺𝗮𝘁𝗮𝗻 𝗱𝗮𝗸𝗲 𝗾𝘂𝗹𝗮𝗳𝘂𝗰𝗶𝗻𝘀𝗮. "𝗠𝗮 𝘀𝗵𝗮 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵.... .𝗽𝗲𝗿𝗳𝗲𝗰𝘁 𝗺𝗮𝘁𝗰𝗵" 𝗙𝘂𝗮𝗱 𝗱𝗶𝗻 𝘆𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗶 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗳𝗮 𝗴𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗯𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻 𝗿𝗶𝗴𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘀𝗵𝗮 𝗮𝗶𝗸𝗶. 𝗦𝗵𝗶 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻 𝗸𝗮𝗹𝗹𝗼𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲,𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝗮𝗺𝘀𝗵𝗲𝘀𝗵𝗶 𝗺𝗮𝘁𝘂𝗾𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗸𝗲 𝘀𝘂𝗿𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗷𝗶𝗻𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮 𝗯𝗮𝘀𝗵𝗶. 𝗡𝗲𝗺𝗮𝗻 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝘆𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮𝘆𝗶,𝘀𝗮𝗶 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗯𝗮𝗻𝘇𝗮 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶,𝘆𝗮 𝗳𝗶𝗱𝗱𝗮 𝘄𝗮𝘆𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗶𝗿𝗮 𝗮𝗯𝗯𝗮..... "𝗔𝗯𝗯𝗮 𝗺𝘂𝗻 𝗴𝗮𝗺𝗮,𝗼𝗸𝗮𝘆 𝘁𝗼" 𝗠𝗮𝗶𝗱𝗮 𝘄𝗮𝘆𝗮𝗿 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗮𝗹𝗷𝗶𝗵𝘂𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲 "𝗦𝗮𝗶𝗸𝗮 𝘁𝗮𝘀𝗼 𝗺𝘂𝗷𝗲 𝗮𝘆𝗶 𝗺𝗮𝗸𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮𝗻 𝗴𝗶𝗱𝗮𝗻 𝗮𝘂𝗿𝗲". 𝗬𝗮 𝗳𝘂𝗿𝘁𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗱𝗮𝗿𝗶𝘆𝗮𝗿𝘀𝗮. 𝗗𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗹𝗼 𝘆𝗮𝗯𝗶 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻 𝗴𝗮𝗹𝗮𝗹𝗮 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗮𝗻𝘀𝗮. "𝗞𝗮 𝗳𝗮𝗿𝗮 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗶𝘆𝗮𝗸𝗮𝗻𝗸𝗮 𝗳𝗮......𝗳𝗮𝗱𝗮 𝗰𝗲 𝗺𝗮𝗸𝗮 𝗮𝗸𝗮𝘆𝗶 𝗺𝘂𝗻 𝗿𝗮𝗯𝘂?" 𝗬𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗳𝗮𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗿𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘁𝘂𝗻𝗶 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗶 𝗾𝗼𝗳𝗮,𝗱𝗼𝗹𝗲 𝘆𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲 𝗵𝗮𝗿 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗿𝗮𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗻 𝘆𝗮 𝗶𝘀𝗮 𝗵𝗮𝗸𝗮. 𝗦𝗵𝗶 𝘀𝗮𝗺 𝗯𝗮𝗶 𝗸𝗮𝘄𝗼 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗮𝗯𝘂𝗻 𝘇𝗮𝗶 𝗷𝘂𝘆𝗲 𝗯𝗮,𝗱𝗮 𝘁𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗮 𝗺𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝗯𝗮𝗿𝗶 𝗮𝘆𝗶 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶?,𝘁𝗮𝗯𝗯𝗮𝘀 𝗱𝗮 𝗿𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗼 𝘄𝗮𝗻𝗰𝗮𝗻 𝘁𝘀𝗼𝗵𝗼𝗻 𝗻𝗮𝘁𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝗸𝗶𝗿𝗮 𝗺𝗮'𝗮𝗶𝗸𝗮𝘁𝗮𝗻𝘀𝗮 𝘀𝘂 𝘀𝗵𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗿𝗮 𝗮𝘂𝗿𝗲𝗻 𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗮 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻,𝘆𝗮 𝘁𝗮𝘁𝘁𝗮𝗿𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘁𝗮𝗳𝗶𝘆𝗮𝗿𝘀𝗮 𝘀𝗮𝗶 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗴𝗮𝗺𝗮 𝘂𝘇𝘂𝗿𝗼𝗿𝗶𝗻𝘀𝗮 𝘁𝘂𝗸𝘂𝗻𝗻𝗮,𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗶𝗻 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗿𝘂𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗸𝗶 𝘆𝗮 𝗺𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗹𝗮𝗺𝗮𝗿𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝘀𝗲𝗿𝗶𝗼𝘂𝘀. 𝗤𝘄𝗮𝗾𝘄𝗾𝘄𝗮𝗿𝗮𝗻 𝗺𝗼𝘁𝘀𝗶 𝗸𝗮𝘀𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗮𝗯𝗯𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗻𝗮𝘀𝗶𝗵𝗮 𝗴𝗮𝗺𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗻𝘁𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗵𝗮𝗹𝗮𝘆𝗲𝗻 𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗮𝗸𝗲 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗮𝘀𝘂 𝗹𝗮𝗳𝗶𝘆𝗮,𝗸𝘂𝗻𝘆𝗮 𝗱𝗮 𝘁𝗮𝘂𝘀𝗮𝘆𝗶𝗻 𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝘀𝗵𝗶 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲𝗻 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲. 𝗬𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗶,𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗮𝗶 𝗻𝗲 𝗺𝗮𝘀𝘂 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗳𝗮 𝗴𝗮 𝗺𝘂𝘁𝘂𝗺𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮 𝗱𝗮 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲𝗻 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲 𝗮𝘂𝗿𝗲 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗻𝗮 𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲.....𝗮𝘂𝗿𝗲 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮𝘆𝗶 𝗶𝗿𝗶𝗻 𝗻𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮,𝗯𝗮𝘄𝗮𝗶.𝗺𝘂𝘁𝘂𝗺 𝗶𝗿𝗶𝗻𝘀𝗮 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗶𝗷𝗶𝗻 𝘀𝗵𝗶 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗮𝗸𝗸𝗲𝗻 𝗹𝗼𝗸𝗮𝗰𝗶𝗻 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗯𝗮 𝗯𝗮𝗿𝗲 𝗻𝗮 𝘄𝗮𝘁𝗮.....𝘄𝗮𝘁𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗶𝗹𝗹𝗮𝗰𝗲𝘁𝗮 𝗻𝗲 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗱𝗼𝗻 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗶𝘁𝗮 𝗱𝗮𝗯𝗶'𝘂𝗻𝘁𝗮.......𝘆𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗻𝘂𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗴𝗶𝗿𝗺𝗮 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻 𝗮𝗱𝗮𝗱𝗶𝗻 𝗸𝘂𝘀𝗸𝘂𝗿𝗲𝗻 𝗱𝗮𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗳𝗸𝗮 𝗮 𝗿𝗮𝘆𝘂𝘄𝗮𝗿𝘁𝗮. "𝗞𝗮𝗱𝗮 𝗸𝘂 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗯𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗴𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗲𝗻 𝗺𝗮𝗿𝗶𝘆𝗮 𝗯𝗮" 𝗔𝗻𝗻𝗶 𝘁𝗮 𝗳𝗮𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝗺𝗶𝗾𝗲 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗺𝘂𝘀𝘂 𝘀𝗮𝗹𝗹𝗮𝗺𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗳𝗲,𝗾𝗮𝘀𝗮 𝗾𝗮𝘀𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮 𝗷𝗶𝗳𝗮𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗼𝘂𝗾 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗿𝗮. 𝗝𝗶 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝗷𝗮𝘄𝗼𝘀𝗵𝗶 𝘆𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗴𝗲𝘀𝗵𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝘆𝗮𝘂,𝗱𝘂𝗸 𝗻𝗮 𝗺𝗲𝘆𝗲 𝘇𝗮𝗶 𝘀𝗮𝗸𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗶𝘆𝗮𝘆𝗲 𝘇𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗱𝗼𝗴𝗼𝗻 𝗷𝗮𝘄𝗮𝗯𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗺 𝘀𝗵𝗶 𝗯𝗮𝗶𝗱𝗮 𝗮𝗹𝗮𝗾𝗮 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶?. Duniyata na kudi ne 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 12 Page 12 Har qasan ranta takejin wata izza tana mamayarta sanda take takowa inda yake zaune yana jiran fitowarta. Kansa a qasa,baima dagashi ba ballantana ya qarewa ginin daya zuba kudi da kudinsa akayi kallo. Burinsa daya yayi ya fita ya wuce inda zaije ya kwanta ya huta,don ya gaji matuqa......ga bikin bude company nan da kwana uku a gabansa,gobe da jibi dinma ya tabbatar baida hutu saboda baqinsa zasu fara sauka kuma. Har bayason kallon komai na gidan,yana tuna masa yadda ta dinga uzzurawa kowa da kalar a siya kaza a saka mata kaza,bayan komai a rubuce yake a hannun kamfanin da ya bawa kwangilar ginin. "Zaku wuce kenan?" Ta tambayeshi bayan sun gaisa ba tare data damu ta tambayeshi komai ba. Kansa ya gyada a hankali,ta gyara zamanta tana kiran sunansa kai tsaye "Muhammad.....inaso ka bani hankalinka da kyau,magana zan maka me muhimmancin da itace ta biyu a rayuwarka da zan sakeyi maka ita". Baice komai ba bai kuma motsa ba,illa dai kawai ya tattara kunnuwansa yana jiran DA WANNE ZATA ZO?. "ka san wa na aura maka?.....zabin raina" Ta masa tambaya da amsa gaba daya. Yanayin datayi maganar ya sakashi daga fararen idanunsa masu tarin kwarjini ya dan kalleta,akaci sa'a itama shi take kallo,sai ta jinjina masa kai "Eh......itadin zabi na ce,saba mata wulaqantata ko tozartata tamkar ni mahaifiyarka mariya ka yiwa hakan.......ina me baka umarni ka riqeta kayi mu'amala da ita kamar yadda kowanne namiji yake mu'amala da matarsa da yakeso.......zan iya komai akan cusguna mata muddin kayi......idan nace komai kuwa ciki harda fushi dakai me tsanani". Bai shirya ba a wannan karon ya daga kansa da sauri ya sake kallonta "Wacece ita?......meye shirinta?.......dame ta shigo?" Sune tambayoyin da har a cikin mota yakai maimaitawa cikin ransa. Cikin kowanne jijiya dake kai jini zuwa zuciyarsa cike yake qyamar yarinyar da qaqqarfan zargi a kanta,baya shinshino alkhairi ko qwaya daya a kanta,ta kowacce fuska ITA DIN SHARRI CE. Tun daga ranar daya fahimta itace zabin maamah data fara saukar masa da zazzafan umarni da maganganu a kanta.....tun daga ranar daya fahimci ita dince dai wannan wadda tayi fashin online wa kamfaninsa kudaden da ko namiji me taurararriyar zuciya da tsananin taurin kai iyakarsa kenan......tun a wancan ranar ya sake tabbatarwa kansa akwai wasu abubuwan ma masu yawa da bai sani ba a kanta.....amma koma meye.....koma mene zai tabbatar ya koya mata darasin rayuwa.......zai sauya mata DUNIYARTA da kalar horon da ba zata sake gigin aikata irin rayuwarta ta baya ba......zai sakata tasan meye ainihin TARBIYYA GIRMAMAWA KUNYA DA GASKIYA. Tsaiwar motarsu shine abinda ya fincikoshi daga duniyar tunani zuwa ta zahiri. Ya waiwaya yadan dubi farouq dake qoqarin baiwa guard din da sukazo dasu umarnin yadda shigarsu zata kasance. Ko sau daya farouq bai katse masa tunanin ba ko ya sako masa hira. Wani irin mutum ne daya karanceshi ya kuma fahimceshi sosai,yasan babu yadda zai shiga wajen mahaifiyarsa bai fito da guzurin damuwa ba,shiga lafiya da fita lafiya duka tamkar sa'a ce a wajensu,wannan ya sanya bai fiya masa katsalandan akan kowanne yanayi yaga ya fito dashi ba. A nutse ya dinga bin tsarin ginin da kallo. Baisan inda farouq ya samo gidan ba,don basa cikin gidajensa sam sam,saidai kuma ya cika da mamakin yadda tun daga farfajiyar gidan ta zama sak irin yanayin ginin da yake so,kuma zabinsa. "Alhamdulillah" Farouq ya furta yana dubansa,shima shi din ya kalla,yaja numfashi kadan sannan yace "Shikenan?,hankalinka ya kwanta?,saika wuce gida ka kwanta" Murmushi kadan farouq ya saki,ya miqa hannu bayansu. Kyakkyawan bamboo basket ya fiddo,wanda aka yiwa wani irin ado da tsari,can qasan ransa yana jin tsoro sosai kan yadda yake ganin rashin baiwa komai daya shafi auren muhimmanci daga wajen fu'ad din. Baya jin tsoro akan zaiyi wani maras kyau ba......saidai bashi da tabbaci ko guarantee din zaiyi komai daidai. "Ga tsarabar amarya" Ya fada yana ajiye basket din a tsakaninsu. Harara ya watsawa farouq din sannan ya fara yunqurin bude murfin motar,sai daya fice din sannan yace masa "An gaya maka harda ni a wannan wasan yaran?" "Please mana fu'ad,waye ya gaya maka ana shiga wajen amarya haka?,take it.......it's sunnah fa" Baiko waiwayeshi ba ya fara nufar hanyar dake nuni da shine ainihin qofar shiga gidan gaba daya. "Aurenma sunna ne kuma jihadi zanyi". "Jihadin daukan fansa?" Ya fada a ransa a fili yana dariya qasa qasa. Murfin motar ya balle shima ya biyo bayansa duk da baida niyyar shiga cikin gidan don duka ba tsarinsu bane,a qasan ransa yana fata da addu'ar Allah yasa reshe ya juye da mujiya. Dab da bakin kyakkyawar qofar ya dukansu suka tsaya kamar wadanda aka yiwa umarni,a nutse farouq ya sunkuya ya ajiye basket din sannan ya dago yana duban tsakiyar idanun fu'ad. Koda baiyi magana ba fu'ad din ya fahimci magana yake gaya masa da idon. Farouq ya cancanci kowacce girmamawa da qauna,don haka sai ya sunkuya kawai ya dauki basket din yaci gaba da takawa "Muhammad" Yau farouq din ya kirashi da zallar sunansa da ya jima da manta rabon da yaji ya kirashi dashi. Waiwayowa yayi suka hada idanu. "Don Allah......kayi dukkan abinda ya dace,ka riqeta yadda ake riqe kowacce macen aure". Idanu fu'ad ya lumshe yana budesu lokaci guda,shima nasa idanun cikin na farouq "Banyi maka alqawarin zaman aure irin na kowanne miji da mata ba......ban maka alqawarin cewa zataji dadi kaman kowacce mace ba.......amma zan kyautata idan ta kyautata.......manufar aurendai kuma banajin zata canza,dole tayi wannan karatun,saidai shima zaizo a duk yanayin data zabi yazo" Daga haka ya juya yana shigewa don bayason farouq ya sake neman karyashi da kowacce kalma daga bakinsa. Ba zata iya cewa ga yanayin data wanzu a ciki ba tunda su momma bahijja da sauran mutanen da basufi ashirin ba suka juya suka barta a gidan da suke fama jaddada kyau da tsaruwa da kuma dukiyar dake ciki wanda babu daya a ciki da yayi mata. Ko bayan wucewarsun shuru ne yaci gaba da wanzuwa cikin gidan,jifa jifa tana jin tamkar haushin kare daga dan nesa kadan daga inda take. Ko sau daya bata janye mayafin kanta ba,saima qara duqunquna da tayi tana daga zaunen saboda yadda azababben zazzabi yake sake sauko mata. Wani irin tsoro mara misali yana saukar mata,kalar tsoron da bata taba jin irinsa ba. Empty takejin kwanyarta,kaman an kwashe komai dake ciki an zuba tsoro da rashin nutsuwa,sai muryar matar dake da sunan surukarta a yanzu wadda keta mata kai kawo ita da dukkan dokokinta cikin tsakiyar kanta tamkar ana mata bita kada ta mance. "Assalamu alaikum warahmatullah" Ya furta qasa qasa yadda baya zaton akwai wanda zai jishi,saidai don kawai yasan sallamar wajibi ce a musulunci koda babu kowa cikin gida,Ko ina da haske tarwai tamkar rana,ba wani qwai da yake a kashe. Da idanu yake bin parlor din da kallo,wani tsari me kyau da ya dace da ra'ayinsa tamkar dashi farouq yayi shawara wajen tsarin gidan,tun daga kan color na paint dana furniture din. A nutse yaci gaba da takawa cikin parlor din hannunsa zube a aljihun shaddarsa. Bai tsaya ba sai daya isa tsakiyar parlor din,ya aza basket din hannunsa saman wani dan qaramin table dake tsakiyar falon. Juyawa yayi yana ci gaba da bin kowanne makunnin fitila dake falon yana kasheshi daya bayan daya,har sai da hasken daya rage kawai dake farfajiyar gidan wanda ke ratsowa ta lafiyayyun curtains din da aka zagaye falon dashi. Sai daya tabbatar ba wani sauran abinda ya rage sannan ya sauya akalarsa zuwa upstairs da yake kyautatan zaton a can ne sashensa yake. Stairs na farko kadai ya taka wayarsa tayi qara. Ya dakata ya sanya hannunsa a aljihunsa yana cirota da niyyar kasheta gaba daya,don a matuqar gajiye yake,baya buqatar duk wani abu da zaiyi disturbing nasa. Sanda ya bude da nufin kashewar saqo ya cika screen na wayarsa. *_welcome home mr jadda,Its strongly warning Cease all preparation,Stop all activities,good night,have a nice night_*. Maimaita karanta saqon yayi kusan sau uku,zuwa yanzu ranshi ya fara baci,ya kuma hango zallar rainin wayo daya fara shiga cikin lamarin. Koma su waye suna bibiye da duk wani motsi nasa kenan?. A irin wannan saqon da suke aike mishi,ya tabbatar inda suna da ikon cimmasa da tuni sun cimmasa din. Da baya ya dawo ya zauna saman daya daga cikin kujerun falon wadda tafi kusa da stairs dinsa. Mutum uku ya nema,ya aike musu da komai,sannan ya saka binciken cikin schedule dinsa na gobe,ya kashe wayar ya jefa a aljihu ya miqe a nutse yana wucewa saman. Babban parlor ne da akayi masa wani tsari na musamman,wanda ke dauke da dining area well designed,sai dakuna bedroom biyu da Master room guda daya dake da lafiyayyen balcony da zai baka daman ganin gidan gaba daya gaba da baya. Abinda ya bashi mamaki komai nasa an jera masa,kayanshi da komai nasa,abinda farouq kadai bai taba ba abinda ya shafi dakin sirrinsa dake wancan gidan nasu. Master bedroom din ya zaba,ya tura ya shiga yana rage hasken fitilun,ya qarasa a hankali ya zauna daga bakin sofa bed ya ware hannayensa dake saman cinyarsa yana karanto addu'o'in wanzuwa cikin sabon muhalli *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 13 Har qasan ranta takejin wata izza tana mamayarta sanda take takowa inda yake zaune yana jiran fitowarta. Kansa a qasa,baima dagashi ba ballantana ya qarewa ginin daya zuba kudi da kudinsa akayi kallo. Burinsa daya yayi ya fita ya wuce inda zaije ya kwanta ya huta,don ya gaji matuqa......ga bikin bude company nan da kwana uku a gabansa,gobe da jibi dinma ya tabbatar baida hutu saboda baqinsa zasu fara sauka kuma. Har bayason kallon komai na gidan,yana tuna masa yadda ta dinga uzzurawa kowa da kalar a siya kaza a saka mata kaza,bayan komai a rubuce yake a hannun kamfanin da ya bawa kwangilar ginin. "Zaku wuce kenan?" Ta tambayeshi bayan sun gaisa ba tare data damu ta tambayeshi komai ba. Kansa ya gyada a hankali,ta gyara zamanta tana kiran sunansa kai tsaye "Muhammad.....inaso ka bani hankalinka da kyau,magana zan maka me muhimmancin da itace ta biyu a rayuwarka da zan sakeyi maka ita". Baice komai ba bai kuma motsa ba,illa dai kawai ya tattara kunnuwansa yana jiran DA WANNE ZATA ZO?. "ka san wa na aura maka?.....zabin raina" Ta masa tambaya da amsa gaba daya. Yanayin datayi maganar ya sakashi daga fararen idanunsa masu tarin kwarjini ya dan kalleta,akaci sa'a itama shi take kallo,sai ta jinjina masa kai "Eh......itadin zabi na ce,saba mata wulaqantata ko tozartata tamkar ni mahaifiyarka mariya ka yiwa hakan.......ina me baka umarni ka riqeta kayi mu'amala da ita kamar yadda kowanne namiji yake mu'amala da matarsa da yakeso.......zan iya komai akan cusguna mata muddin kayi......idan nace komai kuwa ciki harda fushi dakai me tsanani". Bai shirya ba a wannan karon ya daga kansa da sauri ya sake kallonta "Wacece ita?......meye shirinta?.......dame ta shigo?" Sune tambayoyin da har a cikin mota yakai maimaitawa cikin ransa. Cikin kowanne jijiya dake kai jini zuwa zuciyarsa cike yake qyamar yarinyar da qaqqarfan zargi a kanta,baya shinshino alkhairi ko qwaya daya a kanta,ta kowacce fuska ITA DIN SHARRI CE. Tun daga ranar daya fahimta itace zabin maamah data fara saukar masa da zazzafan umarni da maganganu a kanta.....tun daga ranar daya fahimci ita dince dai wannan wadda tayi fashin online wa kamfaninsa kudaden da ko namiji me taurararriyar zuciya da tsananin taurin kai iyakarsa kenan......tun a wancan ranar ya sake tabbatarwa kansa akwai wasu abubuwan ma masu yawa da bai sani ba a kanta.....amma koma meye.....koma mene zai tabbatar ya koya mata darasin rayuwa.......zai sauya mata DUNIYARTA da kalar horon da ba zata sake gigin aikata irin rayuwarta ta baya ba......zai sakata tasan meye ainihin TARBIYYA GIRMAMAWA KUNYA DA GASKIYA. Tsaiwar motarsu shine abinda ya fincikoshi daga duniyar tunani zuwa ta zahiri. Ya waiwaya yadan dubi farouq dake qoqarin baiwa guard din da sukazo dasu umarnin yadda shigarsu zata kasance. Ko sau daya farouq bai katse masa tunanin ba ko ya sako masa hira. Wani irin mutum ne daya karanceshi ya kuma fahimceshi sosai,yasan babu yadda zai shiga wajen mahaifiyarsa bai fito da guzurin damuwa ba,shiga lafiya da fita lafiya duka tamkar sa'a ce a wajensu,wannan ya sanya bai fiya masa katsalandan akan kowanne yanayi yaga ya fito dashi ba. A nutse ya dinga bin tsarin ginin da kallo. Baisan inda farouq ya samo gidan ba,don basa cikin gidajensa sam sam,saidai kuma ya cika da mamakin yadda tun daga farfajiyar gidan ta zama sak irin yanayin ginin da yake so,kuma zabinsa. "Alhamdulillah" Farouq ya furta yana dubansa,shima shi din ya kalla,yaja numfashi kadan sannan yace "Shikenan?,hankalinka ya kwanta?,saika wuce gida ka kwanta" Murmushi kadan farouq ya saki,ya miqa hannu bayansu. Kyakkyawan bamboo basket ya fiddo,wanda aka yiwa wani irin ado da tsari,can qasan ransa yana jin tsoro sosai kan yadda yake ganin rashin baiwa komai daya shafi auren muhimmanci daga wajen fu'ad din. Baya jin tsoro akan zaiyi wani maras kyau ba......saidai bashi da tabbaci ko guarantee din zaiyi komai daidai. "Ga tsarabar amarya" Ya fada yana ajiye basket din a tsakaninsu. Harara ya watsawa farouq din sannan ya fara yunqurin bude murfin motar,sai daya fice din sannan yace masa "An gaya maka harda ni a wannan wasan yaran?" "Please mana fu'ad,waye ya gaya maka ana shiga wajen amarya haka?,take it.......it's sunnah fa" Baiko waiwayeshi ba ya fara nufar hanyar dake nuni da shine ainihin qofar shiga gidan gaba daya. "Aurenma sunna ne kuma jihadi zanyi". "Jihadin daukan fansa?" Ya fada a ransa a fili yana dariya qasa qasa. Murfin motar ya balle shima ya biyo bayansa duk da baida niyyar shiga cikin gidan don duka ba tsarinsu bane,a qasan ransa yana fata da addu'ar Allah yasa reshe ya juye da mujiya. Dab da bakin kyakkyawar qofar ya dukansu suka tsaya kamar wadanda aka yiwa umarni,a nutse farouq ya sunkuya ya ajiye basket din sannan ya dago yana duban tsakiyar idanun fu'ad. Koda baiyi magana ba fu'ad din ya fahimci magana yake gaya masa da idon. Farouq ya cancanci kowacce girmamawa da qauna,don haka sai ya sunkuya kawai ya dauki basket din yaci gaba da takawa "Muhammad" Yau farouq din ya kirashi da zallar sunansa da ya jima da manta rabon da yaji ya kirashi dashi. Waiwayowa yayi suka hada idanu. "Don Allah......kayi dukkan abinda ya dace,ka riqeta yadda ake riqe kowacce macen aure". Idanu fu'ad ya lumshe yana budesu lokaci guda,shima nasa idanun cikin na farouq "Banyi maka alqawarin zaman aure irin na kowanne miji da mata ba......ban maka alqawarin cewa zataji dadi kaman kowacce mace ba.......amma zan kyautata idan ta kyautata.......manufar aurendai kuma banajin zata canza,dole tayi wannan karatun,saidai shima zaizo a duk yanayin data zabi yazo" Daga haka ya juya yana shigewa don bayason farouq ya sake neman karyashi da kowacce kalma daga bakinsa. Ba zata iya cewa ga yanayin data wanzu a ciki ba tunda su momma bahijja da sauran mutanen da basufi ashirin ba suka juya suka barta a gidan da suke fama jaddada kyau da tsaruwa da kuma dukiyar dake ciki wanda babu daya a ciki da yayi mata. Ko bayan wucewarsun shuru ne yaci gaba da wanzuwa cikin gidan,jifa jifa tana jin tamkar haushin kare daga dan nesa kadan daga inda take. Ko sau daya bata janye mayafin kanta ba,saima qara duqunquna da tayi tana daga zaunen saboda yadda azababben zazzabi yake sake sauko mata. Wani irin tsoro mara misali yana saukar mata,kalar tsoron da bata taba jin irinsa ba. Empty takejin kwanyarta,kaman an kwashe komai dake ciki an zuba tsoro da rashin nutsuwa,sai muryar matar dake da sunan surukarta a yanzu wadda keta mata kai kawo ita da dukkan dokokinta cikin tsakiyar kanta tamkar ana mata bita kada ta mance. "Assalamu alaikum warahmatullah" Ya furta qasa qasa yadda baya zaton akwai wanda zai jishi,saidai don kawai yasan sallamar wajibi ce a musulunci koda babu kowa cikin gida,Ko ina da haske tarwai tamkar rana,ba wani qwai da yake a kashe. Da idanu yake bin parlor din da kallo,wani tsari me kyau da ya dace da ra'ayinsa tamkar dashi farouq yayi shawara wajen tsarin gidan,tun daga kan color na paint dana furniture din. A nutse yaci gaba da takawa cikin parlor din hannunsa zube a aljihun shaddarsa. Bai tsaya ba sai daya isa tsakiyar parlor din,ya aza basket din hannunsa saman wani dan qaramin table dake tsakiyar falon. Juyawa yayi yana ci gaba da bin kowanne makunnin fitila dake falon yana kasheshi daya bayan daya,har sai da hasken daya rage kawai dake farfajiyar gidan wanda ke ratsowa ta lafiyayyun curtains din da aka zagaye falon dashi. Sai daya tabbatar ba wani sauran abinda ya rage sannan ya sauya akalarsa zuwa upstairs da yake kyautatan zaton a can ne sashensa yake. Stairs na farko kadai ya taka wayarsa tayi qara. Ya dakata ya sanya hannunsa a aljihunsa yana cirota da niyyar kasheta gaba daya,don a matuqar gajiye yake,baya buqatar duk wani abu da zaiyi disturbing nasa. Sanda ya bude da nufin kashewar saqo ya cika screen na wayarsa. *_welcome home mr jadda,Its strongly warning Cease all preparation,Stop all activities,good night,have a nice night_*. Maimaita karanta saqon yayi kusan sau uku,zuwa yanzu ranshi ya fara baci,ya kuma hango zallar rainin wayo daya fara shiga cikin lamarin. Koma su waye suna bibiye da duk wani motsi nasa kenan?. A irin wannan saqon da suke aike mishi,ya tabbatar inda suna da ikon cimmasa da tuni sun cimmasa din. Da baya ya dawo ya zauna saman daya daga cikin kujerun falon wadda tafi kusa da stairs dinsa. Mutum uku ya nema,ya aike musu da komai,sannan ya saka binciken cikin schedule dinsa na gobe,ya kashe wayar ya jefa a aljihu ya miqe a nutse yana wucewa saman. Babban parlor ne da akayi masa wani tsari na musamman,wanda ke dauke da dining area well designed,sai dakuna bedroom biyu da Master room guda daya dake da lafiyayyen balcony da zai baka daman ganin gidan gaba daya gaba da baya. Abinda ya bashi mamaki komai nasa an jera masa,kayanshi da komai nasa,abinda farouq kadai bai taba ba abinda ya shafi dakin sirrinsa dake wancan gidan nasu. Master bedroom din ya zaba,ya tura ya shiga yana rage hasken fitilun,ya qarasa a hankali ya zauna daga bakin sofa bed ya ware hannayensa dake saman cinyarsa yana karanto addu'o'in wanzuwa cikin sabon muhalli. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 14 15 Da farko maganar taso yiwa maamah din banbarakwai,amma koda ta tuna wacece hajja a wajen ta da kuma tata fafutukar da suka gama yi tare suke ma kuma kanyin sai taji wannan din ba komai bane.....ai rama halasci sai dan halak,banda ma plan din da take dashi batajin zai zama wani abun damuwa don laila zata zauna gidan. Ta tabbatar bata da matsala da laila,ko ita din tana iya zama me sanya musu idanu akan plan dinsu. "Kada ki damu hajja,ni ba abinda bakiyimin ba,kinfi qarfin haka a wajena.....hakanma qarin samun tsaro ne,don yau nakeson tura zuwaira ta zauna dasu ta dinga sakamin ido akan komai". Murmushin qasan zuciya hajja ta saki,bahago shu'umi ne fiye da yadda take zato,ya gaya mata,ya sake gaya mata dama ba damar musu......mariya ba zata iya musanta mata ba. "Na gode sosai mariya....Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci". Kai ta girgiza tana murmushi "Ba wannan tsakaninmu,kinfi qarfin komai a wajena......ko yau tana iya shiryawa sai zuwaira ta biyo ta dauketa su wuce,don banason magariba tayi basu isa gidan ba" Ta fada tana daga wayarta ta duba lokaci. So samu ace tun da safen nan ya karya da breakfast din yarinyar da zai zama lullube da makamanta,to amma sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba'aje ba. Da wani irin farincikin samun nasara ta isa gida. Ta samu laila din zaune a falo tana kallo. Kusan tunda ta kammala karatu aikinta kenan. Hajja tayi tayi a samar mata aiki ta fara tace sammm ita ba zata iya yawo a gari kowacce safiya ba,hasalima ba zata iya barin baccin safe ba,idan ta barshi waye zaiyi mata shi?. Sai data sha ruwa sosai da lemo,sanyinsa ya sanyata ta fara dawowa hayyacinta sannan ta maida dubanta kan laila dake matse matsen waya. "Mansura ta kawomin kayan nan kuwa?" Kai laila ta girgiza alamun a'ah ba tare data dauke idanunta daga kan wayarta ba. Hotunansa ke matuqar jan hankalinta,kullum kwanan duniya ta kalleshi kota tuna dashi sai taji kaman bata tare da nutsuwarta. Tsaki hajja taja ta jawo wayarta tana mita ita daya "Yarinyar nan inajin sai taje gidansu tayi kwana biyu sannan zata shiga hankalinta". Dab da kiran data mata zai shiga sai gata ta shigo. Niqi niqi dauke da kaya wanki a wanke a goge a hannunta. Mansura daya daga cikin surukan hajja da suke rayuwa gida daya,suke kuma karban duk wani mulki isa da izza tata hannu bibbiyu don ba yadda suka iya,an dauresu da duk wani zaren sihiri da zai bata damar mallakarsu kamar yadda ta mallaki mazajensu. Ko sallamarta bata amsa ba sai harara data jefeta dashi "Uban me kika tsaya yi?,na baki wanki tun bayan asuba da kadan amma sai yanzu zaki gama don bakisan muhimmancin kayan ba?" Bata amsa mata ba saboda nauyin kayan har sai data zubesu. "Kiyi haquri hajja,sai dana sallami yara suka wuce makaranta,abbansu ya fita kasuwa sannan....." "Sannu dadi 'ya'ya dadi miji,bakisan aikina gaba yake da nasu aikin ba su duka?,kada ki sakemin irin wannan?" "Kiyi haquri" Ta fada kanta a qasa,saita janye kallonta daga kanta tana sake jan tsaki "Laila tashi ki kwashe kayan nan ki zuban a wardrobe". Sai sannan ta cire kanta ta kalli kayan "Kai.....gaskiya hajja sunyimin nauyi bazan iya ba.....saidai a barsu a nan,zuwa anjima idan na tashi na kwashesu daya bayan daya". Tsaki hajja din ta sake ja ta maida dubanta ga mansura din "Kwashesu kikai min wardrobe,kuma bance ki zauna ba bare ayimin bincike a daki". Itadai batace komai ba ta tsugunna ta kwashe ta wuce dasu. "Zaki ajiye wayar nan muyi magana ko sai na fasata?" Hajja tayi maganar da daga murya,abinda ya sanya laila kashe wayar ta ajiye agefe,sannan ta juyo wajen hajja "Gani" Sai data dire cup din hannunta sannan tace "Kaman yadda nasha gaya miki ina da plan ina da tanadi a kanki.....tanadina ba kowa bane face muhammad fu'ad jadda.....mamallakin jadda diamond chore resources.....dan qawata mariyah" "Ahhhhhh" Laila ta fada tana fidda idanu cikin tsananin mamaki da kuma gigita. Wani abune da bata taba kawoshi cikin kanta ba,hasalima batasan akwai qawance har haka tsakanin momynta da mahaifiyarsa ba "Wasa kikemin hajja?" Ta fada tana kallonta sosai gudun ganin samu da rashi "Na taba wasa irin wannan dake?" Maimakon ta amsa mata saita daka wani irin tsalle tayi kanta ra ruqunqumeta. "Wayyo Allah mamana......i love you so much mamana......you fulfill my dream" "Kinga shashasha zata karyani......da Allah zauna muyi magana dake don gidansu zaki koma da zama na wani dan lokaci" Ido ta sake watsowa waje,tana jin komai kaman cikin shirin film ko labarun hikaya "Serious?" "Ubanki" Ta fada tana watsa mata zagi da yatsu biyar,saita saki dariya ta koma tana zama din kamar yadda hajja ta umarta. Baki ta daga zata watsawa mansura kira sai gata ta fito "Yauwa saiki wuce ki tafi,ki rufen qofa.....ki gayawa madeena nan da minti talatin ta dafamin madara ta kawomin,wallahi kuma aka wuce haka sai ranta yayi mummunar baci". Kai a qasa ta amsa mata ta juya tana ficewa. Sai data fita din sannan ta maido hankalinta ga laila "Kina jina ko?" 𝙎𝙖𝙗𝙧𝙚𝙚𝙣 Sake duban lokaci tayi,sha biyu saura na rana. Tunda ta farka tayi wanka da sallolinta bataji motsin kowa ba,don hatta securityn dake aikin kula da gidan bakajin motsin kowa,sanin da sukayi cewa hayaniya da motsi me qarfi na daya daga cikin abinda boss din nasu bayaso. Uwa uba ma su dake first gate bata yadda na ciki kamarta zai iya jiyosu. Bawai yunwa takeji ba,amma a jikinta takejin ya kamata ta sawa cikinta koda ruwan dumi ne. Kaman ba zata fito din ba amma ta miqe,ta lalubi mayafi ta lullube jikinta sannan ta sanya plate shoe dinta na jiya ta fara nufar qofa ba tare da tasan takan gidan ba ko kuma daga inda zata fara ba. Rufaffen hallway din ta soma ratsawa,wanda aka qawatashi da wani irin wall led light na musamman,da wasu irin qananu masu haske da suka sake fidda ainihin kyan wajen. Tattausan runner carpet ne shimfide duka tsahon wajen tsakanin kowanne qofar daki zuwa na dan uwansa an qawatashi da wasu irin nature frames masu daukan hankali. Daga bangon dake facing naka kuma,babban console mirror ne da zai baka daman ganin kusan dukka jikinka har kusan cinyoyi. Akwai plants masu kyau data gani cikin flower vase masu wani irin daukan hankali,bata sani ba masu kyau ne ko ma decoration. Guri ne daya cika da hasken da koda allurarka idan ta fadi zaka iya tsugunawa ka dauka,ko ina fes da wani irin matsanancin tsaftar da babu qura ballantana ka saka ran samun wani abu waishi datti saman lafiyayyen marbles din dake lullube kuma shimfide a qasan wajen. Duk zuqar iska guda daya idan tayi da qamshi take kai mata har hanjinta,qamshin da sam bata da tabbacin daga ina yake fesowa ya karade kowacce iska dake kai kawo a wajen duk kuwa da a rufe hallway din yake. Idanunta kafe akan staircase din dake gabanta. Batasan ina bane bata kuma fatan sani,nan din inda aka ajiyeta ma kawai tana jin ya isheta harta kammala abinda zatayi tabar cikin rayuwarsu,fatanta daya shine idan ta isa staircase din ta samu wata qofar tsakanin hagu da dama cikin dan lugu biyu da take ganin alamunsa. Ajiyar zuciya ta sauke sanda take dab da bakin stair case din,akwai wasu qofofi hagu da dama,saidai ta daman tafi mata kama da qofar da zata sadaka da wani gurin. Solid wood door ne me qofar biyu data dace da kalan gidan gaba daya dake bata kalan gold and off white,dayan pivot door ne wanda tafi kyautata zaton wani gurin na daban zai sadaka dashi,don haka ta nufi hannun damanta,ta sanya hannu ta murda handle din ta bude qofan a hankali kamar me tsoron wani abu. Wani irin tsararren parlor ne da kana kallonsa zakasan ilimi hankali da dukiya duka sunyi amfani. Well designed parlor me wani irin sassanyan yanayi me jan hankali. Babban swarovski crystal chandelier din dake tsakiyar falon ce kawai a kunne,amma duka fitilun dake zagaye da falon a kashe suke,saidai duk da haka hakan bai hana fitar ainihin kyau da tsaruwar falon da aka qawata da kujerun qasar Italy. Kutsa kai taci gaba dayi cikin falon kamar me tsoron sautin takunta,tako ta ina tsarin gidan yana dada kwance mata kai. Wani irin tsari dake da matuqar sha'awa da daukan hankali. Idanunta suka fada daya sashen falon. Glass door ne da zai baka damar hangen wani guri da aka qawata da wani irin shuke shuke masu launika daban daban masu daukan hankali. Wajen yafi mata kama da qaramin lambun da zai taya mazaunin falon debe kewa. Ta sake wurga idonta.....ba wata qofar a nan data mata kama da qofar kitchen,sai wata qofar shigen qofar farko data bude. Ita ta nufa kai tsaye,tana jin yadda qafafunta suke nutsewa cikin lallausa Italian Versace carpet daya dace ta kowacce fuska da kalar tsarin falon. Steps hudu masu fadi ta soma cin karo dasu,wanda ta nan zata taka ta sauka cikin wani falon na daban da yasha banbam dana farko ta kowacce fuska. Furniture din ciki girma da tsari,saidai kusan komai nacan akwaishi anan,illa na wannan falon yafi na wancan yawa da girma. Rukunin kujeru biyu ya dauka saboda girmansa. Sabanin wancan falon,wannan tafkekiyar tv plasma din da tafi qarfin Wall wooden TV stand din aka girketa samanta ce a kunne. Saudi qur'an ce kunne,saidai kuma sautin karatun sam baya fita. Lullube kowanne bango yake da tsadaddun curtain masu wani irin kwarjini da haiba,kowanne maqale jikin Drapery hardware,abinda zai baka daman ganin qifofin da sukayi saura ta wajen banda yalwataccen dining area da aka yiwa ado na musamman da roman shade curtain da zai baka daman kallon wani sashe na kitchen da glass door ya rabasu. Qaramin tsaki taja tana janye kallonta daga kallon kowanne tsari na parlor din. Finally bayan ta gama duk bulayin ta samo kitchen din da qyar,don haka ta taka a nutse tana hawa steps din da zai sadata da dining din zuwa kitchen din. Sak tayi canma tana kallon kitchen din,don wata aljannar duniyar ce da bata san ta ina zata fara ba. Komai a kitchen din baqonta ne,ba wani abu da zatace ta masa farin sani idan ka debe kayan amfani na yau da kullum da kowanne kitchen ake samu. Ya qawatu sosai da custom cabinets da aka sarrafa da wani irin gogaggen katako datayi imani badai daga qasar nan ba,yabi sauran kayan cikin gidan yazo ne daga wata qasar daban. Tunaninta ya dawo da baya,shin yaushe duka suka samu wannan kudin?,a ina?,da har aka samu daman zuba mata wannan uwar dukiyar cikin gidan?. Anya kuwa bayan mutunci da kawun ya saida mata ba hada harda 'yancin jere ga kowacce diya budurwa ba?. Iya wannan tunanin ya sake sanyawa taji komai na gidan ya fice mata a rai,baya kuma burgeta ballantana taba haskenshi. Taja qafafunta da sukayi mata nauyi tana nufan gas glass stove din tana fatan ta kunnashi daidai kama kowanne. Sai data bata lokaci shi kansa wajen gane kansa sannan ta saki ajiyar zuciya. Taja da baya tana baza ido don hango inda zata samu koda ganyan shayi ne,don dama cimar bata wuce haka. Daga can ta hango wata qofar,ta taka zuwa wajen tana addu'ar Allah yasa ta samu abinda takeso,don duka ta gwada duba cabinets din bata samu komai ba aciki,da alama shi kam banda kayan kitchen din da aka jera ba'a taba komai ba. Cikin sa'a ta tadda yalwataccen guri da yafi mata kama da store saidai na musamnan. Don ba abinda yake zube a qasa hatta kuwa da buhunhuna da kwalaye,kusan duka wajen shima an masa kanta sosai kamar kanti ko shago,an saka komai a bangarensa daidai da kwalayen maggi kuwa. Daga gefe babbar freezer ce wadda batabi ta kanta ba,don ko sha'awar budewa bataji ba,to ta bude taga me?,ba wannan ne a gabanta ba. Bangaran spices na tea ta nufa,ta bude ta debi kowanne daidai yadda zai isheta,daga wannan ba abinda ta qara ta dawo ainihin kitchen din,ta bare tukunya daya,ta nufi sink ta kunna famfo ta debi ruwa,sannan ta dawo ta kunna gas stove din ta dora bayan ta zuba komai. Minti goma tsaf ya tafasa,ta soma duba mazubin da zata juye ta wuce dashi,don sam batason zamanta kitchen din. Tea set ne kala kala,ta rasa ma wanda zata dauka. Taja qaramin tsaki still,komai na gidan ya fiya fi'ili da feleqe,tunda ta tashi komai ma sai tasha wahala take laluboshi,iya yau kawai.....neman kitchen da dafa tea ya zame mata alaqaqai?,ina ga sauran rayuwarta cikin gidan. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 15 16 Qarshe dai wani Wedgwood tea set din qasar chaina ta dauka ruwan sararin samaniya,ta juye duka ta zuba sugar a mazubin sugar din sannan ta dauka tray na set din cak tana wucewa ciki dashi. A yanzun tafi fahimtar hanyar da take komawa ba kamar dazu ba. Tabbas duk yadda takai gason ta kushe komai ta kasa,duk.yadda takeso komai kada ya burgeta a gidan hakan ya gagara,dole ta sallama saidai still zuciyarta na gaya mata "Allah yasa da kudin halal akayi komai" (😂 yarinya tunda dai kin fara mora ai magana ta qare). Bata tashi tunawa da personal wayan da ta bata ba sai data kusa kammala shan tea din. Qarar wayar ya Haifa mata da wata irin faduwar gaba. Wayace data jaddada mata cewa ta bata ita ne kadai saboda personal use dinta,bata bata ita don ta kira kowa ba sai ita kadai. Hannu ta tura qasan inda wayar ta fada tun a jiya da zazzabi ya kamata,ta duba fuskar wayar sunanta ya bayyana baro baro 𝙈𝙖𝙧𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙖𝙙𝙖𝙢 shine sunan data zabi ta sanya mata saman number. A zahiri tana qoqarin hana kanta daga wayar ne,don bata da buqatar jin muryarta kwata kwata.....amma a badini sai taji kamar ana tilastata daga wayar. Can qasan zuciyarta ta dinga jin bata da wani sauran sukuni saina daga wayar,a sanyaye ta latsa ta kuma kara wayartata a kunneta "Amarya.....ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da taja wani nannauyan numfashi tana qoqarin daidaita kanta kafin ta furzar da iskar a hankali a kuma sirrance "Ina kwana?" Ta fada da sassanyan murya. Murmushi maamah ta saki,da gaske aikinta na jiya ya ratsata yadda takeso,ta tabbatar banda haka bataga alamun zata samu gaisuwa wajen yarinyar ba koda na minti daya ne "Lafiya lau....ya baqunta?" Batasan wacce kalar amsa zata bata ba,don haka ta zabi tayi shuru. Itama shirunta ba shine damuwarta ba,isar saqonta zuwa ga kunnuwanta shine damuwarta don haka ta dora. "Zuwa anjima kadan zan aike miki da me aiki da kuma 'yar 'yar uwata......zata zauna daku nadan wani lokaci ne.....me aiki zatayi aiki ne kadai da umarninki,da tayaki abinda kike da buqata......amma kula da muhammad da dukkan abinda zaici ban dorawa kowa ba yana wuyanki......kada ki damu da wanzuwarsu.....dukansu sunsan da tafiyar.....saboda haka ba buqatar boye boye wajen gudanar da aikinki,kiyi komai kawai gaba gadi. Abu na gaba muhammad bame sauqi bane.....kada ki sanya rai koki damu da rashin cin abincinki a zangon farko......kawai kici gaba da dafawar.....kici gaba da shiga lamarinsa.....kici gaba kuma da dukka qoqarin ki na ganin yaci yasha din.....yana da tsananin miskilanci......yana kuma da tsantsamin da sai kin zama me tsananin tsafta kafin ki samu abinda kikeso.....ina fata kin fahimta?". Can qasan ranta suya sosai zuciyarta takeyi. Tanajin maganganu na taso mata da ya kamata ta maidawa maamah.....amma sai takejin kamar biyayya wa umarninta ya zame mata tilas ne kawai,ba buqatar musu ballanta jayayya "Kin jini?" Ta sake tambaya don tabbatar da taji komai din "Eh naji" "Yauwa.....saikin sake jina ko?,idan akwai tambaya ko wani abu daya shige miki duhu......qofa a bude take". Kasa cewa komai tayi,sai kawai ta sauke wayar daga kunnenta tana ajeta gefe tare da binta da kallo. Shawarwari kala kala zuciyarta ke bata game da wayar,wata zuciyar na cewa ta zare layin ta karyashi ta yar,wata nace mata ta kashe wayar ta wurgar a dustbin,wata kuma na gaya mata ta sakata a silent tayita kira ba'a dagaba,amma daga qarshe ji tayi ko guda daya ba zata iyayi ba. Bawai don bata buqatar hakan ta faru ba....aah haka kawai taji aikata hakan bazaiyi ba,saita nutsa yatsunta cikin gashinta kawai tanajin kanta kamar ana yamutsashi......umarninta kadai take da muradin cikawa. Kusan saman idanunsa hasken alfijir ya fara keta duhun sararin samaniya yana kore duhun daya mamayeta,duniya ta fara haskaka da siririn hasken nan dake juyewa izuwa hasken rana dake wadatar duniya da halittun cikinta. Wayarsa ya kalla,a gida a lokuta irin wadannan ya kammala duka wasu addu'insa.....yana shiri ne ya fita gym da yake bawa awa daya.....so amma a yau din yadda yakejin jikinsa da sauran gajiya bazai iya komai ba,sai ya miqa hannunsa yana jawo wayarsa da yaga tana haske sanda qarfe bakwai da rabi na safe ya cika. Joshua ne.....ma'aikacinsa dake kula da bangaren marketing da price na gold da Diamond a kamfaninnikansa. Yana cikin manyan ma'aikatan da baya iya tsallakema kiransu. Cike da mamakin kiran sassafe irin wannan ya sanya wayar a kunnensa "Hello......" Fu'ad ya fadi da muryarsa maras hayaniya musamman daya kasance yanzun safiya ce "Hello sir........good morning sir......ina expecting zuwa yanzu baka duba business side news paper da magazines ba ko?" "Morning Joshua.......what's going on?" "Sir......sun karya darajar gold da Diamond duka tsakanin tsakiyar daren jiya zuwa yau da safe". "La'ilaha illlallah" Labbansa suka motsa ya furta a nutse idanunsa suna lumshewa. Daga yadda Joshua ke masa magana adan rude ya tabbatar abun ba qarami bane. "Cool down Joshua......i will be online yanzu in sha Allah" "Okay sir......but sir a irin wannan yanayin da sabon kamfani ke shirin fara aiki akwai hadari sosai a ciki.....akwai barazanar tsayawar abubuwa da yawa mo durqushewarsu......sir inaji a jikina an shirya wannan abunne kawai". "Calm down Joshua,ba abinda zai faru in sha Allah.....let work together okay?". "Okay sir....." Ya amsa da damuwa sosai a cikin muryarsa. Kiran ya yanke yana sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da maida hankalinsa kan fuskar wayar tasa. Dole ya miqe a nutse ya fara bincika inda system dinsa suke da sauran kayan aikinsa. Cup rabin qaramin cup tasha taji tea din ya isheta. A nutse ta maidashi ta ajiye tana bin cup din da kallo. Ya mata kyau sosai,amma kuma ba wannan tunanin bane a qasan ranta,ta janye idanunta tana lumshe. Ta ina rayuwa zata fara?,yaya rayuwar zata kasance?. Idanunta ta bude,sai suka sauka akan wayar da matar dake amsa sunan surukarta ta bata jiya. Daga jiya zuwa yau sai takejin komai kamar ya canza. Har a ranta da zuciyarta sam bata jin matar ko kadan.......tana jin wani qaqqarfan abu a kanta da yafi kama da qiyayya......qiyayyar batasan ta mece ba.....saidai koma meye baya rasa nasaba da katsalandan da suka yiwa rayuwarta ita da d'anta. Tanason kiran momma amma batasan me zatace mata ba.....kuma kaman a yanzun ma yayi safiya da yawa ta kirata din. Yadda taji zuciyarta nason karyewa taji bataso......batason ta karaya tun bata gama fuskantar komai ba. Gidan yayi mata shuru da yawa,duk da dama can ita ba ma'abociyar son hayaniya bace....ko a gidansu zaka samu dakinsu a rufe kirif don rage yawan hayaniyar mutanen tsakar gidan nasu,a mafi yawan lokuta ma tafi qaunar shurun,sai takejin wata irin kewa tana shigarta.....kewar huda.....kewar nadra....kewar haneefa. Takan tsinci kanta a wani yanayi maras dadi idan ta tuna dasu.....ta yaya zasuci gaba da rayuwa?. Tana da nutsuwa kadan idan ta tuna suna tare da momma bahijja,tayi imani zata cika abinda tace din,amma duk da haka bata shirya barinsu a wannan matakin ba. Yunqurawa tayi ta miqe dauke da tray din don ta maidashi inda ta daukoshi,tako ina tanaji komai da zatayi amfani dashi a cikin gidan na wucin gadi ne kuma na aro ne a wajenta,bata da hurumin zafafa mu'amala da komai na gidan. A karo na biyu ta sake duban stair case din sanda zata wuce ga qofar da zata sadata da parlor din. Sai a sannan ta sake qare mata kallo sosai. Tamkar gine ginen turawa haka aka tsara gidan,wani irin staircase ne me kyau da aka qawata bangonta da wani irin woods royal frames da shukoki masu kyan launi da fararen furanni qananu qananu. Idanunta ta janye tana jin bata da hurumin maida hankali da wajen,saidai girma gidan yana saka mata shakka da tsoro a ranta,tana kuma cike da shakka da tantamar ita kadai ta kwana ne wai a cikin gidan?. Saidai basket din data gani ajiye saman table din falon bayan ta dawo a kitchen din ya fara alamta mata ba ita daya bace ba. Tana shirin janye idonta ta wuce ciki taji sallama daga parlor din farko. Da dan tsoro da mamaki ta maida idanunta kan pivot door din cikin tantamar wanda yake sallamar. Tsahon second talatin tayi,sai taji ta wuce ciki kawai,don bata jin akwai wani abu a cikin gidan da take da haqqin lallai saita kula da yadda zai tafi,saidai taku uku kacal ta sakejin muryar na sake jaddada sallamar. Sallamar tayi mata nauyin da takeji bai kamata ta wofantar da ita ta Kuma wuce ba,dole ta dawo da baya tana dosar qofar,ta turata ta bude tana saka qafanta kan step din idanunta cikin parlor din. Kamilalliyar macace cikin kyakkywar shiga da lullubi,tana a tsaye,gefanta kuma kyawawan kwanduna ne guda biyu ajiye a gabanta. Murmushin data sakarwa sabreen shi ya sassauto zuciyarta,sannan ya zabge kokwanton dake ciki,saita samu qwarin gwiwar ci gaba da saukowa idanunsu cikin na juna "Ina kwana" Matar data kusan haifarta ta gaidata kafin ita takai ga gaisheta. "Ga waje ki zauna" Tace da ita cikin qarfin hali ba tare data amsa gaisuwan ba. A nutse kuma cikin girmamawa ta zauna,sai itama ta samu gefen kujerar ta zauna tana maida mata gaisuwar "Ina kwana?" "Barka da asuba,mun tashi lafiya?" "Alhamdulillah......ya baqunta?" Ta fada da murmushi da kuma kulawa a muryarta "Alhamdulillah" Ta amsa mata har yanxu tana tunanin wace ita. "Anni ce ta aikoni.....tace kuyi haquri har yanzu akwai baqi cikin gidan,shi yasa ba'a kawo breakfast da wuri ba,amma gashi nan harda lunch don kada ayi delay na kawowan da wuri shi yasa ta hada.... Tace da fatan hakan ba damuwa?" Sunan tadan juya cikin ranta,amma kuma farat daya hankalinta sai yakai kan matar. Murmushi tadan saki tana mamakin damuwar da tayi dasu haka "Ba komai.....ayi mata godiya sosai" Ta fadi tana jin wani abu na daban akan matar. Miqewa matar tayi "Sunana baraka.....dadaddiyar hadimar anni ce ni,zan koma,a huta lafiya" Kai kawai ta gyada mata,har ta fice idanunta suna kanta. Sai ta ajiye ajiyar zuciya tana maido kallonta ga basket din gabanta. Tadan xuba masa idanu tana nazarin matar,komai nata cikin dattako.....kuma komai nata akwai alamun nutsuwa me yawa a tattare dashi,waishin WACECE UWA a cikinsu?,wacce mahaifiyar ta ainihi?. Wannan tambayar kusan ita daya ce abar data damu da ita cikin lamarin kaf,sai ta miqe a nutse kaman zata bar wajen,sai kuma ta fasa,ta tsugunna ta dauki basket din,ta taka a hankali zuwa dining area din da aka qawata da wani dunqulalle kuma mulmulallen dining data kasa tantance glass ne ko kuwa dutse?,ta dora basket din kawai akai,sannna ta juya tana sauka ta wuce zuwa dakinta. Sai daya daidaita komai sannan ya hada connection din duk da yakeso. Bincike ya fara yi a kasuwannin hannun jari na gold da Diamond.......da gaske an masa wani irin mummunar faduwa da bai taba ganin yayi hakan ba tsahon fara kasuwancinsa. Baya ya koma ya jinginar da bayansa jikin kujera yana shafa lips dinsa da yatsansa guda daya. Da gaske akwai faduwa da hasara me yawa data samesu,musamman a irin wannan lokacin da kwanaki kadan suka rage kamfani ya fara aiki. Zai zamana kome xasu fitar ko su samar asara ce a garesu,dole su saidashi a qasa da farashin da aka tsara za'a fiddashi. Saqonnin da aka yita turo masa suka dawo masa akai,ya lumshe idonsa ya kuma budesu yana kiran sunan Allah,sai ya sake maida hannunsa kan system din. Kusan duk wani ma'aikaci dake aiki qarqashinsa na kusa dana nesa sai daya nemeshi. Ya bata lokaci sosai yana urgent meeting dasu,wanda hakan ya daukeshi aqalla a wanni masu dan dama. Baisan kuma ya jima din a zaune ba sai da cikinsa ya fara qara. System din ya rufe yana furzar da iska daga bakinsa. Ya tabbata babu abinda zasu iya sakeyi......dole su rungumi dukka hasarar data tunkarosu lokaci guda...... Akwai manufa.......kuma anyi ne da gayya,kuma hakan ya sake bashi tabbacin dukkanin saqonnin da aka aike masa da gaske suke.....sun shirya shiga yaqin tare dashi.....sun shirya jan daga shi dasu. Sai ya saki wani qaramin murmushi. Sunyi gangancin fara tsiro irin wannan abun dashi......ya tabbatar basu gama sanin ainihin waye muhammad a kasuwancinsa ba.......wannan abun koma waninsa bazai sauyashi ba......bazai kuma sakashi ya tsaida kowacce harka tashi ba. Har a jikinsa yakejin a baqon guri yake,banda haka zuwa yanzu da tuni Ameh ya dameshi da batun abinci. Hannunsa ya miqa ya dauki wayarsa ya kunnata daga kashetan da yayi "Subhanallah" Ya furta da hanzari ganin har azahar ta sanyo jiki. Bai kira anni ba.....bai kira farouq ba,baima kira kowa ba wanda aqalla ya dace ya yiwa kowa bangajiya koda kuwa ba shine ya gayyatosun ba,amma aqalla sabodashi suka zo. Anni ya fara kira amma sai yaji wayar a kashe,yasan har yanzu gidan akwai sauran baqi don haka yafi kyautata zaton uzurin daya sakata kashe wayar kenan. Yayi zaton zai samu saqon farouq amma sai ba tarar ba. Ya danji ba dadi,don haka kai tsaye ya fara kiransa. Bugu daya ya daga kamar dai dama wayar tana hannunsa yana jiran kiran nasa ne. A nutse ya masa sallama,daga can background yana dan jin muryar mutane. "Kaji muryar ango......so fresh" Farouq din ya fada kansa tsaye. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 16 "Sai yanzu aka tashi kenan?" Farouq din ya sake fada ba tare daya damu da abinda zaice da farko ba a lallai sai ya tsokalo shi "Eh.....ka nemeni ne?" "Wa?,ni?,ya za'a yi na batawa kaina lokacin nemanka?,waya gaya maka ana kiran ango a irin wannan time din?" "To hell with you farouq a'ahhhhh" Ya fada sounding bored kadan kadan. Murmushi me kama da dariya ya saki wanda har sautinsa ya bayyana sosai. "An maka uziri kome zaka fada you're forgiven" Hannunsa ya dora saman sumarsa yana shafawa,ya fuskanci farouq so yake kawai ya haukatashi "Where's anni?" "Na barta a gida tana preparing na walima....." "Ya salam" Fuad ya fada yana lumshe idonsa. Sam ya mance da batun walimar kwata kwata. "Su haajj na yiwa rakiya airport......they're leaving". "My regards to them please.....idan na sake nutsuwa zuwa anjima in sha Allah i will give them a call" "Ance maka daga yau har wani satin an maka uzuri fa.......ka samu nutsuwa yadda ya dace dudu" Ya rigashi katse wayar wannan ya hana fuad gaya masa abinda yayi niyyar fada din,sai kawai ya zame wayar daga kunnensa,qasan ransa yana fassara maganar farouq da kuma sakata a inda farouq din ke nufi "God forbid" Ya fada qasa qasa. Hasashen gaba days banbarakwai yayi masa sanda ya dora tunanin a muhallin da farouq ke nufi,tattara tunanin yayi ya azashi a mizanin shirme gaba daya,ya fara lalubar number amna. Sai data kusa yankewa sannan ta daga "Hamma" Ta fada a shagwabe. "Hamma ka manta dani.....adda tayi taking dinka away.....as far as yadda zata iya" Ta qarasa fadi da qaramar dariya a muryarta da ba sosai ta bayyana ba "You amna.....lovey dovey will never be forgotten........hayaniya yayi yawa amna.......bansan haka ake abun ba" "Hamma yafi haka fa.....don kaqi bada hadin kai ayi komai" Hannunsa ya dora a goshinsa yana furzar da qaramar iska. Shikam ko zancan bayaso,abinda yake gabansa kawai yanzun shine damuwarsa. "Ya gidan?" Ya tambayeta. "Full with 'yan biki dake jiran walimar anni......ina yini hamma" Ta hade amsa tambayar tasa da gaisuwa. "Alhamdulillah.....how about anni da abba?" "Abba dai ya fita tun dazun.....kuma ina jin sai dare zai dawo........anni tana daga baya da mutane" "Okay.....bata wayar" "Okay hamma" Ta amsa shi tana miqewa gami da ficewa. Bai yanke kiran ba saita maida kunnenta,tana tafiya wajen annin tana ta bashi labarai kala kala. Bai yanketa ba yayi shuru yana saurarenta. Yasan halin amna sarai,bata gajiya sam sam da hira. "Kice ameh ya kirani....." "Okay hamma.....ga anni" Saita miqawa anni wayar,ta samu plastic chair daya daga cikin kujerun dake wajen ta zauna tana kallon yadda aka qawata wajen walimar da wani irin tsari me kyau,tamkar wani hamshaqin event center. "Barka da warhaka anni......ya hidima ya rana?" Murmushi ta sauke,har cikin ranta farinciki yana mamayarta idan ta tuna a yau muhammad dinta ya zama cikakken magidanci "Barka kade me babban suna.....mun tashi lafiya zance ko mun yammata lafiya?". Tambayar tata tadan sakashi yaji nauyi,kada itama fa ta dauka wani abune ya boyeshi,kada ta fassara wani abu na daban akan yarinyar ma da bai samu daman ganinta ba "Lafiya anni alhamdulillah" "Haka akeson ji.....na aika baraka takai muku breakfast da lunch.......nayita so nace idan ta isa ta hadani da d'iyata mu gaisa saina sha'afa......in tana kusa bani ita" Rasa abinda zaice yayi,yadan diririce kadan har hakan yaso ya nun alamu a muryarsa,yayin da annin ta dauka wani abunne na daban ya kawo hakan,kodai baiso aji muryarta a fahimci wani abu,don haka ta katseshi "Kaga rabu da ita.....anjima idan kun iso wajen walima ma gaisa.....za'a fara immediately after asr prayer" "Allah ya kaimu anni.....Allah ya qara girma da lafiya" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ta fada tana jin dadin yadda sam baya gajiya da mata addu'a. Ita ta fara katse wayar,sai shima ya sauke yana kallon fuskar wayar. Inda anni ta sani data qyale walimar nan,duk da ita walima duk inda take albarka ce. Agogo ya kalla har daya na rana yayi,sai ya aje wayar yana jin zuwa yanzu ya kamata ya laluba kitchen ya samu koda tea ne ya sanyawa cikinsa. Duka wani abu daya saba sha da safe irinsu goji berries water da turmeric tea,cinnamon tea da sauransu,wannan ya sanya yake da wani irin cikakkiyar lafiya da kuzarin da idan ya shiga cikin maza kuzarinsa yake fita daban,kaman yadda yake da cikakkiyar lafiya irin ta d'a namiji,wanda yayi imanin banda busy da business daya saka a gabansa suka fatali da komai da yakeji......tabbas da bai isa yakai har wannan lokacin haka ba,dalilin da yasa ya janyewa amfani da wasu abubuwan irinsu ginseng tea,sai time to time idan yana da buqatar hakan,ko ya kwana biyu bai sha ba. Fararen loopers slipper ya sakawa qafafunshi,wadanda suke mahadi ne na fararen pyjamas din jikinsa da suka fidda siga da surarsa. Yanayin fatarsa kadai ya isa ya fadi maka irin wadata da nutsuwa da yake ciki,skin dinsa so fresh da ba lallai ta wata macen ta samu irin wannan kyan da glowing din ba. Sai daya shiga toilet ya daura alwala,ya dauki qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida takalmin ya nufi qofa yana gyara hannun pyjamas dinsa daya tattare. A nutse ta idar da sallara azahar tana maida idanunta wajen sujjadarta. Tana jin idanun a jikinta sunyi mata nauyi,nauyin da bata raba dayan biyu yunwa ce da kuma bacci. Baccin kam tana da tsananin buqatarsa,ita kanta ta sani,saboda ita kanta tasan cewa taci bashin baccin yadda ya kamata,abincinne bata jin akwai muhallin da zata sakashi a cikinta,saidai jikinta na sake gaya mata ya zama dole ta nemeshi. Dole ce ta sanyata miqewa,a nutse ta nade abun sallar,ta gyara yafen dan madaidaicin hijab din data dauko daga closet din nata ta daure igiyar sannan ta juya tana lalubar qofa bayan shawarar da zuciyarta ta bata nata duba cikin kayan da aka kawo ko zata samu abinda zata saka a cikinta. A nutse ya sauko daga saman yana sake jin nutsuwa da gidan da tsarin gidan. Ya dauke idanunsa daga hallway din da yake kyautata zaton shiyyarta ne. Qofan dake damansa ya karya zai bude sai kuma ya fasa,ya koma ya kama handle din wooden door din ya bude yana isa ga falon. Ko ina da komai yana nan kamar yadda ya barshi a jiya,da alamu ba'ayi amfani da parlor din ba kwata kwata. Zarcewa yayi parlor din farko wanda keda kitchen din,ya sauka daga kan step din a nutse sannan ya zarce zuwa dining da hake hango basket akai,da alama saqon da anni tace ta aiko ne. Yana daga tsaye ya miqa hannu a mamakance ya jawo basket din,yadda aka kawoshi haka aka ajiyeshi,da alama ba'a ko budeshi ba ballantana a taba komai a ciki. Waye to ya karba saqon ya shigo dashi?. Ba kowa sai ita wannan shine amsar daya bawa kansa,don ya sani ba wanda zaiyi gigin shigowa cikin gidan saboda sunsan doka da kuma tsarinsa. Duk wani ma'aikaci dake aiki a qarqashinsa,daga cikin company har zuwa cikin gida kowa yana tsayawa iya limit dinsa ne,ba wanda yake wuce qa'idar aikinsa ko kuma limit dinsa. Komai anni ta zuba na duka irin abinda tasan yafiso yaci da safe ya kuma ci da rana,ya sauke qaramar ajiyar zuciya yana sake jin qaunar matar da martabarta suna hauhawa a zuciyarsa. Baiga wani abu da zai taba annin ya bari ba ko wayeshi,take sai yaji ransa yadan baci,ganin kamar ta wofantar da kayan da aka kawo din. Daidai abinda cikinsa yake buqata ya zuba,kafin ya gama duka ya bata wajen saboda rashin sabo,ya manta when last yayi serving kanshi,duk wani motsinsa akwai masi hidimta masa. Tsaki kadan yaja ganin bacin da wajen yayi,ya soma wassafa yadda zai aje masu masa hidima cikin gidan kaman yadda ya saba,don bayajin zai bari ya takura har haka,ya dauko komai cikin qaramin serving tray ya dawo ainihin parlor din,sai ya azashi saman side table. Har zai zauna sai ya fasa,ya dauko remote yana lalubar channel din dake haska rate na dollar pounds da rate na diamond da sauran harkokin kasuwanci. Har yanzu yana cike da mamakin yadda abun ya kasance,duk da iya bincikensa har yanzu ba wanda yasan daga ina faduwar gold din haka rugu rugu ya samo asali. Ya soma sipping pomegranate juice kenan idanunshi suka sauka akan basket din. Tun basket din jiya da farouq ya hadoshi dashi,wanda shi kansa baisan anihin meye da meye a ciki ba. Bacin ran da yaketa qoqarin boyeshi dole a wannan karon ya bayyana kanshi. "What's all these nonsense?" Ya fada can qasa labbansa suna motsawa. Kamar jira akeyi yayi tambayar yaji alamun motsin mutum. Fararen idanunshi ya daga still cup din yana saitin bakinsa,baikai bakinsa ba bai kuma dire ba,ya zube manyan idanunshi a kanta. Karon farko da ya fara mata kallon kai tsaye a rayuwarsa,karon farko da yayi mata kallon da zai iya gane face dinta.....don kuwa a baya zai wahala ya iya cireta cikin mata goma ko biyar idan aka zube masa su. Kwata kwata bata lura da mutum ba sanda take sauka daga steps din zuwa qasa don nufar kitchen,amma da yake cikin dabi'arta akwai sanya idanu da kula da motsin komai da komai dake kewaye da ita,da kuma sanya hankalinta bisa yanayin kowanne abu saita dinga ji a jikinta kamar akwai wani baqon abu da babu shi dazu a parlor din. Juyi biyu ana uku idanunta suka sauka akan nasa........itama karon farko kuma lokaci na farko a rayuwarta datayi masa duba nakai tsaye.....duban dake rataye da abubuwa masu yawan da suka faru. Wani nannauyan abu taji yana fita daga idanunshi zuwa nata yana neman kwarjanta mata shi da wani irin madaukakin kwarjini da bata taba siffantashi a dukka hasashenta dashi ba,sai ta janye idanunta daka kaf sashen da yake tana jin wani bala'e'en haushinsa yana sauka mata a hankali a hankali da wani yanayi me kama da tsanar mutum. Shine silar komai da komai,shine kuma maja ragamar kowacce kalar qaddara data sameta da kuma zata iya samunta a nan gaba. Tashi zuciyar kuwa ta cika da mamaki a yanzun da idanunsa ke sake haska mata qarancin shekaru qarara dake tattare da ita. Wani irin qyanqyaminta da wasarta suna nasar zuciyarsa. A wannan age din nata da duka duka idan tayi wuta bai wuce ace tana level one ba......amma s irin shekarun har take da fikirar SATA SANE FASHI DA MAKAMI TA YANAR GIZO.....abu mafi muni kuma shine KARUWANCI BIN MAZA. Wannan abu na qarshe daya tuna kadai ya sanyashi yaji zuciyarsa ta sake matsewa. Koda aboki ne dashi yake da dabi'ar neman mata......ba aboki ba,koda abokin kasuwancinsa ne kai muddin wannan din dabi'arka ce.....muddin kuma ta bayyana ya sani to yana haqura da huldar kasuwanci dakai. "Zunubinsa daban dude......haka mu'amalarku ma daban.....shi da Allah wannan halin nasa,baka da ikon canzashi" Kadan daga cikin abinda Farooq ke yawan gaya masa. Harara yake balla masa wani lokacin "Bani da sha'awar karbar kudi daga hannun ma'abocin sabon ubangijinsa,wattaqu fitnatalla tusibannal lazina zalamu minkum kaaassah(kuji tsoron fitinar da idan tazo bata shafar iya wadanda sukayi zalinci kadai a cikinku).idan kana neman albarka ubangiji cikin samunka....kayi qoqarin kaucewa masu saba masa,sai taka dukiyar tayi albarka". Irin maganganun nan sun jima suna fafatawa a kansu shida farouq. Ji tayi kaman jikinta na neman rasa duk wani confidence.....hakanan batason wanzuwa a muhallin da yake fesar da iska tana shaqa,sai taji kamar wadda ya fitar ita take zuqa,don haka ta juya a nutse da zummar komawa inda ta fito,tana ji har cikin ranta ta haqura da duk uzurin daya fiddota. "Ke!" Ta tsinci husky voice dinsa da bata taba jinta kamar haka a kusa kusa ba sai yau......karon farko kenan,wannan ya hadu da saukar tsawar tasa ya sanya gabanta wani mummunar faduwa.....kafin ta samu tayi hanzarin daidaita nutsuwarta da tattara dukka qarfin ta. Zuciyarta ke qarfafarta kada ta tsaya.....salon kiran da yayi mata din zallar raini ne.......yayin da ta nashi gefen ya fita hasala. Ya za'ayi ya kirata yarinya qarama irin haka tace zatayi ignoring nasa?,yarinyar da yayi imanin tsakanin musaddiq da saddiq ma babu sa'anta......koda ta girmi amna ma kuwa yayi imanin ba zata bata sama da shekara uku ko hudu ba. "Na rantse qafarki ta sake taku daya daga nan saina kakkaryaki na zubar" Ya fadi a hasale,saboda abinda tayi masan bazai tuna mutumin daya taba masa hakan ba tun sanda sunansa ya shiga duniya a matsayin muhammad fu'ad jadda. Batasan me yayi mata birki ba,har ta daga qafar zata taka step na farko saita mayar ta ajiye. Zuciyarta na mata wani irin suya a qirji. Ita yau sabreen wani d'a namiji ke kwatsawa tsawa har haka?,saboda kawai yana tutiyar ya aureta?. "Dawo ki zauna!" Ya sake fada a kausashe har sai da taji kaman yana daf da ita ne. "Ki sake na maimaita miki kuma....wallahi yau a cikin dakin karnuka zaki yini" Ya furta muryarsa na bawa me sauraro tabbacin da gaske yake. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 17 18 Wasu maqalallun hawaye da bata tsammacesu ba taji suna tsatsafowa daga cikin qwayar idanunta,tayi hanzari da gaske ta dakatar dasu cikin bawa zuciyarta umarnin "Ba faduwa.......ba bada damar ganin lago.....i want to win". Abinda ya saka hawayen komawa kenan,saidai har yanzu tana jin alamunsu. Ta koma ko ta wuce abinta?,duk abinda zaiyi ma yayi?,ko kuwa ta zauna ya lissafa nasa qa'idojin itama ta sanya mishi nata iyakokin?. Bata tantance wanda zata dauka ba saiga kira ya shigo wayartata. Kallon wayar kawai sai taji tamkar wata sabuwar barazanar ce ta shigo cikin rayuwarta,sunan matar datayi saving dai still shi yake yawo. Abisa son ranta bata da Sha'awar sauraronta.....amma bisa tilastawar zuciyarta sai taji ba zata iya tsallakewa kiran ba,a sanyaye ta daga ta saka wayar a kunnenta. "Tun dazun nake zuba idanun ganin kiranki ai.....na dauka zaki nema taimakon abu na farko da zaki fara girkawa a gidan" Muryar maamah kenan da kalamanta na farko data fara jerowa baya ga amsa sallamarta da tayi. Idanunta data lumshe ya tilastawa boyayyun hawayenta saukowa,amma sai tayi hanzarin daukesu tana sauraren muryar matar. "Na manta na gaya miki wannan ko zasu taimaka miki wajen cimma nasara........yana da zafin rai.....yana da kafiya,bayason raini bayason musu.......bayason qazanta........kiyi duk yadda zakiyi ki zama ke kike ci dashi......ki sadaukar da komai masa......ki qarar da tunaninki kan duk hanyar da zaki maido cin abincinsa hannunki.......wannan shine kadai abinda zai sama miki 'yanci....." Saita dakata kamar me shirin bata damar cewa wani abu kafin ta qara "Idan kina da tambaya ko buqatar qarin bayani qofa a bude yake......zuwa anjima kina da baqi......saidai mutum daya ta qaru.....zan miki bayani a kanta.....af na manta na gaya miki.......dazu huda ta tsallaka shop din tsallaken titin gidanku fa". Mummunar faduwa gabanta yayi da ambatar sunan huda kawai a bakin maamah... Da gaske mutanen suke......sun mata tarko da 'yan uwanta,da gaske suke suna bibiye ne da rayuwar 'yan uwanta mahadin numfashinta?,da gaske kowanne motsi nasu a lissafe suke dashi?. Tabi maganar maamah ta tseratar da rayuwarsu?......a yanzu tana jin kamar shine babban haqqin daya zame mata dole ta sauke. Batasan ya iso wajen ba,kawai abinda taji shine zare wayar daga kunnenta. Ba qaramin firgita tayi ba,saita waiwaya da hanzari tana fuskantarsa sanda ya zubawa fuskar wayar idanu lokacin da kiran yake yankewa da sunan mariya b'aro baro akai. Ci gaba yayi da kallon fuskar wayar har sunan yayi disappearing yana sake maimaita full name din nata qasan zuciyarsa. Wani abu ya taso masa.......zarginsa yana daduwa daga kaso sittin cikin dari zuwa kasu casa'in da tara cikin d'ari. A nutse ya maida qwayar idanunsa kan fuskarta,haka kawai taji qafafunta sunyi laushin da kafin ya sake cewa komai ta koma ta zauna saman kujerar dake daura da ita,tana mamakin yadda nature da colour na idanunsa suka sauya kadan. Wayar ya cilla mata ta sauka daidai saman cinyarta,sai ya soke duka hannuwansa cikin aljihun wandonsa yana dubanta kai tsaye. "Kada ki dauka zakiyi duka irin rayuwar da kikaga dama,kada ki dauka zakiyi kalar rayuwar da kikeso.....kada kuma mi rudu da cewa kinzo nan gidan don ki huta......ki debi adadin kudi da dukiyar da kikeso daga jikin muhammad jadda.....idan kin dauki duka wadannan abubuwan a ranki......" Sai kawai wani siririn murmushi ya kubce masa,ya cije redlips dinsa yana dage kafadunsa sama ".......kina ruwa" Ya qarasa fada yana jawo wata ottoman chair 'yar qarama zuwa gabanta yahau kai ya zauna "Kisa a ranki nan kin shigo gidan tarbiyya da gyaran hali ne......gidan qare kukanka.......gidan bin daidai.......wadancan kayan duka da aka shigo dasu kin dauka a caca aka ciyosu?,ko kuma fashin yanar gizo da kutsewa account din al'umma akayi aka samosu da zaki bar komai cikin jakarshi?,salon idan ya lalace baki da asaran komai?" Wasu irin zafi sosai maganganunsa sukayi mata,irin zafin da bata taba kawowa ba. Ko mahaukaciya ce ita ta fuskanci inda batunsa ya dosa ballantana da hankalinta fes,zafin maganar ya tilastata daga oily eyes dinta masu sheqi dake shige da nasa ta kalleshi dasu. Duka girarsa ya dage sama yana dubanta da fuskar da babu digon walwala ko sassauci a ciki "Yes.......gidan nan dama komai da zai gilma a ciki zallar halak ce ta samar dashi.....so that bazan dauki almubazzaranci ba......dole ki kula da komai a daidai sanda ya dace da yanayin daya dace.....zaki zauna a cikinsa kiyi aiki irin na kowacce matar aure......zaki zauna a cikin gida kamar yadda musulunci ya tanada......zaki kuma zaman gyara halinki yadda zaiyi daidai da halin mataye na gari,ta yadda wataqila a gaba idan kin hadu da wanda kika dace da ra'ayinsa,zai dauki mace ta gari ba makwadaiciya me qarancin duka wata siffa me kyau ba.......". Banda sunansu huda,da zabin maamah dake mata amsa kuwwa cikin kwanya batajin zai fadi dukka wadannan kalmomin bata zazzage masa fiye da abinda ya gaya mata ba. Ba zata iya tuna cin mutuncinta da akayi a duniya da yakai wannan muni ba......cin fuska irin wannan a gaban idanunta,cikin salo na gadara da ganin isa. A nutse ta daga idanunta da wani irin coolness ta watsasu saman fuskarsa. Kallon kallo suka yiwa junansu na wasu sakanni,kowa da abinda ke gudana cikin zuciyarsa game da dan uwansa. Fuska ya sake tsukewa sosai ya dage dukka girarsa biyun "I told you.....your attitude needs a serious adjustment.......bazanyi tolerating any nonsense ba.....just obey all of my rules" Yana kaiwa nan ya miqe a nutse yana ajiye mug din sannan ya sake zuba hannunsa a aljihun wandonsa still yana kallonta. "If you have any plans i beg you kada ki fasa......if you collect some money or something else.....kiyi duk abinda kike ganin kin tsara" Yayi maganar wani abu yana taba zuciyarsa,zarginsa kuma yana sake qarfi a kanta da ganin sunan maamah kawai cikin wayarta. Wani mahaukacin bugun zuciya ya haifar mata,ba shiri ta sake daga kanta zuwa gareshi sanda yake barin wajen. Wannan karon kam duk qwarewarta wajen iya boye hawayenta abin ya faskara,fara tsiyaya sukayi kafin ta sake jin muryarsa yana fadin "Qarfe hudu akwai walima wajen anni......bana african time don ban sanshi bama.....i hope you get it" Ya sake fada ba tare daya waiwayeta ba. Kasa tashi tayi a wajen wani irin baqinciki yana nuqurqusarta. Tsantsar tsana da haushin maamah yana sukar zuciyarta. Bata qyale ire iren wadannan abubuwan.......ba abinda yake sakata sarewa ko fargaba,amma ta mata mugun qulli da dabaibayi da 'yan uwanta?,why?.....me su huda sukayi da zata sakasu a wannan wasan?,me yasa ba zata bari suyi tsakaninsu ba a nan zata fahimci wacece sabreen din....muhammad jadda......yana buqatar ta karanta masa karatun d'iya mace,if gana expecting taka kowacce mace don yana da dukiya da kuma kyau......zata so ta zama macen farko da zata banbance masa tsakanin aya da tsakuwa,amma a yanzun hakan kuwa zai yuwu?.....she needs to be very humble don ta kubutar da 'yan uwanta......but ba zata dauki raini wulaqanci da kuma cin fuska daga wajensa ba,wannan shine lokaci na qarshe da zata bari ya jera mata maganganu masu zafi irin wannan,zata saka dukkan effort dinta donta gamawa maamah aikinta cikin sati biyu ta kauce ta barsu da rayuwarsu su qarata,idanma gasashi zatayi ta cinye dukka damuwarsu ce.....itama nata familyn ta sani,zaman lafiyarsu da kwanciyar hankalinsu shine first priority dinta. A nutse ta miqe ta ta soma kauda komai badon maganganunsa ba....sai don da gaske bai kamata abar komai a wajen ya lalace ba. Neman abinci da samunsa abune me matuqar wahala wanda itace shaida akan hakan. Ta killace komai sannan ta tattara ta wuce zuwa dakinta,saidai qasan ranta cunkushe yake da wani irin bacin rai tare da lissafe lissafe masu yawan gaske game da yadda zata tunkari rayuwar. "Don't be sad.....kada ki takura kanki da yawa.....just live your life normally yadda ba zaki cutu ba" Abinda zuciyarta ta dinga nanata mata kenan. Akan idanunta biyu ta buga uku tazo ta shude aka doshi hudu. Bata dako niyyar shirin komai bare akai ga batun zuwa walima. Komai nasu baya burgeta......bata da buqatar kuma ta cudanya dasu sam sam. Daidai lokacin da yake samanshi bayan dawowarsa daga sallar la'asar. Yaga kira daga security din dake waje sun shaida masa yana da baqi gasu zasu shigo ciki. Tunda yaji haka yasan 'yan gida ne.....inda baqin fuska ne lallai saisun nema izini an basu kafin su barsu su shigo,sai ya qarasa shiryawa cikin shaddar daya dauko,don already wandon yana jikinsa kafin yayi receiving call din. Wagambari ce a jikinsa,asalin tsadajjiyar wagambari sky blue da aka yiwa wani irin dinki na alfarma dake nuna zallar zamani da kuma sanin darajar ado da dinki. Ba wani mutum da zaiga sutura a jikinsa ya sake ganinta ya maimaitata,kusan sakawa daya yakewa kaya ya gama dasu,shi yasa duk sati cikin fidda suturunsa ake. Gaban madubi ya tsaya yana karya hular da zai sanya,shi gaba daya a takure yake,ire iren wadannan sabgogin bai saba dasu ba kwata kwata,wani harkar taro na biki,idan kanason ganin karsashinsa kazo sashen maganar kasuwanci. Kayan jikinsa kansu nauyi sukeyi masa,baisan ma me yasa a kayansa na wannan watan aka hada masa da dinkin manyan riguna ba,amna daya tuna farouq sai ya tabbatar shirinsa ne kawai. Halfcover ya sakawa qafarsa dan qasar italy da akayi cinikinsa da dollars masu yawa. Ya sanya hular saman kansa take wani irin mutum.....lafiyayyen half cast ya fito me matuqar daukan hankali da kwantaccen kwarjini daka iya wucewa da zuciyar kowacce d'iya mace. Waya daya ya dauka kawai sannan ya soma barin dakin. Yana sauka ne cikin takunsa dake bayyanar da nutsuwarsa jin kansa da kuma kamun kansa irin na cikakken namijin daya hada abubuwa da dama. "Wow summa wow.....hammana" Muryar amna ta fara sauka a kunnensa sanda yake fitowa zuwa parlor din. Yadda tayi maganar ya sanya murmushi subuce masa,ta kuma tuna masa da lokutan baya da yake very free ba kaman yanzu ba. Kullum ita ke bawa kwalliyarsa mark,anni na zaune a gefe tana musu dariya,saddiq na tsokanarta wani lokaci harsu sanyata kuka,shike tare mata shine ke hanasu. "Hamma ka sake zama ango sak......don Allah BB farouq,kalli ta nan gefen" Sai datayi maganar ya lura da farouq dake zaune kujerar qarshe riqe da wayarsa yana dannawa. Kadan ya daga kai ya kalleshi ya maida ga wayarsa "Yayi kyau mana amna.....amma kubarni nima soyayyata nake qoqarin gyarawa......Allah bazan qara wata uku a qasa ba.....guy dinnan daga jiya zuwa yau kalleshi ya sake canzawa?". "Stop it farouq......" Fuad yayi saurin fadi yana duban amna kafin ya maida kallonsa ga farouq din. Ya fahimci sarai abinda yake nufi,akwai amna a wajen "Hamma........am eager to see my aunty wallahi.....where's she?" Ta furta alamunta na nuna da gaske sabreen takeson gani,tana jin qaunarta sosai har cikin zuciyarta saboda hammanta. "Jeki fito da ita" Ya fada yana yiwa amna nuni da hanyar. Bata ko tsaya sauraren komai ba ta wuce wajen da sauri saurinta. Qarasa takowa yayi wajen da farouq ke zaune bayan wucewar amna din,aje wayar farouq din yayi yana dubansa. "Mutumina......akwai labari kenan" Ya qarashe zancan yana kashe masa ido. Harara ya gasa masa "Gidan jarida na bude daga jiya zuwa yau baka sani ba?" Dariya sosai farouq ya tuntsire da ita. "Idanma hakanne Allah an maka uzuri.....da gaske ba wani abu sabo?,baka kawo kusanci tsakaninku ba?" "Kaga don Allah malam dakata" Ya fada da husky voice dinsa "Na gama gane inda ka dosa gaba daya fa.....na gaya maka ne abinda yasa na kawo ta cikin gidan nan kenan ko kuwa?,ko bunsuru ne ka aje?...." Dariya sosai ta qwacewa farouq fiye da dazu,yayi qasa qasa da muryarsa yana dubansa "Maganar gaskiya ban yarda dakai ba.....i know you kaima ka san da wannan......a hadaka da halal dinka gidan da ba kowa saikai da ita.....kuma kacemin bakayi filling distance din dake tsakaninku ba.....anya wannan kyan da naga kanayi zakacemin duka a banza yake?". Rasa me zaiyi masa ya huce yayi,sai kawai hannunsa ya fada kan remote din dake gefansa,ya shammaceshi ya wurga masa ya sauka a kafadarsa. Duk duniya farouq kadai ke masa irin haka,yana sake hararasa yana zura hannunsa a aljihu ya fiddo wayaraa Idanunta kawai ta ware daga kashingiden da take sanda taji ana knocking na qofar. Kashingidar da ta yita ne kawai tana tunanin abubuwa masu yawa tare da qoqarin cudanya abubuwan dake mata kai kawo cikin kwanya. Tunani kala kala ta dinga yi sanda taji ana knocking din.....shine ya biyota ya sake cin zarafinta ko kuwa?.....wasu ne suka sake zuwa gidan ko ko yaya?. Daga qarshe da taga bata da zabi dole ta motsa labbanta tana fadin "Waye?" "Nice adda....na shigo please?" Amna tayi tambayar cikin zaquwa. Kiran adda din da akayi sai ya sosa mata wani miki,mikin kewar 'yan uwanta wadanda su kadai ke kiranta da wannan sunan. Ambatar sunan ya sakata miqewa ta zauna sosai tana zuro da qafafunta qasa. "Shigo" Ta amsa kawai kai tsaye ba tare da tasan waye ba. "Assalamu alaikummm" Amna ta furta duka tare da shigowarta cikin dakin cikin murmushi tana riqe da handle din qofar idanunta akan fuskar sabreen yayin da fuskarta ke qunshe da wadataccen murmushi "Wa'alaikumussalam" Sabreen ta amsa mata tana mata duban rashin sani. "Ma sha Allah" Amna ta furta a sarari tana kasa dauke idanunta daga kan sabreen,murmushin saman fuskarta kuma ya kasa bacewa. Dama ta sani......ta sani tabbas hammanta ya iya zabe......tasan hammanta lallai zai zabo matar da ba irin ta kowa ba,amma bata taba tsammanin iya zabinsa yakai har kaman haka ba. "I know.....kece adda sabreen dinmu ko?" Tayi tambayar da murmushi sosai tana nunata da yatsa idanunta a kanta. Dan shuru sabreen tayi tana kallonta ba tare data iya amsa mata ba,kwanyarta na mata lissafin wacece wannan din?. Tana da surutu sosai da alama,amma kuma yanayinta kadai ya gaya mata me kirki ce. "Sunana amna hamza kibiya.....nice autarsu hamma fu'ad". Tayi mata bayani a taqaice saboda ganin yadda take mata kallon rashin sani. Ta fahimci sarai bayaninta......qanwarsa takeson cewa,kamar ta basar sai kuma wata zuciyar ta tambayeta "Meye laifinta ita?" Don bataga wani hali na daban tattare da ita ba duk da a yanzun ta fara ganinta,amma bahaushe yace alamar qarfi tana game qiba. Har amnan ta sare,sai kuma taga ta saki qaramin murmushi da yayi barazanar dauke hankalin amnan saboda yadda ya fidda kyawun innocent face dinta "Qaraso mana" Ta furta tana miqewa tsaye tare da komawa saman sofa bed". Dukka energy dinta ya dawo,ta tura qofar a nutse tana ci gaba da murmushi ta tako ciki tana samun wajen zama saman wata sofa din ta daban *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 19 19 "Am sorry aunty.....hala nayi disturbing naki kina hutawa" Ta sake fadi tana murmushi. Maida mata martanin murmushin tayi,wanda har sai da amnan ta furta "Ya salam,wanne irin kyau ne haka?". Kai ta girgiza "Ko kadan....." "Barka da rana,kin yini lafiya?,ya baqunta?,anni na miki ban gajiya,munzo mu wuce dake wajen walima......kowa yanaso ya ganki don jiya baku samu shigowa ba saboda dare ko?" Ta jero dukka abinda ke tafe da ita da wanda ke ranta kamar ba itace anni ta jawa kunne kada tazo ta cikata da surutu ba. A iya bayananta kawai ta gane wacece ita.....diyar matar nan da cikin kalamanta kawai zaka fahimci nutsuwa gami da tarin ilimi a ciki,wannan ya sanya sabreen sake sakar mata jiki kadan,saidai ta wani bangaren tana tunanin ta inda zata zamewa zuwa walimar,don sam bata shirya sake shiga kowanne taro ba. To na meye ma zata yita nuna fuskarta wa danginsu,bayan bawai tazo bane don ta zauna?. "Amma walimar......" Sai maganar tata ta katse saboda daga mata hannu da amna tayi sakamakon shigowar kira,tayi blushing kadan sannan ta kalli sabreen "Anni fa ba zama anyi suruka.....ungo nasan kirannan naki ne". Batason katsewa amna doki da farincikin da take ciki,don haka ta miqa hannu dole ta karbi wayar "Idan ba zaki samu daman zuwa ba diyata kada kiji kin takura.....kiyi zamanki,dama taro ne na sanya albarka,sai a sallami mutanen". Ji tayi ba zata iya mata haka ba,ba zata iya watsa mata qasa a ido ba,don haka tace a hankali "Muna hanya in sha Allah" "To Allah yayi muku albarka,Allah ya kawoku lafiya" "Ameen ameen" Ta amsa tana miqawa amna wayar idanunta nabin amnan da kallo. Ta fahimci wani farinciki takeji sosai,duk da batasan na meye ba,ganin amna din sai ya tuna mata da huda dinta,duk da ta girmi huda,saidai ita kuma ta girmi amna qila sa shekara uku ma ko hudu. Dole ta miqe ta soma qoqarin rage yafen jikinta da dankwalin kanta don shiga wanka,ta lullube jikinta da qaton towel ta wuce tabar amna tana bata labarin sabreen din,abinda yaso badda bacin rai da takurar zuciyar da take ciki ta shige bayi da boyayyen murmushi a qasan fuskarta. Komai na toilet din na kayan wankan ba irin nata bane,amna tunda ta karanta sunan products din da brand dinsu tasan harka ce kawai ta girma akayi. Daga yanayin sulbi da qamshin shower gel din kadai ta sake sallamawa,wannan ya dauketa minti kusan ashirin sannan ta gama. Towel biyu kawai ta shigo dashi,ta daura dayan,dayan kuwa dole ta nade kanta dashi saboda sumarta data jiqa da ruwa,ba wanda zata yafa don suturta jikinta,don haka ta sako shower slipper din zuwa bakin qofar toilet din ta cireshi saman water proof doormats din dake sashe na biyu na toilet din ta murda handle din ta bude qofar. Daidai lokacin daya soma duba agogo ganin sun sakashi dabi'ar daba tasa ba.....dabi'ar daya tsana ya kuma ja mata kunne a dazu da kada ta soma aikatata kwata kwata. Tsaki yaja ya fara lalubar number wayar amna,saidai ya kirata kusan sau uku bata daga ba,wannan ya sakashi miqewa a fusace yayi ciki yana cewa farouq "Ina zuwa". Takawa kawai yakeyi cikin hallway din ba tare da yasan wanne ne dakinta a ciki ba?. Haka ya dinga gota bedrooms din a hankali,sai daya isa na qarshe sannan yadan tsaya cak yana kasa kunne duk yasan bazaiji motsin komai ba saboda yanayin door din,a jikinsa kawai yaji da mutum a nan,sai ya juya yana fuskantar qofar ya murdata da dan zafin nama. Opposite suke tsakanin qofar toilet din dana shigowa dakin,wannan ya sanya kai tsaye kowanne idanunsa ya fada kan dan uwansa sanda qofofin suka bude lokaci guda. Budewar da taja hankalin amna wadda take zaune tana jiran fitowar sabreen. Sarqewa idanunsu sukayi lokaci guda......fuskarta tayi fresh sosai,glowing din nan da fatarta ta qara samu saboda gyaran data samu na musamman ya sake bayyana. Ruwan da tayi wankan dashi ya sabbaba tarwatsewar qwayoyin ruwan saman fuskarta,sai suma zame mata tamkar wani ado,musamman sumar gaban kanta data kwanta sosai ta kuma fito ta qasan towel din daya kimawa kanta don ta samu ya tsotse danshin da yake jiki. Ta sassannin dogon wuyanta duka wasu daga cikin sumar sun kwanta,sai suka zamewa wuyan nata kamar wani ado musamman kafadunya dake a tsaye da wani irin structure me daukan hankali da kuma tudu da zaunawar dukiyar fulaninta sosai a qirjin. Duka cikin qasa da second goma idanunshi suka kai wadannan. Wanda baikai mintunan da hankali da zuciyarka zasuyi zaton duka wannan karatun za'a iya yinsa a wadannan taqaitattun mintunan ba. Haduwar idanunsu na farko yayi mata ba zata,don bata taba kawo bayyanarsa cikin dakin ba,don haka ta maida qofar da wani irin sauri ta koma baya ta tsaya zuciyarta na wani irin bugawa. Idanunsa da yaji sunyi wani irin laushi ya janye daga bakin qofar yana tabe baki "Kamar gaske" Ya furta qasan zuciyarsa,zuciyar tasa tana ayyana masa Allah ne kadai yasan adadin mazan da suka ganta a hakan,tunanin daya sanya wani abu me ciwo ya tsaye masa a wuya. Wai wanne ma tsautsayin ya kaishi ajiye kayan da suke tamkar na kasuwa cikin gidansa?,zai iya killaceshi da gaske ya canza masa rayuwar da ta zame masa jini da tsoka?. "Ba damuta bane......damuwata na koya mata lesson ko saboda gaba......tasan ba kowanne kalar mutum kake tabawa ka kwana lafiya ba". Duban daya maida kan amna sai yaga itama shi take kalla.......daure fuska yayi tamau saboda ya karanci abinda ke fuskarta harda wani qunshe dariya "Karku kuskura ku wuce minti shida.....if not...." Sai ya nunata da yatsa kawai ba tare da yace komai ba ya juya ya fice yana tura musu qofar. "Adda......wallahi hamma ya tsani jira.....nasan kema kin sani,hurry up adda anni ma jira take" Muryar amna data sanar da ita ya fita. Wani wawiyar ajiyar zuciya ta saki,a hankali ta saki qofar data qanqame,sannan tabi hannuwanta da suke rawa da kallo. Da gaske ta tsorata,don tunda tazo duniya ba wani muharraminta daya taba ganinta a haka,wannan shine karon farko. Qoqari tayi ta hade hannayenta waje daya tana matsasu da kyau,sannan ta bude qofar sosai tana fitowa. Miqewa taga amna tanayi "Bari na baki guri adda ki shirya a nutse....." "Yi zamanki.....zan shiga dressing room na shirya" Tace da amna din,don idan ta fita ta barta fitowarta zatayi mata wahala.....infact ma zata iya canza shawarar zuwan. Tsaf ta shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa bayan ta gama bulayin neman kayanta na gida,saidai ko ire irensu bata gani ba,sun lume sun narke cikin uban suturar dake danqare da closet dinta. Chantilly veil ta yafa daya dace sosai da atamfar jikin nata. Ta fito da wani irin kyau da kai tsaye bahaushe ke cewa qyallin goshin amarci.....saidai itakam ba days,tsabar gyaran jikin da tasha ne da kuma yadda ado ya zame mata jiki. "Tubarkalla ma sha Allah......tabarakarrahman......kiyi haquri adda inata tankaki.....i can't control my words ne wallahi". Murmushi kadan ta yiwa amna din,zuwa yanzu sai takejin kamar ta saba da halinta ne ma,tana da saurin sabo da shiga jikin wanda take so "Na gode" Ta fadi tana sanyawa qafafunta wasu high hill wanda kaman an yisu ne dama musamman saboda kayan jikinta. Kamar amna din ta mata magana amma sai ta bari kada sabreen din taga kama ta fiya rawar kai,a haka suka jero suna fitowa zuwa parlor din. Yayi relaxing sosai cikin kujerar kamar wanda bacci ke shirin dauka,saidai babu ko guda daya.....wata lafiyayyar kasala ce ta saukar masa tun daga fitowarsa daga cikin dakin. "Barka da fitowa sister" Maganar farouq kenan da taja hankalinsa,ya dauke idonsa daga email din da yake dubawa wanda duka ya raba hankalinsa gida biyu ne,daya kan ibtila'in faduwar darajar gold da diamond da suka wayi gari dashi......daya akan saqonninsa wanda kusan duka maganar dai daya ce,shirye shiryen bude company da yake tunanin jibi zai wuce abuja saboda baqinsa da yake kyautata zaton zasu fara sauka. Farat daya ta gane muryarsa,kaman amna shima sai take kirkinsa ya lullubeta,bawai murmushi tayi ba,amna ta sassauta fuskarta sosai suna gaisawa. "Ya kwanan baqunta?" "Alhamdulillah" Ta amsa masa itama tana rufe handbag dinta data jefa wayarta a ciki "Ma sha Allah....Allah ya bada zaman lafiya,ya baki ikon riqeshi" Yayi maganar yana maida dubansa ga fu'ad. Ko wajensu baya kalla tun duban farko da yayi musu bayan fitowarsu. Batace komai ba sai amna da tayi murmushi me sauti "Dude.....muje ko?" Farouq ya buqaci hakan "Kuje kai da amna.....gamu nan fitowa" Ya bashi amsa bai ko daga kansa ba. "Alright" Ya amsa masa yana daukan gorar ruwan da fu'ad din ya fito musu da ita yayi gaba amna na biye dashi. Shuru ya shude a falon na kusan mintuna biyu,bata ce kanzil ba kaman yadda shima baice ta tafasa a sauke ba,kowa yana ji da tashi izzar da girman kan. Ji tayi ta dauki iya adadin tsaiwar da zata iya.....ba zata dauki wannan halin nashi sam sam ba,don haka ta juya ta fara motsawa da zummar barin wajen "Hey!....Waye ya baki izinin tafiya" Ya fada da boldness cikin muryarsa. Abun taji ya mata wani iri.......wani baqon abu guda daya cikin rayuwarta. Batasan namiji yayi mata tsawa ba saidai ma ya lallasheta......batasan namiji yayi mata umarni ba.....a kullum ita ke basu umarni.......ba'a keeping dinta ta jira mutum saidai shi yayi jiranta koda awanni nawa tayi nufin qararwa a wajen. *DUNIYAT LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 20 20 Tana tsara komai a sanda takeso a kuma yadda taga dama......kuma a bita a hakan. "Kina tunanin hatta dressing naki zakici gaba da yinsa yadda kika saba?......idan nace komai naki zai canza ina nufin komai din......ciki harda shigar da bata dace ba.....bata kuma yi ba,ki kalli amna.....kin ganta da irin wannan useless mayafin?". Iska sosai ta shaqa har cikin ranta tana jin wani zafi.....abinda yakeyi matan wasu abubuwa ne da babu d'a namijin da ya taba yi mata shi sai shi. Sai taji haqurinta ya gaza jurewa......don haka cikin muryarta me nuna bacin rai tace "Kana zaton baiwa ce daka shiga kasuwa ka siyo?......meye alaqarka da dressing dina?". Maganar tata ta sakashi gyara zamansa sosai. Yadan jijjiga kai "Kin shirya wasan kenan kema?.....musu?,taurin kai.....abubuwa biyu da nafi tsana a rayuwata" Yayi maganar yana kada yatsunsa guda biyu idanunshi akanta duk da baya iya ganin fuskarta "Bauta.....meye marabar dambe da fada?.....kina tunanin kudin da kika sacemin kimar kudin aurenki sunkai yawan haka?......banajin kinkai tsada haka.....well,ba wannan ba,ki shiga ki sauke wannan banzan mayafin ki saka sutura sosai a jikinki......karki bari na maimaita maganata......i hate it". Cak maganan ta tsaye mata a rai,wani irin bacin rai ya taso mata. Wannan ya sanya da sauri sauri ta fara yin gaba,don tanaji muddin taci gaba da tsaiwa a wajen zai iya gano lagon fushinta,abinda kuma taci alwashin ba zata taba bashi dama a kai ba. Ci gaba da birkita closet din tayi bangaren veils cikin bacin rai,gaba daya veils din taji basu yi mata ba,sai kawai tahau tube kayan,ta kwabesu tas ta fara neman wasu daban. Turkey dress hannunta ya fada kai,cikin shigar da tafi so kenan,sai ta fara shirya kanta cikin turkey abaya din wadda cikin qanqanin lokaci ta rufe mata jikinta ruf,ta kuma fiddo da kyakkyawar baby face dintannan. Haka kawai sai taji tafijin dadin shigar,duk da dama tun asali ita din bata iya shigar bayyanar da tsiraici ba.....kawai dai Chantilly veil yana cikin veils din da tafi so,kuma ko a yanzun ba zata bari ya rabata dashi ba. Motsin tahowarta ya sakashi daga kansa a nutse. Duba daya yayi mata ya kauda kanshi,sai ya miqe yana ficewa tun kafin ta qaraso. "Ya Allah......wai BB don Allah a ina hamma ya samo adda?" Amna data kasa daurewa sanda ta hangi sabreen na takowa zuwa inda motoci ke jiransu ta fada. Iya takunta kawai saika dauka rausaya ko kuma yanga takeyi ta cikin hill shoes din data sakawa qafafunta masu igiya. "BB.....wai dama hamma shima yana kallon 'yammata don Allah?". Boye dariyarsa farouq yayi,don sarai yaga isowar fu'ad wajen amma bai nunawa amna ba "Me yasa kika ce haka?" "To ai......hamma fa kaman horror yake......ina noticing nasa duka shekarun nan,Allah saiki wuce ta gabansa amma baisan wacece ke ba......to amma ya akayi idanunsa suka kai kan addana me mugun kyau haka?" "Yaushe kika zama gulmammiya amna?" Farouq daya kece da dariya ya fada yana satar kallon fu'ad dake tsaye kawai ya kasa cewa komai. Dariyan itama takeyi "Allah BB......ban taba ganin mutumin daya iya zaben mace ba irin hammana......da gaske hamma ya hadu tako ina,komai nasa ya banbanta dana kowa" Ta fadi hankalinta kwance batasan yana a wajen ba. Zabura ta danyi da jin gyaran muryarsa,tsaf ta dinke bakinta tana raba idanu "A nan za'ayi walimar ne?" Ya fada yana jifan farouq da wani irin kallo na zaka sani ne. Dariyarsa ya yiwa control yana fadin "No.....aike muke jira,ko ka manta kaika koromu waje zakayi ganawar sirri da madam" "Enough" Ya fada yana tura masa murfin motar kaman zai bugeshi cikin nuna alamun ka soma wuce gona da iri. Hakan shi yayi masa,don haka yaja murfin ya rufe yana gaya masa shi da amna zasu tafi a nan. Baibi ta kansa ba ya nufi ainihin motarsa qirar Mercedes Benz G400d baqa wul daketa daukan idanu wanda haka ke nuna sabuntarta da kuma kalar kulawar da take samu. Da sauri daya daga cikinsu ya bude masa,kai tsaye ya wuce ya zauna sosai idanunsa na sauka a kanta. Ya tsani jira sosai,baisan me yasa take tafiya kaman ba zata qaraso wajen ba,bayan ya tabbatar taga inda ya shiga. _wataqila da wannan take sake samun damar yaudarar maza_ tunanin daya d'arsa masa a rai kenan,wanda ya sake sanya mishi qyamarta ainun,har yakejin kamar ma bazai iya hada numfashi da ita cikin mota guda ba. Ba zata bari ba ba kuma zata sake tayi wani abu na zubewar kimarta da mutuncinta gaban guards dinsa ba,wanda dukkaninsu haushinsu takeji. Bataga meye dalilin da zai zube qatti irin wadannan suna kewaye dashi ba kamar tsohon barawo ko wanda yaci kayan wani ba(a iya nata sanin na iya tsaron daya zama dole me harka irin nashi ace ya samu),me yasa bazaiyi rayuwa normal irin ta mutane ba?,da wannan kalar tasa rayuwar kenan itama yakeso ya tursasata ta zama haka?,tayi rayuwa irin nashi?,bazai yiwu ba kuwa. Daidaita zamanta tayi sannan aka maida murfin motar aka rufe mata,sai motar ta dauki shuru sai sassanyan qamshinsa daya danne nata,har ya zamana duk wani numfashi da zata shaqa tare da qamshin nasa yake zuwar mata hunhunta. Tsaki ta saki a boye yadda bazai ji ba,ta maida kanta daya window din da take zaune daura dashi. Batasan sun fara tafiya ba sai da taga motar ta fara sulalawa tana nufar makeken gate din gidan suna gilma shukokin da aka qawata wajen dasu. Basuyi nisa ba kira ya shigo masa,wanda shi ya zame masa abokin tafiya. Duka maganganun cikin harshen turanci yake yinsu da wani irin accent dake nuna zallar qwarewa gami da gogewa a yaren. Kusan fin rabin maganganun nasa ba wani fahimtarsu takeyi ba,don zuciyarta tayi nisa da wani tunani na daban. Ta wani bangaren kuma yadda yake lanqwasa harshensa ba kowanne word take ganewa ba a matsayin karatunta na wadda ya dakata daga aji biyar biyu na babbar secondary wato senior secondary school. Sanda motarsu ke qoqarin cusa kai ta cikin babbar gate din dake da wani irin girma da kuma jan hankali,a sannan ne ya katse wayar ba kuma don ya gama ba. Ya kashe wayar gaba daya tana kallonsa ta gefen idanu,ya zurata cikin wani dan abu daya matsa ya fito ya saka wayar ya koma ciki. Adan qaramin zamansu na mintuna ta karanci abubuwa daban daban tattare dashi,kusan kaman komai nasa na dabanne kuma daban yake,saita tabe baki sanda suka isa babban parking lot na alfarma da gidan ya mallaka. Qasa tayi da kanta tana jan mayafin data lullube kanta dashi sanda take hangar wasu mata suna bullowa daga wata qofa da tafi kusa da parking lot din,kafin takai gayin komai amna ta bayyana ta kama murfin tana budewa,abinda ya bata daman jin maganganunsu. Muryar amna ta fara ji "Inna uwaisha......ga addan namu.......ku fito mana da ita a hankali" Ta qarasa fada tana qaramar dariyar dake nuna zallar farincikinta "Kinyi qoqari auta sannu.......kin gama naki" Wadda aka kira da uwaisha ta fadi tana matsowa gaban motar "Kamar gaske" Sautin muryarsa ta fita a hankali ya furta sanda kan sabreen ke qasa tana jin wani fargaba haka kawai na haduwa da mutanen da batasan su kuma meye nasu kalar halin ba,sunan auta da taji an ambata sai ya sanya duka tsigar jikinta ya tashi,haneefa da tun da safe take kokawa da tunaninta ta fado mata.....ko yaya ta wuni?. "Zallar karamci da girmamawa da mutuntawa muke gabatar miki" Abinda inna uwaisha ta fada kenan kamar tasan abinda sabreen ke wassafawa qasan zuciyarta. Miqa mata hannu inna uwaishan tayi tana fadin "Sauko a hankali nayi miki jagora zuwa ciki,ki shirya don kowa na dokin jiranki". Bata musa ba ta sakawa inna uwaishan hannunta "Fatabarakallahu ahsanul kaliqeeen......da iya lallen nan ma kawai an tashi kaina yallabai". Inna uwaishan ta fada tana dariya dariya idanunta akan muhammad fu'ad dake qoqarin ficewa a motar sannan ta maida dubanta ga amna data dage mata gira alamun Yes. Inna uwaisha na daya daga cikin makusantan anni da suka daukeshi tamkar d'a,duk da cewa tana da jika qwaya daya amma idan kaga suna raha da amna saika dauka yaya ce da qanwarta,hakanan suma ta daukesu duka mazan gidan. Bai iya cewa komai ba,sai dan motsawa da labbansa sukayi alamun murmushin dole kawai ya sanya qafafunsa ya fice daga motar. Kunnuwanta kawai ke iya jin surutansu amma idanunta suna a rufe. Batasan ina suke nufa ba saidai idanunta na iya kallon lullubabban luxury marbles din dake shimfide a wasu sassan na gidan,a haka taji sun isa wani daki da a nan inna uwaisha tace da ita "Fell free sabreen.....ki shirya amna zata tsaya dake,idan kun kammala zan dawo mu wuce wajen taron,kowa ke yake jira". Kai ta gyada a hankali,cikin ranta kuma tana zancan zucin wanne shirin kuma zata sakeyi bayan na jikinta. Sanda amna ta gabatar mata da komai na shirin shuru kawai tayi tana bin kayan da kallo......shin da saninsu wanne irin aure ne akayi suke wahal da kansu haka da kashe kudade da hidima?,ko kuwa kallo kawai sukewa abun irin duban bangon littafi ga idanuwan da basusan meye a cikinsa ba. Wata lafiyayyar Moroccan gown dake da wani irin ado na daukan hankali......saidai kuma duk da adonnan nata sam bata da nauyi ko kadan. Hade take da wani irin hijab dan qarami da yafi mata kama da na Indonesia ko Malaysia.....a ciki batasan wanne ne ba. Komai na kayan fari ne qal da wani irin haske me daukan hankali. Ita kanta bayan ta gama shiryawa batasan lokacin data dauka tana kallon kanta ba,sai take ganin kamar ba ita ba.....duk da kusan komai ma yana zuwa mata ne da wani irin ba zata da bata taba zato ko kawowa cikin rayuwarta ba. Amna ce ta fara shigowa wadda fiye da dazun a yanzunma ta susuce wajen yabawa sabreen din. "Inna Allah kwanan nan hamma zai manta da wani gold da Diamond" "Maza dai ya jiki" Inna uwaisha ta fada tana riqe hannun sabreen suna nufar qofar fita. Suna shiga wajen tasan sun iso,duk da kusan kowa na zaune a nutse ana sauraren jawabi daga bakin malamai. "Muna yiwa amarya barka da shigowa". Maganar data dauki amsa kuwa cikin hall din,ta kuma bawa maamah damar fara gyarawa tsaf don bayyanar da kanta a wajen. Ringing biyu wayar tayi ya daga yana sakata a kunnensa "Ya kamata ka qaraso wajen walimar fa.....akwai mutanen da zaku gaisa dasu" "Bana kusa" "Kaman yaya?" Farouq ya tambayeshi a mamakance "Eh.....kaman yadda kaji bana kusa,uzuri ya kamani nadan fita" "Why.....you know......" "Anni zata fahimceni idanma kai baka fahimta ba.....sai na dawo" Ya amsa masa yana katse wayar ya maidata ya ajiye. Shi a yanzun kasuwancinsa shine abinda yafi damunsa shine kuma gaba da komai,bai takurawa kowa ya matsawa kowa ba,don hatta da saddiq daya Kamata ace a yanxun suna tare suna duba al'amuran da suka taso musu bai masa magana ba,bai kuma ce komai dashi ba saboda yaga ya sanya kanshi cikin hidimar bikin sosai,ya bashi lokaci ya qare ya dawo hayyacinsa.....tafiya ce dai dasu tsakanin jibi da gata,kuma bazai dage masa qafa ba dole ya shirya su wuce. Girgiza kai kawai farouq din yayi,halin fu'ad saishi,baisan ma yaushe ya fita din ba bayan sun shigo cikin gidan tare. Ya sanshi sarai ya kuma sani,wani irin mutum ne shi da kasuwancinsa ke gaba da komai idan ka dauke shi anni abba da su saddiq,amma koma meye yana ji a jikinsa,yana Kuma fatan duk yadda yakai ga gujewa auren da bashi wani rashin muhimmanci ya zame masa silar shiryuwa da saituwa kaman kowanne magidanci. A nutse farouq ya ratso cikin mutane ya yiwa anni rada. Kai kawai ta gyada sanda idanunta suke kan sabreen dake zaune waje daya bata ko qwaqwaqwaran motsi. A iya haka tana iya hangen nutsuwa a tare da ita,sannan haka kawai takejin qaunar yarinyar cikin ranta. Tana iya hangen wasu abubuwan ta cikin mayafin dake lullube saman kanta,a sanda walima tayi nisa..... Kai kawo na mutane ya qara yawa tata zuciyar cike take da lissafe lissafe kala kala. Lumshe idonta tayi sanda aka fara gabatar da miqa gudunmawa ga amarya,wato kowa zaizo ya zube mata tasa gudunmawar adan wani babban qwarya dake ajiye a gabanta maimakon yin liqi,wanda daga nan za'a fara gabatar da lectures akan zaman aure. Numfashi ta sauke daga can cikin hunhunta,duk cika da batsewar mutanen dake a wajen bata hangi wani nata ko mutum daya ba. Sai takejinta bare a wajen da wani irin rashin sukuni da takura. *DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 21 21 A nutse aka fara zuwa daya bayan daya ana zube sabbin 'yan dubu dubun fil a miqe cikin bundles dinsu a gabanta. Ta rasa tsakanin burgewa da rashinsa wanne takeji cikin zuciyarta?,duk da ta hangi tarin nutsuwa da kamala a komai na taron. Idanunta ta sake dagawa a hankali ta cikin mayafin tana kallon bakin qofar shigowa gurin dake facing dinta......tamkar abinda ake jira kenan saita hangi huda na shigowa. Da farko ta dauka kaman gizo idanuwanta sukeyi mata ko kuma me kama da ita ne,saidai shigowar nadra da haneefa ya qarasa kore mata dukka shakkun data soma ji cikin ranta. Wannan bai saketa ba taga abinda ya kusa doka zuciyarta saboda firgici.....maamah ce.......tana biye dasu da dukkan alamun da zasu gwada maka tare suke......tare suka shigo,don waiwayawa haneefa tayi da alama kiran sunanta tayi,sai taga ta riqe hannunta haneefa na mata murmushi tana maida mata sukaci gaba da takowa wajen tare. "A ina ta gansu?,a ina ta daukosu?,ya akayi taje ko sukazo wajenta?,tun yaushe?,me kuma take gaya musu?" Tayi tambayar sanda taga ta tsaidasu duka su ukun kuma kowacce ta tattara mata hankalinta. Sanye take cikin wata 'yar ubansun super embellished me asalin tsadar da jikinta ke bada wani irin santsi tamkar ba atamfa ba. Tun daga yanayin shigar zaka tabbatar da gaske ta dauki duniyarta dama rayuwarta gaba daya.....hakanan da gaske komanta yana mata dadi yana kuma tafi mata yadda takeso. Daga bayanta hajja harira ce data shirya kanta itama cikin applique lace ruwan sararin samaniya. Ita dinma duba daya zakayi mata ka tabbatar da halin yazo daya kamar yadda abotar tazo daya. Kai tsaye ta daga yatsa tayi musu nuni da kujerar da sabreen ke zaune a kai,sai dukkaninsu suka maida idanuwansu kanta. Fuskokinsu suka cika da farinciki duk da basa iya ganin fuskarta sosai,suka motsa kamar zasu taho zuwa wajenta,amma sai taga ta sunkuya tana magana dasu. Cikin qasa da second talatin taga sun maida hankalinsu gareta.......sun kuma juya suna binta a baya zuwa hanyar data nufa,daidai lokacin da me gabatarwa ke bada sanarwar "Mahaifiyar ango ta shigo......uwarsa kuma zata marabceta" Maganar data finciko hankalin sabreen daga shingen tunanin data afka sanda take binsu da kallo suna biye da maamah sau da qafa.....kai kace ummeensu ce ta dawo duniya. "Uwa?.....mahaifiya?,wacece?" Ta samu kanta da shiga wannan rudanin tare da fatar a yau ta samu warwarewarsa,don haka ta buda dukka idanunta tana bin kowanne kusurwa da kallo tanason samun warwarar rudaninta. Cikin nutsuwa da girmamawa anni ta miqe tana dosar inda maamah ke a tsaye,fuskar annin shimfide da fara'ar data ratsa har qasan zuciyarta. Har yanzu gangar jikinta da ruhinta basu daina jin farinciki da alfaharin aurar da fu'ad ba......wani abu guda daya daya zamewa maamah tamkar dafi tsakiyar tsokar zuciyarta "Ameenatu ce ta aurar dashi" Kalmar da inda tana da ikon gogeta tsaf saita gogeta daga dukkan wata ma'adana ta kalamai. "Barka da zuwa......sannunku da zuwa......" "Uwa kuma mahaifiyar muhammad fu'ad jadda ba,ai haka ya kamata ne gabatarwarki ta fadi" Hajja harira dake tsaye gefan hannun hagun maamah ta furta da wata irin izza. Kallo daya anni tayi mata ta watsar da ita gami da bawa banza ajiyarta,idanunta suna sauka akan fuskar 'yammatan su uku da take ganin tamkar ta taba ganin fuskar a wani waje. Kallonsu kawai tayi suka fara gaidata daya bayan daya,ta amsa musu tana dafa kan kowaccensu da madaukakiyar fara'a da kuma kulawa,kulawar da ta sauka har cikin idanun sabreen wadda ruhinta gaba daya yana a wajen,saidai babban qalubalenta bata iya jin me aka tattaunawa akai. Tun daga tashin anni har tsaiwarta a wajen sabreen na tuna guraren data taba ganin fuskar matar ne. Indai da gaske itace anni......itace uwa ga fu'ad ba shakka ta santa......amma ta yaya haka ta kasance?,ya akayi yake da uwaye biyu?,me yasa anni data taba sani duk da alkhairi ya hadasu ba ita ta nema masa ita ba?,sai waccar baquwar fuskar da bata taba ganinta ba kafin faruwar wannan abun kaf tsahon rayuwarta?. "Barkanki kade Ameenatu.......sannunki da hidima" Maamah ta maida mata da wani irin salon murmushin da ya sanya anni tajishi har cikin jinin jikinta. "Ina tayaki murnar aurar da fu'ad da kika samu damar yi......wannan babbar dama ce da zata zame miki tarihi kuma abun tunawa watan watarana.......ina aka tanadarwa mahaifiyar fu'ad domin ta zauna ita da qannen matarsa?" Tayi tambayar kai tsaye cikin isa...... "Ai albarkacin kaza qadangare kansha ruwan kasko mariya....muhalli har sai kin baiwa wani" Anni ta fadi duk da rabin hankalinta yana kan yaran abubuwa masu yawa suna yawo a ranta. Waiwaya tayi ta yafito muhsina inna uwaisha dake shirin wucewa "Itace mariya.......a cikata da irin karamcin nan da aka gada,koda zata cika hall dinnan da jama'arta.....a tabbatar an gamsar da buqatarsu,a nuna mata dattako da dattijantaka" Dukka anni tayi maganganun da kai da bakasan komai ba zaka dauka zallar magana ce kai tsaye,saidai gasu hajja da maamah din dukkaninsu sunsan magana ce akayi musu me harshen damo. Juyawa abinta anni tayi tana komawa cikin jama'arta,maamah tabi bayanta da kallo tana jin zafin jirwayen datayi musu me kama da wanka. Zafafan baqaqen maganganun data fahimci kowaccensu,amma kuma saiga murmushi yana subucewa daga saman fuskarta "Kwanaki kadan suka ragewa izzarki ameenatu.....na rantse koda pant din dake jikinki da kudin muhammadu aka siyeshi saikin zareshi kin miqomin.......na rantse sai na sanya fu'ad ya gaya miki maganganun da zasuyi silar ajalinki......maganganun da zasu zame miki dafin da zuciyarki zata buga ta tarwatse pieces " Tayi dukka maganganun ita da zuciyarta tana me cike da alwashi. Duk da wadannan abubuwan data samu ta kuma aiwatar zuciyarta ta kasa samun nutsuwa ko qanqani.......sam farincikinta har yanzu rabi ne......daga sanda ta iso bakin qofar mansion House din Alhaji hamza kibiya duka sai taji ta raina nata gidan kwata kwata. Batajin akwai wani gida ko gini da fu'ad zaiyi mata komai kyau da dukiyar da aka narkar ya zauna mata a rai muddin zai zamana muhallin Alhaji hamza kibiya yafi nata......indai zai zamana matsugunnin ameenatu zai d'ara nata. Daina fahimtar komai tayi......daina fuskantar duk abinda ake gudanarwa tayi,dukka idanunta dama hankalinta suna kan 'yan uwanta,suna kan kowanne motsi da kai kawo nasu. Hankalinta taji yana tashi,bata qaunar kowacce mu'amala ko alaqa kome qanqantarta tsakanin maamah dasu,saidai yadda taga tana jansu a jiki,ta wani.mugun sake musu ko ita batajin ta sake musu haka. Haneefa duk girmanta tana saman cinyarta tana wani lallabata,irin lelen da haneefa din keso a matsayinta na auta take kuma qishirwarsa. Cafko hannun amna tayi wadda ta zuge tata jakar ta fara fiddo sabbin 'yan dubu dubu kaman ba'asan ciwo da zafinsu ba.....kamar ba wasu abu masu muhimmanci ba tana zubewa sabreen din. "Kiramin su nadra.....kice suzo yanzu yanzu injini". Dubanta amna tayi duk da bata iya ganin fuskarta sosai. "Su waye?" Ta tambayeta don bata gane ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana qoqarin saita kanta,sai sannan ta tuna amna din bata sansu ba "Sun shigo yanzu su da......." Ta dakata tanason tuna sunan da ake kiranta dashi "Su da maamah" Kai amna ta daga tana hangensu daga nan inda take,kwata kwata bata qaunar abinda zai hadata da matar,bata qaunar kallon da take binta dashi irin kallon dake fita daga idanuwanta zuwa kanta,amma zuwa aiken sabreen ya zame mata dole "Okay" Tace da ita "Na gode" Sabreen ta fadi da sauri saboda jin dadin zatayi mata abinda takeso a sanda bata da damar tashi. Da ido take bin amna sanda take nufarsu,duk wani taku dake qara kusancin ama dasu bugun zuciyarta qaruwa yakeyi,ta kasa dauke idonta daga kansu daidai da second guda har zuwa sanda ta qarasa gabansu. Taga amna ta mata magana,ita kuma ta waiwaya tayi magana dasu kafin ta sake dubanta still ta gaya mata wani abu daya sanya amna din juyowa ta dawo mata. "Me suka ce?" Ta fara da tambayar amna din tun bata gaya mata komai ba "Zasu zo.....zasu taho tare da maamah din wai". Idanunta ta maida ta lumshe tana girgizawa amna kai kawai. Wani irin rikitaccen yanayi yana sauko mata,kada dai ace suna jin wani sauyi na daban akan maamah kamar yadda takejin wajabcin bin umarninta tako ina yana ratsata?. Tun daga wannan sa'ar nutsuwa tayi mata qaura,ta kasa debe idanunta daga kan 'yan uwan nata,duk wani motsi murmushi da kuma fara'ar fuskarsu ya tabbatar mata suna jinsu ne cikin sukuni da farinciki,har zuwa lokacin da aka bada sanarwar isowar mahaifiyar ango zuwa inda surukarta take. Tamkar mejin tsoron wani abu haka zuciyarta taci gaba da bugawa sanda maamah ke kusantota tana takowa wajenta dasu nadra gaba daya. Idonta ta lumshe da sake budesu akansu gaba dayansu tana me kyautata zaton saisun iso gareta ne kai tsaye kafin aiwatar da komai......saidai kuma akasin haka ne ya faru. Kamar kowa suma wajen zuba kudin suka nufa,kowacce ta dire rafas na dubu dubu sabbi guda uku dake hannunsu huda kuma ta zuba biyar. Bin kudin tayi da kallo,suka kuma tsaye mata a rai. "Wai ina momma bahijja?" Tambayar da bata da amsarta batasan kuma wanda zai gaya mata amsar ba. Ta tabbatar daga kansu har zuwa momma ba wanda zai basu wannan kudaden son suzo su zuba a wajen.....amsarta ta fito sanda maamah ta cire wani rafas din ta bawa nadra da zummar ta qara a ciki. "To kuje ku gaisa" Maamah ta basu umarni sanda ta fara zube nata kudaden da suka ja hankalin mutane da dama. "Waye ya kawoku?, yaushe kukazo?,ina momma?" Ta damqe hannun nadra da tafi kusa da ita tana jera musu tambayar a gaggauce daya bayan daya. "Momma ta tafi yau....tun da safen mukazo,mun dawo gidan maamah......" "Tana da kirki adda.....kuma tace kema kina nan,zamuci gaba da ganinki.....kayanmu ma tace basai mun taho dasu ba......kawu yace muyi zamanmu zamufi samun kulawa". "Baki da hankali huda?" Ta fada da sauti me qarfi tana qoqarin janye lullubinta don ta samu damar saka idanunta cikin na huda. "Yi a hankali......idanun jamaa suna kanki" Maamah data sunkuya saman kanta tana maida mata lullubinta ta fada da murmushi akan fuskarta kamar wani abun arziqi take gaya mata. "Ku tafi mu zauna daughters" Ta fada da kulawa sosai a muryarta da cikakkiyar fara'a. Tana jin takunsu sanda suke sauka a wajen,ba damuwa ko wani abu cikin muryoyinsu,tana jin tafiyar nasu na buga zuciyarta sosai,tanaso qwalla ta fita daga idanunta komai qanqantarta ko zataji sanyi,amma ko daya bata samu wannan damar ba. Koda aka kirayi anni saita aike amna da wani qaramin akwati da ba wanda yasan meye a ciki aka ajiye cikin wani salo na siyan girma. *DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 22 22 Kafin a tashi tsaf ta rasa sauran nutsuwarta,wani irin tashin hankali takeji maras misali daga kowanne lungu da sashe na zuciyarta. Ba abinda ke gilmawa ta idanu da zuciyarta sai huda nadra da haneefa......ina momma bahijja?.....ina momma bahijja?,.....da gaske ne sun bawa maamah yaran?,ya akayi haka ta kasance?,ya akayi ta tafi ba tare da sunyi sallama?,ya akayi ta tafi ta barsu bata cika mata alqawarin data dauka akan 'yan uwanta ba?......zata sakene ta kalli rayuwarsu ta balbalce?,ko xatayi dukkan abinda ya kama tayi don ta tseratar da rayuwar yaran?. Wadannan sune tambayoyin da ta dinga yiwa kanta har a sanda take cikin kebantaccen qaramin parlor din da amna ta kawota bayan tashi daga taron,tace ta zauna zasu gana da anni. Dogayen yatsunta da suka sha lalle kawai take murzawa kanta a qasa,zuciyarta na wani irin zafi tare da jin qaguwar su koma gida ta lalubi maamah suyi magana ta sosai da ita.....koda tana jin kamar ta samu ikon sarrafa zuciyarta da bin umarninta cikin wani irin takura da takeji ana yiwa zuciyarta,.....to amma sam bata samu lago akan abinda takeji a zuciyarta game da 'yan uwanta. Qaunarsu darajarsu martabarsu da kuma soyayya da shaquwar data ginu tsakaninsu ba abinda ya sauya. "Assalamu alaikum" Muryar anni ta ratsa falon tana murza qofar ta shigo "Wa'alaikumussalam" Tada daga kanta kadan tana duban qofar gami da amsa sallamar. Kallon kallo suka yiwa junansu,kowanne a cikin su yanason tuna inda yasan fuskar dan uwansa. Sabreen ce tayi saurin watsar da qoqarin lalubo inda tasan fuskar annin,saboda gaba daya hankalinta ba'a nan yake ba,sai ta samu kanta kawai da zamewa daga saman kujerar tana gaidata,wata dabi'a data manta rabon data aikatata,amma a yau ta samu kanta da yin saboda wani kwarjini da taji matar tayi mata. "Koma ki zauna abinki daughter" Ta fada da kulawa amma saita kasa hakan,saita samu kanta da zama sosai tana tanqwashe qafafunta. "Na tsaidaki ko?,ga dare yana qara yi,duk da me babban sunan bai qaraso ba,uzuri ya taso masa daya saka dole ya fita" Kai ta sakeyin qasa dashi ba tare da tace mata komai ba,batasan me yasa matar take mata kwarjini haka sosai ba. "Bari muyi magana a taqaice a gaggauce......da farko ina miki maraba da shigowa cikinmu da kikayi,ina fatan Allah yasa ku zama abokan arziqin junanku.....Allah ya hada hankalinku waje daya......bani bace mahaifiyar fuad,amma idan na kira kaina uwa a gareshi nasan banyi laifi ba,ni din uwar riqonsa ce tun daga quruciyarsa har kawo yau.....hajiya mariya wato maamah itace mahaifiyarsa". Dole bata shirya ba maganar ta sakata daga kai da hanzari ta dubi anni,sai kuma ta maida ta sunkuyar "Baiyi sa'ar uwa ba.....ke kuma bakiyi sa'ar d'an riqo ba" Abinda ta fadi kenan qasan zuciyarta tana jin kamar a tsakaninsu annin ta fita daban. Anya ba halinsa Allah ya duba ba ya hadashi da uwa daidai da halinsa?. Zaren tunaninta ya katse sanda anni ke magana "Yana da kirki.....yana karamci,yana da tausayi yana da tausasawa amma fa.......ga mutumin daya fahimceshi. Bashi da sauqi ya fiya tsauri,bashi da tausayi ga wanda bai fahimci shi waye ba,bayason qarya.....bayason saba alqawari,bayason yaudara baya son ha'inci......sannan uwa uba baya daukar raini. Abu na gaba muddin zakayi wasa da addini taku ba zata taba zuwa daya ba.....muddin ba zaka kasance karimi kamar yadda yake ba ba zasu taba daina sabani ba,wadannan sune kadan daga halayensa.......ameenatu" Ta kirata da sunanta na ainihi,abinda ya motsa zuciyar sabreen kenan sosai "Ban gaya miki duka halayensa ba don na tursasaki kula da yarona.....na gaya miki ne don na sauqaqa miki qofofin zama dashi....na gaya miki ne don kiyi hanzarin mamaye zuciyarsa......na kuma gaya miki ne don na rage miki wahalar fuskantarsa......naso ace na samu zama da wasu mutane mafi kusanci dake don na tambayi naki halayyar na isar masa dasu a shimfide.....domin cikar mafarkina shine......gidan muhammadu yafi gidan dukkanin wani magidance zama aljannar DUNIYA......gidansa ya zame masa kaffara akan kowanne abu daya fuskanta a rayuwarsa a baya" Anni ta qarashe maganar har tsakiyar zuciyarta tana fatan mafarkinta ya tabbata. Miqa hannu tayi a nutse ta kamo hannun sabreen ta sanya cikin nata "Idan har zaki bashi dukkanin kulawa......idan har xaki nuna masa zallar soyayya irin soyayyar da uwar kewa danta.....idan har zaki kasance me addini tsafta da kwalliya.....xaki kula da abincin muhammadu tabbas kin gama samunsa a tafin hannunki......yana cikin yunwar soyayya da kulawa.....muddin ya samu isashiya da zata qosar dashi babu ko haufi kin gama mallakar zuciyarsa dama rayuwarsa gaba daya". Ta saurara ta kuma fahimci duka zantukan annin,saidai cikin nata zuciyar wani magana takeyi na daban "Inama ace zaki fahimci waye danki sani na zahiri ba fuska biyunsa ba......inama wata daban kike budewa sirrikansa wadda ta shirya xama dashi ba SABREEN me zaman wucin gadi ba". Dole ta sanyashi kashe duka wayoyinsa tun a hanya a sanda abdussabur yake tuqashi zuwa gidan anni. A cikin jikinsa da zuciyarsa yakejin wata irin galabaita da bai taba jin irinta ba saboda zurfafa da tunanin da yayi. Yana da kyau yaci gaba da tafiya a gabar da yake na sanya idanu akan kowanne motsi da abinda dukka yake da alaqa da maamah. A zarginsa me girma da qarfi ya sake hawa kan yarinyar.......ya sake samun gamsuwa da cewa akwai shirin daya shigo da ita gidan,tunda har qarfin alaqarsu yakai girman da zata kebanceta da wata number wayar ta daban wadda shi kansa baisan da ita ba. Wunin yau gaba daya fiye da rabin tunaninsa yau duka ya tafi ne akan hakan. Bazaice maamah maqiyayarsa ce ba.....hakanan bazaice bata sonshi ba,amma ta fifita kudi dukiya da abun duniya sama da tasu soyayyar.......kusan yayi mata fari kuma cikakken sanin da dan adam kan iya yiwa zanen tafin hannunsa koma fuskarsa......bazaiyi wasa da rayuwarsa ba.....hakanan bazai barwa maamah kowacce irin dama ba.....hakanan zai saka yarinyar a wasan da zata qara fahimtar batasan komai ba cikin duniya.....zai dafata da ruwa da kuma jinin jikinta. Yayi sallama ya shiga parlor dinne a sanda anni ke miqa mata wata irin takarda me daukan idanu dake qunshe da littatafai na addu'o'i "Akwai tsaftatattun addu'o'in mallakar miji a ciki,wadanda basu da wani aibu illa ko shirka a ciki,saidai suna matuqar tasiri wajen kama miki zuciyar mijinki a gareki" Ko alamun fa'ida bataji cikin bayanin anni ba......wannan mallkar da take fadi inda zata yiwu ta bawa maamah ita ta mallaki dan nata kamar yadda tace,ita kuma ta sakar mata 'yan uwa tabbas shine zatafi farinciki. Yana zaune yana sauraren anni tana jaddada mata "Ki raqe addu'a da kyau.....a yanzun kece garkuwan mijinki,garkuwar gidanki ma gaba daya" Baki ya tabe yana siririn tsaki qasan ransa. Inda anni tasan wacece ita tabbas da bata wahalar da kanta wajen mata wannan dogon jawabin ba,da tayi saving energy dinta kawai saboda gaba,a sanda zata fahimci wala'alla ko haruffan baqin dake cikin littafin ba zata iya hadawa ba ballantana ta karanta,don shi kam daidai da karatun sallarta bashi da tabbaci akai,don ya sani cewa Allah ya fada cikin qur'ani me girma _haqiqa sallah tana hana alfasha da duk wani nau'in abunqi_. Ya tabbatar da nutsatsiya kuma cikkiyar sallah takeyi bata yadda za'ayi ta kasa rabuwa da dabi'ar karuwanci da bin maza. Ko a motar kamar ba wanda yasan da zaman juna. Kusan nasa tunanin ma na tafiyar dake gabansa ne daga yanzu zuwa kowanne lokaci,yayin da nata tunanin ya.lula duniyar yadda zata fidda 'yan uwanta daga wannan wasan da bata shirya shigarsu ciki ba. Sanda suka isa gidan sam bata wani jira guard sun bude mata qofa ba,gurds din da take mutuwar jin haushinsu tun daga sanda suka hanata rawar gaban hantsi a gidansu. A yanzu kuma a wannan gidan ta fahimci dasu ake kowanne motsi,wannan wacce irin masifa ce kamar raqibu da atidu da buwayin sarki ya saukar maka da suka zama lallai ka rayu dasu don su dauki dukkan ayyukanka,masu kyau ko akasin haka. A gaggauce ta wuce duka falukan ta zarce hallway zuwa bedroom din,burinta kawai ta isa ga gallababbiyar wayar ta hadu da maamah. Da zafin nama ta birkita inda ta aje wayar kafin su fita,saidai kuma sama ko qasa ba wayar ba dalilinta. Cak ta tsaya tana gwama numfashi,sai kawai ta bude jakar data dawo da ita ta fidda asalin wayarta da take kiran kowa da kowa da ita. Asalin layin maamah din ta kira,wanda bugu biyu ta daga,saidai bata jiyo komai ba sai muryar haneefa daga gefe da alama hira take mata ita kuma tana fadin "Allah auta?" Idanu ta runtse,ta lura da gaske ta shiryawa wasan...... Ta ruwan sanyi takeso ta cutar da rayukan da basuji ba basu gani ba. "Me kikeso?,me kike buqata?" Ta tambayeta kai tsaye ba tare data damu ta amsa sallamar data mata ba. Wani shu'umin murmushi ta aje,sannan ta jita tana cewa "Haneefa jeki kwanta kema,idan na gama zanzo na daukeki mu wuce daki tare" "Tom" Ta amsa mata kamar yadda yawanci haka maganarta take,abun kuma daya sake sokar zuciyar sabreen kenan. "Mallakamin d'ana nakeso kiyi.....ni kuma zan mallaka miki 'yan uwanki ta ruwan sanyi,dama naki ne". Tayi mata bayanin hankali kwance. Suya sosai taji zuciyarta tanayi,tanason fadin maganganu da dama......tanason tayi abubuwa da dama amma kaman an danne harshensa sai zallar bacin ran dake mata zullo "Why ni?,me yasa saini ne?" Ta fusgi kalmar daga harshenta ta watsawa maamah ita. "Saboda ni a wajenki kawai na hango irin zarrar da nake buqata......a aikinki na gano abinda zaisa aikina ya cimma gaci.....uwa uba kina da wani irin kyau da zai iya saurin rusunar da zuciya ya kuma narka zuciyar kowanne d'a namiji". Qit kawai ta kashe wayar tana jifa da ita gami da cusa dukka yatsunta goma cikin sumarta. Maganganun maman sun isheta haka,a yanzu basu take da buqatar ji ba. Kowacce tsiga ta jikinta ta miqe,taji wani irin matsuwa da fatan isowar kayan aikin maamah din hannunta. Inama ace zai yuwu ta danneshi tayita dura.masa abincin?,daga safe zuwa yamma ya zame mata mallakakke kaman yadda takeso ita kuma ta samu yancin 'yan uwanta. Tabbas! Inda babu 'yan uwanta da maamah din tayi garkuwa dasu,babu abinda zai hanata nuna mata ainihin kalarta da kuma ainihin yadda wasan zai gudana. *DUNIYATA LITTAFI KUDI NE(PAID BOOK)* 08187255862 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 23 23 Har wani nauyi idanunshi ke masa saboda tsohuwar gajiya da sabuwar gajiya dake a jikinsa,ga kuma wadda ke jiransa a gaba. Wanka ya fara yi,sai kawai ya sauya pyjamas dinsa ba tare da yabi takan abinci ba don baijin gajiya zata barshi yayi hakan yabi lafiyar lallausan gadon nashi dake gewaye da kyawawan pillows daa luxury bedsheet din dake qarawa bed din zama wani na musamman me cike da alfarma da wata nutsuwar samun lafiyayyen bacci. Numfashi biyu kacal ya sauke wani lallausan ringtone ya katse masa relaxing din da yayi. Duk kiran da zai shigo wayar yasan na wani makusancinsa ne,hakanan a baya so din ya miqa hannu ya dauko shafaffiyar wayar me wani irin kyan daukan hankali. Sunanta da ya gani ya sanyashi miqewa daga kwanciya zuwa kashingida zuciyarsa tana bugawa,ya lumshe idonsa yana budewa lokaci daya,can qasan ransa yana fatan Allah yasa ba wani jagwal dinne ya taso ba ko zai sameshi. Cikakkiyar sallama yayi mata,ta amsa da wani irin yanayi na karsashi da kulawa. "Akwai baqi a qofar gida,sun gaya min securities na gidan sun hanasu shigowa" Har ya sauke qafafunsa qasan gadon da zummar yaje ya duba ta na'urar tsaronsa,sai ya tuna ashe ba'a gida yake ba nan wani sabon muhalli ne,baida tabbacin an gama installing nasu,dole ya koma ya zauna gefan gadon a nutse yace "Baqi kuma maamah?....at these late hours?" "Eh......ba wasu baqi bane......me aiki ce nace tazo don ta tayata zama,da kuma yanayin gidan naku dole saida mataimaki daban". Numfashi sosai ya zuqa yana fesarwa,kowanne taqi kuma kowanne taku da motsi na maamah magana ce me zaman kanta.....wanzuwar aiki ne da sai ka saka hasashenka da kyau zaka iya cimmasa. "Amma maamah ina tunanin tafiya zamuyi.....dani da itan gaba daya jibi idan Allah ya kaimu....so koda tazo dinma zata zauna a gidan ne ita kadai.....nace if possible ta bari idan mun dawo....i will call you saiki turota" Har tsakiyar kanta taji wani abu ya tsarta mata,hakan kuma ya bayyana har cikin sautinta daya canza nan da nan,abinda ya sake bashi wani haske. "Har zuwa yaushe zaku dawo?". "2to 3days ne.....just bude kamfani kawai zanyi na dawo" Ya bata amsa bawai yana nufin dukkan maganganun daya fada haka suke ba. Duk da bai iya qarya ba......amma a wannan muhallin ya samu fatawar qarya a kansa a yanzu halastacciya ce. Adadin kwanakin da taji basu da yawa sai taji damuwarta taqaitacciya ce........ta cika da fatan tafiyar ta sake basu kusancin da zai damqa mata dukka amanarsa a hannunta,yadda suna dawowa komai zai fara cikin sauqi aminci da kuma nasara "To yayi baida damuwa.....ammmm amma ba....kace su barta ta shigo na bada saqo ta bawa d'iyata". Kai ya jinjina yana cewa "Alright" Sai ya gintse kiran. Wadanda suke on duty ya duba sannan kai tsaye ya kira daya daga cikinsu. Saidai kafin basu damar bata damar shigowa sai daya basu dan qaramin aikin da tun kafin zuwaira ta qarasa ciki suka gama aiwatarwa suka tura masa. Bawai bayan ta shigo cikin gidan ba......tun daga farkon layin daya amsa sunan MUHAMMAD JADDA STREET ta gama raina kanta dama komai nata,bata sake tsinkewa ba sai da suka iso qofar gate gate guda biyu da fuskar gidan ke dashi daban daban......ta gama kuma narkewa gaba daya tun daga harabar gidan har zuwa falon farko da suka zauna suna dakon sabreen. Kowanne motsi da yadda laila ta gaza sukuni,ta kasa danne zallar zalamarta da kuma dimuwa da yadda gidan yake duka kan idanun zuwaira take yinsu,zuwairan da tayi banza da ranta tamkar ma batasan tanayi ba. Mummunar qullaci ta samu zuciyarta dayi akan hajja harira.....ko maamah bata fuskanci manufar harira na hadota da ita ba ta gama karantar komai.....baqinciki qyashi da hassadar ta zauna ita daya a gidan take mata......to itama ta lashi takobin zata gara nata wasan akan laila da hajja,zata kuma murza musu kalar nata zaren. Karo na biyu kiran daya shigo mata yadan darsa mamaki a ranta,saidai a yanzun da 'yan uwanta ke tare da ita,bata jin zata iya tsallakewa kowanne kira da zatayi mata.....don tana cike da tsoro da fargabar shudewar kowanne minti a sanda suke tare da ita. "Ki sauka zuwa falonki kina da baqi.....saqon farko kawai naci su baki.....kiyi qoqarin fara amfani dashi daga gobe zuwa jibi". Bata jira cewarta ba ta katse kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana binta da kallo kamar bata gane yaren da maamah tayi magana dashi ba. 𝐌𝐢𝐧𝐭𝐮𝐧𝐚 𝐭𝐚𝐥𝐚𝐭𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐲𝐚 𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐚 𝐬𝐡𝐮𝐝𝐞 Daidai sanda jerin motocinsa ke fita daga gidan don komawa nasu gidan,tana zaune daga gefe zuciyarta tayi wani irin nauyi dauke da tarin kalamai da al'amura da tayo tsarabarsu cikin gidan. Tasan tayi qasa d window din motar sanda amna tayo mata rakiya tana mata bangajiya,amma batasanma bata maidashi ta rufe ba saboda yadda zuciyarta tayi nisa a wani bigire na daban. Daidai lokacin da yake zaune bayan motarsa yana danna wayarsa yana qoqarin neman location na gidan da yazo din. Nishin motocin yaja hankalinsa ya cire kansa daga wayar yana maidawa kansu. Motocin muhammad fuad jadda daban suke,kaman yadda komai daya shafi jadda diamond chore resources ya fita daban. Cikin qirjinsa yake jin buri da fatan inama ya kasance tamkar wannan matashin me matuqar sa'a?.....wanda ya fado duniyarsa da wani irin sa'a da yayi Imani ba kowanne dan adam ke samun koda shigenta ba. A lokaci na quruciya......da qananun shekaru sanda jini ke zagayawa da kyau a jikinsa......ace ya mallaki d'anyun kudade irin wadannan?.....ya mallaki kyau da sura irin wannan?.....yayi wani irin tambari da kuma suna,sunan daya watsu sassan duniya dama kuma ba'a batun tambarar sunansa a qasarsa ta haihuwa. Kamar cikin majigin film.....kamar wulqawar walqiya cikin sararin samaniya ya hangi wani Kyakkyawar fuskar......fuskar daya aza dukkanin burinsa a kanta......fuskar daya sha kwana ya tashi da cikakkiyar sha'awarta tare da tunanin yadda zai maidata ta zama tasa har abada......fuskar da daga qarshe ta jefashi cikin bala'i masifa da barazanar faduwar kowacce daraja arziqi da wadatarsa a yanzu da yaketa fafutukar maidawa......fuskar da a yanzun ba fuskar da yake yunwar nema ya d'aid'aita rayuwarta irinta. Bazai iya cewa ga sanda ya zamo ya kuma diro daga saman motar ba sai da ya fara takawa da zafin nama da zummar ya kamosu,ingarman motocin suka masa wani irin fit suka barshi da kama iska ba tare ma da sunsan meye shirinsa ba. "Damn it!!" Ya fada a kausashe yana kaiwa iska naushi da hannunsa. Da gaske itace matar da muhammad fu'ad ya aura?,da gaske itace amaryar da akace masa ana yiwa walima yanzu haka cikin gidan Alhaji hamza kibiya?. Wani irin shu'umin murmushi ya subuce masa ya mamaye fushin da yake kwance akan fuskarsa,ya koma ya daki bayan motarsa da hannunsa daya dunqule "Good......komai yayi daidai" Ya kuma fada a fili yana buga wani tsalle ya koma saman motar yana ci gaba da sakin murmushi,a hankali a hankali murmushin nasa yake qaruwa kafin daga bisani kuma ya kece da wata iriyar dariya yana sake bugun bayan motar gami da furta "MUHSEENA" ainihin sunan da yake shine STAMP dinshi. Da sauri ya kuma saukowa,ya bude backseat din motarsa ya finciko wata magazine. Magazine ne da suka fidda sanarwar daurin auren da komai da komai,a sama an rubuta da manyan baqin _THE BILLIONAIRE'S WEDDING FATIHA_ Kusan babbban abinda suka yita jaddadawa shine......bikin babban mutum me arziqi kaman muhammad jadda din,yazo ba tare da wasu shagulgula da aka dade ana hasashen za'ayi ba,luxury events da kowa ke mafarkin zaiyi a matakin arziqi irin nasa,shin meye sirrin?. Murmushi ya kuma saki sanda ya karanta tambayar qarshe,sai yaji kaman shi ya cancanci ya amsa tambayar. "How i wish ina wajen da aka buga labarin nan?,tabbas dana basu full details na wacece wadda ya aura,ta yaya zaiyi shagulgula bayan BARAUNIYA ya aura?,TSOHUWAR KILAKI?" Ya fada a bayyane "Ameenatu!" Ya kira sunanta na ainihi dake rubuce jikin katin. "You will pay it......dole zaki biya ninkin farashinki" Ya sake fadi still a bayyane,boyayyen fushin nan dake kwance qasan ransa yana wani tasowa yana bashi tururin bacin rai har saman fuskarsa. A gaggauce ya koma cikin motar tasa ya wurga magazine din,shima ya shige ya kunnata gami da bata wuta ya finciketa yana barin layin don sam yama mance maqasudin abinda ya kawoshi layin. *_S A B R E E N_* Tun bayan sallar asuba take a zaune saman abun sallarta a qoqarinta na hana kanta komawa baccin daya zame mata al'ada duk safiyar duniya. Bata da matsalar shirya su haneefa breakfast da sauransu,duka wannan huda zatayi kafin su wuce,sai yau abun ya zame mata banbarakwai. Zuwa qarfe bakwai idanunta duka sun daddaure mata sunyi mata wani iri,ta miqe a hankali ta ninke abun sallar sannan ta taka tana nufar wata drawer ta zauna gefan gadon tana jawota. Ledar jiya ce da zuwaira ta kawo mata,ta fiddota tana qarewa ledar kallo. Abubuwa biyu suna karakaina cikin ranta,kokwanto da kuma qwarin gwiwa,saidai kuma qwarin gwiwarta a wannan safiyar tamkar yana son korar kokwanton da takeji,don haka ta riqe ledar da kyau ta fara takawa tana fita a dakin. Can qasan zuciyarta ta birkita da tunanin me ya samu wayar momma?,me yasa ta kasa samunta?. Daga daren jiya zuwa asubar yau ta kirayeta har batasan adadi ba,tanaso taji daga bakinta.......tanason taji me yasa tabar su huda a hannun waccar matar?. Tsaiwa tayi cikin kitchen din tana tunanin me dame zata dafa ko ta soya da komai zai narke a ciki ba tare daya bada wata alama ba?. Aqalla ta kusa minti biyar kafin ta wuce store din. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 24 24 Inda aka yiwa dankali Kyakkyawar ajiya ta duba,ta debi yadda take ganin zai isa,ta bude freezer shima ta debi nema ta rufe tana dawowa kitchen din. Yau sai gata kace kace cikin hidimar hada breakfast,abinda ya zame mata sai lokaci lokaci idan huda bata da lafiya sannan ta karbeta. Awa biyu ta share cikin kitchen din,sanda ta gama ta gama gajiya gaba daya,amma haka ta zaba warmer ta soma zuba komai a ciki. Sanda ta bude ledar da zummar fara gudanar da aikinta cikin ruwan tea da dankalin data soya da kuma farfesun naman sai taji hannunta yana rawa. Hannuwan nata ta sanya da zummar qulle ledar ta maida ciki amma sai sunan HUDA NADRA HANEEFA ya fado mata......daga bisani maganganun maamah suka dawo.mata fes,sai takejin kamar umarni ne akeyi mata na KI AIWATAR. Kai ta soma girgizawa,'yan uwanta sune haqqin farko da suka zame mata wajibi ta fara kubutarwa.......ba zata wofantar da rayuwarsu ba saboda mas'alar mutumin da ko qanqani baisan zafinta ko darajarta ba,don haka ta kunce komai......takuma aiwatar dashi kamar yadda zuwaira ta zana mata,ta debi kayan abincin ta jerasu saman dining. Tsaiwa tayi tana kallonsu,kamar ba zata bar gurin ba,sai kuma taja da baya ta fara takawa tana sauka daga wajen. ▄A nutse yake saukowa daga saman stairs din,sanye da wata lafiyayyar suit ta kamfanin BRIONI da suka zama number daya wajen fidda suit na manyan mutane daga auduga da zararruka masu daraja. Yayi wani irin kyau sassanyan kyau kaman yadda yanayinsa yake nunawa kamar yau din bai tashi da wannan kuzarin nasa ba dake sake bada bayanin cikakkiyar lafiyar da yake da ita. Qafafunsa sanye cikin rufaffun takalman dake faman daukan idanu suna qara bayyanar darajar da yawan nauyin kudaden da aka sanya aka siyesu. Hannunsa daya cikin aljihun trouser dinsa,daya hannun kuma yana sarrafa wayarsa. Sassanyan turaren nan nasa da bai cika hayaniya da yawa ba ina busawa a hankali yana karade ko ina. Wani irin qamshi ne na musamman dake tashin kan mutane da dama,saidai idan ka debe farouq har yau ba wanda zai iya gaya maka exactly sunan perfume din da yake using. Musaddiq da saddiq sunsha zuwa su sata,amma sun kasa samunshi ako ina bare su siya. A yadda yake saukowa daga shi sai wayarsa zaka rantse ba wata muhimmiyar tafiya bace a gabansa,kamar zaije qofar gidane ya dawo. Haka tsarin tafiyarsa yake,baya daukan komai sai documents dinsa da wasu mihimman abubuwa amma banda sutura. Kusan duk qasa ko garin da yake da huldar kasuwanci dasu yana da permanent gidan da ba abinda gidan ke buqata sai isowarsa.....idan ya sauka a wani gurin daban ba gidajensa ba to yayi hakanne saboda salon bad da hankali da wasa da hankulan abokan adawa na kasuwanci ko kuma dalili na ra'ayin qashin kanshi na haka kawai yaso. Duba daya ya yiwa hallway din ya maida idanunsa ga qofar da zata sadashi da parlor din,sai ya maida wayarsa side pocket na rigarsa sannan ya maida daya hannun shima cikin trouser dinsa yana takawa a nutse cikin falon. Sai daya zagaya falon tas ya gama duba komai,ya tabbatar komai yana a muhallin daya kamata ya zauna,sannan ya zarce falo.na biyu ya tabbatar da komai a yadda yakeson ya zama,sannan ya zarce kitchen zuwa store ya duba komai. Sanda yake baro kitchen din hankalinsa yakai kan dining din dake jere da warmers,ya zubawa gurin idanu na wasu mintuna yana qanqance ido,kafin kuma ya sauya akalarsa yana nufar wajen zuciyarsa cike fal da mamaki. Cak ya tsaya kan warmers din yana sake binsu da kallo tamkar wanda ke neman sunan wanda ya qera warmers din a jikinsu. Ya kusa mintuna biyu kafin ya zare hannuwansa daga aljihun ya fiddosu,bakinsa da yake motsi kadan kadan zaka kalla kasan akwai abinda yake fadi wanda duka bazai wuce addu'a ba,sannan ya miqa hannunsa a nutse zuwa ga warmer din yana furta "Bismillah" A fili,ya murzata ya bude. Daya bayan daya ya bude komai,hatta da hot water dispenser din da tayi using ta adana tea din sai daya saka cup ya zuba ya jerasu a gabansa yana qare musu wani irin kallo na qurilla. Ya kusa mintuna biyar a haka,sai ya saki wani siririn murmushi yana girgiza kai,ya saka hannunsa ya maida komai yadda yake kamar ba'a taba ba. Hannunsa ya miqa daga gefan table din ya ciro sticky notes guda daya,yayi gajeran rubutu ya manne mata jin warmer din ya juya da dan hanzari ba kaman dazu ba yana sauka a wajen. "Tabbas ita din aiken maamah ce......" Abinda ya gayawa kansa kawai kenan ya gangara yana ficewa gaba daya daga falon bayan ya tsinke waya guda daya data rage ta telephone din dake parlor din. Kowanne ma'aikaci yana tsaye a matsayarsa suna jiran dakon fitowarsa. Dukka guards dinsa suna tsaye a inda ya kamata kowa ya tsaya. A yau shigar fari kowannensu yayi,da wani irin tsarin shiga da sutura da zata bayyana alfarmar wanda suke aiki a qarqashinsa. Abdulgafar shugaban tawagar tsaronsa shi ya fara nufoshi a gaggauce cike da kuzari yana tarbarsa cikin girmamawa kaman yadda suka saba shi da mataimakinsa jordan "Good morning sir" Ya fara gaidashi kafin muryoyinsu ya karade wajen suna gaidashi suma "Morning.....hope you are fine?" "Fine sir" Suka hada baki wajen amsawa "Good" Ya maida musu yana gyada kanshi. "Jordan" Fuad yayi kiransa "Sir" Ya amsa yana matsowa. "Where's abdulbasit?" "Am here sir" Wanda aka kira da abdulbasit ya furta yana matsowa cikin shigar wani uniform da yasha banban da nasu jordan "Have you finished?" Kai ya gyada a girmame "Yes sir...." "Okay,kada ka manta.....zan bar muku jordan.....jordan,ba shiga ba fita har sai na dawo ko na bada umarnin hakan. Ko waye bazai shiga ba,ko waye kuma bazai fita ba......hope i made it clear?" "Yes sir" Jordan din ya gyada kai,don shi ya fahimci inda aikin yasa gaba,zasu maimaita salon aikin da sukayi satittikan da suka wuce kenan. "Yi mana addu'a" Ya fada a taqaice yana duban abdulra'uf wanda kusan duk sanda qaramin meeting irin haka ya kamasu shike da alhakin hakan. Cikin mintuna uku aka kammala kowa ya wuce motarsu,motocin suka jeru kamar kullum,security din dake kula da qofa ya wangale musu ita suka fice daya bayan daya. "Am on the way......banason jira" Abinda ya gayawa saddiq kenan da yayi kiransa sanda suke a cikin motar,sai ya kashe wayar kawai ya maida aljihu. Titi ya zubawa ido yana fesar da iska daga bakinsa. Baya tunanin maamah zata saka a kasheshi saidai wani abu na daban,amma ita kuma fa?,may be ta tsallake gona da iri,wala'alla ta wice limit da iyakokinta,amma duka ita maamah bata gani ba?,why zata zabi mace me irin wadannan dabi'u da halayen ta kasance a tare dashi?. Tambayar da yaji ta sake quntata zuciyarsa,abinda kuma bayaso ya faru kenan don yau din yana buqatar freshness don gobe rana ce me muhimmanci a wajensa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 25 25 "Nayi zaton tare zaku tafi?" Shine abinda anni tace dashi sanda yake zaune sosai gaban abba suna breakfast dashi. Kai ya girgiza "Ba daman hakan anni,idan munje ma zata dinga wuni ita daya ne saboda ba zama zanyi ba......akwai baqi da sauran shirin da zamuyi daga yau zuwa goben in sha Allah" Kai ya jinjina "To Allah yayi jagora.....yasa a bude a sa'a" "Allahumma ameen" Suka kusa hada baki wajen amsawa shi da abban. "Amma ba za'a kai mata abokin zama ba?" . Anni ta fada cikin salon nuna kulawa. Basarwa yayi don baison anni ta gane komai game da lamarin "Ba ita daya bace anni,banajin zata damu,akwai mutane a gidan". Kai ta gyada "To Allah ya tsare" "Ameen ya rahman" Ya sake amsa mata. Duka duka mintuna arba'in suka qara suka fice a gidan shi da musaddiq zuwa airport inda private jet dinsa ke jiran isowarsu. A hankali hasken ranar dake ratsowa ta tsakanin labule ya soma qarawa dakin haske yana kuma tabbatar da bayyanar rana sosai ya wuce kai tsaye ya taddata har inda take kwance,wanda wannan shine abinda ya sanya idanunta budewa a hankali suka kuma sauka kai tsaye kan agogon dake manne a dakin. Sha biyu na rana saura minti biyar kacal shine abinda idanunta suka gani,abinda ya sanyata ware idanunta gaba daya tana kuma miqewa da dan sauri. Bayan Hannunta ta saka ta mutstsike idonta tana sake duban lokaci,sam batasan tayi bacci me nauyi haka ba,don ko wanka bata samu tayi ba ta koma ta kwanta bayan ta tabbatar ta gama duk abinda ya dace. Miqewa tayi tana miqa,tana jin yadda gajiya kebin duka sassan jikinta,can cikin zuciyarta kuma tana raya lallai zuwa yanzu ya debi abincin yaci,tana sake jin wani tabbaci da qwarin gwiwar komawarta zuwa ga rayuwarsu ita da 'yan uwanta. Toilet ta wuce tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar atamfarJulius gold data zauna mata daidai jikinta da wani irin dinki da bazai takuraka ba. Sai a sannan taji cikinta yana wani yamutsawa....a lokacin ta tuna lokacin data dauka rabonta da wani abu me suna abinci cikakke. Plate tummy dinta ta shafa,sai ta miqe a nutse tana nufar hanyar fita daga dakin. Tun daga nesa idanunta nakan stairs din har tazo ta gotata tana fita falon farkon. Tadan shaqi iskar dake kadawa tsakanin hallway stairs din da parlor din,wani qamshi ne ke kai kawo na daban wanda bata taba jin sassanyan qamshi irinsa ba,wani sashe daban na zuciyarta kuma tana jin kamar ta taba ji ko sanin irin qamshin. Xarcewa falo na biyu tayi,tunda kuma ta fito idanunta suna kan dining din. Gudun zuciyarta ya qaru kadan,yayin da ta cika da fatan taras da komai ya tafi daidai. Bude komai tayi,daga kallon farko ta fahimci ba'a taba komai ba.....daga nan din kuma dukka gwiwoyinta na qafa da hannu sukayi wani irin sanyi,sai taji ta kasa tsaiwa,taja kujera daya ta zauna tana girgiza dispensers din taji ko yawan adadin tea din ya ragu?. Nan ma ba abinda ya sauya,yadda ta zubashi haka nauyin yake,sai ta saka hannuwanta guda biyu tana dafe kanta,daidai sanda idanunta suka sauka kan sticky notes din dake maqale a wajen iska tana dan kadata. Hannu daya ta saka ta ballota daga inda take liqen,ta sanya idanunta akan kwantaccen rubutun dake a tsare kamar wanda aka tafa a inji bawai hannune yayishi ba _mission accomplished_ iya abinda takardar ta qunsa kenan. Jujjuyata ta shiga yi tanason fahimtar saqon dake rubuce a jiki amma ta gaza kaiwa ga nan,abu daya ne kawai ya tsaye mata a rai da baici din ba. A niyyarta ta koma daki ta zauna ta jira wai koda zai sauko yaci bisa rashin sanin ya dade dayin nisa cikin gajimare. Amma qaguwa dason taga yaci din ya hanata komawar,sai tayi zaune a parlor parlor din tana saka kunne akan kowanne motsi na gidan,amma sam motsin da take iya ji din ba wani motsi bane na azo a gani,don hatta da securities na gidan bawai suna kusa da ita bane bare ta jiyo motsin nasu da kyau. Sha biyu daya daya da rabi biyu biyu da rabi ba wani batun motsin kowa da komai cikin gidan,zuwa lokacin ta fara sarewa da lallai bazaya sauko ba,don koda wasa bata kawo cewa wai baya cikin gidan ba. Koda zai sauko a yadda suka lissafa mata halinsa tayi imanin bazaici komai na daga breakfast din ba,wannan ya sanyata cikin mutuwar jiki ta tattare kwanukan tayi kitchen dasu ta ajjiye tana tunanin yadda zatayi da kayan abincin. A makare ranar tayi sallar azahar......har ta idar da sallar tunaninta ya karkata ga me ya kamata tayi?,ta shaidawa maamah din ko ta barta?,kada sanar mata ya sanyata ta dauka cewa gazawa ce har ta nemi yin wani motsi akan qannenta. Wannan tunanin ya sanyata ta share,duk kuwa da cewa wani sashe na zuciyarta a matse yake data gaya matan,amma ta danne da wani irin qarfin hali tana saka ran zai fito yaci na dare. Tana idar da sallar la'asar ta fada kitchen,ko a sannan ma tsaiwa tayi tana tunanin wanne irin kalar abinci zatayi da zaija ra'ayinsa har haqarta ya cimma ruwa?. Sai data kusa qure tunaninta kaf sannan ta zabi abu daya,ya wuce zuwa store tana duba dukkanin abinda take da buqata. Dab da magariba ta baro gaban dining din data cika da warmers masu dauke da abinci. Tana takawa zuwa hallway din tana satar kallon stairs din. Zuciyarta cike da mamakin wanne irin mutum ne shi haka?,wanne irin mugun baqin hali ne dashi da har zai debi wadannan wannin a qunshe a sama ba tare daya sauko ko anji motsinsa ba? "Ko yana zuwa masallacin ma oho" Ta furta a ranta a sarari tana jan tsaki gami da tabe baki,ta tura qofar dakinta ta shiga tana addu'a yadda a daren nan data saka hope me yawa,ta zuba komai da yawan adadi.....Allah yasa a wannan daren komai ya ratsahi har fiye da yadda maamah din keso don ta samu tickets din matsawa daga rayuwarsu ita da 'yan uwanta. Cikin toilet dinta tayi wanka,takuma shirya cikin sassaqan cotton lite material me sauqi. Sallar magariba tayi,sai taci gaba da zama a nan. A hankali yaran suka fado mata,sai taji tana kewarsu,tana so taji!muryarsu koda kuwa maamah din zata kafa mata wani sharadi na daban kafin ta barta ta gansu,wannan tunanin ya sanyata miqewa a nutse tana mamakin duka yau bata dauki wayarta bata kuma yi amfani da ita ba. Kai tsaye tasan inda ta aje wayar tata,can ta nufa,ta daga wajen da zummar dauka,saidai kuma wayar tace daukeni inda kika ajiyeni. Mamaki kadan ya kamata,amma sai ta share tana tunanin qila ta canza mata waje ne ta kuma manta inda ta ajjiyeta,don haka ta fara bincikawa guraren dake daura da nan ko a nan ta ajiye din. Guri hudu duka bataga wayar ba ba alamarta,ganin zata gajiyar da kanta saita ajiye wannan ta koma laluben wayarta ta asali data barta a handbag din da suka dawo da ita jiya dake ajiye saman mudubin nata tunda ta ajiye jakar. Kaf ta lalube jakar sannan ta zazzageta,saidai babu wayarta babu alamarta a ciki. Mamaki yadan sanyata ja da baya,nan ma zuciyarta ta soma ayyana mata wataqila itama ya canza mata waje ne,don haka sai ta fara jaye jayen lockers tana bincike dakin. Wasa wasa har closet dinta ta duba babu wasu alama na akwai wayoyin. A hankali ta dawo tana zamewa ta zauna daga qasan carpet din da aka qawata gaban sofa bed din tana maida numfashi. "Ya akayi haka?,me yake faruwa?,dukka wayoyinta babu ko guda daya?" Ji tayi sam ta kasa aminta ko ta samu nutsuwa,sai kawai ta fadada bincikenta har zuwa kitchen dining area waiko ta barsu a can,saidai babu komai kamar dai yadda ta gani a dakin. A parlor din ta zame ta zauna,tana jin wani shakka da kokwanto na shigarta. Kota wacce fuska bataga waje ko wani sarari da wani zai samu daman shigowa gida irin wannan ba.....me wasu irin madaukakan katangu da kuma gwabza gwabzan security irin wadannan ballantana tayi tunanin wani ya hauro ya shigo musu...... Da sauri ta zauna sosai tana qanqance idanunta sanda wani tunani ya fado mata. "Idan har haka ne shine kenan ya dauke wayoyin?,yaushe?,garin yaya?,a ina kuma ya samu damar aiwatar da hakan?" Tambayoyin dake danqare a kanta kenan data dinga juyasu. Idanunta ta maida tana duban sashen da stairs dinsa suke,zuciyarta na bugawa kadan kadan,tana jin kamar ta tashi ta haura ta sameshi a can,taji meye hujjarsa na daukar mata wayoyi,bayan hakan ba huruminta bane?. Bata fahimci cewa gidan ba kowa ba......ita daya ke rayuwa a cikinsa duk girmansa ba sai da sha daya na dare ta gota a idanunta. Sai a sannan taji wani irin tsoro ya soma mamayarta sanda zuciyarta ke bata hasashen ita daya ce qwallin qwal a gidan. Wani irin karyewa zuciyarta tayi,tsoro yana sake shigarta sanda take qudundune cikin duvet dinta. Bata taba kwana ita daya ba koda cikin dakinsu ballantana a gidansu gaba daya ba.....wanne irin azzalumi ne shi da zaya fita yabarta a gidan da yafi qarfin zaman mutum hudu ma yace ta kwana ta rayu ita kadai?.....ba wayar da zata kira wani ballanta taji sassauci......koda ta duba wayar girke dake parlor din da zummar ta sadata da security din da suke waje taji ko zata samu aron waya daga hannunsu cikin rashin sa'a ta samu an yanke sadarwarta,ba zata iya yin magana da kowa ba banda dakunan dake cikin gidan. Kanta ta cusa cikin pillow din tana jin yadda bugun zuciyarta ya qara tsananta sanda karen dake wani sashe daban na gidan ya tsananta haushinsa. Bata taba tunanin akwai halittar tsoro a qirjinta har haka ba sai yau.....ashe dukka jarumtar da take zaton tana da ita ba jarumta bace.....ko tace ta tsaya ne kadai ta bangaren saita maza daukan darasin rayuwa da sanin ciwon rasa wani abu da xukata suke tsananin so da qauna. Batasan ya akayi ba ta samu da qyar wani takurarren bacci yayi awon gaba da ita. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 26 26 Kwana daya kwana biyu haka awanni suka dinga juyawa da ita cikin gidan,cikin wani irin matsanancin shuru kewa da kuma kadaici. A hankali ta dinga jin wani matsanancin takura,ta yaya zata zauna irin haka ba waya ba gilmawar kowanne dan adam?,tv kuwa sam taqi ta kalleta bare ta gwada kunnata. Da farko ta dauka zata iya jurewa,amma sannu a hankali saita fahimci ashe mutum rahama ne a kusa da kai,koda kuwa ba wata mu'amala da zata hadaka dashi. Tayi dukka juriyar da zata iyayi sai taji haqurinta ya soma gazawa. Wani danqararren bacin rai ne yake cinta game dashi wanda qilan inda yabar mata wayar ma a wannan karon batajin akwai abinda zai mata shamaki daga kiransa ta zazzage masa abinda yake cikinta. Ta yaya ita din da ta kwashi shekara aqalla biyar zuwa shida,ba wata ranar banza da zata fito ta fadi bata fita ba.....yanzu kawai rana tsaka ta wayi gari da mummunan kulle irin wannan?. Ko a baya batata ji a ranta akwai wani lokaci da zayazo a sanyawa qafafunta irin wannan sasarin ba,ba lissafin aure kwata kwata cikin kanta shi ya sanya bata kawo yiwuwar afkuwar hakan a kanta ba koda sau daya. Ranar data cika kwana na hudu,tun qarfe goma na safe taji takai maqurar da ba zata iya jurewa ba. Sha daya da rabi daidai ta kammala shirinta cikin atamfa. Ta taka a hankali zuwa inda take da tabbacin ta ajiye kudinta data shigo dasu cikin gidan,ta bude locker din ta zura hannunta don debosu,don ta gama tsarawa kanta zata taka ta fita ta samu napep duk kuwa da cewa tasan area din kwata kwata yana da wahala kaga abun hawa na haya.....to amma ta gwammace tayi tattaki zuwa babban titinsu tayita jira cikin rana har ta samu abun hawan da zai kaita gida. Zuciyarta da tunaninta gaba daya yana kan taje ta binciki lafiyarsu huda.....kowanne dare dasu take kwana dasu kuma take tashi,suna cikin aminci ko kuwa aah?......da qyar ta iya jure wadannan kwanakin suka shude ba tare da tasan komai game dasu ba. Ta dauka yadda ta dokanta ta fita ne idanunta suke mata gizo sanda ta hangi babu ko burbushin kudi a wajen,amma data bude sosai sai taga gaskiya take gani.......ba komai a ciki kamar yadda ta gani da farko. Mamakinta ya ninku akan mamakinta na kwanaki hudun da suka shude........ta sulale tana sake zama a saman stool din dake kusa da ita. "Wai wa yake da alhakin aikata haka?" Ta sake tambayar kanta tana jin tantama akan tabbacin zargin farko da zuciyarta ta bata. Duk wani karsashi na fitar saita rasashi......yaushe ya samu damar shigar mata daki?,dame dame ya bincika mata?,me zaiyi da wayarta?,dame dame zai bibiya cikin wayar?. Wadannan tunanin su suka sakata a gaba,ta kasa tuna komai ko abinda ya dace tayi,har sai da agogo ya alamta mata sha biyu dai dai na rana. Cikin qarfafawa kai gwiwa ta koma toilet ta sake wanke fuskarta,ta dawo ta wuce closet ta dauki handbag da shoe da zai dace da shigarta sannan ta soma barin dakin tana jefa atm dinta a jaka da zummar idan ta fita ta samu wani guri ta cire kudi daga account dinta. Wannan ce ranar farko kuma karan farko data fito daga cikin gidan a yanayi irin wannan. Faffadar haraba yalwatacciya me wani irin tsari me jan hankali. Kusan gurare da yawa an qawatashi da koriyar ciyawa a maimakon tiles marbles ko concrete da akafi yawan amfani dashi. Sai wasu irin fararen stone da aka zuba a wasu daga cikin hanyoyin da zaka taka ka wuce zuwa haraba ta biyu. Idanunta suna iya gane nata wasu qofofi da babu qofa a jikinsu face wani irin design da aka musu wanda batasan ainihin inda zasu sadaka dashi ba. Sosai harabar ta qawatar da wani irin yanayi da zakayi tsammanin ba cikin qasata nigeria kake ba.....saidai wutar dake can qasan zuciyarta ta danne burgewar da wajen yayi mata,taci gaba da tafiya cikin confidence zuwa qofar gate din da take da tabbacin zata sadata da waje. Tsaye kawai tayi don bata fahimci ta inda zata ratsa ta wuce ba,sam qofar ba irin qofofin data saba gani bane. Gajiya tayi da tsaiwar ta kuma gaji da kallonta da tunanin ta inda zata fita din,don haka ta saka hannu ta soma knocking da tunanin zasu iya jinta. Tun tana knocking din a hankali har ta fahimci ba kowa ke jinta ba,ta qara dada qarfinsa saidai a banza don ba wani motsi da taji da zai bara hope din wani na kusa zaiji ya kuma budeta,wannan ya qara hasala mata zuciya,ko a kurkuku take bangaren muggan laifin kisa ko fashi da makami iya horon da za'ayi mata kenan,don haka ta sake maida kai wajen buga qofar da kyau ba tare da tunanin cewa babu me jinta ba. A hankali wani sashe kadan daga saman qofar ya zuge kanshi da kanshi. Fuskar jordan ta bayyana wannan karon sanye cikin uniform din daya zama kayan sawa ga duk wani ne aikin tsaro dake cikin gidan. "Good afternoon maa". Ya furta da wannan matsananciyar girmamawar da yake mata wadda ba abinda take sawa zuciyarta sai wani irin qarin takaicinsa. Fuskar jordan fuskace da ba zata manta da ita ba ko kadan "Open the door" Ta fada adan fusace tana kallonsa,tana jin kamar ta miqa hannu ta zabga masa mari. Cikin rusunawa da girmamawa kaman yadda ya saba ya fara mata magana da hausa "Am sorry maa......boss bai bada umarni ba,idan ba damuwa ko zaki kirashi kuyi magana tukunna?". Idanunta ta janye kawai daga kan jordan din bacin ranta yana ninkuwa,abinda yayi mata a wancan lokacin shi ya maimaita mata kenan?,waishin me yake daukan kansa ne shi?,don yana da kudi?,yana da dukiya shi yasa yake tunanin zaiyi duk abinda yaga dama?,zai taka wanda takeso a duk sanda yaso?,zai wulaqanta mutane sannan kuma ya kwana lafiya?. Ta ina zata nemeshi bayan babu ko waya guda daya a tare da ita?,ta ina zasuyi magana bayan ya yanke sadarwar gidan gaba daya?,koda ma komai yana nan a muhallinsa ta rantse ba zata kirashi ba. "Kawu ne ya jawo miki" Amsar data dawo cikin kanta kenan. Idan ma kira ne shine mutumin daya kamata ace ta kira,har yanzu tana ji a jikinta kan ta inda ake hawa ta nan ake sauka,kawun shine ya bada ita ya kuma saida mutuncinta.......don ta nata bangaren ba'a kan muhammad fu'ad bane farau shallakewa maza masu kudi da kuma hadari......don haka don shi kadai bazai zame mata matsala ba inda anbi karatun yadda ta saba. Har taji kamar ta sare,sai taga idan ta bari hakan ta kasance yasha da ita,don haka ta matsa bakin gate din "Can you barrow me your phone?". Ta tambayeshi tana kallonsa. Jinin jikinsa yasha,yadan kalleta yana kokwanto. Yaya zata rasa waya tana a gida irin wannan?. "Afwan madam.....amma me zakiyi da waya?" Idanunta da suke mata zafi ta lumshe "Zan kira uncle dina ne.....i lost my phone". Dan jim yayi kadan,sai kuma ya amsa mata yana sanya hannu a aljihu ya fiddo wayar ya miqa mata bayan ya sake bude glass din ya qara girma. Yadda yake bata wayar kamar tana a kurkuku ya sake matsa zuciyarta ya qara yawan adadin bacin ran da take ciki. Wani sashe daban na gidan ta koma ta zauna saman wasu rukunin kujeru da aka qawata cikin wata rumfar bamboo dake bada iska me kyau da sanyi. Da qyar ta iya hada lambobin kawun don ba haddacewa ta taba zama tayi ba.....saidai kawai kira na yau da gobe daya bata daman kallonsu daya bayan daya suka kuma zauna a kanta. Bugu biyu kawun ya daga da cikakkiyar sallamar data kusa sanyata jan tsaki "Kamar gaske" Ta fadi a ranta tana amsa sallamar tasa a daqile. "Wa nake ji kamar sabreena?" Ya fadi da annashuwa cikin muryarsa,zuciyars na bashi tabbacin lallai zama ya soma miqawa,wataqila wani alkhairinma ta bugo tayi masa "Nice" Ta amsashi a hankali "Kai madalla Allah.....ma sha Allah,amma fa naji dadin kiranki kin kyauta diyar albarka,dama inata zube kunne naji kiran naki......" "Eh gashi na kira......na kiraka ne kuma na gaya maka.......wannan mutumin daka saida masa dukka 'yan cina da mutuncina ya kamata ka kirashi ka bashi labarin haihuwata akayi bawai a baiwa aka ribatoni ba.......ka fada masa abinda ke tsakaninka dashi daban da abinda ke tsakanina dashi,bazan iya daukan dukka wannan izzar tasa da izgilancinsa ba......ina da 'yance kafin zuwansa zan kuma ci gaba da kasancewa me 'yanci a rayuwata.....don har yanzu babu d'a namijin da zai dinga ruling dina yadda yaga dama ba tare da naso haka ta kasance ba". "Kai jama'a.....waike wacce irin yarinya ce ne me butulci?,Allah yayi miki wannan babban gamo da katar din da miliyoyin mata ke fatan samu amma ki zauna kina shashanci?,yo Allah na tuba idan ranka ya dade baiyi mulki da izza ba meye zaiyi?,kudi ne dashi fa?,arziqi garai irin arziqin da gwamnati ma wani lokaci biyayya takeyi maka.......ina gani malam rufa'i?,to wallahi bada ni ba.....hasalima ni bamu taba waya dashi ba,dan uwansa kuwa farouqu bazan dauki sirrin gidan ma'aurata nakai masa ba Allah bazai la'anceni ba,in zaki nutsu kiyi biyayya ki tara abinda kika tara karki mana buqulu to,amma wannan jan kunnen bada ni ba.....wane mutum inji mutuwa,Allah baki da hankali sabreena" Har ya qare maganganun idanunta suna kulle saboda yadda yake mata magan da qarfi da hayaniya,uwa uba ita bataga dalilin dogon jawabinsa ba. "Kawu" Ta kirashi a nutse. "Yaushe su huda suka zama cikin kayan gado da har za'ayi rabonsu zuwa ga wata mace da basu hada alaqar komai dasu ba?". "Wata mace?,Allah na yarda dai da gaske akwai sauran qarancin nunar hankali a tare dake.......kina magana akan hajiya mariyah surukarki?,mutuniyar kirki me yawan alkhairi da son zumunci?,yo wannan kika fadi mummunar kalma a kanta aisai Allah ya tsine miki albarka.......ni baza'a zageta dani ba,sai anjima sabreena" Kafin ta ankara ya yanke wayar,abinda ya sanyata a razani ta maida dubanta kan fuskar wayar tana kallonta cikin mamaki. A wannan karon duk yadda taso tare kukan sai da hawaye ya sauko mata bayan ta maida wayar wa Jordan. Sai kawai ta soma tattaki da sassarfa tana komawa ciki cikin yankewar kowanne tsammani. A falo na biyu ta zube don ta gaza isa bedroom din. Wasu irin hawaye masu zafi suka fara gangaro mata. Me yasa rayuwa zata juye mata da zazzafan yanayi irin wannan dare daya?,yanayin da ko s mafarki bata taba tunanin zaya risketa ba?. Ya cika mugu na gaske,ya rufe mata kowacce qofa ko hanya da zata samu sassauci......me ya rage ita kuwa tsakaninta dashi banda itama tayi duk yadda zatayi tayi nesa dashi?,me ya rage banda ta aiwatar da nufin maamah a kansa don ya gwada shiga halin mulkin mallakawa d'an adam yaji idan hakan da dadi?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 27 27 ★★Madaidaiciyar haraba ce wadda yanayinta yayi kama da gine ginen turawa ainun,irin gine ginen qasashen qetare,saidai kuma ba harabar kadai ba.....gidan dama sauran gidajen dake wajen dama unguwar gaba daya ba zaka dauka kana cikin abujar nigeria bane ba. Tamkar shi daya ne cikin gidan saboda rashin hayaniyar jama'a da kuma motsi,saidai a yawancin lokuta yakan zabi yanayi irin wannan don bawa zuciyarsa hutu da kwanyarsa. Bayan doguwar gwagwarmayar tabbatuwar buduwar kamfaninsa ap lagos kwanaki uku da suka wuce,sai ya zabi tsaiwa a abujan don ya sanya ido game da gudanarwar kamfanin koda na sati guda ne kafin ya koma bakin nasa ayyukan da suma a yanzu suke buqatar hankalinsa. Farin boxer ne a jikinsa da wata cotton shirt me gajeran hannu wanda ta bayyana ginuwar muscles na jikinsa,zubi da qirar qarfin da yake da ita. Tataccen natural ruwan blood orange ne a gabansa da ba'a sirka masa shi da sinadarin komai ba kaman yadda yake dabi'arsa ce a haka. Yafison komai natural da za'a sarrafashi da hannu,duk irin dukiyar da yake da ita amma yana sarrafa kanshi wajen sanin abinda zaici,wannan ya sanya yake da wata irin cikakkiyar lafiya. Wayoyin dake gabansa ya sake maida idanunsa akai,ya sake miqa hannu ya dauki daya daga ciki yana jujjuyata. Ba komai a ciki,baiga kuma komai ba. Dayar number maamah dince kawai akai,ba contact ko daya,kaman yadda ba massages a ciki,duk wani social app dake kai baya aiki ba'a budeshi ba,kamar yadda daya wayar take itama. Ba Facebook ba insta ba tiktok,ko watsapp babu duk da yana zaton an taba amfani dashi a kanta an rufe ne. Yanason ya zurfafa binciken sama da haka,amma sai wani sashe na zuciyarsa ya tunasar dashi haramcin zurfafa bincike akan dan adam......amma su ya halatta ya bincikesu har haka?,bayason maamah taci gaba da jefa qafafunta cikin halaka.....dole uwa uwa ce.....mutum daya ce duk duniya ke amsa wannan sunan......kamar yadda yayi imani yarinyar sai ya karanta mata menene rayuwa kafin ya sakar mata qofofin 'yanci ta yadda ba zata sake zama guba ga kowa ba. Maida wayar yayi ya ajiye,yana jin kamar zuwa yanzu ya kamata ya wuce gida hakanan ko don hankalin anni ya kwanta. Ya fahimci kamar tana zargin bai taho da yarinyar ba,amma da yake gwanar kawaici ce ita bata ce masa komai a kai ba. Ya sani ma inda farouq yana nan zuwa yanzu da tuni ya tona mishi asiri,sai Allah yasa suka shiga wata seminar kwata kwata bashi da lokacin kanshi. Wayarsa ya dauko ya lalubi saddiq "Kana ina ne?" Kanshi yadan shafa cikin jin shakka da nauyinsa "Katamfe extension" Ya amsa masa yana addu'an kada ya masa fada. Bayajin doguwar magana a kansa sosai,hasalima wata kasala ke damunsa,ruwan dumi yakeso yasha ya sake kwanciya,don haka kawai ya bashi saqon a dunqule "Kayi magana da team su shirya flight,gobe zamu wuce gida" "Okay in sha Allah" Ya amsashi yana jin dadin yadda bai matsa masa ba bare ya sanyashi baro soyayyar da yake raino a lokacin. Wayar ya mayar aljihun boxer din nasa,sannan ya dauke sauran kayayyakinsa da suke wajen ya fara saukowa daga farfajiyar dake a matsakaicin tsaho,shi ba upstairs ba shi ba qasa ba,amma lallai saiya biyo ta cikin dab da qofar parlor sannan ya shiga parlor din ya wuce duk inda zaije. Sam hankalinsa ba'a wajen yake ba sanda yake saukowar,cikin wani irin mamaki qofar parlor din ta bude sannan ta bayyana gaba dayanta cikin ba zata. Saura kadan ya hada jiki da ita,don ta shigo ne da wani irin zafin nama,banda shima me zafin namar ne yaja baya da sauri da ba abinda zai hana jikkunansu haduwa guri guda. Cikin second biyu ya maido hankalinsa jikinsa,suka fara yiwa juna kallon kallo. Fareeda,d'iya ga ambassador din nigeria a qasar china. Matashiyar da duniya ke gara mata fiye da yadda takeso,ta samu gata.....ta samu ilimi.....ta mallaki kyau......tana da tsananin wayewar da bata barinta fayyace daidai a addininta da ba daidai ba.......wayewar dake haska mata komai ya yiwa ranta dadi.....komai ranta keso daidai ne,wayewar da gatan da sukayi mata jagora tare da nuna mata kome takeso lallai zata sameshi ta kowacce hanya. Doguwa ce fara sannan kuma siririya,wadda ke tattalin jikinta da amfani da mayuka da kuma supplement masu tsananin aji da tsada ba tare data bari zallar hutun da take ciki ya zama jagoran gyaruwar komai nata ba. Zai wahala ka kalleta ka kirata da mummuna kai tsaye......saidai bata cikin sahun kyawawan da kallo daya zai sanya ka gamsu kyakkyawa ce,tana mataki na kyau a middle class....duk da tana kai kanta high class a koda yaushe tana ganin ta cancanta da aje kanta a can. Ta jima tana jin sunan muhammad fu'ad jadda yana gilmawa kunnuwanta.....wani lokaci daga bakin manyan friends dinta yaran gata irinta,wani lokaci kuma daga bakin mahaifinta. Saidai ko sau daya hakan bai taba jan hankalinta ba,saboda tana da wata izza akan namiji da saidai ya nemeta,don ta hada komai da take ganin babu kalar d'a namijin da bata zarce masa ba......in fact tana tunanin ma ita har yanzu cikin wannan duniyar da muke ciki babu kalar mijinta. Sau tari idan sunan ya gilma mata kawai tana surantashi kamar sauran alhazawan masu kudin dake hauka a kanta,masu shekaru,kai duka furfura ko kuma furfurar ta fara ketowa,masu qiba da ajiyayyen tumbi,masu matan aure uku hudu da tarin 'ya'ya. Bisa rakiyar tilas data yiwa mahaifinta nigeria don zuwa bikin bude company din JADDA SPARKLE WORLD daga nan su qarasa garinsu gaisuwar mutuwar qanin mahaifinsa da ya kusa cimma wata uku da rasuwar amma bai samu zuwa ba. Kafaffe kuma tsayayyen yaya ga kakansu qwaya daya daga rage shi ya zuba bala'i akan fareeda,sam yarinyar ba wanda ta sani a cikin su kaf,saboda rabonta da garin tun batafi shekara biyar ba a duniya,basa qaunar zuwa kwata kwata,wannan ya sanya mahaifinta ambassador khaleed mustapha ya tilasta mata saboda rufe bakin mutane. A karon farko da sanarwar bayyanar me kamfanin kan dandamalin jawabi ta ratsa microphone din,ta daga kanta daga kan wayarta da take qoqarin posting hotunanta a shafukanta,ta kuma saukesu akan muhammad fu'ad dake tsaye gaban abun magana yana daidaitashi yadda zai dace da bakinsa. Wata lafiyayyar suit ce a jikinsa data tsone idon duk mutumin dake zaune a wajen. Suit din da musamman aka sarrafata tun daga qasar Italy saboda rana irin wannan. Ta sake fidda tsahonsa da murjewar jikinsa da wani irin mahaukacin kwarjini da ya zame masa garkuwa wajen karya maqiya da abokan gabarsa. Idanunsan nan masu wani irin kyau da bata taba ganin irinsu ba suna yawo saman fuskokin tarin al'ummar da sukazo wajen saboda shi yayi cikakakkiyar sallamar da duk wanda ya sanshi yasan wata abace da baya tsallakewa yinta ako ina koda wanne irin mutane ne a gabansa,ba ruwansa da banbancin addini qabila ko kuma yare.....ako yaushe yana yin abinda xai ci gaba da tuna masa....zai kuma ci gaba da bayyanawa ko waye suke tare cewa SHI MUSULMI NE. Sanda ya fara jawabin taron da wani irin tataccen turanci da lanqwashewar harshen da zaka rantse cikin fadar queen Elizabeth aka haifeshi sai dataji kowacce gaba ta jikinta ta saki. Wani irin abu da bata taba ji akan kowa ba ya soma bin sassan gudanar jini na jikinta yana aika saqo wa zuciyarta,wanda kafin ya kammala bayanansa ya sauka gaba daya ya wuce da nutsuwarta dama zuciyarta gaba daya. Ta fahimci akwai ire irenta da yawa a wajen bayan tashin taron,saidai ba alamun samun fuska ko dama daga wajen kowacce diya mace,wannan dalilin ya sanya tabi ta hanyar mahaifinta. Ta samu damar gaisawa dashi,saidai abu na farko daya sanyaya mata jiki hannu data bashi da nufin suyi hand shaking kamar yadda yake gaisawa da kowa,sai ya jefa mata wani irin kallo ya maida hankalinsa ga wani abu na daban. Bata haqura ba sai data sanya mahaifinta ya nema ganawa dashi a masaukinsa dake banana island kafin yabar lagos kenan,a nan ta fito kanta tsaye ta gaya masa abinda ke dauke dashi,amma sai ya saki wani murmushi daya qarasa qona mata ruwan jiki gaba daya,ya kuma bata saqon daya kusa tashin kanta a aiki. "Am so sorry kinji....ni bana soyayya.....infact ba time na ire iren wadannan shirmen,ina fata kema zaki maida hankalinki akan karatunki okay?" Gaba daya shirme ya dauki abun,yadda ya tsaya ya mata maganar ma ta tabbatar albarkacin mahaifinta taci. Still bata jin zata iya haqura dashi,ta samu daman ganinsa a karo na biyu ba tare da yasan ita bace. A nan ta gane ainihin wayeshi,ya fiddo mata true color dinsa,abinda ya birkitata kenan,batayi qasa a gwiwa ba ta bashi tabbacin bata taba neman abu ta rasa ba.....a kansa kuma ba zata fara ba,zatayi duk yadda zatayi don ganin ta mallaki soyayyarsa ta kuma mallakeshi.....ta kuma ci masa alwashin duk inda ya shiga tana biye dashi har sai randa ta samu abinda takeso. Ko a yanzun zare rafkeken sunglasses din idanunta tayi tana qoqarin sakar masa murmushi,yayin da ransa ya motsu da zummar baci amma kuma mamaki ya mamaye wannan gurbin. "May i ask who's let you in?" Yayi maganar yana qoqarin danne fushinsa. Murmushi ta kuma saki tana rolling idanunta cikin salon jan hankali "As your guest,i think you should welcome me first" Ta furta tana narke murya. Baya ya sake ja kadan ganin tana qara takowa inda yake "What brings you here?" Wannan karon ya fada adan tsaurare,alamun bacin ransa suna fitowa fili. Kallonsa tayi a kaikaice tana sake yadda da maganganun da aka gaya mata a kansa. He's not a womanizer,he's not into playing games with women......ta yaya kike tunanin zakiyi winning kansa?" . Ta tuna da maganar da daya daga cikin qawayenta suka mata. A lokacin ta dauki zancan nata ne a matsayin kishi,saboda samun cikakakkiyar dama da tayi da take ganin zata kawoshi cikin rayuwarta,damar da mata da yawa suke nema basu samu ba. "Am here for you fu'ad.....please ka bani gurin zama tukunna mu tattauna a nutse" *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 28 28 "Get out of my house" Ya fadi ba alamun fara'a ko walwala a tattare dashi. Wannan fuskar me cike da miskilanci,wadda zai wahala kaga wani abu me kama da murmushi a kanta ta sake dinkewa tsaf "Please mana" Ta fada da wata irin shagwaba tana hade hannayenta waje daya "Zaki fita ko sai na kira masu fiddamin dake?" Ya kuma fada yana ware mata idanunsa da suke da wani irin kyau me jan hankali wanda suka sake fusgar hankalinta. Bai ankara ba bai kuma taba kawo haka zata kasance ba ya tsinceta ta fada cikin faffadan qirjinsa tana neman kai masa kyakkyawar runguma. Baiyi wata wata ba bai kuma sake bata koda minti biyar a jikinsa ya yakiceta ya watsar gefe. Wani irin tafasa zuciyarsa keyi,wanna shine karo na farko da wata mace ta rungumeshi irin haka. "Tashi ki fita thn ranki bai qarasa baci ba,stupid!" Ya fadi a tsawace yana nuna mata qofa. Miqewa tayi tana kade jikinta,duk da ba wani baci tayi ko datti ba saboda gurin fes yake da wata irin tsafta da take ta'ammali da ita a komai nasa,cikin borin kunya tace "Yakice ni daga jikinka baya nufin fidda soyayyarka daga zuciyata......zan tafi,amma kuma zan dawo,zan kuma ci gaba da kasancewa dakai,zan zama cikin kowanne motsi naka har sai na cimma nasara na samu abinda nakeso". Daga wannan ta dauki jakarta tana nufar qofa da dan sauri,qasan zuciyarta da tsoron yadda mode dinsa ya koma,amma abinda takeji a kansa ya danne komai. Iska me zafi ya furzar yana shafa sumarsa da tafin hannunsa. Kwata kwata yaqi jinin mace maras jan aji........yana matuqar son mace me aji.....mace me dan wani tasiri kadan na girman kai,wanda girman kai a wajen mace yana alamta alamu na kamun kai,girman kai yana cikin siffar da akeson mace dashi.....amma a mu'amalarta da maza kamar haka. Komawa yayi saman kujera ya zauna yana fidda numfashi me huci. Yana daya daga cikin abinda yasa ya rasa interest akan mata,yana daya daga cikin abinda ya sanya har yanzu ya kasa gano macen da zata sace zuciyarsa kwata kwata.......saboda yanzun mata yana hangen sun rasa dabi'un nan guda biyu zuwa uku masu tsananin tsada fiye da diamond...... Masu tsananin zame musu ado fiye da adon gold a jikinsu,wato KUNYA da kuma KAMUN KAI. Wayarsa ya dauka ya kira abdus_samad yana qoqarin danne fushinsa,bugu daya tak ya daga "Who gave her permission to enter?" Tambayar da yayi kenan a taqaice. "Am sir......" Ya fada adan daburce don jikinsa yana bashi laifi yayi "Did someone invite her in?" Tambayar ta qarasa daburtashi gaba daya,ya kuma fahimci laifi yayi. "Am sorry sir......am sorry,naga diyan ambassador....." "Keep quite......are you out of your sense?,don diyar ambassador ce?,meye alaqana da ita?,dama akwai wannan tsarin na ku barmin mutane suna shigomin guri anyhow?,meye amfaninku idan haka zata ci gaba da kasancewa?" Ya kasa magana kawai sai haquri da yake faman jera bashi,don tunda yake dashi irin fada irin haka bai taba hadasu dashi ba. Bai jira cewarsa ba ya yanke wayar yana ajiye wani tsaki. Ji yayi sam zaman parlor din ya isheshi,bama parlor din bama,abujan gaba daya,ya miqe yana wucewa bedroom dinsa,cikin jikinsa gaba daya yana jin kamar ya yanke inda nata jikin ya tabashi. Bacin rai sosai yakeji a qirjinsa,duk wani nau'i na sabo ya tsaneshi,sai yau gashi ta sakashi abinda yake matuqar gudu da kaucewa. Yasha shiga harkoki da abubuwan dake cakude da mata,amma yanayin kamewarsa da kuma miskilancinsa yasa suke tsoronsa matuqa,ba wadda take zuwa masa da zancan banza,tun daga secondary school university da tafiyansa service,duka Allah ya tsareshi ya kuma tsare imaninsa,duk da irin farkamakin da yake samu. Yana gaban wardrobe yana sauya kayan jikinsa yaji ana masa knocking,muryarsa can qasa da sauran tasirin bacin rai a ciki ya tambaya "Waye?" "Saddiq ne hamma". "Come in" Ya bashi dama lokacin da yake sanya rigar jikinsa. Yanayin yadda yaji sadiq din ya shigo ya tilasta juyawa yana duban fuskarsa. Sai yabi hannunsa da kallo wanda yake dauke da system "What's wrong with you?" Ya tambayeshi yana tsareshi da idanu. Kasa amsa masa yayi,sai daya samu waje ya zauna daga saman carpet ya ajjiye system din sannan yace "We got the announcement........ana zargin an samu muggan qwayoyi cikin jewelry company dinmu". Ya qarasa fada yana buda masa saqonnin da suka samu daga dukkan kafofin dake da alaqa dasu daya nabin daya. Hannuwansa kawai ya zube cikin aljihunsa yana kallon system din. Yanajin wani yanayi yana zagayashi,hankalinsa nason tashi amma yana gayawa kansa da kansa "All is well" A irin wannan lokutan na tsanani,lokutan da jarabawa irin wannan ke tunkararsa rauni yakan rugo da gudu ya mamayeshi.....a irin wannan lokacin yakanji yana da buqatar wata halittar a gefe da zata same masa qwarin gwiwa......banda qannensa banda farouq da yawan daukan mas'alolinsa yake ganin suna masa yawa,ya kamata ya rage masa daukan matsalolinsa haka.....tun daga quruciya kunnuwan farouq zuciyarsa dama gangar jikinsa suke fama da matsalolinsa.....zuwa yanzu ya kamata ace ya huta.....anni,wata irin rumfa ce sha shirgi ita da abban gaba daya,ya kamata kunnuwansu su samu sassaucin jin damuwoyinsu a yanzu haka da girma yazowa kowannensu.......akwai personal mutum da yake buqata daga gefe da zai zauna a wannan matsayin. "Hamma wannan saqonnin barazanar basa da alaqa da faruwar wannan abun kuwa?". Kai yake jinjinawa sanda yake takawa a hankali yana matsawa daga wajen "Definitely......but I'll make it clear im not Intimidated" Ya fada da wani irin qwarin gwiwa yana dora top saman rigar t.shirt din jikinsa. "Let's go.....ka kira William kace ya samemu a can....." "Amma hamma.....flight isn't ready" "We'll take the road" Ya furta yana riga saddiq yin gaba. Kafin sukai ga isa lagos ya gama shirya dukkan abinda ya kamata ace ya tsara din. Suna dab da shiga garin har a sannan idanunshi biyu,ko daya baiji wani buqatar bacci ko kuma ya huta ba. Yaja qaramin tsaki sanda suka dauki hanyar kamfanonin. Ya fahimci ita kalmar SO ko a meye ta shiga wahala ce kawai da walagigi da ruhi,wannan ya sanya banda soyayyar family dinsa bai taba saka soyayyar komai cikin ranshi ba,sai yanzu gashi kwatsam......kamfanin ya shiga ransa har baisan adadi ba......gashi kuma ya zama abu na farko da son nasa keson zame masa wahala,da wannan ya qara ji a zuciyarsa lallai tabbas ya kamata ya nisanci soyayya iyakar iyawarsa. Duk da sun nuna matsayinsa yafi ya taso da kansa amma ya kauda wannan. Ya karbi duk wani bincike nasu ya dora da nashi. Da gaske an samu wani dan qaramin store cikin kamfaninsa cike da qwayoyin da inda wani me qaramin matsayinne ba shakka sai ya tafi dauri gidan gyaran hali,amma da yake a nigeria muke.....kuma kura ma tasan gidan me babban sanda sai ya zamana dakatar da kamfanin kawai akayi sai bincike ya kammala. Bayajin zai iya bari maqiyansa su kalli faduwarsa da wurwuri haka,wannan ya qara masa qaimin shiga binciken da kansa gadan gadan. Ya fuskanci tarin abubuwa masu yawa cikin case din,wannna ya qara masa qaimi,bai kuma yarda yayi handling case din ma kowa ba. Duka da bacci da cin abincinsa qalilan ne. Amintattun experts investigators din daya aminta dasu kawai suke aiki ka'in da na'in,ba dare ba rana. Bai gayawa kowa abinda ake ciki ba banda anni da yace ta tayashi da addu'a,akwai matsala amma qarama ce ba wata babba ba,haka ya gayawa abba da farouq. Saidai sam hankalin farouq ya gaza kwanciya,don yana dawowa daga seminar dinsa ya biyo bayasa a washegari. Yadda ya ganshi ya tabbatar abun ba qarami bane,don ya nuna har a jikinsa don kuwa ya dan rame kadan saboda rashin bawa abinci muhimmanci. Ya sake sallamawa da miqa wuya kan muhamnadun yaci sunan muhammad din,namijin gaske ne da gaske......daga yadda ya tunkari komai yake gabatar dashi da dukka qarfin gwiwarsa da jarumtarsa kadai ya qara tabbatarwa NAMIJIN DUNIYA NE. Yanata qoqarin dodging komai farouq ya dubeshi. "4weeks without me dude.......have you noticed your appearance?.....check your reflection" Ya fada yana kama hannunsa zuwa gaban concealed mirror din dake wajen. Ya kalli fuskar tasa kaman yadda farouq ya buqata,sai ya saki murmushi ya miqa hannu yana shafa fuskarsa. "Chill out mana dude,nayi settling komai,It's come to an end......My evidence supports my claim....and it speaks for itself,all the fact are on my side,na gama komai gobe zasu saki kamfanin.....abu daya ya rage na gano shine,who's pulling the string" Hannunsa farouq ya riqo yana girmama qarfin jarumtarsa,yana jin inama ya samu irin wannan jarumtar tasa "We'll leave no stone unturned,we'll find him together" Rungume kafadar farouq yayi,yana sake jin qaunarsa cikin ransa. A gaba ya sakashi ranar,yasa ya ajiye komai tunda bincike ya kammala. Da kansa ya zauna ya masa gyaran fuska da sauran wasu abubuwa,yana masa suna hira yana bashi labarin nasa progress din da aka samu bayan seminar din. Duk duniya da farouq kadai yake irin wannan sakewar. Ranar duka tare suka qarar da ita,sai dare sannan kowa ya wuce makwancinsa,da zummar gobe da kamfani yaci gaba da aiki jibi tabbas dole su wuce gida,wanda sam bai fahimci meye ma'anar matsawar da farouq din yayi bama. Ya dauki wayar da zummar kashewa ya tarar da tarin miscalls da kuma saqonni,guda daya ya duba ya fahimci wacece. Fareeda ce....saqo bayan saqo kamar bata da wani sauran aikinyi sai tura masa da saqon. "How did she get ahold of my number?" Ya tambayi kansa da kansa. Tunawa da yayi da mahaifinta ya sauqaqe masa wahala,yasan samun numbersa zai zame mata wani abu kenan me sauqi. Tsaki yaja ba tare da yabi takai ba,ya kashe wayar ya kwanta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 29 29 ★Cikin kwanakin har ruwan jikinta takeji kaman ya qare saboda tsabar wani irin kadaici da dumbin tunani da yake cike a kanta. Sati hudu cur tana a cikin gidan......ba motsin kowa ba gilmawar kowa,ba hira da kowa,ba waya,daga ita sai tv sai karen gidan dake haushi nesa da muhallinta. Ada ko parlor din bata fitowa tana qunshe a daki,daga bisani ta fahimci depression na loneliness zai iya kamata,don haka da kadan da kadan ta fara fitowa tana zama. Saidai daga zaman sai bacci,sai wanka sai wata kwanciyar. Gyaran gidan kansa bai wani dameta ba,don tana ganin ba wani muhalli bane da zata damu kanta a kansa,hasalima a nata ganin waje ne da lokaci kawai take jira ta barshi. Abu biyu take gyarawa,bedroom dinta sai kitchen din da ba wani abun arziqi take dafawa ba. Tun ranar da tayi abincin safen nan rabonta da tayi wani cikakken abinci ta sawa cikinta,iyakar yunwa idan ta ciyota ta soya qwai guda biyu... Kota dafa indomie guda daya kota soya potatoes taci shikenan. A kwanakin tana jin yadda qirjinta yake riqewa amma taqi damuwa da wannan bare takai hankalinta kai,abu daya kawai take jira ya dawo,tayi duk yadda zatayi ta cika aikin maamah ta samu freedom. Ta sani tana da wata fitinanniyar ulcer data kusa sanyata tabi bayan mahaifi da mahaifiyarta bayan rasuwar ummensu. Ulcer data samo asali daga matsiyaciyar yunwar da tayi mugun horasu,takaita matakin da take xubda aman jini. Ta jima rabon data tashi,tunda ta samu sassaucin rayuwa suke iya ci su qoshi,amma a kwanakin nan da take bata alamu taqi maida hankalinta sam sam. ★"Alhamdulillah" Shine abinda ya furta lokacin da ya fito daga toilet wanda ya barshi wata guda cur kenan. Shirya kansa ya fara yi cikin butter milk color pyjamas yana tunanin kiran me sunan malam da ameh gobe kowa ya dora aikinsa a inda ya tsaya. Sam har ga Allah ya sha'afa da ita,abinda ya sameshi ya shafe abubuwa da yawa a kansa. Gidan duka ya masa datti a yadda yake tsantseni da tsananin tsafta,ya kammala shirin nasa sai ya kasa saukowa saboda gajiya,ya bude freezer dinsa dake dining area dinsa na sama yana fatan samun wani abun. Wuta ce 24/7 da kome zaka ajjiye a fridge din zaka sameshi fresh. Damammiyar fura ya ciro wadda ba komai cikinta daga nono din sai furar da aka markadasu suka hade jikinsu sosai. Furar daya samu ta masa daidai,don abace dame relaxing jiki da bada bacci me kyau da daddare saboda sinadaran da gero ke dauke dashi. Ta masa sanyi,baya kuma shan abu me sanyi sosai har haka,wannan ya sanya ya ajiyeta ya koma ya kunna tv don ya rage mintunan da zaiyi jiran furar. Kadan kadan takejin kamar wani baqon sauti cikin gidan sanda take baro kitchen inda ta soya qwai guda biyu,tana taraddadin ci ma saboda maiqon dake jiki amma kuma batajin tana da wani abinciii bayan shi. Fargaba taji tana cikata,wani irin matsanancin tsoro ya saukar mata. Sound ne tabbas wanda bata tantance na meye ba. To ko haurowa gidan akayi?,ko wani ne ya shigo ciki ya boye ba tare da sanin securities din ba?. Duka ba kalar tunanin da batayi ba,jikinta na rawa ta qarasa dakinta ta maida qofar ta rufe tana maida numfashi. Jin still da sound din sai tsoron yaqi barinta,ta taka da hanzari tabi duka windows din ta kulle sannan ta dawo tsakiyar dakin ta zauna tana raba ido tare da sauraron koma meye daga inda zai bullo. Sai data masa daidai sannan ya kashe tv din,ya dauketa ya hada da cup da spoon ya wuce daki. Sake kasa kunnenta tayi da kyau,a yanzu ba sound din,saita lumshe ido tana qoqarin saita nutsuwar kanta. Bata taba sanin kadaici masifa bane sai yanzu,bata taba sanin haka yake taba ruhi da rayuwar mutum ba sai yanzu. Wasu hawaye suka biyo ta lumsassun idanunta suka gangaro kan fuskarta. Gaba daya ta koma wata raguwa a kwanakin,zuciyarta kwata kwata ba wannan qwarin da tsaurin sai wani irin rauni da ya sake cikata,sai kawai ta kifa kanta saman pillow din ta saki siririn kuka,fried egg din da bata iya ci ba kenan. ★Bacci yayi sosai wanda da qyar ya tashi sallar asuba wadda duk tsanani zai wahala ta kubce masa. Koda ya koma yunwa ce ta tadashi,cikinsa gaba daya kamar an masa yasa. Yadan yamutsa fuska kadan yana tunanin me zaici?. Inda ameh yana nan ya tabbatar yanzun da yake qarfe sha biyu na rana ya gama breakfast yana jiran umarnin hada lunch da za'a kai company ko kuma ya jirayi zuwan dafa dinner. Brush ya fara shiga yayi sannan ya fito,ya dauki wayarsa guda daya a ciki ya kunnata. Kamar jira akeyi sabbin saqonni suka shiga turereniyar shigowa,baibi takai ba ya lalubi number ameh,bai sameshi ba,yaja dan qaramin tsaki,wala'alla ya lalata wayarsa kaman yadda ya saba,waya bata fiya dadewa a hannunsa ba zakaji ta fadi ko kuma ta lalace,wannan dalilin ya sanya ameh din kansa baida cikakken number boss din nasa,wanda dama kusan duk wanda ya mallaki number wayarsa ya cancanta kuma yana da connection dashi nakai tsaye irinsu ameh din dame sunan malam. Amna ya kira,bugu biyu ta daga. "Hamma......barka da dawowa" "Barka kade amna" "Good morning hamma......ya hanya ya gajiya?" "Alhamdulillah......ya makaranta?,kun fara shiga lectures?". Kai ta gyada "Mun fara hamma......ba dadi hamma ba supporter.......BB farouq yace na cika shirme......ya saddiq tsokanana yake koda kuna nan......nayi missing ya musaddiq har yanzu bai dawo ba......please hamma kace ya dawo haka?" Ta qarasa maganar a shagwabe. "Zai dawo soon" Ya furta badon yana nufin ya barshi ya dawo nan kusa ba. Tun tuni ya aike da musaddiq din wani aiki don ya nisantashi da maamah,bayason zamansa a nan ya tabbatar idan yana nan watarana maamah zataci galaba a kansa. Hakanan baison fitowa kai tsaye ya nunawa musaddiq komai akan maamah "Allah ya dawo dashi lafiya....." "Ameeen amneee......ki hadani da anni idan kin fito.....ki gayawa ameh lallai lallai yazo yau" "In sha Allah hamma" Tana shirin tambayarsa sabreen ya ajiye wayar.....saita bari kawai ta shigo gidan da kanta tayi mata barka da dawowa. Yadda taji yunwa na kama mata cikinta da gaske ya sanyata miqewa bisa dole. Yau kam sanye take da silk sleeping dress maroon color,riga ce iya cinya da wandonta dogo har qasa,saidai kuma tana da dan budadden wuya kadan. Duk da ramewa data danyi hakan bai hana rigar mata kyau ba,ta kuma zauna cif a jikinta. Jikinta ta jawo ta sauka daga saman gadon,tasa hannu ta tattare gashin kanta waje daya a qeyarta,ta taka a haka zuwa gaban madubi,ta jawo dan madaidaicin jewelry organizer din dake saman madubi ta budeshi,hair clip guda daya babba ta maqaleshi sannan ta samu vintage scarf ta daure kanta,wanda jelarsa dankwalin ta zauka kafadar hagu da damanta. Akwai socks a qafarta,wadda sanyin ac din gidan ya sanya dole take sakata saboda yadda marbles din yake daukan sanyi sosai,kwata kwata batasan ya ake controlling duka Airconditoners din ba bare ta daidaita shi,hakanan kawai take haquri. Sauqinta daya ana cikin yanayi na zafin farkon kasancewar damuna,banda haka ta tabbatar ba qaramar illa zatayi mata ba. A nutse ta murda qofar,ta fara leqo da kanta tukunna tana tuna motsin da taji jiya,sai data tabbatar shuru wajen yake ba alamun komai sannan ta fara fitowa a darare tana sanda hannunta dauke da plate din soyayyen qwan. Yau haka nan ya sauko da qafafunsa bai sanya takalmi ba. Fara tas din qafarsa dake da dogayen yatsu yake takawa a nutse yana sauka daga stairs din hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa ta William,yanason sake tabbatar da komai na company din yana tafiya lafiya lau. Sanda ta buda qofar da zata sadata da parlor din farko ta sanya qafarta lokacin ya kusa da stairs din qarshe,wannan ya bashi damar ganin wulgawar mutum ba tare daya tantance waye ba. Dan tsam yayi da ransa sai kuma yadan qara hanzarin saukowar don yaga waye ya gilma din,sam zuciyarsa na masa nisa da tuna tana cikin gidan. Da wani irin sassarfa take qoqarin fita a falon ta sada kanta da falo na biyu na gidan ta boye kanta a kitchen. Murya takeji sosai tana sake kusanto inda take,tsoro ya sake cikata,kenan wani ne ya kwana a gidan akayi mata kwanton bauna?,har sai da akaji fitowarta sannan ya bayyana?. Ta shiga uku,su waye suka shigo?,abu daya ta sani ko zasu yankata su cinye ba wanda yasan sun shigo saboda tazarar dake tsakaninta da security din gidan. Tana saurin isa ga kitchen don ta buya yana sassarfar shan gaban macen daya gani. Kusan dukansu sai abun yazo musu lokaci guda,yana dab da cimmata tunaninsa ya dawo kansa. Ashe yabar wata cikin gida......akwai yarinyar dake rayuwa cikin gidan,wannan tunanin ya sanyashi tsaiwa cak,tsaiwar tasa ta bata damar wucewa kitchen din cikin matuqar sauri ta maida qofar ta kulle harda murza key. Qofar yabi da kallo yana zare wayar daga kunnensa. Mamaki kadan yana kamashi,anya qwaqwalwarta lafiya qalau take kuwa?. A nutse ya xura wayar a aljuhunsa yana dage kafadunsa cikin I don't care manner,sai kuma ya koma saman daya daga cikin kujerun ya zauna yana canza channel,kadan kadan kuma yana kallon falon. Ba wani tarkace bane ko wani abu a ciki,amma tsaftarsa bata masa ba. Ya saba duk inda ya wurga idanunsa ya ganshi fes yana qyalli da daukan idanu,amma a nan din idanunsa suna iya ganin qura a wasu guraren. Qaramin tsaki yaja can qasan ranshi yana fadin bazai dauki qazanta ba. Minti biyar yana jira yaga ta bude qofan amma ba alama,yunwa yakeji sosai,yana buqatar wani abu me nauyi da zai sanyawa cikinsa. Baya wasa sam da cikinsa,mutum ne me son lafiyayyen abinci musamman wanda ya dace da tsarinsa. Miqewa yayi ya taka a hankali ya isa bakin kitchen din,har a sannan tana maqale bayan qofar tana tunanin yadda za'a yi ta kubuta daga hannun mutumin da batasan yadda akayi ya shigo gidan ba. Knocking din daya fara yi a hankali ya sake gigitata,ta qanqame jikinta guri daya tana runtse idanunta hankali a tashe. Sau biyar yana bugawar ba wani motsinta,ranshi ya sake baci,sai kawai yabar wajen yana takawa a hankali ya nufi wata qofa daban da zata sadashi da kitchen din ta baya. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 30 30 Jin an dakata da bugun ya sanyata sulalewa a wajen tana dafe qirjinta. Bata ankara ba hawaye ya balle mata,dama ta yaya za'a barta a gida irin wannan ita daya idan ba dama anyi shirin salwantar da rayuwarta bane da gangan. Tunda take a rayuwarta bata taba sanin tsoro na ainihi irin wannan ba. Qofar data hanga ya sanya taji relief,ta goge fuskarta ta mmiqe a hankali cikin sanda tana nufar qofar ko zata samu wata hanya da zata fice daga cikin gidan zuwa bakin gate. Tana miqa hannunta tana riqe handle din da zummar bude qofar daidai lokacin shima ya bude qofar da dan zafin nama,abinda ya sanyata ta biyo qofar takuma yi kyakkyawan masauki a jikinsa. Dif shi da ita wuta ta dauke musu,ita gaba daya tayi mutuwar tsaye je zuciyarta na wani mahaukacin bugu cikin saddaqarwa kan ta shiga hannun koma waye......yayin da shi kuma ba zatar fadowarta jikinsa ya sanya komai ya tsaye masa can na wucin gadi. Hannunsa ya sanya ya janyeta gefe yana hade rai da wani mugun miskilanci,ya hade girar sama data qasa yana dubanta sanda ta samu ta dafe kitchen cabinet din don ya taimaka wajen tsaiwa "What's this?" Ya furta a dake yana hade rai. Can qasan ransa yana jin haushi haushi yana saukar masa. Da biyu ta fada jikinsa ko meye?,ko tsabar sabawa da hada jiki da wasu ne?,a yanzun an turketa kusan wata guda ba tare da d'a namiji ba ta kasa daurewa?. "Ya kamata ki saita kanki,nan din ba irin sauran guraren da kika saba rayuwa bane....ki koyi controlling feelings dinki" Abinda yace da ita kenan yana takawa zuwa gaba hadi da miqa hannunshi yana bude drawers din sama. Sosai ta tattara dukka dauriyarta da nutsuwarta ta dawo da ita gangar jikinta tana ta kokawar hadiye tsoronta. Wani irin takaici ya kamata bayan data fuskanci shine. Ya akayi tayi gangancin gaza gane shine ya dawo?,bacin rai ya hanata komai,sai kawai ta juya tana takawa zuwa qofar data kulleta da hannunta ta fara bude key din da wani irin zafin nama. Duk da a rude take amma tasan sau biyu ta murza key din,yanzun ma sau biyun ta bude amma kuma data tura sai qofar taqi budewa. Sake murzawa tayi daya biyu har sau uku amma ba alamar qofar zata budu. Wasa wasa haka ta sake gwadawa amma jiya i yau,sai taji gudun zuciyarta na qara daduwa,don burinta kawai shine ta fita a kitchen din. Tayi iya duka qoqarinta amma ko gezau qofan baiyi ba,wannan ya sanya duk wani karsashi nata ya sulale,ta zame hannunta daga jikin qofar zuciyarta fal da tunanin ta yaya zata juya tabi ta daya qofar bayan yana kai kawo a kitchen din yana harkokinsa?. Duk wani motsi nata yana ankare dashi,har yadda ta dinga qoqarin bude qofar amma taqi koda motsi. Idanunshi jifa jifa a kanta sanda yake kai kawo tsakanin store din yana duba abinda zai iya sarrafawa da kuma dawowarsa kitchen din ya fara marinating kifi da zummar ya gasa shi,abinda ya manta rabonsa da yayi. Ya kammala cikin sauqi,saboda akwai komai kawai zubawa zaiyi ya saka a oven ya saita masa lokaci,sai ya saka din ya saita time ya koma ya jingina da kitchen cabinet din yana harde hannunsa a qirji yana jiran time ya cika yayin da yake sauraren voice note din da ya tarar daga William. Da fari baiko kalli sashenta ba koda sau daya kuwa,amma a hankali sanda hankalinsa yayi nisa da sauraren voice din sai kunnuwansa suka sauko masa raguwar sautin yunqurin bude qofar da taketa yi. A nutse ya daga idanun nan nashi dake da wani irin shape da yanayi me daukan hankali ya saukesu a bayanta daya fidda cikakken shape dinta saboda yadda kayan suka zauna mata cif da cif,daga kafafunta zuwa qugunta yayin da qugun zuwa cinyoyinta suka bude sosai suka bada wani faffadan qugu da yalwatattun cinyoyi. Vintage scarf din dake kanta ya zame ba tare data sani ba,saidai yana maqale a wuyanta,wannan ya sanya har clip din kanta pink color daya matse gashinta ya rage tsahonsa da yawansa ya bayyana. Baisan me ya maida idanunsa saman mazaunanta ba da suka bayyana sosai saboda silk material din dake jikinta,uwa uba kuma rigar bata qarasa rufe mata su ba. Abinda ya fara fado masa shine hirar amna da wasu qawayenta daya taba tsinta dake maganar maganin hips da sauran wasu hanyoyin qarawa mace hips. "Ita dinma ba zata kubuta daga amfani dasu ba......" Ya furta a ransa bayan da zuciyarsa ta tuna masa wacece ita?. "Allah ne yasan maza nawa ne suka taba kai hannunsu wajen,maza nawa ne suka taba taba wajen sukasan ya fadi da tudunsa yake" Wani mahaukacin tsaki daya cika kitchen din yaja,wani mummunan bacin rai yana saukar masa. Hannayensa ya saki kawai yana komawa zuwa bakin oven din yana jin zaman kitchen din yana gundurarsa. A duk sanda ya tuna iya shekarun haihuwarta a duniya da tayi kwata kwata na shekara ashirin da hudu cikin ta ashirin da biyar......da kuma adadin yawan mazan da akace masa takai qasa ko kuma ta taba mu'amala dasu,duk sai yaga ta masa baqiqirin,sai yaji wani abu ya tsaye masa a rai idan ya kalli koda gilmawarta ne "Idan tasan me yawan sha'awace me ya hanata ta fadi gaskiyarta a gida ayi mata aure?" Ya sake rayawa a ransa. Kwata kwata baya cikin jerin mutanen dake da ra'ayin riqau akan yaransu mata na sai sun gama karatu kafin a aurar dasu. Ya dauki izinina daga yadda yanayin halittarshi yake......wanda hakan yana daya daga cikin abinda ya sanya ya maida kwanyar da zata tsarta masa tunani na sha'awa a ransa cikin muguwar hidima da sabgar da idan ba mugun qaddara ba baida time da zata dauki wannan feeling din ta harba zuciyarsa har zuwa sassan jikinsa. Saboda kwata kwata bai shirya aure ba,totally mata basu taba burgeshi ba.....uwa uba bai tsara tsomasu a rayuwarsa nan kusa ba,saboda abinda yake kalla kusan dukkaninsu dukiyarka ko nasararka suke aure. (Kira gareku iyaye mata,a matsayinki na uwa ya kamata ki lura da yanayin kowanne yaro da kika haifa,don dukkaninsu ke kika haifesu,don kamanninsu daya hakan bawai yana nufin asalin halittarsu daya ba. Wani lokaci yaro namiji zaiyita nuna sha'awar aure,amma sai a masa caaa ace ya fiya tsaurin ido......wani lokaci yarinya na nuna wannan sai ace ta fiya rashin kunya da tsaurin idanu,ba tare sam da duba da cewa halitta bace daga ubangiji,sai kuyi mata mummunar fahimta,aci alwashin sai an turata jami'a,koshi yaran aci burin zuzzurfan karatu a kansa ko kuma sai yayi kudi. Kuskure ne wannan babban,daga namiji har mace idan aka fuskanci haka tattare dasu,idan tana da manemi nagartacce a aurar da ita yafi alkhairi,idan namiji ne yana da halin riqe kansa,ko kuna da wadatar riqe masa matar kafin ya qarasa zama mutum to a rufa masa asiri ayi auren a huta. Idan ba hali ko koya musu azumin litinin da alhamis,su lazimci karatun qur'ani,yawan tunasarwa da wa'azi,duk juyi kuma kada a dinga barinsu suna yawan kadaicewa a daki,a kusantasu da abokai na gari,da zarar dama ta samu kuma ayi a aurar dasu,Allah ya iya mana ya tarbiyyantar mana ameen summa ameen). Cikin sa'a ya samu ya gasu,sai kawai ya sakashi duka har aluminum foil din cikin plate,ya soma takawa yana hanyar ficewa ta daya qofar. Har ya kusa qofa sai ya fasa fitan,ja yayi ya tsaya sannan a hankali ya waiwayo,sai ya ware idanunshi a kanta yanata qoqarin kaucewa kallon guraren da yake ganin bai kamata ya kalla din ba. Cikin jikinta taji kamar da idanunshi a kanta,tuntuni taji ya tsaya da tafiyar da yakeyi abinda yake bata tabbacin bai fita din ba. Bata qaunar koda wanzuwarsu a waje daya sam shi da ita. Haushinsa takeji sosai,irin haushin da ko gilmawarsa batason gani ballantana qamshin turarensa. Cikin dakiya da jarumta ta soma takowa da zummar gewayeshi ta fice ba tare data yarda ta kalli ko gefen da yake tsaye ba ballantana tasan me ya tsaidashi din,tunda dai taga ya shigo ta nan din ta tabbatar hanya ce duk da bata taba bi ta nan din ba. Sai da tazo daf dashi zata gotashi din,cikin ba zata ya sanya qafarshi yana blocking duk wata hanya da zata wuce. Ta qasa ta kalli yadda yayi blocking din nata,wani abu ya sake zuwa yayi mata tsaye a wuya,sai take jin ta dauki iya abinda zata iya dauka daga gareshi,abun nashi kaman yanason ya qure iyakar haqurinta. Bashi da masaniyar kakkaifar katangar qarfe da garkuwar maamah a gareta shi yasa yake samunta a yadda ya so?,shi yasa yake samun daman juyata yadda yaga dama?,ko yana tsammanin izzarsa da dukiyarsa da sunansa duka su suka siya masa wannan. "Ka ban hanya zan wuce!" Ta fada adan zafafe tana jin zuciyarta kamar zata fashe. Duka abubuwan da yayi mata basu isheshi ba?,yanzun kuma sai ya qara da tarwatsa mata zuciya ta hanyar tsoratata?. Me yasa dole sai ya shiga harkan rayuwarta ne?. Hannunsa ya goye a qirjinsa bayan ya ajiye glass dish din da hake hannunsa yana dubanta. Kana kallon yadda Adams Apple dinsa ke sama da qasa kasan Shima nashi ran ya fara baci. Ya sake gasgata komai a kanta,yadda kunya ke nuna qaranci a tattare da ita. Yayi zaton zaizo ya sameta tayi laushi amma baiga alamun hakan ba. "Excuse me?" Ta kuma fada tana kafeshi da oily eyes dinta wanda ba kasafai ka fiya gane da qwalla a ciki ko babu ba,saboda koda yaushe yanayinsu tamkar an diga mai ko ruwa a cikin su haka suke. Kanta ta maida gaba ta hade jikinta sosai da zummar rabe masa,saidai ya hanata wannan damar,abinda ya sanyata sake tsaiwa kenan tana furzar da zazzafar iska daga bakinta. "Me kakeso ne?!......me kake buqata?,kome da kayi bai isheka ba?,ka kulleni for good one month.....kayi disconnecting komai da kowa daga gareni......yanzun kuma ka dawo kanason kasheni da tsoro?,me kake so?" Tayi maganar zallar bacin rai yana nuna kansa a fuskarta,tana kuma jin radadin abinda yayi matan da gaske. "Enough.....ya isheni!" Ta sake fada tana ware hannuwanta tare da fidda girman oily eyes dinta a kansa. "Am not your......." "Just stop!" Yayi maganar da muryar data ratsa har cikin kwanyarta,ta kuma sanyata runtse idanun dole "Am not your mate......dole kisan da wanne harshe zaki dinga min magana!" Ya sake maimaita mata a tsawace. Ji tayi kaman kanta bazai iya dauka ba,muryarsa tayi amsa kuwwa akunnuwanta sosai da kalar tsawar data manta rabonta da irinta,sai kawai ta juya da zummar koma yayane ya rabeshi ta wuce. Saidai kuma ina,yana ganin shirinta ya sanya hannu ya riqe hannunta da zummar dawo da ita da baya.....don dole ya fara saita mata harshenta kafin komai. Cikin rashin sa'a dukka maballan gaban rigar suka fara balle kansu da kansu saboda riqon da yayi mata. Abinda ya qara yawan adadin tashin hankalinta kenan jin iska ta fara ratsa ainihin fatarta,abinda yake tabbatar mata da cewa tabbas qirjinta tun daga sama zuwa qasa yana bayyana a waje. "Leave me.....ka sakeni!" Ta tattara qarfinta tana fada cikin tsawar da batasan ta yita bama saboda gigita da tsoron fitar tsiraicinta a gabansa,babban abun tashin hankalin da hannu daya taketa qoqarin kamo rigar saboda daya hannun yana riqe cikin nasa. Tsawar tata ya sake rura wutar fushin dake zuciyarsa wadda keta qissima masa abubuwa kala kala a kanta na irin hukuncin da zai mata. Ba'a saba masa rashin kunya haka ba,don haka baima san me ya dace yayi mata cikin zafin nan ba,sai kawai ya sake fincikota da qarfin da sai da taji hannunta ya amsa,batayi wata wata ba ta fada qirjinsa gaba daya. Bakinta yaqi mutuwa,ta tattara dukka qarfinta tana son tureshi tana bayyana tsantsar fushinta cikin maganganunta,ransa ke qara baci,zuciya kuma tana sake tunzurashi......yana da fushi yana da zuciya,amma ba kasafai ya fiya son tashin hankali ba "Shut your mouth" Ya fadi yana dubanta da kyau,saidai kaman bata ji ba,tana magana ne ransa yana baci,ya sakeyi mata riqon tsauri ba tare daya damu da son qwacewa takeson yi ba "Zip it....Hold your tongue" Still fushin da take ciki ya hanata gane me yake fada....zuwa lokacin hawayen da taketa tattalinsu sun fara yiwa kansu gurbi saman fuskarta. "Silence yourself......Don't annoy me!" Ya fada da husky voice dinsa......fushin da yakeji bayason ya bari yayi hukunci a irin wannan lokacin,don haka kawai sainya zabi riqe fuskarta cikin tafukan hannayensa da kyau yana furzar da iska me zafi daga bakinsa a saman fuskarta,idanunshi kan lips dinta dake magana suna rawa,sai kawai ya hade bakunansu guri daya. Wata irin tsotsa yakewa lips din nata cikin salon fushi da bacin rai. Tun a karon farko hankalinta ya fara dawowa kan abinda yakeyi saboda tsananin zafin daya ratsa lips din nata. A lokacin ne kuma ta fara yunqurin tureshi ta raba kanta da mummunan zugin da takeji saman lips din nata amma a banza,don ko motsawa baiyi ba,bai kuma rabu da ita ba sai daya tabbatar taji a jikinta,lips din ya ninka girmansa na asali......sannan yaja da baya yana dan tureta har sai data dafe kitchen cabinet. Qirjinsa sama da qasa yakeyi cikin mode na fushi da kuma mix na wani feeling da yaji yana ratsa tsakiyar fushin nasa. Gefe tayi da fuskarta saboda kuka daya taho mata sosai tana dauke dubanta daga cikin idanunsa da suka sauya launi. "Im not getting into it na zauna ina miki explaining ko doraki a hanya......i have many ways to punish you" Ya fada sautinsa yana rarrabewa kamar wanda yayi tseren gudu ya gaji,sai ya fusgi dish dinsa yana ficewa daga kitchen din. Duk da tasan ya fice din amma ta gaza dago kanta,don jikinta ta tabbatar rawa yakeyi ko ta ina. Sai data kusa minti daya sannan ta motsa da nufin fita itama tacan,amma sai taji QIT kamar an cire maqullin jikin wannan qofar aka murda handle din aka bude sannna aka juya ana barin wajen. Ko daga qamshin turarensa kawai ta gane shine ya bude,batayi wata wata ba ta qarasa wangale qofar ta kuma taka tana fita ba tare da ta tsaya tantancewa da mutum a falon ba ko kuma babu. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 31 _Daga abdullahi dan abbas R.A,wata kuyanga(baiwa)budurwa tazo wajen manzon Allah S A W,ta gaya mishi cewa,babanta yayi mata auren dole,sai manzon Allah S A W ya bata zabi(haquri da auren ko a raba)_ _____________________________ 31 Idanunta a rurrufe ta tura qofar dakin nata ta shiga,ta kuma maida key din ta rufe tana jin kamar zai sake biyota ne. Wani azababben kuka ta saki tana jin yadda labbanta ke wani irin zugi kamar zasu cire daga saman bakin nata. Tako ta ina tun daga saman labban nata har zuwa fuskarta dama qirjinta ba abinda suke fitarwa sai wannan mayataccen qamshin nasa. Ta jima tana kuka gami da murza lips din,tana fatan zugin da takeji ya ragu.....har batasan iya adadin lokutan data shafe a haka ba. Qarar agogon dakin ya sanyata maida idanunta da sukayi mata nauyi saman agogon,lokaci yaja.....saita miqe da dan hanzari ta zauna. Kaman yadda jikinta bai daina rawa ba haka zuciyarta da labbanta basu daina mata zafi ba. Duka hannuwanta ta saka ta rufe fuskarta dashi tana ci gaba da sauraren bugun zuciyarta. "Ba lokacin wannan bane sabreen.....ba lokacin bata lokaci bane wannan,kina sake bawa maamah damar kasancewa da 'yan uwanki ne kawai a kowacce daqiqa....lokacin aiki ne tuquru yanzu don qwatar kai.....ki daina bari normal halittan namiji kamar saura yana firgitaki......wanne iri ne baki gani ba?" Taji ana gaya mata daga can wani sashe na zuciyarta. Abinda ya zaburar da ita kenan ta fara zame kayan baccin jikinta ta daura towel ta wuce bandaki. Wanka tayi ta dawo ta shirya cikin atamfa doguwar riga,ta gyara ta matseshi cikin hair tie masu wani irin adon stones masu garai garai a jikinsu dan madaidaita. Bata saka komai a fuskarta ba,amma tayi wani irin kyau duk da ramar da tayi,saidai kuma fatarta tayi fresh saboda zama waje daya da rashin bawa rana damar qona fatarta,uwa uba har yanzu mayataccen gyaran jikin nan yana nan baibar jikinta ba,batasan wanne irin rantsatsen hadi bane annin ta biya kudi akayi mata. Duk da yunwar dake qwaqular cikinta amma sai taji sam ba zata iya zama ba,hasalima duka tasirin yunwar ya gushe,kitchen take da muradin shiga ta shirya abincin dare,wanda take fatan koda batayi na rana ba aqalla a samu na dare. Da dan hanzarinta take fitowa daga hallway din,hankalinta yayi gaba zuwa kitchen sautin muryarta ya dakatar da ita "Adda sabreen" Amna da shigowarta kenan ta fadi fuskarta cike da murmushi. Suna hada idanu ta sakar mata fuska da salon nata murmushin. Haka kawai tana tuna mata da huda duk da hudan miskila ce ba kaman amna ba,amma sai take mata yanayi da hudan. "Yaushe kika shigo?,afwan ban sani ba ina ciki ina wanka" Ta fada tana neman gefan wata kujerar daban ta zauna. Da murmushinta tace "Adda sai an miki uzuri,matafiyi ba'a rasashi da gajiya a jikinsa,ni har zan kunna wayata ma na duba wani assignment kafin ku samu fitowa" Kyawawan fararen idanunta sabreen ta fiddo waje. "Haba dai,ya zaki zauna kiyita jira,da kin qarasa kinmin magana ai". Bakinta ta rufe da tafin hannunta "Kinaso hamma ya ballan qafa?,ba'a shiga shiyyar dakinsa direct ai,BB farouq ne kawai ya isa". Tabe baki tayi a fakaice,can qasan ranta tana fahimtar tsananin izza gareshi da shegen mulki. Fara sako mata zancansa da tayi yasa sabreen miqewa cikin qarfin hali da son nuna komai lafiya "Bari na baki ruwa kisha" "Am full adda.....saidai na rakaki kitchen naga kaman kitchen zaki shiga" Kafada ta daga da murmushi "Alright.....muje" "Yau hamma za'ayi full da abincin addana.....yadda yakeson abinci me dadi na tabbatar adda na ba daga baya ba.....in fact ma tunda har kikayi nasarar samun hamma na na tabbatar komai kin hada" Tayi maganar da dariya dariyar tsokana. Bata ce mata komai ba,tadai qoqarta sauke mata murmushi kawai. Sanda suka shiga kitchen din duk sai taji ta takura,ta rasa ta inda zata fara,saboda idan maganar qwarewa ake ta fannin girki tasan bata cikin jerin wadannan matan,infact ma ita ba gwanar shiga kitchen bace sam.....to ina ma taga time?,tana ta abinda qannenta zasuci susha su lulluba sutura,suyi magani idan lalura ta taso?. Tasan huda ta tsere mata sosai ta fagen iya girki,don tun tana fita tana barinsu hudan tana musu tsumburin burin har tazo ta qware. "Kaman ya kamata kiyi surprising hamma na ko?" Amna ta fadi da murmushi tana duban sabreen. Kallonta kawai tayi kallon dake nuna alaman tambaya,sai amnan ta daga kafada "Gift dina na yau zan gaya miki best food nashi da daddare.....but nima zaki bani tukuici ki gayamin sirrin skin dinki adda don Allah?" Ta qarasa fada a shagwabe. Abun dariya yaso bawa sabreen saidai batayi ba illa murmushi data saki,ta kalli fatar tata ta kalli amna,ita bataga wani kyau da fatarta tafi ta amna ba "Seriously adda kina burgeni at the first time dana fara ganinki.....kawai naji jinina ya hadu da naki" Ta fadi da gasken ta yadda a furucinta zaka fahimci da gasken take. Kusan tana zaune amna ta hada duka ingredients din na kalar abincin. Ta miqe tana daura apron data gani tana bawa amna daya,sai qararrawar dake kitchen din ta dauki tsuwwa. Amna ce ta duba,saita waiwayo ta kalleta "Kira ne daga bakin gate" Tayi maganar tana miqa mata wayar "Ki daga" Tace da ita,ba musu ta saka a kunne,bayan wasu sakanni ta dawo da dubanta kan sabreen "Wai baqi ne dake.....zuwaira daga wajen hajiya mariya maamah". Maganar taji ta bugu qirjinta don tazo mata kamar a bazata,sam ta mance da issue dinsu,sai ta fara zare apron din tana cewa "Kice a barsu su shigo" Yadda ta fada mata haka ta gaya musu,ta zare apron din ta ajiyeta ta soma dosar kitchen din tana cewa "Ina zuwa amna" "Ba damuwa adda" Ta amsata tana matsawa kitchen din don ci gaba da aikin. Kasa tsaiwa tayi daga cikin parlor din,ta taka har qofar qarshe wadda daga ita sai balcony din da zaka sauka zuwa farfajiyar gidan. Tsaye tayi kawai riqe da qofar,ba abinda ya hanata hango wajen sai lafiyayyen curtain din daya raba tsakaninsu. "Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta fara rasa falon kafin ta bayyana Laila na biye da ita a baya da luggage dinta dake da girma,tana takawa d'ai d'ai,tana sake ganin alatun da aka xubawa gidan,sai take ganin wancan zuwa bataga komai bama. "Wa'alaikumussalam" Ta amsa mata idanunsu yana haduwa waje daya dana laila. Wata faduwar gaba ta saukarwa lailan lokacin da idanunta ya shiga cikin na sabreen dake tsaye tana jiran shigowarsu "Kambu.....who's she?" Ta samu kanta da furtawa a qasan zuciyarta saidai kuma labbanta a sarari ma rawa sukeyi. Yanayin kallon da lailan ke mata sam baiyi mata ba,a nutse da wani irin jan aji ta debe kallonta daga kan lailan tana maidawa kan zuwaira dake qoqarin gaidata "Basai kin tsuguna ba......ta nan ga qofa nan a nan din akwai dakuna a ciki,ku zabi duk wanda yayi muku" Ta amsata a taqaice don ko tsaiwarsu a wajen sai taji bata qauna. Tasan da qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dinga yi cikin gidan *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 32 _Daga abdullahi dan umar R.A yace."manzan Allah S A W ya hana auren shigaari,shi kuwa auren shigaari shine,mutum ya aurar da d'iyarsa ga wani,bisa sharadin Shima wancan zai aura masa tasa 'yar,kuma babu biyan sadaki a tsakaninsu(musanye kenan)_ _bukhari da muslim ne suka rawaito_ ___________________________ 32 Tasan qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dingayi cikin gidan da kuma Yanayin wajen kuma tasan guri ne baqi na kusa bayan boys quaters da gidan ya mallaka na musamman da yake daga can bayan gidan. Bata da matsala dasu,koda dakunan hallway suka zaba kuwa,don kowacce rana a lissafe kwanakinta cikin gidan suke. "To.....to madallah......bari mu qarasa" Xuwaira ta fada tana wucewa gaba laila tana biye da ita. Duk wani taku daya biyu na lailan saisun hada idanu da sabreen din wadda ke tsaye yana karantar yanayin kowanne a cikinsu. Dauke dubanta tayi,sai ta koma saman kujerar falon ta zauna kawai yanayin jikinta yana neman sauyawa. "Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta sake ratso falon. Idanunta ta daga a hankali tana duban zuwaira sanda take takowa falon riqe da waya a hannunta fuskarta a sake "Ranki ya dade.....hajiya nason ganawa dake" Tayi maganar tana miqa mata wani qaramin akwati da sabreen din ta kasa amsa sai binsa da kallo da tayi. Daya hannun waya daya akwati,kuma dukkaninsu idanun zuwaira suna gaya mata ana da buqatar karbar kowanne. Cikin kwanyarta taji ana umartarta data karba,ba wani laka a jikinta ta karba dukkaninsu "Sirri yana da matuqar muhimmanci......hajiya nason sirri matuqa" Ta tsinci muryar zuwaira tana gaya mata. Idanu ta waiwayowa ta zubawa zuwairan,sai kawai ta dauke kanta tana nufar hanyar hallway don komawa dakinta. Kaman ana jira ta shiga dakin wayar tahau kadawa,ta zubawa sunan da zuwaira tayi saving dashi wato hajjaju. Tattaro dukka wata dauriya tata tayi,ta hadiye wani yawu me kauri sannan ta daga kiran ta sakashi a hands free hana ajiye wayar saman cinyoyinta. "Ka kula da ita.....huda kuje ya baki magani kisha kafin ki kwanta.....sannu qawata". Abinda kunnuwanta suka fara jiye mata kenan wanda ya sanya tsigogin jikinta tashi. Ta runtse idanunta tanajin kamar an daukk guduma an kwada mata saman kanta. "Huda kuma?" Ta motsa labbanta tana furtawa a wahalce. Murmushin maama ne ya soma riskarta kafin tace "Eh,huda.....ko bazatayi lalura ba?......kowanne sakaci da zakiyi akwai sakamakonsa kan halittar da kika fi so fiye da komai da kuma kowa......" "Bani huda din" Ta fada kanta tsaye da wani irin yanayi me kaushi. Wata qaramar murmushi me kama da dariya ta saki "Da wuri haka?,zabin cetonsu ai yana hannunki tunda na gabatar miki da dukka kayan aiki.......bansan me yasa kika yanke sadarwar dake tsakaninmu ba.....saidai koma meye wannan ba damuwa ta bace......kowanne ganganci kuskure ko sakaci sakamakonsa rubutacce ne a nan......" "Idan kikayi kuskuren cutar da ko farcen daya daga cikinsu ne......to lallai ba shakka ba mallaka miki danki zanyi ba......zan sadar dashi da kabarinsa ne,zan mallakaws barzahu shi a madadin ki" Sabreen ta fada cikin tsawa da wani irin birkitaccen sauti daya ratsa maamah,taji kuma har cikin jikinta da gaske ta fadi maganar. Ta danyi jim kadan tana jin wata shakka tana ratsa ta,sai kuma ta saki wata dariya "Bismillah mana......indai har kina ganin hallaka mutum kamar muhammad jadda abune me sauqi....." "Akwai abinda yafimin wannan sauqi?.....aikinki ya ninka shi wahala sau dubunnan da bazasu qirgu ba.......idan naso a safiyar gobe za'a wayi gari da sanarwar jana'izarsa hajiya maamah.......saboda haka ki kula......akwai kadarata a hannunki......a nan kuma akwai ruhinki dama kadararki gaba daya a tare dani" Daga wannan ta yanke wayar. Zare wayar daga kunnenta maamah tayi tana kallo. Wani irin mamaki da tsoro yana kamata,wacce irin yarinya ce wanannan?,wadda bata tsoro ko shakkar duk wani abu girman tsoron dake tattare dashi?. Gabanta yayi mummunar faduwa sanda ta tuna zancan idan taso za'a sanar da jana'izar fu'ad din a gobe. Ta motsa da wani irin hanzari ta miqe sai kuma ta koma ta zauna. Waye zata gayawa?,shi fu'ad din?,tace yakula da za'a iya kasheshi?,to waye zai kasheshin?,ya kuma zatayi masa bayani akan yadda akayi ta sani?,ya daina cin abinci?,wannan kuma shine burinta babba a yanzu ya karbi abinci daga hannunta don samun cikar burinta,ta yaya zata sanya idanu akan wani abu daban da zata shirya wanda zai sauka daga kan tsari da kuma muradinta?. Zuwaira ce ta fado mata rai,sai taji tana samun sassaucin tsoron da kuma firgicin da take ciki. Hannunta dukka biyun ta sanya ta dafe kanta. "Huda,ya kula da ita ya bata magani tasha?,who's she?" Abinda ta dinga maimaitawa kenan. Hudan da har yanzu take ganin tana buqatar therapy tana buqatar counselling akan mikin da nasir yayi mata.......yanzun kuma tana shirin sake fadawa wani abun na daban?,kanta da zuciyarta kuwa zasu iya dauka?,ya kamata ta ciyar da d'anta ta kowacce siga muradinta.....idan yaso in taga dama bayan ta mallakeshi ta yayyankashi ta cinye. Abu daya ta kasa jurewa ya kuma gaza barin zuciyarta huda,ta yaya zata ji muryarta?. Bata taba jin dauke wayoyin ya dameta ba irin yau,ta dinga jin kamar tayi hauka idan ta tuna ba wata sauran hanya da zata iya samun damar magana da huda. Sosai tayi qoqarin ganin amna bata gane komai akan fuskarta ba. Ta kama mata aikin sukaci gaba dayi,tana ci gaba da mata hira tana bata labarin fu'ad. Kwata kwata bata jinta ma ballantana ta fahimci abinda amna din ke fada,a haka suka kammala amna ta fito tabar mata kitchen din. Sosai ta zazzaga dukkan abinda ya kamata ta sake juya abinci ya koma ainihin launinsa. Ta tsaya kaman ko yaushe ta zubawa abincin idanu zuciyarta na wani yamutsawa,mafi rinjaye na zuciyarta tana jin kamar wani yanayi mara dadi,wani yanayi da yafi kama da rashin jin dadi?,rashin kyautatawa?,ko aikata abinda ba daidai ba?. Itama bata sani ba,bata taba zaton da hannunta zata iya ciyar da kowanne dan adam abinda bai kamata yacishi ba......saidai abu daya ta sani shine....itadin guba ce ga duk wanda yace zai kawowa innocent rayukan nan guda uku farmaki. Takun da taji dake alamta mata an shigo kitchen din shine abinda yayi bala'in razanata. Da sauri a kuma birkice ta daga kanta tana duban me shigowar. Zuwaira ce fuskarta da murmushi ta qaraso cikin girmamawa. "Afuwa,dama cewa nayi bari nazo naji ko akwai aikin da za'a kama miki?" Tayi maganar tana duban warmers din da a gaban idanunta tana labe sabreen din ta cika aikinta tsaf. Idanunta ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,sannan ta tattaro dukka qarfinta ta bude idonta akan zuwairan "Wannan shine kuskurenku na farko,bana buqatar ki sake shiga wani guri a cikin gidan nan ba tare da kin tsaya kin nemi izini ba an kuma baki" Kai ta rusunar "Ayi haquri bazai sake faruwa ba in sha Allahu" Bata iya amsa mata ba,sai kawai warmers din data mata nuni dasu "Ki kaisu kan dining" Tayi maganar tana dosar qofar fita a kitchen din,don sam bata da qwarin tsaiwa ci gaba da magana. Tana sanya qafafunta da zummar fita tana sako tata qafar abinda ya sanya suka kusa karo da juna,yatsun qafarta suna caki na sabreen haka gwiwarta saita tsaya cak bata ja baya ba bata kuma koma ba. Tsaiwa cak itama sabreen din tayi tana danjin qafarta na dan radadin kadan saboda qafafunta akwai alamun tana ajiye farce. Shirun da sabreen din taji ya sanyata daga kanta ta sauke dubanta akan laila. Tana tsaye cak ba alamun zata kauce mata ta bata hanya. Bisa dukkan alamunta tana jiran sabreen ne ta kauce mata,kota koma sai ita ta wuce. Cikin qasa da second biyu sabreen din taji wani abu ya saukar mata,wani abu me kama da izza da jin mallaka ya mamayeta. Ta lumshe idanunta sannan ta zubesu fes akan laila tana duban tsakiyar qwayar idanunta da wani irin kallo dake qure qarfin halin mutum. Da farko itama laila din ta zuba mata idanu,saidai a hankali wani kakkaifan abu ke ranqwafar da nata idanun. A hankali taji ta gaza jurewa,saita dauke dubanta daga kan sabreen din tana ja da baya,ba tare data sake dubanta ba ta rabata ta wuce a tsanake ba tare data sake duban sashen da take a tsaye ba. Da idanu tabi sabreen din har ta wuce,ta maido dubanta cikin kitchen din tana jin kamar yau karon farko ta tozarta......a karon farko taji wata 'ya mace tayi mata kwarjini,har kuma ta juyata ba tare data furta kowacce kalma daga bakinta ba. Hada ido sukayi da zuwaira,sai zuwairan ta tabe baki tana dauke kai. Cike take dama da lailan,cike kuma take da yadda maamah ta dinga jaddada mata ta girmama lailan,don gidan fu'ad a wajen lailan tamkar gidan mahaifinta yake,tammar kuma gidan yayanta da suke uwa daya uba daya yake. "Idan me guri yazo dai me tabarma nadeta yakeyi,nan din dai akwai macen data amsa sunan matar gidan,komai ayishi bisa takatsantsan". Sarai ta fahimci abinda zuwairan ke nufi,amma sai taga sam bata da lokacinta,don abinda sabreen tayi yafi tsaye mata a rai,yadda zaiyi handling nata. Da gaske komai na gidan yayi mata,da gaske zuwa yanzu tanaso ace itace mamallakiyar gidan. Ta cika gidan da izzarta da mulkinta da kuma ikonta kwatankwacin hajja,tako ina ta zama ME MULKIN gidan. Samun amna tayi tana shirin tafiya. "Har me?" Ta fada cikin nuna kulawa. Murmushi ta saki "Driverna na aje adda tun dazun fa,daga cewa anni zanzo na miki sannu da zuwa". Fararen idanunta da a yau take jinsu wani iri ta kada,bata da energy din dogon magana. Closet dinta ta bude kawai tayita fiddo abinda take ganin ya kamata ta bawa amna. Ta hada abubuwa cikin qaramar jaka me kyau da daukan hankali. Ido amna ta fiddo tana nuna tsananin murna da mamaki "Duka adda?" Ta fada da murmushi. Abun ya burge sabreen sosai,yadda amna din ta nuna,duk kuwa da cewa tasan tafi qarfin duka abinda zata bata din. Fitowar zuwaira da laila daga kitchen din ya danja hankalin amna dake qoqarin ficewa,ta bisu da kallo kawai kafin ta juya a hankali ta fara takawa tana fita daga falon. "Sai haquri ranki ya dade....laila kenan..... D'iyar hajja harira.....hajja harira 'yar majalissar zartarwa hajiya mariya maamah". A badini kyakkyawan masauki maganar zuwaira ta samu,hajja hariran da sukayi tattaki har cikin gidansu suka kai qudurin aurota don su cimma buqatarsu?,ta yaya zata manta wadannan fuskokin,ranar,dama abinda ya faru a ranar....har maamah din tana da qarfin halin ajiye budurwa irin wannan a gidan d'an data haifa?,wanne irin kwado ne wannan?,budurwar da babu wata alaqa tsakaninsu face ta zallar qawancen dake tsakaninsu?,a tsarin abota da mu'amala da zata fishshi dan adam tasu bata kan ko guda daya. Kai ta jinjina,information din ya mata kyau da ma'ana,amma kuma batajin zata sakewa zuwaira ko ta nuna jin dadin hakan. "Ya kamata ki dinga tsaiwa a iyakokinki kawai" Abinda tace da ita kenan tana takawa zuwa hallway dinta don komawa dakinta,duk da har yanzu ba wani cikakkiyar nutsuwa ko sukunin data samu daga uban tunanin dake addabarta,gefe guda kuma tana cike da fata da fargabar sanya abincin a bakinsa ya zarce zuwa cikinsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _ZAFAFABIYAR_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 33 _Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_ 33 ★"ma sha Allah,sannunta da qoqari" Anni ta fada sanda ta gama ganin kayan da amna ta kawo wanda sabreen ta bata. "Tana da kirki anni......amma sai nake ganin hamma me irin halinsa ya dauko,she's so quite,batason hayaniya da yawa,bata fiya bada amsa ba ko magana,tafi yawan murmushi kawai". Murmushi anni ta sauke,har zuciyarta tana sake jin yarinyar tayi mata,a duk wani lokaci da maganarta zata tashi tana sake jin sabreen ta kwanta mata ne. "Ai dama sai hali yazo daya ake iya zama ko?,Allah ya qara hada hankulansu......yauwa farouq yayi nemanki kuwa sanda kika fita......naji kaman yana maganar zaku abuja passport dinki yayi expired,za'a sake miki wani". Idanu amna ta fiddo sannan ta qanqame anni "Anni hala Lokacin tafiya ya kusa?". Dan tureta kadan tayi daga jikinta "Gashi kuwa kin gani keda tafiye tafiye basa isarki" Dariyar jin dadi ta qyalqyale dashi. "Amna wannan tafiyan daban yake a rayuwata Allah,ba wani trip da yakaimin wannan dadi....whole family fa anni.....wannan karan kuma abun zaifimin dadi saboda nima na samu partner addana,adda sabreen,na daina maqalewa su ya saddiq suna wulaqantani,wannan karon tafiyar zai zama na musamman" Tayi.maganar with full excitement. Da kallo kawai amna ta bita kafin ta saki murmushi,ita kanta tasan tafiyar zata qara dadi musamman da idanunta zasu dinga gane mata fuad dinta da iyalinsa a gefe,cikon mafarkinta kenan "Anni bari naje na sameshi" Ta fada tana daga yatsunta gami da lissafa watan da tafiyar tasu zata kama "Yes" Ta furta tana jin farinciki yana lullubeta,saita cilla da sauri zata fita tana cewa "Dis time har abba fa sai na karbi kudin tsaraba a hannunshi,komai bibbiyu zan dinga siya nida addana" "Kunfi kusa ai" Anni ta bata amsa. Dakatawa daga fitar da anni taga amna tayi shi ya sanyata daga kai tana dubanta zuciyarta cike da tambaya. A sanyaye taga amna din ta dawo tana zama gefanta "Lafiyarki ke kuma?" Ta tambayeta tana nazartarta da kyau "Wani abu na gani anni a gidan hamma". Jin an ambaci fu'ad din ya sanyata tattara hankalinta akanta "Me kenan?" Ta amsawa amnan cikin zuciyarta tana fatan ba wata matsala bace a tsakaninsu. "Anni.....me aikin gidan maamah na gani,ita da wata budurwa......bansan budurwar ba amma tana kama da wannan qawar maamah din aminiyarta dinnan....." ".....hajja harira" Anni ta samu kanta da fada ba tare data shirya ba "Eh ita" Ajiyar zuciya anni ta fesar "To shine me amna?" Ta furta cikin hikima. Tun asalin tarbiyya anni irin matannan ne da basa bari yaro yana kawo musu hira ko maganar wani guri. Qasa amna tayi da idonta "Ba komai,kawai anni ji nayi jikina bai aminta dasu ba,daga yanayinsu fa anni kamar a gidan zasu kwana fa,qilan ma komawa gidan sukayi Allah anni". Ta fada tana bata rai. Da kallo tabi amnan,amna din ba yarinya ce qanqanuwa har can can ba,kome ake ciki ko yake faruwa tabbas dole tana gani tana kuma fahimta. "Hammanku majibancin lamura da jama'a ne,bazai zama abun mamaki ba idan anga sabbi ko baqin fuska a gidansa ba,kedai kici gaba da taya dukka 'yan uwanki da addu'a". Kai kawai amna ta gyada ba tare data samu cikakkiyar gamsuwa da bayanin anni ba,ta miqe tana fita daga dakin kamar yadda tayi niyya da farko. Fitar amna dukka sai hankalinta ya dawo jikinta,sam sam taji bata gamsu da wanzuwar zuwaira da waccar yarinyar a gidan ba. Tasan wacece maamah,tasan kuma dukkanin wanda ya rabu da ita yaya dabi'arsa zata iya kasancewa. Indai da wata manufa ko wani qullin daban aran maamah din,muddin tana raye ba zata taba bari haqarta ta cimma ruwa ba. Koda ta dauke idanu akan abubuwa da yawa,koda tayi kawaici akan abubuwa masu yawa....amma a nan ba zata bari ba,ba zata bari tabi fu'ad har rayuwa cikin gidansa ta ruguzata ba. Saita jawo wayarta tana qoqarin danna kiran. *SABREEN* Batasan adadin sau nawa ta leqa dining din ba da zummar ganin ko ta samu nasara ya taba kayan abincin?. Saidai a duk gewayen da zatayi bataga wani alamun taba komai ba cikin kayan dake danqare a table din ba. Ba iya yaci abincin bane kawai damuwarta ba aah......tanaso tayi amfani da wannan damar ta karbi wayarta a hannunsa,tanaso duk yadda za'a yi ta samu cikakken bayanin yadda su hudan suka koma qarqashin kulawa da mulkin maamah. Abun yana tsananin daure mata kai......ta yarda da momma bahijja....ta kumayi imanin haka siddan ba zata bari haka ta faru ba,duk dadai ma batasan ainihin wacece maamah din ba. Sam bata sako kawu rufai a ciki,shikam tasan ko ya fita sanin wacece mariya to zai aikata fiye da hakan ma. Zuwa sha daya na dare haqurinta ya gaza,ta miqe da wani irin kaiwa maqurar haquri tana yafa mayafinta saman doguwar rigar jikinta ba tare data buqaci dankwali ba ta sanya slippers dinta tana bude qofar dakin ta fice. Kamar magen dake kwanton farautar kamun bera haka ta dinga tafiya a hankali tana durfafar stair case din dake facing dinta. Duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,amma kuma tuna huda nadra da haneefa kadai ke qara mata qwarin gwiwa. Tana jin a kansu zata iya komai,zata kuma fuskanta da tunkarar komai da kowa. Cak ta tsaya a stairs din farko tana jin kaman wanda ke kusa sosai da ita idan ya qurawa qirjinta idanu zai iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa ma. "Shi waye?,mutum ne kamar kowa,mutum ne kamar ni,bashi da wuta bashi da aljanna,bai isa kuma ya yankani ya cinye namana ba" Ta gayawa kanta da kanta murya can qasa qasa dukka tana zaton BUGUN ZUCIYARTA zai daidaita. Aqalla ta tsaya jiran mintuna kusan goma amma still ba abinda ya canza,sai kawai ta runtse idanunta ta kama makarin stairs din ta fara haurawa saman da wani irin confidence da batasan daga inda ta aro shi ba. Idan ba jikinta da hancinta ne ya mata qarya ba,to tabbas atmosphere da weather na wajen daban yake dana kowanne bangare na gidan. Wani irin lullumsan yanayi da wani irin kebantaccen qamshi da bata taba jin makamancinsa ba. Bata taba lura da cewa shimfidadden carpet bane kan stairs din sai a yanzun da qafafunta ke barazanar nutsewa a cikinsa. Bayan qafafunta sun nutse din kuma wani irin sassanyan yanayi tafukan qafarta ke riska a can cikin carpet din. Duk yadda taso jure qauyancinta amma abun yafi qarfinta,dole ta dinga bin carpet din da kallo har zuwa sanda ta riski wata pivot door wadda gefe da gefanta duka glass ne da bazaka iya hango ainihin parlor din ba,yayin da daga tsakiya ta kasance ta gogagen katako da aka yima design na zamani wanda ya maidata smart door. Tun daga zubin qofar tasan wajene na musamman kuma kebantacce,ta bangare guda kuma taji dadin samun qofar a bude,banda haka da sai tayi tsaiwar da qofar zata gama tantance wace kafin ta bata daman shiga parlor din. Mutum ne shi me wani irin jiki wanda baya qaunar zafi tun asali,saidai duk da hakan tsananin kare lafiyarsa ya sanya bai fiya kwararawa kansa A.c ba. Duk wanda ya sanshi ya sanshi da wannan dabi'ar na kaucewa abubuwa masu sanyi ciki kuwa harda ac din. Zaune yake saman wata qawatacciyar minotti sofa qwaya biyu dake bayan qwatattun Belgium sofas din da aka yiwa yalwataccen parlor din ado masu wani irin design me daukan hankali. Daga bayan Belgium sofas din aka yi wani muhalli na daban da aka zuba minotti sofas guda biyu wanda suke bashi daman kashingida ko miqe qafafunsa a duk sanda yaso. Dogayen qafafunsa na miqe saman sofa din,yayin da night shirt dinsa ke ajiye a gefe,daga shi sai gajeran wandon rigar wanda iyakacinsa cinyoyinsa. Hakan ya bayyana zallar halittar fararen cinyoyinsa dake lullube da baqa sidik din gargasa. Madaidaiciyar Ac ke kadawa cikin dakin,wadda ba lallai yanayin sanyin ya sanya ka fahimci itace ba saboda glass door din dake hannun hagu na falon da yake a bude,tatacciya iska me kyau dake tasowa daga jikin tsirran da aka qawata wajen dasu tana busowa zuwa cikin falon. Tattacciyar iskar data sanya masa kasala da mutuwar jiki,duk karsashin aikin da yakeyi ya soma raguwa. Turo qofar da akayi shi ya sanyashi dauke idanunsa daga karanta saqon da William ya tura masa ta email da suke buqatar ya duba da kyau ya karanta ya kuma sanya hannu. Fes yake ganin fuskarta wadda ke tsaye daga bakin qofar,fuskar data bayyana tsakanin lullubin mayafinta wanda yadan zame baya kadan ya bawa kwantacciyar sumar dake gaban goshinta daman bayyana sosai. Fararen idanunta da suke da wani irin haske ta zube a kansa wani abu na dukan zuciyarta saboda yadda ta sameshi. Ba wani abu da gajeran wandon jikinsa ya suturta sai qasan cibiyarsa zuwa cinyarsa,don bai samu daman qarasawa gwiwarsa bama sam. Ginannen jikin nasa daya samu kulawa ta kowanne fanni,motsa jiki,tsananin tsafta da kuma cima me kyau. Kwantaccen gashin dake cike da qirjinsa shi ya zamewa faffadan qirijinsa tamkar adon baqin abu bisa farin yanki ko farar takarda. Wani irin kwantaccen gashi daya shirya kansa da wani irin siririn layi har zuwa cibiyarsa ya zarce har qasa. Har cikin jikinta taji rudewa sosai,don wani abune da tsahon rayuwarta bata taba gani ba,hakazalika bata taba hasashen zata shigo ta sameshi a haka ba. Cikin zafin nama ta juya da niyyar komawa inda ta fito,don batajin zata iya ci gaba da daurewa kallon wannan halittar tasa. Da nasa salon hanzarin da kuma son qurewa rashin kunyarta tare da qoqarin fuskantar wani abu daga gareta ya dauki remote na qofan ya dannan close,take ta rufe kanta da wata irin gaggawa kamar qiftawar ido. Cak ta tsaya zuciyarta na bugawa sosai,tsoro yanaso ya kamata Amma kuma wannan dakakkiyar zuciyar ta taso mata,taji a ranta cewa idanma ta juya ta fita ta nuna masa ta damu dashi kenan ta kuma damu da wanzuwarsa a haka. Nasa idanun ya janye daga kanta yana hade ransa tsam waje daya. Duk da kallon data masa bai wuce na second biyar ba amma ya fahimci lallai ta qarewa jikinsa kallo. Hannu ya miqa gefansa ya jawo night shirt dinsa ya zura,sai ya koma ya jingina da fuskar minotti sofa din yana ci gaba scrolling saqon yana dubawa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 34 _Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_ 34 Minti daya biyu uku har zuwa biyar bataji motsin komai ba,wannan ya sanya tayi tsammanin yabar falon ne,don haka ta juyo a hankali tana sake zube idanunta a wajen da yake. Haushi takaici da bacin rai suka hadu suka lullubeta ganin aikinsa yake hankali kwance,sai ta gyara tsaiwarta sosai tana fuskantarsa ganin ya lullube wannan faffadan qirjin nasa,wannan ya dan rage mata kaifin abinda takeji,duk da cewa cinyoyinsa dake a waje nason sakata a razani da tsoro. Rasa ta yadda zatayi calling attention dinsa tayi,sai ta danyi gyaran murya kadan cikin qufula da fusata. Minti guda kaman baisan tana wajen ba kafin ya motsa,ya daga kansa da idanunsa daga kan hasken system din yana zubesu a kanta da wani irin kallo na qurilla. Karo na farko yadda ya tsareta da ido taji kaman yanaso yayi mata nauyi,jajayen lips dinsa hasken fararen qwayar idanunsa wani abu ne da bata taba gani wajen wani d'a namiji ba sai a kansa,akan nasa ma a yau data masa kallo itama nakai tsaye. "Wayoyina nazo karba saboda ina da buqatarsu....... Akwai mutane masu muhimmanci a rayuwata da nake da buqatar na dinga magana dasu" Ta fada tana tsuke girarta da kyau tana kuma tura dan qaramin bakinta gaba wanda sam batasan ma tanayi ba,saboda zuciyarta cike take da haushi. A hankali ya sauke idanunsa zuwa saman qaramin bakin nata data tattara lips dinta duka ta turasu gaba. Wasu irin siraran lips da sai kayi tsammanin jambaki ta shafa musu. Tsigar jikinsa ta zuba kadan saboda bayyanar daya daga cikin abinda ke burgeshi a jikin mace yake kuma lissafin ya sameshi kenan,wato cute lips masu nau'in light pink ko red me haske irin nasa. "A hakar kamar cikakkiyar mace" Ya fada qasan ransa yana jan tsakin da baisan ma ya fito sarari ba. A duk lokacin da zai kalleta sake raina shekarunta yakeyi,hakanan a duk sanda zaya kalletan sai mamaki ya sake cikashi game da yadda ta samu cikakkiyar shaida da certificate din zama KARUWA. shi kam gaba daya ma baisan me yahau kan mazajen dake mu'amala da ita ba,a bisa qa'ida da yanayin halittarsa ta masa yarinta da yawa. Yanason macen daya tabbatar zata iya dauke lalurarsa komai girmanta,ire iren sabreen din guda goma yana ganin yafi qarfinsu nesa ba kusa ba,baima san abinda mazajen da ta dinga tatsewa me suke tsammanin samu haka daga gareta ba da har ta samu tasirin gusar musu da hankali. "Labari kike bani?.....ko tambaya kike?,ko daukan excuse?" Yayi maganar a nutse yana dage mata dukka girarsa guda biyun bayan ya dora qafarsa daya saman daya,ya kuma yi relaxing jikin makarin sofa din. Duk sai ta ji ya muzantata,akanme zai dinga mata tambaya akan abinda ya gama fahimtar inda ta dosa?. Tsaiwarta tadan gyara tanason hana kanta jin nauyin idanuwanta. "Amma dai cikin zamanmu ba sharadin tabamin waya.....wayata sirrina ne,bana tunanin akwai abinda ya shafeka a ciki" Ido ya zuba mata kamar bazaiyi magana ba,yanaso yaci gaba da karantar bayan karatun da yayi mata na binciken da yayi a kanta. Ya fuskanci akwai burbishi da tasirin rashin kunya tattare da ita. Yarinyar da ko saddiq ba sa'anta bane ballanta musaddiq ko farouq.....amma tana da zarrar tsaiwa ta fadi mishi magana yadda takeso. Wannan wani abune da ba wata diya mace data iya fuskantarsa dashi....kai koda dan uwansa namiji yana matuqar shakkar hakan. Uwa uba akwai tasiri na girman kai da rashin tsoro tare da ita,yanaso yaga ya zatayi handling wadannan attitude guda biyun da wadannan shekarun nata?. Kaman zaiyi magana sai wayarsa ta dauki tsuwwa,manhajar da yakanyi amfani da ita wasu lokuta da zata gaya masa cikakken sunan wanda ke kiransa koda bashi da number wayarsa ta karanto masa sunan fareeda Khaleed mustapha. Kusan a tare suka kalli wayar shi da ita,a nutse ya cire hannunsa ya kashe wayar gaba daya bayan yayi rejecting call din,amfanin manhajar kenan ta gaya masa wanda ke kira,basai ya saki aikinsa ya dauka ba ya zamana me kira baida wani muhimmanci har haka,saboda mutum ne shi mai darajta lokaci. Agogo ya kalla sannan a nutse ya maida dubanshi kanta bayan ya sauke qafafunsa duka qasa,abinda ya sanyata sake kame ganinta gudun kada idanun nata su gano mata abinda yafi qarfinta,don ta lura kamar bayajin nauyin zamansa a haka. "Kin tsallake iyakarki,kin shigomin part ba tare da Neman izini ko sallama ba......and kin tsaya kina ban labari akan abinda bai shafeni ba.......wai...." Ya fada yana tsuke fuskarsa sosai gami da maida qafafunsa saman table sabanin dazu dake kan sofa "Meye amfanin zamanki a gidan nan?.. Kina zaton na kawoki ne don na killaceki waje daya kiji dadin rayuwa?,ki samu tsaro kiji dadin ci gaba da qwamushe asusun mutane?,ko na kawoki ne don kizo kicinye min abinci na?,ko kin dauka na daukoki ne don wani abu daban?,thought ma dai nasan ba zaki taba mafarkin wannan shirmen ne wato SO ya sanya na kawoki ba....." Wani radadi takeji yana taba zuciyarta,abu daya da zata iya yabonsa akai takuma san ya qware akai shine baqar magana kamar tsohon mahauci,idaninta da suka fara canza launi takai kansa,ya gyara zamanshi sosai yana hade yatsun hannunsa guri daya yana maida dubansa kanta. "Kina magana akan sharadi yarjejeniya da sauransu......for now ma yakamata kisan me ya shigo dake cikin gidan nan.......Initially don ki gane me ake kira da respect........attitude dinki su koma irin na kowanne mutum.....secondly kuma..........ki maida min dukka kudina da kika debe.....don ban nema kudina saboda mata irinku su mora ba......" Wani kallo harrr ta bishi dashi,sai ya daga dukka girarsa sama "Yes......duk wanda zayaci kudina to yana da cikakkiyar hujjar da zata bashi daman cin in a polite way.......da naso a ranar da kika diba a ranar zan saka a kawomin ke har nan..... " Idanu ta zubawa Kyakkywar fuskarsa yadda yake bayani a nutse hankalinsa kwance. Ashe shi din ma mayen kudi ne?,kallon kitse akewa rogo?. Eh tasan tabbas ta cire kudade masu nauyi da yawan da ita kanta sai data girgiza,amma kuma bata dauka har xai sanya qulafucinsa akan kudin daya tsere musu ba har haka. "Baki da hanyar da zaki biya Muhammad jadda kudinsa?......zan taimakeki tsill dai don kada kiyi prison a banza.........daga yau ya daukeki aikin shara da gyara masa bedroom da kuma wanke masa toilet dinsa......zan biyaki kaman yadda yake biyan kowanni ma'aikaci dame aiki a qasansa.......but.....i will not pay you anything.......zanyi writing down komai har ki kammala biyana" Yakai qarshen maganar gaskiyar abinda yake fada tana fita daga cikin idanunsa. Soma tattare takardunsa yayi "You can go" Ya furta cikin halin ko in kula. A lokacin tana jin kamar ta qarasa gabansa ta amayar masa da dukka abinda ke zuciyarta,tana jin kamar ta isa gabansa ta nuna masa wace real sabreen,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana kwabarta tare da gaya mata any mistake idan tayi itace a ciki. "Ya soma cin abincinki shine abinda ya kamata ki damu dashi bawai maganganunsa ba......if kikayi abinda zai sake sanya masa shakkan sakewa da gidan dukka ayyukanki zasu koma baya.... Sisters dinki zasu ci gaba da zama qarqashin hadari" Maganganun da suka fito daga qasan zuciyarta kenan,suka kuma sanyata tsaiwa cak daga takun data fara don matsawa zuwa gareshi. Remote din ya dauka ya bude mata qofar yana ci gaba da abinda yakeyi "Hey" Taji ya sake fada sanda ta sanya qafarta daya a waje,saita dakata ba tare data waiwayo ba "Mind you....banason qazanta,i don't want it,ki kiyaye". Da sassarfa da kuma hanzari ta soma sauka saga stairs din har kamar zata fadi. Kuka ne yakeson qwace mata amma bataso yaji ko ya gani,don ta yiwa kanta alqawari ba zata taba bari yasan lagonta ba. Baqincikinta yadda ya fadi mata dukka maganar da ke ransa,nata zuciyar da ruhi cike maqil da maganganu amma TARKON da take ciki yasa bazaiyuwu ta fiddasu ba. *_Washegari_* Tun shida na safe zuwaira ke kai kawo tsakanin shiyyarsu zuwa ainihin falon da kuma kitchen din. Jin shuru ba alamun tashi sai ta fara aikin gyaran dukka falukan da kuma kitchen din. Duk wani motsi da zataji hankalinta yana kai,tanaso ta samu cikakken bayani akan komai yadda zata zama cikakkiyar informer na maamah. Tanason bata duk kalar bayanan da takeso don tana son ta doke matsayin hajja harira wajen maamah. Ta kowacce fuska da kuma yanayi tanason ta taka matsayin da zata zama aljihun daman maamah a sanda burin maamah ya cika din. Itama tata zuciyar da ruhin cike suke da nata kalar burin da take fatan zuwan ranar wanzuwarsa. Wani irin qarfi ta sanya ta danne zuciyarta ta fito shirya masa breakfast,duk da asara akayi daren jiya na dukka girkin da sukayi,sai tashi tayi tsakiyan dare ta kwashesu ta zuba a inda ta saba zubawa. Yau din cikakkiyar shiga tayi,ta rufe jikinta sosai tunda ta fahimci ba ita kadai bace cikin gidan. Idanunta duka sunyi nauyi saboda kuka da rashin cikakken bacci. A hankali take ratsa falon hankalinta yana qofar kitchen din. "Barka da fitowa ranki shi dade" Taso ta tsorata kadan,don gaba daya ta manta da wata baba zuwaira a gidan. Ta sauke dubanta a kanta sanda zuwaira ke qare mata kallon qwaqwaf. A jiya batayi cikakken bacci ba sai data gama fahimtar inda kowannensu yake kwana ita dashi. A gaban idanunta ta sauko daga samanshi a gaggauce cikin bacin rai ta fada dakinta,abincin dataxo ta kwashe kuma baici ba,a daren itama bata kwanta ba ta sharhantawa maamah komai. "Ya zama dole na matsa mata lamba ta yaudaroshi ya zama a tafin hannunta" Abinda maamah ta furta kenan,tsoron taurin kai irin nasa yana damunta. Tasan halinsa da kafiya akan abinda baida niyya baiyi masa ba......amma zata sake yin amfani da qarfinta a matsayinta na uwa karo na biyu. "Barka kade" Ta amsa mata a taqaice ba tare data sake dubanta ba tayi kitchen "Nace ba,ba abinda za'ayi kuma?" "Babu....kije saina nemeki" Ta amsa mata a taqaice,don kwata kwata batason doguwar magana gaba daya. Da kallo zuwaira ta bita har ta shige kitchen din,sai ta saki murmushi tana ji a ranta ya kamata taci tudu biyu fa......bangaren maamah din da bangaren yarinyar.....abinda ta kwana kenan tana tunani akai,gwara tayi amfani da damarta,ta yadda koda gaba kome ya faru zai zame mata ribar qafa,salon maganar nan da hausawa kance idan tayi ruwa rijiya,idan kuma batayi ba masai. Dukka 4glass stove gas din ta kunna kowanne ta dora abu akai. Da zafi zafinta ta saka 'yar basirarta ta kammale breakfast din cikin taqaitaccen lokaci,ta gyara inda zata gyara ta fara daukan luxury Warmers din tana jerasu saman dining. Cikin ginshira da wani irin tsanaki gami da nutsuwa yake saukowa daga saman stairs din,kunnensa manne da Bluetooth yana amsa waya,lokaci guda kuma yana qoqarin gyara tie dinsa. Hankalinta yayi nisa sosai cikin duniyar tunani,fargaba kuma na sake cikata kamar kullum na kada a sake tafka asara yaqi cin komai kamar kullum,asarar da take sake kusantata da faduwarta da samun matsala a rayuwarta. Tun daga nesan idanunshi suna kanta,duk da baiga fuskarta ba amma ya gane itace. Sai ya dauke dubansa yana haurawa zuwa steps din ya wuce zuwa kitchen. Qamshinsa kadai shi ya ankarar da ita,ta daga kanta tana bin bayansa da kallo gabanta yana wani irin faduwa,cikin mutuwar jiki ta ajjiye spoons din hannunta taja kujera daya tana jiran fitowarsa cike da hope. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 35 _Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya auri nana fadima,sai manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin sadakinta),sai sayyadina Aliyyu yace "ba komai a wajena" Sai manzan Allah S A W yace "ina sulkenka?"_ 35 Coffee ya hadawa kansa,yayi tsaye jikin kitchen cabinet yana kurba a hankali. Kwanakin nan duka baici wani abincin arziqi ba,sai kame kame da cin abincin waje,wanda yasan totally isn't safe musamman ga mutum sannanne irinsa da ta kowacce fuska cikin barazana da qoqarin kawo musu hari ake ta duk wata siririyar kafa da za'a samu dama. Iya lamarin maamah da yarinyar ya isa zama izina a gareshi,abu a cikin gidan.... Amma kuma farautarka akeyi. Sai yaji gaba daya coffee din ya fice masa a kai,yana qaramin tsaki ya ajiye cup din,ya ciri paper towel ya goge lips dinsa duk da ba baci sukayi ba ya fara takawa a nutse yana fita a kitchen din. Sau daya tak ya kalleta ya dauke kansa,ya taka a nutse yana isa gabanta. Tsaiwarsa ta sanyata daga kanta,akwai inches tsakaninsu amma tana jin kamar ba wani gap daya rage musu. Idanunsa saman lips din nan nata da suke very smooth,ba digon komai akai sai ainihin color dinsa. Smart key na qofarsa ya dora saman table din,ya kuma harbasa gabanta. Ya motsa labbansa zaice wani abu wayarsa ta fara fidda wani tattausan ring me kama da sarewa,irin ring din da zai iya haifarwa da mutum karyewar zuciya musamman ga masu karyayyiyar zuciyar. Fareeda Khaleed mustapha sunan wanda ke yunqurin samun sadarwa dashi kenan aka sanar mishi. Maimaita kiran sunan me kiran wayar ta soma yi kamar ba zata dakata ba. Saman kunnuwanta sunan ya sauka,irin sunan da taji a wancan daren. Iska ya furzar daga bakinsa yana sauke numfashi,sannan yana qaramin tsaki gami da ciro wayar da wani dan zafin nama yana yanke kiran ya jefata aljihun yana sake sakin tsakin. Baki ta tabe qasa qasa tana kauda fuskarta wani sashen,can qasan zuciyarta kuwa gulma take,tasan za'a rina.....koda dukka jikinta kunnuwa ne ba zata taba yarda mutum kamar muhammad jadda bashi da kowa ba.....mutum kamar muhammad jadda baida ajiyayyun 'yammata da yake debe kewarsa dasu ba......ba zata yiwa kanta qarya ba,idan tace mummuna ne ko bai hadu ba tasan tabbas wannan din gundumemiyar qarya ce ta zabgawa kanta......to kuwa tasan zai wahala a rasashi da wasu halaye da sukayi kama da wannan. A iya rayuwarta.....a iya mazan data hadu dasu harda wadanda basu kaishi bama,masu kudi sosai matasa masu jini a jika,taga dabi'u kala daban daban da halayen da bata ma tsammaci ganinsu ba,yaga yadda matan aurensu suke ba komai ba a wajensu......taga irin qalubalen da shuke fuskanta a tattare dasu....matasan cikinsu harma da masu yawaitar shekaru,wannan abun ya sake cire mata sha'awar abubuwan nan guda biyu a ranta SOYAYYA da kuma AURE. Gadai guda daya nan ya cimmata,saidai tana da yaqinin ba zata bari yayi galaba a kanta ba,yayin da take bawa kanta tabbacin tafi qarfin wata soyayya taci galaba a kanta,don idan ka dauke soyayyar qannenta bata taba tsintar kanta cikin soyayyar komai ba,wannan shine yake sake bata yaqini tabbaci da nutsuwan ba zata taba yin soyayya ba....saidai ita a sota (Nace uhmmm....maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta). Idanunsa ya maida saman fuskarta,a nutse ya fara magana kamar wanda ya hada jini da gidan sarauta. "You can start your work today.......but......ya kamata ki sani,nasan komai da yake every single room......sannan nasan place dinshi,so do your own business......kiyi iya abinda akace kiyi" Daga haka sai ya juya a nutse don sauka a wajen,saidai kuma muryar da yaji tana gaidashi ya sanyashi tsaiwa yana juyawa wajen. Zuwaira ce a durqushe a wajen,da yanayin da yake tabbatar masa ba yanzu yanzu ta shigo ba. Sunkuyar da kanta tayi sanda ya zube mata kaifafan idanun nan nasa,yayi mata wani irin kwarjini da bata taba ganinsa idanun kowanne mahaluki ba sai a kansa. Wannan kwarjinin nasa ya sanya suke qauracew waje duk sanda ya shigo gaida maamah. Sosai goshinta ya soma tsatstsafo da gumi,tana ganin kamar a iya kallonsa kadai zai iya bankado komai ya kuma fallasashi. "Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye ba wani wasa ko sassauci a muryarsa,abinda ya sanya zuwaira ta ida rudewa,ga turancin daya jefeta dashi wanda ya saka a duhu "Eh....na'ammmm.....eh" "Wacece ke?" Ya maida mata tambayar da hausa. Caraf ta kama maganar tasa "Nice zuwaira.....zuwaira ce,me aikin da hajiya maamah ta aiko don taya uwargida sabgogi da hidimomin gida". Ta qarashe fada tana daddafe hannuwanta a qasa,saboda ji tayi kamar zata fadi daga tsugunnen. Hannayensa kawai ya zube a aljihun wandonsa yana ci gaba da kallonta,yana kuma son ganin fuskarta sosai. Duk wani daya rabi maamah yana da nashi question mark din a wajensa.....duk wani wanda maamah zatayi qoqarin hada connection tsakaninsa dashi baida aminci ko nutsuwa kwata kwata dashi,don haka yake sake shawarwarin qarawa musaddiq kwanakin zamansa a qasar da ya aikeshi ba tare da wani qwaqwaran dalili ko kuma buqatar hakan ba. Hannayensa nasa ya sauke ya soma takawa yana sauka daga wajen,zuwa sannan qiris ya ragewa zuwaira ta saki fitsari a wando. "Kada na sake ganin gilmawarki cikin gidan nan indai ina nan......duk ranar kuma da kikayi sake hakan ya faru.....ki fara hada kayanki na barin gidan nan....basai nace ba" "In sha Allahu ranka ya dade,tuba nake" Ta fada dukka jikinta yana rawa. Daga ita har sabreen ba wanda yacewa da dan uwansa komai. Kusan minti biyar da fitarsa sannan ta tattara qarfinta ta miqe tana sake hawa steps din dining da sabreen ke zaune akai. Fuskarta qunshe da munafukin murmushin nan ta soma gaidata "Barka da asuba ranki ya dade.....ashe har kin gama aikin?,ba zaki jira nazo ba?,hidimar ai sai tayi miki yawa,da sai na rage miki ai.....iyaka idan na gama abincin ki bada kalar maganin da za'a zuba a ciki......kedin abar tausayi ce ranki ya dade,kullum addu'ata da fatana ki kubuta daga hannun hajiya mariya lafiya" Zuwaira tayi maganar cikin matuqar sanyin muryar.....tsantsar alhini da kuma nuna damuwa. Tunda zuwaira ke maganganun nan a jejjere sabreen bata daga kai ta kalleta ba sai da tazo gabar qarshen maganar tata. Kalmar tausayi data furta a maganar nata yaja hankalin sabreen ya kuma tsaye mata a rai. Sosai ta zubawa zuwaira idanu tana son tantance gaskiyar abinda ta fada,saidai kuma abun mamaki haka kawai sai taji ta kasa gamsuwa da ita. Boyayyen numfashi ta sauke,sannan ta tattara hankalinta a kanta tana hade ranta tsaf "Wannan duka ba huruminki bane.....kiyi abinda ya cancanci kiyi kawai" Sai ta miqe daga saman kujerar tana niyyar tafiya. Da sauri zuwairan ba tare da ta ji ciwon tsaidata a wata iyaka da tayi ba tace "To ranki ya dade abincin fa?,yauma saidai a zubda?" "Idan kina da buqatar ci kya iya ci ai" Ta amsa mata da gatse tana sauka daga step din idanunta yana sauka kan laila dake shigowa parlor din. Sanye take da robber gown wadda tabi kowanne shape na jikinta ta lafe mata. Fuskar nan fes da kwalliya zaka rantse ba safiya bane ba. Ba komai a kanta sai wani qaramin bandana da bai rufe komai a gashin kanta ba. Wani mahaukacin tashin qamshi jikinta keyi,wanda turaren turare ne na musamman da aka tanada saboda wani mutum na daban. Duk da fuska ko kuma jikinta ba wata kwalliya.....amma haka kawai ta fusgi hankalinta. Sassanyan kyan nan nata da baya buqatar kwalliya ko wani abu makamancin haka yana nan shimgide saman fuskarta. Haka kawai taji ta muzanta duk da kwalliyar dake jikinta,amma duk da haka sai taji ta raina kanta. Tashin farko wasu kalmomi na hajja suka dawo mata fes cikin kwanya suka qara mata azama da qwarin gwiwa. Muhammad jadda kawai take da buqatar gani,don haka taci gaba da shigowa falon tana jin izza tare da fatan ko yaya ta gwadawa sabreen wani abu da zai sosa ranta. Kallo daya ta yiwa lailan ta watsar da ganinta a wajen,taci gaba da wucewa ciki ba tare data damu da kallon qurillar da laila ke mata ba. Ita sam bata ma dauketa a sunan damuwarta ba,damuwarta ta tsaya ne kan yadda yake neman maidata boyi boyin qarfi da yaji. Ta share masa sassa ta hada da wankin bandakinsa dama underwears dinsa,tana jin koda sama da qasa zasu hade ba zatayi wannan aikin ba. Lumshe idanunta tayi tana qara jin takaici yana cikata. Bashi da masaniyar hatta da girkin da take masa dole ce ta sanya take masa ba?,har wani qyashi da baqinciki ke rufeta gami da kasalar bacin rai duk sanda ta tsinci kanta dumu dumu a kitchen tana hidimar dafa masa abinci. Dakinta kawai ta wuce bayan ta saqale masa key dinsa jikin qofarsa,tana fatan ya dawo ya samu sassansa da muqullansa a inda ya barsu. Dining din laila ta wuce kai tsaye tana wani taku kai kace itace matar gidan,ranta ya cika maqil da kishi da hassadar sabreen din. Ko daga nesa ka hangosu sabreen din ta fita quruciya.......amma miskilancin yarinyar da shegen girman kanta mamaki yake bata. Bata taba mata kallo biyu ba....kai zata ma iya rantsewa sau daya ta mata nutsasten kallon cikin idanu Randa taso blocking mata hanya. So take ko yaya taga wutar kishinta a idanunta,to amma kullum suka hadu tana yin kamar babu aka kawo gidan aka ajiye ba dan adam ba. "Ma aka dafa?" Ta tambayi zuwaira Kai tsaye tana latsa wayarta sanda zuwaira ta kusa gama kwashe warmers din. "Sai yanzu Allah yayimin tashi,don haka saiki jira na gama da aikin matar gidan tukunna" Zuwaira ta gaya mata gatse gatse gami da satar idanunta ta gasa mata harara. Kullum ta tuna warning da kuma jan kunnenta akan ta yiwa yarinyar biyayya da hajiya mariya da hajja uwar yarinyar suka mata akan tabi yarinyar sau da qafa bama matar gidan ba.....sai taji kamar ta zabge yarinyar da mari. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 36 _An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace,manzon Allah S A W yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta har gari ya waye_ *_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan qin da tayi kuma ta samu ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna ganin bata samu wannan shahadar da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_* 36 "Ki gaggauta da Allah.... Am starving,ko ki bani wannan da kike debewa in fara dashi" "Sannu akuya......" Zuwaira ta fada a ranta,amma a fili saita ajiye mata warmer din tana cewa "Zaki iya ci mana.....amma kafin kicin ki fara sanarwa tsohuwarki gudun maida laifi a kaina" Ta fada dadan zafin rai. Haka kawai sai laila tasha jinin jikinta,don haka ta miqe tana sauka daga wajen "Fresh nakeso.....kada ki wuce minti talatin" Bata ma iya amsa mata ba ta dauke ragowar warmer din tana wucewa kitchen din gami da jan tsaki qasa qasa. Tafiyar minti arba'in da shida ta sadashi da mansion House din alhaji hamza kibiya. A qofar tafkeken gate din dake qara nuna alfarmar dake cikin gidan motocin suka tsaya bisa umarninsa,don yanaso ne ya gaida anni ya fito......ya kuma haida maamah din sannan ya wuce office din. Akwai cushewar ayyuka sosai yau din bisa schedule din da saddiq dinsa na yau da saddiq ya tura masa tun jiya da dare,wannan ya sanyashi fita da wuri. Wani irin qarin investors suketa samu a dukka kamfanoninsu,duk da yana yin komai bisa kula don ya tabbatar akwai mutanen dake bibiye dashi,kuma nasararsa a wancan lokacin yayi imanin ta tarwatsa musu dukka shirinsu..... Faduwarsu kuwa da shurunsu yayi amannar bawai suna nufin komai ya wuce bane. Gidane dake cike da tsari,da kuma kusan duk wanda yake gidan bisa tsari da sanin ya kamata yake zaune. Kowa yasan aikinsa,tun daga kan security guards da sauran masu aiki na cikin gida dama farfajiyar gidan,hakanan bayin Allah da suke daukan nauyi dake wani sashe daban na cikin gidan me kama da qaramin estate kowa bisa tsari da sanin ya kamata yake. Duk girman gidan ko.ina fes yake da wani irin tsafta da qamshi. Ya zuqi qamshin har cikin hunhunsa sanda yake zama saman sofas na qaramin falon anni da mutanen da suke mafi kusanci da ita ne kadai ke iya haurowa har nan. Ba abinda ke saukar masa da nutsuwa kasala gami da tayar masa da wnai Tsunammen feelings irin qamshi. Duk sonshi da qamshin wannan ya sanyashi haqura dashi kan bedsheets da duvet nashi da pillow,wanda muddin ya kwanta akai da qamshi irin wannan to zai wahala bai kwana cikin wahala ba,ko kuma ya tashi da mafarkin da zai wajabta masa wanka kafin yakai ga sallar asuba. Normally yanaso kowanne kusurwa na inda zaiyi mu'amala dashi ya zama kaman haka,sai ya lumshe idonsa kafin ya budesu sanda yaji sallamar anni. Da dogon hijabin nan nata har qasa ta shigo wanda ke alamta masa sallar walaha take ya tasota. A wajenta ya koyi sallar walaha,tun yana yi yana fashi batabi jininsa ba har takai ya saba,ko a ina yake,kome kuma yake yi sai ya katseshi yayi,saidai idan abubuwan sunsha kansa ko sunfi qarfinsa ba yadda zaiyi. Fuskarta shimfide da kararramammen murmushin nan nata ta qarasa shigowa,tayi bismillaha tana zama saman kujerar abinda ya sanyashi zamowa daga samanta yana gaidata. "Tashi ka koma ka zauna" Tace dashi don ba kasafai yake iya zama saman kujerar ba idan suna kai ko ita ko abbansu,harma da maamah din kanta. Kai ya girgiza yana tanqwashe qafafunsa saman carpet kamar qaramin yaro "Nan ma ya isa anni.....akwai kunun tsamiya?" Kai tadan daga tana dubansa. Batayi tsammanin zai qara tambayar abinci ba sam sam daga wajenta,don kuwa a yanzun magidanci sunansa,saidai kuma ta masa uzuri,don tunda akayi auren bai taba neman komai ba,don haka tace dashi "Akwai.....kasan dole ne kullum sai an yiwa abbanku.....har yanzu gargajiya taqi barinku,bari nasa a kawo maka" Ta fada da murmushi. Shima tsadajjen murmushin nan da kusan annin tafi kowa ganinsa a duniya ya sake "Anni akwai abubuwa masu muhimmanci me tarin yawa a gero,inda mutane sunsan meye gero anni da kusan duka mun koma cinsa". Murmushi ta kuma yi tana miqewa gaba daya "Gaskiya mana naga kun qulla kyakkyawar alaqa da fura.....nikam wannan traditional doctor din naka ya sake canzaka gaba daya" Murmushi kawai ya saki,shi kansa ya sani kalar cimarsa ba iri daya bace data kowa,sau tari a wani taro ko a sanda ya buqaci cin abinci da baqinsa na Africa ko nan Nigerian,sukan cika da mamaki idan sunga kalar abincin da yake ci. Da kanta annin ta shiryo komai saman tray,harda qarin lafiyayyen qosai da kuma farfesun kan rago da yasha kayan qamshi tafarnuwa da wadatacciyar albasa. Akwai abinda takeson ta karanta a tattare dashi a fakaice a matsayinta na uwa bawai kai tsaye ba. Tun daga ranar da amna ta gaya mata zaunuwar zuwaira a gidan ko sau daya bata taba hutawa da tunani ba. Ta kasa aminta hakanan ta kasa gamsuwa. Fu'ad dan maamah ne halak malak,duniya ma ta shaida hakan,saidai tana jin bai kyautu tabar mata rayuwarsa ba,rayuwar da aka fafata aka sha fama kafin fara daidaituwar komai a cikinta. Allah shine ya raya muhammad fu'ad din,amma kuma itace sila,tasha fama qwarai da gaske,faman da har batason tunawa,faman da shine ya zama silar shaquwa tsakaninsu me yawan gaske. Har batason tuna wahalar da tasha dashi kafin cire shi daga depression daya samu kansa a ciki. Tana shigowa ya miqe,bai barta ta qaraso ba ya isketa a hanya ya karba tray din ya qaraso dashi. Sanda yake shan kunun a nutse yana kuma cin qosan tana zaune a gabansa tana karantarsa,tana jin zuciyarta na matsewa,ta kuma damu tayi masa maganar dake qasan ranta,duk da haka tayi jarumtar sanda ya kammala sannan a tsanake tace dashi. "Muhammadu...." "Na'am anni" Ya amsa mata a nutse yana jin wata nutsuwa da qoshi na musamman yana ratsa cikinsa. "Nace anya yarinyar nan basai an taimaka mata da qarin masu aiki ba?,gidan nan sai nakega ko masu aiki nawa aka zuba masa yana buqatarsu ko don sauqaqawa matar gidan,duk da yake kai baka fiya son mu'amalar masu aiki ba cikin sha'aninka". Murmushi kadan ya saki,baisan wanda a duniya ya sanshi sosai ya kuma karanceshi tas sama da anni ba. "Kiyi duk yadda ya dace anni......" Ya bata amsa cikin girmamawar data sake sanyata ta jishi a ranta sosai. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 37 _Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi ne😄),yace:Manzan Allah S A W yace "da me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa na sabo,tabbas da ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara arba'in shine yafi masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_ _Bukhari da muslim ne suka rawaito_ 37 "Da ina tunanin na tura mata ma'u da maigidanta malam ibrahim.......zataji dadin zama da ma'u sosai.....ina kyautata zaton haka,malam ibrahim kuwa koda kana da ma'aikata da sauransu zakaji dadin zama dashi in sha Allah". "Anni ki zartar da komai da kike ganin ya kamata......ba buqatar sai kin gayamin anni" Ya sake fada har a zuciyarsa yana jin annin ta isa ta zartar da komai din. Kai ta jinjina tana dan murmushi,har qasan ranta tana jin dadin yadda ya bata girma da kuma dama,duk da cewa tasan cewa abune me wahala ya musanta akan duk abinda tace din. Har bakin parlor na biyu tayi masa tattaki,bakin ta fal cike da addu'ar data zame mata dole,kowacce rana dukkaninsu su hudun basa kaucewa samun kyakkyawar addu'arta da bata gajiya da binsu da ita. Qafarta daya saman daya take zaue cikin qawataccen parlor din nata da idan ka kirashi kai taaye da aljannar duniya bakayi kuskure ba,duk da ita a nata ganin sam har yanzu bai kai matsayin da take buri tsari da kuma mafarkin yakai ba. Dukkan hankalinta ta baiwa zuwaira dake zayyane mata jawaban da muhimmancinsu a wajenta ya wuce kimar komai data mallaka a duniya. Jawabin dake da wani irin kima tamkar ta zinare a idanunta. Duk da bayanan ba abinda suke haifar mata sai wani irin tashin hankali. ba irin bayanan da take buqatar taji kenan ba.....amma duk da haka suna da muhimmanci a wajenta,don sune zasu zame mata tamkar tsani kuma fitilar da zata haska mata matakalar da zata taka zuwa matakin gaba. "Amma fa tana qoqarin ganin ta aiwatar da aikinta......saidai ban hangi wata shaquwa soyayya ko kusanci da junansu ba ko kadan" "Wannan kuma aikinta ne......ita kuma ya kamata ace ta fara samar da wannan dangantakar a tsakaninsu......a nan gazawar tata ta fito.....ta kowacce hanya ya kamata ta yaudari zuciyarsa har ya aminta da ita ya miqa mata wuya.......aikinki yana kyau zuwaira,ina buqatar magana da ita yanzun nan kafin na yiwa tufkar hanci tun daga tushiya" "Yanzun zan sadaki da ita uwar dakina" Zuwaira ta fada cikin karsashi gami da jin dadin lambar yabon data samu. Batasan adadin sau nawa ta duba agogo ba tana zaman jira da dakon kiran zuwaira. Qaguwar da tayi ya hanata jira zuwairan ta kirata ta maida kiran zuwa wayarta. Ya shiga a daidai kuwa,sanda take rusune daga bakin bedroom din sabreen tana qoqarin fahimtar da ita amfanin kiran. "Ina jinki kamar d'iyata ko jikata....ki daure ki saurareta,taqi kadan zai rage ku rabu in sha Allah". Duk bata gamsu da matar ba,duk da batajin nutsuwa da matar ko kalamanta,amma a ciki akwai abinda takejin gaskiya ne,a ciki akwai abinda takejin da gaske ya kusa tabbata din TAQI KADAN YA RAGE SU RABU. Hannu ta saka ta karbi wayar,sai ta tura qofar bedroom din ta rufe ta koma ciki. Tana takawa cikin idanunta suna kan fuskar wayar,yau din a matuqar tunzure take,so batason wani magana da zata sake hasala hali da kuma yanayin da take ciki. Gaban madubinta taja stool ta zauna,sannan ta kunna wayar ta sakata a hands free ta dorata saman madubin,sannan kuma a hankali ta maida idanunta saman fuskarta kamar me kallon maamah din zaune a gabanta. "Ina jinki" Ta furta a nutse yana goye hannuwanta a qirjinta. "Ina fata kina cikin lafiya da kuma aminci qarqashin kulawar d'ana?" Tayi maganar a nutse tana son kamo bakin zaren ainihin maganarsu. Kamar ba zata amsa mata ba,sai ta daga idanunta daga kallon dogayen yatsunta da gaba daya lallen da akayi mata na aure ya fice tas,tamkar ma ba'a taba digawa yatsunta lalle ba,ta maida oily eyes din nata cikin madubin daya bayyanar da fuskarta dinnan me shimfidadden kyau dake dauke yau din da wani irin kwantaccen fushi. Zubawa fuskar tata idanu tayi kamar yau ta fara ganin kanta da kanta,iya kallon kawai yana motsa zuciyarta gami da tuna mata a karan kanta wacece sabreen,wani sashe na zuciyarta ya motsa yayi aikin daya jima baiyi ba,taji wani abu ya darsu a zuciyarta wanda ta jima tana yunqurin daddago dashi amma yana komawa "Ki ajiye wannan a gefe.....yaya jikin huda?" Tayi mata tambayar da take kwana da ita tana tashi ba tare da tasan waye zata yiwa ita ya kuma basu cikikkiyar amsar da take buqata ba. "Jikin huda?.....alhamdulillah......saidai ban da tabbacin yadda ya kamata ya kasance". A hankali ta lumshe idonta tana son yiwa amsar tambayar tata fashin baqi. Bugun zuciyarta yana son ninka gudunsa saboda samun mabanbantan amsoshi daga mabanbantan lunguna da saquna na zuciyartata wadanda basuyi daidai da fatanta dama abinda takeso taji ba. "Mu ajiye wannan......zan dan yaba miki game da yadd kike qoqarin ciyar dashi abinda muka baki,saidai har yanzu kin gaza cimma manufar abinda kikeyi din......caring kulawa.....ba wata halitta da batasan kulawa.....dole ki fara samun zuciyarsa kafin ki samu cikinsa da jikinsa....." ".......ba wannan cikin jarjejeniyarmu.......wai shin..kina zaton ina da buqatar zuciyarsa?,ko ina da buqatar hanyar da zata sadar dani ga shiga zuciyarsa?". Tayi maganar kanta tsaye da wani irin tsauri,saboda zafi da a yau zuciyarta keyi mata,tana jin kamar wani abu me kama da gajiya da kuma fara jin takura yana mintsinin zuciyarta. Murmushi me sauti maamah din ta saki tana gyara zamanta "Bana fatan ki samu zama ko shiga zuciyarsa na dindindin,a taqaicema dai....banda yanayi irin na lalura banjin kinkai quality din da zan baki license na shiga zuciyar mutum me tsada,namiji irin muhammadu ba.....amma karki manta,dole ne ki sadaukar masa da komai don isa ga burinmu.....idan nace komai ina nufin komai da komai fa,na zabeki ne saboda ina da tsammanin zaki iya bada komai don cikar muradina.....koda kuwa jikinki ne...." "Ya isa!" Ta furta a tsawace saboda jin maganar tata ta fara shallake guri,uwa uba tana neman fin qarfin kanta. "Kibi a hankali......a yanzun duk da ban mallakeshi ba,amma zakisha mamakin abinda zai biyo baya idan har na shaida masa matarsa tana min shouting tana kuma dagamin murya....." Zafin radadin maganarta ta farko bata saketa ba,don haka bata maida hankali sosai akan maganarta ta biyu ba. Burinta shine ta furzar mata da abinda yake ranta,tana jin kamar takai maqurar da zasu dinga wasan tamaula da ita tsakanin ita da d'anta. "Zanci gaba da ci dashi kaman yadda iya abinda yake zayyane kenan a bisa yarjejeniyarmu......daga hakan banajin zan qara akan komai.....faduwarki ko nasararki ya ta'allaqa ne da yadda na samu tabbacin lafiyar qannena" Daga haka ta katse wayar kawai tana ajeta a gefe. Taso tayi tariyar maganganun da sukayi da maamah din,amma a yau sai taji gaba daya bata da buqatar tuna komai.....kawai tana jin ba zata iya ci gaba da zamowa kamar tamaula tsakanin su ba. Wani irin confidence takeji,saita miqe tana komawa bakin qofar da zummar ajewa zuwaira wayarta,ta dauka duk sanda ta dawo,don ko haduwa da ita bata sonyi. Ga mamakinta a tsaye ta sameta a bakin qofar kamar wadda aka bawa gadinta. Wani kallo ta jefeta dashi tana jin sam matar bata mata ba "Ba wani abu da ake buqata?" Ta fada da sauri bayan ta karbi wayar ganin sabreen din na zummar shigewa ciki "Babu" Ta bata amsa a taqaice tana maida qofarta ta kulle. Yadda yau yarinyar ke amsa mata magana a tsaitsaye sai takejin kamar akwai abinda ta taka,akwai abinda ya bata confidence a kanta. Ci gaba tayi da juya wayar a hannunta tunaninta yana yin nisa gami da rarrabuwa kashi kashi. Wani tunani ya kutso mata cikin kwanyarta "Me yasa ba zaki murza kambunki ba?,ki gwada qarfin iko da mulkinki ba har akan fu'ad din?" Wani sashen na zuciyarta ya bata shawara. Shuru tayi tana sauraren daya bangaren tare da juyar maganar cikin kwanyarta. Kai ta gyada tana bawa kanta tabbacin tabbas wannan din zaiyi aiki.....koda baiyi diki dari bisa dari ba to akwai yiwuwar samuwar galaba. Tana qoqarin kiransa ta shaida masa tana buqatar ganinsa sallamarsa ta mamayeta. Tana amsa sallamar farinciki na cika zuciyarta yadda Allah ya dubeta ya jefo mata shi,saidai a saman fuskarta ba haka bane. Ranta yana hade,hakanan ta boye duk farincikinta don tanason ko meye zata gaya masa ya daukeshi da muhimmanci. Sai daya iso gabanta ya zame yana gaidata ta hanyar tsugunawa saman qafafunta. Bayan ya gama gaidata din shuru ya biyo baya,a nutse yace "Ba komai da ake buqata?,ba wani matsala?" Yayi tambayar data zame masa wajib duk sanda yazo gaidatan don qoqarin sauke haqqin Allah da yakejin ya zama wajibi ya sauke din. Kai ta girgiza fuskarta a daure. "Ba abind nake buqata.....amma matsala dai akwaita". Daidaita tsugunnonsa yayi kafin ya zame ya zauna sosai a gabanta. Duk sanda tayi wannan yanayin kota furta magana makamanciyar wannan zai wahala idan ba wani aikin bane zaya zameshi. Idanunsa yadan lumshe gami da budesu duka lokaci guda cikin qoqarin hadiye fargabarsa,yana tunkarar qalubale komai girmansa.....gaagwarmaya komai wahala da kuma taurinta,amma har yanzu zuciyarsa baya iya jure wadannan halayen da maamah din,dabi'unta suna kassarashi,ya kasa sabawa,baisan me yasa ba,ko don ita dinn wata jigo ce da abubuwanta ke tafiya ba yadda ya kamata ace sun tafi ba?. "Wacce matsala ce?,me yake faruwa?" Ya tambayeta a nutse. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 38 _Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_ *_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa a jiki_* 38 "Muhammadu" Ta kirashi da ainihin sunansa,ba tare kuma data bari ya amsa ba ta dora "Nikam bansan a rayuwa akwai wani abu da yafi haihuwarku da nayi muhimmanci ba" Idanu ya zuba mata yana jin tamkar ya tashi ya fita da gudu ya tserewa maganganunta,don yasan zai wahala ba kamar kullum bane,dora masa nauyi da mas'uliyyar da zai gaza dauka kota masa tauri. Kai ya girgiza,ya buda baki zai magana ta sake danneshi da kalamanta "Bansan wanne irin rashin muhimmanci nake dashi a rayuwarku ba da har zan zartar da hukunci cikin rayuwarka,nace kum ga alfarma ko abinda nakeso kayimin ka gaza yi din,ace har yanzu maganganun ameenatu da umarninta yana zama gaba da nawa?" Ta qarashe maganar tana jin dacin haka sosai har cikin zuciyarta. Batasan wanne tozarci ma ya kamata ameenatu ta fuskanta ba aduk sanda haqanta ya cimma ruwa,har yanzu idan tayi hasashen abinda zata saka ta fuskanta sai taga wannan hukuncin yayi kadan. Sam baya qaunar ta dinga sanyo maganar anni cikin maganganu da ayyukansu,don bazai iya tuna sanda anni ita tayi magana a kanta ba indai ba alkhairi ba. "Muhammadu.......yanzu ni da hannuna na baka amanar yarinyar mutane......na roqeka ka mu'amalanceta kamar kowanne miji da mata.......ka kyautata mata ma faranta mata,ka jata a jiki amma haka ga gagara?,ka kasa cikamin wannan alfarmar da zata bayya a irin kima da martabata a idon yarinyar?". Qasa yayi da kansa,shi maganar ma nauyi tayi masa sosai akai. Ta wani gefen kuma ranshi da zuciyarsa suma motsa. Yanzu har taurin kan yarinyar da tsaurin idonta yakai ace ta kawo ma maamah qararsa?,har da maganganu irin wadannan marasa dadin ji?. Sai data gama dukkan wani fada baice komai ba,har sai da tayi shuru sannan yace "Kiyi haquri,in sha Allah za'a sake yin qoqarin gyarawa da canzawa". Ya furta a taqaice. Har cikin ranta yadda ya amsa mata haka a sauqaqe ya faranta mata sosai "To Allah yayi albarka" Ta fadi kalmar da bazaice when last da yaji ta fada ba. Muryarsa a sanyaye ya amsa mata,sannan ya miqe yana mata sallama yana fita daga falon. Tun kafin ya qaraso Jordan ya wangale masa qofa,da wani irin zafi ya isa ya shige motar Jordan ya maida murfin motar ya rufe. Suit dinsa na sama ya fara ballewa yana zareta daga jikinsa saboda wani irin zafi da yakeji tun daga zuciyarsa har cikin fuskarsa. Iske me qarfi ya fesar daga bakinsa bayan ya zuqi wata "Wanne abune meqarfi da girma a tsakaninsu bayan wannan?" Ya jefawa kansa da kansa tambayar yana motsa labbansa. "Ita ta shiga jikin maamah ko maamah ce ta shiga jikinta?" Ya sake maimaita tambayar da ba wanda zai iya bashi amsarta. Yanzun har matsayinta da girmanta wajen maamah yakai ya samu sanyawar albarkar maamah din saboda dalilinta?,wanne aiki take mata haka me faranta rai bayan abinda yake suspecting?. Tunanin daya rakashi kenan har cikin office dinsa,ya kuma wuni yana tayashi zama,duk kuwa da uban tarin ayyukan daya samu suna jiransa. Duba documents da sanya hannu cikin wasu takardun,wasu takardun suna da buqatar hankalinsa da nutsuwarsa kafin yakai ga sanya hannu,da qyar ya hada hankalinsa bayan sallar la'asar ya soma duba wasun,bayan ya yiwa kansa matsayar matakin da zai dauka. Komawa tayi ta sake kwanciya bayan sallar la'asar din,tana lissafin nan da awa daya koda rabi zata shiga kitchen saboda shi.....saboda mutumin da ba ganin girma qima ko martaba sam sam tsakaninsu. Idanunta ta runtse,a yau tana jin wani zafi zafi na yadda maamah ta bautar da ita. Batasan me yake tilastata lallai saita yi sai kuma ta cika muradin maamah din ba. Tsaki taja tana bude idanun nata,sai suka fada saman gift din da anni ta bata ranar da suka je. Dan murmushi ta saki qasan zuciyarta,matar ta kwanta mata a rai,tana da wani irin calmness me taba zuciya nutsuwa da kuma wani irin kwarjini. Tashi tayi tsam ta daukosu ta dawo ta zauna saman abun sallarta data tashi ta soma budewa tana tuna fuskar matar da takejin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanzu. Littafin farko ta dauka daya qunshi addu'o'i akan kowanne abu,harkokinmu na yau da kullum. Shafin farko ta bude,sai ta dinga tuna zamanin da ummensu ke raye,Lokacin da take tsaye a kansu kai da fata,ba batun fashin islamiyya ko wani abu da yayi kama da wannan. A duk dare itace malamarsu,zata zauna a tsakiyarsu saita tabbatar kowanne karatunsa ya zaunar masa akai,musamman karatun addini da a nan tafi qarfi,na bokon tafi jiran abbansu idan ya dawo,musamman idan ya zamana itace da girki,idan ba ita bace dole saita dauki uzuri an bata lokaci. Hannu tasa ta shafi addu'ar farko da sam ta mantata cikin rayuwarta,ummensu itace ta fara koya mata ita tana kuma iya tuna lokacin har yanzu,sai ta tashi ta koma saman sofa ta zame kadan tana bin addu'o'in daya bayan daya tana dubawa suna kuma sake tuno mata da kansu. Sosai takejin dadin karatun,don ya debe mata kewa me yawan gaske. Babu zato daga saman kanta din,daidai wata kyakkyawar qaramin luxury stand taji qaraurawa tana kadawa. Zubawa wajen ido tayi,wata mulmulalliyar na'ura ce da take zubi da telephone. Tunawa tayi amna ta taba dagawa tayi kira zuwa parlor sanda sukazo,sai a sannan ta tuna na'urar sadarwa ce da aka shiryata duka gidan da kuma tsakanin dakunan gidan har zuwa Kutchen,wannan ya bata qwarin gwiwar saka hannu ta daga ta sanya a kunnenta. "Ranki ya dade......malamarki ce tazo,sabuwar malamar da yallabai ya daukar Miki saboda karatun yamma". "Malama kuma?" Ta tambayi kanta da kanta cikin tsananin mamaki tana son tuna yaushe sukayi wannan maganar da shi?. "Duk cikin salon da zai miki mugunta ya cusguna miki ne kaman yadda ya dauki alwashi". Ido ta lumshe tana budesu sannan a nutse tace mata "Ki sallameta zuwaira......ko kuma ta jira wanda ya tattagota din" Daga nan ta kife wayar tana komawa ta zauna qirjinta a quntace. Wannan abun da yayi me yake nufi kenan?,ita din jahila ce?,ko batasan komai ba saishi zai sanya a karanta mata?. Wannan tunanin ya tsaidata,sai data gama baqin ran da bacin ran sabon salon wulaqanta mutum daya bullo dashi......hakanan ba don taso ba ta miqe tana wucewa kitchen. Tana shiga zuwaira na fadowa,sai ta waiwayo tana kallonta. Cikin jikinta wani abu ya bata,ta yaya duk wani motsinta zuwairan kamar tana biye dashi ne? "Ranki ya dade dame za'a taimaka miki dashi?" A nutse ta juya kawai ta fara aikin gabanta,kamar ba zata amsa mata ba sai kuma ta tura mata lettuce da cabbage carrot da peas tace ta gyara ta yanka mata. Zaman kurame kawai sukeyi cikin kitchen din,zuwaira nata satar kallonta tana son ta dan tabota da magana don ta gina alaqar sabo a tsakaninsu amma bataga wannan fuskar ba sam "Tashin hankali" Zuwairan ta fada qasa qasa,daga ita har mijin haka fuskokinsu suke kamar na shanu? Ta tambayi kanta,ita dai har yanzu bata taba ganin fara'a ko dariyar dayansu ba. Sai da suka kammala komai sannan ta fidda magungunan zata cakuda kaman yadda ta saba. Ta bude murfin ta karkata gorar,sai kuma ta tsaya cak. A hankali ta daga idanunta ta zubesu akan zuwaira data tsaida komai tana son tabbatar da zubawar. Karon farko da cikin jikinta taji kamar nauyin idanuwan wani yana kallonta zatayi abinda bashi ya dace ace tayi ba akan wani,duk kuwa da tasan jirgi daya shine ya debo zuwaira da ainihin me kwangilar,amma a yau saita ji wani nauyi. "Zaki iya bani space?" Ta jefa mata tambayar taba dinke girarta sosai fiye da dazu. "Au to....to ranki ya dade" Ta fada adan daburce sannan ta juya tana fita a kitchen din. Haushi ya sanyata kwarara da yawa,idan komai ya qare ai a huta,taga ta inda zata tuhumeta kuma,sai taja tsaki tana jefa roban a shara sannan ta juya ta fice tana baiwa zuwaira dake falo umarnin taje ta jerasu,sai ta wuce kai tsaye zuwa dakinta. Itama din a gaggauce ta shiryasu tana kallon kayan,baki ta tabe,tana jin haushin yadda lafiyayyen abinci irin haka yake salwanta,ga nasu iyalan can cikin yunwa da buqatar abincin da baikai wannan bama,amma akan mutum daya anata asarar lafiyayyen abinci irin wannan. Hankalinta ta maido jikinta da sauri,saita juya tana barin falon cikin son kiyaye dokarsa da tsoron kada ya dawo ya sameta a wajen kamar yadda ya shardanta mata. K'arfe Tara da wasu mintuna motocinsa suka tsaya a farfajiyar gidan bisa halastaccen parking da kowanne driver na kowacce mota ya qware akai. A nan harabar gidan ya barsu ya wuce ciki shi dame sunan malam,wanda iyakarsa qofar parlor din farko ya juya shima yana komawa cikin guard da security na gidan dake qoqarin tabbatar da tsaro da lafiyar kowacce mota kafin masu tafiya su wuce a sake tabbatar da tsaron gidan sannan a maidashi a rufe kaman yadda yake,shida da fita kuma sai da izinin masu gidan. A hankali yake ratsa falon farko zuwa na biyu kafin ya isa stairs dinsa. A gajiye yake don duk sanda yayi dare irin haka a company to tabbas cinkoson aiki ya riqeshi ne. Tun daga nesa yana taka stairs din ya hangi maqullin maqale jikin qofar,ya isa a hankali ya sanya hannu ya cire sannan ya tura qofar parlor din. A nan zarginsa ya tabbata,mug din da yayi amfani dashi a daren jiya yana zaune abinsa dirshan saman side table din,yayin da dish din da yayi amfani shima dashi yake zaune saman dining abinsa hankali kwance. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 39 _Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan Allah S A W ya ambaci ranar juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA YA ROQA DIN". sai manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana baida tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_ Wani bacin rai ne karon farko ya sauko masa,ba abinda ya dawo masa akai sai abinda ya faru a dazu. Yadda maamah ta fitittike tana jaddada masa yadda takeso ya mu'amalanceta ko ya kula da ita,amma ko kusa ko alama shi baiga alamun tasan darajar kalmar aure ba koda kuwa auren 'yar tsana aka daura,ballantana shi data deba kudaden da ranta keso,karamci kuma ya sanya suka qara mata da wasu abubuwan da shi kansa baisan me su anni suka kashe ba. Duka sai yaji abun bai masa ba bai kuma zauna masa akai ba,ya kamata ya qara bata lesson. Yana takawa zuwa bedroom din nasa yana watsar da kayan hannunsa,kama daga socks takalminsa suit briefcase dinsa da sauran tarkacen daya shigo dasu. Wani budewa hancinsa yakeyi yana tsukewa saboda bacin rai,ya tsani raini ya kuma fahimci halinta ne,ya tsani rashin kunya ya kuma karanci dabi'arta ne. Bai dakata ba sai da yayi wanka,ya hadawa kansa fruit salad a gurguje yasha,sannan ya zauna yana jawo wayar sadarwar yana kiran number dakin nata. Ta gama komai tuntuni,ta kuma jima da kwanciyar saidai baccin da baizo ba. Tayi mamakin jin kiran,saita sanya hannu ta dauka tana tunanin zuwaira ce,ko meye kuma ya faru a daren nan oho?. Muryarsa taji sabanin muryar zuwaira da tayi tunanin itace. Har tsakiyar kanta sautin muryar ta sauka mata da wani irin zuzzurfan amo "Hello" Ya fada yana qoqarin hadiye bacin ran dake taso masa. Matsar da kan wayar tayi daga kunnenta da zummar sauke wayar,kaman yasan abinda take shirin yi ta tsinci muryarsa cikin zafi yana magana "Kika kuskura kika sauken waya....zakisha mamaki na". Tsauri umarnin nasa yayi mata,saita samu kanta da gaza ajiye wayar. Sau tari tana mamakin yadda yake cin galaba a kanta haka da sauri,umarninsa yake saurin ratsata,wani abu guda daya da ta raina akan kowanne d'a namiji. Bata taba zato ko tunanin akwai wani lokaci da zaizo da wani namiji zai iya juyata ko ya canzata daga abinda yayi mata daidai cikin rayuwarta ba,sai ga abun yana tafiya cikin rashin zato bare tsammani.....kamar a cikin duniyar mafarkinta. Ci gaba tayi da riqon wayar ba tare data ce komai ba,haka daga nasa bangaren bataji ya sake furta komai ba. Kusan minti daya wayar na a riqe a hannunta,sakannin kuma suna ci gaba da motsawa. Kaman daga cikin wayar taji an murda qofa an kuma budeta. Sauyin yanayin qamshin daya soma mata sallama ne ya shaida mata tabbas an bude mata qofa,ba kuma cikin wayar bane a zahiri ne. Tana kwance ne rub da ciki,don haka ta waiwaya kadan don tabbatarwa da idanunta. Muhammad jadda ne,tsaye daga baki qofar dakin yana riqe da handle din,daure da lallausan farin towel wanda ke dauke da tambarin VERSACE baro baro a jiki. Gaba daya towel din ya daurashi ne daga iya qugunsa,ya kuma sauka sosai zuwa mararsa,abinda ya bata damar ganin full ginannen jikin nan dake cike da lallausar gargasa data kwanta tayi luf luf. Fadin kafadunsa ya sanya bata ko iya hangen qofa,sai yau ta sake fahimtar GIANT ne na gaske,da murjajjen jiki da kuma ginannun tsokokin damtse dana qirjin wato(muscles). Wani mahaukacin faduwa gabanta yayi,a yau taga abinda bata gani ba a wancan ranar data sameshi a parlor dinsa.....ko don yau din a tsaye yake da dukka tsahonsa da kuma wadataccen haske a dakin nata?. Duk yadda take da kafiya da taurin rai sai data gaza ci gaba da kallonsa,wani irin tsoro ya kamata wanda ya tilasta mata maida kanta ta kwantar saman pillow tana baiwa qofar dakin baya,wato qeyarta ke kallon qofar kenan. Gabanta ya sake yankewa ya fadi sanda taji ya maida qofar ya rufe gami da murxa key,ta fidda idanunta dukka biyun waje tanason yin hasahen abinda zai iya faruwa da ita,saidai bata gama wannan ba taji an sanya hannu an birkitota gaba daya,sai gata ta koma rigingine a maimakon rub da ciki da take a dazu. Gaba daya ya zame mata rumfa saman kanta,tamkar me barazanar hanata ganin komai na dakin sai wannan mudadden jikin nasa. Da hanzari ta sanya tafukan hannayenta guda biyu da zummar tureshi saboda yadda yake neman hade space din dake tsakaninsu,amma ko gezau kamar ma ba wani hannu daya sauka a jikinsa. Bai bata second chance ba ya kama hannuwan nata ya matse cikin hannunsa guda daya. Qoqarin qwatar kanta sosai ta farayi tana tureshi,amma baiko motsa ba,yana riqe da hannuwanta gaba daya yana kuma ci gaba da zube mata idanunsan nan "Ka sakeni......ka cikamin hannu" Ta fada sanda ta fahimci ko kusa ko alama bata da qarfin da zata iya amsar kanta a hannunsa. Ta cikin idanunta ya fahimci laushi tayi,hakanan qarfinta ne ya fara qarewa. Bayajin zai qyaleta haka sai ya bata mummunar barazanar da ba zata qara kai qararshi wani guri ba. Duk dabaya tunanin wani tsoro me yawa a tattare da itan duba da ita din WACECE?. Ba wani sabon abu bane a wajenta cudanya da maza,duk da maza suna suka tara kamar yadda mata suma suka tara suna. "Inajin a matse kike a sauke miki jarabar da take damunki ko?,wannan ya sanya ba kunya cikin idanunki kika je kina kai qara a inda kike tunanin za'a sanyani sexual affairs dake ko?". Duf wuta ta dauke mata,daga iya kalmar sex data shigo maganar ta tabbatar lallai babbar magana aka baro. Yaushe takai qararsa?,kuma gurin waye?,me tace tana da buqata?,duka wadannan tambayoyin sune suka soma mata yawo saman kai,kuma inda tana da hali tana da buqatar amsarsu,saidai a yadda komai yake a hautsine bata jin tana da tattararriyar nutsuwar nemansa da wadannan amsoshin. Tana aje wannan tunanin yana sakin hannun nata,ya miqa hannu da wani irin zafin nama zuwa Coller din rigarta,wadda tsaurin riqon da yayi mata ya bawa bottom daya damar tsinkewa fit. Fitarsa sai ya zamana kamar ya hada da fitar nutsuwa daga gangar jikinta,wani tashin hankali ya rufto mata har kala biyu. Na farko yadda yayi kusa da ita da towel din da kadan ya rage marabarsa da tsirara,don babu abunda ya lullube illa mararsa zuwa gwiwarsa,na biyu kuma fitar maballin rigarta sai ya tuna mata waccan ranar a kitchen. Ranar da har yau idan ta dauki rigar data sanya a ranar sai taji qamshin wannan mayataccen turaren nasa,abinda ya sanyata kenan tayi adabo da rigar duk kuwa yadda take sonta. Saboda duk sanda ta sakata haka yadda abin ya faru zai yita dawowa kanta,hakanan kuma zatayita tuna yadda ya azabtar mata da lips haushinsa yayita kai komo kenan a ranta har sai ta raba kanta da ita. Matse hannunta yayi yana saukar dashi daga gaban rigar don so yake ya tsinke maballi na biyu,kafin ta iya komai har ya samu nasarar yin hakan,ya kuma wuce zuwa maballi na gaba,abinda ya sakata saka hannuwanta dukka biyun ta cukuikuye gaban rigar,cikin fushi kuma taci gaba da magana "Don't touch me.......ka daina tabani mana.... Wai mene haka?!". Ta qarasa fadi sanda ya tattara hannuwanta da zummar turesu,cikin rashin sa'a hannuwan nasa suka samu nasarar sauka daidai saman tudun qirjinta wanda ke tsaye car babu bra. Sabonta ne idan zata kwanta dukka saita ciresu,don tana jin kamar suna hanata cikakken bacci. Daga shi har ita ba wanda baiji kaman an yarfa masa wuta a jikinsa ba,yayin dashi ya hada wani azababben shock daya ratsa jininsa da wani irin mahaukacin gudu ya aike saqo qwaqwalwarsa ya kuma dawo da saqon yana rabawa zuwa sassan jikinsa gaba daya. Taji komai har cikin jinin jikinta,sai taji kamar an zare mata dukka wata laka tata da wani irin firgici da tsoro bakinta ya furta "Please......don Allah ka bari" Kalaman nata na qarshe ya fito da zirarowar hawaye zuwa saman kuncinta. Duk yadda yaso ya zarce da tsoratata gami da gigitata cikin mugunta sai yaji ya kasa,haka ya sake mata rigar yana dauke idanunsa daga kanta ba tare daya bari sun sauka a inda take boyewar ba tamkar sulalewar ruwan kalkashi a tafukan hannun mutum. Zuciyarsa ta cika da wani irin mahaukacin mamaki......daga ina wannan weakness din ya taho?,ya tambayi kansa da kansa can qasar zuciyarsa. Bai taba niyyatar zai dauki mataki akan wani abu ba tare daya qarasa aiwatar da qudurinsa ba,bai taba jin rauni akan duk wani abu daya sanya a gaba ba sai akan wannan dan qaramin aikin. Tattare jikinta tayi waje daya tana neman hanyar sauka daga saman gadon,amma sai ya sanya gwiwarsa ya take gefan rigar,ya waiwayo a nutse ya zube mata idanunsan nan masu dauke da wani kakkaifan maganadisu,wanda duk yadda sukakai ga haske sun surka launi a yau din. "Kina zaton zan hada jiki dake ko?,over my dead body......duk randa zan hada jiki dake ki sanya a ranki ranar mutuwarki ne kawai yazo,don zan niqaki da kyau kaman yadda engine ke niqa tsaba ya koma gari....." Yatsunsa ya murza saman fuskarta sannan yace "Sharadi guda biyu ne zan baki idan kin kiyaye shikenan.....na farko....kada ki kuskura ki sake kaiwa maamah qarata koda akan meye kuwa....ban hanaki kaiwa anni ba idan kinga zaki iya fine.....sharadi.na biyu duk randa na sake miki umarnin yin wani abu kika watsar kina daukan kanki wata tsiya.....zakiga abinda zai biyo baya,sai na sanya an sako Michael yayi dambu da namanki,ki tashi kizo ki gyaran sassa.....ki kuma samu note pad ki rubuta day one don lissafinmu yafi tafiya daidai" Yana kaiwa nan yaja jikinsa yana sauka daga gadon,ya kuma fara takawa hankali kwance yana fita daga dakin. Da sassarfa yake haurawa saman cikin tuhumar kansa da kansa. Baisan kanshi da kasawa ko gazawa ba,ya akayi ya kasa bata mummunan punishment yadda ya kamata?. Koda ya tsaya gaban mirror na toilet din,sai ya dinga jin haushin kansa da kansa. Baisan wani weakness nasa ko kadan ba......amma sai ya samu kansa yana tsoron kada fa wannan ya zama shine weakness dinsa?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 40 _Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_ _harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_ ________________________________ Moroccon cotton jallab ya saka ta maza maroon color me gajeran hannu,wadda aka yiwa ado da gold din zarurruka masu kauri. Har hantar cikinta sai data kada sanda taji fitowarsa zuwa falon,amma ta dake bata nuna ba,tana duqe tana goge stand tv lokaci lokaci tana goge 'yan hawayen daketa qoqarin lallai sai sun sake karya mata zuciya. Kai tsaye ya wuce saman minotti sofa dinsa yana lumshe idanunsa,wata azababbiyar kasala nason saukar masa. Dole yana buqatar wani abu da zaiyi awakening dinsa for some hours don yana da aiki. "Ke..." Ya kirata idanunsa suna lumshewa kadan. Kiran ya mata ciwo,amma kuma dole ta nuna tasan da ita yake maganar. "Bring me some coffee" Ya furta yana dauke idonshi a kanta ya lumshesu don kaucewa kallonta. Ajiye duster din hannunta tayi qirjinta na mata wata suya,ta fara takawa don isa qofar da zata saukar da ita daga saman "Hey.....ina zaki?" Ya furta da rashin qwarin murya. Sai kuma ya mata nuni da nasa kitchen din da idanunsa,kai tsaye ta gane me yake nufi,ta kuma canza akalar tafiyar tata zuwa can din. Tayita dube dube da tsoron kada ta tabo wani abun duba da yanayin machine da utensils din dake kitchen din daya sake shan bamban dana qasa nesa ba kusa ba. Da qyar ta samu ta kammala,duk da bata da guarantee din yayi ko baiyi ba,don itadai ba damunta yayi ba,koda ya dameta ma ba irin wannan bane.....nasun irin nasun ne wato daidai matsayinsu yaku bayi. Saman tea tray ta hado da cups. Ta qasan idanu cikin lumsassun idanunsa yake kallonta sanda take nufoshi da wani irin kallon da zaka rantse da Allah bacci yakeyi. Yana qoqarin binciken kansa me yasa yaketa tunawa da abinda ya faru?,amma ya rasa dalili,haushin kansa sosai yakeji a yanzun,yana ganin kamar wannan hanyar ta sanya tsoro a zuciyarta bazatayi aiki ba.....zata iya dasa masa matsalar da zata gagari gangar jikinsa watan watarana. Yadda jikinta yayi laushi sosai yake karanta,yana mamakin macen data saba mu'amalantar maza kala daban daban me ya sanyata jikinta yayi laushi don ya mata wani qaramin riqo da bai taka kara ya karya ba?. "Kana murzata ne ta hanyar da ba haka su suke mata ba,da ta irin tasu hanyar ce qila ba abinda zai sanya jikinta laushi" Wani sashe na zuciyarsa ya bashi amsa. A gabansa ta ajiye tana jin inama zata samu wata dama ta zuba masa wannan abun cikin tea dinsa?,qila cikin kwanaki uku ta samu nasarar da zata cika aikinta,ta tattara tabar wannan DUNIYAR tasu ta koma tata ainihin duniyar. "Serve me" Ya fada da murya can qasa. Sake baci ranta yayi,gaba daya a hankali yana son canzata ta koma 'yar aikinsa kenan kome?. Tsugunnawa tayi a nutse ta soma zuba masan tana qoqarin danne zuciyarta amma ta kasa jin relief. A sanda parlor din ya dauki shuru,wayarsa da tafi kusa da ita ta soma kuka alamun shigowar kira. Kallo daya ta yiwa wayar ta dauke kanta,yarinyar kullum ce dai wato fareeda khaleed mustapha. Qaramar tsuka taja,ita ta sani zaa rina,mutum kamar muhammad jadda ace yana zaune lafiya bisa kyawawan dabi'u?,ai ta qalubalanci wannan. Banda akwai wata gurbatacciyar alaqa me zai dinga shigo da kiranta cikin wayarsa a kowanne dare?,a daidai lokaci irin wannan da mafi yawan lokuta yake kebancewa shi kadai?. Tana miqa masa coffee din yana daukan wayar yana kallon screen din ransa yana baci,ya dauke dubansa daga kan fuskar wayar da yakeji kamar ya bugata da bango saboda yadda tsananin nacin fareeda ya soma shallake hankalinsa,ya aje dubansa akan fuskarta dake a dinke sosai. "Fara sha kafin ki bani" Yace da ita a taqaice. Duban rashin fahimta tayi masa,sai ya kafeta da idanu kafin yace "Do you think am a fool?,kina zaton zan karba nasha any how?....." Ya qarasa maganar yana daidaita zamanshi sannan ya tura mata teatray din "Take a sip first" Sai data ja numfashi sosai ta aikawa hunhunta sannan ta samu zuciyarta taci gaba da aiki yadda ya dace,me yake nufi data fara sha?,ta tambayi kanta. "Kada ki barwa kanki qofar zargi" Wata zuciyar ta shawarceta. A nutse ta dauka mug din ta kurba kadan sannan ta ajiye masa,zata motsa yace "Hang on for a bit" Ya fadi cikin halin shariya yana maida hankalinsa kuma kan fareeda tare da tunanin ta inda zai bullo mata. Ambassador yana da kima da mutunci a idanunsa,musamman daya kasance babba harda furfura a fuskarshi,saidai fareeda tana crossing line da yawa da baya bari a crossing masa shi. "What's bothering you?" Ya fadi adan fusace,yayin data narke marya Kamar qanqanuwar yarinya "Kaineee" Labbansa duka ya cusa cikin bakinsa yana qoqarin hadiye takaicin data bashi. Sai ya sauke idonsa akan sabreen wadda baisan ta soma barin wajen ba sai a sannan. "Where to?" Ya jefa mata tambayar data tabbata yanason jin inda zata ne. Ita ba zata tsaya tana jinsa yana hirarshi da matan banzanshi ba,ba damuwarta bane ya yanke dukan abinda yake ganin ya dace da rayuwarsa.....amma ita kuma ba wanda zai tilastata yin abinda batayi niyya ba......wannan din dabi'arta ne da ba canzawa. Sai data yi qaramin yaqi da zuciyarta sannan ta iya lanqwasa harshenta ta sarrafashi tana fadin "Dare yayi inaso na kwanta" "Idan kin gama you can go" Ya fada cikin halin ko in kula yana katse kiran fareeda itama gami da sanyata a DND mode sannan yaja coffee dinsa ya soma kurba. Sassa ne na alfarma dake da yalwa wadatar kayan alatu dana qarau wadanda ke buqatar a gogesu,wannan shi ya sake bata mata lokaci ya kuma dauketa har kusan sha biyu na dare abinda ya bata mamaki samunsa sa tayi dungurgur ya sanya system a gaba ya zuba mata idanunsa yana sarrafata,wanda motsin takunta ya sanyashi rage mata haske sosai har baka ganin abinda ke allon. Baki ta tabe ta qarasa,zuciyarta na ayyana nata waye ma yasan abinda yakeyi tsakiyar darennan. "You are free" Ya amsa mata ba tare daya waiwayota ba,sai ta fara nufar qofar a ran ta tana fadin "Shi mugun mutum ba kasafai bacci dama ya fiya damunsa ba". Gyaran yayi masa sosai,don yafi qawatar dashi fiye da coffee din,don sam bai masa dadi ba irin yadda yakeso ya kasance ba. Jallab din jikinsa ya zare ya wuce toilet da zummar daura alwalar kwanciya bacci. ★Duk a kasalance take kowanne aiki a yau,tun daga safiya zuwa daren da take kammala girkin daren. Sai takejin wani irin qosawa,gaba daya ta fara gajiya da komai. Tunda take wannan shine karon farko data aboci kitchen safe da dare da zummar dora sanwar girki. Kamar ko yaushe bayan ta kammala abincin,ta taka a hankali tana nufar inda ta boye akwatin. Ta jawo ta miqa hannu ta fito dashi sannan ta bude. Kayan cikin ta fara fitowa dasu kaman yadda ta saba,daya bayan daya kuma ta soma zubasu saman abincin ta cakude dasu. Yau daya sai ta tsaya kawai tana kallon abincin,wani irin rashin dadi takejin zuciyarta tana mata a yau din,a kasalance ta maida kayan ta kuma rufe ta maidasu ma'ajiyarsu sannan ta dawo ta soma daukansu zuwa dining don yau kwata kwata ma bata bari zuwaira ta shigo mata ba. Batason doguwar magana,hakanan batason sanya idanu da wannan shegen binbinin kallon da take binta dashi a kowanne daqiqa. Dab da zata isa dining din saita dinga ji kamar qamshinsa. Batasan ya akayi ba.....amma tun daga waccan ranar ta haddace wannan nataccen qamshin turaren nasa da har yanzu yake maqale jikin rigunanta guda biyu. Sosai takejin qamshin,to amma ta raba idanunta ko ina cikin parlor din bata ga wani alamun shigowarsa ko shigowar wani ba. Agogo ta sake kalla sanda take ajiye warmer din,mintuna kadan ya rage ayi sallar magariba.....wannan lokacin kuwa ba lokacin dawowarsa gida bane,don qarfi da yaji ta haddace lokacin dawowar tasa saboda yadda ta aza dukka damuwarta akan cikar burinta na yaci abincin. Watsar da tunanin tayi,taci gaba da shirya komai ta kammala,ta tsaya kawai tana kallon yadda komai yake jere saman dining din. "Inama ace yau daya burina ya samu ya cika?" Ta furta qasan ranta duk da tana jin wani sashe na zuciyarta kaman yana qyamatar hakan ya faru,sai kuma ta juya tana nufar hallway din da zai sadata da dakin. Dab da zata shige laila ta murda pivot door din tana shigowa falon tayi kwalliya sosai cikin wani silk material da aka tsarawa dinkin daya dace da shape din jikinta sosai. Red ne colour dinsa wannan ya sanya farar fatarta data samu gyara da pills na qara fari da allurai na qara hips da sauransu ya sake qawata shigar tata. Kome takeyi tana da cikakken goyon bayan hajja wadda a kullum burinta ta fita daban,ta kuma zama daban din ta kowacce hanya cikin mata. Idanu suka hada,sai sabreen din ta dauke idonta kamar kullum,ta kuma taka a nutsenta tana wuceta,tana jin bata da wani lokaci nata sam sam. Da idanu ta raka sabreen da wani irin kallo na qurilla,allurar kishi tana tsikararta,tana tambayar kanta da wanne irin products haka take amfani masu tsananin qarfi?. Tana ji ana cewa kowanne dan adam tara yake bai cika goma ba.....to amma ita sai take ganin tamkar a halittar sabreen goma take cif cif!. Tsaki taja tana maida dubanta kan dining din. A yunwace ta shigo,ta samu zuwaira kuma bata nan,tabbacin a yau kenan saita shigo da kanta neman abinda zataci. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 41 _Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_ __________________________ Matsawa taci gaba dayi zuwa wajen dining din,tana cike da haushin yadda a kullum ake jigilar qawata wajen da warmers na alfarma wadanda suke bata tabbacin abinci ne lafiyayye.....to amma kullum idan ta tuna maganar da hajja ta gaya mata akan abincin sai ta maida qwalamarta bisa tilas. Asali ita din mutum ce da ba kasafai ta fiya bawa irin wadannan abubuwan muhimmanci ba. Hasalima tana ganin idan ba dominka aka shirya abu ba bazai taba tasiri a kanka ba. A nutse ta isa wajen,ta kuma jawo warmer din farko ta soma budeta,budewar da ya qara adadin yunwar da takeji taji kuma bata da wata hanya illa ta toshe yunwar dake sakadar mata hanji kamar bata taba cin komai ba. Yau gajiya takeji sosai a jikinta,wannan ya sanya data idar da sallah isha'i wanda duka zama tayi a wajen bayan magariba sai data yi isha din sannan ta tashi. Wannan Dabi'arta ce qwaya daya da har yanzu bata rabu da gangar jikinta ba,burbushin raino da tarbiyyar ummensu,bata wasa da sallah sam koda bayan gushewar ummen,kuma ita kanta ta hori 'yan uwanta sosai akai (Ko hori yaranku da sallah.....tana da matuqar tasiri wajen hana bawa sabon Allah da kuma gyara halinsa,kamar yadda Allah ya fada cikin qur'aninsa me girma,tabbas sallah tana hana alfasha da munkari,Allah ya bamu dacewa ameen summa ameen). Tana shirin shiga wankan saita samu kanta da maimaita addu'o'in data karanta a littafin da anni ta bata wanda shi ya qara sanyata jin dadin zaman. Tana nanata addu'o'in suna tuna mata da zamanin da suke qananu......lokacin da ummee ke korasu makarantar allo ranakun weekend,ita hadiyya da sameeha. Qaramin murmushi ya kubce mata,tadan girgiza kai tana jin kewar lokacin quruciyar tata,tana jin inama tana da ikon dawo da wancan lokacin,ashe ba abinda yakai zamanin quruciya dadi. Pyjamas ta saka baqaqe gaba daya da suka sake haska mata fatarta,sai ta dora qaramin farin Malaysian hijab saman kanta bayan ta nannade gashinta a tsakiyar kanta cikin ponytail holder,hakan ya sanya kan yadan tashi kadan kamar tayi acuci maza na. Fararen flip flops ta zurawa fara tas din qafarta,wadda duk wani lalle ya fita a jiki,sai tsantsar haske daga qara da gogewa kamar jini zaiyi tsartuwa. Hankalinsa na rarrabe akan wayarsa sanda yake qarasowa cikin falon. Daidai lokacin da laila ke saukowa daga dining din sai ya zamana mutum na farko da idanunta suka fada a kai. Cak ta tsaya ana zare duk wani noti na jikinta,wannan shine karon farko data taba gaba da gaba da muhammad jadda,kusan duka a baki ko cikin magazines da news paper take ganinsa. Duk yadda tasha fasaltashi a zahirinsa ya wuce nan,wani irin ingarman namiji da a iya tafiyarsa kadai ta hangi izzarsa da kuma cikar isarsa. Kaman a jikinsa yaji ana kallonsa,wannan dalilin ya sanya daga idanunsa yana duban sashen da yaji jikinsa yafi rinjaye. Suna hada idanu gaba daya kwarjininsa ya mata wani irin mamaya data gaza riqe kanta,duk wata zarra da jin kai da takeji tana dashi a matsayinta na diya mace ya sulale yayi nasa waje. Yadda ya kafeta da idanunsan nan masu qunshe da wani sirri sai taji komai yana kwance mata "Barka da dare" Tayi namijin qoqarin furtawa bakinta yana son hardewa "Yauwa" Kawai ya amsa mata dashi. "Nice laila....'yar gidan hajja.....hajja harira ta maamah" Tayi bayanin a nata zaton hakan zai burgeshi ko kuma ya sake bata matsayi na musamman a matsayinta na 'yar aminiyar mahaifiyarsa. Fuska yadan yamutsa kadan yana fahimtar inda ta dosa. "Yayi kyau.....ban fadi muku banson kowa around us ba idan ina gida?" Yayi maganar fuskarsa na wadace da wani irin daurewa kamar baisan sunan wani abu waishi dariya ba,don dama da bacin rai ya sauko. Kasaqe tayi tana mamaki,tabbas zuwaira ta shaida mata,amma ko a sannan kallon banza ta watsa mata ta wuce dakinta,don tana ganin ita ta wuce wannan dokar tayi aiki a kanta. Tana jin kanta tamkar ita din halastacciyar 'yar gidan ce,don haka bata ma wani tsaya amfani da dokar ba bare ta kiyayeta. Tana shigowa a duk sanda taso tayi abinda takeso ta fita,saidai da yake dukkaninsu ba ma'abocin zaman falon bane kowa sabgar gabansa yake shi yasa ba wanda ta taba karo dashi a cikinsu. "Get out of my sight......and kada ki sake bari mu hadu" Ya fada cike da zallar umarni ba tare kuma daya kalli sashen da take ba yaci gaba da tafiya kansa tsaye zuwa dining din. Ajiye wayoyinsa yayi bayan ya gama abinda yake,ya maida hankalinsa ga abincin yana dubansa. Yau zai kawo qarshen duka wannan drama din ya ayyana hakan a ransa,daidai sanda take fitowa daga parlor din zuwa ainihin falon da yake ciki. Kai tsaye dama idanunta kan dining din suka fada,don ya zame mata wani aiki na daban kiyaye waye a wajen da kuma duba waiko ya zauna cin abincin?. Bataso yadda tashin farko suka hada idanu ba don zaya dauka ne kawai kallonshi takeyi,take tata izzar itama ta motsa,ta dauke kai sosai tana takawa zuwa qofar kitchen. "Hey.....com here" Ya fada da matsakaiciyar murya. Tanason gwada masa tsiwar amma tana tsoron abinda zai biyo baya,dole ta dawo din fuskarta shimfide da kalar nata miskilancin. "Serve me" Ya fada cikin basarwa yana bude wayarsa. Cak ta tsaya,tana jin kamar kunnuwanta ne suke jiye mata ba daidai ba. Ta zuba masa abincin fa ya buqata?,ta tambayi kanta tana neman qarin haske. "Zuba abincin nace" Ya sake maimaita mata ba tare daya dubeta ba. Wani irin abu taji ya tsargawa sassan jikinta. Ta dade tana fatan zuwan wannan ranar,ta dauka duk sanda taxo din zata kasance mutum da tafi kowa murna a duniya,amma kuma sabanin murnar mutuwar jiki taji. Matsawa tayi sosai gaban table din,ta ware qananun luxury table mat din ta sake shimfidasu,sannan ya zari plate da bowl ta soma zuba komai tsaka tsakin quantity sannan ta jera masa a gabansa. Wayar ya ajiye a gefansa,ya miqa hannu da kanshi ya ciro spoons guda biyu ya saka cikin abincin sannan ya dubeta "Oya.... Let's eat together" Ya furta yana matso da drinks din da aka aje a wajen duk da ba abun shansa bane sam sam duk wani drink da company ta sarrafa. Ba shiri ta bude idanunta a kansa,ji tayi kaman an dauko guduma an shirga mata. Cikin qasa da minti daya tayi qoqarin daidaita nutsuwarta dukka a qoqarinta na daidaita komai,ta girgiza kai tana fadin "Na qoshi". Sake ware idanunshi sosai yayi a kanta yana dubanta,abinda ya sake sanyata kenan a tsilla tsilla,tana kyautata zaton akwai wani abu me nauyi da idanunsa ke dauke dashi,wanda muddin ya kama zuzzurfan kallo irin wannan sai kajishi har qashinka. "I think kin fito ne ke debi abincin right?" Daburcewa tayi yanda ya kama abinda ya fito da ita din kansa tsaye kamar me gani har hanji. Bata saba qarya ba koda wanne irin hukunci aka tanadar mata,wannan ya sanya kai tsaye ta bashi amsa da eh. "Good.....kinga wannan shi yafi kamata muci tare ko?" Ya fada cikin sigar saukar dakai yana turo abincin gabanta. Kanta ta sake kadawa,gaba daya yana birkitata ganin yadda yake matsantawa saita zauna sunci abincin "Seat down!" Ya fada da wani irin husky voice yana buga hannunsa saman table din har abincin dake cikin plate din yana watsewa saman table din. Batasan sanda ta zauna ba kaman yadda ya buqata tana qoqarin kaucewa kallon fuskarsa da har hancinsa ya fara yin ja alamun tsananin bacin rai wajen farin mutum kenan. "Kinsan abinda zan gaya miki guda daya?" Yayi maganar qasa qasa kamar ba shine yanzu ya buga wannan tsawar ba,bai jira ta amsa ba ya dora da fadin "Duk sanda kika qara yimin girki a gidan nan saikin cinyeshi tsaf!". Gigicewa ta sakeyi da abinda yace,maganar daya fada kawai ta sanya hasashenta ya tsaya daidai inda take zatonsa "Be warned!" Ya furta yana ranqwafowa sosai saman kanta har tana iya sheqar dumin numfashinsa da yake futarwa daga hancinsa. Baya yaja ga kwashe wayoyinsa,zuciyarsa na masa wani irin zafi ya soma sauka daga wajen yana dosar hanyar da zata sadashi da stair dinsa. Maamah uwarsa ce,ba yadda zaiyi da ita,amma zaiyi dukkan abinda zai iya ya toshe kowacce qofa da zata samu nasarar budeta a kansa ko kuma waninsa muddin yana da iko da masaniya. Koda ya koma saman duk yadda yaso yayi keeping kanshi busy ya manta da komai sai ya kasa. Mahaifiyarsa......macen daya biya kudade aka daura mata igiyarsa..... A duniya idan akwai wasu mata da sukafi kowa kusanci dakai suna sama da wadannan ne?. Me suke nema a tare dashi?,amsar daya kasa laluba kenan. Sosai abun ya dinga masa ciwo,shi yasa ko sau daya bai taba aminta da ita ba,ko sau daya bai taba jin ya gamsu da ita ba......takowacce fuska tana da qatuwar lam'a da tabon da shi shine babbar shaida......bayan tarin shaidun da ya samu har abinda be nema bama an bashi,ta yaya zai iya kallonta a matsayin wankakkiya?,ta yaya zai iya yafe mata?. Yanason ya zame mata lesson me girma a rayuwarta,zai kuma ganar da ita kuskurenta na shiga rayuwarsa hakanan kai tsaye. Daga qarshe dai dole ya kunna karatun qur'ani daya karade ilahirin sassan nasa,yayi kwance kawai idanunsa a lumshe sautin yana shiga kunnensa,sannu a hankali kuma nutsuwa ta fara samuwa a jikinsa. Ko qwaqwaran motsi kasa yinsa tayi ballantana ta tashi daga wajen,batasan adadin lokutan data shafe zaune a wajen ba,har sai data daga idanu taga agogo yana gaya mata qarfe goma da rabi saura mintina biyar sannan ta iya miqewa. Zuwa sannan hatta da qafafunta sunyi wani irin nauyi da sanyi,saita gaza shiga kitchen din ta zarce hallway din sannan ta fada dakinta. Rasa abinda ya kamata ta tuna tayi,ganinta yayi kenan koko yaya?. Karon farko da taji wata irin nadama na saukar mata. Ya akayi ta biyewa mamah din ta yarda ta ciyar dashi gubar da batasan ranar yankewarta ba?,wacece maamah din?,me kuma take qullawa?,me take buqata ne a rayuwarta sama da rayuwar da take ciki?. Zafi sosai takeji cikin ruhinta,tunda take bata taba sha'awar ciyar da wani ko shayar d wani wani abu me illa irin wannan ba,koda sanda take shirya gyara zaman mazan da suka zabi harka da mata kuwa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 42 _Daba abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace "mafi falalar sallah bayan sallar farilla itace sallar dare_ *_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqa😄,Allah ya bada ikon jurewa_* ____________________________ ★Qarfe tara na safiyar alhamis ce wadda aka wayi gari da lullumi qwarai,sakamakon hadarin farko daya fara hada jikinsa tun bayan sallar asubahi. Bai bada ruwa ba amma kuma ya yiwa rana shamaki daga fitowa tayi rawar gaban hantsi kamar yadda ta saba kowacce safiya saman sararin samaniya. Yanayin sai ya haifar da yanayi me dadi da kuma sanyaya zukatan da suke cikin wani yanayi. A irin wannan lokacin ne muhammad jadda mamallakin kamfanin jadda diamondchore resources yake saukowa a hankali daga samanshi. Cikin shigar aiki,saidai kuma yau zaka dauka juma'a ce saboda shigar kaftan yayi. Dinkin zamani daya zauna masa sosai,ya kuma fidda sigar kyan nan nasa da kana kallonsa zaka tabbatar tabbas halfcast ne shi din wato ruwa biyu. Cikin parlor din ya samu tuni ameh ya kammala shirya masa komai na breakfast dinsa. Ameh din shi ya koma masa girki tun bayan wancan abun daya faru,yaja daya daga cikin kujerun wajen ya zauna ameh din ya gaidashi cikin rusunawa. Amsawa yayi da kulawa sannan ya fara serving nasa,yana yi yana dibansa da labarai,wanda kusan dukansu labaran da suka fita ne a jaridar safiyar. Ameh din yana da karance karance da yawan sauraran kafafen yada labarai,don haka a mafi yawan lokuta idan bai samu damar duba news paper ba shike bashi latest na cikinsu. A nutse ta maida littafin amdatul ahkam da take dubawa,ta kuma d'auki zaduzzaujaini ta sakashi a ciki don yin alama akan inda ta tsaya din. Saman side bed drawer tayi masa kyakkyawar ajiya tana jin wata nutsuwa tana ratsata. Sati guda kacal kenan da fara karatunsu da rumaisa'u d'iyar malam amma wani nutsuwa takeji da gamsuwa da karatun. Rumaisa'u din da tayi tsananin mamakin ganinta a matsayin malamarta da ya dauko mata domin daukan karatun addini a hannunta. Zuwanta kusan uku tana rejecting tana qin fitowa......sai ana hudun ta fito da zummar yiwa malamin ko malamar bayanin ta daina wahalar da kanta tana zuwa......ta gayawa wanda ya aikota dalibar bata da buqatar wani karatun. Ganin rumaisa'u din sai ya zagwanye komai daga zuciyarta,ta cika da mamakin zuwanta gidan,saidai daga baya rumaisa'u din ta gaya mata "Hamma muhammad tsohon dalibin malam ne" "Gwara da kika ce tsohon" Sabreen ta furta a ranta. Don tako ta ina bataga ta inda ya dace ko ya cancanta mugu maqetacin mutum kamar fu'ad din ba ya hada alaqa da malam ba. Daga haka ba wani zance daya qara shiga tsakaninsu,sai hiran duniya kawai da kuma karatun daya biyo baya. Da farko kawai dai tana sauraren rumaisa'u dinne,amma karatun kwata bayayi mata wani armashi ko burgeta. Saidai lokaci guda kuma a rana daya data arawa rumaisa'u hankalinta sai taji karatun ya fara shiga kanta,mafari kenan data fara hada hankalinta da zummar Tsintar abinda ta Tsinta,saidai tafi tafi sai ta fahimci karatun yafi qarfin ka tsinta kawai. Ita kanta rumaisa'u mamaki takeyi ainun....mamakin yadda karatun yake gudu saboda yadda suke qara karatun da yawa. Ta sallama da gaske karatun yana gudu ne saboda wata irin sharp brain da Allah ya bawa sabreen din,irin kwanyar da bata taba ganin irinta ba. Don duka karatun da sukayi da yammaci,zuwa wani yammaci din sabreen din ta narkashi ya koma cikin kwanyarta. Tun asali tana da bala'in son karatu,musamman na addini din,saidai wani dalilin me zuwa ya ture wani. Ratayuwar hidimar qannenta saman wuya da kafadunta ya sanya tilas ta haqura da komai ta tattara ta ajiye,a yanzun kuma data fara shiga cikin abun sosai sai takejin komai kamar an yaye mata wani hijabi ne da da ya lullube kwanya da idanunta. Tun sanda ta fahimci ya ajiye cook dinsa cikin gidan saita saita lokacin ta,sanda zata fito tayi sabgarta daga shi har cook din nasa basa gidan,hakazalika kafin su dawo ta kammala komai ta koma daki abinta. Tayi mamakin yau da taji yunwa da safe da wuri haka,to amma kuma idan ta tuna ba wani abun arziqi take ci ba musamman jiya da dare bata saka wani abu me muhimmanci a bakinta ba sai taga ba abun mamaki bane. Indonesian hijab down squeeze ta saka saman soft and cotton nigh gown din jikinta da bata fidda siffarta ba,saidai tadan lafe mata a mazaunai saboda taushinta. Hijab din ya qara qawata mata fuska,fuskar data fita sosai ta tsakiyar hijab din da wani irin kyau kai kace itama haifaffiyar Indonesia dince. Ta qarasa gaban mirror ta qara turare a jikinta dan kadan kamar yadda ya zame mata wajibi,sai ta tsaya tana duban fuskartata. Wani irin glowing skin dinta yakeyi wanda ita kanta ta rasa dalili,saidai a yawancin lokuta tana bawa kanta amsa da wataqila zaman guri daya ne,sabanin baya da kullum muddin gari zai waye rana ta fito to zata saka qafarta a waje ta fita. A hankali take tako hallway din,yau kawai tana jin nishadi cikin ranta sosai da cikakkiyar nutsuwar da batasan dalilinta ba,kwanyarta tana bitar wasu daga cikin karatuttukan data haddace,a haka ta rasa parlour na farko ta wuce zuwa na biyu. Tana murza glass door din ta sanyo qafafunta ya daga idanunsa a hankali daga inda yake zaune ya zubesu fes saman fuskarta,idonta ya shiga nasa,sai ta janye nata idon a hankali,ta kuma ja da baya tana komawa da bayan a maimakon fitowa da tayi niyyar yi. Sam bata qaunar gamuwa dashi,a kwanakin data janye kanta daga komai da zai sanya su hadu ta kama karatunta sai take samun wata irin nutsuwa a zuciyarta. Ta dauki kwanaki rabon daya sanyata cikin idanunsa,daga shi har maamah sai takeji kamar Allah ne yayi mata maganin matsalarsu. Janye nasa idanun yayi shima bayan ta koma da baya tana kuma komawa ciki. Yadan jijjiga kai kadan yana daukan mug din gabansa ya sanya a bakinsa. Tana gyara bedroom dinsa kamar yadda sukayi sharadi,saidai daga wannan ko gilmawarta bai sake gani ba tun daga ranar. Can qasan zuciyarsa tana cike da wasi wasi da kuma qiyasi akan abubuwa da dama. Sai yake zargin shurunta dana maamah dukka kamar akwai wani magana a qasa,don haka ya jawo wayarsa ya kira me sunan malam. Cikin qasa da second ashirin suka gama magana,ya shaida masa ya nema farouq ya turo amintacce kuma sirrintaccen me musu installing CCTV. Mules din qafarsa ya maida,sannan ya ciri napkin guda daya yana goge dan abinda ya bata masa hannu kafin yace da ameh. "At night.....ka dafa paw paw leaves ka ajiyemin da duminsa.....daga yau inaso ya zama first drink dina for morning". Kai ameh ya jinjina cikin girmamawa "As you wish sir". Sai ya sauka a nutse amma hankalinsa yana dan kan qofar kadan,yanason sake tabbatarwa komawa tayi ta fasa shigowa saboda yana wajen?. Murmushi ameh yayi yana binsa da kallo,sosai boss dinsa yake burgeshi,yayi aiki kafin wajensa gidajen manyan attajirai da dama,amma baiga mutum me kiyaye lafiyarsa da yasan sirrin abinci ba irin boss din nasa ba. Yasan duk wani abu da zai gyara lafiyarsa a matsayinsa na namiji,yasan duk wani abu da zai gyara masa lafiyar ido da fatarsa,hakanan yasan duk wani abu da yake natural anti aging remedies kala kala. Ire iren abubuwan da shi yake tanadarwa manyan da yayi aiki a qarqashinsu don inganta lafiyarsu da gina garkuwar jikinsu suke qin ci ko sha don ba dadi a baki ko basusan muhimmancinsa ba......sai gashi shi kullum ne sai an tanadar masa da wannan abun morning and evening. Akwai hadin salad daya dinga mamaki sanda yaga yana cinsa farkon xuwansa,musamman da yake yasan yadda yake inganta qarfi da lafiyar d'a namiji,da yawan wasu abubuwan ma shike qaruwa dashi a wajensa. Baya son maggi da yawa a abinci,kaman yadda sanyi zaqi da kuma maiqo da abokansa bane sam sam (Mata da yawa suna complain din rashin lasting din mazansu a other room,sunsha magani sunsha maganin amma a banza,anata samun sabani da sauran masu matsaloli,to wallahi wallahi da yawansu maggi shine yake kashesu,inda kinsan yadda maggi yake kashe lafiyar mazajenmu da kinyi mugun gudunsa kuwa,kiga mace ta saka farin magi a abinci,tazo ta saka wadancan cubes din kala daban daban,ta hada drink ta laftawa miji sugar,ga uban sanyi,abinci mai yana kwanciya,ba ruwanki da manja ma sam sam,to billahillazi kunji na rantse muku haka zaita zame miki mace,kuma duk irin maganin da zaisha fa a banza,muddin ana kan cin magin nan,tashi daya ba zaki iya dainawa ba,amna gradually zaki dinga janyewa,idan goma kike sawa ki koma bakwai daga haka ki koma hudu,tabbas indai zaki dimanci haka zaki ga canji,ki ajiye farin maggi kwata kwata,zaqi da maiqo duka ki rage masa,hadin wancan salad din in sha Allah zan kawo muku shi a gaba,ya gwada cin na sati biyu bayan kin janye magin kiga ikon Allah,koda me gida yana da lafiya ma normal ne kina iya hada masa shi ya dinga ci,amma ina maimaita muku ku raba kanku da kayan d'an d'anon nan,Allah yasa mu dace). Kamar kowacce safiya muddin yana da isashen lokaci......ba baqi ba meeting na early morning da sauransu,zuwa duba lafiyar anni da gaida maamah din yana cikin schedule dinsa na kullum. A farfajiyar gidan kamar ko yaushe ya samu guard dinsa,kowa na tsaye akan aikinsa. Bai qaraso bama amma tuni Jordan ya buda masa bugatti dinsa yana jiran qarasowarsa. Cikin girmamawa da nuna kulawa suka gaidashi ya amsa yana bincikar lafiyar kowa kaman kowacce safiya,sai daya tabbatar da kowa lafiya sannan ya miqawa saddiq da kusan a makare yake isowa kayan hannunsa,wannan dalilin ya sanya baya samun shiga cikin gidan duk zuwan da yakeyi. Sun dauki hanya sosai kiran musaddiq ya shigo masa,ya fidda wayar yana connecting nata da Bluetooth dinsa yana amsa wayar. "Hamma na gama komai......sai yaushe zan dawo?" Musaddiq din ya amsa a karye da alama gida yakeson dawowar. "Ka dawo kayi me?" Ya tambayeshi yana jin tantama a dawowar tasa. "Hamma nayi missing anni......nayi missing saddiq". Iska kadan ya furzar daga bakinsa wadda ta fita da qamshin mint leaves saboda mouth fresh dinsa kenan na dindindin " Anni kuna waya haka saddiq.....kuma ko ita nasan bata da damuwa me yawa a tafiyarka.... Dude ne kawai nakeji ban kyauta masa ba dana dauke masa personal assistant......shima nasan ya fahimceni.....oops......anyways......nan da sati biyu zamu hade a madeena in sha Allah,it was family trip time". Har a muryarsa yaji dadi "Hamma na Manta da lissafinma.....okay..." "Hope komai naka ba matsala ko?,daga can zaka iya shiga koda Jeddah ne sai ka qaraso madeena" "Direct entry zanyi hamma.....i can't wait to see my family". "Alright....ka kula da kanka" Ya furta cikin kulawa "Na gode hamma" Ya ambata suna ajiye wayar. Wayar ya zubawa idanu yana tuna wasu abubuwa da suka shude..... Ita rayuwa dukanta tana komawa tarihi ne watarana......bai taba zaton a rintsin da suka fuskanta shi da musaddiq ba akwai ranar da zatazo kamar haka komai ya wuce ba......yadda kula da musaddiq da bashi rayuwa me kyau ya sanya hannuwansa sukayi kanta.....tunaninsa ya dimauta,kwanyarsa ta kusa jirkicewa da daina iya tuna kome me kyau.....ambaton sunan maamah ya zame musu kamar wata jarabawa. Hannunsa yasa ya shafi fuskarsa yana son ajiye tunanin a gefe.....yanzu yanzu zai iya rasa kowacce nutsuwa tasa,ya kuma rasa duk wani courage na aiki daya fito dashi a yau din. "Gidan maamah zai fara tsayawa" Yace da saddiq don ya shaidawa driver din shi kuma ya sanar da ayarin motocin. Yayi hakanne don yasan muddin ya shiga gidan maamah a yanayin da yake ciki na tuna munanan abubuwan data aikata baga rayuwarsu kadai ba......anni itace zata zamewa zuciyarsa yayyafin ruwan sanyin da zai wanke duk wani baci da ransa yayi. Kamar kullum da qafa ya taka daga inda suka ajiye motocin zuwa cikin gidan. Malam sa'adu ya matso da sauri yana bude masa qaramar qofar kasancewarsa shugaban masu gadi na gidan a yanzu. Tunda aka mallakawa maamah din wannan gidan yafi qarfin gadin malam sa'adu shi kadai,dole sai daya hada mata da security,amma kuma kowa yana qarqashin malam sa'adun ne wanda shike da permanent chair. Har kullum burgeshi hali da dabi'ar muhammadun takeyi,ya taka dukkan wani matsayi da bawa zaizo ubangiji ya kaishi a rayuwa,amma bai dauki hakan a bakin komai ba. Gaisawa sukayi kamar kullum,sannan ya taka yana shigewa cikin gidan da ma'aikatan dake bakin aiki kowa yake zubewa yana gaidashi. Daidai sanda yake sallama a falon daidai sanda take fitowa daga kitchen din gidan,Hannunta dauke da qatuwat warmer kamar ma rinjayarta takeyi. Huda ce,ta bishi da kallo tana amsa sallamar tasa cikin kallon baqunta. Yadan sake dubanta kadan,sai yake jin kamar yasan fuskar,amma kuma sai ya kauda wannan tunanin yana neman wajen zama,daidai sanda take gaidashi cikin ladabi daya zame musu jiki tun tale tale "Ina kwana?" Ko daya maida dubansa kanta sai yaga har ranqwafawa tayi irin na ban girman nan "Lafiya la....." Amsa gaisuwar ta katse saboda yadd warmer din taso subuce mata daga hannunta. Cikin zafin nama ya isa ya karba yana fadin "Kibi a hankali......" Sai ya taka yana kaita saman dining din ya ajiye. "Maamah ko?" Ta tambayeshi qasa qasa kaman me tsoron tambayar,don itadai yana mata kama da mijin adda sabreen din su. Kai ya jinjina kadan a ransa yana mamakin ina kuma maamah ta samota?. "Bari na kira maka ita" Ta fada da dan saurinta,can qasan ranta yana cike da murna,yau kam taga wani daya danganci addansu.....ko gaisuwa ta aike mata tunda yawan lokuta maamah tana cewa ta kira basa kusa. Wayar hannunta da maamah ta bata kuwa da komai akai,hasalima suna waya kusan kullum da momma bahijja,amma batasan me yasa number adda sabreen din kota kira sam sam bata shiga ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 43 A step na biyu taga maamah din tana saukowa daga saman,hannunta cikin na haneefa daketa bata labari. "Yammatana ya akayi?" Ta tambayi huda tana dan sake mata murmushin nan nata da kusan sun sana dashi. "Baqo ne kikayi" Ta fada tana dan waiwayawa inda fu'ad ke zaune,hannunsa dauke da remote yana sauya tasha,bawai kuma don yanason kallon bane aah....sai don kawai bayason kallon fuskar maamah din sakamakon abubuwan daya tuna da suka motsa ranshi. "Muje to" Ta amsata har qasan ranta tana jin dadin yadda huda din ta kasa gane wanene. Tanason sanyata ta koma daki don kada suyi wata magana da zata fahimci wayeshi a wajensu?,amma kuma ta rasa wanne uzurin zata bata tunda dai abinci zataci akan dining. Uwa uba kowanne motsi nata da maganganunta tana yinsu ne a ankare,bata bari tayi wani abu da zai sanya shakka a ransu ko ta gaza juyasu yadda takeso. Tunda suka sauko din haneefa ta zubawa fu'ad ido. Tabbas shine mijin adda sabreen,ta ganshi har sau biyu bata kuma mance ba,sannan bata sake ganinsa ba sai yau. Saman kujerar maamah ta zauna,haneefa ta zauna a gefanta still idanunta suna kanshi ta kasa daukewa. Sanda ya gama gaida maamah din sai nasa idanun suka sauka akan yarinyar. Kamanninta suka fusgi idanunshi sosai,ya sake ganin wata kamar ta daban bayan wadda ya baro dazu tana me komawa falo bayan sun hada idanu. Murmushi haneefa ta sakar masa sanda taga shima ya dan kafeta da ido. Ya murmusa kadan tana shirin janye idanunsa sai yaga ta zame tana fadin "Ina kwana mijin adda sabreen?". Kallon mamaki yake bibta dashi,mamakin da bai gama sakinsa ba tace "Sunana haneefa nice autan adda sabreen,'yar mitsisiyar dakinmu". Baisan ya akayi murmushi ya ratsa miskilar fuskar nan tasa ya bayyana ba,ashe masu son sarautar autancin suna da yawa. Yanayinta sak sai ya tuna masa da yanayin amna. " Ya isa haka haneefa....kije kuyi break ko ki koma daki wajen nadra ku kalli cartoon" Maamah tayi hanzarin dakatar da tattaunawar tasu. A nutse ya cira kansa yana duban fuskar maamah din,haka kawai sai yaji yana da buqatar ci gaba da magana da yarinyar. "Qyaleta muyi hira maamah....she's very smart" Ya fada da wani irin tone a muryarsa,wasu abubuwa da wani irin gudu suka fara bijiro masa,yayin da gumi ya fara tsargawa maamah ta cikin rigarta. Ta sani,tafi kowa ma samin haneefa she's very smart,fiye ma da zatonta,wannan ya sanya tafi janta a jiki da kuma kaffa kaffa da ita. "Indai surutun haneefa ne saika gaji dashi......ni kuma magana nakeso nayi dakai,next time idan kazo sai kuyi hirar" Ta fada tana dan hade rai gami da gyara zama. Sake dubanta yayi a karo na biyu,abubuwa biyu suka hade masa waje guda. Har yanzu dabi'ar nan tata tarashin son yara tana nan?,banbanci qarara me kuma fadin gaske na farko tsakaninta da anni. Indai haka ne yara uku ne cikin gidanma kenan?,akwai daya a cikin daki?. Me ya kaita dauko yara har uku?,ita da basu dameta ba?. Meye abun damuwa don yana hira da yarinya qarama?. Agogonsa ya kalla,sai ya maida dubansa ga fuskarta. "Ba damuwa ai,yau muna da enough time sama da kullum". Kafin ya sake cewa wani abu haneefa tace " Zaka kaini naga adda sabreen?......don Allah hamma kada kace aah" Ta fada tana narke murya. Maganar taja hankalin huda dake saman dining,itama saita ajiye spoon din abincin da takeci ta maido hankalinta kansu. Gumin dake tsatsatsafowa maamah din ya sake yawaita,da sauri kamar ana tankadata tace "Aah fa haneefa......ni da kaina mukayi zan kaiku haka ne?". "Eh amma har yanzu baki kaimu ba maamah,shi kuma hamma ma daga can yake ko?" Ta maida tambayar kansa. Kansa ya gyada a nutse yana karantarta. "Maamah ki barshi ya kaimu ko anjima ne,in yaso saimu dawo da kanmu" Huda itama ta saka baki,don da gaske sunyi tsananin kewar sabreen din. Sanda ta waiwaya da nufin yiwa huda din magana sai maganar fu'ad ta dakatar da komai. "Jeki dauki hularki kuzo muje nasa a ajiyeku" Yayi maganar kansa tsaye,maganar data daki tsakiyar kan maamah da wani irin ba zata. Har ga Allah kanshi tsaye ya fada kuma hankalinsa kwance,kawai dai a cikin zuciyarsa ya dade da rashin aminta da kowanne motsi na maamah din. Bashi da gamsuwa akan abubuwa da yawa sa suka shafeta,shi yasa a kusan komai idanu da zuciyarsa suna akai. Cikin qasa da minti uku sai gasu kowacce da mayafinta. Dab da zasu fita daga falon ta kirayi sunan huda da yanayin da tunda hudan tazo gidan bata taba gani cikin muryarta ko sautinta ba. Fuskarta a dinke ba fara'ar nan da suke kwana suke tashi da ganinta akan fuskarsu "Kada ku wuce ko ina,daga can ko dawo gida,zanwa driver magana zai biyo bayanku,karku wuce awa daya......." Idanu huda tadan zuba mata,sai kuma kawai ta gyada kai mamakin sauyawar maman tana kamata. Tasha musu alqawarin fa zata kaisu.......sai kuma daga baya tace ai wani uzuri ne ya taso sai bayan wani lokaci,duk da ta lura akwai permanent driver a gidan da yake zaune baya aikin komai. Yana zaune daga cikin motar saidai qafafunsa suna a waje ba'akai ga rufe masa murfin ba suka fito. Yadan daga kai ya kallesu,dukkaninsu suna kama da ita saidai qaramar ta fisu daukan kamanni sosai da ita. Mamaki kadan yana dan kamashi na ganin banbanci muraran tsakaninsu. Dukkansu da alama suna da sauqin hali da kuma tarbiyya sosai,don ba wanda ya gaidashi a tsaye a cikinsu saida suka rusuna "Ta fita zakka kenan" Ya gayawa kansa da kansa yana sauko qafafunsa qasa ya fito waje. "Abdulgaffar" Ya kirayi shugaban tawagar tsaron nasa,ya matso da gaggawa yana rusunawa "A cire mota daya a sakasu a kaisu gida" Ya bada umarni hankalinsa yana kan kiran fareeda dake shigo masa. Kaman yadda baya gajiya da qin dagawa hakanan itama bata gajiya da kiran nasa,yaja wani dogon tsaki yana komawa motar,ranshi yana tsananin baci da kalar wannan kiran nata da dukkanin numbers dinsa,kamar wadda batasan abinda ya dace ba,baisan ma ya akayi take da dukka numbers din nasa ba. "Soulmate" Sunan da tayi kiransa dashi kenan da wani irin salo na kashe murya da jan ra'ayi. "Why?.....ke bakya gajiya da kira ne?,it's so annoying.....please don't do it again.....stop it" Ya fada da sautin bacin rai a muryarsa. "Haba ka fahimceni mana" Ta sake fada da hanzari cikin tsoron kada ya katse mata wayar..... Kada ya ajiye wayar bayan ta samu dama ya daga wayar bayan dukka wahalar da tasha "Na fahimci me?....ke bakya ganewa cewa macace ke?,ke ya kamata abi bawai kibi ba?.....kina mantawa mace da kamun kai aka Santa?.....". Da sauri take girgiza kai "Indai a kanka ne bani da wadannan qualities din....." "Okay....then karki sake kirana....." Yaja qaramin tsaki yana yanke kiran hadi da jan dogon tsaki yana wurga wayar gefe. Gaba daya soyayya tana sake tona masa kanta a matsayin wani abu da yafi komai zama matsala da takura a rayuwa,shi yasa bazai bari ta kunno rayuwarshi yanzu ba har sai sanda ya shirya ya kuma kebe mata lokaci nayin nata. Idanunshi akan motar BMW din da aka sanyasu a ciki,sai da yaga fitarsu a gidan sannan yayi musu umarni suka tashi motocin suna fita suma daga layin. Sauke labulen window din da yake bata daman ganin farfajiyar gidan tayi cikin wata irin matsananciyar fargaba da kuma tashin hankali. Gaba daya kowacce idea tata ta kunce,ta rasa wanne zaren tunani zata kamo?. Wacce irin baqar rana ce yau?,wanne tsautsayi ne qaddara ya sanyata lokacin shigowarsa ya kubce mata har ta saki yaran haka?. Idanunta ta mayar saman agogo......sai a sannan ta lura,yau ya sabawa lokacin shigowar tasa ne,ya shigo da wuri ba kaman yadda ya saba ba,sai tasa hannu tana sharbe gumin fuskarta da tafin hannunta. Da dan hanzari ta taka da kanta tana fita farfajiyar gidan tana qwalawa mansir kira,kiran daya sanyashi sakin duk abinda yakeyi ya qaraso babu shiri. "Ka fito da mota,kabi bayan motar jadda diamond zuwa gidan muhammadu......akwai yara da sukaje gaida matar gidan,suna shiga minti goma kacal ka aika su taso ka dawomin dasu......mansir?,idan ka kuskura aka samu akasi baka maidominsu akan kari ba to ka kuka da kanka......ban yarda ku biya ko ina ba......ban kuma yarda ka ajesu ako ina ba" Ta fada tana zare idanu tanaji a jikinta tamkar wani abu zai faru. "In sha Allahu ba zaa samu ko daya daga ciki ba" Daga haka saita juya tana komawa ciki. Kasa zama tayi ko a cikinma,a jikinta takejin kamar akwai wani abu da ba daidai ba "Ki kira zuwaira kisa ta kula miki da motsinsu" Wani sashe na zuciyarta ya bata shawara. Bibbiyu ta dinga hada stairs din tana haurawa samanta,cikin lokaci qanqani ta isa dakinta,ta zauna gefan gado tana daukan wayarta dake saman drawer ta fara kiran zuwairan. Saidai kash!,kiran farko aka shaida mata kwata kwata wayar a kashe take,ta sake gwadawa cikin rashin gamsuwa da bayanin farko na na'urar......still sukace mata yana a kashe,ta sake dai gwadawa a karo na uku,nan dinma amsar dukka daya ce,saita ajiye wayar a gefanta tana jan wani matsiyacin tsaki *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 44 _Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_ "Tur da halinki zuwaira,Allah wadai da halinki" Ta fada tana cika tana batsewa,har cikin ranta tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan da kanta. To amma kuma idan tayi duba ga wasu abubuwa,hakan bame yiwuwa bane,dole taci gaba da zama tana gwada kiran akai akai,yayi da idanunta ya ta'allaqa akan agogo tana qidanye da mintunan fitarsu daga gidan. Daga qarshe ta sare kan samun xuwaira,to amma dole tana da buqatar kiran wani da zame zame mata garkuwa a can gidan "Laila" Zuciyarta ta tunasar da ita. "Yauwa" Ta fada da madaukakin zumudi,ta soma lalubar number wayar lailan. Duk da safiya ce amma ta kusan awa guda da rabi a gidan nasu. Cikin asalin dakin da yake shine mallakinta,saman gadon sun qule ita da mahaifiyarta hajja harira wadda ta tsareta da idanu bayan ta gama zayyane mata karonsu da fu'ad na qarshe. Sai da tayi kaman ba zata daina kallon nata ba kafin taja wani tsaki tana dauke dubanta daga kanta. "To wai meye ma amfanin zamanki a gidan laila?,kada ki zama albasa mana wadda batayi halin ruwa ba?,na kaiki gidan badon kin rasa wajen zama ci sha ko sutura ko kuma gata cikin naku gidan ba.....na kaiki ne saboda ki karanci komai.....ki haddace komai ki kuma bi kowanne taku da motsi na kowa a gidan kafin mu fara gabatar da namu shirin koda kuwa.mariya batayi nasara ba......nasarar mariya ko faduwarta ba damuwata bane.....hasalima inda zata fadi hakan shine daidai a tare dani......kinsan me?" Kai laila ta girgiza tana jin faduwar gaba da kiran sunan maamah da akayi. "Nasarata itace ya kamata ta fara samuwa......nasarata ita ya kamata ta fara wanzuwa kafin ta mariya........ni ya kamata na fara samun fu'ad na mallaka miki shi......muddin mariya ta rigamu samun fu'ad to ba shakka dukkan wata nasara da muka sanya rai a kanta zata iya zuwa mana da tsauraran hanyoyi da matakai......shan kai nake da buqata mu yiwa mariya laila.....donme kikaje kika kwanta kina bacci?,waye ya gaya miki nasara na zuwa ta sameka har inda kaka?,bakisan fita ake a nemota ba?!" Tayi maganar da alamun qunan rai a cikin muryarta,hatta kuma da lailan ta karanci haka,saidai batasan me yasa a kwanakin nan takejin sam bata da damuwa akan wannan lissafin na hajja ba......tamkar wannan lissafin an zare mata shi kwata kwata daga zuciyarta. "Ban sauka ba hajja......kawai dai saina dinga jin kamar idan mukayi hakan bamu kyautawa maamah ba,kamar idan mukabi komai a sannu zaifi....." . Baki kawai hajja harira ta sake tana kallon laila da wani mamaki daya taru a fuskarta,kuma koda ta zubawa lailan idanu saita karanci da gaske take maganar. Tana shirin yin magana aka turo qofar aka shigo. Madeena ce dauke da serving tray data jero dukka kayan dadin da aka dafawa hajjan a matsayin abincin safe. Tun asuba take tsaye don kawai ta faranta mata,kuma bata da tabbacin zata yaba ko kuma tayi accepting abincin gaba daya. "Gasu hajja an gama....." Ta fada tana rusunawa ba tare data iya hada ido da ita ba. Wani abu me nauyi da girma ya riga ya sauka a zuciyarta game da zancan laila,don haka bacin ran daya taso mata maimakon ta huceshi akan laila sai ta fara ragewa akan madeena "Wannan wanne irin iskancin banza ne?,ina ciki muna sirri da yarinya saiki wani bankowa mutane daki?". Murya a karye cike da ladabi tace "Kiyi haquri,kin manta ke kikace idan na gama na kawo miki a daki zakici" "Naji da Allah.....koma dashi ki aje saman table......tsnnnnn" Ta qarasa da tsaki. "Awnnn..... Me dame kika dafa mata ne?" Laila tayi tambayar tana maida dubanta ga madeena wadda je tiri tirin fita da tray din. Ido kawai hajja ta zubawa laila tana mamakin yadda take nuna halin ko in kula da magana me muhimmanci irin wannan. Dawowa madeena tayi ta durqusa ta bude mata dukka bowls da warmers din,sai lailan ta karyar da wuya. "Wallahi meat pie nake mugun kwadayin ci da safen nan.......don Allah hadamin yaji naman rago cikin sosai" Ta fada kanta tsaye da sigar umarni. "Tom" Madeena ta amsawa lailan wadda a qalla tayi qanwa ta hudu da ita,ta miqe ta kwanukan tana sauka. "Idan da a rayuwa tsaiwa ake duba abinda ya kamata......inda a rayuwa jira ake sannan ayi abinda ya dace........tabbas ke kanki da baki juya matan yayunki kamar haka ba" Hajja tayi zancan tana tsare laila da ido tare da qoqarin maida mata girman zancan cikin zuciyarta. Dan muskutawa laila tayi tadan kashingida,har yanzu a ranta ita batajin damuwar komai,duk da kuwa bayan kowacce daqiqa sai hoton kyakkyawar fuskar nan tasa ta gilma ta gaban idonta,abinda ke sakata sakin ajiyar zuciya lokaci lokaci gami da sakin qaramin murmushi. "Inaso komai sauya.....inason ki canza akalarki daga yau.......dole gobe ki dawo ki karbi naki kayan aikin......ki kula da zuwaira......banason tasan komai.....bana son kuma ta fuskanci komai" Ta fada tana tsareta da ido. Saidai bata kai ga amsawa ba wayarta dake saman kanta ta dauki tsuwwa. Tana daga kwancen ta daga kanta tana duban me kiran,saidai ganin sunanta kadai ya sanyata wani irin zabura hadi da tashi zaune. Hakan kuma baiyi mata ba sai data zamo daga saman gadon ta durqusa a qasa sanda take daga kiran hade da sallama. Dukka wadannan abubuwan da tayi su suka ja hankalin hajjan sosai taji tanaso taji da wanne mutum me matuqar girma da daraja haka a rayuwarta take waya?. "Ina kwana maamah.....kin tashi lafiya?,kiyi haquri inata zuci zucin na kiraki na gaidaki da safen nan.....amma na kasa tuna waye zan kira". Maganar ta yiwa maamah banbarakwai,to amma bata wani kawo komai a ranta ba,duk da laila bata taba mata magana da ladabi rusunawa da kuma kirki irin haka ba "Ba komai,kina gida ne zan baki wani aiki?". Rawa jikinta ya hauyi saita miqe tana daukan mayafinta "Bana gida maamah.....amma bani minti goma sha biyar yanzu zan isa gidan,saiki gayamin abinda kikeso ayi miki ko mene". Mamaki kadan ya sake kamata,to amma a yanzu garkuwa kawai take nema don haka ta amsa mata da "Okay......idan kika isa ki kirani" "Ko kibar wayarma kawai on hold karki kashe yanzu yanzu zan isa,zanyi sauri ma saboda agama komai da wuri". Wani mamakin dai still ya kamata,amma sai tace " Zan sake kiranki" "To" Ta amsa mata tana sauke wayar. Jakarta ta kaiwa sura,kamar ma ta manta da hajja dake wajen,kowanne sashe na jikinta rawa yakeyi,ta jefa wayar a jaka ta rataya tana yafa mayafinta. Sai a sannan hajja da mamaki ya kasheta ta kira sunanta da qarfi "Waike da waye kike waya haka lokaci guda hankalinki ya tashi?". Murmushi ta sakarwa hajjan sanda take saka takalminta "Maamah ce fa?,ta tambayeni ne ina gida?,wani aiki zata sakani kinga ya kamata na koma ai.....bai kamata ma ace na fita ban tambayeta ba,amma zan bata haquri daga baya.....hajja na tafi,idan na gama mata da wuri zan tambayeta,idan ta barni gobe na dawo zan dawo". Mamaki da ganin almarar abun ya hanata cewa komai,ta sanqame a wajen kawai baki bude tana bin laila da kallo wadda keta sambada sauri kamar zataci da baka. *_turqashi?,wai meke faruwa?,nace meke faruwa ne jama'a?,shin qaiqayi ne koma kan masheqiya ko kuwa yaya?,wanda lamarin nan ya yiwa dadi ya danna 1😂,wanda baiji dadi ba ya danna 2_* *_gasu huda a hanyar zuwa gidan addansu,yaya zata kasance kenan?_* *_yanzu wasan zai fara tafiya daidai💪🏽_* *_muje zuwa🙌🏽_*45 _Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_ Ware idanunta tayi sanda ta isa dining area,sai ta tsaya cak tana sake ware idanunta da kyau tamkar wadda bata gani sosai,kwanyarta na gayawa zuciyarta kawai yaudarar kanta takeyi,basu huda dinta bane.....ba nadra a wajen......auta haneefa tana hannun waccar azzalumar "Adda.." Muryoyinsu suka zame mata kamar tsani a gareta na tashi daga wani dogon mafarki,kamar wadda aka daki bayanta,sai ta fara nufarsu tanason ta tabasu don ta tabbatar shin su dinne?. Allah ne kadai ya sauko da ita daga steps din,don qafafunta hardewa kawai sukeyi har zuwa sanda ta isa garesu. Haneefa da tafi kusa da ita ta jawo,ta miqa hannu tana shafar fuskarta,sai kuma taja hannun huda ta riqe d kyau,sannan ta dafa kafadar nadra. Murmushi suka fara yi mata,da alama sun gane abinda take nufi,kuma dariya sukeso suyi mata,saidai yanzun ba Lokacin dariya bane. "Ku tsaya a nan ina zuwa" Shine abinda ta fada kenan tana juyawa ciki cikin gudu gudu sauri sauri. Ko ina a jikinta rawa yakeyi,batasan ya akayi suka kubuto ba,tana ji a jikinta addu'ar data tsananta a wannan Lokacin Allah ya karba mata. Birkice closet dinta tayi wajen neman hijab daya tamkar idanunta basa gani,da qyar idanunta suka nuna mata wani ruwan sararin samaniya,ta sanya hannu ta fuzgoshi ta saka,sannan ta dawo falon. "Ku taso......ku taso mj tafi" Ta fada da wani irin hanzarin daya sanyasu tsaiwa kawai suka zuba mata idanu,har sai data fusgi hannun nadra da haneefa sannan huda ta biyo bayanta a mamakance. Tana riqe da hannuwansun take ratsa farfajiyar gidan,girmanta yasa take ganin kamar ba zasu fita daga ciki ba maamah zata riskesu,kamar tayi nisa da yawa. Security da sauran ma'aikata nata zubewa suna gaidata,amma ita ba wannan bane a gabanta,don ko gane gaisuwar nata basa yi. Kai tsaye kuma a karon farko security suka bude mata gate ta fice. Taci gaba da jan hannunsu da wani irin sauri da kaf rayuwarta bata tana yin tafiya da irinsa ba "Ina zamuje adda?,ko zama baki barmu munyi ba?" Haneefa ta tambaya adan shagwabe saboda saurin da suke zubawa din ya fara isarta "Zaki gani auta......karki damu" Ta ambata tana duban hanya,daidai sanda ta hangi tahowar motar da tafi mata kama da motar da akan kawo maamah a ciki. Hagu da damanta ta duba,ba wani gurin labewa. Unguwa ce da dukka gine ginenta ke bisa tsari,layukansu shimfide da wadatacciyar kwalta,manyan gidaje da kowanne gate yake a kulle dame gadi ko kuma kare. Cikin ikon Allah ta hangi gida daya da qaramar qofar dame gadi kan fito a bude,saita jasu zuwa can ta kuma turasu ciki itama tana me shigewa. A gabanta motar tazo ta wuce da gudu,saita sake kamo hannun haneefa tana cewa "Kuzo mu tafi" Zuciyarta na tsananta bugu qwarai. Sai da sukayi tafiya me nisa kafin su samu adaidaita sahu,kasancewar unguwar unguwace ta masu kwalli masu hannu da shuni,zai wahala kaga abun hawa na haya a cikinta. Koda zai shigo ma sai ainihin security da suke gadin unguwar sunyi checking sun tabbatar da amincinsa da ingancinsa. Basa wasa ta wannan fannin saboda dukka unguwar manyan mutane ne a cikinta. Sai data tabbatar me abun hawan yayi nisa da unguwar sannan ta sauke ajiyar zuciya,ta juya a hankali tana kallonsu sai taga dukkaninsu ita suka zubawa ido,da alama qarin bayani suke nema. Murmushi kawai ta saki,ta dora hannunta saman kansu ta shafa tana cewa "Zakuji komai......bari mu isa". Kamar yadda zama ya gagareta haka tsaiwar ma sai taji kamar tana neman gagararta. Wani tashin hankali takeji mara misaltuwa,yaran su kadai ne hope dinta,idan har tayi loosing yaran tabbas bata da wani sauran hope. Yadda take juya yarinyar tayi imanin bawai girman asiri bane.....don dama ya bata tabbacin abun bame qarfi bane,idanma me yawan addu'a ce kwana uku zai saketa. In kuma me qarfin kurwa ce da tsananin hasken taurari sati biyu zuwa wata daya zai iya sakinta. A yadda take maida mata magana da tsananin izza da rashin tsoro,ta tabbatar komai ya saketa,kawai tana biyeta ne saboda yaran da suke hannunta.......idan babu su ya zata kaya mata kenan?. Wani tashin hankalin ya sake rufto mata data tuna da waya fa a Hannun huda. Ita ta siya mata ita sati guda daya wuce kenan data sake jawota jikinta. Yau idan sukayi amfani da wayar suka kira wani fa?. Abinda ya sakata rarumar tata wayar don sake kiran zuwaira ta karbo mata wayar ko da qarfi ne,tana me manta ma wayar zuwaira din a kashe take. Cikin sa'a bugu biyu ta dauka,muryarta na nuna alamun bacci. Ashar ta lailayo mata wanda ya sanya zuwaira miqe ta zauna da duwawunta "Dama bacci na aikeki kiyi?Kinsan aikinki kuwa?,kinsan muhimmancin abinda na aikeki kiyi zuwaira?!" Maamah ta tambaya a tsawace tana jin kamar ta jawo zuwaira daga cikin wayar ta zabga mata mari. Rawa jikin zuwaira ya dauka,batason tayi asarar maamah tun yanzu alhalin bata samu tudun dafawa ba. "Kiyimin aikin gafara hajiya......tuba nake" "Ki rufemin baki,ki tashi ki dubamin cikin gidanku,daga parlor din matar gidan har bedroom dinta,akwai qannenta da sukazo,ki fara karbamin wayar hannun babbar,minti goma kuma nace ki qara musu su taso ki biyosu har sai kin kawominsu gidannan". "Angama ranki ya dade" Ta fada tana miqewa da hanzari har dankwalinta yana faduwa,duk da ranta a bace yake ainun da irin tsawar data daka matan. Parlor ta duba na farko dana biyu duka ba kowa. A kitchen ta samu ma'u tana juye mata kunun a flask gudun kada yayi sanyi jin shuru bata dawo ba. Ido suka hada mau ta dauke dubanta a wajen. Haka kawai jininsu baizo daya da zuwairan ba,duk da ma'u bata nuna mata komai,saidai ita zuwairan cike take da haushin ma'un ganin yadda sabreen din ke mu'amalantarta sama da yadda take sakar mata. Ko ina na gidan ta duba,tana shirin fita farfajiyar gidan ta duba can sai ga laila ta shigo afujajan "Ina matar gidan?" Lailan ta tambayi xuwaira. "Ban sani ba nima" Ta bata amsa cikin jin haushi zuciyarta tana raya mata itama aikin dubata ta bata. Dole data gama dube dubenta ta dawo parlor din,daidai sanda ma'u ta kammala komai tazo ta rabesu tana ficewa abinta ba tare da tace da kowa komai ba. Dukkansu qoqarin kiran maamah suke don kowa ya fara shaida mata yadda ake ciki. Laila ce ta fara samunta,cikin tsananin biyayyar data sanya zuwaira sakin baki tare da tunanin ko wani sabon makircin shiga jikinta suka qullo ta tsaya tana dubanta "Maamah kaman bata gidan nan fa?". Wata zazzafar zufa ce ta karyo mata,taji kamar gudawa zata tsinke mata. To amma yaushe suka shigo da har za'ace basa cikin gidan?. "Kun duba ko ina da ina?" Kai laila ta girgiza tana duban hallway din "Banda bedrooms dinta" "Me kuke jira?,ku dubamin har can" Ta bata umarni a tsawace har sai da wayar hannun lailan ta kusa faduwa. "Zan shiga na duba" Lailan ta fada tana duban zuwaira. Wani kallo ta watsa mata tana samun daya daga cikin kujerun ta zauna tana tabe baki. Da karsashinta ta soma nufar dakunan,har cikin ranta tana jin dokin shiga taga dakunan ya suke?,tunda koda hallway din bata taba takawa ba bare akai ga shiga ciki. "Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa lokacin dame napep ya ajiyesu a qofar gidan. Sai a sannan hankalinta ya dawo jikinta,ta tuna bata riqo komai a hannunta ba. "Don Allah dan yi haquri,bari a karbo maka kudinka,fitar ce ba'a tsanake ba" Ta fada tana dubansa. Bai wani damu ba sam,saboda yanayinta kadai ya tabbatar masa idan bai samu qarin abinda ya kamata a bashi ba to tabbas ba za'a rageshi da komai ba. Waiwayawa tayi ta kalli su huda "Ku shiga ciki ku karbomin dubu biyar wajen titi". Huda ce tayi gaba suka bita a baya. Basu jima ba nadra ta fito da kudin ta miqawa sabreen din,ta karba ta bashi sannan suka wuce cikin gidan a tare. Tana sallama aishatu ta fara gani,tana duqe tana wankin uniform dinta daga can bakin famfon da akayi musu saboda hidima irin wannan. Tadan zubawa yarinyar idanu farinciki yana ratsata. Ko a iya aishatu kawai idan ta kalla tana jin wani farinciki da sassauci yana ratsata,kamar ba aishatun da aka debe tsammani da rayuwa da ita ba,kamar ba aishatun da idan ka fita ba zakayi tsammanin zaka dawo ka sameta a raye ba. Sai data dago don yin shanya suka hada idanu,ta watsar da uniform din,ta rugo da gudu tana kiran sunanta "Adda sabreeennn" Ta maqaleta da kyau,sai itama ta tsugunna tana rungumeta cikin jikinta qwallar farinciki na sauka a idanunta. "Aishatu......haka kika koma?......alhamdulillah" Ta fada tana shafa sumarta me santsi. "Adda na warke.......na samu sauqi adda" Ta fada itama tana kwantar da kanta a kafadarta. "Ki barta ta qaraso ciki mana aishatu" Muryar titi ta ratso kunnuwansu tana dubansu cikin murmushi,daga nesa kuma tana kallon yadda sabreen din tayi wani irin kyau,fatarta ta qara tsananin haske da wani irin murjewa,sai glowing takeyi duk da tadan fada kadan qibarta ta ragu. Tana riqe da hannun aishatun suka shiga parlor din titi. Duka sauran yaran falon suka miqe don basu fahimci ita ake magana ba. Dukkaninsu suka baibayeta suna qoqarin kiran sunanta,sai ta zame kawai ta zauna tana rungumesu cikin jikinta gaba daya tana kiran sunansu daya bayan daya. Ruwa da lemon zobo da titi din ke saidawa ta dire musu tana zama gefanta. Sai a sannan yaran duka suka tashi suna ficewa don basu sarari. "Banyi zaton sake ganinki nan kusa ba" Titi ta fada bayan sun gama gaisawa da gaske farinciki yana nunawa saman fuskarta,duba da sanin babban mutumin data aura. Murmushi sabreen din tayi wanda yakai mata har zuci,musamman data tuna daga rana irin ta yau ta nesanta maamah din da rayuwar qannenta kenan,nesantawa ta har abada "Me zai hana titi?,ban fara fita bane kawai" Ta amsata tana gyara zamanta "To ma sha Allah,ubangiji ya sanya alkhairi,ya bada zaman lafiya ya kade fitina". Bata amsa duka wadannan addu'o'i na titi din ba,sai tace da ita "Alfarma nazo nema titi don girman Allah" Kallonta titi takeyi wani yanayi yana bin fuskarta "Haba sabreen.....haba don Allah,aike din kifi qarfin alfarma......saidai bada umarni kawai" Murmushi ta saki tana girgiza kai,har yanzu suna mata wani madaukakin kallo. "Su huda na kawo miki,inaso kuma ki riqemin su zuwa wani lokaci,don Allah titi ko nan da qofar gida bana so su leqa idan zai yiwu bare sukai ga fita waje.......akwai gagarumar matsala da take tunkararmu gaba daya,akwai masu bibiyar rayuwarsu,ki kulamin dasu don Allah". Sosai maganar ta shigi titi,saita girgiza kai tana fadin "Aiko su din ba jininki bane sabreena sai inda qarfina ya qare......ba abinda bakiyi mana ba,banda ke da Allah ya jefo mana da yanzu bansan a wanne bigire rayuwarmu take kai ba......zan kula miki dasu fiye da yadda kike muradi" "Na gode titi......kina da tsohuwar waya da bakya amfani da ita?" "Banga abun godiya a nan ba,hasalima kamar wajibi na na aikata.....akwai wayata da kika canzamin sanda zamuyi tafiyar nan......bari na dauko miki ita" "Idan zan samu da wata wayar daban zanyi kira" Ta fadi tana qoqarin hada numbers din momma a kanta. Banda tana da kaifin basira da saurin riqe abu ba yadda zata iya hada number wayar momma din,saidai cikin ikon Allah ta hadasu tsaf ta kuma kira zuciyarta na bugawa da fatan ta kira daidai. Bugu uku aka daga,muryar momma ta mamaye speaker din tana amsawa da sautin da yake kama sak dana ummensu,sautin da har tata mutuwar ta risketa ba zata manta dashi ba. "Mom......momma" Sabreen din ta kirata bakinta yana rawa idanunta suna cika fal da hawaye. "Sabreena?.......kun dawo?,yaushe kika dawo?" "Daga ina?" Ta tambayi momma din a mamakance qwallar idonta suna tsagaitawa. "Tafiyar da kukayi mana ke da me gidan.......ko sanda zan koma ai naso haduwa dake dole sai hannun surukarki nabar qannenki.......saboda dole sai passport dinsu ya zama ready.....duk dama dai munyi magana tana ta iya bakin qoqarin ta,kuma kusan kullum sai munyi waya da yaran". Mamaki ya sandarar da sabreen,sai ta bude bakinta a hankali "Momma me ya faru?,ban fahimta ba,ita ta nema ki bata su?"46 "Eh kusan hakanne,don naso ganinki ban samu ganin naki ba......tafiyar tawa bata shiri bace......abbansu ne rashin lafiya ta taso masa,dole kuma ana buqatata a kusa,a yadda na tsara zan jira passport din nasu da komai ya kammala,amna dole na tafi saboda jinyarsa,saidai ba inda zan barsu don ban aminta da hannun kowa ba. Randa nake wannan tunanin saiga surukarki Allah ya jeho ta. Ita ta roqeni na bata yaran zata sanya mai gidanki yayi magana don a kammala basu komai da wuri,tace kuma zata turosu ko ta kawominsu da kanta,to amma lokacin da nayi tsammani ma sai gashi har ya gota. Kawai abinda yake kwantarmin da hankali duk sanda mukayi waya da yaran alamu suna nunamin basu da matsala ko damuwar komai". Kai kawai sabreen ke jinjinawa tana sake girmama kaidin maamah din. Ta tabbatar ita zata kawo tsaiko a samun fasfunansu,wataqila ma kuwa an samu ta riqe ne taqi gayawa momma din. Tanason ta yiwa momma bayanin da zata fahimceta,amma kuma bataso ta daga mata hankali. Tana ji a jikinta zata iya komai,kuma wannan lokacin kamar wata dama ce da Allah ya ara mata akan maamah din "Momma" "Na'am sabreen" "Komai da kike kallonsa a haka yanzu a zahiri ba'a haka yake ba........abinda zance rayuwarsu tana cikin hadari babba........basa hannunta yanzun suna wani hannun na daban,saidai bana son ki gayawa kowa,don Allah mommma......koda ta kiraki kiyi kaman bakisan abinda yake faruwa ba.......in sha Allah nan da kwanaki kadan zan turosu su biyoki". Shuru momma din tayi tanaji a jikinta ba lafiya "Amma sabreen me yake faruwa?". "Ba wani mummunan abu bane momma,kada ki tashi hankalinki.....kawai dai komai kiyishi kamar bakisan anayi ba" Kai ta jinjina bawai don hankalinta ya kwanta ba sukayi sallama. Tana ajiye wayar ta sabule zobunan hannunta guda biyu na gold,ta kama hannun titi ta zubasu tana kallon idanunta. "Yanzu bani da contact na kowa.....inaso ki saida wannan,ki nema mutumin da ya muku visa na fita india ya yiwa su huda duka su ukun komai,inaso kada su wuce sati biyu a nan don Allah titi". Zobunan ta kalla sannan ta maida dubanta ga sabreen "In sha Allah.....zanyi duk yadda zanyi na miki abinda kikeso". Kai ta jinjina tana jin wata nutsuwa tana saukar mata. Murya ta daga ta kira huda,ta shigo ita daya,abinda ya sanya titi miqewa don basu guri. "Ina wayar hannunki?" Ba musu ta dauki wayar daga kan cinyarta ta miqawa sabreen din. Saita karbeta tana juyata a hannunta. Waya ce me asalin tsada da kyau wanda kusan sai wane da wane. Idanunta ta maida fuskarta tana kallonta "Huda baki dago komai ba?,bakiji komai ba game da matar da aka kira da sunan uwar mijina?" Tayi mata tambayar kai tsaye tanason samun wani abu daya danganci maamah. Shuru hudan tayi,tana qoqarin recalling komai,tun daga ranar farkonsu cikin gidan kawo yau. Siririyar ajiyar zuciya ta sauke,a hankali ta maida dubanta ga sabreen "Inajin kawai batamin ba.....duk kirkin da take gwadana mana sai nakeji jini na da nata kaman bai hadu ba.......sannan yadda take mana kirki kaman ba haka dabi'arta take ga masu aiki qarqashinta ba" Hudan ta fadi abinda da gaske haka takeji a zuciyarta take kuma hasashe. Wani siririn murmushi sabreen ta saki tana saukar da kanta qasa gami da juya wayar hannunta. Anzo daidai gabar da tafiso.....anzo daidai wajen da zata gwadawa maamah shege......anzo daidai gurin da zatayi wasa da hankali da kuma tunaninta kamar yadda mage kanyi da qadangare ko bera a duk sa'ilin da yayi gigi ko kakambar shiga hannunta. Daukewa murmushin fuskarta yayi lokaci guda,ta maida kallonta kan hudan "Ina fata ba wani abu na cutarwa data taba muku......idan kuma akwaishi ko da da mugun kallo ne ina saurarenki". Kai ta girgiza tana kallon addar tata,tanason kuma fahimtar dalilin da yasa taketa mata tambayoyi haka "Babu kwata kwata adda......saidai kawai nidai hankalina ya kasa nutsuwa da ita... Musamman da ya zamana kusan ko yaushe tana mana alqwarin zata kawomu wajenki sai kuma ta gaza cikawa.....har sai da mijinki yazo.....shi yace ta barmu muje". Jinjina kai take tana duban huda dake bayani,fuad ne kenan.......me yasa yace suzo din?,shima akwai yiwuwar yana da nashi boyayyen manufar?. "Kinsan garkuwa tayi daku?,kidnapping a fakaice?" Tambayar ta zowa huda a bazata,ta zaro idanunta waje tana dafe hannunta saman qirjinta. "Kidnapping fa adda?" Kai ya gyada mata gami da lumshe idanunta,sai kuma tace "You are free in sha Allah.....zaku bi momma mali soon......abu daya nakeson na gaya miki ko bayan kun tafi......be smart as much as you can.......ki dinga amfani da kwanyarki da basirarki.....ki kula da nadra da Haneefa,ki zame musu garkuwa kamar yadda na zame muku.....sannan......ki zama mara saurin yarda da mutune,walau maza ko mata,a family yake ko a wajen family......saurin yarda tushen kowacce rushewa ce" Ta qarasa maganar tana nunata da yatsa. Iska ta zuqa sosai sanda take cikin napep din sannan ta furzar da ita waje,tana jinta kamar mutumin daya dauki dutsen dala da gauron dutse yau Allah ya 'yan tashi ya samu saukeshi daga saman kansa. Sakayau take jinta,wani farinciki yana ratsata gami da iskar abun hawa wadda ta manta rabon data ratsata. Ta ware idanu sosai tana kallon titi.....Don yaushe rabonta data fito?,ko fitarta ta qarshe cikin rufaffar mota ne qarqashin kulawar jami'an tsaro. "Sabreena Ahmad AKA MUHSEENA" Sunan da taji an ambata kenan saitin kunnenta. Ko daga bacci ta tashi tasan waye?......wannan wata shaidace kuma stamp ne daya kasance nasa shi kadai. Mashkur....ta gayawa kanta da kanta,don haka ta tattara dukka nutsuwarta da qarfin halinta ta maida sashen da sautin ya fito. Shi dinne,zaune a seat din driver,ya dafe dukka hannuwansa saman steering din motar yana jifanta da wani zazzafan kallo. Duk da yadda haushinta da wutar son daukar fansa ke ruruwa a ruhinsa.......amma hakan bai hana shaidan harbawa zuciyarsa wutar matsananciyar sha'awarta ba. A yadda yake hangen wani lafiyayyen kyau a tattare da skin dinta......wani irin kyau da abaya fatarta bata sameshi ba,sai yakejin burinsa ya ninku zuwa gida biyu,YA DAUKI FANSA sannan kuma YA KASHE QISHIRWAR SHA'AWARTA A RANSA. Dadaddiyar qishirwar data maidashi sakarai kuma shashasha a kanta duk da tarin tsananin wayonsa. "Damn it!" Ya furta da qarfi yana dukan steering din motar tasa gami da cije lips dinsa gami da kashe mata idanu guda daya. Salin alin ta dauke dubanta daga kansa,tana jin wani matsanancin faduwar gaba yana saukar mata. Faduwar gaban da bata taba ji ba a kansa ko akan wani d'a namiji ba idan ka dauke fu'ad din "To ko wannan shine haqqin aure da kowacce mace kejin nauyinsa a kanta?" Ta tambayi kanta da kanta tana jinjina girman abun. Kafin ya sake cewa komai traffic light ya sakesu,motarsu ta riga tasa yin gaba. Cikin mamaki sai ta samu kanta da addu'ar kada ubangiji ya bashi ikon ganinsu har ya biyosu yaga gidan da take,duk da ta sani......gidan su zai wahala ya zama wani boyayyen gida da zai wahalar da za'a iya ganoshi. *MUHAMMAD FU'AD* Basuyi nisa can can ba ya tuna yabar file dinsa a gida,wanda file ne dake da muhimmanci ya dubashi a yau ya tura da bayanan cikinsa ga company din da suka nema sanya hannun jarinsu a kamfanin. Ba kasafai ya fiya son yin alqawari ba tare daya cikashi ba,idan har hakan ta kasance ta tabbas baida yadda zaiyi ne,don haka ya sanya su saddiq sukayi gaba,shi kuma suka juya da wasu motocin suna dawowa gidan. Wuri wuri zuwaira tayi ta shiga raba idanu sanda taji dirin shigowar motocin nasa harabar gidan. Raba idanu ta shiga yi sannan ta furta kalmar "Na shiga uku!" Bayan ta tuna gargadin da yayi mata a ranar daya fara ganinta. Yadda tasan halinsa ta kuma haddaceshi bata haddace fuskarsa haka ba,ta tabbatar yazo ya sameta a sassan kamar yadda ya gargadeta shan ruwanta a gidan ya qare. Wani abu guda daya da bata qaunar ya faru......zaman gidan yafi mata zaman ko ina......zaman gidan cike kuma yake da 'yanci,ba kyara ba tsangwama,hakanan ba nauyayen aikace aikace a cikinsa,sabanin gidan maamah din da yake cike da tsarabe tsarabe kala kala. Wuf tayi ta miqe tana dosar qofar da zata sadata da sassansu kamar zata ci da baka,cikin ranta cike fal da Allah ya qarawa laila tare da fatan ubangiji ya hadata dashi yaci zarafinta har fiye da tunaninta taga yadda abun zai kaya. Da nutsuwar nan tasa ya shigo cikin falon,idanunsa suna kan inda ta tsaya a dazun sannan ta waiwaya tana komawa ciki. Ya janye lumsassun idanunsa yana wucewa parlor na biyu,daga nan ya doshi qofar da zata sadashi da hallway da kuma stairs dinsa. Saurin ja yayi da baya kaman yadda itama taja da baya da sauri. Ya zuba mata idanu yayin da ita kuma kwarjininsa yaso bugar da ita. Bata shirya ba amma sai gata tana rusunawa gami da gaidashi "Barka da safiya hamma.....ya aiki?" "Kece laila?" Ya tambayeta yana dinke girarsa tsaf saboda yadda yaga abun ya masa wani iri. Ta yaya zata ratsa privacy dinsu ta shigo har nan wajen?,wani irin rashin hankali ne da ita matar gidan zata bari haka ya faru?. Shi din wani irin mutum ne me tsananin son privacy,kamar yadda yake da iyakoki akan komai daya shafi rayuwarsa.....kuma kowanne mutum da nashi iyakar. Murmushi ta saki tana wani karyar da wuya gami da rolling idanunta a kansa "Eh hamma.....nice.....baka gane ni ba?,nazo ne duba.....ammm.....ammm sabreen,maamah nason magana da ita da gaggawa,so kuma unfortunately sai na duba ko ina na gidan amma babu ita.....infact ma ta fita.....". Banbarakwai yaji maganar kamar da wani yare daban take magana. Ta fita?,zuwa ina kenan?,sannan da izinin waye ta fita?. Ajiye duka maganganun yayi gefe guda yana dubanta "What I have told you tun ranar farko?.....so ki hada kayanki kibar gidan nan" Yayi maganar da murya me kaushi dake cike da zallar umarni. Hukuncin ya daketa so sai hakanan ya mata tsanani,iya ganinsa data sakeyi yanzu ya sake tada tsimin soyayyarsa a zuciyarta,saita dubeshi a rikice "Amma hamma....maamah ce....." "Arguing won't help the situation" Ya fada da wani irin yanayi maras hargagi saidai kuma me ban tsoro ne a idanuwanta. Sum sum da wani irin sagaggiyar gwiwa tsoro da bacin rai ta miqe tana fita daga wajen. Ya bita da wani irin matsiyacin kallo,sannan yaja tsaki kamar zai tsinke harshensa. Har ya taka stair case din sai kuma ya dakata. Ta fita bata gidan?,maganar ta dawo masa fes cikin kansa. Juyawa yayi don tabbatar da abinda lailan ta fada,ya fara bincike gidan guri guri. Kaf ya gama duba ko ina a gidan,ya kuma tabbatar bata nan din. Wani wutar fushi yaji tana ruruwa cikin ransa,yana so yaje ya saukewa duka Securities na gidan,amna kuma wata zuciyar na gaya masa MARTABAR AURE koda sunanta MATARKA KADAI A FATAR BAKI. Samun kansa yayi da bin lafiyar daya daga cikin kujerun parlor din farko,yayi relaxing kawai a ciki yana jin yadda jijiyoyin kansa suke harbawa,ba abinda zuciya bata raya masa ba,ina ta tafi?,wajen su waye taje?. "Da igiyar aure na?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin yadda zuciyarsa yadda take tafasa. Bai taba tunanin akwai wata diya mace da zai bari tayi masa wasa da igiyoyin aurensa da ya biya sadakin daya nemo da guminsa ya bayar ba,kai koda sadakarta aka bashi muddin da sunan muhammadu fu'ad jikan jadda aka daura bazai taba bari wani abu ya gilmawa mutuncin igiyarsa ba......idan shi ya warwareta tofa wannan daya. Ba kasafai ake barin napep shiga unguwar ba,wannan ya sanyata dole ta sauka daga baya ta sallameshi,sannan ta fara takawa cikin nutsatsen takunta zuwa street din nasu. Duk gidan dake da security a wajen suna ganinta sai taga suna miqo gaisuwa da wani irin respect,abun sai ya shiga bata mamaki ita kanta. Wai har girma da matsayinsa yakai wannan?,sannu sannu sai taga alamun mamaki bisa fuskar duk wanda ya ganta tana takowa da qafafunta. A hankali taji alamun tafiyar tayar mota daga bayanta. Bata waiwaya ba,don tun can dama ita bame damuwa da abinda bai shafeta bane47 _Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya auri nana fadima,sai manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin sadakinta),sai sayyadina Aliyyu yace "ba komai a wajena" Sai manzan Allah S A W yace "ina sulkenka?"_ "Ameenatu" Taji muryar nan dai ta dazu tayi kiranta. Sai da taja numfashi sosai tana son danne bugun da zuciyarta keyi sannan ta waiwaya inda ya daidaita motarsa saitinta,yana zaune kusa da window yana murxa steering hankali kwance fuskarsa shimfide da wani shu'umin murmushi. "Na rantse wannan karon ba zaki sha ba......na miki wannan alqawarin muddin na haifu cikin uwata da ubana......lallai saina maida sha'awata a kanki......sai kuma na bankadawa duniya wacece ke bayan na maido kudadena cikin dukiyata......ki rubuta ki ajiye" Daga haka yayi saluting nata,sannan ya taka motar da gudu yana wuceta. Bata fasa takawa tana nufar gida ba,kamar yadda bata fasa bin bayan motarsa da kallo ba har ya qurewa street din nasu. Wata mahaukaciyar fargaba tana ratsa zuciyarta,sunan mashkur tare da cikakken sanin wayeshi yana gewa tunaninta,a haka ta isa qofar gidan,ta kuma yi tsaye tana duban dogayen katangun gidan kamar me karantar ilimin zanen gidaje. Tana wassafa yadda zai iya tsallake wadannan dogayen katangun mansion House din......tana qiyasta ta yaya zai iya wuce wadannan securities din da samudawan dake tsaron kowacce kusurwa ta gidan?. Tsaron gidan kadai ya dan sanyawa zuciyarta nutsuwa.....saidai kuma bai kore fargaba ko kuma ya mantar da ita wanene ASALIN MASHKUR BA. Gangar hankalinta bata dawo jikinta ba sai data sanya qafafunta cikin gidan,idanuwanta kuma sukayi mata arba luxury cars dinsa dinnan dake ajiye a parking lot na gidan. Sai yanzu ta tuna bata nema izinin kowa ba sanda zata fita,don sam ta manta hakan yana cikin wata doka dake kan kowacce macen aure.....baya ga haka.....a lokacin ba abinda take iya tunawa illa hanyoyin da zata nesanta rayuwarsu da maamah din. Da confidence din ba lallai su hadu ba har ta wuce daki.....ba lallai ma yasan bata a cikin gidan ba ta tura glass door din parlor din tana sanya qafafunta. Da bude qofar da haduwar idanuwansu lokaci guda ya faru. Iya kallon data gani cikin rusunannun idanuwansa sun bata wata fargaba da bata taba jinta akan kowa da komai ba. Dakiya ta aro ta azawa ranta,tana jin a ranta a yanzu daidai take da kowa a cikinsu.....ko shi ko mamarsa. Tana jin lokaci bijirewa dukka wani sharuda nasu yazo,tana jin abinda ya rage mata biyu ne......ta samu tabbacin fitarsu zuwa mali a sannan takejin zaman wannan qallagaggen gidan dama me gidan gaba daya ya qare mata. Cikin dakiya da basarwa taci gaba da takowa kaman bataga kowa zaune a parlor din. Tsaf ya gama karanta da kuma fahimtar abinda take shirin aikatawa. Ba za'a fishi sanin miskilanci take taken miskili da kowacce dabi'a tasa ba,sai ya dauke kai kaman bai damu da takunta ba,zuciyarsa na sake matsewa,ransa kuma yana qara baci har zuwa sanda ta raba tsakiyar falon. Ba zato ba tsammani ta tsinceshi a gabanta. Tsaiwarsa yayi mugun dab da ita,hucin fitar numfashinsa da wani irin dumi da yake bayyanar da bacin rai da zuciyarsa ke ciki yana sauka saman goshinta. Motsawa tayi da nufin ja baya don bata tazara a tsakaninsu qirjinta na wani irin bugawa,saidai da tsananin zafin naman nan nasa ya cafki hannunta yana matsawa da kyau "Daga ina kike?!,ina kika fita?,gurin waye kika je?" Ya tambaya a jere cikin tsawar data ratsa dodon kunnenta har sai data runtse idanunta. Tattara dukka qarfinta tayi ta sabule hannunta daga nasa,wanda ta samu sauqin hakanne saboda banguls din hannunta ya riqe saita zame ta barshi dasu,saidai ko taku biyu batayi ba ya rufo mata baya,sai ya zamana tana tafiya da baya da baya,shi kuma yana maida qafarsa kowanne gurbi data cira qafartata. Kowanne taku guda daya sai qwayar idanunta sun gauraya da nashi. Abinda take gani cikin idonsa batasan wanne iri bane......wani yanayi ne da bazata iya fasaltashi ba. Yana sake kunsatota yana sake maimaita mata tambayoyin da suke sake razanata,bata ankara ba taji ta bugi bango,tabbacin kowanne space ya qare mata kenan,sai tayi cak sanda ya iso dab da ita,cikken motsi idan tayi yana iya sata ta kasance cikin jikinsa. "Gurin wa kika je?,me kuma kikaje yi nace!" "Ban sani ba" Ta fada da rawar murya tana qoqarin daidata mode dinta. Ko kusa ko alama bata tanadi amsar da zata bashi ba.....shi kuma ya matsa mata da tambaya.....tambayar da ba abinda take mata sai qara fusatata......GURIN WA KIKA JE?,ME KIKAYI?,idan ya fada din sai taji kamar ha debo garwashin wuta ya watsawa sassan jikinta ne. Ba abinda yake tuna mata sai mummunar kalmar yawan mutane musamman na cikin gidansu suke jifanta da ita.....kalmar da koda ta nuna ta shanyeta tana iya hana idanunta bacci da wani matsanancin fushi da bacin rai.....shima irinta yakeso ya ara ya yafa yayi aiki da ita a kanta?,batajin kunnuwanta zasu iya jurar ci gaba da jin ana jifanta da kalmar da bata da masaniyar komai a kanta. Hannuwansa ya dunqule waje guda yanason hana kansa marinta da zuciyarsa keda muradin yi. Bayaso yakai hannunsa jikinta......baya so ta zama mace ta farko daya fara mari duk kuwa da yanajin ta cancanci haka. "Karki bari nayita maimaita maganata......ina kika fita ba tare da izinina ba?....wajen wa kika je?!!!!" Yayi zancan da wani irin qaraji daya sanyata curewa waje guda,kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa "Banje wajen kowa ba.....ni ba wajen wanda naje" "....You're going to regret messing with me,for the last time....ina kikaje?" Ya sake tambayar yana sanya hannuwansa duka biyun dake a dunqule ya daki bangon da take maqale a jiki ta saitin kunnuwanta. Abinda ya sake gigitata kenan ta saka hannuwanta duka biyun tana toshe kunnuwanta gami da rruntse idanunta. Zuwa sannan kowacce jarumta dake jikinta tabi ruwa.....ba abinda ya rage mata sai rauni daya narke zuwa kuka. Cikin qasa da second biyu ta tsinci hannuwan nata jikin nata hannun dake toshe da kunnenta yana saukesu,da wani irin taushi da sanyin murya taji yana fadin "Is okay......wanne irin matsoraciya ce ke?.enough,stop crying please" Bata qara tuna komai ba ta tsinci kanta saman faffadan qirjinsa,ya sanya hannunsa daya ya lullube bayanta,daya hannun kuma yana shafa gadon bayan nata da irin salon da uwa kanyi don lallashin jaririnta. Wani sassanyan qamshi dake ratsowa daga qirjinsa da kuma kowanne sashe na jikinsa ya cika hancinta da wani irin sanyi daya soma qoqarin daidaita yanayinta. Saidai hakan ya gaza samuwa,don qarasa rudata yayi,daga yadda kunnuwanta ke iya jin yadda zuciyarsa take bugawa kadai ya tabbatar mata fusatarsa ta gaske ce......amma me ya sanyashi sauya yanayi haka cikin qanqanin lokaci tamkar wahainiya?. To kodai yana da boyayyun aljanu da suke sauyashi haka da sauri?. Bata gama wannan tunanin ba muryar ma'u ta zame mata amsa "Ina neman afuwa ranka ya dade.....ayimin afuwa" Ta furta da tsananin kunya tana sadda kanta qasa. Bata taba tunanin zatazo ta samesu haka dab da juna ba,kwata kwata ma batayi tunanin suna nan ba,tasan me gidan dai ya fita......dawowar da tayi kuma tazo dubawa amna ko ta dawo?,don sun hadu ta daya qofar sai kawai ta shiga sassanta da taji sabreen din bata nan. Kai kawai ya gyada yana ci gaba da shafa bayanta kadan kadan "Hajiya amna ce tace nazo na duba kota dawo......" "......ta dawo.....amma batajin dadi,kice ta qaraso" Da sauri ma'u ta amsa ta juya tana ficewa a gaggauce. Kaman yana jira ne ma'u din ta fita ya saka hannunsa ya tureta daga jikinsa. Banda yana kusa da bangon daya bata kariya ba abinda zai hanata zubewa qasa. Da wani fusataccen kallo yake dubanta. "Kada ki dauka na yarda ne da abinda kika gayamin......muddin na bincika na samu wani abu na daban saina miki mafi munin hukuncin da baki taba tunani ba......hakanan duk ranar da kika qara gangancin fita koda qofar gidan nan ne ba tare da izinina ba......saikinyi dana sanin sani na........nan din gida ne da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta halas.....ba bariki bane ba ba kuma hotel ko gidan karuwai ba" Daga haka ya juya yana daukan file dinsa dake ajiye saman daya daga cikin kujerun falon yana ficewa da sassarfa. Wani irin kuka ne yakeson qwace mata amma tana hana kanta,don idan har kunnuwanta sun jiye mata daidai amna na gidan,kuma zata iya iskota koda wanne lokaci,dole ta tattaro dukka wani bacin rai tana hadiyeshi,saidai kuma abinda takeji yafi qarfin abinda zuciyarta zata iya dauka,sai bacin ranta ya zabi fita ta hanyar fitar hawaye daga idanunta zuwa saman fuskarta,ta lallaba tana neman kujera daya ta zauna a kai tana dafe da kanta. "Oh god........ damn it....." Abinda ya dinga maimaitawa kenan cikin mota yana saka yatsunsa cikin sumar kansa. Ya manta yaushe ne lokaci na qarshe daya fusata irin haka.....yaushe rabon da yaji zallar bacin rai irin wannan dake ratsa kowanne sassa na jikinsa. Ya alaqanta hakan da tozarta igiyar aure da yake shirin faruwa. Sai ya samu kansa da blaming kansa,me yasa zai daga hankalinsa har haka?,ai duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa. Ransa yaji yana qara baci,sai ya yiwa driver magana ya qara speed na motor din.48 _An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace,manzon Allah S A W yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta har gari ya waye_ *_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan qin da tayi kuma ta samu ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna ganin bata samu wannan shahadar da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_* *MAAMAH* Tunda ta cewa zuwaira taje ta duba mata su taci gaba da kiran wayarta ba qaqqautawa don ta matsu taji feedback,saidai kuma shuru ba'a picking wayar. Saita koma kiran wayar laila ita dinma duka sammakal. Kamar ta dora hannuwanta akai tayita rusa ihu haka taji,ta tsinewa zuwaira da laila a ranta batasan adadi ba "Dukkaninku baku da amfani" Ta fada da fushi,sai taji kamar ba zata iya zama ba....wannan karon zata tafi gidan fuad da kanta ne ta dubo meke faruwa ba tare da damuwa da komai ba. Tana taka qafarta kiran zuwaira ya shigo,tayi qoqarin hadiye fushinta tana fatar samun feedback me dadi,saidai amsar da zuwaira ta bata ya kusa sanyata zubewa qasa warwas "Bata gidan ita kanta.....kuma akan idanuna ta dawo ita kadai". Iya haka kadai ya bawa maamah amsar abinda taketa zulumin ya faru. Ta kwashesu,ta tseratar dasu,amma dai bata sare ba,tana da sauran hope,don haka kai tsaye ta fara kiran number huda. Kiran duniya computer ta gaya mata ta kuma jaddada mata wannan layin a kashe yake. Ta laluba wayarta kaf ta rasa number wayar bokanta tana me mancewa da cewa mutumin baya riqe waya,yo mutumin dake rayuwar tsakiyar dajin Allah ina gaya service ma bare waya ta dameshi?,mutumin da yake kewaye da aljanu,suke kai masa saqo kuma ku amso masa ko daga ina ne?,me zaiyi da waya?. Hajja harira ce ta fado mata,ba bata lokaci ta danna number dinta tahau kira. *Hajja harira* Tun fitar laila bata iya tashi daga wajen ba,idan tace ta qulla tunani sama da dubu da kwancesu tsaf a wajen ba zatayi musu ba. Duk wani tunaninta idan yaje ya dawo a waje daya yake cakewa,tun tana neman qaryata abinda take zargi har zuciyarta ta gama yin ittifaqin amsar dai itace "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta furta da wani matsanancin tashin hankali. Tayi imani muddin abinda take zargi ne ya tabbata.....to lallai laila zata qare rayuwarta kaf wajen bautar maamah...... Asiri ne da bashi da makari sai mutuwa.....yaci uban bita zaizai,yafi uban tace saidai kafin tace. Ita mariya zata yiwa haka?,wannan shine sakamakon alkhairin da ita tayi mata?. Kamar tasan itace a gaban tunaninta saiga kiranta ya shigo. Kamar kada ta daga amma kuma wani tunani daya darsu a ranta ya sanyata gyaran murya ta daidaita muryarta sannan ta daga din. "Al'amura kamar suna shirin kwabewa hajja.....ina tsoron kada zancan mutumin nan ya fara tabbata......ki taimakeni hajja". Maamah ta fada da tsananin damuwa,damuwar data saka hajja taji wani bangaren na tata damuwar da tashin hankalin suna samun sassauci.....ko banza ba ita kadai ke cikin damuwa ba......ba kuma ita kadai zata ci gaba da zama a cikinta ba,taci alwashin dukka yadda zatayi zata yi don maamah taci gaba da tabbata cikin damuwar ta,waye ya gaya mata yaro yana wasa da kan maciji koda kuwa ya rasa abun wasa?. Yanayinta ta daidaita don yayi dai dai da yadda maamah zataso taji,tana mamakin zallar rainin hankali irin nata. Bayan mummunar sakayyar da tayi mata,kuma wai ta nemeta da tata matsalar tamkar ma batasan me ya faru ba?. "Me yake faruwa?" "Garkuwata ta subucemin......daga yanzu zuwa kowanne lokaci zan iya fuskantar barazana daga wajen abun hari na,kowanne hope nawa kuma ya subuce hajja.....meye abunyi?" Ta qarasa maganar da sigar tambaya cike da damuwa. Iska hajja ta furzar tana dan bubbuga tafin qafarta kadan kadan,a nutse tace da ita. "Bani lokaci mariya nayi tunani......mintuna kadan nake buqata". Jikinta a sanyaye ta amsa mata suna katse wayar su dukka biyun. Wayarta take dan bugawa cikin tafin hannunta cikin salo na tunani. Mariya shegen kai ce,tana da nata matsanancin wayon da kai da kake rayuwa da ita kayi kadan ka fahimci komai idan ba ita taso ba.......saidai kuma a wannan yanayin da ake ciki mariya tana tafin hannunta ne. Bata isa tayi wani motsi cikakke ba ba tare da ita ba,itace ginshiqin.....itace kuma madogarar. To shin batasan abinda tayi mata bane?,batasan me ya faru ba?,ko tsananin iya bariki ce kawai?. "Inaso na samu tabbaci" Ta furta tana daukar wayarta data aje tun daxun ta sake lalubar number maamah din. Bugu daya tak ta daga,ta sanya wayar a kunnenta tana kiran sunan hajja. "Duk abinda zaka daukoshi ko ka matso dashi don biyan buqatarka......kuma ya gaza yin wannan aikin sai nakega bashi da wani amfani,kau dashi kawai zaifi.....me zai hana ta gusa daga rayuwar fuad tun kafin matsalolin da boka ya baki a dunqule su fara bayyana har sufi qarfin shawowarki?....ga laila nan?,umarni na da naki sune zasu zama abun binta,a azata a bigiren da wannan ke kai,nayi Imani da laila......tabbas ba zata sabawa tsarinmu ba......sirrinmu kuma a lullube". Nauyi maamah taji maganar tayi mata,sannan sam bataji maganar ta kama hankalinta ba. Har cikin jininta da zuciyarta takejin laila bata mata ba,kwata kwata bata dace da wannan aikin ba,bata dace ma ta zama matarsa ba koda na minti guda ne kuwa. Tasan wacce hajja farin sani,tana tunanin ita ko yaronta zasu kubuta daga ayyukanta ne?,sai ta girgiza kai a fili tana jin abun bai kama hankalinta ba. To amma dole sai tabi ta takatsantsan kafin ta fahimtar da hajja din,tafi kowa sanin hajjan akan laila bata dagawa kowa da komai qafa. "Aah fa hajja harira,laila ni dake duka 'yarmu ce......ba zamj jefata cikin wannan risk din da wahalar ba......qyale bare dai,wanda idan ya sabawa tsarinmu kowanne mataki zai iya fadawa kansa........kamar yadda itama wannan din MUMMUNAN SAKAMAKO na rantse miki da Allah zai yita bibiyarta......ba zan qyaleta ba,sai na banbance mata tsakanin aya da tsakuwa!" . Turqashi!.....hajja ta fada qasan ranta,kai tsaye a bayyana ko a kaikaice maamah bata qaunar laila ta kafa tarihin zama matar muhammad me jadda.....wannan shine amsar tambayarta kai tsaye idan aka cire kauce kauce. "Ke yanzun wanne shiri ne na gaba kike ganin ya kamata muyi?" Ta mata tambayar tana relaxing kanta don samun bakin zaren daga inda zata dasa nata aikin. "Ki bari tukunna na samu nutsuwa daga wannan,abubuwa su hau kan saiti,zaki ganewa idanuwanki ba tare da nace dake komai ba". Ta fadi mata kaman yadda ta saba. Tana da boye duk wani shiri nata,zai wahala tana kan shiri ka sani,ko a baya wannan ne ya zama SILA da sanadin da LAILA ta shiga DUNIYAR lissafinta,qila data tsaya neman fashin baqi wajen boka kamar yadda hajja taso suji......ba shakka da qila yanzun haka laila bata fada wannan BAQAR MASIFAR ba....dukka hajja ke wannan tunanin cikin ranta tana jin wani bacin rai yana taso mata. Hajjan ta bude baki zatace wani abu sautin kukan laila ya mamayi kunnuwanta daga cikin wayar. Wani abu ya daketa,tayi shuru tana sauraren tambayar da maamah keyi mata kafin kiran ya yanke. "Tashin hankali!" Ta fada a sarari tana miqewa tsaye,ji take kamar ta wuce kai tsaye gidan maamah amma wata zuciyar na jan kunnenta "Sai kinyi kamar baki sani ba......sai kinyi kamar baki fahimci komai ba,saikin maida komai ba komai ba". Wadannan maganganun suka sanyata rusuna ta koma ta zauna wuta naci gaba da balbala a zuciyarta. Daidai sannan nafessa ta shigo da mopper da broomstick tare da sallama a sanyaye cikin girmamawa. "Ubanme kika shigo kiyimin?". Kai ta sunkunyar "Kiyi haquri,haidar ne ya tashi da zazzabin haqori yau shi yasa ban shigo sharar da wuri ba". Duk da jikanta ne bata tsaya ta nuna kulawa ko alhinin komai ba,hasalima bata fahimci gaya mata take baida lafiya ba yaron,sai ta daka mata tsawa tana fadin " Sharar da bakiyita dazu ba sai yanzu ko?,baqar munafuka,fita ki bani waje". Tashi sosai hankalim nafeesa yayi,take idanunta suka tara ruwan hawaye,tana tsoron me zata gayawa d'anta a kanta idan ya dawo,tanason aurenta batason ta kashe mata shi,wannan ya sanya ta sulale tana tsugunnawa ta soma mata magiya tana bata haquri "Ki tashi bani waje kafin na rufeki da duka,sharar ce nace banaso ko ana dole?" A nan ta fahimci bawai iya rashin sharar bane kawai da ba'ayi ba ya sanyata haka,akwai wani abu na daban da ya bata mata rai,wannan ya bata sassauci sai ta miqe tana sake bata haquri ta bude qofar ta fita gami da rufe mata. A qasan ranta tana tafe tana addu'ar "Ubangiji ka qara mata damuwa fiye da damuwoyin data sanyawa zukatanmu.......ya rabbi ka shagaltar da ita da damuwarta ta yadda zata zame mana mu kuma hutun da bamu taba samunsa cikin gidajen mazajenmu ba".49 _Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_ *_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa ko dauda a jiki_* 49 Ta furta har tsakiyar ranta tana jin ciwon bautar da suke ciki,wadda basusan ranar fitarsu a ciki din ba,sunfi kyautata zaton wataqila sai ranar da surukar tasu ta kwanta dama. Ajiye wayar maamah tayi a gefanta tana duban laila da hawaye ya yiwa fuskarta shabe shabe "Lafiya laila?,me yake faruwa?" Ta maimaita tambayar tana riqe hannunta "Hamma fu'ad ne maamah......ya koreni". Fuska ta ya mutse tana duban lailan,tashin hankalin da take ciki a yanzun bata jin yakai korar laila daga gidan fu'ad,duk kuwa da cewa hakan da yayi taji ya tabata ya kuma qara bacin ran da takeji a ranta. Ya nuna bata isa ba kenan kamar yadda ta saba.....amma yanzun ba shine abinda ya kamata ta damu dashi ba.....tanason tasan ina yaran?.......ina suka shige?,meye manufar yarinyar?,meye takunta na gaba?. "Kina da buqatar ki koma gidan?" Maamah tayi mata tambayar kai tsaye,don son tabbatar da maganar da sukayi da hajja a yanzun. Shuru lailan tayi,tana jin tamkar kowanne tsari na zuciyarta da kuma tunani na qwaqwalwarta ya birkice,tsare tsarenta......burikanta dama duk wani abu dake gabanta sai takejin yana sauya muhalli. Tanason fu'ad sosai......tana kuma jin soyayyarsa.......amma sai takejin zama da maamah yafi mata zama da fu'ad dadi......hakanan ko me maamah ta furta shine umarninta,to tabbas zata iya aikatashi komai tsanani da tsaurinsa. "Inason hamma fu'ad sosai,inaso na aureshi.......kuma hajja tayimin alqawarin sai na aureshi....." Maganar sai ta zowa maamah banbarakwai,tayi mata saukar ba zata,ta xubawa laila idanu tana mamakin furucinta tare da tantamar lafiyar qwaqwalwar laila din. "Tayi miki alqawari?,yaushe kenan laila?" Maamah data tattara dukka hankalinta akan lailan ta fada cikin tsananin mutuwa da kuma sanyin jiki. "Tun sanda ake shirin auren hamma fu'ad.....ta kaini gidan na zauna don na karanceshi tsaf,sannan ta bani ayyukan da zan bashi yaci saboda jawo da hankalinsa kaina da kuma siyan soyayyata......wanda daga qarshe takeson ya dawo hannunta gaba daya". " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Maamah ta fada tana jin saman kujerar yayi mata tudu da yawa,ba zata iya zama a kai ba duk da laushinta,sai ta sulale ta zauna sosai a qasa. Ta sake zubawa laila idanu sosai maganar na ratsata,amma kuma tana cike da tantama da tunanin cikakkiyar lafiyar kwanyar laila. "Tabbas laila ta fara shaye shaye" Shine abinda maamah ke ayyanawa a ranta. Ba yadda za'ayi hankalin laila daidai......lafiyarta kuma qalau ta dauki babban sirri da labarin cikakkiyar cin amana irin wannan ta gaya mata. "Don Allah kada kiyi fushi dani.....kome kike buqata zan miki maamah" Laila ta fada alamu na bayyana kuka nason qwace mata. Al'amarin ya sake jefa maamah a madaukakin mamaki "Me kikeso in sake baki labari?" Laila da gabanta keta faduwa cikin matsanancin tsoron kada ta batawa maamah ta fada tana durqusawa a gabanta. Mamaki ya sake kashe maamah,ta sake saka idanu ko zataga wani abu na tabin hankali ko hauka tattare da laila,saidai ko kadan bataga wannan ba illa tsantsar biyayya da faranta rai da takeso ta yiwa maamah din. "Ki nutsu mariya.....ki nutsu,makashinka tabarmarka......makashinka yana tare da kai" Wata zuciyar ta ankarar da ita,wannan ya sanya ta aje mamakinta da tunaninta meke faruwa?,ta maida hankalinta ga laila "Tashi ki zauna sosai muyi magana" Cikin hanzari ta miqe ta koma inda saitin inda maamah ke nuna mata ta zauna. "Me yasa kika yanke hukuncin gayamin sirrinku ke da mamarki?" Ta tambayeta da matsanancin mamaki. "Saboda ya zamemin dole na inyi miki biyayya.....inajin cewa ke din kamar uwargijiyata ce.....ni kuma baiwarki,inajin kamar dama can an halicceni ne don na miki biyayya,inajin komai zai iya samu na muddin ban miki biyayya ba......burina na mutu ina miki biyayya.....burina na mutu ina bauta miki". Ta qarashe maganar da zallar gaskiya da kuma yanayin da yake nuna cewa da gaske take furta maganar dake cikin ranta din. Kowacce tsiga ta jikin maamah sai data zuba,wannan shine kwatankwacin abinda take buri,take fata take kuma mafarkin taji ta kuma gani daga wajen fu'ad......ya akayi haka ta kasance akan laila. "Laila......akwai abinda aka dafawa fu'ad a gidansa baici ba ke kika ci?" Ta jefa mata tambayar da zallar kokwanto a ranta. Kai tsaye ta gyada mata kai tana dubanta "Eh.....kwana hudu da suka wuce,naci abincin dare a dining dinsu" "Shikenan!" Maamah ta furta tana runtse idonta,tayi tsam da ranta bata iya cewa komai ba. Tsahon wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,kafin kuma a hankali taji kowanne tashin hankali yana sulalewa daga zuciyartata. Idanunta ta ware akan lailan "Meye shirinku a kaina.....meye shirinku akan fu'ad?" Tambayar data yiwa laila kenan tana da yaqinin da tabbacin zata gaya mata komai tiryan tiryan. Shuru maamah tayi tana biye da laila din har ta gama kwashe mata bayanin komai. Ba bayanin yadda lailan ta zayyane mata komai bane yafi daga mata hankali ba,qulli da tuggun da hajja ta shirya qarqashin nata shirin shine abu mafi tsoratarwa da razanarwa a wajenta. Don baje sirrinsu tasan zata samu information akan dukkanin abinda ya shafi hajja sama da abinda laila ta gaya mata ma a yanzu.....muddin wannan hadadden tanadin data yiwa fu'ad ne ya isa cikin laila.....to ko kashi lailan zatayi kuma take da buqatar ta shaida mata kafin ta yishi.....lallai ko bayan gida zai kashe laila ba zatayi ba sai da yarjewar maamah. Take dukkanin wani alhini da fargabar cin abincin da laila tayi ya fice daga zuciyar maamah. Baqincikinta daya asarar data jawo mata,gagarumin shirinta daya baci,wanda ta kashewa maquden kudade masu yawan gaske don ta samu fu'ad a hannunta,yanxu samun laila me zai tsinana mata?,banda kaya da zata zame mata?. Idan akwai riba guda da zata samu itace......ribar nunawa hajja kuskurenta na ha'intar qauna da aminci da tayi "Lallai zan mulki laila ko don na nunawa hajja itadin qanqanuwar maciyar amana ce.....zan mulki laila a gaban idanunta.....zan kuma bautar da ita yadda take bautar da d'iyoyin mutane cikin gidanta". Duk da takaici tashin hankali da baqinciki daya cika mata zuciya amma saita dubi laila da dan murmushi "Zaki zauna dani?" Da sauri ta daga kanta tana jin kamar an mata rahama ne "Zan zauna.....zan zauna dake maamah.....hakan yafimin komai dadi a duniya" "Da kyau" Ta fada a hankali,dan daga murya tayi sannan ta kira daya daga cikin masu aikinta na gidan tace "A bata daki" Ta bisu da kallo sai data tabbatar sun fice a falon sannan ta maida hankalinta cikin jikinta, Iska me zafi ta furzar tana lula kanta cikin duniyar tufka da warwara......babu babban target dinta a yanzu haka idan ba sabreen ba. Bata gidan ta fita.....shine abinda ta yita nanatawa tana shafa lips dinta da yatsantsa. Da sauri kaman wadda aka tsikara ta jawo wayarta,ta tafi kai tsaye izuwa ma'ajiyar lambobi ta zarce can qasa. A jere numbers din nasu suke,saidai kuma tayita kai kawo akan waye zata kira a cikinsu?,waye yafi zafin aiki?. Cak idanunta ya tsaya akan wata number da aka rubuta sunan HANZARI bata tsaya jinkiri ba ta danna kan number ta tura gaba izuwa kira. Bugu daya tak aka daga,da wata iriyar birktacciyar murya ake fadin "Allah yabar mana ke uwar dakina maganin kuka na". Wannan kirarin nasa yana fasa mata kai ainun,kuma ko a yanzun shi kadai ya bata tarin qwarin gwiwa "Nayi missing target hanzari.......ka shirya ko da kowanne lokaci zaka iya jin kirana......idan kiran kuma ya tabbata......babban aiki nake da buqatar ayimin wanda daga shi bani da sauran haufi ko matsala" "An gama uwar dakina" Ya fada da qatuwar muryarsa,bata jira komai ba ta kashe kiran,ta kuma maida akalar kiran nata zuwa ga number huda. Abu daya dai ake sake gaya mata,layin a kashe yake,saita saita lokutan da zataci gaba da kira daga nan har zuwa awa ashirin da hudu,ta aje wayar ta kuma shiga tunanin meye abunyi na gaba?. *MASHKUR* A hankali ya sake gilmawa da motar ta gaban gidan,ba kuma wai don yana da wani abunyi ba ko kuma lalura ke sanyashi wannan zirga zirgar da yakeyi ba......aah,yana yine saboda nazartar gidan da kuma dukka wani kai kawo na jama'ar gidan dama ma'aikatan dake aiki cikin gidan daga dare har rana. Wadanda suke shifting da kuma wadanda zamansu kenan. Yayi gaba,amma sai yaci gaba da kallon gidan ta rearview mirror yana kada kansa a hankali. Babba duk inda yake babba ne,gidan na daya daga cikin dream house dinsa daya jima yana tunanin idan har ya samu yadda yakeso a shekaru goma masu zuwa zaya mallaki irinsa. Hannunsa ya sanya ya daki steering din motar yana jin wani zafi cikin ransa. Yarinyar tasha dashi da yawa a rayuwa,banda wani abu daya rinjayi zuciyarsa tabbas plan A dinsa a yanzu shine zai zama plan B,plan B kuma shine a plan A,to amma duka wannan bazaiyi aiki ba......yana ganin gwara ya fara diban ganimar tukunna,idan yaso ko meye zai faru daga baya me sauqi ne. "Ina fata ka gama kallon komai?" Yayi magana da mutumin dake zaune a back seat wanda zai wahala ka iya fahimtar da mutum a gurin. Kai ya jinjina yana motsa system din dake saman cinyarsa "Na gani......aiki ne me bala'in hatsari da dukkaninmu zamu jefa rayuwarmu cikin hatsari........amma kuma,ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba.......let's try it......idan mukayi winning...." Sai ya saki murmushi yana rufe system din "Zamu kasance mutane mafi sa'ar zuwa duniya" Ya qarasa maganar yana dukan bayan kujerar dake a gabansa. Iya nasarar da yayi musu hasashe ta saka mashkur qyaqyacewa da dariya "Inaso naji dandanonta.....inaso naji ya take.....bansan adadin mafarkin da nayi a kanta,ban taba sanya kwadayina akan wata 'ya mace ba tunda na fara sanin 'ya'ya mata....wannan macen ta zullemin bansan ya take ba sai a kanta,dole ta fahimci wannan kuskuren data aikata!" Ya fada da qwarin gwiwa qwarai da gaske,yana jin ya zaqu da komai ya tabbata. "Bazan iya dogon jira ba Mike.......ka shirya komai tsakanin kwanakin nan biyu" Daga hakan sai kawai ya qarawa motar wuta sosai suna gaggawar ficewa daga layin. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 0818725586250 _Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi ne😄),yace:Manzan Allah S A W yace "da me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa na sabo,tabbas da ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara arba'in shine yafi masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_ _Bukhari da muslim ne suka rawaito_ 50 ★Daure da babban towel ta fito daga wanka,qaramin tana tsane doguwar sassalka sumarta dake a jiqe sharkaf da ruwa,alamu dake bada tabbacin wankesa tayi. Idanunta a lullumshe tana jin kalan nauyin da yayi mata saboda kukan da tasha a jiya. Duk da nauyin da zuciyarta tayi mata amma ta wani fannin sai take jinta sawai kamar wani nannauyan dutse dake danne da ita ne ya sauka. Tun daga jiyan data tabbatar ta miqasu hannun da bata haufi akan zasu cutu ko wani abu maras kyau zai samu riskarsu. Tana daga gaban madubin,kadan kadan tana hangen yadda iska take kada labulayen dakin,wata sassanyar iska me dadi kadan kadan tana ratsowa cikin dakin. Lumshe ido ta sakeyi sanda ta gama gyara gashinta ta matseshi cikin ponytail holder bayan ta lanqwasa jelarsa me tsaho sosai,fuskarta ta fito sosai,sai ta sake lumshe manyan idanunta da suka rusuna sosai. Zuciyarta ciwo takeyi idan ta tuna da tuhumar da yayi mata jiyan,tana jin wani zafi cikin qirjinta duk sanda kalmar "Wajen wa kika je?" Ta dawo mata a kunnenta "Me kikayi?" Tana sake sakata jin zuciyarta na matsew a qirjinta. Vibration din da taji daga gefanta shi ya ware zaren tunanin dake qulluwa cikin kanta. Maida dubanta tayi wajen,wayar huda data karba ce wadda ta sakawa charge tun da asuba,bayan wayar ta cika kuma sai ta kunna kanta da kanta kamar yadda tsarin wayar yake. Sunan MAAMAH data gani ya isheta bayanin wacece,wani matsiyacin tsaki taja tana janye idanunta daga kan wayar,sannan ta juya tana wucewa closet dinta don neman kayan da zata saka. Idan ta tuna abinda d'anta da ita sukayi mata,sai taji kanta ya cika da shawarwarin hanyoyin da zata dauki mummunar fansa a kansu kafin ta tattare tabar rayuwarsu. Duk da cewa nashi me sauqi ne,don baiyi yunqurin taba mata kowa nata ba,saidai ya taba mata zuciyarta da munanan kalmomin da koda tayi nesa da rayuwarsa bata jin zata iya mancesu. Har zuwa yanzu da take wannan tunanin ta rasa wanne kalar abu ya kamata ta yiwa maamah?. Abu daya tayi ittifaqi akai shine......tabbas zata banbance mata tsakanin aya da tsakuwa......zata kuma shayar da ita mafi girman mamaki. Tabbas inda tana da ra'ayin d'anta......lallai da zata mallakeshi a gaban idanunta ne,mallakar da babu boka babu malam.......mallaka ta ruwan sanyin da sai ta gwammace bata sanyata a shirmen shirinta ba. Har ta ciro kayan ta dawo ta shirya cikin Palazzo da blouse data kasance cif cif jikinta don bata buqatar kaya masu nauyi kiran bai daina shigowa ba,ta kammala ta feshe jikinta da turare . Scarf ta sanyawa kanta sannan ta taka a hankali tana isa inda wayar take sanda take dab da tsinkewa. Stool taja ta zauna bayan ta daga kiran ta sakashi a handfree ta kuma ajiye saman mirror table din tana tattara hankalinta akai. "Dawa nake magana?" Abinda ya fara fita kenan daga bakin maamah da wani yanayi na zaquwa da son jin wayar a hannun wa take?. Idonta ta lumshe sannan ta bude "Gaggawar ta meye?,kina tunanin wayar huda zata kasance a hannun wani qato ne?,ko a hannun wata sabanin halastacciyar 'yar uwarta data shirya sadaukar da tata rayuwar saboda tasu?". Maganar ta kama zuciyar maamah sosai,ta kuma saukar mata da matsananciyar fargabar data bata tabbacin KOMAI YA QARE saidai a sake sabon zubi da lale. "Naga alamar hakan......kin kuma yi qoqarin sadaukar da rayuwarki ma 'yan uwanki.....ni shaida ce,amma inaso kisan wani abu guda.......kina wasa da baqin kumurcin maciji ne daya shirya dukka dafinsa da xummar harbi ga duk wanda yabi ta hanyarsa" Wani dan murmushi ta sakarwa maamah din tana murza hannuwanta,har yanzu tana jin bata gama dawowa ainihin sabreen dinta ta asali ba......amma kuma da alama komai yana bisa hanyar saituwa "Shi wannan macijin.....idan har yayi sake halittar data fishi sanin kogon da yake kwana yake kuma tunqaho dashi.......tabbas akwai yiwuwar a cimmasa har inda yake......a kuma sanyashi ya yanke wannan kan dake dauke da dafin da kansa da kansa ba tare da yasan hakan ta faru ba....." "Ke dakata qaramar alhaki!" Maamah ta furta bayan dukkan haqurinta ya gaza da yadda yarinyar dake qarqashin igiyar auren d'anta ke iya maida mata magana me zafi haka kanta tsaye......ba shayi ba fargaba,yarinyar da a haife dukka cikin 'ya'yanta ba sa'anta. "Shshshsh....." Sabreen ta fada tana dora yatsanta akan lips tamkar maamah na zaune a gabanta. "Meye na saurin fusata haka?.....ina cewa abun baiyi zafi har haka ba?" Ta furta da alamun murmushi cikin muryarta. "Yaro man kaza......yaro baisan wuta ba sai ya taka..." "Your royal highness......har yanzu bansan meye dalilin wadannan zafafan kiraye kirayen ba da safennan". Iya maqura a rainin hankali maamah tana jin sabreen tayi mata shi,ta dinga qoqarin tausa kanta da daidaita kanta kada yarinyar ta tunzurata furta abinda batayi niyya ba. "Yaro yaro ne.......sabreena......kina da masaniyar cewa nice na tsugunna na haifi fuad?" Dan murmusawa tayi kadan sannan tace "Haka naji labari!" "Amma kina da yaqinin ni na daukoki ko kawoki cikin gidan na maidaki sunan matarsa?.......idan naso qasa da awa biyu rak! Zaki rasa wannan damar?" . Qaramar dariya ta saki ma maamah din,ta gyara zamanta sosai tana kallon kanta a madubi. A yau hirar nishadi take bata a maimakon razani da take samu a kwanakin baya da suka shude. "Kina zaton kina da wani makami da zaki iya fiddani daga gidan yaron naki?........kiyi haquri da abinda zance......amma ko shaidan a yanzu bai isa ya fiddani daga gidan yaron naki da kike tutiya ba........bana son danki ko kadan bazan kuma taba sonshi ba......amma yadda kika sakoni cikin rayuwarku......kika maidani matarsa da qarfin qwanji dana kudi.......to haka fitata daga gidansa da rayuwarku zata kasande bisa zabin kaina a kuma duk sanda nayi niyya......so kibi a hankali,bawai sonshi nake ba.....infact ma baiyimin ba.......amma bazan fita daga rayuwarku ba har sai sanda nayi niyya" "Qarya kike....baki isa ba!" "Dama bance na isa ba......amma zan gwada saiki tayani tabbatarwa...." "Kina kirawa kanki ruwa!,zaki iya rasa rayuwarki ta dalilin haka fa!" "Bari na fara raba naki d'an da rayuwarsa tukunna ki fara ganin kalar wannan baqin cikin kafin ki aiwatar a kaina......zan shayar dashi ruwan guba a ruwan shayinsa na yanzu a maimakon tsubbace tsubbacenki....." Tana kaiwa nan ta kashe kiran tana ma kashe wayar gaba daya. Murmushi ta dinga yiwa kanta a madubi,hirar ta sanya mata nishadi sosai,ko ba komai ta dasa mata tsoro da fargici tabbas na mintunan data ambata. Da gasken haka shine ya faru. Wani irin gumi ya fara tsatstsafowa maamah da wani irin kalar tashin hankali. Zuwa yanzu bata da tabbas akan yarinyar.......tana ji a jikinta zata iya aikata komai da tace din. Kasa zama tayi,jikinta yana rawa ta soma lalubar layin fu'ad tanason gargadarsa akan ya kaucewa komai da zai fito a yanzu daga hannun yarinyar. Kira kusan goma tayi masa a jere saidai ba wanda ya daga,abinda ya sake tsananta tashin hankalinta kenan,ta dinga duban agogo tana qirga mitunan da yarinyar ta kwasa mata. Daidai lokacin ma shi ya jima a office. Ayyukane da yawa a gabansa da suka hade masa saboda jiya bai samu yin komai ba a office din yayi baqi da suka tsaidashi har zuwa dare. Daga jiyan zuwa yau komai zaiyi yana yinsa ne cikin wani irin fushi da zafin ran da hatta saddiq ya fahimci akwai abinda ke damunsa,kuma tabbas ranshi a bace yake. Ture file din gabansa yayi yana jan wani mugun tsaki. A duk sanda ya tuna ko abun ya fado masa a rai sai yaji wani mugun bacin rai yana lullubeshi. Tashi yayi daga kan ainihin kujerarsa yana takawa a nutse,yasa hannunsa yana sassauta tie din dake wuyansa cikin wani irin yanayi da yakejin kamar numfashin da yake shaqa yana masa kadan. "Why i cares so much?" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin zafi. Ba kasafai yake sanya kulawarsa ko damuwarsa akan komai ba sai abinda yake da muhimmanci a rayuwarsa. Ya tabbatar a karan kansa she's nothing to him amma me yasa abun yake masa zafi "Igiyar aurena" Abinda yake da tabbacin shine dalilin tsaiwar abun a ransa. Sai daya sassauta tie din hade da belt din suspenders din jikinsa,sannan ya jsa ga dispenser dinsa ya tsiyayi ruwan sanyi ya rage sanyinsa ta hanyar zuba ruwan zafi kadan akai,sannan ya koma saman recliner chair din dake gefe wadda aka ajeta don gajeran hutu irin wannan ya zauna akai. Kadan ya samu sassauci sanda yasha ruwan,ya dire cup din idanunsa suna sauka kan wayarsa dake haske. Da farko ya share yana tsammanin fareeda ce data zama kaman wata mahaukaciya. Kusan kullum cikin canza layin da zata kirashi dashi gudun kada yaqi dauka. Layinsa nada wani tsari na hana baqin numbers shigo masa amma nata kiran ya tsallake wannan shingen bai kuma san dalili ba. Sabanin mamakinsa sai yaga maamah. Baya iya qin daga wayarta komai runtsi,duk da daga ita har anni zai wahala su kirashi a irin wannan lokacin,sai ya jawo wayar ya daga yana sanyata a kunnensa. "Kana ina?" Abinda ta fara tambaya kenan tana qoqarin daidaita muryarta "Ina office.....wani abu ya faru?" Ya tambayeta a mamakance "Daga yau wannan yarinyar......." Sai kuma ta dakata saboda wani qaqqarfan gargadi da aka watso mata daga can qasan zuciyarta. Dan jim tayi shima sai yaci gaba da sauraronta baice komai ba "Shikenan,ka kula dai da kyau" Ta yanke tunaninsu su duka biyun da fadin haka. Wani haushi ya cikata bayan ta aje wayar,ita yarinyar zatayi wa wasa da tunani irin wannan?,tabbas idan har ta bari yarinyar ta qara kwanaki uku a gidanma.......bata amsa sunan mariya ba. *_to masu karatu......me maamah zatayi da zai saka auren sabreen qarewa cikin kwanaki uku?.....wanne qwarin gwiwa ko tabbaci sabreen ke dashi wanda yasa taci alwashi ko shaidan bai isa ya kashe mata aure ba?.....muje zuwa jama'a,WANNAN ALQALAMIN NA HUGUMA ZAZZAFA NE_* *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 51 _Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_ _harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_ Sai data fara lalubar number da take da muradin yin magana da ita sannan zuciyarta taci gaba da kwabar data fara mata. "Da kinason gayawa fu'ad me?,ya saki yarinyar?,kada ya amince da ita?,kada yaci abun hannunta?,bayan ke kika aura masa ita?,ke kika bashi tabbaci akan ingancinta da kuma cancantar aurensa da ita?,bayan ko sati biyu ba'ayi ba ke dindai ke kika kafa masa sharadin ya bata kulawarsa?,ya sota?,ya jata a jikinsa?,kinason dabawa kanki wuqa?,kinason sanya wani zargin saman zargin dake kansa naki?". Wannan tunanin ya sakata sakin ajiyar zuciyar tana kiran number da tazo kai,a gefe guda tana mamakin abinda ya hana hajja nemanta ko zuwa gurinta ko tuntubarta akan matsalar da ta shaida mata jiya,TABBACIN DUKKAMIN MAGANGANUN LAILA BA QARYA KO SHAKKA AKAI KENAN. Sai taja qwafa tana gyada kai "Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha" Ta furta a bayyane,daidai sanda taji an murda qofar dakin an shigo laila ta bayyana. Da kallo tabi lailan har zuwa sanda ta qaraso gabanta. Ta durqusa saman gwiwoyinta wani abu da bata taba yiwa maamah shi ba duk da matsayinta na qawar mahaifiyarta shekara da shekaru. "Ina kwana maamah" Ta furta cikin tsantsar ladabi har bata iya hada idanunta da nata. Kai ta daga ta kalleta,dukka wani bayanin plan nasu da lailan tayi mata jiya sai ya shiga dawo mata kanta tar tamkar a lokacin take labarta mata. Wani bacin rai da radadin da wanda akaci amana keji ya taso mata,sai ta maida kanta ga waya kawai tana tura masa saqo. Sai data tabbatar saqon ya shiga sannan ta kalli laila,wadda kafin lokacin duk wani kalar tashin hankali laila ta shigeshi. Tana jin kamar ta dora hannunta aka ta yita zunduma ihu,iya yadda maamah taqi amsa mata gaisuwa ya sanyata cikin firgicin kodai wani laifi tayi mata?. A yanzu a rayuwa bata jin akwai wani abu da zai daga mata hankali sama da taga fushin maamah.....ko kuma tayi wani abu da zai saba umarninta. "Lafiya qalau....." Amsa matan kawai da tayi ya sanyata sakin wata sassanyar ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ba wani abu tayi daya bata mata rai ba. "Na shiga dakinki naga basu shareba.....na gyara miki,saiki duba idan akwai abinda baiyi ba ki gayan a sake gyara mikin". A nutse take qarewa laila kallo,ji take a ranta inama ace fu'ad ne haka a gabanta yake wannan bayanin bawai laila ba?,inama ace aikinta ya fada daidai?,i yanzu da batasan wanne irin farinciki take ciki ba.....lallai da zata kasance wata halitta mafi farinciki a fadin duniya,ta qarasa wannan tunanin tana runtse idanunta gami da budesu. "Basai na duba ba,saidai anjima kafin na kwanta ki sake" "To ba matsala.....waida so nake naje wajen hajja.....jiya muna magana bamu gama ba kika kirani" Kai ta girgiza,duk da tanason sake samun information,don tayi imanin duk abinda zasu tattauna tamkar a gabanta za'a yishi,to amma kuma tana buqatar ta kammala da aikin sabreen tukunna......tabbas komai da zai biyo baya me sauqi ne. "Ki kirata ki gaya mata nace ba yau ba,zan duba gobe na gani idan ya dace kije goben" Ta fada kanta tsaye tana ci gaba da riqon wayarta cikin jiran tsammanin shigowar kiran hanzari nan da kowanne lokaci. Sanda laila ke gayawa hajja saqon maamah kai tsaye murmushi ta saki bayan sun gama wayar tana jinjina kai "Mariya!.....Mariya,zan miki babban karatun da gogewarsa sai a cikin kabarinki,a sanda qasusuwan mowacce halitta ta jikinki ta gauraye da qasa,kin bani qofofi masu yawan gaske ba tare da kin sani ba.....zan shiga ta kowacce qofa......na fita ta kowacce qofa.....na shiga kuma cikin rigarki na dimauta duniyarki......sannan na hana muradinki da mafarkinki su zama gaskiya" Abinda ta fada kenan tana qurawa wayarta idanu dake aje tana ta burarin nemon taimakon a daga kiran daya shigo. Tun safen har azahar zuwa la'asar da tayi dukka cikin dakon shigowar kiransa take. Sai bayan la'asar din liqis cikin ba zata daya daga cikin masu aikinta suka shaida mata tana da baqo me suna hanzari. "Ki rakoshi can cikin setting room,kada a barshi a waje" Ta fada cikin doki da zumudi,ta miqe tana daukan dankwalinta ta maida kanta,har ranta tana jin mafita tana tunkaro ta. Fitowarta ya sanya hanzari sauke qafafunsa da suke dore daya saman daya. Sanye cikin baqar shiga,wandon jeans da shirt dukka baqaqe,sai baqar hular Ascot cap daya jawota tadan rufe fuskarsa kadan. "Barka da fitowa" Yayi maganar yana miqa mata nannadaddun takardun dake hannunsa,sai ta fasa zama ta sanya hannu ta karba sannan ta zauna dasu ta soma budewa tana cewa "Aiki dakai akwai jan kudi.....amma kuma akwai hanzari kamar yadda sunanka yake" Ta fadi a nutse tana bin list na sunayen da kallo da kuma hotunan. Sai data gama qare musu kallo tas sannan ta kaudasu daga fuskarta tana kallonsa "Kin gansu hajjaju?" Ya rigata fada,sai ta gyada kai ranta yana yin fari. "Kayi qoqari sosai hanzari.....amma waye kake ganin ya dace mu dauka?" Ta fadi maganar tana sake kallon list din. Matsowa gaba yayi kadan ya miqa mata hannunsa yana cewa "Kawo nan ki gani" Ba musu ta miqa masa,ya aza takardar saman teburin dake tsakaninsu yana binsu da yatsa daya bayan daya,kafin daga bisani hannunsa ya tsaya daidai fuskar mashkur,sai ya daga kai yana kallonta. Duk da baiyi magana ba bai kuma ce komai ba amma maamah ta fuskanci abinda yasa gaba da abinda yake nufi. Sai ta zuba masa idanu tana sauraron qarin bayaninsa. "Wannan shine mashkur......dan tsuntsu me wayo kenan..." Yayi maganar yana sake xuba yatsunsa saman fuskar mashkur. Sake jan hoton gabanta tayi,tunda ya aje din dama kusan fuskarsa tafi jan hankalinta. Yana da kyau daidai misali,wanda zaiyi daidai da plan dinsu,ta jinjina kai tana duban hanzari "Yayi......a tsara komai.....amma karka manta,secretly" Ta fada tana nuna hanzari da yatsa. "An gama" Ya furta yana murmushi. *FAREEDA* Ci gaba tayi da duba bayanan,murmushi yana sake wanzuwa saman fuskarta. Murmushin da takejin yana gauraya da farinciki da take da yaqinin zai zame mata tabbatacce ta hanyar samarwa da zuciya da ruhi abinda sukesu ta sassauqar hanya. Sake bude shafin qarshe na takardun tayi,take hotonta ya mamaye screen din tab din nata gaba daya,shafin qarshen daya zama shine na qarshe data bude cikin dukka bayanan data samu. Ta barshi a qarshe ne saboda dukka sauran shafukan na dauke da full details da bayanan da suka faranta mata rai sosai,sukayi kuma daidai da muradinta. Hoton sabreen din daya cika allon tab din ta zubawa idanu. Wani abu yana tsarga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafukan qafafunta. Wani mahaukacin wutar kishi ke ruruwa cikin zuciyarta. Ta kusa kwashe sakanni talatin a haka,kafin ta dafe dukka hannuwanta saman kujerar da take kai tayi zullo zuwa gaba har a sannan ta gaza dauke idanun nata. Labbanta suka motsa kadan rana son kiran ainihin sunan nata,saidai ya tsaya ne can qasan maqoshinta ba tare da sautin harafin ya fita ba. Adan hanzarce ta maida hannunta saman tab din tana komawa shafin da yake da alaqa da komai daya shafi sabreen din,ta sake karantawa sosai kamar me shirin haddace komai daya shafeta "How comes?" Ta tambayi kanta tana yamutse fuska lokacin da takai qarshen bayanan "Karuwa?......How did he get married to her?" Ta sake tambayar kanta da kanta "She's karuwa officially fa?" Ta kuma nanatawa cikin zallar mamaki. Ba wata amsa data samu daga kowanne sashe na kwanyarta,saita dage kafadunta duka biyun sama tana sakin murmushi,lallai komai zai tafi da alama daidai "Fu'ad isn't your type madam.....its over between you too" Tayi maganar tana nuna hoton sabreen da dan yatsa,saidai ba abinda ya canza zuciyarta daga mahaukacin kishinta da takeji. Ta kowacce fuska,ta kowanne bangare sabreen din ta yaga mata indai ana batun kyau ne da sassanyan zubi da ta tabbatar yana daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin fu'ad din,banda hakan.....yadda ta samu full details dinsa zai wahala ya nuna interest akan karuwa har ya aureta. "It's my turn......my time to shine has come" Ta fada da qwarin gwiwa,ta miqe tana nufar closet dinta ta sauke luxury luggage dinta guda daya ta fara selecting kaya tana shiryawa a ciki ba tare da jiran kowa cikin masu aikinta ba. Cikin qasa da mituna sha biyar ta gama packing komai da komai nata,sannan ta dawo ta dauki wayarta ta kira number abbanta. "Hello dad....." Ta fada a shagwabe. Ita din 'yar gaban goshinsa ce da dukka yaransa babu wanda ya kamo matsayinta a zuciyarsa. A kullum tana maida kanta tamkar 'yar shekara goma a gabansa,haka shima yake biye mata,saidai hatsabibancinta da girman izzarta ta dara tashi shi da yake da muqamin ambassador din gaba daya. "Dad.....ayimin booking flight please......gobe nakeso if possible,it's an urgent dad..." Ta furta a shagwabe kamar yarinyar dake tsakanin shekara shida zuwa bakwai "Thank you dad" Ta fada da murnarta jin ya bata tabbacin zaisa a mata booking private jet. Da murmushi sosai a fuskarta ta soma turawa zababbun qawayenta da za'ayi tafiyar tare dasu request. Cikin qasa da minti goma ta gama komai,sai ta sauke wayar ta matsa gaban dan wani madaidaicin table dake dauke da tukunyar shi sha ta fara qoqarin hadata. Tanajin a yanayin da take ciki na farinciki ita daya zata tayata sarrafa murnarta, Kyakkyawar zuqa tayi mata tana bulbular da iskar daga dukka qofofin hanci da bakinta,ta lumshe idonta fuskar sabreen na mata shawagi tsakanin tunaninta da qwayar idanunta "Blast it!" Ta fada da qunan zuciya tana kaiwa iska naushi,tana jin kaman tayi using acid ta dauke wannan kyan da ya hanawa zuciyarta sukuni. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 0818725586252 _Daga dariq dan shihab RA,manzon Allah S A W yace "juma'a haqqi ce kuma wajibi akan kowanne musulmi yayita cikin jam'i,sai akan mutum hudu kawai(ta sauka),MACE,BAWA,YARO DA MARA LAFIYA"_ _Abu dawud ne ya rawaito_ ★Shuru ne ya biyo baya duk da wayar tana riqe a kunnenta. Dukka bayanan zuwaira ta gama saurara wadanda suka gama bata tabbacin lallai da gaske yaran sunyi nisan da ba wanda zaice ga inda suke......uwa uba kuma yarinyar tana ci gaba da harkokin gabanta hankali kwance kamar ba wani qalubale a gabanta. "Ni kaina yanzu komai na taba ko nace zanyi mata dakatar dani takeyi,waccar munafukar me aikin da ameena ta kawo mata yanzu da ita takeyi,munafuka me shegen iyayi da bariki,idan kikaga yadda takeyi mata zaki rantse da Allah sabreena ce babba ba ita ba". Wani tattauran yawu maamah ta hadiye,tsananin bacin rai yana sake cikata "Ki saurara,ki sanya dukka kunnuwanki da hankalinki dama idanunki kan gidan......kada kice komai,kuma kada kiyi komai,akwai gagarumin al'amari da zai faru cikin gidan.....abu daya nakeso kiyimin,ki kasance me bibiyar diddiqi bayan faruwar lamarin" Abinda maamah ta gaya mata kenam ta kuma yanke kiran. Bin wayar tayi da kallo......har a sannan tanaji a ranta muddin tabar sabreen din taci galabar ci gaba da rayuwa tana shan inuwa da arziqin danta lalallai ba shakka bata cika mariya. Shekaru da gwagwarmar rayuwa da gogayya da tayi da kalar mata daban daban bai amfaneta da komai ba.....shekarun data kwashe ma a duniya basuyi mata amfanin komai ba,dole ta fiddota daga gidan......wannan shine zai bata damar yin walagigi da rayuwarta da kuma d'aid'aita rayuwarta kamar yadda ta d'ai d'aita mata burinta. Qarfe daya da rabi na rana driver din hajja ya faka motarsu qarqashin muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci. Koda ya tsaida motar ya kuma kasheta amma hakan bai sanya hajja fitowa daga cikin motar ba. Da idanu take bin kowanne sashe na ginin gidan da kallo tamkar yanzu ta fara ganinsa. Saidai sam a badini ba wannan bane damuwarta ba......ba kuma shi take kallo ba. Tana nazarin yadda ALKHAIRI ya juye izuwa SHARRI,ta gama tura mota tsaf tana shirin buleta da balbalin hayaqi maras dadin shaqa?,hayaqi mafi cutarwa cikin qofofin hanci da kwanyarta?.. Wata gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,sannan ta balle murfin motar yau da kanta tana fitowa,sabanin a baya da sai driver ya fito da kansa ya bude mata sannan ta fito. Gyara yafen mayafinta tayi,kanta tsaye kuma take takawa zuwa hanyar da zata sadar da ita da ainihin cikin gidan. Duk taku daya idan tayi la'anar maamah take cikin ranta,tana ji a jiki ta jefeta a wata kalar musiba da batasan ranar fitarsu ba. Zuciyarta tana mata wani qunci da ita kanta batasan iya adadinsa ba......amma wani sashen na zuciyartata yana sake jaddada mata "Fushi ba naki bane.....nasara bata masu gaggawa ko saurin fushi bace!" Wannan shine abinda yaketa mata burki take hadiyewa da qyar. A jiya da qyar bacci barawo ya dauketa,cikin fargaba da tsoron fitar dukkanin sirrinsu daga bakin laila..... Yanayin aikin bokansu dabanne,a aikin da aka tanadarwa fu'ad harda na rariyar baki,wanda baida wani sirri na kansa sai abinda maamah ta buqaci ya sirranta,muddin maganin yayi tasiri a jikin laila kamar yadda aka tsara.....hakan yana nufin duk wani sirri nata yanzu a tafin hannun mariya yake?. Wannan tunanin ya hana mata cikakken bacci da safe,ta dinga qididdiga da lissafin wucewar sa'o'i don ta samu ta fito zuwa gidan mariyan. Tanaso taga yanayin fuskarta,abinda zai nuna shine zai zame mata amsa na abinda take zato da zargi. Duk da cewa na tsuburi ya mata alqawarin ba abinda laila zata iya gayawa maamah.....to amma tasan aikin bokansu daban yake dana kowanne boka. Sau daya tak! Yake maka aiki.....idan har yayi maka na biyu to tabbas ka taki sa'a,uwa uba yawan yawan ayyukansa basu da makari.....shi yasa ta jima tana murza zaren rayuwarta ta kowanne fanni.....a yanzu kuma bata fatan wata matsala tazo mata ta wannan fuskar. Idanunta akan parlor din maamah.....falon da kullum maamah din ke kusheshi da ganin tsadar kayan adon ciki bai kama qafar na gidan alhaji hamza ba.....Parlor din da ita kuma hajja harira kullum kwanan duniya ta daga kai ta kalleshi sai kishin zamowarsa mallakar mariya ya baibaye zuciyarta da wata irin hassada me tsananin qarfi. Iya bariki da qwarewa wajen boyewa koma waye yanayin da kake ciki ya sanya maamah din bata taba fahimtar komai ba. Takun da taji ana fitowa daga kitchen ya sanyata waiwayawa cikin tsammanin daya daga cikin masu aikin gidanne wadanda su zasu yiwa maamah maganar ta iso tana son ganawa da ita. Amma kuma sabanin hakan,laila ta gani a gaba,dauke da kwando cike da warmers kala kala,saman rigar jikinta kuma apron ce a daure. "Laila?!" Ta kira sunanta cikin qaraji da wani kalar madaukakin mamaki tana takawa da hanzari don isa gabanta. "Sannu da zuwa hajja" Lailan ta furta fuskarta shimfide da murmushi dake nuna ba wani abu da takejin ba daidai bane "Bari na ajewa maamah abincinta nazo mu gaisa" Ta furta tana wucewa dining din. A nutse ta shirya komai.....kamar ba lailanta diyar gata ba,lailan da idan taci abinci ko kwanon da taci abincin batasan ta janyeshi ba......lailan da saidai tana mimmiqe saman sofa ko gado ta zabi abinda take da sha'awar ci.....wannan lailan itace yau a kitchen da rigar 'yan aiki?. Sanda ta kammala shiryawar saita dago tana murmushi,suka hada idanu da hajjan tace "Ina wuni?,na kira miki maamah din?,Allah yasa bata kwanta bacci ba don tace ko waye yazo kada a tasheta" "Gani nan laila baccin baizo ba....kun gama ne?" Maamah dake saukowa daga stairs din ta fada. Tare suka daga kai suna dubanta,sanye take da applique lace purple color da ya dan ciza kadan,dinkin doguwar riga da aka qawatata da wani irin dinki me daukan hankali. Shigar tabi jikinta....wadda ke bayyanar da zallar izzarta da isarta. "Kun gama laila?" Kai ta shiga gyadawa kaman mara hankali da sauri "Mun gama maamah ko akwai wani abun?". Ta fada a rusune. Murmushi maamah ta saki tana dafa kafadarta "Amma dai yau kin koyi yadda ake dambun gargajiya da kuma liver salad ko?". Murmushi ta saki kaman wata shashasha "Sosai ma maamah.....ai kin taimaken na gode sosai". Ta fada tana rusunawa a wajen. "Shikenan,yanzun zaki iya yin wanka,idan kin gama kiyi zamanki a daki kada ka fito yanzu" "To maamah" Ta amsa mata a ladabce tana juyawa ba tare data dubi ko bangaren da hajja take tsaye ba. Idanu suka hada da hajjan,wata tayi wata irin mutuwar tsaye. Gefe guda kuma taci gaba daya tamkar qwaqwalwarta ta daina aiki ne gaba daya. Wani qaramin shu'umin murmushi maamah ta saki,ta juya da hanzari bangare da laila ke tafiya "Au.....nikam nace kin gaida mamanki kuwa?" Kai ta girgiza tana fadin "Bakice ba ai". Fuska kadan maamah ta bata "Haba ke kuwa auta.....yarinyar kirki,zo ku gaisa mana....wataqila sanda zata tafi ai baki fito ba". Dawowa tayi ta rusuna har qasa tana gaida hajjan abinda bai taba faruwa ba kenan tsahon rayuwarta. Da fari idanuwa kawai hajjan ta saki tana kallon lailan,har sai da taji lailan ta maimaita gaisuwar sannan ta duqa tana dagota daga tsugunnon da tayi "Ki dauko mayafinki kizo mu tafi gida" Ta fada muryarta na rawa amma tana qoqarin danne rauninta don bata fatan maamah din ta gani. Kai ta girgiza tana duban maamah wadda tayi kaman batasan abinda ke faruwa ba,tana laluben wajen zama hankalinta akan fuskar wayarta "Nafison nan hajja.....ni ki barni a nan" Ta fada tana zamewa daga jikin maamah din ta wuce abinta hankalinta kwance zuwa hanyar dakin da aka bata. "Bismillah.......zauna mana surukata" Maamah ta fada fuskarta a sake. Kalmar suruka din da maamah ta fadi shine ya sanya hajja jin wani abu tamkar wutar lantarki ta fusgeta. Cikin qasa da minti guda gumi ya fara tsatsatsafo mata ta kowacce kafar gashi ta jikinta. "Atika!" Maamah ta qwalawa me aikinta kira,wanda cikin qasa da minti daya ta bayyana,sanin da sukayi mata batason ta kiraka ka samu jinkirin zuwa. "Dauki remote ki kunnawa surukata A.c,karki saka da yawa kada kuma ta saukar mata da zazzabi" "To hajiya" Atika ta fada da rawar jiki tana me aiwatar da abinda maamah ta umarceta. Zagayawa kawai kalmar takeyi cikin kunnuwan hajja.....indai har kalmar surukuta zata fita daga bakin maamah a wannan yanayin,lallai ne ba abinda bata sani ba kenan. "Ki maida hankalinki jikinki hajja......har mariya ce zata firgitaki har haka?". Wani sashe na zuciyarta ya bata qwarin gwiwa har ta samu qarfin halin tattara 'yar nutsuwar jikinta tana neman wajen zama gami da fuskantar maamah. "Mariya......zuwa nayi na duba lafiyar laila.....ya kuka tashi?". Murmushin nan dai ta kuma saki,sannan ta ajiye wayarta a gefe tana bada hankalinta gaba daya a kan hajja "Laila tana lafiya......kuma zata ci gaba da kasancewa lafiya sumul a hannuna......kinsan na iya riqon 'ya'yan jama'a" Ta fada hankalinta kwance. Murmushin qarfin hali hajja ta saki,sannan ta jinjina kai "Ai na sani mariya......mun tashi lafiya?" "Lafiyarmu sumul qalau hajja....." Daga nan ta fada nazarin da wacce kalma zata tunkareta. Idanunta ta daga tana duban maamah. "Muna magana jiya sai kuma Kira ya yanke....." "Eh wannan case din na gama solving nasa,saura fitar result" "Zancanmu fa kan laila da fu'ad?" Hajja ta jefa mata tambayar kai tsaye,duk kuwa da cewa ita kanta me bawa wani amsa ce.....saidai tanaso takai mariya inda take buqatar aje. Buda baki maamah tayi da nufin cewa wani abu......amma sallamar jarma daya daga cikin masu gadin gidan yayi sallama daga can bakin qofar falon. "Malam jarma ya akayi?" Maamah ta buqata sani sanda yake duqewa a wajen "Baqi gareki hajiya......ban sani ba zasu iya qarasowa ko a maidasu?". Fuskarta da dan mamaki take dubansa "Baqi kuma?,daga ina?" "Diyar ambassador Khaled mustapha ce,haka tace a gaya miki". Wani madaukakin mamaki ya cika maamah din,ba ita kadai ba,hatta da hajja sunan yaja hankalinta qwarai da gaske. Miqewa maamah din tayi tsaye tana dubansa "Maza ayi mata izini ta shigo......na tabbatar koma meye ya kawota nan,silar haihuwar ALKHAIRI ne fu'ad" Ta furta tana jin wani irin alfahari da haihuwarsa fiye da kowanne lokaci. Uwa uba tana yine da biyu,don ta tabbatar gaba daya hankalin hajja yana kan abinda yake faruwa. Sanye take da wani matsiyacin yadi da aka narkar da kudade masu nauyi kafin siyansa da yagalgalashi,aka kuma yi masa dinkin fitted gown data zauna a jikin laila......kai kace a jikinta aka dinkashi. Yadda dinkin ya zauna mata a jikinta.....hatta da dagawar numfashi daga cikinta da qirjinta kana ganin gudanarsa. Ba mayafi a jikinta,sai dankwalin material din da aka mata wani dauri dashi saika rantse hula ce ta kafata. Wasu nau'ikan dan kunne manya ne a kunnenta,wanda suke tafe da.manyan banguls da suka dace sak kalar material din jikinta kamar a company daya aka qerasu. Highhill ta sanya masu tsananin tsini sarqafe da igiyoyi,kaman yadda qwayar idanunta ke saye da tafkeken glass daya kusa cinye rabin fuskarta. Labbanta kwance reras da lip gloss,iya wannan kadai zai gaya maka tafiya akayi irin ta masu abun,ba wahalar hanya tunda sararin samaniya ne yayi aikin. Yadda take taku daya bayan daya tana takowa ciki,idanunta kan kowanne sashe na parlor din tana yaba alatun da aka zuba.....haka bakinta ke bada satin qas qas na chewing gum din da take taunawa cikin bakinta. Tana daga tsakiya,gefe da gefanta kuma fitattu kuma manyan qawayenta ne,lubna da jalilah,daga bayanta kuma masu aikinta ne data taho dasu suma guda biyun. Fuskar fareeda ba boyayyar fuska bace musamman idan kaidin ma'abocin kallon news ko dabdala a social media ne. Kusan duk wani motsi na mahaifinta ko na siyasarsa zaka ganta a ciki zaka kuma tsinceta a ciki dumu dumu. Lafiyayyen murmushi ya kubcewa maamah,ta taka a hankali tana marabtarsu. Doso sun da maamah tayi shi ya sanya laila cire glass din fuskarta dukka a qoqarin ta na nunawa girmamawa ga maamah din. Cikin qasa da minti biyar suka yiwa kansu mazauni a parlor din,sannan kuma gabansu ya cika da nau'in kayan ciye ciye daban daban na alfarma. "Nasan zakiyi mamakin zuwana wajenki maamah?" Ta fada tana qoqarin karyar da muryarta. Kai maamah ta jinjina,tako ta ina tanajin wani girma yana hawa kanta53 _Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan Allah S A W ya ambaci ranar juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA YA ROQA DIN". sai manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana baida tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_ "Eh to.....zai iya kasancewa abun mamakin ta wani fuskar,ta wata fuskar kuma ba abun mamaki bane,musamman idan kikayi duba da irin kalar zuri'ar da Allah ya bani" Tayi maganar da nufin jifa ga ma'anoni guda biyu tana gyara zamanta. Kai laila ta jinjina tana tsare maamah da ido,tun kafin tazo ta hadu da ita tasan wacece ita,don haka ko sau daya bataji d'ar ba na samun nasara ta hannunta ba. "Ko zamu iya kebewa muyi magana?" Laila ta fada tana duban maamah. "Me zai hana?,bismillah" Maamah ta fada tana miqewa,sannan ta fara takawa,sai kuma ta tsaya tana duban hajja,wadda keta kokawa da zuciyarta akan tayi abinda ya kamata "Yi haquri hajja.....zamu gana,yanzu zamu fito" Ta fadi mata tana sakin wani murmushi dake dauke da ma'anoni da dama. Sabon mariya ne......jifan maqiyi da murmushi ko kuma abokin adawa,wannan shine kusan makami na farko da take fara yaqar zuciyar abokin burminta,yayi tsammanin ita din wawiya ce.....itadin ba wani abu da zata iya,saidai kuma daga qarshe reshe ne yake juyewa da mujiya,sai taje maka da wani irin kalar farmakin da zaya kaika qasa koda baka shirya hakan ba. Bata da cikin mutanen da mariyan zata iya farmaka ta haka har kuma ta samu galaba,saboda sanayya ce ta kar da kar,ba wani abu ko hali nata da zata layance mata dashi. Dan madaidaicin parlor din shima sai daya ja hankalin laila,duk da ba wani baqon abu a ciki wanda bata sani ba.....amma yanayin tsarin da yadda aka zuba komai luxury ya bala'in shiga ranta. Wannan karon maamah ta fahimci haka,saita jefeta da murmushi sanda take zama tace "Hala kema ya burgeki?,aikin muhammaduna kenan.....komai nasa me tsari ne". Lumshe idanu laila tayi tana sake ji yana kuma shiga ranta,jini da jijiya harma da b'argonta qaunarsa tana sake ratsata "Inama zaki lamuncemin na zama matarsa.......bisa farashin dala dubu d'ari" Ta furta qasa qasa tana kallon maamah. Zubawa laila idanu tayi sosai tana jin sautin muryarta yana zagaya dakin,duk kuwa da cewa ta kammala taqaitaccen bayanin nata dake qunshe da saqo me tsananin nauyi.....ci gaba tayi da kallon laila tana son tantance Gaskiyar abinda ta fada ko kuma akasin hakan.....magana ake ta kusan million dari da hamsin ko da sittin fa......kawai don tanason fu'ad?,kawai don tanason ta aureshi?. Wane sashe na zuciyarta da kwanyarta da yake da kaso mafi girma wajen tsara mata komai ya harba,wannan ya sanya duk wani abu data shirya ambatawa ya wargaje,take ta sauya yanayin fuskarta daga me yalwar fara'a zuwa tsukakkiya "Wane irin magana ne wannan?,ance miki neman kai nakeyi da yaro na?" Tayi maganar a dake cikin qoqarin nuna bacin rai,da kuma tankwabar da tayin gwaggwabar garabasa da ribar da zata iya samu. Ga mamakinta murmushi laila ta saki,hankalinta kuma a kwance ta koma tayi relaxing jikin kujerar tana duban maamah,sannan a nutse ta daga qafarta ta dora daya saman daya tana ci gaba da dubanta. "Karki wahalar da kanki.....kada kuma ki wahalar da shari'a,kada kiyi kaman bakison kudi hajjiya......idan sun miki kadan kawai kice na qara miki,sai na qara mikin a wuce gurin.....fu'ad kawai nakeso,kudi ba matsalata bace sam sam". Sake tsare laila tayi da ido a karo na biyu tana karantar gaskiyar abinda take fada har zuciyarta. Qwaqwalwarta ta lula zuwa duniyar tunani duk da bata barta tayi nisan zango ba. Akan me zata bari tayi asarar kudin da take gani a gabanta yanxu haka?,bayan tana da damar mallakarsu?. Tabbas akawai manufar turo laila da ubangiji yayi cikisu a daidai wannan lokacin da take neman dukka hanyar da zata cisge sabreen daga gidan fu'ad.....babu ko shakka laila itace macen daya dace ta maye mata gurbinta. Duka ma a ture ta batun kudaden da zata mallaka......babban abun alfahari ne a yadda ubangiji ya yiwa yaronta kudi yabi sahun manyan masu kudin africa ma gaba daya......ace kuma yau shine yake auren diyar mutum kaman ambassador khaleed mustapha,wanda a muqamai dai na duniya tana jin ba wanda bai riqe ba,saidai kuma a lahira idan ana riqewa. Lallai ne ita mariya sunanta yana dab da sake fantsama cikin bakunan al'umma.....qawaye dangi da 'yan uwa,tana dab da sake taka wani matsayi na zama cikin manyan matan da fu'ad har yanzu yaqi sakar mata jelar macijin tayi wasa da ita da kyau,....wannan shine mafarin da tauraruwarta ta gaza yin haske kaman yadda takeso. Sunanta takeso ya zama cikin jerin sahun sunayen mata masu aji da sukafi kowanne mata a africa da duniya ma wasa da kudi.....cikin jerin sunayen iyayen attajiran 'ya'ya da kowanne taro ake kwadayi da rububin gayyatarsu,saboda sun zama bangon sugar ko na zuma,masu yayyafin kudi in dollars not in naira......don tana jin zuwa yanzu a arxiqinsa ita kanta tafi qarfin yin kyauta da naira. "Ki rubuta dukka adadin da kikeso" Ta tsinci muryar laila tana fadi,saita sauke idanunta akan abun rubutun da laila ta aje a tsakaninsu tana rutsata da idanu. Maida dubanta tayi kan fuskar laila,duk da alamu sun nuna tasan wani abu a kanta......amma ba zatayi saurin bada kai bori yahau ba haka da wuri gudun raini. "Ba ta wannan nake ba.....kawai ina duba cewa mahaifinki babban mutum ne da yakai kowacce uwa taso hada jini dashi.....ko don saboda shi zan shige miki gaba har ki samu fu'ad.......amma samun muhammad ba abu bane me sauqi......da gareshi akwai wasu tsauraran matakai,kamar yadda nima daga wajena akwai wani mixani da nakeso duk matar da zai aura lallai saita cikemin su cif da cif......yanzu haka rashin cike wancan mizanin daga matarsa ta yanzu ya sanya take fuskantar barazanar gutsirewar aurenta daga yanxu zuwa kowanne lokaci" "Daga yanzu zuwa kowanne lokaci?,ashe ma baki da guarantee......ashe baki da tabbas?" Laila ta fada da narkakkun idanunta dake nuna yadda suke da kyakkyawar alaqa da kayan maye "Ai kawai kiban wannan kwangilar.......nan da jibi ko gata.....kwanaki uku idan sunyi yawa zata zama tarihi a rayuwarsa......shiga cikin mutane xai gagareta......bama ita kadsi ba,haka dukka wani dake da nasaba ko alaqa da ita" Tayi maganar da cikakken qwarin gwiwar daya sanya maamah tsayawa ta xubawa laila ido. Daga jin alwashin dake fita daga bakin laila kadai ya isa ya gaya maka ita dinma wata akwai wani magana ta daban a kanta......itadin ma a shirye take "Dole kema nayi takatsantsan dake.....aminta dake haka lokaci guda babban kuskure ne......amma dole na fara miki da karin maganar nan da hausawa ke fadin DUK WANDA YA RIGAKA KWANA DOLE YA RIGAKA TASHI. Murmushi ta sake mata tana dubanta,ta sake yalwata fara'ar dake saman fuskarta tana kallonta. "Wannan ba wani abu bane da zai zama matsala......na baki wuqa da nama.....idan akwai wani information da kike buqata dukka a shirye nake na baki shi". Kai laila ta jinjina tana sakin murmushi " Zan iya gaya miki har fiye da abinda kika sani......ina da labarin abinda na tabbatar ke baki sanshi ba". Ta qarashe maganar tana bude handbag dinta qirar kamfanin Hermes ta zaro cheque. Rubutu tayi samansa hankali kwance tayi kuma sign dinta,sannan ta miqawa maamah. Kudi ne a rubuce kamar yadda ta furta zata bayar da farko,maamah din bata gama wannan tunanin ba muryarta ta sake fargar da ita "Wannan din somin tabi ne.....muddin kikayi nasarar zama surukata,zaki mallaki wata power ta fada a ji a manyan gurare da dama ta hannun mahaifina". Komai ganinsa maaamah ta dinga yi kaman cikin mafarki,duk da ta tattara dukka mamakinta ta hadiye don ba buqatar laila ta karanci komai. "Zamu iya ganawa dashi a yau?" Laila ta tambaya maamah tana jin kwadayin ganinsa a daren yau. "Baki da matsala da wannan" "Zamu wuce masauki yanzu haka don mu huta sosai,bayan magrib sai na dawo,hakan yayi?" "Yayi" Maamah ta fada tana daga zaune har yanzu,don mamakin da taketa boyewa yaqi barin zuciyarta. A gabanta Laila ta miqe tana fita daga parlor din,maamah kuma ta rakata da idanu. Tana fita daman jira takeyi,ta miqa hannu ta jawo cheque din tana dubawa "Da gaske adadin ta rubuta,akwai genuine din signature nata da komai?" Sake jujjuyashi tayi a hannunta,sai kuma wani murmushi ya qwace mata. "Lallai ni mariye me sa'a ce,ko rashin samun fu'ad a hannu akan lokaci na yarda lokaci kawai ne baiyi ba" Ta gayawa kanta da kanta tana gyara zamanta sosai tana jin kamar kanta zai fashe saboda wata izza da take saukar mata har tsakiyar ruhinta. Ta zubawa guri daya idanu murmushi na fita daga fuskarta lokaci bayan lokaci. Yau da wacce irin sa'a ta tashi?,wacce addu'a tayi yau?,babu....shine amsar data bawa kanta da kanta,don ko basmala cikakkiya bata jin tayi tun daga safe kawo yanzu. A dan fusace ta juyo jin an murda qofar ana shigowa,saboda ita din bata sakarwa kowa da kowa shigo mata guri kai tsaye ba....ko waye kai saika nema izini ta kuma baka. Idanu suka zubawa juna ita da hajja,saita janye cheque dinta tana lanqwasheshi ta daga pillow din kujerar gefanta ta saka a qasansa. Idanun hajja yana kai,abun kuma ya sake haifar mata da wani matsanancin bacin rai. Iya wannan abun da mariya takeyi kawai ya isa gaya mata komai daya faru ya faru ne bisa son ranta da kuma zabinta. Tunda suke da mariyan ba rufa rufa irin wannan tsakaninsu......tayi baqi ta kasa ganawa dasu a gabanta?,taga takarda duk da batasan ta mece ba amma mariyan ta jata ta boye?. "Kinga surukarki ko?,diyar ambassador khaleed mustapha" . Maamah ta sake maimaita abinda tasan already hajjan ta jishi. "Musaddiq ne kenan shima????". Kai da maamah kr girgizawa ya hana hajja qarasawa. " Fu'ad dai,d'ana fu'ad ". Da wani mahaukacin mamaki hajja ke bin maamah dake doka murmushi da kallo "Kinga Kalar surukan da ake fatan samu......wadanda za'a ciccibi juna....ba wadanda suke hangen turmusheka kai da mafarkinka ba.....maciya amana masu fatan kayi gyangadi su kafta maka sara.......zan shiga ciki in huta,ina da baqi anjima......idan kin gama ki rufe gurin.....karki damu kanki da lamarin laila......dama haka rayuwa take.....ka riqe dan wasu kaima a riqe naka,duniyar juyawa take haka da sauri........su madeena sun isheki zama.....ni kuma laila kadai ta isheni" Tana qarasa maganarta ta fara takawa zata fice54 _Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_ "Mariya!" Hajja da zuwa lokacin ta kasa riqe kanta ta kirata a hautsine "Koda wasa......koda tsautsayi kada kiyi tunanin cutar da laila......karki manta dukka sirrikanki a nan suke" Tayi maganar tana nuna mata tafin hannunta. Murmushi ta kuma sakar mata sannan ta juyo sosai tana amsata. "Wadannan sirrikan da kike da ganin sun isa abun tunqaho.....nabar miki su halak malak kiyi yadda kikeso dasu.....laila kuwa a yanzu mallakina ce,baki da hurumi a kanta,idan kuma kina ganin zaki iya to bismilla,ga fili ga me doki,kinsan dakin dana sanya aka sauketa ai" Ta furta tana nuna mata hanya,sannan ta juya hankalinta kwance tana fita daga dakin. ★k'arfe biyar da rabi yammacin ranar jerin luxury cars dinsa sukayi matsugunni a babban sashen ajiyar motoci na mansion House din nasa. Wani baqon abu daya kwana biyu baiyi ba,wato dawowa gida a lokaci irin wannan. Dawowarsa da wuri shine qarfe takwas zuwa tara na dare,wanda ita kanta matar gidan batasan lokutan dawowarsa ba. Kaman ko yaushe daga farfajiyar gidan ya tsaida kowa ya kuma sallami kowa,wanda kusan quarters ne guda daga can wani sashe daban na gidan da yawancinsu suke da nasu apartment din,ba lallai ma ka fahimci da wasu dake rayuwa cikin gidan bayan ainihin masu gidan saboda nisan tazarar dake a tsakaninsu. A hankali yake takawa zuwa ciki suna magana da farouq qasa qasa. "Na fita daga company,kuma ina tunanin sai gobe zan sak shiga......wani irin headache ne yake matsamin tun jiya......but daga dazun zuwa yanzu kaman ya qaru" "Dude.....kana over work fa?,Allow your self downtime......kana da aure amma a suna kawai......kasan benefit na aure kuwa da ba zasu qirgu ba?....Emotional support and mental health duka zaka samesu if ka bawa matarka damar shiga rayuwarka".... " Hey.....zaka fara ko?,waye ya gaya maka kowacce mace ake bawa dama ta shiga rayuwarka?,wasu matan poison ne fiye da yadda kake kimantawa,they are wicked" Ya fadi yana hadiye wani yawu lokacin da madaurin tunaninsa ya warware yana koma masa can shekarun baya.....sanda maamah ta zama silar rasa lafiyar mahaifinsu duk da kasancewarsa mutum ke kazar kazar,ta kuma zama silar barinsa sararin da suke kai yanxu suke rayuwa akai wato DUNIYA. Daidai sanda ta sauka daga saman high chair din data zauna a akai cikin kitchen din suna taba hira da ma'u,wadda take hada qullin wainar shinkafa zata soya musu "Bari na dauko na dawo" Tace da ma'u din tana gyara yafen qaramin Chantilly veil din data lullube sassalkan gashinta. Furucin nasa ya sanyata tsaiwa cak sanda muryarsa ta kaiwa kunnuwanta saqon da yake isarwa farouq,sai taja da baya tayi tsaye jikin qofar yana jiran wucewarsa don ta wuce itama zuwa dakin. "Let's try not to judge people and instead understand their perspectives". "Am not judging fa......dude ba zaka gane bane,na iso gida.....i need to rest.....call you later" "Okay byee" Farouq ya fada yana sauke wayar iska ya furzar daga bakinsa yana duban file din dake gabansa cikin katafaren kamfanin sarrafa kayan abincinsu dake sharada industrial area. Yanaji a ransa zai sake rage kwanakin tafiyar nan tasu ko wataqila hakan zai kawo kasuncin da yake fata tsakaninsa da ita. Yasha attempting saka amna cikin abun,yasan zatayi aiki sosai.....saidai kuma amna din quruciya tayi mata yawa,baisan ya zata dauki abun ba,uwa uba yana buqatar yayi komai cikin sirri. Shurun da taji cikin parlor din ya sanyata tunanin ya wuce,ta sauke siririyar ajiyar zuciya,kunnuwanta na maimaita mata da meye da meye ya fada akan mata?. Siririn tsaki ta saki zuciyarta na siffantashi da jerantashi cikin sahun mazan da sam bausan mutuncin diya mace ba....suke mata kallon kuma wata halitta da bata da wata daraja kwata kwata. Siririn tsakin daya sanyashi daga kansa a hankali daga rufe bottle na ruwan da ya tsaya ya bude yasha saboda yadda maqoshinsa ya bushe,yana ji kamar bazai iya qarasawa saman ba. Guri daya idanunsu suka hadu,ya kafeta da qwayar idanunsa da sukayi wani laushi tubus saboda yadda ciwon kan ke sara masa lungu da saqo na cikin kansa. A hankali ta zare nata idanun daga kanshi,sannan ta koma da baya zuwa kitchen din ba tare data qara koda second uku a wajen ba. Kansa shima ya dauke yana ajiye robar,sannan ya soma takawa a nutse yana wucewa ciki kafin ya haura zuwa saman. Tun daga wancan ranar bai qara ganin gilmawarta ba cikin gidan,wasu lokutan ma sai yaje gaida anni ta tambayeshi iyali take fado masa a rai. Wani irin mummuna fito na fito yayi da kansa akan damuwa da abinda tayi masa a ranar din,yana ganin bai cancanci ya sanya damuwarta a ransa har haka ba.....sai ya sake qarawa kansa wani busy din akan wanda yake ciki,yana saka ran wannan ya zama silar mancewarsa da komai,wanda yawan ayyukan da suka zarta qa'ida din daya azawa kansa yake kyautata zaton shine silar wannan ciwon kan da ya fara fama dashi. A gajiye da wani irin bacin rai da baisan meye dalilin faruwarsa ba daga shigowarsa gidan ya dinga zare suit din jikinsa yana zubarwa,duk da cewa ba al'adarsa bace hakan. Bathroom ya wuce kai tsaye,ya hada ruwa me dumi da zai dace da yanayin sassanyar iskar dake kadawa,wanda asalinta hadarine daya hado,bai saukar da ruwan ba,amma ya canza kala zuwa ruwan toka,ya kuma bada iska me sanyin dadi dake busawa da qamshin qasa,yanayin da yake bada tabbacin anyi ruwa a wani gurin kusa da kano. Mintuna kusan arbain ya fito daure da towel,gargasar jikinsa dama sumar kansa duka sun jiqe da ruwa. Faffadan qirjinsa dake lullube da gargasa ya fara gogewa da towel din yana isa gaban madubi,daidai sanda yaga wayarsa na haske. Kaman ya share saboda bayason doguwar magana,amma koda ya duba yaga maamah ce sai ya zamana bashi da wani zabi daya wuce ya daga kiran. Sai daya zauna saman bean bag chair din dake ajiye a gefe sannna ya daga hade da sallama. "Barka da yamma" Ya dora da fada yana lumshe idanunsa saboda yadda kansa yake sarawa. "Barka kadai......kana office ne?,inason ganinka idan kun tashi,akwai muhimmiyar magana da zamuyi da kai,sannan akwai baqi da sukeson ganinka" Ta fada kanta tsaye. Yatsun hannunsa da baya riqe da wayar ya cusa cikin sumarsa,yanajin yadda ta jero buqatunta kai tsaye ba tare da neman jin uzuri ba.....ya ya wuni?,akwai damuwa?,yana da lafiya ko babu?. Baisan sai yaushe wannan dabi'ar tata na damuwarta itace kadai damuwa zata sauya ba.....baisan sai yaushe zata damu da damuwar wani ba ta aje tata damuwar da son kan a gefe ba. "Bana company na dawo gida....." "Okay,to ya za'a yi kenan?,don duk yadda za'ayi inason ganinka lallai lallai a yau din,ko meye kakeyi ka katseshi kazo ka sameni" Ta sake fadi da dukka sautin da zai gaya masa da gaske take. Jaririyar ajiyar zuciya ya sauke yana cire yatsunsa daga sumar tasa "Ciwon kai nake maamah.......amma zansha magani na kwanta zuwa anjima zan shigo" Ya fada da raunanniyar murya,yana jin har qasan ransa ya rasa wani part me girma a rayuwarsa,yanajin ya rasa wani abu me matuqar muhimmanci a rayuwarsa. Duk da yana da anni,yana da farouq,yana da saddiq da musaddiq,amma lokuta da dama yana jin kamar shi kadai ne.....yanajin kamar shi kadai yake rayuwa a duniyar,wani irin maraici da kadaici yana mamayarsa. "Allah ya kaimu,kada kayi dare da yawa Allah ya sawwaqe" Ta hade maganar duka lokaci guda. Ya jima idanunsa saman wayar yana kallonta,zuciyarsa na tuna masa abubuwa da dama ciki harda abbansu. Tun asali shike damuwa kuma shike kasa bacci idan dayansu baida lafiya,koda ciwon baikai ya kawo ba. Tun da can ita din bame damuwa da lamuransu bace,tafi damuwa da duk hanyar da zata maida taro ta koma sisi. Sai daya bushe tas bai sani ba kafin ya miqe yana isa ga walk-in closet dinsa,boxer kawai ya zura bayan ya mulke jikinsa da cream dinsa,ya kuma shafe jikinsa da turarukansa,sai ya koma gefen gado ya zauna bayan ya balli wasu tabs na saukar da ciwon kai ya sha,ya dauki remote guda uku,daya ya zuge duka labulayen dakin dashi,daya ya kashe hasken duka fitilun dakin banda ta gefen gadon,dayan kuma ya saisaita sanyin ac din yadda zai daidai da yanayin da yake ciki. Cikin duvet ya shiga ya duqunqune yana lumshe idanunsa gami da sauke nannauyan numfashi,ya lumshe idanunsa yana son fatattakar kowanne tunani da lissafe lissafe ko zai samu brain dinsa tadan huce. Ana kiraye kirayen sallar magariba ya farka daga gajeran baccin daya daukeshi,yaji dadi sosai a jikinsa,sai ya wuce toilet yayi tsarki ya daura alwala. Masallaci ya wuce kai tsaye,akayi magariba da ishai duka dashi,sannan ya dawo ya shirya cikin tattausar exclusive Morocco ta maza me zuwa hade da wandonta. Kalar royal blue ce,sai akayi mata ado da gold zare daga wuyanta hannu aljihu qasan wandon da tsagar gefe da gefe na rigar. Wata zagayyar hula ya dora saman kansa ruwan gold din,wanda yawanci yankin larabawa su sukafi ta'ammali da ita,take farin bafullatanin nan muhammadu jikan jadda ya fito da wani irin kyau da zai wahala ka kalleshi sau daya ka kauda idanu (Niko nace uhmmmm,kaman kuwa yasan zance akazo yi gurinsa😂). Clogs ya sanya gold color,ya feshe jikinsa da mayen turarensan nan dake saurin kama zuciya. Key ya laluba a ma'ajiyarsu ya dauki spare key din daya daga cikin motocinsa. Yau din da kansa yake sha'awar yin driving,abinda ya jima rabonsa da yayi. Yanason ya shaqi fresh air dinnan shi kadai ba tare da wani a gefensa ba wai da sunan yana kare lafiyarsa ba. Ta kammale komai a daki kaman yadda ta saba duk dare,wanda idan ta shiga kuma ita da fitowa koda hallway ne sai kuma da safe. Tun wancan ranar ta sake jin ta tsani dukka wani abu da zai sake hadasu ko ya hada alaqarta dashi. Idan ta tuna tambayarsa din kuma takanji wani mugun haushinsa na sake mamayarta,tana jin a sannan me yasa bata amsa masa da eh wajen wani naje ba?. Sai data zauna tsaf sannan ta duba night stand fridge dinta babu ruwa ko qwaya daya a ciki. Baida girma fridge din,don haka kadan kadan take saka ruwan saboda gorar zata cika waje. Miqewa tayi tana yamutsa fuska,ta dauki Indonesian hijab dinta navy blue ta zura wanda ya haskata matuqa,ya kuma fidda lallausar sumar dake kwance gaban goshinta. Harta miqe ta dauki wayar huda da zuwa yanzun tayi nisa da amfani da ita,tayi playing drama din da take kalla daga inda take,a haka ta fita rabin hankalinta yana kan wayar. Wannan dalilin ya sanya bataji saukowarsa ba daga stairs din saboda lallausan clogs din dake qafarsa baya bada sauti ko kadan,duk kuwa da cewa da dan sassarfa yake saukowar yana gaggawar isa ga mota,so yake yaje ya dawo da wuri akwai ayyukan da bai samu daman yi ba dazu,yanaso ko cikin daki ya ragesu. Stairs din ya danyi kwana kadan wanda sai kazo rabi sannan zaka hangi wanda ke fitowa daga farkon hallway din,kaman shima......sai daya zo rabi sannan ya ganta. Idanunsa suka sauka saman fuskarta data fita fes cikin tsakiyar hijabin kalar luxury Morocco din jikinsa. Hasken dake fitowa daga cikin wayar ya haske fararen idanunta dake sheqi kamar an diga mai. Bai fasa saukowa ba kaman yadda taci gaba da takawa idanunta kafe akan wayar,har sai da cikin jikinta taji kamar ta iso qofar da zata sadata da parlor din. Daga kan da zatayi ta tsinceta dab dashi sanda yake stair din qarshe. Sai ta juya a hankali da zummar yi masa yadda ta saba wato komawa don ta kubcewa hada numfashi dashi.55 _Daga abu hurairah RA yace,manzan Allah S A W yace: "ku kashe baqaqe guda biyu koda kuna cikin sallah; MACIJI DA KUNAMA_ Taku biyu kacal tayi ya cimmata,ya kuma sanya hannunsa ya dawo da ita baya,sai gata tsaye cak a gabansa kaman ba inda ta matsa. Idanunta tsakiyar nasa idanun da suka qaa girma kadan saboda ciwon kan dazu,yayin da hucin numfashinsa ya dinga fita cakude da qamshin turaren jikinsa yana kaiwa ga hancinsa. "Wanne kalan dodo ne ko abun tsoro a jikina da kike gani?" Ya jefa mata tambayar a zafafe yana ware mata idanunsa. Ja baya tayi niyyar yi da sauri saboda yadda ta dan tsorata kadan da yadda idanun nasa suka qara girma,ga wani shimfidadden kwarjini dake fita daga cikinsu ya daki zuciyarta lokaci guda ya kuma ninka gudu da bugun zuciyartata. Hannunsa qwaya daya ya sanya yasake dawo da ita gabansa yana sake bude mata girman dukkanin idanunsa. "Ki nunan abinda ke baki tsoro a jikina nace!" Ya fada da dan tsawar takaicin abinda takeyi masan. Shi tun farko mutum me dan kai tsaye,koda laifi kayi masa yafison ka fuskanceshi kai tsaye.....haka koda matsala kake dashi yafiso ka tunkareshi kai tsaye ku warwareta. So take ta maida masa me zafi ko zata fanshe abinda ya gaya mata ranar nan,amma sai ta lalubi kwanyarta da bakinta tsaf ta rasa komai kamar an mata sata. Ringing din wayarsa ne ya sanyashi maida dubansa ga wayar. Kusan a tare idanunsu suka kai kai,kuma daga shi din har ita sunga sunan da yake rubuce a kai FAREEDA KHALED MUSTPHA. Maida dubanta tayi ga fuskarsa ba tare da tasan dalilin hakan ba,sai kawai ta zabi ta zille ta tsakanin qofar ragon da yayi mata,saidai kuma tana motsawa kamar hankalinsa yana maqale ne a jikinta ya daga kai ya watsa mata idanunsa bayan ya maida wayar aljihu ya sakeyin kicin kicin da fuska. "Daga yau duk ranar da kika qara ganina kika koma kaman kinga dodo saina biki har cikin dakin na zaneki tas ciki da baya". Maganar tayi mata banbarakwai,kamar wata nadra ko haneefa?,wannan mamakin ya bayyanata tsakiyar qwayar idanunta da baisan me yasa yake yawan sanya nasa idanun a cikinsu ba duk sanda magana irin haka ta hadasu. "Kina mamaki ne?,ko kina ganin kin wuce duka?,ki gwada koda gobe ne ki gani.....and,daga yau kada ki sake ganina baki gaidani ba......tunda ko banza ana ci dake ai ko?,koda ban baki abinda wadancan suke bakin ba" Ya qarashe maganar yana sakar mata hanya. Cikin qasa da second uku ruwan hawaye ya tararwa idanunta,ya za'ayi ya qara mata ciwo akan wancan ciwon,tana jin lallai yau ta barshi ya tafi haka yaci bulus din da ba'a taba cinta a kanta ba "Ka daina burga kaman kana da abun bayarwar.......ni bana buqatar ragowar su fareeda tunda akwai masu fresh......." Cak maganar ta tsaye mata a maqoshi sanda yayi wani irin waiwayowa daidai sanda yake dab da zarcewa falon. Batasan ta juya ba har ta soma tafiya zuwa dakinta ba sai da taji tana taka lallausan carpet din dake shimfide daga tsakiyar wajen. Dif wuta ta dauke masa,zuciyarsa ta shiga raya masa nau'ikan hukunci mafi tsauri daya dace yayi mata. Saidai kiran wayarsa ya sake katse masa duk wani hanzari,ya duba kiran a fusace yana tunanin fareeda ce,amma ganin maamah ya sanyashi tattare duk wani bala'i daya taso masa ya hadiyeshi,sannan ya daga wayar yace da ita a taqaice "On my way" "To ka hanzarta" Maamah ta fadi tana jin dadin yana hanya bawai yaqi amsa kiran nata bane. Kai ya jijjiga yana takawa a hankali yana ficewa,saidai a ransa yaci alwashin dole ya ajiye mata abun tunawar da bazai sake fadin magana ta maida masa ba. Duka duka shekarunta nawa amma sanadin aure raini yana neman shiga tsakani?". Ya fada qasan ranshi sanda yake tayar da motar. Da wani irin speed yake jan motar,wanda dama sabonshi ne gudu a mota,ba tun yau ba ba kowa ke iya shiga mota ba indai shine zai tuqa. Idonsa ya lumshe yana tuna abinda tace masan,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa.....zai wahala cikakkiyar budurwa me kunya ta iya fadin hakan.....ita kuwa bata cikin kowanne sahu,dom haka idan ta fadi sama da haka ma fuad kada kayi mamaki.....kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa. Har ya isa gidan maamah wannan kalmar ta kasa fita a ranshi "Ragowar su farida....kamar ma kana da abun bayarwar" Har cikin ransa ya gamsu ta rainashi,sai ya samu Kansa da kallon Kansa a side mirror,yana tuna dararen da yake kashewa a tsaye ba tare daya isa ya kwanta ba bare ya samu cikakken bacci saboda tsananin yadda ya kame kanshi. Da wannan bacin ran,da kuma tunanin hukunci mafi tsananin daya kamata ya dauka ya isa parlor din maamah. Mamaki na gasken gaske ya cikashi lokacin da yayi sallama ya tsinci fareeda cikin masu amsa masa sallamar tasa. Tana zaune hankali kwance saman sofa din parlor din. Sanye take da riga da wandon Palazzo daya bude sosai daga qasa. Rigar me gajeran hanny ta lafe a jikinta ta kamar yadda Palazzo din ya fidda shape din hips din ta zuwa qugunta. Bandana ce kawai saman kanta,hannunta riqe da wayarta. Kallo daya tak ya mata ya dauke kansa kai kace bai taba sanin wata halitta a duniya me ire iren kama da ita ba. Qasan maqoshinsa kuwa kawai kaiwa da kawowa maqogoronsa yakeyi,adams apple dinsa yana motsi daga sama zuwa qasa,ya taka a nutse kuma kai tsaye ya wuce gaban maamah din a ladabce. Tunda yayi sallamar ya shigo taji gaba daya an tsinke duk wata jijiya daka iya baiwa dan adam kuzari daga jikinta. Tunda take haukan son fuad bata taba tunanin haduwarsa da kyansa ya zarta yadda ta gagganshi bama sai yanzu data ganshi cikin shigar mutanen Morocco,wanda nan Nigeria zaka ga suna kama da tufafin da sarakuna ke sanyawa musamman idan suna ganawa da baqi cikin gida. Numfashinta cak yaso tsayawa,muhammad fuad ya wuce yadda take hangensa a nesa,a take taji tabbas zata iya sadaukar da komai data mallaka don ta samu fuad din a matsayin mijin aure (Anya....fuad din fa me tsada ne......amma muje zuwa,tunda kin kama maamah wataqila kina da rabo). Kusan duka gaisuwar da sukayi shida maamah da gajeriyar gabatarwar da maamah tayi masa bata ji ba "Baquwar taka ce muhammadu.......ina me umartarka ka saurareta ka kuma fahimceta.....duk wanda yayo tattaki qafa da qafa ya taho gareka saboda yana sonka ba qaramin masoyi bane,idan Allah yaso kuma matarka ce" Ta fadi maganan qarshe tana yunqurawa ta miqe. Daga kai yayi yana duban maamah sanda take jifan fareeda da murmushi,da salo kuma na bada goyon baya take cewa "Gashinan fareeda,bari na shiga na fito kafin ku gama" _idan Allah yaso kuma matarka ce_ yaji amsa kuwwar maganarta ta qarshe tana nanata kanta cikin kunnuwansa. Maganar sai taso ta masa kama da maganar data masa daidai sanda ta tilastashi auren waccar yarinyar.......me yake shirin faruwa?.ya tambayi kansa. "It will never happened" Ya fada yana qaryata komai da zuciyarsa ke qiyasta masa zai iya faruwa. "Hi......ka ganni har gida?,yanzu ka yarda garin masoyi baya nisa ko?" Ta fada tana sakar masa murmushi,murmushin nata dake daidai da diban garwashin wuta ta watsa masa. Wannan bai dameta ba,yanayin fuskarsa duka bata sakashi a mizanin damuwa ba.......zai gata ta zame tana saukowa qasa. Ta qaraso dab dashi tayi Zaman raquma tana dubansa "Please Muhammed kada kayi rejecting dina.....na maka alqawarin zame maka duk kalar matar da kakeso kake buri" Ta furta da tsananin narkewa. "Stop it please......ke me yasa baki nemawa kanki martaba mutunci da kima?". Ya fada bayan ya daga mata hannu ya dakatar da ita daga maganan farko launin idanunsa sun fara sauyawa saboda bacin rai. A rikice ta girgiza kai ganin yana juye mata zuw wannan fuad din me wahalar samu.....wannan fu'ad din me tsananin tsauri "Mutunci martaba da kima duka susha zamansu muddin zan samu muhammad fuad". Shuru ya ratsa qarshen maganarta,ya xuba mata ido yana sansano alamu alamun hauka tattare da ita,sai ya matsar da fuskarsa kusa da tata kadan,da wani sauti can qasa wanda tsanantar bacin rai da kuma sarawar da kansa yayi ya dawo da ciwonsa sabo fil ya tilas masa maganar a haka yace "Gashi shi kuma muhammad fu'ad din saida wadannan abubuwan ake samunsa......." Daga haka ya miqe tsam da zafin nama,sai gata ta miqe tare dashi cikin tsoro da fargabar kada yaqi tsayawa ya saurareta duk da kuwa ta dangana da mahaifiyarsa. "Umarni nake baki......ki tattara kayanki kibar gidan nan,kada na dawo jibi na sameki,don gobe ma tayimin kadan,bazan iya shaqar iska a wajen da kika dade a cikinsa ba". Yana kaiwa qarshe ya juya da zafin nama me gauraye da fushi ya soma fita. Ta dauka zata jure saita kasa,ta bishi a baya da gudu gudu tana kiran sunanss,saidai ko ta kanta baibi ba,ya bude motarsa ya shige ya kunna ya tasheta da wani irin qarfi ya fusgeta yana fita a gidan,don ko sanda ta qaraso sawayen motar kawai ta samu,saita zube a wajen tana qwala kiran sunansa,abinda kunnuwan maamah suka jiye mata kenan,ta fara saukowa da sassarfa daga sama. Baisan yadda yakai kanshi gida ba saboda tashin hankali da tsananin ciwon kan daya saukar masa,shidai yaji daya daga cikin security nasa na cewa yabar motar daga nan zai qarasa shigo da ita ya gyara parking din. "Sai yaushe maamah zata canza?,sai yaushe zata zama cikakkiyar uwa?,sai yaushe zata zabi girma da mutunci sama da kudi?,sai yaushe?,sai yaushe?". Kusan wannan shine abinda ya sanyashi kwana ya kuma tashi da ciwon kan daya hanashi fita,ya kuma kashe dukka wayoyinsa don baya qaunar ya nemi wani ko shi a nemeshi. *_WASHEGARI__* *_BAQIN DARE_* *_MUHAMMAD JADDA RESIDENT_* *10:45 NA DARE* Tunda ta fara kallon film din hankalinta bai kwanta ba sai yau da taga qarshensa. Duk da cewa ya bata mata lokaci sosai,don sai a yanzun sha daya saura na dare ta kammala......amma kuma ya haifar mata da wani irin nishadi a zuciyarta,nishadin da duk idan ta tuna yadda rayuwar stars din ta kasance a ciki sai taji ta saki dan murmushi kadan. Sam ita din ba ma'abociyar kallo bace......wannan shine film na farko data fara kara full kuma wai korean series. Idanunta ta lumshe tana shaqar iskar dake kadawa sosai take kuma yiwa kanta hanya ta windows din dakin da yawanci yakan barshi a bude saboda samun fresh air da tafi iskar ac artificial air dadi a wajenta. Gabanta yadan buga kadan,tayi kuma hanzarin bude idanunta sanda taji kaman motsin taba window din. Ta tsaya cak daga qoqarin fidda rigar jikinta da takeyi,tsahon mintuna biyar bata sake jin komai ba,saita matsa gaban windows din dukansu,ta bisu daya bayan daya ta zugesu,ta kuma sanya musu lock. "Sabreena kin zama matsoraciya" Ta tsokani kanta da kanta,ta kuma sakarwa kanta da kanta din murmushi. Ita kanta batasan yaushe ta koma hakan ba,saidai girman gidan koda rana ce ta take tsoro yake bata,duk da tassn cike yake da security musamman idan ma'u ta gama kai kawonta ita da ameh kowa ya wuce gefansa. Towel ta daura babba,har zata wuce toilet din taji kaman yau garin da iska,don haka ta miqa hannu ta dauki hijab din da tayi salla dashi ta zura a jikinta ta wuce bandakin. Tana wankan amma kadan kadan takejin gabanta yana faduwa wanda ita kanta batasan dalili ba. Yau din sai ta samu kanta da rage tsahon lokacin da takan dauka a bandakin,cikin qasa da mintuna goma ta kammala,tayi brush ta busar da kanta,sannan ta daura towel din ta maida hijabinta ta fara takowa tana fitowa. Sanda ta dora hannunta akan handle din gabanta ya sake yankewa ya fadi. "Hasbiyallahu wa ni'imal wakeel" Ta furta a hankali kaman yadda yanzu yadan fara zama a jikinta,don cikin jadawalin karatunsu da rumaisa akwai azkar sosai da addu'o'i masu yawan gaske. Jiki a sanyaye ta murda handle din ta jawo qofar ta bude sannan ta fito,kai tsaye ta soma nufar madubi. Abun mamakin yadda takejin baqon qamshi cikin dakin,tadan tsaya kadan tana buda hancinta still qamshin takeji,sai kuma tunanin iskar dake ratsowa ta cikin rufaffun windows din qilan ke debo qamshin daga waje zuwa dakin,don haka hankalinta kwance ta qarasa gaban mirror din tana duba fuskarta da jiya taqi wani qurji qwaya daya ya fito mata. Wutace tsaf ta dauke mata kafin wata mahaukaciyar faduwar gaba ta rufto mata,tun daga saman kanta har zuwa yatsun qafafunta da ganin fuskar dake tsaye a bayanta. Dagawa qirjinta ya shiga yi daga sama zuwa qasa cikin wata irin razana da takejin kamar tana shirin dimaucewa ne......sake matsota yakeyi idanunsa cikin nata,kaman yadda fuskarsa ke shimfide da shu'umin murmushin nan data saba gani a fuskarsa a shekarun baya. "Mmmm........." Ta dinga yunqurin fadin sunansa,amma sai taji kaman an sanya gum an manne labbanta na sama da qasa guri guda. *_TOFA!_* *_WAYE WANNAN?_* *_NACE WAYE WANNAN?_* *_MUHAMMAD FU'AD NE DA KANSA?_* *_KO KUMA WANI MUTUMIN NE NA DABAN?_* *_TURQASHI_* *_Allah yasa muna cikin masu rabon ganin ranar litinin lafiya_* *_karku yadda karki yarda aci gaba da sukuwa da zamiya cikin labarin nan ba tare dake ba_* *DA SAURAN KALLO!!!* Tofa nayi qarqaf😂😂 Allah ya bani ikon baku na ranar monday🙏🏽🙏🏽🙏🏽😂56 _Daga ummu habiba uwar muminai Allah ya qara yarda a gareta tace,naji manzon Allah S A W yana cewa "duk wanda ya sallaci raka'a sha biyu daga rana zuwa dare(bayan sallar farillai guda biyar),Allah zai gina masa gida dasu a aljanna_ _muslmin ne ya rawaito_ _raka'o'in nan sha biyu sune,biyu kafin asuba,hudu kafin azahar da biyu bayan azahar,biyu bayan magariba,biyu bayan isha'i saiki qara da wuturi_ _Sannan akwai hidisi me zaman kansa abdullahi bin umar ya rawaito,manzan Allah S A W yace ALLAH KA YIWA BAYAN DAKE SALLAH RAKA'A HUDU KAFIN SALLAR LA'ASAR RAHAMA_ *_IBADA DUK IBADA CE,AMMA MAFI SOYUWAR AIKI A WAJEN ALLAH DUK QANQANTARSA SHINE WANDA ZAKA DAWWAMA KANA YI,SAIKA DAUKI WANDA KASAN ZAKA IYA DOREWA_* Tana kallonsa ta cikin madubin yana ci gaba da kusanto inda take,saidai gaba daya ta kasa motsa koda yatsanta ne ballantana tayi tunanin abu na gaba daya kamata ace ta aiwatar. Shu'umin murmushinsa da kallon da yake dubanta dashi duka ba wanda ya fasa,yaci gaba da kusantota kowacce gaba ta jikinsa tana jin wani shauqi tare da dokanta ta sadar da kanshi gareta. Irin yadda ya fitinu da ita ba abu bane me sauqin fassarawa ba......sai kuma gashi a bagas zaice ko a banza wata hanya ta samun isa gareta ta riskeshi cikin sauqi,wanda zai iya kiran hakan da qatotuwar sa'a cikin rayuwarsa. "Mashkur!" Ta fusgi sunan da hanzari ta kirashi a tsawace bayan ta maimaita la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen har batasan adadi ba. Tsaiwar da yayi ita ta bata damar waiwayowa da wani irin hanzari kamar wadda aka fusga. Idanu ta zuba masa kaman yadda shima idanun ya zuba mata yake kallonta da dukka iyakacin kallonsa. "Me ya kawoka gidan mutane?......har dakin matar aure?" Ta fadi da wata irin birkitacciyar murya data cika da razani da tsoro. Wata irin dariya ya qyaqyace da ita,harda komawa ya fada saman gadon nata,sannan ya tashi ya miqe yana fuskantarta. Ya bude baki zaiyi magana a hankali sautin saukar ruwan saman farko ya baqunci kunnensu,shatin ruwan ya fara sauka ta glass din windown dakin sai ya saki murmushi yana dawo da dubansa kanta. "Kin gani ko?,.....ko Allah ma yana sona......ko Allah ma yasan kin cuceni....kuma ko Allah yasan kedin azzaluma ce,wannan zubar ruwan shi zai sake toshe kunnen duk wani da kike tunanin zai ceceki ko zai kawo miki dauki,duk da kuwa wannan ginin gidan naku dama kaman anyishi ne domin ni,yana riqe sirrin kowanne motsi yadda ya kamata". Ya fada yana kallon yanayin roofing na dakin yana sakin murmushi. "Nayi mamaki wai da kike tambayata abinda ya kawoni,bayan akwai basussuka na da yawa a kanki?". "Mashkur ka haukacene?,kasan gidan waye ka shigo?,gidan matar aure har tsakiyar dakin aurenta..... " Fara takowa yayi yana sake nufota yana dariya "Ina cikin gidan muhammad fu'ad jadda,the owner of jadda diamondchore resources.......sannan ke din sabreena ce,mata a wajensa.....bayanin yayi daidai?" Ya jefa mata tambayar yana dage mata dukka girarsa biyun bayan ya tsaya daga takowar da yakeyi. "Ko kina buqatar wani qarin bayanin?......kinaso ne na gaya miki da license dina na shigo gidan nan?,da license daga hannun wata mace mafi kusanci da me gidan?". Daukan tunaninta yayi ya luluqa wajen lalubar ma'anar abinda yake fada,da license daga hannun wata mace mafi kusa da me gidan?,wace kenan?. Kaman yasan abinda take tunani a kai yace "No dear......kada ki wahal da kanki wajen tunanin wace..... Ki bari na gama kashe qishirwata sosai sannan mu zauna mu tattauna..... I need you.....na azabtu da yadda asara biyu ta fadamin......babu ke ba kudina......come please" Ya furta yana kawo mata cafka. Batasan tana da tsananin zafin nama har haka ba sai data kufce masa ya kama iska. Sukabi hannunsa da kallo dukka su biyun shi da ita. Shi dariya ya saki yana jijjiga kai "Kada ki dauka kedin me sa'a ce ko da yaushe.......idan a wancan karon kin kubcemin...... Na rantse wannan karon baki isa ki kubuta ba,koda kuwa a gaban mijinki ne a yau sai na kashe qishirwar dake raina" Ya furta yana daga rigarsa,take ta hangi hancin bindiga daga aljihun trouser dinsa. Kaman an debo bulo an jibga mata haka taji wani matsanancin tashin hankali ya keto mata,bata gama sauke abinda ya taso mata ba ta ganshi ya taso mata yayo kanta gadan gadan. Wani irin qarfi ne yazo mata,ta tattara hijabin jikinta da batakai ga cireshi ba da kyau ta haura sofa bed din dake gabanta ta wuce tsakiyar gadon "Ka fita min a gida.... Ka fita tun ban tada security din gidan nan ba" Ta fada tana duban sashen da wayar girke take a dakin wadda zata baka daman kiran kowanne sashe na gidan. Ta shiga shock sosai sanda ta lura ya gutsire wayar gaba daya ya fasa kan,duka yaushe yayi hakan da ko alama bataji ba. Dariya ya saki yana cewa "Kinga abinda ya samu telephone din ko?....." Bata bari ya qarasa ba ta tattara dukkanin qarfinta ta kwarara ihu tana fadin "Wani ya taimakeni" Abinda ta dinga maimaitawa kenan har sai da taji maqoshinta yana wani suya da radadi. Dakatawa tayi hawaye suna cika idanunta,tana duban mashkur dake qyaqyata dariya. "Zan iya qara miki lokaci kici gaba da ihu......kiyita ihu har iya yadda kikeso". "Fuad!. ....fuad!!!!" Ta sake qwalawa kiran sunansa. Karo na farko da ta fara ambatar sunan nasa kenan. "Yana can yana bacci" Ya fada yana juyi kaman zai taka rawa "Na sakashi bacci,kuma bazai tashi yanzu ba,sai na gama hutawa da matarsa" Ya sake maimaitawa cikin yanayin nishadin da kana kallonsa zakayi imani yakai masa har qasan zuciyarsa nishadin da yake ciki. "Mashkur,........ka saurara haka,ya kamata kasan kuskure kake tafkawa ba qarami ba.......ketawa matar aure haddi mashkur?!" Ta furta a tsawace. Dariyar nishadi ya saki yana kallonta,ya kama button din rigarsa ta saman ya fara ballewa yana zareta ya yar. "Kada kiyi kaman bakisan komai ba.......kina tunanin yaune na farko dana fara kwanciya da matan aure?,na kwanta dasu har bansan adadi ba......kawai ke dince ta daban,kin kasa fita a raina......bazan miki qarya ba,koda na dandana yadda kike banajin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba......shawara daya kawai zan baki,kada kiyimin gaddama.......ki bani kawai salin alin don na tabbatar kinsan komai,ba wani abu baqo a wajenki" Sasai kalamansa sukayi mata nauyi a qirji,ta tabbatar inda za'a tsaga jikinta ba za'a taras da jini ko digo ba saboda tsananin tsoro da fargici. Ranta yakai maqurar baci sanda taga yana yunqurin haurowa gadon "Har ka mutu mashkur ba zaka taba samun komai daga gareni ba.... Ko gawata tafi qarfinka mashkur bare gangar jikina a sanda numfashi yake busawa". "Well.....tunda kin zabi muje ta haka dake!" Da furucin da haurowarsa saman gadon duka lokaci guda suka faru. Wani tsalle tayi da zummar barin gadon,saidai kuma ya samu nasarar take qasan hijabinta da qafarsa ganin zata kufce masa,abinda ya sanyata data dira din bata sauka a daidai ba,hannunta ya daki side bed ya bada wani irin qum. Qara ta saki cikin tsananin azaba......azabar da bata hanata ci gaba da qoqarin qwatar kanta ba,cikin sa'a santsin bedsheets din dana hijabinta suka sanyashi ya zame zaman lallausar katifar,saita miqe itama,amma ta kuma zamewa take fuskarta ta bugi gefan bedside din still. Bata damu da radadin daya sake ratsata ba.....sake miqewa tayi tana harin qofa,abinda ya lura dashi kenan shima ya miqe da azama,tana isa qofar shima yana qarasawa sanda take kici kicin bude key din,ta finciketa ya watsar ya saka key ya kulle qofar. A zafafe yabar bakin qofar yana nufar qofar toilet yana cewa. "Yau zaki gane waye mashkur.....tunda baki zabi komai ya kasance ta hanyar maslaha ba" Key din jikin qofar toilet din shima ya murza ya kulle,tana kallonsa sanda take qoqarin sake tashi saboda buguwar da tayi a hannu da fuska,yadan bude window din waje ya watsa Keys din sannan ya sake waiwayota. "Kaji tsoron Allah mashkur......kada ka keta haddin aure.......da auren wani a kaina.......ba bazawara ko budurwa bace!" "Allah yasa tattabara ce ke" Ya fada cikin rashin damuwa yana durfafota da sassarfa kaman me wasan motsa jiki. Cafka ya sake kawo.mata ta sake samun nasarar gocewa abinda ya sake qona masa rai,sai kawai ya zabi ya galabaitar da ita.....don duka alamu sun nuna masa cewa gwana ce wajen iya zilliya,kada ta bata masa time ta kuma bata masa plan,don haka yakai mata naushi. Ya sameta ta kafadarta ne yayin da nashi hannun ya wuce ya daki bango,abinda ya sanya wata azaba me tsanani ratsa kwanyarsa. "Ouch!" Ya fada cikin tsananin jin zafi,yayin da zuciyarsa ta sake tunzura "Ni xaki sanya naji rauni?". Yana kaiwa nan ya shammaceta yakai mata qafa ya kwasheta,take ta fadi ta bugu da qasa. "Wayyo Allah na" Ta fada cikin tsananin radadi tana riqe qugunta gami da runtse idanunta. Wannan shine abinda ya bashi daman isowa gareta,ya kama bayan kanta inda ta tattare gashinta tayi gammo dashi ya riqe gam. Wata azaba ta ziyarci tsakiyar kanta zuwa qwaqwalwarta,ba shiri ta sake qwalla qarar da zuwa yanzu ta yanke tsammani akwai me cetonta. Yana riqe da kan nata ya turata har saman dressing table dinta,baiyi wata wata ba ya buga goshinta samanshi,take goshin nata ya fashe,saidai kuma tana dagowa ta dago da bedside lamp da akayi ado da ita saman mirror din ta kwatsa mata ita tsakiyar kanta,abinda ya sanyashi sakinta ba shiri yana dafe da wajen. Duk da wajen bai shafe ba amma take yayi wani malulu azaba ta shiga ratsashi tako ina. Ya kalleta sanda jini ya fara diga jikin sky blue din hijabinta yana jin wani fushi mara misali yana saukar masa. Bai taba tunanin zaiyi minti biyar ba daga sanda ya shigo dakin ba tare daya samu galaba a kanta ba,sai gashi yanzu wankin hula yana neman kaishi dare... 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 57 57 _Daga abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace "mafi falalar sallah bayan sallar farilla itace sallar dare_ *_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqa😄,Allah ya bada ikon jurewa_* Ga mamakinta sai taga ya samu waje ya zauna yana mulmula wajen. Tsahon mintuna tana tsaye tana kallonsa tana dafe da inda jinin keci gaba da diga bata da abun tareshi. Ko na minti guda taqi yarda ta dauke kallonsa a kanta gudun kada ya mamayeta bata shirya ba. Hannun nasa ya sauke,ya fidda kwalin wiwi,ya zari guda biyu ya kunna musu ashana sannan ya sanya duka biyun a bakinsa ya soma zuqa cikin gwanancewa. Yadda ya tsara zaiyi da ita sai yaji me yasa bai taho da kayan mayensa ba?,ko banza yafi samun kalan nishadin da yakeso?,ya yanke ya fara zama yasha wiwi dinne don yadan huce kadan ta yadda zaifijin gardin abun. Tunda ya kunna wiwi din hankalinta yayi mummunan tashi. Ta san tabbas zata shiga wani mummunan yanayi ne da idan batayi wasa ba xai galabaitar da ita. Asthma dinta,ba kalar hayaqin dake saurin tayar da ita irin hayaqin wiwi taba da shisha. Matsawa baya ta dinga yi tana duban yadda hayaqin ya fara gauraye dakin,yana canxa yanayinsa daga ainihin qamshi xuwa gurbataccen warinta maras dadin shaqa. Dukka hijabin ta cukuikuyeshi tana rufe hancinta dashi,a hankali tana jin yanayinta yana son ya fara sauyawa. "Zaki fahimci abinda ake nufi yau da asalin fyade" Kamar mugun dawa haka ya miqe zumbur ya kuma nufota,ta juya itama da nata hanzarin da nufin barin gurin,saidai tuni ya miqa hannu ya danqo hijabinta ya dawo da ita gabansa tana fuskantarsa. Yadda take qoqarin toshe hancinta a nasa tunanin ya karanci batason warin wiwin ne,don haka ya zuqeta sosai ya kuma soma fesa mata ita saman fuskarta. Kauda kanta tayi sosai tana dauke numfashin da zuwa sannan tana jin kamar ya fara daina isarta "Ba wannan hijabin ba?" Ya fada yan yamutsa hijabin cikin hannunsa,abinda ya sanya ta takurewa gaba daya guri guda tana qoqarin neman hanyar da zata samu iska me kyau gudun gushewar hankalinta,wanda wannan na daya daga cikin damar da zai samu cikakkiya kan ya aikata komai hankalinsa kwance. Wata wawiyar zuqa ya yiwa wiwi din ya sake fesa mata kan fuska,sannan ta birkitota gaba daya yana kici kicin fincike hijabin daga jikin ta. Dole ta daga fuskarta,duk da yamutsewar hazon dakin dole ta bude kafofin shan iskarta ta fara masa magana a rarrabe "Kada ka ketamin haddi na,kada ka lalatamin mutuncina" Tayi.maganar sanda ya samu nasarar salube kan hijabin daga kanta. Bayyanar sassalkar sumarta ya sanyashi sake gigicewa,bai taba tunanin ta mallaki suma har haka ba. "Wow" Ya fada yana qoqarin samun wuyan hijabin don itace hanya mafi sauqi da zata bashi damar tsarge hijabin cikin sauqi daga jikinta. Ta fahimci abinda yake shirin yi,saita tattara dukka dan qarfinta ta cukuikuyeshi da kyau tana kiran sunansa cikin qaraji gami da fadin "Kada ka aikata!.....ka qyaleni mashkurrrr!!!!". A hankali ya bude idanunsa wadanda basu sauka akan komai ba sai agogon dake gefan gadon nashi. Idanu ya zuba mishi kafin ya miqa hannu a hankali yana jawoshi yana duba time da weather na gari. A nan yaga alamun saukar ruwan sama,sai ya maidashi sannan a hankali ya furta addu'a yayin saukar ruwan sama 'ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI'AN'. A nutse ya tashi daga kwanciyar,ya motsa kadan yana sauke qafafunsa daga qasan gadon wanda suka sauka daidai bedroom slippers dinsa yana jin yadda gaba daya ciwon kan da yakeji din ya sauka. A yanzun tsabar ta'ammali da home remedies ya sanya ba kasafai ya fiya afawa kansa qwayoyin bature ba yayin zazzabi da ciwon kai ba. Miqewa yayi ya fara takawa zuwa qofa yana mamakin yawan baccin da yayi,yadan shafi cikinsa yana jin yadda yunwa ta fara yamutsa hanjinsa,don haka ya yanke shawarar ya sauka qasa kawai yaci abinci,yadan duba ayyukansa koda na awa biyu ne kafin ya sake kwanciya. A parlor ya tsaya ya duba wayarsa,ya samu tarin miscal amma ciki na farouq yafi yawa,ya samu saqonsa da yake masa mita akan bai bada komai na tafiyarsu ba bayan saura sati guda. Qasan zuciyarsa kawai yayi murmushi yana sauka daga duba saqonnin. Har ya aje wayar wani tunani ya fado masa,sai ya tsaya ya zubawa qofa idanu. Yana tuna tahowarta ne jiya daga bedroom dinta zuwa qofan falo. Tabbas idan idanunsa ba qarya sukayi masa ba kallo yaga tanayi. "A ina ta samu waya?,waye ya bata waya?" Ya yiwa kansa tambayar a bayyane yana zurfafa nazarin ta inda zata samu waya tana cikin gida. Kaman yadda ya sanya doka ya sani ba wanda ke shiga gidan,sai amna da tazo baifi sau biyu ba. Amna kuwa yayi imanin ba zata taba bata waya ba musamman idan ta gaya mata shi ya karbe. Duk abinda yayi ko ya aikata amna tasan yana da dalili,ta fita saninsa,so ba zata karya dokarsa ba. Kai ya jinjina yana tuna fitar da tayi ba tare da sani ko izininsa ba rannan,tabbas wayar tana da alaqa da wannan fitar duk da ya bincika babu wani abu da yayi kama da gurin wani taje.....amma how and when ta samu waya?. Tambayar data masa susa kenan a qirji. Yanaji kaman ya kamata ya maida hankali a saka CCTV din. Company din yazo har sau biyu shi yace su bari ya zama free ya kirasu,yana jin kamar gamsuwa daya fara bawa kansa don tana karatun addini sosai a yanzu ta hannun jikar malam.....kaman bai kamata ya bata amanna har haka ba. Da wannan tunanin ya bude smart door dinsa,ya kuma fara sauka zuwa qasa. Abinda ya soma bashi mamaki shine jin gaurayar wani qamshi qamshi me kama da wari wari da gauraye stairs din. Koda ya kawo qarshenta sai yaji warin yana dada qarfi,ya tsaya cak yana buda hancinsa sosai,a nan yaji daga inda warin yafi qarfi. Mamaki ya kamashi sosai,yana da wani irin experience na iya hasashen abu da gano sauyawar motsi ko yanayi kaman wanda ya karanci aikin binciken tsaro na sirri. Fara takawa yayi zuwa cikin hallway din a hankali,yana sake shiga ciki xarginsa kuma na sake qarfafa saboda daduwar warin da sai a sannan ya fahimci warin wiwi ne. "Wiwi?" Ta maimaita sunanta can qasan maqoshinsa sanda ya iso bakin qofar dakin. Tsaiwar da yayi duka baifi ta minti guda ba,amma sai yaji jikinsa bai aminta da dakin ba,baya buqatar yayi knocking don ba qa'idar bincike bace akan abinda kakeson ganin gaskiyarsa quru quru,juyawa yayi da sassarfa yana tuna inda yaga an tanada a dakin nasa saboda ajiye kowanne key na kowacce qofa ta gidan a matsayinsa na mamallakin Master bedroom. Dubawa daya ya hango master key,sai ya daukoshi yana juyawa gami da saukowa kai tsaye yana nufar hallway din. Ta riqe ya riqr,yaja taja,har daga baya ya fahimci kamar hayaqin wiwin din kawai ke iya bugar da ita. Hakan ya sakashi tsugunnawa ya dauki guntuwar data rage,ya jata da kyau ya fesa mata a fuska. Numfashin ta ne ya soma yankewa,ta jawoshi da wani irin hanzari tana tuna komai zai iya faruwa idan ta sake ta rasa numfashinta. Ci gaba yayi da bulbula mata tana ci gaba da riqe numfashin nata da taimakon hasbunallahu wa ni'imal wakil da take ambata cikin maqogoronta. Dariyar mugunta ya saki,sai kuma yace "Are you asthmatic?" Bai jira komai ba ya danna mata wiwi din a baki,abinda ya birkitata kenan ya sanyata hautsinewar da batasan sanda ta daki al'aurarsa da gwiwar qafarta ba,tsananin zafi ya sakashi sakinta gami da hankadata....dukka jikinta ya gama saki,numfashinta kuma yayi qaura daga gangar jikinta,wannan ya sanyata tafiya luuuuu bakin qofar dakin,wanda haka dama ya saita da nufin fuskarta ta daki qofa ta kuma suma kafin ya gama daidaita radadin daya ziyarceshi. Saidai kuma tana isa bakin qofar sai yayi daidai da sanda ya murza handle ya bude,abubuwa biyu duka dakeshi,warin wiwi da fadowarta qirjinsa da guntun wiwin a bakinta,sulalewarta a jikinsa ya sanyata ta gangara ta fadi ta gefen bakinta,ta qarasa zubewa a jikinsa unconscious. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 58 58 _Daga ibn abbas RA,manzan Allah S A W yace"duk wanda yaji kiran sallah baije yayi sallar ba(ya zauna ya yita a gida).to bashi da sallah,saidai idan wani uzuri ya hanashi fita(kamar yanayin firgici na rashin tsaro ko tsoro)_ Dukkanin hannayensa ya sanya tallabota jikinsa yana bin guntun wiwin din daya fadi da kallo. Maido dubansa ya sakeyi fuskarta cikin wani irin yanayi dashi kansa baisan yadda zai fassarashi ba,sannan ya sake daga kansa yana bin mashkur dake tsaye da wani birkitaccen kallo. Na wucin gadi tsaf tunaninsa ya tsaya kafin qwaqwalwarsa ta dawo da aiki,yayi hanzarin maida dubansa fuskarta da take bayyanar da gushewar numfashi a tattare da ita. Tattarota yayi sosai sannan ya dagata cak yana jin wani abu yana zagayaw a gangar jikinsa. Waye wannan cikin dakinta?,waye wannan da yanayin da ya tabbatar masa ba mutumin kirki ko aziqi ne ba.....me ya kawo qaton gardi cikin tsakiyar dakinta daya kaure da mummunan warin wiwi. Duka yana da buqatar wadannan amsoshin,to amma kuma hankalinsa ya rabu gida biyu yana jin kamar ya fara cetar numfashinta da ya dauke shine abu mafi muhimmanci na farko a tare dashi. "Ina zakaje da ita?" Muryar mashkur dake a shaqe ta sauka a kunnuwansa sanda ya fara dosar qofar dakin da ita. Wani mahaukacin mamaki ya kasheshi daya sanyashi waiwayowa ya zubewa mashkur idanunsa. A karon farko kaifin birkitattun idanun fu'ad din suka ratsa nasa jijiyoyin idanun suka kuma aike saqo ga sassan jikinsa,saidai kuma a yadda yakejin zuciyar tasa a tsike......ba muhammad jadda ba...koma waye zai iya fito na fito dashi indai akan cikar muradinsa ne. "Shawara zan baka ka ajiyeta ka rufe mana qofa......don ba suma ba......ko mutuwa tayi tabbas sai na biya buqatata a kanta.......ita ta kira wannan ruwan.......ita ta kira fitina a sanda fitinar take bacci". Wani dummmm fu'ad yaji kunnuwansa sun masa na wani lokaci,take wani irin gumi ke dumi ya soma fesowa ta kowacce kafar gashi ta jikinsa. Idanunsa suka soma sauya launi tamkar an diga jan zabibi a cikinsu. Murna da mamaki suka cakude suka saukarwa mashkur sanda yaga ya sake turo qofar dakin yana dawowa. Saidai shakku sun cikashi a sanda yake tuna waye muhammad fu'ad?......wanne risk ya tsallake kafin ya zama abinda ya zama yanzu?,kafin ma ya mallaki asalin abinda ya zama shine silar arxiqinsa a yanxu?. Kyakkyawar ajiya yayi mata saman sofa din,da wani irin zafi ya miqe yana nufar inda mashkur yake tsaye yana danne da inda ta doka masa bedside lamp da har yanzu wajen yake masa matuqar zugi. Tun daga yadda idanunsa suka jirkice da kuma yadda jikinsa yake wani irin shaking hankalin mashkur ya fara dawowa jikinsa. "Dakata!......kada ka qaraso nan wajen!" Mashkur ya fara da qarfi shima yana qoqarin ciro bindigar dake maqale a qugunsa. "Waye kai?!" Fu'ad ya watsawa mashkur tambaya da sautin tsawar data sanya dukka dakin ya dauki amsa kuwa ba tare daya damu da bindigar dake riqe a hannun mashkur din ba. "Sanin koni wanene bazai maka amfani ba......abu daya zan baka shawara kaman dai dazu,ka juya ka fita salin alin ka barni da ita". Kalmar tasa ta qarshe ta sake zamantowa tamkar digar ruwan dalma saman sabuwar fatar jariri. Ya daga qafarsa ya soma takawa da wani irin fushi zuwa inda mashkur ke tsaye idanunsa na sake ninka rinewarsu,kai kace bai fahimci da gaske bindiga bace a hannun mashkur ba. "Waye kai!!!" Ya sake maimaitawa kaman zai tsaga dakin da muryarsa yana jin wani bala'i daga saman zuciyarsa. Takowar tasa da yadda yake durfafarsa ba wani sauran tsoro......yana tunkararsa ne kai tsaye kaman bindigar wasan yara ce riqe a hannunsa bata gaske ba shine yake saka dulmiya mashkur a matsanancin mamaki......mamakin da yake qarasa dauke ragowar duk wata nutsuwa dake jikinsa yana kuma dagula masa lissafi da Kalar jarumtar da yake hange tattare dashi. "Ina sake gaya maka,kaman yadda ta jawoni rayuwarta......yau ko zaka mutu sai na kwanta da matark......." Bai samu daman qarasawa ba saboda saukr kwalbar turare saman daidai bakinsa,ta kuma fashe a take,abinda ya bata daman yankan wani sashe na fuskarsa.......ya kuma sanya jini soma diga. Saukar kwalbar a fuskarsa ya sanya bindigar subucewa daga hannunsa. Jinin daya soma diga a fuskarsa baija hankalinsa ba fiye da faduwar bindigar daga hannunsa. Yayi imani bashi da garkuwar data wuce masa bindigar,kuma muddin ta subuce masa to tabbas dukkan wata dama ta subuce masa,tuna wannan ya sanyashi durqusawa ya saka hannu yana laluben inda ta tsalle ta fadi. Daga can gefan gadon ya hangota,da azama da kuma sassarfa ya zura hannunsa da zummar daukota,saidai kuma ya makara,don yana dora hannunsa akai qafar fu'ad na sauka saman hannun nasa. Da dukkan qarfinsa ya take masa hannun,wani irin zafi da radadi suka ziyarceshi yana jin kamar dukka yatsunsa biyar sun karye. Daya hannun nasa mashkur ya sanya da nufin ture qafar fu'ad din,amma ta nan ma ya rigashi ta hanyar sanya daga qafar tasa ya daki tsintsiyar hannun fu'ad din,bai kuma bari radadin ya gama ratsashi ba ya sake take daya hannun da dole ta sakashi ya zare hannun daga saman bindigar. Da qafa fu'ad ya daki bindigar ta qarasa shigewa can qarqashin gadon,abinda ya daga hankalin mashkur kenan "Komai zai iya kwabemin......dole na samu abinda nazo nema koda guda daya ne cikin biyu...." Bai qarasa qulla mafitar data dace dashi ba wani kyakkyawan naushi ya saukar masa a tsakiyar kansa. Azaba ce ta ratsashi tun daga tsakiyar qwaqwalwarsa har zuwa tafin qafarsa,bai murmure ba wani lafiyayyen naushin ya sauka a kumatunsa. Qarfin naushin ya sakashi yin baya,yayu taga taga zai fadi ya dire da qafarsa. Cikin abinda bai gaza second daya ba yaji wani abu me yauqi da gishiri ya cika masa baki,dole ya hadiye ko ya zubar wanda zubarwar yakejin zaifi masa,sai ya furzar din yana jin yadda kansa ya sake qullewa da azabar data zarce har cikin bakinsa. Furzar da jinin saman marbles din ya bada sauti,saiga haqoransa nan jere reras guda hudu da haskensu ya bayyana cikin jajur din jinin. Idanu warwaje yake duban fu'ad,ya tabbatar ya masa illa ta farko kenan da har ya mutu da ita xai tafi lahira?,zuciya ta ciyosa,ta yaya yana namiji shima haka ya tsaya ya masa irin wannan barnar,wannan tunanin ya sanya koda yakai masa naushi na uku ya kauce ya naushi iska,sannan kuma hannunsa ya zarce zuwa ga glass din madubi dake daura da wajen,take ya tarwatse zuwa piece's,ya kuma samu lallausar fatar hannunsa ya yanki inda yakeso. Cikin qasa da second daya shima jini ya soma diga da mugun gudu a a tafin hannunsa da bayan hannun nasa,wannan shine abinda ya baiwa.mashkur qwarin gwiwa,ya kuma Tunxura fu'ad ya sake kai masa wani naushin ba tare daya damu da jinin da yake zubarwa ba. Ya sake samunsa still a wuyansa,zuwa sannan qaramin fitsari ya qwace ma mashkur saboda azabar da yaji ta sauka akan kowacce jijiya tashi. Yanke hukuncin maida martani yayi,cikin nasa fushin yakai masa nasa naushin yans cewa "Bari na nuna maka iya tawa bajintar" Saidai baiko qaraso inda yake ba ya yiwa hannun nasa wani mummunan bugun da sai da yaji qarar qaramin qashin dake riqe da tsintsiyar hannun nasa. Wani ihu ya kwarara don azaba,ihun da lallai inda qaramin gida ne wala'alla har jama'ar dake farkon layinsu sai sunji......sautin ihun nasa ya samu ratsawa tsawa ta kowacce kafa dake dakin,ta kuma isa ga kunnen daya daga cikin securities na gidan dake on duty a daren,yaketa kuma kai kawo domin tabbatar da tsaron gidan da amincin masu gidan. Tsayawa yayi sosai yana son tantance daga inda qarar ya fito,a lokacin fu'ad ya sake isa inda yake ya kuma daki gwiwarsa da qafa,abinda ya sanyashi zubewa saman gwiwoyin nasa shima yana sakin ihu karo na biyu saboda yadda yaji qoqon gwiwarsa kaman ya fice fit daga jikinsa. "Zan saka kayi nadama,zakayi dana sanin abinda kakemin......wallahi sai na d'an d'ani xumarta kamar yadda kuma kuka d'an d'ana......saina huce fushina a kanta,sai nayi mata fata fata......" Wani mulmulallen abu me kama da wuta yazo ya daki zuciyarsa,har baisan sanda ya sake saka hannu yakai masa dukan daya sanya haqoransa na gaba wannan karon suka baqunci waje ba yana wani irin huci kamar tsohon kumurci. A gigice ya sake fidda idanunsa yana kallon haqoransa guda biyar zube a gabansa cikin jini,a qiyasi ya rasa haqora aqalla goma sha biyar,sha biyar suka rage masa a baki......sai ya saki wata kururuwar data tabbatarwa security din daga cikin gidanne. Wayarsa ya zaro ya fara kiran number gaggawa ta cikin gidan,saidai kiran daga parlor hallway xuwa sassansa ya tsaya,bai kawo dakin sabreen ba saboda datse layin da mashkur yayi. Cikin gunji duk da yadda jini yake ambaliya a bakinsa amma bai fasa duban fu'ad dake jawo wata cable me kauri ba yace "Saina lalata rayuwarka......sain......" Maganan ta katse saboda wani naushin daya sake xuba masa a tsakiyar kai,take wuta ta dauke masa,sashen maganarsa kuma ya dakata na wucin gadi,sannan ya tafi yifff ya fada akan jininsa jikinsa yana saki,komai baya aiki illa numfashinsa dake fita a wahalce. Da qafa ya dakeshi ya juyashi,ya tsugunna yana sanya cable din daga hannunsa zuwa qafafunsa,sai daya tabbatar ya daureshi sosai sannan ya fara jansa kaman mushe ko kayan wanki yana bude dakin ya fiddoshi. Sai daya kawo parlor na biyu sannan ya zubeshi a tsakiya. Jijiyar kansa na wani mugun gudu da harbawa ya qarasa gaban telephone ya fara kiran sashen tsaro na gidan. "Yes sir......" Security din dake tsaye yana jiran kota kwana ya fada sanda kiran fu'ad ya riskeshi. "Ku bincika min cikin gidan nan da kewayensa.......ina kyautata zaton akwai wani mutumin daban.....na baku minti goma kacal" Yadda yaji muryar boss din nasu a yau sai yaji wani tsoro da razani ya kamashi,bai taba magana dasu da irin wannan sautin dake cike da fushi da tsawa ba. Maida wayar yayi sannan ya matsa cikin hikima ya qyasawa abokin aikinsa. A zuciye ya wurgar da kan wayar,sannan ya juyo yana takowa zuwa inda ya ajiye mashkur. Zagayashi yayi har kusan sau uku,zuciyarsa na masa wani irin tsalle a qirji,ba abinda zuciyarsa ke gaya masa illa ya dauko bindigar ya fasa tsakiyar kansa da ita. Numfashi yaja sosai,sai ya juya yana komawa ciki bayan tunawa da yayi da ita,sa'annan muddin yaci gaba da zama a gaban mashkur zai harbeshi dinne abinda yaketa qoqarin hana kansa aiwatarwa. A bude qofar dakin yake,wannan ya bashi damar shiga kansa tsaye. Dakin da zuwa sannan gaba daya komai na cikinsa ya hargitse,banda fasasssun glass da kwalaben fitilar data kwatsawa mashkur ba komai a qasan,sai wargatsatstsun kayan dake saman dressing table dinta da suka tarwatse a qasa. Inda take kwace ya maida idanunsa,har yanzu tana kwance inda ya barta din,idanunsa kafe a kanta ya qarasa gabanta. Sauka idanunsa yayi a saitin bakinta,pink lips dinta da suka sauya launi kadan suka kuma bushe qamas,hoton yadda wiwin ta zauna akan lips dinta ya dawo masa,wani mulmulallen abu ya tokare masa wuya,da sauri ya ture hoton daga kwanyarsa,ya tsugunna a gabanta yana tunanin me zaiyi mata?,me ya kamata ya fara yi?. Sake maida dubansa yayi ga fuskarta wadda har dogon dokin wuyanta ya bayyana,hakanan wani sashe na kafadunta saboda saukar hijabin da ya fara samun nasarar yagawa. Sauka dubansa ya qarayi xuwa saitin qirjinta,inda a daidai nan hijabin ya nuna muguwat cukuikuyewar da zata gaya maka an riqe wajen ne da mugun riqo. Qirjinsa yaji ya wani doka,yawun bakinsa kuma yaji ya dauke qaf kaman ba'a taba halittar yawu cikin bakinsa ba. Abinda bai taba ji ba tsahon rayuwarsa yau karon farko ya jishi......wata mummunar faduwa gaba,sannan take yaji hannuwansa da qafafunsa sun fara rawa sakamakon tunanin daya bijiro masa. Sake xubawa wajen ido yayi,yayin da zuciya ta fara masa imagination na hannuwan mashkur a wajen,wani abu me qarfi ya daki zuciyarsa har sai da ya fusgo numfashinsa da kyau,dai dai sanda yaji itama ta ja numfashin da matsanancin qarfi har sai da qirjinta ya daga. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 59 59 Da wani irin yanayi numfashin nata ya soma fita,abinda ya sanyashi karon farko tunaninsa yazo masa cewa asthmatic ce. Miqewa yayi yana ranqwafawa saman kanta da nufin dagota ya canza mata makwanci duk da abinda yakeji,yana dagata din towel din jikinta yana zamewa ya kuma fadi saman qafafunsa. "La haula wala quwwata illa billah" Ya furta a sarari da wani irin bugawa da zuciyarsa tayi yana jin sautin har cikin kunnuwansa. Wani jiri da dan qaramin duhu yaji yana mamayarsa har sai daya lumshe idanunsa yana jan numfashi da kyau,ya tattaro dukka ragowar qarfinsa ya hada waje daya sannan ya soma takawa da ita ya ajiyeta saman gadon. Zamewa hijabinta ya qarayi,santala santalan fararen cinyoyinta suka fito,ya dauke idonsa da sauri yana jin yadda bugun zuciyarsa ya dake qaruwa,sai ya sanya hannu yana jan hijab din yana jin zuciyarsa na qara quntata waje daya kaman an daureta a tsakanin qirjinsa "Why?" Ya fada da mabayyanin sauti yana jin idanunsa na masa wani yaji yaji. Ta yaya wani zai samu hanyan shigo masa gida?,garin yaya hakan zata faru?. Kai ya girgiza,hankalinsa bazai dauki wannan ba.......kanshi da tunaninsa ba zasu iya karba ba. Taimakon gaggawa ya soma bata kaman yadda sukewa anni idan irin haka ta taso. Sam ya kasa hada bakinsa da nata saboda warin wiwin da yake tashi daga ciki,wanda yana daya daga cikin abubuwan mayen da ya yiwa muguwar tsana. Laluba aljihunsa yayi,sai a sannan ya tuna da wayarsa,ya cirota a nutse yana budewa gami da nemo number saddiq. Saddiq dinne kadai yasan bai fiya bacci da wuri ba,shima kaman shi yake,yanayin aikinsu ya sanya sukan iya raba dare a gida suna rage ayyuka. Bugu daya tak kuwa ya daga,muryarsa can qasa yace "Barka da dare hamma..." Bai amsa gaisuwar tasa ba yace masa. "Ka nemomin Dr rubayya......please ku kawota gida yanzu if possible" "Subhanallah...waye baida lafiya hamma?". Rasa amsar ma da zai bawa saddiq din yayi,sai kawai yace masa "Ba wani abu bane can.....just kayi sauri ku qaraso". Sauke wayar saddiq yayi yana duban farouq dake zaune a gefansa,wanda tunda ya daga wayar yaji da waye suke waya ya maida hankalinsa wajen duk da idanunsa suna kan system dinsa yau din yana sashen su saddiq dinne,don shima aiki gareshi sosai,sun samu sabon iri da sukeson su fara gwadawa manoma da manyan manoma da 'yan kasuwa,yanaso yayi settling na komai kafin ya kwanta,charger dinsa na system dinsa tayi masa tutsu,dole ya shigo ya karbi ta saddiq din ya jona gudun kada tayi shutting down. "Lafiya yace maka ba?" Farouq ya fada kansa tsaye yana duban saddiq. Daga masa kai saddiq din yayi,sai farouq din ya soma tattare ayyukan nasa waje daya ya killace yana cewa "Ka kirata kace zamu biyo mu dauketa......fu'ad bazai taba gaya maka worsening na komai ba indai shine". Ya furta yana saving ayyukan da sauri cikin aikin nasa,wannan ya sanya saddiq shima ya soma qoqarin kiran nata. Sai daya ajiye wayar saman bedsheets dinnan sannan ya lura da hannunsa da har yanzu yake tsatsafar jini. Radadin dake cikin zuciyarsa ya danne wanda yake ji a hannunsa,shi yasa sam bayajin komai a hannun nasa. Idanunsa ya sake mayarwa kanta,sai kawai ya samu kansa da miqewa yana daukan wayarsa,ya daidaita iskar dakin saboda gumi daya gani saman goshinta ya qara hasken qwan dakin sannan ya fara takawa cikin takatsatsan gudun kada ya taka wani abu ya soma fita a dakin yana komawa parlor. Tun bai qarasa ba ya hangesu sun cika hannunsu da wani baqin kakkauran matashi wanda ke sanye da baqaqen kaya full dress,tun daga hula riga zuwa wandon jikinsa. Iya riqon da sukayi masa kadai zai gaya maka yadda ya matsu a hannunsu. Ci gaba yayi da takowa yana karantarsa,duk wani alamu dake nuna tashin hankali da rudani sun tabbata a fuska da jikinsa. "Sakeshi" Fu'ad ya fadi yana jin hatta da security din gidan suma a yau bazasu tsira a hannunsa ba. Gaban mashkur ya qarasa ya zauna saman kujerar falon "Ku zaunarmin dashi a nan" Ya fada yana musu nuni da gefan mashkur din. Wani mugun duka sukayi masa wanda ya sanyashi zubewa ba shiri yana fasa qara. "Ku jirani a waje" Fu'ad din ya fadi yana qoqarin hana jinin dake diga a hannunsa bata sofa din da yake kai. Kallon fu'ad kawai matashin yakeyi,yana jin yadda kashi da fitsari gaba daya suke neman kufce masa,saidai kuma yasan babban kuskure na gaba da zaiyi shine ya saki fitsari ko kashi a wannan kyakkyawan falon. Zai iya cewa a tarihin rayuwarsa kaf.....a tarihin manya manyan laifukan daya aikata a rayuwarsa bai taba cin karo da mutumin da yayi masa kwarjini irin muhammad jadda ba. Yana zube a gabansa yana jira yaji koda wata kalma daya daga bakinsa amma ko qwayar idanunsa bai daga ya kalleshi ba bare ya sanya ran wata tambaya zata biyo baya,ta goge jinin hannunsa kawai yake da lallausar tissue din daya ciro a tissue box din dake gefansa. Bawai yayi hakan bane saboda ciwon yana da muhimmanci a rayuwarsa ba.....a'ah......yayi shuru ne saboda a yanzu babban muradinsa shine yayi mummunan lahani a garesu da babu me iya gane fuskokinsu,duk kuwa da cewa ko a yanzun fuskar mashkur ta haye tayi kumburin da dukka wata halittar fuskar ta sauya daga asalin yadda take,abinda yake sake sanya tsoro me yawa kenan ga zuciyar hanzari. "Don Allah me gida.... Kayimin rai,ka tausayamin me gida......don girman Allah". Kalaman hanzari kenan wanda ya gaza jiran yaji abinda fu'ad din zai fada. Cillar da tissue din yayi,sannan ya daga idanunsa da har yau launinsu bai koma daidai ba ya aza akan hanzari "Waye ya gayyato ka?,duka ku biyun kuma waye ya aiko ku?' Tambayoyi guda biyun da a wajen hanzari suke masa kamanceceniya da tambayar kabari ga kafiri a ranar daren farko "Shine!.....shine wallahi" Hanzari ya fada yana nuna mashkur dake yashe a qasa har yanzu bakinsa na fidda jini. A yadda mashkur din yake yayita qoqarin murgina kai ya kalli koda idanun hanzari ne amma ya kasa ballantana ya fadi wata kalma da zata zama kariyar kai a gareshi. Kiran sunan mashkur da hanzari yayi shine abu mafi sauqi.....mafita mafi sauqi a gareshi akan ya ayyana ko ya ambaci daga inda ainihin kwangilar aikin ta fito,wanda fadin daidai yake da fadawar mutanen da suka jibanceshi da yawa cikin masifa da bala'in da baisan ranar fitarsu ba......gwara ya danganta kanshi da mashkur.....kusan yasan waye.....kuma koda yafi haka hatsari yazan bazai zartashi a hatsari da hatsabibanci ba.......koda ya zartashi yasan bazaikai mutanen da suka qirqirar da aikin ba. "Kana da masaniyar cewa maqabarta ka kawo kanka?......nan da kake zaune Motuare ce?!" Ya furta da sautin da hatta da mashkur sai da yaji kaman an buga masa guduma still saman ka bayan masifar azabar da yake ciki. Firfito da idanu hanzari yayi.......yayi gwagwarmayar rayuwa da yawa......ayyukan rashin imani bila'adadin......ya shiga komar Jami'an tsaro masu yawan gaske......da wannan kadai yana iya gane mutum da muhallin da ake magana ta gaske kai. Salati ya debo wanda ya manta rabon da ya ambaceshi a bakinsa,sallah kanta ba'a maganarta sam bars aje ga gurbin xama ayi wani xakiri ko tasbihi. "Zip your mouth!" Fu'ad ya furta da fushi "Ko burbushinku ba zaa samu ba.......daga yau ba zaku sake gigin tsallaka gonar wani ba" "Innalillahi wa inna alaihi....." Ya jiyo muryar daga can gefe tana fada cikin maqyarqyata saboda tsananin tsoron data shiga. Duk tsawarsa guda daya sai taji kamar ana finco mata hantarta tare da qoqarin bintiko zuciyarta daga muhallin da take a dashe. Waiwayawa yayi yana mamakin wanda ya rage a falon bayan ya bada umarnin kowa ya fice. Zuwaira ce tsaye yana rawar dari kamar wadda ruwan da yayi saura har yanzu yake sauka kadan kadan a kanta ya qare. Sulalewa tayi a wajen tana jin wata razana tana saukar mata,idanunsa sun mata wani kaifi da bata da juriyar daukarsu. Yadda yake magana ga duk wanda yake falon zai tabbatar abinda yake fadin zai aikata ne. Ba wasa ko digo cikin kalamansa. Itakam a yanzun ina ta shirya mutuwa?,a irin wannan qadamin da take lissafin sake inganta rayuwarta da jin dadin da yake hange daga wasu?,itama ta samu ta dandala ta baza nata ikon da isar kafin zuwan randa zata bar numfashi?,shine tun a yanzu a gabanta wannan manya manyan alkaba'in yake faruwa?. Idanu ya zuba mata da kyau yana qoqarin karantarta,saidai kuma kafin yayi nisa an murza pivot door din daga can wajen falon an shigo. Farouq ne a gaba,Dr rubayya a tsakiya sai saddiq daga bayanta . Shigowarsun kawai cikin falon....hada idanunsa da farouq sai yaji kaman an janye wani kaso na bala'i da masifar da yakeji tana kunnuwa cikin zuciyarsa. Wani irin tashin hankalin da baisan dame zai fasaltashi ba. Dr rubayya na qoqarin gaidashi.....saidai shi hanyar hallway din kawai yake nuna mata da yatsa ba tare da yace komai ba,sai itama bata sake magana ba kasancewar halinsa ba baqonta bane,ta wuce da kayan aikinta kai tsaye zuwa hanyar. "Ka leqa ka kiramin saddam......suzo.su biyu" Yace da saddiq da rinannun idanunsa da suka sanya saddiq shan jinin jikinsa bayan mutane biyun da ya gani zube a wajen. Shima baice komai ba ya juya yana fita daga falon. A nutse farouq ya isa gabanshi,ba tare da yace komai ba duk da idanunsa na nuna kaduwa da abinda yake gani ya kama hannunsa yadan juya sannan ya saki "Dude.......wai meke faruwa?" Ya qarasa maganar yana saka idanunsa cikin na fu'ad din. Janye nasa idon faud din yayi daga na Farooq yana hadiye wani abu me tauri daga qasan zuciyarsa. To shi ta yaya ma zai fara bada wannan mummunan labarin?,yace meye?,yace masa wiwi ya kamasu suna sha har ya bugu asthma dinta ya tashi?,ko yace masa ta gayyato maza cikin gidan sun bugu sukaso gwada mata qarfi?,ko kuma yace sharri akayi mata?,barayi zai kirasu ko 'yan fashi?,zaice sun hauro masa gida ne?,gida ma irin nasa?,gidan da ba wani abu daya isa ya shiga ko ya fita cikinsa saida cikakken tsaro da kulawar security......waye hankalinsa zai dauka?,waye zai yadda da wannan labarin?. "Ka kwashesu ka sakaminsu a cage din dogs dincan....." Ya fada yana miqewa sanda hanzari ke qoqarin riqo rigarsa a gigice "Kayi mana rai oga.....ka hukuntamu duk yadda kaso,amma kada ka hadamu da karnukan can.....wallahi ko kafin safiya sun gama cinye namanmu oga...." Yayi magana fitsarin da yaketa son riqeshi yana kubce masa. Tun shigowarsu gidan yanayin karnukan ya tabbatar masa sunsha banban da dukka karnuka daya sani. Basu bi ta gefensu ba.....amma wani abun mamaki yadda suketa haushi ya ninku,yana ganin sanda me kula dasu ya dubasu,ya kuma yiwa security na gidan magana suna sake bincike sassannin gidan amma basu ga komai ba saboda sun shigo ne ta hanya mafi sirri da samun tabbaci,kuma sun samu mafakar da binciken me bincike bazai taba kaiwa nan ba. "What are you waiting for?!!!" Fu'ad da dama dukkaninsu suma a cike yake dasu ya fada a tsawace,ba shiri suka durfafesu,hanzari yayi wuf ya kama qafarsa yana sake roqonsa. Wani wawan duka yakai masa da qafar daya sanya hanzari zubewa warwas,basu saurara masa ba suka sungumeshi suka hada da mashkur da tsabar razana ya kasa magana,sai yakejin kamar qiyama ce zata tashi. Yasan illar karnukan,don sanda yake sharafinsa ya ajesu a gidansa sun kusa guda biyar,hakanan baisan adadin mutanen da ya sanya suka yagalgala ba. "Karku sakasu a cikin cage din.....ku ajiyesu dakin kusa dashi" Ya basu umarni sanda suke kicin kicin fita dashi. "Okay sir" Suka amsa masa sanin wayeye farouq wajen boss din nasu. Shi daya ne duk duniya yake tada hukuncin da fu'ad yayi kuma ta zauna ba tare da haufi ko kankare ba,shi yasa suka karba umarnin nasa kaman yadda ya basu. Yadda yaga komai yasan ba lafiya ba.......yadda kuma yaga yanayin hannunsa da gidan ya tabbatar akwai gagarumin wani abu daya faru.....uwa uba wani kwantaccen fushi d yake gani a fuskar Fu'ad ya sanar masa akwai matsala ko a yadda ya fita a fusace. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 60 60 Tun bai qarasa inda yake hangen security na gidan daya tara ba yakejin muryarsa dauke da fushi me nauyi. Fada yake da duka zuciyarsa da jikinsa ma,sam kaman ya manta dare ne a yanzun......daren ma kuma irin daren da akayi ruwan sama ya dauke wanda ke ninka kowanne dare a shuru da daukewar sawu. "Your services are no longer required......you were fired!" "Ya salam" Farouq ya fadi,abinda yaketa sauri ya dakatar dashi kenan. Fushinsa na yau yanata bashi mamaki,sau tari shike daukan abu da sauqi......yawancin lokuta shike jan qafa da jan lokaci akan abubuwa irin wadannan......yana bin komai da lura a kuma tsare,har sai ya tabbatar dashi a inda ya dace. Kasa cewa komai yayi,don su kansu ma'aikatan da security din dake on duty a daren kowa cikin matuqar tashin hankali yake. Yadda suke roqonsa da mabanbantan harsunansu dukka sai suka bawa farouq din tausayi. Kowanne a cikinsu idan ka dubi fuskarsa ya kadu da hukuncin ba zata na me gidan nasu. "Calm down.....ya isa" Farouq ya isa gabansu yana fadi bayan komawar fu'ad din ciki. Hankulansu kuwa suka bashi cikin mutuwar jiki hankali a tashe. "Ku kwantar da hankalinku.....kowa ya koma bakin aikinsa kafin wayewar gari......but,ku sake tsaurara kula kafin muga abinda hali zaiyi. Duk da bawai tabbaci ya basu na cewa ya dawo dasu bakin aiki ba amma hakan ya faranta musu. Sun sani babu wani guri da zasu samu walwalar rayuwa da 'yanci da albashi me tsananin azabar tsoka kaman gidan jadda.....salary yake musu na kece raini......irin salary din da sunyi imani ko a villa suke aiki babu me biyansu irinsa. Uwa uba ga ihsani da alkhairi da suke samu kowanne lokaci,wanda ya kusan kamo abinda ake biyansu albashin aikinsu. Da yawansu suna jin idan ba gidan Muhammad jadda ba babu a inda zasu iya aiki,shi yasa suke riqe da aikinsu fiye da yadda ma yake tsammanin zasuyi. A parlor ya sameshi a tsaye kaman wanda zama ya gagareshi. Baice masa komai ba ya taka inda yake tsayen ya riqe hannunsa sannan ya wuce dashi,suka ratsa hallway din suka saura samansa. Saman monotti sofa ya zaunar dashi,ya taka da kansa zuwa shiyyar da aka tanada don ajjiye first aid box,don kusan yasan komai na gidan tunda shine ma tsara yadda zai kasance din. A gabansa ya zauna,ya bude box din ya ciro cotton wool da spirit ya tsiyaya ya fara goge masa ciwon. Sai a yanzu yake danjin radadin da hannun ke masa amma kadan kadan,saidai har yanzu abinda yakeji a zuciyarsa ya dara wanda ke a hannunsa. "Ko meye da sauqi ake daukarsa......da irin wannan temper din da kake ji a ranka komai fa bazai warware ba" Farouq ya fada yana qarasa goge masan,har yanzu kuma yana mamakin abinda ya birkita nutsatsen mutum irin fu'ad din. Duk da ya sani,ba abu bane me sauqi a keta alfarmar gidanka a shigo maka ba......to amma kuma yadda yasan fu'ad zai iya cewa tun wani zamani can daya shude rabon da yaga wannan attitude din a tattare dashi. Wayar tafi da gidanka din dake falon,wadda ke ajiye kusa da console mirror din parlor din ce ta dauki tsuwwa. Saddiq dake zaune daga gefe dukka jikinsa a mace ne ya dauka "Daga hallway bedroom ne" "Ka daga ko Dr rubayya ce" Farouq ya fadi sanda yake tattare ragowa ragowan audugan da yayi amfani dashi. Maganan second goma sukayi kwata kwata,ya sauke wayar yana duban farouq "Dr ce ke magana.....tace ta kammala......amma wai tanason ganin hamma". "Ka gaya mata tayi abinda ya dace kawai basai nazo ba" Ya fada yana jin ciwon kan daya tashi da jin dadin ya sauka yana son dawowa. Kai farouq ya girgiza yana dubansa,muryarsa a qasa qasa yadda saddiq bazaijishi ba yace "Dole kaje tunda tace kaje din.....dole saika gwadawa duniya halinka?" Idanunsa da har yanzu basu koma fararensu ba ya watsawa farouq,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya tsuke bakinsa. Kamar bazai tashi ba kafin ya miqe yana kiran sunan Allah,wanda motsawar bakinsa ne kadai zaisa gane hakan. A hankali yake sauka zuwa qasan,saidai duk sanda ya kusanci dakin sai abun daya faru mintunan baya yayita dawo masa. Bama irin idan ya tuna ba komai a jikinta......daga ita sai towel sai hijab,sai yaji tamkar iskar da yake shaqa tayi masa kadan. Su biyu a daki tana daga ita sai shi.....su biyu a dakin da babu cikakkiyar sutura a jikinta......gaban hijabinta yasha cukuikuiya?.....duk sanda ya kawo nan sai ya lumshe idonsa saboda ji yake kaman an dauka adda an kafta masa sara a tsakiyar kansa. Handle din ya murza ya tura ya shiga da sallama saman labbansa. Ma'u dake gyara dakin ta dago daga kwashe sharar data gama,ta rusuna tana gaidashi duk da dare ne,sannan ta kwashe dustpan da vacuum cleaner din tayi waje dasu. Haka kawai ya samu kansa da bayason kallon fuskarta,don ba abinda yake tuna masa sai a yanayin data fado jikinsa. "Numfashinta ya koma normal,kuma yanzun haka bacci take me kyau.....ko da wanne lokaci ma zata farka abinta........amma please sir......koda asthma dinta baiyi tsanani ba at least ya kamata ace an ajjiye mata in healer.....and ya kamata ta dinga kula da gujewa ta'ammali da abubuwa masu hayaqi da yawa". Kai kawai ya jinjina ma Dr rubayya "Allah ya qara afuwa yasa kaffara.......idan kuma ana buqatar wani abun.....am ready in sha Allah,koda yaushe kuka kirani am available for your needs". "Thank you" Ya fada can qasa da kalar miskilancin nan nasa da ba wani baqon abu bane a wajenta. Already kafin ta fita ya kira saddiq ya gaya masa gata nan su maidata gida,yana kuma sauke wayar kiran farouq ya shigo masa "Mu duka mun wuce gida,but.....na kira wasu daga cikin guards dinka an qara akan na cikin gidan......in sha Allah kome zaiyi daidai......but please please.....karka dauki doka a hannunka akan mutanen nan". Farouq ya fada cikin narke murya. Ya dade da sanin halinsa,muddin ranshi yakai qololuwar baci irin wannan bai iya hukunci ba. "Kaji?" Farouq ya sake maimaitawa jin yayi shuru baice komai ba. "Alright" Ya fadi a hankali kamar wanda maqoronsa ke masa ciwo yana gintse kiran. Iska ya sake furzarwa daga bakinsa,daga jikinsa har zuciyarsa babu wani abu dake masa dadi,sai ciwo kawai.....wani irin ciwo me radadi a gangar jiki da zuciyar. Karon farko ya maida dubansa saman fuskarta,wanda daidai nan idanunsa suka hangar masa wayar dake gefan pillow dinta. Wani abu ya tsarga masa har yatsun qafarsa,sai ya miqa hannu ya dauko wayar. Tabbas itace wayar daya gani a hannunta shekaran jiya.....wayar da baisan yadda akayi taxo gidan ba ta kuma zama mallakinta har take amfani da ita. Jujjuya wayar yayi sosai yana qare mata kallo,sai ya latsa malatsin gefe haske ya kawo,ya sanya dan yatsa ya shafi fuskarta take ta bude. Bangaren kira ya shiga ya soma dubawa,kirane da numbers barkatai wanda kusan dukansu babu suna. Ci gaba yayi da dubawa har zuwa kan date din shekaran jiya wanda wata number data qare da 01 itace number qarshe da aka amsa kira da ita. Kai ya jinjina a hankali yana komawa bangaren saqonnin karta kwana wato sms. Dunqule hannunsa yayi da kyau yana ci gaba da duba saqonnin da suka shigo da mabanbantan numbers suma,wanda dukkaninsu suna dauke ne da nau'ikan kalaman soyayya iri iri,saidai kowanne saqo ba wata amsa guda daya da ta maida masa. Kasa ci gaba yayi da dubawa saboda yadda dukka jikinsa ya dauki tsuma,sai ya kashe wayar ya jefata aljihunsa sannan ya miqe yana dubanta da wani zafin zuciya. Takawa ya soma yi a hankali,har cikin jiki da zuciyarsa yana jin bazai iya zama da ita na daren gaba daya ba a daki daya,sai daya hau saman sannan ya kira sashen ma'u yace taje ta kula da ita,baima aje wayar daidai ba ya dora kansa a hankali saman sofa din yana fidda numfashi kansa kaman zai fado. Tunani ne iri daban daban suke barazanar tarwatsa masa kai,ya rasa da wanne zaiji?,da wanne zai fara?,meye daidai cikin hasashensa meye ba daidai ba?,ganin yana neman rasa nutsuwarsa cikin qasa da minti talatin,sai ya miqe a gaggauce ya jawo earpiece ya toshe kunnuwansa da karatun qur'ani,abinda ya sanya duk abinda yakeji ya soma sauka a hankali,nutsuwarsa ta soma daidaita,nauyin da yakeji a qirjinsa da zuciyarsa suka soma raguwa,sannu a hankali ya maida idanunsa ya lumshe wani bacci yana yin awon gaba dashi a cikin falon. *_TO ASUBA TA GARI......SAIDAI KUMA KO DAME SAFIYAR RANAR ZATA WAYE MUSU DASHI?_* *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 61 61 Tun daga sanda ta farka bata samu wata nutsuwa ko kwanciyar hankali ba sai bayan data tabbatar ba wani abu a jikinta da mshkur din ya samu kaiwa gareshi "Allah na gode maka.....Allah na gode maka" Ta dinga maimaitawa cikin bandaki hawaye na layi bisa kuncinta. Wanka ta sakeyi dab da asuba da ruwa me dumi sosai,koda ta fito ma'u ta ajiye mata wasu kayan da zata saka. Har zata fita ta bata waje ta canza kayan tace ta zauna,tana jin ma'u kamar jininta,tana jin gamsuwa da dabi'un ma'un. Mutum ce me kamun kai sosai,kawaici gami da kauda kai daga kan komai da bai shafeta ba ko kuma ba'a sanya da ita ba,wannan yana daya daga cikin dabi'un da suka sake sanyawa hankalinta ya kwanta da ma'un. Ko data shirya hijabi da abun sallah ta buqata,ma'un ta bata ta koma ta zauna. Ta shimfida ta tada sallar. Isha'in da bata samu yi ba a dazu ta bayar,sannan ta dora da shafa'i ta kuma zarce da nafilfilun da ita kanta batasan adadin guda nawa tayi ba. Sam sam bata jin koda digon bacci a idanunta,samun kanta tayi da tsananta addu'o'i masu yawan gaske cikin sallarta. Idanunta sun zubda hawaye masu yawan da adazu bata zubda su ba,jikinta yayi wani mugun sanyi zuwa bayan wani lokaci,qafafunta sunsha tsaiwar da zama kawai take da buqata,saita zauna din tana irga tashihi da yatsun hannunta. Tuna abinda ya faru da ita dazun kawai razani yake haifar mata,yayin da kwanyarta tayi nisan zango wajen tunanin waye yake da alhakin zamewa mashkur jagoran daya risketa har cikin dakinta. Tayita qoqarin tuna abinda ya faru bayan zubewarta amma ta kasa tuna komi......abinda kawai take iya tunawa sanda ya shigo dakin da fadawa jikinsa da tayi tana neman tallafi cikin kubcewar numfashi. Kiran farko dana biyu duka akan kunnenta akayi shi,bayan sauran masallatai sun tada tasu sallar sai itama ta miqe ta bada nata faralin. Ci gaba tayi da zama still a wajen......tana tsammanin wai ko zataji bacci amma babu shi ba alamarsa. Wani firgici takeji har tsakiyar zuciyarta wanda bada taimakon hailala da takeyi zuwa yazu batajin zata iya zaman dakin ma gaba daya. Sanda gari yayi haske ta kalli ma'u dake gefe a zaune,qaunar ma'un da darajarta yana qaruwa cikin idanunta. Sam tana lura da ita batayi bacci ma itama "Kije ki huta ma'u.....baki samu bacci ba kema" Sabreen ta fada muryarta a karye da wani irin sanyi da bata taba yi ba. Dan murmushi ta saka tana gyara zamanta "Ba wani damuwa.....bai kamata ai na barki ke kadai ba......saidai ko idan kina buqatar cin wani abu?" Kai sabreen ta girgiza mata "Bana buqatar komai.....kije kidan rage baccin ma'u ki kintsa......kya dawo daga baya,bana buqatar komai". Kai ta jinjina sannan ta miqe tana mata sallama ta fice. Qarasa shafa addu'o'inta tayi ta miqe tana son jin qara watsa wani ruwan dumin ko jikinta zai qara yi mata dadi. Wannan karon saita taka zuwa bakin qofa ta murza lock dake jikin qofar kamar me tsoron maimaituwar abinda ya faru daren jiya ya sake faruwa,sannan ta juya a hankali tana wucewa toilet din. Tare dasu Jordan da farouq ya kawo suka wuce sallar asuba,wadda duk da qarancin baccinsa hakan bai hanashi samun sallar asuba ba. Tun daga fitarsu zuwa dawowarsu su kansu sun fahimci sam yau ba'a mode dinsa yake ba. Idan kai baqo ne a rayuwarsa ba lallai ka fahimci lokutan walwalarsa dana bacin ransa ba......kawai zai zame maka kaman daya ne saboda rashin fara'a da bai da ita......amma gasu da suke tare dashi tsahon shekaru,suna iya fahimtar walwalarsa da akasinta dukka qarqashin dabi'arsa me kamanceceniya da juna. "Mu qarasa ciki jordan" Yace da jordan din bayan sun shigo ainihin farfajiyar gidan. Ba musu ya takewa uban gidan nasa baya suna takawa zuwa dakin da ya bada umarni a ajjiye masa su. Duk da kusan dabi'ar gidan shuru ce,amma a yau tana jin gidan ya sake zama shuru gaba daya. Hakan yake don tun daga gate din farko na gidan zakaji gidan yayi wani mugun shurun da ko tarin wani babu. Zaka rantse da Allah mutuwa akayi cikin gidan saboda yadda kowa ya sake shiga nutsuwarsa. A mugun kasalance da wani irin rashin kuzari ta shirya cikin atamfa dinkin plain zani da riga,wanda babu wani ado da akayi mata ko guda daya face qwarewa da gwanancewar dinki daga telan nasu. Dare daya amma gaba daya ta fada,tayi wani rama da ta bayyana har a qasusuwan wuyanta,fuskarta tayi fayau,inda ya fashe a jiya sai yanxu ya fito sosai ta ganshi. Tsaga ce 'yar siririya bame yawa ba,fuskarta tayi wani fayau kaman wadda tayi zazzabin dare. Koda ta kalli fuskarta gaba daya sai taji zuciyarta ta karye,ta koma da baya a hankali tana sake tuna yadda mashkur ya fado mata daki. Duk wanda wani bala'i ya sameshi kalleshi kawai......ashe fiye da haka matan da ibtila'in fyade ya fadawa suke ji?. Raurau idanunta sukayi,can qasan ranta sai ta samu kanta da godewa Allah da ya bata ikon tsame mata da yawa da suka fuskanci ibtila'i irin wannan zuwa sauyin rayuwa daya kawo musu sassauci da rangwame. Qasa tayi da kanta,daidai lokacin da taji ana mata knocking. A nata zaton ma'u ce......wannan ya sanyata kanta tsaye ta nufi qofar ta kuma bude tana bada hanya,saidai a maimakon ma'u anni ta gani,gefanta kuma amna ce tsaye tana riqe da purse din annin. Wani irin nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,tayi qasa da kanta tana basu hanya. "Ai jikinma yayi kyau.....basai mun shigo har uwar daki ba,mu koma falo mu gaisa a can" Anni ta fada cikin dattakon nata tana juyawa da nuna alamu na surukuta "Da kun qaraso din dai anni" Sabreen ta fada adan kunyace da nufin tsaida annin "A'ah qaraso nan din sabreen.....ki fito a hankali karki gaggawa" Anni ta fadi tana qara yin gaba,amna da abun yaketa burgeta takeson tayi tsokana nata binsu da dariya. Dukka hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana qare musu kallo cikin quntataccen qaramin store din ajiyar kayan aikin sola dana engine din gidan idan ya samu matsala. Daga daren jiya zuwa yau idan ka kalli fuskokinsu sai kace basu bane,kada ma mashkur daya kwana a daure yaji labari. A duk sanda ya kalli mashkur din shi kadai yasan abinda yakeji......har yanzu maganganunsa sunqi daina amsa kuwwa a kuwwa a kunnensa.......har yanzu ya gaza daina tuna sunyi gamayya a daki guda qarqashin abun shaye shaye guda. Taku biyu yayi y is gaban qofar yana duban mashkur din "Waye ya aikoka?,ko kaine ka aiko kanka da kanka makasarka?" Kai ya mirgina alamun eh.....koda meye zai faru bayajin zai iya buda baki ya fallasa wannan sirrin.......sirrin da idan har ya bari ya fita to tabbas shima ya gama jin dadin rayuwarsa har gaba da abada koda yayi escape. Abu ne bisa sharadi da yarjejeniyar da aka qullata bisa masaniya da kuma abinda zai faru a qarshe. Sosai fu'ad ya zuba masa idanu yana karantarsa,yanayinsa ya tabbatar masa bai shirya fadin gaskiya ba duk da baqar wahalar da ta nuna kanta a tattare dashi. Bayajin zai iya wahalar da kansa tsaiwa yana batawa kansa lokacin tambayarsu,yana da wadanda zasu tafi masa dasu har su gane kuskuren da suka tafka na shiga gonar da ba nasu ba. Hannu kawai ya daga ya yiwa Jordan alama,Jordan din ya jinjina kai sannan ya juya yana fita hanyar waje da sassarfa irin ta majiyin qarfi,cikin qasa da minti biyar sai gashi sun shigo da wani. Kakkauran mutum ne,me qiba da madaidaicin tsaho,yana da baqar fata data haska sosai cikin color din uniform din 'yan sandan dake jikinsa. Maqale da jikin rigar rubutun sunansa ne S.nuhu,wanda iya rank dinsa zai nuna maka cewa shine commissioner of police na jahar gaba daya. Salute na juna sukayi shi da fu'ad din,sannan yace "Yallabai yace idan da damuwa ayi gaba dasu" Kai fu'ad ya jinjina yana baro jikin qofar yana takowa a hankali gami da dubansa "A wuce dasu a ajjiyemin su,har sai zuwa sanda na buqacesu". Kai s nuhu ya gyada cikin girmamawa,daga yanda fu'ad yayi maganar ya gama fahimtar komai. Suna girmamashi kaman yadda yake girmamasu,tun daga can copral har zuwa matakin qarshe na samansu,wannan ya sanya basuyi qasa a gwiwa ba suka bashi kyautar jami'an tsaro cikin mutanensu,mutum ne me qoqarin kiyayewa da mutunta doka. Yana da qarfin mulki dana dukiyar da zai iya komai da yaga dama musamman a yanayi irin na qasarnan da zaka iya komai ba komai bane,amma baya yin hakan,komai din yana qoqarin ganin ya azashi akan mizanin daya dace. "Don girman Allah ka taimakeni.....kayimin sutura.....yallabai ni na fadi gaskiya,na fadi gaskiyata......iyakar gaskiyata kenan". Hanzari ya fada yana hade Hannayensa waje guda yana kallon fu'ad da tuni ya soma wucewa xuwa cikin gida. Ko muryarsu bayason ji bare yakai ga kallon fuskokinsu,don haka baiko waiwayo ba bare ya saurareshi. CP s.nuhu ya daka masa tsawa "Miqe muje......ku daukeshi ku samin a mota,mutanen banza kawai......banda ma me jadda din kuka samu waye kamanshi da zaku keta masa haddin gida ku shiga ku wayi gari haka da sauran lafiyarku?,ba a nan zamu gane gaskiyar taka ba......muje don ubanka" Cp ya fada shi kansa abun yana masa takaici. Sam baisan da zuwan annin gidan da safen ba,don haka kanshi tsaye ya shiga falon hankalinsa yana ga samanshi. So yake ya isa ya kulle kansa don baya buqatar ganin kowa kaman yadda bai buqatar hayaniya ko dogon magana sam sam. Saidai yana sanya qafarsa a falon yaji muryar annin sanda take fadin. "Allah ya qara lafiya......yasa kaffara,saiki dinga kula da jikinki da kyau,Allah ya inganta". Murna ta kama amna,duk yadda taso cinye maganar amma sai data fito " Anni......wai.....wai hamma shima ya kusa zama daddy?". "Ungo nan" Anni ta fada tana watsa mata yatsunta biyar,saita saka hannu ta qunshe bakinta tana dariya. Shikam daga shi har sabreen dake zaune daga gefe maganar tazo musu a wani irin ba zata. "Allah ya inganta?....zama daddy?,wata qaryar ta gilla musu kenan?" Ya fada qasan ranshi yana yamutsa fuska gami da watsa mata wani irin kallo duk kuwa da cewa yana nesa kadan dasu,sannan dukkansu ba wanda yasan ma ya shigo parlor din. Kai ya jinjina wani abu yana tsaye masa a wuya "To yaushe tayi cikin?" Yaji tambayar ta taso daga ransa,take yaji kansa ya qara masa wani nauyi saboda wani tunani da yazo ransa. Dukka juriyarsa da yakejin kamar tana sulalewa ya tattaro yana sake maimaita sallamarsa,suka daga kai dukansu suna amsawa banda sabreen da tayi qasa da nata idanun tana jin sam sam bata sha'awar dubanshi. Gefan anni ya zauna kaman yadda ya saba a gida,duk sanda zai iso gabanta gefan ta nan ne wurin zamanshi. Tuni amna ta kama kanta tana gaidashi cikin tsoro,don tasan zai wahala baiji abinda ta fada ba. "Ina kwana?" Sabreen ta samu kanta da fadi duk da bata dubeshi ba,haka kawai takejin wani irin nauyin anni. "Lafiya qalau.....ya jikin?" Ya furta a dake yana dan duban fuskarta kadan wajen daya lura a jiya ya fashe,baiga komai ba don ta rufe wajen da dan kwali,sai ya dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana masa zafi. Ba abinda ya hanga saman fuskartata sai guntuwar wiwin daya gani jiya a bakinta,zuciyarsa ta sake matsewa,baya jin zai samu wani nutsuwa a zuciyarsa muddin bai samu cikakken bayani abinda yake faruwa ba ko kuma ya farun. Hankalinsa ya maida kan annin ya soma gaidata cikin nutsuwa da girmamawa. Yaji dadin yadda farouq bai daga mata hankali ba ya gaya mata abinda ya faru a gidan ba jiya da daddare,yadai gaya mata kawai sabreen dinne bata da lafiya "Allah ya qara lafiya.....sai ka kula da ita sosai.....inajin idan zai yiwu ma nabar amna a gidan,don a yanayin mace irin haka zaman kadaici qara miki ciwo kawai yakeyi". Dan satan kallon anni yayi,ya fuskanci tunda ta zauna a wajen kawai kallon me ciki take yiwa sabreen din,inda anni tasan cakwakiyar da yake ciki zama zatayi tayita masa kuka. Kwata kwata a birkice yake kan lamarin,kusan komai nema yake ya dagule masa,yana jin kamar kwanyarsa ta daina aiki yadda ya kamata. Ya lumshe idanunsa yana jin ciwon yadda mahaifiyarsa ta xama silar qulluwar alaqa tsakaninsa da yarinyar da kullum munanan boyayyun halayenta sake bayyana sukeyi. "Ashsha......da kinyi zamanki ai,ina ke ina hidima damu ke da ba cikakkiyar lafiya gareki ba?" Anni ta fadi sanda Sabreen din ta fito daga kitchen ta ajiye mata tray dake dauke da spicy black tea soyayyen qwai da kuma farfesun kan rago wanda ta yi tun shekaran jiya waccan amma ta kasa ci,kasancewar ita din cin abinci ba damunta yayi ba. Zataci din amma gutsul gutsul kamar na dan qaramin yaro,shi yasa ko yaya ita ko ma'u suka girka abu sai yayi musu yawa. Sallamar da akayi daga bakin qofa ya maida hankalinsu can. "Sannunku dai.....gafaranku" Zuwairan ke fadi tana rarraba idanu. Zuciyarta cike fal da fargaban kada shigowarta ya zama silar barinta aiki.....amma kuma tana jin relief na wani fannin idan ta tuna tana da assurance na bazaice komai ba muddin annin tazo gaidawa. Zubewa ta gaidashi,amsawa daya yayi mata,ganin hakan sai ta tattara hankalinta ta maida kan annin tana zuba gaisuwa. "Ya mukaji da wannan abu?" Zuwairan ta fada duk da a tsorace take. "Ke!" Fuad ya fadi da kakkaurar muryarsan nan dake saurin isar da saqo gun wanda aka kira saboda zurfin muryar da wani irin kaifi *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 62 62 "Eh......na'am" Ta fadi adan zabure "Kin taba samun matsalan qwaqwalwa?" Ya tambayeta kai tsaye da wani kallo da yaso rikita duk lissafinta. Kai ta fara girgizawa "Ranka ya dade.....aah" "Good" Ya jinjina kai "Bacen a gun" Ya fada a taqaice wanda yana kaiwa qarshe tana miqewa da hanzari gami da cewa "Tuba nake.....tuba nake". Daga shi anni har amna binta sukayi da kallo,a mamakance anni ta maido dubanta kansa bayan ta fice "Allah me mutane.....ina ka samo wannan Muhammadu?" "Maamah ce....." Ya fadi a taqaice yana jin wani abu game da matar tare da bin hanyar da ta wuce da kallo kaman tana wajen har a lokacin. Tun bai qarasa ba ta fahimci inda zancan ya dosa,kai kawai ta gyada tana fadin "Allah ya rufa asiri......mu zamu wuce.....diyata" Anni ta fadi tana murmushi. Qasa sabreen ta sakeyi da kanta tana dan qaramin murmushi. Karon farko idanunsa suka soma kaiwa kanta,karon farko kuma yaga wani abu me.kama da murmushi akan fuskarta......hakanan lokaci na farko da yaga wani alamu na wata aba wai ita KUNYA a tare da ita. Tsaki yaja qasan ranshi,bayajin wannan abun da takeyi har qasan ranta take yinsa,yadda ta wani sunkuyar da kanta,abinda bai taba gani ba a tare da ita sai yau. "Allah ya qara sauqi kinji.....ki kula da jikinki da kyau" Anni ta fadi tana jin yaqinin kamar abinda dai take hasashen ne yake tare da sabreen. Har cikin zuciyarta takejin yarinyar,tana kuma jin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanxu,amma kuma ta gaza tunawa. "Ameen anni.....na gode" Siririyar muryarta da yau kadai tayi wani irin laushi ta fito tana furta hakan har yanzu kanta a qasa. Dukkaninsu suka takawa anni xuwa inda lafiyayyar BMW dinta take jiranta da masu tsaro lafiyarta mutum biyu "Zamu tafi tare da amna din.....amma anjima da dare in sha Allah zata dawo,sai kinfi jin dadin xaman......nasan halin Muhammadu....indai kin ganshi gida zaune to saidai annual leave dinshi yazo ko kuma baida lafiya da gasken gaske". Haka kawai ta samu kanta da kallonshi ta gefen idonta. Duk da ba dogon zama sukayi ba,gajeran zama ne maras dadi da ma'ana,zaman da baida wani alqibla ko kadan,amma ta karanci dabi'u masu yawa tattare dashi. Aiki kaman baisan ciwon kansa ba,kamar kuma yafi kowa sanin muhimmancin lokaci,bata taba ganinsa ba system ko takardu ba.....sannan zaman kadaici baya damunsa sam sam. Suna a tsaye motar ta soma motsawa tana fita ta tafkeken gate din gidan. Idanunta akan bayan motar,tana jin kaman ta hanasu tafiya ita da amna din,dan wanzuwarsu na qananun mintuna kadai sai taji kaman an rage mata wani nauyi da takeji a zuciyarta. Lallai maraici babbar masifa ce,ciwo ne wanda bashi da magani har xuwa randa naka ajalin xai ruskeka,wanda ya rasa uwa shi daya yasan irin asarar daya tafka da ba zata fadu ba. Sai da motar ta gama ficewa tas sannan ta tuna a inda take a tsaye,da kuma wajen waye take?. Ba tare data juya ta kalli inda yake a tsayen ba ta juya a hankali tana komawa ciki. Da kallo ya bita ranshi yana sake masa susa......idanunsa suka sauka kan hips dinta da suka bayyana sosai saboda mayafin dake saman kanta bame girma bane,take zuciyarsa ta wullo masa hoton hijabinta na jiya da yasha cukuikuiya,wani zazzafan abu me tauri ya taso masa da ya sanya ya gaza riqe kansa,sai kawai yabi bayanta yana jin ya zama dole lallai lallai yasan kome. Tana dab da isa qofar da zata sadata da parlor dinsu na farko ya cimmata. Bata zaceshi ba ta tsinceshi a gabanta. Kallon kallo suka yiwa junansu,wani irin kallo na tsakiyar idanu,tsakanin shi da ita kowa zuciyarsa na dauke da wani irin nauyi da baisan yadda zai rageshi ba. Ta dauka zata iya jurewa ci gaba da kallon tsakiyar idanun nasa amma sai taji ta sare nan da nan,ta janyesu bugun zuciyarta na daduwa wanda batasan meye sila ba. Qasa tayi da kanta,so samu ta rabeshi ta wuce saboda fushi take gani cikin idanunsa,ita kuma yanzu qirjinta bazai iya daukan fada masifa ko tashin hankali ba hakanan. Kai kawo kawai adams apple dinsa keyi alamun akwai abinda yaketa qoqarin hadiyewa,jiyan ce kawai ke dawo masa,yana tuna sanda ya dagata towel din jikinta daya xame warwas a qasa,daga ita sai hijabi. Sai daya tabbatar yayi babban aikin rage fushinsa da abinda yakeji sannan ya soma magana,cikin bacin rai amma kuma yanata kokawar kalmasa harshensa,don bayani yake buqatar ji,duk da cewa ta kowacce fuska.....duk kuma inda ya juya.....kowacce hujja idan ya daga,ya tattaro ta nan data can ba abinda take sake nuna masa sai ainihin WACECE ITA. "Wancan lokacin.......na taba ganinsa cikin hotel a abuja yana cigiyar karuwarshi da suka kama daki,ta kwashe masa kudade masu yawa kwatankwacin yadda ya faru da kamfanin JADDA DIAMOND CHORES RESOURCES,sanda naga fuskan wayar ba kowa bace a ciki sai KE!......Wanene shi?,ya akayi ya shigomin cikin gidana?,cikin dakin da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta halak?". Wani irin duka tambayar tasa tayi mata,wadda tazo mata hade da labarin da batasan ya faru ba......eh ta taba binsa abuja.....kuma aikin mashkur kusan shine aiki na qarshe da tayi har yau kuma bata sake sha'awar maimaita wani abu makamancinsa ba.......amma yaushe ya fiddo hotonta ya nunata a matsayin karuwa yana cigiyarta?. KARUWA kalma mafi muni da tafi tsana taji ta gilma a kunnuwanta......duk yadda takai tsakaninka da ita muddin xaka kira wannan sunan a gaban fuskarta......to takan iya manta ya kuke da ita?. "Am asking you......" Ya fada yana jin ya soma hasala ganin shurun da tayi kamar ba da ita yake magana ba. "Ban sani ba......." Ta bashi amsa muryarta tana so ta fara rawa. Me zata gaya masa wanda zai sanya ya fahimceta?. "Baki sani ba kaman yaya?,ya shigo har dakin ba tare an fasa kowanne gini na gidan nan ba......ya shigo dakinki ba tare da kinyi yunqurin kiran koda security daya na gidan nan ba......ya shigo dakinki daidai lokacin kwanciyar baccinki?,a sanda kike daure da towel kadai da hijabi?" Ya qarasa maganar yana qarasawa dab da ita,yana kuma kaiwa qarshe a tsawace har sai data lumshe idanunta ta kuma gaza budesu. Tsawa......tsawa,bata son tsawa,bata qaunarta,tsawar ma daga wajen d'a namiji.....wanda tuni ta karanci sun jima da raina ajawalin mata. Wani abu data jima da shawa kanta alwashi,raini.....wulaqanci.....izgili da toxarci na da namiji,ita ko 'yan uwanta ba wanda zata lamunta ya daukesu. "Ban sani ba nima" Ta sake maimaita masa don da gasken batasan yadda akayi mashkur ya shigo ba. "Harda wayar daya baki kenan itama ita ta kawo kanta?!.....nace ita ta kawo kanta?!!!" Ya fadi da qarfi kaman yana shirin fasa mata kunnuwa. "Stop it!.....wanne kakeso na amsa maka?,wacce tuhuma kakeso na baka amsarta?!" Itama ta maida masa muryarta na rawa,oily eyes dinta suna qara walainiya cikin hasken ranar daya fara dagawa. "Ni kikewa shouting?" Ya tambayeta da tsananin mamaki,saidai kuma qarar wayarsa ta janye magana ta gaba da yaso fadi. Bai fiya daga waya a cikin irin wannan yanayin da yake cikin tsananin fushi ba......amma yana expecting kira me muhimmanci daga gurin wani dan kasuwa mazaunin qasar ivory Coast,dole ya ciro wayar. Shi da ita dukansu akan sunan FAREEDA KHALEED MUSTAPHA ya sauka,ita ta fara janye idanunta tana jin wata wani fushinta yana ninkuwa. Ya sanyata a gaba da tarin tambayoyinsa amma shi a daidai lokacin karuwarshi ko yarinyarsa.....batasan da wanne suna zata kirata ba ita ke kiransa?. Ta nashi bangaren banda muhimmancin da wayar ke dashi a wajensa tabbas ba abinda zai hanashi tarwatsata ita kanta wayar a wajen bama fareeda kawai ba. "Sorry sir" Yaji an fada da sauri,abinda yakai hankalinsu kenan wajen. Me sunan malam ne,da sassarfa yake barin wajen saboda kunyar yadda ya samesu a tsaye dab da juna,baisan kuma zai samesu a hakan ba da bai biyo ta wajen ba. "Zo nan" Ya kirashi a nutse yana duban hannunsa dake dauke da newspaper daya saba ajiye masa duk safiya daga kamfanin jaridu daban daban. Sunkuyawa tayi ta zame ta gefansa tana takawa don barin wajen,haka kawai taji bama zata iya zama ta fuskanceshi ba sam. Kwata kwata bata yarda dashi ba Shima.....wacece faridan?,meye alaqarsu da koda yaushe layinsa cikin karbar kiranta yake?. Yana jin wucewarta amma bai waiwaya ba don hankalinsa yana kan me sunan malam. "Good morning sir" Ya sake gaidashi cikin girmamawa yana rusunawa ba tare daya miqa masa newspaper din ba kaman yadda ya saba,duk da yawancin lokuta ma yana samunsu ne a daura da dining suna jiran fitowarsa,idan ga kammala dubawa kuma zai kwashesu sai kuma fitowar gobe. "Morning.....how you doing?" "Fine sir" Still ya kuma amsa masa amma ba alamun zai miqa masa su. Abun yadan bawa fuad mamaki,yana shirin miqa masa hannunsa don ya bashi kira ya kuma shigo masa. Kai tsaye aka gaya masa farouq ne don haka ya daga ba wani bata lokaci "Good morning dude" Farouq ya furta kaman yadda ya saba masa,saidai kuma daga can qasan muryarsa kaman yana iya tsinto wani abun "Morning......mun tashi lafiya?" "Fine.....ya jikin naka?,ka fita ne ko ka sauko daga stairs?" Duka farouq din ya cure tambayoyin ya masa,abinda yaja hankalin fu'ad kenan. "Ban fita ba......na sauko qasa na rako anni yanxun xan koma ciki". "Good.....but do me a favor mana" Ya fada yana fatan idanunsa basuga abinda ya gani ba. "Ehnnnnn" Fu'ad ya fada yana jin zaquwa na jin abinda zai fito a bakinsa. "Kayi skipping duba newspapers na yau mana......instead of that ka bani aron time din muyi magana" Yadda farouq yayi maganan kawai ya sanyashi yasha jinin jikinsa,sai kawai ya miqawa me sunan malam hannunsa yana masa nuni da newspapers din da yake rqe dasu yana kafeshi da idanun nan nasa da kwarjini ke cike dasu kullum ba tare da ya sauke wayar a kunnensa ba. "Kowanne lokaci na yini na zan iya baka farouq,not the only news time" Ya bashi amsa sanda me sunan malam ya miqo masa newspapers din da hannu biyu cikin mutuwar jiki,ya kuma janye daga wajen da sassarfa don bazai iya tsaiwa yana dubansa a sanda yake kallon labarin dake buge a jaridar ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 63 63 "Wannan abun kawai nake buqata please" Farouq ya maimaita sanda ya shiga motarsa dake farfajiyar gidan. So yake yaja maganan da tsaho sannan ya cimmasa kafin ya duba abinda ke faruwan saidai sanda yake bashi amsa na qarshe yana bashi amsar ne sanda idanunsa suka sauka akan tittle na labarin da yaci shafin farko gaba dayansa na jaridun guda biyu. *_TSINTAR DAMI A KALA_* _BABBAR JARABAWA......SHIN KUSAN WACECE ASALIN MATAR MATASHIN MILLIONAIRE DINNAN MAMALLAKIN KAMFANINNIKAN DAKE SARRAFA GWALA GWALAI?_ "Farouq.....you have my time,amma kafin sannan......" Maganar ta yanke masa sanda makeken hotonta ya biyo bayan title din ita da mashkur. Hoto ne da aka daukeshi gaban wani hotel da sunan kawai ya iya kalla ba tare daya tantance wanne bane.......sanda ya bude mata murfin motar ita kuma tana qoqarin fitowa a motar yana riqe da handbag dinta. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ya fada yana jin dukka gabbansa suna daukan dumi kafin daga baya kuma suyi wani irin sanyi kaman ba'a jikinsa suke ba. _mrs muhammad fu'ad jadda sabreen ahmad_. Baya jin idanunsa zasu iya ci gaba da kallon abinda ke gabansa,sai kawai ya hade newspapers din waje daya ya curesu a hannunsa yana takawa zuwa cikin gidan ba tare daya tsaya tuna cewa magana suke da farouq ba,kuma yabar farouq din akan line na waya. Shuuuu din da farouq yakeji ya sanyashi qarfafa zarginsa akwai abinda ya faru,sai kawai ya aje wayar ba tare daya kasheta ba,ya tada motar da wani irin hanzari wanda yanayin gaggawar da security na gidan suka ga yanayi ya sakasu dage masa qofa ya fice tun bai qaraso ba. Bazaice ga wani abu da ya faru daga sanda yakai kansa samansa ba banda azababben ciwon kai da yake masa kutufo kota ina. Ba abinda bakinsa ke furtawa sai Astgafirullah yana me kyautata zaton akwai wani abu daya aikatawa ubangiji wanda ba daidai ba shi yasa ya jarabceshi da wadannan abubuwan. Dukka komai akan yarinya daya?.......yarinyar da koda ta zame masa zabi a nasa qashin kan hakan ba lallai ya tabbataba banda miqewa da kafewar maamah akan lamarin?. Da qyar ya iya amsa sallamar farouq sanda ya bude smart door din ya qaraso cikin parlor din idanunsa akan fu'ad. A yadda yaga idanunsa sun jirkita ya tabbatar labarin ya gama ruskarsa. Da idanu yabi farouq din,har zuwa sanda ya qaraso,ya tsugunna ya debi duqunqunannun jaridun ya bude ya kuma rufesu a take. "Da gayya aka buga wannan news din......." "To menene qaryar da sukayi a ciki?.....ban karanta sauran labarinta a qasa da suka saka ba.......amma wanne ne qarya farouq?" Maida dubansa yayi kan fu'ad da yake dubansa kai tsaye. A zahiri jijiyoyin kansa ke tashi sosai har sun nuna ta farar fatarsa,wanda abadini yake nuna ciwon kai yakeyi sosai,irin ciwon kan da ya dinga addaba masa sanda yake fama da matsalar depression dinsa,wanda ya tabbatar ya jima rabonsa dashi..... Sakin baki yayi yana kallon fu'ad din daya fara magana cikin sanyi saidai akwai zafi me yawa a kalamansa. "Stop dude.....ina gaya maka.....don't judge book by his cover.........ka daina judging mutane haka" "Judging nasu nake ma?,bayan ina da full details na evidence akan duk maganan da nakeyi farouq akan yarinyar?" Yayi maganan da sanyin dai,amma lafuzzansa na nuna zallar zafin da yakeji. "Evidence kadai bazasu tabbatar da hakan ba.......kayi managing personal boundaries tsakaninku kaman na kowanne miji da mata,akwai buqatar wani sensitive......" "Haba mana!" Fu'ad da yakeji zuciyarsa na matsewa kaman zata fashe ya tsaida farouq yana zama sosai yana jin jiri daga inda yake zaunen. "Kada bakinka yakai nan wajen.......bakasan wacece ita bane farouq?,bakasan sunan da kowa yake kiranta dashi ba?,baka gani jikin newspapers ba?" "Na gani.....na kuma sani......kuma ka rigani sanin haka kace zaka daukota ka gyarata......ya akayi ka kasa fu'ad?" Ya jefa masa tambayar yana riqe habarsa. Kansa ya jijjiga sosai yana duban farouq "Ban kasa ba......bazan kuma kasa ba......abu daya kemin burki.....duk sanda na kalleta sai naji tayi qanqanta da yawa nayi mata kalar azabobin dana tanadar mata......tayi mitsitsiya na sanyata a prison din dana shirya mata......amma duk sanda ta aikata wani abu kota bullo da wani abun........sai naga nine naketa kuskuren kallon tayi qanqanta......a abinda zuciyata ke rayamin wannan karon......duk hukuncin da yazo na dauka a kanta a tunanina na qarshe dashi zanyi amfani......" "Banda divorcee......" "Harda shi idan ta kama" Ya fada confidently. Ido Farooq ya zuba masa kawai,ga mamakin fu'ad sai yaga ya saki wani irin murmushi yana girgiza kai. Shima duban farouq din yake kafin yaji murmushinsa ya bata masa rai. Bayajin a yanayin da yake ciki ya kamata wani abu me kama da murmushi ya fita a fuskan farouq,don haka ya miqe tsam yana dosar bedroom dinsa. Da hanzari farouq ya miqe yana kiransa "Wait dude.....wait" Don ya tabbatar wannan bedroom din nasa me smart door idan ya shiga ya rufe baka isa ka bude ba muddin bai sakaka cikin wadanda zasu iya budeta ba. Bai saurareshi ba ya shige dakin abinsa,da qarfi ya rufe qofar yabar farouq a nan a tsaye. A yanzun da baya ganinsa sai murmushinsa ya ninka na dazu,bayan minti uku yayi qoqarin daidaita kansa,ya matsa yana daukan telephone na falo din ya kira cikin dakin nasa. Yayita kira yana jiyota tana ringing,kaman bazai daga ba kafin ya daga daga baya,ya sakata a kunne ba tare da yace komai ba. "Am really sorry dude.....na hango wani abu ne daban da yake durfafoka da matuqar qarfi fiye da qarfin guguwa......amma it seems like baka ganshi ba baka kuma fahimceshi ba......anyways kayi aiki da hankalinka da intelligent dinnan dana sanka dashi.......am always free,and then it's time to act for koma waye behind all these issues......na tabbatar akwai wani abu boyayye......think wisely......am always by your side.....take a rest,but please kasha magani". Sanyaya ranshi sosai maganganun farouq sukayi,yayi shuru kawai yana saurarenshi bai iya ce masa komai ba......shi kansa baisan me yasa a bangaren nan kaman qwalqwalwarsa bata iya aiki daidai ba?. Yana jin kamar ya gaji......yana buqatar hutu da gaske na jiki dana kwanya "Am tired farouq......I'm feeling burnt,i need some time to unwind and focus on my well-being......kayi magana da saddiq.....i want him to schedule my annual leave cikin kwana uku". "Kowa ma lokacin hutunsa yazo......International gateway to Maldives" Ya furta yana motsa labbansa gami da jefa hannunsa sama yana kwatanta yadda jirgi yake cillawa sama yayin daya cirata daga qasa. "Zan kawo nesa zuwa kusa......zan dawo da mafarki zuwa gaskiya......komai zai warware.....zan kuma baka mamakin yadda zan juya maka rayuwarka dare daya" Farouq ya fada yana dariya kaman mummunan abu irin wannan bai faru ba. Kawai wani nishadi yakeji qasan ransa idan yayi imagination na yadda komai zai kasance,sai yaji kawai ya qagu shi Kansa lokacin yayi,sai ya juya ya tattare key da wayarsa yana maidawa aljihu ya soma sauka yana barin gidan,ko saddiq dinma bazai nema ba.....shi zai shirya komai,sai komai din ya kammala sannan kowa yaji ya gani. *_tom......me karatu?,wanne plan kake tunanin farouq yana dashi akan fu'ad?,muje zuwa_* Yana driving a mota amma tunani fal kanshi. Tunda yake bai taba hangen wani abu daya jigata fu'ad komai tsananinsa ba kaman wannan......anya ba burbushin wannan halittar daya tsirowa zuciyarsa kuwa?, wadda kusan itace jigo na kowanne tsanani da wahala da zuciya kan iya shiga akan wani dan adam?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 64 64 Bayason irin fushin da yakeji cikin ruhinsa da jikinsa gaba daya......yana buqatar yayi cooling down ko yaya ne,a lokacin ayar nan da taxo cikin alqur'ani me girma ta fado masa "Ku saurara.......da ambaton Allah kadai zukata ke samun nutsuwa" "Sadaqallahul azeem" Ya fadi yana miqewa hadi da fara jin sassauci daga tuna ayar kawai. Toilet dinsa ya shiga,ya daura alwala me kyau,sannan ya dawo cikin dakin yana kunna chandelier din dake kafe tsakiyar dakin,wadda ke hade da Bluetooth da kuma fanka me bada sassanyan iskar data banbanta data sauran fankoki. Remote ya dauka ya kashe hasken don baya buqatarsa,ya kuma kunna speaker din dake jiki yana daidaitata da wayarss,take muryar fasihin malamin nan limamin ka'aba wato sheik abdurrahman assudais ta karade dakin cikin sauti mafi tsarki na karatun alqur'ani. Relaxing yayi sosai soman sofa din dake dakin yana jin wani sukuni ya soma ratsahi,kaf a cikin malamai idan akwai wani sauti da yafi so yafi qauna bazai wuce sautin sheik abdurrahman assudais ba,wannan dalilin yaja ra'ayinsa qira'arsa gaba daya ta juye zuwa ta sudais din sak.....da wannan qira'ar yayi sauka,kuma har yau itace a bakinsa. Idanunsa a lumshe yana ci gaba da bin sautin,bazaice yana jin yunwa ba ko kadan,zamansa a haka duk duniya yafi komai yi masa dadi,a haka ya shafe kusan awanni biyu har zuwa sanda wayarsa tayi haske,kira kuma ya shigo wayar tasa. Hannu ya sanya ya jawo yana dubawa,ganin me kiran ya sakashi daukan remote din dake gefansa,ya kashe volume din gaba daya sannan ya daga wayar yana sakata a hands free. "Good afternoon sir......yanzu haka dukka shugabannin gidan jaridan suna hannunmu". Zamanshi sosai ya gyara cikin kujerar yana harde qafafunsa waje daya "Well-done,good job khaleed,akaiminsu housing estate na darmanawa.......by 4 zan fito in sha Allah" "Yes sir" Ya fada cikin tsananin nuna ladabi,bai sake jiran komai daga wajensa ba ya kashe wayar yana ajeta gefe. Bai sake batawa kansa rai da tunani ba ya dauki remote din da xummar qara volume din,cikin ransa yana jin bazai sake barin komai ya bata ranshi har haka ba......ko meye ya faru da ita ita ta jawo......amma fa bazai taba lamunta a taba masa igiyar aure ba,ko kuma sunansa ya fito a ciki ba ko na ahalinsa. Wani kiran ne ya sake shigowa dole ya aje remote din. Asp ne yake kiran,shima bai jinkiri ba ya daga. "Sir........mun sama musu gurin ajiya na musamman......kuma zamu tuhumesu da kyau har sai sun fadi gaskiyar wanda ya aikosu". "Na gode......but inaso ku barmin wannan a hannuna......ku ajiyesun irin ajiyar data dace dasu har xuwa sanda zasu furta wanda ya basu hanya da daman shigowar" "Okay boss...." "Thank you" Ya sake fadi labbansa suna motsawa. Wannan bacin ran da yaketa son hadiyewa still dai ya sake taso masa,ya sanya hannunsa ya shafi kansa. Zai iya cewa tun daga guards dinsa zuwa securities dinsa amintattu ne,bashi da ko kwanto da ko shakka akan koda mutum daya daga ciki,duk da dan adam tara yake bai cika goma ba......kuma wasu daga cikin 'yan adam din masu iya canzawa ne a duk sanda sukaso a karan kansu,walau dalili na son zuciya ko makamancin hakan......amma su kam yayi imanin yadda yake mu'amalantarsu daban yake da sauran yadda masu gida ke mu'amala da yaran gidansu. Kyautatawarsa a garesu ta daban ce kaman yadda qaunarsu a gareshi ta daban ce. To amma a yanzun yadda yakejin zuciyarsa komai ma yana iya faruwa......sannan a yadda yasan ya gidansa yake,abune me wahala a iya keta tsaron gidan a shigo haka siddan ba tare da idon sani ko mataimaki sannanne ba. Volume dinsa ya qaro yana fatan sake samun nutsuwa da daidaituwar zuciyar da zata bashi qwarin gwiwar fita zuwa yammacin. Bai tashi ba sai da akayi sallar azahar,ya daura alwala ya fito don halartar jam'in sallah kaman yadda ya saba muddin yana kusa da masallaci. Dukkanin ma'aikatan kowa rabe rabe ya dinga yi daga ganin fitowarsa. Zukatansu a razane yake abinda ya sanya gidan ya sake daukan shuru gaba daya kamar ba wata halitta a gidan me rai da tayi saura. Bai dawo cikin gidan ba sai la'asar,don ganinsa yau free haka da rana ya sanya masu buqata suka dinga shigowa masallacin. Bai hanasu ba ya zauna ya dinga sauraren kokensu daya bayan daya. Ba wanda ya bari ya tashi a wajen ba tare da gaggwaban abun alkhairi ba,jordan na tare dashi shi ya tashi sauraronsu,sukayi la'asar ya miqe ya wuce gida qirjinsa cike da nauyi. Sai yake sake ganin yadda ubangiji ke tsara rayuwa yadda yaso.......matsalar wani bata wani ba......a yadda unguwar take baiyi zaton masu qaramin qarfi dake neman taimako na shawagi a cikinta ba. Ya dubi kansa sanda yake wucewa ta babban glass door din da zaka taras a gate din farko na gidan. Ubangiji ya azurtashi da dukiya me yawan gaske......lafiya da wadata......saidai ya samu naqasu ta bangaren uwa da mace ta gari,wanda wadannan abubuwa biyun sune jigo a rayuwar kowanne dan adam. Ga wasu can su kuma nasu burin shine INAMA MUNE ME JADDA?,ba tare da sunsan ainihin waye me jaddan ba?,me yake fuskanta?,wacce rayuwa take going through......(wannan ya zamana izina a garemu gaba daya,kafin kayi burin inama kaine wane?,kayi tunanin mene rayuwarsa ta badini?,kayi tunanin wadanne qayoyi ya tattaka da tsinika kafin yakai ga isowa nan inda yake?,ko yaushe idan kaga wani mutum da rayuwarsa ke burgeka,ma roqa Allah ta hanya daban bata hanyar Allah yasa na zama kaman wane ba.....bayan fuskar wane dinnan kawai kake gani bakasan cikinsa ya yake ba,Allah ka kyautata rayuwarmu,ka bamu tsira duniya da lahira)" Da tarin tunane tunane yake ratsowa falon daya xama wani irin shuru. Gaba daya kallon gidan yake wani iri,har a gangar jikinsa yakejin ya gaji da xaman cikinsa. Wuf ya hangi gilmawarta daga kitchen kaman zata kifa tana nufar qofarsu. Har yaci gaba da tafiya wani abu ya sauko cikin tunaninsa "Ke!" Yayi kiranta da wani amon sauti da a take ya tara zazzafar gudawa cikin tumbinta "Na'am......na'am ranka ya dade" Zuwaira ta fada wadda ke rungume da wani abu da baisan meye ba. Hannuwansa ya zube cikin aljihun wandonsa yana qare mata kallo,zuciyarsa tana raya masa wani abu game da ita. Wani abu me kama da xargi tuhuma da kuma rashin aminci a kanta yaji yana tsarga masa. Irin kallon jadda din ba kowanne mutum ke iya jurarsa ba,sai mutum me babbar kurwa,me babbar kurwar ma wanda ya cika da gaskiya da kuma amana,ba wani ha'inci cikin lamarinsa,wannan ya sanya zuwaira ta dinga jin kamar yana karance duk wani sirri dake tattare a qirjinta zuwa cikinta,tamkar ya sanya microscope yana tantance adadin qulla qulla da harqallar data taba shiryawa tsahon rayuwarta,wannan ya qarawa adadin zuciyarta gudu,ya kuma hanata ci gaba da daidaituwa akan qafafunta,saita sulale ta duqa saman qafafunta "Allah ya taimaka.....tuba nake,bansan kana cikin gidan ba ai......da ba'a fito ba,wannana bun daya faru ranka ya dade shine ya hanani nutsuwa.......hajiya naketa son dubawa aga yanayin da take ciki....." "Ke" Ya sake kiranta yana dage dukka girarsa sama guda biyun. "Na'am yallabai na'am......." "Ki tarkata komai naki kibar gidannan cikin qasa da minti goma....." "To an gama ranka ya dade,aisai a komawa hajiya maamah baya goya marayu" Ta furta tana jin wani sassauci da rangwame a ruhinta. A abinda takeji yanzun sallamarta shine babban gatan da yayi mata,duk sanda taji muryarsa sai kowacce kafa ta jikinta ta jiqe da gumi. Sai a yanxu take ganin cewa da gaske xaman gidan jadda yafi qarfinta,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. A baya tana tunanin duk randa yace taje ya sallameta zataji tashin hankali maras iyaka......amma a yau sai takejin kamar 'yanci ne daga bata zuwa zamowa halastaccen d'a. "Kinsan me?" Ya fada yana sake dubanta,saita dakata tana saurarensa. "Bazan dubi tsufanki ko digon furfura koda qwaya daya dake tsakiyar kanki ba......muddin naxo na sameki kin koma gifan gidan maamah........ki tabbatar daga ranar kin tashi daga aiki......kiyi nesa da ita da komai da kowa daya danganceta.....and hakan bawai xai sakaki kin tsira ba,duk mutumin da yake gidan nan daga kwana uku baya zuwa jiya da abin ya faru baxai tsira ba a waje na......wanda kawai zai tsira shine MAI GASKIYA ". Duburbucewa tayi har akwatin kayan asirin maamah na shirin tarwatsewa daga hannunta. Gab gab gab haka hannuwanta da qafafunta suka dinga haduwa waje daya,wannan wanne irin kalar tashin hankali ne?,wanne irin yaro ne wannan maras imani.... Lallai dole mallakarsa ta yiwa mariya wahala,zuwaira ta furta hakan a ranta sanda take ta qoqarin kai kanta ga sassansu don ta samu ta sulale kaman yadda ya shawarceta. Ayadda ta sanshi tana ganin ko cinye namanka yace zaiyi zai iya......musamman shi daya mallaki masu gidan ranar da babu me tuhumarsa ko bin ba'asin abinda yayin. Gaba daya wunin yau duka hankalinta yana kan wayoyinta,bama ita ba.....hatta da fareeda kowanne motsi nata yake kan social media's tana hasashen watsuwar abun a kowacce kafan sada zumunta. Sanda taga ankai azahar shuru sai duk wata nutsuwa ta soma barin gangar jikinta,hankalinta ya gaza kwanciya kwata kwata,ta kuma shirya kai tsaye ta kira driver ya dauketa zuwa gidan maamah. A sannan ita dinma duban wayar take tayi.......tanaso ta samu wani haske ko yaya yake.......tunda ta zauna take saqa yadda komai zai kasance.......take qiyasta irin tozarcin da zata yiwa sabreen. Lallai sai ta sanyata ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa.......ita kanta batasan adadin yawan tozarci da qasqancin da zata sanyata ta fuskanta ba. Mamakinta ya tsananta ainun da rashin samun kai,sai taji ta kasa jira,kai tsaye ta daga waya don kiran fareeda,amma sai fareedan ta hutashe da ita saboda turo qofan setting room din da tayi ta shigo tana taunar chewing gum kaman yadda ya zame mata al'ada,duk kuwa da cewa yau din bata cikin wannan mode din,amma cin chewing gum din ya zame mata dabi'a. "Ke nake shirin kira yanzun.......banga tasirin aikinki ko wani motsi na daban ba" Maamah din ta furta kanta tsaye tana duban idanun fareeda. Idanu tadan xubawa maamah din,mamakin dabi'arta tana dan kamata. Kanta tsaye take magana akan duk wani abu daya shafi buqatarta,ba ruwanta da wata matsalarka ko fuskantar yanayin da kake ciki. Kanta ta dauke tana qarasowa ciki,sannan ta yiwa kanta mazauni saman hannun sofa din tana harde hannuwanta a qirjinta "Wannan shine aiki mafi kashe kudi da nayi......sannan shine aiki mafi jinkirin samun nasara" Tayi maganar tana duban maamah din. "Masu aiki sun kammala.......naki aikin da nawa duka ba wanda ya kawo result me kyau........abu daya ya rage shine,ki kira d'anki ki tuntubi sakamako daga gareshi". Gyara zamanta maamah tayi tana duban fareeda,ta soma fahimtar wasu halayenta da inda dabi'unta suka sanya gaba,bata gayawa fareeda tayi failing a nata agenda din ba.....ya akayi amma ta sani?. "Na yarda har abada yaro yaro ne.......kina tunanin samun galaba akan duk wani lamari daya shafi fu'ad abune me sauqi?,inda kuwa hakanne da bakizo gabana ba......da babu ke cikin babin qaddararmu sam sam" Maamah ta fadi tana duban fareeda. "Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi bazai hango ba..........a naki lisssafin kiran fu'ad kai tsaye na jefeshi da salon tambayoyinki abune me sauqi da zai sanya mu wanye lafiya?" Ta qarasa maganar tana duban fareeda data zubawa maamah nata idanun. "Kina iya kiransa ta wata siga daban ki kuma zaqulo bayanan da kikeso......amma zai zama babban kuskuren rayuwarki ki biyo masa ta waccan hanyar taki....." "Amma bisa alqawari da yarjejeniya.......xaki zama tsanina na mallakar fu'ad haka ne?" "Har yanxu ina kan wannan bakan.......amma fidda sabreen daga gidansa aikinki ne......zai iya zama nawa aikin,amma kuma salon aikin nan da yake zamowa ba waji bi". Sun jima suna kallon kallo tsakaninsu,kowanne da kalar saqar dake cikin zuciyarsa game da dan uwansa,kafin fareeda ta fiddo wayar da musamman saboda kiran fuad din ta tanadeta. Da kowacce waya da kuma kowanne layi ta kirashi ba zata sameshi ba saida wannan wayar kadai. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 65 65 _Manzon Allah S A W bai taba aibata abinci ba,idan ya burgeshi sai yaci,idan kuma baiyi masa ba sai ya qyaleshi(ba tare daya aibatashi ba)_ Tsaf ya shirya cikin trouser dark blue na yadin vicuna,yayin da sanya black shirt data fidda ainihin kan sassalkar fatar nan tasa me tsananin haske,wadda ta cakuda da hutu da jin dadin dake bayyana kansa cikin kowanne hali yake. Kyakkyawar qasumbar fuskarsa da bata da cika irin ta cukus ta sake qawata fuskarsa da sanya masa kwarjini,tana da santsi kwatankwacin sumar dake lullube saman kansa. Baqa ce sidik kaman gashin girarsa dana idanunsa,hakanan kaman sauran gargasar dake lullube da sassan jikinsa. Agogo fata ya daura a tsintsiyar hannunsa me tsananin tsada daya dace da shigarsa dama tsadar kayan jikinsa,yabi ko ina na jikinsa ya feshe da lallausan turaren nan nasa me taushin qamshi. Tsananin dauriya kawai ta sanyawa ruhinta,tun bayan dawowar amna da batakai magarib ba kaman yadda anni tace taketa qoqarin shimfida walwala akan fuskarta,duk da cewa abun ba haka yake ba daga qasan zuciyartata. Amna din ta dabance,tana da barkwanci da sakin jiki ga duk wanda ta yarda dashi,wannan ya sanya cikin qasa da awa guda taji nauyin dake qirjinta yana raguwa,lokaci lokaci labarun amnan suna sake dauke hankalinta daga yanayin da take ji. Ita ta tilastata da yammacin kan su fito daga daki zuwa kitchen "Wainan fulawa nake sha'awa.......yakumbo ce take mana,ta tafi ganin gida tun wancan satin,muje na gwada ko zan iya please adda" Ba zata iya qin tankwabar da tayinta ba,haka ta maqala hijab saman doguwar rigarta ta bita kitchen din,wanda a qarshe sabreen dince ta hada Mata wainar ta soya mata ta kuma tara mata a warmers. Ta cika da mamakin yadda akayi amnan ta iya girki kala kala amma bata iya wainar fulawa ba. Qwarewar amnan a girki yana bata sha'awa,harma takanji tana sha'awa itama iya kalolin abinciccika. Suna a saman dining tana kallon yadda amnan ke santin wainar fulawan,time to time tana murmushi kawai. Ta sake yarda da gaske rayuwa mataki mataki ce,kowanne da kuma kalar muhalli da hurbin data ajeshi. Duk da fiye da rabin hankalinta bashi a wajen,amma hakan ba hanata jin saukowarsa ba a jikinta. Qamshin turarensa ne ya fara isa ga hancinta,kafin daga bisani qamshin ya fara mamaye parlor din. Cikin dabara ta dauke duban ta daga wajen da yake takowa,tanason nuna sam sam ma bata ganshi ba. Duk sanda fuskarsa zai bayyana a gareta,ba abinda yake tuna mata sai tambayoyinsan nan data tsana,tambayoyin dake matuqar qona masa rai ba kadan ba. "Hamma......barka da yamma" Amna ta furta da murmushi saman fuskarta sanda ta waiwaya ta ganshi,sai ta aje wayar hannunta tana bashi hankalinta gaba daya "Barks lovey dovey" Yayi maganar da wani kwantaccen sauti daya sanya sabreen taji tsigar jikinta ya zuba,take kuma ta daga kanta a hankali kaman me tsoron ganin wani abun tsoro,duk yadda taso ta yiwa idanunta shamaki amma sai da suka fada kan fuskarsa,ta kuma ci karo da wani yanayi dake shimfide saman fuskarsa din. Shi ba murmushi ba sannan kuma ba'a daure fuskar take ba......saidai yana yin ya nuna ya zama very calm ba kaman yadda take ganinsa kwanakin da duka wadannan abubuwan suka faru ba. Zamewa amna tayi tana sake gaidashi bayan gaisuwar daxu,ya amsa yana motsawa alamun xai wuce. Wayarsa dake riqe a hannunsa ta fara bada wani sassanyan sautin sarewa maras hayaniya da yawa,kafin daga bisani sunan FAREEDA KHALED MUSTAPHA ya fita tarwai ta cikin speaker din. Duk yadda taso watsar da sunan daga cikin kunnuwanta amma hakan ya gagara. Sunane data jima tana jinsa akai akai,har kuma ya soma zama a kwanyartata. Maida hankalinta tayi ga amna amma saita gaza ci gaba da hakan,batasan yadda akayi idanunta suka dauketa zuwa fuskarsa ba. Wayar ya daga zuwa fuskarshi yana duban me kiran,sosai ya zubawa numbers din nata idanu,manhajar daya dora kan wayar tasa ke harbawa daga gefan hagu na wayar tana nuna masa abinda fareeda din ke aiki dashi wanda ke fasa duk wani shinge da zai saka number dinta,duk sanda ta jira kiran ya samu damar isowar gareshi kai tsaye. Dan qaramin murmushi ya subuce masa wanda iyakacinsa labbansa,saidai a nata idanun qaruwar murmushin ta gani. Idanunta taja ta lumshe daga kallon dark pink lips dinsa. Batasan me yasa gabanta yayi wata wawiyar faduwa ba,sai kawai taji bata da sha'awar ci gaba da zama a wajen. Tsam ta miqe sanda amna ke ce masa "A dawo lafiya hamma...." Ta fara saukowa daga steps din,a cikin jikinta taji amna din na satar kallonta,wani nauyi ta sakar mata da bisa dole ta motsa labbanta tana fadin "Adawo lafiya" Sosai yaji kalmomin sun zama baqi a kunnensa,har ya motsa kaman zai waiwaya sai kuma baiyi hakan ba ya amsa "Allah yasa" Yana takawa gami da ficewa da takun nan nasa da ta dade da haddaceshi. Wani irin taku yakeyi tamkar namijin toro,zakayi tunanin wani saraki ne,ko kuma yana qawata takun nasa daidai da yadda zaija hankalin masu kallonshi. Ficewarsa daga falon ya bata wani qaramin sukuni,sai ta fasa komawa dakin ta sauka saman sofas din dake falon ta zauna tana maida numfashi. Idanunta ta maida hanyar daya wuce din "Fareeda KHALED MUSTAPHA" Sunan ya dawo mata radam a kunne,murmushinsa kuma ya sake giftawa ta idanunta,ta sake lumshe idonta ta kuma budesu lokaci daya "Waya sani ma ko ita ta kirashi?,wa yasan inda zasuje?" Ta furta can qasan zuciyarta tana tuna irin tuhumomin da take gani a kanta cikin idanunsa. "Waye yasan abinda shi yake aikatawa ma?" Ta sake samun kanta da fada qasan zuciyarta. Ko daya ba zata taba aminta da cewa shi din a tsare yake ba......taga matasa masu tarin yawa da ni'ima da baiwar dukiyar da yake da ita yasu bata taka rabinsa bama......amma qazantar dake cikinsu sai Allah. Kamar dai shi......a haka kamilallen mutum....amma badininsu wata irin danqararriyar qazantace maras dadin gani ko tabawa. "Adda......." Taji muryar amna daga gefanta. Fararen idanunta ta daga tana duban amna gami da katse tunanin dake kai kawo a ranta "Amna" Ta amsa mata murya qasa qasa tana nazartar fuskarta. Fuska ta narke sosai tana zagayowa gabanta ta zauna. "Nace wani abu adda bazai zama shishshigi ba?" Tayi maganar da alamun son ta furta abinda ke bakinta. Qaramin murmushi ta sakar mata don ta bata nutsuwa da gamsuwa akan duk maganar da zatayi "Fadi amna mana" Sai data gyara zamanta tana maida mata murmushin sannan tace "Yaaa saddiq yana bani labarin hamma......duk da na fisu sanin hamma ta wasu abubuwan.......amma ya saddiq kuma zai iya fina saboda shi din PA dinsa ne.....duk inda zai saka qafa a gida ko a office suna tare.......kinsan waye hamma kuwa?,ya yake?" Tayi tambayar da murmushin daya kusa zama dariya akan fuskarta. Numfashi taja a boye tana jin sunansa kawai da amna ta kira yana qara yawaita bugun zuciyarta,inda zata iya zata dakatar da amna daga yi mata duk wata hira data shafeshi......kwanaki kaddan suka rage masa cikin rayuwarta.......tana jiran kawai ranar da zata samu tabbacin su huda sun isa mali lafiya hannun momma bahijja.......a wannan lokacin komai zai tarwatse. "Saikin fada amna" Ta fadi bawai don ranta yana so ba,sake gyara zama sosai tayi ta riqo hannun sabreen "He's a loving and caring partner.he wants a deeply romantic connection with his wife" Ta fada murya can qasa,kaman tana tunanin yana kusa dasu kuma tana tsoron kada ya jiyota. Dukka idanunta sabreen ta fiddo waje tana kallon amna,yadda amna din tayi maganar da wani confidence da qwarin gwiwa ya bawa sabreen mamaki.....can qasan zuciyarta kuma sai taji kaman tanason taja hira kadan da amna din. Abu daya dai tayi amanna fuskar fuad ta gida daban......fuskarta ta gidansa daban.....kamar yadda fuskarsa ta mu'amalarsa ta waje daban,banda haka mutum kaman fuad dinne zata siffanta haka?. "Kina da ja ko adda?......" Ta tambayi sabreen kai tsaye,tana jin tanason tayi hira da ita.......tanaso ta fadi mata abinda ta fuskanta ko ita ta fahimci ba daidai ba "I swear adda........He envisions a future where he and his wife grow old together,hand in hand......ko a gabana wannan yasha fadinsa......musamman idan suna hira na sako da sako shi da BB farouq.......hamma na yana son soyayya,ya kuma cancanceta......hammana yana son kulawa......that's why yakeji dani,komai na hammana daban yake a wajena.....tausayin hamma nakeji coz....He suffered a lot in his life He had a rough past" Ta fada dukka a jere tana riqe da hannun sabreen kaman hakan shine zai saka ta fahimta abinda takeji a zuciyarta na tausayin hamman nata. Baki da idanu kawai sabreen ta sake tana kallon amna,tana sake gasgatawa da imanin cewa eh lallai da gaske wannan mugun yana da muhalli me girma da fadi a rayuwarta......amma wanne irin hardness ne haka ya fuskanta?,mutumin da ya rayu tsakanin iyaye biyu 'yan uwa hudu?,mutumin dake cikin daula da dukiya?. "Believe me adda......please,ki qara akan kulawan da kike bawa hamma,He's passionate about building a strong loving relationship with his wife.......na dade da sanin duk wadda ta samu hamma fuad.....She's the luckiest woman alive and she's incredible fortunate" Murmushi ta samu kanta da subucewa dashi,saita miqa hannu ta riqe amna din sosai bawai don maganganu da yabo a kansa sun burgeta ba,aah......sai don ita din mutum ce me girmama 'yan uwantaka,saboda tasan girman soyayya da qaunar dake tsakanin 'yan uwa me girma ce......itace babbar shaida ta farko akan hakan akan kanta ma. "Duka wannan yabon amna......anya baki fiya son kanki da yawa ba kuwa da wannan birkitaccen hamman naki?" . Murmushi amnan ta saki itama,har qasan ranta taji dadin yadda sabreen ta karba maganganunta,amma har ga Allah tana son matar hammanta ta zama dream wife nashi kaman yadda dukkaninsu suka fahimta "Ki budewa hammana zuciyarki da kyau.....zaki sha mamaki adda.......inajin tukuicin zuwa dubai zakimin duk sati.....nayita zuwa ina ganin burj" Murmushi ta sakeyi kawai batace komai ba......abinda ya bawa amna daman sake cewa "Adda.......na baki kadan daga tarihin hammana dana samu tun kafin a haifeni.....wannan ne kadai zai zame miki jagora wajen sake fahimtar waye.....ya kuma.baki qwarin gwiwan tallafarsa" Zame hannuwanta tayi daga cikin na amna tana girgiza kai "Zaki bani.....amma ba yanzu ba amna.....kinga bana jin dadi sosai" Itama tayi maganar tana narkewa amna kaman yadda amnan keyi. Murmushi ta saki tana tuna warning nata da anni tayi akan ta kula da ita,kuma kada ta matsa mata da yawa,don haka sai tace "Mu barshi pending......har sai kin samu lafiya" Kai ta gyada tana lumshe ido kadan "Na gode" Har qasan zuciyarta tana jin dadin yadda amna ta fahimceta ta qyaleta. Sam bata son jin komai daya shafeshi,saboda tasan zasu fadi kirkinsa ne kawai bawai don haka yake ba,zasu fadi kirkinsa ne don haka yake nuna musu a fuska da mu'amalarsa da su,amma a waje kuwa.....babban azzalumi ne a wajenta mugu kuma. Maida dubanta tayi kan maamah "Ban taba kiran wani d'a namiji da adadi me yawa ba irin wannan sai d'anki......na masa kiran qarshe......inaso naga naki qoqarin" Abinda fareeda ta fada kenan ranta yana motsuwa hadi da qara baci akan lamarin. Bata taba daukan plan dinta bazaiyi wani aiki ba,kudade ta kashe masu nauyi don a buga ninkin adadin news paper din da aka saba bugawa a kowacce rana......sannan a fiddata tituna a kuma rabata kyauta ga kowa basai kowa ya siya news paper ba a ranar. Guri daya maamah ta zubawa idanu tana murza tafin hannunta,tana ji a jikinta lokaci yayi da zata koma wajen boka ta zube masa komai.......ta gaya masa buqatarta ta gaba,ta zube masa ruwan kudin da ko bai shirya ba dole yayi aikin nan......daga can wani loko na zuciyarta tana fargaba.......tana fargabar kalamansa na can watannin baya......kalamansa na qarshe a haduwarsu ta qarshe dashi. _taurarinta nada tsananin haske da wahalar cusa kai a cikinsu.......tabata abune da zai iya zuwa da nasara da kuma akasinta.........KINYI KUSKUREN ZABINTA......amma itace mahadin masarrafin b'arin nasa tauraron..........taurarinta sune abokan tafiyar nasa taurarin.........kusan komai nasu suna kamanceceniya da juna.......ITACE TA DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMU GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA_ Gumi ne taji yana tsatsatsafo mata......a take sai taji ai kaman ta fara shiga matsalar daya ambata mata. Sai yanzu kwanyarta ta fara aikin da a wancan lokacin bata yishi ba wato na fahimtar ma'anonin maganganunsa. Kenan aikin banza takeyi?,kenan ba wadda zata iya cika mata burinta akan faud sai sabreen din da take kokawar fitarwa a gidan?,wannan wanne AKASI NE da boka ke magana a kai wanda yace muddin ya gushe ita zata iya cika mata burinta......wanne akasi ne?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 66 66 _ko kisan manzan Allah S A W da kansa ya kasance yana neman tsari daga sharrin abinda ya aikata da wanda bai aikata ba? Yakan ce"Allahumma inni a'uzu bika min sharri ma amiltu wamin sharri ma lam a'amal"_ _shi daya kasance Allah ya gafarta masa duk wani abu da zaiyi da wanda ma yayi,ina gake?_ Dukka jikinta sai ya dauki wani irin dumi,tamkar ma ta manta da fareeda dake zaune gefanta,wani yalwataccen tashin hankali ya duro mata......cikin qasa da minti guda taji tana tsananin buqatar ganinsa. "Ke nake sauraro" Muryar fareeda ta yanke mata tunaninta. Idanu ta zubawa fareedan na wasu daqiqu kafin ta kammala tunani a kanta dukka cikin sakanni,murmushi ta sakar mata. "Mu da kikaga muna cimma nasara a rayuwarmu......ba da gaggawa muke tafi da komai ba......kibarmin komai a hannuna......indai kinga baki samu fu'ad ba.....to tabbas bani na haifeshi ba". Maganar ta faranta ran fareeda duk da ta xuba mata kokwanto me yawan gaske. Amma itama ta yarda da kanta......tasan kuma nata kalar takun,don haka ta miqe da nata murmushin tana ajiye mata bundle na dollars. "Ki qara da wannan......amma buqatata yazo ya ganni koda na minti talatinne kacal" Ta furta tana zuge zip din Jakarta,a qasan ranta kuma tana samun tabbacin da gaske ne fu'ad baya sakar mata zallar ruwan kudi.......abu na farko daya fara jefa mata shakka a zuciyarta akan matar. Matashin billionaire irin muhammad jadda......wanda tsananin yawan dukiya da arziqin daya mallaka a gefe guda quruciya da kyau su suka saka mata kwadayin mallakarsa......kudaden data bata din ya kamata ace a kullum a arziqinsa basufi kudin siyan wasu qananun abubuwa ba....amma ya zamana ita ke fara'a da samunsu?. A arziqin mahaifinta idan aka kasa arziqin fu'ad hamsin qwaya daya ne.....amma ace ita karan kanta tana da qarfin halin yin kyauta irin wannan?. TABBAS AKWAI MAGANA.....MAGANGANU MA,ta furta a sarari qasa qasa. Kudin kawai take juyawa a hannunta farinciki yana kamata. Ta samu kudin da zata tunkari aikinta,duk da tana baqincikin yadda kudin xasu salwanta,amma kuma idan ta tuna da ribanya ribarsu da zatayi sai taji koda ta salwantar da finsu ma ba komai bane. Saidai tana buqatar magana da yarinyar.......maganar da zata sake bata haske akan mataki na gaba da zata tabbatarwa boka shi take da buqata. Wa zara kira?zuwaira..... Kira daya biyu uku hudu har goma wayar zuwaira a kashe take. Tayi tsaki har batasan adadinsu ba,da waye zatayi magana ya hadata da yarinyar?. Tsam ta miqe data tuna daxun maganarsu ta qarshe zuwaira ta gaya mata yarinyar taje gidan ita da mamarta,saidai batasan ko tana can ko sun dawo ba. Ta qwalawa badawiyya kira "Ki tafi gidan hamza ki karbomin number wannan yarinyar" "To hajiya" Ta amsa mata a ladabce sannan ta juya tana ficewa ba tare data tsaya jiran komai ba. Hannunsa ya sanya saman labbansa kawai yana sauraren bayanin manager na gidan jarida na qarshe da yakeyi,wanda banbancinsa dana sauran qalilanne "Amma wallahi wallahi ranka ya dade kaman yadda 'yan uwana suka fada ne......wallahi bansan sadda aka buga labarin ba......ni dinma kamarsu gayyata na samu na taron 'yan jarida unexpected.......amma sanda na iso na samu jaridar ta fara fita hannun dealers na dakatar da saidata......waye zaiyi wasa da mutum kamar kai?,wanne gangancinne zai debi mutum......ko baya ga haka kana da mutunci da martabar da bai kamata mu bari a bata sunanka dana iyalinka ta wannan hanyar ba" Mutumin da aqalla ya kusa shekara sittin a duniya ya fada cikin matsanancin takaicin yadda duk karamci irin na jadda jaridarsa ta shiga sahun wadanda suka ci masa mutunci....duk da Allah ya taqaita an daqile fitar jaridar. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana sauke qafafunsa qasa,kanshi yana sake daukan zafi da lamarin. "Inason list na dukka mutanen dake da aiki a ranar a dakin buga labarai.......da full details na kowa" Ya fadi a ransa yana jin zaiyi aikin daya jima baiyi ba. "Sir.......ai mun kammala wannan.....muna jira ne kawai ka gama ji daga bakinsu......dukkanin dealers din mun karbi copy na newspapers din daga hannunsu,yanzu haka ba wanda keda sample nata.....Allah yasa munyi abun da sauri basukai ga rarrabawa qananun 'yan kasuwa ba,mun samu dukkanin jerin mutane hamsin da uku dake da aiki ranar a gidajen jaridu ukun......saidai mun rasa mutane uku a ciki,mutum daya daga gidan kowacce jarida......abinda ya qarfafa zarginmu akan suke da hannu.......na tura ma'aikata don binciken inda suke,kuma ina saka ran koda wanne lokaci zasu bani information,amma sauran mun tabbatar basu da masaniya akan komai" Wani abune daya tsaya masa tun jiya ya dinga sulalewa yana narke masa,ya gyada kai yana jin sassaucin dunqulallen abun daya tare masa wuya. Kafin yayi magana aka nemi izinin shigowa dakin. Ma'aikacin ya duba ya kuma bada izinin shigowa. Salute nasa sukayi mutum biyun da suka shigo,suka kuma miqa masa wani takardu. "Auwal sadi.....nura mahadi......labaran isyaku.....gaba dayansu mun samu tabbacin sun fita daga qasar nan kusan awanni biyu da suka shude,saidai kowannensu mun samu tabbacin qasar daya sauka.....auwal ya sauka a uk.......nura South Korea......shi kuma labaran ya sauka a china". "South korea.....UK.....china" Fu'ad ya furta sunayen a fili yana irgawa da yatsunsa,sai ya fesar da iska a bakinsa yana maida dubansa kan CP. "Well done sir......i really appreciate your effort,thank you for your hard work.......a sallamesu inason muyi magana privately" "Okay sir" Ya amsa masa cikin girmamawa. Cikin qasa da mintuna ya sallami kowa,ya kuma riski fu'ad din cikin motarsa qirar Mercedes sprinter. Duk yadda yaso mazewa da ganin alatun dake cikin motar tamkar kana cikin wani hamshaqin parlor din bawai mota ba amma ya gaza,sai daya daga kanshi ya kalli saman roofing din da yafi kama da lafiyayyen roofing din dakin sanda fu'ad ke qara hasken cikin motar daga galaxy blue stars zuwa brighter light. "Ina expecting tafiya nan da kwanaki uku......inason kayi gaba da kula da komai har zuwa sanda zan dawo......saidai banason binciken ya dakata......zanyi qoqarin ganin an kawosu daga dukka qasashen da suka tsallaka din don su fadi wanda ya basu contract din......wadancan mutum biyun kuma,ko tambayarsu bana fata kuyi.....ajiya na baku......irin ajiyar nan ta ma'anan ajiya" Yakai qarshen maganar yana tura cheque na kudi daya rubuta masa masu yawan gaske. Kai ya girgiza "Nop sir.....bazan amshi komai ba,aikina ne nakeyi kuma dole mutum irinka a masa aikin daya dace saboda alfanunsa ga al'umma". Wani abu dake gefansa ya dannan wata qaramar ma'ajiya ta fito,ya jefa cheque din yana cewa "Ba bribing naka nakeyi ba.......wannan din kyauta ne na baka,na jima da sanin wanene kai......inda baka cancanata ba ko qwandalata ba zata shiga hannunka ba.....kana daya daga cikin mutane masu aiki tuquru da qoqarin kamanta gaskiya duk da yadda qasarmu ta lalace.....so you deserve it,xan baka koda bakamin aikin komai ba" "Thank you sir.....thank you so much" S.nuhu ya fada yana jin dadin gwaggwabar kyautar da me jadda din ya bashi. Tunda wuri taqi zaman parlor din don batason ma ya dawo shi ya gansu ko ita ta ganshi,ta zame tayi zamanta a daki dole amna ma ta biyo ta can. Tana saman sofa din dake gefe daya a dakin,amna na zaune saman tattausan carpet din tana assignment. Idanunta kan takardun tana jin sha'awar amna din,tana jin inama ace itace ta samu dama irinta amna?,inama ace ta samu daman zuzzurfan karatu kaman amna?,wadda gata ya sanya tace bazatayi karatu wata qasar ba tsabar samun dama. Maida bangon littafin tayi tana duban sabreen cikin murmushi "Done......sai yanzu hankalina ya kwanta...lecturer dinnan mugu ne adda.....any mistake game over" Murmushi ta tayata dashi,ta jawo jakarta tana qoqarin maida litattafan "Adda......kin taba jin labarin labarin uwar data watsar da yaranta tun suna qananu ba tare data damu da waye zai kula dasu ba?,waye zai zama gatansu?" Takai qarshen maganar tana zuba idonta akan fuskar sabreen. Maganar sai tayi ma sabreen wani iri,a hankali ta girgiza kanta "Aah amna" "Kin taba jin labari,bayan wasu shekaru ta dawo garesu,amma kinsan me yasanya ta dawo garesu?" Kai sabreen ta sake girgizawa "Kudi......arziqi da rufin asirin da suka samu tazo ci,ba yadda suka rayu bane damuwarta......ba lafiyarsu ko akasinta ba". Idanu sabreen ta zubawa amna tana jin labarin ya kasa kama hankalinta,tsahon wasu mintina ba wanda yace da kowa komai,har sai da sabreen ta fara magana "Wanne irin cukurkudadden labari ne wannan amna?,a ina kika jiyoshi." Qaramar dariya amna ta saki tana janye jakarta gefe "Labarin mijinki kenan.....hamma na....." Bata qarasa ba shigowar saqo wayarta ya katse sauran maganar dake bakinta. Wani irin shuru sabreen tayi lokacin da hankalin amna yayi kan wayarta "Maamah?,mariya?....." Abinda kawai sabreen ke iya juyawa cikin ranta kenan "Bai rayu da ita ba?......batasan komai nasu ba?......batasan wahalarsu ba?,dukiyarsu tasa ta dawo??,dukiya???" Tarin tambayoyin da suka jujjuyawa cikin kwanyarta kenan. Maganganun amna gaba daya sai suka kasance mata kamar ta jefeta da wata cukurkudaddiyar sarqa,ta kasa hada daya da daya ya bata biyu. "Unbleavable!......oh my god!" Amna ta furta da wani irin qaraji,abinda ya yanke zaren tunanin sabreen kenan,ko kafin ta farga har amna ta fado jikinta ta cukuikuyeta "From nigeria to Maldives........wedding bells adda.......wedding bells" Ta fada tana dariyar dake cakude da farinciki zalla a muryarta. Qoqarin dagata sabreen takeyi cikin murmushi da mamakin abinda ya sanyata tsananin farinciki irin haka "Zaki karyani auta" Ta fada a dan shagwabe tana riqe amna din. Da sauri ta dagata tana fadin "Am sorry adda.....wani irin mamaki uncle BB ya bani......yayi surprising dina irin wanda ya jima baimin ba......adda hutunmu na wannan shekarar zai fara daga Maldives......kinsan mafarkaina akan wajen kuwa?,kowanne year idan anzo zaben wanne qasa za'a je idan na kawo sai BB da saddiq sun kushemin.......yaa musaddiq kawai ke goyon baya na" Ta qarasa maganar muryarta a narke,da alama tana jin haushin yadda abun yake kasancewa. Dan murmushi sabreen ta saki,don ita inda take maganar ma batasan ina bane ballantana tasan muhimmancin da yake dashi ba da za'a dokanta aje. "Your dream have come true" "Really adda.......adda wannan shine tafiyan da zatafimin kowacce dadi da alama......ina da sister like you nima wannan karan.......ha saddiq ya daina yimin gori idan za'a fita......i don't know yadda zan miki bayanin Maldives......but gani ya kori ji" Dan qaramin murmushi ta aje mata kawai don ita bataga wani abun doki ba a nan. "Labari na biyu adda.....muna da biki,borno zatayi kira......bikin BB farouq date din yayi daidai da dawowarmu da sati biyu kacal". "Ma sha Allah.....Allah ya sanya alkhairi" "Wannan qarshen shekaran bame sauqi bace adda......can't wait......bari na bawa besty labari" Ta fadi tana laluben number wayar aminiyarta guda daya da take da ita. "Adda......anya ba honeymoon BB farouq ya hada muku keda hamma ba?" Amna ta dakata daga qoqarin kiran besty din nata da take tana duban sabreen. Bata jira ma sabreen ta bata amsa ba ta saki dan qaramin ihu tana tsalle gefe "It makes sense👌.....that's my big bro farouq" Amna ta fada tana dariya nishadi kaman zai kasheta. Baki kawai sabreen ta kama tana kallon amna "Amna......nace miki binku zanyi?". Tana dariya ta bata amsa " It's for the whole family adda........kowa ma yana tafiya hutu a wannan lokacin,indai kai under jadda family kake......hatta ma'aikatan dake aiki cikin gida lokacin hutunsu ne.....kawai dai,nayi mamakin rage date din da aka saba tafiyan" Ta fada tana duba wayarta. Rasa abinda sabreen zata fada tayi,maganan gaskiya ita sam bata shirya zuwa ko ina dasu ba,don bata jin tana cikin family dinsu,hasalima tazara take son bayarwa tsakaninsu. Duk sanda amna ke waya da qawarta ita tayi nisa wajen juya maganganun amnan. Wani irin mamaki ke tsarga mata,wai dama haka matar take tun usul?,ta yaya zata samu gaskiyan abinda amna ta gaya mata?,tun tale tale gurbataccen hali gareta?,indai haka ne mene yaran sukayi me muni da zata cutar dasu?. Kwanyarta ta sake harbawa,da qarfi da yaji ta soma qoqarin hada daya da biyu ko zata bata daidai *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 67 _Manzan Allah S A W yace "idan dayanku zaiyi fada/zai daki dan uwansa,to ya guji fuska/kada ya mari fuskarsa_ 🧏🏽 _sai a kiyaye,mari ko dukan fuska haramunne a musulunci_ "Biri yayi kama da mutum,tsananin qaunarta da duniya da kuma dukiya,shine silar qoqarin mallakar d'anta ta qarfi da yaji?,wannan shine daliinta?". Numfashi ta fitar me nauyi tana saka hannuwanta saman fuskarta " Adda......maamah keson magana dake" Amna da sunan maamah din ya fito ta true call din ya gaya mata wace ta fada kai tsaye,duk da bata da tabbacin da sabreen takeson magana. Hannu kawai ta bawa amna,tana maida wayar kunnenta. "Har yanzu kina kan bakanki?,kinci gaba da lamuntar jefa rayuwarki cikin hatsari maimakon tseratar da rayuwar taki?,a naki tsammanin kin tsira kin tseratar da yan uwanki?" "Idan kura tana maganin zawo ta yiwa kanta mana?". Dif maamah tayi,batayi gaggawar amsa mata ba,don maganar ta jefeta da wani qudundunanniyar ma'ana. "Kece kike sake tafka kuskure akan kuskure......kuma kwanaki dukka wani sirrinki yana qarewa.......komai yana dab da bakaduwa tamkar yadda iska ke diban lallausan gari tana watsashi cikin mutane........ashe ba kaina kika fara nuna rashin sanin darajar halittar D'A ba......ashe baiwa ce sanin darajar haihuwa a zuciyar iyaye......d'anki bashi da muhalli ko daya a zuciyata ko rayuwata,.....kaman yadda banda sha'awar zaman aure dashi......saidai fita a gidansa da rayuwarsa duka sai sanda naga dama... Kinsan yaushe nake nufi?" Bummm zuciyar maamah ta buga tun bataji qarshen zancen ba "Zan fita ne a sanda na gama karanta masa ainihin WACCE KALAR UWA yake da ita......ba don ina sonsa ba......sai don alkhairi guda daya tak da yayimin........ya karbo 'yan uwana daga hannunki ya kawominsu......abinda yayi silar takawarsu tudun muntsira......ya sanyasu hayewa duk wasu qananun qullinki.....zan saka masa da iya wannan,don bashi da wata nagarta ko guda daya da zata sanya sabreen sha'awar kasancewa dashi......ki riqe wannan......ki rubuta ki ajiye......sabreen ce zata zame miki silar BANKADA!" Tana kaiwa nan saita kashe wayar ta azata saman cinyarta tana ci gaba da lullube fuskarta "Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" Ta dinga maimaitawa,tsanar uwa da danta duka suna turereniya cikin zuciyarta. Ko da amna ta dawo abinci kawai taci ta fara list na abubuwan da zasu buqata lokacin tafiyar da abinda zasuje dashi. Ba wani abu data tofawa amna sai idanu da take binta dashi. Ba qaramin jarumta tayi ba da take iya binta da murmushi ba,gaba daya ganin abun take a wani abu maras yuwuwa,ita ba ahalinsu bace,bata kuma tunanin zata zama ahalin nasu.....hasalima gaba daya lissafinta yafi karkata ga qarawarta gaba kafin sukai ga dawowa daga yawon qasashe hudun da suka tsara zasuyi,kowacce qasa zaman sati guda zasuyi,ciki kuwa harda umra data zame musu dole duk lokaci irin wannan. Dukka maganganun sabreen sukayi mata tsaye a rai,a daren ranar duk inda ta juya furucinta ne ke mata kai kawo a rai. Tanaso jin rauni game da yarinyar yana sauko mata,amma wannan dakakkiyar zuciyar da shedaninta dake gefe suna gaya mata _karamar halitta irin ta mace......yarinya qarama me qananun shekaru bai kamata taga rauninki ba.....bai kamata ace itace taci galaba samanki ba_. Abu daya ta kasa samun aminci akan yarinyar shine 'Yiwuwar aikata komai". Ko ba'a fada ba ta sani......sabreen zata iya aikata komai,tana da taurin zuciya da qwarin zuciya dama zarrar da zata iya yin komai.....wannan zarrar tata ita taja hankalinta ta zabota zuwa ga aikin da bata taba kawo komai zai warware da wata irin faduwa da rashin nasara haka ba. Tunda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba. Ta jira har sanda gari yasha,sannan tayi wanka,ta shirya kaman kullum da qasaitattar shigar nan tata dake qara mata jin izza da jin takai inda ya kamata ace takai din,saidai bata qarasa gabar da take da muradin qarasawa ba. Wayarta ta fitar ta kira driver dinta,ya tabbatar mata yanzu haka yana cikin mota yana jiranta,kai tsaye ta dauki jakarta tana yafa mayafinta ta fice. Dab da zata bar falon taji laila na kiranta "Maamah" Tsaiwa tayi tana jan tsaki,don bata shirya komai ya dakatar da ita ba. Qarasowa lailan tayi,ta kuma zube a gaban maamah din. Sam tun daga waccan ranar bata iya tsaiwa gaban maamah.....magana ce ko gaisuwa zubewa takeyi a gabanta tamkar bawa da uban gidansa. "Ina fatan ba wani abu nayi miki ba maamah?" Ta tambaya da tsananin tsoron kada ranta ya baci "Naga zaki fita baki tasoni ko kisa an gayamin ba" . Wani qaramin tsaki maamah din ta saki,wannan abun ya fara isarta,ba wani motsi da zatayi sai yarinyar ta buwayeta. Irin wannan abun da akan fu'ad ya fada tabbas zata iya cewa tafi kowanne mutum sa'ar zuwa duniya. Ko yaya taga fuskarta ta canza takanyi kaman zata fashe da kuka,komai kuma har abinda bai dace ta sani ba game da lailan lailan saita gaya mata "Unguwa zanje,kafin na dawo ki gyara falo din,ki hada da bedroom din,duk abinda kika gani ki ajiyeminshi inda kika ganshi,kada kibar kowa ya hauramin sama,akwai underwears dina dana cire ki wankesu ki shanya a backyard ki jira su bushe ki dawo min dasu ciki" "In sha Allah an gama,Allah ya dawo dake lafiya" "Amin" Ta amsa tana yin gaba. Sau tari idan taso bautar da laila sama da haka sai wata zuciyar ta gaya mata lailan kome tayi bisa jagorancin mahaifiyarta ne,wannan ya sanya take sassauta mata akan abubuwa da dama. Tafiyar awa daya da rabi cif suka fara gangarawa mummunan jejin,sai da suka sake kashe wata awar sannan suka isa. Daga nesa ta sanya driver din ya sauketa,sannan ta tattare zanin tsadaddar atamfar jikinta ta fara tsallake qayoyi da busassun tsirrai tana wucewa ciki. Gurine da zaiyi wahala kaje ka taras d wani duk da tarin al'ummar dake zuwa wajen a kulli yaumin neman duniya,tamkar sun manta da wata rana da zaa shimfidesu babu wannan ruhin daya zama masarrafi na motsinsu da kai kawonsu izuwa gurare daban daban. Ba wata kafa a jikinta da bata fitar da gumi sanda take zaune a gabansa tana jiran bayanansa na qarshe. Da qyar ta samu ya ganta.....don sharadinsa ne baya aiki biyu akan matsala guda daya. "ZANGON NASARAKI guda daya ya rage miki......BANKADA zata sameki.....tonon asirinki zai fara daga yanzu zuwa kowanne lokaci.....zangon nasararki zai iya narkewa ya dulmiya sanadin hakan!!!" Ya furta da wata irin murya maras dadin amo. Dukkanin 'ya'yan hanjinta taji sun tattara sun cure guri daya,idanunta suka qara girma saboda wani sabon kalar tashin hankali da bata taba jin makamancinsa ba "Kanaso kacemin itace zatayi nasara a kaina?!!!" "Me muka gaya miki wancan karon?!!!!......" Wasu muryoyi da tafi tsammanin sun kusa guda goma sukayi amsa kuwa a wajen kafin bokan ya karba "KINYI GANGANCIN ZABOTA......SAIDAI TAURARONSA DA NATA TAURARIN KADAI SUKA DACE......ITACE KADAI MAHADIN AIKINKI........zabi biyu gareki.....ko ki kasheta duk wani burinki ya dulmiya ya koma mafarki......ko ki barta ta rayu kina kallonta kuma naki burin shima yana raye amma babu wata dama ko hanyar cikashi.....zan miki wani aiki guda daya......amma daga kansa!....ina me gargadinki kada ki kuskura ki sake dawomin akan matsalar data shafesu.......aiki yayi kyau ko akasin haka......". "Na gode da wannan dama daka bani.....na tare dakai su dafa maka" Ta fada jikinta yana rawa da jin qarin dama guda daya,abinda a tarihinsa bai taba ba maimaicen aiki. "Zaayiwa na tare dani da ma'aikata yanka......zasusha jini wadatacce da zasuyi aikin jinkirtawar tonuwar asirinki........yayin da zangon nasararki ya kama......nan da kwanaki goma sha hudu zuwa ashirin da daya......kiyi duk abinda zakiyi wajen ganin muradinki ya cika......ke zaki yiwa kanki wannan aikin.....mun miki alfarmar samun jinkiri kadai.....amma ki sani tabbas RANAR HASARA DA RANAR TABEWA TANA NAN ZUWA.......DOLE KI FUSKANCETA DA DUKKANIN ZUNUBANKI.........KIYI NESA NESA DA MATSANTAWA TAURARINTA........BA NASARA TA KUSA KO TA NESA......NATA ZANGON NASARAR YANA DAB DA FADOWA HANNUNTA". Duka bayanansa bai wani dameta ba......zangon nasararta da damarta guda daya daya tabbatar mata ita tafi komai yi mata dadi. Kudade masu kaurin da suka haura million hudu ta zube masa,sannan ta fita da baya da takalmanta a hannu ranta fes,tana gayawa kanta dogon zangon tunani ya zame mata dole don samun kyakkyawar mafita. Tabbas ta kowacce fuska tana da buqatar barin sabreen gidan koda itace murfin nasararta.......gwara tasan yadda zatayi ta maye fareeda da ita a madadin cikar burinta. ★Hadith yana daya daga cikin karatuttukan da suke mata dadi qwarai. Sau tari idan suna karatunsa da rumaisa yafi kowanne littafi daukan musu lokaci. Ko a yanzun da take zaune tana bita amna na zaune a gefanta,sunata hira da anni wanda rabinta kusan na tafiyarsu ce jibi,lokaci lokaci kuma da tsare tsaren abinda zaa gudanar da bikin farouq. "Anni....gata karatu take,ki mata magana don Allah" Ta fada a narke. Duk da sabreen batasan akan me amna ke magana ba,amma sai data daga kanta da sauri. Tana balain jin kwarjinin matar da ganin kimarta,daidai nan amnan ta miqo mata wayar tana danne dariyarta hadi da hade hannun alamun am sorry. Da idanu ta nuna mata zan kamaki sannna ta karbi wayar tana sakawa a kunne "Barka da dare d'iyata.....ina fatan dai bata miki shirme?" "Barka da dare anni....." Ta fada tana murmushi "Ya jikin naki?...ina fata dai kinji sauqi?" "Alhmdlh na warware....anni na gode" "Ba godiya ai tsakanin uwa da d'iyarta......nace ba,nasan halin yarona sarai,duk sanda tafiya irin haka ta kama saidai a tayashi shirya kayanshi shi kansa,nace idan akwai wani abu da kuke buqata na tafiyar kiyi magana....karki daukeni suruka ameenatu ni mamarki ce,ki rubuta sai a kawo,idan kuma ta amnan zakiyi to saiku fita tare goben,saiki masa magana" Kunya ta sake kamata,bangare daya kuma tana jin wani iri. Ta aza an soke zancan tafiya da ita ne kwata kwata,don tun randa akayi maganar da amnan tace BB farouq yace ta bada details dinta da sauransu bata sakejin komai akai ba. "In sha Allah anni......Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" "Ameen ameen,a baya magaji ne yake hada masa necessary abubuwan da zai tafiyar dasu.....ina fata yanzun zaki maye gurbin hakan?" "In sha Allah" Ta amsawa annin tana jin wani qaton nauyi ta aza mata akai,daga nan ta miqawa amna wayar ta maida kanta kan karatun. Amma kuma sai karatun ya gagareta,saboda batasan yadda zata cika maganar anni ba. Batason haduwa dashi kwata kwata,hakanan idan batayi yadda annin tace ba zai zama kaman rainuwa,kuma amna da akayi a gabanta ba zataji dadi ba. Dabara ce ta fado mata,ta rufe littafin tana duban amna data gama wayar. "Kina da number magaji din?" "Eh ina da" Amna ta amsa mata "Faka faka kiramin shi" Ta furta tana gyara daurin dankwalinta. Sosai abun ya yiwa amna dadi,ta kira magajin ta hadata dashi. "So nake nasan da meye da meye ake hadama boss idan zaiyi tafiya?". Tayi maganar tana miqawa amna hannu alamun ta bata takarda da abun rubutu. A ladabce ya dinga zayyano mata tana rubutawa,har ta gama tsaf tayi masa godiya ta yanke kiran,ta miqawa amna bironta ita kuma ta miqe da takardar a hannunta,amna ta bita da kallo tana murmushi. Tasan abinda take shirin yi,zataje ta hada masa jaka tana tunanin baya nan kafin ya dawo,saidai tun daxun taga shigowarsa,kawai bata gaya mata bane tunda ta lura ba hawa saman take ba,itadai adduarta daya Allah yasa adda sabreen din bata cikin sahun shashashun matan nan da basu iya baiwa miji kulawa,duk da itadai a hakanta a halittarta bataga alamun hakan ba. Duk da tana da yaqinin baya nan,amma duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,kaman yadda numfashinta ke fita da nauyi. Bude smart door dinsa bame wahala bane a wajenta,saboda tuntuni ya sanyata cikin sahun masu shiga kai tsaye. Ko ina fes kaman yadda ta saba,yana fita da safe take shiga,tasan lokacin fitarsa,zai kuma wahala ya wuce wannan time din be fita ba,zata shiga ta kintsa komai. Duk da baya barin komai sai dan goge goge da qananun datti,bai taba barin underwears dinsa ba koda kuwa singlet nashi bata taba gani ba,abinda ma ya sanya mata qaramar nutsuwa kenan. Bedroom dinsa ta wuce,tayi kuma amfani da details din da magaji ya bata ta dinga fiddo da komai,sai data hada shi tsaf sannan ta rufe briefcase da luggage din ta ajiyesu a gurbin da ta tabbatar zai wahala ya kasa ganinsa. Yadda batayi zaton ganinsa ba haka shima baiyi wannan zaton ba. Batasan ya shigo saman ba kwata kwata. Ta zare idanunta daga cikin nasa idanun da yau take ganin kamar sun rusuna sunyi kuma laushi,can qasan ranta tana mamakin yadda ya balbalawa kansa A.c tayi qau a falon,abinda iya saninta dashi ba sabonshi bace. Idan kaga ya kunnata ma to tabbas ranan ana zafi,ko kuma bai samu irin fresh air din da yakeso ba. Kanta ta dauke sosai ta fara takawa zata wuceshi,yau daya sai taji tana jin shakkar giftashi,koda kuma bata kalleshi ba tana jin kaman idanunsa a kanta suke. Allah ne kadai ya sauko da ita,don bibbiyu bibbiyu take hada stairs din tana saukowa,tana jin kamar zai biyota yayi jan masifar daya saba,tana kawowa bakin bedroom dinta ta saki numfashi tana danne qirjinta. Sai data bacewa ganinsa ya dauke kansa daga wajen yana maida hankalinsa kan wayar huda dake hannunsa wadda yakewa kallon wayarta. Tun ranar yake sake zurfafa bincike cikin wayar......amma kullum abinda zai gani a ciki taba masa rai yakeyi. Tarin massages na nuna zallar soyayya da kewa,zuciyarsa ba irin abinda bata raya masa yayi ba amma yana danneta d wani irin qarfi dashi kansa baisan yana da ita ba. Abu daya ke taka masa burki,cases din da zaiyi tafiya ya bari,amma ya tabbatar zuwa sanda zai dawo komai yayi settling......a lokacin zata kwashi kashinta a hannu,zaikaita ainihin kurkukun da itace asalin wadda ya tanadar mata. Qarar wayarsa ya janye hankalinsa daga wancan tunanin,ya dauka yana dubawa don kusan duka saqon da zai shigo masa me amfani ne. _ko a kusa ko a nesa duk inda zaka ina tare da kai,toshe kirana bawai yana nufin toshe soyayyarka daga zuciyata bane........ferree dinka ce_ ta saka sign na kiss da love daga qasa Matse wayar yayi a hannunsa,yanajin bai taba jin tsanar wani abu a duniya ba irin yarinyar......tabbas tace zataci gaba da bibiyarsa nan da sati daya zai nema mahaifinta yayi magana dashi. Y janye diyarsa ya siya mata girman da ita ta gaza siyawa kanta. ★A daren washegari zai shigo mata amna tayi kawai da wata irin luggage da itadai idan tace ta taba ganin akwatin daya mata kyau irin wannan tayi qarya. Komai da matafiyi zai buqata an kammala mata shi an damqa mata a hannu. Wayar amna ta karba tayi kiran titi bayan ta zuba numbers din titin data rubuta ta aje saboda gudun bacewa. Har yanzu tana mamakin yadda wayar huda ta sake bacewa a dakin,saidai zuciyarta tanata qarfafa mata zargin shine ya sake daukewa.......don tun randa wancan incident din ya faru bata sake ganinta ba. Magana sosai sukayi da titi din dasu huda,ta kira momma bahijja ma ta mata sallama,hankalinta ya kwanta sosai data samu yaqinin cewa kwana uku da tafiyarsu suma zasu isa mali,kunya tadan kamata sanda momma din ke tsokanarta honeymoon zasuje? "Saura satittika kadan ya rage nima na biyo bayansu zuwa tushen mahaifiyata momma" Ta furta a ranta. Sosai taji zuciyarta sakayau,hankalinta ya sake kwanciya,amma saita dinga jinta cikin wani kadaici,tana jin kamar ita daya tayi saura a Nigeria,saidai kuma tana jin sassauci idan ta tuna itadinma kwanaki kadan zata iskesu su sake shimfida sabuwar rayuwa me inganci tare. _hmmmm,nace ko dama zata bada daman hakan?_ *_MALDIVES........_* *KOMAI NISAN JIFA*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 0818725586268 *_Na muku post saboda jiran kwana biyu da kukayi,don Allah banason complain,dole zaa zo inda kuketa zakwadin🧏🏽🤦🏽‍♀️🙄_ _Allah don isar mulkinka,don buwayarka,don girman soyayyar da take tsakaninka da muhammadurrasulillahi,dukkaninmu bayinka ne,amma akwai bayinka dake zaluntarmu suna fitar mana da pages,Allah kafi kowa sanin yadda muke wahala,mun killace haqqinmu bamu tilastawa kowa ba akan yazo inda yake,amma suna biyomu suna zaluntarmu YA ARHAMAR RAHIMEEN KAFI KOWA SANIN BAMU ZALUNCESU BA....YA ALLAH KO WACECE IDAN BATA DAINA BA ALLAH MUN GATA NAN,MUN KAWO QARARTA KOTUNKA ME ADALCI,YA ALLAH....YADDA TAKE TARWATSA MANA KASUWANCI UBANGIJIN SAMMAI DA QASSAI KA TARWATSA NATA KASUWANCIN,ASARAR DA TAKE JA MANA ALLAH KA NINNINKA MATA WANNAN ASARAR AKAN NATA KASUWANCIN DON ISAR MUHAMMADUR RASULILLAHI A FADARKA AMEEN_ *_REPUBLIC OF MALDIVES_* *MALÉ* *Velana international airport malé_* Misalin qarfe hudu agogon Maldives wanda yayi daidai da qarfe takwas na dare agogon Nigeria private jet din mallakin Muhammad fu'ad jadda wanda ke dauke da sunan JADDA WINGS ya sauka a babban filin tashi da saukan jiragen sama na velana international airport dake babban birnin Maldives wato malé. Daidai sanda jirgin ya kammala tsaiwa gaba daya sabreen ta sauke numfashi a hankali tana lumshe idanunta gami da budesu kusan lokaci daya. Wani abune da take ganinsa tamkar cikin mafarkanta,gata cikin qasar da koda sunanta sai lokuta d'aid'aiku ta taba jinta ballantana mafarkinta yakai ga zuwa qasar. Tun daga kano zuwa lagos da suka sauka na wasu mintuna,kafin daga bisani jirginsu ya taso zuwa Maldives tasan tabbas duniya cike take da yalwa da fadi. Abu guda daya daya dinga bata sha'awa.....wanda ita kanta batasan abun na burgeta ba,sai data samu kanta tana fatan "Allah yasa nan gaba kadan rayuwarmu ta kasance kaman haka....ni huda nadra haneefa". Bawai kalan arziqin jadda family bane abinda yaja hankalinta da gasken gaske ba....a'ah.....kalar qaunar juna.....bawa juna kulawa da kuma soyayyan juna da take gani a idanunsu irin na zallar 'yan uwantaka. A tsakaninsu zata iya cewa ta zama 'yar kallo kome daukan rahoto,duk kuwa da cewa sunata qoqarin jefota cikin hirarrakinsu da kowacce magana data shafesu. Sau tari saidai ta murmusa kawai,tana karance da halayen kusan kowa a cikinsu. Farouq nada tsananin kirki......yana da nuna kulawa da soyayya da 'yan uwansa,yana da wasa da dariya da 'yan uwansa.....amma mugun muskili ne kuma hutsu idan baiga dama ba. Saddiq yana da zuciya,yana da saurin fushi amma kuma yana da saurin saukowa,yana da kula da damuwa qwarai da gaske da al'amarin 'yan uwansa. Musaddiq dataji sunata waya dashi kafin tashin jirginsu,wanda a yanzu haka shi yayi landing ma a Maldives din,bazatace ga hali ko dabi'arsa ba,illa abu guda daya data lura. Shima me yawan nuna kulawa ga 'yan uwansa ne da damuwa dasu. Sai oga boss muhammad fu'ad jadda.........shi kadai halinsa yasha banban ta kowacce fuska da 'yan uwansa......ta fuska daya sukayi musharakar halaye,wato ta fannin qauna ga 'yan uwansa......wata irin qauna da a fuska ba zaka ganta ba,hakanan a fili ba zakaga wani alamun damuwa ko kulawa da lamarin kowa bama tattare dashi,saidai kuma yana ankare da motsin kowa da kai kawonsu. Wani irin bahagon miskili da koda magana zaiyi saika rantse ya lissafe take,bayason lafuzansa kuma su qare,kaman tattalinsu yake,baya magana ya maimaita maka,kaman yadda bai fiya nuna damuwa ko zafafawa akan al'amura ba. Zaka dauka bai damu da komai ba,baya kuma kula da komai,saidai kaifin lurarsa akan komai tasha banban data kowa. Yana da wani irin fahimtar komai da kowanne motsi dake kewaye dashi,yana da kaifin lissafi,dogon tsinkaye da nazari kafin yayi magana. Ba'a kan komai kakeji yayi magana ba,ba kowanne abu bane zai kalla yace wani abu ba koda yana sane da wannan abun. Dukkaninsu sunyi tarayya akan abu guda wato son anni......kowa a cikinsu wani unique love yake nunawa annin da qauna me tsananin yawa......takan shiga lissafi me zurfi idan maamah ta fado ranta,amma kuma idan ta tara da 'yan maganganun da amna ta fara yi mata,sai taga lallai komai yana da nasaba da wannan. Ko yanzun ma da jirgin ya tsaya,saddiq nata fiddo musu luggage dinsu daga overhead compartment jordan na sauka dasu,shi kam sai a sannan ya rufe system dinsa da batasan abinda yakeyi ba a ciki tunda jirgi ya daga. Tun zamansu daga lagos har kawo yanzu tana gabanshi. Tana jin farouq daya gaji da yadda ya bata hankalinsa yace "Yallabai hutu fa zamu tafi,tun yanzu ka fara bata tsarin hutun?,ya kamata komai a ajjiyeshi a side ko?". Kai ya girgiza,kaman bazaiyi magana ba,sai daga baya ya daga idanunsa ya zubewa farouq dinsu "Ba zaka gane ba.......koda na tafi hutu bazai yiwu har ta internet na tafi offline ba" Baki farouq ya tabe yana jinjina kansa,can qasan zuciyarsa shi yasan me yake tsarawa. Jordan ne ya qarasa ya tattare masa dukka tarkacensa,yayin da shi kuma ya miqe yana zube hannuwansa cikin aljihun 3pices suit din jikinsa yana takawa gaban anni. Duqawa gabanta yayi kadan yana gyara mata zaman takalmanta da take qoqarin sakawa. "Ina fatan zaman jirgi bai saka ciwon qafarki ya tashi ba?" Murmushi ta saki,tana fatan yadda yake da tsananin kulawa a kanta taga yana yin sama da haka akan matarsa. "Alhmdlh......last checkup din da mukaje ai sun bada dokoki,kuma na kiyaye alhmdlh......je ka duba matarka" Ta fadi tana miqewa hadi da ambaton bismillah. A kunnen sabreen anni ta furta hakan,numfashinta yadan tsaya na wucin gadi,ta danyo rolling idanunta tana miqewa. Batason kowanne abu da zai hadata dashi ballantana ya gasa mata magana. Maganan daya gaya mata kafin tasowarsu daga lagos kadai ya isheta basai ya qara mata da wani ba. Cikin ma'aikatan airport dinne,wani a cikinsu yaketa haba haba dasu ita da amna. Itakam bata kawo komai cikin ranta ba,don bata ma sake masa ba,amna ce kawai ke dan amsa tambayoyinsa,har zuwa sanda zasu wuce sai yace "You look so familiar madam....." Ya fada yana dubanta da murmushi. A dan mamakance ta waiwaya tana dubansa,kafin kuma tace komai ya sake fadin. "A abuja......hotel din....." "Stop mr man!" Dakakkiyar muryar fu'ad ta dakatar da mutumin cikin kaduwar hanji. Sam baiga isowarsa wajen ba,mutumin tun dazu yake masa kwarjini. Duqar da kansa yayi da sauri cikin rawar jiki yana cewa "Sorry sir". Bai ko kulashi ba ya kalli amna,da idanu yayi mata sign na ta wuce,sai tayi qasa da kanta tana yin gaba. Ganin amna ta wuce itama saita taka zata bita,bai hanata ba,yabi bayanta shima,saidai ya gasa mata maganar da sai da qwalla ta diga ta samu sassauci "Shi abun qwarai da mummuna tabo gareshi......mu'amala da tarin mazaje ba shine mutuntaka ba ta d'iya mace.... Mutuncinta namiji daya da zai amsa sunan mijinta,bariki bata da riba kota rana daya ce kuwa......duk wanda zai hada zuri'a da macen bariki saiya shirya......ba qaramin cutarwa bace ga 'ya'yan da zasu haifa idan aka ture nashi matsalan na qashin kansa". "Macen bariki......mu'amala da tarin mazaje" Wadannan kalmomin su sukafi komai tsaye mata a rai. Wanne irin mummunan kallo yakeyi mata ne wai har haka?,wanne mummunan fassara yake mata ne?. Tana ji ta soma gajiya,ta fara kaiwa iyaka,daga yanzu zuwa kowanne lokaci zata iya fashe masa.......ba zata iya ci gaba da dauka ko jurar irin wadannan tuhume tuhumen da maganganunsa da basu da tushe ba,tana jin zuciyarta da idanunta na mata wani irin suya,bata samu sassauci ba sai bayan da jirginsu ya doshi Maldives......hirarrakin family din da uwa me goya marayu wato anni ita ta sama mata relief a zuciyarta,saidai tana jin ta wani irin sake tsanarsa,ta kuma sake tsanar hada komai dashi. Gabanta ya tako,abinda ya sanya amna gocewa da sauri tunda ita ke first seat da zummar yin gaba "Karki fita......ki jirata" Ya fadi da husky voice dinnan nasa data sake dakewa,tun daga tashinsu daga lagos din bayan wancan abun daya faru zuwa yanzu tana ankare da hamman nata. Sai dacin rai kawai yakeyi wanda shi kansa baisan yana yi ba,jifa jita take satar kallonsa,har a sannan kuma ta tabo sabreen "Adda........wai dama haka hamma yake da kishi?,daga cewa you look familiar?.....haka hamma yake sonki?" Ta fada tana murmushi kaman abun yana burgeta. Sau daya tak ta kalli fuskarsa sanda yake fama da system dinsa,saita maida idanunta ga window din jirgin tana duban yadda suke dai da daidai da gajimare. Abun yana burgeta,tunda shine karon farko data fara keta hazo......saidai can qasan ranta yana cunkushe da halayensa. "Ba kishi bane.....izza ce wulaqanci da kuma izgili.....har yanzu banga wani kyakkyawan halayensa guda daya ba......koma dai meye saura kwanaki kadan suka rage na barshi shi da halinsa dama tarin dukiyar dake sanyashi dagawa izgili da girman kan ma" Tayi dukka maganar a ranta,amma a fili murmushi kawai ta yiwa amna. Amnan bata damu ba taci gaba da dauko mata gulmarsa kadan kadan,tunda ta saba da halinta na wannan fannin. Ba komai sabreen din ke bude baki ta bada amsa ba a maganganu da dama. To a yanzun da yake tsaye a gabanta bata dubeshi,sam bata qaunar hada idanu dashi. "Ko meye zakiyi a yanzu ki dinga tunawa akwai igiyata a kanki......bazan kuma lamunci kowanne abu da zai zama tozarci ga igiyata ba......zan iya daukan kowanne mataki mara dadi muddin kikayi wani abu daya sabawa shari'a......ki kula,ki kula da kyau". Kasa jurewa tayi,haka siddan daga saukarsu a qasar,kowa ya sauka da walwala itama ta samu ta fara tattalin tata zai watsa mata ita. Fararen idanunta ta daga ta watsa masa wani.kallo tsakiyar idanu. Wani haske suka fitar sosai saboda fushin dake cikinsu,wani salon kallo da baiyi kama da harara ba,shi kuma ba kallon banza ba. Ta motsa siraran lips dinta zata ce wani abu,sau kuma taga hakan baida ma wani fa'ida......bata da sauran lokacin batawa,don haka ta soma qoqarin rab'eshi ta fice. Sosai taji an damqi hannunta da wani tsatsauran riqo,ta waiwayo da hanzari tana dubansa,ya damqeta ne ba tare da ya ko waiwayo ya kalleta ba,qeyarsa kawai take iya gani,da hannu daya ya jawota ya dawo da ita gabansa,ya sanyata a tsakanin idanunsa yana mata wani irin kallo da taji ya tsaye mata a sassan jikinta,ya kuma soma sauke rashin kunyar da taji tana taso mata "Duk sanda kika sake gangancin wuceni ina magana.....na rantse da Allah sai na gwada miki ina da banbancin da lusaran mazan barikinki marasa daraja......dole ki amsa min kowacce magana kaman yadda nakeso.....don banajin muryarki tafi tawa tsada ko daraja.....ko banza adadin mazan da sukaji muryarki baikai adadin matan da sukaji tawa ba......kinjini?!" Ya furta da dan tsauri idanunsa na kallon wani gurin daban sabanin cikin idanunta "Eh naji" Ta amsa a sanyaye kanta yana kallon qasa. Shigowar farouq ta gani daga bayansu,wanda ta tabbatar shi bai gani ba,sai ya sakar mata hannun yana juyawa gami da takawa a hankali yana ficewa a jirgin. Hawayen da take riqewa ne suka yiwa kansu da kansu hanya. Ta sanya tissue tana daukesu "Ya isa......ya isa" Take gayawa kanta da kanta. Tana cin alwashi a ranta ko ya bata takardarta.....ko bai bata ba,sauna sauka a nigeria zaman aurensu ya qare......ko ya sallameta ko bai sallameta ba wannan duka damuwarsa ce,alwashi ta ciwa kanta.....wannan karon babu abinda zai dakatar da ita......ba kuma wanda zai hanata. A hankali ta fara takawa itama tana nufar qofa da shimfidadden matakalar da aka jinginewa jirgin. A nutse take sauka tana qoqarin daidaita mode dinta gudun saka damuwa a zukatan amna da anni. Three pieces turkish gown ne a jikinta,wadda take hade da strips skirt da kuma blouse data zauna daidai jikinta,tayi kuma took in da ita kaman yadda tsarin kayan yake,sannan ta kawo doguwar gown din kayan me budadden gaba data sauka har qasa ta kuma bude sosai daga qasan. Qafafunta high hill ne masu madauri da suka dace da kalan rigan. Sosai kayan suka karbeta,baka ganin komai sai fuskarta,zaka rantse da Allah bata hada nasaba ta kusa ko ta nesa da nigeria ba. "Wallahi anni adda sabreen kyau takeyimin......komai nata me kyau ne.....duk kayan data saka sai naga kaman don ita aka yisu" Ta fadi maganan tana matsawa kunnen anni,saidai fuad dake tsaye daura dasu yaji abinda ta fada din. Haka kawai ya samu kansa da daga kan nasa,suka kuma yi masa jagora a kanta duk da yadda yake qoqarin hana hakan faruwa. A kasalance take tafiya saboda bacin rai,sai hakan ya sake zama kaman cikar adon tafiyartata. Idanunta suna lumshewa kadan gami da bude kansu duk a qoqarinta na hana zuciyarta karyewa,ta kuma hana idanunta zubda ruwan hawayen da takeji suna tattara kansu. Amna dake mata murmushi ta maidawa martanin murmushinta,abinda ya sanya pink lips dinta motsawa kadan. "Ya salam" Ya fada can qasan ransa saboda tsigar jikinsa da yaji ta zuba yarrrr.....tun daga tafin qafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Wanccan ranar ya tuna.......ranar daya sanya lips dinsa saman nata......shi.kadai yasan me yaji,shi kadai yasan yadda ya iya qwace kansa daga yanayin daya shiga......yayi imani a ranar inda ace shi din manemin mata ne,baisan adadin mata nawa zai nema ba a ranar.....inda shi mashayi ne,baisan adadin kwalba nawa zaisha ba......inda ace shi din asharari ne bayajin cikin kwana uku ma wata macen zata sauke masa abinda yaji a jikinsa a wannan lokacin. Bayajin zai iya ci gaba da tsaiwa a wajen bare ta fahimta ko farouq ya gano canzawarsa,don haka sai ya juya kawai yana takawa a nutse yana matsawa daga wajen gami da sake kame kansa da kyau gudun zubewar kima. Dukkaninsu motar da tazo tararsu ta dauke,mota ce me seat kusan hudu bayan wajen hutawa daga can baya. Shi da farouq suna seat guda,sabreen anni da amna suna set na qarshe. "A ina ka samar mana gida?" Fuad dake gyara agogon hannunsa ya tambayi farouq. Takardun hannunsa ya fara budewa daya bayan daya kafin yace yana tsaida idanunsa akan wata takarda guda daya. "RANGALI ISLAND RESORT......garden villa na masa mana gida.....baiyi tsada cancan ba,duk da Maldivian Rufiyaa mukayi cinikin,ahmad ne ya siya gidan ta hannun wani,da nayi converting kudin da naira sai naga basuyi yawa ba" . Kai kawai ya jinjina,farouq akwai iya aiki,musamman idan akazo batu na tafiya tourism. "Ina fatan yalwatacce ne,kasan mun sake qaruwa this time?". Idanu ya zuba masa,kaman yace masa waye ya qarun da sukayi yawan da zaa nema bangajejen gida?,amma sai yaga kulashi ma bata time da plan ne,don haka ya bishi da " Yes" Kawai farouq yace masa yana boye dariyan dake qasan ransa. Idanunta akan hanya sanda suke wuce lafiyayyun hanyoyin da suka sha banbam dana qasarmu nigeria. Ko daga iya nan ta tsaya ta tabbatar wata duniya ta daban ta shigo. Ta shigo wata duniya da tayi nisa qwarai da tata DUNIYAr data rayu cikinta. Qarfi da yaji takeson komawa 'yar qauye,ta sauke nannauyan ajiyar zuciya sanda motarsu ke shiga wani street me dauke da lafiyayyar hanya da wadatar tsirrai. daga gefe da gefan hanyoyin tana iya hangen ruwa can nesa dasu,wani irin ruwa dake bada blue colour,bata sani ba.....color dinshine haka ko kuma 'yar tazarar dake tsakaninsu take nuna mata haka. Daidai qofan wani madaidaicin kyakkyawan gida motar ta fara slow kafin ta samu wajen tsaiwa. Su suka fara fita suka jira fitowar anni,sannan ita da amna suka biyo bayanta. Tare suka jera da farouq har qofan gidan su kuma suna biye dasu,jordan da drivern motar suna biye dasu da luggage dinsu. Dab da zasu isa qofan gidan qofar ta bude da kanta. Farin matashi ne ya bayyana wanda duka duka shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas ba,daga gefansa musaddiq ne da suka jero tare,wanda kamanninsa da fuad ta wasu bangarori da yawa suke bayyana kansu. Yana sanye da jeans da shirt yayin da musaddiq jikinsa ke sanye da jallabiyya saqar marocco,kansa kuma akwai qaramar hular da mukafi mata laqabi da tashi ka fiya naci haka ma mutumin dake gefan musaddiq din. Akwai haske sosai saman fuskar tashi dake bayyana musulunci tattare dashi. Da sassarfa musaddiq din yake qarasowa garesu,idanunshi duka suna kan anni,yana isowa gaban nata baiyi duba da wani girmansa ba,ya bude dukka hannayensa ya rungume annin yana fadin "I missed you so much anni......sai naji kaman ba zakuzo ba.....kwana biyu kawai amma sai naji tayi nisa" Murmushin dake shimfide kan fuskarta kadai ya isa ya gaya maka farincikin dake ranta na ganinsa da tayi,zallar qauna irin wadda ba kasafai ake samunta wajen wani ba idan ka dauke uwa. "Kayi nisan kiwo yaro na......ka tayani roqon hammanku kada ya sake daukemin kai har haka" Ranqwafowa yayi wajen fuskar annin,yana yin qasa qasa da muryarsa don kada fu'ad yaji "Na rantse anni nima bazan sake yarda ba.....ki jawa danki kunne" "Kai kai......hamman?,ai kuwa kaman a kunnensa" Amna data zuro musu kai ta fada tana raba idanu. Duban amna yayi yana dan yamutsa fuska "Bama haka dake auta......kinsan ni dake duk muna together" Ya furta yana daga mata yatsunsa biyu cikin salon son samun goyon bayanta. Fuska ta shagwabe tana cewa "Zan iya haqura nayi shuru idan tsarabata tafi ta kowa yawa" Tayi maganar tana kashe ido daya sannan ta dora "Idan kuma ba haka ba.....ga addana a gefe,ita zan gayawa ta shaida masa abinda kace da mijinta" Ta qarasa maganar tana nuna sabreen da yatsa. Sai a sannan ta lura da sabreen din dake gefansu. Ya dora idonshi a kanta yana dan kafeta da kallo na wasu sakanni. Sosai yaji yasan fuskartata,ba yau ne ranar farko daya fara ganin fuskar ba. Cikin qasa da second biyar ya tuna inda ya santa. Tabbas bazai taba iya mantawa da fuskar ba.....fuskar data dinga fada saboda lafiyar anninsu.......fuskar data zama silar ceto rayuwar anninsu,to amma kuma sai yaji kaman bai kamata farat daya haka a matsayinsa na baquwar fuska a gareta yayi gaggawar tuhumarta inda ya santa ba.....ballanta ma ita din da take matsayin yaaya a wajensa. "Tuba naki adda.....ayimin aikin gafara.....da gaske hamma baida dadi shi yasa takeson hadoni dashi" Ya fada yana hade hannayensa duka biyu waje daya. Batasan ya akayi murmushi ya qwace mata ba,murmushin daya afku saman idanun fu'ad dake dan nesa kadan dasu yana karbar takardu hannun ahmad tare da sake karbar wasu bayanai,don tuni farouq ya wuce cikin gidan yana sake duba yanayinsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 0818725586269 Wani abu ya hadiye da baisan meye shi ba,wato ita duk inda taga maza sakin jikinta takeyi?,a ina tasan musaddiq da daga haduwar farko xata sake masa fuska da murmushi har haka?. Idanu ya xuba mata yana kallon yadda take duban musaddiq kai tsaye. "Anyi maka.....amna ma na tabbatar tsokanarka take,don kullum cikin kewarka take,nasha labarinka a wajenta sosai". Ta fada har zuciyarta tana mamakin family din. Kowa na gidan kenan me kirki ne,shi kadai ne maras kirki,maras fara'a,marason jama'a?. Ta tambayi kanta sanda idanunta ya sauka a kanshi. Cikin sa'a idanunsu suka sarqafe guri guda,kusan tare kowa ya dauke dubansa daga kan dan uwansa,sai ya miqa hannu yana karbar takardar hannun ahmad. Da yaren dhivehi asalin harshen mutanen qasar ahmad din yake masa godiyan da batasan ta mece ba. Ga mamakinta sai taji ya maida masa shima da yaren sannan ya ya soma takawa shima yana wucewa ciki da qasaitaccen takun nan nasa. Tana jin muryar musaddiq yana fadin "Godiya nakeyi" Tare da maida kansa ga anni. "Zan kamaki,saikin gayamin dalilin da yasa kina kewata amma baki taba fadimin ko sau daya ba". "Diyata zo mu wuce ciki,wadannan idan kika biye musu zaki wuni a tsaye ne kam" Anni ta furta tana saka hannunta ta kamo hannun sabreen suka fara wucewa cikin gidan. Duk kunyar anni sai ta kamata,tayi qasa da kanta tana biye da ita. Batasan wani abu a duniya da takejin nauyinsa haka ba kaman annin,tana da wani kima a idanunta na musamman. "Yanzu nake shirin leqawa na kiraki ki shigo ciki......wancan shirmammiyar tunda ta hadu da dan uwanta kuma ai shi kenan.....may be daga nan ma yawo zasu wuce iyayen zumudi". " Saddiq....." Fu'ad dake zaune hannun kujera yana duba takardun daya karba yayi kiran Sadiq dake qoqarin daukan ruwa a fridge. Samun kanta tayi da lumshe idonta,batasan me yasa muryarsa take mata nauyi da yawa ba,ba ita ya kira ba,amma sautin kiran yakai mata har tsakiyar qirjinta. Muryarsa tana da wani irin amo me ratsa mutum koda ba dakai yake magana ba. "Na'am" Sadiq yabar abinda yakeyi ya waiwaya yana dubansa,bai daga kai ya kalleshi ba yace "Fita ka gayawa musaddiq kada suje ko ina" "Okay" Ya fada yana ajiye ruwan gami da kama hanyar fita. Numfashi kawai ta aje tana tabe baki,kowa a sake yake amma bandashi,ya iya bada umarni,daga wannan sai wancan,kuma yana iya gama magana dakai kaf ba tare da ya kalli fuskarka ba,ta rasa wanne irin mulki ne haka a cikin jininsa?. Idan kuma muguntarsa ya motsa,ta lura kowa ma da idanu yake hukuntashi,ko don yasan akwai wani abu me nauyi a cikin kallonsa oho?,saita dauke kai gefe tana tabe baki,idanunta kuwa suka sauka kan wani glass door wanda daga nan kana iya hangen wani ruwa nesa kadan dasu dake lullube da farin yashi kaman ta miqa hannu ta kamo. "Gidan ya miki anni?" Ya fada yana sauke takardar daga fuskarsa bayan ya gama jan ajin nasa. "Tubarkallah ma sha Allah" Anni ta fada cikin walwalar data bayyana har saman fuskarta tana kallon kowanne sashe na gidan "Allah ya qara rufa muku asiri duniya da lahira.....Allah ya ninka albarka cikin rayuwarku" "Allahumma ameen" Suka fada shi da farouq a kusan tare. "Anni ta shiga ta huta.....akwai awa kusan daya da rabi kafin sallar magarib.....inajin yau ba wanda zai fita sai gobe idan Allah ya kaimu" Ya fada yana duba agogon hannunsa sannan ya sauke. Cikin aljihun trouser dinsa farouq ya sanya hannu ya ciro key,ya kuma nufi wani daki cikin dakunan dake parlor din,ya bude dakin ya tura qofan yana duban amna "Ja luggage dinki dana anni kikai muku ciki" Yace da ita daidai sanda take shigowa, Amsa masa tayi to tana yin yadda yace din,ya waiwaya yana kallon musaddiq da musaddiq "Bude dakin can musaddiq ku sakawa addanmu nata kayan" Ya fadi yana miqawa musaddiq din key din,sannan ya kalli Sadiq "Saka mana namu a dakin musaddiq sai muyi squatting......addanmu ki shiga ki huta" Ya fada cikin murmushi da girmamawa fal muryarshi,qasan ransa kuma wasai da yadda plan dinsa ya tafi daidai. Harde hannayensa yayi kawai a qirji yana qarewa farouq kallo,wato abinda ya tsara ma ran shi zaiyi kenan?,shi yasa koda ya buqaci picture ko video na gidan ya hana mishi gani. Yasan sarai shi fu'ad din yake kalla,ya kuma shiryama koma meye zaice ko zaiyi,don haka ya basar yaqi kallonsa kaman baisan ma yana a wajen ba. Fridge kawai ya bude yana duba meye da meye a ciki yana kuma masa lissafin me dame ya kamata su ajiye na kwanakinsu a qasar. Wani haushi ya cikashi,ya cika yayi fam da rainin hankalin da farouq din ya shirya masa. To amma a yadda yaga farouq din ya tabbatar ya shiryawa duk wani rigimarsa ne,so dole ya fara bin komai a hankali,tunda basu kadai bane,akwai anni,bazaiso kuma anni taji ko taga komai ba. "Wanne irin gida ne wannan farouq?" Ya fada calmly yana qoqarin danne takaicinsa. Sai daya ajiye gorar hannunsa sannan ya waiwayo yana dubansa "Me fa?" Yayi tambayar kansa tsaye. Sai daya lumshe idonsa ya bude lokaci guda yana jin takaicin rainin wayon farouq da idan ya motsa tsaf xai iya cewa ma bai sanka ba. "3bedroom?,why not a siya me 4bedrooms farouq?" "Akwai baquwar halitta ne a cikinmu da bata samu waje ba?". Kai fu'ad ya girgiza yanason gajarce maganar,don ciki yakeso ya shiga yayi bacci ko na awa daya ne "Babu.....amma dakunan sunyi kadan.....kafi kowa sanin bana iya hada daki da kowa ba ko tun ba yau ba?" "To dawa na hadaka.....kajimin mutum zaimin sharri" Rainin hankalin farouq yakai masa ko ina,yana dab da bashi naushi idan baiyi wasa ba,sai ya ware hannunsa daga qirji yana dubansa "Ka canza plan dinnan,ta koma dakinsu anni tayi squatting tare dasu,saddiq su kwana da musaddiq.....kai kuma muje mu kwana tare". Baya yaja da sauri yana zare ido kaman yaga abun tsoro. "Mu kwana da kai?,alfanun uban me zanyi maka fu'ad?,me zakaji da kwana da namiji gardi dan uwanka bayan ga halalinka a gefe?" Maganar ta fara girmar kunnuwan fu'ad,tun ba yau ba yasan farouq idan baiso ba tantirin kansa ne,baisan sanda hannunsa yakai kan cup din da saddiq yasha ruwa ba ya jefeshi dashi,Allah yasa yana da zafin nama ya cafe "Na rantse da Allah xan ruguza maka kai......kai wanne irin dan iska ne?,maganan da nake maka daban yadda zaka juyan zance daban?,ta yaya zan kwana da wata alhalin muna muhalli daya da anni?". Dariya tana cin farouq amma ya maze "To ba dole nace haka ba?,ga mace me namiji zai maka?,nima bazan kwana da gardi ba,ka cire riga wannan qattin muscles din naka suyita bawa mutum tsoro.....in fact ma ni na fara rehearsal na yadda zan fara kwanciya daga ni sai fannah ta....anni kuma da kake magana akwai wanda zai kaita son ganinku tare....ko turmusheta kayi a gabanta ai saidai tabar muku gurin da gudu.....banson gulma banson k......" Bai qarasa ba yaji saukar abu a qeyarsa,agogon hannunsa ya kwance ya sake jifansa dashi don ya rasa dame zai jefeshi wannan karon. Dafe wajen yayi ya waiwayo yana dubansa fuska a hade "Amma dai kasan wannan zallar cin zali ne ko?,ni nakar xomon?,kaje ka yiwa anni bayanin abinda yasa zaka aikota kwana da ita daki daya mana da kanka". "Ya isheka farouq" Ya fada yana nunashi da yatsa,alamun ya fara qureshi. "Oho" Ya fada yana sungumar ruwansa yayi dakinsu baiko sake waiwayoshi ba. Shuru ne ya ratsa falon bayan wucewar farouq din,sai motsinsu kadan kadan da yake jiyowa daga dakunansu. Maganar gaskiya farouq ya cuceshi,inda kuma yasan da wannan da tuni ya sanya an canza musu gida da yafi haka yawan dakuna kafin su qaraso. Miqewa yayi abisa dole yana soma dosar dakin,abu daya ya sani shi bayason takura,yana son bajewa sosai ya sake a duk inda ya zabi rayuwa,so wanzuwarta cikin dakin kuwa bazai bari ya zama silar hanashi sakewa ba. *Maamah* Sake juya tickets din hannunta tayi guda biyu tana sake qare masa kallo. Mamaki da wani irin dunqulallen baqinciki yana yayyanka zuciyarta. Ta rasa wanne hamshaqinne ya juya tafiyar daga farkonta ta koma qarshe?. Maldevis shine waje na farko da zasu je a qa'ida kaman yadda ta samu tabbacin dukka iyalin gidan alhj hamza kibiya can suka wuce.....saudiyya kuma shine waje na qarshe da zasu ziyarta daga nan kuma sai gida Nigeria,amma wanne hamshaqinne ya karkatar da tata akalar tafiya daga saudiyya kafin ta sauka maldevis sannan su rankaya su wuce turkey tare?. "Hajiya ameena.....tabbas wannan aikin ameena ne" Ta fadi tana jin wutar qiyayyar matar tana sake ninkuwa a ranta. Zazzafar iska ta furzar tana fitar da idanunta waje irin na zallar takaici da kuma tunani. Ita kuwa ta yaya zata dagawa ameena qafa?,ta yaya zata bar ameena taci gaba da shaqar iska cikin aminci?,ba ragi tsakaninta da ameena har abada......yadda bata barta ta samu cikakken iko da mulki da 'ya'yanta ba.....tabbas haka zata zama silar tarwatsa nata ahalin gaba daya,duk wanda ya gaya mata cuta ba shakka ita mutuwa zata gwada masa,sai kawai taja wayarta tana laluben fareeda,tana jin wannan karon a gaban idanun ameenatun zata gwada mata nata izzar da qarfin mulkin kasancewar uwar data dauki cikin fu'ad tayi naqudarsa ta kuma haifeshi.......a gaban idanun kowa zata gwadawa sabreen ta isa da danta......zata nuna mata kuma tana da ikon sanya yaronta ya auri mata d'ai d'ai har guda uku rigis bayan ita. Shuru fareeda tayi tana sauraren bayanan maamah,saidai kuma zuciyarta cike fal da bacin rai da baqin kishin sabreen. Wata zazzafar iska ta furzar tana ajiye bututun shisha dinta ta gyara zamanta "Maldives ai gida ne......ina da sauran visa din qasar da ban gama cinyeta ba,muddin na samu ticket jibi warhaka ina can......ko ba ticket zan sanya daddy yamin hiring private jet......kya sameni a can" Daga haka ta yanke wayar tana latsa wayarta ba bata lokaci tana neman number wayar daddy din nata. Tafasa kawai zuciyarta takeyi,wannan karon da zafi zafinta zata shiga,zata budewa sabreen aiki sosai kaman yadda zata budewa fu'ad,tana jin komai mai sauqi ne......amma zata bari ta tabbatar da samun private jet ko ticket to Maldives. Bugu daya rak ya daga,ba kasafai ta fiya masa sallama ba,kusan sallamarta kiran sunansa ne "Daddyyyy.....maldevis" Ta fada da wata irin shagwaba kamar yarinyar da aka Haifa jiya jiya "Mamana......maldevis a daren nan?" "Daddy gobe......ina da sauran visa na da kamin last two months.......ticket kawai daddy nakeso......please daddy,it's an urgent need daddy". Murmushi ya saki yana juya kai kafin yace "Wani irin emergency issue ne haka ya taso mamana.....nifa mamana yanzun duk hankalina yana kan aure,kiyi aure haka mamana.....ki zabi duk kalar mijin da kk so zan tsaya miki" Maganar sai taji kaman tazo akan gaba,ta saki dariya tana cewa "Nayi maka alqawari daddy.....indai na samu wucewa Maldives gobe ko jibi,ina dawowa zan gabatar maka da mijin da zan aura" "Really mama na?!" Ya tambaya da excitement cikin muryarsa "Yes dad.....na taba maka qarya ne?" Ta sake fada cikin narke murya "No mamana......bani minti goma.....i will get back to you" "Thank youuuuuuu" Ta fada da sautin dariya tana sauke wayar. Lips nata ta cinje tana duban wayar gami da saqa abubuwa iri daban daban akan fu'ad. Zuwa sannan ta gama karance halayensa na girman kai da izza,yana da tsananin taurin kan data tabbatar ita din kanta shaida ce,taso koda bata aureshi ba ya bata hadin kai su mori quruciyarsu tare,amma martanin da yayi mata ya mata ciwon data jima tana riritashi a zuciyarta. "Tabbas saina biyo masa ta bayan gida,idan baiyi wasa ba sunansa ne zai fito a next newspapers da magazine ba na waccan karuwar matar tasa ba......tunda shine garkuwarta.......shi din ya kamata na taba qarfinsa" Ta fada da murmushin mugunta tana murza yatsunta bayan ta tabbatar da hukuncin daya fado ranta shine abinda ya kamata ta zartar. Qarar wayarta ya dawo da hankalinta,ta daga da sauri ganin me kiran. Wani ihun murna ta saki sosai tana jin dadi "I love you daddy......thank you so so much......bansan ma ya zan gode maka ba" Ta fada duk a rude saboda jin dadin samun ticket na tafiya Maldives jibi. Tana Lagos don haka ba ita babu bin jirgi zuwa Lagos din,kawai kanta tsaye jibi zata bi qatar Airways zuwa can "Ki kawomin miji kawai bayan kin dawo" "Baka da matsala dad....." Ta fada tana yanke kiran. Tun a daren ta gama komai,ta gama hada komai ta kuma tanadi komai gudun samun matsala goben kada ta tashi da uzurin da zata tashi ba'a daidai ba har ya jawo ta hada kayanta ba daidai ba. *_hmmmmmm,uhmmmmmmmmm_* 69 Wani abu ya hadiye da baisan meye shi ba,wato ita duk inda taga maza sakin jikinta takeyi?,a ina tasan musaddiq da daga haduwar farko xata sake masa fuska da murmushi har haka?. Idanu ya xuba mata yana kallon yadda take duban musaddiq kai tsaye. "Anyi maka.....amna ma na tabbatar tsokanarka take,don kullum cikin kewarka take,nasha labarinka a wajenta sosai". Ta fada har zuciyarta tana mamakin family din. Kowa na gidan kenan me kirki ne,shi kadai ne maras kirki,maras fara'a,marason jama'a?. Ta tambayi kanta sanda idanunta ya sauka a kanshi. Cikin sa'a idanunsu suka sarqafe guri guda,kusan tare kowa ya dauke dubansa daga kan dan uwansa,sai ya miqa hannu yana karbar takardar hannun ahmad. Da yaren dhivehi asalin harshen mutanen qasar ahmad din yake masa godiyan da batasan ta mece ba. Ga mamakinta sai taji ya maida masa shima da yaren sannan ya ya soma takawa shima yana wucewa ciki da qasaitaccen takun nan nasa. Tana jin muryar musaddiq yana fadin "Godiya nakeyi" Tare da maida kansa ga anni. "Zan kamaki,saikin gayamin dalilin da yasa kina kewata amma baki taba fadimin ko sau daya ba". "Diyata zo mu wuce ciki,wadannan idan kika biye musu zaki wuni a tsaye ne kam" Anni ta furta tana saka hannunta ta kamo hannun sabreen suka fara wucewa cikin gidan. Duk kunyar anni sai ta kamata,tayi qasa da kanta tana biye da ita. Batasan wani abu a duniya da takejin nauyinsa haka ba kaman annin,tana da wani kima a idanunta na musamman. "Yanzu nake shirin leqawa na kiraki ki shigo ciki......wancan shirmammiyar tunda ta hadu da dan uwanta kuma ai shi kenan.....may be daga nan ma yawo zasu wuce iyayen zumudi". " Saddiq....." Fu'ad dake zaune hannun kujera yana duba takardun daya karba yayi kiran Sadiq dake qoqarin daukan ruwa a fridge. Samun kanta tayi da lumshe idonta,batasan me yasa muryarsa take mata nauyi da yawa ba,ba ita ya kira ba,amma sautin kiran yakai mata har tsakiyar qirjinta. Muryarsa tana da wani irin amo me ratsa mutum koda ba dakai yake magana ba. "Na'am" Sadiq yabar abinda yakeyi ya waiwaya yana dubansa,bai daga kai ya kalleshi ba yace "Fita ka gayawa musaddiq kada suje ko ina" "Okay" Ya fada yana ajiye ruwan gami da kama hanyar fita. Numfashi kawai ta aje tana tabe baki,kowa a sake yake amma bandashi,ya iya bada umarni,daga wannan sai wancan,kuma yana iya gama magana dakai kaf ba tare da ya kalli fuskarka ba,ta rasa wanne irin mulki ne haka a cikin jininsa?. Idan kuma muguntarsa ya motsa,ta lura kowa ma da idanu yake hukuntashi,ko don yasan akwai wani abu me nauyi a cikin kallonsa oho?,saita dauke kai gefe tana tabe baki,idanunta kuwa suka sauka kan wani glass door wanda daga nan kana iya hangen wani ruwa nesa kadan dasu dake lullube da farin yashi kaman ta miqa hannu ta kamo. "Gidan ya miki anni?" Ya fada yana sauke takardar daga fuskarsa bayan ya gama jan ajin nasa. "Tubarkallah ma sha Allah" Anni ta fada cikin walwalar data bayyana har saman fuskarta tana kallon kowanne sashe na gidan "Allah ya qara rufa muku asiri duniya da lahira.....Allah ya ninka albarka cikin rayuwarku" "Allahumma ameen" Suka fada shi da farouq a kusan tare. "Anni ta shiga ta huta.....akwai awa kusan daya da rabi kafin sallar magarib.....inajin yau ba wanda zai fita sai gobe idan Allah ya kaimu" Ya fada yana duba agogon hannunsa sannan ya sauke. Cikin aljihun trouser dinsa farouq ya sanya hannu ya ciro key,ya kuma nufi wani daki cikin dakunan dake parlor din,ya bude dakin ya tura qofan yana duban amna "Ja luggage dinki dana anni kikai muku ciki" Yace da ita daidai sanda take shigowa, Amsa masa tayi to tana yin yadda yace din,ya waiwaya yana kallon musaddiq da musaddiq "Bude dakin can musaddiq ku sakawa addanmu nata kayan" Ya fadi yana miqawa musaddiq din key din,sannan ya kalli Sadiq "Saka mana namu a dakin musaddiq sai muyi squatting......addanmu ki shiga ki huta" Ya fada cikin murmushi da girmamawa fal muryarshi,qasan ransa kuma wasai da yadda plan dinsa ya tafi daidai. Harde hannayensa yayi kawai a qirji yana qarewa farouq kallo,wato abinda ya tsara ma ran shi zaiyi kenan?,shi yasa koda ya buqaci picture ko video na gidan ya hana mishi gani. Yasan sarai shi fu'ad din yake kalla,ya kuma shiryama koma meye zaice ko zaiyi,don haka ya basar yaqi kallonsa kaman baisan ma yana a wajen ba. Fridge kawai ya bude yana duba meye da meye a ciki yana kuma masa lissafin me dame ya kamata su ajiye na kwanakinsu a qasar. Wani haushi ya cikashi,ya cika yayi fam da rainin hankalin da farouq din ya shirya masa. To amma a yadda yaga farouq din ya tabbatar ya shiryawa duk wani rigimarsa ne,so dole ya fara bin komai a hankali,tunda basu kadai bane,akwai anni,bazaiso kuma anni taji ko taga komai ba. "Wanne irin gida ne wannan farouq?" Ya fada calmly yana qoqarin danne takaicinsa. Sai daya ajiye gorar hannunsa sannan ya waiwayo yana dubansa "Me fa?" Yayi tambayar kansa tsaye. Sai daya lumshe idonsa ya bude lokaci guda yana jin takaicin rainin wayon farouq da idan ya motsa tsaf xai iya cewa ma bai sanka ba. "3bedroom?,why not a siya me 4bedrooms farouq?" "Akwai baquwar halitta ne a cikinmu da bata samu waje ba?". Kai fu'ad ya girgiza yanason gajarce maganar,don ciki yakeso ya shiga yayi bacci ko na awa daya ne "Babu.....amma dakunan sunyi kadan.....kafi kowa sanin bana iya hada daki da kowa ba ko tun ba yau ba?" "To dawa na hadaka.....kajimin mutum zaimin sharri" Rainin hankalin farouq yakai masa ko ina,yana dab da bashi naushi idan baiyi wasa ba,sai ya ware hannunsa daga qirji yana dubansa "Ka canza plan dinnan,ta koma dakinsu anni tayi squatting tare dasu,saddiq su kwana da musaddiq.....kai kuma muje mu kwana tare". Baya yaja da sauri yana zare ido kaman yaga abun tsoro. "Mu kwana da kai?,alfanun uban me zanyi maka fu'ad?,me zakaji da kwana da namiji gardi dan uwanka bayan ga halalinka a gefe?" Maganar ta fara girmar kunnuwan fu'ad,tun ba yau ba yasan farouq idan baiso ba tantirin kansa ne,baisan sanda hannunsa yakai kan cup din da saddiq yasha ruwa ba ya jefeshi dashi,Allah yasa yana da zafin nama ya cafe "Na rantse da Allah xan ruguza maka kai......kai wanne irin dan iska ne?,maganan da nake maka daban yadda zaka juyan zance daban?,ta yaya zan kwana da wata alhalin muna muhalli daya da anni?". Dariya tana cin farouq amma ya maze "To ba dole nace haka ba?,ga mace me namiji zai maka?,nima bazan kwana da gardi ba,ka cire riga wannan qattin muscles din naka suyita bawa mutum tsoro.....in fact ma ni na fara rehearsal na yadda zan fara kwanciya daga ni sai fannah ta....anni kuma da kake magana akwai wanda zai kaita son ganinku tare....ko turmusheta kayi a gabanta ai saidai tabar muku gurin da gudu.....banson gulma banson k......" Bai qarasa ba yaji saukar abu a qeyarsa,agogon hannunsa ya kwance ya sake jifansa dashi don ya rasa dame zai jefeshi wannan karon. Dafe wajen yayi ya waiwayo yana dubansa fuska a hade "Amma dai kasan wannan zallar cin zali ne ko?,ni nakar xomon?,kaje ka yiwa anni bayanin abinda yasa zaka aikota kwana da ita daki daya mana da kanka". "Ya isheka farouq" Ya fada yana nunashi da yatsa,alamun ya fara qureshi. "Oho" Ya fada yana sungumar ruwansa yayi dakinsu baiko sake waiwayoshi ba. Shuru ne ya ratsa falon bayan wucewar farouq din,sai motsinsu kadan kadan da yake jiyowa daga dakunansu. Maganar gaskiya farouq ya cuceshi,inda kuma yasan da wannan da tuni ya sanya an canza musu gida da yafi haka yawan dakuna kafin su qaraso. Miqewa yayi abisa dole yana soma dosar dakin,abu daya ya sani shi bayason takura,yana son bajewa sosai ya sake a duk inda ya zabi rayuwa,so wanzuwarta cikin dakin kuwa bazai bari ya zama silar hanashi sakewa ba. *Maamah* Sake juya tickets din hannunta tayi guda biyu tana sake qare masa kallo. Mamaki da wani irin dunqulallen baqinciki yana yayyanka zuciyarta. Ta rasa wanne hamshaqinne ya juya tafiyar daga farkonta ta koma qarshe?. Maldevis shine waje na farko da zasu je a qa'ida kaman yadda ta samu tabbacin dukka iyalin gidan alhj hamza kibiya can suka wuce.....saudiyya kuma shine waje na qarshe da zasu ziyarta daga nan kuma sai gida Nigeria,amma wanne hamshaqinne ya karkatar da tata akalar tafiya daga saudiyya kafin ta sauka maldevis sannan su rankaya su wuce turkey tare?. "Hajiya ameena.....tabbas wannan aikin ameena ne" Ta fadi tana jin wutar qiyayyar matar tana sake ninkuwa a ranta. Zazzafar iska ta furzar tana fitar da idanunta waje irin na zallar takaici da kuma tunani. Ita kuwa ta yaya zata dagawa ameena qafa?,ta yaya zata bar ameena taci gaba da shaqar iska cikin aminci?,ba ragi tsakaninta da ameena har abada......yadda bata barta ta samu cikakken iko da mulki da 'ya'yanta ba.....tabbas haka zata zama silar tarwatsa nata ahalin gaba daya,duk wanda ya gaya mata cuta ba shakka ita mutuwa zata gwada masa,sai kawai taja wayarta tana laluben fareeda,tana jin wannan karon a gaban idanun ameenatun zata gwada mata nata izzar da qarfin mulkin kasancewar uwar data dauki cikin fu'ad tayi naqudarsa ta kuma haifeshi.......a gaban idanun kowa zata gwadawa sabreen ta isa da danta......zata nuna mata kuma tana da ikon sanya yaronta ya auri mata d'ai d'ai har guda uku rigis bayan ita. Shuru fareeda tayi tana sauraren bayanan maamah,saidai kuma zuciyarta cike fal da bacin rai da baqin kishin sabreen. Wata zazzafar iska ta furzar tana ajiye bututun shisha dinta ta gyara zamanta "Maldives ai gida ne......ina da sauran visa din qasar da ban gama cinyeta ba,muddin na samu ticket jibi warhaka ina can......ko ba ticket zan sanya daddy yamin hiring private jet......kya sameni a can" Daga haka ta yanke wayar tana latsa wayarta ba bata lokaci tana neman number wayar daddy din nata. Tafasa kawai zuciyarta takeyi,wannan karon da zafi zafinta zata shiga,zata budewa sabreen aiki sosai kaman yadda zata budewa fu'ad,tana jin komai mai sauqi ne......amma zata bari ta tabbatar da samun private jet ko ticket to Maldives. Bugu daya rak ya daga,ba kasafai ta fiya masa sallama ba,kusan sallamarta kiran sunansa ne "Daddyyyy.....maldevis" Ta fada da wata irin shagwaba kamar yarinyar da aka Haifa jiya jiya "Mamana......maldevis a daren nan?" "Daddy gobe......ina da sauran visa na da kamin last two months.......ticket kawai daddy nakeso......please daddy,it's an urgent need daddy". Murmushi ya saki yana juya kai kafin yace "Wani irin emergency issue ne haka ya taso mamana.....nifa mamana yanzun duk hankalina yana kan aure,kiyi aure haka mamana.....ki zabi duk kalar mijin da kk so zan tsaya miki" Maganar sai taji kaman tazo akan gaba,ta saki dariya tana cewa "Nayi maka alqawari daddy.....indai na samu wucewa Maldives gobe ko jibi,ina dawowa zan gabatar maka da mijin da zan aura" "Really mama na?!" Ya tambaya da excitement cikin muryarsa "Yes dad.....na taba maka qarya ne?" Ta sake fada cikin narke murya "No mamana......bani minti goma.....i will get back to you" "Thank youuuuuuu" Ta fada da sautin dariya tana sauke wayar. Lips nata ta cinje tana duban wayar gami da saqa abubuwa iri daban daban akan fu'ad. Zuwa sannan ta gama karance halayensa na girman kai da izza,yana da tsananin taurin kan data tabbatar ita din kanta shaida ce,taso koda bata aureshi ba ya bata hadin kai su mori quruciyarsu tare,amma martanin da yayi mata ya mata ciwon data jima tana riritashi a zuciyarta. "Tabbas saina biyo masa ta bayan gida,idan baiyi wasa ba sunansa ne zai fito a next newspapers da magazine ba na waccan karuwar matar tasa ba......tunda shine garkuwarta.......shi din ya kamata na taba qarfinsa" Ta fada da murmushin mugunta tana murza yatsunta bayan ta tabbatar da hukuncin daya fado ranta shine abinda ya kamata ta zartar. Qarar wayarta ya dawo da hankalinta,ta daga da sauri ganin me kiran. Wani ihun murna ta saki sosai tana jin dadi "I love you daddy......thank you so so much......bansan ma ya zan gode maka ba" Ta fada duk a rude saboda jin dadin samun ticket na tafiya Maldives jibi. Tana Lagos don haka ba ita babu bin jirgi zuwa Lagos din,kawai kanta tsaye jibi zata bi qatar Airways zuwa can "Ki kawomin miji kawai bayan kin dawo" "Baka da matsala dad....." Ta fada tana yanke kiran. Tun a daren ta gama komai,ta gama hada komai ta kuma tanadi komai gudun samun matsala goben kada ta tashi da uzurin da zata tashi ba'a daidai ba har ya jawo ta hada kayanta ba daidai ba. *_hmmmmmm,uhmmmmmmmmm_* *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 70 Sam sam bata fahimci daki daya farouq ya hadesu ba sai da ya murda handle din ya shigo cikin sallama. Daidai lokacin da taketa qoqarin kauda luggage din zuwa kyakkyawan gurin ajiyar kaya dake a dakin bayan ta ware scarfs din kanta ta daure sumarta dashi. Kallon juna sukayi,sai kowa yayi qoqarin dauke idonsa daga kan dan uwansa. Haka kawai ta samu gabanta da faduwa,tunaninta kuma ya koma baya na yadda aka kasafta dakunan "Tashin hankali!.....shine part na na?" Ta fadawa kanta da kanta. Sam sam bata taba hango yiwuwar wanzuwarsu a daki daya ba......ita da mutumin da basa ga maciji sam sam,ta yaya zata iya hada numfashi dashi qarqashin rufin daki guda daya?,lallai inda tasan da yiwuwar faruwar hakan wannan kadai a wajenta ya isa dalilin da zai hanata yin tafiyar ma gaba daya. Sakin abinda takeyi tayi ta kuma ware veil dinta ta lullube kanta dashi dukka tana satar kallonsa. Baiko nuna yasan da tsaiwarta a wajen ba,hasalima yanata daddaga labulayen dakin yana laluba sauran gurare irinsu socket na dakin,switch da sauran gurare saboda tsaro,gudun samun wata boyayyar camera da basusan da ita ba. Baisan ta fice ba sai da yaji alamun jan qofar,ya bi qofar da kallo kafin daga bisani ya dauke dubansa daga wajen yana ci gaba da abinda yakeyi. Wannan dukka ba take taken raini bane ba?,amma ba wanda ya jawo masa illa farouq,kuma tabbas zaija kunnensa,bazai yiwu cikin qasashe biyu da xasu sake zuwa a gaba ya qara hada musu guri ba,duk da kusan duka qasashen ba inda baida gida mallakin kansa uku ko hudu,da kansa zai zabi gidan da yakeso saboda gudun faruwar hakan. Sai daya tabbatar da lafiyar dakin sannan ya soma rage kayan jikinsa,don bazai iya bacci haka ba,ko wankan ma bayajin zaiyishi sai idan ya tashi,duk da farouq nason rage masa jin dadinsa.....don da gaske hutu yazoyi,yazo.ya huta inda ba zaa sashi magana bs ko ciwon kai. Turus tayi sanda ta fito parlor din,wayam ba kowa sai dan motsinsu daga dakunansu. Bin duka qofofin dakunan dake kulle tayi da kallo,saita rasa meye abunyi. Da kunya dai ta jewa dakinsu anni wanda ta tabbatar a yanzun suma hutawa sukeyi,idan ma taje tace mata me?. Ba zata zauna daki daya da d'anta ba wanda mijinta ne a qa'ida duk duniya kuma haka suke kallonsu?,wanda sukasan sahihin zamansu mutanene daidaiku.......hatta da amna bata sanya ran ta gama fahimtar komai da komai. Rasa madafa tayi,dole a qarshe kwanyarta ta gaya mata bata da sauran wani abunyi illa ta koma dakin ta rungumi haquri na yau,zuwa gobe saita nemawa kanta dalili da mafitar da zata sanya a raba dakin. Daidai sanda ya isa bakin qofa da zummar kashe switch na qwan ita kuma ta murza qofar ta shigo. Baikai ga kashewa ba,don haka tsaf ta ganshi. Murdadde kuma qaqqarfan muhammad fu'ad jadda,ma'abocin daga qarfe da dukka surar jikinsa ta koma ta qarfafan maza,saidai surar batayi muni ba,ta dace da zatinsa ta kuma shekarunsa. Babu komai a jikinsa sai gajeran wando iyakar cinyoyinsa,gaba daya faffadan qirjinsa dake lullube da ni'imtaccen tattausan gashi ya tare kusan rabin qofar dashi,abinda ya sanyata saura kadan ta fada qirjin nasa,abinda kuma ya saka tsoro ya kusan sanyata shidewa,ta daburce duka cikin qanqanin lokaci,saita juya da hanzari da zummar ficewa a dakin don ba zata juri ganinsa haka ba. Sosai ya raina sanya hannu qwaya daya ya jawota zuwa gabansa,yanzun hakan ma yayi mata,ya kuma ajeta a gefe,ya saka hannu ya murza key din qofar ya rufe dakin,ya cilla key din saman gado sannan ya juya yana kashe switch din. Dakin yayi duhu,saidai duhun bazai hanaka ganin komai dake dakin ba amma bada fitacciyar suffarsa ba. Takawa yakeyi hankalinsa kwance zuwa gadon kaman ba'a tube yake ba "Sannu a hankali wataran zan baki mamaki tunda na hanaki wannan rainin hankalin da kikemin kaman dodo......sai kace a kaina kika taba ganin namiji a t......" Sai kuma bai qarasa ba yaja tsaki sanda yake dora kansa saman pillow hadi da lumshe idanunsa ya sauke numfashi. Komai ta kasa cewa saboda tsoro daya cakude da takaici. Ta zuba ma fuskarsa idanu duk da bata iya ganinta sosai tana jin bacin rai yana taso mata. Ta tsani koda kalma daya ta hadasu shi yasa take kauce masa,don kowacce magana zai gaya mata bame dadi bace a zuciyarta da kunnuwanta. Don kanta ta samu waje ta nade tana curewa guri daya bayan ta gaji da tsaiwa,don tuni yaja duvet ya rufe jikinsa dukka gaba daya har saman kansa. Tsakiyar baccinsa ya dinga ganinta tana nufoshi cikin swimsuit sanda yake zaune daga gaban swimming pool din yana kallonta. Kanta tsaye ta yiwa kanta mazauni saman cinyarsa,yayin da albarkatun qirjinta yake tokare masa fuska da wani irin salo na tsokana,baisan ya akayi ba ya samu kansa da goga fuskarsa a jikinsu,abinda ya tashi kowacce tsiga ta jikinsa kenan,kowacce kafar jikinsa ta soma fidda zufa,ya kuma jawota ya qanqameta da kyau yana cusa fuskarsa tsakiyarsu kaman me neman taimako. Wani birkitaccen salo takeyi masa,wanda ya taimaka wajen fitarsa a hayyacinsa,ya kuma juyeta saman sun lounger din da yake kai,take al'amura suka fara kankama tsakaninsa da ita. Karar fadawar wani abu ruwan dake gabansu shi ya farkar dashi har a zahiri. Idanunsa ya runtse da qarfi yana jin wani abu yana yawo a sassan jikinsa. Yana jin tamkar a yanzun idanu biyu komai yake faruwa,wani irin zazzafan yanayi da ya jima bai tsinci kanshi a ciki ba saboda yadda yake yawaita yin takatsantsan. "Why?,why?" Ya tambayi kansa da kansa muryarsa can cikin maqogoronsa. Me yasa zata biyo shi har baccinsa?,ba zata qyaleshi ya huta ba kenan?. Ko a baya da yake fuskantar irin mafarke mafarken nan......babu guda daya daya taba ganin ainihin fuskar ko gangar jiki,wannan shine na farko da komanta ya bayyanar masa a zahiri. Fitowarta daga toilet shi ya sanya ya ware rinannun idanunsa a kanta. Duk da bata iya ganinsa sosai amma taga alamun ya farka daga baccin. Dama ya kamata ace ya farka din,tunda agogo ya nuna mata lokacin magariba yayi,amma kuma batasan yadda zata tayar dashi ba,to ya samawa kansa lafiya daya farka din. Dakin ya mata duhu saboda yadda duhu ya soma mamaye garin,saita laluba har ta dace da makunnin ta kunna qwan dakin,take haske ya gauraye ko ina tarwai. Idanunsa ya lumshe yana cusa shi cikin pillow "Oh shit" Ya fada qasa qasa. Qoqarin tashi yake kafin hakan takai ga faruwa sai gashi ta rigashi kunna hasken dakin. Ta yaya zai iya tashi ya miqe ya wuce zuwa bandaki a yanayin da yake ciki?,tambayar dashi kansa baisan amsarta ba. A nata bangaren ta gama gajiya da zaman dakin,burinta kawai ya budeta ta fita,bataga wani alfanun zamansu suna musayar numfashi ba idan ba tsabar muguntar nashi bane ya motsa. Ta duba luggage dinta ma sam bata ga hijab ba,sai mayafai ta hada kusan uku dasu zatayi sallar. Ba ita ta hada kayan ba,zata iya cewa batasan ma meye a ciki ba,anni ce ta musu siyayyar duk da uban lodin kayan da suke da wanda ita kanta batasan adadi ba,amna kuma ta shirya mata tace basai ta buda ba ta saka mata komai,ta kuma biye matan bata duba ba. Bashi da wani sauran abinda ya rage illa dole ya tashi din,don haka ya tattara uban duvet din ya nadeshi a jikinsa ya sauka yana wucewa toilet din a gurguje. Ta danyi mamakin shigarsa toilet fa duvet,amma sai kuma sai ta kauda abun daga ranta ta shimfida abun sallah tana jiran lokaci ya qarasa cika. Ya jima a toilet din yana qoqarin ganin yanayinsa ya daidaita,yasha azaba qwarai har ya dinga tunanin anya yau zai tsallake kuwa?. Kowanne jijiya ta jikinsa aikawa take da saqo,sai bayan kusan minti talatin ya samu yanayinsa ya dawo daidai,amma abinda yakeji a jikinsa bai sauya ba tunda jikin bai samu abinda yakeso ba. Dukka jikinsa ya wani mutu qwarai da wata irin kasala data sakar masa da nauyin jiki,haka yayi wanka ya daura alwala ya fito. Sauqinta daya data samu tana sallah sanda ya fito din,don da alama a yanzun ma gaba gadi ya fito abinsa,ya buda kayansa ya shirya cikin Moroccan jallabiyya black me adon golden din zare,ya saka qaramae gold din hula ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki key ya bude qofan ya fice don zuwa su hada jam'i dasu saddiq kaman yadda suka saba duk sanda sukayi tafiya a qasashen daba masallaci a kusa da masaukinsu. Fitarsa sai taji kaman ta samu 'yanci ne,ta kammala sallarta ta fada wanka. Koda ta fito lokacin isha'i yayi,tasan qwarai tana da nauyin wanka,amma na yau ya haura na kullum saboda ba qaramar wahala tasha wajen gane yadda zatayi amfani da kayan bandakin ba. Da karsashinta ta isa ga luggage dinta,saidai kaf ta cajeshi babu wata suturar arziqi da zata iya sakata ta fita,sai uban lingerie data zuba mata kaman karuwar dake neman customer. Takaici ya sanyata komawa ta zauna ta rafka tagumi,kusan mintina ashirin ta kashe a haka kafin ta jawo akwatin ta sake birkiceshi ko zata dace. Baqinciki ya sanyata daga lingerie din daya bayan daya tana qare musu kallo. Kaya ne na rashin kunyar da ita kanta kunyar wasu a ciki takeji idan ta daga "Amna kin kwafsamin.....kin kasheni......shi yasa kikace kada na duba kayan" Ta fada a fili daidai sanda ta daga wata lingerie din da aka yiwa wani yanka na wulaqanci,aka fidda gidan mama daga qasa kuma aka mata wata huda. Shigowarsa da sallamarsa duka lokacin guda ne,ta saki rigar da sauri ya bita da kallo,ta miqa hannu da gaggawa ta tattareta ita da sauran tana zubawa a akwatin sannan ta miqe. Tanason masa maganan ya turo mata amna amma batason halinsan nan,ya kammala abinda yakeyi ya doshi hanyar fita "Idan kin gama abinda kikeyi din ki fito za'ayi dinner" "Don Allah ka turomin amna" Ta katsi numfashi tana fadi da sauri har sai daya waiwayo ya kalleta,karon farko da magana ta nutsuwa da respect harma da begging a ciki ya taba hadasu,sai baice komai ba ya fice abinsa. Harara ta ballawa qofan tana jin baiken kanta,me yasa ma ta roqeshi?,gashinan ya yarfata a banza,dama me hali ai baya fasa halinsa,ta tsugunna tana hade kayan cikin takaici. Saidai ko gamawa batayi ba amna tayi sallama,ta tsaya daga qofa tana leqowa a darare. "Ki shigo malama" Ta furta tana jifanta da harara. "Shigowa makwancin hamma din kai tsaye haka hadari ne" Ta fada tana shigowa kaman yadda ta buqata. Tana mamakin irin tsoronsa da sukeyi da yadda suke kiyayarsa qwarai. "Yau fada zamuyi dake har anni saita shigo sasanci" "Me nayi adda?" Ta tambaya tana waro idanunta gami da dafe qirjinta "Kayan da kika zubamin dama kenan amna?" Ta tambayeta tana dan kama kunnenta. Dafe kunnen tayi dariya tana kamata,duk da riqon babu zafi amma tace "Wayyo kunnen autar anni......aradu anni ce tace duka na zuba miki su,ni kuma da naji tace haka saina kwashe wadancan......bansan mix ya kamata ayi ba" . Kunya ta saukarwa sabreen,sai kawai ta saki kunnen amna din "Saikije ki daukomin hijab dinki,kayan fice ficen ma duk na fasa sakasu tunda baki sakamin kayan zaman gida na arziqi ba,da hijab zanta zama" "Kaina bisa wuya na" Ta furta tana dariya gami da ficewa. Gudun jira sai kawai ta shirya kanta cikin riga da wandon,rigar ta sauko mata har saman mazaunanta,wandon kuma cif jikinta,don ya fidda sigar santala santalan cinyoyinta da faffadan qugunta. Murda qofan ya sanyata juyowa da sauri tana zaton amna ce ta dawo,saidai a maimakon amna din sai taga hammanta. Fuad ne tsaye fuskarsa babu walwala,kai tsaye ya soma kallonta tun daga qasan qafafunta,idanunsa kuma suka cake akan qirjinta,abinda ya sanya yaji wani yarrr tsigar jikinsa ta zuba. Fes abinda yaji da dumi da qamshin da wajen kiyi ya dawo masa fes a qwalqwalrsa,sosai jini ya harba ko ina a jikinsa,yayi gaggawar damqe numfashinsa gami da hana faruwar abinda yake shirin faruwar dashi. Kallon qurillar da a yau yayi mata karon farko a tarayyarsu ya ratsa kowanne jini dake gudu a sassan jikinta. Idan tace zata juya masa baya nan ma tasan bata tsira ba,komai na jikinta ita kañta tayi imanin a bayyane yake. "Karki fara gangancin fitowa a haka......ki nema kinomo ko hijab ki saka a jikinki". Sai ya saki qofar yana juyawa yana jin numfashinsa kaman zai tsaya da aiki. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 71 71 Tun kafin ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na daidaituwar al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun muhimmanci. Ba jiya ko yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata tun basu mallaki hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu guda ne tattare dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling irin na kowanne lafiyayyen namiji. "Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa sanda fu'ad ke zama a dining din kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana cewa "Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya kamata ba" "I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa yasan farouq din bai aminta ba. Tare suka jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan wayarsa yana duban sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya umarta ba,saboda yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi ganin karon farko tayi abinda yace da ita. Gaida anni ta sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq da yake da sauqin kai. Amna ce ta soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring anan qasar wato hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da dama. Yawa yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa wajen iya sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni ko kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki bane babba. "Sabreen" Anni ta fada tana dubanta "Na'am anni" "Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza mata,amma hakanan ta miqe ta dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana kallonsa wai ko zaice ya isa haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan wayarsa "Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta raya mata. Wato fareedan ce mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida lokacinta?. Duka anni na ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta "It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka ko?". Kansa ya daga ya dubi anni yana gyada kai yana sakin qaramin murmushi. Karon farko data gayawa kanta da gaske yana da kyau kaman yadda takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu me kama da murmushi akan fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba wanda yake samun fu'ad din a asalin fu'ad dinsa sai anni. "Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan abincin data zuba masan. Abinci sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar bare a cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi. Sai kunnuwa data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a goben. Amna keta lissafin abinda zasu kashe "Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta girgiza kai "Ko sisi amna.....me zan siya?" "Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu fa,zakiga abubuwa da yawa da zasu burgeki.....kinji anni wai batason komai......adda komai sai tace bataso?". "Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da dolla account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana murmushi,kunyarta tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke wayoyinsa. "Zan kwanta anni" "Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare ya fara" A nan ya barsu ya gangara ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa. 71 Tun kafin ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na daidaituwar al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun muhimmanci. Ba jiya ko yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata tun basu mallaki hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu guda ne tattare dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling irin na kowanne lafiyayyen namiji. "Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa sanda fu'ad ke zama a dining din kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana cewa "Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya kamata ba" "I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa yasan farouq din bai aminta ba. Tare suka jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan wayarsa yana duban sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya umarta ba,saboda yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi ganin karon farko tayi abinda yace da ita. Gaida anni ta sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq da yake da sauqin kai. Amna ce ta soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring anan qasar wato hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da dama. Yawa yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa wajen iya sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni ko kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki bane babba. "Sabreen" Anni ta fada tana dubanta "Na'am anni" "Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza mata,amma hakanan ta miqe ta dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana kallonsa wai ko zaice ya isa haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan wayarsa "Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta raya mata. Wato fareedan ce mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida lokacinta?. Duka anni na ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta "It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka ko?". Kansa ya daga ya dubi anni yana gyada kai yana sakin qaramin murmushi. Karon farko data gayawa kanta da gaske yana da kyau kaman yadda takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu me kama da murmushi akan fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba wanda yake samun fu'ad din a asalin fu'ad dinsa sai anni. "Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan abincin data zuba masan. Abinci sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar bare a cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi. Sai kunnuwa data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a goben. Amna keta lissafin abinda zasu kashe "Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta girgiza kai "Ko sisi amna.....me zan siya?" "Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu fa,zakiga abubuwa da yawa da zasu burgeki.....kinji anni wai batason komai......adda komai sai tace bataso?". "Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da dolla account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana murmushi,kunyarta tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke wayoyinsa. "Zan kwanta anni" "Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare ya fara" A nan ya barsu ya gangara ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa. Wani mummunan horo kawai yakeji farouq yayi masa na hadashi kwana daki daya da ita. Gaba dayansa sai yake jinsa kaman a birkice yake,tun yana qaryata wanzuwarta daki daya dashi ne ya sanya yanayinsa komawa hakan,har yayi amanna cewa hakanne. A dare daya tak ya kasa samin isashen bacci har zuwa wayewar gari,wayewar garin da ya tashi da ninkin rashin kuzari da karsashi a tattare dashi,fiye ma da yadda ya kwana jiya. Kowanne motsi farouq yana ankare dashi,dariya qasan ranshi kaman zata kasheshi. "Duk dacin ranka.....duk miskilancinka halittar mace tafi qarfinka ko kai waye......qaton tuzuru dakai sai taurin kai da kafiyan da ba inda zasu kaika?,dama can sarari ka samu,nisan tazarar dake tsakaninku ya sanya kake ganin kamar baka da wata buqata ko sha'awa irin ta d'a namiji.....wallahi qarya kake fu'ad......a wannan fannin ni kaina na sallama maka.....zan gani idan tusa zata hura huta......daga yau zuwa gobe kawai na baka,if kaci gaba da taurin kai.....nasan matakin da zan dauka a kanka" Farouq yayi dukka wannan gulmar cikin zuciyarsa yana duban fu'ad dake zaune yana kurbar maca and ginseng tea. Kaman baiso yake daga cup din zuwa bakinsa,shi kansa,ranshi a jagule,baiso irin wannan yanayin ya tasammasa a irin wannan lokacin ba sam,saidai koma meye zaya faru bayajin zai yarda koda da wasa ya hada jikinsa da ita. Jikin da akullum ya kalla sai yayita lissafin adadin maza nawa ne suka rabeshi?,adadin maza nawa ne suka tabashi?,dame dame sukayi da ita?. Yana da bala'in qyanqyami na fitar hankali,wannan qyanqyamin ya sanya bayajin shikam ko mata biyu zai iya aura,gwara ya tattara mutuntakarsa a muhalli daya. Uwa uba wani irin kishi ne dashi,ba kuma wai yanzu ba,tun tale tale zai iya cewa da kishin ya tashi,dashi aka halicceshi. Baisan maruka nawa yasha daga hannun maamah ba sanda take kawo maza gidan abokan kasuwancinta da suke siyan shaddodin da ta soma business dinsu ba,baisan adadin yawan dukan da yasha a kansu ba......saboda muddin zaka sanya qafarka a gidansu,to shi kuwa zai kafe ya cake a qofa ya hanaka qarasawa ciki. "Babanmu baya so......ya hana maza shigar masa gida,ka koma ka aiko qanwarka ko yayarka" Wadannan sune lafuzzansa a yayin da fuskarsa kan cika da wani irin fushi da zafin zuciya. Kusan baki suke sakewa,kusan duka duka shekarunsa a sannan ba zasu wuce goma sha daya ba,amma zuciyar manya gareshi,zuciyar data kubuta daga dukkanin tsoro saboda kare martaba da haqqin mahaifinsa. Wani lokacin idan ta jawoshi ta daka ta daka,abbansa dake daki kwance yana jiyya shi zaita kiransa,shi zai lallasheshi,yakan ce "Komai na duniya me wucewa ne me babban suna.....komai kuma haquri ne yake zama silar cin nasararsa......ka daina bari ana tabamin lafiyarka me tsadar nan kaji?" Sau tari duk kalan dukan da zata masan ba kasafai ya fiya kuka ba,duk da cewa duka ne ba kadan ba,wani lokaci harda abinda bai kamata ayi dukan ba. Idanunsa saidai suyi jajir,yayita hadiyar yawu da wani irin tsauri "Abba......gidanka ne fa,ta yaya kana kwance zasu dinga tsallakowa suna shigo maka?" Murmushi yakan yi,duk da yakan tsinci ciwo cikin murmushin nasa "Watarana sai labari me babban suna". Ire iren wadannan hirarrakin da abbansa har yau ya kasa sabawa da tunasu,har yau ya kasa jin Normal ne a rayuwarsa,har yau kansa baya iya jure tunasu,duk sanda sukazo masa sai yaji kaman kansa zai tarwatse,sai ya sakejin wani abu yana sanya nisa me tarin yawa tsakaninsa da maamah din,yakan ji kaman bazai iya qara idanu ya kalleta ko ya mutuntata ba......amma ta wani fannin.........uwa data cancanci a kirata mahaifiya irin ameenatu anni......itace ke riqo da hannunsu a ko yaushe,ta kuma qarfafesu da yi mata biyayya. Rana daya daya fahimci ta fara sana'ar dalilin aure,adadin maza da matan dake kai kawo a gidan suka dadu,a ranar ya yiwa wani mummunan rotsen da da qyara aka kashe maganar a police station. Ranar nisan kwana ne kadai ya kawoshi yau da ake magana,don ta sakashi a daki ne ta masa wani irin duka da sai da ya daina numfashi,tun abban nasu dake daga kwance ba daman tashi ya ceceshi yana kiran sunanta gami da qoqarin dakatar da ita,har yawun bakinsa ya dauke tsaf,yayi shuru ya zubawa sarautar Allah ido,yana jin sautin dukan da maganganunta,amma baya iya jin koda tarin muhammad. Yasan halinsa.....sha wuya ne dake iya shanye zafi da tsananin duka,yasan kowanne irin nau'in azaba take masa bazaiyi magana ba. "Me shegen baqin hali irin na ubansa.......baka isa ka hanani neman kudi ba wallahi,yadda talauci ke neman kai ubanka ramin qabarinsa tun lokacinsa baiyi ba......ni bazan zauna talaucin yayi ajalina ba". Qarshe dai musaddiq ya aika ya dinga zuba masa ruwa kafin ya farfado. Ta dauka zai rusuna daga ranar,amma sai taga kaman ma bashi ta daka ba,sai ya canza sabon salon kora da hali wajen yayyanka musu takalmi,karta mota da sace tayoyin motar ko na babur.......still marasa haquri a cikinsu police station suka.kaishi da qyar ta karboshi,zuciyarsa kuma na a tsaye bai rusuna ba,dolen dole ta tattara ta canza sana'a,waccan din saidai tayi a wani wajen daban amma ba cikin gidansu ba. Ajiye roban maca root din dana ginseng farouq yayi yana kallonsa. "Amma yallabai......wadannan abubuwan biyu kaman suna enhancing libido fa.....and..... ". Wani kallo fu'ad ya watsa masa da idanunshi da sukayi laushi qwarai,ya miqa hannu yana fusge container din ya ajiye a gabansa "Baka lura kuma yana boosting energy ba?" Ya fada cikin jin haushi. Dariya sosai ya qunshe farouq din yana gyada kai kaman qadangare "Yes.....yes na gani,kaman kai kenan da kayi loosing energy dinka ko?.....wannan bazai boosta maka komai ba dude.......you need a......." "Zip it" Ya katseshi da kakkausan kallon nan nasa. Shikam farouq bai gama maganansa ba,baiga abinda zai sanya a hanashi fadin abinda yai niyya ba,sai ya janye baya yana daga kafadu. "Duk wani abu da zai maidaka namijin gaske you're Comsumpting......but ka kasa kunna engine din kadan......" Bai qarasa ba ya cire spoon din cikin mug din ya jefeshi dashi,abinda ya sanyashi kasa qarasa maganan......amma kuma ya kece da dariya,wanda shigowar anni parlor din ya dakatar dashi daga dariyar. "Farouqu.....zoka miqawa muhammadu ya dubamin wannan address din.........wata qawata ce muna magana dazu ashe sun shigo suma". Karbar address din yayi ya kalla,bai gane gurin ba don haka ya miqawa fu'ad. "Few kilometers ne tsakaninmu,zaki je ne anni?" Ya tambaya yana dubanta. "Eh amma sai wajen gobe nake tunani.....tunda yau kaman naji amna tana fadan inda zasuje,ba zaa bar gidan ba kowa ba duk da ba wani abu bane". Kai ya jinjina ya ajiye takardar,sannan ya daga mug dinsa yana shanye ginseng tea dinsa abinsa,ba tare da ya maida kai ga kallon da farouq yaketa binsa dashi ba. Dukkaninsu farouq ya xuba a mota suka fice. Sosai suka zaga garin,guraren da sukaje sun kusa biyar,amma duk da haka amna bata gaji ba,fadi takeyi "Ya farouq.....don Allah mu zaga Maldives gaba daya kafin mu tafi,tunda island ne baida girma can can". Dariya musaddiq ya bushe dashi yana kallonta "Kinsan yawan guraren da suke dashi kuwa amnee......a qalla fa gurare dari da tamanin amnee,yaushe zamu iya zagayeshi?" "But......amma please BB,gobe ma ka fita damu,inason naci rihaakuru fish paste.......kifin Maldives please ya musaddiq" Ta fada tana narke murya. "Ki bani cin hanci mana saina roqar mana shi,harda traditional market dinsu.......rannan naga suna saida abubuwan gargajiya sosai.......i assured zakiji dadin gurin" Maganan musaddiq ta sake gigita amnee,ta dinga roqar farouq,har sai data saka sabreen a ciki. "Please BB farouq......a taimaki autan anni mana" Sabreen din ta fada da sassanyar muryarta dake da wani irin nutsuwa. Murmushi farouq ya saki,tana da kima a idanunsa da martaba me yawa,yana ganin mutuncinta sosai saboda yanayin nutsuwarta da kamun kanta. "An gama tunda.matar.oga ta saka baki" Dariya ya basu dukkaninsu har ita sabreen din sai data murmusa kadan. Har yau ya kasa yarda ko sau daya da binciken fu'ad a kanta......baisan meye dalili ba,duk da ya sani shi din mutum ne mara gaggawa akan kowa da komai......amma gaba daya halayensa sun canza a kanta,bazaice kuma ga wani dalili babba guda daya ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 72 72 Kusan dare ya soma nisa sanda suka isa gida,basu kuma lura da hakan ba sai da suka shiga parlor din gidan suka sameshi zaune saman qananun sofas din dake a falon. Yau idanunsa suna saye cikin farin glass wanda hasken allon system din gabansa ya sake fidda hasken kwalbar glass din. Kallo daya farouq ya masa yasan ta baci,ba kasafai ya fiya amfani da glass din ba sai idan idanunsa suna masa wani iri,don yana zuqe hasken kowanne abun amfani kafin ya samu shiga kai tsaye cikin idanun nasa. Gaba dayansu kowa sum sum ya soma shigewa cikin falon yana dosar qofar dakinsa. Mamaki ya cikata ganin har suka tako veranda din farko na gidan sunata karadi abinsu kuma cike da karsashi......amma da ganin wanzuwarsa kowa ya kama kansa. "Sai da safe" Ta tsinci muryar farouq da shima ya kama kansa zuwa dakinsu,abinda ya sanya jikinta yin laqwas itama ta qara hanzari zuwa nasu dakin ganin kowa ya fashe daga parlor din. A gaggauce ta shige toilet da duka kayan wankanta,tayi wankanta ta kuma shirya a can,tana fitowa kuwa ta nade saman sofa din data kwana jiya akai tana curewa waje daya cikin comforter din data dauke. Bawai sanyi takeji ba ko wani abu,kawai tanason takurawa kanta ne tayi bacci kafin ya shigo. Bata jima da kwanciya ba kuwa taji shigowarsa,ya ajiye komai a muhallinsa ya taka zuwa toilet. Da alwalarsa ya dawo dakin,kamar jiya ya shimfida abun sallah ya fara sallolin da batasan sanda ya gamasu ba,don gajiyar da tayi yau din ya dinga sassauke duk qashin jikinta gajiya tana fita. ★W A S H E G A R I★ K'arfe hudu na yammaci dukkaninsu suna tsaye gaban motar suna qoqarin shiga,saidai gurin ya kaure da hayaniya wanda kusan qananun fada ne da musu tsakanin saddiq da amna wanda dukkaninsu bakinsu baya iya shuru. Tuni Jordan yayi zaune mazaunin driver yana jira su kammala shiga "Anni tayi warning na kaiwa dare......i think wancan hamman naku yakai qararku an fitar masa da mata har dare.....oya guys.....hurry up muje mu dawo" Ya fada yana dan buga seat din motar,abinda ya sanya musaddiq soma shiga yana cewa amna. "Yau zai gane qaramin talaka ne....... Don't argue with him.......shigo auta" Musaddiq ya shiga maganan don ya kawo qarshen fadan. Juyawa amnan tayi ta miqawa sabreen wani baqin kati da yafi kama da atm "Matar oga.....yau ina jakanki.......ga wannan anni tace na baki,naki kudin tsarabar ne da boss ya saka miki kiyi siyayya". Bin card din tayi da kallo,ita bata taba ganin card ma irinsa ba,to amma kuma ita me zatayi da kudinsa?. Ko fitarsu jiya ma ba wani abu ta siya ba,amma duk da haka saida farouq ya cikata da siyayyar da ko budewa ma batayi ba. Hannu tasa ta karba card din kawai,ta daga qafanta tana niyyar shiga motar sautin musaddiq ya sauka a kunnenta "Wow........kallemin guy dincan" Ya fada yana tabo sadiq "Tashin sense" Saddiq ya furta yana kallon fu'ad dake tahowa. Cikin wani irin taku me dan sassarfa,sanye yake da wasu lafiyayyun suspenders da suka sake bayyana ainihin zallar quruciyarsa,suka kuma sake kwashe shekarunsa suka boyesu tas......saika rantse da Allah shi din sa'ansu saddiq ne. Saman kansa homburg hat ce data fidda kyakkyawar fuskarsa da wani irin kwarjini da kwantacenn kyau da zai iya gaya maka lallai shi din ruwa biyu ne da ake kira da halfcast. Sosai kayan suka zauna masa a jikinsa,rigan na dan bayyana muscles din da jikinsa ke dashi,wannan kadai zai gaya maka qaqqarfa kuma ginannen jikin da yake dashi. "Gayennan yana wuta.....anya ba zamu koma ciki mu canza dressing ba......kada maldivians dinnan su dauka age mate dinmu ne fa" Musaddiq ya fada sounding seriously. Dariya sosai amna ta fashe dashi tana dora kanta kafadar saddiq "An gaya muku ya fu'ad wai sa'anku ne?,ku sallama kawai ku huta......idan kanajin babban kifi to shine.......kunga maza kun raina kanku ko?" Dungureta saddiq yayi yana janye jikinsa "Zakiyi dariya da kyau ai......abinda ya kamata ki fara tambaya ko ki damu dashi shine dalilin da yasa ya fito.....ku koma ciki ba zaku je ba,ko ya fito ne mu fita tare kinga yau shikenan......ba sauran sakewa" Tsit dukkansu sukayi,saboda sunsan halinsa zai aikata da gaske. Kowa ya dauke wuta a cikinsu suna fargabar hukuncinsa,har zuwa sanda ya qaraso. Da ido kawai ya yiwa Jordan inkiya ya fito daga mazaunin driver din,ya zagayo kujerar me zaman banza ta kusa da driver ya shiga yana cewa farouq "Shiga mu tafi". Da kallo farouq ya bishi,har ya shiga ya zauna,ya daga idanunsa masu cike da kwarjini ya kalleshi yana daga waje "Ko ba zaka tafi bane ka tsaya kana kallona?" Kai kawai farouq ya kada yana tunanin abinda ya sauya ma fu'ad ra'ayi ya aminta da karan kansa zai bisu. Yau fitar dadinta sai taji baikai na jiya ba tun akan hanya,duk hirarsu suna kiyayewa da hayaniya ko abinda zasu fadi. Hira suke da farouq a gaban mota duk da batajin me suke fada,a haka suka isa guri na farko. Sunyi yawo sosai cikin kasuwannin da suke da kayan gargajiya na al'adun qasar Maldives.....sunyi siyayya kaman ba gobe,duk da bata taba komai daga card din da amna ta bata ba,hasalima a cikin mota ta barshi cikin handbag dinta da bata fito da ita ba. Gurare da yawa idan sunje zamansa yake cikin mota,dama shi din bai damu da shiga gurare irin wadannan ba. Koda sunyi tafiya guraren da yakanje gurare ne da suke da alaqa da kasuwancinsa,ko tarihi na kasuwanci ko kuma zai amfani kasuwancinsa,shi yasa yau din suka cika sosai da mamakin ganin yabi bayansu,duk da dukkaninsu kowa ya ta'allaqa hakan da sabreen ce sila. Guri na qarshe da suka je,suna fitowa ya miqa hannu ya karba key na motar daga hannun jordan "Zaka iya komawa gida" Yace dashi kai tsaye. Takawa yayi a hankali ya isa gaban motar,hannunsa daya zube a aljihun wandonsa,yasa hannu ya bude motar ya shige seat din driver. Junansu suka kalla tsakanin saddiq da musaddiq da amna,mamaki ya cika kowa ganin yau hamma da kansa zaiyi driving?,wani abu da suka jima basu ga yayi ba "Zaku shigo mu tafi ko na wuce abuna?" Ya leqo kansa yana magana dasu da miskilar fuskar nan tasa. Har rige rigen shiga suka dinga yi kowa mamaki kwance qasan zuciyarsa. Kaman yadda kusan komai nasa ya banbamta dana kowa haka tuqinsa,driving yakeyi cikin wata irin qwarewa da nutsuwa,gudu baiyi yawa ba......haka babu laqai laqai. "Ina muka nufa ne sir?" Farouq daya kula ya sauya hanya ya tambayeshi yana kallon fuskarsa dake a dinke tsaf. Shi kwata kwata ma guraren da sukaje kaman basu bashi walwala ba ko kadan. "Siyar daku zanyi na qara jari" Ya amsa masa a taqaice yana sake maida dubansa sosai ga titin. Dariya sosai farouq ya saki yana relaxing jikin kujerar motar "Hakan yayi ai......dadin abun bamu kadai ka debo ba ai" Yayi maganar yana turo p_cap dinsa gaba. Sarai ya gane me yake nufi,shi kuwa bazai kulashi ba,saboda neman wajen da zai dan sake samun relief kawai yakeyi. Sannu a hankali suka shiga Vaadhoo island sunan dake rubuce baro baro a allon sanarwa. Ihu amna keson saki na murna amma sanin wanda ke driving bayason magana me tsauri ko hayaniya ya sanyata danne bakinta ta dole tana duban saddiq dake zaune opposite dinta. Gira ya daga mata alamun tambaya,saita nuna masa map na inda suke ta qaramin screen din dake maqale a gefansu. "Vaadhoo.......glowing island!......sea of stars" Ta fada da wani irin farinciki daya lullbeta don sai a sannan ta lura da sun qaraso glowing island din. "Addana.......mijinki is very incredible wollah.......kinyi dace......kin dace....he's very calm,ya iya surprise,komai nashi unique ne" Ta fada farinciki yana kamata,farincikin yau zata ga inda ruwa yake haske......yashi da qasar gurin itama ke haske tamkar an watsa taurari,wannan yana gaya musu qila ya musu booking na kwana a wannan sabuwar duniya,ko kuma zasu kai dare a wajen suka yadda komai yake gudana. Murmushi kawai tabi amna dashi......babu wani abun burgewa tattare da yayan nata......itace dai bata sani ba. Amma kuma sai itama ta samu kanta da fara sallamawa al'amarin sanda suka isa adhaaran prestige,ma'aikatan wajen kuma suka iso suna maraba dasu,da alama sunsan da zuwansu wajen. Da idanu kawai take bin gurin,da gasken gaske ta zama 'yar qauye tuburan. Gidaje ko dakuna zatace saman ruwa da wani irin tsari me jan hankali. Bata da sauran abunyi illa bayansu da tabi kaman yadda taga sunbi daya daga cikin ma'aikatan saman wani shimfidadden abu daya zama hanya kuma abu daya da zai hanaka tafiya saman ruwan. Kai tsaye zata iya kiransa hotel ko gidan saukan baqi. Suka miqawa kowannensu wani dan card da komai da komai,sai amna ta daga kai ta kalleta bayan ta gama dubawa. "Ga inda zamu zauna can.....zamuci abincin dare a nan.......zami fita sea of stars muyi kallo harmu shiga idan da yiwuwar haka.....komai mukeso zamuje mu karba......amma adda naso kwana zamuyi......inama hamma yace mu kwana?" Amna ta fada tana duban sabreen da hankalinta yake kan ruwan dake gaban door glass din. Shimfidadden ruwa ne iya ganinka wanda yake bada kalan sky blue,abun akwai mamaki yadda mutane keta harkokinsu Kai tsaye suna kai kawo kaman cikin gidajensu suke. "Muje dakinmu adda" Amna ta fada da doki tana yin gaba,bayan ta fidda wayarta ta fara daukan hotuna da videos. Bata yiwa kanta da kanta qoro ba,idanu ta bude sosai tana kallo,yanayin iska da tsarin wajen ya banbanta da duk wani guri data taba zuwa. Gaba daya hankalinta a tashe yake,kaman yadda tunaninta yake a jagule waje daya. Iya zunzurutun dollars din data kashe don tsara komai,tun daga zuwanta Maldives da zamanta a wajen ba wani abu bane na damuwa muddin buqata zata biya. Bahaushe yace ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba. Ya zuwa yanzu da take zaune gaban glass door din tunani ne fal zuciyarta,tana jin kamar tayi wauta da take zaune tana lissafin zai wahala fu'ad din ya tsallake wannan island din ba tare daya shigoshi ba. Tayi zurfi cikin tunanin daya cika mata kwanyarta taji sn daneta daga baya gami da maqaleta da kyau. "You didn't missed your target......you hit it!" Wanda ke maqale a bayanta ta fada da murya me qarfi. A zabure ta cire hannuwanta daga wuyanta gami da waiwayowa gareta,tana jin abun kaman mafarki,idanunta dukka a waje take dubanta "Ki gayan gaskiya.....bazan iya jurewa ba idan kikacemin qarya kike" "Wallahi wallahi me jadda ya shigo......but shi da familynshi ne duka,but kaman dakuna daban daban ne" "Thank god.......ki miqawa wannan Chinese boy din wannan abun.......banason kuskure......after 30minutes zan shiga dakin,ya saka cameran daidai yadda zai nuna komai.......ya tabbatar yayi diluting tablet din a ruwa da lemonsa". "Done!......breaking news zaya fita zuwa ga Nigeria" Ta fada tana barkewa da dariya,yayin da fareeda ta tayata da qaramar dariya mata sauti. Juyawa tayi ta fita,sai ita kuma ta soma zame kayan jikinta da gagggawa tana wucewa wata siririn hanya da zai kaita toilet. Cikin qasa da minti goma ta fito,ta kuma tsaya a side din dressing ta soma balle wasu turaruka tana shafe lungu da saqo na jikinta,ta ware gashin kanta da kyau ta jiqashi da sassanyan qamshin turare,sannan ta bude wani jaka ta zazzage kayan ciki tana dagasu kafin ta fara shirya kanta a cikinsu. Wasu gantalallun riga da wando ne,very skinny,ba iya jeans din ba,har rigar data sanya. Ba wani sirri boyayye ko bayyananne da Allah ya wadatata dashi da bai fito ba walau qashi ko tsoka,me tudu ko me kwari. "Wow......wow" Taji an fada daga bayanta. Kadan ta juya tana kallonta don batasan ta shigo ba. Hannu ta watsa mata tana tambayarta alamun yayi? "Perfect.......kome kamun kan mutum ya ganki sai ya fada......ga kuma wadancan abubuwan na aikinsu yadda ya dace.......zance zaisha banban nan da nan......fatan nasara" Ta fada tana daga mata babban yatsa. Wani shu'umin murmushi ta saki tana takawa gaban madubin,ta sake juyawa sosai a gabansa tana qarewa kanta kallo. Ita kanta ta yaba da kanta ballantana wata halittar d'a namiji?. "Yadda bai sassautawa zuciyata ba bazan sassauta masa ba.......sai na tabbatar na zama cikakkiyar matarsa da shaidu na halas sannan zan barshi ya shaqi numfashi me kyau" Ta qarasa maganar tana daukan chewing gum ta jefa a bakinta tana duban qawartata "Sai na dawo?" Ido ta lumshe sannna ta budesu a kanta. "Inajin inama ace nice yau zan samu nasarar kasancewa da namiji irin muhammad jadda......koda bai aureni ba babbar nasara ce wannan a wajena......best wishes" Wani kallo fareeda ta watsa mata "To mayya........wata miyar ai sai a maqota,babban goro sai magogin qarfe kuma" Dariya ta sheqe da ita "Na sani qawata" Itama saita tayata tana ficewa zuciyarta fes yau din. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 73 73 Karo na uku ya sake daukan cup din yana kurban tataccen ruwan strawberry din da shine abu na farko daya soma zaba akai masa. Ya maida cup din ya ajiye yana zare belt din suspenders dinsa. Sosai gurin ya masa kyau ya kuma qawatar dashi,banda annin da suka baro a gida ita daya ba shakka ba abinda xai sakashi qin yanke hukuncin kwana a wajen,amma ko iya hakan ma nan da eleven yasan ya samu refreshment din da yakeso ai. Mamaki ya cikashi jin an murda qofar an kuma shigo,ya waiwaya yana tunanin saddiq ne ko musaddiq,saidai kuma fuskar daya gani tasha banban da fuskokinsu gaba daya. Da kanta ta fito don karbawa amna grilled fish dinta don girmamawa ga yarinyar yadda take kimantata da ganin girmanta,amnan tana da wani irin kirki da sauqin kan da yake bawa sabreen mamaki,don haka tace "Zauna addanki ne zata amso kifin nan da kiketa kwadayi". A gurin ta samu musaddiq shima zai karba nasa order din,wani tsari ne dasu akan grilled fish......zaka je wajen da kanka,zasu nuna maka inda kifayen ki ninqayarsu cikin ruwa ba tare da sanin kwanakinsu qayyadaddu bane,zaka nuna irin kifin da kakeso take a ciroshi a gasa maka a baka ka wuce. Kusan tare suka zaba aka kuma musu irin gashin da sukeso,musaddiq din ya miqa mata daya plate din hannunsa "Addanmu......taimaka ki miqawa hamma wannan please.....kunfi kusa da dakinsa....Allah yasa banyi laifi ba" Murmushi kawai tayi ta karba,tana mamakin yadda suke bata girma haka,bayan duk cikinsu idan ka dauke amna bata girmi kowa ba. Ason ranta tace ya taimaka mata ya qarasa masa dashi,to amma tana jin nauyin kasa masa alfarmar ko don yadda suke daukanta. A nutse take takawa tana duba dakin da take tunanin kamar ya shiga ciki. "Na gaya maka.....kana ganin kaman d wasa nake?......zanci gaba da kasancewa a kowanne taku naka......zan kasance cikin kowanne fitar numfashi da daqiqa naka.......makahon so nake maka.......i can't imagining yadda xan iya ci gaba da rayuwa babu kai". Tayi maganar tana karantar qwayar idanunsa. Tanaso ne komai ya kankama a jikinsa kafin takai ga cikar burinta.......tanason kowanne hankali yayi nesa da tunaninsa kafin ta aiwatar da komai. Wani qaqqarfan yanayi dake taso masa ya sanya ya kasa cewa komai. Kokawa kawai yakeyi da abinda yakeji din,yanason tabbatarwa da ba wannan qaqqarfan abun bane ke qoqarin motsawa?. Yana tsaka da wannan kokawar da duk wani control dake aiki a jikinsa ya tsinci fadowarta jikinsa,ta sanya dukka hannayenta ta masa wata irin bahaguwar runguma kaman zata shige cikinsa tana fadin. Sake kallon number dakin tayi da kyau,ta sake samun tabbacin shine,saita murza handle din tana murmushin hattararta da yadda ta iya gane dakin,ta tura qofan tana sanya qafafunta ciki. "I need you......i need you please jadda......kada ka juyawa zuciyar dake sonka baya.....ka bari na sauke maka abinda kakeji.......kaima kana cikin irin yana yina......na gani a qwayar idanunka" Kalaman da ta fara maraba dasu kenan kafin qwayoyin idanunta su sauka a kansu. Idan idanunta ba qarya sukayi mata ba fareeda khaleed mustapha ce cikin mummunar shiga.......dukka su biyun suna a tsaye,yayin data samu kyakkyawan maxauni a qirjinsa saboda tsahonsa daya shanye nata. "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Ta fusga daga qasan zuciyarta zuwa labbanta,saidai sautin baikai ga fita a sarari ba ta samu ta janye qafafunta ta koma da baya. Dukka jikinta bari yakeyi,abinda ya sanya plates din guda biyu duka suka kife ruf a qasa. "Sorry madam" Wata murya ta tsarga saman kanta,kafin ta dago ma har ya tsuguna yana kwashe duka plates din. Baya taja kawai ta tsaya tana qoqarin maida numfashinta daidai,don bata da wani qarfi na kwashe barnar da tayi sam. "Relax Sabreen relax mana.....fareeda dince baki sani ba?,ko fareeda dince bakisan yana bibiya ba?,sau nawa kikaga kiranta a wayarshi da luluqin dare?,me kudi ne fa?,yana da kudin da zai iya gayyatar ko wacce mace ta debe masa kewa......that's why aure baya a gabansa......karki yaudari kanki sama da haka ma zaki iya gani...." "And then waye shi a gurinki da zaki rude har haka?" Wannan gigitacciyar tambayar ta fado mata,abinda ya sanyata gayyato duk wata nutsuwa dake kowacce kafa ta jikinta ta azawa ranta tana duban matashin daya miqe yana dubanta da plates din a hannunsa. Cikin harshen turanci ya fara mata magana "Sannu ko?,muje su canza miki wani kifin" Duk da ba'a hayyacinta take ba amma koda ta dubeshi da kyau sai taji a jikinta mutumim africa ne,duk kuwa da cewa shi din ba baqi bane. Duk wani zaren tunaninta ya gama kwancewa,don haka bata da wani zabi illa binsa ta karbowa Sabreen wani kifin,saboda bata da abinda zatace mata idan ta koma dakin haka. Tana biye dashi yana qoqarin janta da hira da mata tambayoyin da bama iya amsa masa takeyi ba saboda yadda zuciyarta ke tsananin gudu. Hannunsa daya ya sanya ya yakice fareedan gefe zuciyarsa tana wani irin mahaukacin bugu. Fushi da feelings gaba daya sun hadu suna neman sauya tsarin bugun zuciya dana numfashinsa. "Wacce irin dabba ce ke?,a hankalinki kike kuwa?" Ya fada da wata irin tsawa data kusa tarwatsa duk wani plan nata......amma data tuna wannan shine plan dinta na qarshe saita miqe da hanzari tana cewa "Bazan taba iya qyaleka ba,sonka mahadin bugun numfashina ne....ka soni please.....koda na iya yaun....." Bata samu damar qarasawa ba saboda wani bahagon mari daya dauketa dashi yana huci,sai gata qasa warwas ta zube bayan ta tuntsura ta dawo ta zauna. Huci yake fitarwa sosai yana jin yadda jikinsa ke sake rikicewa "Daga yau ya zama na farko kuma na qarshe da kika sake shiga hanyata ta kowacce fuska.....if not.....zan batar dake ne a banza......idiot kawai mara amfani!" Yana kaiwa nan ya miqa hannunsa ya dauki key din motarsa da wayar dake ajiye tare dashi guri daya,bai kuma tsaya sauraron kukan data saki tana kiran sunansa ba ya sanya kai ya fice. Yana ji a jikinsa ba daidai yake ba,hakanan baya jin zai qara koda minti guda cikin island din ba.......kaman yadda bazai iya tsaiwa nemansu farouq ba,haka ya nufi hanyar barin wajen wani irin fushi yana lasar zuciyarsa. Kaman cikin gizo idanunsa suka sauka a kanta. Tana tsaye suna facing juna ita dashi. Ya miqa mata kifin da aka nadeshi cikin aluminum foil yana sakar mata murmushi. Bata da wani zabi da ya wuce maida masa martani duk da irin abinda takeji qasan ranta. "Thank you" Ta fadi tana juyawa. Taku uku kacal tayi ta tsinceshi a gabanta babu zato ba tsammani. Wani irin zazzafan kallo take tsinta cikin idanunsa.....wani kakkaifan kallo da kaifinsa ya zarce na takobi.....kallon da tsananin bacin rai yake da matuqar tasiri a cikinsa. Kallo ne daya tabata har cikin b'argonta ya aika saqo sassan jikinta,saidai girma da nauyin abinda ta gani qasa da minti biyar cikin dakinsa ya dakushe kowacce razana tata. Nata fushin ne yake tasowa wanda a dazu tsananin razana da tayi ya cakude da firgici ta rasa ainihin abinda takeji sai yanzu. Yatsansa ya daga yana nuna fuskarta,sai kuma ya sanya hannusa ya damqi nata hannun ba tare daya damu da plate din dake hannunta ba,ya finciketa da wata irin sauri daya qure yanayin adadin tafiyarta ta kasa daidaita tafiyarta da tasa,sai hadawa da tayi da sassarfa. Qoqari taketa yi ta qwace hannunta amma ko cikakken motsi ta kasa yi a hannunsa,kaman yadda bai saketa ba haka bai waiwayeta ba,har sai daya dangana da motar. Seat din gaba ya bude ya kuma sanyata a ciki ya rufe,sannan ya zagaya seat din driver ya shiga,ya tayar da motar d wani dan irin zafin nama,yayu reverse ya fusgeta da wani irin gudu na tashin hankali. Dimaucewa tayi gaba daya har sai data sanya tafukan hannayenta ta rufe dukka kunnuwanta. Ta kasa kallon titi ko sau daya saboda yadda jikinta yake gaya mata irin gudun da yakeyi da ita. Tsahon tafiyar mintina ashirin da sukayi bakajin komai sai qarar iska dake son kutse ta cikin window din motar. Birkin da yaja da wani irin qarfi shi ya kusa sakata tintsurowa daga nata seat din. Murfin ya bude ya fita.....ta dauka a nan abun zai tsaya amma sai taga yana zagayowa inda take zaune. Sake bude motar yayi,ya kuma cafko hannunta kamar dazu ya fito da ita,ba tare daya tsaya kulle motar ba yaci gaba da janta har zuwa cikin gidan. Suka ratsa veranda suka wuce parlor suka tuqe zuwa ga bedroom dinsu. Sai da sukakai tsakiyar dakin yaja burki yana sakinta da qarfi,ta turje taja ta tsaya tana haki idanunta a kansa. Haki yake yana nunata da yatsa,yana son yayi magana amma yadda zuciyarsa ke bugawa a jejjere cikin son wuce qa'idarsa ya sanya ya gaza fadin komai. Kaman daga sama ya fusgo kalaman "Da kowanne namiji ma tsayawa kikeyi?,kowanne namiji ma fuska kike bashi?,wacce iri ce ke!,nace wacce iri ce ke?". Wani kalan tashin hankali taji yana sauke mata saman kai,ta runtse idanunta ta kuma budesu lokaci guda fushinta na qara hauhawa.....wanne irin dan rainin hankali ne shi haka?,ta gaji!,takai maqura! "Daga rana irin ta yau ba zaki sake fita daga nan ba har sai randa zamu bar qasar nan.......zakita zama a dakin nan naga ta yadda zakiga wani d'a namijin,waishin kowa ma burgeki yakeyi?,kowa ma son kudinsa kike?" "Eh......kaman yadda kowacce mace take burgeka!.....kaman yadda kake shirya plan ka kama masauki kawai don ka hadu da wata!.......idan kaga namiji yana burgeni to tabbas shi din ba ragowar wasu bane.......ba sauran wata 'ya mace bane......isashen namiji ne da yake da abun bayarwar ba muna maza b......." Tun daga tsakiyar kanta jijiyar dake aike da saqo ta harbawa kwanyarta saqon KINYI KUSKURE!. Da wani irin hautsinannen yanayi ya waiwayo yana fuskantarta bayan kalamanta sun masa shamaki daga fitar daya fara niyyar yi "Me kika ce?......ragowar wasu?......mema kika ce rannan?,bani da abun baki ko?......kina tunanin zan hada jikina dake ne?. Araharki tayi yawa da ko da wasa ban sha'awar kasancewa tare dake,saidai a yau har cikin raina nakeji ya kamata na karbi sadakina......har kuma cikin raina nakeji ya kamata na banbance miki tsakanin ragowar wasu da wadanda suke da abun bayarwa dama wanda basu dashi.....tare da hakan ina me baqinciki da zaki zama mace ta farko da zata karbi budurcin muhammad fuad" Maganarsa taxo qarshe daidai da sanda shima ya kaita qarshe,ya kuma hadeta da bangon daya zama guri na qarshe da zata sanya qafafunta. Hannu daya ya saka ya soma tsinke button din gaban rigarta na sama,yayi wani irin tsalle yana fita daga gaban rigar tata ya fadi saman marble din dakin. Kafin tayi wani yunqurin ya sanya hannu ya tsinke na biyu,na uku ya biyo bayansa a jejjere da wani irin sauri idanunshi na kafe tsakiyar nata. Caraf ta kama yatsunsa tana riqewa da wani irin kalar tashin hankali,ganin button daya ya rage farar vest din dake manne a fatar jikinta ta bayyana. "Kada ke ketamin haddina......kada ka tab......" Kalmar keta haddin data fada ta zafafeshi da kyau,sai yaji kaman ta gama raina masa wayo. Shi daya biya sadaki shi ake kirawa keta haddi?,cikin qasa sa second biyu ya raba rigar da jikinta ya kuma tsinke hannuwan vest din jikinta ya zameta zuwa saman cikinta. A firgice ta nemi dunqulewa waje daya,saidai ya rigata ta hanyar lalubar tafukan hannayenta ya sanya nasa a ciki ya kuma kafesu da bango,har a lokacin cikin idanunta kawai yake kalla,yanason magana amma kowacce kalma ta gagara fita a bakinsa,yanason ya koya mata darasi fiye da yadda take tsammani,yanaso ya kashe bakin nan gaba daya,ta yadda koda da wasa akace mata ta yiwa wani me suna muhammad rashin kunya ba zata fara ba. Tsoron da yake gani a yanzu cikin idanunta ko kadan bai sanya a ransa na gaske bane,yafi kallon hakan da zallar rainin hankai kawai dason kad'ar da hankalinsa. Hannayen nata ya saki da sauri ya riao qugunta d wani irin zazzafan riqo,ya kawo fuskarta saitin tasa kafin yaja da baya yana sanya fuskarsa cikin wuyanta yana sauke mata wani irn numfashi me dumi daya gigitata lokaci guda. Ba ita daya ta gigice ba.....duk wani kwantaccen tsumi dake jikinsa sai daya motsa,ya kamo numfashinsa da qyar sanda ya cusa fuskarsa tsakanin breast dinta. Wani lallausan qamshi dake fita tsakaninsu yaqarasa wargaza lisaafinsa,ya kuma tayar da aikin qwayoyin da yasha ba tare da saninsa ba. Hannunsa ya sanya ya fara murza fatar jikinta,daga kafadarta zuwa yatsun hannunta sannna ya zurasu cikin nasa ya damqesu waje daya. Qafafunsa yaji ba zasu iya daukansa ba,baya so kuma ya rasa qarfinsa ko daya ko yaji wani softness akan hukuncin da zai mata. Yanason ya bata babban darasin da bazata iya gogeshi ba,yanason ya goge duk wani raini da take masa.....sassaucin da yake gwada mata yanason ta fahimci adalci ne irin nasa da ganin damarsa......daga qarshe yanason ya banbance mata karatun maza suna suka tara. Rabata yayi da qasa yana jefata saman gadon. Tayi juyi da zummar kifewa ta sauka a gadon da muryarta da take wani irin shaking "Banaso......nace maka bana so.....ni ba 'yar iska bace" Wani malalacin murmushi ya qwace masa tamkar wanda ya bugu sosai da kayan maye,wanj gefen na zuciyarsa kuma na masa ciwo da kalmarta. Auren nasa ne iskanci?,bayan duk wani yawo data gama yi lungu da saqo?,shi zata rainawa hankali ta nuna batasan komai ba banda ma lallai ta rainashi?,ai ya zama dole ya goge wannan rainin daga rana irin ta yau. "Zaki gane waye dan iskan gaske tsakanina dake" Ya fada yana tarota,yayin da rub da cikin ya zame masa kaman wata sassauqar hanya ta rabata da bra dinta,ya kuma birkitota idanunsa suna sauka akan qirjinta. Kaman an jona masa wuta haka yaji,a lokacin da take sanya duka tafukan hannayenta tana rufe qirjin nata kuka yana qwace mata. Baqinciki yadda ya tsiraitata yana kamata,bata tsira da komai ba sai fatar jikinta,siraran tafukan hannayen nata basu wani rufe abun arziqi a jikinta ba,sai ta fara yunqurin jawo duvet,abinda ya bashi daman kauda hannayen nata ya kuma maye gurbinsu da faffadan qirjinsa. _na gaji,tun safe nake qoqarin hada muku pages dinnan don na burgeku🥹,muje zuwa a gobe in sha Allah_ _wallahi wallahi duk wadda ta fitarmin da pages dinnan bazan iya yafe mata ba,yadda zata daukeshi ta fiddashi ubangiji ya qwace abunda tasha wahala a kansa daga hannunta🥲🥲🥲🥲_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 74 74 Nauyinsa gaba daya ya aza mata,abinda ya sanya numfashinta yin nauyi,yayin da nasa numfashin ya soma qoqarin yin qaura daga gangar jikinsa. Shi daya yasan kalar abinda yaji sanda farar jikinsa ta manne da tudun qirjinta. Karon farko a rayuwarsa da ya taba jin wani abu makamancin wannan.....karon farko da wani abu me kama da wannan ya taba gilmawa rayuwarsa. Baisan yadda zai iya controlling feelings dinsa ba a irin yadda wani magnet yake jansa ba. Hannunsa dukka biyun ya sanya ya riqe kanta cikin tafukan hannayensa yana kallon fuskarta. Idanunsa ya sauka akan pink lips dinta da suka sake zama pink sosai. Magana takeyi da alama amma kunnuwansa basa tantance abinda take fada. Motsasun da takeyi sai suka zame masa kaman wata tsokanarsa takeyi......shauqinsu ya kamashi sosai saboda irin nau'in siraran lips din da yake muradi ne......amma kuma sai wani abu yazo ya tsaye masa a wuya sanda zuciyarsa ta darsa masa "Ko mutum nawa ne suka dora bakinsu akai?" Yana kaiwa qarshen maganar ya dora lips din nata saman nashi,ya kuma lalubo na qasa ya riqeshi gam tsakanin harshensa. Kaman ya samu lollipop haka ya dinga sarrafashi,cike da wani irin zafin zuciya da yakejin yana watsuwa saman qirjinsa. Tun kwanyarsa na darsa mana adadin mazan da suka kai jikinsu da bakinsu wajen da duk hannu da bakinsa zaikai har ya birkice gaba daya. Zuciyarsa tayi wani irin rauni......rauni na baqinciki,bangare daya kuma wani irin zazzafan shauqi na azalzalar zuciyarsa. Komai kwanyarsa sai ya cakude......haduwar abubuwa guda biyu a gangar jikinsa duka lokaci guda,sai ya dinga ji kaman zai zaunce......kaman gangar jikinsa da qwaqwalwarsa ba zasu iya daukan komai ba. "Ka rabu dani......bace banaso......bana so......ka sakeni......ba 'yar iska bace ni" Maganganunta na qarshe kenan da yaji ta furtasu labbanta suna rawa kaman yadda kowanne sashe na jikinta yake rawa,idanunta sun fito sosai sun qara girma kaman yadda wani irin hawaye me dumi ya cikasu fal har ya gaza adanasu suka fara zirarowa. Labbanta qirjinta dama wasu sasassa na jikinta dukka radadi suke mata. Komai yana mata da wani irin zafi da zata iya kiransa na mugunta kai tsaye. Wani mahaukacin tsoronsa tuni ya gauraye jikinta da zuciyarta. Tsoron abinda ta fuskanci yana da niyyar yi.....wani abu guda daya wanda ko a irin mafarkan da mutane keyi ita bata taba mafarkin faruwarsa a kanta ba. "Why?" Ya tambaya da tasa muryar dake rawa kaman wanda kejin sanyi. Ya ware mata idanunsa da farinciki ya koma kaman an diga manja. Labbansa da suka sake zama red sosai shima dukkansu rawa suke,da alama akwai abinda yake da niyyar fada me nauyi daga zuciyarsa amma sunwa lips dinsa girman da lafazin ya kasa fita. "Why?!.....me yasa baki jirani ba?" Ya sake fada wannan karon a gigice sannan kuma a tsawace,kaman mawunyacin zaki. Tsawar tasa ta qara gigitata,ta rasa me ya kamata tayi sai kawai ta saki kuka. "You're just 25yrs old.....me yasa baki jira rana irin na yau ba?,waye da waye ya taba tabaki?.......na rantse sai nayi ajalinsu......saina kashesu!" Ya fada da wata birkitacciyar murya da zata tabbatar maka tabbas ba'a hayyacinsa yake ba......hakanan kuma fushine danqare a zuciyarsa. "Me yasa suka shigamin gona ta?,me yasa kika basu dama?,me yasa?......Bari naji meye sukaji?,bazan qyalesu ba!" Ya fada a zafafe cikin fitar hayyaci yana zamewa kadan daga jikinta tare da rage daidaita tsahon nasu da yayi. Hannunsa ya aza saman cikinta ya kuma fara saukar dashi zuwa qasan mararta. Wani numfashi taja me tsaho har wani rami dake qashin wuyanta yana lobawa ciki. Duk yadda hannayenta ke rawa batasan da sauran ragowar qarfinta ba sai da taji hannunsa a wajen da ba wata halitta data taba bari takai wajen ba,ta yiwa hannunsa mummunan riqo da muryarta dake rarrabewa. "Kk.....kak....karka....yimin haka......kayi haquri please,don Allah". "Ina da abun bakin ai?,baki sani ba?" Ya tambayeta yana dage dukka girarsa akan fuskarta rinannun idanunsa na qara girma. "Nas......na" "Shshsshshh" Ya fada tana dora dogon yatsansa akan lips dinsa yana ci gaba da duban tsakiyar idonta. "Don't tell me kin sani......zakifi ganewa idan kika gani a aikace...." Ya fada lokaci guda yana ture hannunta. "Don All........" Ta sake yunqurin masa magiya.....wannan karon kuka take da gaske,saidai baima barta ta qarasa ba ya maida gurbin maganar tata da cewa "Karkimin magiya ko ki hadani da Allah.......nima dan iskanne......ya kamata nabi sahun sauran ko?......but definitely saikin bambance tsakanina dasu......." Ya fada yana ture hannun nata da gasken gaske wannan karon,ya kuma maqaleshi a inda bata da damar motsawa. Tana jin sanda iska ta qara yawaita a gurin,alamun dake nuna hijabin dake wajen ya yaye. Ta runtse idonta da qarfi tana jin zuciyarta tana tsintstsinkewa gaba daya,wani abune da bata taba imagining ba kaf rayuwarta "Ban taba bawa kowa kaina ba.....ban taba bari ko yatsana an riqe ba.....na rantse maka......ka yarda dani" Ta fadi tana fata da yaqinin ya qyaleta,wanda ko a iya hala ya barta ta tabbata ya gama da ita......ya kalli jikinta yadda ranshi keso ta cikin hasken fararen qwayayen dakin,wadanda suka yiwa dakin qawanya tarwai kaman rana. Wai inji bahaushe yace ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,sam baima fahimci bayaninta ba.....don a sannan ba wannan bane a gabansa.........yanaso ne ya huce duk wani haushinsa a kanta......koda tayi mu'amala da maza million......yanason dasa mata stamp dinsa......wanda zata mutu tana tunawa MUHAMMAD JADDA daban yake da sauran maza,sau daya tak a rayuwarsa yakeson ya aje mata wannan tarihin da zai kasa goguwa a ranta,daga rana irin ta yau bayajin xai iya sake bin hanyar da mazan da basu da adadi suka bi. Randa tace masa baida abun bayarwa......ragowarsu fareeda,tsananin kai zuciya nesa kawai yayi.......a daren yaso yayi mata yadda ba zata sake marmarin bin wani d'a namiji ba.....amma a yau yana jin zai tattara mata duka hukuncin da ko maza dari ta taba bi tabbas sai gabbanta sun gaya mata. Maidata yayi jikinsa gaba daya,ya manneta cikin jikinsa da wani irin tsatstsauran riqo kaman zai ballata. Hatta da bakinta sai daya kasheshi tas ta hanyar sakayashi cikin nasa bakin dake fidda qamshin mint leaves,yadda numfashinsa ke fita da dumi sosai yake ratsa qofofin hancinta yana aikewa qwalqwalwarta wani irin saqo me rikita lissafi,matsanancin tsoro ya shigeta na yadda a yau komai nashi da nata suke gauraya waje daya......yawun bakunansu.......numfashinsu,dumin fatarsu dama laushinta,qamshin jikkunansu na lausasan turarukansu dama komai da komai. Cikin tsakiyar wannan firgicin......tana tsaka da tunanin mafita ta tsinci baqon abu yana wanzuwa a jikinta.......baqon abu mafi gigitarwa da debe hankalin diya mace musamman a sanda bata tsammaceshi ba. Wani irin azaba ta ziyarci kwanyarta irin wadda bata taba ji ba,duk da bakinta toshe yake da nashi amma hakan bai hana wani irin gunji fita daga hancinta da bakinta ba,ba wata kalma data samu daman fita.....amma gunjinta abune da idan kana dab da dakin kana iya tsinkayen motsin fitarsa. Yadda yake samarwa kansa gurbi a hanyar da wani yanayi da yayi masa kama da sabon muhalli sai abun ya gigitashi da wani irin mamaki. Zato yake daga gareshi ne......baiyi yadda ya dace ba,don ko a mafarkan da ya sha yi bai taba darsawa a ranshi zai samu wani abu me kama da sunan budurci watk virginity a tattare da ita ba,don haka ya sake mata dukka qarfinsa ya kuma soma samawa kansa hanya da dukka kuzarinsa zuciya na gaya masa ya fanshe duk wata kebewarta da wani d'a namiji karon farko kuma na qarshe kaman yadda ya tsara hakan ya kasance. Sake gigicewa tayi da kalar azabar da takeji "Ban taba yi ba......ka qyaleni!" Abinda takeson ta fada kenan amma bai bata daman haka ba. Ci gaba yayi da abinda ya saka a gabansa,yana jin wani irin yanayi da bai taba tsintar kansa a ciki ba yana mamayarsa. Yana sake kutsawa yana sake shiga mamakin abinda yaketa taraswa din,wani irin abu yakeji saman kansa me kama da hauka......kowanne hanya da kunnuwansa zasu isar masa da wani sauti har yakai ga kwanyarsa don ta tantance abinda ya dace yayi da wanda bai dace ba.....limit din daya kamata ya tsaya da wanda zai wuce dukka sun toshe,wata duniya daban ya zarce wadda baya ganin komai kuma bayajin komai.......daga shi sai abinda ya sanya a gaba kawai. Komai ya qarasa kwance masa sanda ya tabbatar ya gama bude kowacce hanya ya kuma kai qarshe,ya fara aiwatar da komai da wani irin tsumammen kuzari da bai taba tunanin ya jima haka a ajikinsa ba. A lokacin ne shima komai ya qarasa kwance masa,bakinta da yake rufe dashi ya gagara ci gaba da riqonsa ya sulale yana cusa fuskarsa tsakanin wuyanta da qirjinta. "Hammm.......hammmmmmmmmaaaaaa" Ta samu kanta da fadi da wata lanqwasashiyar murya tana jin kaman mala'ikan mutuwa ne yake saukar mata. "Yaaaaafffff......fffuuuuu......hammmmm" Ta sake hado kalmomin da zummar tsaidashi ko bashi haquri tana ji a ranta wataqila taci nasara ya saurareta,wataqila ya sassauta mata azabar da yake gana mata komai girman laifinta a gurinsa,wataqila ya.mata wannan alfarmar karon farko data taba neman alfarma irin wannan a wajensa.......saidai kuma inaaaa........wani azaba daya ratsa tsakiyarta sai dukka kalaman suka subuce mata,numfashinta kuma ya qwace mata.....duhu ya ziyarci idanuwanta da kwanyarta. Yaji ya kuma ga kaman haruffan sunansa akan labbanta,saidai baisan ainihin abinda bakin nata ya fadi ba. Duk da ya fahimci inda komai ya dosa yana kuma ta qoqarin controlling kansa amma ya kasa.......ya kasa yiwa kansa waigi.......ya gaza tsaida kansa ko saisaita kansa koda na minti daya,bayajin kuma akwai wani abu dake da qarfin daidait nutsuwarsa a daidai irin wannan lokacin. Wani irin sabon kuzari yakeji a jikinsa da bai taba jin irinsa ba.....wani sabon qarfi yakeji tattare dashi,yana jin kaman akwai inda yakeso ya isa,akwai inda yakeso yakai dole dole......kaman idan bai isa wajen ba zai iya mutuwa.......kaman idan bai qarasa muhallin ba akwai wani abu maras kyau da zai iya faruwa dashi,yana jin wani abu can kusa da ransa dama zuciyarsa gaba daya,yana jin yadda yake shawagi cikin wani sarari da baisan iyakar fadinsa ba. Wulgawar wani second cikin tunani da lokacinsa da wani irin gigitaccen yanayi shi ya dawo da hankalinsa jikinsa. Wani irin numfashi me dauke da wani irin sauti kamar numfashinsa yana shirin barin gangar jikinsa ya sauke......saukar numfashin da tafi kamanceceniya da gurnanin zaki,kowacce gaba a jikinsa ta saki ya aza mata dukka qarfinsa wani zazzafan gumi naci gaba da keto masa ta kowanne kafan gashi dake jikinsa. Qin sakinta yayi ko ya raba jikinsa da ita.......yana jin kamar idan ya matsa koda kuwa Inches biyu daga gareta zata bace masa......yana jin ko yaya ya motsa kadan zata iya subuce masa,yana jin kamar motsinsa yana iya sanyashi ya rasata. Wata qaqqarfar runguma yayi mata cikin ni'imtaccen ingarman qirjinsa. Jiqaqqen gumin dake tsakanin sumarta goshinta da wuyanta gaba daya ya dinga gangarowa yana cakuduwa da nasa,scents na turaren jikinsu ya sake zama wani irin me sanyi tsananin jikkunansu. Wani irin ni'imtaccen qamshi yakeji yana tashi daga jikinta.......qamshin daya zamewa hancinsa na daban,irin qamshin da zai iya rantsewa bai taba jin abu me dadi a hanci irinsa ba......all over her body ko ina idan zai iya tunawa wani irin qamshi me laushi yake fitarwa. "Dama haka matan suke?" Ya tambayi kansa yana qiyasta adadin shekarun daya dauka yana zaluntar kansa ta hanyar haramtawa kansa wannan nutsuwar da wannan ni'imtacciyar rayuwar. Tunaninsa kaf ya dawo da baya da baya har zuwa sanda ya fara maidata mallakinsa.....har zuwa sanda ya fara keta gonar tasa. "She's a virgin?" Labbansa suka motsa ya furta a fili saidai can qasan maqoshinsa,tamkar dai yana tsoron fada,tamkar dai yana tsoro kada kowa yaji. Yanajin yadda maqogoransa gaba daya ya soye kaman ba wani sauran yawu daya rage a jikinsa. Wani qaqqarfan abu yaji yana mamayarsa bayan wani irin nauyi da yaji tamkar ya sauka tsakanin qirjinsa zuwa mararsa. Yana jinsa yayi wani irin sakayau tamkar ma idan ya miqe iska zata iya dibansa ta watsar. Wata irin nutsuwa da bai taba cin karo da irinta ba ke ratsashi,kaman sabuwar iska sabuwar rayuwa da kuma sabon ruhi aka bashi. Yana jin wani yanayi na daban na musamman na mamaye ilahirin bargo da jininsa. Idonsa ya runtse da qarfi yana fadin "How did it turn out like this?,what's the story behind this??" Ya sake maimaitawa kaman me tsoron kowa da komai,kaman bayaso kowa yaji fitar sautin daga bakinsa. Kwanyarsa na cakudewa da kalolin tunanuka iri daban daban,negative da positive dukka lokaci guda. Dif!. Kowanne lantarki dake kansa ya dauke ya daina aiki na wasu sakanni kafin kuma a hankali engine din karbo saqo da aikewa ya soma motsawa yana dawowa saitinsa. Fuskarta da yanayin reaction dinta kukanta dukka hade da magiyarta lokacin da yake yunqurin kaiwa bangon da yake muradi.......yadda labbanta suka dinga motsawa.....yadda oily eyes dinnan da bai taba lura da tsananin haskensu da sheqinsu ba irin yau suke jujjuyawa cike da tsoro firgici da razanin kasancewarsu abu guda "Wannan shine tsoron da akan gani idanun kowacce d'iya mace a darenta na farko......ranarta ta farko da zata fara sanin d'a namiji?" Ya tambayi kansa sannan ya amsawa kansa da cewa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 75 75 "Yes...yes" Zamewa yayi daga gareta yana rage mata nauyin daya aza mata. Tafukan hannayensa gaba daya ya sanya yana qoqarin dago fuskarta da sumar kanta ta zame labule a tsakaninsu,fiye da rabin hankalinsa yana kan dukiyar fulaninta da suke wani irin fusgar hankalinsa suke sanyashi jin kaman ya qare rayuwarsa a tsakaninsu ba tare da ya motsa ko ina ba. Hannu ya sanya ya yaye sumar data rufe fuskartata jikinsa gaba daya yana rawa ya kasa samun daidaito. Tari Tarin abubuwa keta kutse cikin tunaninsa suna fara masa tilawa.....tun daga randa furucin farko ya fara hadasu da ita,yanata qoqarin tuna abinda ya soma gaya mata.......yanata qoqarin tuna da wanne harshe yare ko lafazi zaiyi amfani ya fahimtar da ita HAQURI bisa Tarin kalamansa marasa dadi da ma'ana wadanda baisan adadin yawansu ba. Da wata irin martaba kima da darajarta da sukayi masa fadowar bazata cikin tsokar zuciyarsa,suka cakuda da kowanne digon jini dake yawo cikin jikinsa yakai fuskarsa saman tata ya hadesu guri guda,hancinsa ya saitu da kyakkyawan hancinta me tudu da tsaho. "Am.....soo.....amsor....." Yayita qoqarin maimaitawa yana jin wani matsanancin ciwon kai daya saukar masa lokaci daya. Sai ya zame kansa ya saukar dashi a kafadarta yana cusa fuskarsa cikin wuyanta. Yana ji ne kaman ya zama wani irin ragon mutum kuma rarrauna......yana jin kaman kuka yakeso yayi ko zai sake rage nauyin dake cikin zuciyarsa. "Ya akayi na zama haka?,how?" Ya tambayi kansa,kafin kuma a hankali ya dora labbansa saman kunnenta cikin salo na rada. "Can you hear me.....am sorry......i didn't mean to......to" Sai ya kasa qarasawa saboda bugun numfashinsa daya tsaya cak lokacin daya fahimci babu fitar numfashi sam a hancinta. Fuskarsa ya sake kaiwa daidai hancinta,da gaske ba fitar numfashi sam sam a tattare da ita,wani abu da yazo masa a tsananin ba zata ya sanyashi gigicewar da har baisan sanda ya kira sunanta ba "Sabreeeennn" Ya furta yana tashi sosai hannayensa dafe da gadon,saidai kuma danshin da yaji cikin tafin hannunsa ya sanyashi kai idanunsa wajen ba shiri. "Jini?" Ya furta yana sake fidda idanunsa waje,ya fadi kalmar ne kamar me tambayar kansa da kansa,kamar kuma me bawa kansa da kansa tabbaci. Da sauri ya saka hannu yana jawo comforter din da rabin jikinta yake a rufe rabi kuma take kai,take ya saketa don bazai iya kallon yadda lafiyayyen jan jini ke kwance a jikin farin comforter din ba,jikinsa ya dauki rawa gaba daya......kai kace ba shine mamallakin kamfanin diamond da gold dinnan ba.....kai kace ba shine Muhammad jadda dake razana zukatan maza ba......kai kace ba shine dan gwagwarmayar nan ba.....hustler na gaske wanda baisan tsoro bs bare maganan ja da baya....yakan iya sanya qafarsa kan kowanne bigire ko mataki da ake fargaba saka qafa saboda hatsarinsa....yana fafata da koma waye komai hatsarin dake tattare dashi......yau sai gashi labbansa na sama dana qasa suna haduwa ya gaza koda ambatar sunanta. "Me ka aikata haka fuad?,me ka aikata mata?" Ya fadawa kansa da kansa da qarfi yana sanya tafukan hannayensa dukka biyun yana kama kansa da kyau. Sauka yayi daga gadon da gaggawa yana nufan fridge din dake killace a daya daga cikin corner din parlor din ya bude. Sassanyan ruwa ya fiddo,ya dawo saman gadon yana tattarota cikin duvet din da shi kansa yayi bala'in staining sosai ya azata saman cinyarsa. A cikin tafin hannunsa ya zuba ruwan ya soma shafa mata daga fuska zuwa wuyanta. Sau uku kenan yana yin hakan.....amma ba wani motsi da tayi. "Oh my god!...." Ya fada yana wurgar da gorar ruwan ta fadi qasa ta fata tsiyaya. Fuskarsa ya kafa saman nata fuskan,ya riqe hancinta ya kuma bude bakinta ya soma bata iska ta ciki. Mintuna kadan yaji taja wani irin numfashi da ya tsarga mata har tsakiyar cikinta kafin ta fiddoshi,dagawar qirjinta ya alamta masa dawowar numfashinta,sai ya miqe yana duban fuskarta da tayi wani irin jawur idanunta da suke a rufe suka nuna dagawarsu. "Sabrrrrrr" Ya taqaita sunan nata saboda fitar hawaye daga rufaffun idanunta suka kuma gangaro ta gefan kunnenta. "I was wrong to do that......How can i make it right?" Ya fada yana jin hankalinsa na sake tashi. Bay qaunar kuka sam sam sam,musamman kuka na diya mace. Daya daga cikin abinda ya dinga daga masa hankali lokacin quruciya kukan musaddiq......kukan musaddiq a duk dare sanda maamah ta tafi ta barsu.....kukan abbansa sai ya zama abu mafi tsanani da azaba daya taba gani.....wadannan abubuwan suka sanya ya tsani kuka ainun.....duk da yana da tsananin dakiyar nuna bai dameshin ba. Hannunsa ya dora saman goshinta don cire mata gashin daya sake lullube mata goshin,yana jin kowacce kalma ya debo saita qwace daga bakinsa.......yanajin duk duniya ba wata kalma harshe yare ko lafazi da zaiyi daidai da kunnuwanta idan ya fadesu......shi a karan kansa yakejin kamar ba'a qirqiri wata kalma ta ban haquri da ta dace ko zata dace da girman laifinsa ba. Da sauri ya janye hannunsa yana jin yadda fatar jikinta ke fidda wani irin huci kaman yadda jikinsa ke fitarwa "Ya salam.......ya salam......am sorry,i hurt you sabrrr......Am sorry.....i hurt you,I'll do everything possible to make you feel better" Ya fada yana neman yadda zai gyara mata zamanta a jikinsa. Jinginarta a jikinsa jinta take kaman wani nau'in azaba na daban,batasan yadda wata rai zata fahimci yadda takeji ba.....tana jin kamar zata sake suma ne,don numfashinta sam baya kaiwa hunhunta yadda ya kamata. Tanaso ta gaya masa ya janye jikinsa daga nata amma ba wannan bakin,sai kawai kukanta ya qaru akan nada,abinda ya sake hargitsashi kenan. A zahirin gaskiya baisan yadda zaiyi mata ba don baisan yadda akeyi ba,hasalima shi bai taba zama yayi tunanin zuwan rana irin wanna ba a nan gaba a rayuwarsa bare ya nemi ilimin yadda akeyi ba. Jikinsa ya zame yana jin yadda zazzabi ke dafa qasusuwansa......amma tashin hankalin jinin da yake gani daga jikinsa ya dame wannan. Wayarsa ya dauka,sai ya samu kansa da rasa wanda zai kira.....wazai kira?,wa zai gayawa?,yace masa me?. "Farouq" Kawai shine sunan daya fado masa. Bai damu ba da yadda farouq din zai kalli abun.....abinda kawai ya dameshi yadda zai ceci ranta daga ta'addancin daya tabbatar yayi mata. Idan ya daga kai ya kalli inda jinin ke kwance sai yaji ya aikata baqin fasadi ne kawai yau a daren nan,qaramin kisan kai kawai yakeji ya aikata. "Hello......zamu kwana ne....wajen nan fa yayimin,ina tunanin dawowa nida fannah....." "Am at home" Kawai ya fada da wani irin sound da yaja hankalin farouq din. Aje yanayinsa yayi gefe da wasan dake cikin muryarsa ya bawa fuad hankalinsa "Is something wrong?" Ya fada da tsananin kulawa a muryarsa. Sai daya runtse idanunsa sannan ya budesu yana maidasu inda take kwance sannan yace "Yes farouq......a rude nake.....please help.....i don't know what to do" "You are not alone......am here to help,take your time and tell me what's happening?" Farouq ya sake fadi cikin yanayin kwantar da murya. "We had our first night farouq......i caused her serious injury" Ya fada da tsananin nauyin abinda yake fita daga bakin nasa,saidai kuma ya zama dole yayi hakan,don gani yake kaman tana dab da komawa sumanta. Wutace ta daukewa farouq din. Shima maganan ya masa dan nauyi kadan,duk da ya jima da sanin duk wadda zatayi irin wannan karon da fuad din abun bazai zama da sauqi ba. Don ya bashi relief sai yace. "Relax....ina zuwa". Yana sauke wayar daga kunnensa. Murmushi kadan ga qwace masa duk da qasan ransa tausayin adda sabreen ne fal. Yasan za'a fuskanci hakan daga fuad din,duk da tsananin wayewarsa da sanin lunguna da saqo na qasan duniya.....gogewarsa da mmu'amalarsa da kalar mutane daban daban jinsi daban daban......amma yau saboda tsananin kamewarsa da zame kansa daga dukkan wani batu ko sabga data shafi wannan fannin ya rasa yadda zai taimakawa matarsa. A ransa yaji tabbas ciwon ba qarami bane tunda yaji damuwa sosai a muryarsa. Ya jima yana kallon number wayar anni ta qasar yana kwatanta yadda zai kirata ya gaya mata. Wannan din wani training ne nata data musu. Ko.meye nasu idan ya samesu komai nauyinsa bata yarda wani ya fara jibantar matsalarsu ba kafin ita bare a nan din baisan waye zai kira ba,dole ya koma ya shiga sms ya tura mata saqo kaman haka. _"Muhammad yana dakinsa......he needs your assistance"_ yana tura mata ya aje wayar,don bayason ta kira neman qarin bayani don wabillahi baisan ya zai mata shi ba. Tsaiwa cak yayi kuma wani abu yana dawo.masa da baya. "Ya akayi first night yazu musu da hakan if ba virgin bace?" Ya raya maganar a ransa,sai kuma yayi saurin kawar da ita don shi ya jima da qaryata duk wani hasashe na fuad tun ba yau ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 😀😀😀😀😀 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 76 76 Sanda saqon ya iski anni dawowarta gidan kenan,tazo ta samu gidan ba kowa basu dawo ba. Daki ta wuce ta sauya kaya ta dauki wayar tana fitowa parlor da zummar kiransu taji me ya kaisu yin dare bayan tayi warning dinsu kan hakan kafin su tafi?. Jiya sam bataga sukuni ko walwala saman fuskar fuad ba,kuma tana ankare dashi,yadda ya kasa ya tsare a falon,bai koma daki ba sai bayan dawowarsu. Tasan yana da zurfin ciki sosai,ba kasafai ka fiya sani ko gane abinda yake damunsa ba,amma ita din uwace,koda wanne yare sukayi magana su dukkaninsu tana iya fahimtarsu. Shigowar saqon ya dakatar da ita daga qoqarin kiran nasu da takeyi "Wani sabon sakarcin ne kuma haka?" Ta fada tana zama saman kujera da gorar ruwan dake hannunta ganin me saqon farouq ne. Sau biyu tana maimaita saqon,tasan tunda ya fada da gaske fuad na cikin gidan,duk da bataji alamun akwai kowa ba a ciki,amma sai kuma saqon yaja hankalinta. Cikin fargabar kada wani mummunan abu ne ya faru dashi ta ajiye gorar ruwan tana maida hijab din jikinta,ta miqe idanunta kan qofar dakin,ta taka a hankali ta isa qofar. Knocking ta fara yi,knocking din farko ya sauka kunnuwan fuad dake tsugunne gaban gadon yana monitoring numfashinta,gani yakeyi ko yaya ya matsa zai iya sauke idanunsa a kanta ya tarar ba numfashi tattare da ita. "Waye?" Yayi namijin qoqarin tambaya "Anninku ce" Ta fada a nutse. Idonsa ya lumshe ya kuma bude duka lokaci daya yana furta "Rabbi yassir wala'ta'asir.....ya salam sallim" Yana jin kaf rayuwanshi idan ka debe rayuwar da maamah ta jefasu y taba shiga tashin hankali irin na yau ba. Baisan ta yaya zai bari anni ta shigo ta gansu a haka ba duk da zuwa yanzun ya saka Moroccan jallabiyya a jikinsa tun sanda ya kira farouq. Ita dince sam jikinta yaqi tabuwa masa,da yakai hannu kusa da ita sai maga ruwan hawayen dake idanunta yana qaruwa,ba bakin magana sam sam a tare da ita,amma duban data masa guda biyu tal ya karanto wani irin fushi da kyara a tattare da ita. "Ki taimaka please.....ki bari ko riga na saka miki" Wani fusataccem fushi ne ya sauko mata,ya saka mata riga bayan ya gama ketata ya kuma keta haddi da duk wani mutunci nata da take taqama dashi,ta kuma killaceshi tsahon lokaci?. Yadda ta maida idanunta ta kulle ba tare data ko motsa ba ya tabbatar masa bata buqatar ganinsa ne gaba daya,ga anni na tsaye a qofa dole bazai yiwu ya barta tanata jira ba,haka ya doshi qofar can qasan ransa yana fadin "Me yasa kayi haka farouq?" Yana qiyasta da wanne idanu zai daga ya kalli anni?. Fuskarsa kawai ta kalla da yadda ya bude qofar cikin rashin karsashi tasha jinin jikinta. "Kana lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da ido. A yau dai ko karen hauka ne ya cijeshi baya jin zai iya kallon idanun anni bare ya mata bayani. Ratsewa yayi gefe da alamun bata hanya. Itama batace komai ba,ta maida dubanta ne daga cikin dakin tana hango iya abinda zata iya gani din wanda carpet ne da dressing mirror kawai take iya gani,sai ta maida dubanta kan fuskarsa da a yau yakejin idanun anni tako ina a kansa da wani irin nauyi. Batace komai ba itama ta ratseshi ta soma takawa cikin dakin,wanda taku biyu kacal tayi shi kuma ya fice yana laluben inda zaije ya aje kayan kunyanshi nesa da annin,saidai a taku na hudu idanunta suka sauka akan Sabreen,jinin dake jajur yayi staining jikin duvet da comforter din ya marabceta,cikin qasa da second uku ta fahimci me ya faru. "Subhanallah" Ta fadi tsigar jikinta yana tashi. Tasan ko meye ya faru a wajen artabu akasha ba kadan ba,ko tayi taurin kai yaje mata da dukka qarfinsa,qarfin da sam sam tsakanin nata da nashi baizo daya ba. "Muhammadu......maida qofar nan ka rufe" Annin ta fada da madaukakin sauti sanda yake dab da bakin qofar parlor din. Cak ya dakata da abinda yakeyi din,ya maida qofar ya kulle kaman yadda anni ta buqata,ya dawo kuma a hankali cikin parlor din yana laluben wajen zama. Gangar jiki duka da zuciya sai yakejin kaman ba tasa ba,zafin zazzabi yana ci gaba da lullubeshi yana raunana jikinsa,saidai yadda kunyar anni ta rufeshi tafi masa nauyi akan zazzabin. A mamakance take isa gaban gadon "Ikon Allah" Tafada qasan ranta,wato ita dake lissafin ganin result ta hanyar dauka jika,ashe karatunma sai yanzu aka farashi?. Sautin muryar anni cikin dakin sai tayi fatan inama qasa zata tsage ta wuce ciki?,yanzun yana da tsaurin idanun kiran ummansa taga barnar da yayi?,wanne irin terere ne wannna yaja musu?,anni fa.....anni,ya manta surukarta ce?,ya manta akwai kunya me girma tsakaninsu?. "Subhanallah......ya salam" Anni ta.maimaita wannan karon a sarari saboda jinin data gani muraran daya wuce wanda ta hanga daba bakin qofa. Dukka jikinta yayi sanyi sosai,ta tabbata babban barna muhammad din yayi. "Sannu......tashi a hankali ki qarasa bandaki" Anni ta fada tana kamata da tsananin takatsantsan ta yadda zafin ciwukan jikinta ba zasu dameta da yawa ba. Wata siririyar qara sabreen din ta saki,qafafunta kuma suka lanqwashe tilas ta koma ta kwanta duk da anni riqe take da ita. Hawaye ne ke fita ta gefen fuskarta,tsananin tausayinta ya kama anni. Bata taba kawowa muhammad xai gwada rashin haquri irin haka ba,dole yarinyar tana buqatar motsawa ta gyara jikinta kafin ma a samu bakin zaren gane iya adadin barnar data afku. Yana daga falon amma.yana iya hangensu saboda a bude anni tabar qofar,uwa uba yana zaune saitin wajen,saidai yayi kaman bashi a wajen. "Muhammadu" Anni ta kirashi kai tsaye,ya amsa yana tasowa. Idanunshi a kanta yana sauraren bayanin anni. "Akwai ruwa me dumi a toilet.......ka kaita ta gyara jikinta tukunna.....ina zuwa" Anni ta fada tana nufar qofa don itama zuwa yanzun kunyar ke neman kayar da ita. Hakan yayi masa,yabi bayan annin ya maida qofar ya murza key,sannna ya tako zuwa ciki yana nade hannun rigarsa. Sai yanxu kwanyarsa ta fara dawowa aiki,bazai kuma saurareta ba zaiyi kaman yadda anni tace,zaiyi yadda ya dace,dom haka yana qarasawa gabanta ya sanya hannu ya dauketa cak kaman jaririya haihuwar yau,ya lullubeta cikin qirjinsa yana wuce toilet din da ita. Yana jin yadda ta damqe hannuwansa da kyau,da alama haushin dake cikin zuciyarta ne takejin kamar riqon tsaurinta a garesa zai sassauta abinda labbanta da bakinta ba zasu iya fada a yanzu ba. Sake yaye mata dukka suturar jikinta yayi,ta sake runtse ido abun yana mata zafi. Cikin wasu mintuna jikinta ya zama bayyananne a wajensa?,yana qare mata kallo haka kanshi tsaye da kaifafan idanunsa da takejinsu a kanta?. "Bazan kalleki ba indai har bakison hakan.....zan kulle idanuna har saikin bani izinin na budesu" Haushi da takaici suka lullubeta,harara takeson jefa masa zazzafa amma bataji idanunta suna a daidai din da zai ga harara tata yadda ya kamata. Banda ya raina mata wayo yana tsare yana qare mata kallo da wani irin yanayi dake qara kashe masa gangar jiki.....amma kuma yana gaya mata zai kulle idanunsa?, daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa ta furta a ranta. Sake dagata yayi cak ba kuma bata lokaci ya sakata cikin bathtub din da anni ta hada ruwa me dumi qwarai. Wahalalliyar qara ta saki da muryarta dake nuna duka qarfinta ya qare. "Ka sakeni....ka cireni a ciki" Ta fada hawaye na layi bibbiyu akan fuskarta. Wani irin narkewa zuciyarsa tayi da tsananin tausayinta da bai taba jin irinsa akan kowacce diya mace ba idan ka cire anni da amna. Saidai ko kafin ma yayi mata yadda tace ta sake masa wani zazzafan cizo a hannunsa dake dafe da tub din. "Ouch!" Ya fada yana runtse idanunsa saboda tsananin cizon data sakar masa. Ware manyan idanunsa dinnan yayi a kanta bayan ya budesu,idanun da bataji komai tsahon xamani zata iya mance memory din daya aje mata a yau. Labbansa ya motsa yana jin zafin zazzabin har cikin idanunsa,to amma yanayin daya sakata a ciki yafi komai da yakeji ciwo. Ya sani ya shigeta ne da duk wani qarfinsa,yana tsammanin samunta budaddiyar hanya ga kowa......sai abun yazo masa a wata irin bazata a sanda bazai iya controlling din kansa ba kuma "I'm truly sorry for the pain I've caused" Ya fada da wani irin calmness cikin muryarsa,sai ya sanya hannu yana cirota daga bathtub din,yana jin bazai juri barinta tana jin abinda takeji din ba......baisan girman pain din ba bare ya kwatantashi,saidai koma meye ya tabbatar radadinsa ya wuce wasa. Bedside drawer ta isa tsigar jikinta na sake tashi gana girgiza kai da jinjina barnar data tabbatar ba qarama yayi ba,wayarta ta dauka ta duba last call dinta. Qawarta da suka rabu dazu hajja saudat ta kira. "Kuna da wata gynecologist ne mace da zata iya home service kuwa?" Anni ta tambayeta kai tsaye. "Eh akwai.....'yar qasar syria ce.....tana da kirki sosai fadwa haleem". "Na gode.....kimin magana da ita please,ki bata address na gidana.....if possible tunda bamu da nisa kada ta wuce one hour" "In sha Allah kusa muke ai" "Na gode" Anni ta fada tana katse kiran. Farouq ta koma kira,saidai kira har biyu bai daga ba,sai ana ukun sannan ya daga yana sosa kai. "Ku kwana a can,ku biyasu kudin kwana daya.....but kakaimin amna gidan saudat acan nakeso ita din ta kwana" "Okay.....in sha Allah" Farouq ya amsa shima yana jin dadin hakanma da tace,don shi kansa a yanzu ji yake ya zama surukinta,ina ga fuad din. Yadai tabbatar ba zasu qarke lafiya ba idan ya dawo hayyacinsa,to amma wa suke dashi sama da anni?,itace qawarsu abokiyarsu kuma. _uhmmmm....tofa,sabreen naga kin dauki zafi da yawa😄😄.....amma dai muje zuwa_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 77 77 Da wani irin yanayi yake wanke mata kowanne sashe na jikinta da ruwan shower gel din. Wani kuka take saki kawai tana ji har a ranta ya gama da ita,bata da wani sauran qarfi da zata dakatar dashi ko guda daya,cizo kam ta masa shi har batasan adadi ba,amma ko a fuska baya nuna mata yaji zafinsa bare akai ga dakatawa da abinda yakeyi,tamkar ma ba jikinsa take ciza ba,idan ta saka bakinta ma tsaiwa yakeyi har sai ta cire don kanta. Shi kadai yasan me yake sake ji cikin jikinsa,ji yakeyi kaman baiyi komai bama,wani sabon feeling ke taso masa saboda santsin shower gel din dake sassan hannuwansa wanda da tafin hannu kawai yake dauraye mata jikin ba tare daya nema loofah ba. Kafin ya gama wanketa launin idanunshi sun sake canzawa sosai,numfashinsa yana masa nauyi tsakanin qirjinsa da hunhunsa,inda zai samu....inda zai yuwu yana buqatar sake kasancewa tare da ita ko yaya ne.....koda na mintuna kadanne,amma shi kansa yasan yadda take a yanzu dole tana buqatar medical care. Bai taba jin ya zama addicted to wani abu ba irin wannan abun,cikin qasa da wasu awanni qalilan yana jin kamar an halicci abunne sabodashi shi kadai. Hannunsa ya sanya ya riqo qugunta bayan ya fiddota daga bathtub din. Idanunta yake kalla sosai wadanda suka rine saboda azabar kuka. Taqi kallonsa ta kuma sanya duka hannuwanta biyu tana turashi baya,amma ko motsi baiyi ba bare tasa ran zai matsa. Yadda takejin dumin fitar numfashinsa a rarrabe yana sake dasa mata matsanancin tsoronsa,shigen wannan yanayin taji daga gareshi dazu,a yanzun idan yace zai maimaita abinda yayi dazun ta tabbatar saidai ta taqaitawa kanta wahala kawai tayi sallama da duniya......ita kadai tasan abinda takeji,ita kadai tasan radadin da takeji yana ratsata a duk wani motsi da zatayi. "Sabrrrrr....." Ya fada da sautin dake kama da rad'a,wani irin narkakken sauti dake da amo na can qasan maqoshi,idanunsa cike fal da wata irin mahaukaciyar soyayya da baiyi zaton cikin zuciyar tasa akwai wani space daya ragewa wata halitta ba. Kanta ta dauke gefe,maganganu takeson gasa masa amma tana jin idan ta tsaya ta maida masa koda kalma daya ma yana da wannan darajar ashe?. "Sabreeennn" Wannan karon ya kira sunanta full da wani irin sassanyan kuma kwantaccen sauti. Idonta ta lumshe tana mamakin jin sunan yau radam saman bakinsa,kiran sunansa a bakinsa daban yake da yadda kowa ke kiranta,kaman yadda komai nashi yake daban haka furucin sunanta a bakinsa.....amma kuma zuciyarta saita ture hakan,haushinsa ya taso ya maye gurbin wannan. "I know.....nayi abubuwa masu yawa......na bata miki rai da yawa......na gaya miki maganganu masu yawa......i hurt you.....i really hurt you even...." Sai ya kasa qarasawa saboda yadda zuciyarsa take rauni. "Na bata miki da yawa.....na sani,but dukan abinda nayi shine akan hujja da evidence da binciken da nayi wanda yazo da negative reviews......sabrrrr" Ya sake kiranta a karo na uku yana sake zube qwayoyin idanunsa dake cike da shauqi a kanta,yana jin kamar ya dauketa ya bude qirjinsa ya boyeta,yana jin kamar ya hadiyeta ya huta da abinda yakeji qasan zuciyarsa. Ganin da gaske ba zata kalleshi ba sai ya sanya hannu qasan habarta yana juyo da fuskarta. A zafafe ta qwace tana hadiye kukan daya taso mata,ba abinda take muradi a yanzun irin ya sake mata qugunta tayi nesa dashi,ya gama kalle komai da komai nata.....wannan laifin nasa batasan yadda zata gogeshi ba. Sake kamo fuskar yayi ta qwace,sai kawo ya jawota cikin jikinsa ya mata wata kyakkyawar runguma. A karo na biyu fatar jikinsu ta sake haduwa guri daya,wani qaton numfashi ya qwace mata,kaman yadda qaramin yaron da yasha kuka kan saki ajiyar zuciya sanda ya samu kyakkyawar runguma da lallashi daga wajen mamansa. "My heartfelt apologies" Ya sake fada da wani sassanyan sauti me tada tsigar jiki yana miqa hannu ya sake musu ruwa saman kansu shi da ita. Saukar ruwan ya sake tayar masa da abinda yakeji ninkin na dazu,abinda ya qarasa gigitashi kenan,ya dagata yana hadeta da bangon toilet din,ya fara abubuwan da yasan zai samu sauqi da sassaucin abinda yakeji. Wani irin tsoro ne ya sake kamata,takaici da baqincikin yadda yake sarrafa jikinta yadda yaga dama,sai ta sake sakin kuka me sauti tana sake tureshi dakai masa duka da siraran tafin hannunsa. Ba abinda yaji saiji da yayi ma kaman tana sake zugashi,sautin kukanta kawai yake iya ji daya sake zame masa kaman zuga zugi,don sai ya dinga jin kaman kukan wani abu daban takeyi bana baqinciki ba,deep inside yasan na baqinciki ne,but bazai iya qyaleta ba ko yaya......yana buqatar samun sassauci koda baiyi me gaba daya ba,yanajin zuciyarsa da rayuwarsa tana sake mannuwa da ita,yana jin kamar duk wani fitar numfashinsa ya ta'allaqa da ita ne. Sai daya tabbatar ya samu nutsuwar da yake da buqata sannan ya jata jikinsa yana fitar d wani zazzafan numfashi,ya gama kashe mata jiki da tsoro itama,dole ta jingina da jikin nasa tana jin yadda zukatansu ke wani irin gudu,musamman shi da bugun zuciyarsa ke shiga cikin kunnenta sosai saboda kan nata dake kwance a qirjinsa. Duk da ruwan dake zuba saman kansu yana kwaranyewa a sassan jikinsu gaba daya amma hakan bai hanashi tantance dumin hawayenta saman fatar jikinsa ba. Ya gaza bude idanunsa,sau hannunsa guda daya yake shafar sassalkan gashinta daya watsu har gadon bayanta,ya kuma manne sosai saboda ruwan dake zuba "Am sorry......I'm genuinely sorry,My apologies from the bottom of my heart" Ya fada yana kissing goshinta softly. Ture fuskarsa tayi tana sake qayyade adadin rashin imaninsa......tadai san saboda itace kawai ya gwada mata wannan rashin tausayin,banda haka ta tabbatar inda duka mata haka sukeji ba abinda zai sanya su zauna ko suci gaba da yin aure. "Leave me" Ta fada tana qoqarin tashi daga jikinsa. Hannunsa ya sanya ya damqota sosai yana cewa "I can't......ko mutuwa bata isa ya rabani dake ba sabrrrrrr.....zan yita baki haquri har ranar da numfashina ya fita daga gangar jikina......zanta baki haquri ko sau dubu a rana kikeso.....karki wahalar damu gaba daya ta hanyar cewa na barki ko na nisanceki.....don wallahi wallahi wallahi bazan iya ba......i can't do it" Ya qarasa fada yana sake matseta jikin bango sosai sannan ya fara tsarkake jikinsa idanunsa a kanta. So yake qarfi da yaji sai ya cire kowacce kunya daga idanunta,tsaiwarsa haka a gabanta tana jin shine abu mafi girma firgici da razani da suka taba gani. Cikin mintuna kadan ya gama ya kashe shower din,ya jawo babban towel ya wareshi. Ta dauka zai rufa ne ko ita ya bata daman rufawa.....maimakon haka sai ya jawota jikinsa ya bude towel din ya nadesu su biyun a ciki. Shi da ita ba wanda numfashinsa baiso yin qaura ba saboda yadda jikinsu ya sake gauraya dana juna "Shshshsh" Ya fada yana qoqarin daidaita numfashinsa,don bayason tace komai,hannunsa ya sanya a gadon bayanta ya matseta cikin jikinsa gami da rabata da qasa kaman yadda zaka rungumi yaro a haka suka fita a toilet din. Batasan da gangan yayi ba?,oho.....amma gaba daya suka zube a gadon yana fadawa samanta. Ya aje mata nauyinsa sosai har sai da numfashinta ya fara nauyi "Oh....sorry" Ya furta yana dagata gami da bar mata towel din a tare da ita. Rintse ido tayi tana qin dubansa,bai damu ba ya jawo boxer dinsa dake yashe a gefe tun dazun ya saka,ya sanya hannu ya sauketa zuwa sofa bed ya fara tattare comforter da bedsheets din harma da pillow case din,don bayason anni ta sake dawowa idanunta su gani. Toilet ya koma ya shiga sheqa musu ruwa,jikinsa yayi wani irin sanyi ganin yadda ruwan ke wanko jinin. Da gaske ya shigeta ne da tabbaci da yaqinin ta riga ta saba......ya kuma samu qofar a kulle gam....dole taji ciwo koma wanne iri akace masa taji. A yadda yakejin cikakkiyar lafiya a jikinsa ya sani,koda bazawara ce yaje mata da irin yanayin jiya lallai saita yabawa aya zaqinta ballantana ita din da take sabon hannu. Luggage dinta ya bude,ya fidda mata kaya bayan ya saka wata sassauqar riga a jikinsa over sized shirt da wandonta. Fara ce qal data dace da black trouser dinsa. Sama sama yake jinsa shima,saidai abinda ke gabansa ya shafe komai. Da rinannun idanunta ta dubeshi sanda ya aje mata kayan,tana so ne ya matsa ya bata waje ta shirya amma bataga alamun xai matsa din ba,hasalima tsaye yake a kanta ya zube duka hannayensa a aljihun wandonsa kaman zai lasheta,ya zube mata nauyayan idanunsan nan yana jin kamar ya buda qirjinsa ya fiddo mata mahaukaciyar soyayyar data sakar masa. "Ka fita zan shirya" Ta fada a taqaice ba tare data kalleshi ba,hannayensa ya fidda daga aljihunsa ya juya a hankali ya fita. Duk yadda taso ta miqe sosai don ta shirya amma hakan ya gagareta,ba zata iya tsaiwa normal kaman kowa ba,abinda ya sanya hawaye yaci gaba da zuba a idanunta,saita dinga jin data sani ta barshi ya taimaka mata,amma kuma batason komai da zai dinga hadata dashi. Da qyar ta lallaba ta saka underwears dinta ta maida rigar,sannan ta lallaba hannun damanta ta kwanta tana ci gaba da fitar da ruwan hawaye. A nutse anni ta murda qofar tana shigowa da sallama,wata kunya ta taso ta lullubeta,saita rufe idanunta tamkar me bacci,tana fata annin taji kaman baccin takeyi ta juya ta barta. "Sannu....." Anni ta fada a hankali da alama ta fahimci ba baccin takeyi ba. "Zaki iya tashi?,doctor zata shigo ta dubaki". Kai kawai ta gyadawa anni ba tare data iya furta komai ba,ta motsa a hankali tana tunanin yadda zata tashi din. Matsawa annin tayi ta kamata a nutse tana cewa "Yi a hankali" Tausayinta yana kama annin. Yanayin yanayine bame dadi ba,iya yau kawai ta fahimci yaron nata yadda jikinsa ke agine hakama komai nasa "Allah ya baki ikon jurewa" Annin ta fada cikin ranta. Sai a yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake kaucewa abubuwa da dama,azumin litinin da alhamis akai akai,harma wani lokaci yakanyi azumin annabi dawud,yau yayi gobe ya huta. Wani lokaci takance "Ka dinga hutawa mana me babban suna......ga azumi ga aiki,shi kansa aikin busy din da kake sakawa kanka pressure din tana yawa". Sau tari murmushi kawai yakeyi ko ya kafa mata hujja da *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 78 78 "Ba isashen time na tsayawa cin abincin,wani lokaci azumin yafi,idanma banyi ba coffee ne sai ruwa sai fura ko yoghurt ". A yau ta fahimci ainihin dalilinsa,saita dinga furta " Alhamdulillah" Qasan zuciyarta. Da gaske Allah ya tsare mata yaranta gabansu da bayansu kaman yadda take yawaita addua a dukka salllolinta na nafila ko na farilla. Tayi imanin inda wani ne ya samu cikakkiyar dama irinta fu'ad din,tarin dukiya kyau ilimi da suna da yayi a duniya ba irin haramtattun ayyukan da bazai aikata ba,ta sani akwai dubban mata dake a shirye su bada kansu ga irin wadannan mutanen,koda ba zasu samu komai ba a wajensu daukaka ce ace yau suna tare dasu. Sai data zaunar da sabreen yadda zataji dadin zaman sannan ta juya a hankali tana fita parlor din. Minti daya ta dawo tare da baquwar fuskar. Dr fadwa siririya fara tas,duba daya zaka fahimci shekarunta duka duka ba zasu haura arba'in ba zuwa da biyu. Anni tana gaba dauke da tea tray,Dr fadwa na biye da ita. Qasa sabreen tayi da qwayar idanunta,ba zata iya kallonsu ba dukka su biyun,har Dr fadwa dake matsayin baquwa a idanunta. Ajiye tea tray din anni tayi tana duban Dr fadwa. Kai Dr fadwa ta gyadawa anni,sai annin ta maida dubanta ga sabreen "Ga likita na.....zata dubaki in sha Allah,ki saki jikinki.....itama 'yar gida ce" Kai ta dagawa anni a hankali,tana jin takun anni da fitarta a dakin,ta kuma ja qofar ta rufe musu. Dubanta Dr fadwa take tana kuma karantarta. Ko ba'a gaya mata ba ta fahimci ita din bame saurin sakewa da mutane bace,ta miqa hannu a nutse ta kama hannunta ta sanya a nata,abinda ya sanya sabreen daga kanta ta kalleta da risunannun idanunta. Da sassauqan turanci take tambayarta da sakakkiyar murya. "Kinci abinci?" Kai ta girgiza mata a hankali. Ba zata iya tuna wani abincin kirki da taci ba,tun na dazun kafin su fita,ko acan wajen cin kifi ma bata saki jiki taci komai ba,kasancewar ita ba ma'abociyar cin abinci cikin jama'a bane. Kai tsaye Dr fadwa ta jawo tea tray din zuwa saman cinyarta tana matsawa dab da sabreen "Ki saki jiki kici abinci......sai na dubaki,kada ki damu da yawa......hakan yana faruwa ga 'ya'ya mata da yawa,musamman da yake yadda kowacce mace halittanta daban,haka kowanne namiji shima nashi halittan daban......fashewar budurcin mace yana iya kawo fitar jini.....amma komai zai zama daidai kinji?" Kai ta daga a hankali,ta kuma miqa hannu tana karbar mug din da anni ta hada mata tea me dumi sosai da kauri. Ita kanta tasan ba komai a cikinta,ballantana kuma da abun ya faru sai taji kamar anyi mata yasa,kamar an kwashe 'ya'yan hanjinta gaba daya,kamar iska tana turata zuwa gaba. Kadan kadan take shan tea din,dr fadwa bata matsa wajen kallonta ko yi mata wata tambaya ba ta daban,ta bata time sosai tana duba wayarta har taga ta ajiye. Wayar ta bari ta daga kai tana kallonta,batasha da yawa ba amma saita qyaleta don tasan lallai yanayin bame dadi bane. Kauda tray din tayi ta matso kusa da ita tana dubanta "Sunana fadwa kefa?" "Ameenatu" Ta furta idanunta suna dan lumshewa "Sabreen sunan inkiya?" Kai ta gyada,saita fidda takarda fara ta rubuta sunan akai. "Eheennn......ina ne yake miki ciwo yanzu?" Shuru tayi don tamabayar tayi mata nauyi da yawa,uwa uba ma gurare da yawa ciwon suke mata,tun daga lips dinta......qirjinta....hatta da tafukan hannunta da suka sha murxa zafi zafi takeji suna mata. "Ki sake sosai kiyimin bayani,shi yasa madam ta fita ta bamu guri......zai iya zama ciwo me zafi nan gaba idan baki bayani ba". Hannu tasa ta nuna mata wajen ba tare data iya kallon idanun fadwa ba. "Alright......zan duba wajen idan ba damuwa?" Ta fadi da nufin neman izini. Dif tayi abun yana mata wani iri,shikenan ita kuma jikinta ya zama wani budadden guri? "Kiyi haquri....saboda lafiyarki,bazai dauki lokaci ba" Ta fada da sigar lallashi. Kai ta gyada mata a sanyaye. "Kin shirya?" Dr fadwa ta fada tana kallonta sanda ta kwanta kamar yadda ta kwatanta mata. Kai ta gyada mata tana rufe idonta saboda kunya. A hankali ta fara dubata cikin qwarewa da nutsuwa yadda ba zata fama mata ba. "Oh my god.......subhanallah" Abinda ta fada kenan tana maida mata doguwar rigarta. "Kin masa gardama ko musu?" Dr fadwa ta fada tana kallon fuskar sabreen din da tuntuni ta canza kala zuwa red. Tambayar sai ta zama kaman ta bata license din sabon kuka,ita me zata ce mata?,batasan ma me tayi ba.....musu ko taurin kan batasan wanne ne tayi a ciki ba,batasan wanne ne ya faru ba. "Irinsu sir.......ba kasafai za'ayi musu musu a irin wannan lokacin a wanye lafiya qalau ba.....next time kada ki qara musu ko gardama,mijinki yana da duk wani personality da kowacce 'ya mace zatayi alfaharin samunsa a matsayin miji,.....kulawa da tattali yake buqata,ko don gaba kada ki sake matse jikinki da hana masa kanki haka". Sanda take fadin next time din ji take kaman ta ture Dr fadwa,itakam wacce irin sauna ce da zata yarda taci gaba da zama da mutum irinsa?,wanda bisan ciwo ko darajar dan adam ba?,balle ma har hakan taci gaba da faruwa wai a gaba?. Daidai nan anni ta tura qofar ta shigo,da murmushi take tambayar Dr fadwa "Kin gama?" Kai ta girgiza tana dan murmushi itama "Aah fa......madam yaronki aiki ya baro.....bleeding din data dinga yi ta samu tier ne.....so dole sai an mata stitches..." Idanu kadan anni ta fiddo,har jikinta tana jin wani iri. Lallai Allah kadai yasan azabar da tasha tunda har an kai ga batun dinki. "Gurin yayi ciwo sosai gaskiya.....harda bruises banda tier din,dole a dinki wajen,inda first degree tier ne da sauqi....so amma yanzun ma idan kina ganin a bari......" "No.....a dinke Dr" Anni tayi saurin dakatar da Dr fadwa din. A yadda taga yanayin fu'ad din da idanunshi ba yadda zata bari a bar sabreen din a bude,tun sanda momma ta gaya mata marainiya ce takejin kamar kula da sabreen din wani haqqi ne daya rataya a wuyanta. "Kiyi haquri a dinke sabreen kinji?,wannan gurin shine mutuncin duk wata d'iya mace a wajen mijinta.....akwai zafi amma zai wuce kaman bai faru ba,wannan shi ake kira da cikakken mutunci mijinki ya zamana shi ya karbi wannan abun ba wasu shashashai a waje ba.....nayi alfahari da hakan......na kuma yi alfahari dake kaman yadda nasan yake a wajen mijinki" Anni ta fada a tausashe hannunta saman kan sabreen da kunya ta hanata koda motsawa bare ta bude idanunta. Sake fita anni tayi ta basu waje don sabreen din ta sake sosai. Dr fadwa kuma ta shirya komai,ta kuma yi mata allurar da sai data zubda qwalla kafin a gama,batasan azaban yana gaba ba sai da aka fara dinkin. Neman sakayya wajen Alla data dinga yi har batasan sau adadin nawa ta fadi ba,saidai duka cikin ranta takeyi,bakinta baya iya furta komai sai ruwan hawaye dake fita Dr fadwa na mata sannu. Kasa zama yayi a falon,sai kawai ya tura qofar dakinsu saddiq ya shige. Kwance yayi kawai saman gadonsu,ya kasa tuna komai sai hankalinsa dake can dakin inda ya barosu,yaji shigar dr fadwa da anni da fitowar annin duka,baisan me yake faruwa ba don haka ya kasa samun nutsuwa. Gefe guda wani irin sarqaqiya ya shiga. "KARUWA" Sunanta ma farko kenan daya fara zuwa kunnensa,yaci gaba kuma da zuwa masa daga bakunan mabanbantan mutane. Kenan dukka wadannan bincike da shaidun duka shaidan zur ne?,duka shaidan qarya ne?. Idan har hakan ya kasance kuma ganin da yayi mata a hotel fa?,mashkur dake hannunsu a yanzu haka yana nemanta afujajan da sunan wadda ta kwashe masa komai nasa?,ganinta da yayi fa tare da mika'il?,a cikin kamfaninsa tana fitowa daga toilet dinsa?,binciken daya tabbatar kuma ita ta kwashe kudaden asusun kamfaninsa fa?,wannan kuma mene?. Ta yaya zai fahimta?,ta yaya zai gane?,waye zai warware masa?. "Ka nutsu fu'ad.......diban kudi yasha banban da bada mutunci.....don tana kwashe kudaden maza.....don kana ganinsu tare hakan ba yana nufin tana basu kanya bane,kowanne matsayinsa daban,cakudasu waje daya kuma shine zai sanya ka kasa banbance inda komai ya dosa" Wani sashe can qarqashin lungun zuciyarsa ya gaya masa. Sau uku yana leqa parlor din ko zaiga ko yaji motsin anni ko wani abu da zai bashi haske amma baiji ba. Kunyarsa da kawaicinsa duka suka qare,sai kawai ya buda qofar dakin ya fito kai tsaye yana tunkarar dakin. Itace ta farko da idanunsa suka fada kanta bayan bude qofar da yayi. Ta wani sake fadawa farat daya saboda masifar dinkin. Ko baka santa ba tsakanin a wannin nan idan ka kalli fuskarta zakasan tayi kalar kukan da bata taba irinsa ba. Idanunsa ya maida kan Dr fadwa,likitan da sai da tazo ya tuna ya taba saninta a Egypt,ta taba dubashi da yayi wani zazzabi,hankalinta kuma da nutsuwarta shine abinda ya sanya ya bata daman bashi magani. "Welcome sir" Ta fada cikin girmamawa. Kai ya gyada yaja kujera yana zama hankalinshi a kanta. Daga kallon da yayi mata ta fahimci qarin bayani yake nema. Dama kuma dole akwai buqatar masa qarin bayanin don ta fahimci kaman yana cikin mazan nan marasa haquri akan abinda ya shafi janibin auratayya. "Mun kammala,anyi mata stitches.....but please sir,tana buqatar hutu na koda 3to 4 weeks kafin a sake tabata,saboda a bawa dinkin daman warkewa yadda ya kamata". Ido ya lumshe sannan ya bude yana jinjina kai. "Mun gode....ta yaya zaa biyaki?". "Madam ta biya sir.....Allah ya qara lafiya" Kai ya jinjina yana girmama qaunarsu da anni. Tsantsar kulawa da qauna irin wadda akasan uwa kadai take da wannan zuciyar. Komai idan ya kama qoqari takeyi tayi musu shi ba tare data jira yin kowa ko cewar kowa ba. Tatttare kayanta tayi ta fice taja musu qofar. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 79 79 A hankali ya dauke dubansa daga kan qofar zuwa inda take zaune. Idanunsa ya zuba mata yana jin akwai wani boyayyen abu ciki rayuwarta,wadanne irin masharrantan mutane ne tattare da ita haka?,wadanda ba zasu iya fadin alkhairi a kanta ba?,wadanda ba zasu iya suturta aibunta ba a sanda akazo bincike a kanta ba?. Idan bai manta ba,ya samu tabbacin cikin wadanda suka bada shaida a kanta harda matar babanta,sanda yake jaddadawa abdul haleem bayason fake bincike,baya son kuma gurbataccen shaidu. "Wacece a cikinsu?" Ya tambayi kansa da kansa yana takawa gabanta,tausayi da wata irin mahaukaciyar qauna tata tana hudashi. A yanzun yana jin a shirye yake da duk wani mutum da zai taba rayuwarta,a shirye yake ya bada dukkan abinda ya mallaka a kanta.....in fact a yadda ta zame masa mahadin numfashi a yanxun......ba dukiyarsa kadai ba.....hatta da rayuwarsa a shirye yake ya bata ita. Yana jin ya shirya kame duk wani wanda ya bada shaidar banza a kanta,ya shirya tuhumarsu ko su waye....komai yawansu.....komai kuma kusancin dake tsakaninsu da ita. A jikinta takejin wanzuwarsa a wajen,wannan ya sanya ta sake zabar ci gaba da rufe idanunta,har ya iso gefanta,ya zame kan gwiwoyinsa yana aza qarfinsa akai. Hannusa ya miqa ya kamo tattausan tafin hannunta,ta motsa da sauri ta nufin zamewa amma ya rigata,ya kamo hannun nata da daya hannun ya saka tsakiyar hannayensa yana duban rufaffen idonta. Dukka kalamansa sun gama qwace masa,komai ya auno sai yaji bai hau mizanin bada haquri ba....amma hakanan zaici gaba da gwadawa don ya shirya karbar ko meye daga gareta hannu bibbiyu. " Can you feel any pain or discomfort?" Ya tambayeta kaman zai maida idanunshi cikin fuskarta. Shuru ne ya zame masa amsa,bata ko motsa ba ballantana ta nuna tasan da ita yake. Sake matsa hannunta yayi kadan a tausashe,ya motsa labbansa yace "Sabrrrrr" Nan ma shuru ba wani motsi ko amsa. Jawo hannun nata yayi kadan,ya kuma matso dashi ya dora tafin hannun nata saman qirjinsa saitin zuciyarsa. Tabbas har cikin jininta taji bugun zuciyarsa.....kaman yadda dumin cikin hannunsa da wanda taji cikin qirjinsa ya tabbatar mata da zazzafan zazzabin da yakeyi,amma ko daya sai taji bataji tausayinsa ba. "Im filled with regret for what i did,am truly sorry......please kice wani abu man" Ya fadi cikin zaquwar ji daga gareta,amma still ba wani canji. Shurunta sai yaji yana kasheshi har cikin tsokar zuciyarsa,shirunta sai yaji yana masa wani irin ciwo......baya fatan ta zama me hukunci da shuru wanda kusan halinsa kenan,ya kuma san ciwon hakan. "Sabrrrr......I'll do everything to prevent it on the future nayi alqaw....." Future din daya fada shi ya sanyata janye hannunta sa wani irin sauri,saidai kuma kash zafin namansa ya qure nata,kafin ta samu daman boye hannun ya sake kamoshi yana jin wani nisa da takeson haifarwa tsakaninsu. Cikin yanayi na karaya ya sake aza tafin hannun nata saman kuncinta,ya kuma dora kansa akai kaman wanda ya samu pillow "My heart was beaten past sabrrrrr........zata iya bugawa wallahi......please sabr say something mana......" "Ka qyaleniiiiii....." Ta fada cikin daga murya tare da wani irin sautin kuka wanda yayi daidai da shigowar anni. Tsaiwa tayi cak tana dubansa,kaman zata koma sai kuma ta tuna da zancan Dr fadwa,don haka ta qaraso cikin,amma ta dauke kai kaman bataga abinda ya faru ba. Idanunsa ya aza kan annin,sai ya janye jikinsa daga wajen yana komawa inda dr fadwa ta tashi wajen data ajiye documents din da tayi rubutu a ciki. "Daughter" Ta kira sabreen a hankali wadda ke qoqarin boye hawayenta da mode na fuskarta. "Naam" Ta amsa tana murmushi "Akwai ciwo ko ya ragu?,idan akwai tace tayi prescribing wasu magunguna,ta tura ta pharmacy dinsu zaa karbo ko a kawo miki". " Akwai ragowa" Ta fadi tana jin yadda gurin ya daddaure mata "Zai daina in sha Allah" Maida kallonta tayi kansa. "Ka hada mata kayanta da duk zata buqata......zatayi matsa zuwa dakina,zan kula da ita zuwa sanda ciwon zai warke" Anni ta fada adan dake. Da mamaki ya kalli annin yana jin rashin dadi yana saukar masa,abun sam bai masa ba,yana ganin kamar shi yafi cancanta a bari yayi jinyarta,yayin da sabreen taji kamar an mata rahama,wani sanyi ya fara sauka saman zuciyarta.....zata matsa daga kusa dashi......zata bada rata me yawan gaske kuwa tsakaninsu,tana jin sai taso ma zata bari idanunsa ya hadu da nata,tabbas da wannan damar zatayi amfani tayi nesa dashi,nisan da zai fara tun daga yanzu har kuma abada _uhmmm.....sabreen,anya me jadda zai bari kuwa?,to dai zami gani_ Kaman yadda ani ta buqata haka ya hada mata kayan,yana kallo anni ta kamata a hankali har suka fice a dakin. Ba jimawa ta dawo ta dauki luggage din nata ta sake fita,sai ya koma ya fada saman Kujera kaman wanda baida laka a jikinsa. Dakin yake bi da kallo,sai yake ganin dakin ya masa wani mugun fili kaman an dauke wani abu da yaci gurbi me yawa a dakin. Hannunsa ya kutsa cikin sumar kansa yana fidda numfashin daya qara zama me zafi saboda zazzabin jikinsa. Wannan zaman bazai masa ba,yana jin kaman bazai iya kwana a dakin shi daya ba,kaman ya masa girma,abinda bai taba ji ba kenan tunda yake kwana a daki shi daya ba sai yau. Wayarsa ta dake gefe ce ta dauki ringing,kaman bazai daga ba amma ya daure ya miqa hannu,anni ce,a sanyaye ya daga yana fatan ba wani abun bane da zai sake sanya nisa tsakaninsa da sabreen din ba "Ka nema magani kasha kaima jikinka akwai zazzabi". Da qyar ya motsa labbansa yana fadin "To" Ta katse wayar ya sauke shima yana jinjinawa da kulawa tare da damuwa da lamarinsu irin na anni. Hannu ya dafa zai miqe ya aza hannunsa kan takardar da Dr fadwa ta rubuta,ya dauketa zummar sauya mata waje,idanunsa suka sauka kan sunanta. "Ameenatu Ahmad" Ya furta sunan a fili "Is her real name ameenatu?" Ya tambayi kansa a mamakance. Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi,wani abune da bai taba sani ba sai yau "Ya rahman" Ya furta a karye. Duk wata me suna ameena darajarta daban yake a ranta,kima da mutuncinta ya zarta na sauran mata a wajensa duka dalilin anni. Koda list aka kawo masa idanunsa ya sauka kan sunan ameena yana fara tsinceta daban kafin kowa. "Ameenatu" Ya maimaita sunan can qasan maqoshinsa yana jin wani abu me matuqar qarfi yana kwaranya tare da jinin jikinsa zuwa zuciyarsa da kowanne sashe na jikinsa. Qarfin abun yana jin kamar yafi qarfinsa da gasken gaske bare ya tareshi. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 80 80 A daddafe ya nemi magani yasha,har cikin ransa yake ji tabbas Allah yana sonshi,ubangiji na qaunarsa......bai debe komai da kowa daga hannunsa ba......Allah ya dubeshi,ya killace masa ita da wani irin tsaro da bai taba tunanin wanzuwarsa a tattare da ita ba. Duk da ciwon kansa sai ya samu kansa da tashi ya wuce toilet,qarfe daya saura na dare,ya daura alwala ya dawo ya shimfida abun salla ya kabbara salla. Raka'a biyu rak yayi amma sun kasance masu tsaho sosai,kuka sosai yakeyi cikin sujjadarsa cikin godewa Allah da kuma yaba karamci irin nasa. Ya sake imani da karamcin ubangiji me girma da fadi ne,ya masa wani irin ba zata mara misali da bai taba kawota ba. Duk kusan inda ya juya fadi dakin yake sakeyi masa,wani irin emptiness yakeji cikin dakin qirjinsa dama zuciyarsa.....wata irin kewa da bai taba jin irinta akan kowacce halitta ba sai a kanta,duk shudewar daqiqa daya tana dawo masa ne da yammacin zaice ko darensu na daxu. Ya zuqi numfashi ya fesar yana jin kaman daren yayi masa nisan da gari bazai waye ba ballantana ya sake ganinta. Bayajin baya ga anni akwai wanda zai masa hakan......bazai lamunci wani ya rabasu koda kuwa na qiftawan ido ne. "Me yasa ban dauketa ba kafin anni takai ga yanke wannan hukuncin?" Ya tambayi kansa yana jin ciwon nisan data masa. Hannunsa yakai kan qirjinsa daidai inda faffadan qirjin nasa ya manne da nata a dazu. "Beautiful" Ya furta yana shafa labbansa bayan ya tuna kyan gurin ga qayatarwarsa. A cike suke kuma a tsaye da wani irin shape me jan hankali,ba wata alama data nuna hannu ya taba kawa wajen koda na kwanaki qalilan ne. Wani numfashin ya sake fitarwa........ Yaji yana buqatar sanin duk wani me mummunar shaida a kanta.....yanason sake tusa bincikensa.......yaji yana shaawar bin kowanne diddigi na rayuwarta....koda bata gaya masa da kanta ba dole zaiyi wannan aikin. Bayason kunnuwansa da zuciyarsa su dinga tuna masa maganganun daya gaya mata "Kyakkyawar Kalma sadaka ce" Ya tuna wani sahihin hadisin ma'aiki akan furta kalma me kyau ga dan uwanka musulmi. Baisan me yasa yake kasa controlling anger dinsa a kanta ba,baisan me yasa yake tsananin jin zafin komai daya shafeta ba.....sai a yanzu daya soma tuhumar kansa da fadawa soyayya a sanda baisan ita bace saboda mummunar shaidar da ya yiwa soyayyar. Yaga mata kala kala da suka kawo kansu gareshi.....mata iri iri dake da wata irin qazamtacciyar rayuwa,amma bai taba jin zafin rayuwar da suke ciki ba saboda ya bawa kansa amsa da baya da issue dasu,bugu da qari ma su suka jefa kansu suka zabi wannan rayuwar. Daga daren zuwa wayewar gari ya zame masa wani zamani daban me zaman kansa......kamar ba tazarar awanni bane kawai a tsakaninsu. Yayi sallar asuba cikin daki ne karon farko da zai iya tuna sanda hakan ya faru,ya kuma ci gaba da zama a wajen yana hailala istigfari,salatin annabi kaman yadda ya saba,sannan ya zarce da karanta wasu shafuka cikin qur'ani. Sanda ya rufe mas hafin qur'anin daga kan tab dinsa da yayi karatun dashi gari ya soma haske. A irin wannan lokacin yakan fita gym ne,amma a yanzu baya da wannan kuzarin da zai iya fita ko ina,fatansa kawai gari ya qarasa haske yaji motsin su annin ya samu chance na ganinta. Kansa ya aje gefan gadon yana lumshe idanunsa,hannunsa saman kayanta da tun daren daya zaresu ya watsar bai iya kwashesu ba. Yamutsasu yakeyi cikin tafin hannunsa a hankali wani sabon feeling na sake shigarsa. Kowacce safiya sassanya irin wannan yakanyi fama da irin wannan yanayin tun asali can dama......a yanzun sai abun ya zama double,ya jawo vest din da bra din duka ya cusa a hancinsa yana shaqar sassanyan qamshin nan daya dasa masa tarihi cikin rayuwarsa. (Tsokaci:- Mostly maza suna samun feeling sosai daidai wannan time din,saiki kula da buqatar mijinki,ko yaro gareki namiji koda qarami wanda bai balaga ba daga lokacin zuwa wayewar gari ki lura da kyau,indai tsiraicinsa yana dagawa a irin wannan lokacin to tabbas lafiyayye ne,idan kuma kikaga akasin hakan to sai a fara nema masa magani). Ba abind qamshin ke sake masa sai qara tada zaune tsaye,kaman ya shide kayan cikin hancinsa haka yakeji,ya tattarasu ya mannesu a qirjinsa yana qoqarin baiwa kansa haquri. Baisan sanda wani irin bacci yayi awon gaba dashi ba,wanda ya cika da mafarkanta kala kala,ko wanne waje suna tare cikin shauqattancen yanayi me tafiyar da hankali,da wani irin yanayi mai tafiyar da hankali. Koda ya farka yanayin daya samu kansa a ciki ya sabbaba masa sake wani wankan ibadan,sannan yayi gama garin wanka ya fito daure da towel yana duban a gogo. Baisan wanne aiki yayi haka ba da har yunwa ke zaqalqalar cikinsa,saidai duk da yunwar da yakeji ganinta yana jin yafi masa cin abincin muhimmanci. A nutse ya shirya cikin wasu pajama masu dogon hannu butter colors da aka yiwa adon gold color din zare da mix din baqi dan kadan daga gaban rigar da tambarin kamfanin Louise Vuitton. Fuskarsa tayi fresh sosai da wani irin sassanyan yanayi a kanta. Yadda ya gyara sumarshi ya sake zama very calm guy,idanun nan dake da wani irin sirri sun rissuna sosai,ya feshe jikinsa da sassanyan turarukansa yana sake maida dubansa ga agogo. Karfe sha biyu harda wasu mintuna akai agogon qasar Maldives. Yayi mamakin tsahon lokacin da yaci yana baccin,sai ya maida turaren ya zura flip flops masu taushi da suka dace da adon gaban rigar. Idan ka kalleshi zaka dauka wani guri zai fita ne,haka yake,yana da wani irin tsari da koda cikin gida yayi wanka zaka ganshi neat very well dressed. A nutse ya murza qofan dakin yana fita parlor din,ba kowa a ciki bama motsin kowa,sai ya taka zuwa saitin dakin anni yana duban dakinsu farouq dake alamta masa har yanzu basu dawo ba. A nutse yayi knocking,yayi tsai yana irga adadin gudun zuciyarsa tare da raya abubuwa da yawa da zasu iya faruwa cikin dakin. "Shigo mana" Anni dake fitowa daga toilet ta fada. Koda bataji muryarsa ba ta tabbatar shine yake knocking qofar,abinda ya sanyata gyara zamanta sosai saman wani tattausan carpet dan madadaici da anni ta shimfida mata ta zauna a kai. Boubou gown ne a jikinta mai taushi ta asalin 'yar qasar Egypt wadda tafe da mayafinta. Milk color ne da adon lime green a jiki daya sake qawata yadin rigar. Gashinta na tattare waje guda ta kuma daureshi da sassauqan dauri da bazai dameta ba. Fuskarta tayi wani irin fayau ta kuma qara haske da glowing,duk da kana ganinta zakasan cewa ba komai saman fatarta tata,ko man arziqi bata shafa ba. Kwana da annin zata iya kiransa wani abu dake cike da baiwa da kulawa,tayi wani bacci da bata taba tunanin zata yishi ba saboda dinkin dake a jikinta. Ta dauka radadin ciwin shi zai fara tagayyarata,ya kuma hana mata baccinta,sai gashi ta samu wani irin bacci hankali kwance cikin kulawar annin da ko yaya ta motsa itama sai ta motsa,idanunta da hankalinta duka yana a kanta. Umdatul ahkam ne saman cinyarta take duba karatun baya da sukayi da rumasa'u. Annin ta lura bata da waya ko wani abu da zai debe mata kewa,a lokacin Umdatul ahkam din yana hannun annin,taga sabreen din tana yawan kallon littafin,don haka ta tambayeta. "Ko zaki karanta?" Kai ta dagawa annin a kunyace,tun jiya ta gaza cire kunyar nan da annin tace mata ta cireta,ita ba suruka take a wajenta ba,ita din uwa ce amma ta kasa. Hatta da bubu din jikinta yanzu haka ta annin ce "Ki amfani da wadannan,saikinfi sakewa yadda dinkin za'a samu ya warke da wuri" Anni tace da ita. Itace abu na farko da idanunsa suka fara sauka akai. Ya janye dubansa daga kan fuskarta zuwa ga littafin hannunta,haka kawai yaji wani sanyi yana ratsa zuciyarsa,ya motsa labbansa yana yin sallama cike da fatan zata daga kanta ta kalleshi koda ba zata amsa ba,amma maimakon hakan sai anni ta amsa mata tana turr hijabinta data cire kafin shigarta bandakin ta zauna gefan gadon tana nuna masa stool din dressing mirror din gami da karantar yadda dukka hankalinsa yake a kanta tamkar zai wuce gabanta kai tsaye. Ta godewa Alla daya bata basirar dauketa daga dakin.... A matsayinta na babba abinda take gani cikin idanunsa muddin ta barshi da ita tasan dinki koda guda nawa za'ayi mata warkewarsa saita Allah. Zama yayi saman stool din yana qoqarin maida mode dinsa daidai da yadda ya saba yiwa annin,duk da wata irin kunya dake rugowa da gudu tana dabaibayeshi,ya kasa kallon tsakiyar idanunta yadda ya saba. "Barka da safiya anni.....ina kwana?" Ya furta yana rusunawa duk da a zaune yake. "Barka kade......an tashi lpy?" Sassalkar sumarsa ha shafa da tafin hannunsa yana satar kallon sabreen ta qasan hannun nasa. Wannan tambayar ta anni sai yakejin kamar gatse yake masa amma ya amsa da "Lafiya alhamdulillah......yame jikin?" Ya hada kunyars waje daya yana nufin kaita qasa da kuma son janyo hankalin sabreen da ko motsawa batayi ba ballantana ta nuna tasan yana wajen. "Alhamdulillah" Anni ta amsa masa a taqaice,don ita kanta tuna abun kawai yana sakata cikin wata irin kunya. Idanu anni ta maida kanta,zuwa yanzu ko ita yarinya ce ta gama fahimtar wanne irin zama sukeyi,saidai tambaya daya data kasa samun amsarta.....ta yaya ta zama zabinsa bayan baya so?. "Sabreen" Anni ta kirata,kiran daya sanya ta daga kai zuwa ga annin ba tare data kalli sashensa ba. Wani iri yaji.....shi yake da muradin ta fara kalla,shi takeso ta dinga fara kalla kowacce safiya idan yana da ikon hakan. "Mijinki ya shigo". Lumshe idonsa yayi yana jin dadin kalmar da yadda ani ta fadeta da wani irin taukidi "Kul.....ba kyau a wajen mace taqi gaida miji......Allah bazaiyi farinciki da hakan ba" Anni ta fada tana jin wani abu yana taba ranta a kansu duka su biyun "Ya Allah ka taqaita musu jarrabawarsu......kada ka sanya soyayya ta zama wata sabuwar jarrabawa a garesu". "In sha Allah anni" Ta fada tana dan jin nauyin abinda tayin,bawai a kansa ba.....a'ah akan anni ne. Tsam annin ta miqe tana cewa. "Bari na duba matar can ko ta dora abincin rana?". Saita nufi qofa a hankali tana ficewa daga dakin harda jan qofar. Wani dadi ya dinga ratsashi da anni ta basu wannan space din,sai kawai ya harde hannayensa duka biyun saman qirjinsa yana qare mata kallo. Wani irin kallo ne da yasha banban d kowanne irin kallo,wani irin kallo dake cike da shauqi da matsananciyar soyayyar da yakeji kaman tafi qarfin wannan faffadan qirjin nasa dama tsokar zuciyar dake lullube a ciki. Wani kalan so da yafi qarfin a hada sunan son shauqi dama qauna duka a dunqule waje guda,baima san sunan da zai bata ba. Yana ganin yadda ta maida dubanta kan hadith din tana buda shafin gaba,alamun ta gama da shafin baya kenan. Boyayyen murmushi ya saki wanda ya tabbatar ba zata gani ba,tayi masa wani irin mugun kyau tamkar furen fulawa. Lips dinta ya kalla da kyau,ta sake tsuke dan qaramin bakinnan nata waje daya,da gani kai basai an gaya maka ba akwai fushi kwance cikin zuciyar 'yammatan nasa. "Zansha tsiwa.....zansha rashin kunya,amma duka ina maraba dasu,akwai kebantacce kuma killataccen gurin da aka tanada saboda su" Ya gayawa kansa da kansa yana jin shauqinsa yana qaruwa a iya kallonta kawai kafin yaji kallon ya daina gamsar dashi,duminta kawai yake da muradin ji,duk da zuciyarsa tana gargadarsa da cewa kuskure ne aikata hakan,musamman a mode din da take ciki,uwa uba kuma cikin dakin anni?. Saidai kuma magnet din dake jansa yafi qarfinsa,bazai iya controlling kansa ba. Tsam ya miqe ya sauka daga saman stool din,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa,ya motsa labbansa a nutse. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 81 _An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A W,sai tace: dabi'unsa alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin kalolin kyawawan dabi'u dukka haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_ 81 "Sabrrrrr" Ya kirata da sautin nan dake ratsa kunnuwanta ya aike da wani saqo me sauri zuwa kwanyarta. Ko motsawa batayi ba bare ya kula da taji kiran ko bata ji ba,sai ya sauya shawara shima,ya cire hannunsa daga aljihun wandonsa ya fara takawa inda take zaune. Sarai taji takowarsa,amma sai takejin bata da wani sauran abinda zataji tsoro tattare dashi. Batasan gaibu ta gayawa kanta ba sai da taji hucin numfashinsa dab da fuskarta,kafin ta daga kai ya sanya hannu ya zare littafin ya sanyashi a gefanta,ya kuma maida gurbinsa da kansa. Yayi kwanciyar rigingine ne,fuskarsa na kallon sama tana kuma kallon fuskarta,ya hade hannayensa a qirji kaman me sallah,ya tsurawa qirjinta ido daya fuskanci zuciyarta ce take bugawa shi yasa ya fara dagawa sama da qasa kadan kadan. Boyayyen murmushi ya saki.....tana da raunanniyar zuciya me cike da tsoro,saidai,kuma fushinta taurin kanta da kafiyarta kaman suna so su rinjayeta. A tsorace take ainun da yadda ya kankane mata cinta,bata so kuma tayi masa magana sam sam,tana jin bai cancanci kalaman bakinta ba. Haduwar jikinsa da nata sai ya tuna mata da wanzuwar fareeda data gani yammacin jiya cikin jikinsa,abinda ya hadu da fushinta ya sake zafafan zuciyarta kenan ta tattara lausasan tafukan hannayenta zata ture kansa daga cinyarta. Hannuwansa ya saka ya riqesu yana kallon tsakanin haskensu da taushinsu da tun a idanu ma suka nuna hakan. "Kin cewa anni zaki dinga gaisheni....kuma tamkar alqawari ne,bayan ta fita kuma kin karya alqawarin da ko minti uku bai cika ba.....na taso da kaina don nazo na gaidaki sai kuma ki koreni?,kinyimin adalci kenan?". Idanunta ta zuba masa a zafafe kalmar adalcin daya fada tana bata haushi. Shikam har yayi maganan adalci idan akazo batu a kansa?. Batajin zata bari yaji koda kalma guda a bakinta,don haka ta gwammace hadiye takaicinta,ta maida kanta gefe bata furta komai ba tana qoqarin zame kansa daga cinyarta. Ganin haka sai ya juya da zafin nama ya koma rub da ciki,still kanshi yana kan cinyarta. A wannan karon ma sai ya qaro da sanya hannayensa ya zagayo bayanta dasu ya mata zobe kanan ya sakata a Tsakanin hannayensa. "Good morning my sweetest women..........ina fatan kin tashi lafiya?" Ta fada yana sauke wani irin ajiyar zuciya gami da lumshe Idanunsa yana mamakin yadda take saka zuciyarsa bugawa haka. Duk da baya dubanta haka ta zubewa qeyarsa me kwantacciyar suma idanu,tana jin gaba daya ya zame mata qarfen qafa. Duk wani motsi da zatayi don qwatar kanta sake qanqameta yakeyi sosai,hatta da tafukan hannayenta ya mannesu cikin nasa,ya saki ajiyar zuciya sannan yace "Ina fatan kowanne ciwo da kika ji ya zame miki silar samun rahamar ubangijinki.......na gode......na gode.....na gode sau babu adadi da killacemin kanki da kikayi......na gode da kika qaryatamin zancan mutane a kanki.....kika kuma bani tabbacin da bandashia baya" Kaman susa bisa ciwonta haka maganganunsa suka zame mata,ta qwace hannun nata da qarfin zuciya irin nata tana ture kansa,amma sai ya sake rungume hips dinta sosai kaman zai maida kansa cikinta. "Duk yadda zakiyi qoqarin korata daga rayuwarki wannan din mafarki ne......bazan iya ba......bazan iya barinki ba koda na second guda ne,indai zan iya rayuwa babu ruhi ko numfashi......tabbas zan iya rayuwa babu ke.....ke din ruhina ce.....numfashi na ce.....kuma jinin jikina,a cikinsu wanne ne idan babu rayuwa zata tabbata da cikakkiyar ma'anarta?" "Ya isa......ka dagani" Ta fada adan tsaurare saboda wani irin nishi da sauti da yake sakar mata daya sanya ta fara daina gane komai,wata irin tafiyar tsutsa yakewa tafukan hannayenta da take jinta har cikin qasusuwa da bargonta. "Ka daga ni ko na maka ihu na kira anni......." Murmushi ya sakar mata hankalinsa kwance ba tare daya motsa ko ya fasa abinda yakeyi ba "Ki taimakeni ki kiramin ita......wataqila zata tayani gaya miki irin matsayin da me jadda ya baki.....ita din uwace dake fuskantar kowanne yare da 'ya'yanta zasuyi magana dashi". Da gaske yake mata,bataga wani alama ko kadan a tattare dashi na razani ko tsoro ba,saima sake gyara zamansa da yakeyi saman cinyoyinta kamar ya samu wata DUNIYARSA a wajen. "Zan sake maimaita miki.....zanta baki haquri.....zanta baki damar horani har zuwa sanda zaki huce........amma karkiyi zaton akwai wani kalar bore da zakiyi da zai sanya na haqura dake.....kece rayuwata.....banajin bugun numfashi na yana fita da sunan kowacce mace a duniya sai ke" Ya qarasa fadin maganan yana sake qanqameta. "Wayyo dinki na" Ta fada da qarfi,abinda ya sanyashi miqewa a gigice a kuma razane yana riqeta da kyau. Ya bude baki zaice wani abu ta sanya duka hannuwanta ta tunkudeshi sai gashi ya tafi da baya ya fadi. Ba wani abu da taji na zafi ko ya samu dinkin nata,tayi hakanne dama kawai don ya saketa. Baiyi wani qoqarin tashi ba saima sake bajewa da yayi yana sakar mata murmushi "Next time ba zaki nasara ba" Daidai nan anni ta turo qofar a gaggauce saboda sautinta kaman da taji. Shigowar anni ya sakashi miqewa da sauri,yana dan kade jikinsa a kunyace. Yadda anni ta zuba masa idanu yasan tuhumarsa takeyi ba tare data jefa masa kalmar tambaya akan tuhumar tasa ba. Ta janye Idanunta ta mayar kan sabreen "Lafiya?" Tambayar ta yiwa sabreen nauyi,batasan me zatace mata ba,sai tayi qasa da kanta ta kasa amsa mata. "Zaka iya tafiya abinka,amma kasan ba'a takurawa mara lafiya right?" Tuni ya Fahimci me anni ke nufi,sai kawai ya gyara hannun rigarsa yana fadin "Afwan" Ya juya yana fita a hankali bayan ya saci kallon sabreen din data kasa cikakken motsi. Gabanta anni ta qaraso a hankali,taja stool din daya tashi akai ta zauna tana dubanta. "Sabreen" Ta kirata a tausashe. Da qyar ta motsa labbanta tana amsawa sa "Na'am" Tana lanqwasa yatsunta,ta tabbatar idanun anni sunkai kan littafin da fu'ad ya aje a gefanta,wanda duk wanda ya kalla zaice ita ta aje din don yafi kusa da ita. "Ki lallaba jikinki ki warke yadda ya kamata,kada ki yarda kiyi sakacin da dadin bakinsa zai sanya ki bashi dama ya lalata abinda ke jikinki.....dukkaninsu 'ya'yana ne....kuma nasan halin kowa......shi namiji da kike gani dukkaninsu halinsu daya,abu kadanne ya banbanta wannan da wancan" Anni tayi maganar kanta tsaye. Tsoro da kunya suka cakudu suka sanya hawaye taruwa idanunta,kunyar kada anni ta dauka wani abun suka aikatawa,ko ta bashi daman yin wani abu da ita. Muryarta yana raurau,idañunta cike da hawaye ta daga kai tana duban gefan annin. "Wallahi Allah anni ni ban......" "Shshssh.....bance kiyi rantsuwa ba sabreen,kome meye ya faru babu haramci a ciki,mijinki ne halal din juna kuke......amma nasan halin maza sarai.....akan wannan wajen komai ma zasu iyayi.....kusan a nan aka sanya hankalinsu,a nan ne kuma ke kike da power din iya sarrafasu yadda kikeso.... Dole ki bashi kulawa ta musamman,don ke nan ne naki mulkin yake......a yanayin da kike ciki dinnan kuma ba wani abu bane don ya miki dadin baki ya karba,tsaf kika bashin amshewa zaiyi.....amma sabuwar wahala kuma takice". Gaba daya kunya ta sakata saka hannunta ta rufe fuskarta tana sakin kuka,ya cuceta ya sakata jin nauyin anni,ya sanya anni tana tunanin wani abu a kanta "Wallahi Allah anni......ni ba komai da......" "Kul....ni ban tambaya ba,namiki bayanin da zai amfaneki ne,nace kuma ki kula,bance ki fadamin sirrinku ba,maza oya......goge hawayen" Anni ta fada tana tashi zuwa gaban dressing table,ta kuma jawo wata locker dake jiki ta ciro wasu kwalaye guda biyu ta dawo wajen sabreen din wanda ta sanya gefan mayafinta tana share hawayen daya zubo mata. Ba zata sake yarda ko fuskarta ya gani ba bare yasa anni ta zargeta,idan shi baida kunya ita akwai kunya a jininta. "Daga gobe wannan sabun dashi zaki dinga amfani wajen tsarki,idan kikayi sati daya akwai saqon da zai iso zan baki ki amfani dasu,zan miki bayani suma idan sun iso". " Na gode" Ta fada tana jin kunya tana dawainiya da ita,amma sai ta lura ita anni ko a jikinta,tamkar yadda uwa zatayi magana da 'yartane wadda shaquwa da fahimtar juna yayi nisa a tsakaninsu. Kyakkyawar farfajiyar gidan ya fita yana tasbihi qasan ransa,ranshi fes da wani irin farinciki da yaji yana samun mazauni a zuciyarsa. Tabbas ya sake yarda...kudi ko wadata ko wani jin dadi na rayuwa bata taba cika saida macen aure.....cikar kamalar namiji itace aure ya yarda da wannan. A tsakanin jiya da yau,duk da birkitaccen yanayin da komai yazo masa sai yake jinsa a wani cikakken mutum me cikar kamala da mutuntaka,duk wani nauyi dake kowanne gaba na jikinsa kaman an sanya ruwa an wanke masa. Kwanyarsa a yanzu a cike yake da tunanin yadda zai gina kyakkyawar rayuwar auratayya ne kawai,gidan dake cike da soyayya da kuma qaunar juna.....irin qaunar da zata maida gidansu tamkar dausayin aljanna ta duniya. Bai damu ko kadan da dukka wadannan boren nata ba,yayi imani na wani dan lokaci qanqani ne,kuma zata yishi ta gama......komai zai daidaita. Yayi alqawarin dimautata da zazzaqar soyayyar da zata mance kanta gaba daya,ko tanaso ko bataso,ko ta yarda ko kada ta yarda......zai nuna mata qarfin qwajin zuciya da nasa salon na sace zuciyar d'iya mace,a banza ma yake aikata hakan ba tare da yasan yaushe hakan yake faruwa ba?,ballantansa wannan me license?. Zamanshi kenan cab ya tsaya a qofar gidan nasu.ba wani me maida hankali bane shi kan abubuwan da basu shafeshi ba,don haka ya maida kansa ga wayarsa yana duba sunan da yayi saving number CP s.nuhu. a yanzun yana jin wani qaimi da wani irin priority a kansa na tunkarar dukka badaqalar daya baro a Nigeria. Indai har ya sameta a cikakkiyar mace budurwa wadda mutuncinta bai samu koda rawa ba balle tasgaro to tabbas dukka mutanen can akwai daga inda suka bullo,akwai kuma mabanbantan dalilai da suka shigo da ita rayuwarta. Me suke buqata?,wanne dalilai ke garesu?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 82 _Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremu🙏🏽)_ _bukhair da muslim_ 82 Tun yana daga cikin motar idanunsa suka sauka akan fuskar fu'ad din. Wani irin murmushi da ya fito tun daga qasar zuciyarsa ya wanzu a fuskarsa. Tabbas aure rahama ne kaman yadda mata suke rahama ga rayuwar wanda ya dace dasu. Daga inda yake yana iya hangen wani annuri na musamman na fita daga miskilar fuskar nan da ba'a lamunce mata murmushi ba a kowanne lokaci sai lokaci lokaci idan shi da kansa kuma yaso hakan,amma a yau yana ganin wani sakewa akan fuskar daya tabbatar koshi me fuskar ba lalllai yasan da ita ba. "That's my bro muhammad fu'ad jadda" Ya fada qasan ransa yana taya fu'ad murna gami da kama murfin motar ya fito. Ci gaba yayi da kallonsa ba tare dashi ya sani ba,idan har za'a tambayeshi mutum na farko dake bashi mamaki a duniyarsa fuad dinne.......mutum na farko da rayuwarsa tamkar madubi ce a wajensa.....mutum na farko da tausayinsa bai taba raguwa a ransa ba fuad dinne. Yana da sauqi kayi masa mummunar fassara idan bakasan halinsa ba,bakasan wanene shi ba,amma kuma kuna wuce wannan level din dashi zaka fahimci mutane irinsa a duniya qalilanne. "Ka kama kanka farouq.....banda tsokana da yawa,kafi kowa sanin wayeshi" Ya gayawa kansa da kansa saboda yadda yakejin wata dariya nason fara taso masa tun bai qarasa wajen da fu'ad din yake ba "Ka wuceshi kawai kaman baka ganshi ba indai kasan ba zaka iya riqe dariyarka ba" Wani sashen na zuciyarsa ya bashi shawara don da gaske dariyar nan bayajin zata riqu. Yafi yarda da shawarar zuciyarsa ta biyu,don haka ya zaro wayarsa yahau kiran fannah ba tare daya shirya ba,a sannan harsu amna sun wuce cikin gidan. Baisan adadin sau nawa murmushi ya kubcewa fuskarsa ba. Duk da waya ce a hannunsa amma ba abinda yake gilmawa idanunsa sai ita din. A wannin da suka shude masa sunyi masa wani irin tasiri da har ya mutu ba zasu taba goge masa ba. Wasu irin mintuna na musamman da suka fara cikin fushi suka kuma qare da wani abu me matuqar ban mamaki da bai taba kawoshi ba a ransa. Bai lura da saqon ba don haka cikin sauqi hannunsa ya danna saqon ba tare da ya shirya ba *_Kada ka taba tunanin zaka subucemin.....kada ka taba tunanin zaka kubcemin........a shirye nake nayi komai don na mallakeka.....ciki kuwa harda taba alaqar dake tsakaninka da KARUWAR da kake kira matar aure a gareka,fareeda khaleed mustapha_ Wani irin kallo yakewa saqon yana sake karantashi daga farkonsa zuwa qarshensa, "Karuwa?" Ya maimaita sunan da wani irin yanayi da yakejin kaman ana yankar naman zuciyarsa. "Fareeda?" Ya sake maimaita nata sunan yana jin wani irin fushi yana taso masa. Fareeda da ire irenta baya jin zai dagawa waninsu qafa da kalmar KARUWA ta fita a bakinsa muddin suna nufin kalmar ne akan SABREEN. Zaiyi shari'a da kowa a kanta......zai kuma tsaya mata akan duk wanda ya jefeta da wannan kalmar. Har ya fara laluben number fareeda din kai tsaye Muryarshi kawai yaji ya daga kai yana kallonsa. Farouq ne,shi kuwa da gasken gaske wai bai ganshi ba,ya daga hanci sama yana amsa wayar kanshi a sama yana duban qofar gidan. Ganinsa kawai sai yaji fushinsa ya soma sassauta,dan uwa kuma abokin kuka tun daha quruciyarsa har kwanan gobe bai fasa ba. Tsaf ya gama karantar farouq din,sanin da yayi masa sani ne ba na yau ko na jiya ba,ya gama karantar abinda ya shirya,don haka har ya gotashi ya sanya hannu ya fincikoshi baya gami da zaunar dashi a gefansa. "Zauna kayi dariyarka yadda kakeso" Ya fada yana shan mur gami da dage girarsa dukka biyun sama tare da qoqarin danne abinda ya taso masa game da saqon fareeda. Maganar fu'ad din sai ta zama kaman tsokana ga farouq din,take kuwa kowacce dariya dake cinsa ta fashe,ya soma qyaqyatata,harda sauka daga kan concrete chair din ya zame yayi Zaman dirshan cikin grass carpet din yana dariyarsa abunsa. "Kayi me isarka,don wallahi muka shiga ciki kayimin a gaban yaran nan saina faffasa maka baki" Ya sake fada yana hade ranshi "Aah...me yayi zafi?,bani na kar zomon bafa,wallahi ko ratayar ma ba'a bani ba" Ya fadi yana qoqarin danne dariyarsa. Wani kallo ya watsawa farouq din yanata qoqarin maintaining girmansa. "Farouq?" "Allah ya taimakeka" Farouq ya fada yana daga masa hannu da shigen gaisuwar sarakai "Kada ka batamin mode dina" Ya fada yana ware masa idanunsa duka a kansa. "Ango ai baka laifi koka kashe dan masu gida......girmanka ne,Allah ya taimakeka tuba nake....." Naushi ya kawo masa Allah ya rufa masa asiri ya kauce ya samu iska,farouq din ya sake komawa da baya yana sassauta dariyar tasa,don magana yakeso suyi me muhimmanci. ★ *FAREEDA* Da qyar ta tattara kanta tana laluben hanyar fita daga dakin. Tunda take a rayuwarta bata taba jin ta muzanta irin na wannan ranar ba,don ko data koma daki kasa hada idanu tayi da lubna qawarta. "Ke da zaki bude wuta kuyi spending night din gaba daya kya dawo haka da wuri?" Ta tsareta da tambaya sanda ta hautsina kayanta tana laluben inda take ajiye kayan mayenta ko zata samu wani abu da zai dauke mata baqincikin da takeji. Bata samu komai ba,abinda ya sake hautsinata kenan,ta kama gashin kanta ya damqe da qarfi sannan ta sake tana dakawa lubna tsawa "Get out of my sight.....idiot" Tabe baki lubna tayi tana matsawa gefe. Ta sani indai muhammad jadda ne ta qwallafa rai a kansa yanzun ma ta fara wahala da sonshi,bata taba jin wadda a tarihi ta taba samun koda alamu alamun nasara ba a kansa. Da qyar ta iya hada abinda ya bugar da ita ta zube tana bacci ruhinta cike da cin alwashin cikin mutuncin maamah idan ta farka,tare da shaida mata ta dawo mata da kudadenta da dukka taci muddin ba zata iya mallaka mata d'anta ba. Ta dauka duniya ba wadda take da iko dashi sama da ita....ta kuma dauka mallaka mata shi shine abu mafi sauqi da zata iyayi mata. *MAAMAH* Tun saukarta a qasar ba zata ce ga wata cikikakkiyar ibada data iya samu ta aiwatar ba,dukka hankalinta da tunaninta yana a kansu. Me dame yake kashewa ameenatu?,me dame sabreen ki shiryawa a kanshi?,ta bayyana masa sirrinta ne kaman yadda taci alwashi ko.kuwa?. Babban a binda yafi damunta da tsaya mata a rai batun fareeda,gashi har yau din ba taji komai daga gareta ba,bata kirata ba ita kuma bata da number wayarta bare ta fara nemanta. Abu daya ta sani shine.......tabbas.....kofa zatayi yawo tsirarara.....koda malami ko babu.....koda boka ko babu saita nunawa SABREEN DA AMEENATU girman isarta akan danta. Idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba ba shakka ita din ba diyas halas bace. Bayan sallar la'asar kawai saita kasa sukuni,tsakanin jiya da yau kawai saita dinga jin kaman wani abu zai faru ko ya faru,wannan ya sanya ta lalubi number wayarsa ta soma kiransa cikin jin isar mallakinta ne shi ya kamata ya zamanto sai yadda tace ko ta lamunce sannan ayi. Qarar wayar fu'ad din ta sanya hankalinsa ya koma kan wayar daga kan farouq da ya fahimci iya shege kawai yakeson samun dam yayi masa......baisan yadda zuciyarsa ta tumbatsa da wani irin yanayi akan yarinyar ba?. Komai bai dameshi ba irin yadda zai maidata mallakinsa fiye da yadda ya maidata a yanzun......yanaso ita kanta a jikinta ta sallama cewa ita din mallakarsa ce har abada,sai ya kalli farouq ya daga masa yatsa alamun zai amsa wayar. Kai ya jinjina masa,saidai kafin yakai ga dagawar wayar ta yanke. Qoqarin lalubota yakeyi ya kira sai tex ya fado masa _"Duk wanda kayi gangancin kamawa ko hukuntawa cikin mutanenmu dake hannunka.......ba shakka labarin matarka zai zama labari na farko da zai zama fitaccen labari kowacce safiya saman jaridun qasar mu da qasashen dake huldar kasuwanci dakai,suke kuma ganin kima da daraja a tare da kai_ Wani irin fusgar hankalinsa saqon yayi,saidai kuma kafin ya sarrafa kwanyarsa ya fahimci komai kiran maamah ya danne saqon,dole ya kauda abinda ke taso masa ya daga kiran yana sawa a kunnensa,bakinsa dauke da addu'ar "Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta taj'alal hazna iza shi'ita sahla". cike da fatan ba wani abu bane na daban zata baro dashi ba bayan abubuwan dake dabaibaye dashi ba. *_Da sauran masu bibiye da rayuwarsa kenan_* *_Ya zafafa da gaske wajen yin campaign na samun soyayyar ta,xaiyi nasara ko kuma zata zille masa?_* *_shin fareeda zatayi nasara ta hannun maamah kuwa?,kaman yadda tayi nasarar sanyashi auren sabreen a wancan lokacin?_* *_munata gangarowa da MAFARIN warwarar kowanne qulli da tonuwar binnannun asirai_* *_sai ince muje zuwa dai_* *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 83 _An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_ _2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_ _Bukhari da muslim_ 83 Cikin cikikakkiyar nutsuwarsa yayi sallama,zuciyarsa bata fasa neman dauki da ambaton sunan Allah ba. "Wa'alaikumussalam" Ta amsa masa a dake,tanaso ya fahimci cewa lallai shi din me laifi ne a wajenta.....wannan fahimtar tata da zaiyi ya zama sila kuma jagora zuwa ga wanzuwa da amsar babban burinta a yanxu na auren fareeda. A nutse ya fara gaidata,ta amsa masa a dake kaman dazun. Shuru ya ratsa na wasu sakanni kafin tace. "Baku hadu da fareeda bane?" Mamaki kadan ya kamashi,mamakin yadda akayi maamah din tasan da zuwan fareeda Maldives. "Mun hadu" Ya amsa mata kai tsaye,kasancewar mutum ne shi da wahala ko tsanani basa sakashi yayi qarya. "Amma me ya hanaka zama me masaukinta?......tunda kana da tabbacin ba don kowa tazo ba sai don kai". Mamaki ya sake kamashi,ya lumshe idanunsa yana jin takaicinsa yana sake daduwa. Gaba daya maamah din kowacce rana sake jirkita takeyi tamkar wahainiya,wasu abubuwan nata da takeyi sai ya dinga ganin tamkar ba cikin hayyacinta take ba. Maamah ke magana,uwar data kawoshi duniya,inda wani ne ya masa magana makamanciyar wannan yana da amsoshi masu yawa da zai bata. "Bansan da zuwanta.....batayi shawara dani ba kafin ta taho.....and a yanzun ina da iyali maamah,bani da wata alaqa da ita ta kusa ko ta nesa,banda dangantaka da ita" Ya amsa mata da kwantacciyar murya duk da tarin quna da bacin ran da yake ji na cin zuciyarsa. Idanunta ta qanqance cikin jin tashin hankali yana ratsata a hankali a hankali. Meye yake shurin faruwa?,meye yake faruwa da har yau din fuad da bakinsa ke ambaton INA DA IYALI?. Yaushe ne ta samu wannan matsayin a wajensa?,wata kalma da bata taba jin ta fito daga bakinsa ba?. Tarin masifa da wani irin tsanar sabreen tana ratsata,batasan wanne kalar abu ya kamata ta yiwa yarinyar ba......a yanzun a dukka illar da aka mata a rayuwa bayan ameenatu sabreen din itace ta biyu,koda ta raba sabreen da fu'ad bata jin taci riba idan tabar yarinyar haka siddan taci gaba da rayuwarta,tana jin ya kamata ta ajewa rayuwarta wani babban tabo ko miki da zai sanya koda a gaba zata zamewa wasu izina a kanta. To amma babban qalubale da barazanarta a yanzu shine TA WACCE HANYA ZATA RABASU?. Haka kawai take jin matsanancin faduwar gaba da fargaba idan ta tuna kalaman sabreen akan auren fu'ad,bawai ta fara son fu'ad bane matsalarta,idan hakan zata kasance ma zai zame mata daidai,tsoron shine shi fu'ad din......yana da wata irin zuciya da bata iya soyayya ba kaman yadda bata iya qiyayya ba......yana da wata irin zuciya me riqe abinda takeso da gasken gaske..... Wata irin zuciya da idan tana so tana so.....idan bataso bataso,zuciyar da zata iya sadaukarwa da abinda takeso komai data mallaka.....ta zamewa abinda take qauna kariya daga dukkan wata iska ko kuma guguwa. "Wanne iyalin kake magana akai fu'ad?,iyalin da nice silar wanzuwarsu a rayuwarka?.....ko kuma iyalin da babu wata kima ko martaba a tattare dasu?.....ko kuma ni da aka tsinceni daga ayarin tafiya aka wofantar dani saboda kun nunawa duniya bani da wata daraja a wajenku?,ni din ba kowa bace a wajenku?". Wani ciwon kai dukka maganganunta sukaso tasar masa lokaci daya,ya sanya tafin hannunsa ya dafe goshinsa yana murzashi a hankali tare da lalubo me ya kamata yace mata?,gefe guda kalmar IYALIN DA BASU DA WATA KIMA KO MARTABA tana masa zillo cikin kwanya. "AKWAI WANI ABU A LULLUBE" yaji wani saqo na zuciyarsa yana gaya masa. Idan har maamah ta aura masa sabreen ne saboda ta yarda da tarbiyyarta kaman yadda tace da farko......me ya kawo wannan maganar a kanta a yanzu?. Bayajin akwai wani abu qwaya daya da zai iya tunawa wanda ya taba hadasu koda cikakkiyar magana bare yayi tunanin akwai abinda ta taba yi mata. "Fareeda ta taso qafa da qafa.......ta sameni har muhallina......ta girmamani matarka ta tabamin haka?,fareeda tabar qasarta ta biyoka har inda kake,bata da kowa batasan kowa ba saboda tana sonka.......me matarka ta taba yi me kama da wannan?". Kanshi yaji ya sake qullewa......a yau din duka me ya kawo maganganu akan sabreen?,me yahau kan maamah duka akan sabreen din?. "Ina me baka umarni a matsayina na uwar data haifeka.......nan da kwanaki goma zan bar qasar nan......ba wani jirgi da zanbi,ba wanda zaizo ya daukeni....kai da kanka nakeso kazo ka daukeni ka kuma kawoni Maldives......ka kuma soke barinku qasar ka daidaitashi da nawa barin har sai na kammala uzurina sannan mu tafi......daga qarshe ina me baka umarni kaje kaga fareeda......ka kuma marabceta kaman yadda kowanne baqo yake marabtar baqonsa......wannan umarni na ne indai nice na haifeka" Daga haka ta yanke kiran ba tare data jira cewarsa ba. Shima wayar ya sauke daga kunnensa yana kallonta,kafin ya sakata a tafin hannunsa yana dan dokata kadan kadan. Kallonsa farouq yayi kafin ya aje dubansa ga wayar hannunsa. Ya fahimci wadda tayi kiran ya kuma ji wani abun da take cewa saboda magana take da qarfi da kuma fushi. A abinda yake lisssfawa zaiwa fareeda kowanne ya debo sai yaga yayi masa kadan. A hankali maganganun maamah din sai yaji kamar suna tafiya da farincikinsa suna son rushe duk wata walwala daya samu. Idanunsa ya bude kan farouq yana hadiye kowanne bacin rai da maamah ta sanya masa da rudanin saqon daya shigo wayarsa a dazun. "Ina jinka......kaman magana kakeso muyi ko?" Yace da farouq. Idanu yadan zubawa fu'ad din,sai yaji tausayinsa yana kamashi. Kowacce ni'ima da baiwa ta rayuwa Allah yayi masa......amma ya rasa UWA TA GARI. Ya sake yarda tabbas rayuwa jarabawa ce,hakanan kowanne dan adam akwai inda tashi jarabawar take,ba wanda yake samun jin dadin duniya dari bisa dari. Murmushi farouq ya sakar masa,sai yaji bazai iya kowacce magana dashi a irin wannan yanayin ba,don haka ya sauya akalar zancan yana yin murya qasa qasa "Wai yaya akayi wannan gingimarin ta iya hawa saman keke?,karaya nawa keken ya samu?,duk da ni shaida ne akan yadda keken ya kusa komawa akwala sabod......" Naushi yakai masa cikin sa'a ya daki iska. Ya fahimci lallai da gaske farouq so yake ya maidashi birin wasanshi. Gefe farouq ya koma yana dariya,can qasan ransa yana jin dadin hararar da fu'ad yake watsa masa,yasan tabbas ko bai nasarar gusar da baqincikinsa ba zai rage masa wani abu. "Wallahi ka iya bakinka akan iyali na......kada ka yarda mu saka qafar wando daya dakai" Yayi maganar yana nunashi da yatsansa. Ido farouq ya zaro yana daga hannuwansa sama "Ya salam.....kace me?,iyalinka?,unbelievable.....wazai tayani jin wannan kalmar.......sabreen won the battle" Qaramin dutse ya dauka zai jefeshi ya kwasa da sassarfa ya wuce cikin gida yana cewa "Wallahi ta haukatashi......ya zama madoki" Tilas dariya ta subuce saman labbansa. Sai da farouq ya bacewa ganinsa sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa. Kai tsaye ya kira jordan sukayi magana ta wasu mintuna sannan ya kashe,ya kalli agogonsa yana lissafin awannin da suka rage su kaishi gurin target dinsa. ★K'arfe takwas na dare agogon Maldives ya gama shiryawa cikin wasu lafiyayyun trouser da t.shirt. ta fidda sigarsa sosai da wani sassanyan kyau ke tsayawa a zuciyar dukkanin 'ya macen data Kalleshi. Wani irin mutum ne da zai wahala ka kalleshi ka kauda kai,koda baka furta komai a kanshi ba amma zai tsaye maka a zuciyarka da idanuwanka. Jikinsa yabi ya feshe da turarukansa,sannan ya sanya sau ciki a qafarsa,ya dauki wayarsa da maqulli ya nufi qofar fita daga dakin. Dukkaninsu suna dining area suna cin dinner. Kusan tunda suka iso garin tare suke cin abincin safe dana dare,na rana ne kowa da tsarin cin abincinsa bai yuwu suci lokaci guda. Ire iren wadannan abubuwan sune suke qarawa iyalan anni hadin kai qaunar juna shaquwa tare da fahimtar juna. A kanta idanunsa suka fara sauka,wani irin abu ya tsarga masa tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa. Tun jiya bai sake sanyata a idanunsa ba,suna dakin annin ita da amna. Bazaice ga abinda sukeyi ba,amma lokaci lokaci yana jin muryar amnan da motsinsu,ita kanta amnan bata sake fitowa ba. Ita da amna suna seat din kusa da juna,kaman magana suke qasa qasa,baka iya ji saboda musaddiq da saddiq da suka cika gurin da musunsu da bai gane ma akan meye suke musun ba. Kaman wadda aka umarta,nata fararen idanun da a kwanakin yaga kaman sun qara girma ta daga ta watsa masa cikin rashin sanin shi dinne ya is wajen. Qwayoyin idanunsu suka gauraye da wani irin mabanbantan feeling. Da sauri ta janye qwayar idonta yayin da nata kallon a gareshi ya zame masa kamar wani irin dafi daya sabbabba mutuwar dukkan wasu gabbai a jikinsa. Tsigar jikinsa ta zuba sanda ta soma motsa wadannan siraran lips din nata tana tauna Chip's din dake gabanta. Bazai taba manta abinda yaji daga kowanne sashe na jikinsa ba a ranar farko daya soma tsotsar tausasan lips dinta ba......wani mahaukacin saqo da suka aike masa da baisan inda zai iya adana yawansu a kwanyarsa ba. Yanzun da take juyasu tana tauna sai ya zamana tamkar tsokanarsa takeyi haka yakeji tana aika saqo kowanne sassa na jikinsa. Fitowarsa ya sassauta tashin muryar saddiq da musaddiq din,kowa ya maida hankalinsa jikinsa,kasancewar sunsanshi mutum ne da baison ire iren musunnan nasa. Yakance "Shashanci ne wannan,kuna da abubuwan yi da yawa a gabanku cikin rayuwarku,shi ya kamata ku fuskata" Sau tari musaddiq yakanyi dariya idan bai wajen "Shifa hamma ya dauka kowa irinsa ne.....ba baki nayi mana ba,amma ba zamu iya achieving abinda yayi achieving ba.....we are doing the best,amma ba zamuyi kaman nasa ba". Kujerar dake opposite dintata ya zauna,sam table din baida fadi sosai,wannan yana iya sawa idan ka zura jiki da yawa gwiwarka ta iya taba ta abokin zamanka. Zamansa a wajen sai taji kaman gaba daya ya cika wajen.....kwarjininsa da qamshin sassanyan turarensa gaba daya ya gauraye wajen. Nauyin idanuwansa takeji har tsakiyar kanta,abinda bata taba ji ba a kansa tsahon tarayyarsu. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 84 _Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_ _Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_ 84 "Barka da fitowa hamma" Amna ta fada wadda sun hadu yau kusan sau uku sun riga da sun gaisa already. "Lovey dovey.....barka da dare" Ya fada cikin wani irin aji kaman me qididdige adadin kalamansa na ranar. Murmurshi amna ta saki qasa qasa. "Hamma.....kada ka saka adda sabreen taji kishi fa.....sunan nan for now ya kamata ace nata ne". Daga shi har ita nauyi maganan ya musu musamman da anni ke a wajen,wadda tayi burus kaman bataji ba tana qarasa shan black tea dinta. Amnan ya kalla sannan a dabarance ya saci kallon sabreen din. Bayajin akwai wani suna daya cancanci ya kirata dashi......har yanzun duk sunan daya bata sai yaji tafi gaban wannan sunan. Daidai lokacin tana jefawa amna harara da fararen qwayar idanunta ne,wani irin kyau yaga ta sakeyi masa,tsigar jikinsa yaji ta zuba sosai har sai daya lumshe idonsa. "Ka maida hankalinka fa.....aiki zaka fita kayi" Wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa ganin tana neman dagula dukkanin lissafinsa. "Yi serving hammanku takwarata" Anni data kammala shan tea din ta yiwa sabreen magana. Hakan ya masifar yi masa dadi,sai ya ajiye mug din daya dauko da farko yayi relaxing bayansa jikin kujera yana jin jikinsa yana sake mutuwa gaba daya....wani irin feeling yana taso masa yana sake kashe masa duk wani kuzari nasa. Sai data ji gabanta ya fadi da anni ta fadi haka,amma dole ta ajiye fork din hannunta ta miqe,fork din yabi da kallo,gaba daya ya gama karantarta,bata qaunar abinci ko kusa ko alama....bayajin zai iya bari taci gaba da hakan,dole ta dinga cin abinci me inganci tana qoshi,bayajin indai zata dinga zama ba abincin kirki zata iya dauke lalurarsa yadda yakeso. Shi kansa wani lokaci yana tsoron kansa,tun a lokacin da yake shi kadai ma.....shi da kansa yasan yana da buqatar mace me juriya kafin ya samu abinda yakeso. Faruwar abunnan kuma ya tabbatar masa sa zarginsa,bai taba kawowa ma zata iya dauke buqatarsa.....duk da abinda ya farun yasan akwai aikin gaggawa da kuma rashin sabo a tattare da ita,amma yasan cewa lallai akwai aiki a gabansa,dole sai ya horar da ita yadda zata dace da muradi da tsarinsa. Kwata kwata ya mance ya samu farouq a wajen,ya shagala wajen qare mata kallo ta qasan idanunsa. Zaka dauka sam ba ita yake kallo ba,amma kowanne motsi da zatayi idanunshi suna kanta sanda take zuba masa abincin. A cikin qaramin hijab take,amma shi ba hijab yake gani ba,wannan kyakkyawar surar tata yake gani,kyakkyawar surar da yakejin koda zata shekara a yana ganinta zallarta bazai gaji ba......kyakkyawar surar data kusa qwace kowanne tunani tasa,ta kusa sanyashi manta waye muhammad jadda gaba daya. Wani sashe na zuciyarsa dake danqare da mahaukacin kishinta ya soma masa zafi,gani yakeyi musaddiq saddiq da farouq dake zaune a wajen suma suna iya ganin abinda yake gani.....yana jin kamar duka suma qare mata kallo sukeyi. "Gyara kintsi yallabai.....anni fa na wajen nan kada a tafka abun kunya" Cikin kunnuwansa ya tsinci muryar farouq yana fada. Cikin dakiya ya gyara zamansa yana basarwa,abinda ya kusan sawa farouq ya fashe da dariya. "Shi yasa ake cewa bawa yaji tsoron Allahnsa koda yaushe" Farouq ya kuma fada sama sama. Tunu fuad ya gama karantar abinda yake fada,so amma yanzun baida energy din kulashi. Hannu yasa don karbar mug din da take miqo masa,cikin dabara ya hade da zara zara yatunta da suka ja hankalinsa sosai,ya kuma motsa hannun nasa yana lullube bayan hannunta da tafin hannunsa. "Thank you" Ya fada da wani irin sauti can qasan maqoshinsa yana karbar mug din. Kaman an yarfa mata ruwan sanyi haka taji sanda dumin tafin hannunsa yake ratsa kowacce jijiya ta jikinta,ta koma ta zauna tana jin cikin ta duka ya gama cushewa ta qoshi da chips din,sai ta koma juya cokalin kawai. Tana jin hirarrakinsu amma ita din ta gaza cewa komai,kaman yadda shima ta fahimci jifa jifa yake cewa wani abu. Kanta da idanunta cikin plate din,ta gagara daga idanunta saboda yadda takejin kowanne motsi nata ita yake kallo,ranta ya dinga baci kadan kadan,wannan wanne irin kallon wuce qa'ida ne?. Ta aje kallo a muhallin mazan bariki,wanda yawancinsu suna amfani da wannan hanyar idan sunso dilmiyar dake su afakaki komarsu.....wannan dalilin ya sanya da wurwuri take qarawa namijin da ya fiya kallon wuta. Amma wannan karon nasa kallon sai taji ya banbanta da nasu,don nashi kashe mata jiki yakeyi,ya kuma aza mata wani kwarjininsa sosai da har yake hanata sakewa. Tsoro sosai taji sanda taji ana lalubar tafin hannunta ta qasan kujerar. Ta fidda idanu waje tanason fahimtar waye,saidai ya bata haske ta hanyar cewa. "Miqo min tissue paper dincan please" Da wani narkakkiyar murya. Kallonsa tayi ya kashe mata ido daya,ta janye dubanta da sauri tana tura masa tissue din,ya dauka ya aje gefe yana ci gaba da cin abincinsa tabbacin ba amfani zaiyi da ita ba kenan. Tana ji tana kuma gani yaci gaba da murxa tafin hannun nata ta qasan table din,lallausan tafin hannunsa yana saukar mata da wata irin kasala da kuma tsoro,bai bata dama ba ballantana ta miqe ta nesanta kanta dashi,ba kuma zata iya nunawa kowa abinda yake faruwa ba. "Amman adda.....you look familiar,tun randa kuka iso Maldives naji kaman na taba ganin face dinki......kin taba zuwa asibitin SAMHG?" Musaddiq ya shigo da maganar cikin hirarsu. Duban musaddiq tayi tana qoqarin daidaita yanayinta kada wani ya fahimci akwai abinda ke faruwa under the table. "Eh......kaman sau daya ba......na taba kai wata....." Zancanta kuma sai ya katse,ta maida dubanta kan fuskar anni. Duk tsahon watannin da kwanakin sai yanzu fuskar ta dawo mata fes cikin kanta. Matar nan data fadi wajen sallah asma dinta taso tashi. "Exactly anni itace..." Ya fada yana sakin murmushi sosai gami da ture abincin gabansa. "Anni ya akayi kika samota?.....wannan data dinga mana masifa saboda mun barki ba kowa a wajenki.....wannan dinnan dataqi bayyana kanta bare ki gode mata,bayan ta dawo miki da jakanki ba'a dauki komai a ciki ba". Maganganun musaddiq suma sanyashi daga kai daga abincin da yakeci yana maidawa kan fuskarta gami da matse yatsunta softly cikin nasa,yanason yaji qarin bayani,yanason samun tabbacin da gaske ita ta taba cetar anninsu?. Anni da mamakin duniya ya isheta ta ware hannunta tana sakin qaramar dariyar farinciki "Ban sani ba musaddiq......hammanku zaka tambaya.....duk da shima nasan bai sani ba,tunda bai santa ba" Ta qarashe maganar tana kamo hannun sabreen ta riqe cikin nata "Yau kuwa zan miki godiyar da nayita so nayi miki ban samu dama ba.......sai gashi cikin hikimar ubangiji wadda ta ceci raina ta zama mata ga yaro na......dame zan saka miki sabreen?". Numfashi taja sosai kaman numfashinta zai qwace mata saboda yadda ta qasan table din fuad din ke mata wani irin salo tsakiyar tafukan hannayenta. Ta kasa fadin komai,sai muryar anni data sake ratsowa. "Komai zan miki ban saka miki ba takwara.....lallai kinyimin abinda bazan iya saka miki dashi ba.....wallet dina babu ko sisi da aka taba a ciki,kaman yadda wayata ta dawo lafiya lau.....ubangiji ya jiqan magabatanki ya kyautata makwancinsu.....na gode na gode sosai". Murmushin jin nauyin annin ta saki tana yin qasa da kanta. "Ba komai anni......idan har kana da hali dole ka taimaki wanda yake buqatar taimakon nan,da jikinka koda kudinka". Kai take jinjinawa tare da sake qaunar sabreen din,qasan ranta kuma tana tsara wanne abu zata mallakawa sabreen madadin kirkinta gareta?. Hirar yadda abun ya faru a ranar aka fara maidawa,kadan kadan yana kallon fuskarta yana cin abincin,kallon dake qara bashi qwarin gwiwar cin abincin. Duk wani hirar abun da sukeyi sai yakejin kamar suna qara mata gurbi ne da muhalli cikin rayuwarsa. "Ashe ta mallaki wannan dabi'ar me kyau?" Ya tambayi kansa yana tuna kiran wayar anni daya dinga yi a wancan lokacin. "Dama can me tsiwa ce.....dama can bata da tsoro" Ya fada qasan ransa yana tuna yadda ta daga wayanshi har sukaso yin fada. Tana kallonsa ya gama laqai laqai dinsa,abincin da zaici cikin minti ashirin sai daya jashi talatin da biyar,kafin ya gama duk ta jiqe da gumi,tayi saurin miqewa tana cewa "Bari nayi fitsari" Sanda ta samu ya cire hannunsa a nata. "Karki yadda da tsarin yin nesa dani......bazan lamunta ba" Ya fada mata qasa qasa sanda take giftashi. Numfashi kawai ta dinga saukarwa cikin bandakin tana jin bacin ransa,haka kurum zai fara zame mata takura ya hanata sakewa?. Wucewarta yasa yaji cin abincinsa ya qare,ya dan ture plate din yana miqewa. "Anni zanje Vaadhoo......but bazan jima ba". Maganansa ya daki kunnenta sanda ta murda qofar dakin anni zata shige. Bata fasa shiga din ba,duk da tayi kaman ta tsaya ta kuma waiwaya ta kalleshi. " Vadhoo kuma?,wajen wa?" Ta tambayi kanta tana zama gefan gadonsu zuciyarta na tuna mata abinda ya faru na qarshe a wajen a waccan ranar.......ranar data bashi dama ya bude wata qofa da ba tashi ba....qofar da bata tanadawa kowa ita ba. Kusan minti uku tayi zaune a wajen,bata shiga bandakin ba bata kuma san me take tunawa ba. Wani mugun tsaki taja,hankalinta yana dawowa jikinta "Ko ina ma zaije menene naki a ciki?" Ta tambayi kanta da kanta sannna ta miqe da confidence tana shiga bandakin don rage fitsarin da taji mararta ta tara. Sanda Jordan ke bude masa murfin motar yaji amna na kiransa. Sai daya shiga ya zauna yabar qafafunsa a waje sannan ya jira isowarta. "Ga card dinka hamma" Ta fada tana miqa masa black card din. Hannu yasa ya karba yana juyawa. Yana jira yaga nawa aka cira?,amma har yau baiga an dauki ko sisi ba. "Amneee.....kun gama amfani dashi ne?". Kai ta mirgina tana dubansa a shagwabe kaman yadda ta saba musu. "Hamma.....adda na kam daban take,taqi karba ma bare ta cire komai,duk inda akaje ko za'a siya abu sai tace bata buqatan komai.....haka adda take wai?,bata da buri sam sam?". Idanusa yadan lumshe yana kuma budesu lokaci guda,wani abu yana saukar masa a zuciyarsa. Yasha aje abubuwa masu daraja da amfani a dakinsa amma koda ta gyara masa inda ya aje komai haka yake zuwa ya sameshi. Baisan adadin dollars da pounds din da yake ajiyewa ba amma ko qwaya daya bai taba dubawa yaga ta zara ba. Kai yake jinjinawa,yanason karantar wacece ita?,yanason ya santa sani na zahiri.....a dazun yaji anni na yiwa iyayenta addu'a marainiya ce da gaske?. Wani guri ya danna ya zira card din,yana jin a jikinsa bazai iya tafiya bai ganta kusa dashi ba,bazai iya tafiya baiji dumin jikinta ba,qilan idan ya tafi a haka bazai iya aikata komai ba,don haka yace "Jeki ki kiramin ita......but kiyi sauri ana jirana" "To" Amna ta fada tana juyawa ciki. Tana fitowa daga toilet din amna na shigowa. "Matar hamma hamma yana kiranki.....yace kiyi sauri zai fita ne" Ta fada da dan dariya alamun tsokana kenan a muryarta. Ta bude bakinta da zummar aika masa ba zata samu daman zuwa ba saita hangi anni na shigowa daga baya,wannan ya sanya taja bakinta ta rufe. Batasan me zata cewa amna ba,zataje ko bazata je ba......amma yadda anni tayi magana ya tabbatar mata annin tayi supporting taje din. "Idan kin dawo takwara ga ragowan magungunanki nan" Ta aje wata 'yar jaka a hannunta ta juya tana bar musu dakin. Sai dataga fitar anni ta gasawa amna harara. "Tsakaninki da Allah shi ya aikoki?,banason wasa amna?" Ido ta zaro waje tana duban sabreen gami da son boye dariyarta. "Am serious Allah adda......ba ruwana shikeson ganin matarsa" Ta fadi tana watsa hannaye. Harararta ta sakeyi ta taka tana neman hijabinta daidai nan anni ta sake shigowa. "Kuyi da jiki kuzo inason ganinku" Maganan ya gaya mata da ita anni take,sai kawai ta zunduma hijabinta tayi gaba tana qunquni cikin zuciyarta. Itakam ta shirya barinsa cikin kwanaki kadan,....don meye zaita kusanta kanshi da ita?,waima ba zaluntarta da cutarta yakeso yayi ba?,kuma duka yayi?,meye sauran abinda yake nema kuma?. A hankali ta dinga takawa har ta isa dab da bakin qofar motar inda yake zaune. Tunda ta fara takowar idanunshi yana zube a kanta ta side mirror. Ya lumshe idanu ya bude yafi sau goma,yana jin tana tayar masa da makamansa,wani irin taku gareta da bai taba lura dashi ba sai yanzu......takun qasaita takeyi kamar na bijimin dawisu. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 85 85 "Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen" Ya motsa labbansa yana fada yana kallon yadda sassan jikinta ke juya kansu sanda take takawar. Da hannunsa ya dafe kansa yana jin kishi yana cin zuciyarsa,ta fita da abaya me madauri......ta fita da Chantilly......ta fita da qaramin mayafi duka dai kenan kowa ya taba ganin jikinta?. "Dole na killace kayana" Ya fadawa kansa da kansa cikin qwarin gwiwa. Kaman bashi yake neman susucewa ba sanda take takowar ba ta cikin madubi,data iso gabansa sai ya zubawa fuskar nan tasa wannan izzar tasa data sanshi da ita. Ya dubeta a kaikaice. "Haka ake zuwa kiran miji,ka yima mutum tsaye aka?" Ya fada a dake girarsa a tsuke. Duba daya ta masa ya mata kwarjini ta dauke kai,ta soma mita qasan ranta saidai batasan labbanta suna motsawa ba "Waye yace ka kirani ina zamana?,sai kayi rayuwarka nayi tawa ai,kada wanda ya damu wani" "Shigo ki gayamin abinda kike cewa" Yayi maganar duka da jawota cikin motar lokaci guda,sai gata kwance a qirjinsa ya dafeta sosai cikin jikinsa,yasa daya hannun nasa yana rufe murfin motar,sannan ya taba wani abu take glass din motar duka suka zama tentac fitilun motar suka koma blue me haske da fari. Sun samu cikakken tsaro da hijabi ta yadda bame iya ganinsu. Qoqarin tashi takeyi a jikinsa amma ya hana mata wannan damar,ya mata wata kyakkyawar runguma data sanya numfashinsa ya soma sauya. Maimakon ya barta ta tashinma sai ya kamo fuskarta ya riqeta dab da tashi yana kallon qwayar idanunta,hannunsa daya sauka a qirjinta zuwa wuyanta yana jin yadda zuciyarta ke bugu tak tak tak. "Ms kike fada dazun?,speak louder" Yayi maganar hucin numfashinsa daya gauraya da qamshin mint na bakinsa tare da sassanyan turarensa suna neman lahantata da tsoronsa da kuma wani kwarjini. Mutsu mutsu ta fara yi cikin tsoron sauyawar da taga launin idanunsa sun fara yi tace "Nifa bance komai ba" Shuru ya mata bai amsa mata,sai qarewa kyakkyawar fuskarta kallo da yakeyi,kwantacciyar gashin gira dana ido,pink lips dinta da suka dan dago saboda yadda ya riqe fuskarta. Ajiyar zuciya ta kubce masa,ya fahimci kaman akwai tsorosa a lamarinta abinda bai fara ganinsa ba sai bayan faruwar abun,duk da Dr fadwa ta gaya masa zai iya experiencing hakan a na gaba dama.....so dole next time yabi komai a sannu. Hannu ya sanya ya fara zame hijb din jikinta yana hade rai. "Ba cewa nayi fa kizo muje gidan wa'azi ba......wannan abun haramunne ki sanyamin shi....na kiraki ne na koya miki yadda ake gaida miji fa". Sosai ta tattamke hijab din tana jin hankalinta yana tashi. Kai ta fara girgiza masa,tasan muddin ya fidda mata hijabin ya sake gamawa da ita. "Karkiyi gardama......bana so" Ya fada mata da idanunsa da suka qarasa jirkicewa yana girgiza mata kansa gami da kallonta kai tsaye ta cikin nata qwayoyin idanun. Bata yarda ba ta fara qoqarin saita hanashi cirewa,bata Ankara ba ta jita luuu ta zame ta kwanta,sai daga bisani ta Fahimci kwantar da kujerar yayi ta koma kaman wani qaramin gado. Daga qasa ya sanya duka qarfinsa ya tattare hijabin a zafafe,abinda ya sanya ta gefe da gefe jilbab din ya soma yageqwa dinkin yana farkewa,bai saurara mata ba sai daya tsargeshi ta bangare daya ya koma kaman mayafi,kafin sannan hawaye ya gama jiqa mata fuska. Qarasa tattareshi yayi ya zareshi daga jikinta,take skirt dinta da iyakarshi qaurinta ya bayyana,vest din jikinta data dameta ita fito wadda zallarta ta saka babu ko brazier a jikinta. Saman na shanunta idanunsa ya tsaya,ya zuba musu idanu yana kallon yadda suka cika rigar. Wani irin shauqi ke fusgarsa zuwa garesu,don haka ya miqa hannayensa da zummar kaiwa garesu ya cire rigan data masa shamaki dasu. Tunawa tayi last time da haka ya fara,don haka ta hada dukkanin qarfinta ta riqe masa hannu. "Don't fight it" Ya furta low and husky voice dinsa,idanunsa a tsaye car cikin nata kaman yana tabbatar mata da gaskiyar abinda ya fada mata dinne Idanunsa full with mixture emotions. Kai ta sake girgiza masa,ba zata iya barinsa yaci gaba da rabar jikinta har haka ba.....in fact ma bataga dalili ba,ta sake daga hannunta da nufin tureshi,saidai ga mamakinta tsam ya riqe hannayen nata,ya jawo wani abu kaman belt a jikin motar ya maqale hannayen a jiki. Bazai iya handling hannayen duka biyu lokaci guda a yadda yake jinsa ba......haka bazai iya kuma jurar yadda zata hanashi rawar gaban hantsi ba. Idanu ta fiddo duka waje tana dubansa gami da duban hannayen nata,daidaita tsahonsu yayi,ya sanya hannuwansa ya tallafo fuskarta,yasa hannunsa yana matsar da gashinta daya barbazu a fuskarta zuwa gefe. "Am sorry if i misbehaved you......nutsuwa zaki bani dan kadan.......bazan wuce iyaka ba.....nima ina buqatar lafiyarki......inaso ki warke da wuri" Yayi maganar qirjinsa na dagawa da wani matsanancin bugun zuciya. Kafin tace komai ya hade bakinsu guri daya,ya kuma fara yamutsata da kalan wani abu da bata sanin meye shi ba,batasan kuma akwai kalar abun a duniya ba. Kuka sosai ta saki na yadda yake yamutsata son ranshi,gashi kuma bata da ikon qwatar kanta,tana ji tana gani ya isa ga inda yaketa fusgar hankalin nasa. Fuskarsa ya boye a tsakaninsu kafin ya soma sauke mata wani zazzafan huci daya dinga sauka kai tsaye cikin fatarta yana ratsa sassan jikinta. Ko daya kukanta bai dakatar dashi ba,har sai da yaji ana knocking motar da dan qarfi. Zame jikinsa yayi gefe yana jan tsaki me qarfi,abinda ya bata damar komawa rub da ciki ko zata samun sutura da jikin kujerar motar. Da qyar ya iya bude idanunsa,jikinsa ya gama sakewa gaba daya ya azashi kan qaramin allon computer din dake maqale a wajen. Farouq ne tsaye hankalinsa kusan duka akan wayarsa,yana kallonsa ya sake saka yatsunsa yayi knocking,sai kawai ya dunqule hannunsa ya daki kujerar da yake kai,kafin yaja jikinsa yana miqewa. Hannunsa yasa ya birkitota a tausashe,ta saka hannuwanta tana kare jikinta....saidai batasan sanda ta saki hannayen nata ta damqo hannunsa dake shirin yaye skirt dinta duka zuwa cikinta ba,wanda dama tuni ya tattare ya bayyana santala santalan cinyoyinta. Birkitattun idanunsa ya zuba mata,kai take girgiza masa da guntun hawayenta. Bayani yakeson mata amma ya kasa,koda ya bude bakinsa ba kalmar data iya fita,har sai da yaja gyaran murya sannna ya samu maqogaronsa ya washe. "Inason na gani ne ko dinkin ya warke......ba wani abu zanyi miki ba" Ya fada a tausashe. Kuka ta kuma saki tana jin wani rikitaccen yanayi yana mamayarta,duk yadda yayi mata bai isheshi ba har sai ya bankada sirrinta?. Wani knocking da farouq din ya qara saki shi ya ratsa har kwanyarsa ya kuma dakatar dashi,ya kalli farouq din ta camera din yaji kaman yakai masa naushi ta ciki. A hankali ya saki skirt din,ya kuma zame hannunsa daga nata ya miqa hannu yana dagota,sannan ya taimaka mata ta maida kayanta gaba daya. Yana daga zaune a wajen ya dannan lock ya bude mata,ta sauri ta soma sauka ta fice tana kauda kanta ba tare data yarda sun hada ido da farouq ba. Sai daya tabbatar ta fita ya sanyo kai ciki. Idanunsa yakai kan kujerar data koma qaramin gado,sai ya maida dubansa kan fuad dake zaune dafe da kansa da dukka hannayensa duka biyu farouq din zaiyi magana ya saka hannu ya bude daya side din motar ya fice da sauri,sai ya bishi da kallo sannna daga bisani ya sheqe da dariya,ya saka hannu ya dauke masa agogonsa da da alama baisan ya fice a hannunsa ba. "Allah yasa ta haukataka" Farouq ya fada yana mimmiqewa abinsa saman kujerar abun yana masa dadi. Ba yaro bane shi,yana kallon wajen yasan da magana. Kai tsaye ya wuce cikin gidan,Allah ya taimakeshi bai samu kowa a parlor ba,sai ya zarce zuwa dakinsa yana sauke numfashi cikin tsananin kasala. Tun a motar ya tabbatar wanka ya kamashi,ya fidda kayan jikinsa gaba daya ya wuce toilet ya sakarwa kansa ruwa me dumi. Gilmawarta kawai idanunsa suke ganin cikin toilet din,kowannw motsi nata......fitar hawaye cikin kyawawan idanunta da bai taba lura da wani irin tsaga da zubi da Allah ya basu ba sai yau......tausasan lips da tafukan hannayenta.....wani irin cikakken hips da bai taba ganin irinsu ba duk da cewa kallon mata ba dabi'arsa bace daman. Sai da yaji nutsuwa tazo masa sannan yayi wankan ya fito,ya sake shirya kansa cikin wasu qananun kayan ya kuma ficewa. Koda ya koma motar baiko kalli farouq ba,ya rufe murfin ya bawa Jordan umarnin ya tayar su tafi. Bata iya komawa cikin gidan ba,saita zagaya ta baya can tana tattara nutsuwarta. Ta kusa mintuna talatin kafin ta samo kanta,ta sake gyara hijab dinta sannan ta wuce cikin gidan gabanta yana faduwa,tana fatan Allah yasa kada anni ta gane komai. Kaman wata mara gaskiya haka ta tura qofar dakin tana saka kanta. Duban farko anni tayi mata ta tabbatar kuka tayi,sai ta dauke kanta kawai tana tattare kayanta ta fita ta basu dakin. Fitar annin yadan bata nutsuwa kadan,ta taka a hankali ta zauna saman sofa inda amna ke zaune tana buga game. Bata cewa amnan komai ba don batasan me zata fada ba,gani take yarinyar itama ta karanci komai,kawai saita zame ta kwanta ta maida idanunta ta kulle. Ga mamakinta sai komai ya dinga dawo mata,zuciyarta ta dinga wani irin bugu sanda ta motsa taji jikinta yana fidda sassanyan qamshin nan nasa. "Qamshin turaren hamma adda sabreen.....ko ya sammiki ne ki sanmin nima?" Amna data tsaida game dinta ta fada tana duban sabreen. Gabanta ya fadi,tadan ware idanunta kadan tana duban amna,saita rasa ma abinda zata ce mata,don haka ta juya kwanciyarta tana bawa amna baya sannan ta amsa mata da "Bacci nakeji amna please". Qaramin murmushi ya subucewa amnan "Ni na sani.....hamma na bazai qyaleki ba.....hamma na ba gama garin maza bane,saikinso hamma kamar ba gobe.....sai kinso hamma sama da komai da kike dashi" Amma a fili sai tace "Ayi bacci me dadi tare da mafarkin hamma na" Tana jinta amma bata ce komai ba,tsoro takeyi kada ta fadi abinda zai sanya a gane komai tattare da ita. Har suka soma daukan hanya ba wanda yace da kowa komai,sai daga bisani fuad din ya gyara zamansa yana tambayar farouq ba tare daya kalleshi ba "Ina zaka ne ka shigo mana mota?" Yayi maganan a dake,wanda duka farouq yasan yayi ne don borin kunya kada ya sake masa magana kan abinda ya shigo ya tarar. "Kai ina zaka?" "Vaadhoo" Ya amsa masa kai tsaye. "Me zakayi ne a Vaadhoo?" Farouq ya tambayeshi yana duban. "Gurin fareeda.....but don't ask too much" Ya amsa masa a gajarce. Bai iya qarya ba.....shi yasa ya masa kandagarki. Motsawa kadan farouq yayi,yaga fareeda a ranar kafin su baro vaadhoo din,kuma jikinsa haka kawai ya bashi akwai abinda ya faru. Ba kasafai ya fiya son barin fuad idan yana fushi ya dauki.mataki akan mutum ba,shi yasa fitowar da yayi ya zargi wani abu ya kasa zama ya biyoshi,ya Tabbatar indai wani abu ne ya hadashi da fareedan bazai barta tasha da kyau ba koda waye ubanta,to amma sai yakama bakinsa,baiso yace wani abun farouq din ya sauya shima. _uhmmmm.....fareeda?.....ga maza nan gareki....malam farouqu ko muhammad jadda zai barka ka shiga har inda zaije din?,bari mu gani_ _maza maganin maza....da d'aya da d'aya komai zai fallasa_ _ina muku barka da litinin da cikakken yaqinin mun dawo sai munga abinda ya turewa buzu nadi,na gode_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 86 86 Idanu sosai farouq ya zuba masa,kaman zaiyi magana sai ya fasa ya maida kansa kan wayarsa sukaci gaba da chart da fanna. Abu daya ya sani shine,bazai bar fuad ya qarasa wajen fareeda shi kadai haka kai tsaye ba,don yasan halinsa sarai.....bai iya daukan abubuwa serous ba. Jifa jifa suke maganganu da suka shafi kasuwanci,wanda saisun samu dama irin haka sukeyi,duk da kusan shirun fu'ad yafi yawa. Har yanzu tsigar jikinsa zubawa takeyi idan ya tuna abinda idanunsa suka gani tattare da ita karo biyu kenan,har yanzu yana jin kowanne sassa nata cikin hannunsa da jikinsa kaman suna tare. "Anya zan iya barinta for 2months kuwa?" Ya tambayi kansa cikin shakka da kokwanto. Ba jimawa suka isa Vaadhoo suka kuma wuce glowing beach. Wayarsa ya ciro a nutse,ya rubuta gajeran saqo ya turawa mutum biyu sannan ya maida wayar aljihunsa yana gyara zamanshi. Yasan manufar farouq.....yasan meya sanya ya biyoshi,shi kuma baya fatan abinda zai rageshi ko ya hanashi cin uban fareeda la'ada waje. Zarginta yake dari bisa dari akan wasu abubuwa da dama,yana da tabbacin zaiji abubuwa da dama daga bakinta akam sabreen. Ya shirya kare mutuncinta da martabarta,ya shirya tsaya mata a duk inda ake buqatar wanda zai tsaya maka......ya kuma shirya nunawa duniya ita din matarsa ce kuma iyalinsa ce dake da kima mutunci da martaba kaman kowacce mace. A hankali motar ta dinga ratsa farin yashin da bame yawa ba,kasancewar sasannin tsibirin ruwa yafi yawa,ba kasafai kake doguwar tafiya bisa mota ba saidai boat boat. Kyakkyawan parking jordan yayi,fu'ad ya sanya hannunsa ya bude motar yana sanya qafafunsa waje. Budewa farouq yayi shima ya fita,ya zagayo gefan fu'ad din sannan suka fara takawa zuwa muhallin da aka tanada saboda zaman shan iska. Da idanu ya yiwa jordan alama,sai yaja baya ya barsu su biyun har suka isa saman kujerun. Suna zama wasu Maldivians guda uku suka qaraso. Cikin harshen dhivehi daya kasance yaren qasar,biyu daga cikinsu suka zauna dayan ya juya zuwa sashen da aka tanadi abubuwan sha saboda baqi. Ba jimawa ya dawo ya zube musu halal drinks da ruwa da gasashen kifin da aka wadata da vegetables da da lemon. Agogon hannunsa fu'ad ya kalla,yaja baya yana miqewa. "Ina zuwa" Ya fada yana basarwa,hankalin farouq yakai kanshi,amma maganan da daya daga cikinsu ya masa cikin harshen turanci ya dauki hankalinsa,ganin fu'ad din gaba kadan ya matsa yana waya bawai gurin ya bari ba gaba daya sai ya maida hankalinsa kan mutumin,saboda ya masa magana akan abinda ya shafeshi ne wato harkar noma da Samar da iri da taki na zamani. Sannu sannu ya bashi hankalinsa sosai saboda hirar tayi masa,da wannan fu'ad ya samu ya zille abunsa ba tare da farouq ya ankara ba. Yana takawa zuwa dakin shida Jordan ranshi na sake baci. Ya tabbatar a ranar akwai abinda yasha......akwai abinda ta bashi. Yaya akayi ma tasan dakin daya sauka?,har ta samu access da dakin cikin sauqi?,bayan wajen ya sani wajene me tsaro da matuqar sirri. A lokacin tana zaine d'ai d'ai saman gadon tana busa shisharta. A kwanakin shisha kawai take bugawa cikinta ta hada da syrup. Tuni ta kori lubna daga dakin,saboda tana jin bata buqatar kowa a kusa da ita. Tana buqatar abinda zatayi refreshing damuwarta kafin tasan abinyi next. Bata taba tunanin zata hadu da asara da faduwa ba irin wannan,ta dauka komai zai tafi daidai,musamman data san cewa ba qaramin dosage ta sanya a zuba masa ba. Sai gashi cikin mintuna qalilan komai ya wargaje,tsananin taurin kansa da kafiyarsa ya hana komai yayi tasiri. Tun bai murda qofan ba qamshin flavors din ya soma masa maraba,ya yatsine fuska rai bace yana isa qofan. Duk da wajen mutane da yawa flavour na shisha qamshi yake musu.....amma tsananin yadda ya tsani shaye shaye ya sanya shi a wajensa baida maraba da warin wiwi. Daga ranar kuma da bincike ya tabbatar da zuqa daya na shisha daidai yake da ka shanye sigari kara dara biyu ya sake mata muguwar tsana,inda Allah ya rufa musu asiri kaf dinsu Allah ya duba addu'ar anni a kansu,babu me shan komai koda shishan da wasu suke mata kallon ba abar shaye shaye bace. Kallon farko da suka yiwa juna ita dashi,ita din saita dauka cikin gizanniya take ganinsa bawai me jadda bane real ain. Ta ajiye tiyo din shishan tana miqewa zumbur farinciki yana ratsata,wata mayaudariyar zuciya daga can cikin qirjinta tana gaya mata "Ya rasa me kashe masa wutan sha'awarsa.....har yanzu abun na ruruwa a jikinsa shi yasa ya dawo miki......ya tabbatar ke zaki iya masa wannan aikin" Da wannan yaudararrun kalaman ta soma tafiya da sassarfa tana nufarsa fuskarta da shimfidaddiyar fara'a. Saidai kuma dab da zata isa gareshi ya qare yatsunsa biyar ya sauke mata wasu lafiyayyun maruka guda biyu qwarara hagu da dama,marukan da suka sanya kowanne connection na jikinta tsayawa na wucin gadi kafin komai ya dawo mata aiki. Sai a sannan sashen dake gaya mata gaskiyar komai ya fara aiki,ta lura da wani lafiyayyen bala'i dake kwance saman kyakkyawar fuskar da a yau ta juye kaman ta mayunwaci kuma fusataccen zaki. Nuni kawai ya mata da hannu na wajen zama,ta kalli gurin sannan ta maida dubanta kanshi zuciyarta na mata wani irin zafi. A yau ita fareeda Khalid mustapha wani d'a namiji ya sanya hannunsa saman fuska.....isashiyar macen da mata da dama suke buri gami da fatan hawa matsayinta?......macen da batasan adadin mazan da tayi rejecting ba da suke fatan mallaka mata komai nasu don ta kasance tare dasu?. "Ni ka mara?" Tayi tambayar da yanayin dake nuna tsananin zafin da marin ya mata,bawai ga iya fuskarta kawai ba.....har cikin zuciyarta da ruhinta. "Kina buqatar qari ne?" Ya tambayeta yana dage dukka girarsa guda biyu,hannayensa xube a aljihun wandonsa don ya tabbatar idan ba hakan yayi ba zai iya rufeta da mahaukacin duka. Shi kuma bai shirya aza hannunsa saman qazamin jikinta ba.....don bayajin ta samu wannan darajar. Marin da yayi mata dinma ya gaza shanyewa azo gabar ne,yana kuma son bata alamun cewa gagarumin bala'i ne ta daukowa kanta da bata da qarfin ikon tarewa kanta shi. Taku ukun da yayi yana jifanta da wani qasqantaccen kallo ya sake rage tazarar dake tsakaninsu sosai,wannan ya qara yawan kwarjininsa cikin idanunta,ya kuma sake qara mata tsoronsa. Abinda tafiso a rayuwarta shine ya kusantota,amma a yanzun da ya kusantota din sai take jin kamar wani baqin kumurcin maciji ne yake nufota. Da hannu ya sake nuna mata seat yana zube mata idanun nan nasa dake da wani ajiyayyen kwarjini na musamman,wannan karon ba musu ta koma da baya ta zauna,saidai har qasan ranta tana rubuta abinda yayi matan a matsayin yaci bashi. Gabanta ya iso yaja kujera dab da ita ya zauna,har tana jin fesowar qamshin sassanyan turaren nasa. Bata taba tunanun kwarjininsa yakai haka ba sai a yanzu daya sake kafeta da idanunsa da suka qara girma,ya zuba mata idanu kaman bazai daina kallonta ba. Ba abinda yake gani tattare da ita sai wata mummunar mace maras aji da kuma fasali idan ya dauko hoton fuskar sabreen dinsa ya kwatantata da tata. Wata ballagazar mace da babu wani abun burgewa qwaya daya tattare da ita. "Tambayoyi ne zan miki su da bansan qwaya nawa bane,amsarsu kawai nake da buqata.......samun amsoshinsu sune kubutarki.......ki manta ubanki waye da farko.....sannan kema ki manta wacece ke......kiyi tunanin makomarki da abinda zai iya faruwa dake.......ki manta kin bawa mariya ahmad kudade don ta mallaka miki Muhammad fu'ad....." Ya fadi maganar yana jin wani d'aci yana tasowa daga qasan zuciyarsa,yana jin zuciyarsa kuma ta matse waje daya. Da wani irin zafin nama ta bude idanunta a kansa tana mamakin ta yaya yasan da wannan deal din?. Sai daya hadiye abinda ya taso masan sannan yaci gaba da magana. "Baki da wani ko wani abu da zai iya mallaka miki wannan muhammadun har abada" Ya sake fadi yana nuna qirjinsa da yatsarsa. "Koda babu ameenatu sabreen a gefe na......ballanta tana cikin DUNIYATA tana cikin rayuwata....na tsere miki tserewa ta har abada.....bama keba,duk wasu mata ire irenki......WAYE YA BAKI DAMAN KIRAN MATATA DA KARUWA?.....WAYE YA BAKI WANNAN LASISIN?" ya mata tambayar farko da ita tafi tsaye masa a wuya fiye da kowanne abu. Wata irin wutar kishi ta taso mata,ta kuma yaudareta da cewa ya zauna ne yaci fuskarta kawai......ta yaya tana cikin jerin masoyansa zai zauna yana mata tambaya akan wata mace da batajin ta fita komai?. "Au bakasan karuwa kowa yake kiranta ba?,bakasan karuwa ka aura ba dama?". Ta fada tana danne tsoron dake taso.mata,saboda yadda zuciyarta ke qarfafa mata gwiwar idan yaga tsoro a idanunta to tabbas ta karya lagon kanta da kanta. Labbansa na qasa ya cije yana kausa kansa daga fuskarta,kalamanta suna qonashi da wani irin zafi. "Jordan" Akwai yace yana dunqule hannunsa waje daya,saboda bayason yakai hannunsa kan qazamin jikinta. Taku daya jordan ya qaraso bayanta,wanda kwata kwata bata kawo komai a kiran nasa da yayi ba,ba zato ba tsammani taji an take yatsun qafarta an kuma murjesu da kyau har sai data fasa wata qara tana jin azaba tana ratsata,qarar yatsun kuma suka baqunci kunnenta da qas....qas.....qas...daya bayan daya,tabbacin qasusuwansu ne suke rarrabuwa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 EID MUBARAK TO YOU ALL ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEN SUMMA AMEEN SHUKRAN JAMEE'AN🙌🏽🙌🏽🙌🏽🥰🥰🥰 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 87 87 "Ka dagani......ka sakeni!qafata.....qafata" Ta fada a mugun rude kuka da fitsari dukka yana qwace mata lokaci guda,sake take dayar yayi sosai yadda itama yasan zataji a jikinta ba alamun tausayi sam a tare da jordan din. Sai daya kalli fu'ad sannan ya bada damar ya matsa baya,ya dauke qafarsa yana cewa. "Kiyi magana dashi da manners.....kiyi magana dashi in a polite way......idan ba haka ba kafin bincike ya kammala duka sai na kusa dake sun kasa ganeki". Ko jordan bai fadi haka ba ta fahimci abinda ke shirin faruwa kenan. " Shut up!" Fu'ad ya daka mata tsawa yana kallon yadda ta sauya launi tun karon farko. "Wannan shine ya baki qwarin gwiwar buga sunana dana matata a jarida?.....bakisan ta fiki daraja ba?,ta fiki mutunci......ta fiki duk wani abu da mace ke jin tana taqama dashi ba......su wadanda suka baki shawarar aikata hakan basu gaya miki waye muhammad jadda ba?!" Ya jefeta da tambaya yana jin wani tururin bacin rai yana taso masa. Tayi matuqar rudewa,ta kuma girgixa qwarai da gaske. An gaya mata....ma'aikatan ma sun gaya mata,da qyar ta samu suka yadda zasuyi aikin. Sun jaddada mata waye jadda din,amma a sannan idanunta basa ji basa gani,burinta kawai ta bata mata suna......ta tona mata asirin da shi kansa baisan dashi ba,ta saka masa shakka da kokwanto me yawa a kanta. "Su waye kika aika cikin gidana har dakin matata!?" Ya sake mata wata tsawar da sai da taji 'yar qwarya qwaryar gudawa ta hadu a cikin ta ta cure lokaci guda,glass doors din dakin kaman zasu tsage saboda yadda suka amsa. Tashin hankali......kada dai ace ta taka sahun barawo?,da yaushe kuma aka shiga gidan nasa?......wata shigar akayi bayan wadda mahaifiyarsa tasa ayi?. Da sauri ta fara girgiza kai tana dubansa da sabbin hawaye,don gaba daya yatsunta bata jinsu a gangar jikinta. "Ban sani ba wallahi.....bani bace.....saidai.....saidai....." B'am bakinta ya bame ya kuma kasa kama sunan maamah kaman yadda take da marmarin shaida masa ita ce. Tanason gaya masa mahaifiyarsa ce,ga sunan a bakinta amma ta kasa furtashi waje,ta dinga kokawa da harshenta amma kaman wadda gabbai ko rassan maganarta suka samu matsala. "Saidai me?" Ya tambayeta yana tsareta da idanu yanason samun ragowar tabbacin da yakeson samu. "Na gidan jaridan......nice" Maimakon wancan bayanin ta sake bashi yaqini akan wancan tana sunkuyar da kanta,baqinciki da bacin rai yana cika zuciyarta. Me ya sameta ta kasa gaya masa sirrin da baisan dashi ba?,idan ita yasa an mata irin wannan mummunan dukan ita kuma da take uwarsa tana son taga ya zaiyi da ita. Idanu ya zuba mata,yana ji a jikinsa akwai saura......akwai abinda yayi saura.....akwai abinda jikinsa yake bashi game da ita wanda ya rage bata fada ba. Saman qafafunta ya maida kallonsa bayan yaja kujerarsa nesa da ita. Ta sauqaqawa kanta wahala......don ba qaramin bugu yaso Jordan yayi mata ba da qattin qwanjinsa. Yaso ya rage mata adadin yawan haqoran dake a bakinta ko zasu zame mata tunasarwar shigarta hurumin muhammad fuad anan gaba,ya kuma zamewa 'yan baya izina. Qafar ta tasa tayi suntum cikin qaramin lokaci,alamun mummunan targade ko karaya sun samu wajen zama. Banda ita din mace ce baya jin iya wannan dukan ya wadatar dashi,amma duba jinsinta yakeyi.....idan yace zai zazzage dukka muguntarsa a kanta ba zata wanye lafiya ba. Ya maida kallonsa ga fuskarta da har ta suntume,kamatunta sun tasa sun soma hayewa saboda munin marin daya sauke mata,idanunta har sun fara yin ciki "Zan baki dama ta qarshe da zaki fice daga rayuwata.....ki kuma sanyawa ranki baki taba sanin wata me suna sabreen ba.....fu'ad kuwa ki saka a ranki a saqe saqen mafarki kika taba saninsa.......saidai kafin sannan......na baki wata guda kacal kije kiyi jinyar qafafunki da fuskarki,zan sake waiwayarki......ba kuma waiwaye na arziqi ba. Sa'arki daya labaran ba inda suka fita.....yau da newspapers dinnan sun fita...." Sai ya kada kai daga hagu zuwa dama "Ko buzunki ba za'a samu ba ina me tabbatar miki da wannan" Ya qarasa fada yana nunata da yatsa. "Kije kiyi jinya kafin amsa tuhuma ta gaba......ruwanki ki gayawa babanki......ruwanki ki rufe bakinki wannan matsalarki ce......amma inaso ki rubuta ki ajiye.....idan ma kina da plan na guduwa wani guri da kike tunanin zaki samu tsaro to ki sani.......lahira ce kawai zaki tafi ki kubuta daga tuhumar muhammad jadda" Daga haka ya miqe tsam yana takawa yana barin dakin. Har yakai qofa sai ya dakata,ya juyo ya watsa mata wani kallo sannan yace. "Daga yau.....na yanke duk wata alaqa tsakaninki da maamah......idan kuma baki yarda ba ko kina doubting akai......ki sake koda kiran layin wayarta ne.....koda sau daya ne" Ya furta yana daga doguwar yatsarshi dan manuni,sannna ya sanya qafa ya fice abinsa. Tunda tazo duniya ba'a taba gwada mata azaba irin wannan ba......tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin qasqancin d'a namiji ba irin na jadda. Inda wanine yau yayi mata wannan abun ta tabbatar bazaisha ba a hannun daddynta dama ita kanta. To amma.muhammad jadda fa?,ta sani farin sani cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. Alfarmarsa ta wuce duk yadda ake tunani,duk arziqi da alfarmar ubanta da take taqama dasu bai wuce yaron jadda ba. Ta sake tsinkewa da lamarinsa sanda daddynta da kansa yake bata labarin yadda fu'ad din ya soke masa wata kwangilar millions of naira,wanda gwamnatin tarayya taso bashi amma jaddan ya fahimci cin hanci da rashin kyan aikin yayi yawa. Ya fusata a sannan baisan waye jaddan ba,ya kuma bazama da zummar a nemo masa wayeshi a hada musu zama....saidai randa ya soma yi masa ganin farko ya kuma zauna dashi da qyar ya qwaci kujerarsa ta ambassador. Har qasa yakai yana hurwa da neman ya rufa masa asiri,ya barshi ne bisa sharadin komai zai dinga tafiya bisa adalci da amana,ya kuma tsaya da iya muqami da dukiyar da Allah ya bashi. Tun daga ranar suka yiwa juna farin sani,labarin da daddyn nata kuma ya bata ya sanya mata tsananin son mallakar fu'ad din. Tanason namiji me qarfin izza da mulki gami da iko takowacce fuska,a duk inda ya tsaya yayi magana za'a dakata a saurareshi,a duk inda yayi umarni dole za'a bi.....to amma sai gashi dare daya komi ya watse komi ya wargaje mata daga hannunta. "Zan iya barinsa kuwa?" Ta tambayi kanta sanda wata zuciyar ta fara mata saqa da mugun zare.....zuciyar ta fara ayyana mata daukan BAQAR FANSA da kowanne irin hukunci daya kamata ta zartar kawai a kansa. _uhmmmm,nidai nace wanda baiji bari ba yaji hoho_ Ido farouq ya zuba masa sanda yake dawowa wajen. Sai a sannna hankalinsa ya kawo abinda fu'ad din yayi masa. Cikin dakewa da kuma basarwa yace yana zama. "Sarkin noma.....na dawo" Sarai yasan magana ya gaya masa,amma ganin ma ya zaro wayarsa ya soma lalubar wata number sai kawai ya qyaleshi da duk abinda zaice dashi,illa dai yace masa. "Ina fatan baka rabata da numfashinta ba" "Ta samu wannan tsiran saboda batayi musu ko gardama ba" Yana kaiwa nan ya saka wayar a kunnensa yana magana da daya bangren. Ya kusa mintuna talatin yana amsa wayar kafin daga qarshe ya rufe da "Aikinka na kyau CP.....good job,akwai zuwaira......akwai harira ko something hajja......yes......yes" Daga haka sukayi sallama. Zazzafar numfashi ya sauke yana aje wayara a gabansa gami da watsa idanunsa saman glowing beach din da ruwansa ya fara komawa sea of stars,hakanan yashin dake kwance a wajen ya soma glowing sosai kaman an warwatsa taurari a qasan wajen. "Wai wanne irin kame kake ne dude?.....har mutum nawa zaka saka a kulle maka?". Idanunsa da suka masa nauyi saboda tunanin daya cika zuciyarsa ya janye ya maida kan farouq,ya kafeshi da idanu sosai saboda tunaninsa ba'a wajen yake ba. Gaba daya tunaninsa ya ta'allaqa a kanta,yana jin a yadda yanayin wajen ya masa kyau da dadi kamata yayi ace tana tare dashi yanzu haka a gefansa,ya shaqi daddadan qamshin jikinta.....lallausar fatar nan tata me wani irin dumi me bawa zuciya da gangar jiki nutsuwa. "Duk wanda ya taba kiranta da karuwa......duk wanda ya taba yi mata sharri ko qazafin zina ko neman maza......bazan qyale kowa ba farouq". Kallonshi sosai farouq yakeyi yana kallon yadda idanunsa suka jirkice da wani irin giyar soyayya me qarfin gaske. Ya karanci wani muguwar kwankwada fu'ad ya yiwa giyar soyayyar sabreen din,ta kuma bugar dashi fiye da yadda ya kamata. "To amma ai sai ka hada da kanka da kanka a kullewar ko?" Ya fada yana dage masa girarsa duka biyun sama. Kallon days jefeshi dashi ya tabbatar masa b'arna fu'ad zai masa,ya sanshi yasan abinda zai iya aikatawa,don haka yaja kujerarsa baya da sauri yana dariya. Qwafa yaja yana gyada kai,baisan abinda yakeji ba tabbas farouq da bai qara masa ciwo akan ciwo ba. Barinsa yayi yaci dariyarsa me isarsa kafin ya kira sunansa. "Yes sir" Ya amsa masa har yanzun lamarin fu'ad da gaske yana bashi dariya. Yana sassauta masa ne kadai saboda yasan bashi da wani gurin samun sassaucin sai wajensa. Sai daya ware idanunsa a kansa sosai sannan ya tashi ya zauna yana dubansa. "Me yasa soyayya take haka ne?" Yayi tambayar sounding serious......saidai kuma abun ya bawa farouq dariya amma ya danneta. "Me tayi maka kuma?" Ya tambayeshi yana matse dariyarsa da kyau. Kasa magana yayi don baisan ma yadda zai kwatanta masa ba,sai kawai ya dora hannunsa akan qirjinsa da yakeji zuciyarsa na azalzalarsa akanta. Ya dauki wasu sakanni kafin ya iya buda bakinsa a hankali da wani irin calmness. "Bansan adadin Lokacin da na dauka ina sonta ba......amma inaji a jikina ba sai bayan abun nan ya faru ba na fara sonta.....kaman wani dadadden so ne daya saba dashi.....na taso dashi,aka kuma haifeni dashi". Sosai maganganunsa ke ratsa farouq......da gaske ne fu'ad din yana sawun mutanen da suke iya boye so ba ko su daukeshi da sauqi ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 88 88 "Kayi qoqarin koya mata yadda zata soka........ta fahimceka.......tasan ainihin waye kai da kuma rayuwarka,daga nan komai zaizo da sauqi......zan baka kowanne kalan goyon baya da kakeso.....nayi maka alqawari......amma nima kayimin uzuri daya alfarma daya" Ya fada yana kama hannun fu'ad din. "Fadi muji dude" Ya fada yana sake jin qaunar farouq da kimarsa tana ratsashi. "Duk sanda naga taka kalar haukan soyayyar ka yiwa Allah karka hanani inyi dariya......i swear wallahi kai babanmu ne ta nan.....nayi imani da gaske irinku masu shuru shurun nan kunfi kowa zurmawa da iya rikita mata". Danawa bayan hannun farouq dake cikin nasa duka yayi yana zame hannunsa sannna ya miqe. "Ka lallabani farouq......kasan Allah zan daga aurenka?". "Iyeeee.....eh ai kayi haka mana,tunda kai ka samu kanka ka zazzage lalurarka ta shekara da shekaru...." "Idan bata haukatani ba farouq kai zaka haukatani" Kawai yace dashi yana yin gaba abinsa. Da sauri farouq din ya tashi yabi bayansa,don yasan tsaf zai iya tafiya ya barshi a wajen. Tuni suka gaya masa an biya kudin komai da komai tun kafin suzo ma,harda qarin wasu kudin spare da yayi ragowa idan suna buqatar qarin wani abun. ★Karo na kusan barkatai ya qara daga fuskar wayarsa ya kalla yana hadiye wani abu me tauri a maqoshinsa. Kwanaki kusan takwas kenan rabon daya sanyata a Idaninshi,tun ranar da sukeja Vaadhoo Island shi da farouq bata sake bari yaga face dinta ba. Da farko yayi tunanin zai jure,kwana daya biyu uku hudu ana biyar din yaji bazai iya ba,yakai bango kaman numfashinsa na shirin masa qaura. Ba ganin face dinta ba kuma jin muryarta?. Koda ya shiga dakin da nufin gaida anni tanajin alamunsa take shigewa duvet ta kwanta abinta. Ya fuskanci kaman tana garkuwa ne da anni wadda ba lallai ta fahimci abinda yake faruwa. Yana jin nauyin anni yana jin kunyarta,amma ta fara kaishi bangon da yakejin yana dab da ajiye kunyar a gefe. Wayar amna ya soma kira yana sanyata ta bata wayar. A kunnensa yakejin sanda amna take bata wayar amma saita karba ta kife taci gaba da sabgarta. Idan ya kira amna ta wayar anni tana bashi tabbacin wayar na hannunta,sai mintuna suyita tafiya babu ko motsinta bare tarinta. Da yaga haka saiya koma kiran annin yasa a bata,still dai haka take masa,kwanaki uku kenan yau tana masa haka,adadin kwanakin da lissafinsa yake gaya masa jibi ne yarjejeniyarsu da anni na zuwa daukota daga macca. Bazai iya jure wannan ba......da kansa ya sanya order din wayoyi har guda biyu aka kawo mata,Falcon supernova iPhone 6 pink diamond edition irin wayar dake hannunshi kenan. Sai iphone 4s elite gold. Dukkaninsu wayoyi ne masu tsananin tsada da ba kowa yasan da zamansu ba,saboda ba kowa keda qarfin tattalin arziqin mallakarsu ba. An qera jikinsu ne da diamond da kuma gold masu tsananin daraja. Yana jin cewa idan ya bata wayar ya zamana tana da tata mallakin kanta dole idan ya kira ta daga din. Har ya gama shirin kwanciya tun goma na dare amma kewar nan da yakeji ta hanashi kwanciyar,ya tashi ya sanya pyjamas dinsa light blue da suka amsheshi sosai ya sanya flipp flops dinsa ya kwashi wayoyin ya wuce dakin anni. Tana zaune abinta qasan carpet dauke da littafin hadisinta da yafi mata dadi akan komai a yanzun. Tayi kyau kaman wata 'yar baby cikin milk color din Indonesian hijab me haske sosai daya fidda fuskarta. Tunda taji sallamarsa wani abu ya tsarga mata,ya shammaceta sosai,yau ko qamshin turaren nan nasa da takeji bata jishi ba. "Barka da dare anni...." Ya fada cikin girmamawa yana zama saman sofa din dake opposite dinta,kansa tsaye yau duka idanunsa suna kanta. Ji yakeyi kaman yayi shekara takwas ne bai ganta ba bawai kwana takwas ba. A yau din har anni ta ankar da hakan,tadan dauke kai kaman bata gani ba cikin jin nauyi tace. "Barka kade me babban suna.....mun yini lpy?" "Alhamdulillah" Ya amsa mata yana maida dubansa ga amna data tsugunna tana gaidashi. "Lovey dovey.....barka da dare" "Barka kadai hamma". Sak tayi,bata da niyyar magana kowacce iri ta hadasu,amma gaisuwar anni data amna ta daureta,dole ta gyara zamanta daidai sannan tace "Barka da dare,ina yini?" Kowanne gaba ta jikinsa sai data amsa sautinta,bai taba sanin yayi masifar kewar muryarta kawai bama sai yanzu,amma duk da haka ya dake yana hade fuska. "Bazan amsa ba.......sau nawa ina kira a wayar amna nace ta baki?.....sau nawa ina kiran wayar anni a baki saiki ajemin waya.....saboda kin rainani?". Dukka duf dakin yayi,nauyi ya kama anni da kunya......yayin da sabreen din wata masifaffiyar kunya nauyin anni da fargabar kada ya ballo magana gaban annin ya kamashi. Amna kanta sak tayi,saita miqe kawai ta fara lalubar hanyar fita kada ayi fadan soyayya a gabanta,duk abinta itama wani lokaci tana kunyar annin. "Anni" Ya kira annin kai tsaye yana maida dubansa sashenta. "Muhammadu" Ta fada cikin jin nauyi itama. "Ta rainani anni.....a qasana take amma tana iya aje waya idan na kirata". "Baki kyauta ba takwara....bakisan aljannar mace tana qarqashin qafar mijinta ba?.....kada ki sake kinji ko?". Qasa tayi da kanta zuciyarta na karyewa tare da tarin haushinsa. Tun ranar da taga fareeda kwance a jikinsa ta tsani ganinsa ta kuma tsani ganin fareedan itama. Dama can sun shirya abunsu ne shi yasa da suka gama yawace yawacensu ya kori Jordan ya kaisu can saboda suna da agenda din haduwa......sannan daga qarshe saboda zalunci yazo yayi mata mummunan fyade irin wannan......ya karbi abinda sam ba nasa bane. "In sha Allah anni......kayi haquri". Ta fada a sanyaye ba tare data kalleshi ba. Wani abu ya hadiye a wuyansa,shi ba haka yaso abun ya tsaya ba,ba haka yakeso ba.....sam bai gamsu ba. Yana tsaka da wannan tunanin yaga ta ajiye littafin ta miqe tana cewa " Zan dauko ruwa kitchen " Tayi maganar ba tare da yasan dawa take ba.....izinin wa take nema?,saidai kawai ya tsinci anni tana cewa. "To ba laifi" Sai ta taka a sannu ta fice. Yadan bita da kallo kafin ya dauke kanshi,shi ya sani ba wani ruwa da zata sha,kawai ta aikata hakanne don kada ta zauna inda yake. Kwata kwata zaman dakin sai ya yaji ya gundureshi. Ya miqawa amna kwalayen wayar wadda shigowarta kenan yana cewa. "Ki ajiye mata idan ta shigo ta zaba" Sannan ya miqe yana cewa anni. "Jibi zanje na taho da maamah daga saudiyya.....kwana biyu kawai zan dawo in sha Allah" "Ma sha Allah,hakan yana da kyau,Allah yayi albarka,banda banbancin fitowar visa ma ai da tuni.muna nan a tare,Allah ya kaika lafiya" Amsawa yayi da ameen yana fita a dakin gami dayi mata sai da safe. Guri kawai ta samu tayi zamanta cikin kitchen din,zaman nan din ya fiye mata zama a dakin,qarfin halinsa kawai take gani,ga mari ga tsinka jaka?,ko kunyar annin bayaji kansa tsaye yake kai mata qararta?. Sam sam yaji ya gagara wucewa dakinsa kaman yadda yayi niyyar yi,duk da yau din ransa yadan baci da ita. Sauya akalarsa yayi zuwa kitchen din,yanason ya tabbatar tana can din ko kuwa?,me ma takeyi?. Idanunsa ya zube a kanta,tana gaban sink ta kunna famfo kawai ta tara hannuwanta kaman me lissafin adadin digon ruwan daya fado hannunta. A hankali yake takawa don bayason ta jishi,ya samu nasarar isa dab da ita kuwa kafin mayataccen turarensa ya shaida mata isowarsa. Ta motsa da hanzari da nufin waiwayowa,saidai kuma ya rigata da hanzari da kuma zafin nama yayi mata kyakkyawan masauki cikin qirjinsa. Ta baya ya rungumeta tsam,zuqar farko da ya yiwa jikinta daddadan turarenta ya ratsa qofofin hancinsa ya kuma tayar masa da duk wani ajiyayyen tsumi dake jikinsa. Numfashinta ya kusa daukewa saboda yanayin jikinsa da taji ya fara canzawa,maimakon ya barta ta zame yadda take ta qoqarin yi sai ma ya sake manneta da jikinsa yana zura fuskarsa tsakanin wuyanta,ya kuma tura daya hannun nasa ta saman rigarta yana qoqarin kaiwa ga wancan wajen. Hannunsa take qoqarin riqewa....bai hanata ba amma kuma ya soma zare duk wani qarfi da take dashi saboda dumin numfashinsa da yake sakarwa sasannin wuyanta zuwa cikin kunnenta,take kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa harda muryarta. "Ka bari don Allah" Ta fada cikin rawar murya,sai ya dakata cak yana hautsinota ta dawo suna fuskantar juna. Da rinannun idanunsa da suka fara canza kala yace mata "Ke kinsan girman Allahn ne?" Yafada yana dage mata girarsa duka biyun. Samun kanta tayi da kasa kallonshi,saita kauda fuskarta gefe. Hannu yasa ya dawo da fuskartata daidai saitin tasa yana dubanta. "Uhnnn.....nace kinsan girmansa?.....kinsan aure dukansa sunansa aure a wajen Allah?,kina matar aure amma baki iya kula da mijinki ba?.....baki iya komai bafa.....idan nace komai ina nufin komai irin na mata....matan ma matan aure........kinaso na mutu ne sabreen?" Mamakinsa ya kamata,ya gama rungume rungumensa sannan yanzu ya mata wata magana ta daban?. "Bakya kishina ne?" "Sonka nake da zanyi kishinka?" Ta fada a tsiwace tana murguda bakinta. Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu kusan lokaci guda,siririn murmushi ya kubce masa yana kallon baby face dinta da danjaririn bakinta data murguda masa. Ba abu me dadi ta gaya masa ba,don maganar ta sokeshi a tsakiyar zuicyarsa,saidai kuma ta masa wani mugun kyau,kuma yaji ta bakinta ko ba yawa a wannan fannin. Sake jawota yayi ya matseta da kyau kaman zai rabata gida biyu,ya sanya yatsarsa guda daya ya fara zagaye labbanta sai tayi sauri zata turasu ciki,ya shammaceta ya hada mata da yatsan nasa,dole ta saki labban nata,abinda ya bashi daman riqo fuskarta da kyau ya kuma hade labban nasu waje daya. Wani irin sarrafasu yakeyi a tausashe da nuna zallar qauna,abinda bata zata ba daga gareshi. Ta dauka anytime kiss abune me zafi ga labba,cikin minti biyu taji kowacce gaba a jikinta tana saki,kafin kwanyarta ta ankarar da ita suna kitchen sakamakon qarar qofar kitchen din. Tureshi tayi da sauri,ta saka bayan hannunta tana goge labban nata. Da fushi a muryarta tace. "Banason wannan abun.....wannan ai qazanta ce" Tayi maganar ne da harara,harara data fidda farare sol din idanunta. Kamar dafi haka yaji ta zuba masa jikinsa dukka ya amsa,ya shammaceta ya jawota ya sake matseta yana same hade bakunansu,ya tattara miyau din bakinsa duka ya dure mata. Bai barta ba sai daya tabbatar ta hadiye sannan ya sake boyeta a qirjinsa sanda ta saki siririn kuka. "Am so sorry.....inason mu sake zama abu daya ne bayan wanda muka sake zama din.....amma tunda na miki ba daidai ba.....biyani yawu na" Ya fada yana qoqarin sake kai bakinsa cikin nata. Ta gama fuskantar wayo ne kawai yake son ya mata,don haka ta fara qoqarin hanashi amma bai bata dama ba,haka ya dinga zuqe duk wani yawu dake bakinta sai da numfashinsa ya fara fita daban daban daga qirjinsa sannan ya sake ta yana maida numfashi. "Duk abinda na miki idan bakiso zaki fara biyana daga yau......ki karbi wayarki a hannun amna" Yana kaiwa nan ya juya yana barin kitchen din saboda jin yana neman loosing control dinsa. Ya riga yayi alqawarima ransa indai ba takura yayi maqurar iyaka da zai iya shiga halaka ba.....bazai sake karbar komai ta qarfi ba....zaiyi iya yinsa ya amintar da ita. Idanunshi a rufe suke,sam bai kula da farouq dake zaune a parlor din ba sai da yaji muryarsa yana cewa "Ranka ya dade sir" Yana dunqule hannunsa irin na girmamawa. Kallo daya ya masa ya fahimci zai wahala bai shiga kitchen da zummar dauko wani abun ba idanunsa sunyi masa gamo,don haka baima tsaya biye ta tasa ba ya wuce daki abinsa yana jin dariyar farouq din. Saidai qasan ransa yasha alwashin tasu ce shi da farouq din,yaga alaman bazai taba barinsa ya sake ba.....baya jin zasu qare zamansu a Maldives a wannan gidan....musamman da maamah ke dab da isowa,yana jin gidan tabbas ya musu kadan ,don haka ba wanda ya sani bayan ya sakarwa kanshi ruwa ya fito,ya yiwa Jordan maganar duba musu wani apartment din a siya zuwa nan da jibi yalwatacce sosai da yafi wannan. Sulalewa tayi a nan tana dafe da kanta,da qyar ta iya saita kanta ta miqe tana gyara yamutsatsen hijabinta da tuni ya saukeshi daga kanta. Can qasan ranta tana mamaki,wanne irin tsafta ne dashi haka?,duk sanda yayi kusa da ita irin haka qamshin mint leaves ne ke fita a bakinsa,wanda da alama ya kama bakin nasa sosai,wanne irin freshener na baka yake amfani dashi haka?. Tsaki taja qasan ranta tana ture wannan tunanin daga ranta,ta matsa gaban sink ta ringa watsawa fuskarta ruwa don kada ta koma anni ko amna wani ya gane wani abu,sai data tabbatar taji daidai sannan ta dauki gorar ruwa daya ta fita a kitchen din. Farouq din yasan tabbas zata fito,bayaso kuma taji kunya ko nauyinsa,don haka sai ya wuce dakinsu bayan shigewar fu'ad,wannan ya bata daman shigewa dakinsu salin alin. Qin yarda tayi ta hada ido da kowa kota zauna,sai tayi shigewarta duvet kawai tana qundundunewa waje daya. Amna tana toilet,batasan kuma ta shigowa ba sai data fito. Cikin hanzari ta qaraso dakin tana cewa. "Albishirinki adda?" Daga can qasan maqoshinta ta amsa da "Goro". Tana bin amna da kallo wadda ta dosota da kwalayen waya guda biyu ta zauna gefanta. Duka biyun ta zaresu daga kwalinsu,bakinta ya kasa rufuwa. "Ya Allah kaban miji irin hammana.....you're luckiest woman adda....." Idanu sabreen tadan fidda "Bakwa kunyar anni amna?,yanzun da tana dakin haka zaki ce?" Dariya ta qyalqyale dashi. "Ki zabi daya.....idan nice ma duka zance inaso......falcon supernova.....the most expensive phone in the world.....it's worth more than 77mil in naira......irinta hamma na ke using,ita kuma wannan itace ta biyun ta a tsada" Amna ta fada tana juya duka wayoyin tana duban sabreen. Adadin kudaden kawai sai da suka sanya kanta yayi tsawa,million saba'in da bakwai?,ina zata kai irin wannan wayar?,wacece ita?,waye ubanta a Nigeria?,idam shi ya riqe matsayinsa yakai ne.....arziqinsa yakai....amma kuma ita fa?,ita da take dorin dosano?,kwanaki nawa ya rage mata ra barshi ma kwata kwata?. Numfashi taja ta lumshe idanunta tana kullesu,ba zata iya gayawa amna kai tsaye bata so ba.....ba zata kuma karba ba,don haka tace. "Ki ajiyesu,zan duba gobe" "Done.....amma please ki dauki irinta hammana please adda" "Naji" Tace da amna don kawai ta bata wuri ta shaqata. _nikuwa nace ya kamata sabreen ki karbi wayar nan don ki gigita surukarki hajiya maamah da ita,kin bata tabbacin mallakar fu'ad da taketa fafutuka taki ce kenan_😂😂😂 Tana sane ta narke tun daga daren ranar har wani daren,tayi qaryar zazzabi don kada anni tace taje suyi sallama da fu'ad da zai tashi zuwa macca kai tsaye gobe da safe. Ta samu nasara kuwa.....don har ya shigo ya musu sallama tana kwance tana baccin qarya.....duk da cikin jikinta tana jin idanunsa a kanta suna yawo,ya juya ya fice su anni suna taka masa. _Turqashi......maamah bisa hanya_ _komai fa yana shirin faruwa me karatu_ _idan nace komai.ina nufin komai ma😂_ _pages din gobe masu zafi ne,kada ka yarda su wuceka_ _Ya zata kaya tsakanin maamah da sabreen ga anni a tsakiyarsu?_ _yaya zata kaya sanda maamah ta fahimci zazzafar soyayyar sabreen a idanun susutaccen d'anta?_ _shin zata iya dauka?,ko zata cika qudurinta na rabasu?_ _Shikenan fareeda ta haqura?,ko zata sake wani motsin?_ _waye da waye ne suka shiga hannu?_ _ita kanta fareedan ta sha ko kuwa?_ _akwai ragowar zafafan al'amura fa masu karatu,muje zuwa ga gangarar labarin_🧏🏽 *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 89 89 Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana dan dafe goshinsa,duk wani energy nasa yaji yana tafiya,ta yaya zai iya tafiya wani qasar ba tare da sunyi sallama da ita ba?. Ya sani ya kuma fahimci tana sane duk tayi hakan,wayarma daya batan baiga alamun ko guda daya a hannunta ba. Iska ya sake furzarwa yana jin tsoron kada dai furucinta na rannan ya zama gaske da tace bata sonshi. Sai ya zura hannunsa a aljihunsa ya fito da wayarsa ya fara kiran number amna. Ita da anni ce kawai a dakin,annin ita ta karbi wayar saita miqa mata tana cewa. "Hammanku ne......basu tafi ba kenan" Ba zata iya musu da annin ba bata kuma fita ba bayan ta bata wayar bare ta aje wayar yadda ta saba masa. Ta latsa ta sanyata a kunnenta,ta motsa labbanta a hankali tana amsa yin sallama. Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar sautin sallamartata. Yayi jarumtar daidaita yanayinsa don bayaso ta fahimci komai,don yana son komai zai gaya mata ta daukeshi da muhimmanci. "Ina kika shiga?" Ya mata tambayar a gajarce data rasa amsar da zata bashi. Shuru tayi tana kame kamen abinda zata gaya masa,bata samu ba har ya sake cewa. "Kinsan tafiya zanyi yau really?" Can qasan zuciyarta tayi qaramin tsuka tana cewa "To mene ruwana da tafiyarka?,ka wuce mana ta can ma karka dawo Maldives,amma a fili sai ta zabi jan bakinta tayi shuru. "Alright......yayi kyau....ina wayar dana bawa amna ta baki?,baki dinne bata yi ba?". Ya sake tambaya da wani irin shan qamshi da bata taba ji ya mata ba,hakan sai ya mata kwarjini gami da taba zuciyarta. "Ta bani" Ta amsa masa a hankali kaman wadda batason tayi magana. Amsan ta bashi haushi kadan,don shi daya yasan yadda ya matsu da jin muryarta amma taja wayar ta ajiye. "Bakiga daman amfani dashi ba kenan?.....well....bazan miki komai ba a yanzun.....amma kika sake har na dawo na samu wayar a yadda na baki ita.....sai nayi punishing naki ta hanyar da bame iya karbanki......and idan ma kin bude kin fara using da ita....if kika ce zakimin abinda kikemin a wayar anni da amna bawai kin tsira bane.....take care of your self......byee" Ya fada yana sauke wayar. Sai a sannan yaji zuciyarsa ta koma daidai,duk da ba irin wannan sallamar yaso suyi ba,amma at least ya samu nutsuwa kadan. Bayaso ya fiya zafafa mata da yawa....don baida tabbaci ko yaqinin zuciyarta ta karbeshi,saidai ko meye yana da yaqinin bazai qyelata haka ba,sai yayi mata dashe da kuma ginin da bazai kankaru ba. Wayar tabi da kallo kafin ta ajiyeta a gefanta. Sau tari idan yana wani abun sai zuciyarta ta dinga gaya mata plan ne kawai da siyasa irin ta 'yan kasuwa,kamar kawai yanaso yaci gaba da mata wayo yana amfana da jikinta ne. Har yanzu ta gaza gasgata kanta wai mutum kamar muhammad fu'ad da mutunci ko arziqi ba shine silar gamuwarsu ba ace dare daya don kawai ya amshi budurcinta ya koma haka ba. Kulawa qauna soyayya da wani irin mayataccen yanayi da bata taba ji ko gani ba. A duk mazan da sukayi alaqa dasu a baya bata taba ganin wani abu na musamman kebantacce tattare dasu irin wannan ba. Da gaske wannan shine son?,da gaske wannan din ake kira da soyayya ko kuwa yaudara ce zallarta?. _to masu karatu ku bata amsa_ ★ *_Makka/Jeddah_* Tafiyar awa biyar zuwa shida ta kaisu garin jedda,a nan ya tsaya yayi wanka ya saka hirami ya dauki niyyar umararsa. Daga nan kuma lafiyayyen train ya daukesu kai tsaye zuwa makka.....motar da aka tanadar masa ta qarasa dashi masauki cikin hotels mafi tsada dake dab da harami. Fairmont makkah clock Royal tower nan ya zaba,ko maamah dinma yasa an maidata can,hotel ne dake da kusanci sosai da haram,kai tsaye daga dakinka kana iya hango ka'aba. Baida gurin sauka duk zuwan da zaiyi sai nan din,saboda samun kusanci da Allah da samun daman yin addu'o'insa sosai koda cikin dare ya farka. Sau tari yakan jima gaban window din dakinsa yana qarewa dakin Allah kallo,cike da shauqi da tsoron azabarsa da kuma fatan samun rahamarsa,yana jin inama yayi zamansa a nan ya qare rayuwarsa. Nutsuwarsa da samun salamar ruhinsa daban yake jinsu a ransa duk lokacin daya shigo wajen,yana jin kansa sosai kusa da Allah,don haka koda ya iso wucewa yayi kai tsaye yayi dawafi da sa'ayi yayi sallarsa raka'a biyu ya sauke umararsa. Bai nema ganin maamah ba sai daya sauke faralin umran da bayajin zata isheshi. Zuwa yanzu baisan sau adadin nawa yayita ba.....bayajin kuma zai daina yin nata muddin da numfashi a jikinsa da kuma damar zuwan. Dakinsa ya koma royal suit ya sallami abdulbasit da abdul gaffar da abdus sabur wanda su ya sanya suzo su zauna tare dashi. Hiraminsa ya cire ya nema wasu kayan ya sanya yana duba lokaci. Akwai gajiya sosai tattare dashi,yana buqatar ya hutawa kwanyarsa sosai don ya samu space din yadda zai iya tunkarar ko meye maamah zata zo masa dashi. Labulen dakinsa ya daga,idanunsa suka sauka akan dakin Allah,wajen tarwai yake da cikakken haske kamar kullum,da tarin bayin Allah masu neman duniya dama lahirar gaba daya. Bayason wani babban abu ya faru tsakaninsa da maamah a irin wannan wajen,dole yana buqatar neman taimakon Allah. Nannuyar ajiyar zuciya ya sauke sanda fuskarta ta dawo masa tarwai cikin idanunsa. Idanunsa akan ka'aba din,ya sanya hannunsa saman qirjinsa ya dafe yana jin yadda qirjin nasa ya cika da soyayyarta,a hankali ya furta. "Ya raheem......kada ka bawa mahaifiyata galaba a kaina muddin da sabonka da kuma son zuciya tazo". Sai ya dakata yana jan numfashinsa sosai. "Ya ubangiji.....kaine mahaliccin zukata.... Kaine ke iya jujjuyasu a duk sanda kakeso,ya rabb,kafin kowa sanin menene abinda ke zuciyata na ainihi a kanta,ban aikata mata komai ba don na zalunceta ko na cuceta ba,ban aikata mata komai saboda qiyayya ko abisa sanina ba....ya rahman....ka sanya mata matsananciyar soyayyata a zuciyarta,ka sanya ta soni irin son da nagartacciyar uwa kewa d'anta......irin son da bashi da misali.....irin soyayyar da na jima ina fata da burin samu daga wajen macen aurena.....ya ubangiji,na gode maka abisa kowacce ni'ima da kayi a gareni.....na yadda cewa mahaifiyata itace jarrabawar rayuwata......na rasa soyayyarta soyayya ta ainihin da aka santa daga zuciyar uwa zuwa 'ya'yanta.....ya Allah yadda kayimin madadi da anni.....na roqeka kayimin madadi da ameenatu sabreen.....ka maidata sanyin idaniyata......Allah ka azurtani da salihan yara ta tsatsonta.....ka sanya albarka cikin kowacce tarayya da zanyi da ita....Allah ka wankemin idanuna da samun qarin 'yan uwa nagartattu bayan su musaddiq,wato yaran da ameenatu zata haifamin" Ya qarasa addu'ar labbansa suna sanyi,zuciyarsa tana jin wani irin sassauci da sauqi,a take kuma sai kewarta ta cikashi. Baisan me ya sanya dukkanin burinsa a yanzu ya fara karkatawa kan samun 'ya'ya ba......abune daya jima a ranshi,amma halin maamah da yadda ta watsar da rayuwarsu ya kashe wannan burin. Yana ganin duk macen da zai dauko ma haka zata kasance akan 'ya'yansa kaman yadda maamah tayi musu ta kuma yiwa abbansu. Sakin labulen yayi a hankali,yana ji a jikinsa tamkar dukkanin addu'o'insa sun amsu,sai ya koma ya zauna bakin gadonsa yana daukan wayarsa. Maamah din yaso kira don ya shaida mata ya iso,amma cikin rashin sa'a sai ya kasa samunta. Hakan ya masa dadi,don ko ba komai zai samu ya matse gajiyar daya debo,don haka ya aje mata tex kawai,sai ya tsinci kansa da neman layin wayar sabreen din. Bai taba zaton zai samu wayar a bude ba,bai dauka zataji warning dinsa ba,amma ga mamakinsa dab da zata tsinke aka daga. Lumshe idanunsa yayi yana jin qarin wani sassaucin da rangwamen yana sauka a zuciyarsa,ya koma da baya ya kwanta akan gadon bayansa bayan ya sanya pillow qasan kansa. Shuru kawai tayi tana sauraren iskar dake fita ta wayar. "Baki iya sallama ba?.....me yasa kullum kike maida kanki yarinya sosai?" Ya tambayeta a tausashe yana jin ba dadi baqin halayenta. Ta maida kanta wata sokuwa a gabansa,ba dogon magana sam.....musu ko tsiwarma sai taga dama takeyi masa su. "Assalamu alaikum" Ta samu kanta da masa sallamar. Qasan ranta a tsorace take da maganansa kadan kadan. Tanaso su rabu ba tare daya sake taba jikinta ko ya kasance da ita ba......amma ta duba ta dubo ba wani hanya daya rage illa ta bishi ta yadda ya bullo mata,ba tare daya ankara ba zai wayi gari babu ita. Wani sauti na daban yakeji yana shiga kunnensa tamkar yau ya fara jin amsuwar sallama. "Amincin Allah kema ya tabbata a gareki DUNIYATA.......gani kusa da dakin Allah.....me kike buqatar na roqa miki?". Ya fada da wani kwantacce kuma sassanyan sauti da shauqi da kewa suka cikashi. Har cikin jikinta taji maganarsa ta mata dadi,tana da tarin buqatun da zata roqa a wajen Allah idan har qaddarar zuwa wajen ta tabbata a kanta. A yanzu dukka ta qosa subar Maldives,tana jin nauyin tambayar amna wanne guri zasu je next.....amma a nata zabin a ture dukka kowacce qasa a barta a tsakanin saudiyya zuwa madeena. Tana tsaka da wannan lissafinne taji muryarsa yana cewa. "Na roqo ubangiji yasa ki soni....irin matsanancin son da ba zaki iya rayuwa ba tare dani ba.......na roqi Allah ya sanya ki zama madawwamiyar ni'ima a gareni......na roqeshi kada ya baki ikon barina koda kina da nufin aikata hakan.......ya mallakamin rayuwarki gaba daya daga farkonta har qarshenta.......sannan na roqeshi ya bani 'ya'ya masu yawa ta jikinki.....duk shekara so samu ki haifemin tagwaye ko uku uku......" "Please mana" Batasan sanda ta tsaidashi da fadin wadannan kalmomin ba. Tunda ya fara jero mata abinda ya roqa din zuciyarta ke wani irin bugu,ta sani gurin da yake wajene da babu wasa a cikinsa.....wajene da komai ka roqa amsashshe ne a wajen Allah......tana tsoron kada addu'arsa ta cita.....kada ta kamata,idan hakan ya kasance ina zata saka burin rayuwa tare da 'yan uwanta bisa kyakkyawar rayuwa?. Dan qaramin murmushi ya subuce masa yana jiyo alamun tsoro cikin sautinta. "Tsoron me kike haka?,akwai cutarwa cikin addu'ata?" Ya tambayeta yana ji a ransa inama hirar zatayi tsaho tsakaninsu. Kai ta girgiza kaman yana gabanta,da gaske tsoro yana sake cikata. "Wannan son kai ne.....zallar son kaine a cikin addu'arka,ka roqi Allah wani abun daban ba wannan ba" Tayi.maganar da dan hasala a muryarta tana ganin kaman da gayya yayi hakan. Boyayyen murmushi da bai bari taji sautinsa ba ya subuce masa. "Me ruwanki da abinda zan roqa Allah yayimin?" "Ina da ruwa dashi.....saboda a kaina ka roqi ubangiji...." "Ke kuma kina tsoron hakan ya tabbata?.....to idan akan wata daban na roqa fa?" Shuru ya ratsa kunnensu na wasu sakanni kafin yaji tace "Wannan kuma ruwanka bana sabreen ba" Ta samu kanta da fada,sannan ta gimtse wayar tana kasheta gaba daya. Yaji saukar layin nata,sai ya zame wayar daga kunnensa murmushi yaqi barin fuskarsa. Me yasa tun asali baiyi dabarar bata waya ba kaman haka ya kuma kafa mata sharuda ba,haka hira da masoyi take da dadi dama?. To amma wani hanzari ba gudu ba.....me yasa tayi shuru sanda yayi mata tambaya ta qarshe kafin tace ruwansa?. Maido fuskar wayar yayi saitinsa,ya rubuta mata gajeran saqo ya tura mata,ya koma ya kwanta rigingine wayar ba rungume a qirjinsa. Wani murmushi ke fita saman fuskarsa kadan kadan,zuciyarsa cike da fatan saisaita kansa akan yarinyar.....don da haka ne kawai zai saitata a hanyar da yakeso ta tabbata a kai. Shidai baisan ya akayi bacci yayi awon gaba dashi ba,saidai ya cika mafarkansa duka,cikin kowanne gani da zai mata cikin qauna soyayya da kuma kulawa. Harda wanda ya gansu kewaye da yara qananu masu kama dashi sosai. Wannan mafarkin shi ya haska asubarsa,ya shiga bandaki ya daura alwala cike da wani kwantaccen farinciki qasan ransa. Cikin jallabiyya 'yar Indonesia fara qal ya shirya ta maza,ya shafe jikinsa da lallausan turarensa ya saka hular tashi ka fiya naci saman kansa fara qal itama,ya dauki tasbaharsa counter data kasance farar itama. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 90 90 Wayarsa ya zura a aljihunsa bayan ya duba number dakin maamah. Kai tsaye can ya nufa yana tafiya da cikakkiyar nutsuwa a tare dashi,bakinsa dauke da ambaton Allah. Yanaso ya samu sahun gaba gaba,wannan ya sanya yake tashi da wuri koda yaushe,ya kuma isa masallacin da wuri. Kallon kallo suka yiwa juna shi da maamah din,alamu sun nuna tashinta kenan a bacci. Bata ce masa komai ba ta saki qofar ta juya zuwa ciki ya bita a baya. Guri ya samu ya zauna yana duban dakin dake cike da kaya wanda ya tabbatar tsaraba ce. Yaushe ma taxo?,yaushe ta samu daman yin ibada sosai har ta fada yin wata tsaraba?. Duk abinda zata siya din ba abinda bata dashi a gida,amma fadan hakan kaman laifi ne a wajensa. Bandaki ta shiga ta daura alwala sannan ta fito,tana sauya hijabin jikinta ya soma gaidata kaman yadda ya saba cikin bata haqqinta na uwa daidai misali na girmamawa. "Ka shigo tun jiya.....sai yanzu aka baka daman zuwa inda nake?". Idonsa ya kawar,shi yasan ko.meye zai faru tsakaninsa da maamah din bame sauqi bane,saidai ko meye ya gayawa Allah yana kuma da yaqinin komai zaizo masa cikin sauqi. "Nayi qoqarin kiranki ban sameki ba,na aje miki saqo na dauka zaki amsa,banyi zaton a irin lokacin zan sameki a daki ba shi yasa na koma na huta,sai bacci ya daukeni" Ya fada a taqaice. Qwafa kawai taja tana qare masa kallo a fakaice. Ita kadai tasan me takeji a ranta,ita kadai kuma tasan me ta shirya zata aiwatar.....tana ji a ranta idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba lallai ta cika lusara asararra,wala'alla fareeda din itace wannan hasken nasarar guda daya da boka ya mata albishir dashi. Har ya gama shiryawa suka fice tare bata sake cewa komai ba,dama ba wani sabo ko shaquwa tsakaninsu ballanta hira me kama da irin wannan ta biyo baya. Zata iya cewa bata taba samun sallar asuba irin haka ba kaman yau,basu bar masallacin ba sai da gari yayi haske,suka hadu gaban hotel din nasu ya dauketa yin breakfast duk da akwai bada breakfast a tsarin hotel din nasu. Ba wani abu ya karba ba illa coffee,itakam abubuwa da yawa yasa aka ajiye mata,yana sipping coffee din nasa amma hankalinta yana kanshi. Inama ace wannan kulawar ita daya a duniya yake bawa irinta?,inama yadda suka zauna a haka haka yake zama da ita koda yaushe yana kula da duk wani motsinta......yana jira yaji umarninta ko haninta?. "Muhammadu" Ta krashi bayan ta gama tauna yadda zata fuskanceshi. Burinta a yanzu bai Gaza ganin fitar sabreen cak daga rayuwarsa ba. Da idanu kawai ya amsa mata ta hanyar kallonta. "Wacce irin mace kake aura mara hankali da tunani kuma mara kirki Muhammadu?". Gaba daya sai maganar tazo masa a bazata,ya kasa kuma fahimtar abinda maamah keson cewa. "Banda yarinyar nan bata da kirki bata da mutunci batasan girman uwar mijinta ba.....bata taba kirana ta gaidani ba?,bata taba tambayar lafiyata ba.....bata ma taba nemana ba wai sunan tana auren d'ana?,ni kuwa wallahi ba'a haifi diyar da tana auren dana kuma zata min riqon sakainar kashi ba" Ta fada cikin fada sosai tana dan dukan table din da suke kai kadan. Zame hannunsa yayi daga jikin mug din yana zubawa maamah din idanu. Zaren tunanukansa suna qulluwa waje guda cike da wani irin mamaki. A nan dimma akwai wani qullin?, ya tambayi kansa da kansa. A abinda yake kallo akwai cikakkiyar fahimtar juna tsakanin maamah da sabreen wanda shi ya zama silar daukota zuwa rayuwarsa,a yanzun me ya bata wannan alaqar da jikinsa ya jima yana gaya masa gurbatacciya ce?,to kodai zai samu wani hint din a nan ne?. Tabbas inda a watannin baya da suka shude maamah ta fadi haka akan sabreen bazai dameshi ba.....in fact ma zai dauka ta fara gane wacece menene kuma halinta,amma kuma a yanzun sai yaji kalaman kaman sunyi tsauri da yawa. Ya shirya tare mata fada ko batanci kowanne iri ne kuma koda waye,don haka ya gyara zamansa yana fadin. "Maamah.....inajin kinfi kowa sanin wacce iri ce sabreen.....tunda daga hannunki ta fito,kuma na tabbatar ba zakimin zaben tumun dare ba.....amma maganan waya bata da waya,duka wayoyinta suma hannuna". Har tsakiyar kanta taji wani abu ya tsarga mata,wato ita yarinyar zata gwadawa bariki ta bashi wayoyinta?,a tunaninta yin hakan shine zai sanya ta tsallake tarkunanta?. Ta jima tana zaton salwantar da wayoyin tayi,wannan yayi saving nata bata taba gwada Kiran layukan ba,inda ta kira din kenan yana iya zargar komai ko ya binciko komai?. "Sannan kiyi haquri zan mata fada zata gyara" Ya sake fada yana kallon reaction na maamah din. Yadda ta daga kai da sauri tana dubansa ya sake bashi wani qarin percentage na zarginsa a kanta. Yaushe alaqa tayi nisa tsakaninsu da yake kareta?,yaushe ma duka duka ta kirashi ta masa jan kunnen ya kula da ita?,bariki ce ko nata kalar tsubbun ta shayar dashi kaman yadda jikinta keta bata zata aikata haka?. "Ai karma ta gyara....ni d'ana bazai auri mace daya ba ballantana ta samu daman juyashi da zaton nata ne ita kadai,don haka ka shirya........na zabar maka fareeda mazaunin matarka ta biyu......muna komawa da sati biyu kacal zaayi komai a gama.....don banajin tafiyarka da sabreen zatayi nisan zango,akwai canje canjen dabi'u da halaye da nake ji a tattare da ita" Sosai yake kallonta,ba kuma don komai ba sai don maganganunta masu kama da almara. Auren fareeda wannan yasan wani abune da bashi da maraba da tatsuniyar gizo da qoqi,uwa uba ma fareedan dukkaninta ba damuwarsa bace,don tana under control nashi,kowanne motsi nata yana sane dashi.....abinda kawai yaja hankalinsa shine zancan sabreen. Wanne sauyin halaye take ji game da ita?,meye dalilinta dukka na damuwa da al'amuranta?. Wanne laifi mutumin da baka jinsa ko ganinka yayi maka da zata dinga zarginsa da aza masa laifi kacokam haka?. "Kar kayi kuskuren cewa zakamin gardama akan auren fareeda,nasani sarai shurunka yana nufin abubuwa da dama.....muna dab da muhallin amsa addu'a,zanje gaba ga Allah na roqeshi ya fiddamin haqqin haihuwarka da nayi" Idanunsa ya lumshe maganganunta suna sukarshi. Baisan me yasa ako da yaushe barazanarta iri guda bace a kansu,yadda ta damu da neman haqqin Allah a kansu bata damu da nema musu albarka haka ba?. "Relax.....cool down.....badai fareeda bane matsalar?" Kai ta jijjiga "Itace" "Done" Ya fada da wata ma'anar ta daban. Shi kadai yasan me ya sake shiryawa me kuma zaiyi. Binta da kallo yake kawai sanda taci gaba da cin abincinta,yana hangen tarin sassauci data samu can boye cikin fuskarta da karbar zancan fareeda da yayi. Wani irin quna zuciyarsa keyi musamnan idan ya tuna duk wannan abun da takeyi fa siyanta fareeda kenan tayi. TO TA YAYA TA HADU DA SABREEN?,MENENE SILAR HADASU AURE DA ITA?,MEYE MANUFAR?. Wasu tambayoyi da suke masa susa a qirji,ya tabbatar tunda take muradin hadashi da fareeda bisa wats manufar.....tabbas haduwarsa da sabreen ma akwai manufa,saidai ita sabreen yasan bata da kudin da zata siya maamah.....to meye SILA?. Ba wadda ta fado a ransa a sannan sai hajja,a take kaman an cillota cikin tunaninsa,saboda muhimmancin abun a take ya ciro wayarsa ya tafa qaramin massage ya tura yana cewa. _ina buqatar kowanne motsi na rayuwarta ya zama abun bi kafin na qaraso,bata buqatar kamu,amma ina buqatar ayi mata daurin talala_ sai daya tabbatar da shigar saqon sannan ya maida wayar aljihunsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 91 91 Sosai maamah tayi amfani da wannan damar ta dinga karbar kudade daga hannunsa tana tsaraba. Baice komai ba don ba wannan muhallin bane,bai kuma hanata siyan abinda duka take so ba. ★ *_makka to Maldives_* Kwanaki shida sukayi a maimakon kwana biyu ko ukun da ya tsara zasuyi. Kusan ita ta dinga jan kwanakin duka a nufinta na tafi da tsarinta yadda takeso. Abu daya ne kawai yake dan bata mamaki,yadda take kasa samun wayar fareeda kwata kwata,ta gwada dukka layukanta amma ta gaza samunta,mamakinta yana sake daduwa idan ta irga kwanakin taga ko sau daya bataga gilmawar kiran fareedan ba. Sun sauka Maldives dab da sanda rana ke shirin faduwa,wannan ya sake haska tsibirin ma'abocin ruwa da wani irin yanayi me daukan hankali. Baki kawai maamah ke tabewa,a zahirin gaskiya ba zata ce island din baiyi mata ba,saboda guri ne da yafi kama da aljannar duniya,amma baqinciki da bacin rai suna cikata idan ta tuna cewa ahalin alhaji hamza suka zabi wajen. Ranta ya sake baci sosai cikin wani irin baqinciki da fushi sanda taji tsadar da rayuwa cikin tsibirin yake dashi,da kuma yawan adadin kudaden da ake kashewa kowanne kwana daya cikin resorts da sauran guraren dake kewaye da wajen. "Nikam banga abun burgewa a nan waje ba.....guri duk ruwa,koda yake ba lafinka bane.....kai ka zama dan amshin shata ne kawai sai abinda aka tsara maka,kuma tsabar zallar mugunta ne saboda basusan zafin dukiyar ba,ba tasu bace......dolla million nawa ka kashe musu?" Ta maida tambayarta ga fu'ad dake zaune a gefanta cikin motar da Jordan yazo daukarsu. Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana rufe idonsa gami da budesu,tunda yake bai taba jin kwanaki masu wahalar wadannan ba,wadansu irin kwanaki ne da sam babu armashi a cikinsu. Ya sanya ran samun nutsuwa daga wajen sabreen tun ranar farko data daga wayarsa,saidai kuma bai sake samunta a waya ba har yau da suke dawowa qasar. "Farouq ne ya dauki nauyin komai" Ya bata amsar da azahiri haka take,gida ne kawai zai iya cewa nashi sai jet din da suka taho a ciki. Idanu ta dauke tana tabe bakinta. "Haka dama zaka ce,saboda kana qoqarin basu kariya,ina jiye maka ranar nadamar damqa ragamar rayuwarka a hannun mutanen da basusan ciwon haihuwarka ba.....gefe daya ga matar da nake kyautata zaton zuwa yanzu sun hada baki da ita don su sake cimma manufofinsu" Gaba daya maganganunta baya qaunar jinsu,baya iya daukan kowanne mummunan kalami a kan ahalin alhaji hamza kibiya din. Sun masa komai a rayuwa,idan yace komai yana nufin komai din,don wataqila idan bacin su da yanzun baisan rayuwarsa a wanne matsayi take ciki ba. Duk maganganunta yayi shuru yana jinsu,qananun mitoci ne da basu da tushe ballantana makama. Banda zata fassara abun da wani yanayi na daban tabbas da gida daban zai kamata tayi zamanta ita kadai,saidai hakan yasan ba mafita bace,ba abinda zai sake jawowa sai wani damuwan na daban. Tun anesa ya hangi musaddiq da saddiq zaune daga gaban gidan. Sanye suke da kaya iri daya black jeans da white din t.shirt. Tsaf zakayi tunanin twins ne saboda yadda komai nasu ya kusan zama iri daya. Sosai maamah ta qanqance idanu tana dubansu,wani irin abu yana tsarga mata "Turqashi" Ta furta qasa qasa. Da alama ameenatu tana ci gaba da mamayar komai daya kasance mallakinta. A sanda hankalinta yayi nisa,ta dogara kuma da sabreen hakan sai ya zamana kaman ta bawa ameenatu wata qofa ko dama naci gaba da baza mallakarta tsakanin yaranta. Ba zata iya tuna watanta nawa bataga musaddiq ba,jininta.....tsatsonta,ya gaya mata fu'ad dinne ya aikeshi wani aiki dubai da Qatar,amma yanzun gashi tare da ameenatu,gashi manne da ahalin alhaji hamza kibiya. Tsaiwar motan yaja hankalinsu su duka,motar ba baquwarsu bace don haka dukkaninsu suka miqe zuwa gaban motar. "Barka da zuwa maamah" Musaddiq ya fada yana niyyar karbar jakar hannunta. Kasa jurewa tayi ta jefeshi da harara duk data sakar masa jakar. "Uwarka ta taso daga wani gurin amma ka gaza zuwa airport tarbarta kana nan manne da uwar wasu?". Maganar ta masa ba dadi har hakan ya bayyana saman fuskarsa. Yadan basar yana amsar jakar sannan yace. "Hamma ne.....bai bada assurance na yau din zaku taso ba". " Barka da zuwa maamah ina yini?" Saddiq ya fada yana dan matsowa kusa da musaddiq. Waiwayowa tayi,ta aje masa wani kallo tun daga sama zuwa qasa kafin ta amsa masa sheqeqe tana bin bayan fuad zuwa cikin gidan. Koda riga ta gani a jikinsu baqincinta takeyi,gani takeyi kudin fuad ne ya siya musu wannan riga takalmi da kuma daular da suke ciki ma gaba daya. Tana ganin sunyi amfani da nasibin danta ne kawai suna morarsa bayan sun rabata dashi. Tunda ta idar da sallar la'asar take manne da earpiece a kunnenta tana sauraron karatun littafin umdatul ahkam. Sanye take da Indonesian set skirt ne da hijab dinsu madaidaici sai rigar da iyakarta qugunta. Dark green ne da suka haska fatarta sosai,ta tattare gashinta ta daureshi tsakiyar kanta bayan amna ta gama jagwalgwala matashi da sunan zata mata kitso. Ta kasa kitson saboda santsinsa,don haka ta bisu da hair clips ta tattare mata shi,ita kuma ta daureshi da ribbons don tace ba zata saka mata hair ppin ba. Kayane masu taushi da sakewa a jiki,duka anni ce ta saya mata su kusan kala shida. A kwana biyar din sauqi ya samu sosai,ita kanta a jikinta takejin ta warke da taimakon wasu irin herbs 'yan Indonesia da anni ta bata. A kwana biyar din ta wani murje,hankalinta kwance bata ganin wulgawarsa bare fargaba ta dameta. Hatta anni ta karanci yadda hankalinta ya sake kwanciya,ta daiyi murmushi kawai saboda tasan tsakanin miji da mata sai Allah,bare wadannan data fahimci yanzu ne yake fafutukar gina gwamnatinsa. Batasan me za'ayi ba a gidan,don duka hankalinta yana kan karatunta,itadai ta shiga kitchen tana taya amna da anni girki. Annin ta fara fita ta barsu a ciki,amna ta fidda Warmers din tana shiryawa,ita kuma ta tsaya tana gyaran kitchen din. Idanunta d'ai d'ai cikin parlor din tana kallon wata sabuwar duniyar. Fuad ya dauke idonsa a kanta yana sallama don sanar da anni da amna dake dining suna magana shigowarsu. "Wa'alaikumussalam......marhaba da matafiya" Anni ta fada da murmushi saman fuskarta tana saukowa daga dining area din tana nufosu. Tun bata qaraso ba maamah ta fara qare mata kallo,tayi kyau cikin super embellished me asalin tsadar. Kwanciyar hankali nutsuwarta da riqonta da ibada sun sanya wani irin kwarjini akan fuskarta gami da fidda ainihin quruciyarta,kai bakace itace uwa ga saddiq da farouq ba. Tako ta ina sai take ganin annin ta fita samun duniya ne,wannan shine sirrin wannan kyan da take gani tattare da ita. Dom ta sutura tana sanya sama da suturar dake jikin annin a yanzu. "Barkanku da zuwa.....saddiq ku dauki luggage dinta zuwa daki......me babban suna ya akayi baka bada exact time din da zaku sauka ba?" Anni ta fada tana dauke kai daga irin duban da maamah ke mata "Na sha'afa ne anni.....amma gamu mun iso alhamdulillah" Yayi maganar yana shafa sumar kansa,gaba daya hankalinsa yana wajen amna yana tunanin ganin sabreen tare da ita. "Alhamdulillah.....haka akeso ai.....bismillah Mariya mana kunata tsaye?" Anni ta fada tana jifan maamah da murmushi. Idanu maamah ta janye a kanta,tana jin wani abu yana tokare mata wuya. Yau ita akewa tayin zama a gidan d'anta?. "Da baki gaggawa ba ameenatu,zama kam nina cancanceshi" Ta fada tana son maida maganar cikin yanayi na wasa wasa. Sosai maganar ta samu muhalli a zuciyar anni,ita kuma ta sani bawai da wasa mariya ke maganar ba,saidai koma meye ta shiryama zama da mariya din albarkacin muhammad fu'ad din. "Zo mana amna" Anni ta fada tana kiran amna dake zaune kawai. Haka kawai takejin batason rabar matar......bata son yanayin kallon da take binta dashi. Qarasowa tayi inda annin take,ta sani sarai anni na iyayi mata fada don haka ta rusuna tana gida maamah data fidda mayafinta ta aje gefe da bawa kowa na wajen tabbacin tazo gurin data isa ne. Kaman yadda ta saba amsa musu gaisuwa haka ta amsawa amna. "A gabatar mata da ruwa....sun sha hanya ita da hammanki". "Karki kawomin zallar ruwa,lemo nake buqata da wani abun tabawar bawai dangin ruwa kadai ba" Daga amnan har anni ba wanda ya nuna yaji abinda tace,illa anni ta dubi amna "Ki duba fridge kiyi warming pizza da samosa ki hado dashi". Kai amna ta gyada a sanyaye tana nufar kitchen din. Har yanzu ta kasa aminta da gamsuwa matar wai itace mahaifiya ga hammansu. Gefe anni ta samu ta zauna tana gayawa kanta da kanta. Maamah ta cancanci kawaicinta kawai saboda fu'ad din. Sam sabreen bataji shigowar amna ba sai data gama hada kayan zata fita sannan ta riqota tana cire earpiece din kunnenta. "Ki cewa anni an kammala,sai meye za'a dora mata?". Kai kawai ta gyada mata ta fice,tanason ce mata hamman ya dawo amma kuma yanayin sanyin jikin data tsinci kanta a ciki ya hana mata. Sake daga kansa yayi cikin matuqar zaquwa yana sanya ran ganin fitowarta a kitchen din tare da amna. Saidai a yanzun ma amnan kawai ya gani ta fito. Iska ya zuqa sosai yana fesarwa "Me take buqata dashi ne?,hauka take so ya fara gwada mata tuburan?" Ya tambayi kansa yana jin zuciyarsa tana quntata waje daya. Sheqeqe maamah tabi tray din da amna ta shiryo,ta tabe baki wanda muraran duk wanda ya kalleta zai gani. Baya amna taja tana gayawa anni saqon sabreen,abinda yasa ruwan da maamah ta kurba yayi mata cak a maqogaro. Juya zancen takeyi tsakanin rai da zuciyarta. Me haka yake nufi?,kyakkyawar alaqa tsakanin sabreen din kena da ameenatu?,yarinyar ke niyyar zame mata qadangaren bakin tulu ko.kuma ameenatun?,waye ainihin matsalarta a cikin su biyun?. Ta bangaren fu'ad din sai ya dinga ji ransa yana sake baci....dole ya sake tabbatar mata ita mallakinsa ce,dole ya sake tuna mata muhammad fu'ad mijinta ne.....mijin da bazai juri qaurace masa ba.....mijin da bazai juri bada umarni tasa qafa ta take ba saboda raini. "Kice ruwan zafi kawai zata dafa......ta fito ga baqi sunzo tazo su gaisa". Anni ta fada tana duban amna. Baisan ya miqe tsaye ba,shidai yaji yana gayaw anni "Bari na samo warm water.....nasha sanyi a haram da yawa" Yayi maganar yana jin wani magnet yana jansa zuwa kitchen din,ba tare da ya tuna waye da waye a wajen ba. Ajiye cup din hannunta maamah tayi tana binsa da kallo sanda yake takawa hankali kwance zuwa kitchen din. Tuni amna ta wuce dakinsu don ba zatayi gangancin komawa kitchen din ba tunda can hammansu ya nufa. Wani mamaki yake kashe maamah tana daga zaunen. Ita din ba yarinya bace haihuwar jiya ko yau,ta sani sarai ita yabi....sabreena yabi bako shakka. Daga yanayin fu'ad din kawai tasan akwai abinda ke jansa zuwa can din,wani dakiya da shariya ta gani tattare dashi wanda bata taba ganin irinsa ba. Yadda yake tafiya zuwa kitchen din hankalinsa kwance kaman ba wani idon kunya a wajen?. Sanda tayi nisa da binsa da kallo a lokacin anni itama tayi nisa da qare mata kallo da kuma fahimtar rudewarta da kuma canzawar yanayinta lokaci guda. "Ya rabb......kasa addu'ar dana bata tsahon dare ina yinta ce ka amsa.....ubangiji ka sanya wannan mummunan qullin ka juyar dashi zuwa kyakkyawa". Anni ta sake jaddada addu'arta can qasan zuciyarta wani murmushin nishadi yana subuce mata. "Tabbas kina dab da ganin yadda ubangiji ke jujjuya al'amura......kina kuma dab da samun ciwon hauka muddin akan Sabreen da fu'ad ne" Anni ta sake fada qasan ranta. Ba jiya yau ko shekaran jiya ba take karantar duk wani motsi na fu'ad ba.....me babban suna ya canza gaba daya.....ya shiga wata gawurtacciyar koma ta soyayya wadda tayi imani shi kansa baisan girman abinda ya fada a cikinsa ba......karantar irin wannan yanayin kuma sai uwa ko gawutaccen masoyi. "Zan shige daki na shirya.....naga magarib tana dab da isowa.....ga masaukinki can,a huta lafiya" Muryar anni ta dawo da ita daga rudanin data shiga. Bata sake cewa maamah din komai ba,saidai ta barta da kallon murmushin dake kwance akan fuskarta. Ita ba zata bari fu'ad ya fito ya sameta ba ballanta yaji kunya ko ya raga daga soyayyar da yayi niyyar nunawa matarsa ba.....ta barwa maamah ta fara kallon sample kafin anihin abun ya bayyana a idanunta gaba daya. Idanunta ciki ciki tabi anni da kallo har ta isa dakinta. "Ta ina kuma ameenatun ta sake bullomin?" Ta yiwa kanta tambayar zuciyarta cike da kokwanton murmushin data gani saman fuskarta. _turqashi😂😂,anya maamah nan din gidan zamanki ne kuwa?_ _maji ma gani dai_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 92 92 A hankali ya tura qofar kitchen din sannan ya maidata ya rufe a nutse bayan ya karanci earpiece ne a kunnenta,sai ya maida bayansa jikin qofar kitchen din,ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo. Ta fidda hijabij jikinta ta saqaleshi a hanger na kitchen din don tafi jin dadin yin aikin,bata da damuwa kan musaddiq ko saddiq,dukkaninsu idan zasu shiga wani guri cikin gidan saisun tsaya daga waje sunyi sallama. Sassalkan gashinta da amna ta kame mata su da hair clips masu kaloli da shapes daban daban jelarsa ta baje sosai a bayanta. Baqi sidik ne yanata shining saboda ko da can ita din bame wasa bace da gyaran jikinta ma gaba daya. Idanunsa ya lumshe yana bin sauran sassan jikinta da kallo,qugunta ya bude sosai ta cikin skirt din dake jikinta,shape dinta ya fita sosai da duk wani sura na kyau da Allah ya bata. "Ya salam" Ya furta qasan ransa saboda wani irin magnet dake fusgarsa zuwa gareta. Wani sashe na zuciyarsa ya raya masa inda wani tsakanin musaddiq da saddiq ne ya shigo a haka zai ganta?. Raba jikinsa yayi da qofar ya fara takawa a nutse yana dosarta. Dukan hankalinta yayi nisa wajen killace plates din data wanke. Kwata kwata bata kawowa ranta wai dawowarsa ba ballantana shigowarsa kitchen din ba. Ta gama jerawa tayi taku biyu baya don matsawa daga wajen,santsin man daya diga a qasan tiles din ya kwasheta,tayi baya zata fadi a matuqar tsorace. Hannayensa ya sanya duka biyun ya tarota,take ta samu masauki a faffadan qirijinsa. Gam ta sanya hannu tana riqeshi ba tare data fahimci a jikin wanda take ba,tunaninta duka ta samu wani abunne ta kama. Fadowarta jikinsa ya bashi daman qarewa kyakkyawar fuskarta kallo. Karon farko da wannan tsiwatacciyar fuskar ta fito a matsayin matsoraciyar fuska. Sauke idanunsa yayi saman qirjinta dake sama da qasa alamun tsoro muraran da kuma yawan adadin bugun da zuciyarta ta qara. Cikin qasa da second ashirin hankalinta ya fara dawowa jikinta bayan ta tabbatar batasha qasa ba,ta zuqi numfashi sosai wanda hakan ya taimaka mata wajen isar lallausan qamshinsa qofofin hancinta ya kuma isar da saqon waye me turaren cikin kwanyarta. Idanunta ta ware da sauri,take suka fada saman fuskarsa dake dab da tata,sukayi wani zuzzurfan musayar numfashi daya hautsina masa tunani karon farko. Kyakkyawar fuskar nan tasa dake shimfide da wani irin kyau da ba kowacce fuskar d'a namiji ke da baiwar irinsa ba.....wani irin kyau me cakude da kwarjini musamman cikin narkakkun idanunsa da kallon cikinsu yasha banban da idanun kowacce d'a namiji data taba kalla. Cikin sauri ta tura qirjinsa baya tana zamewa daga jikinsa,saidai ya gwada mata halittar sam ba daya bane ta hanyar miqa hannunsa ya damqota. Wata kyakkyawar runguma yayi mata ta baya gana matseta cikin jikinsa,ya aza fuskarsa saman kafadarta,sannan ya motsa labbansa da wani irin nannauyan numfashi. "Am back.....am home.......but......" Ya fada yana dagata gami da juyo da ita gaba daya tana fuskantarsa sosai. Raina kanta tayi sosai ganin yadda ta koma 'yar qarama a gabansa,ya kuma ritsata da wannan kallon nasa yana duban duka qwayoyin idanunta kafin ya jefa mata tambayarsa. "You break my rules hajjaju.....don't blame me indai na tashi hukuntaki" Yayi maganar cikin nuna mata da gaske yake yana miqa hannunsa zai shafi gefan fuskarta. Baya taja da sauri,abinda ya sanya ya tsaya ya zuba mata ido. Da gaske take batason koda yatsarta ya taba.....ko yaya ya kusanta kanshi da ita saitayi wani abu da zai nuna bataso. "Ya kamata kabar kitchen din nan kafin wani ya shigo ya ganka" Ta fadi masa tana qoqarin maida hijabinta. Taku uku ya isa gabanta,ya sanya hannu ya fusge hijabin yana kuma jawo kujera dab da ita ya zauna ranshi a hade yana fadin. "Wace irin mace ce ke?.....bakiyi kewata ba?" Yayi tambayar da gasken gaske tun daga qasan zuciyarsa,yana fatan ko sau daya yaji tace tayi kewarsa. Wani kallo ta watsa masa sannan ta janye idanunta,ta taka tana kashe gas din sannan ta soma tafiya a nutse zuwa bakin qofa. Iya hakan ya bashi tabbacin ficewa zatayi,ba kuma zaka kulashi ba kenan. A zafafe ya miqe yana wurgi da hijabin nata,ya sake shan gabanta yana mata wani duba nakai tsaye. Ko ba'a gaya mata ba zuwa yanzu tana saurin gane abinda ya taba zuciyarsa. Sauyawar yanayinsa wani abu ne da yake saurin razanata. Soma hade tazarar dake tsakanin su yayi yana duban idanunta sosai. "Na tsani nuna halin ko in kula......na tsani wannan attitude din.....Please behave.....or I'll have to take disciplinary action" Yayi maganar har zuciyarsa yana nufin abinda ya fada din soft lips dinta masu kalan red dake motsawa kadan kadan alamun tsiwa na cinta suna fusgar hankalinsa. Yasha imagination na sanda zata mallaka masa su ba gardama ba tare daya qwata da qarfi ba......bama iya su kadai bama.....dukkaninta yakewa wannan fatan da kuma burin. Lallausan tafin hannunta ya matsa yana sauraren Jin muryarta. Muryar data zame masa abokiyar hirarsa a mafarki tun waccan ranar data amsa wayarsa a garin makka. Idanunta ta jjanye daga kanshi,har yanzu batajin zata iya kulashi din......duk sanda ta kalli fuskarsa fareeda take gani kwance cikin qirjinsa.....duk sanda ta kalleshi munanan maganganunsa a kanta take tunawa.....muguntarsa da musguna mata da mugayen maganganu,don haka ta taka zuwa side din hagunsa da nufin rabeshi ta fice. Cak ya dagata ya azata saman kitchen cabinet din ba tare da tunanin tayi kusa da qofa ba,ko kuma jama'ar dake gidan ba. Hannayensa ya sanya ya zagaye bayanta dasu,ya hana mata kowacce dama da zata raba jikinta da nasa,ya kuma yi kane kane a fuskarta ya hanata matsawa ko kadan,da wannan daman ya samu ya riqe lips dinta da suke tsone masa idanu ya fara aike mata da wani irin tattausan kiss. Ba wannan zafin ba kuma wannan hanzarin,wani irin sarrafata yakeyi da wani irin sanyi da salo daya soma zare mata duk wani kuzari da takeji da kuma zafin da takeji a kansa. Duk wani tunani nata ya tsaya cak tun daga sanda ya wuce cikin kitchen din. Wani abune da yazo mata a bazata wanda bata taba tunanin zai faru ba. Yau fu'ad ne a gabanta ya tsallake yabi mace kitchen da zummar zai samo ruwan dumi?. Cup din hannunta ta ajiye tunaninta yana komawa baya,ta saita dukkan idanunta da hankalinta akan qofar kitchen din tana lissafin mintuna nawa zaiyi kafin ya fito. Falon yayi shuru saboda wucewar kowa sai ita daya data rage,ta dauke kanta tana duban agogon hannunta bayan shudewar mintuna biyar din data tabbatar ko dafa ruwan za'ayi wadannan mintunan sun wadatar. Kujerar da take kai din sai takejin kamar ta mata nisa da bakin qofar. Miqewa tayi tsam tana canza kujera mafi kusa da bakin kitchen din tana sauke wani zazzafan huci,tanata qoqarin hana zuciyarta ci gaba da hasashen abubuwa daban daban da zuciyarta ke saqa mata. "Da gaske yarinyar nan 'yar bariki ce.....da gaske bariki takeson gwadamin?.....wai uban me yakeyi a kitchen din?,da gayya ta tsareshi kenan don ta gwada mata iyakarta?" Wadannan tunane tunane su sukaci gaba da kai kawo tsakanin zuciya da kwanyar maamah. Sake matsawa tayi kujera ta gaba tana sake zurfafa jinta da kuma idanunta akan qofar kitchen din,amma bata iya jiyo komai,abinda ya sake assasa baqincikinta. Wai wanne tsautsayi ne ya hanata tsaiwa a nigeria tasa ayiwa fu'ad da sabreen din mummunan farraqu?,irin farraqun da ko me irin sunanta zai tsani ballantana ita da kanta. Maida idanunta tayi ga agogo tana duba adadin lokutan da aka shafe. To badai dafa ruwan dumi ba....ko dan mutum za'a dafa a wannan gabar yaci ace ya dahu wani irin tsalle zuciyar ta keyi,wani sashe na zuciyar na bata shawarar shiga kitchen din da kanta taga qaryar rashin kunya. Sau uku tana miqewa sai ta koma ta zauna cikin shakka da kokwanto. Batasan ya zataji ba idan taje ta tadda daidai da abinda tunaninta yake bata. Qaqqarfan motsin da taji daga kitchen din ya qarasa tunzura zuciyarta,ta miqe da wani irin gaggawa ta durfafi kitchen din. Baya fahimtar komai sai sabreen din dake gabansa......kowanne sashe na jikinsa karbar saqo yakeyi iyaka,baisan wanne irin kebantaccen shauqi yakeji haka a kanta ba. A yadda yakejin kansa a lokacin yana jin kamar duniyar ma tayi musu kadan shi da ita. Ya sake zurfafa harshensa cikin bakinta yana sake zare mata duk wani kuzari nata. Qwace masa numfashinsa ya dinga yi yana kamoshi da qyar,a daidai wannan lokacin maamah ta qaraso bakin qofar kitchen din cikin zaton zata samesu tsakiya ko qarshen kitchen din. Tamkar an juya kwanyarta daga sama zuwa qasa haka taji. Wani irin shock jikinta ya dauka na tsakanin mamaki da kuma tsoro,jikinta da qafafunta gaba daya suka dauki kyarma,saita juya da matsanancin sauri tana jin juwa na shirin kayar da ita. Tana juyawa yana zare bakinsa a nata,baiganta duka ba,amma yaga wani sashe na rigarta. Zazzafan numfashi ya furzar yana cure hannun sabreen dukka cikin kasa hadi da kifi fuskarsa a bayan hannuwan nasu yana qoqarin daidaita numfashinsa. "Maamah" Ya fada can qasan ranshi,kwata kwata ya manta ya barta a parlor,amma yayi tsammanin yadda anni ta wuce daki itama dakin ta nufa. Daga fuskarsa yayi data sauya launi yana zubesu saman tata fuskar. Fuskarta ta kawar tana qoqarin dauke hawayen dake shirin zubo mata. Ya gansu,don haka ya sanya hannu da nufin dawo da fuskarta saitin nasa,saidai ta rigashi ta hanyar ture hannuwan nasa. A wahalce a kuma kasalance yace. "Na jima ina baki wannan shawarar......zanci gaba kuma da maimaita miki ita....kada kice zaki gwada raba kanki dani......zaki wahalar da rayukanmu ne kawai......don fu'ad bai shirya rabuwa da duk macen data sanshi a d'a namiji ba......fu'ad bai shirya rabuwa da sabrrrr ba" Yana kaiwa nan ya zame hannuwansa daga nata,yaja baya still idanunshi a kanta yana tunanin maamah na parlor din har yanzu ko tabar wajen. Har takai qofar dakinta ta fasa shiga,ta samu kujera ta zube tana qoqarin qwato koda abu guda ne cikin tarin abubuwan da suke karakaina a kanta. Da gaske bariki ne zalla za'a gwada mata?......ta samu nasarar mallakarsa ne?,yaushe ta ingizashi zuwa soyayyarta?,tayi imani a banza fu'ad bazaiso mace irinta ba......matar da karuwanci da bariki suka zama shaida kuma tambarinta na farko koda mutuwa tayi?. Hannuwansa ya miqa mata bayan ya gama daidaita mode dinsa. Bata ko kalleshi ba bare yasa ran zata bashi hannun nata. "Musunki da gardamarki zasu iya tunzurani na aikata abinda banyi niyya ba.....karki manta kawaici kawai nakeyi miki.....karki yadda kawaicina ya qare......kika bari hakan ta faru.....to tabbas ki rubuta ki ajjiye zan daukeki na kaiki wata duniya da ba wanda ya isa ya ganki sai muhammad fu'ad shi kadai". Fararen idanunta da suka sake glowing saboda siririn hawayen da yake a ciki ta watsa masa,kai tsaye ya saka hannu yana dafe qirjinsa hadi da lumshe idanunsa kafin ya sauke hannun nasa ya saka hannu ya kamo lallausan tafin hannunta yana sauko da ita. "Kinci bashi da yawa na rashin kula da abubuwan da suka ratayi a kanki nawa......duk wani abu nawa daya kamata ace kinyi bakiyi ba ki rubuta ki ajiye ya shiga sahun bashi". Kasa musanta masa tayi sanda yake riqe da hannunta suna fita a kitchen din. Hannun kujera ta koma ta zauna tana hade hannayenta a qirji zuciyarta tana mata wani irin zafi. Bata jin zata iya daukan wannan abun sam ba zata jura ba.....tana da shakka idan har zata iya barin sabreen a gefen danta har xuwa lokacin data tanadar mata. Sanda ta daga idanun nata don sake duban kitchen din sai tayi kyakkyawan gani,yana riqe da hannunta gam da taketa qoqarin zamewa. "Kina qarawa kanki laifi akan laifi......please ki hutar da kanki" Ya fada yana lumshe idonsa gami da jin yadda riqe hannunta kadai ke sakarwa jikinsa wadansu kaifafan makamai. "Muhammadu" Ta kirashi da wani kaifi da yake nuna zallar bala'i da bacin rai da zuciyarta ke ciki,musamman data lura bai ankara da wanzuwarta a wajen ba. _ayimin afuwa a karbi wannan ba yawa,mu hadu gobe in sha Allah_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 93 93 Kiran data masan yaja hankalinsu shida sabreen din,idanunsu suka hadu karon farko ita da sabreen suka sakarwa juna wani kallon kallo kafin sabreen din ta janye idanunta salin alin tana kuma sulale hannuwanta daga cikin nasa. Ta kowanne fanni jikinta ya bata al'amura da dama akan matar daga kallon farko kawai,ta danne zuciyarta tadan ciji labbanta na qasa ta taka a hankali tana qarasawa gabanta. Abinda bata taba kawowa zai faru ba,sabreen din ta zame a gabanta tana fadin. "Barka da yamma". Ruwan mamaki ya gama kasheta,ta dauke idanunta daga kanta tana maidawa kan fuad din. Sam idonsa bai kansu,kamar ma bashi a wajen. "Turqashi.....ni zaki saka cikin kokwanto?" Ta ayyana a ranta. Cikin kwanakinsu dashi a saudiyya ta dinga jeranta masa huduba da qorafin rashin kirkin matarsa da fatan samun wata kafa da zata sake nesantata daga rayuwarsa.......a yanzun kuma sai ga yarinyar da take complain a kanta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa. "Ta yaro kyau take bata qarko......idan kinsan wata bakisan wata ba yarinya". "Lafiya qalau......sai yau kika iya tunawa da wanzuwata?" Tayi maganar tanason tabbatar da maganarta ta farko a zuciyar fu'ad da ya fara wucewa zuwa dakinsu. "Aah fa.....wannan d'iyar tamu sai kin mata uzuri.......tunda mukazo Maldives ba lafiya.....yanzun haka jinya take" Muryar anni ta ratsa plan din maamah din ta kuma wargazashi,sannan ta saukar mata wani irin gigitaccen yanayi daya hautsina kwanyar maman. "Bata da lafiya?,me kuma ya sameta?" Tayi subul da bakan jefa tambayar dake yawo tsakanin zuciya da harshenta. "Tashi daga tsugonan nan karki wahala da yawa.......jeki watsa ruwa ki huta,Allah yayi albarka" Anni ya fadi tana taya sabreen ta miqe. Ko waiwayen maamah din sabreen bata sake yi ba......zubewarta a gabanta yana da nasaba da musaddiq.......mutum ne cikakke d'aya da d'aya,wanda ke tsananin ganin kimarta da kuma mutuncinta......idan har zata iya wuce mahaifiyarsa saboda wani abu daban da tsakaninsu ne kawai.....to tabbas bata mutunta mutuntawar da yake mata ba. Ya girmeta amma baya iya gaidata a tsaye ba tare daya duqa mata ba.....dame zata biyashi. Yadda maamah tabi sabreen da kallo zuciyarta na wani irin duka ya sanya anni sakin gyaran murya. Dawo da dubanta tayi kan annin ita kuma ta basar tana cewa "Dazun kina tambayar me ya sameta.....lalurarmu ca ta mata......matar aure ai ba'a rabata da qananun lalurori" Anni ta fada tana ajjiye diffuser din da dama ita ta fito da ita ba tare data sake kallon fuskan maamah ba. Wani dummm taji kunnuwanta har qwaqwalwarta sunayi. Maganan anni maimakon bata haske sai duhu ma data sake sanyata a ciki. Lalura ta mata ciki ko bari?,wanne anni ke nufi a ciki?. Tsaye tayi a wajen kamar sakarya,kafin wani lokaci falon ya sake zama sai ita daya a ciki. A daren tayi nadamar da batasan adadinta ba na tsananta bincike har kunnuwanta sukaji mata maganar da ta gaza samun amsarta. Magana me harshe damo mafi rudani data taba ji. Idan tace a daren tayi bacci to tabbas me karatu ma yasan tayi qarya,ta qulla ta kuma kwance har batasan adadin sau nawa ba. Tayi rantsuwa ta kuma lashi takobin muddin ciki ne da yarinyar......muddin tayi kuskuren samun juna biyu da muhammadun lallai saita sakata cikin nadama da dana sanin da babu ranar fitarta. Daga qarshe ta yanke shawarar sanya idanu a dukka motsinsu don tasan wanne mizani zata dora mataki na gaba ★Jiyan tunda wuri ta gama shirinta ta kwanta abinta,don haka daga maamah har d'an nata babu wanda yaga gilmawarta sam. Cikin rashin sani maamah din ta tsareshi wajenta da hirarrakinta marasa armashi,a nata tunanin Daki daya suke kwana,duk da tana kokwanton hakan a ranta,amma zargin cikin da takeson tabbatarwa ya kasa bata nutsuwa ko tabbacin taren suke ko ba tare ba. Duk da akwai cook dinsu ta musamman dake zuwa musu girki tun a wancan gidan,amma sai ta kasa kwanciya bayan gari ya fara haske. Daga amna har anni da bacci ya dauke saman abun sallah tana tsaka da karatun qur'ani basusan da fitar ba. Haka kawai takejin bai kamata ace ita da amna duka suna kwance ba har sai sun jira cook tazo. Ta san ba wani qwarewa tayi da kalolin girke girke irin nasu na masu hannu da shuni ba,amma ko yaya tana da rawar da zata taka,tana kuma da gudunmawar da zata bayar,zata kuma iya dafawa aci ba qorafi ko mummunan rashin dadi. Shuru parlor din nasu,kowacce qofar daki kuma a rufe,haka ta ratsa a nutse har ta isa kitchen din. Bata da tabbacin ya tashi,amma still sai taqi fidda hijabin nata,don ma qarami ne bazai hanata kowanne aiki ba,ta fara duba freezer da ma'ajiyar abincin tana tunanin me dame zata fara aiwatarwa kafin matar ta iso?. Tunda ta idar da sallah tana saman abun sallar,bawai kuma zikiri ko karatun qur'ani takeyi ba.....aah babu ko guda daya. Ta zauna ne kawai tana gadin lokaci,ta zauna ke kawai tana sanya kunne da idanu akan kowanne motsi da zata iya jiyowa daga parlor din. Tunda yayi sallar asuba shi dinma bai koma ba,wani irin bacci ne mara dadi kwata kwata ya daukeshi. Zuwa lokacin yana jin kamar haqurinsa yana dab da qarewa,cikin sati hudu anci sati uku.....baisan wanne haqurin zaici gaba dayi ba sama da wannan. A jiyan sanda ya baro wajen maamah yayi zaton daya koma dakinsa zai samu anni ta turo ta,ya fuskanci anni ma kaman tana bayanta ne,banda haka yaci ace an duba lamarinsa an bashi matarsa. Farouq kadai yasan zai iya masa wannan aikin,saidai kuma shaqiyancin farouq din kawai yasan ya isheshi kafin ya samu yayi masa abinda yakeso din. Kayan jikinsa ya canza zuwa kayan motsa jiki da suka fitar da murdaddiyar surar nan tasa da ginannen jikinsa. Kwana biyun da bai motsa jiki ba sai yake jin jikinsa kaman yana masa ciwo,ya sanya rufaffun takalma a qafarsa ya kashe wayoyinsa ya ajiye ya fito. Already ya samu gym nan kusa dasu,ba wani nisa ne tsakaninsu ba,don a qasa ya qarasa da sassarfa. Awa guda kacal ya gama ya kammala ya fito,suka jero shida jordan suna magaganu jifa jifa akan abinda ya shafesu. A nutse ya buda qofar parlor din yana takawa a hankali,idanunshi still akan qofar dakin anni. Idanun nasa ya janye yana lumshesu,yana jin inama zaya samu daman da zai qarasa gareta. Wata kewarta ke ratsashi....kewarta ba kuma iya kewar fuskarta kawai ba......dumin jikinta.....qamshinta.....da tausasan labbanta.....harda tsiwar nan tata da wani lokaci take maidata qanqanuwar yarinya ba tare data san da hakan ba. Har zai wuce dakinsa yaji yana buqatar ruwa,tunda baishan ruwa yawanci bayan kammala motsa jiki sai bugun zuciyarsa ya daidaita. A nutse yake takawa xuwa kitchen din,cikin jikinsa da zuciyarsa sai ya dinga jin kaman akwai wani abu me muhimmanci a wajen,kaman yana qara kusanci da wani bangare na musamman daya tsage daga zuciyarsa. Idanu ya zuba mata sosai sanda yake hangota,kaman shigen jiya saidai yau tana maqale da farin mayafi,tana tsaye gaban tarin Irish potatoes din da take barewa a nutse da peeler. Idanunshi ya lumshe yana kuma budesu duka lokaci guda,yana jin wani abu yana taso masa. Tun daga waccan ranar.....tun daga kuma wancan lokacin zuciyarsa bata sake samun nutsuwa ba,yana jinsa kaman bashi bane,yana jin kamar an sauyashi ne da wani mutum na daban ba muhammad jadda ba. Ta hana zuciyarsa hutawa tun daga wancan lokacin,ta kuma hana masa damar sanin WACECE ITA?. A jikinsa yake jin akwai wani daban tattare da ita.....akwai wani boyayyen labari a bayan wannan matsiwaciyar fuskar. Kaman jiya dai,yau kam baisan me ya dauke hankalinta har haka ba,gwara jiyan akwai earpiece a kunnenta,wanda sai bayan ya zare yaji abinda take saurara din. Takawa yakeyi a hankali har ya isa bayanta. "Salam alaikum" Ya fada yana harde hannunsa a qirji qamshin turarenta me wani irin sanyi yana buso masa. Wani irin faduwa gabanta yayi,ta tsorata ainun da jin muryarsa dab da ita,amma sai ta dake taqi waiwayowa,ta motsa labbanta muryarta can qasa ta amsa "Wa'alaikumussalam" Ba tare data waiwayo ba tana ci gaba da bare dankalin. Shuru ya ratsa tsakaninsu,ya fahimci ba zata juyo bane don haka ya taka yana zagayawa ta gabanta a nutse ya tsaya a gaban nata,tazarar inches kadan tsakaninsu. Hannu ya miqa kawai ya zare peeler din daga hannnunta,ya kuma miqa daya hannun ya zare irish din da take barewa. Fararen idanunta ta daga da zummar masa tsiwar tata,saidai cikin sa'a caraf suka shige tsakiyar nasa idanun. Da sauri ta kauda qwayar idanunta gefe,duk wani rashin kunya data tanadi yi masa ya soma zurarewa gefe. "Duk karatun da kukeyi har yanzu baki koyi gaida miji ba?" Ya tambayeta calmly da wani irin sassanyan sauti. Gaza dubansa tayi saboda yadda kwarjininsa yake neman cika kitchen din gaba daya. Wadannan muscles din nasa ba qaramin tsoratata suke ba,har bata qaunar ya sanya qananun kaya. Ita daya tasan me takeji idan ta gansu,ita daya tasan irin qwarin da suke dashi,saita zabi matsawa daga wajen ko zata samu daman shaqar iska me kyau wadda bata gauraya da dumin numfashinsa ba da kuma na turarensa daya qara sanyi saboda cakuduwa sa gumin jikinsa da yayi. Da qafa kawai ya tokareta,sannan ya daga nashi fararen idanun ya watsa mata,tayi zaton zai janyesu daga kanta don haka bata janye nata ba,idanunta suka sauka a hankali saman redlips dinsa masu tudu da wani irin shape,quarter million din dake zagaye da habarsa zuwa zaman labban nasa ya sake zamewa labban nashi wani ado na daban. Haka kawai tsigar jikinta taji ta tashi,abinda bata taba ji ba tsahon ganinta da duk wani d'a namiji. Qoqarin janye idanunta tayi,da qyar ta samu nasarar yin hakan kowanne sashe na jikinta taji yana daukan sanyi,rudewa taji tana shirin yi kaman barawon daya shiga tuhuma a hannun hukuma. Wani siririn murmushi daga can qasan zuciyarsa ya qwace masa "Dama bakisan ni naga dama nake qyaleki ba yarinya" Ya fada can qasan ransa,amma a sarari sai ya juya gefansa saman cabinet din,ya ajiye peeler din da Irish din,ya sanya hannuwansa ya zagayesu ta mazaunanta yana jawota jikinsa da dan zafi zafi,abinda ya bata daman zubewa a qirjinsa kafin ta daga kai tana neman qwacewa. "Stop ita DUNIYATA" Ya fada softly idanunsa a kulle yana yadda fatar singalilin hannun ta ke gogar nashi tana tayar masa da tsigar jiki. "When.....sai yaushe zaki fahimci cewa KECE DUNIYATA?" Ya qarasa maganar yana ware idanunshi gaba daya akan fuskarta. Wannan karon kasa jure kallonsa tayi,saita runtse idonta tana hade rai sosai. "Banaso kana tabamin jiki.....bana so" "Am addicted to you.......tabaki shine favourite thing a rayuwata gaba daya" Ya maida mata amsa kai tsaye yana me bata tabbaci ya kuma sake matso da ita sosai yana mannata da jikinsa. Gigicewa tayi sanda taji ta saki ajiyar zuciya tare da tashi ajiyar zuciyar,kunya da wani irin takaici ya lullubeta,abinda taji haduwar jikinsu ya saukar mata ba zata iya shanyeshi ba idan bata bawa zuciyarta daman numfasawa ba......to amma kuma ta dauka a boye ta saki nata ajiyar zuciyar. Fitar sautin ajiyar zuciyar tata ya sakashi ware dukkanin idanunsa a kanta yana dubanta,duba ne na qurilla da son gane meye ya taba wannan zuciyar?. A gaggauce gama shiryawa tsaf cikin Holland vlisco me asalin tsadar,an xuba mata dinkin manyan mata na buba,ta kuma cika wuyanta da hannunta da kayan ado na gold. Macace me son izza da alfahari,wadda idan tazo guri so samu kowa ya dusashe a gurin sai iya tauraruwarta kadai. Ta tsaya gaban madubi ta tabbatar komai yayi a shigarta sannan ta juya ta dauki wayarta tana nufin fita a dakin. So take ta kasa ta tsare......so take komai zai dinga wakana cikin gidan ya dinga kasancewa saman idonta,bataso tsakanin sabreen ko fu'ad wani yayi wani motsi da zai zarta ganinta da idanunta,wannan karon salon da zata bullo musu dashi na dabanne,har sai ta samu tabbatuwar nasara a gareta. Tanaso da iya dressing dinta kawai ameentu ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ameenatu ta sake tabbatarwa da kanta cewa ita din fa itace mahaifiya ga muhammad jadda.......ba wata mace a duniya ta biyunta. Cikin takun isa take fita parlor din tana qarewa ko ina na parlor din kallo. Siyan gida a qasashen waje musamman gidaje irin wadannan ba abu bane da za'ayi maganan qananun kudade ba. Abinda ta lura dashi wasa wasa ameenatu ta maida mata yaro saniyar tatsa kenan,taja wata irin qwafa tana samun sofa guda daya ta hakimce a kanta. Daga inda take ta sanya remote ta kunna tv,tayi sa'a tashar farko ta kamota a inda suke gabatar da abincij breakfast na yaren mutanen qasar china. Minti uku kacal taji tunaninta ya koma ga kitchen din gidan,tanaso ta tantance dame dame ya jibge musu suke ci?,wanne irin gadara kuma ake gwadawa a wajen?,don haka ta miqe tsam tana maida flats shoe dinta tana nufar kitchen din. Yau kam sai data shigo sosai sannan idanunta ya sauka a kansu. Mugun gigicewa tayi fiye da jiyan,saboda yanayin data gansu a yau din yafi na jiyan munin gani. "Na shiga uku ni mariya!" Ta fada muryarta na rawa tana yunqurin juyawa,wanda saurin da take ta matsa a wajen santsin gurin ya debeta ta kusa zamewa,cikin taimakon Allah ta kama murfin freezer ta riqe tana tsaiwa saman qafafunta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 94 94 Daga shi har sabreen din sai a lokacin suka dawo hayyacinsu. Ita ta fara zamewa ta tsakiya tana raba jikinta da nashi haushi yana cikata. Yana son lalla qarfi da yaji sai ya koya mata dabi'ar da ba tata ba......lallai lallai sai ya sanyata tana yin abinda ba halinta ba.......batasan me zata masa da zai sanyashi nesanta kansa da ita ba. Batason yadda yake warning nata kan bata isa ta raba kanta dashi.......a nata wajen ba wani abu me sauqi a wajenta sama da wannan din......zaman Maldives ya bashi wannan damar,isarsu Nigeria kuma zata yanke kowacce alaqa da yake tunanin ya qulla da ita. Juyawa tayi tana fita a kitchen din ba tare data sake kallonsu ba. Qirjinta ne kawai yake bugawa da wani irin bacin rai da kuma rudanin abinda ta gani din. "Wanne irin asiri tayi masa?,wanne irin asiri ne wannan?,maqale mata?" Ta dinga jerawa kanta tambayar da bata batasan amsarta ba. Yadda zuciyarta ke matsewa da bacin rai sai takejin idan tayi shuru tsaf zuciyarta zata iya bugawa......don haka ta soma sakin ruwan sababi. "Wanne wacce irin masifa ce?,gida sai kace gidan arna?,to wallahi ni bazan lamunci wannan ruwan tantirancin da barikin ba ehe....dole kowa ya gyara zamanshi,ni ba shashashar uwa bace ko banzar suruka,kome mutum yazo dashi ina daidai dashi ne". "Oops" Abinda fu'ad ya fada kenan yana dafe goshinsa da tafin hannunsa,zuwa yanzu yanajin anya zai iya rayuwa da mutane kuwa muddin yana tare da sabreen din?,anya gidan nan duk da haka bai musu kadan ba?,wannan zaman zai yuwu kuwa?. Duba daya sabreen tayi masa ta zare idanunta tana lalubar hanyar fita daga kitchen din ranta a bace. Jiya tayi zargin giftawar mutum dama a kitchen din,koda suka fita sukaga sai ita kadaice a falom zuciyarta ta dinga raya mata ita ta shigo......amma ba kasafai ta fiya son dorawa dan adam zargi ba,don haka ta cire abun a ranta,qarshe ma ta gayawa kanta. "Idanma itace ita ta jiyo......zaiyi mata dadi idan idanunta suka gani ta kuma tayata rabata da maqalallen d'anta. Dab da zata fice a kitchen din yayi caraf ya kamo hannunta yana sake janta jikinsa. Dubansa tayi idanunta na bayyanar da bacin da ranta yayi "Bayan maamah din ko akwai wanda kakeso ya sake shigowa ya ganmu ne?" Ta masa tambayar da salon gatse kanta tsaye tana duban qwayar idanunsa duk da tsaurin da kallon yake mata. "Yes" Ya bata amsa shima kai tsaye yana kallonta "Saura anni.....anni ce akwai ta rage bata gani ba.....ita nakeso ta gani.....don ta hakanne kawai zata fahimci ina tsananin buqatar matata". Har tsakiyar kwanyarta taji yadda ya fidda sautin maganar,wani abu me kama da jin kunya da nauyinsa ya danso kamata,saidai tana ganin ya kamata ta fito masa a mutum don ya sasssuta yadda yake yawan hada jikinsa da nata. Da alama da gaske yake fadi....da gaske yakeson annin ta gani,tunda daga nan inda suke tsayen tana iya jin muryar annin na tambayar maamah "Lafiya mariya?" Batajira jin amsar da zata bata ba ta soma kokawar qwatar kanta. "Annin ma?" Ta fada tana ware idanunta cikin kallon me kama da harara harara. Yadda ta yiwa idanun nata kusan kasheshi yaso yi,hannunsa ya miqa a hankali ya nufi gashin idanunta da suka sake zara zara saboda buda idanunta da tayin,abinda yadan saukar mata da tsoro ta rufe idonta da sauri. Kusan dariya abun ya bata,ya zuba mata idanu yana ganin yadda zuciyarta ke bugu sosai tun daga wuyanta zuwa qirjinta dake lullube da hijabi. "Bakisan harsashin da kika sake jefamin ba da wadannan idanun naki ba......a karo na gaba tsiwar nan zan cire gaba dayanta na maida gurbinta da zazzafar soyayya....." Ambatar soyayyar ya sakata bude idanunta a kanshi,tanason nuna masa tawayenta koda ta hanyar murguda baki ne amma tana kokwanton kada ta jawa kanta,sai kawai ta zabi zame jikinta daga nasa gudun kada annin ta samu isowar kitchen din. Still sake riqe hannunta yayi,ga mamakinta hankalinsa kwance yake janta zuwa falon kaman wani dan jagora. Daga can qarqashin zuciyarsa kuma wani kokwanto da mamaki ne fal ransa. Me yake tunzura maamah din a duk sanda ta gansu haka a tare?,bayan tafi kowa sanin igiyar aure ce ya hadasu?,me yasa yake ganin fushi kwance a fuskarta game da sabreen bayan a nashi tunanin zatafi kowa murna da farincikin kasancewar hakan?. Idan bar ba mantuwa yayi ba.....duka duka ba'a yi watanni biyu ba data masa kyakkyawan warning akan bawa yarinyar kulawa.....meye ya canza wannan?,wannan kadai yana sake bashi signal na AKWAI WANI ABU. Dukka juriyarta da dakiyarta ta tattara sanda suka iso parlor din,kanta tsaye ba tare da tabi ya banbamin maamah ba ta wuce zuwa dakin anni. Ko wani bai gaya mata ba tasan maamah din ta bita da kallo ne,kallon da ita daya tasan ma'anarsa. Tana qasan shower tana jin yadda ruwan kebin sassan jikinta amma mayataccen qamshin nan nasa bai matsa ko nan da can ba,duk inda ya aza hannunsa a jikinta sai ta tuna idan takai hannunta,ta kammala wankanta tsaf ba tare da tasan yadda suka qare a parlor ba don ba damuwarta bane. Ta jona dryer nan cikin toilet din da busar da kanta,sai abun ya fado mata a rai. Hala kishi maamah take da ita?,hala maamah tana tsoron kada ta karbe mata yaro?,qila maamah tana zaton mallakarta ce ita sabreen ke niyyar qwacewa?. Siririn tsaki ta saki a ranta tana fadin "Inda tabi a hankali ma wannan rayuwar tasu batamin ba......dab nake da bar mata d'anta" Tayi zancan cikin ranta saidai idanunta na kallon fuskarta ta madubin dake gabanta. Dif sai kuma tunaninta ya tsaya cak tana sake maimaita furucinta na qarshe. "Idan shi zaki iya barinsa.....zaki iya barin anni da amna?" Tambayar data tsaida duk wani tunaninta kenan,sai ta samu kanta da neman tabbacin zata iya ko ba zata iya ba?. "Su nadra huda haneefa sunfi muhimmanci cikin rayuwata" Ta gayawa kanta a gaggauce tana kunna dryer din da hanzari tana son binne wannan tunanin daga ranta. Idan banda rudin zuciya ma duka duka yaushe ta sansu?,yaushe ta fara rayuwa dasu da har zata shiga shakkar iya barinsu?. A nutse ya shirya cikin riga da skirt na sakakkun English wears. Basu kamata ba amma sun mata wani irin dan banzan kyau,musamman sata daure gashinta data gyarashi da kyau tsakiyar kanta. Wani qaramin hijabin ta samu ta sake dorawa saman kanta,saidai wannan din da kadan ya rufe saman qirjinta. Tana jin amna na mata tsiya "Wannan kwalliyar adda bazan iya cankan nawa hamma zai siyeta ba......kullum sai na dinga jin inama nice ke adda....inama nike da kyanki?" Harararta tayi "Zageni da kyau amna.....har kina iya cewa wai na fiki kyau?". " Da gaske nake adda....ke kam ba zaki gani ba tunda a jikinki yake" "Bazan gani ba dai saboda kin fadi abinda bashi bane.....matsamin kada lokacin walaha ya kubcemin" Ta fadi tana sanya dogon hijabinta,da wannan suka rabu amna ta shiga wanka ita kuma ta tayar da sallar. Tana shafa addu'o'inta anni ta shigo tana dubanta. "An gama breakfast.....lokacin cin yayi....ki fara yin gaba kafin amna ta gama nata laqai laqai din" . Kanta ta daga ta dubi anni,tanason gaya mata ba zata fita ba..batason sake fita kwata kwata bare taga matar,maganganunta na dazun sun mata zafi data dangantasu da kafirai,amma kome zatayi tana duba musaddiq ne. Bataso taci gaba da kusantar inda take har hakan ya jawo musu matsala,amma sai taga kaman bai dace ta gayawa anni ba zata fita ba. Abun sallar ta nade,ta rage hijabin saman sannan ta sanya tattausan bedroom slipper din tana fita a dakin. Kowa yana saman dining din a zaune kan tashi kujerar,wanda ya rage kawai ita anni sai amna. Cook din na tsaye tana serving kowa da kalar abincin da yafi sha'awa. Hankalinsa yana ga farouq wanda ke gwada masa wani sabon app da suka qirqira don manoma. Musaddiq da saddiq na nasu hiran saidai qasa qasa,sai ya zamana maamah din ce kadai zaune tana qarewa abincin alatun kallo tare da jin bacin ran kudin da aka narka tun daga hiring me girkin zuwa kudin kayan abincin. Maamah dince mutum ta farko data fara ganinta,kallo daya tak da sabreen tayi mata ta fahimci abinda ke kawo a ranta. Batason irin wannan kallon haka......saidai ta bawa kanta tabbacin indai wannan dabi'ar na tare da matar zai wahala su rabu lafiya. Ba komai zata iya dauka daga gareta ba,abinda ta dauka a baya ma ya wadatar.....yanzun tana jinta 'ya me cikakken 'yanci ne da bata qarqashin juyawar kowa. Cikin jikinsa yaji alamun wanzuwarta a wajen,ya daga kansa a natse yana duban sassan da take tahowa. Fuskarta tayi masa kyau kaman ba dazu ya ganta ba,tafiyarta me cakude da nutsuwar nan tana tsananin burgeshi,tun a wani lokaci can baya ba tare da yasan da hakan ba. Kasa dauke idanunsa yayi daga kanta,yana fatan ta dubeshi da fararen qwayar idanun nan nasa. Ta gefe yaji an taboshi,sarai yasan farouq ne don babu me masa haka saishi "Ina fata ba idanunka ne a kanta ba?" Ya soma tambayar farouq din ba tare daya dauke idonsa a kanta ba ko g waiwayo ya dubeshi ba. Can qasan zuciyarsa dariya ta taso masa ya danne,shi bama ta dalilin tabashin yake ba,abinda ya dameshi kawai kada ya kalle masa mata?. Ya manta saman table din akwai mamansa?,sam kaman baisan da wanzuwarta ba?,ita yake qoqarin ankarar dashi,don tun fitowar sabreen din maamah din ta fahimci mayataccen kallon da fuad din yake binta dashi,abinda ya sake tunzurata,ta dinga kokawa da zuciyarta da kuma fuskarta akan ta shanye amma ta gagara yin hakan. "Ni bazan kalli haram ba.....don soon halal dina na tafe......amma dai ka gyara idanunka akwai iyaye a wajen" Shaf har kuma ga Allah ya mance da maamah din a wajen,furucin farouq din ya ankarar dashi,sai kawai ya zare idonsa akan sabreen din yana dojewa kallon maamah,don shine hanya daya da zai kaucewa tuhumarta ko bacin nasa ran. "Ta yaya zamu rayu a wajen nan?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin idanun maamah a kansa saidai yaqi yarda ya kalleta ko sau daya,sai ya jawo tab din gabansa yana ci gaba da duba taswirar da suke magana akai kafin fitowarta shi da farouq. "Matsa kusa da mijinki kiyi serving nashi". Furucin anni kenan daya sauka a kunnensa bayan fitowarta daga daki tayi joining nasu a dining table din. Sosai maganar ta anni tayi masa dadi,ya murmusa can qasan ransa yana addu'ar a daren yau ta bashi matarsa. Yana jin yakai taki maqura tako ina,muddin kuma akaci gaba da tafiya a haka baisan me zai faru ba. Satar kallonsa tayi kaman yadda maamah ta saci nasu kallon. Har ta buda baki zatayi magana sai wata zuciyar ta tunasar da ita,wawa shike saurin fasa abinda ke cikinsa,sai taci gaba da juya abincin tana noticing kowa. Ganin baiko kalli sassan da take ba bayan annin tayi magana sai ya bata qwarin gwiwar miqewa,ta matsar da kujerar dake kusa dashi a hankali ta yiwa kanta wajen tsaiwa. Cikin takatsantsan take zuba masa komai,don ya tattara komai ya ajiye ne ya zuba mata idanu yana bata order zuba kaza,rage kaza,kaza kadan zaki zuba. Wannan yaso daburtata,don sau biyu yana kai hannu yana riqe serving spoon din da take zuba abincin dashi da zummar kada ta zuba masa mayonnaise da man farfesun naman kan ragon daya dan taso a sama. Ita daya sai kuma maamah suka fahimci yana sane yake hakan,don duk riqewar sai ya hada da hannunta cikin nasa. Da qyar ta samu ta kammala zuba masa din,sannan ta aje komai a gabansa. Dubawa take tana neman plate din da zata zuba nata abincin,duk da tasan zai wahala ta iya cin abin arziqi,don ya sanyata a gaba da idanunsa da suke sake zama marasa kunya marasa jin nauyin jama'a. Tun asali ta tsani yawan kallo,to amma shi din ta fahimci ya qware sosai wajen wannan dabi'ar,abinda yafi bata mamaki shine......kana iya wuceshi baisan waye kai ba.....kana iya gama sabgoginka a kusa dashi baima tantance me kakeyi ba......amma ita me yasa yake sha'awar sanya mata idanunsa?. "Zauna muyi squatting.......wannan abincin ina zan kaishi?" Ta tsinci muryarsa katsam yana fadi gami da gyara mata kujerar dake kusa dashi. Yadda wuta ta dauke mata haka wuta ta daukewa maamah,kaman kuma hadin baki wajen duka sai ya dauki shuru,sake tura kujerar yayi kusa da ita,bata da wani option sai janyota da tayi ta koma a sanyaye ta zauna a kai. Tayi zaton shikenan,zai tsaya iya haka ne,a'ah......sai daya sake janyo tashi kujerar ta zama kusa da ita sosai har gwiwoyinsu suna gogar na juna. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 95 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX *_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_* *_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_* *_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya qaruwa dasu?_* *_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_* *_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_* *lace* *kowanne nau'in shaddodi* *yadika na maza da mata* *mayafai* *lafaya* *takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana* *sarqoqi da agoguna* *under wears* *abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza* *_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA YI KINA DORA RIBARKI?_* *_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_* *Sassauqan farashi me ban mamaki* *_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine muradinmu_* _______________________________ 95 Ya jima yana tsara yadda bata abinci zai zamo qarqashin kulawarsa. Yana ankare da yadda take walagigi da cin abinci,wani abu sam da bai dameta ba,a iya zamanta a gidansa ya lura da haka,kusan duk sati sai ya leqa store din gidan don ya duba koda akwai wani abu daya qare ba kuma zata iya magana ba a qaro mata,duk sanda ta shiga yana samun kitchen din danqare da kayan masarufi alamun dai ba wani amfani akeyi dasu ba. Tsahon wahala da rayuwar da yayi zamanin quruciya me cike da rashin gata da wahala yasa yasan illar da yunwa ke dashi,wannan ya sanya sam baya wasa da lamarin ciyarwa,koda kuwa ga mutanen da ba'a qarqashinsa suke ba. Sau da dama idan ya kalleta yakan ji a ransa zatafi haka murjewa da cika muddin ta maida kai ga abinci,bayason ta zama raguwa ko ta kasa jurewa lalurarsa,shi yasa yake ganin shi yafi cancanta da kanshi ya tsaya a kanta ta wannan bangaren. A hankali taji saukar sassanyan tafin qafarsa saman qafarta. Wani abu taji ya tsarga mata har cikin kwanyarta. Ta daga idanunta a hankali ta zubesu cikin nasa,kusancin dake tsakaninsu yayi tsananin kusa da har ya sanya ta hangi wani abu cikin qwayar idanunsa. "Be serious mana....kisa hannu kici abinci ko na baki da kaina" Ya fada da sound din da babu meji sai ita. Idanun ta kawar don ya gama kashe mata jiki,ta dubi zara zaran yatunsa daya sanya cikin abincin masu farare qal din nails da lunula a qasan farcen daya qarama faratansa kyau. Batayi ko lomar farko ba amna ta fito cikin skirt itama da riga English wears,sakakku kaman na Sabreen din,hannunta dauke da wayar sabreen da sam ta manta ma da babinta. "Adda.....na saka miki ita tayi full charge.....nikam ko iya yau ne a bani aronta" Ta fada tana murmushi gami da miqa hannu ta aje mata ita saman table din a gabanta. Bata gama aje numfashin data shaqa ba idanunta suka sauka akan wayar, "super nova....diamond edition" Sunan wayar kai tsaye yazo kanta daga kallon farko da tayi mata tana sake kallonta da kyau don tabbatarwa da kanta batayi dimuwa ko kuskure ba. "Tashin hankali......kambun bala'i" Ta samu kanta tana fadi can qasan ranta a tsananin gigice. Wayar million sabain da kusan bakwai a hannun karuwar 'yar barikin?,ita kuwa tana me?,yarinyar data dauko ta zame mata tsani na samun ire iren wadannan damarmaki sai a wayi gari tana budewa kanta da kanta nata damarmarkin?,wanne irin bacci tayi haka ita mariya?,wanne irin asararren bacci tayi?,yarinyar da a iya duniyanci da qwarewa duka baifi ta lomaceta ba?,me yasa take neman zame mata qadangaren bakin tulu?. Ba zato ba tsammani naman data zuba a bakinta romonsa ya subuce mata ya wuce mata mashaqar iska,take tari ya sarqeta me matuqar qarfi ta shiga yinsa ba qaqqautawa. Musaddiq da yafi kusa da ita shi ya bata ruwan data samu tasha tarin ya lafa,sannu kawai suke mata,sai taji gaba daya iskar wajen ta mata kadan ba zata iya zaman wajen ba,don haka tsam ta miqe tana sauka a wajen hannunta saman qirjinta anni na mata sannu cikin kulawa. "Ku debi abincin ku bita dashi" Anni ta fada. A gareta sai taji kaman chance anni ta bata na matsawa daga wajen,don haka ta motsa da nufin miqewa amma ya maidata ya zaunar da hanyar danne mata qafa. Idanunta ta daga ta kalleshi,sai ya dage mata dukka girarsa biyun yana tsare gida. Dole taja bakinta tayi shuru gudun tashin tashina gaban anni "Amna diba kikai mata" Fuad din ya bawa amna umarni kai tsaye,tana kallo amna ta shirya abincin musaddiq ya dauka mata wasu suka gangara zuwa dakin annin. Koda ta shiga dakinma still numfashinta tana jin kaman baya isarta,sai ta kunna a.c ta dauki remote din ac din tana qure number qarshe,kafin ta qarasa gaban gado tana wurgi da dan kwalinta. Me yasa duk wani kafi da ta sanya aka mata baya aiki a kanta?. Ta tambayi kanta da kanta. Duk mutumin da zata daukeshi aiki cikin tafiyarta.....duk mutumin da zai ratso da kansa tsakiyar harqallarta sai ta tabbatar ta mallaki bakinsa da tunaninsa.....to amma ita me yasa ta kasa samuwa cikin tafin hannunta?. "KINYI KUSKUREN ZABOTA......AKWAI NADAMA ME YAWA......TAURARINTA BASA TABUWA" Duka maganganun bokan suka dawo mata kamar sannan yake furta mata su. Juyawa tayi tana neman zama daidai nan musaddiq dake gaba ya shigo amna na biye dashi. "Anni ce tace a kawo miki daki,idan kin huta sai kici" Cewar musaddiq. "Saboda ga mayunwaciya?.....shi zaki a jejinsa har sai an masa tayin abinci?,aisaidai abinda ya farauto yaci ya bawa sauran namun daji su qarasa abinda ya rage din" Ta fada tana makawa amna harara. Amna din bata ko daga kai ta kalleta ba,tadai qarasa ta ajiye tray din kusa da inda musaddiq ya ajiye nasa ta juya tana ficewa,sai shima ya soma bin bayanta ba tare da kowa yace komai ba. "Kai musaddiqu zo nan" Ta kirashi a fusace ganin yabi sahun amna. Qofar ya saka zai dawo ciki ta watsa masa harara "Rufen qofata shashasha mara kishin uwarsa,kaima ka soma hawa turbar dan uwanka ko?,an zagi uwarku shine zungui zungui zakabi bayanta?" Ta fada a matuqar hasale,a yau tana jin shi kansa musaddiq din ya zama silar faruwar wasu abubuwan. Yau inda ace ya bata goyon baya da nasarorin da zata samu zuwa yanzu sun haura haka. Baice komai ba ya rufe qofar ya dawo ya zauna yana dubanta. "Uban waye ya siyawa waccar karyar 'yan barikin waya me tsada har haka?" Ta fara jifansa da tambayar da tafi damunta. Fuska yadan yamutsa kadan yana maimaita sunan,hankalinsa ma gaza cafko ainihin wa take nufi. "Kai maida hankalinka.....sabreena nake nufi" Cak tunaninsa ya dakata na wucin gadi cike da mamaki. Dama addan take kira da wannan mummunan sunan?. "Hamma ne....amma ai ta cancanci abinda yafi waya ma maamah,tunda ita din matarsa ce,kuma yana da halin siya mata,uwa uba ma kuma tana da hankali da nutsuwa,ta cancanci fin haka ma" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.....kasan me kake cewa musaddiq?" Maamah ta fada cikin tsananin tashin hankali,idan har abinda kunnuwanta suke jiye mata lallai shima ya shiga tarkonta......sai taji gaba daya hankalinta yana qoqarin kubce mata. Amma da yake bariki iyawa ce,sai tayi qoqarin maida hankalinta gangar jikinta sannan ta zauna a gefansa. "Amma meye amfaninka a gurinsa musaddiq?,dan uwanka yana irin wannan almubazzaranci da dukiya amma kana ganinsa?,ba zaka saitashi ba?,ba zaka hanashi ba?,ba zaka sanarmin ba don in daidaita al'amuransa ba?,wayar million saba'in wa matarsa uwarsa bata da ta ko million talatin?". Shuru kawai yayi maganganun maamah suna masa banbarakwai. Kai tsaye zai iya cewa ta jahilci rayuwarsu da gasken gaske,kuma kome zai gaya mata ba fahimtarsu zatayi ba,don haka ya zuba mata idanu kawai yana dubanta har takai qarshen maganarta. Da kanta ta sallameshi ta koma tana zama cikin matuqar firgici da bacin rai,zuwa yanzu tana kyautata zaton BOKAnta tabbas ya gaza.....yaqin nan da bakinta zata yishi,da dukka wata power irin ta uwa da Allah ya bata. Wuni guda gaba daya bata bawa kwanyarta wani sukuni ba ko kadan,gaba daya tunaninta ta tattarashi akan yadda zata yanke wanzuwar sabreen cikin rayuwar d'anta. Zuwa sannan jikinta yana bata ci gaba da wanzuwar sabreen din bazai haifar mata da d'a me ido ba. A dukka shawarwarinta zuciyarta tafi rinjayarta ta bangare guda......ta raba auren ko da tsiya koda tsiya tsiya......da qarfi da yaji koda kowa hakan bai masa ba.....zata gwada qarfin qwanjinta da kuma adadin girma izza da nata ikon na uwa. Wannan saqar data gama yi ita ta sanya ta fita cin abincin daren ranar da wani irin izza da cikakkiyar qwarin gwiwar samun mafita. Ta samesu duka saman dining din,ta bisu da kallo daya bayan daya tana jin ciwon yadda annin ta samu daman hade kansu duka,yaran da suke nata da wadanda suke ba nata ba. Ta saki qaramin shu'umin murmushi qasan ranta tana bawa kanta tabbacin komai dab yake da qarewa.....muddin ta samu nasarar yage KASKA wato sabreen daga jikinta,sauran zata qarasashi ne da dukka qarfinta. Kujera taja ta zauna tana shaqar iska d'ai d'ai,ta sake ware idanunta tana nan sashen da fu'ad yake saidai bata ganshi ba,ta buda baki zatayi tambaya ya shigo parlor din da nutsatsen takunsa. Sanye yake da suspender da Fedora hat datayi matuqar masa kyau,tamkar wani baturen England,kunnensa maqale da earpiece amma dukka hankalinsa yana kan sabreen dake zaune gefe idanunta akan amna da wunin yau duka take more wayar sabreen din. Wani abu ya sosa masa zuciya,baisan wanne irin taurin kai gareta ba......koda wasa bai taba tunanin zata sanya qafa ta shure maganarsa ba,saidai nan kusa yayi imanin zai ladabatar da ita don duka cikin halinta shine hali guda daya da bazai iya jurarsa ba. Kaman dai dazun anni ta sanyata tayi serving nashi,ta miqe a hankali daga gefansa tana qoqarin zuba mishi soyayyar shinkafar. Hannu ya sanya ya jawo cucumber a gefansa ya tura gabanta yana fadin "Slice it" Ya fada da wani irin shanqamshi daya dan bata mamaki. Hannu ta saka ta jawota,ta dora saman plate ta soma yankawa. Sosai zuciyarta tayi zurfi a tunani,abinda ya janye hankalinta kenan har wuqar da take yanka cocumber din ta taba hannunta. "Wayyo Allah na" Ta fada tana yarfar da hannu tana jin zafi da radadin wuqar yana shigarta. "Yankewa kikayi adda?" Amna ta fada da sauri tana matsowa,abinda yaja hankalinsa kenan zuwa gareta daga kan wayar da yake latsawa. "Ya salam" Ya fadi yana jin tsigar jikinsa na tashi da jinin dake biyo hannunta,har baisan sanda wayar hannunsa ta sulale ba maamah tabi wayar da kallo. Tuni ya miqe ya kama yatsan da jinin ke fita yana kallo,har cikin jikinsa yakejin kamar shi ya yanke din. "Me yasa bakiyi a hankali ba?" Ya fada yana zube mata fararen idanunsa. Kanta ta kawar gefe tana jin kallon nasa ya aza mata nauyi da yawa,uwa uba ga maamah a wajen da batason komai ya sake hadasu. "Musaddiq......duba dakin anni ka samo mana abun wanke ciwo" Ya fadi yana janyeta daga tsakanin dining din zuwa kujerun falon ya samu waje ya zaunar da ita yanayin tsaye a kanta. Da qyar maamah ta iya lalubar numfashinta,ya zama dole a yau ta datse wannan igiyar......ya zama dole ta bata ta kuma tarwatsa koma meye yarinyar ta qulla.....kowanne irin shu'umin malami ta samu ita mariya saita nuna musu qarya suke duka ita dashi din. "Idan ya gama qaramar haukar......ka gaya masa ni uwarsa mariya ina kiransa zuwa dakina" Ta bawa musaddiq saqon don tana jin kota gefansu ba zata iya rabawa ba bare ta tsaya tayi magana da dayansu shi ko sabreen din. Kai tsaye hanyar dakinta ta nufa tana harhada hanya.....a yau koda sakin sabreen shine abu na qarshe da zata aiwatar a rayuwarta saita tabbatar ya afku kafin ranta ya fice daga gangar jikinta. *_dan dan dan dan dan dan.........masu karatu.....uhmmmmm......bakina da goro.....zamu gani kuma......shin xai tabbata ko kuwa?,sai nace ku tara dani ranar litinin in sha Allah,na gode_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 96 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX *_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_* *_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_* *_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya qaruwa dasu?_* *_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_* *_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_* *lace* *kowanne nau'in shaddodi* *yadika na maza da mata* *mayafai* *lafaya* *takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana* *sarqoqi da agoguna* *under wears* *abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza* *_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA YI KINA DORA RIBARKI?_* *_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_* *Sassauqan farashi me ban mamaki* *_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine muradinmu_* ____________________________ 96 _An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A W,sai tace: dabi'unsa alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin kalolin kyawawan dabi'u dukka haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_ A nutse ya zaunar da ita saman kujerun yana riqe da yatsar tata tamkar wadda taji wani gagarumin ciwo. Sosai idanusa suka bayyana tsananin damuwa,ya tsugunna a gabanta a hankali idanunsa na saman fuskarta. Bata yarda ta kalleshi ba,tana ji kusancin dake tsakaninsu kaman yana sake yin yawa,tana ankare da yadda maamah tabar wajen cikin wani irin yanayi da yafi kama da zallar fushi da kuma fusata,a haka musaddiq din ya dawo ya aje masa qaramin akwatin yana komawa da baya don barin wajen kaman yadda sauran suka bari da d'aya da d'aya. Dukkaninsu wata kalar soyayya suke gani a shimfide saman fuskarsa,kaman yadda idanunsa basu boye komai ba. Murmushi ya subucewa farouq din yana jin fu'ad yana sake tafiya dashi,duk da komai yasan yana yinsa ne ba cikin hayyacinsa ba saboda bugar dashi da giyar soyayya tayi.......ya sanya P_cap dinsa yana daukar key din motarsu ya saka a aljihunsa don fita dama ke garesu da daren ya soma sauka ta bayan kujerun yana barin parlor din,don shi kansa bazai iya zama yaga ya wannan love game din zai wakana ba. Wani sashe na zuciyarsa kuma cike taf da mamakin mode din maamah......fushin dake tattare da ita da saqon data barwa musaddiq. Ya jima yana wani tunani akan matar......ya dade yana wani hasashe a kanta,saidai a sanin da ya yiwa fu'ad ba zasu kasa hasaso abu guda ba. Zama yayi sosai gaban nata yana fida spirit ya tsiyaya cikin wani dan abu na silver,ya tsoma a auduga sannan ya dago yana kallonta. Still taqi bashi daman kallonta. Wani irin yanayi takeji yana bibiyar zuciyarta kaman zai narkar da ita. Yau ita sabreen yankewarta a hannu ya zama damuwar wani?,wani baqon lamari ne a wajenta da batasan ya zata fassarashi ba. "Kin shirya?" Ya tambayeta da wani irin sauti,kasa ce masa komai tayi sai ya dora audugar saman yatsan nata. "Wash" Ta fada tana qoqarin janye yatsanta gami da runtse idonta. Hanata daman hakan yayi,sai ya zubawa fuskarta idanu yana ganin yau d'aya wannan tsiwar ta tafi sai alamun rauni da radadi. "Am sorry" Ya fada can qasan maqoshinsa da wani kalan sauti daban ba irin na dazu ba,abun daya tilasta mata bude idonta ta zubesu cikin nasa. Abinda yakeso dama kenan,sosai yayi qoqarin riqe qwayar idanunta cikin nasa,ya matso da yatsar saitin bakinsa yana busa mata a hankali,abinda ya hadu da sanyin spirit din dana bakinsa ya bada wani abu daya sanya tsigar jikinta zubawa,tanaso ta janye hannun ya hanata,hakanan dole tabar masa hannun tana jin yadda jikinta duka ya mutu. "Ya daina zafin?" Ya tambayana yana dorawa kansa alhakin yankewartata. Kai ta gyada masa a hankali,burinta kawai ya gama yabar mata hannunta ya matsa daga kusa da ita din. Tsaf ya gyara,saida jinin ya tsaya da fita sannan ya kammale komai,ya qwalawa amna kira ta qaraso. "Ki dauke kayan.....ki kula da ita zanje na dawo,zamu taho tare da anni" Kai ta gyada tana tsugunna tana hade kadan gami da yiwa sabreen sannu. Kai kawai ta daga,ita bataga wani ciwo da taji wanda yakai girman sannun da take mata ba. Hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana kallonta,har sai da amna ta gaya hada komai suka wuce dakin annin. Ajiyar zuciya ta subuce masa,yana saqa abubuwa da yawa a kanta,sai sannan ya duba inda yabar farouq a zaune,baya nan,yasan kuma ya fita qilan yana jiransa cikin mota,don haka sai ya fara takawa a nutse yana barin parlor din ba tare da musaddiq daya basu space ya isar da saqon maamah ba. A mota ya samu farouq yayi d'ai d'ai suna shan hira da fanna dinsa. Kusan duka hirarsu yanzu tafi rinjaye ne akan shirye shiryen bikinsu. Baice masa komai ba ya miqa masa hannu ya karbi key din motar ya shiga ya tayar da kansa suka fara fita daga gidan gaba daya. Basuyi nisa sosai ba farouq ya kammala wayarsa,ya ajiyeta gefe yana cewa. "Sai yanzu hankalinka ya dawo kenan?" Ya fada yana kanne ido daya da sigar tsokana. Waiwayawa yayi ya balla masa harara sannan ya dauke kansa,kaman bazai tanka ba sai daga baya yace. "Ina baka shawara kaqi ji ko?.....ina gaya maka ka dauke idanunka daga kan lamarina ni da iyali na amma kaqi ji ko?". Sosai dariya ta zowa farouq,ya kuma soma yin abarsa yana cewa. "Allahu akhbar......dadin abun ma muma mun kusa aje iyalin nan muji abunda akeji......muji ya giyar soyayyar nan take bugar da mutum" Qaramun murmushi ya saki daya sake fidda kyan fuskarsa yana duban hanya. "Kota tashi bugar dakai farouq ba zaka ji abinda nakeji a kan sabrrr ba.....nata son daban yake a zuciyata......ban taba jin soyayyar abu a raina har haka ba.....bansan daga ina wannan qaqqarfar alaqar ke sake gina kanta ba duk wayewar gari zuwa faduwar rana" Yakai qarshen maganar yana furzar da numfashi a bakinsa. Ido farouq ya zuba masa.......tabbas zuwa yanzu ya tabbatar da gaske MAHAUKACIN SO fu'ad din yakewa sabreen,irin soyayyar da bai zaci zata kamashi ba har ibada. Miskilancinsa da komai nasa na dabanne.......amma zuwa yanzu soyayya tana sauyashi zuwa wani mutum na daban,idan ya zauna yana masa magana akan yadda yakejin sabreen din cikin ranshi abun yana bashi mamaki sosai......yana jin kaman ba me babban sunansa ba,wanda komai da kowa basu dameshi ba idan ka cire su da anni. "Inaji a raina da zuciyata......akwai wani abu cikin rayuwarta......akwai boyayyen abu.......i need to know farouq". "Kabi a sannu........da sannu zakasan komai din". Kai ya gyada masa. "Na sani......but am eager to know about everything about her......inaji kaman akwai sauran mutane daya kamata na hukunta bayan wadanda suke hannuna yanzu" Yayi maganar yana jin kalmar karuwa da kowannensu ya taba fada a kanta tana masa zafi har can qasan ransa. "But naji maamah tana nemanka ma...." Farouq ya fadi yana tsoron kada fu'ad din yaji amma yaqi zuwa. "Maamah kuma.......ba wanda ya fadamin" Ya furta haka kawai yaji gabansa yana faduwa. Ba kasafai kiranta ke zama alkhairi ba.....kai zaima iya generalizing cewa kiranta ba wani alkhairi ko abu me muhimmanci da d'a zai iya tsinta a cikinsa. "Musaddiq ta fadiwa.....bansan me yasa bai gaya maka ba" "Yabar parlor din ne......anyway koma meye zamu koma gidan.....saina qarasa" Ya fadi zuciyarta tana son lalubo dalilin kiran amma ya gaza. Kai kawo ta dinga yi cikin dakin nata tana tattare kowanne tashin hankali da take ganin zata sauke masa har zuwa sanda zata tursasashi guntule igiyar jarababben auren data hada. Bata taba dana sanin aikata wani abu ba irin hada aurensa da sabreen......tabbas yarinyar tana neman zame mata qadangaren bakin tulu......itace cikakken ma'anar karin maganar nan da ake cewa DAN HAKKIN DAKA RAINA SHIKE TSONE MAKA IDANU. Inda qannenta suna hannunta kawo yanzu tayi imani da yaqinin da batasan ma wanne hukunci zata sakasu su karba ba a madadin 'yar uwarsu ba. Minti daya zuwa goma sha biyar ta lissafa amma bataji shigowarsa ba,wannan ya sakata daukan wayarta ta kira musaddiq. Ba'a daga ba amma taji an turo qofar dakin nata an shigo. Koda ta waiwaya musaddiq dinne,ajiye wayar tayi tana dubansa. "Ina yayan naka?". "Na shiga daki kafin ya kammala,ina fitowa na tarar sun fita shi da BB farouq". Wani irin kallo ta watsa masa cikin fushi tana qanqance idanu. "Kasan me kayi musaddiq?!,kasan muhimmancin wannan kiran kuwa?....har yakai na baka saqo ka kasa zama ka jirayeshi ka isar masa?,kana hauka ne musaddiq!" Ta fada da wani yanayi daya bashi mamaki me kama da zata kai masa duka. A mamakance ya shanye mamakin yana yin qasa da kansa kafin yasake dubanta. "Kiyi haquri,idan ya dawo saina sanar masa,ko ina sukaje nasan ba nisa sukayi ba". " Baka da hankali.....bani da wannan lokacin,bani da Lokacin bata lokaci......wuce ka kiramin sabreen" Ta sake fada cikin daga murya tana nuna masa qofa. Mamaki ya sake kamashi ganin yadda ta birkice,yaga dai koma meye duk inda sukaje a gidan zasu dawo su kwana.....amma duka me ya kawo wannan yanayin mara dadi?. Yankewa kansa wahalar tunanin yayi ya juya a salube yana fita a dakin. Tana zaune daga gefan gadon tana duba hotunan da amna tace ta dauka a wayarta sanda saqon ya isketa. Ta daga kai tana duban musaddiq a mamakance. "Taje inji maamah" Ta sake maimaita saqon tana zubewa musaddiq dubanta. Tana juya dalilin kiranne da kuma abinda zai iya biyo baya a kiran. Bawai tana tsoron zuwa bane.....babu shakkarta ko dis cikin ranta.....bata wani tsoro ko shayin fuskantarta......kawai tana duba girman musaddiq ne da tabbas zata ce masa yaje yace mata bata zuwa. "Gani nan zuwa" Ta amsa masa tana aje wayar a gefanta sannan ta miqe tana zura qaramin Malaysian hijab dinta ta taka a hankali tana dosar qofar fita a dakin. Zuciyarta fal saqe saqe,cikin jikinta takejin koma meye ya sanya ta kira BA ALKHAIRI BANE.....koma meye kuma ta shirya fuskantarta. Tana tsaye ta zubawa qofar idanu tana dakon shigowarta,tana jin kaman tayi nawar isowar.....a haka ta murza qofar ta shigo kai tsaye ba tare data maida qofar ta kulle ba. Kallon kallo suka yiwa junansu me wani irin zurfi kafin maamah ta soma magana. "Bakisan adadin kuskure da wasan da kikayi da rayuwarki ba sabreen......bakisan gona da adadin iyakokin da kika sanya qafa kika tattaka ba......amma koma meye a yau zan yanke wannan alaqar da kike taqama dashi......yau dinnan.....kuma a nan wajen zan tabbatar miki da tsinkewar igiyoyin aurenki". Manyan idanunta ta maida ta lumshesu a nutse sannan ta budesu. "In har don wannan ne ni banga dalilin kirana da kikayi ba......wani abune da ke daya ya shafa maamah.....don Allah saboda daraja da mutuncin musaddiq da nake gani na roqeki kibarni na huta..... Allow me to rest.......tsakanina dake ba kare bin damo. Contract ne nace bazanyi ba dama ba tun yau ba,yana da wahalar gaske na yiwa rayuwata hukunci ayi challenge dina a sakani warwareshi......na bar miki contact dinki......na karbi rayuwar qannena kuma akwai abinda yayi saura?" Ta qarasa maganar tana zube mata idanunta wadanda suka fara tunasar da maamah wace ainihin sabreeen din......ta fara juyewa kuma zuwa tsohuwar sabreeen da ake dab da jana'izar halayenta. Wani irin mamaki maganganunta suka bawa maamah din,ranta ya sake dugunzuma. "Kina tunanin kinci bulus?,rayuwar yarona zaki gwadawa bariki?,a gaban idanuna zaki gwada aiki a kansa?" "Wanne yaron naki?" Ta fada cikin calmness. "Indai wannan ruhin dakike burin mallaka ne kike tunanin nayi wani abu a kai to ki hutar da kanki......banason wata hayaniya akan hakan don bani da sauran buqatarsa a rayuwata". "Yanzu kuwa zan tsinke duk wasu igiyoyi da suke tsakaninku" Ta fada a zafafe tana sungumar wayarta. Tana jin ya mata tsaho ta jirayi dawowarsa......ya mata tsaho har sai sanda ya dawo gidan ta gwada mata koda magani ko babu akwai sauran power na uwa da zata iya sakashi ya mata dukkan abinda tayi niyya. Mamakin maamah din ya sake cika sabreeen din. Tanaso ta gogewa matar haddar kanta tsaf.......tanaso ta gwada mata wani abu kansa amma inda akaci sa'a har yanzun da take tsaye bata jin jituwar halayensu shi da ita.....tabbas don a tsukin kafin ta hada karonta tabar rayuwarsu saita aje mata zazzafan darasi. Mummunan faduwa gabansa yayi sanda kiran ya shigo wayarsa,abinda zai iya cewa ya manta rabon da ya jishi. "Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis......aslih li sha'ani kullahu fala takilni ila nafsi darfata ainin" Ya motsa bakinsa a nutse ya karantata kafin ya daga wayar ya hadata da earpiece din da ya jawo ya saka a kunnensa,don ba kasafai yake magana da ita a hands free ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 97 97 _An rawaito daga manzan Allah S A W yana cewa"babu wanda zai shiga aljanna alhali akwai qwayar zarra na haqqin dan'uwansa a kansa_ _Bukhari da muslim_ "Muhammadu kana jina?" Tayi lafazin da wani irin kaushi. "Ina jinki maamah" "Indai ni uwarka ce dana haifeka.....na shayar dakai nono na har ka zama mutum.....ina umartarka a duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu......a sanda kake shigowar kuwa ina buqatar shaidar sakin matarka sabreeen......ma'ana ka datse dukka igiyoyin aurenka dake wuyanta.....muddin baka dawo ka aikata hakan ba daga yau ka dauka sunanka tsina......". Da wani azama ya latse kiran don bazai iya saurara ba. Sauti mafi muni da zai iya cewa kunnuwansa sun sake saurara kenan bayan tsahon shekaru.....sauti na biyi da ya kusa sanyashi kaman zai zare bayan sautin ALLAH YAYI MASA RASUWA ME BABBAN SUNA.....KUYI HAQURI...a ranar da ake gaya masa rasuwar mahaifinsa. Subuce masa steering motar yayi abinda ya ankarar da farouq kenan,ya sanya hannu da wani irin zafin nama ya kamoshi yana furta. "Subhanallah" Da wani irin qarfi. Karbar steering yayi yana qoqarin maida hankalinsa jikinsa amma sai yaji hakan ya gagareshi,wannan ya sakashi gangarawa gefan titi ya tsaida motar yana fita daga ciki. Numfashi yake ja sosai zuwa hunhunsa yana jin iskar da yake shaqa ta masa kadan,ko tambaya daya ya kasa amsawa farouq dake gefansa,sai daga baya ya fusgi kalmar "Mu koma gida farouq.....now" Bai musa ba ya bude masa murfin motar,ya taka da wani irin yanayi yana shiga,shima ya shiga mazaunin driver ya kunna motar yana juya kanta zuwa hanyar da suka baro. Ga mamakinta sanda ta sauke wayar a fusace saita samu idanun sabreeen a kanta da wani irin nutsuwa tana dubanta. "In don wannan abunne.....ai da basai kin tasoni ba,zaki iya aiwatarwa koda bana wajen" Ta fada tana zama saman stool din dakin tana kallonta. "Sabreeen tana zaman zamanta aka gayyatota kan abinda bai cikin tsarinta......sabreeen tace bataso.....ba zatayi ba akayi amfani da rayuka uku masu matuqar muhimmanci fiye da nata ruhin aka sakata yin abinda bata taba yiwa wani ba......ta yaya a yanzun saboda ita din ba kowan kowa bace za'a cisgeta daga inda aka dasata?" Kai ta girgiza. "Yadda aka gayyatoni ba shiri......bazan fita a sanda ban shirya ba,saboda gaba a guji taba rayuka irin na ameenatu din.....da kin kwantar da hankalinki ma zan fita.....amma fa a sanda nayi niyya,a sanda koshi wanda kika hada alaqarmu dashi din bai shirya ba......amma tunda kin zabi na fita a sanda kikeso kaman yadda kika shigo dani a sanda kikeso......inajin ya kamata shi wanda akayi komai dominshi yasan yadda aka qulla abun aka kuma warwareshi.....don nagaya yanamin wani gani gani yana kuma kallona a matsayin makwadaiciyar dukiyarsa......bayan kuma ata nan gefansa akwai uwarmu gaba daya" Tayi maganar fuskarta da murmushi kaman me fadin wasu kalmomi masu dadi. Abinda kenan yake sake qule maamah......yadda qaramar alhakin ke zama tana yaba mata zance duk yadda taga dama. Iya wannan kadai ya isheta hujjar qwace suna da license na zama surukarta. Suruka take nema irin wadda zata juyata kaman d'iyar data haifa,wadda zata bita kaman yadda raqumi yake biyar akalarsa ba saba hanya. "Kina tunanin ke dinnan qaramar alhaki kina da wani hujja dalilo ko qwarin gwiwar fadan magana akaina d'ana ya yarda?". "Aah" Ta fada idonta akan wayarta tana dannawa wadda ke sake tsokane idanun maamah. "Ni bance dole ya yarda ba....amma dai qila wannan zai taimaka" Ta qarasa maganar tana kunna wani sauti wanda sai data waiwayo dashi maamah ta fahimci video ne. Tayi matuqar kaduwa,ta kuma yi mummunar razana da yadda ta gansu tarwai ita da Hajj harira......rana ta farko da suka fara takawa gidansu dakinsu suna gabatar mata da contract din aurenta da fu'ad. Komai ya fita kaman yanzu ake dauka,da sautin muryarsu da komai. Boyayyen murmushi ta saki ganin yadda abun ya daki.maamah da wani.irin razanannen yanayi. Boyayyar CCTV camera din data saka a parlor din kenan ba tare da sanin kowa ba. Zama da JIB ya qareta abubuwa da yawa,tun sanda tayi noticing canzawar huda awancan lokacin da Naseer yaso bata ta,ta yanke ta sakata,wanda ita ta taimaka mata taga duk wani motsi na huda.....ya kuma sake qarfafa mata zargin da shi yayi sila ta gano komai. "Wannan kawai zan nuna masa don yasan cewa bani na kawo kaina rayuwarsa.......ba sonshi nake ba.......ban taba kuma sonsa ba.....banajin kuma zan soshi din.......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......" Maganarta ta tsaya a nan sanda lallausan qamshinsa ya marabci hancinta.....kaman giftawar walqiya kuma sai gashi a wanze cikin dakin a wani birkitaccen yanayi. Wani irin kallo da yake saukar mata shi ya sanyata zare idanunta daga kanshi. Wani irin birkitaccen kallo yake mata zuciyarsa na wani mahaukacin bugawa da kalamanta na qarshe da kunnuwansa sukayi katarin ji "Ba sonshi nake ba......ban taba kuma sonsa ba,bana jin kuma zan soshi din......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......". Inda tasan girma da nauyin da kalaman sukayiwa qirjinsa tabbas ba zata fadesu ba. Janye nasa idanun shima yayi daga kanta da suke sake sauya launi saboda bacin ran da yakeji cikin ransa. Yayin da idanun maamah suke zube a kansa ita kuma.....zuciyarta na quna tare da jaddada mata baqar mallaka sabreen din tayi masa da yake kasa sukuni a duk sanda take waje......yake kasa aza idanunsa akan kowacce halitta idan ba ita ba. Da confidence dinsa ya shiga cikin dakin,yana jin cewa idanma tazo ta gayawa maamah ne bata sonshi don ta sanya su rabu.....ba shakka ta dauko aikin da bazata iya qareshi ba.....a yanxu a kuma yadda yake jinta a kusa da kowacce jijiya ta jikinsa.....ko mutuwa bayajin xaya lamuncewa ta rabashi da ita. "Gani" Ya fada yana dosana gefan sofa din dakin. Idanu maamah ta zuba masa tana jin wani irin abu yana birkitata. Ga qoshi ga kwanan yunwa,gashi a gabanta cikin qasa da mintunan data nema ya isketa......gashi a gabanta cikin neman umarninta ya kuma cikashi.....rijiya ta bada ruwa guga ya hana. Ko sau daya koda a cikin mafarkanta na zahiri da na badini.......bata taba tunanin sabreen din nada kaifin basirar ajiye kowacce hujja data shafi rayuwarta ba.....tunanin hana faruwar hakan ya sanyata bata waya ta musamman da zasu dinga communicating......wadda bata nadar komai....komai din kuma idan ya nadu ma zai goge kanshi da kanshi ne automatically. "Tashi kaje kawai.......zan sake nemanka a lokacin da ya dace" Ta fada tana zubewa sabreen wani kallo dake nuna zallar gargadi da yiwuwar afkuwar komai a karonsu na gaba. Sam sam sai yaji hankalinsa ya gaza kama maganar maamah din.......kamar ba ita bace ta kirashi ga waya mintuna kadan da suka shude ba cikin wani irin zazzafan yanayi?,to meye ya sauyata da sauri haka?. Waiwayawa yayi kai tsaye yana duban sabreen,saidai idanunta kaf baya kansu yana kan wayar hannunta. Sake maido dubansa yayi ga maamah,har yanzu shi take kallo......saidai kuma da alama kalaman bakinta na sallamarsa ba sune a qasan zuciyarta ba. "Kaje nace" Ta sake maimaita masa tana fargabar kada yaci gaba da zama ta kunna video din a gabansa. Kaman bazai miqe ba sai kuma ya miqe din,ya sake duban sabreen da still tayi kaman bata wajen kaman kuma ba kowa cikin dakin. Maganganunta suka dinga tsikarar zuciyarsa da wani irin ciwo. Girman qin da take masa har yakai ta zauna ta fayyacewa duniya?,ta fayyacewa kowa?,shi kam idan bai dasawa sabreen jarababben sonshi ba rako maza yayi duniya kenan,da wannan zafin da fushin ya fice a dakin. Miqewa tayi sanda ta tabbatar ya fita,tadan kalli maamah din kadan,kaman zatayi magana sai kuma ta shanyeta tana tuna cewa ba sa'arta bace. "Karki saki jiki kiyi farinciki da tsammanin kin kubuta ko kinci nasara akan mariya.....a'ah....wasa farin girki wannan,hausawa sukace somin tabi ne wannan hatsin gara a buta". Dan waiwayowa tayi,sai ta sake mata murmushi kawai tana sanya qafarta waje. Bawai kaman jiran fitowarta yake ba......dama jiran fitowartata yake......ba zato ba tsammani taji ya cafke hannunta,bai kuma tsaya sauraren komai ba ya soma tafiya da ita zuwa bakin qofa. "Ina zaka kaini?.....ina zamuje?.....ka sakarmin hannuna......wannan bai kamata ba,ni ba inda zanje......ka sakeni......wai ina zamuje?" Ta sake tambayarsa da qarfi wanda ko sau daya bai waiwayo ya kalleta ba sai daya tabbatar ya sanyata cikin motar ya kwashe qafafunta ya maida ciki ya rufe ya kuma zagayo ya zauna gefanta. Wani irin zama da ya bata daman jin irin hucin dake fita daga can cikin zuciyarsa har saman fuskarsa. Ya tsareta da kallo da idanunsa da sukayi kaman kwanciyar jini daga qasansu saboda zallar bacin rai.....farar fatar fuskarsa itama ta canza launi zuwa reddish kaman wanda aka dinga yamutsa fuskar da maruka. "Zan kaiki na killace......a muhallin da ba wanda ya isa ya ganki......zan kaiki inda zamu rayu daga ni sai ke.....zan kaiki inda ba zaki sake ganin kowa ba sai muhammad fu'ad.....zan kaiki wajen da soyayyar fu'ad ce kadai 'yancinki da zaki samu" Yayi maganar yana sauke don rage radadin da zuciyarsa ke masa. Kafin tace wani abu ta fahimci motar tasu ta fara motsawa tana fita daga gidan. Hankalinta ya dan tashi,saboda sanin halinsa da tayi,to amma sai tabi shawarar zuciyarta ta hanyar dakewa kaman abinda ya fada din bazai tabbata ba ko bai dameta ba. Tana iya jin wata irin birkitacciyar ajiyar zuciya da yake saukewa,har tsakiyar kwanyarta takejin fitar ajiyar zuciyar wanda ba zata ce ga dalili ba. Ya maida bayansa yayi relaxing sosai jikin kujerar yana sauke numfashi kaman wanda yaci kuka. A hankali taji ya laluba tafin hannunta ya sanya nashi. Mannewa sukayi guri guda abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,tana iya jin yadda dumin tafin hannunsa yake bin kowacce jijiya ta jikinta dake aika saqo,tayi yunqurin zame hannun amma ya hanata,saima ya sanya hannunsa guda daya ya tayar da motar,cikin qwarewa yake sarrafa steering din da hannu daya suna ficewa daga gidan. Batace masa komai ba.....amma jikinta ya soma sanyi da ganin hanyar da suka dauka. Basu taba bin hanyar ba duk a fice ficensu. Wani irin guri ne da zata iya cewa tsahon rayuwarta bata taba ganin gurin makamancinsa ba.....wani tsuburi na musamman dake kewaye da ruwa wanda kafin su qarasa dab da wajen ya ajiye motarsa,tun bai fito ba ma'aikatan gurin suka qaraso. Idanunta ta daga tana duban sunan dake maqale a signboard CONRAD RANGALI ISLAND RESORT. Sanda take dawo da idanunta ya kammala kashe motar ya zare belt din jikinsa,tattausan tafin hannunsa ya miqa mata yana tsareta da fararen idanunsa,a hankali ta kalli hannun sannan ta kalli fararen qwayar idanunsa da suka fara komawa daidai a lokacin. Yayi wani irin laushi gaba dayansa,tun daga qwayar idanunsa zuwa gangar jikinsa zaka karanci hakan. "Banaso.....karkimin musu.....na gaji.....na gaji da jin musu,taurin kai,saba maganata.....i beg you koda na awanni kadanne kawai kibi umarnina,koda na iya yau ne" Ya fada da wani sauti me matuqar laushi. Haka kawai taji wani abu me kama da tausayi yanason saukar mata.......duk wani izza da qasaita nashi duka ya zuge tsakanin tafiyarsu zuwa yanzu. Gefe guda halaye da dabi'un matar da take kiran kanta a matsayin mahaifiyarsa yana dawo mata. Wanne irin barazana wannan uwa keyi da rayuwar d'anta?, ta tambayi kanta. Tunawa take da rayuwar da tayi a gidansu,tsakanin kawunta da kishiyoyin mahaifiyarta,dabi'unsu da mu'amalarsu a kanta gaba daya wasu iri ne da basu da dadin ji ballantana gani.....ta fuskanci rashin nutsuwa da barazana me tarin yawa......yau inaga ace mahaifiya da kanta keyi maka haka?. Tana tsaka da wannan tunanin ta tsinceshi saman kanta,har ya zagayo ya bude mata qofar side dinta,bai gaji ba ya sake saka hannunsa ya kama tafin hannunta yana tayata fita a motar. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 98 98 _Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremu🙏🏽)_ _bukhair da muslim_ Sosai ya riqeta yana zagayo da hannunsa zuwa qugunta,sai ta kasa janyewa kaman yadda ta saba saboda idanun mutane,zagaye da ma'aikatan suka taka har zuwa inda wani boat ke ajiye. Kadan kadan zuciyarta ke bugawa saboda shimfidadden ruwan dake zagaye da wajen fari qal da yake bada wani color me kama da sky blue. "Ina zamuje saman ruwa kuma?" Ta tambayi kanta tana jin tsoro yana shigarta. Tunda take a rayuwarta wanna shine karo na farko da zata taba shiga jirgin ruwa,duk da wannan din wani irin jirgi ne da zai nuna maka tsadar da yake dashi,tsarinsa daban yake da sauran jiragen da take gani,yana da wata fargajiya da kujerun zama masu daukan hankali. Bata fahimci maganar da suke ba don cikin harshen Dhivehi suke magana yaren 'yan qasar. Can qasan ranta tana mamakin yadda ya iya harshen haka,a zamanta dashi taji yana yaruka kala kala da batasan yadda ya iyasu ba. Hannunta ya sanya cikin nasa suka fara yin gaba don shiga boats din,saita tsaya ba tare data motsa qafarta ba tana matse yatsunsa cikin nata ba tare da tasan tayi hakan ba. Zuciyarta ke bugawa kadan kadan cikin tsoron shiga boats din,ta yaya zasuyi tafiya saman ruwa?,ruwan ma shimfidadde irin wannan?. Kallo daya yayi mata ya karanci tsoron da yake idanunta,yayi qasa qasa da muryarsa duk da bajinsu za'ayi ba yace "You're safe.......idan kina tare dani you are safe......ki shirya zamu koma rayuwa cikin ruwa,har sai sanda kika koyi soyayyar muhammad jadda.....i can't lose you" Yana kaiwa nan ya sake sanyata a jikinsa sosai yana takawa da ita saman katakon da zai qarasa dasu cikin jirgin. Dole qanwar naqi tsoron ya ladabtar da ita tayi zaune cikin jikinsa,har zuwa sanda suka qarasa shiga,sai a sannan taga irin qawatar da aka yiwa boats din sosai,banda saman ruwan suke da bazata yarda cikinsa suke ba. Bai barta ba sai daya zaunar da ita saman qawatattun kujerun dake a wajen,ya samu wadda ke fuskantar tata ya zauna yana goye hannayensa a qirjinsa idanunshi a kanta. Har yanzun idan ka masa zuzzurfan kallo zaka karanci ranshi yana bace ne,yana kawai qoqarin dannewa ne. Tana jin nauyin idanunsa a kanta sosai,inda zai mata alfarma da ya rage nauyinsu a kanta. Ma'aikacin jirgin ne ya qaraso yana miqa masa wasu qananun blanket guda biyu masu taushi,ya sanya hannu ya karba ya ajiye a gabansa daidai sanda jirgin ya fara motsawa yana harbawa cikin ruwan. Ido ta runtse tana curewa waje daya,'ya'yan hanjinta suna kaduwa tana jin kaman zata nutse ne a ruwan,sanda jirgin ya tashi sosai ya fara keta ruwan da gudu sai taji kaman kanta zai juye,wannan ya sanyata bude qafafunta ta cusa kanta a ciki zuciyarta na wani irin bugu. Batasan sanda ya iso gabanta ba,ta daiji lausasan hannayensa saman tafin qafarta. Ta dago idanunta a hankali tana kallonsa,sai ya miqe ya ware blanket din yana lulluba mata,sannan ya koma ya tsugunna a gabanta yana lalubar tafin hannunta. Bata hanashi ba,don tana buqatar wani a kusa da ita,yadda ruwan keyi takejin kaman zasu fada ne,sai ta maida idanunta ta kulle gam. Tana jin yadda yake murza tafin hannun nata daga gefe,tamkar me dauke da wani sihiri a nasa a hannun......a hankali sai taji bugun zuciyarta yana daidaita,tsoronta yana raguwa sosai. Tafiyar mintuna idanunta suka fara hangen wani gini tsakiyar ruwan,mamaki ya cikata har sai data ware idanunta sosai tana duban ginin. Qawataccen gini ne da yake a tsakiyar ruwan,tako ina ruwa ne ba wani qasa a wajen ko wani tsandauri kusa da wajen bare tace ga yadda akayi dabara aka dora ginin. "The Muraka hotel" Ta fadi sunan data gani an rubuta manya manya sama. "Hotel?" Ta maimaita sunan qasan ranta,wanne irin hotel ne haka tsakiyar ruwa?,ta sake tambayar kanta a mamakance. Kada dai yace mata nan zasu zauna?,cikin ruwan kaman wasu 'ya'yan aljanu?. A sanyaye ta aza idanunta a kan fuskarsa sanda jirgin ke tsaiwa daidai wata hanya me kama da gada da ta tabbatar ta nan ne zasu qarasa ainihin ginin hotel din. Girarsa duka biyun ya dage mata da wannan miskilar fuskar nashi,sannan ya miqe a nutse yana zare hannunsa daga nata,ya miqa hannun ya cire mata blanket din sannan ya sake kamata ta miqe tsaye suna fita a boat din yana magana da ma'aikatan. Wata qaramar mota ce me qafa uku me budadden sama ta tsaya a gabansu,ya kama mata hannu tana taka cikin motar sannan shima yabi bayanta,a hankali driver din ya gaidashi ya amsa masa da yarensu sannan ya tashi motar suka fara ratsa gadar. Tashin hankali.....ta fada a ranta tana ware idanu tana kallon rayuwa a cikin ruwa. Tun basu qarasa ba ta dinga ganin mutane jifa jifa tsakanin hanyar zuwa hotel din suna al'amuransu hankali kwance. Ita kallon ruwanma kawai dake gefe da gefen gadan ta qasansu daga mata hankali yake,a tsorace take har batasan sanda ta cure a kafadunsa ba. Boyayyen murmushi ya saki batare daya kalleta ba bare ta gane hakan. Yana buqatar wannan tsoronne dama a tattare da ita,samuwar tsoron shine zai sake kusantata dashi......samuwar tsoron shine zai tattaro masa dukka rayuwarta a hannunsa,a inda ba anni ba amna.....ba farouq ba musaddiq ba kuma saddiq ballantana tayi tunanin zata janye jikinta dashi,zata rayu dashi shi kadai......daga shi sai ita a duniyar da ba wanda ya sansu,a duniyar da bazata iya guduwa ko ina ba. Gajeriyar tafiya ce ta kaisu bakin qofar shiga hotel din. Luxury iya luxury da ko bakasan abinda duniya ke ciki ba idanunka zasu gaya maka. Wani irin gini na alfarma da zata iya cewa bata tsammaci samunsa a haka ba. Wayarta dake hannunta tadan kada,ta bude tafin hannunta tana kallon fuskar wayar. "Welcome to the muraka,the first world's under water villa" Idanunta ta janye daga kan wayar tana maidawa fuskarsa,sai ta kasa cewa komai illa tsoro da take sake jin yana mamayarta. Binsa kawai takeyi har zuwa reception,inda suka karbi komai ya kuma sake riqe hannunta suna takawa a hankali zuwa dakinsu. Ta kasa tsaida idanunta guri daya,mamakinta yanata qaruwa yadda take taka wajen tamkar a gida. Tana taka tsandauri alhalin tasan tsakiyar ruwa suke tsundum,ta sake riqe yatsunsa da kyau ko tsoron da takeji zai ragu. Sanda yake bude qofan living room din dake dauke da bedroom dinsa da toilet harda kitchen mutuwar tsaye tayi. Glass doors ne tako ina da zai baka daman ganin kowacce fuska ta shimfidadden ruwan da suke kai. Luxury suite ne dake da bedroom biyu living room biyu duk da daya take gani a yanzun. Baice mata komai ba yana riqe da hannunta har suka shiga bedroom din. Zare hannunsa yayi daga nata,yaja baya yana zube hannunsa a aljihun wandonsa yana dubanta. "Ga first bedroom.....muje kiga dayan,saiki zabi wanne zaki zauna a ciki" Yayi maganar idanunsa suna lumshewa yana jin wani abu ya soma fusgarsa a kanta. Fararen idanunta ta aza masa,ita sam batasan ma yadda zata kwana cikin wannan ruwan ba,hannunsa ya miqa ya sake riqo yatsunta yana fita a dakin. Daga wani sashen daban suka iske stairs da sukayi qasa,ya ware yatsunsa yana zurasu cikin nata ya jawota jikinsa sosai sannan suka fara takawa zuwa qasan. Idanunta ta fidda sosai zuciyarta na harbawa da mugun gudu ganin suna nutsewa qasan ruwa. Tsoronta ya sake ninkuwa tana kallon yadda sukeyin qasa ta bangon glass da ginin yake dashi. Jikinta duka ya dauki rawa ganin yadda halittun ruwa ke linqaya a cikinsa suna wucewa abinsu hankali kwance ta bangon glass din. "Hamm......" Ta motsa bakinta don kiran sunansa amma saita kasa. Ya jita sarai,kuma yana jin tasirin tsoro sosai a muryarta da jikinta duk da bai waiwaya ya kalleta ba. Idonsa ya lumshe yana son sake jin sunan HAMMA a bakinta wanda sau daya tak ya taba ji ta ambata a wancan ranar. Ba inda zai kawota ya boyeta yadda yake so......ya dora mata karatun da yakeso irin nan din. A nan ne kawai yake da tabbacin cire wannan tsiwar tata gaba daya ba tare da yayita cusa kansa zuwa gareta ba. Yaji dadin samun information din tana da tsoro wasu lokutan,wannan ya sake bashi qwarin gwiwar ci gaba da zama a Maldives ko don saboda ita. "Nidai.....wannan gurin" Ta sake fada muryarta na sake tsinkewa saboda hango wani babban kifi yana matsowa kusa da glass din. "Wayyo Allah na" Ta fada da qarfi tana ruqunqumeshi cikin jikinta da wani irin tsatsauran riqo daya sakashi sakin wata qatuwar ajiyar zuciya. Wani irin riqo ta masa da ya tabbatar inda a hayyacinta take ba zata masa shi ba,ya ware idonsa yana duban abinda ya tsoratata. Wasu irin kifaye ne guda biyu masu girma da suka matso dab dasu kaman masu sansanasu,sai suka juya abinsu suna wucewa gami da kada jelarsu. Qaramin murmushi ya subuce masa,inda wannan ne a the Muraka ya fara bata tsoro to tabbas wata babban dama ce a wajensa,zasu kuma qulla kyakkyawar abota da tsoro din. Duk da sun tafi amma bai tadata a jikinsa ba,don yadda ta maqale shi din shi yayi masa,sai yaji wani sashe na nauyi da bacin ran da yakeji yana kwaranyewa. "Is okay.....sun wuce fa,ba abinda zasuyi miki..... You're safe na gaya miki" Ya fada cikin sauti na rada dab da kunnuwanta,abinda ya sanya tsigar jikinta tayi wani irin yarfawa kenan. Fuskarta ta daga a narke tana dubansa,duban da yayi kusanci da yawa a tsakaninsu har suna musayar numfashin juna,tadan taka zata ja da baya ya riqo bayanta ta hanyar tarota da tafin hannunsa yana sakar mata wani irin abu cikin idanun nasa. "Stay close to me" Ya fada can qasan maqoshinsa yana qoqarin danne feeling da yakeji yana taso masa a kanta. Yana gayawa kansa ba yanzu ba......ba yau ba. Bata taba jin kasala irin na yanzu ba,saita sauke dubanta daga kansa saidai fuskarta da yanayinta gaba daya ya fidda wani quruciya tata sosai,har ya fara contemplating akan ainihin shekarunta. "Tsoro nakeji......ka maidani wajen anni" Ta fada da wata shagwababbiyar murya da batasan ta yita ba. Wani qawataccen murmushi ya saki,ya saketa yaja hannunta zuwa wata lafiyyar sofa dake wani corner na dakin zai zaunar da ita,saidai suna zuwa dab da wajen wasu gungun kifaye suna iso zasu wuce. A zabure ta taka tana sake fadawa jikinsa ta riqeshi da kyau,muryarta da zuciyarta suna karyewa. "Ka gani ko?" Ta fada kaman zata saki kuka. A wannan karon duk yadda yake danne dariyarsa sai da ta fito da wani irin nutsatsen sauti. Riqet yayi da kyau yana qarasawa da ita gefan gadon ya zaunar da ita,ya koma gabanta ya tsugunna a nutse saman qafafunsa. Kanta ta daga sama,still ruwa ne sosai a saman nasu da wasu halittun ruwan suna rayuwa abinsu hankalinsu kwance,fuskarta a kwabe a kuma narke ta kalkeshi,saita nuna gurin da yatsa tana tabe baki kaman qaramin yaro zai saki kuka. Gaba daya yanayinta yaji ya tashi kansa.....dukka quruciyarta da tsoronta sun gama bayyana,abinda bai taba gani ba tattare da ita,hakan ya bashi wani irin farinciki da sai daya sanya fuskarsa cikin tafin hannunta yana boye dariyarsa. Baisan haka muraka zai bashi farinciki ba......tabbas da ya jima da kawosu gurin,wannan tsoron yakeson gani cikin idanunta. Daidaita mode dinsa yayi yana kallonta. "Meet my gaze" Ya furta da natsatsiyar muryarsa yana cire wasa a yanayinsa. Kaman yadda ya buqata haka ta tattara hankalinta dama idanunta cikin nasa. Bata taba zaton zata iya dogon kallo cikin qwayar idanunsa ba sai yau. Batasan me ya riqeta ba har ta iya kallonsa na tsahon wannan lokacin,saidai tsakanin mintunan taga abubuwa masu yawa cikin idanun nasa......taga kuma abubuwa masu yawa. Wani irin kyawawan idanu da yau ta fara karantar hakan,tsahon wasu mintuna suna yiwa juna kallon qurilla wanda dukkaninsu da yanayin daya haifarwa da kowa,hannunta ya sake riqewa sosai yana murza a nutse "You're under my watch....I'll shield you.....i promise to keep you safe.....take my word for it" Ya fada yana bata tabbaci. "Yaushe zamu koma gida?" Ta fada cikin sanyi da wannan tsoron dake gilmawa cikin idanunta. Dan qaramin murmushi ya sake mata wanda ya sanyata qifta idanunta sau biyu akan fuskarsa. "Is in your hand......." Idanunta ta fidda waje tana waresu a kanshi "Ni kuma?" Ta tambaya cikin rashin wayo. Kafadarsa ya dage mata "Yes......" Ya fadi tare da ajiyar zuciya,muryarsa ta sake zama low sosai,yayi qasa d qwayar idanunsa yana kallonta. "I crave love and affection in my life,i need someone to talk to,someone who cares......ina da anni ina dasu musaddiq,amma inajin still akwai wani ruhi da nake da buqata daban bayansu cikin rayuwata......Can you fill that role?" Ya jefa mata tambayar yana sake tsareta da kallo. Karon farko da takejin wani abu daban a kanshi. Yana dasu anni amma yana kewar wani abu.....me yasa dukka zancansa babu maamah a ciki?,me yasa duka wannan qaunar da shaquwa da take gani tsakaninsu da maamah bata ganinsa tsakaninsu dasu?. "Don't stress yourself" Ya fada yana miqewa gami da zame hannunta cikin nasa. "Which apartment you prepare?,up or down?" Ya tambayeta yana goye hannunsa a qirji yana son ci gaba da ganin drama dinnan tata. Idanunta ta dan ware a narke tana dubansa kaman ruwan hawaye na kwanciya🥹,tana tunanin wanne gurinne zaifi mata,ta zauna a qasan ruwa da kifi ya hallakata?,ko ta zauna a saman shima still ruwan dake kadawa yayita kawo mata farmaki?. Qasa cikin ruwa take tsundum da take ganin kaman glasses din da suka zama katangun dakin kaman zasu tsage ruwan ya shigo.....shi kuma saman nisan ruwan da suke ciki kawai ya isheta firgici. "Is alright......ki zauna a qasan,zan koma saman" Ya fada yana fara takawa. Ai batasan sanda ta hantsilo ta biyoshi a baya ba,ja yayi ya tsaya yana danne dariyarsa. "Eheennn" Ya fada yana dubanta da salon tambaya. Kasan masa magana tayi,sai qasa da tayi da kanta tana murza yatsunta,haka kawai yau takejin nauyinsa,ita magana ta Allah daga saman har qasan ba inda zata yarda ta zauna ita daya,gani take kaman zata rasa rayuwarta ne. To amma ta yaya zata gaya masa hakan?,fada masa hakan ma ai daidai yake da ce masa su rayu daki daya,idan kuwa zasu zauna daki daya kenan yana nufin suyi sharing komai?. "We can room mate?" Ya tambayeta a tausashe yana lalubar qwayar idanunta. Tambayan ta mata tsauri,a zahirin gaskiya a yanzun ba wata mafitan da tafi wannan,don dai ita ba zata bari ta zauna ita kadai ba......amma kuma tana juya yadda hakan zai kasance. "Let's room together" Ya fada yana wucewa zuwa matakalun da zasu maidashi sama. Wannan karon sai da yayi da gasken gaske sannan ya hana dariyarsa fitowa,don duk inda ya aje qafarsa nan take jefawa,bata yarda ma ya koma saman ya barta a dakin can qasan ruwan ba. Tana tsaye ya dauki wani luggage me kyau da batasan sanda aka kawoshi ba da wani kwali na daban. "Ranar farko zai zama a dakin sama.....rana na biyu underwater nakeso nayi bacci......hakan yayi?" Ya fada yana daga gira daya gami d qarewa tsoronta kallo a fakaice. Kai kawai ta gyada don nata da wani sauran zabi,tsoron da takeji ma ya isheta. "Okay.....stay here.....zan duba wani abu zan dawo yanzu" Ya fada yana bata tabbaci da idanunsa. Kai ta daga masa,tana kallo ya bude qofan ya ratsa living room ya fice. A sanyaye ta sauke idanunta ga ruwan da take kallo gashi gata,wai a haka cikin daki kake kaman ka sanya hannu ka kamoshi. Kujerar da aka aje gaban qofar glass din ta matsa ta zauna tana sake ganin kusancinta da ruwan. "Subhana man kalaqal kalqa wa'ahsahum adad" Ta fada a ranta tana sake jin girman zatin Allah yana kamata. Ba shakka da yawanmu 'yan adam bamusan waye Allah ba,kawai muna fadinsa ne a bakunanmu ba tare da halasto girmansa a zukatanmu ba. Iya halittar ruwan ya ishi bayinsa sake sallamawa lamarinsa. Ta sauke numfashi tana maida kallonta cikin dakin,idanunta ya sauka kan littafin dake ajiye saman dan qaramin table din dake gabanta. Hannu ta miqa ta dauka,ta fara budewa,cikakken bayani ne akan gurin,taswirar dakin da suka kama inda toilet da restaurant da komai yake. Idanunta ya tsaya cak kan farashin wajen,adadin kudin da zaka biya duk kwana daya tal,dollar dubu hamsin kimanin million saba'in da wani abu. Idanu ta fidda waje mamaki yana kasheta,zuciyarta ta kasa gasgata farashin,ko a mafarkinta bata taba tunanin akwai me kudin da zai iya wannan ba daga qasarmu,amma sai take ganin kaman yayi yawa kudaden.....kaman yayi almubazzaranci,sai wani sashe na zuciyarta ke tuna mata hirar da amna ke yawan mata na hamma din. Tabbas ya isa ne yakai.....kudinsa kuma ya zarta yadda take kallonsa,mutumin dake sarrafa diamond da gold ya fitar qasashen qetare......gold ko diamond din kamfaninsa kaman abinci yake a wajensu saboda farinjininsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 99 99 _Daga abdullahi dan mas'ud R A yace:manzan Allah S A W yace "BAZAI SHIGA ALJANNA BA,DUK WANDA AKWAI KWATANKWACIN KWAYAR ZARRA(MAFI QANQANTAR ABU) NA GIRMAN KAI A ZUCIYARSA_ _muslim ya rawaito_ Ajiyar zuciya ta sauke tana rufe littafin,yayin da a can qasan zuciyarta taji ta raina matsayinta,wacece ita da har zama zai hadasu da mutum me daraja irin muhammad jadda din?,mutumin da iya yau kawai tasan ya tserewa matakin rayuwa da ita.......ya mata nisa fau fau......ya kuma tsere mata irin da mugun nisan tazarar nan.. "Amma me yasa duk da wannan tarin matsayin nasa da zai iya auren kowanne nau'in mace a duniya.....duk da wannan dukiyar......kyau da ilimi dake gareshi ya nacewa rayuwarsa sai ni?,me yasa ya kasa rabuwa dani yaje yayi rayuwarsa?" Tambayoyin da suka zo kanta kenan. Ta kalli wayarta dake ajiye gefe,ada tana mamakin yawan kudin wayar,sai gashi a nan din kowacce rana zasu kashe kimanin kudin wayar a kwanan gurin kawai,banda personal cook da taga suna dashi da komai da komai da za'a zo kullum a maka personally. "Allah me iko" Ta fada bayan data kunna wayarta ta tadda WiFi da cikakken network na wayar,ta maida dubanta kan ruwan,kaman ba'a kan ruwa suke ba?. Daidai nan ya tura qofan ya sake shigowa,tadan zabura kadan saboda da gaske a tsorace take. Murmushi ya saki dan siriri daya qara masa wani kwarjini da kyau. "I'll safeguard you....indai kina tare da Jadda kisa a ranki baki da sauran tsoro ko damuwa" Ya fada a tausashe sanda yake qarasowa dakin da wani kyakkyawan tray a hannunsa ya ajiye saman table din gabanta. Haka kawai taji kalamansa suna samun matsugunni a zuciyarta,su huda suka fado mata......indai har hakan ya tabbata hakan na nufin qannenta zasu iya rayuwa da ita?,qannenta zasu samu kowanne kalan rayuwa da take mafarki?" Ta tambayi kanta idanunta zube kan price na wajen ba tare da tasan nan din ta bude ba. To amma meye tabbacin da take dashi a kansa?,kada fa ta rudi kanta........yanzun nan ta sake fahimtar wanne irin tarin dukiya da girman matsayi da yake dashi.......tasan cewa kwata kwata babu hadi tsakaninsu......zaren ba kalar yadin bane......bata da wani assurance. Baya kadan yaja a hankali,ya sauke gwiwoyinsa qasa yana tsugunnawa a gabanta,hannu ya sanya yana janye littafin yana sauke idanunsa a wajen,saita bishi da kallo haka kawai tanajin kaman yayi almubazzaranci......kaman ya kamata tace wani abu,kaman ya dace ta masa gyara. "Wannan.......gurin nan kaman yayi tsada da yawa......muna da wajen da zamu kwana fa?". A nutse ya daga idanun nasa yana ajesu a fuskarta,wani abu me kama da murmushi shimfide saman fuskartasa,har tsakiyar zuciyarsa yana jin dadin kusanta kanshi da ita,koda kuwa na qananun sakanni ne sai yaji yana samun nutsuwa. "Duk tsadarshi baikai ki tsada ba.......You're priceless,no cost is to high......I'd spend my last dime on you,you're worth every penny" Ya qarasa fadi yana duban idanunta......yanajin inama zata bashi dama ya shige jikinta.....ya dora kansa saman kafadarta?,ya sauke ajiyar zuciyar da zata kawo masa sassauci da irin yanayin da yakeji a zuciya da gangar jikinsa". Karon farko da itama ta zuba masa idanu......tanaso ta tabbatar da gaskiyar abinda ya fada ko kuma akasinta......tanaso ta tabbatar har zuciyarsa abinda ya fara ko wani sabon salon yaudarar ne?. Kasa jurar kallonsa tayi kama kullum,ta dauke kanta ta maida still saman ruwan,tana ganin yadda duhun dare ya cakudu da hasken fitilun da aka wadata duka resort din dashi,jifa jifa halittun kifaye nau'i daban daban suna kai kawo. Lissafin kudin take cikin ranta,inda zai rabawa marayu irinta wanne dadi zasuji,saita kasa shuru still,ta buda bakinta a hankali ba tare data kalleshi ba. "Inda zaka kaishi qasata.......akwai tarin marayu da marasa qarfi da zasu shiga cikin walwala da farinciki sanadin haka.....zasuyita sanya maka albarka.....mutane masu yawan gaske da suke kwana cikin yunwa da ciwo......suke kwana cikin halin babu.....'yammata da yawa sun rasa mutuncinsu sanadin talauci,iyaye da yawa sun rasa 'ya'yansu saboda abinda zasu sanya a bakinsu" Takai qarshen maganar wani abu yana taba ranta,wani abu yana taso mata yana tuna mata abinda ya wuce a baya. Sosai.....sosai da sosai maqurar gaske yaji tayi wani bala'in burgeshi......irin burgewar da ya jima baiji wani dan adam ya masa ita ba. A bangaren taimako idan ana maganarsa.....baisan adadin mutanen da suka dogara da rayuwarsa ba......baisan adadin mutanen da suke qarqashin kulawarsa ko kulawar wasu nashi ba,ba'a iya Nigeria kadai ba......bai bari tallafinsa ya tsaya a qasata ba kawai,ya leqa maqwaftan qasashe sosai,saidai kusan komai zaiyi baya bari a fadi sunansa ko a saka sunansa,wani kaso mafi girma na dukiyarsa ya ware ya kuma sadaukarwa al'umma........to amma kuma hirar tasu,yana buqatar tayi tsaho,yana buqatar wannan kusancin a tattare da ita......yana kuma cirar wasu abubuwa daga sautin muryarta da yanayin yadda take maganar daga qasan zuciyarta.....kamar akwai wani abu daya shafeta cikin maganganunta. A nutse ya miqe yana zama kujerar dake facing nata,yana zube idonsa a kanta tare da qoqarin lalubo qwayar idanunta. "Exactly......kin kawo point me girma......me zai hana ki karbi aikin a hannuna?.....a matsayin personal assistant nawa a wannan bangaren?" Maganar tasa taja hankalinta sosai har sai data waiwayo ta dubeshi da raunanan idanunta. Wannan din yana daya daga cikin cikar burin rayuwarta,ta zama sila na shigar da farinciki zukatan wasu,ta zama sanadin yayewar damuwar wasu....amma tana ganin kaman zatayi shishshigi ne ta shiga rayuwar da sam ba tata bace. Ya fahimci akwai kokwanto sosai cikin kallon da take binsa dashi,sai ya sakar mata murmushi yana dunqule hannunsa guri guda,saboda kallon da take masan kaman tana sakar masa wasu harsasai ne cikin jikinsa. "Da gaske......ina buqatar irin hakan.....irinki cikin rayuwata.....amma wannan karon ni zan biyaki.....bake zaki biyani ba" Ya qarasa fada yana kallon qwayar idanunta. Murmushi dan siriri ya qwace mata,ta kawar da kanta gefe tana kaucewa ganinsa. Wani irin kyau fuskarta ta sake masa,murmushinta ya tsaya masa a zuciya,ya kasa dauke idonsa a kanta,iya adadin murmushin da ya taba gani akan fuskarta qididdigagge ne,ashe haka murmushi yake mata kyau?. Yasan me ta tuna,don haka shima boyayyen murmushi ya saki,ya ciri wata farar takarda da abun rubutu da suka samu a gurin ya tura gabanta. "Zan shiga wanka......kafin na fito ki rubuta adadin salary din da kikeso,daga kan million goma har million dari". Waiwayowa tayi a nutse,ta dafe takardar tana dubansa. "Ba komai ne akeyinsa saboda kudi ba......kaman yadda ba komai bane kudi ke iya siyansa ba......wasu ladaddakin sunfi duniya da abinda ke cikinta muhimmanci a rayuwar d'an adam" Ta qarasa furucin yana duban labbanta da suke motsawa da wani irin yanayi dake matuqar daukan hankalinsa. Kai ya jinjina yana miqewa gami da matsawa a nutse yana zare socks din qafarsa. "Na sani....saidai ko Allah daya haliccemu ya sanya ladan kowanne aiki.....kaman yadda idan nayi aiki haqqina ne ka biyani....haka idan akamin haqqi ne akan kowa na biyashi" Ya qarasa fada sanda yake zare rigar jikinsa. Kanta ta dauke da sauri daga kansa zuciyarta na harbawa,batason kallon wannan ginannen jikin shi wai baisan hakan bane?. Murmushi kadan ya saki,ya karanci me take daukewa kan sarai,sai ya fara takawa zuwa inda ta maida kan nata,ya saka hannu yana zuge duka curtain din da suka zama hijabi ga idanuwa,suka lullube gilasan suka hana mata kallon ruwan dake gabanta din. Maida idonta tayi ta lumshe,da alama dai taci alwashin ba zata kalleshi din ba. Kai ya jinjina,shi kadai yasan me yake saqawa a zuciyarsa......da sannu zai saita komai kan tsarin da yakeso,a nutse yabi kowanne curtain ya zugeshi,sannan ya dauki bath set dinsa ya soma dosan toilet. Kadan ta bude idanunta taga yana tafiya bandakin,tasan kuma indai ya shiga ita daya zai bari sai ruwan nan dake kada hankalinta. Zumbur ta miqe da gudu gudu ta rufa masa baya,sai ya tsaya ya waiwayo yana kallonta sanda ya sanya qafarsa a qofar toilet din. Yadda ya zuba mata idanu ya sanyata yin qasa da kanta,tasan yana neman ba'asin biyoshin da tayin,tana wasa da farcenta tace. "Tsoro nakeji" A shagwabe har batasan sanda sautin tattausar muryarta ya koma haka ba. Wani numfashi ya zuqa me zurfi yana dubanta,yana bala'in son shagwaba fiye da yadda kowa zai fahimta.......saidai ba wanda yasan da wannan dabi'ar tasa saishi kadai,don ya sanya a ransa ba shagwabar da zata burgeshi saita matarsa. Yana cikin jinsin mazan da shagwaba ke tafiya dasu,yasa hannunsa yana shafan qirjinsa dake cike da gargasa muryarsa a maqoshi yace. "Ba wani abu fa.....kina cikin aminci,na miki alqawari daga yanzu har qarshen numfashinmu.....ba iya nan kawai ba.....a dukka fadin rayuwarki ba wani abu daya isa ya sake cutar dake muddin fu'ad yana raye". Idanu ta ware tana kallon qasan curtain din,ruwan yadan kada alamun wucewar kifi. Tanason kallonsa ta tabbatar masa da tsoronta amma kuma batason kallon muscles dinnan nasa. "Still tsoron dai?" Ya tambayeta yana dage mata gira,saita daga masa kanta. "Okay.....yanzu to ya zamuyi?" Ya tambayeta yana zube mata idanunsa. Satar kallonsa tayi kadan sannan ta dauke kanta,itama bata sani ba......batasan ya zasuyi ba,kawai dai abinda ta sani ba zata yarda ta zauna ita kadai ba. Kaman yasan abinda take saqawa yace mata. "Zaki shigo ciki ki jirani na gama wankan?" Ya mata tayi yana da tabbacin ba zatayi accepting ba. Waro idanu tayi tana kallonsa kai tsaye tana mantawa da batason ganin qirar jikinsa ma. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 100 100 _Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_ _Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_ "Ki zauna to ki jirani......bazan iya kwanciya banyi wanka ba.....if not ki shigo sai muyi wankan tare" Ya fada yana matsa mata hanya. Ai da sauri sauri taja baya,ya saki murmushi ya matsa kusa da stool ya dauko mata ya ajiye mata qofan toilet din "Oya.....zauna a nan". A sanyaye ta zauna din kaman me gadinsa,yayin da shi kuma ya wuce ciki. Sai daya shiga ya kunna shower sannan dariyarsa ta subuce.... Bai taba kawowa a ransa muraaka zai kawo masa wannan kusancin da yaketa fata tsakanin shi da ita ba sai yanzu......tabbas inda yasan da hakan da tuni ya jima da daukota wannan duniyar. Idanu ta yita rarrabawa,tana sanyawa a ranta muddin taji wani abun da baiyi mata ba zata afka bandakin ne,komai ta fanjama fanjam,saidai har ya gama din ba taji komai ba. Daure da towel ya fito a tsukakken qugunsa,ya fito mata sak kaman wani dan wasan dambe na duniya. Kanta ta dauke ta miqe tana basarwa gami da barin wajen zata koma saman sofa. "Kiyi wanka ki sake kaya kizo muje muci abinci" Ita da yayi zancan abinci ma saita rasa cikin wannan rayuwar ruwan ina za'a samu wani abincin kirki. Bata musa masa ba don itama ya zame mata al'ada yin wankan kafin ta kwanta,saita dinga dube duben wanne sponge xatayi amfani dashi?,in fact ma tafiya ce ta dole dole ko kayan da zata sauya bata taho dasu ba. Miqa mata bath set dinsa yayi yana kafeta da ido,salin alin ta karba don wannan kallon nasa bata qaunarsa,wani iri yake sata tana ji gaba daya. A tsorace ta kammala wankan,duk minti guda sai taji kaman kifayen zasu shigo su sameta,data gama ma hakanan ta maida kayan data cire ta fito dasu. Sanda take shigowa ya kammala shirinsa tsaf,cikin polo shirt fara qal me ratsin black,sai black trouser shima daya zauna a jikinsa sosai yana nuna zallar hasken fatarsa. Duk yadda taso ta qaryata kanta sanda zuciyarta ke fadin yayi kyau amma ta kasa haka,wani irin kyau kayan sukayi masa kaman saboda shi aka qerasu. Kallo daya ya mata ya dauke kansa,ya dauki wayarsa yana cewa. "Ga kaya nan ki canza.....ki sameni a sitting room" Yana fadin haka yayi gaba. Taku biyu tayi da zummar biyoshi ya dakata yana waiwayowa. Wata siririyar dariya ta qwace masa. "Dama matsoraciya ce ke har haka?,bazan tafi na barki ba.....zan baki space ne ki shirya,in kuma kinaso zan zauna na tayaki shiryawar.....nima zanzo hakan" Fuska ta bata tana dakatawa daga binsa din. Kai ta girgiza yana sauke murmushi ya juya yana barin dakin. Jikinta ta qanqame waje daya kafin daga bisani ta nufi luggage din daya nuna mata,ta kwantar da ita ta zugeta tana duba kayan ciki. "Turqashi" Ta fada bayan ta ajiye rigar qarshe data daga a kayan. Kusan an sake maimaita abinda amna ta mata,kaf kayan bataga wata riga da zata suturce mata jiki ba,wasu irin kaya ne masu kama da qannen dasu gwara babu su,sai kawai ta zauna a qasa tana saka kayan a gaba gami da buga tagumi da hannu daya. Lokaci yake dubawa,sai yaga ya wuce qa'idar lokacin wanka da shiryawarta,wanda tuni ya fara riqewa a kansa,aje wayarsa yayi ya miqe yana komawa dakin. Kanta ta dago suka hada ido,sai ya maida dubansa ga akwatin,tayashi tayi itama,ta kalli akwatin ta kuma kalleshi,idanunta kadai sun gaya masa abinda take nufi,ya saki qofan ya qaraso ciki. A gaban akwatin ya tsugunna ya fara daga kayan shima,tun baiyi nisa ba ya cire wata gown yana ajeta gefe. Da ido tabi rigar,saboda ta dagata taga yadda take,kusan gaba daya bayan rigar a kwakwashe yake sai zararruka da ake zargawa ta bayan rigar a daure. Ta gaban kuma ajiyayyen breast cup ne da koda me zubabbun qirji ta tabbatar sai sun tashesu tsaye ballantana irin nata. Da idanu yayi mata nuni kan ta dauka ta sanya,tsoro ya bayyana qarara a fuskarta,tadan ware idanu kadan tana jifansa da alamar tambaya. Idanu ya lumshe mata gami da kada kai,ya tsugunna ya dauki rigar sannan ya soma takawa a nutse yana rage tazarar dake a tsakaninsu. Dab da zai isa ta fahimceshi,saita yunqura da zummar janyewa amma ya fita zafin nama don tuni yayi ram da hannunta cikin nasa. "Kowanne musu da taurin kai akwai cost dinsa a wajen nan" Ya rada mata a kunne sanda yake rungumeta cikin jikinsa yana lalubar zip din rigar tata. Kai ta soma kada masa,don indai zai rabata ne da wannan rigar tamkar ya rabata da komai ne,saboda ba komai din a jikinta,don bata iya maimaicen pant da brazier ba don haka ta zura rigan kawai ba tare data sanyasu ba,da nufin ta nema wasu idan ta fito. "Ka bari......zan saka Allah" Ta fada a tsorace muryarta tana rawa. "Is too late" Ya furta can qasan maqoshinsa yana shaqar daddadan qamshinta duk kuwa da cewa wanka tayi. Bai bata damar fadin kalma ta biyu ba ta zuge rigar tsaf da jan zip qwaya daya tak. "Don't move.......saka miki kawai zanyi muje muci abinci......musu ne banaso.....kinqi ki gane kuma.....leave me mana na gama miki a nutse mu wuce?,idan da rigima kuka kikeso to na iyata kwando kwando" Ya sanya labbansa saman kunnenta ya karanta mata. Idanunta a runtse tsigar jikinta na zubawa,daga yadda yayi maganar tabbas da gaske yake......wata zuciyar ya shawarceta tayi haquri na sakanni ya saka matan kaman yadda yace.....dole ya barta idan ya saka mata din ai. Wani abu ta hadiye a maqogoronta cikin matuqar tsoro tana kulle idanunta,tana jin wani iri na yadda zai sake samun damar kallon surarta da taba jikinta a karo na biyu bayan alqawari da tayiwa kanta makamancin hakan bazai sake faruwa ba......tana jin sanda iska ta hura fatar jikinta,tana jin sanda yadan rabata da jikinsa ya salube rigar ta sulale qasa. Dukka jikinta ya dauki rawa da bari ganinta cikin yanayin da ko mahaifiyarta bata taba ganinta ba.......duk da ba haske bane tarwai a dakin amma ba abinda zai hanaka ganin mutum sosai da sosai,tsoronta ya ninku,ta dinga jin kaman qasa ta tsage ta hadiyeta a ciki. Da qyar ya kamo numfashinsa dakeson kubce masa saboda sauka da idanunsa sukayi a wajen. Ya miqa hannunsa yana me burin isa gurin,sai kuma ya tsaya cak yana janyesu a hankali,wata qatuwar ajiyar zuciya ta kubce masa kaman yaron da aka yiwa dukan tsiya yaci kuka ya qoshi,da wani irin zafin nama ya juyata fuskarta ta daina facing dinsa,saidai can dinma ba sauqi,hips dinta ke tsokane masa idanu,sai kawai ya rabata da jikinsa waiko hakan zai sanya ya rage ganin abubuwan da yake gani din. Baisan shima nasa hannuwan rawa sukeyi ba sai bayan ya zura mata rigar ya dagata daga jikinsa yana zazzarga mata igiyoyin dake riqe da bayan rigar. Sosai hannuwansa suka kama rawa,daure igiyoyin suka gagareshi. Ya runtse idanunsa da matuqar qarfi yana fatan daidaituwar mode dinsa,saidai ko daya bude ba abinda ya canza saima numfashinsa daya fara fuzga kaman me ciwon asthma. Hannuwansa ya dora saman kafadunta gaba daya ya juyo da ita da wani irin hanzari,yadda red din gown din ta sake haskata sai yaso.tafiya da ragowar numfashinsa da yake kokawa dashi. Gaba daya labbansa rawa suke kaman me rawar sanyi ya soma lalubo kalmominsa...... "DUNIYA TA.... please,kiyimin alfarma na sake kasancewa dake karo na biyu......please na roqeki karkice zaki hanani" Firgicin data shiga ya kusa fin nasa,take itama jikinta ya kama rawa,ta zare idanunta duka a kansa tana jin kaman zasu zazzago tsabar tsoro. Ta motsa labbanta zatayi masa magana a tsorace amma ya rigata "Am so sorry.....naso na barki har sai sanda kika fara sona.....naso na barki har sai sanda kika gamsu da kanki kikayi accepting muhammad fu'ad......but.....kece DUNIYATA bani da wani gurin zuwa sai wajenki din dai" Sake rudata kalamansa sukeyi,batasan yadda zata masa bayani bama,neman gurin tsira kawai takeyi,saita saka hannunta tana neman zame hannuwansa daga kafadarta. Sarai ta fahimci a rude yake kaman yadda take a rude,idanma tace zata tsaya masa bayani bazai fahimta ba. Damqe kafadun nata yayi idanunsa suna sake juyewa hadi da canza launi. "Please mana.....na miki alqawari wannan karon......I'll be gentle with you.....i will never harm you again" Ya fada yana jin kaman ana qara izashi zuwa gareta.....kaman yana qara loosing tunaninsa gaba daya. Sake buda baki tayi still bata sare ba,duk da tsoron dake sake dabaibayeta da nufin masa bayani ko kadanne,amma sai.ya kama hannuwanta duka ya sanya tsakiyar tafin hannunsa kaman me begging dinta "Please....please.......na yadda da kowacce kalan tuhuma zakiyimin......na yadda da kowanne zarginki a kaina......kome kikace nayi ina neman gafara akai......kinqi bani dama tun a baya nayi bayanin kaina......I'm pleading with you.......grant me this favor" Ya qarasa maganar yana zubewa a gabanta...... Ji yake ya shirya rasa komai.....ya shirya kuma sadaukar mata da komai,yayi qasa da kansa yana jiran cewarta jikinsa naci gaba da rawa. Wani abu ya tsarga mata jin digar wani abu me dumi saman tafin qafafunta,wata irin faduwar gaba ta ziyarceta saboda abinda zuciyarta ta raya mata. "Muhammad fu'ad jadda ne kuka a gabanta?,muhammad fu'ad fa?,wanda gidan jaridu da mujallu kowacce fitowar rana zuwa faduwarta suke rububin buga labari akan kamfaninsa......suke rububin fidda labari akan kalan jarumtarsa tun kan ya balaga har zuwa girmansa......jaddan da qasashen duniya keyi dashi?,jaddan da maganarsa manyan kamfanonin qasashen qetare dake sarrafa diamond sukeji?,yau shine under her feet?. Daidai inda zaren tunaninta ya tsaya kenan,sai dauko mata sunkutarta da fu'ad din yayi zuwa lafiyayyar shimfidar da muraaka suit suka zubeta musamman saboda masoya masu yawon watan zuma wato honeymoon irinsu fu'ad din. "Am sorry DUNIYATA.....am sorry my world" Shine abinda ke fita daga bakinsa cikin wani irin gigitaccen yanayi. Tsoro ne fal qirjinta da zuciyarta,tuni ta fara sakin nata kukan tana hango kanta gaban Dr fadwa ana sake dinketa. Tana sake rewinding azabar da tasha wancan ranar.....ta kasa mantawa da yanayin daren da kuma lokaci. Hatta da wucewar kowacce daqiqa a lissafe take a wajenta....abune da ya kasa barin kanta da mafarkanta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 101 101 _An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_ _2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_ _Bukhari da muslim_ "Kar ka cutar dani" Ta fada a galabaice tana jin yanayinta yana canzawa. "Bazan iya cutar dake ba.......sonki ne yayimin yawa.....ki taimakamin na koyi controlling nasa" Ya fada ba tare daya saurara mata ba. "In ka cutar dani ko ka zalunceni......" "Ki daga hannu ki roqi Allah ya hukunta miki ni.....ki roqi Allah yayi miki sakayya......ya jarabceni da wani son da yafi wannan yawa da fadi" Ya fadi yana tallafo kanta gami da sanya jirkitattun qwayar idanunsa cikin nata dake cike fal da hawaye......dukka hannayensa suna rawa kaman wanda aka tsamo daga ruwan sanyi. Idanunsa kawai firgitata suke,ta saka hannu zata riqeshi saidai ko kadan bayason sakejin wata magiya tata,don haka ya rufe bakinta ruf da nasa. A hankali ya shiga aike mata wasu irin zafafan saqonni.......wasu irin abubuwa da tun tana turewa har suka fara kama mata kwanya.....suka jefa ta a duniyar tunani.....suka dauki duk wani tsoro nata da fargabarta sukayi cilli dasu can bayan gadon.....suka gusar da duk wani hankalinta tunaninta taurin kanta tsiwa dama tsoronta. A hankali saiga me jadda yana komawa fagen,fagen da bai taba zaton zai sake ziyarta ba karo na biyu cikin rayuwarsa.......yayi musu ragama da jagora zuwa wata sabuwar duniyar da shi da ita basusan akwaita daban bace.....tasha banban da duniyarsu ta wancan karon nasu. ★Tun yana dakon jiran fu'ad har ya soma lalubarsa cikin gidan,don dakinsu ya shiga zaman jiransa. Ko ina ya duba bai ganshi ba,bai wani zurafafa tunani ba ya dauki wata motar ya fita ya zauna da baqin nasu,suka kammala meeting din ya sallamesu,ya kuma hada duka documents din a take ya aika masa ta email. Kaman yadda suka tsara daga wajen sai ya wuce dauko anni data tafi wani herbal center a traditional market dinsu. Suna mota take tambayarsa fu'ad din "Mun fito tare so uzuri ya maidamu,sai nace bari nazo na daukeki" Daga haka suka rufr chapter din suka dauko wata har suka isa gida. Komai anni ta gama har tayi shirin kanwaciya amma bataga sabreen ba. Tana saman abun sallah tana shafa addu'ar shafai da wutirinta tace da amna. "Ina ameenatu ta shiga ne?" Kai ta girgiza,itama tun dazu take nazari "Ban sani ba wallahi anni,maamah dai tayi kiranta,tunda ta fita kuma bata dawo ba". Shuru anni tayi haka kawai taji gabanta yana faduwa. " Maamah ce ta kirata?,tunda ta fita kuma bata dawo ba?" Ta sake maimaita statement din tana duban idanun amna. Kai ta gyada mata. "Turqashi" Anni ta fada tana miqewa hankalinta yana tashi,zuciya ta fara fasalta mata abubuwa kala daban daban da zasu iya faruwa. "Indai wani abune ya faru kaman yadda zuciyata ke gayamin......indai wani abu mariya ta aikata na cutarwa ga ameenatu.......tabbas saita gane bata da wayo......a wannan karon saina nuna mata ainihin kalata" Anni tayi maganar a zuciyarta tana zare hijabin jikinta,ta dauki dankwali ta daura tana duban amna "Ki zauna ina zuwa" Abinda kawai tace da ita kenan ta murda qofar tana ficewa. _tofa.....😂😂😂,me anni zatayi?,masu karatu ku tarota,ku gaya mata ba ruwan maamah a nan......dan annin ne yayi kidnapping takwararta da kansa_🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️😆😂😂 Daidai lokacin da maamah ke dakinta,abun duniya yana sake ta'azzarar mata da wani irin zafi qunci da tashin hankali. Kaf tunaninta ya karkata akan yadda zata raba sabreen da wannan copy din video din da yake hannunta.....rabata dashi din shine tamkar mabudin iya wurgar da ita daga rayuwarsu cikin qasqanci da tozarcin data tanadar mata. Ta duba agogo ta duba agogo har sau babu adadi......ta duba agogo duk bayan kowanne wucewar daqiqa.....cikin saka ran fuad zai dawo ya lallasheta......fu'ad zai dawo yaji meye damuwarta kaman kowanne d'a yakewa iyayensa,saidai tun tana dubawa tana kuma lissafawa har ta bacewa lissafin. Kowacce alama da shaida ta nuna mata bazai dawo ba.....ya fita abinsa ne,bashi kuma da niyyar bata wannan lallashi da kulawar da take yunwarsa. Ranta yakai qarshen baci,da gaske dai bai dauketa uwa ba mahaifiya.....kunnuwanta na tuna mata wata hira da taji musaddiq da saddiq nayi,suna gulmar fu'ad din. Ya fita aiki ranar sai gashi ya dawo da Rana,suka dinga dariya suna gulmarsa,wai da zai fita ne yaga ran anni kaman a bace....da yaje office ya kasa sukuni,dawowar da yayi yazo zagayata ne ya tabbatar ta warware,ba kuma wani a cikinsu bane ya bata mata rai ba. Tuna wannan kawai ya sake hura wutar zuciyarta,sai kuma ta tsinci knocking da fushi yasa ta kasa tambayar waye,ta miqe kawai ta bude qofar a fusace. Anni ta gani a tsaye tana duban ta,wani irin kallon kallo dake dauke da ma'anoni da yawa a zukatan kowannensu. "Zuwa nayi duba sabreen.....ta shiga dakinki kuma har yanzu bata dawo ba?,ina kika kaita?". Me neman kuka ne wanda aka jefa da kashin awaki,wanda yake jiran kadan ya fashe,saita fito daga dakin gaba daya tana duban anni tana huci. "Dama dab nake da zuwa wajenki na tambayeki wanne irin baqin sihiri kika yiwa 'ya'yana?,wacce irin shirka kika ta'ammali da ita ameena?,da yake bani da haqqinki sai gashi kin kawo kanki da kanki kina tambaya akan abinda ni yafi cancanta na tambayeshi". Mamakin maamah din ya kasheta,ta zuba mata idanu sosai tana ganin yadda take haqilo kaman zata fidda maqogoronta. "Mariya......tambaya daya ce nayi ina kika kai sabreen?,don bata dawo dakinta ba". Wani banzan kallo ta watsawa anni tana dubanta. " Au.....bacewar karuwa dama abun mamaki ne?,har akwai mamaki don an wayi gari an tarar karuwa ta gudu daga dakinta?" "Subhanallah" Anni ta fada tana ware idanunta akan maamah mamaki yana ratsata. Surukarta?,matar d'anta take kira karuwa saboda wani son zuciya nata?. "Ameena.....ina me baki shawarar warware duk wani qulli da kikasan kin yiwa yarana tun daga zamanin quruciya zuwa yanzu.....idan kuma kinqi wallahi wallahi ni mariya bazan qyale ba......na dauki cikin yaran wata tara na haifesu.....naci kashinsu da fitsarinsu amma rana daya azomin da bariki da salon mallaka?,ubanme kike basu wanda ni bazan iya basu ba?,uban me kike musu?". Sosai zagin ya sosa zuciyar anni,sai ta koma ta zauna tana qare mata kallo hannayenta harde a qirjinta. Duk wasu sarari da filaye na yiwa maamah kara zuwa yanzu sun fara cika,bata kuma da saura wanda zata bude mata taci gaba da zuba jujinta. Kai tsaye kuma hankalinta kwance ta kirata "Mariya......abinda na basu baki dashi.......kin kuma rasashi har abada......yadda kika kasa rungumarsu kiji qansu a sanda suke da rauni......to kema kin rasa wannan cikakken tausasawar sai wadda zasuyi miki donsu fita haqqinki da haqqin addininsu......shima wannan din xasuyi miki shine saboda sun mori iyayen goyo da sukasan hagunsu da damansu.....daidansu daba daidai ba......banda haka ke dasu dama dukkan abinda suka mallaka sai gani sai hange daga nesa. Inda ce hankalinki a daidai yake......inda ace hankalinki cikin jikinki yake.....ba cikin dimuwa kike ta neman duniya idanu rufe ita da abinda yake cikin ta ba......da baki buqatar bayani kan me yasa kika rasa kike kuma rasa kowacce dama,take kuma kufce miki.......bari na gaya miki wani abu.....ni ameenatu na tsere miki.....ni ameenatu ba zaki taba kamoni a zukatan naki 'ya'yan ba bare nawa 'ya'yan.....sauran dukkanin abinda zaki zata ko ki tuhuma wannan ke kika sani.....kuma keda zuciyarki......zuciyar bawa birninsa,abu daya zance miki shine......kada ki yarda kada kuma ki kuskura wani abu ya samu sabreen,idan kikayi wannan gangancin to tabbas zan saka a binneki a cikin qasar Maldives me tarin farin rairayi" Ta qarashe maganar tana nuna maamah da yatsa,sannan ta miqe tsaye sosai. "Daga yau gobe zuwa jibi naga dawowar diyata cikin gidan nan.....ko da fu'ad ne yace zaiyi ganganci da rayuwarta shi dake aurenta saina hukuntashi.....ballantana ke da nake kyautata zaton kwangilarta kika dauko". Anni na kaiwa nan ta juya tana barin wajen,tanata qoqarin controlling fushinta kada maamah din ta ganshi. "Aikin banza kenan qafafa da mallakin wani.....ke me ya hanaki haifar kamarsa?,kinga sai kiji dadin yin mulkin mallakar da kyau ba tare da kowa yaga wallenki ko ya qalubalanceki ba" Tayi maganar da nufin fusata zuciyar anni. Da wani lafiyayyen murmushi ta waiwayo tana kallonta. "Banda abinki tunda kin haifomin ai kin hutasshe dani......don yadda nake hutawa ko asalin wadda ta kotseshi bata rabauta da wannan ba....idan kinajin tsuntsu daga sama gasashe to fu'ad ne a hannun ameenatu" Ta qarashe maganar tana bude mata tafukan hannayenta sannan ta juya taci gaba da tafiya abinta. Kamar hauka zai kamata haka taji maganganun anni saman kanta. Kasa shuru tayi ta soma zuba ruwan masifa da zagi. "Ameenatu.....nafi qarfinki....nafi qarfinki wallahi,bakisan wacece mariya ba....kibar ganin zamani ya cimmata......to ki giwa ta fadi tafi qarfin wawa,tafi qarfin kiyashi ya jata.....zan nuna miki asalin wasan indai na haifu cikin uwata da ubana". Bataji komai cikin abinda take fada ba,don already ta wuce daki ta kuma maida qofar ta kulle. "Bari yazo shima zai sameni.....bazan sake kwana gida daya da wannan annamimiyar makirar ba.....dole yazo ya zaba,koni ko ita" Ta fada kaman zararriya tana jawo luggage dinta tana watsa kayanta ciki,sai kuma ta tsaya cak. "Ina yarinyar ta shiga?" Ta tambayi kanta gargadin anni da fuskar daba wasa tana dawo mata,saita saki kayan hannunta ta koma gefen gadon ta zauna. Wani gumi ne ya tsargo mata tana jin hankalinta ya fara kadawa. Anni tana da power din da bata da ita.....tabbas ne wannan,don idan akace ana buqatar ganin fuskar maman muhammad jadda ta anni ce za'a fara nunowa.....daukakar fu'ad ta sanyashi alaqa da manyan mutane da hankali baya zato,da yawansu kuma suna alaqa da anni a matsayin itace mahaifiyarsa......KENAN UMARNI DAYA ZATAYI A KANTA AYI MATA YADDA TAKESO?. Tambayar data sanya 'ya'yan hanjinta curewa waje daya kenan,saita jawo wayarta da sauri tana nemam number fu'ad. Kiran duniya wayarsa a kashe,ta kira tun tana irgawa harta bacewa lissafi,sai ta aje wayar kawai gefe tana tunanin meye abunyi?. _😂😂😂,maganin dan banza karen maguzawa ko inji hausawa.....shin a wannan lokacin hajiya maamah xata shiga hannu ko kuwa?_ _meye hasashenku?_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 102 102 Tsaye take gaban qawataccen madubin bandakin me tsananin haske da hasken rana daya soma mamaye sararin samaniya ta bullo ta wasu sassan glasses na bandakin ya kutso ciki. Daure take da bathrobe me tsananin taushi,fara qal data zauna a jikinta bisa taimakon igiyoyin dake maqale a jikinta,saman kanta daure da towel data nade gashinta me tsaho da santsi,wanda ruwan da ya jiqashi ya sanyashi kwanciya ta gaban goshinta dama wasu sassa na wuyanta. Brush ne riqe a hannunta.....amma sai ta kasa matsa toothpaste a jiki,saita buge da kallon fuskarta ta jikin madubi data fito tarwai kaman ka saka hannu ka ciro. Daren jiya ke faman mata yawo cikin kwanya......tanata tuna shudewar kowacce daqiqa a tsakaninta dashi. Iya yawan abun kunyar data tafka bazai barta hada idanu dashi ba,ba zata iya ba sam koda daidai da minti daya. Duk yadda take tunanin abun zaizo kaman na farko sai komai yazo mata da ba zata,saida komai ya kammala sannan ta tsinciki kanta tsakanin hannuwansa,bata da wani zabi illa fashe masa da kukan kunya. Ya sani sarai......yasan abinda takema kukan,amma sai yayi kaman bai fahimta,ya lalace sosai wajen rarrashinta......daga qarshe ya juye mata tashi kalar shagwabar data sake tsumata,ta sanyata tayi luf ba shiri tana jin kunya da nauyinsa suna kamata. Zare brush din daga hannunta da taji anyi ya sanyata firgita "Good morning sleepy head" Ya fada yana tsaye daga gefanta ya kashe mata idanu yana qoqarin saka mata toothpaste din. "Morning" Ta fada tana sadda kanta qasa tana jin wani irin nauyinsa da bata taba ji ba. Tunda taji ya tashi ita taqi koda motsawa,har yayi wanka ya fito yayi sallah yadan fita a dakin,fitar nasa tayi amfani dashi tayi wuf ta shiga wankan da xummar ta shirya kafin ya fito tayi sallah ta sake boyewa cikin duvet. "Feel free......brush kawai zanyi na fita" Ya fada yana matsowa bayanta. Dab da ita ya tsaya,har jikinsa yana gugar nata,fuskarsa ta fito bayan tata ta cikin madubin,ya zube idanunsa fes da suka qara wani irin haske saman tata fuskar ta cikin madubin. Wani irin murmushi ne kwance a fuskarsa.....wata irin shimfidaddiyar walwala da makamanciyarta bata taba wanzuwa saman fuskar tasa ba da annuri suke fita daga fuskar tasa. Qwayar idanunta yaketa laluba yana son ya kalla amma ta hana mishi kallo,ta zura brush din kawai a bakinta tana wankewa tana kuma jin yadda yake sake shigewa jikinta da sunan brush zaiyi. Ta gefe da gefen cikinta ya zura hannuwansa ya zari brush dun,ya saka toothpaste duk a hakan yana sake shige mata,ya tura brush din bakinsa ya soma wankewa shima a hankali yana sake maida idonsa ga fuskarta data futo sosai ta madubin. Wani kallo yake mata ko qiftawa baya yi,yana fatan tayi kuskure ko sau daya ta daga kai ta kalleshi,yana son karantarta ta cikin idanunta sosai,ya sake matsawa sosai jikinta yana sansana kanta dake fidda wani irin sassanyan qamshi. Ta gama nata brush din amma tanata juyashi a hannunta,ta rasa yadda zata gaya masa.....ta kasa daga kai ta kalleshi ma bare ta samu qwarin gwiwar gaya masa. Ya karanci hakan,murmushi ya qwace masa. "Wannan kunyar daga ina?" Ya tambayi kansa da kansa daga can qasan zuciyarsa. Yana sane yaci gaba da cinye musu lokaci,yanason tayi magana amma kuma ta gaza,har zuwa sanda taji ta soma tuqewa,saita ajiye brush din,ta kuma juyo da hanzari tana fadin. "Ni na gama" Qurjinsa ta fada kai tsaye,don babu wani space da zai bata daman wucewa. Kan qirjinsa idanunta suka fada,ni'imtaccen gargasar qirjin tayi maraba,ta daga idonta a hankali tana kallon tazarar nisan tsahon dake tsakaninsu. Ya fita tsaho sosai,duk da cewa ita din ba gajeriya bace,idanunta suka sauka kan Adam's apple dinsa daya fito sosai ta maqogoronsa kaman zai fado. Wani abu guda daya tal da yake burgeta ga halittan namiji kenan......batasan meyasa yake burgeta ba,amma dai tasan yana bata mamaki,ta jima kuma tanason taji abun ya yake,tauri ne dashi?,yana musu zafi ko kuwa?,ba tare da tunanin komai ba ta miqa yatsanta a hankali zuwa wajen ta tabashi. Cikin kowanne jini dake harbawa a jikinsa yaji saukar yatsan nata,ya hadiye wani abu daya sanya Adam's apple din motsi yayi qasa ya sake dawowa saman. Kasa jurewa abinda yakeji din yayi,sai ya fincikota sosai zuwa jikinsa ya matseta a qirjinsa da kyau yana dora fuskarsa saman wuyanta. "Wannan tsokana ne ai......yanzun kuma inda zan ritsaki kona nema fansa saiki isheni da kukan banza......har a kiramin anni ma da momma ko?". Kunya ce ta kamata me tsanani,akan jiya yake tsokanarta ta sani......sannan ita kanta batasan ma'anar abinda tayin ba yanzun,taji tana sha'awar tabawa ne kawai. "Nifa wannan gaisuwar baiyimin ba......ina buqatar zuzzurfan alaqa tsakanin da iyalina......inason ki zama qawata.....aminiyata......mamana.....yayata.....qanwata....oh" Sai kuma ya tsaya yana dagota daga jikinsa gami da dan dukan goshinsa. "Ashe fa ance sai anyi shawarar za'a soni ko aah ko?" Ya fada yana ware mata idanunsa. Kauda kanta tayi gefe daya zuciyarta na bugawa,wani murmushi yana son kubce mata amma tana hana hakan,bata ankara ba taji ya dagata cak ya azata gefan sink din bandakin,hakan ya bawa santala santalan cinyoyinta daman bayyana don bathrobe din ta dage kadan. "Kinsan me?" Ya fada yana tsayawa tsakanin cinyoyinta,hucin numfashinsa dana daddadan turarensa yana sauka a fuskarta. "Karki wahalar da kanki DUNIYATA kice saikin koyawa kanki sona......" Daga kai tayi ta kalleshi abinda yakeson gani kenan dama tun dazu,saidai ita din tayi hakanne saboda mamakin maganarsa. Girarsa ya dage mata dukka biyun yana jin dadin ganin qwayar idanunta. Oily eyes daya jima yana kokwanto shin akwaisu?,sai gasu a jikin abinda yake mallakinsa gaba daya. "Yes.....iya soyayyar da nake miki ma ta ishemu mu rayu ni dake.....bake kadai bama.....har babies din da zamu haifa nan gaba" Ya fada yana dora hannunsa saman plate tummy dinta,abinda ya sanyata jan wani irin numfashi saboda tafin hannunsa guda daya daya dora saman budaddun cinyoyinta. "DUNIYATA....Kinsan yara nawa nakeso ki haifamin?" Kasa amsa masa tayi,tafi buqatar ya matsa baya kadan kada ya dagula mata lissafi,abinda ta fahimta kaman yana son sake mata wayo ne kawai yake saka kusanta kanshi da ita. "Karka zaqe da yawa.....har yanzu ban gama yanke hukunci ba" Ta fada cikin tsanani dakiya. Dariya yakeso yayi sosai amma ya dake,ya fahimci qarfin hali irin nata da zallar qi fadi dake dawainiya da ita. "Don't worry.....kedai ki tayani ji ma kawai ya wadatar dani" Yana kaiwa nan ya sunkuceta gaba daya tamkar ya dauki 'yar jaririya yana takowa zuwa bedroom din. "Ka saukeni" Ta fada a narke,saboda ta lura gaba daya ya raina dagata,ya maidata kamar wata 'yar bebin roba. "Ta yaya zakiyi nauyi kina wasa da abinci?,indai kinason mu shirya saikin koyi cin abinci irin na muhammad fu'ad" Yakai qarshen maganar yana direta saman sofa bed,sannan ya fara takawa a hankali zuwa saman dressing table yana kwaso kayan shafanshi data tabbatar yafi qarfin talaka irinta. Gabanta ya zubesu gaba daya sannan shima yabisu ya zauna a gabanta yana tankwashe qafa tamkar bawa da uban gidansa. Ya soma bude cream cream din da wasu irin abubuwa da batace ga sunansu ba ya fara tatsawa a hannunsa sannan ya kamo hannunta yana juye mata su a ciki. "Zaki iya haifamin yara dozen biyu?" Yayi maganar murya a sanyaye da wani zuzzurfan sauti yana riqe da hannunta da yake maida cream din daga hannunsa zuwa nata. Idanu tadan wara tana dubansa da kyau. "Please am serious.....ko through IVF ne.....a dinga saka miki biyar biyar.....nayi alqawari ba zaki sha wahala ba.....zan biya ko nawa ne a ciresu cikin aminci.....zan kashe miki ko nawa ne DUNIYATA.....nayi alqawari" Mamaki sake kasheta yayi ganin yadda yake maganan da dukka gaskiyarsa,hakan ya bayyana itama a idanunta,sai ya saki wani murmushi yanayin fuskarsa yana canzawa. "Kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana sakar mata hannu don ta samu daman shafa man daya tatso mata. "Naso mu da yawa abbanmu ya haifa.....nayi wannan burin saboda gidan masu yara da yawa yana burgeni,saidai kuma mu biyu aka haifa.....inaso na tarawa abbana zuria me yawan gaske.....zuri'ar da zasu dawwama suna masa addu'a da sadaqa jariya.....bani da sha'awa ko burin auren mata biyu.....dake kadai nakeso na rayu DUNIYATA shi yasa nakeso ke din daya ki zama uwar dukka yarana" Ya qarasa fada yana dubanta. "Baga fareeda ba?" Tayi zancan da wani yanayi da ya sanya murmushi kubce masa,yadan dafa goshinsa yana cewa. "Maganan fareedan bai wuce ba?..... apologize din da nayi jiya baiyi ba?.....okay am ready to repeat it" Ya fada yana jinjina yadda abun yafi tsaya mata a rai fiye da komai. Kafadunta duka biyun ta daga tana kauda kai "Ina ruwana nikam.....am temporary......" "Temporary?" Ya katseta cikin maimaitawa yana dubanta da kyau ba tare da ya barta ta qarasa fada ba,sai ya ajiye boyayyen numfashi "You're my world.....kece DUNIYATA sabrrrrr....na rantse da Allah.....banda ubangijin daya haliccemu ba wanda ya isa ya qwaceki a hannuna.....ke kanki baki isa ki raba kanki dani ba.......ko mutuwa ina kai qararta wajen Allah.....muddin tana da nufin rabani dake ubangiji ya hukuntamin ita". Sosai maganarsa ta ratsata,taci gaba da shafa wa hannayenta man cikin wani irin kasala ba tare data dago idanunta ta kalleshi ba. "Ya kamata muje kiyi break" Ya fada yana katse shirun hadi da miqewa. Batasan me ya matsa yayi ba sai daya miqo mata rigar saman cinyarta. Rigar jiya ce dai da bata saka ba,saita daga ido tana masa kallon Why?. Kafada ya daga yana watsa hannuwansa. "Zan iya saka miki if ba zaki iya sawa ba" Kai ta girgiza masa da sauri,don ta tuna jiyan,daga saka rigar labari yasha banban. "To ka fita sai na shirya" Ta fada a shagwabe still "Inje ina?,bayan ko na fita dinma saina dawo na taimaka miki na daure miki rigar kin manta?" Ya fada hannuwansa na goye a qirjinsa yana qare mata kallo,don hatta cikin bathrobe din ba qaramin kyau tayi masa ba. "Na rufe idona.....inkin gama sakawa ki gayamin" Ya fada yana juya mata baya gami da maida kallonsa qofa yana ganin gilmawar ruwa ta tsakanin labulayen da basu gama rufuwa ba. A gurguje ta saka rigar,tanayi tana waiwaye wai kada ya juyo ya ganta bata sani ba. Dariya yakeyi abinsa can qasan ransa,don yana ganinta tarwai ta wani glass dake gabansa ba tare da ta sani ba. "Zan iya juyowa?" Ya tambaya yana danne dariyarsa. "Eh" Ta fada tana turo baki gaba,abinda yayi matuqar burgeshi har yaji kaman ya kama lips din ya shanye. A nutse ya dinga bin igiyoyin yana daure mata,kowacce daya saiya tambaya "Tayi haka?" Kai take daga masa mafi yawa,ta koma kaman kurman qarfi da yaki,ta tabbatar kaf halittun bayanta ya gama qare musu kallo,tana jin yadda yake sakin ajiyar zuciya time to time. Yadda maroon din rigar ta zauna daga bayanta kadai ya qawatar dashi gami da tafiya da hankalinsa. Ya dora yatsunsa a hankali saman fatar wuyanta,inda wajen ya danyi jajaja. Hannunta ta dora saman nasa tana dan danne wajen,guri kusan uku duka haka sukayi,yasan kuma shine sila,zare hannun nasa yayi yana juyo da ita tana fuskantarsa. Idanunsa ya lumshe yana kuma budesu duka samanta. "You look so gorgeous" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin sassanyan yanayi yana duban qirjinta da yayi redness shima guri uku. Yatsantsa yakai wajen yadan taba sannan yace "Does it hurt?" Fuska ta kwabe masa cike da shagwaba kaman zata sake masa kuka,sai ya yarfar da hannunsa yana fadin. "Ayyah.....sorry,bari na fanshi wannan ciwon" Ya fada yana ja da baya fuskarsa da murmushi. Luggage dinsa ya kwantar ya bude,ya ciro wani dan mitsitsin box ya tako gabanta. "Qaramim gift ne....for you duniyata" Ya fada yana ciro wani siririn agogo dake zuba qyalli. Koda bakasan meye ba kasan abune me matuqar daraja,kallo daya zakayi masa kasan abune me tsadar gaske,bashi da girma ko fadi amma yana daukan ido sosai. Matsowa yayi kusa da ita sosai,ya miqa mata hannunsa yana kallonta da ido. Ta fahimci me yake nufi amma saita noqe,bai wani tsaya jiranta ba yasa hannunsa ya kamo hannun nata sannan ya fara saka mata agogon. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 103 103 "Ya subhanallah" Ya fada yana juya hannun cikin tafin hannunsa. Ya mata wani irin kyau kaman saboda ita aka qirqireshi,ya zuba idon hannu yana jujjuyashi kafin a hankali yace. "Our latest wrist watch...2025,kin masa kyau duniyata.....nayi accepting wannan design din saboda ke,koda baiyi daidai da ra'ayin dealers dinmu ba,i love it for the sake of you" Ya qarasa maganar a tausashe yana kai hannunsa yayi kissing hannun nata,still idanunsa a kanshi,ya zura hannunsa a aljihunsa ya fiddo wayarsa ya laluba wata number ya kira. Bugu daya aka dauka,da hausa taji yana magana. "Mun siya design dinnan......sannan madam ta ninka price din da wasu dollars din akai ainihin price din". Ya fada a nutse da alama yana magana da wasu ne " Alright " Taji ya sake fadi yana katse kiran,yana maida wayar aljihunsa tana dubansa idanunta a warwaje,sai daya daga kai sannan suka hada ido,fuska ta narke "Wacce madam din?" Ta tambaya da siririyar muryarta dinnan,miskilin murmushi ya sake mata "Akwai wata bayan ke?" Saita sake fidda idanun "Ban da kudin siya fa....thought dai bansan nawa bane" "Amma kina da muhammad jadda ko?" Ya furta yana ja baya kadan idanunsa a kanta. Yana jin dadin kallonta sosai,sai yakejin duk wata tsohuwar kewa ta rayuwarshi tana sulalewa,yana jinsa wani sabon mutum na daban. Duban hannun nata tayi,haka kawai taji kaman ya saka mata wani abu me daraja da yawa,sai takejin hannun ya mata nauyi. "Na gode.....na gode sosai" Ta samu kanta da furtawa a sanyaye. Wani tsadajjen qaramin murmushi ya saki yana girgiza kansa. "No.....no need duniyata.......ba irin wannan godiyar nakeso ba.....the only one i want........" Sai bai qarasa ba ya mata nuni da shimfidadden gadon. Da sauri ta juya masa bayanta tana kasa hada ido dashi,ta fahimci yana bawa abunnan muhimmanci tamkar baisan kayan kunya bane?. A nutse taji ana yafa mata abu ta baya,ta daga kanta sai taga wata baqar sassalkar abaya ce,manal alhammadi shine tambarin da yake maqale a hannun rigar,ta fidda idanunta tana jin wani abu yana girmamarta,ta taba jin company din,wanda dukka abayas da yake fitarwa luxury ne masu tsada da aji sosai,ta sansu ne saboda ita din masoyiyar abayar ce. "Ba wani kunya tsakanin muhammad fu'ad da duniyarsa......ba kunya tsakanin muhammad fu'ad da matarsa......abinda kawai yake buqata......madawwamiyar soyayya da zata mamaye rayuwarsa.....ta bashi wani farinciki da nutsuwa daya rasa a rayuwarsa.....duk da cewa ina zaqewa da yawa.......amma wannan abun nake bara" Ya rigata fada kafin ita ta fada. Boyayyen murmushi ya subuce mata,wato daga jiya zuwa yau ya fara haddace irin kalmominta kenan da take yawan maimaita masa?. Juyo da ita yayi yana zura mata hannayen rigar ya furta "Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.....komai saikin masa kyau?" Yayi maganar yana dage girarsa. "Komai saina masa kyau?.....ko komai sai yamin kyau?" Ta tambayeshi tana mamakin yadda yake juya maganar daga qarshe ta koma farko. "Kece kike musu kyau basu keyi miki ba.....don dama kedin me kyau ce.....you're not ordinary duniyata" Yayi maganar sanda ya dago daga tsugunnan balle mata button din da yayi har qasa. Mayafin ya warware yayi mata lafiyayyen rolling tana tsaye tana kallon ikon Allah,ya kama hannunta zuwa gaban mirror yayi tsaye a bayanta. "Duk wani abu me daraja rufeshi akeyi a killaceshi" Ya furta a nutse yana duban kyakkyawar fuskarta ta cikin madubin,yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa saboda ita,kishinta yana sake ratsashi da kyau,yana sake jin tabbas......lallai ba wanda zaisha ba kuma wanda zaici bulus daga cikin mutanen dake hannunsa a yanxu.......tun daga kansu mashkur har zuwa kan zuwaira da bibo. "Ga aro nan na baki.....idan munci abinci mun dawo zaki bani kayata" Ya fadi wannan karon yana dan sanya seriousness saman fuskarsa. Dan dubansa tayi kadan,sai ya gyada mata kai alamun tabbatarwa. Yanaso ne yayita kallonta,yanason wucewar kowacce daqiqa tayishi bisa idanunsa,yanaso yaci gaba da kallon baiwa da ni'imar da Allah yayi masa,yanaso su kasance a haka shi da ita......da zaiyiwu su qare rayuwarsu cikin irin wannan yanayin na dagashi sai ita. Yana maqale da hannunta suke sauka zuwa bangaren cin abinci,private ne wanda ya dauko musu cook dinne musamman saboda iya su biyun. Sun samu dining room din cike da cima kala kala,abincin Africa da wasu na Nigeria. Macace da batace ga daga qasar da take ba,ta tarbesu cikin haba haba sannan ta fara serving nasu cikin kulawa,lokaci lokaci tana magana da fu'ad da hankalinsa ke waya cikin yaren Dhivehi,har ta kammala ta juya ta fita tana basu guri. Juya spoon din take kawai a plate din tana hadiye wani abu a qirjinta. Batasan meye ba amma ya tsaye mata a wuya. Bai ankara ba,sai daya gama uzurinsa da waya sannan. A mamakance yake dubanta. "Start mana madam....banason wasa da abinci fa?". "Itama fareedan ce?" Ta tambayeshi da wani salo daya sanyashi karantar zallar kishin dake kwance a idanunta,saidai kuma a sarari qwalla ce kwance saman oily eyes dinsa,sai suka qara wani sheqi. Dariya yakeson mata saboda wani irin farinciki yaji yana lullubeshi,tun daga saman zuciyarsa yana sauka ta kowanne sashe na gangar jikinsa. Har ya fara winning haka da wuri? Ya tambayi kansa yana taya kanshi murna,amma a bayyane sai ya lanqwasa fuskarsa alamun tausayi. "Me kuma nayi?". Muryarta na rawa kadan tace. "Kunata magana da yaren da banaji.....tanata maka hira kana amsawa?". Wannan karon kam kasa boyuwa dariyarsa tayi,abinda ya tunzurata kenan. " Karki wuce gona da iri sabreen,karki rudu ki fada soyayyar abinda ba yafi qarfin ajinki.....abinda yafi qarfinki,abinda baki da tabbas a kansa.....shin kin Manta maamah tana nan?". Tambayar data tarwatsa duk wani qwarin gwiwa da take qoqarin tattarawa kanta,taji kuma komai ya tsaya mata cak. Dab da ita ya dawo ya zauna,ya kama hannayenta ya saka cikin nasa yana matsawa a hankali. "Kin taba ganin mutum ya canza DUNIYARSA?" ya mata tambayar kai tsaye,qasa tayi da kanta don sai takejin tana son jefa rayuwarta cikin hadari ne kawai,muddin ta sakewa zuciyarta ta fada sonshi to ba shakka ta fada babban tarko......babban tarkon da zai bawa maamah daman walagigi da rayuwarta yadda taga dama. "Amsar itace aah......ke duniyata ce,babu daman na sauyaki ko na hadaki da wata ko wani abun......ni muhammad jadda naki ne ke kadai,don ke kadai aka halicceni.....ki rubuta wannan ki ajiye" _to zamu gani,anya hajiya maamah zata qyale kuwa???_ *ANNI* Tun a jam'in sallar asuba da sukazo yi taga bata ga fu'ad ba.....still da tace farouq ya turo mata shi komin dare baizo ba,har suka gama waya da abba Alhaji hamza kibiya dake tashi umrar ta kwanta amma ba fu'ad din ba dalilinsa. Sanda suka kammala sallar sai tayi zaune kawai tana lazimi,tunaninta yana rarrabuwa,bataga fu'ad ba......bataga sabreen ba,duka ina suka shiga?. Ta wata fuskar sai takejin relief na rashin ganinsu su duka biyun,don zuciyarta na qissima mata wani abu,ta wani bangaren kuma bataso ta sake jikinta akan hakan,saboda tasan wace mariya din. Takwas saura farouq ya shigo gaidata. Yana daga zaune gabanta ya dan dubi amna dake kwance tana shirin komawa bacci "Ta duba qur'aninta kuwa?". Kai anni ta daga masa " Ta duba" Sai ya jinjina kai. Wani sabo ne da raino data musu dukkansu,dole kowacce safiya....komai uzurinka ko meye kakeyi ka fara duba qur'ani kafin komai. "Kiramin fu'ad.....ka gwadamin dukka layukansa" Anni ta fadi tana gyara zamanta. "Na gwada wani tun jiya a kashe,amma bari na gwada sauran" Farouq ya fada hankalinsa kwance,don shi kam ya gama hasashen inda aka haihu a ragaya ma. Baya tunanin ko maamah ta yiwa fu'ad farin sanin da shi yayi masa. Daya bayan daya yabi layukansa yana kira amma kowanne gaya masa ake a kashe yake,sai ya daga ido kawai yana duban anni da fuskarta ta shiga damuwa. "To ina ya shiga?,ina kuma sabreen?". Dariyarsa ya danne yana dan saka alhini a saman tasa fuskar shima "Karki damu anni in sha Allah jikina yana bani suna tare,bari na tura masa email da SMS duka" Ya fada yana fara rubuta saqonnin ya kuma aike masan kaman yadda yace,duk da yasan zai wahala ya gani a kwanakin nan,lallai indai ya samu nasarar dauke sabreen ne tofa sai baaba ta gani. *MAAMAH* Idan tace hankalinta a kwance yake daga daren zuwa safiyar tayi qarya. Ta kirashi ta kirashi har batasan adadin sau nawa ba. Tabbas ta sani,a yanxu duk duniya idan ameenatu tace itace mahaifiya ga fu'ad,kuma tana tuhumarta batan sabreen ba wanda ya isa ya hana a daureta,ba wanda zai fiddata idan ba fu'ad din ba,da sauran mutuncinta,bataso wasan ya qare a haka,saidai hakan ya sake ninka qiyayyar anni sosai a ranta. Ita daya taketa shawa kanta alwashin saita yiwa ameenatu abu mafi munin da ba zata tabawa mantawa da ita ba,idan don tayi wannan ne don ta nuna mata iyakarta ne ganin suna qasar da ba tasu ba.....to tabbas ita kuma zata bar mata wani babban tabo a rayuwarta da ba zata taba mantawa dashi ba. Musaddiq ta kira ta sanyashi nema mata fu'ad din,saidai shima kiran duniya wayar sunqi tafiya. "Maamah wayoyinsa a kulle suke" Maganan data sake sakata a taraddadi da tunane tunane iri iri. "Kada fa ya zamana ameenatu ta salwantar mata da yaro ne takeson tayi garkuwa da ita akan batun haka da wuri?" Wannan shine tunanin daketa mata kai kawo. "Ya kamata ki xama cikin shiri.....ki xama a ankare.....karki nuna mata tsoronki,ki tabbatar mata da.naki zargin kema" Abinda zuciyarta take nanata mata kenan,wanda shine kuma ya bata qwarin gwiwa. Cikin kwanakin sai ya zamana wani irin zama ake a gidan,kallo kallo kawai akeyi tsakanin maamah da anni din. Duk da maamah tana cikin d'ari d'ari da tunanin inda fu'ad da sabreen dinma suke......amma ta azawa ranta wani dakiya. Ta fannin annin kowanne taku na maamah din saman idanunta yake,ba komai take dubawa ba sai idanun yaransu da suke rayuwa guri daya,zai zame musu wani abu na daban kuma na tashin hankali idan suka ga wani sabani muraran a tsakaninsu,banda hakan a shirye anni yake akan maamah wannan karon.....duk da tana danjin relief idan farouq na bata tabbacin fu'ad da sabreen din suna lafiya. Farouq din ya fahimci abinda ke faruwa,saidai bai nuna musu komai ba,yayi ma kaman bai sani ba,saidai time to time shima yana neman fu'ad din ta waya,amma dif kakeji ko sau daya bai taba katarin samunsa ba.....a haka sannu a sannu sai gashi an kwashe sati guda cif ba wanda yaji motsinsu ko yasan inda suke. Zuwa sannan hankalin anni ya tashi sosai,kusan kullum sai tasa farouq ya kira mata shi,mafi qaranci sau biyu a rana,saboda kwanakin barinsu Maldives kusan za'a ce yayi,kwana uku ko hudu suka rage musi,gashi babu shi ba sabreen din. Tun tana yiwa maamah din kara har abun yaci tura,ranar daya rage kwanaki uku subar qasar,da wani yammaci suna parlor. Amna ke mata kalba saman dogon gashinta da tafi masa kalba akan kitso,maamah tana daga gefe zaune tana kallo cikin tv. Ta tsiri wannan zamanne kawai don ta nunawa anni ba abinda zai tsoratata,hakanan itama me cikakken iko ce,duk da cikin rashin cikakkiyar nutsuwa itama take. Ba sabreen ce ma damuwarta ba danta shine damuwarta,idan tana da damuwa akan sabreen din bazai wuce na yadda take gudun kada anni ta fake da wannan ta tozartata a idon duniya ba. Farouq ne ya shigo da sallama,kaman yadda suke koyi da tarbiyyar anni da umarninta,ya yiwa maamah barka da gida,ta amsa masa a d'age kaman yadda ta saba. Mugun haushinsa takeji.....tana ganinsa a asalin tantirin munafuki tun daga quruciyarsa kawo yanzu,kai tsaye zata iya cewa shine kanwa uwar gami da yaja mata yaro cikin gidansu ya hadashi da mayun iyayensa da suka kasa sakar mata kurwar d'a,suka hanata taci arziqin d'anta yadda ya dace. Ko a yanzun gani take cutar fu'ad kawai yakeyi yana amfana da arziqinsa,yana tatsarsa ne shima.....ba wani tare da suka samo arziqin,ba kuma wai iya harkar noma da kayan abinci yake wannan fantamawar ba,dukiyar gold da diamond din d'anta ce. "Farouq......kwanaki uku suka rage mana mubar Maldives.....ka samomin 'ya'yana?" Tayi maganar cikin salon son isar da saqo ga maamah. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 104 104 Kalmar 'ya'yana din kuwa ta daki zuciyar maamah da wani matsanancin kishi. Wato har fu'ad dinma ya tashi daga sunan dan riqo ya koma danta?. "Aah anni....inata dai qoqari" Ya amsa mata yana fahimtar inda saqonta yasa gaba. Kai ta jijjjiga "Zan sabawa fu'ad kuwa muddin qafafunsa yasa ya tafi bai sanarwa iyayensa ba.....idan kuma wani keda hannu kan hakan....na rantse da Allah ko waye bazan barshi ba.....tashi kaje,tsakanin yau da gobe nakeso ka lalubomin shi" Kai kawai kada mata yana tashi,maimakon ya koma daki sai ya juya yana sake ficewa a gidan. Yau din Jordan ya nema kai tsaye,shima ya gaya masa tun randa suka fita tare bai sake ganinsa ba. Ci gaba yayi da bibiyarsa ta waya amma a banza,sai ya koma ya lalubi system dinsa da yakan ajiye schedule nasa da komai. Yasan password nasa da komai don haka kai tsaye ya bude ya shiga. Zallar aminci ne da yarda da kuma dawwamammiyar qauna,shima iya abinda yaje nema ya shiga ya duba kawai ya fito. Bai samu bayanin komai ba,hasalima bai ajiye inda zashi ba banda ranar da sukayi zasu fita din satin baya daya wuce ranar daya bace kenan. Awa daya ya bawa ransa zai sake kiransa,idan bai sameshi ba kuwa aikin safa da marwa ya sameshi cikin tsibirin Maldives,wala'alla sai yayi hayar boat ko skis ya gewaye tsibirin Maldives ya nemowa anni 'ya'yanta. "Oops.....wannan soyayya taku nima ta jefani kwale kwale.....where are you?.....anni ke kika jawo,da kin damqa masa matarsa salin alin dani kaina ban tsinciki kaina a halin da nake ciki ba" Ya fada yana furzar da iska daga bakinsa gami da yin relaxing jikin kujera yana lumshe ido. Murmushi ne kuma ya qwace masa saboda hango fuskar maamah da yayi,tayi wani laushi da yaushi ba tare data fahimci hakan ba "Wato anni kema kinsan takan tsiya?" Ya fada qasan ransa yana komawa ya kwanta sosai saman sofa din. ★Gaba daya ya wani narke saman sofa din bayan ya miqe qafafunsa saman table din gabansa daya dora system dinsa. Tun dazun ya kunna system din amma ya gaza saka mata password ya budeta. Sai yau yakejin ya kamata ko farouq yasan inda yake,don yayi imanin ko kowa bai nemesa ba anni zata nemesa,zata kuma damu da rashin ganinsu. Gilmawarta kadai a gabansa yana debe hankali daga gangar jikinsa,a kwanakin nan shi kansa yasan mahaukacin so yake mata wanda baisan adadinsa ba. Idan ya kebe yana salla,yana yawan tuhumar kansa wanne irin so yake mata wannana?,abu daya ke sanya masa relief addu'o'in daya debe tsahon rayuwarsa yana yi akan. "Ya Allah,idan ka tashi dasamin soyayyar wata 'ya mace.....ka jarabceni da soyayyar da zan iya.....ka dasamin soyayyar macen data dace dani ta dace da rayuwar 'ya'yana,macen da zata soni itama sama da yadda nakeson kaina....macen da ni karan kaina takeso ba abinda na mallaka ba.....macen da zata fifitani sama da kowa da komai....tsaftatacciyar mace.....kamila aaqila....aabida,ya Allah,kada ka jarabceni yadda ka jarrabi mahaifina......ubangiji ka azurtani nida dan uwana da matayen da zasu rufe ciwukan da suke cikin zukatanmu kaman yadda kayi mana baiwa da samun anni". Idan ya tuna wannan addu'ar sai yaji son da yakewa sabreen din ba komai bane.....yayi imanin Allah bazai wofantar da addu'ar da aka dauki tsahon lokaci ana qwanqwasa qofarsa saboda ita ba. Duk wasu kaya nata tunda sukazo wajen tayi bankwana dasu,daga kayan safiya zuwa na dare duka tana shigarta ne a bisa zabinsa. Tun tana dojewa har ta fara ragewa,don idanma tace zata musa shi zai tubeta ya kuma sanya matan. Yayi amfani sosai da damarsa......yayi amfani da tsoronta da gurin ya mata wani irin sabo da kwana a jikinsa,ya sanya wata shaquwa me qarfi a zuciyarta da wannan. Ranar farko da hakan ta fara kasancewa..... Tayi wani irin bacci da idan zata iya tunawa irin baccin qarshe da tayi saman cinyar ummenta ranar da asthma dinta ya tashi. But bacci cikin jikinsa yana da wasu qa'idoji da ta kasa kiyayesu har yanzu. Wani sabon abune kwanciya hakanan ba tare data rabawa jikinta komai ba....shi kuma kullum sai ya maimaita mata bayan ya maidata yadda yake "That's my rules". Daga qarshe wayo yake mats,wayon da yake sanyawa washegari ta tashi da matsananciyar kunyarsa da bata iya hada idanu dashi. Duk yadda taso ta gano yadda yake iya cimmata ya firgitata ya fiddata daga saitinta ta kaucewa wannan abun amma ta gagara......wani lokaci har jira takeyi yayi wani motsi don tayi masa tawaye.....to amma da an iso gurin sai ya sanyata ta manta wacece a ina kuma take?,sai bayan qura ta lafa ta isheshi da kukan banza da qorafi. Wani lokaci ya biye mata ya lalace wajen rarrashi.....wani lokaci kuma yaja hancinta "Har yanzu baki fara koyan maida martani ba......am dreaming about it,saikin gama kwashe alkhairan kuma ayitamin kukan abunga...." Gulma tason yakeson cewa,fadi ne kawai bazaiyi ba. "Sabrrrr" Ya kirata jikinsa yana sake macewa. Wani irin Palazzo ne a jikinta da wata 'yar top data zauna mata sosai a jikinta,ta kuma bayyana masa albarkatun qirjinta yadda yakeso. Kanta yasha hair pins wanda shi ya zauna ya shiryata,ya kuma gyara mata kan yadda yakeson gani. Yasha wahala sosai wajen nesanta kanshi da mata,ya kame kansa,ya runtse ganinsa ya kuma kiyaye al'aurarsa.....wannan ya sanya yaci alwashin ko meye dake burgeshi game da mace sai yayi qara'insa a jikin matarsa......sai ya kalla yadda ranshi keso. Yana ankare da ita a takure taka,yasan zaayi hakan,don shima ko sau daya bai bari idanunsa sun huta da kallonta ba. Duk sanda yaga dari darinta akan sakin jiki ga d'a namijin da ya kasance mijinta sai yaji wani qunan rai da bacin rai ga wadanda suka dinga sadakar mutuncinta,suka kuma dangantata da sunan KARUWA. "Zo kiji" Ya fada a galabaice yana miqa mata hannunsa sanda tazo gilmashi. Baima bata lokacin tunani ba ya sanya hannunsa ya jawota saman cinyarsa yadda ya saba mata. Sam bata masa nauyi wajen dauka ko jawowa,kaman wata leda yake daukanta. Matseta yayi a jikinsa yana rungumeta sosai,ya kuma dauko system din ya aza saman cinyarta yana saka password dinsa. "Massages nakeson dubawa amma gaba daya kin hanani sukuni.....sai rarrabamin hankali kike,gwara ki zauna mu duba tare,wataqila nafi samun nutsuwar dubawar" "Me nayi kuma?" Ta tambaya a shagwabe. Hancinta yaja yana kashe mata idanu "Aah hajiyata....komai mafa kinyi.....satar da kikayi a gangar jikin muhammad fu'ad.....zuciyarsa dinnan ta tafi kenan,bana jin zata dawo masa har abada" Ya fada yana sakinta gami da fara buda saqon farko wanda ya sakashi sakin murmushi ganin saqonnin farouq a jejjere a jejjere. Na qarshen ya fara budawa wanda bai wuce mintuna talatin da turowa ba. _"You're rocking the boat,you're fanning the flames.......dude.....ka shiga hankalinka ka dawo gida.....yaqi zai barke tsakanin ummominka.....am serious dude"_ shine saqon qarshe daya gani mintuna talatin baya. Dan murmushi ya saki yana tabe baki,yasan abinda farouq zai masa qarya.....ya kuma san wanda bazai masa qarya ba,wannan statement din nashi yasan real ne ba wasa yake masa ba,sai ya danna replies ya soma bashi amsa _"Step back BB.....leave them.....nasan anni ba zata biye abun yayi worst ba.....ina nan ina neman hadin kan DUNIYATA.....zamu hadu a airport ranar Tuesday to makka in sha Allah"_ yana tura masa ya koma duba ragowar saqonni masu muhimmanci yana ragewa,saidai kusan bayan kowanne minti daya sai ya tura kansa cikin rigar ta. Tureshi tayi har sau biyu,ana ukun yayi warning nata "Idan kika sake ban yafe ba" Idanunta dukka ta fidda idanunta waje tana dubansa a mamakance,rai ya hada "Yes....aikin karanta walau alattanur ko wajen rumaisa?" Qasa tayi da kanta tana tunawa da hadisin,ya kuma aza mata wata irin kunyarsa sosai. Yadda yaga tayi ya masa dadi.......da gaske karatun yana kama zuciyarta har haka,tsaf fa zai iya komawa wajen malam ci gaba da daukan karatuttukan da zasu sanyashi sake sanyata ta sake zama sassanya.....buqatar maje haji sallah. Yadda tayin ya bashi daman dauke hannuwansa daga can system din ya maida inda yafi muradi da wani tattausan yanayi yana sake shigewa jikinta. "So kike na zama dan is......" Batasan ta saka tafin hannunta saman bakinsa ba.....batasan sadda hakan ta kasance ba sai data tsinciki narkakkun idanunsa cikin nata,hakan sai ya zama kaman wani lasisi ta bashi kenan daya sakashi yunqurawa dauke da ita,daidai sanda saqon farouq da mamakin fu'ad din ya kasheshi ya shigo system din,ta baya ya saka qafa ya tureta ba tare daya damu da idan ta fadi zata iya fashewa ba "Just leave me have this moment,don't dampen the mood" Yayi maganan kaman wanda yasha giya ya maku,saidai duk da hakan abun mamakin shine,sanda ya mata masauki saman tattausan gadon da harshensa dake hardewa yace da ita. "Let me relish this moment,and then I'll tell you more about fu'ad. Ya kamata kisan waye fu'ad......am ready to make you DUNIYATA da gasken gaske.......inason kisan komai nawa da gaske......". *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 105 105 _Barkanmu da dawowa,fatan munyi sallah lpy,ubangiji ya maimaita mana cikin lafiya aminci da kwanciyar hankali_ Batasan me yake tsarga mata ba duk sanda ya kirata ta DUNIYATA ba,wani irin feeling takeji yana motsa zuciyarta,wanda tun tana qaryatawa har ta soma yarda tana jin wani abu a ran nata duk sanda ya ambaci sunan. Yafi mata dadi ya kirata DUNIYATA akan ya kirata my world. Susutacciya ya maidata yadda ta fahimci ya soma maidata a wadannan kwanakin,lallai so yake sai ya matso komai a kansa dake cikin zuciyarta. Ta sani tabbas muddin zaici gaba da wannan salon......muddin zaici gaba da tafiyar da ita da wannan tsumammen yanayin to ba shakka zata gaza boye duk wani abu dake zuciyartata kuwa.......yana kuma dab da maidata mahaukaciya da gasken gaske,zata rasa duk wannan dauriyar tata da basarwa da takeyi. D'aya bayan daya ya dinga zare hair pins din da dama shi ya zauna ya jera mata su,duk daya idan ya zare yana ware gashinta me tsaho baqi da santsi,wanda zuwa yanzun hair mist dinsu shi da ita ya zama guda daya,kaman yadda mayataccen mouth fresh dinsu ya zama products daya. Kusan komai nata cikin kwanakinnan ya canza mata zuwa kalar wanda yakeso,qamshinta,creams lip gloss da komai ma......komai kuma me tsada ne fiye da tunaninta,ranar data duba kudin perfume din daya sauya mata zaune kawai tayi tana binsa da kallo ba tare da yasan ma me ake ba. Su huda na wata duniyar duk da tayi imanin suna cikin kulawa......amma ita tana nan tana rayuwar da take ganin tafi qarfin matsayinta?. Sai daya zare mata duk pins din,sannan ya kutsa yatsunsa cikin sumarta yana barbazata yadda yakeso,ta fahimci tana daya daga cikin abubuwan da suke matuqar burgeshi ga diya mace. Kaman yasan abinda yake saqawa muryarsa me kama data mashaya ta sauka a kunnenta "I love it duniyata......kina da komai da nakeso..... Please ki sake bani dama na gina miki wasu dabi'u.......na dade ina kame kaina daga kallon Haram da kuma zina.......i only want my pure halal.......please ki qarasa mallakamin kanki da rayuwarki gaba daya I want the best from you,i want the best relationship with you" Ya qarashe maganar yana mata wata kyakkyawar runguma kafin ya fara maidata birkitacciya yana cireta daga ainihin tunani nutsuwa da saitinta. Batasan wanne abu daban yake buqata daga gareta ba.....batasan wanne best yake nema ba bayan duka fitar da ita daga tsarinta da yakeyi. Yana sakata jin wani irin nauyi da kunya da bata taba tsintar kanta a ciki ba. Ko yanxun da qura ta lafa tana gaban madubi yana tsaye a bayanta yana bata dan kunnenta tana maidawa daya bayan daya,ya kafeta da idanu murmushi na fita daga kan fuskarsa qasa qasa. Idan yana kallon fuskarta a irin wannan yanayin sai komai ya dinga dawo masa. Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa kaman zai fashe don tsananin cika da qaunarta da sukayi,yadda yakeji a duk sanda suka kasance da juna.....yasha imagination abun idan tana participating itama,yana kwadayin yaga wannan lokacin. Taku uku ya qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya dora fuskarsa saman kafadarta yana dubansu a tare shi da ita ta fuskar madubin. "Idan Allah ya bamu 'ya'ya......wanne irin kyau xasuyi my world?". Wani kunya ya saukar mata,tayi qasa da kanta qaramin murmushi yana subuce mata. Shima murmushin ya saki,a duk sanda kunya haka ta bayyana saman fuskarta tana mata wani irin kebantaccen kyau na musamman. "DUNIYATA.......Why aren't you responding?" Idanu ta daga alamun tambaya ba tare data yarda ta kalli tsakiyar idonsa ba. Ya fahimci haka,sai yasa yatsunsa yayi gefe da gashinta yana cusa bakinsa ta kunnenta abinda ya sanya tsigar jikinta tashi. "On bed dear......" Ta fahimci inda ya dosa,don haka bata bari ya qarasa bama ta soma neman inda zata boye fuskarta. Ire iren rashin kunyarsa suna sakata jin wani irin nauyi ba kadan ba. "Ko sai randa aka yanke shawarar ana sona ko ba'a sona?" Ya sassauta muryarsa yana fadi qasa qasa gami da riqe hannayenta da kyau qaramin murmushi yana subuce masa. "I hope wannan ranan zata zo soon.......na matsu,ko akwai wani abu da ake buqatar nayi da za'a gayan I LOVE YOU MUHAMMAD FU'AD JADDA?....." Ya tambayeta da gasken gaske,har qasan zuciyarsa yana sha'awan jin ta fadi hakan. Kai ta girgiza tana basarwa,neman tserewa takeyi ya kuma fuskanceta,don haka ya sunkuceta kawai yana nufan stairs din da sukayi dakin qasa. Idanu ta fitar waje,har ha Allah tsoron dakin qasan nan takeyi,yatsa ya saka ya lakuce mata hanci yana girgiza kai. "Relax.....you're safe my world.....bazan taba yin wasa da DUNIYATA ba fa". Kasa ce masa komai tayi sai idanu data lumshe tana shaqar daddadan qamshinsa daya cika mata hanci,ta kwantar da kanta a qirjinsa tana jin bugun zuciyarsa. Batasan me yasa ko yaushe bugun zuciyarsa daban yake ba,wani bugu ne me sauri sauri wanda tasan qa'idan bugun baikai haka sauri ba. Idanunta saman dakin duke kallo,yadda ruwa yake gudu saman kansu tare da kifaye kala kala ba tare da ko damshin ruwa ko qwaya daya ya tabasu ba,ta dauke idanu tana tasbihi ga ubangijinta. Saman lafiyayyen gadon dakin ya ajiyeta,ya dawo gabanta ya tsugunna yana zagaye hannuwansa da qugunta. "Muhammad fuad jadda.......d'an alhj Muhammad ne,haifaffen bafulatanin mambila......,ta gefan mahaifiya kuma...." Sai ya danyi shuru yana hadiyar numfashi. "Mariya da akafi sani da maamah itace mahaifiyata.....bafulatanar mayo belwa ganye local government" Hannuwanta ya riqe a tausashe cikin nasa zuciyarsa na karyewa. "Lokaci na farko da zan bude bakina na fasawa wani dan adam daban rayuwata.....waye ni?....me naji me na fuskanta?.....sabrrrrrr.....abbana......abbana yana cikin jerin sahun mutumin da nafiso nafi qauna kaf cikin rayuwata.......saidai mun rasashi a sanda mukafi qaunarsa......mun rasashi a sanda mukafi buqatarsa......mun rasashi saboda wa'adinsa ya cika.....amma da taimakon maamah". Kai ta daga tana dubansa,tana ji yana tayar mata da wani mikin ciwo dake zuciyarta. Kai ya gyada mata idanunsa suna sauya launi. "Ta shayar dashi guba......ta dura masa miyagun maganganu da suka qarasa illata gangar jikinsa da zuciyarsa,suka Haifa masa da ciwon zuciya......kalmomin bakin maamah su suka jefa abba na a matsanancin ciwo......ciwon da haquri ya gadar dashi dashi,ya kuma ci gaba da tara masa guba na maganganun da suka zama silar fashewar zuciyarsa daga qarshe. Tun a gaban idanunsa muje ganin qasqanci da wulaqanci,ba wanda yake samun tausasawa ko kulawa daga gareta,daga shi mijinta harmu 'ya'yanta......bazan boye miki komai ba......bamusan dadin uwa ba,bamusan wani abu da ake kira dadi tsakanin mahaifiya da 'ya'yanta ba,mun rayu tamkar irin rayuwar da bawa zaiyi a hannun ubangidansa,walwala 'yanci da farinciki dukka yayi mana qaura,mun rayu tamkar agololi kuma 'ya'yan riqo......abbanmu kuma ya zama tamkar wani yaro gida bame gida ba......ba abinda tafi bawa mutunci da kima sama da KUDI sama da tayi KUDI sama da abbanmu dole ya zama me KUDI ya nemo KUDIn da zatayi kalar rayuwar da takeso,yayi lafiya ko kada yayi......ya rayu ko kada ya rayu,muyi lafiya tarbiyya ilimi mu tsaftatu mu qoshi duk basa cikin lissafinta,abinda ya dameta shine KUDI.....sabrrrrr..... Mun rayu cikin qasqantacciyar rayuwar da al'umma suka gaza janmu a jiki a garin da bamu da kowa,kowa yana ganin tunda wadda tayi silar zuwanmu duniya ta gaza tallafawa da tausayawa rayuwarmu,lallai mudin akwai wani abun aibu ne a tattare damu. Taji a rant ba zata iya rayuwa damu ba,ba zata iya zama damu bs,ta watsar damu da abba dake buqatarta saboda matsanancin ciwon zuciya dake sake kwantar dashi....duk inda abba bai qwallafa rai a soyayyarta ba,tayi nesa dashi shi yafi alkhairi,kunnuwansa xasu daina kwana su wayi gari da jin munanan kalmominta a kansa wanda hakan shizai bashi lafiya da wuri.....saidai kuma sonta ya zame masa jarrabin rayuwa,ya kasa haqura da nesanta kanta damu da tayi,ya sake zame masa silar hauhawar ciwonsa. Nayi kwasar kashi......nayi aikin bola da hannuwana duk don na kula da musaddiq da abbana......nayi sharar kasuwa nayi ta kwata har bansan iyakarsu ba kawai don na samo abinda xan kula da abbana da musaddiq.......munci abincin bola saboda gudun yunwa kada ta halakamu.......na kwana da GAWAr abbana.......na kwana da gawar mahaifiyar abbana JADDA saman cinyata dukkansu ba tare da nasan mutuwa sukayi ba ko bacci?,naci gaba da gadin gawarsu ba tare da nasan ya akewa gawa ba?,a shekarun da duka duka baifi a koreka daga bakin gawa ba idan kana da gata don kada kaga abinda shekarunka basukai ba. Jadda tazo mana da wani irin gata da muka dinga tunanin wahalarmj ta yanke......ta saida duk komai nata don tazo ta kula damu......ta bamu wani jin dadi wanda ko maamah da tayi silar zuwanmu duniyata tsahon shekarun da mukayi tare da ita bata taba bamu irinsa ba. Saidai sanda muke tsaka d wannan tunanin ashe ragowar kwanakinta na rayuwa yazo qararwa tare damu ajalinta yazo mata a kusa.....ta sake kwanciya ta barmu a wani irin yanayi. Daga sannan muka sake gane meye ma'anar rayuwa?,muna ta tunanin maamah zataji labarin komai......zataji tausayinmu ta dawo garemu amma inaaa......wanda yayi nisa bayajin kira........wata kalma da maqocinmu ya fada a kanta sanda ya dawo daga kudu yace mana ya ganta a can.......taqi barin raina da zuciyata.......har yanzu da ita nake kallonta.......bansan ranar da zata bar zuciyata ba.........maamah dinnan dai da daga qarshe naji duk duniya ba wani abu da nake qyamatar ya kusanci inda muke......itace silar mutuwar abba......ke daya kikasan wannan a duniya......na kamata har sau uku tana ciyar dashi da abubuwan da likita ya hanashi ci saboda suna tunzira ciwonsa.......suna kuma iya sanyawa komai ya faru dashi ciki harda rasa rayuwanshi......a dukk ukun nan dana kamata tayi alqawarin ba zata qara ba.....mantawa takeyi ne......na fahimci abinda ya sanyata take aikata haka ta hirarta da qawarta da har yanxun nake tunanin kamar matar nan harira da suke tare ne......so take ta kashe auren,so take abbanmu ya saketa shi kuma yaqi......tace tana buqatar tayi arziqo,tana buqatar freedom amma yaqi sallamarta....wannan shine dalilinta......shine kuma silar tunzurar ciwonsa har ya kaishi ga kushewarsa......ba ita ta kasheshi ba kenan sabrrrrr?" Yayi mata tambayar da wani irin yanayi daya tsorata sabreen qwarai da gaske.......yanayin da yake tabbatar mata wani abu ne guda daya da yake masa ciwo har yau har gobe a zuciyarsa......salon tambayar data tabbatar ya jima yana so ya yiwa wani dan adam ita......amma rashin jin kowa a matsayin na kusa da zuciyarsa sosai ya sanya ya gaza furtawa kowa,yadda yayi tambayar kaman hankalinsa na neman gushewa daga jikinsa sai ta kama kafadarsa da kyau tana riqewa kuka yana shirin qwace mata......tana jin ashe suna da yawa irinsu wadanda suka rayu cikin wulaqantacciyar rayuwa?......amma dashi dake da sauran uwa a raye........dasu da ba ko daya ga dangi masu tsananin jifa da zumunci waye yafi rashin sa'a. "Sabrrrr" Ya rigata sakeyin magana duk da tana buqatar magana dashi. "Idan kika gwada yimin abinda maamah ta yiwa abbana......nima mutuwa zanyi kaman abba.......saboda na fahimci zuciyata irin tashi ce......bamu iya soyayyar qarya ba,bamu iya soyayya da wasa ba,bamu iya yiwa masoyi qaramin riqo ba.......a halittarmu yake.......wannan ya sanya na tsani soyayya na kuma tsani kowacce 'ya Mace......anni ce mace qwaya daya data fara samun qauna irin ta uwa daga gareni bayan faruwar komai......amma hatta da amna bata samu komai daga gareni ba sai sanda naga tana shirin mutuwa ta barmu........bazan jure ba sabrrrrr idan kikace zaki gujeni......bazan iya dauka ba idan kika ce zaki barni sabrrrrr,da gaske nake nima mutuwa zanyi" Ya qarasa fada muryarsa da dukkanin jikinsa suna wani irin rawa,tabbacin ya tabo mikin da baida kamarsa a rayuwarsa. Gaba daya sai ta rude,ta rasa yadda zatayi dashi,ga wani irin ciwo daya tayar mata wanda baida magani illa itama tabar hawayen idanunta su sauka ko xata rage abinda takeji tsakanin qirjinta zuwa zuciyarta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 106 106 "Kasan wace sabreen din da kake muradin ta tabbata a matsayin taka?". Ta fada muryarta na yayyankewa. Wani kyakkyawan riqo yayi mata yana sakata cikin jikinsa. "Na sani......na sani,iya abinda kuma na sani a kanta ya isheni yanxu haka......abinda ya ragemin ME YASA WANNAN TSAYAYYAR SABREEN DIN sauri bada kai ta yarda da wannan muhammad jadda din?,shima bana fatan kiban labari,da kaina zan lalubo......duk wanda keda hannu wajen maida sunanki wancan mummunan sunan baxai shaba.....sai na hukuntashi" Ya fada jikinsa na daukar rawa gaba daya. Luf sukayi a jikin junansu,kowa yana qoqarin controlling yanayinsa,sannu a hankali yanayinsu ya fara daidaita,saidai kuma a hankali taji jikinsa yana daukan wani irin dumi......kafin kace meye wannan zazzafan zazzabi ya rufeshi me tsananin zafin da har cikin fatarta da tsokarta takejin zafinsa. Rudewa tayi sosai,ta fara qoqarin zamewa daga jikinsa tana fadin. "Zafin yayi yawa......yayi yawa ka bari a samo magani". "Banaso ki kira mana kowa a gida.......inason kwanakin nan biyu da suka rage nayisu dake.......banason kowa ya shigo tsakani" Ya fadi dumin numfashinsa yana saukar mata saman goshinta. Kai ta girgixa hankalinta yana tashi. "Jikinka yayi zafi da yawa...akwai buqatar temperature din yayi qasa". Sake sanyata yayi a jikinsa ya lullubeta da kyau "It's not......haka fever na yake......zai sauka" Ya fada yana lumshe idanunsa duk kuwa da cewa yau zazzabin na daban yake jinsa,don har kusan cikin qasusuwansa yakeji kaman ana karyasu,saidai kwanciyarta a jikinsa yafi masa komai a yanzu haka. ★Shi kadai ya dinga dariya sanda saqon fu'ad ya tarar dashi. Hannu yasa yana shafa kwantaccen sajensa yana duban saqon yana sake karantawa. Wato ko yaya kusanci yakai tsakaninka da iyaye akwai sanda soyayya da matar aure ke diban nasu kason idan kusanci yakai kusanci. Bai taba tunanin akwai sanda fu'ad zai nemi kebewa shi daya ya barsu tsahon kwanaki ba tare da ya buqaci kowa yasan inda yake ba....ko ya rabi kowa ba. A nutse ya maida masa amsa sannan ya juya akalar motar yana komawa gida don bawa anni saqon d'anta. Fitarsa dama kenan daga gidan yana tsammanin zai iya samunsa a wani gurin,amma yanayin amsarsa kawai ya tabbatar masa ba zai ganshi ba koda ya shiga neman nasa. Suna dab da kammala kalbar da amna kewa annin ya shiga parlor din,yadda ya barsu a daxun haka ya samesu,kowa zaune yana sabgar gabanshi. "Anni.......sai kisa haquri,ba zaki samu ganin yaronki ba sai Thursday a airport,haka yacemin" Ya fada yana daga kafadunsa. Maganan farouq taja hankalin maamah duk da bata waiwaya sashensu ba bata kuma nuna taji abinda suke tattaunawa ba,ta riqe waya kawai a hannunta kaman tana daddannawa amma maganganunsu take saurara. Qaramin murmushi anni ta saki,iya bada saqon da yayi a gaban maamah dinma ya wadatar mata,tabbas zai isar mata da wani muhimmin saqo,duk da ta san farouq din ya fadi ne kawai ba tare da wani nufi ko wata manufa ba,ya fada ne kanshi tsaye. "Indai suna lafiya alhamdulillah,lafiyarsu tafimin komai" Sosai maganar ta soki maamah,ta tattaro wani yawu me tauri ta hadiye da qyar tana qoqarin daidaita numfashinta. "Na rantse da Allah yadda kika dasa baqinciki cikin rayuwata.....saina dasa miki fiye dashi a taki rayuwar......indai har ban aikata haka ba lallai ba shakka ni mariya 'yar zina nake" Ta fada cikin zuciyarta wata wutar daukan fansa tana ruruwa cikin zuciyarta. A yanzun inda za'a bata bindiga.....aka ce ta kashe maqiyinta qwaya daya da tafi tsana a duniya.....to xata nemo harsasai guda biyu ne,ta kashe Alhaji hamza da ameenatu.....harsashinta na ukun kuwa muddin ya samu to sabreen ce ta gaba. Tayi imanin bariki ce zallah......zallar barikice ta sanyata janye mata yaro,wannan dukka plans din yarinyar ne,ita ta shirya ta tsara ta kuma gabatar,amma indai da numfashi a gangar jikinta saita gaya fahimtar da ita tazarar shekaru a rayuwa ba qarya bace,dukkan wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi. Har tana niyyar miqewa ta wuce dakinta,don ba abinda take gani a parlor din face abinda zai daga mata hankali yakuma sake tunzura mata zuciya,sai ga musaddiq ya shigo. Ta dauka itace mutum na farko da zai fara gani,tayi zaton itace ta farko da zai fara zarcewa wajenta,saidai gaba daya hankalinsa yana kansu anni. "Lalala....waye ya saki kitso?" Musaddiq ya fada yana fito da idanunsa waje ba tare daya lura anni takewa kitson ba. Kwabe fuska kuwa tayi tana nuna anni da bata ganinta da comb din hannunta. "Nice nan dan gidanku" Anni ta fada tana hade rai,saidai kuma qasan hade ran nata murmushi ne boyayye a kwance da zaka iya karantarsa. "Ai banga ke bace" Ya fada yana shafa kansa yana saukar da ganinsa qasa gami da qoqarin boye damuwarsa. "Maza ka qarasa sakaltata.....tunda shi wancan yayi gudun hijira......nidai wallahi karku sakani cikin masu yiwa mijin da zata aura bayanin sangartacciyar da zai aura ahto" Farouq ya fada yana miqewa gami da jifan musaddiq da harara. "Basai kun wahalar da kanku ba BB.......mijin yafi kowa fahimtar wacece ita.... Lafiya qalau ba wanda zaiji bari ya gani" Musaddiq ya fada kansa tsaye yana aje dubansa kan fuskar amna. Maganan yadan tabata,sai ya hade mata da jin nauyi,bakinta yayi murus tayi qasa da idanunta tana tsaga kalban anni din. Ganin haka sai shima ya juya xai fita,sai a sannan subutar bakin da yayi ya dawo masa. "Kan uban buhun babbakun bala'i" Maamah ta fada tana jin numfashinta kamar zai tsinke daga hunhunta yayi qaura yabar gangar jikinta. Ba ita kadai ba,kusan duk wanda yake wajen ya dauki haske,saidai nasu kyawawan zukatan cika sukayi da farinciki duk da basu nuna hakan kai tsaye ba. "Kai musaddiqu!" Maamah ta fusgi sunansa da wani irin sauti sanda yake bin bayan farouq xasu fice a falon. Farouq din bai dakata ba ya fice abinsa,sai musaddiq daya tsaya sannan ya dawo da baya. "Ban ganki ba kina falon ashe.....barka da yamma". "Don uban banka ta yaya dama zaka ganni?,ai ba zaka taba ganina ba daman tunda idaniyarku ta jima a kulle,amma aidaka shigo kaga qannen uwarka da yayyen uwarka rututu ko?". Maganan ta masa nauyi qwarai,bayaso kuma taci gaba a haka,don yasan inda qarshen maganar xata tsaya. "Ba'a canzawa tuwo dai suna wallahi.....komai tsahon xamani da shudewarsa dole abar masa sunansa.....dole kuma abar masa siffa da kamarsa........kasan me yasa na tsaidaka?" Ta tafi Kai tsaye ga abinda yake tsunkulin zuciyarta. "Inaso na gaya maka ka shaidawa dan uwannaka........ban haifi yaron da xai yiwa kansa zabin matar aure ba,yadda na kawoku duniya ba tare da shawarinku ba......haka zan zabawa kowanne days a cikinku kalar macen da tayimin.....ba kuma uban daya isa ya hanani tunda ba adopting naku nayo ba,haka ba tsintoku nayi ba.......mutum ya sabamin kuma daidai nake dana tsine masa albarka sai me?,da can ma aina rayu babu shi......tashi ka bani waje shashasha wand baisan gurin dake masa ciwo ba". Tsam ya miqe kamar yadda ta buqata,zuciyarsa na masa wani irin bugu kaman zata balle qirjinsa ta fito,a haka ya lalubi hanya ya fice yana fatan samun wadayacciyar iska da tafi ta parlor din yawa. Ko sanda zata gama da farouq tuni anni ta jima da wucewa dakinsu ita da amna,suna shiga anni ta maida qofar ta rufe,idanunta zube saman fuskar amna da yanayi na tuhuma take kallonta. "Amna!,kalleni da kyau!!" Anni ta fada adan tsawace tana budewa amna dukka girman idanunta,abinda bai taba faruwa ba tsakaninsu. "Akwai wata alaqa ta daban bayan ta yaya da qanwarsa tsakaninki da musaddiq?" A dan tsorace amna ta daga kai ta kalli anni,wani irin tsoron annin ya mamayeta abinda bata taba ji ba a kanta tunda ta haifeta. Koda cikin tsoro take muddin anni na gefenta tana samun aminci,amma yau annin ce abar tsoron da kanta. "Tambayarki nakeyi kinyi tsaye kina qaremin kallo" Anni ta fada bayan ta lura da yadda zuciyar amna kr bugawa. Ba zuciyar amna kawai ba,itama tata zuciyar bugawa takeyi......tana bugawa bawai don tsoron mariya ko tsoron abinda zata iyayi bane.....aah,tana bugawa ne saboda tsoron fitina. Bata qaunar wata fitinar sam a shekarunta da suka fara turawa,ko a yanzunma a haka addu'a take Ubangiji ya ganar da mariya......yasa ta fahimci rayuwa a zahirin yadda take. "Bab......babbu anni" "Kin tabbatar?" Ta sake tsareta da tambayar tana dage girarta duka sama. Kai ta gyada mata a sanyaye,ba kuma don wai tana da tabbacin ba. "Idanma baki da tabbacin inaso ki samoshi a duk inda yake,gina alaqa mukeso ayi bawai a sake rusata da sabuwar matsala ba" Tana kaiwa nan ta wuce cikin dakin tabar amna da tarin nazarce nazarce cikin kwanyarta,tsoro da fargaba suna cikata,tana jin kamar wani farinciki yana dab da barin rayuwarta. ★Tsakanin jiya da yau gaba daya zazzabinnasa kusan cikin jikinta yayishi,jinyar tasa da komai nasa ya nadeta ya hanata aiwatar da komai,sallah kawai ke tashinsu. Duk wani motsi nasa idan ta kalleshi labarinsa ke mata yawo,duk da tanajin akwai ragowar side da bai gama cika ba,tana tsananin buqatar jin yadda anni ta iya riqon kafaffen mutum irin fuad ta maidashi cikakken mutum haka ta ruwan sanyi,tanata jera labaran nasu......tanason banbance shi da ita waye yafi wani fuskantar qalubale?. Ta wani fannin gaba daya ya aza mata nauyinsa,ya narke mata ya zama wani shagwababbe shagwababbe za'ace?. Wannan narkewar tasa kuma ta fahimci yana sake amfani da ita ne yana budewa kansa wasu rufaffun qofofi dake cikin lungunan zuciyarta. Yanayin kallonsa me sanyata tana jin kamar zata narke ne......ko yaya ya riqe mata hannu sai taji kaman ta mallaki farincikin duniya ne dana lahira,kwana cikin jikinsa ya zame mata wani abu na musamman ga gangar jikinta dama zuciyarta,ta yadda komai nauyin baccinta.....muddin ya saketa ko ya matsa daga jikinta sai nata barcin yayi qaura. Ta fahimci wani abu tattare dashi,yana da tsananin ibadar da duk riqon da zazzabin yayi masa hakan baya hanashi tashi sallar dare,hakanan ko meye yakeyi idan time na sallah ya shiga xai ajiye yaje yayi,koda itace cikin jikinsa duk yadd yake mararin jinsa tare da ita to zai ajeta gefe sai ya bada farillan nan ya hada da nafilar kafin ko bayan kowacce sallah. A hankali sai taji wani quruciyar data rasa sanadin hawan girma kanta tana dawo mata. Ita dinma saita sake zama wata sakaltacciya,zuciyarta ta koma baya can sanda take da gatan ummienta da abbanta. A safiyar ranar alhamis dinne ya bude dukka wayoyinsu shi da ita,duk da shi din taga kaman kwana biyu yana buda wani dan qaramin abu shi ba tab ba shi ba system ba yana fita outside deck yana zama yayi wayoyin da batasan da waye yakeyi ba. Ita ta fara shiga tayi wankanta a sannan yana salatud dhuha kafin ya kammala. Tasan muddin ya kammala zaice saisun shiga sunyi wankan nan tare,abinda ta kasa sabawa har yanzu,saidai idan Allah ya bashi sa'a yayi mata kutse,takanji kamar ta koma cikin cikinta saboda kunya. Tana gaban mirror tana shiryawa yana addu'o'insa,baice mata komai ba harta gama shirinta cikin Turkish dressing. Budadden wando me kama da Palazzo da rigarsa data sauko har gwiwa me dogon hannu. Ta masa wani irin kyau da ya sanya ya dinga jin tsigar jikinsa na tashi,to amma ba daman yin komai saboda awa biyu kadai ya rage Lokacin tashinsu. Banda private jet nema da warhaka suna airport din. Yana fara cire kayansa ta nufi qofa zata gudu setting room,taku uku ya cimmata ya maida qofan ya rufe ya sanya lock,sannan ya koma a nutse yana qarasa fidda kayan jikinsa. Gefe daya tayi da kanta zuciyarta na bugawa,har yau har kwanan gobe ta kasa sabawa da wannan kalar abun nashi. Yana ganinta baice komai ba,ya kammala ya daure qugunsa da towel,bata ankara ba ba kuma zato kawai taji yayi sama da ita ya fara takawa yana dosar bandaki. Wutsil wutsil ta fara da qafafunta tana bashi excuse. "Na gama shiryawa fa..... Please ka saukeni,zan jiraka Allah bazan fita ba" Bai kalleta bama sai daya shiga toilet din. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 107 107 "Nasha gaya miki ai......duk sanda kikayi rushing to bathroom kikayi taking shower baki jirani ba......sunan wannan wankan FAKE.....Bakisan sunna bane miji da mata suyi wanka a tare suna kamfata a mazubi guda daya?......bakisan hadis dinnan ba?" Ya fadi bayan ya zumbulata a bathtub ya dafe hannayensa duka gaban bathtub din yana zube mata narkakkun idanunsa. Gefe tayi da kanta da idanunta da suka cika da qwallar yadda ya sanyata ta jiqe gaba daya,a tsaiwar da yayi a gabanta tana tsoron towel dinsa ya kwance batasan ya zatayi ba. "Mu gama wankan na nuna miki number na Hadith din da raweeh din" Yana kaiwa nan sai gashi tsundum cikin bathtub din. "Zakiga takan tsiya" Ya fada qasan ranshi. Shigewa jikinta yayi sosai shigewa bata wasa ba. Wasu irin abubuwa ya fara mata bayan ya samu nasarar cire mata komai data shigo toilet din dashi. Fahimtar inda ya dosa ya sanyata fara doje masa tana barin ya bari.....lokaci zai qure fa?,saidai cikin qasa da mintuna biyar ya yaudare bakinta da duk wani kuzari nasa da salon yaudarar nan tashi,tayi luf tana sauke numfashi gami da amsar saqonninsa da kyau,duk kuwa da yadda zuciyarta ke warning nata. Shurun da taji ya kusa sanyata bude idanunta,Allah ya taimaketa batakai gayin hakan ba zuciyarta ta gaya mata ke ya tsaya yake kallo. Haka dinne,ya zuba mata idanu yana karantar yadda dafin da ya zuba mata yake bibiyar duk wani jininta da bugun numfashinta,amma qi fadi irin nata da tsananin jan girma da ajinta ya hanata zubda makamanta ta fito masa a mutum.....saidai ya shirya maganinta shima wannan karon,duk da ya samu dukkan wata shaida data tabbatar masa ya bude wata babbar qofa a zuciyarta da rayuwarta gaba daya,qofar daya tabbatar ba wani mahaluki daya taba zuwa koda kusa da ita......yayi nasarar bude zuciyarta gaba daya da wata irin nasara da bai taba kawowa a ransa ba. Saidai ya lura yadda take da wani irin aji na daban.......haka soyayyarta take ta daban..... Ya samu aji yadda yakeso da kamun kai har fiye da yadda yake hasashen za'a samu wajen wata diya mace,komai nata me ajinne. "Lokaci yana qurewa......quick" Ya fada yana zare jikinsa daga ita gami da barinta a yanayin data zurma dukka jikinta da zuciyarta. Kasa motsawa tayi ko kadan,tayi shuru tana jin wani abu yana mata yawo kowanne sashe na jikinta. Karon farko da taji wani abu me kama da haushi ya tsaya mata a wuya,da haushi sanda kake expecting wani abu daga gurin wani kuma ya zamana baka samu komai in return ba. Kasa motsawa tayi,yana wankansa hankali kwance yana satar kallonta,yadda tayi relax cikin ruwan ya masa dadi. Nan kusa yasan zai samu dukkan abinda yake buri da muradi,ya kammala wankansa tsaf ya daura towel ya nufi qofa yana cewa. "Hurry up". Da qyar ta bude idanunta,idanunta suna cika da hawaye,haka kawai taji zuciyarta tana karyewa,sai ta dinga jin zafin abun a zuciyarta. Dolenta ko tanaso ko bataso tasan wanka ya kamata,don bata da tabbacin bai kamata din ba. Can qasan ranta taji wani abu me kama da haushinsa yana kamata,don haka koda ta fito ta samu ya gama shiryawa. Wani irin sassanyan kyau yayi cikin 3pieces suit saqar kamfanin Hugo Boss dan qasar Germany,rufaffen takalmin qafarsa na kamfanin berluti ya sake fitar da kimar shigarsa,ya kuma qara fidda ainihin darajar dukiya da Allah yayi masa. Kallo guda dayan data masa kowanne sashe na zuciya da gangar jikinta ya aminta da tsananin kyan da yayi,ya kuma soma qoqarin hura wutar daya kunna mata a toilet,sai tayi ta mata don ba'ace ta maza ba,ta danne komai daga ranta ta soma takowa cikin dakin tana yin kaman bata san da zamanshi ba. Comb din da take taje kanshi dashi ya ajiye yan lumshe idanunsa,shan qamshinta yayi masa dari bisa dari,sai ya sake fidda mata wani kima daban a idanunsa. Takowa kadan yayi ya tsaya daga bayanta,yana qare mata kallo,shauqinta yana fusgarsa,saidai duk da hakan yayi qoqarin controlling kansa yana boye hannayensa cikin trouser dinsa. So yake ya manna mata taji irin yadda yakeji a kanta ko yaya ne. "Sabrrrrrr" Ya kirata da wani irin tone daya kusa tarwatsa duk wani dauriya nata. Yi tayi kaman bata jishi ba,ya leqa fuskarta ta gefe sanda take qoqarin goge ruwan sumarta. Wani dadi ne ya kusa sumar dashi,duk da qoqarin boye masa ruwan sumar nata da takeyi amma tuni shi ya gama fahimtar inda karatun ya sanya gaba. Lallai tarkonsa yayi kamu......tarkonsa ya kama kurciya. Yanason tabbatarwa da gaske fushi tayi don ya barta saman hanya?,don haka ya qara taku biyu gaba zuwa inda take yana kuma sake ambatar sunanta. "Sabrrrr" Idanunta ta sake lumshewa gami da budesu,saidai har yanxun dai bata motsa ba bare ta amsa masa. "My world" Ya sake kiranta yana qara rage tazarar dake tsananin su har yanxun yana leqen fuskarta. "Duniyata" Ya fada da wani coolness daidai sanda ya isa bayanta ya kama qugunta ya riqe yana mannata da jikinsa. Duk wata tsiga ta jikinta sai daya tasheta da iya haka kawai,to amma duk da taji haka hakan baxai sanyata saurin bada kanta ba,don haka ta hada qarfinta duka tana qoqarin turashi gami da cewa. "I need to get dressed" "No....you don't" Ya amsa mata yana juyo da ita gaba daya suna facing din juna,sannan ya juyata zuwa yana hadata da bango gami da ajiye mata wani zazzafan kiss. Ta fahimci so yake kawai ya birkitata ya sake tafiyanshi kaman daxu,itakam wani irin sanyi takeji yana ratsa mata qasusuwanta da kyau kaman ana hura mata ac. "Am cold" Ta fada tana sasssuta muryarta saboda yadda yake qara kashe mata jiki. "I'll keep you warm" Ya bata amsa muryarsa can qasan maqoshinsa,a zafafe ya soma aje mata kisses masu dimauta nutsuwa. Kamo hankalinta tayi da qyar tana kauda fuskarta,jikinta nema yake ya fara shaking,matakin da tasan indai takai ba zata iya qwatar kanta ba. "Am not wearing anything under this towel" Da bugaggun idanunsa ya saki murmushi yana dafe bangon da dukka hannayensa "I know" Ya fadi yana daga girarsa sama. Sosai taja numfashin daya aike mata da sassanyan turaren nan nasa dake kasheta,yadda ya sakata a tsakiyar yana baza mata qamshinsa da dumin numfashinsa tana jin kaman zata sume ne. "Please" Ta fada da raunanniyar murya. Batason yaga faduwarta ko lagonta gaba daya,amma ta karanci kamar ya shiryawa hakanne. "Don't fight it" Ya fada yana qoqarin maida bakinsa cikin nata. "Am in towel fa...." Ta fadi tana qarasa narke masa gaba daya. "I don't care" Ya fada kaman me rada yana jin yadda shima ya fara kunnuwa,ya sanya hannunsa yana mayar mata da gashin kanta daya rufe fuskarta baya gami da saka idanunsa sosai cikin nata kaman bazai daina kallonta ba,wani irin sassanyan kallo yake mata kaman zai hadiyeta,abinda ya sanya taji qafafunta kaman zasu watsar da ita. "Yau zamu fita a muraaka......still Muhammad fuad anata tunanin hukuncin da za'a yanke a kansa?". Kasa bashi amsa tayi,daidai nan wayoyinsu suka dauki tsuwwa lokaci guda kaman hadin baki. " Farouq ne,wallahi nasan farouq ne" Ya fada a wani jigace. Sosai dariya ta taso mata,amma bata da qarfin yinta,saidai wani mamaki ya kamata da taga daya daga cikin masu kiran farouq dinne. Kiran farouq din ita ya ceceta,sai yaja baya ya zauna yana daga wayar,ita kuma ta kwashi kayanta ta koma toilet din. Sanda ta fito ya gama hada komai,ya bita da kallo kafin ya daga yatsansa yana karkadawa. Luggage dinta ya sauke,ya birkitata da kyau ya ciro wata oversize abaya,ya hado da wani Malaysian hijab ya miqa mata. Bata musa ba ta karba,zata koma ciki ta sauya ya bake ko ina gami da mata nuni kan ta shirya a nan. Bata tsaya jan dogon magana ba,tunda ta fahimci makara suke gab dayi,ta shirya tsaf ya kama igiyan rigar dana hijab din duka ya daure mata sannan yaja baya yana kallonta. "Ya salam.....How can i disguise you?" Yayi Maga nan da gaske yana jin da zai yiwu ya hana kowanne ido kallonta kome wahala zai iya bin tsarin. "Oho nima ban sani ba" Ta fada tana tura baki gaba don da gaske tana jin haushin abinda ya matan,duk da tana qoqarin nuna bata damu ba. Dariyarsa ya danne yasa hannu ya jawota baya yana basarwa. "Karmu fita ki canza......if not.... I'll be open about my feelings for you....i won't feel ashamed of anyone...." Idanunta ta fidda warwaje,a yadda ta shaida rufewar idanunsa akan duk abinda zuciyarsa ta karkata akai,tasan zai iya aikata komai da komai,tana kuma tsoro da nauyin hakan. Hancinta yadan matse yana gane tsoronta. "Don hana hakan faruwa......Handle me delicately....fine" "Ya salam" Ta fada tana jin fargabarsa yana kamata. Hannu ya miqa ya riqe hannunta yana fadin "Ki barshi,Jordan zai kula da komai da muk....." Bai qarasa fada ba dumin hannunta ya ratsa sassan jikinsa,sai ya dakata da maganar yana kai hannunsa goshinta da sauri. "Ya salam......fever?,when?" Ya fada a rude. Idonta ta kada kadan,ita ta dauka ma zafin jikin bai fito ba,iya ita kadai takejinsa a qashinta. "Bai dade ba......i will be fine" Kai ya girgixa yana yana azawa kansa laifin,yana ganin kaman maidata ruwa da yayi da sanyata zubawa kanta ruwa shi ya jawo hakan. "No.....mu tsaya ki samu relief,zansa farouq yayi magana da......" Hannunta ta dora da sauri saman nasa hannun. "I'll manage". Dan jim yayi yana kokwanto kafin yace. "Really?" Kai ta gyada masa duk da yadda taji kanta yana sara mata. Bataso ace duk jama'ar dake can suna jiransa jiran ya tashi a banza saboda ita kadai,hakan sam baiyi tsari ba,sannan ita kanta bata qarfafashi yayi abinda ya dace ba. Yadda yake riqe da ita kaman zaiyi mata tafiyar da qafafunta ya sanya mata Tsananin jin kunya,saidai gurin ta sake fahimtar na masoya ne,kowa sabgar gabansa yakeyi,a haka suka iso private boat din da iya ita dashi kawai zai fitar zuwa Conrad island su ruski motarsu su wuce airport,don ko Jordan wani boat din daban ya biyo ba nasu ba. *MAAMAH* Kaman wadda bata da aikinyi haka ta dinga bin diddigin shudewar kowanne awa da minti na zamansu a gurin da delay din fu'ad na qarasowa gurin. Ba shakka banda idanunsu ameenatu a wajen ba abinda zai hanata komawa gefe tayi kuka koda na minti ashirinne,wataqila ta samu sassaucin abinda takeji cikin zuciyarta. Yau ita mariya ta wayi gari karyar farautarta ta farauto abinda take da muradi ta sakashi a gaba tana wasa dashi yadda taga dama?. Yau ita mariya ita ke zaune tana jiran dakon isowar yaronta?,wata macen bariki ta riqeshi tsahon wasu kwanaki?,a yau da take jiran qarasowarsa kuma sai time din da taga daman ganinsa kowa zai ganshi?,ita kuwa idan batayi taba rayuwar mutanen nan biyu ba ai tayi asarar zuwanta duniya. Guda gudan baqinciki haka ta dinga hadiyarsa tana korawa da yawun bakinta,tana sake tsarawa da shirya yadda zata gigita rayuwarsu duka su biyun idan sun sauka Nigeria. Tana jin kamar idan ta jira su koma ya mata nisa,don haka ta koma gefe ta zaro wayarta tana duba wata number tana jin gwara ta shirya komai tun yanzu,ta yadda komai din zai fara da wuruwuri. Sauran ma'aikatanta dake hannun yanzu haka dukansu bata da wata damuwa a kansu,tasan akwai babban aiki a kansu daba wanda ya isa ya furta sunanta da sunan toxarci ko tona asiri. Tana qoqarin kira wani kiran ya shigo. Matsanancin mamaki ya kamata ganin sunan fareeda yana yawo saman screen din,bata tsaya jinkiri ba ta daga wayar tana kiran sunanta. "Na'am....ya kike?" Tayi namijin qoqarin tausar kanta ta karya harshenta ta tambayeta. "Ina kika shiga fareeda?,bayan kinsan babban aiki muka tunkara?" Sake hadiye wata guduma da taxo kan harshenta tayi,tasani cewa banda tana tausar kanta ta samu isa ga dalilin kiran da tuni ta jima da daddannawa mariya zagi. "Kowanne aiki ma yazo qarshe......kowacce magana anzo qarshenta......kowanne al'amari dadinsa da wuyarsa sun qare..... Kedai kawai turamin date din da zaku iso Nigeria,da airport da zaku sauka,kano ko Lagos ko abuja". Daga kai tayi tana duban musaddiq dake nesa kadan da ita. "Musaddiq" Ta kirashi tana sauke wayar,waiwayowa yayi sannan ya fara takawa a hankali har ya iso gabanta,a tsume ta danna kan number ta miqa masa wayar. "Kayi confirming na date din komawarmu da airport din da zamu sauka ka rubutamin a nan ka tura". Wayar ya karba yana kalla,number ba suna,hakan yadan saka shakka cikin ransa,amma ta wani sashen kuma daya tuna kalmar UWA UWA CE sai ya rubuta kaman yadda tace din,ya tura bayan ya gama kalle numbers din tsaf sannan ya miqa mata yana barin wajen. Details din daya rubuta take kalla "Me fareeda zatayi dashi?" Taji tambayar ta tsargo mata. Cak ta tsaya tana son laluba amsar amma kuma saita kasa. Wani sashe na zuciyarta sai taji yadan shiga fargaba kadan,sai kuma daya sashen ya taso ya danneshi yana gaya mata. "Fareeda masoyiya ce....wataqila akwai mafitar data samo mana,zatayi abinda ni na kasa yi wataqila" (Ni kuwa nace ummm inji me ciwon haqori......ba girin girin ba tayi mai dai,maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta). Aje wannan tunanin tayi tana tureshi gefe,ta kashe wayar tana ajeta da zummar ci gaba da lissafin sai yaushe zata bar fu'ad din ya qaraso?,sai kuma idanunta sukayi mata kyakkyawan gani. A nutse suke takowa da wani irin qyallin da idan ka kirashi na amarci bakayi laifi ko kuskurr ba. Kanta yana aje saman kafadarsa wanda tayi hakanne bisa dole saboda jiri jiri data fara ji. Da farko taqi ganin zasu shiga jama'a ne,amma daga baya dole ta kwanta din saboda indai batayi hakan ba tana iya faduwa ko ya dagata ya dauketa in ya tabbatar hakan zata faru. Tsakiyar qirjinta kuma wani abune ya dunqule mata,tana jin kaman amai ne yake taruwar mata,saidai bata gasgata hakan ba ganin lafiya qalau take ai,bataci wani abu daya bata mata ciki ba bare tace. "Na shiga uku......la haula wala quwwata" Maamah ta fada tana jin yanayinta yana hautsinewa gaba daya....... "Anya.....anya.....anya?" Ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta tana tsoron furta abinda ke cikin zuciyarta. "KINYI KUSKUREN ZABOTA" Maganar bokan ta sake maimaita kanta cikin kwanyarta. "Bazai faru ba.....saidai ita tayi danasani" Ta fada tana furxar da iske me qarfi daga hunhunta zuwa bakinta. _uhmmmmmmmmm_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 108 108 Idanunta ta dan lumshe kana ta budesu,tana iya hangen maamah dake farko,farouq daga gefanta kadan yanata amsa waya,anni daga can gaba ita amna. Musaddiq da saddiq ne bata hango ba,ko kuma yadda amai din yaketa faman mata kai kawo tsakanin cikinta da maqogorone ya hanata ganinsu oho "Amai nakeji" Ta fada qasa qasa kanta a kafadarsa,don ta tabbatar zai iya kufce mata tsaf kafin sukai wajensu. Hannunsa yasa ya riqe hannayenta sosai,kafin ya sake riqe tafin hannunta da kyau yana cewa "Ga can hanyar washroom,zaki iya qarasawa?" Ya tambaya a tausashe. Kai ta jinjina masa "Oya.....be fast" Ya fada yana mata riqon da zataji dadin tafiyan da kyau,duk da ba haka ranshi yaso ba,yaso ace ta bari ya rage mata wahalar tafiyar kawai. Murmurshi farouq ya saki,daga inda yake yana kallonsu,duk kuma da bayajin abinda suke fadi amma yadda yake kaffa kaffa da ita ya tabbatar masa dude dinsa ya qarasa zarewa......hauka tuburan na soyayya yasan ya sameshi,baisan kuma ya za'a qare da lamarin kula da gold da diamond ba,lokaci yayi na daukan sabbin ma'aikata kenan amintattu na kusa kusa dasu. Ta bangaren maamah kuwa ta shaqa iya shaqa,wannan karon kasa riqe ashar dinta tayi sai data furtata,ta furzar da iska tana dan dukan gefanta. Ta yadda duk macen data taba bariki.masifa ce,abune a jininsu da komai dadewa sai an saida hali. A nata tunanin sabreen tana sane tayi hakan,tunda ta ganta,tayi ne kawai don kada su hadu da fu'ad din kai tsaye,tayi ne kawai don ta nesantata dashi,daga qarshe kuma tayi ne kawai don ta gwada mata tata iyakar. "Zakiga taki iyakar a sanda kika qare a gidan tabbabbu mahaukata" Ta fadi a fusace tana qoqarin danne abinda takeji. Tanajin kaman ta saka hannu aka ta fasa ihu,tana jin kaman yanzu yanzu ta bude ido taga babu sabreen an shafe babinta daga tarihin rayuwarsu.....akwai lokaci abinda zuciyarta keta nanata mata kenan. Ta yarda da hakan,to amma shi lokacin yaushe xaixo?,amsar tambayar da bata santa ba kenan. A nutse ya koma baya yana qare mata kallo bayan ta gama aman tana wanke kyakkyawar fuskarta da take wani fresh da ita. Ta kammala ta gyara hijab dinta sannan ta juyo,saidai ba zato ba tsammani ta sameshi tsaye yana qare mata kallo kamar yau ya fara ganinta. Qaramar harara ta watsa masa da fararen idanunta,sai ya daga hannayensa sama alamun surrender sannan ya hade tafukan hannayensa alamun ban haquri kafin ya sauke yace. "Kinci wani abune da yake baki reaction?" Ya tambaya da yanayi na seriousness. Dan shuru tayi tanason tunawa,saidai kuma iya saninta ba wani abu da taci din. Kai ta girgixa masa tana tsane hannunta da towel din daya miqo mata. Taku biyu yayi ya matso gabanta,ya cire hannunsa a hankali yana taba fuskarta kafin ya xare ya xurashi ta qasan hijabinta yana tattaba dogon wuyanta. Abinda ya dauke mata numfashinta kenan na wucin gadi,don bayan jin temperature na jikinta sai daya hada da tsokanota har sai da taja baya tana ture hannuwansa. Jirin da taji yasa ta tsaiwa tadan dafe kanta,kaman walqiya yakai gareta tana riqota jikinsa. "Idan bazai yiwu ba mu wuce Seychelles......ki qara hutawa a can saimu samesu......xatafi burgeki akan Maldives" Ya qarasa maganan cikin kulawa. Fararen idanunta ta sake watsa masa. A abinda take gani cikin idanunsa ba hutawa zai barta tayi ba,saidai ya qara mata lalura ne kawai. Batasan inane Seychelles ba.......iya Maldives ma ya suka qare ya kaita qasan ruwa?,ita kuma Seychelles ai qila cikin cikin kada(crocodile)xasuyi rayuwa. Ta fahimci a son ranshi kowa ya mutu a barsu su rayu su kadai. "Muna sake makara" Ta fadi a shagwabe kaman xata narke. Abunda yayi masifar qayatar dashi,har sai da yaja baya yana gwada yadda tayin. Dariya taso qwace mata amma tayi hanzarin kauda kanta,sai kawai ta dauki wayarta ta soma takawa zata tafi ta barshi. "Ganganci ma kenan" Ya fada yana zaburowa ya daidaita tafiyarshi da tata. Wannan karon farouq suka fara taraswa,suns hada ido da farouq din dai ya wani basar,yana dauko wannan tsohon dabi'an nasa na miskilanci wa mutane ya azawa fuskarsa. "To waye ya damu dakai?" Farouq ya fada yana jifansa da harara,ya maida kallonsa ga sabreen da kunya ta fara mata qawanya. Tanaso ta zame hannunta ne daga nashi amma yaqi bata damar hakan "Madam barka da zuwa......inajin xamu iya wucewa ayi miki screening,minti arbain ya rage lokacin tashin yayi dama" Farouq ya fada a girmame. "Izinin wa ka nema da xaka kama yiwa mutane magana da mata?,if kana da wani important issue da kakeso lallai kayi magana da ita a kai ba gani ba?,dani zaka fara magana na nema maka izini ai ko?" Fu'ad ya fada sounding seriously. Dariya ta kama farouq sosai,yaja da baya ya kama kabbara kafin yace "Dole ne kam,dole ne na nema izini ai.....don ko bugeni kayi na fadi ai ba'a shari'a da wanda ba cikin hayyacinsa yake ba......madam kiyi haquri kinji......wannan zama dashi sai me haquri". " Na rantse harda Allah farouq kana qarawa kanka da kanka kwanakin bikinka ne" Fu'ad ya fada da gaske gaske,abinda ya sanya farouq ya fara shiga taitayinsa kenan. Yasan halinsa,idan har yace abu yasan ta yadda zai maida abunnan yadda yace din,shi kuwa wannan ruwan madarar soyayyar da yaga ana aiwatarwa shi a haramta masa wanzuwar tasa ai anyoshi......gwara yaje ya dandana shima kam. "Nif bance komai ba.....daga welcoming naku?.....madam ki qarasa ciki" "Ba ruwanka......banason kana min magana da mata fa,kana takurata,banaso kana sata magana.....she's sick". "Sick?" Farouq ya tambaya,daidai sannan taji xamanta tsakanin drama din farouq da fu'ad ba nata bane,ta sabule hannunta ta qarfi ta soma yin gaba tana barinsu. "Dude......ba sake lahani kayi mata ba ko?,wallahi wannan karon anni ba zata barka ba". Harara ya wurga masa "Wai sa'anka ne ni farouq?" "Inafa.....mutumin da yaje inda ni banje ba?" Murmushi ya saki,yasan da gaske farouq ya damu dashi da lamarinsu ne gaba daya,kowacce tambaya yana yinta ne don tabbatar da lafiyar kowannensu. "Juts a fever" Ya maida masa a taqaice idanunsa suna kan sabreen data iss gaban maamah ta tsugunna tana gaidata. "Allah yasa qwallonka ne ya fada a raga......zanso naga first born na gold runner" Sosai maganar taja hankalin fu'ad,sai ya kasa cewa farouq komai yadai bishi da kallo. Zuciyarsa bugawa takeyi so fast amma yanason dakatar da ita. Bayason maganan farouq ta masa tasiri,ya tasirantu da cewa shine kuma bashidin bane. Sautin dariyar maamah a sanda take tsugunne gabanta tana gaidata shi yaja hankalinta,ta daga kanta a hankali ta kalleta. Qaqqarfan murmushi takeyi da gaske wanda yafi kama da dariya "Kin gama naki......ni kuma zanyi nawa" Abinda tace da ita kenan kawai tana maida kanta ga wayarta. "Tashi kije yarinya" Hakanan ta samu qwarin gwiwar aje mata murmushi itama sannan ta yunqura ta miqe tana fadin "Hasbunallahu wani'imal wakeel,ni'imal maula wa ni'imannasir". Da kallo maamah ta bita sanda take takawa tana barin wajen. Ta aje mata shakka sosai cikin ranta,ta sani itadin kuma shaida ce,ba kasafai murmushin yarinyar yake xama alkhairi ba,so amma koma meye wannan karon ta shirya kawar da ita me gaba daya idan ta kama ayi hakan. Amna ce ta rugo da sassarfarta ta kawo mata runguma,abinda ya kusa sabbaba faduwarsu gaba daya,Allah ya kawoshi ya sanya hannu ya tareta ta fada hannunsa. "Ki kula" Ya fada adan dake sannan ya maida dubansa ga amna. "Be soft with her amna" Kai ta gyada a sanyaye kunya tana kamata. Kwanaki ne kadai tayi bata ga adda sabreen din ba,amma sai taga ta canza mata gaba daya. Wani ajiyayyen kyau na musamman,qamshinta da komai nata ya zama wani na daban *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 109 109 a nutse amna ta riqe mata yatsu,duk da yadda ta fahimci fu'ad din kaman yafi so tabar masa kayansa,to amma itama sabreen ita ta naniqewa,saboda bataso yayi wani abu daban da zai sanyata jin kunya gaban anni. Tayi imani kuma dukka hankali da idanun maamah yana a kansu,nunawa ne kawai ba zatayi ba. Abu guda daya daya tsaye mata a rai,ya gaza barin kwanyarta ta huta duk da yadda takejin jikinta shine dariyar maamah din. Ta gama karantar kowanne taku da motsi na matar......ta kuma sake sallamawa al'amarinta daga labarin fu'ad din. Ta tabbatar ba wata halitta da bazata iya cutarwa ba tunda har ta iya cutar da mijinta da kuma d'anta. Directly or indirectly tana farautar rayuwar 'ya'yanta ne ba tare da tasan hakan ba. A ranta taji dole ta qara takatsantsan da ita fiye da baya,sai taji kaman a baya ma kulawa da kiyayewa al'amuranta da takeyi kaman tayi sakaci,tabbas inda tasan wacece ita har haka......inda tasan wacece ita irin sanin da tayi mata a yanzu lallai ba shakka zata kiyaye komai nata fiye da yadda tayi a baya. "Hannunki dumi adda.....kaman akwai zazzabi a jikinki" Amna ta fada cikin kulawa dab da zasu qarasa kusa da anni. Kai ta girgizawa amna din tana sanya murmushi saman fuskarta "Ba wani me yawa bane......zai sauka in sha Allah,karki gayawa anni ki daga hankalinta" Dan jim tayi kaman ba zata amsa ba,don bataga dalilin da mutum baida lafiya ba kuma sannan yace kada a fadi. Hannu anni ta miqa mata sanda take shirin durqusawa ta gaidata. "Dawo nan ki zauna" Ta fada qasan ranta wasai da farinciki. Iya yadda taga fu'ad din ya koma a 'yan kwanakin da baya kusa dasu kadai ya bata tabbacin lallai komai yana tafiya daidai,ba fu'ad kawai ba.....hatta sabreen din ta canza mata gaba daya. Fatarta wani glowing kawai takeyi,hakanan idanunta sun qara haske da kuma girma. Tsananin kunyar anni takeji kaman zata nutse......ko kusa ko alama yadda takejin nauyin anni yana kamata batajin koda kusa da haka akan maamah,bata ce kuma ga dalili ba. "Sai kuma ka buge da sacemin diya ko?" Anni ta fada tana duban fu'ad daya gaidata. Karon farko shima kunyar anni ta kamashi,tattausan murmushin nan nasa da anni ta jima bata gani ba ya subuce masa,yasa hannunsa ya shafi baqa sidik din sumarsa da kudin da take lasa yayi jarin mutane da yawa. Matsawa amna kadan tayi kusa da anni tana rada mata sabreen din zazzabi takeyi. A nutse amna ta dubi fu'ad "Me ya samu ameenatu?" Fararen idanunsa ya sauke kan fuskar sabreen din sannan ya dubi anni. "Dan zazzabi ne dazu da zamu fito ya sauko mata......nace ma muje ta karba magana but ta dage wai zatayi managing" Kai anni tadan kada kadan. "Manage da ciwo?......to Allah ya sawwaqe,idan muka sauka dubai bai tsaya ba sai taga likita,ba kyau zama da ciwo ai" "Ameen" Ya amsa yana satar kallon sabreen din. Jinsu kawai takeyi,amma wani sabon amanne suketa kokawa dashi. "Bani ruwa amna" Ta fada a hankali tana tunanin idan tasha ruwan zai fada mata. Motsin bakinta kadai ya kalla ya fahimci me tace,ya matso a hankali bayan ya karbi gorar ruwan hannun jordan dake nesa kadan dasu,ya bude mata ya tako inda take yana tsugunnawa saman qafafunsa yakai robar bakinta. Tsam maamah ta dauke idanunta tana kullesu gaba daya,qirjinta na sake bugawa sosai tana jin kaman haki yanason kamata. Zazzabi?.....wanne irin zazzabi bayan ba'a Nigeria ake ba ballantana ace malaria ce?,wannan tsugonnan bata ruwan......ko ita da take uwarsa ba zata iya tuna ranar daya tsugunna haka gabanta yana bata ruwa ba......lallai dole ta batar da yarinyar nan bat daga duniya. Kai ta girgiza masa alamun xata iya sannan ta karba da kanta. Kurba uku tayi taji kaman ya isheta,sai ta miqa masa robar. "Is okay?" Ya fada yana motsa labbansa a nutse idanunshi a kanta kaman me tsoron kada ta bace masa. Kai ta gyada a kunyace tana saka kanta cikin mayafinta,bataso batason wannan kallon,halakata yakeyi gaba daya. "Kai Muhammadu" Maamah data gaza jurewa ta qwala masa kira,tana jin ya kamata ko yaya tayi wani abu da zata shiga lamarin ciwon don samun report da zai bata daman aiwatar da duk abinda ya dace da gaggawa. Tsam ya miqe yana amsa mata,sannan ya fara takawa gabanta sanda farouq ya iso yana gaya musu lokacin tashinsu yayi. "Sakamin takalma na......bazan iya durquso ba" Ta fadi tana qoqarin saisaita fushinta. Baice komai ba ya tsugunna gabanta yana tura mata takalman,ta fara saka qafafunta a ciki qirjinta a quntace. "Ita matar taka me ya sameta da ni bani da mutuncin sanin komai saidai naji daga bakin bare?". Daidai sanda ta gama zura takalman sai ya zare hannuwansa yana shirin miqewa. " Zazzabi ne kawai......shima din dazu ne yazo bawai a kwance take ba". "Zazzabi?,tana iya cin abinci?" Kai ya gyada mata a nutse don baisan me zaice mata ba,ita sabreen idan ya sakata sahun masu cin abinci ma ya zalunci sakamakon da zai gayawa.me bincike. "Akwai tashin zuciya?" Ta sake tambaya cikin bin qwaqwafi da son tabbatar da zarginta. Kai ta girgiza mata alamun a'ah. "Ciwon mara ko ciwon ciki fa?" Ta sake tambaya tana kafeshi da idanunta. Kansa ya mayar gefe kafin ya dawo da dubansa kanta. "Ban sani ba maamah.... Duka duka zazzabin na awa daya ne". " Eh dama da irin sakacinnan naku sai ciki ya shiga ya fice abinsa ma baku sani ba......banason ganganci da rayuwa shi yasa nake tambaya,dama wani aikin ai sai uwa ita data damu da rayuwar 'ya'yanta damuwa ta haqiqa.......tana yin amai ne?" Tambayarta ta qarshe da yaji yakai bango,hannuwansa suna zube a aljihun wandonsa sai kawai ya zubewa maamah kallonsa. Karon farko kenan tun bayan shudewar shekaru ashirin kusan da hudu rabon daya kalleta tsakiyar qwayar ido irin haka. Komai daya danganceta yaji yana dawo masa.......gaba daya tambayoyin nan nata basu zama komai ba face suna sake bude masa wani abu da yake zargi a kanta. Duk yadda ake maganar kwarjininsa bata taba yarda da gaske yana da wani irin kebantaccen kwarjini ba sai yau. Idanunsa sukayi mata wani irin nauyi,sai taji tana daburcewa. "To Allah ya kawo sauqi,sai a bincika ai aji meye,ko tsohuwar malaria ce" Ta fada tana miqewa tsaye,wanda hakan bai sakashi dauke kallonsa ba a kanta,har sai da yaji muryar farouq "Dude....." Waiwayawa yayi yana dubansa,sai ya nuna masa agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa,wannan shine ya ceci maamah daga irin kallon nasa ya juya yana nufar farouq din. "Wai......ka jini da yaro?,haka yakewa mutane?......muje zuwa,na rantse har da Allah muddin abinda nake zargi ya tabbata ga yarinyar nan bazan taba aminta na hada jini da ita ba......muddin wani me rai ne a jikinta ni mariyatu bazan bari ya taka duniya ba" Ta fadi tana cike da fatan ya zamana ma ba abinda take tunani bane. Amna najin takunsa a bayansu ta zame hannunta daga na sabreen din ta qara sauri zuwa gaba ta cimma anni abinta suka jera tare. Matsowa yayi yana daidaita tafiyarta da tashi,ba zato y dauki hannunsa ya aza saman kafadarta yana jawota zuwa jikinsa. "Kinga yadda kike tafiya kuwa?,you need my support......dont reject it" Ya qarasa fada yana furzar da iska. "Inajin body temperature dinki kaman yana hawa......you need medical care........banaso komai ya tabaki duniyata" Ya fadi yana waiwayawa ya dora mata qwayoyin idanunsa. Nauyin nan dai taji,sai tadan basar tana dauke kanta gefe "Zafin kaman na dazu ne,bai wani qaru ba" Ta fadi saboda batason yace zaa kaita asibiti. Idan tayi ciwo a Maldives ba zata damu ba......amma ciwo tsakanin makka da madina bata son hakan ta kasance,saboda qashene da take da burin xuwa a rayuwarta kafin ta koma ga mahaliccinta.....qasa ce da ta tara tarin shigifar addu'o'i take kuma kuma son tayi bajakolinsu a nan.....ba zataso wani abu ya kawo.mata tsaiko ba. Tana da tarin buqatun da batasan adadinsu ba,batasan kuma kwanaki nawa zata shafe kafin ta gama jerosu ba. Ba idanun wanda sukayi masa nauyi,a haka suka jera suna taka steps na jirgin har suka isa ciki. Suna shiga din matuqin jirgin yayi salute nashi sannna ya bashi hannu sukayi musabaha ya buqaci magana dashi,wannan ya sanya ta zame jikinta suka jera da amna suna wucewa ciki don samun seat din zama. Tuni maamah ta yiwa kanta mazauni a executive suit,a nata zaton shine guri na qarshe da yafi kowanne tsari,batasan sam da VIP suit ba,wanda wada dama mazauni ne na fu'ad din shi kadai,saidai idan yaso wani ya shigo ya zauna. A Aminitiy anni tayi zamanta,zaman jirgi ba baqonta bane,amna ma a nan ta zauna sai sabreen ta zauna kusa da ita suna taba hira abinsu,saidai komai ya tsaye mata a wuya,hatta ruwan da tasha. Yana takowa ta tsakaninsu xai wuce VIP suit zazzafan aman ya taso mata,ta saka hannu da nufin tareshi ta miqe da saurin don wucewa lavatory.......saidai inaaa,wani karo da tayi da fu'ad din take aman ya qarasa fitowa ta kuma soma kwararashi tun daga qirjinsa saman lafiyayyar suit dinsa har saman qafafunsa. Ba wannan bane damuwarsa.......yadda take kakarin amai duk jikinta yana kyarma shi yafi daga hankalinta,ya bita da sauri a rude yana fadin. "Subhanallah......ya salam......sannu.....am sorry" Kaman zai sake mata kuka. Yadda ya kanainaye abarsa su anni sai baya suka tsaya suns jera mata sannu tana ci gaba da yunquri kaman zata fidda kayan cikinta. Kafin ta gama kanta ya fara sarawa da wani irin ciwo,zazzabi jikinta kuma ya sake ninkuwa akan nada. Shi ya karbi ruwan daga hannun daya daga cikin crew din ya bata tasha saboda yadda take haki,ya saka hannu ya dagata suka wuce lavatory. Da idanu take binsa kawai sanda yake qoqarin gyara mata jikinta ba tare da ya damu da qazantar data zuba masa a nasa jikin ba. Idanunta ta lumshe a hankali a kansa sanyi yana ratsa gabbanta. Ta dauka zaiyi mata fada,ko zai nuna fushi saman fuskarsa,ko yayita hargagi idan ta kama ya tureta ma,amma sai taga sabanin hakan. Gaba daya ya bata attention dinsa,tanaji anni na cewa amna ta biyosu ko xata tayashi da wani abun yace "no need.....zauna kawai". Wani irin abu taji yana ratsata a kanshi,ta zuba masa ido sosai sanda yake goge mata saman qafafunta da takalminta daya dan baci,saita miqa hannu ta zaro napkins dake ajiye a lavatory din ta tsugunna a gabansa tana daidaita tsahonsu. A nutse ya dago suka hada idanu,fararen zagayyun idanuwansa sun qara haske wanda suke sauya launi nan da nan da wani abun ya taba zuciyarsa,sai ta langabe sannan a nutse ya dora napkin din saman qirjinsa tana cewa. "Am sorry" Ta furta a hankali. Labbanta yabi da kallo yana jin suna qara burgeshi,murmushi ya subuce masa wanda ya sake qara fidda kyansa,hannuwansa duka ya saka ya daga kafadunta suka miqe tsaye,idanunta yake kalla "Sorry for what?" Shima ya tambayeta muryarsa can qasan maqoshi. Idonta ta janye tana nuna qirjinsa da yatsarta,sai shima ya maida dubansa wajen. Murmushi ya kuma saki,ya kamata yana jinginata da jikin mirror din gurin,sannan yaja da baya ya soma balle button din suit din farkon,ya xareta ya ajiyeta a gefe,ya sake balle button din ta biyun itama ya ajiyeta a gefe,sai ga shirt din cikin ta ukun ta fito fes ba abinda ya tabata. Idonsa ya sake dagowa ya kalleta sannna ya daga mata kafadunsa gami da watsa hannuwa alamun ba abinda ya sameshi. Murmushi ta saki itama abinda ya kusa narkar dashi kenan,fararen jerarrun haqoranta sun fito reras tamkar adon lu'ulu'u,har qasan ranta taji dadi da dayar rigar bata baci ba,ya sunkuya a nutse ya zare takalman qafarsa sai socks kawai daya rage,sai ya miqa hannu ya kama hannuwanta,a hankali yace "Kinga abinda nake gudu ko?,zazzabin nan ya dawo sosai". " Ba matsala......zai" "Da matsala mana......bakisan yanzun nan sai na rasa nutsuwata ba saboda wannan zazzabin?" Ya tambayeta da dukka idanuwansa a kanta suna kuma karanta gaskiyar abinda yake fadi daga qasan zuciyarsa ne. Wani abu na daban takeji,wai yau ita ake damuwa da ciwonta?,matar da saidai ta damu da ciwon wasu amma nata ciwon dai damuwar qannenta ne kurum?. A nutse ya riqe mata hannu suna takowa har xuwa bakin wani dan box,yasa hannu ya danna ya budeshi,saiga loafers masu kyau ya ciro ya saka a qafarsa sannan ya kalleta *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 110 110 "Zan iya daukarki mu qarasa?" Kai ta girgiza masa da sauri,sai ya dauke kai bai sake cewa komai ba. Qafafunta takejin kamar ba zasu iya daukarta ba sanda daya daga cikin crew din ke gyaran wajen aman haka taja jiki tana komawa gurin ta. Xarginta yana sake qarfi da kowanne motsi na yarinyar,amma jikinta da zuciyarta sunqi aminta da cewa coki zai iya kasancewa a jikinta. Ita ta kawo yarinyar rayuwarsa kuma har yanxu bata manta da fafatawar da akayi dashi kafin ya karbeta ba......to mene haka yayi sautin sauya masa ra'ayi game da yarinyar idan ba sihiri bane?. Wannan abun yafi qarfin bariki......ta samu kalar kulawa da damuwar da ko amernatun bata sameta ba. Har yanzunda take zaune idanunta suna iya gane mata yadda hankalinsa yayi mugun tashi da aman da takeyi din,baya jin kunyar kowa dake tsaye a wajen,kamarma ya manta da wanxuwar kowa a wajen saishi da ita kawai....dole ta lalubo musabbabin ciwon nan da dukka iyawarta,musaddiq ne kawai kuma zatabi ta kanshi ta samu information din da takeso hankali kwance. Tayita zuba idanu ta gansu ta inda su anni ko maamah suke amma sai tsintar kanta tayi a VIP suit. Ta yita maimaita sunan bayan ganin wajen,wajen yaci sunansa dari bisa dari,zama rantse da Allah ba cikin jirgi kake ba,don ko windows sai ka danne wani abu sannan zai yaye maka su. Akwai mini bed da sofas masu tsananin kyau da taushi a gurin,tamkar kana cikin wani qawataccen madaidaicin parlor maras tarkace da hayaniya,harda office area da aka yiwa gurin daya ajiye tarkacen kayan aikinsa kamansu system dinsa da wasu documents nashi. Gadon yaso tayi kwanciyarta amma taqi,sai ya ajiyeta saman recliner,ya jawo foot setter din dake qasanta ya dora mata qafanta akai sannan ya lullubeta da wani sky blue din blanket sannan ya juya a hankali yana fita a wajen ta wata qaramar qofa. Numfashi taja sosai tana saukewa,tana yawo da qwayar idanunta cikin wajen. Wani nutsatsen guri ne da yaci sunan VIP suit din,daga ita saishi a wajen,guri ne da idan kana nan bazakasan meye yake faruwa cikin jirgin bama. Tabbas duniya girma gareta kuma fadi gareta,sannan ta sake yarda ta sallama kuma rayuwa mataki!mataki ce. Daga shigarta family din jadda taga abubuwa masu yawan gaske da idan a baya akace mata akwaisu a duniya hankalinta bazai dauka ba,da gaske ne kudi ba wasa bane.....arziqi kuma ba qarya bane......kudi nada wani irin power......suna mallakawa mutum girma da fadin ikon da baisan iyakarsu ba. Wani lokacin idan ta kalleshi sai ta dinga jin yafi qarfinta nesa ba kusa ba......ya kuma tserewa ajinta.....wani lokacin saita dinga jin kokwanto da shakkar sake masa dukka gaba daya.....kada a gaba ya samu dukkan komai ya kuma zame ya barta tunda tabbas ita ba ajinsa bace,saidai kuma wucewar kowacce daqiqa da second yana sake bata dukkan wani dalili na soyayyar gaskiya a aikace ba wai a baki ba. Maida idonta tayi ta rufe tanajin yadda zazzabin ke ratsa qasusuwanta,gefe guda kuma tana jin irin tababar da akeyi tsakanin bangarorin zuciyarta dukka akan MUHAMMAD FU'AD JADDA. Motsinsa taji kafin taji sautin nutsatstsiyar muryar nan tasa da sautari takan mata gizo. "I'd appreciate it if everyone could stay where they are,am looking for some peace and quite,i need some time to myself.......madam bata da lafiya" Yayi maganar cikin dakiya da miskilancin nan nasa. "Okay sir" Crew din data kawo masa abubuwan daya buqata ta fadi tana juyawa bayan ta ajjiye masa. Idanunsa ya daga ya mayar kan farouq daya tsayar daga qofa ba tare da ya barshi ya qaraso ba. "Karkace komai.....wannan saqok ba da crew dinka kawai kake ba.....ni akewa jirwaye da kaman wanka.....aini kaina yanzu nasan kafi qarfina.......system zaka bani zan rage wani aiki kafin mu qarasa dubai......acan zamuyi layover". Hannu ya miqa cikin shariya ya jawota ya miqa masa yana kafeshi da idanu,dole dariya ta qwacewa farouq ya amsa yana komawa. "Wallahi duk kaci bashi saina rama" "Can maka" Ya fada yana takowa ciki,sai tayi saurin lumshe idanunta don kada ya kamata tana qare masa kallo. Rigar ta zauna masa sosai ta fidda muscle dinsa dake boye a rigar,hakanan ta sake haskashi qwarai,dram dinsa da farouq sai data sakata murmusawa duk da yadda takejin zazzabin na rarakarta. Shikam yayi sa'a daya samu amini kaman farouq a sanda yake cikin yanayi na tsanani......ita ta rasa kaman farouq din,ta kuma rasa abbanta da ummienta,su huda kadai suka rage mata,take taji wata kewarsu tana kamata. Tayi nisa a tunaninta ta jishi cikin jikinta. "Oya.....get up" Ya fada yana dan dagota. Mug din hannunsa ta kalla,ita yanzu ba zata iya sawa cikinta komai ba,saita langabe masa tana girgixa kai. "Bazan iya sha ba" "Even a little?" Ya tambayeta tana dage mata girarsa dake da cikakken eyebrows,kai ta daga masa a hankali tace. "Zansha idan na huta.....I'm feeling nauseated" Hannunsa yasa a tausashe ya shafi gefan fuskarta,sannan ya jawo wani qaramin ottoman sofa ya zauna a kai. Haka kawai ya sakata a gaba,yana kurbar tea din yana qare mata kallo kaman wanda ya samu mirror,blanket dinta taja zata rufe fuskarta ya saka hannu daya ya riqeshi gam. "Ki barni mana na kalla......wannan face din kawai nake kalla naji nutsuwa ta saukarmin" Ya fada a karye kaman wani maraya,har sai da taji tausayinsa ya tsarga mata. Hakan bai isheshi ba,koda ya kammaka sai tsintarsa tayi cikin blanket din,ya haye recliner din abinsa yana cusa kansa a cikin blanket din "Wannan ta miki fadi,bari na cike miki space din daya rage" Ya fada yana shigewa abinsa ya kamota cikin jikinsa sosai. "Kai....ya salam......your temperature is too high" Ya fada yana matseta a jikinsa sosai. Ita kanta ta sani,qaruwa kawai zazzabin yake,sai kawai tayi luf a jikinsa shi kuma yayi mata masauki me kyau. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kowanne yana sauraren bugun zuciyar dan uwansa,suna jin sanda jirgin ya soma motsawa,bayan wasu mintuna kuma ya cira yana lulawa sararin samaniya dasu. ★a awannin da sukayi suna tafiya cikin sararin samaniya duka bacci tayi sosai,duk da irin zazzabin dake a jikinta bai kuma sauka ba. Tafiyar awanni biyar suka sauka a dubai Abu Dhabi. Movenpick hotel and apartments nan farouq ya kama musu,5star hotel ne dake da tsada saboda kusancinsa da burj alkhalifa. Ya zabar musu shi saboda yafi kusa da American hospital. Kafin su qarasa ma tuni yayi booking Dr din da zata dubata,don ya tabbatar fu'ad bazai yarda mo giyar wake yasha namiji ya taba sabreen ba. Cikin mintuna kadan ya kammala dubata,akwai test da taso ayi amma fu'ad din yace suna kan hanya,awanni kadan zasu wuce madina,a can za'ayi mata general checkup gaba daya,ta bata kawai taimakon da zazzabin zai sauka. Ruwa ta saka mata wanda zai suake zafin zazzabin,ya kuma bata qwarin jiki,wannan ya sabbaba ba mata wani sabon baccin bayan wanda tayi. Kwata kwata hankalinta yaqi kwanciya kaman yadda bataso fu'ad din yace abar test din ba,zataso taji mene ne?,wanne irin lalura ce wannan tun daga wata uwa duniya har nan gurin?. "Wanne irin abune da zai sanya ka hana a gwadata aga abinda yake damunta?,idan akayi maya treatment da ka fa?" Maamah data kasa hadiye abinda yake cin ranta ta fada tana duban fu'ad. Duba daya anni tayi mata ta maida dubanta ga plate din abincinta da yake dukkaninsu suna kan dining table. Maganin shege karen maguzawa,ta fahimci duk wata alqibla ta maamah.......tana kuma karance da dukmotsina,wannan dalilin shi ya sanya duk sujjadarta idan ta aza goshinta a qasa saita yiwa Allah magiyar ya sanya rabo ne a jikin sabreen din,wala'alla wannan ya zamewa mariya ishara a rayuwarta. "Ni banason wannan tangal tangal din da rayuwa,karo na gaba dole a gwadata asan me yake damunta,ayita zauje da ciwo ba'asan wanne iri bane?". "Na alkhairi ne" Shine abinda anni taso fadi,saidai kuma ta duba cewa da d'anta take magana.....bari ta barta da pain din rashin sanin taqameme din ciwon sabreen din,sai hasashe sai zargi da zato da zai hana zuciyarta nutsuwa guri guda. Shurun da akayi mata ya sake qonata sosai,taso tayita jan maganan ne amma ba wanda ya tayata a cikinsu,dole ta qunshe maganarta,daga qarshe ma abincjn qin ciyuwa mata yayi,saita koma daki ta kasa zama. "Ko na sakashi ya kawomin ita da xummar zan kula da ita zuwa safiya?,ta nan wataqila na fahimci komai?" Ta shawarci kanta da kanta,saidai ita kanta tasan wannan shawarar bame bullewa bace,don bataga ta inda zai aminta ya bata sabreen ba,mutumin da bai jima da dawo da ita cikinsu ba. Wayarta ta dauka ta djnga laluben da wanda zata zanta,sam sam bataso rabuwarsu da hajja a irin wannnan lokacin ba bayan muradanta basu kammala cika ba. Number bokanta ta shiga hasashen inama akwaita?,inama yana riqe waya?,saidai nan ma ba wani mafita dole Takoma ta zauna tana tunanin zai wahala ta zauna a makka ko!madina harsu gama kwanakinsu,tanajin zata saka ya sanya a maidata gida ne,idan yaso su sa taho daga baya,kafin su iso djn kuma ta gama nata shirin......sai fashewar bomb din💥. ★★ _WASHEGARI_ *_GAMO DA KATAR_* _Prince muhammad bin abdul'azeez airport (madina)_ A tausashe yake riqr da tafin hannunta sanda suke saukowa daga cikin jirgin har suka kammala saukowar. Batasan kallonta yake ba sai daya matsa hannunta,tadan daga kanta ta dubi idanunsa. Haka kawai takejin wani farinciki yana shigarta duk da rashin dadin da jikinta da takeji.......farincikin sauka a birnin madina......birnin da ba birni kamarsa,wanda yake qunshe da baiwawwaki masu tarin ni'imomi da falala. Saukarta a garin kadai ya tuna mata labarin madeena da ummensu tasha basu. "Gari ne dake da wani irin nutsuwa a cikinsa,kana sauka zakasan yasha banban da duk wani guri da kuka taba zuwa a duniya". Ta sake samun tabbaci yanzu haka,ta kuma sake gamsuwa da hakan dari bisa dari. " Zuciyata tanata rayamin baby zaki haifomin sabrrrrr......ki daure ki cikamin wannan mafarkin nawa......ni kuma zan fansar miki da ko mene na mallaka a rayuwata" Ya qarasa maganar yana kallon gabansa sanda suke dab da isa arrival hall. Idonta ta zare a kansa,ta jima bataga wani mutum me jarabar son yara ba irinsa,batasan me zata ce masa ba,don haka ta zabi yin shuru. "Zaki bani baby my world?" Ya sake tambaya yana dan matsa hannunta kadan na tare daya kalleta ba. Shuru ta sake yi sai shima bai qara tambaya ba har suka qarasa gurin. Hannu taga yadan daga,saita maida dubanta ta gurin. Saddiq ya hango,sanye da baqar jallabiyya ta maza da baqin hiram. Quruciyarsa da kyansan nan da suka gada daga gurin anni ya sake fita sosai. Kaman giftawar walqiya,kaman kuma cikin majigi idanunta ya subuce zuwa gefansa. Farar matashiya ce,sanye da baqar abaya itama,hannunta dauke da welcome board dake dauke da sunan ADDA SABREEN AHMAD. Ta kasa ganin fuskar matashiyar don ta kare fuskartata da board din. Jinin jikinta taji ya harba da gaske da wani irin gudu,saita soma leqawa ta hagu da dama tanason ta tabbatar abinda take zargi ne ko kuwa kawai hasashe ne irin na zuciya?. Ta leqa ta sake leqawa amma bataga fuskar ba,sai kawai ta maida dubanta ga fu'ad don ta tambayeshi yana ganin abinda take gani kuwa?. Gani tayi hankalinsa baya wajen,don haka ta sake maida dubanta gurin,saidai kuma a yanzu alluna uku take gani maimakon daya,kuma kowanne dauke da sunanta,hakanan kowanne me riqe dashi ba'a iya ganin fuskarta. Cak ta tsaya tana qare musu kallo,tana jin bugun zuciyarta yana qaruwa. Bataso ya zamanto gizo idanunta suke mata,ta laluba kuma ya zamana ba abinda take muradi ba,bataso ta saka rai akan abinda daga qarshe zai zamanto ba haka yake ba,ta daga yatsunta tana sake irga allon daya bayan daya,a hankali ta samu bakinta da furta. "Huda.....nadra.....haneefa" Murmushi me sauti ya subuce masa ganin yadda ta fadi sunansu a jere a yadda suke. Sautin murmushinsa ya tabbatar mata yana ankare da komai,ya latsa wayarsa ya aike saqo a gaggauce ga saddiq wani irin ruhin soyayya da 'yan uwantaka yana ratsashi. Yaso musaddiq tamkar haka a duniya......a sanda ya tabbatar bashi da wani gata daya rage masa saishi daya......ashe akwai wata halitta daban a gefe dake tsananin kulawa da rayuka har guda uku a matsayinta na diya mace?. Daya bayan daya suka sauke board din,su dinne.....huda nadra da haneefa......sune amma fuskokinsu sun canza daga su hudan data sani watannin baya sun koma wasu mutane na daban da kamanninsu ke nuna zallar jin dadi nutsuwa da kwanciyar hankali. Jikinta duka ya dauki rawa,fuskarta ta gauraya da kalolin emotions har guda biyu,dariya da kuma kuka,ta soma qoqarin kwasa da gudu don ta cimmasu,tana ganin kamar tafiya tayi kadan ta kaita garesu. Caraf yayi ya riqe hannunta. "Bi a hankali......mrs muhammad jadda......bani da tabbacin babu baby ne a jikin ki,still baki da cikakken lafiya......muje na rakaki.....su dinne,zaki cimmasu cikin salama da nutsuwa". " Kai....kain...." Bakinta yana rawa tanason tambaya da samun tabbaci. "Shshssh..... Muje" Ya fada yana mata nuni da lumsassun idanunsa. _Allah sarki....dan uwa rabin jiki_🥹 *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 111 111 Tun kafin ta qarasa garesu hawaye sun gama wanke mata fuskarta,taqi dauke idanunta daga kansu koda na second guda,tana ganin kamar idan tayi hakan zasu bace mata kafin ta sake bude idanun nata. Suma basu iya jira ta qaraso garesu ba,da wani irin sauri suka tunkarota kowa yana qoqarin fara isa wajenta. Gudun nan daya hanata batasan ta yishi ba sai da ta jita cikin jikinsu,dukkaninsu su ukun qoqari take a lokaci guda ta samu damar rungume kowa. Bata fahimci kuka sukeyi ba sai da suka zube duka a jikinta suka sulale qasa duka har ita din. Sheshsheqa sosai sukeyi kowanne da sunanta a bakinsa. Wani irin sautin kuka ne me taba zukata,kukan dake cike da kewa da qaunar juna irin wadda asalin soyayyar 'yan uwantaka take bayarwa. Ko fu'ad a wannan karon baya yaja ya tsaya yana rungume da hannayensa,kallonsu kawai yakeyi baiyi yunqurin yi ko cewa komai ba,saboda yasan wanne irin ciwo ne zukata sukeji a irin wannan lokacin. Ta rasa sunan wa zata fara ambata?,sai kuma ta saka hannu ta fara dago haneefa auta. Fuskar autan ta sake cika sosai,duk wani kamanninta da ita sun sake bayyana,tayi wani irin haske wanda da alama shine asalin color din fatarta. "Auta......auta kece?" Ta fada wani kukan farinciki yana sake tsinke mata. Kai haneefa ta gyada tana dariya da maqalallun hawaye akan fuskarta. "Nice adda......adda kin qara girma.....adda kin zama balarabiya" Haneefa ta fadi tana shafa hannun sabreen dake riqe da nata hannun. Qaramin dariya daya taho da hawaye ta saki tana maida kallonta ga huda. Hudanta ta sake zama budurwa sosai,abun abun mamaki kaman wadanda aka saka famfo ake hurasu. Kamarsu itama ya sake fita,duk da baikai kamannin dake fuskar haneefa ba. "Adda......ban zaci zamu sake ganinki da wuri ba" "Nima haka adda......" Muryar nadra ta sanyata waiwayawa. Itama nadra din kaman sauran,saidai nata kamannin da ummenta ne suka fito sak kaman an tsaga kara,abinda ya raunata zuciyar sabreen sosai ta miqawa nadra hannu. Ba musu ta dora nata hannun akan na sabreen din suna duban juna. "Nadra?....ya akayi kukayi irin wannan girman?,me kuke ci?" "Komai me kyau adda.....komai mai dadi hamma ya tanadar mana,komai da zamuyi amfani dashi muci ko musha yasha banban dana dubban mutane adda" "Hamma?" Ta tambaya a mamakance,sai huda ta gyada mata kai tana duban fu'ad dake nesa kadan dasu. Kanta ta daga ta waiwaya zuwa inda yake tsayen,zuwa sannan tare da saddiq suke tsaye,batasan maganar da sukeyi ba amma taga yana miqawa saddiq din wani card. "Hammanki adda" Haneefa ta bata tabbaci. Maganan data sanyata dauke dubanta daga kanshi zuwa kansu. Kai huda ta gyada mata still tana qara tabbatar mata. "Ya Allahu ya salamu.....when......and how?" Ta tambayi kanta. Duka yaushe yayi hakan?,duka yaushe yasan da yaran?,yaushe yasan inda suke?,yaushe ya shirya komai?. Ko yawan using da wannan na'urar da yake sanda suna muraaka suit yana da alaqa da shirinsa akan haka?,take taji amsar tambayar tazo mata. Wani kakkaifan abu a kansa taji ya huda zuciyarta,ta lumshe idanunta tana jin yadda yake kwarara cikin kowanne sashe na zuciyarta dama gangar jikinta. "Muhammad fu'ad jadda" Sunansa kadai ya dinga amsa kuwa cikin kunnuwanta. "Amma kun saba alqawari.....kun karya yarjejeniya sister" Muryar nan tasa dake cike da tarin nutsuwa ta ratsa rufaffun idanunta,sanda ta budesu sautin murmushin huda ya sauka a kunnenta. "Wallahi hamma itace.....adda ne ta fara sakamu kuka" Ta amsa masa tana miqewa gami da riqe dariyarta. Idanunta ta bude fes saita samu tattausan tafin hannunsa gaban fuskarta yana miqo mata shi. "Next time sai naci tararku idan kuka sake sanyamin mata kuka......get up my world" Ya fada yana duqawa kadan yasa hannuwansa yana daga kafadarta. Wani sanyi taji yana ratsa sannan jikinta,ta ware idonta a kansa sanda yake miqar da ita tsaye. Fuskarsa fresh kuma normal kaman baiyi wani abu ba,ta laluba labbanta zuciyarta dama kwanyarta gaba daya,tanason zaqulo kalaman da suka dace tace dashi wani abu amma ta rasa. Gyara mata veil dinta yakeyi yana sake rufe mata jikinta gami da jan hannun abayarnata "Wannan kallon.......bakison zuciyata ta huta hala?" Ya tambayeta yana balle mata button guda daya daya zame na abayarta. Idanunta sunyi raurau sosai sun cika da hawaye,ko sau daya so take ya kalleta......koda na second daya ne wataqila zaifi fahimtar girma da martabar abinda yayi mata,don ta tabbatar kalaman baki sunyi qanqanta su isar da abinda takeson isarwar,saidai yaqi ya kalletan har sai daya gama sannan ya zube mata fararen idanunsa. Wani abune da yake yawan bata mamaki,a iya mazan data taba kallon idanunsu ba zata iya tuna mutum daya da idanunshi suke da haske haka ba......koda kwatankwacin nasa kuwa. "Akwai wani abun?" Ya sake tambayarta yana kallonta. Labbanta ta motsa amma sai ya saka yatsunsa biyu ya b'ame mata su. "No need......bana son godiyarki ko kadan......it's my duty......aikina ne na baki duk wani abu da zai baki farinciki......haqqina ne samar miki da duk wani abu da zai baki nutsuwar zuciya data gangar jiki......aikina ne.....dole na ne na matso miki da dukka farincikinki kusa dake.....har yanzu jikinki da dumi,mu qarasa" Ya fadi yana riqe hannunta cikin nasa sannan ya kira haneefa ya saka mata ita a gefenta,ya kira huda ya sakata a daya gefen,yaja nadra baya sukabisu a baya yana mata magana qasa qasa wadda sabreen batasan me yake tambayarta ba. Tuni ta kame a owners corner,tanason ta sake tabbatar da duk wani motsi da xai gayawa kowa ita din isashiya ce. A bude tasa abar mata qofofin lafiyayyar motar,tana shaqar iska d'ai d'ai tana ratsata,tana jin qofofin abubuwan daya kamata ta aiwatar kaman suna bude mata. Tana jin tsaiwar anni a daura da ita,ita da amna da musaddiq da take jira su samu xama sosai tayi masa iyakoki da lamuran annin. Batason duk wani abu da zai ci gaba da sanya kusanci tsakaninsa da yarinyar can me kama da uwarta,zata iya kowanne kalar hauka xata kuma iya cinye komai ta daure har ta gama da matsalar amma banda alaqa tsakaninsa da amna din,don yanzun haka sautin dariyarsa da yarinyar tana jinsa har tsakiyar kanta. "Musaddiq" Ta kirayeshi tana leqo fuskarta daga motar. Sam yana mancewa da wani warning na maamah din,kiranta ya dawo dashi cikin hayyacinsa,ya amsa mata a nutse sannan ya dubi anni. Da ido ta masa alaman yaje ya amsa kiran mamarshi "Ina zuwa" Ya fadi qasa qasa yana takawa zuwa inda take. Kallo take qare masa tun daga sama har qasa,ta kowanne fanni abun babu sauqi ne wai?,wai me yasa sabbin matsaloli suke sake kunno mata kai?. "Anya ka samu isashen ilimin sanin darajar uwa kuwa?.....a ina ka taba ganin mutum yabar wajibinsa ya dauki mustahabbi?" Kasa cewa komai yayi,bayason ya fadi wani abu da zata tunzura taci gaba da zazzago maganganun da ya tabbatar anni tana ji,don muryarta a bude take magana ko wanda ke nesa zai iya jin sautinta,kasancewar garin gari ne maras hayaniya sam sam,albarkacin wanda yake kwance cikinta. "To tunda nayi maka a daki bakaji ba......bari nayi maka a gaban kowa da kowa......ni mariya ahmad.......indai nice nayi cikinka watanni tara na haifeka.....na haramta maka zuri'ar hamza kibiya da ameenatu haramci na har abada.....idan ka sake nuna wani abu makamancin haka kuma ban yafe maka ba". Idanu fu'ad dake qarasowa wajen ya runtse maganar tana hudashi,duk wani motsi nata qara bashi yaqini yake a kanta,tana sake haska mishi kanta da kanta tana fadada zargin da xai iya cewa qiris ya kusa zama tabbaci. ".......kaji na gay......" Ta dora da maganar da takeyi saidai kuma kasa qarasawa tayi sakamakon qwarewa da tayi da yawun bakinta. Bawai tayi qwarewar Allah da annabi bane.....ba kuma ta qware bane haka siddan,abinda idanunta suka hasko mata shi ya janyo mata qwarewar ya kuma zarce mata da wani matsanancin tari daya sanya idanunta firfitowa waje. Fu'ad yana takewa sabreen da qannenta baya kaman wani dan aikinsu......mutumin da shi kansa garada ne masu yawa suke gadinsa....... Saukar idanunta akansu huda ya qarasa dauke duk wata wuta ta jikinta na wasu sakanni. Ta ina yaran suka bullo?,daga wacce shiyya ko jaha?,ko duk cikin zallar iya barikinne na yarinyar?. To waima da kudin ubanwa sukazo madeena?,waye ya dauki nauyinsu?. Indai amsar dukanta FU'AD ne to lallai ta zaunar dashi ta karanta masa komai kenan a kanta?. Indai haka ne ai la shakka zataga wani sauyi ko alamu saman fuskarsa,to amma bataga komai ba.....wai ya abun yake?. Tarin tulin tambayoyin da suka hana tarin lafawa da wuri,har sai da taji maqogoronta ya fara zafi,ta karbi ruwan da musaddiq yake bata ta kurba still idanunta akan yaran. A yadda suka rabu dasu rabuwar qarshe......bata nuna musu duk wani plan nata ba,tayi qoqarim basu gata da kulawa,a yanzun tana zaton zasu iso gurinta cikin fara'a da girmamawa ne kaman yadda yake a baya,saidai yanzun ga tarin mamakinta sun gaidata ne a tare......irin gaisuwar da zaka yiwa baquwar fuskar da baka taba ganinta ba. Bata iya amsa musu ba saboda mamakin da ya ciyota,ta bisu da idanu sanda suke motsawa gaba wajen anni suna gaidata. "Ma sha Allah......aah 'yammata,lafiya alhmdlh,da alama kun rigamu sauke taku umrar.....nasan halin saddiqu da kyau,bazai bari ku zauna ba dama.......ga photocopy din takwara ameenatu......ma sha Allah,Allah ya yiwa rayuwa albarka" Dukka muryoyin anni suka dinga dukan kunnenta sanda suke haraman barin wajen bayan rarraba motar da kowa zai hau. Madeena kusan ta zame masa muhalli,don haka yana da gidaje nasa na qashin kansa kyawawa har guda biyu. Ba wani gari a duniya da yake jin nutsuwar da ko jaririn dake cikin mahaifiyarsa baikaishi samunta ba irin madeena,ta biyunta makka,to amma yanzun saboda yana buqatar sabreen din ta huta sosai,sai yasa aka kama musu amenities a intercontinental Darr alhijra,saboda yafi kusa da masjid annabawi. Duk yadda yaso ya kasance a motarsu sabreen din amma sai ya dage mata qafa,don wataqila akwai maganganu da suka shafesu da zasuyi a tsakaninsu daya kasance sirrinsu ne,don haka ya tura saddiq motar maamah su tafi tare,amna da anni,shi kuma ya karbi key da kansa ya kira musaddiq "Shiga muje" Ya fada yana shiga mazaunin driver ya tayar da motar suna fita a nutse. Bayajin xai iya barin wadannan sakannin su wuce maganan dake ransa yana cizonsa,shi yasa da zafi zafi ya nemi kebewa da musaddiq din. Shuru ya ratsa tsakaninsu har zuwa sanda suka dauki hanyar intercontinental,muryar hamman nasa ta masa saukar ba zata. "Musaddiq" "Na'am hamma" Ya amsa a sanyaye har yanzu muryar maamah tana bugun tunaninsa. "Kanason amna?" Tambayar da bai bata tsammani ba ta fita daga bakin hamman nasa. Har wani firgicewa yaji yayi,yaji kaman baiji abinda fu'ad ya fada daidai ba. "Nn...na'am hamma?" "Nace kana son amna?" Ya sake tambayarsa idanunsa nakan titi yana sauraren amsarsa. "Hamma.....amma hamma" "Ba sunana na tambayeka ko nace ka maimaita ba......kanason amna?,eh ko a'ah?,banason wani sharhi" "Ina sonta hamma" Ya amsa masa yana yin qasa da kansa a sanyaye. Kai kawai fu'ad ya jijjiga,bai kuma sake cewa dashi komai ba,yayin da yabar musaddiq din da saqe saqe a ransa masu yawa,ya matsu yaji hamman nasa ya sake cewa wani abu amma bai sake fadi ba,kuma tunda har mintuna sukayi nisa yasan ba lallai ya furta komai din,don haka yayi qarfin hali ya motsa. "Hamma.....maamah ta fadi cewa bataso ta kuma r......." Wani kallo ya waiwaya ya watso masa duk da tuqi yakeyi sannan ya maida dubansa ga titi. "Kayi magana akan abinda kowa yakeso da wanda bayaso amma banda maamah......bana buqatar komai nata ciki harda ra'ayinta da meye bataso da wanda takeso......abinda na sani kawai shine na sauke haqqinta na ci sha sutura muhalli da lafiyarta......sai biyayya akan abubuwan da basu sabawa mahalicci da kuma addini na ba.....baya ga wadannan komai a kanmu nata ba dole bane". Yadda hammansa yayi magana ya sanyayar masa da jiki,ya sani gaskiya ya fada....kuma koshi yana yaba masa yadda yake qoqarin bata girmanta. Sun rigasu isa intercontinental din,don sanda fu'ad ke parking a parking lot na gurin ga motocinsu nan ajjiye,ya tsaida motar yace da musaddiq. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 112 112 "Ka shiga ciki ina zuwa......ka fada mata zan shigo yanzu.....but idan naga tana kuka zan nesantata da kowa har sai ta daina". Har zuciyarsa abun ya qawatar da musaddiq,ya amsa masa a girmame yana bude motar sannan ya fice. Da kallo fu'ad ya bishi har ya bacewa ganinsa,iska me zafi ya furzar daga bakinsa,ya sake yarda har yanzun shine garkuwar musaddiq,zai kuma ci gaba da zame masa garkuwa har sai ya tabbatar da cikar kamalar farincikinsa. Hannu ya dora saman center console na motar ya dauki wayarsa,ya gyara zaman kujerarsa sosai yayi relaxing sannan ya soma lalubar number wayar abbansu wato alhj hamza kibiya. Bisa jagorancin saddiq suka wuce amenity din,sannan ya nunawa kowa dakinsa. Amna dai da anni,nashi dakin shida musaddiq.....dakinsu huda suma su uku,sai dakin boss din nasu da duniyarshi......farouq ne ya zama shi kadai daban. Sabreen murmushi ta saki sanda suke bude dakinsu huda da sukace tazo taga wani abu,tana jin farouq yana balbalin masifa. "Shi tuzuru dama abun rainawa ne......shi yasa aka wareni kaman wani barawo......duk wanda yayimin abu saina rama.....Allah ya kaimu lokaci,sati ukun ai kamar yau ne". Idanu sabreen ta firfitar waje tana kallon matar dake zaune saman abun sallah.....momma bahijja ce cikin kamilalliyar shiga. Idonta ta murxa tana jin mafarki takeyi da gaske "Qaraso sabreena.....mommmanki ce". Da gudu ta qarasa jikinta ta zube tana sakin wani irin hautsinannen kuka "Momma duk kun gama birkitani.....kun gama bani mamaki,momma dama zakuzo?". "Ko niyya babu me ita,duka aikin mijinki ne". Kalmar ta sauka sosai a zuciyarta,ta ruqunqume momma sosai tana hangen kamilar fuskar nan tasa. Wanne irin mutum ne shi me abun mamaki haka?,wanne irin mutum ne shi wanda ya iya nemowa abokin rayuwarsa maqurar farinciki?. "Zazzabi kike haka sabreena?" Momma ta fada tana dagata a jikinta. "Shine momma.....zai sauka,don Allah kada ki bari hamman nan yaji,tsaf zai sakani kwanciya asibiti" "Kinsha magani?" Ta tambayeta cikin kulawa,kai ta gyada mata,duk da tasan ba wani magani da tasha tun a dubai,ta maida kanta ta kwantar saman qafafunta tana cewa. "Ya akayi komai ya faru momma?,bani labari?" Ta furta tana riqr hannun haneefa da kyau cikin nata. Doguwar waya ce da sai da suka shafe aqalla awa biyu ba kadan suna tattaunawa da alhaj hamza din,daga qarshe abban yayi shuru kafin ya sake magana. "Na fahimceka muhammadu.......kuma na gamsu da bayananka da hujjojinka........amma me zai hana ka jira na qaraso nan din ko ku ku dawo gida?". Kai ya girgiza " Kayi haquri abba.....bawai inason inyita musu dakai bane.... Amma karka manta annabi ya fada mana,ba'a jinkirta aikin alkhairi gaggauta yinsa ake" "Na sani muhammadu banaso ka kirawa kanka matsala ne gaka kai daya" Murmushi ya sake saki yana yin gefe da kansa. "Abba...ka manta muhammadu nake?....ka manta wannan me babban sunan?" Qaramin murmushi ya qwacewa Alhaji hamzan "Ban manta ba kam.....jarumin gold daga qasar yarbawa da inyamurai" Wannan karon shi kansa fu'ad saida murmushinsa ya fadada "Ka samu alhaj muhyidden,yana alranuna unguwar da gidanka yake......Allah yasa haka shi yafi alkhairi......amma kabi komai a hankali,idan akazo batun iyaye bin komai ake a sannu" "In sha Allah abba.....na gode" Ya amsa masa yana jin wani farinciki yana ratsashi sukayi sallama. Zaune kawai abban yayi da waya a hannunsa. Wanne irin yaro ne wannan Allah ya baiwa mariya amma har yanxu batasan baiwar da Allah yayi mata ba?,tabbas ahmadu ya dace da kalar yaron da yake zamewa mutum sadaqatul jariya bayan ranshi.....Allah ya gama masa komai......baisan wanne irin qauna yaron yake gwada musu ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana tashi "Ubangiji yasa albarka albarkacin wajen......yasa kuma silar zuwan komai qarshe kenan a tsakaninsu". Kansa tsaye ya wuce nashi dakin,so samu ace tana tare dashi a wannan lokacin.....to amma kuma yasan yanzu dole ne ya mata uzuri ya daga mata qafa,ya kuma bata dama sosai na ganawa da 'yan uwanta,don haka sai kawai ya rage kayan jikinsa ya shiga wanka. Tsaf ya shirya cikin jallabiyya,sai gashi ya juye sak balaraben madina. Wayarsa ya dauka ya kira saddiq bai sameshi ba,don haka ya kira musaddiq. Bugu daya ya dauka cikin girmamawa. "Ka fadiwa saddiq ya shirya nan da thirty minutes mu wuce masjid.....banason wannan ragoncin naku" "In sha Allah hamma......amma maamah tacemin idan ka shigo ka shiga tana son magana da kai". Agogo ya kalla,indai zai bata minti ashirin sauran lokacin zai ishesu tafiya,ya amsa masa da okay yana katse wayar. Ya sani babu wani lokaci da kiranta ya zama na alkhairi,babu wani lokaci da kiranta ya zama me dadi,shi yasa ya yanke koma meye gwara yaje yanzu ya jishi ya tattara damuwarsa ya tafi masallacin ma'aiki da ita ya juyeta a can. Kafin ya fita ya duba number da abba ya tura masa,yayi kiran alhj muhyidden ya nema inda zasu hadu. A girmame yace zai sameshi a masaukinsa,hakan ya yuwa fu'ad nauyi,don babba ubane a wajensa,don haka duk wanda ya jibanceshi yana masa kallon uba shima. "Ka zabar mana guri,zan iskeka in sha Allah ko a ina ne". Nutsuwar fu'ad da hankalinsa ba wani baqon abu bane a wajensa,don haka cikin masallacin yace su hadu bayan sallah isha'i,ya duba lokaci sai ya yanke daga sallar la'asar din yayi zamansa har isha'i acan yayi jiransa,don yana da tarin addu'o'i daman da zaiyi. "In sha Allah zan zauna ta babus salam". Ya fadawa alhj muhyidden. A nutse ya dauki casbaharsa,ya sake feshi jikinsa da lallausan turarensa sannan ya saka wasu loafers masu taushi marasa nauyi ya fice a dakin. Ita daya cikin dakin tunani kaman zai fasa kwanyarta,tana zaune daga gefan gadon,madarar almara'i ce a gabanta tana tsiyaya da kadan da kadan tana sha,don batajin abinci xai wuce ta cikinta. Kwata kwata jinta take kaman akan qaya,lissafin kwanakin da zasuyi a qasar takejin sun mata yawa sun mata kuma nisan da kamar ba zata iya jira ba. Ganin yaran ya sake gigita tunaninta,tun sanda ta samu ta sabule yaran daga hannunta dama tana tare dasu?,ko wani gurin ta kaisu?,ya akayi suka kasance a nan gurin?. Tunaninta ya katse sanda akayi knocking qofar dakin,idanunta ta daga ta kalli qofar,tasan ba kowa bane sai fu'ad din,murya a cunkushe tace "Shigo" Qofar ya murda ya tura ya shigo,don bayan fitar musaddiq tace yabar masa qofar a bude. Kallo daya yayi mata yasan dai kaman kullum ne,kaman yadda aka saba wani abu da ya shafi buqatar qashin kanta ya sanya ta kirashi,saman dressing mirror ya qaraso,ya dosana kadan ya zauna samansa yana dubanta. "Gani" Ya fada a nutse yana shirya jin komai da zai fita a bakinta. "Muhammadu......wai nikam duniya na haifawa kai ne?,wanne irin wauta da hauka kakewa rayuwarka?,sam ba ruwanka da tattala rayuwarka?,ba ruwanka da sanin ya kamata?,ka zama baitul mali ka maida kanka bayin wasu?". Dukka maganganunta tana yinsu ne cikin fada zafi da kuma daga murya. A nutse ya lumshe idanunsa sannan ya budesu. "Yanzun me akayi?,me ya faru?" Ya tambayeta a nutse yana qare mata kallo. Bayason ranshi ya baci ko kadan,yanayin abubuwan maamah suna neman fara ta'azzara,shi daya yasan me ya adana a zuciyarsa daya shafeta,sirrika masu nauyi da tsanani wanda ita kanta batasan da hakan ba. Ido itama ta zuba masa,saidai nauyin nasa idanun yafi nata,dole ta janye idanun nata. Tanajin zallar rainin hankali da wayo a al'amarinsa......tanajin wani irin ciwo da yadda ya gagara zuwa hannunta tamkar ba ita ta haifeshi ba. "Tuni na dade da sanin ni din marainiyar wayonka ne........wadannan yaran daka debo meye alaqarka dasu da har ka fara barnatar da dukiyarka a kansu?" Ta tambayeshi a zafafe. Idonsa ya dauke yana qoqarin jawo sabuwar iska zuwa hunhunsa,al'amarin maamah yana daure masa kai maqura......tana yin abubuwa da zummar ba wanda yasan kalarta ta badini a nata hangen?. "Maamah......nayi tunanin kece me bawa wani labarin alaqar dake tsakanina dasu ko?,a wajenki na fara sanin dacewar kulawa da qannen matarka,na dauka idan nayi hakan nima wani abune me kyau nayi?" Yadda ya amsa matan ya mata wata bulala data ratsata matuqa,shuru ya gifta tsakaninsu na wani lokaci,wani sashe na zuciyarta yana gargadarta "Ki kula da dukka amsar da zaki bashi.....akwai.magana cikin maganganunsa". Abinda wani sashen yake nanata mata kenan. " Muhammadu.....ka saurara da kyau ka jini,qannen matarka ko wani abu makamancin haka ba damuwata bane......ba ruwana da alaqarka dasu,bana buqatar wata hidima tsakaninka dasu,wannan maganar da gaske nake gaya maka ita,tunda kai ka zama abinda ka zama,bazan sanya ido mata su sakamin yaro a tsakiya sai yadda sukaga damar yi dashi ba......bazan lamunta ba,tun wuri ka saki dui wata hidima tasu,banaso na sake ji ko na sake gani muddin kana neman albarka daga wajena". Wata qaramar dariya ta taso masa amma.ya kwantar da ita ta hanyar lumshe idanunsa,ya jinjina kanshi da kyau mamaki yana sake cikashi. "Kana jina?" Ta fada da mugun zafin da takeji a ranta. "Maamah.....cikin arziqin da Allah yayimin......ina iya daukan dawainiyarsu data danginsuma gaba daya ba tare da komai dana mallaka ya samu matsala ba......dukka mutumin da ka kawoshi nan wajen yayi ibada kana da lada na musamman,duk aikin alkhairin da kayi asalinsa kana da lada daidai da wanda yayi aikin ba tare da an tauye ladan kowa ba.......maamah......tabbas inda albarkar uwa ita ke sawa yaro ya rayu.....ba shakka da tuni mun jima da amsa sunan GAWA,so inaga ba matsala bane ka zama silar sanya farinciki a rayuwar wani......dukiyarmu da kason wasune dole a ciki da ubangiji ya sanyata cikin tamu.....ya zama dole ka raba ka bawa kowa don fita haqqinsu da ubangiji ya dora maka.....ina fatan ba wani magana a ciki daya bata miki" Ya qarasa fada yana miqewa. Mutuwar zaune tayi kalamansa suna bata mamaki me tsanani,kasa ce masa komai tayi har ya fara takawa zuwa qofa. "Muna kusa da masjid nabawi,dukka sallolinku zaku iya qarasawa kuyi a ciki.....ni na wuce sai zuwa dare" Ya qarasa fadi yana ficewa cike da fatan kada ta sake cewa komai din bare ya tsaidashi. A bakin elevator ya samu su musaddiq,sai kawai suka wuce zuwa masallacin. Suna tattaki a qafa yana sauraren hirarrakinsu,yayin da nashi Hankalin yayi nisa zuwa wani guri na daban. ★Sau uku tana juyawa tana qare musu kallo cikin daren,idanunta duka suna tsakanin huda nadra da haneefa da kuma momma bahijja dake kwance saman nata gadon. Tashi tayi ta zauna sosai,zazzabi takeji yana sake qaruwar mata,ko amai din sai data sakeyi dazu amma bata bari kowa a cikinsu ya gani ba,saboda wannan farincikin da wannan walwalar take so taci gaba da gani saman fuskarsu,batason ganin komai da zai bata wannan yanayin. Hadewa jikinta tayi waje daya tana jin sanyi,yayin da can qasan ranta ya cika da ambatonsa. Tana ji ya gama yi mata komai na rayuwa.......tanaji ya gama mallakar komai nata.....gangar jiki da kuma zuciya,tana jin ya sayi wani babban gurbi a rayuwarta da rufe babinsa ba abu bane me yuwuwa. A yanzun daya qarasa cika mata burinta..... Sun gaya mata abubuwa masu yawa da ya yiwa rayuwar su wanda bata taba kawowa mafarkinta hakan zai kasance ba. Wani irin gini da ya yiwa rayuwarsu har ya zarta nata mafarkin a kansu.....ko yanzu ta fadi ta mutu ta godewa Allah......tana da dukkan tabbas da yaqini akan rayuwarsu. Haka kawai takejin kaman yayi tsaho ace ta jirayi gobe kafin tayi masa godiya.....sai takeji ya cancanci ta abokanceshi a wannan daren. Tafi kowa sanin yadda waje yake masa qunci idan ta matsa......tafi kowa sanin yadda yake qulafucinta da son kasancewarsu tare. Tun saukarsu bai nemeta ba ko a waya,tasan kara kawai yayi mata bawai don hakan yakeso ya kasance ba. Zazzabinta da komai da takeji ta hadiye,ta shiga bandaki ta sake wanka,ta dawo cikin dabara tana tunanin inda zataga luggage dinta. Ba luggage amma akwai wani bag daban data shigo dashi,kusan duka sabbin kaya ne a ciki,saita samu kanta da neman rigar da tasan zata dace da yanayin. Tsaf ta gyara sumarta cikin hair mist dinta,ta kuma tajeta ta saketa a gadon bayanta. Yadda farar tattausar rigar maras tsaho ta zauna mata a jikinta ita kanta ya burgeta,komai ya fito das das a jikinta da wani irin salo me daukan hankali,saita nema dogon hijabin daya rufe mata jikinta ruf ta aza saman rigar,ta dauki wayarta ta taka a hankali tana fita a dakin. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 113 113 Waiwaye ta dinga yi don ta tabbatar da kowa bai ganta ba,ta qarasa qofar dakin a nutse tana fatan samunta a bude. Taci sa'a kuwa,don tana murdata ta bude din,sai ta tura ta shige a hankali. Abinda bata sani ba tayi shuka idanun makwarwa,daidai sanda maamah ke fitowa daga dakinta da zummar sauka floor din qasa ta rage zaman kadaici koda cikin reception ne. Dif wuta ta dauke mata,wata qaqqarfar guduma ta saukar mata. Lalubawa tayi ta nema kujerun da suke ajewa jifa jifa ta cikin hallways din ta zauna ganin duhu yana nemam giftawa idanunta tana maida numfashi,maganar da sukayi da ita ta qarshe ta dawo mata. "BANA SONSHI....BAZAN KUMA TABA SONSHI BA.....BANMA SHIRYA ZAMA DASHI BA.....AKWAI LOKACIN DA XAN TAFI.....AMMA ZAN TAFI NE KAWAI SANDA NI NA TSARA NA TAFIN,BAWAI SANDA KE KIKA SHIRYA FARUWAR HAKAN BA". kai ta jijjiga tana sake dilmiyewa cikin mamaki. Wato ita yarinyar take rainawa hankali kenan?,ita takewa wasa da hankali?,wai ya akayi kaman ita mariya yarinya 'yar cikinta wadda inda fuad mace ne yaci ace jikarta ce amma take wasan kura da hankalinta haka?. Dukan kujerar tayi ta miqe tana komawa cikin dakin,zata kasa ta tsare taga iya awannin da zata dauka kafin ta fito a dakin. Matsakaicin haske ne a dakin,da alama ya kashe kowanne qwai banda side lamp din dake gefen Kujerar data hangoshi kwance samanta. Yana kwance sosai ya miqe dukka wannan tsahon nasa,hasken fitilar ya haske fuskarsa sosai. Qur'ani ne a bude kife a qirjinsa,da alama yana tsaka da karantawa bacci ya daukeshi. Baqar sumar nan dake habarsa da qasan hancinsa girarsa da zara zaran eyelashes dinsa sun sake qawata fuskarsa da wani irin annuri. Ita kanta saita samu kanta da qare masa kallo,har zuwa sanda ta isa gabansa cikin sanda. A hankali ta tsugunna a gabansa tana sake matsawa dab dashi,qamshinsa ya taso ya daki hancinta,abinda ya sakata lumshe idanunta ba tare data shirya ba saboda dadi da nutsuwa da qamshin ya saukar mata. Cikin takatsantsan ta miqa hannunta tana zare alqur'anin da yake rungume dashi,ta daga tana duba wacce surar yake. Alama ce saman ayar muhammadur rasulullah bisa dukkan alamu nan yake karantawa,ta motsa bakinta a hankali ta furta. "Sallalahu alaihi wa sallam" Ta sanya bakinta kan ayar a nutse tayi kissing nata sannan ta rufe qur'anin ta adanashi. Sake dawowa tayi ta tsugunna saitin fuskarsa tana qare masa kallo. Karon farko data karanci ainihin sassanyan kyau da Allah ya masa baiwa dashi. Ba banza ba yake da wani irin kwarjini da ba kowa ke iya saka idanunsa kan fuskarsa zuwa cikin idanunsa haka kai tsaye ba,labbansa sukayi mata kyau sosai,ta miqa hannu tana taba dogayen eyelashes dinsa sannan ta sauko zuwa labbansa masu kalan red tadan taba. Motsawar da taga yayi sai ta janye hannunta da sauri zuciyarta tana bugawa,dan gyara kwanciyarsa yayi kadan zuwa hannun damansa,abinda ya bashi daman fuskantarta sosai itama ya bata daman ganin fuskarsa sosai. Hannunta ta sake miqawa ta kama yatsunsa,a hankali ta motsa labbanta. "Ka dage sai da ka farauci wannan sabuwar zuciyar......ka dage da qarfin zuciya dana damtse sai daka fanshi wannan ruhin da baisan soyayyar kowa ba saita 'yan uwansa......ka nuna sadaukantaka da jarumta har sai daka yaudari zuciyar marainiya ameenatu......wallahi na sallama......sabreen ta sallama maka,ta mallaka maka......ta kuma miqa wuya.........na baka dukkanin soyayyata dari bisa dari......ka cinye yaqin.....kayi nasara......na karbi faduwar ta wannan bangaren muddin wannan shine faduwar......ka mamaye DUNIYATA ka sabuntata da irin DUNIYAR kowanne mutum.....nima kaine DUNIYA TA" ta qarasa fada tana kallon zara zaran yatsunsa masu farare qal din farce kaman baya taba komai dasu. Motsin da ya dan sakeyi ya sanya gabanta faduwa "Idan yana jin duk abinda kika fada fa?" Wata zuciyar ta gaya Mata,saita fidda idanunta dukka waje tana miqewa da hanzari a ranta tana cewa. "Da na gama jin kunya". "Ina zaki tafi kibar zuciyar da kika gama lugiguitawa?" Muryarsa ta daki kunnenta me dauke da alamun bacci yatsunta na cikin wanda yaci nasarar cafkesu sanda take juyawa zata fice. Zare idanunta dukka tayi gabanta na harbawa,kada dai ace yana jinta?. "Zan iya cewa kunnuwana sun manta dajin wata kalma me dadi a rayuwarsu irin na yau......karki tafi ki barni cikin wayen wadannan kalaman" Yayi maganar yana saukowa daga kujerar sannan ya sakar mata hannum yana takowa bayanta. Kane kane yayi a bayanta yana rungumota ta baya ta hanyar aza hannuwansa saman ruwan cikin ta. Ya cusa hancinsa ta wuyanta yana zuqo daddadan qamshinta daya soma aike saqo sassan jikinsa da wani irin hanzari (Karki raina turare,kada ki rabu da turare amatsayinki na matar aure,duk yadda zan gaya miki rawa da muhimmancinsa a wajen matar aure ba zaki gane ba......amma hatta da sha'awa turare yana tayar da ita,musamman irin masu sanyi da laushin qamshin nan,amma ki lura,akwai inda za'ace ki kama kalar qamshi guda da mijinki xai ganeki dashi,tom wani.namijin ba haka yake ba,wani yafison kullum da kalar da zaiji a jikinki,bayason kala dayar nan,saiki fahimci mijinki wanne iri ne). "Sabrrrrr" Ya kirata a rikice yana jin wannam feeling din da yakeji a kanta yana taso masa. "Hamma" Ta amsa masa itama idanunta a lumshe tana jin yadda saukar hannunsa a jikinta yake haifar mata da wani irin yanayi me wahalar fassara. Magana yakeson sakeyi mata amma ya kasa,sai kawai ya fara tattara hijabin zai rabata dashi. Hannunsa ta riqe sannan a hankali taja baya,ta tattare hijabin da kanta ta zameshi daga jikinta ta wurgar dashi gefe daya. "Ya subhanallah" Ya furta bakinsa yana rawa. Zai iya cewa bai taba ganin sanda tayi masa kyau irin yau ba,tayi ado sosai da gashinta irin yadda yakeso ya gani. Kowacce boyayyar sura ta jikinta ta bayyana yadda yake da muradin ya gani,kafin ya qara kowanne motsi ta qara sanda bashi mamaki ta hanyar balle hannuwan rigarta suka zame ta saka hannunta da kanta ta zare rigar zuwa qasa sannan ta fara takowa har inda yake ta iskeshi. Wani irin mahaukacin tarba yayi mata cikin tsananin yunwarta,yana jin kamar yau ne rana ta farko daya fara sanyata cikin idanunsa,martanin data soma maida masa ya sanya yaji bashi da wata jarumta sam,yana gudun suci gaba da tsaiwa tsaf zasu iya zubewa,sai ya sauqaqa musu ya dauke abarsa ya qarasa da ita inda sukafi wayo. Kirif ya rufe musu fuskokinsu da mayalwacin gashinta dake fesar da qamshin hair mist dinta. Gaba daya ya shiga wani rudani da bai taba shiga irinsa ba tsahon kasancewarsu tare. Komai yayi mata saita maida masa martani,duk inda ya nufa kafin ya qarasa tayi masa jagora,sai yaji kaman ya kurma ihu ko xai samu sassaucin dimuwar dame yawo cikin kwanyarsa. Yanaso ya gaya mata ta sassauta saboda kada ta jashi yayi mata babban aiki,don yana iya jin dumin dake jikinta,amma inaaa ta qarasa dimauta kowanne tunani nasa,ba abinda bakinsa ke iyayi banda furta sunanta a jejjere da bada zazzafan kiss da karbar martani daga gareta. "Ki soni sabbrrrrr......na rantse da Allah ni kadai nasan me nakeji a kanki......ki soni,zan miki komai....zan zame miki komai.....zan mallaka miki komai". Fuskarsa ta riqe sosai cikin hannuwanta tana dubansa,gaba daya kamanninsa sun sauya ya birkice sosai. "Muhammad" Ta kirashi "Fu'ad" Ta maimaita "Muhammad jadda......ameenatu ta yarda ta soka......ameenatu ta yarda ta mallaka maka kanta da rayuwar ta,ameenatu ta zama taka har gaban abada....dakai da ameenatu yanxu duka abu daya ne.......ka gayawa kowa wannan cikin alfahari taqama isa da samun tabbaci" Ya riga ya sallama,gaba daya ta gama susuta qwaqwalwarshi......yasan a yau kam duk wanda yayi kusa da yawa da dakinsa zai iya jin motsin da xai saka zargi a ransa,baisan me yake yi ba kaman yadda ya manta wayeshi. A lokaci ji ya dinga yi inama akwai wata duniyar ta daban da zai iya maidasu shi da ita?,duniyar da babu kowa saisu kadai?,wannan albishir daya samu daga bakinta......daga gari me tsarki yafi komai masa dadi da zame masa tarihi cikin rayuwarsa. Wani irin dare suka raya,daren data sakar masa dukka ragamarta,ta cika masa mafarkinsa ta hanyar bashi kowacce gudunmawa da cikakken hadin kai,saiga muhammad fu'ad din yana mata kuka sosai kaman qaramin yaro. Kukan daya sake susutata itama,banda abune da ubangiji ya sanyashi ya zama sirri tsakanin ma'aurata......tabbas duniya data cika da mamaki idan akaga matashin zaki gwarzo irin muhammad jadda yau a gaban mace yana mata kuka har haka. Ita kanta a rikice take,ta kuma aikatu sosai a hannunsa duk da controlling din kansa daya dinga qoqarin yi,kafin wani lokaci zazzafan zazzabi ya sake rafketa bayan amai data yi a jere har sau uku. Abinda ya daga hankalinsa kenan,ya tsaftacesu shi da ita,ya kuma shiryata cikin abayarta me sulbi shima ya sanya jallabiiyyarsa,ya duba asibiti mafi kusa ya kirasu donsu dauketa aje a duba masa ita,don bayajin zai iya jure wannan zazzabin yaci gaba da taba masa ita. Cikin mintuna qalilan motar al_ansar hospital ta iso suka wuce da ita. Baiko samu tsaiwa gaya musu ba,don kiran sallar farko kawai akayi,sai ya rubuta saqo kawai ya turawa Farooq. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 114 114 Ko na second daya bai barta ta matsa daga jikinsa ba,tana kwance cikin jikinsa da wani irin yanayi. Cikin kowanne numfashi da zai sauke ko zai fitar jinsa takeyi da wani irin maqalallen yanayi a cikin zuciyarta,duk bayan minti kadan sai ya tambayeta "Ina ne kuma yake miki ciwo?,menene yake damunki?,me kikeso?" Ido kawai take lumshewa,don ita kadai tasan me takeji cikin qasusuwanta,saidai tana qoqarin nuna masa all is well saboda ta fahimci a gigice yake,amma duk da haka bataga nutsuwa a tattare dashi ba,kaman me gani har hanji,ya fahimci duk wani motsinta. Yanayin zazzabin ya sanya suka fara bata taimakon gaggawa a daki na musamman,kafin daga bisani su fara gudanar mata da test har kusan kala biyar suka tafi kan zasu dawo da result din. Sanda tayi farkawa na biyu bayan tayi sallar asuba gari ya waye sosai,kusan goma saura na safe. Shine mutum na farko data fara gani,fuskarsa ta fito fes yana zaune daga gaban gadonta yana jan tasbaharsa,lokaci lokaci yana duba saqonni a wayarsa. "Sabahal khair muffin" Cikin ba zata muryarta ta sauka a kunnensa. A nutse ya daga kansa ya sauke mata idanunsa. Itama shi take take kallo da fararen idanunta murmushi na fita daga fuskarta. "Muffin?......thanks ny world" Ya fadi sunan data bashin yana masa wani mugun dadi. "Sabahannur......khaifa asbahti?" Ya fada da tataccen larabcin da kana ji zakasan yasan qa'idar kowanne harafi a cikinsa yana nutsa tafin hannunsa cikin nata. "Asbahatu bikhair walhamdulillah" Ta maida masa da murmushin nan nata data tsinceshi saman fuskarta. Kansa ya langabe gefe guda kaman wani qaramin yaro,fuskarsa a narke yace mata. "I'm scared that am going to loose you,i know it's stupid,but i just can't stop thinking about it" Murmushi ta saki tana danjin nauyinsa kadan "Ka wahalar dani ne kawai......you won't lose me,am not going anywhere in sha Allah". Riqe hannunta yayi sosai cikin nasa. "That's my wish in sha Allah,you're the most important thing in my life" Sosai maganganunsa suke sake samun mazauni a zuciyarta,maganar amna data taba fada mata ta dawo mata fes akai. "You're the luckiest woman da kika samu hamma na" A yanzun take sake tabbatar da maganganun amnan,duk da a baya ta qaryata hakan. "Have your breakfast and then brush your teeth" Idanu tadan bude kadan tana kallonshi kafin ta sauke dubanta kan jerin kayan breakfast din daya jawo gabanta saman dan wani gado. "Ehnnnn" Ya fada yana dage mata girarsa,ya fahimci akwai abinda takeson fadi. "Brush din xai zama first ko?" Kai ya girgiza "No.....Brushing teeth after breakfast helps remove food particles and maintain oral hygiene" Shuru tayi murmushi na qwace mata,ba a banza ba takejin su musaddiq na gulmarsa. Komai nasa yasha banban dana kowa,tsare tsarensa ba irin na mutane bane. A jikinsa ya ajiyeta,ya dinga qoqarin bata breakfast din amma ta kasa cin komai a ciki. Iya black tea kawai ta dinga kurba,tana sha yana kallon fuskarta yana qarfafa mata gwiwa,a haka tasha rabi da qyar. Saidai tana kammalawa ya dawo duka,ta wankesu tsaf da aman shi da ita. Hankalinsa tashe ya danna wani guri,qasa da second sha biyar wata nurse ta iso. Zata karbi gyaran wajen ya dakatar da ita da harshen turanci. "Barmin zan gyara,aman nan da takeyi ne banaso,inaso shima ya tsaya ko ya tafi,ya kamata abinci ya tsaya a cikinta hakanan". "Likita yana dab da shigowa da dukka result na gwajin da akyi mata,sai a sannan zaa san abinda ya kamata ayi mata,amma yanzun xan sake saka mata ruwa don kada jikinta yayi rauni da yawa". Yana tsaye a gefe ranshi a jagule ta gama mata komai sannan ta fice,koda ya matso sai ya samu har bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke,yana jin kamar ya dawo da ciwon jikinsa,agogo ya kalla.....yau din juma'a ce,yanason samun sahun gaba gaba a masallacin ma'aiki,duk da zuwa yanzun ma yasan ya makara,baya ga haka akwai wani al'amari me muhimmanci da zai aiwatar a can din,wanda bayajin akwai abinda zai sanyashi jinkirtawa ko dakatawa a wannan ranar ta juma'a. Rana ce mafi dacewa daya aiwatar da al'amarin. Idan yace zai koma gida ya shirya ma ya bata lokaci,don haka ya daga waya kawai ya kira farouq. "Ka turo saddiq ko musaddiq......ina buqatan Friday attire please". " Ina kusa da hospital dinma......but bari na koma na duba maka kayan...." "Thanks dude" "Don't mention it....ya jikin nata?" Dubansa ya mayar kanta sannan yace "Alhmdlh....she's sleeping,inaso naje mosque ne na dawo kafin ta farka" "Zaa kula maka da ita dude....kada ka damu,dukansu na barsu suna shiryawa zasu taho nan" "Alright" Ya fada a taqaice yana ajiye wayar. Ba jimawa farouq ya qaraso,dauke da wata leda me kauri. A nan parlor din dakin ya zauna,shi kuma ya wuce ciki inda gadon sabreen din yake. Cikin qanqanin lokaci ya shirya,Moroccan jallabiyya ce fara tas me asalin tsada me adon gold din zare,sai zagayayyar hular nan irin ta larabawa wadda set ce tare sukazo da hular da loafers din dake ciki iri daya. Wani irin sassanyan kyau ya aje,saika dauka balaraben Morocco dinne,ya matsa inda take kwance tana baccinta kaman ba abinda ke damunta,ya sunkuya yayi kissing dinta sannan ya fara takowa yana fitowa. Tun bai qaraso parlor din ba yaji muryar farouq dana likitan,yana tsaye sanye da farar lab coat dinsa suna hira sama sama da farouq din. Fuskarsa sake ya miqawa fuad hannu cikin sanin darajar dan adam da iya aiki,shima ya bashi suka gaisa,sannan ya fara bude takardun hannunsa. "After conducting the necessary tests,I'm pleased to inform you that your wife is pregnant...." Likitan ya fada da murmushi a fuskarsa. Karon farko da yaji ya koma kaman dan koyo a fannin turanci,kaman ma baya gane komai. Ya zubawa likitan idanu yana buqatar qarin bayani,muryar farouq ta dawo dashi hayyacinsa. "Alhamdulillah......ya rabb lakalhamd.....alhamdulillah......muna godiya sosai likita" Farouq daya kasa zama ya fada yana kama hannun likitan da kyau ya riqe cikin nasa. "Allah ya inganta......ya bata lafiya me dorewa.....ina tayaku murna" Abinda likitan ya fada kenan yana murmushi,sannan ya miqawa farouq takardan gwajin yana masa bayani. "Idan ta tashi a bacci za'a qarasa bata duk wani treatment daya kamata" "Mun gode" Farouq ya sake maimaitawa yana karbar takardan likitan ya juya ya fice. Ganin gaba daya fuad din ya zama wani statue ya sanya farouq kai masa duka "Dude......kayi nasara.....ka jefa qwallonka a raga daidai" Sai a sannan ya tattaro kalaman bakinsa da qyar "Am going to be a father?" Ya tambayi farouq cikin neman bayani gamsashe. "Yes dude.....bakai kadai ba,harda ni,anni zata zama grandma for the first time......zamuyi yaro ko yarinya dukanmu......" Bai jira farouq ya kammala ba yayi masa wata wawiyar runguma hawaye suna kubce masa. "Ya rabba.....antal kareemul lazi ya yaraddu sa'eelan,la'ilaha llla antar rahmanir raheem......shukran ya Allah,shukran" Sai muryarsa ta karye,ya dora fuskarsa saman kafadar farouq kuka nason qwace masa. "Bansan wannan jarumin muhammadun da saurin kuka ba.....duk da na lura sabreen ta maidashi baby da gaske" Farouq ya fada shima zuciyarsa tana raunana amma yana qoqarin bawa kansa qwarin gwiwa. Kansa y a daga yana riqe farouq da kyau,yanata qoqarin masa magana amma ya kasa,sai kawai ya jijjigashi yana kada kai sannan ya taka da sassarfa yana komawa dakin. Baccinta take kaman yadda ya fita ya barta,ya sake sumbatarta a goshi da labbanta,a hankali ya furta "Kece duniyata.....na gode,na gode" Sai ya rufe mata qofar yana komawa parlor din da sauri. "Zanje nayi sallah masallaci......zan kuma aiwatar da wani abu,idan zakaje mu hadu a hanya" Ya fada yana saka hannu ya kwashe takardun ya zubasu a aljihunsa sannan ya fita da sassarfa bayan ya sanar musu su aika me kula da ita zaije juma'a ya dawo. Ba inda yakejin ya kamata yaje ya juye farincikinsa da godiyarsa ga Allah irin cikin rauda.....ya godewa Allah daya samu wannan labarin a irin wannan wajen,banda haka ya tabbatar sai yayi qaramin hauka saboda farincikin yayi masa girman da zuciya ba zata iya daukarsa ba ita kadai. *_BAYAN AWA DAYA DA RABI_* *_B A Z A T A_* Anni,amna,musaddiq,saddiq dukkaninsu suna zaune a parlor din dakin asibitin bayan sun shiga sun dubata tana bacci sun fito. Huda haneefa nadra da kuma momma bahijja sune kadai daga cikin dakin,suna taba tasu hirar kadan kadan wadda ke cike da farincki da qaunar juna. Maamah dake zaune kallon kowa takeyi kawai daya bayan daya,yanayin yadda taga sabreen a yanzu ya soma sauke mata duk wani qwarin gwiwa da takejin tana dashi akan ba ciki bane a marar sabreen din. A shigarsu ta dazu ta gama qare mata kallo da kyau,ba abinda idanunta suka hango mata kuma banda dashewa irin ta me yaron ciki. Iya wannan abun kawai data gani ya sanya gumi ya fara yanko mata,duk da yadda zuciyarta keta qarfafata tana mata romon bakan cewa ba ciki bane. A yau din batajin zata matsa daga asibitin nan ba tare da an gwada yarinyar nan ba anga uban abinda yake damunta ba. Sake jan qaramin tsaki tayi jan qasa qasa tana gyara zamanta. Gaba daya zaman wajen takeji ya gundireta,daidai lokacin fu'ad ya turo qofar dakin da sallama a bakinsa ya shigo. Sannu da zuwa dukkaninsu suka fara masa banda maamah dake jifansa da wani irin kallo. Saddiq musaddiq da amna dukka suka gaidashi da tambayar me jiki,ya amsa musu cikin kulawa kafin ya qarasa gabansu anni yana gaidasu. Da qyar maamah ta amsa,ta bishi da kallo sanda yake miqewa zai wuce ciki "Zo nan muhammadu" Ta kirashi,sai ya dawo ya samu waje yana zama kujerar dake fuskantarta. "Wannan ciwon da yaqici yaqi cinyewa ina ganin ya kamata a auna yarinyar nan asan me yake damunta,kada mutane suna zamansu lafiya taje tana yawo da ciwo tana yada ma mutane tunda gata ga yadda take a baya". Sosai maganar maamah ta sokeshi,ya kuma fahimci inda ta sanya gaba,anni kuwa sai da tayi da gaske ta iya controlling kanta. Idonsa ya lumshe kana ya budesu ya gyara zamansa. "Ba wani ciwo da ameenatu take dauke dashi a jikinta......tunda nine mutum na farko dana fara karbar mutuncinta na 'ya mace......ciwonta na yanzun kuma nine silarsa.....ga bayanin nan a rubuce" Ya fada yana zaro takardar,sai kuma ya dakata yana dubansu. "Naji dadin ganinku a tare gaba daya" Ya fadi yana sake zura hannunsa a aljihun rigarsa. Dollars dubu biyu ya fiddo sabbi kar a miqe,ya miqawa maamah takardar ya kuma miqawa anni kudin. "Abba......alhaji hamza kibiya ta hannuna ya karbawa musaddiq mahmud jadda auren amna......bisa sadakin dala biyu biyu lakadan ba ajalan ba......ta hannun wakilinsa abokinsa alhaji muhyidden kibiya da tarin shaidu cikin masallacin annabi muhammad SAW,bisa yarjewar waliyyansu ni muhammad fu'ad jadda da kuma abba wato alhaji hamza kibiya"...... TURQASHI!......FU'AD.....NACE ME JADDA?,WANNE IRIN MATCH KA TARO HAKA?,KO TAKARDAR DA MAAMAH TA WARWARE BAKA BARI TA GAMA DUBAWA BA?. TO NIDAI JAMAA WANNAN FADAN YAFI QARFINA NAYI NAN😂😂🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 115 _____________________________ _kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun yaranki da dinkuna marasa ma'ana?_ _HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS KIDDIES WEARS,irin dinkunan yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki kuma bakisan inda zakikai ayi miki ba ko kina tsoron tsada_ _Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas dagwas_ _ready _MS KIDDIES na nan kano gwammaja_ *TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani* _Maza tuntubeta a nan_ +234 708 865 2858 Ko Instagram account dinta https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA== ______________________________ 115 Dukkanin wani da yake numfashi a wajen saida jinin jikinsa ya daskare na wucin gadi,qwaqwale da yawa suka dakata da aiki na wasu mintuna,yayin da idanuwa sukayi warwaje a kansa. Kowa dubansa yake d wani irin madaukakin mamaki da tarin ba zata,dukkaninsu kowa kwanyarsa ta kasa fahimta ko sarrafa maganarsa. "Mem.....me kake cewa fu'ad?" Anni mutum qwaya daya da tayi qarfin halin sake tambayarsa tana jin yadda jinin jikinta uske tsinkewa. A nutse ya dubi annin nashi,yana da qwarin gwiwa da zato me yawa a kanta,don haka kansa tsaye yace. "Na aurar da amna ga musaddiq cikin masjid nabawi bisa shaidu da wakilai da sadaki dala dubu biyu" Sai a sannan kwanyar wasu daga ciki ta harba ta kuma dawo da aiki,ciki harda amna. Wani tsananin tsoro taji yana shigarta,ta shige jikin anni tana buya a bayanta gami da cukuikuyeta,idanunta kuma suna sauka kan fuskar maamah. Wannan fuskar da take bata wani tsoro haka kawai,fuskar da batason kallonta saboda duk wani yanayi da alamu na rashin wanzuwar alkhairi tattare da ita tana ganinsu......a yau mamallakiyar wannan fuskar itace a mazaunin surukarta?. Shi kuwa musaddiq kama hannun saddiq yayi ya riqe da kyau yana qoqarin tuna maganganunsa da hamman masa mintuna ashirin baya da suka wuce kafin ya shigo cikin asibitin. Abubuwa biyu ke masa kai kawo suna gwarabkiya cikin zuciyarsa,farinciki da kuma fargaba da wani sofane na tsoro dan kadan. Kalaman bakin maamah wani irin daci da dafi ne dasu wanda ya kasa sabawa da jinsu,baya qaunar komai ya hadashi da ita alkhairi ko sharri,dadi ko akasinsa. Idanu kawai anni ta zuba ma fu'ad tana jin tsigar jikinta na tashi. Wanne irin tashin hankali ne haka fu'ad din ya rakito mata tana zaman zamanta tana lallaba tsufanta?. Wacce masifar ce ke shirin wanzuwa?,meye kuma zai afku gaba ga amnanta?. "Allah ya sanya alkhairi......yasa anyi a sa'a" Lafuzzan suka fita daga bakin maamah da tayi qoqarin ware idanunta daga qanqancesu da tayi. Ba wanda kalamanta basu bawa mamaki ba.......kaman yadda suka janyo hankalinsu ga fuskarta wadda ta maida idanunta kan takardar hannunta tana qoqarin hana zuciyarta tsananin bugun da takeyi,tare da fatan gumin dake yanko mata ya tsane jikin atamfar jikinta ba tare da kowa ya gani ba. Abu guda daya data sani shine......tabbas fu'ad ya siyawa amna tikitin salwantar rayuwarta......don bataga ta inda zata bari itakam da ranta da lafiyarta ta hada jini da alhj hamza kibiya ba..... Idan fu'ad baiyi wasa ba a wannan karon,zata rufe idanunta tayi hukuncinta kan me uwa da wabi......zata mance da alaqar dake a tsakaninsu tunda har ya iya mancewa da matsayinta a wajensa. Saddiq musaddiq harma da amna sai lafazin maamah din ya sanya suka fara jin abinda ke ransu yana sassauta,wanda sam ba haka bane a qirjin anni da fu'ad. Wani duba sukaci gaba dayi mata,kowannensu yana son karanto ainihin ma'anar maganarta. Sun riga da sun sani.........banza bata kai zomo kasuwa......hakanan kowa ya tuba don wuya to tabbas babu lada.......ba haka kawai maamah zata bada amsa ga lamari me girma irin wannan ba......ba haka siddan zata miqa wuya ga al'amarin daya fado bagtatan irin wanna ba.....TABBAS AKWAI WATA A QASA. Lokacin da idanunta suka kai kan conclusions na gwajin sabreen din sai ta fara qanqance idanunta a hankali,ji tayi kaman debi yaji an watsa mata cikin idanunta kafin a hankali taji kaifin ganinta kaman yana raguwa. "Ciki?,sati uku?" Tambayar data samu daman motsa labbanta ta yiwa kanta da kanta kenan. Iskar dakin taji tana mata wahalar shaqa,kamar babu isashiyar oxygen dake wulgawa ta wajen,takai hannunta wuyanta tana janye mayafin data yafa waiko yana cikin abinda ya jawo mata qarancin iska,still sai taji ba abinda ya canza. Da gaske iska ke neman mata kadan,wannan ya sanya ta soma jan iska da qarfin gaske tana aikawa hunhunta don ta samu taci gaba da numfashi,yayin da ilahirin jikinta ya soma rawa kadan kadan. Musaddiq ne ya fara ankara da hakan,don fu'ad tuni ya soma takawa xuwa dakin da sabreen take don kaucewa kallon tuhumar da anni ke jifansa dashi. Baida matsala da duk wani tuhuma na maamah ko kuma kalar kowanne qalubale daga gareta,damuwarsa daya yadda annin dama zata karbi abun,ko ita dinma ya shirya mata,don bayajin akwai wani abu guda daya daya dace yayi sama da wannan din. "Lafiya?.....kaman numfashinta baya kaiwa" Anni data iso gurin ta fada tana duban hannunta wanda takardar gwajin da fu'ad ya bata ta sulale ta fadi a qasa. Yanayin sautin anni ya sanyashi dawowa da baya,yadan daga qafa yana qarasowa wajen,sai yayi saurin matsawa wayar dake ajiye a dakin don neman daukin likita ko nurses ya soma kira. Minti guda kacal sai ga mutum biyu tare da likita sun qaraso,saman wheelchair aka dorata sannan suka turata xuwa dakin da yake daura da wannan. Dukkaninsu suna farfajiyar dakin daga waje,suna jira suji bayanin da likitan zai fito dashi. Duk bayan sakanni sai anni ta daga idanu ta dubi fu'ad,gaba daya ya gama warware mata zaren tunaninta. Wannan wani abune nashi na daban,tsahon zamanka dashi zaku iya qareshi ba tare da ka iya fadin gundarim halayensa ba gaba daya,yakan zo da abubuwan da hankali da tunani basu kawosu ba,yana da bada mamaki irin hakan,saidai bata taba kawowa zai iya aikata qunar baqin wake irin wannan ba. shima kansa ya sani,duk wani kallo da anni take masa yana cure ne da mamakinsa,saidai ya sakawa kansa wannan dakiyar da juriyar da wani irin basarwa,don haka ko sau daya yaqi kallon anni,saidai yasan shi take kallo ta gefan idanunsa. Basu wani jima ba suka fito,suka qaraso gaban fu'ad din. "Ba wani abu bane me tsanani,kawai ta shiga shocked sosai daya sanya jininta hawa lokaci guda......irin wannan case din yana iya jawo mutuwar barin jiki ko bugawar zuciya idan yazo da akasi.....zuwa yanzu dai ita Allah ya tsallakar da ita,saidai kuma jininta yahau sosai,an mata allura ya kuma sauka alhmdlh,nan da awa daya ma zata iya tafiyarta gida.......amma fa sai tana kiyaye saka bacin rai da damuwa a ranta". "Na gode Dr" Fu'ad ya fadi yana bawa Dr hannu sukayi musabaha ya wuce. Musaddiq ya kalla sai ya taka zuwa cikin dakin saddiq ma ya bishi. Idonsa yaketa qoqarin kawarwa daga annin don kada su hada ido ya soma takawa zai shiga ya duba maamah din amma sai sautin annin ya katseshi. "Ka kyauta" Ta fada kai tsaye,abinda ya sakashi dakatawa daga tafiyar da yakeyi kenan. Shuru ya ratsa na wasu mintuna,sai kuma ya dawo da baya a nutse ya tsaya gaban annin. Hannuwanta ya riqe yana zaunar da ita daidai sanda take fadin. "Kaga irin abinda ka jawo ko?" Zame takalmin qafarsa yayi ya zauna sosai a gabanta ba tare daya damu cewa marbles bane a wajen. "Ban jawo komai ba anni.....kuma komai bai faru ba,ko ba wannan maganar irin wannan ranar irin wannan lokacin yana dab da faruwa da maamah....... Tunda muka tashi bamu san wani abu farinciki ba sai a sanadinku.......musaddiq ya rasa abubuwa masu yawa tun yana yaro......yanzun kuma a sanadinta sai a haramta masa abinda yake buri yake muradi yake kuma so?,bayan a baya ya rasa abinda yake buri da muradin kuma duka ya haqura?" Tambayar tasa tadan taba annin,saidai duk da haka sai takejin kaman bai kyauta ba abinda ya yiwa maamah,ko ba komai ita ta haifi musaddiq din ta kawoshi duniya. Ta bude baki zata sake magana yayi caraf ya riqe hannunta sosai,abinda bai taba yi ba. Idanunta ta daga tana duban nasa idanun,wadannan alamun bacin rai mai tsanani din sun bayyana sosai cikin idanunsa,alamun ranshi ya motsu sosai. "Kina tunanin ga musaddiq......zan bari amna ta auri wani a waje koda baice yana so ba?,wanin da bamu da tabbas a kanshi?,wanin da ban isa na hukuntashi ba idan ya cutatar da ita duk yadda muke sonta kuwa?.........Karki sake cewa komai anni don Allah na roqeki,bakinki kada ya sake furta komai a kansu idan ba fatan alkhairi ba......indai har yanzu kin yarda kina kuma ji a ranki ni da musaddiq 'ya'yanki ne.....amna qanwata ce halak malak kamar yadda musaddiq yake....to karki sake cewa komai sai fatan alkhairi.....ko meye zai faru.....ko menene zai taso anni na roqeki ki saka idanu.....nike da alhakin hakan kuma nine zan dauka". Gaba daya ya gama kashe mata jiki,ya kuma kashe duk wata kalma da yake da yunqurin fadi. Fu'ad din wani mutum ne na daban,ajiyar Allah ne,yana da kaifi wajen komai nasa,kaman yadda nutsuwa da dattako ta mamaye dabi'arsa gaba daya. "Kai da abba kuka hada baki ko fu'ad?" Anni tayi tambayar a sanyaye. Wani dariya ya tasowa fu'ad,yayi qasa da kansa yana murmusawa kafin ya daga kansa ya sake maidawa ga annin. "Ba ruruwan abbanmu.....kada ki sashi a ciki anni,aikin Muhammadu ne,ni kadai na kitsa abuna.....saboda asara ce babba ace ba wata dangantaka da alaqa ta dindindin tsakaninmu da ku anni.....kun gama yi mana komai a rayuwa....kun bamu ruhi me tsafta.....ruhi bana rai ba.....ruhi na dabi'a addini tarbiyya da ilimi da kowanne dan adam yake da buqatarsa........ba wata sakayya da zamu iya yi muku sama da wannan" Shuru sukayi dukkaninsu,jinjina kai kawai anni takeyi. Duk duniya ba wanda zai kaita son hada jini da musaddiq......to amma ita fitina ba abar so bace. "Amma anni......me kike tsoro ne duk da tarin jarumtar da kike da ita?" Ya fada cikin salon tsokana don yadan bata wani nutsuwar zuciya. Harara ta jefa masa tana dan murmushi kadan kafin ta amsa masa "Kafi kowa sanin ameenatu ba raguwa bace.....ameenatu ba matsoraciya bace.....fitina ce kawai ameenatu bataso,ita din me son nutsuwa da kwanciyar hankali ce". "Na shaida hakan" Ya fada yana murmushi sannan ya sakar mata hannunta. Miqewa tayi tana cewa "Muje na dubata.....saika samu kadan zauna da ita,ka kwantar mata da hankali ka fahimtar da ita har ta samu nutsuwa". Murmushi kawai ya saki yana zube hannayensa a aljuhun rigarsa. Anni tana wasu abubuwan kamar batasan halin maamah din ba,kamar ita din baquwa ce a dabi'unta. A zaune suka sameta saman gadon,har sun zare ruwa da alluran da suka saka mata. Ga oxygen din da suka cire mata a gefe. Dakin shuru,banda qarar ac bakajin komai,musaddiq da saddiq na zaune saman kujera suna zaman kurame su da ita. Kallo daya tayi musu shida annin ta dauke kanta daga sashensu,don ci gaba da kallon nasu bazai iya Haifa musu da me ido ba,hasali ma jarumtar da take jin zatayi tsaf zata iya kwaranyewa tayi nata wajen. Shigowarsu ya sanya musaddiq da saddiq ficewa,don dama shikam musaddiq zaman ya gundureshi,hanya kawai yake nema. "Ya jikin?,Allah ya sawwaqe ya qara afuwa" Ido maamah kawai ta runtse,batason jin sautin muryar anni sam sam. A halin da takeso ta ganta kenan,ta kuma ganta,saidai tana bawa kanta da kanta tabbacin wannan shine gani na qarshe da zatayi mata a haka,next time lallai zai zamana annin ce kwance saman gadon asibiti kamar haka......wannan alwashin saita cikashi koda numfashinta zai qare. Juyawa anni tayi ya fita tana basu waje,ya matso gabanta kadan yana mata sannu da jiki. Idanu kawai ta zuba masa na wasu sakanni,sannan a hankali ta bude bakinta. "Ci gaba da qirqirar sabbin kurakurai suma kuskure ne.......yayin gyaran kuskuren kuma komai yana iya faruwa da kowa ma......kasa a maidani gida.....jibi nakeso na koma nigeria" Iya abinda ta fada kenan tana yunqurin sauka daga saman gadon. Baice mata komai ba ya bita da kallo,saidai kowacce kalma data fita a bakinta ya rubutata tsaf ya ajiyeta,ya juya ya taka a hankali yana fita a dakin don cika umarninta. Tsaye sukayi a farfajiyar asibitin sanda motar da jordan ke tuqawa da maamah din a ciki tana barin cikin asibitin. Musaddiq ya motsa don komawa ciki bayan bacewa ganinsu da motar tayi. Caraf fu'ad ya damqo hannunsa,musaddiq ya waiwayo da sauri yana duban idanun fu'ad din. Ko sau daya bai kalleshi ba,yaci gaba da riqe hannunsa yana takawa dashi a hankali har zuwa gaban motarsa,yana isa abdulgafar ya bude masa ya tura musaddiq ciki sannan shima ya shige abdulgafar ya rufesu. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 116 ______________________________ _kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun yaranki da dinkuna marasa ma'ana?_ _HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS KIDDIES WEARS,irin dinkunan yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki kuma bakisan inda zakikai ayi miki ba ko kina tsoron tsada_ _Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas dagwas_ _ready _MS KIDDIES na nan kano gwammaja_ *TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani* _Maza tuntubeta a nan_ +234 708 865 2858 Ko Instagram account dinta https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA== ____________________________ 116 Wadannan tsumammun idanun nasa da ya saba hukuntashi dasu tun yana qanqaninsa ya zuba masa. Wani irin kallon qurilla me dauke da tarin ma'anoni da suka sanya jikin musaddiq yin sanyi tun kafin fu'ad yace komai. "Wanne irin tsoro nake gani cikin idanunka musaddiq?" Fu'ad ya jefa masa tambayar yana nuna qwayoyin idnunsa da yatsunsa. Tambayar tadan daburtashi,har ya rasa me zaice masa. "Ashe kai maqaryacin masoyi ne?......bakason soyayya batason ragwantaka ba?,bakasan mata basason ragon namiji ba?,bakasan soyayyarka bata cika soyayya ba sai ka amince zaka iya fuskantar dukkan wani qalubale da hatsari akan masoyiyarka ba?,bakasan soyayya bata amsa sunanta ba sai ta samu sadaukarwa tsananin kulawa da jure duk wani tsanani ba?........you're very stupid musaddiq muddin baka xama tsayayyen namiji ba akan amna......na aura maka amna don ubanka saboda ka kula mana da ita.......ban tsaya a matsayin waliyyinka ba saboda amna ta samu wani uban bayan abba.....ni waliyyin amna ne da bazan lamunci duk wani rashin kulawa daga gareka ba a kanta......ka riqe musu yarinya da kyau.......ka xama jarumi a kanta koda kai rago ne.......wallahi wallahi bazan daga maka qafa ba idan har naga ko naji wani abu mara kyau dangane da ita a kanka ba......yiwa auren amna riqon wasa ko ka bari tsoronka ya jagoranci igiyar aurenta dake hannunka.....to kasa a ranka baka taba sanin wani me sunan muhammad jadda ba". Gaba daya jikin musaddiq yayi laushi tubus......yana tsananin qaunar amna,irin qaunar da bai taba yiwa kowa irinta ba,to amma kuma tsoron fitinar maamah yana neman dakushe masa komai,duk da yaji cikin ransa ruwa da iska.....ko zaa saka kanshi gabas a yanka bazai iya rabuwa da auren amna ba. Qofa yasa aka bude masa ya nuna masa hanya,musaddiq ya kalli fu'ad din sai ya sauka salin alin daga motar,yasan ba lallai a yanzu ya wani bawa ban haqurinsa muhimmanci ba. Abu guda daya tak daya tuna yaji ya kwaranye masa duk wani bacin ransa.....cikinsa dake kwance cikin mararta wanda ita kanta batasan dashi ba,murmushi ya subuce masa ya sauka a hankali daga cikin motar yana komawa asibitin. A hankali ya tura qofar falon yana shiga,idanunsa suka fada kan anni. Tana tsaye da takarda a hannunta tana dubawa,shigowar tasa ya sakata daga kai ta kalleshi. Wani kwantaccen farinciki me ban mamaki ya gani saman fuskarta wanda bai taba ganin irinsa ba. Ya zare idonsa yana duban takardar sosai. Takardar dazu ce da maamah ta saki,take ya fahimci dalilin wannan murmushin,kawai sai ya shafa sumar kansa,karon farko yaji kunyar annin ta saukar masa,ya taka da dan hanxari yana wucewa cikin dakin. Sosai murmushi ya subuce mata,ta saki sassanyan ajiyar zuciya tana jin zuciyarta na wankewa daga dukkan wata fargaba da bacin rai. "Ubangiji ka rabasu lafiya,ka yiwa abinda aka samu albarka" Ta furta a sarari tana ninke takardar. Wani sanyi ne yaji yana ratsa zuciyarsa sanda yayi ido hudu da ita. Tana zaune tsakiyarsu huda......haneefa tana gefanta a zaune hannunta cikin nata. Hira sukeyi irin hirar da kana kallon fuskarsu zakasan qauna da soyayya gami da shaquwa irinta 'yan uwantaka ta huda su. Murmushi ne kawai ke fita a fuskarta,wani irin murmushi da yake sake qawata fuskarta da wani irin lallausan kyau me daukan hankali. Jingina jikinsa kawai yayi da jikin qofar,ya langabar da kansa yana qare mata kallo. Kallo yake mata irin kallon da mutum yakewa DUNIYARSA a sanda tayi masa dadi.....irin kallon da mutum yakewa ruhinsa a sanda yake tsananin buqatarsa da kuma sonshi. Duniyarsa rayuwarsa dama nutsuwarsa gaba daya yake gani tattare da ita. Daren jiya yake tunawa,wani irin dare me tsayawa a tsakiyar zuciyar masoyi,ta shayar dashi wani zazzaqan abu da bai taba hasashe ko mafarkin akwai irinsa ba sai a lokacin. Cikin jikinta ta dinga jin kamar akwai wani ido na musamman dake kallonta. A hankali tayi slow da hirar tana watsa idanunta cikin dakin,sannu a hankali ta hango fuskarsa a tsakiyar qofar yana qare mata kallo. Murmushi ya sakar mata wanda ya qara mata nauyinsa,sai ta danyi qasa da kanta,shi kuma ya tura qofar gaba daya yana shigowa. Tsam momma ta miqe tana fadin "Qaraso mana......dama masallaci nakeso mu wuce ai,ita ta riqemu wai lallai zamu barta ita kadai,tunda gaka kazo alhamdulillah" Momma ta fada cikin yanayi na surukuta tana maida takalmanta. A nutse ya qarasa gaban gadon ya bawa haneefa dake zamowa tana sauka daga saman gadon hannu fuskarsa qunshe da murmushi yayi bump din hannunta data miqa masa yana kuma amsa gaisuwar huda da basu hadu da ita dazu ba "Muna da meeting anjima" Ya fada yana dubansu,sai suka sanya dariya suna bin bayan momma bayan sun amsa masa da "Yes hamma". Shi da ita duka da kallo suka bisu har suka fice,shine ya fara dawo da dubansa kanta kafin itama a hankali ta maida duban nata kanshi. "Karki ma fara cewa zaki tambayeni akan mene" Ya rigata fadi,sai murmushi ya qwace mata tayi qasa da kanta. Idonsa ya lumshe a kanta sannan ya taka a nutse ya jawo kujera zuwa gaban gadonta. A hankali ya zauna yana sake matsowa kusa da ita har gwiwoyonsu na gogar na juna,ya saka lausasan tafukan hannayensa a nutse ya kamo nata cikin nasa yana murzawa a nutse. "Ameenatu" Ya kirata a tausashe murya a karye kaman wanda baison kowa yaji sirrinsu. Kiran da yayi mata har cikin tsokar naman jikinta,ya kuma aike mata da saqo ta cikin jinin dake gudu a jijiyoyin jikinta. Labbanta ta motsa kadan tana amsa masa da "Na'am" Sai ya lumshe idonsa labban nata suna daukan hankalinsa. "Ina dauke da wani albishir ameenatu,yayi girma da nauyi sosai a qirjina" Ya qarasa fada yana zame hannunsa daga cikin nata,sannan ya maida kansa ya kwantar saman cinyoyinta kamar wani qaramin yaro. A hankali ta daga hannunta ta dora saman sumarsa tana nutsa yatsunta a ciki,laushin sumar da santsinta suka ratsa yatsun nata,sai suka sauke ajiyar zuciya lokaci guda shi da ita kowa yana jin soyayyar dan uwansa tana keta jininsa. "Ameenatu wannan zuciyar da wannan gangar jikin duka naki ne.....kulawarki take buqata kici gaba da bata muddin kinaso ta rayu yadda ya dace" Ya fada yana jin yadda bugun zuciyarsa ke daduwa daga yadda take yamutsa sumar kansa kawai. "Zaka samu sabreen fiye da yadda kake fata.....zaka samu dukkan wani cikar burikanka a tattare da ita.....harma abinda tunani bai taba baka ba". Maganarta ta tsumashi sosai,ta kuma sakashi daga kanshi daga cinyarta. Idanu ya zuba mata sosai yana kallon qwayar idanunta,sai itama ta samu kanta da mannewa kallon nasa,kafin ya miqe a hankali tsaye a gabanta. Hannuwansa ya miqa mata,sai itama ta aza nata ciki ya tashe tsaye sannan ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki ya maida hannuwansa ya lullubeta da kyau. Ajiyar zuciya ce ta subuce masa,ya kwantar da kansa saman kafadarta. "Sabrrrrr........kinsan kin bani wata kyauta da ba wani dan adam daya taba bani makamanciyarta?" Ya soma da jefa mata tambayar data kasa gane ma'anarta. Shurunta ya fahimtar dashi cewa ya sanyata a duhu,don haka ya zare jikinsa a hankali sannan ya juyata ya rungumeta ta baya yana sake nutsata sosai cikin jikinsa. A tausashe ya dora duka tafin hannunsa saman mararta,ya dora habarsa saman kafadarta yana saka tausasan labbansa saitin kunnenta. "Sabrrrrr......you're pregnant......ciki ne dake,cikin muhammad jadda......zaki zama uwar 'ya'yana ameenatu". Wani irin abu ne ya tsarga mata tun daga tsakiyar kwanyarta har tafin qafarta,bugun zuciyarta ya qaru sosai. Samun kanta tayi da saka nata tafin hannun saman nasa dake mararta tun dazun,ta kasa fadin komai,don duk kalmar data kamo sai taji ta qwace mata,tana ci gaba da sauraren saukar numfashinsa cikin kunnenta. "Are you happy sabrrrrr?" Ya tambayeta a raunane yana fatan ya sameta cikin irin yanayin da yake jin kansa shima. Kai ta gyada a sanyaye,tanajin wani irin yanayi yana ratsata,mamakin yau itace wai dauke da ciki?,itama zata zama UWA?,zata haifi d'a ko 'ya a cikinta?,abun kamar cikin mafarki. "Alhmdlh" Ya fadi yana sauke mata tattausan kiss a wuyanta,a hankali kumya ja dawo da ita tana facing dinsa sai ya rungumeta tsam a jikinsa. Shuru ya ratsa tsakaninsu na sakanni,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa ta cikin kunnuwanta dame kwance a qirjinsa,sosai kaman akwai wani abu dake taba zaman lafiyarta,kusan minti biyu sannan ya sauke sassauqar ajiyar zuciya a sanyaye sannan ya dagata daga jikin nasa yana kallon fuskarta. Qwayar idanunta ya laluba ya saka nashi a ciki,da wani irin coolness ya sake kiran sunanta. "Kinji yadda zuciyata take bugawa ko?" Ya jefa mata tambayar yana lalubar tafin hannunta ya matse gam cikin nasa. Kasa amsa masa tayi da baki sai kai data gyada mass,saboda cikin idanunsa abubuwa ne masu yawa ta gani suna yawo. "Sabrrrr.....na gode da kika karbi ajiyata da sauri haka......inajina kaman ni kadai nake rayuwa cikin duniya......ashe rashin haduwa da tawa DUNIYAR shine sila......sabrrrr......bansan dame zan saka miki ba......bansan kuma da meye zan gode miki ba....kome na kalla sai naga kamar yayi kadan,alfarma daya kawai nakeso ki yiwa rayuwata. Kallonsa da kalamansa gaba daya qara kashe mata jiki sukeyi,mamakin irin tsananin son da yakewa yara ne yake sake kamata,ta motsa labbanta a hankali "Tame?" "Kiyimin alqawari zaki rayu dani....kiyimin alqawari ba zaki taba rabuwa dani ba.....kiyimin alqawari zaki zauna dani,da dadi ko babu.....cikin wadata ko talauci.....sabrrrr kiyimin alqawari ba zaki taba tafiya ki barni da yara ba.....zaki zauna dani dasu a duk yadda nake ko suke,mu rainesu tare.......kiyimin wannan alqawarin sabrrrr cikin wannan garin me tsarki". Idan ba qarya idanunta sukayi mata ba hawaye ne kwance cikin idanun muhammad jadda din......taja numfashi sosai har kaman kayan cikinta zasu hade waje daya. Ita daya ce mutum na farko a duniya data taba ganin wadannan tsadaddun hawayen da suke zuba SILAR QAUNA daga idanun me jadda......tana fata ta zama mutum.na qarshe da zata gansu,kuma ta zama sila na goge hawayen daga idanunsa gogewa ta har abada. Abu daya ta lura dashi har yanzu yana da tsoro game da halin mata......har yanzu wannan ciwon da maamah ta dasawa rayuwarsu yana masa zugi da radadi.....har yanzu yana jin kaman abinda ya faru da abbansu zai faru dadshi,a yanzu haka a shirye take ta goge masa dukkanin wannan fargabar da shakkun,don haka ta zame hannuwanta daga nashi,ta sulale tana duqawa saman gwiwoyinta,sai ya gaza tsaiwa ya silale shima ya bita. Hannuwansa ta riqe da kyau tana kallonsa cikin tsakiyar idanunsa. "Allah ya zama shaida.....annabin Allah ya zama shaida,ni ameenatu sabreen na shirya rayuwa dakai da dukka abinda zamu haifa......na sadaukar maka da dukka rayuwata sadaukarwa ta har abada......dadi ko wuya sunyi kadan su raba tsakaninmu.....zan zauna dakai tamkar dominka kadai aka halicceni,bazan barka ba muddin bakai ka buqaci hakan......". Ai bai iya barinta ta qarasa fada ba ya hade bakinsu guri guda. Sai daya tabbatar ya kwashe ragowar maganar tass daga bakinta sannan ya zare bakinsa daga nata yana kallonta da birkitattun idanunsa. "Ta yaya zan iya rayuwa ba'a duniyata ba?.......ta yaya dan adam zai rayu babu duniyarsa?,indai babu ta yadda hakan zata kasance....to ki sanya a ranki ni Muhammad jadda don ke kadai MAAMAH ta haifeni". Batasan sanda ta zube saman kafadarsa ba tana jin wani irin alfahari yana ratsata,tana jin tabbaci da yaqini suna ratsata.....ashe akwai sauran maza irin muhammad jadda din?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 117 117 Guri kawai ta samu ta zauna cikin dakin daya kasance ita daya ce qwallin qwal a ciki. Duk yadda taso ta cinye ta kuma jure ta kasa,bata ankara ba kawai taji ta fashe da kuka. Ta yaya haka zata kasance?,bata tsira da komai ba sai hawan jini?. Wanne irin kafaffen yaro ta haifa?.....aure tsakanin musaddiq da amna?,wacce irin asara ke bibiyarta har haka?,da gaske kamam yadda boka ya gaya mata taurarin nasararta ke bacewa?,taurarin nasararta ke dakushewa?,ina dukka kaifin hankalinta da zallar iya takunta suka tafi?(ta mance cewa shi Allah gwanin hikima ne,yana iya yiwa bawa talala,yayi shekaru aru aru yana zalinci,a nasa hangen da tunanin nasara ce,sai Allah ya barshi da wayonsa da tunaninsa,ya turo.masa nasara a gabansa,plan dinsa yayita tafiya daidai,kwatsam idan yaso kamashi zai da damqeshi a tsakiyar wannan plan din da shirin nasa da yake tunanin sune mafita a gareshi,sai ya zurma yayita bundum bundum. Idan yana da rabo sai ya gane zunubansa da kuma kusakurensa yayi gaggawar tuba....idan baida rabo kuwa,zaiyita ganin INA DA SAURAN DAMA,INA DA SAURAN LOKACI yana tsaka da wannan lissafin sai ubangiji yayi ram dashi,dauri gaba dauri baya,me kwanceshi kuma sai ubangijin daya qulle abinsa. Duk runtsi.....duk tsanani,duk yadda za'a je a dawo karka yadda ka cuci kowa,daka cuci kowa gwara kowa din ya cuceka. Duk juyin da za'ayi ka tabbatar zuciyarka wankakkiya ce......kana bacci amma sai ubangiji ya zama jinka ya zama ganinka,ya zama me jagorantar al'amuranka,ubangiji ka barmu a naka duniya da lahira,karka bari duniya da abinda yake cikinta ya rufe mana ido don girman zatinka,karka bamu damar cutar kowa don isarka🙏🏽🙏🏽🙏🏽). Abune a rayuwarta data manta rabon data yishi wato kuka,shekaru masu yawa da suka shude mata,amma sai gashi yau tana zubda hawaye sanadin anni amna da sabreen. "Lallai dole fansa ta biyo baya.....lallai dole ku biya bashi da fansar zubar wadannan hawaye......dole sadaukarwa ta biyo baya.....wala'alla akwai rayuka da zasu salwanta......rayukan da shudewarsu shine silar wanzuwa da samun nutsuwar zuciyata" Ta fadi a fili tana kallon idanunta da suka tasa saboda kukan data share mintuna tana yi. A gaggauce ta sake goge fuskarta ta,sannan ta koma wajen luggage dinta ta soma ninke kayan ciki tana zuba wadanda suke gefen gado da kuma cikin toilet din dakin. Tanajin ta qagauta gari ya waye,tana jinta.kaman saman qaya,a jikinta da ruhinta takejin bata da wani sauran zama a garin,bata da sauran abinda ya rage mata da zata zauna tayi cikin qasar(subhanallah). ★Sau tari wata soyayyar tana zamewa madubi kuma abar sha'awa ga wanda ke gefe yana kallo. Wani memories din na wasu masoyan kan samu wajen zama na din din din cikin kwanya ya kasa gushewa saboda girman tsumammiyar soyayya zallar kulawa da qauna me gusar da hankali saboda tsananin kusanci da kulawa tsakanin masoya. Fu'ad da sabreen......soyayyarsu ta zamewa wasu tamkar makaranta.....ko kuma allon da zaka kalla ka karance ilimin dake shimfide a kanshi. Wucewar maamah Nigeria ya samar da nutsuwa me tarin yawa ga wasu zukata,wadanda sam basusan gaibun dake tattare da tafiyartata ta barsu ba. Wani lullubabben gaibu me cike da duhun sirrikan da ita kadai ta barwa zuciyarta shi. Samun sararinta da gushewar wanzuwarta a family din ya bada damar baje kolin soyayya masu dauke da nau'ika kala kala. Sabreen da fu'ad,suna rayuwa da nunawa juna soyyaya da kulawa tamkar sun manta da akwai wasu halittun dake gewaye dasu suna tasu rayuwar. Sau tari idan fu'ad yayi wani abun saidai kowa ya runtse idanunsa,don ba wanda yake gani sai sabreen da cikinsa dake manne a jikinta. Gaba daya kaman ya mance da kowa sai ita sai hidimarta,wani lokacin hankali yafi zuwa jikinta akanshi,don takan tuna da anni a wajen ta rage wani abun. Duk da abun ya zowa anni a sabo,amma saita zama suruka me yawan bada uzuri da dauke kai. Bata shiga tarayyarsu ko kadan,saita dinga nesa nesa dasu gudun ji masu kunya duka ita dasu. Wannan soyayyar sai ya hura wuta biyu......tsohon tsumin soyayya ya balle tsakanin musaddiq da amnansa,duk da cewa daga nesa nesa ake komai don anni bata bari abun ya zurfafa da yawa. Su dinma duk yadda sukaso su boye dole ita soyayya bayyana kanta takeyi koda an boyeta. Sannu a hankali sai wata wutar munafukar soyayyar ta soma kunnuwa kuma daban tsakanin saddiq da huda. Duk wani nuqu nuqu da sukeyi hakan bai hana sabreen karantar komai ba,ranar sun dawo daga masallaci take tseguntawa fu'ad hancinta ya lakace mata. "Kin iya sa ido duniyata.......banda nidin ina da qarfin kurwa banjin zan qwace filin soyayyar da akewa su huda.......Allah ya taimakeni nayi hasashen tsaf zaki iya guduwa ki barni.......nayi miki yankan baya na kawo miki su.....to me ya rage?". A mamakance ta zare idanu dariya tana qwace mata,sai ta boye kanta cikin qirjinsa tana qoqarin musanta maganar. Saidai kuma a zahirin gaskiya cike take da mamaki,wanne irin mutum ne fu'ad din me tsananin kula har haka?,ta yarda dari bisa dari baya wasa da duk abinda yakeso. Duk wadannan abubuwan da yake faruwa bai hanasu ibada ba tuquru........zamansu tsakanin makka da madeena yafi yiwa fu'ad dadi sama da kowa,tunda ko banza yace za'a qiri halittar danshi ko 'yarshi a guri me tsarki da tsarkakken ruwan zamzam wanda shine komin sabreen. Komai da zamzam takeyi,shine ruwanta nayin komai,iya falalar ruwan zam zam kawai ya sanya yake qara jin nutsuwa da zamansu a nan. Tuni ya mata register da komai na zuwa awo da haihuwa,don yace indai yana da rai da lafiya to tabbas a garin madeena yakeso a haifa masa yaransa,ya tsara komai ba tare daya gayawa kowa bama. *_K'ADDARA KO GANGANCI?_* _KALLON KALLO_ Sau uku tana rolling sassalkar luxury Egyptian abaya din tana warewa. Kawai sai tayi zaune gaban madubin tana ware hannuwanta gami da binsu da kallo. Batasan me yasa ba......batasan kuma me yake faruwa ba,shagwabata da yayi da yi mata hidimar komai ne sila ko kuma cikin jikinta ya sanya ta zama raguwa?. A karo na hudu ta sake gwadawa sai veil din ya sabule salin alin daga hannunta. Ido ta zubawa fuskarta,sai taji hawaye kawai ya kubce mata. Murmushi ya saki yana qarasa sanya link din hannun kuftan jikinsa,ya soma takowa a hankali zuwa bayanta. Tun daxun da taketa drama ita da dankwalin yana kallonta,yasan qarshen maganar dama ta sanya kuka tunda ta zama rigimammiya ta gaske. Kafadunta ya kama ya tasheta tsaye,suka hada ido sai yayi qoqarin danne dariyarsa,saidai tuni ta riga ta gani. Daga hawaye sai ta sakar masa kuka me qaramin sauti. "Subhanallah......me kuma nayi?" Ya fada yana dora damuwa saman fuskarsa duk da da gasken dariya yakeson yayi. "Ya isa....am sorry if I offend you" Ya fada yana sakata a qirjinsa. Shaqa daya ta yiwa turarensa nutsuwa ta fara saukar mata,sai ya bata lokaci sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya dagata yana duban fuskarta. "To mene ne?,.....uhmmm.....tell me" Tabe baki tayi,ta miqa hannu taja kumatunsa. "Ba mayafinne yaqi dauruwa ba,sannan kuma kai kazo kanamin dariya saboda ina ramewa kai kuma kina qiba". Wannan karon kecewa yayi da dariya sosai harda riqe ciki. B wani bane ya jawo masa wannan jagwal din ba sai amna,haka kawai ta sashi gaba vanilla ice cream takeson sha,suka yiwa anni wayo suka fice wadda ta jima da hanata shan kayan zaqi da sanyi. Koda sukaje kasa sha tayi.ma gaba daya sai ya fita a ranta,shi kuma duk da bai dameshi ba amma sai yaji ya masa dadi,yasa aka kawo masa ya soma sha,ashe tana ankare,ke amna kika ce "Hamma madeena ta karbeka Allah,ka karbe jikin adda ka hada da naka,kanata kumatu" Ta fada tana dariya. "Lovey dovey.....kin manta ni yayan mijinki ne kenan?" Ya fadi hakanne don shine abu daya yanzu da yake kashe bakin amna,ya kuma fadi hakanne don ya fuskanci sabreen din har ta kumburo fashewa kawai take jira tayi. Ashe abun dashi ta kwana sai yanzu ake fashe masa shi. Sulalewa yayi ya durqusa gabanta,ya zagaye hannunsa a bayanta yana dora fuskarsa saman mararta. "Kazo mu bawa mama haquri....mun hanata qiba mun hanata cin kayan dadi....mun tuba....zamu gyara halinmu" Ya qarasa maganar yana hade hannuwansa guri daya. Da ido ya bita ganin daga kuka ta koma buga murmushi,ya girgiza kai kawai a ransa yana gulma,wato me ciki sai a barta kawai.....abun kuka ko bacin rai baya mata kadan,cikin dabara ya jata ya sauya mata yalwataccen mayafin rolling din ya daura mata da kanshi,don bayason wani sashe na jikinta ko kadan ya fita wani ya gani. Yana gama mata ana knocking qofar,yasan waye farouq ne,qiri da muzu ya zama fusataccen qarfi da yaji,yace fu'ad ya jawo masa raini,ya hada tuxurantaka da aure da qannensa,in fact ma qanin bayansa ya rigashi amsa sunan me aure,wannan ta saka dole qasa daya data rage musu akayi cancelled trip din sai bayan wani lokaci,aka aikewa da iyayen fanna date na bikin sati biyu masu zuwa wato sati biyu da komawarsu nigeria kenan. Hannunta cikin nashi yadda suka saba suka fito a dakin,ta zame hannun nata a dabarance ta qarasa gaban anni ta gaidata,ta gaida momma wadanda zasu sauka duka a nigeria,da yammaci kuma jirgi zai wuce dasu mali saboda washegari huda zatayi ton prints na jarabawar kammala secondary school. Haka suka wuce airport cikin motocin da a nan qasar yake barinsu sai kuma zuwa na gaba. Anata zuba soyayyar munafunci tsakanin amna da musaddiq,huda da saddiq daketa babbasarwa kaman ba komai tsakaninsu,angon gobe farouq kuwa anata sallama da fanna ta waya shima ya bude wuta sosai don shirye shirye sun gama kammaluwa,ranar kawai suke jira. Ita kuwa kanta yana kwance kawai saman kafadarsa. Tun bata saba ba har ya riga ya saba mata,wata kasala take fama da ita,bata iya cikakken zama ba'a jikinsa. Tunda jirginsu ya tashi take jin gabanta yana faduwa lokaci lokaci,tadan rufe idanunta kadan tana jan sunan Allah,ko shima sabuwar faduwar gaban tana cikin laulayin ta yiwa kanta da kanta tambaya. Idonta ta rufe tana fatan bacci yayi awon gaba da ita wai ko zata samu sassaucin abinda takeji,tana iya jin sanda ya sanya blanket ya lullubeta,sannan ya sake rufeta da faffadan qirjinsa yana rufeta tsam cikin jikinsa,ajiyar zuciya me sanyi ta subuce masa ya dora habarsa saman kanta a tausashe. Cikin zuciyarta take roqon Allah......kada ya bata ikon butulcewa wannan bawa ko juya masa baya.......ita kanta wani lokaci irin yadda yayi nisa a soyayyarta tana jin kamar tata zuciyar zata narke a kansa. Tsakanin ita dashi batasan waye yafi wani yin nisa ba,waye yafi wani yin zurfi bs,fatanta kawai shine kada su zama masu butulcewa juna a tsakaninsu. Tafiyar awanni biyu jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano dake kano. Sai takejin farinciki yana ratsata duk da ta baro wani guri mai muhimmancin gaske a rayuwar duk wani musulmi. Abu guda daya da yaci gaba da farautarta shine faduwar gaban dake qara tsanantar mata,duk sai take jinta a rikice har zuwa sanda suka qaraso inda jerin gwanon motocin jadda diamond suke jiran qarasowarsu. Kusan dukkanin guards dinsa sun zo tararsa cike da girmamawa da kuma kewarsa da sukayi na tsahon lokaci. Sabule hannunsa yayi daga cikin nata,abinda ya sanyata daga kai ta kalleshi kenan. Murmushi ya sakar mata me taushi yana dubanta. "Zaku fara yin gaba saboda ki samu zama dasu huda kuyi sallama......zan qaraso yanzun......nasan a gajiye kike amma ma'u ta tanadar miki komai.....kada kice zaki jirani,kiyi wanka kici abinci kiyi bacci sosai......yau akwai biyan bashi" Ya furta maganan qarshen qasa qasa yadda ba wanda zaiji musu sirrinsu. Duk da yadda gabanta ke tsananta faduwa,duk da yadda takejin kaman zaini wani wawan nisa da ita......irin nisan da takejin tazararshi tayi yawa amma saida murmushi ya subuce mata. A tausashe yayi kissing goshinta yana dubanta. Raunin da yake ganin cikin idanunta shi kansa baisan na meye ba,ya saka hannu da kansa ya bude mata qofar motar dasu huda ke jiranta,ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata abayarta data fito waje ya maida ciki. "Kada ka dade" Ta samu kanta da fadi masa a karye sanda yake shirin rufe mata qofar "In sha Allah" Ya bata amsa yana jin dadin kulawa da damuwa dashi din data nuna,ya rufe qofar a tausashe sannan yaja baya ya kira abdulgafar sukayi magana,ya kira abdulbasit shima sannan ya sallamesu suka tashi motocin da zasu kaisu gida,ya rage sauran wadanda zaiyi amfani dasu ne kawai. Ta cikin side mirror din motar tasu ta zuba masa idanu,suna sakeyin gaba yana nisa da madubin har ya bacewa ganinta,saita lumshe idonta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tana jin karadin su huda sanda suke fita daga airport din amma ta gaza saka baki a hirarsu,kawai tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa ne.......har zuwa sanda qarar harbin bindiga har sau biyu ya sauka a kunnenta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta fada da wata irin zabura tana ware idanunta gami da miqewa ta zauna sosai faduwar gabanta yana ninkuwa. Salatin da taja shi ya sanya kowa a motar ya dauke wuta,momma dake seat din gaba ta waiwayo da hanzari tana kallon fuskar sabreen din. Huda ce tayi qarfin halin fara tambaya "Lafiya adda?". " Qarar harbin bindiga huda......bakuji ba?" Ta tambayesu a rude tana raba idanunta akan fuskarsu. "Nidai banji ba" Huda ta fada tana girgixa kai "Naji....harbi ne,amma kamar nesa da nan" Momma ta fadi tana dubansu daga inda take "Nima naji momma" Nadra itama ta fada tana dubansu. Kan hanya hankalinta yakai,sai taga kaman driver din nasu ya qara gudun motar fiye da yadda suka fara tafiyar,hankalinta taji yana neman dagawa sosai,sai ta kalli su momma din tanajin kaman haki yanason kamata saboda tsananin bugawar da zuciyarta takeyi. *_Tabdijan.......meke shirin faruwa ne?,me kuke hasashe?,me karatu mu hadu gobe idan me duka ya kaimu_* *_akwai yaqi kenan_* *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 118 118 "Momma ba'a nesa harbin nan yake ba......koda a nesa dinne bawai ness can damu ba......mun baro su hamma a ciki momma.....bamusan me yake faruwa ba.....driver!" Ta ambata da qarfi kaman numfashinta yana son qwace mata. "Yes madam" Ya fada da dan qarfi shima yadda zata iya jiyoshi. "Mu koma mu duba boss......qarar harbi nakeji". " Am sorry maaa.......nima naji,kuma umarni ne na boss din shi ya horemu,duk sanda mukaji abu irin wannan kada mu sake mu koma da baya......kuma ko a tsarin tsaro ma hakan ganganci ne.....kiyi haquri mu qarasa gida.....we are safe in sha Allah". Yana kaiwa qarshen maganarsa qarar wani harbin a jejjere har guda biyu ya sauka a kunnensu. Qarasa gigicewa tayi gaba daya,jikinta da muryarta gaba daya suka dauki rawa. "Ta cikin airport dinnan ne momma.....idan safe nake hamma fu'ad fa?" Ta jefawa momma tambayar cikin rauni hawaye na gangaro mata. Girgixa kai momma tayi wadda ke qoqarin boye nata tashin hankalin. "Bazaiyiwu a koma ba kaman yadda kika ce.....hasalima baki da tabbacin a inda suke abun yake faruwa ko wani shiyyar ne na daban.....koda a inda suke ne ma shima bazaiso ace koma meye ya hada dake ba....." Momma take fadi cikin son lallashinta. Sam hankalinta ba'a jikinta yake ba,bata ma kama maganar momma ba saita jawo jakarta jikinta dukka yana rawa ta fiddo wayarta tana cewa. "Gabana yanata faduwa ne momma,tabbacin akwai wani abu da ba daidai ba" Tayi maganar tana zaro wayarta da zummar kiran number fu'ad din. Abun takacin abinda kuma ya sanya a karan farko tayi Allah wadai da halinta shine. Ba number wata number da tayi kama da tasa cikin contact dinta,sai a sannan ta tuna,waccan tafiyar da yayi ya kirata sau daya,batayi saving number nasa bama,kuma koda ta duba call log babu number a wajen. Kuka ne ya qwace mata ganin yadda suke qara nisa da airport din ba tare da tasan halin da yake ciki ba.....don gaba daya jikinta yana gaya mata akwai gagarumar matsala. "Ni ku saukeni......xan koma na dubashi,zan tabbatar da lafiyarsa saimu taho tare dashi" Ta fada muryarta na rawa. "Kiyi haquri madam......aikina bazai cika ba saina kaiki gida lafiya.....aikata hakan zai zama zunubi mafi girma a wajen boss,har gwara na kaiku gida na miki alqawarin dawowa na duba miki lafiyanshi". Abdul rauf ya bata amsa shima yana jin damuwa sosai da fargabar kada wani abu me muni ya faru da ogansu. Sam bata gane abinda momma ke fadi mata ma,ta rarumo wayar ta soma lalubar number anni ko amna. Number amna ta fara gani saita kira kawai tana fatan ta samu su daga don su suna motar gabansu. Bugu daya aka daga,anni ce ba amna ba,kai tsaye ta fara magana. "Anni harbi akeyi cikin airport anni.....kice musu mu juya mu koma,munbar hamma a can,dukkanmu mun taho saura shi kadai". Asalin damuwa anni tana ciki,amma ta danne don kada ta kashe mata qwarin gwiwa. "Kiyi haquri sabreena......in sha Allah yana lafiya,don bamusan me yake faruwa ba,da mutane da yawa a ciki bamusan akan meye harbin ya kasance ba....." "Anni jikina yana bani wani abu.....anni don Allah ku barni na koma" "Ameenatu" Anni ta kirata da asalin sunanta. "Na'am anni". " Kita karanta lahaula walaquwwata illa billah.......bari mu qarasa gida saimu laluba abinda ya faru kinji?". Ba yadda zata iya ci gaba da musu da annin,don haka tace mata to kawai tana sauke wayar daga kunnenta ba tare data kashe ba. Hannu momma ta miqa ta dauki wayar suka fara magana da anni. "Ta shiga damuwa,don Allah bahijja ki bata baki,kinga ba ita daya bace,a irin wannan yanayin bata buqatar tashin hankali". " In sha Allah anni" Daga haka ta ajiye wayar ta kamo hannun sabreen din. Duk wani kalar bada baki da bada haquri momma ta yiwa sabreen din,saidai kawai tana jin momma dinne bawai don ta gamsu da dukka abinda suke fada ba,tana ji a jikinta akwai wani abu maras kyau daya taba hammanta,a cikin zuciyarta da ruhinta takejin hakan. Yadda anni taji muryarta ya sanya tayi ma abdur ra'uf magana dukansu suka wuce zuwa mansion House din alhaji hamza kibiya. A babban parking lot na gidan motocin dukka suka tsaya. Abdulgafar ya qaraso ya bude mata side dinta,su huda da momma suka fita ta daya side din. Da qyar ta miqe bayan ta zuro qafafunta waje,jikinta idanunta dama zuciyarta gaba daya takejin sun mata wani irin nauyi. Duba daya zakayi mata ka fahimci hankalinta baya jikinta,daga airport din zuwa gidan kuwa idanunta sun fara tasawa saboda kukan data matsawa kanta dashi. A hankali da wani irin sanyi ta zube idanunta akansu anni wadda ke tsaye ita da musaddiq da saddiq,dukkansu su biyun waya sukeyi,amna kuma da alama tanata qoqarin samun wata number ne amma kiran yaqi shiga. "Anni na kasa samun wayarsa,a kashe take" Muryar amna kenan data sakata jin wani jiri yana niyyar kayar da ita. Baya ta koma kawai ta jingina da motar data fito a cikinta,tana jin momma sama sama tana riqe hannunta. "Na samu Jordan" Muryar saddiq kenan daya fada da wani irin kuzari,abinda ya sanya anni da su amna duka dawowa gabansa suka tsaya. Dif sukayi suna jiran joradan ya daga,amma harta qaraci ringing dinta ta katse bai daga ba. Idanu sabreen ta mayar ta lumshe,tana jin yadda bayan wucewar kowanne daqiqa zuciyarta ke ninka gudu kaman zata tsaga qirjinta ta fito,tana jin wata sallamawa tana ratsata,tana jin cewa da gaske wani abu ya taba mata hammanta......da gaske wani abu ya faru dashi cikin airport din,sai qafafunta suka fara rauni tana jin suna fara gazawa wajen dauke nauyinta. A kunnenta kira na uku ya yanke ba tare da jordan ya daga ba. "Wallahi shine.....Allah wani abun ya faru dashi.....naji a jikina fa" Ta fadi da qarfin muryar da har na nesa saida suka jiyota,wanda kafin su huda sukai ga riqeta ta sulale a wajen tana sakin wani tsumammen kuka tana jin mararta na riqewa gam. Da wani irin sukunannen gudu anni ta qaraso,suka dagata ita da momma Hankalin annin yana tsananin tashi. "Karkiyi mana haka sabreen......ba abinda ya faru dashi mana.....ga jordan nan an samu wayarsa dagawa ne baiyi ba". Idanunta fal da kuka wadanda zuwa yanzu sun canza launi zuwa red ta kalli anni. " Indai da gaske lafiya qalau ne ya daga wayar yayi bayani mana?,ya daga wayar yace ba abinda ya faru mana anni?,me ya hana wayar hamma shiga bayan sanda muka fito a jirgi ma ya amsa kira?". Rudata kawai tambayayoyin sabreen sukayi gami da sage mata gwiwa,saita rasa amsar bata. Duk da haka ta rungumota jikinta tana cewa. "Amma kamar fatan alkhairi ya kamata kiyi ko sabreen da hasashen alkhairi?" "Na kasa anni.....zuciyata ce taketa gayamin akwai abinda ya faru dashi,ba laifi na bane......DANGANTAKAR ZUCIYA ce tsakanina dashi.....ko meye ya sameshi zuciyata zata gayamin saboda alaqar dake tsakaninmu" . Sosai anni ta lura kaman hankalinta yana neman gushewa ne,don haka ta sake riqeta da kyau tana cewa. "Shikenan,mu shiga ciki,zan tabbatar miki lafiya qalau yake.....zan kiramiki shi kuyi magana". Tamkar raguwar ciwo ko zugi daga kasu daya cikin dari shine kawai d'an abinda furucin anni ya yiwa sabreen cikin zuciyarta. Anni da momma suka riqeta da kyau kowa cike da fargaba duba da abinda yake jikinta tattali yake buqata kaman yadda tun a madina likita ya gaya musu suka wuce da ita zuwa ainihin babban falon gidan. Baya kadan anni ta dawo tayi magana da saddiq kan yayi duk yadda zaiyi ya samo ainihin abinda ya faru sannan ta kira musaddiq suka wuce akan yazo ya zauna yayita kiran fu'ad har sai an sameshi ya daga suyi magana ko hankalinta zai kwanta. Kaman yadda hawaye yaqi tsaiwa a idanunta haka ma kuka yaqi dakatawa. Ruwa me sanyi sanyi anni ta saka aka kawo Mata,ta tsiyaya mata ta miqa mata tana fadin. "Karbi kisha tukunna ko zuciyarki zatayi sanyi" Kai ta girgiza kawai fuskarta shabe shabe da hawaye,abinda yake taba zukatan su huda kenan har sai da anni ta sanya ma'u ta janyesu zuwa wani falon na daban. "Ko nasha anni bazai iya wucewa ta wuyana ba.....inaso nasan halin da yake ciki ne kawai". A sanyaye musaddiq daya gaji da kira ana ce masa a kashe take ya dubeta,sai kawai ya ajiye wayar ya miqe tsam.yana duban anni "Ina zuwa" Ya fada yana fita da sassarfa daga dakin. Kiransa anni takeyi saboda jikinta ya bata abinda zai aikata daga yanayin tashin nasa,amma baiko waiwayo ba bare ya dakata. "Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Anni ta fada tana sadda kanta qasa. Awa guda kenan amma ko daga security dinsa da guards dinsa ba wanda ya samu labarin abinda ya faru. Sun koma airport din amma tun daga tafiya me nisa ma an hana shiga gurin bare su binciki abinda ya faru.....ina yake?,wanne hali yake ciki?. Duk da sun bayyana kansu a mazaunin masu tsaron lafiyarsa amma an dakatar dasu an kuma basu haquri ance su jira,ko meye ake ciki daga baya zasuji. Zamewa tayi sosai a nan inda tayi sallah tana kukan zuci,tana jin kamar zata hadiye zuciyarta. Batasan ta inda zata fara rayuwa ba idan wani abun ya samu Muhammad........batasan ta yadda zata iya karbar wannnan qaddarar ba. Me yasa rayuwa zatayi mata haka ne?,me yasa rayuwa zata zo mata da irin wannan yanayin ne?,me yasa rayuwa take wasan kura da ita?,take nesantata da wadanda ta sanya rai da fata me tsanani a kansu?,take nesantata da duk mutumin da zai jibanci lamarinta?,duk mutumin data dora rayuwarta da burinta a kansa?. A nan tayi la'asar ba tare data ko motsa ba,anni tasa aka shigo mata da abinci amma ko sha'awa baya bata ballantana tayi tunanin ci. Xuwa qarfe biyar ta koma tamkar ruwa saman abun sallar,zuciyarta na sake yayyankewa da tsananin tsoro da tashin hankali. Biyar da mintuna anni ta sake shigowa. Duba daya zaka mata itama kasan hankalinta ba'a kwance yake ba. Musaddiq da saddiq da baisan fitarsa ba har yanzu bai dawo ba,hakanan tasa wayar still tana kashe shima tunda ya fita yabar gidan. A sanyaye ta qaraso gabanta tana qoqarin tattaro dukka dauriyarta waje daya,ta zauna a qasa daidai saitin qafarta tana kallonta. "Tashi ameenatu" Anni ta fadi cikin jarumta. Kaman ba zata iya tashi ba ta daddafa ta tashi. Amanta uku ba wanda ya sani,abinda ta dauka tayi adabo dashi tunda ta samu kulawa a madeena sai gashi tashin hankali ya sanya ya dawo. A cikin aman nan guda uku ba kalar azabar da 'yan hanjinta basu gani ba,don babu komai a cikin nata. "Kinyi imani da Allah da ranar lahira?" Kai sabreen ta gyada mata hawaye na fara taruwan mata. "Kinyi imani da Allah shine me rayawa shine me kashewa?,shike bada kariyarsa akan kowanne abun halitta?". Kai ta sake gyada mata hawayen data riqe suna sauko mata. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 119 119 " To inaso ki yarda da Allah ki kama ambatonsa....kibar masa kuma lamarinsa.....karki dauki haqqin abinda ke kwance a mararki ta hanyar hana kanki abinci.....don cin abincinki ko rashin cin ba abinda zai canza saima cutar da yaronki,ki samu wani abu ko ba yawa ki sakawa cikin naki". Hawaye sosai take tana kada kai. "Ba hanya anni.....bana jin abinci xai samu hanyar wuce kwata kwata". "To ai akwai abu me ruwa ruwa a ciki,ki duba ko yaya kisha" Ta fada tana buda kwanukan gabanta. Lafiyayyen kunun gyada ne da yasha madara yayi fari sol,da kanta anni ta zuba mata a mug ta saka sugar dan daidai sannan ta miqa mata. Karba kawai tayi tana wassafa yadda zata sanya a bakinta,kai.anni ta jinjina mata cikin son bata qwarin gwiwa,wannan ya sakata kai mug din bakinta. Kurba uku kawai tayi ta dire,annin bata matsanta mata ba ta dauka kawai ta rufe ta bata ruwa. Kurba daya shikam ta ajjiye,saboda batajin zai zauna a cikin ta. Bakinta ya saba da zartsin zartsi na taste din zam zam. Annin ta fahimci haka,don haka ta qwalawa ma'u kira tace ta duba store ta ciro zam zam babban roba. Ba jimawa ta dawo dashi,annin ta bude ta tsiyaya ta bata. Wannan karon anci sa'a,tas ta shanyeshi ta ajiye cup din,hakan ya yiwa anni dadi,saita matsa ta dauki counter tasbaha ta maqala mata a yatsunta "Hasbunnallahu wa ni'imal wakil,wallahu galibun ala amrih sau ba adadi" Kai ta gyada a hankali tana jin hankalinta yana karkata ga addu'a maimakon kuka da bala'in tashin hankalin da takeji. Sai da anni taga ta kama sannan ta miqe a hankali ta nufi qofar ta fita tana rufe mata da nufin dawo dasu huda ciki su tayata zama. Fitar anni da second talatin kadai wato rabin minti taji kamam muryar musaddiq cikin kunnuwanta. Sakin counter din tayi ta miqe qirjinta na wani irin mahaukacin bugu,cikin sanda kaman barawon daya shirya gagarumar sata ta nufi qofar,ta kamata ta bude a hankali,sai muryar musaddiq din ta fito tas. "Muje ka gayan me ya faru,koma meye banaso sabreen taji" Taji anni tana fada. Sakin qofar tayi a hankali ta fara takawa tana biye da bayan annin,duk da cewa akwai ginin hallway daya rabasu basa iya ganinta amma ita tana iya jinsu sosai,cikinta hautsinawa yakeyi sosai,tana cike da tashin hankali da fargabar abinda zataji daga bakin musaddiq din. Hannun musaddiq kawai anni ta kama kai tsaye ta ajeshi saman kujerun da suke matsakaicin falon,tashin hankali da rudani sunaso suyi galaba a kanta amma tana cinyewa. "Gayamim musaddiq......ina fu'ad.....ina me babbban suna?" Shuru ya danyi,yana juya yadda zai bata incomplete information,saidai shirunsa zaifi zame mata damuwa sama da amsarsa "Sun harbeshi" Ya fada a hankali kaman bakinsa bayason fada. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Anni ta shiga maimaitawa. Wani irin bugu maganar ta yiwa sabreen,abu na farko daya fara zuwa kanta shine SUN KASHESHI. Nutsuwarta da hankalinta ne gaba daya suka fara gushewa,sannu sannu saita fara daina jin abinda musaddiq yaci gaba da fada.....duhu ya fara gilmawa idanuwanta,ta suma sulalewa a wajen ta zube saman rug din. "Harbin farko ya kauce basu sameshi ba,ya hangi maharbin sai yayi nufin binsa shine ya sameshi a harbi na biyu dana uku......suna tare da yaa farouq,tare ma suka yunqura suka bishin,amma yanxun ba'a ga ya farouq ba,ba'asan ina yayi ba.....shi kansa hamman da jordan dinma ba'asan ina akayi dasu ko yaya akayi dasu ba" Ya qarasa fadawa anni maganar zuciyarsa tana girgiza. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Taci gaba da maimaitawa tana jin zuciyarta na wani irin jijjiga kaman zata ballo daga qirjinta ya fado. "Musaddiq ina abbanku?" Ta tambaya saboda tana jin duk wata jarumta tata da dabararta ta qare,tana buqatar tallafin abban a kusa. Kaman yasan shi take nema sai gashi ya sako kai,kai tsaye ta miqe ta nufeshi,bata kuma tsaya bata lokaci ba ta fada qirjinsa hawaye yana sauka daga idanunta,wani abu da bata taba yi ba gaban yaran tsahon shekarun. "Ya isa ameenatu.....kiyi haquri.....duk inda suke da halin da suke ciki za'a samosu in sha Allah,karki daga hankalinki da yawa,idan hakan ya faru ita kuma sabreen muyi yaya da ita kenan?". Kiran sunan sabreen din ya ankarar da ita,ta janye jikinta daga abban gabanta yana faduwa. Sai sannan ta tuna tayita maimaita innalillahi da qarfi a dazun,wanda zai wahala baikai cikin dakin da sabreen din take ba. "Bari na dubota abba" Ta fada tana juyawa da sassarfa tana nufar ciki. Tuntuben da tayi da ita shi ya sakata taja baya da sauri,kasa jurewa abinda idanunta suke gani tayi,sai kawai ta saki qara tana kiran sunan abba a gigice. Shima ya kadu da jin qararta,wani abu da bai taba ji ameenatu tayi ba komai girman jarrabawa,don haka da sauri yayo hanyar dakin musaddiq yana biye dashi. "Maza jeka kira mommanta.....kada ka bari yaran su biyoku" Abba yace da musaddiq saboda a yadda anni ta gigice yasan ba zata iya riqe sabreen ba. Ba shiri momma data tayar da sallar la'asar din da bata samu daman yi ba sai sannan ta sallame tabi bayan musaddiq. A gigice ta duqa gaban sabreen tana dagata,saidai ba wani alamun numfashi a tattare da ita. "Nutsuwa zakuyi ku taimaketa ta hanyar daukota mu wuce asibiti da ita" Abba yayi qoqarin dawo musu da tunaninsu jikinsu. Kaman gawa haka suka dagata,suka wuce kuma kai tsaye bakin farfajiyar shigowa gidan,don tuni musaddiq ya sanya an matso da mota gaban ginin. Makeken private hospital dinnan da babu kamarsa kaf Nigeria suka nufa da ita wato Noor hospital. Idan ka shiga zakayi tsammanin kana qasashen qetare ne bawai a Nigeria ba kuma gida kanon dabo. Asibiti ne da yake mallakin Muhammed fu'ad jadda.....amma a sirrance mallakar ta kasance,ba kowa bane yasan da hakan. Duk wani kalar kayan aikin da bamu dashi sai a qasashen qetare ya kawosu ya zuba don hana masu kudinmu fita neman magani waje. Donsu din kawai dama yayi asibitin,don babu wani me qaramin qarfi da zaiyi gigin kai kanshi nan. Saidai kuma kusan duka kudaden da ake samu ta asibitin ana tafi dashi ne ta hanyar hidimar al'umma,don baya ci ko karban ko sisi a ciki,saboda baida buqatarsu. Dr hajar da Dr mubeena ne suka karbeta,don ba wani likita namiji da yayi kuskuren zuwa inda take,duk da dama kusan haka tsarin asibitin yake,mata likitoci mata ke karbarsu,maza kuma likitoci maza. Cikin qwarewa suka shiga bata taimako don maido numfashinta kan saiti gudun rasa abinda take dauke dashi,sun samu nasara saidai sun mata allurar bacci saboda ta sake samun nutsuwa sosai,don ta shiga shocked ba kadan ba. Sunyi duk wasu gwaje gwaje daya kamata,harda su scanning da basu tsaya anyi a madeena ba,saidai abinda scan din yaketa nuna musu ya sanyasu a mamaki. Hankalinta kwance take cikin dakinta tana ninke lace din data siya jiya naira dubu dari tara da tamanin,ta kuma budeshi don ta tabbatar shi dinne. Zuciya cike da saqe saqe da taraddadin cikar mission dinta da tafiyarsa daidai?,ko kuma akasin hakan wato FADUWA wanda ko sunanta bata qaunar taji. Har yanzu zuciyarta tana mata susa idan ta tuna fattatakar da bokan yayi mata,sam yama qi saurarenta,wanda ita bataga dalilinsa naqin sauraron nata ba bayan tana cika masa aljihu da kudi. Ta dora kyakkyawan zato akan hajja....duk da tasan mutum ne shi da ba'a sakashi ba'a kuma hanashi......amma tana da zato me girma akan hajja din,wannan ya sauya akalar tunaninta na taci gaba da riqon laila. Zuwa yanzun lailan ya fara zame mata kaya,don ba wani abu da zata iya aiwatarwa na qashin kanta saita tambayi maamah din. Daidai da cin abinci wannan sai data fatattaketa,tace kada ta qara tambayarta don zataci abinci,taci ko kada taci wannan ya rage nata. Ko yanzun da akayi mata knocking sai data ja tsaki,tasan bazai wuce laila din ba,don cikin masu aikinta ba wanda ya isa ya qaraso nan wajen sai idan ita ta nemi ganinka. "Waye?". Ta tambaya cikin 'yar qaramar fusata. " Laila ce".lailan ta fada jiki da muryarta dukka suna rawa. Har ta bude baki zata koreta,sai kuma taji kaman akwai raunana a muryarta don haka tace "Meye kuma?,kinsan banason damu ko?". "Kiyi haquri.....wani abu ne ya faru nazo nuna miki,nima yanzu naga an sakashi a page din jaridar breakers". "Shigo" Ta bata dama kai tsaye tanason jin me tazo dashi. Sanda ta shigo jikinta yana rawa ta miqa mata wayar hannunta. Hannu ta sanya ta karba cikin yamutsa fuska sai kuma ta waro idanunta dukka waje. "AN KAIWA SHARARREN MATASHIN ATTAJIRIN NAN FARMAKI A FILIN TASHI DA SAUKAR JIRAGEN SAMA HARI WATO MUHAMMAD FU'AD JADDA.....HARMA ANA KYAUTATA ZATON BACEWARSA.....YANZU HAKA BA'ASAN INDA YAKE BA". Sake qarewa rubutun kallo tayi da kyau,ta maimaita rubutun ta sake maimaitawa sai kuma murmushi ya subuce mata duk da zulumin daya cika wani sashe na zuciyarta. "Lokacin tarwatsewarki ameenatu yayi.......tabbas wannan itace dama ta ta farko a kanki kafin na isa ga dama ta biyu na qarasa murqusheki.....na kuma jefa rayuwarki data ahalinki cikin halin ni 'yasu" Tayi maganar a sararin tana jin dadin samun wata gwagwgwabar dama da ta sameta ta sassauqar hanya. Idanunta ta zube akan laila dake kallonta kawai. "Kina da hanyar da zaki hadamin 'yan press?,ina da buqatar gabatar da taron 'yan jarida.......ya kamata na fara gwadawa ameenatu nawa salon da kuma ainihin kalata" Kai laila ta girgiza. "Bansan yadda zamu kirasu ba.....amma ina da qawa da take aiki gidan radio.....zan shaida mata sai suzo din". "Hakan yayi.....gobe da sassafe nake buqatar su hallara a harabar gidan nan,bayan gida radio dinsu ina buqatar ta qara da gayyatar wasu kafafen yad'a labaran dama na jaridun......zan biyata akan wannan aikin gayyatar" Maamah tayi maganar tana lalubar number musaddiq,can qasan ranta baqincikin yadda musaddiq ya kasa kiranta a matsayinta na mahaifiyarsu ya shaida mata abinda ya farun sai a rariya ta gani. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 120 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 120 Dab da zata tsinke ya daga,kafin yakai ga gaidata ta amshe "Duk tsiya tuwo dai sunansa tuwo.....kuma.basai kayi hakan ba zaka tabbatar min ni ba komin komai bace a wajenku.....abu ya samu dan uwanka musaddiq saidai naji labari a wani wajen?,yanzun kuna ina?". Tafin hannunsa ya sanya ya riqe goshinsa saboda yadda kansa yake sarawa......ta dage ita kuma still saita qara masa wani ciwon. "Muna asibiti" Ya amsa mata a taqaice. "An ganshi ne?" Ta tambaya yana fargabar bayyanarsa kafin ta qullawa ameenatu jakar tsabar data shirya qulla mata. "Adda sabreen ce....." "Tayi bari?" Ta qarasa masa da abinda zuciyarta ke fatan ya kasance. Sai daya janye wayar a kunnensa yana dubanta kafin ya maida cike da mamaki. "Wanne asibiti ne?" Ta tambayeshi tana kauda waccan tambayar ganin bai bata amsa ba. "Noor hospital" Iya abinda dama takeson ji kenan,tana kuma da buqatar zuwa idan barinne sabreen din tayi ta karbi barin da hannunta ta taho dashi nan ta bawa karnukansu su cinye su shanyen jinin,ta kuma aikawa sabreen din video din ta yadda zai zame mata wani mummunan ciwon. Sharp sharp ta shirya,ta kuma kira driver ya fidda mota suka wuce noor hospital kai tsaye. Masifa ta dinga yiwa driver din,tana ganin kaman baya sauri.....kamar ba zai isa akan lokaci ba. Cikin qasa da minti arba'in sai gashi cikin noor hospital saboda uban gudun data sanyashi ya dinga zubawa. "Scanning din da mukayi mata ya kasa bamu ainihin abinda mukeson gani.....saidai mun samu nasarar ganin two embryos,hakan yana alamta akwai d'a biyu cikin mararta.....iya abinda muka gani kenan,mararta akwai nauyi da aiki fiye da marar me dauke da yaro guda daya....so that dole ta dinga kiyaye wasu abubuwan.....bacin ranta.....aiki me wahala da nauyi da duk abinda zai sanya mata stress.......babies din suna lafiya......amma idan ba'a basu kulawar data dace ba.....komai zai iya faruwa" Bayanin likitan kenan da dukkaninsa ya sauka a kunnen maamah data shigo dakin da qarfinta,saidai ta samu annin da dr mubeena tana mata bayani a parlor din dakin da sabreen din take. "Za'a kiyaye in sha Allah Dr...." Anni ta fada jikinta yana sanyaya,tana sake girmama hukuncin ubangiji da girman qudurarsa da zatinsa. "Allah kaine Allah,baka da abokin tarayya Allah.....yadda ka samar da wadannan halittu naka a mahaifar mahaifiyarsu cikin wani salo da hikima irin naka.....Allah ka fidda mahaifinsu ka kiyayeshi daga dukkan hadari" Anni tayi adduar da take har zuciyarta ba tare da tasan da wanzuwar maamah a wajen ba. Duk da taso tazo ta samu gudan jinin yaron a leda amma saita samu akasin haka.....daga tunanin yaro daya ya koma biyu....bugu da qari ma kuma ana bata tabbacin raunanniyar lafiyar da suke da ita.....to amma har yanzu tana da sauran abinda ya rage wanda zata girgixa duniyar anni.....a yanzu zata gudanar da plan A......plan B din kuma ta ajewa kwanakin da suke zuwa a gaba. "Zaki gama munafuncinki tsaf.....da duk wata munafukar addu'arki ki gayamin inda kika kaimin d'ana.....ni dama nasan za'azo wajen.....ko ba dade ko bajima dole sai kinyi yunqurin salwantarmin da yaro saboda ki handame abinda ya mallaka......to wallahi baki isa ba......ni mariya nice uwar FU'AD,bazan kuma qyaleki ba idan yarona ya salwanta". Cak anni ta dakata daga buda qofar ainihin dakin da sabreen ke ciki,waiwayowa tayi a nutse cike da mamaki tana duban maamah din "Mariya?,kinsan abinda bakinki yake fada kuwa?". Wani kallo maamah ta watsawa anni,cike da alfahari da samun tabbaci akan qudurinta. "Na sani mana ameena.....kina tunanin ba'a hayyacina nake ba?.....UWAR RIQON MUHAMMAD JADDA TAYI KIDNAPPING DINSA SABODA NEMAN KUDIN FANSA......A HALIN YANZU BA WANDA YASAN INDA TA BOYESHI....ya kikaga taken wannan labarin a gidajen rediyoyin Nigeria africa dama duniya gaba daya?" Har tsakiyar kanta anni taji wani abu ya tsarga mata "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" "Dama ki riqe abarki zuwa gobe.....don kuwa goben warhaka bana tunanin kina cikin masu cikakken 'yanci kamar haka". Ta qarasa fada tana takawa hankali kwance tana wucewa dakin da sabreen din take. Duk wata jijiya ta kanta ta gama tashi saman goshinta,ba abinda qirjinta yakeyi sai bugawa da wani irin matsanancin fushi. Kowacce kalma data fita daga bakin maamah a kunnen sabreen ta sauka wadda ke zaune ta jingina da fuskar gadon tana kokawa da kanta ta samu tasha tea din ko babu yawa. Zubawa maamah ido tayi sanda take shigowa dakin,qasan ranta cike da damuwar yadda ta samu sabreen din zaune sosai.....ba wani alamu na fitar hayyaci ko jigata a tattare da ita. Kallon kallo sukewa junansu,yayin da kallon da sabreen ke ajiye mata ya kasance wani qazamtacce kuma wulaqantaccen kallo da bata taba ganin irinsa ba a kanta. Hakan bai sage mata gwiwa ba,taci gaba da takowa har ta qaraso dab da gadonta sannan ta janye dubanta daga kanta ta maidashi kan ledar ruwan da aka gama qara mata. "Inda zan baki shawara ki dauka......da zaifimiki kyau salin alin ki kwanta a zare miki cikin nan cikin girma da mutunci......" ".......idan ba haka ba zaki sanya a kwantar dani a kasheni sannan ki qwaqule abinda yake marata?" Lafuzzan suka fita da wani irin fushi da yaja hankalin maamah din zuwa gareta. Wani zazzafan kallo take sauke mata tana kuma ajiye mug din hannunta. "Eh ina nufin abinda na fada din......kina zaton don kin aikata hakan zai bani mamaki?" Ta jefa mata tambayar tana dage dukka girarta sama,sai kuma ta girgiza kanta. "Ko kadan bazanyi mamaki ba......matar data zabi duniyarta akan lahirarta?,.....matar data zabi salwantar yaranta ta tsira da qazantar duniya wato kudi!......ke nake zargi......ke nake zargi da harbin FU'AD!......ke nake zargi da batarmin da MIJINA UBAN 'YA'YANA......" Ta qarasa maganar tana dora hannunta saman mararta,wasu zafafan hawaye suna taruwar mata. Sosai maganar ta zowa maamah a bazata,amma bata dauketa da wani muhimmanci me yawa ba tunda tana ganin sabreen din bata da wani power hujja ko damar da zata iya aiwatar da komai a kanta. Girarta ta dage duka tana yiwa sabreen duban mamaki,wani qaramin murmushin rainin wayo yana fita akan fuskarta "Ko?......sannu tattabara uwar aure.... Sannu me miji,to idan nidince fa?,sai yaya?". Idanu sabreen ta zuba mata kafin wani kwantaccen murmushi ya sauka saman fuskarta,abinda ya soma sanyawa maamah dawowa hayyacinta. Ba jiya ko yau ba,ta sani murmushin sabreen din bashi da dadi "Kina daukan abun da sauqi ne har haka ko?.....haihuwar muhammad da kikayi hakan bazai qareki da komai ba a sanda kike qoqarin rabani dashi......haihuwarsa bazai qareki da komai ba a sanda kike qoqarin tabamin shi....lafiyarsa hankalinsa ko dukiyarsa........ko waye yayi gigin tabamin DUNIYATA sai inda qarfina ya qare........ciki kuwa harda ke......ke mahaifiyarsa wadda tayi rainonsa na shekara sha hudu kawai......fu'ad DUNIYATA ne.....duniyar da ko mutuwa nayi za'a binne ni a tsakiyarta". Wani gigitaccen yanayi maamah ta shiga,idanunta bibbiyu duka a warwaje take kallon sabreen din. Kalaman yarinyar na yau sun girmi hankalinta,saidai duk da haka zuciyarta tana tuna mata ita din MARIYA CE FA.....giwa kuma kota fadi tafi qarfin wawa. "Kinyi kuskuren fara son abinda nice silar zuwansa duniya......" "Amma ina me farincikin bake kika halicceshi ba ko?" Ta maida mata idanunta tsaye a kanta. "Ba wani doguwar sa'insa bane tsakanina dake kodon albarkacin wannan dake kwance a marata...." Ta fada tana nuna cikinta da yatsa. "Sassauqan umarni ne na ki fiddomin mijina ko ina ya shiga.......awa ashirin da hudu kacal kike dashi.....sannan......taron 'yan jarida karki fasa.......hakan shi zai sauqaqewa muhammad sanin asalin launin kalar mahaifiyarsa" Ta qarashe maganar tana daga mata wayar hannunta. "Maimakon zazzafan labarin uwar riqo me kidnapping dan riqonta.....wataqila sai labarin ya canza akala zuwa labarin BAQAR UWA" Ta qarasa fada da wani mugun confidence daya nuna har cikin idanunta. Wani gigitaccen kallo maamah ke yiwa sabreen din,wannan wacce irin BAQAR JARABA ta hadu da ita?,sam sam ta mance da batun video da yake cikin wayar,lallai kuwa da ta nemi hanyar da zata salwantar dashi,saidai a yanzun ba salwantar da video din kawai take nema ba......tana neman sassauqar hanyar da zata shafe babin sabreen......ta kuma shafe labarin rayuwarta gaba daya daga duniya. Ko sau daya itama bata daga qafa daga kallon maamah din ba,a wannan karon tanajin takai maqura.......itama takai qarshe,kuma ko meye zai faru saidai ya faru. Ko kadan bata yi mata kallon bil'adama cikakkiya a yanzun. Tanajin ta shirya tunkarar kowanne yaqi,ta shirya tunkarar kowanne qalubale akan muhammad fu'ad dinta......tana jin ta shirya ta sadaukar da komai a kansa koda hakan yana nufin salwantar numfashinta. Tsaiwar maamah a wajen yayi mata,don tana jin akwai sauran maganganu daya kamata ta gaya mata,idanunta suna lumshewa da wani irin bacin rai,mararta tana murda mata da wani irin ciwo ta kalli maamah "Ina kyautata zaton har yanzu bakisan asalin wace sabreen ba......amma lokaci ya kusanto da zata shaida miki ainihin kalarta.......har yanzu baki tunzura sabreen ta nuna miki wace ita ba......to amma yanzu anzo wannan gabar.....duk inda za'a juya duk inda zakiyi ki tsaya tsakaninki da ita,huda nadra haneefa anni farouq musaddiq da saddiq.......uban gayya DUNIYATA fu'ad......wadannan din ahalina ne.....jinina ne,iyaye kawunnai kuma kakannin abinda yake yake cikina ne,uwa uba me gayya DUNIYATA jadda.......taba daya daga cikinsu?" Saita girgiza kanta tana sake tsareta da idanu. "Bazai taba zame miki abu me sauqi ba.....jeki gwada idan zaki iya.....zabi ya rage naki.....nima wayewar garin goben nake jira.....ki tara 'yan jarida.....idan kinso kiqi nemomin mijina kiga yadda DUNIYARKI zata tarwatse a karo daya" Takai qarshen maganar rashin tsoronta qarara yana bayyana. "Idan kin fita ki rufen qofan" Sabreen da amai ke tasowa ta fadi tana zamowa a nutse daga saman gadon ta doshi bandaki da 'yar sassarfa gudun kada ta zube aman a wajen. Dif tayi tana sauraren sautin yunqurin aman da takeyi daga bandaki.....wasu irin taurari suna zagaya kwanyarta tun daga gaba zuwa baya "Wacce irin lalacewa ce ta sameki MARIYA?" Ta tuhumi kanta da kanta tana jin wani zazzafan gumi yana karyo mata. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 121 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 121 Daga nan inda take tana iya jin kakarin aman sabreen da take kwarashi da wani irin wahala da kuma galabaita. Aman tana yinsa ne da dukka zuciyarta da wani irin karyewa da sarewa,wani irin rauni ne yake cikata a duk sanda ta tuna "Ba fu'ad a gefanta.....qarfinta.....rayuwarta......kuma duniyarta gaba daya,hasalima ba wanda yasan yana ina......yana raye ko ya mutu,me gobensu zata haifar musu su duka?". A maimakon tausayi dake sauka zuciyar kowacce 'ya mace a sanda taga 'yar uwarta mace cikin hali na ciwon laulayi saboda sanin ciwonsa da tsananin da yake dashi......a bangaren maamah fitar aman sabreen sai takejin kamar wani sauti ne na barazana a gareta......kamar wani sauti ne dake gaya mata dukkan komai naki ya kusa zuwa qarshe.....asirinki zai tarwatse muddin haduwa da tabbatuwar alaqa yaci gaba da wanzuwa tsakanin sabreen da fu'ad. "Ya zanyi na cire cikinnan?,ya zanyi na rabata dashi?" Abinda zuciyarta ta dinga gaya mata kenan da wani irin qunci da tsananin takura. Yunqurin aman shi ya sanya anni qarasowa cikin dakin da wani irin mutuwar jiki da sarewa,zallar mamaki da kuma tsananin tsoron hali da kuma dabi'ar maamah din. Da baya da baya ta dinga tafiya har takai bakin qofar dakin,idanun maaman akan anni,haka idanun anni din itama akan maamah,saita juya tana fuskantar qofa ta murdata ta fice. Asalin gigicewa takeji gaba daya har cikin kwanyarta,me yasa duk wani motsi da zatayi sai yarinyar ta zame mata cikas?.....me yasa take zamewa rayuwarta da duk wani motsinta matsala ne?,yaya akayi ta gayyato matsala cikin rayuwarta?. Idan ta duba ta sasanni da dama sai taga takunta na baya yafi kyau......takunta na baya yafi fita akan wanda take fafatawa bayan shigowar sabreen rayuwarta. Batasan me ya dauki hankalinta ba tun a wancan lokacin da har tabar yarinyar da video din bata salwantar dashi ba,ko a sannan tana ganin bata da wani power.....ba kuma abinda zata iyayi?,ko wannan shine sila?. Cikin tausasawa da tausayawa anni ke riqe da ita,tun tana iya fitar da dan abinda ta samu kurba har ya zamana ba komai cikin aman sai yawu kawai,abinda ya qara adadin galabaitarta kenan,don tanata yunqurin aman kuma babu wani sauran abinda yayi saura a cikinta. Wani hawaye na taru idanun anni sanda take kwance ana qara mata ruwa gudun kada galabaitar ya taba lafiyar yaran da suke cikinta,tausayin sabreen din yana ratsa anni sosai. Ta sani ba abu bane me sauqi wajen mace ta shiga irin wannan yanayin.....ko ita a baya data taba rasa abba,bawai rashi na mutuwa ba,aah saidai rashi na rabuwar aure na dan lokaci,ita kadai tasan me taji,ita kadai tasan ya taji.....ita kadai tasan abinda ta fuskanta,to ballantana wannan,wani yanayi ne da babu tabbas ko sahihancin zance akanshi.....wani yanayi ne da ba wanda yake da tsayayyen abun fada akai. Gefe daya lalurar ciki.....ga qananun shekaru,ga kuma uwa uba me kankat wato MARAICI. Ta wani bangaren kuma abinda ke daga mata hankali shine.....irin maganganun da taji ana musaya tsakanin maamah da sabreen,wanne irin makami yarinyar ke dashi har haka da ya girgiza mariya farat daya?. Batasan adadin lokutan data share a zaune gaban sabreen ba,tana riqe da carbinta wanda har yatsunta sun fara zafi saboda riqonsa. Dare yayi nisa sosai,ita kadai ce kawai,don ta hana kowa zama tare da sabreen din sai ita,gani takeyi babu wanda zai iya kula da ita irin yadda takeso,gani takeyi dole ita kadai ce zata iya bata wannan kulawar. Yadda taga rana haka taga dare,sau daya tak sabreen ta farka tsahon daren zuwa safiya,ta bada tea dan kadan,bacci ya sake kwasheta ta koma. Sai anni take ganin baccin yafi zama alkhairi akan ta zauna idanun ta biyu tana kuka,ko don saboda lafiyar yaran da take dauke dasu. *_WASHEGARI_* K'arfe tara na safe a nan ta yiwa alhj hamza kibiya.....musaddiq da saddiq da sauran guards na fu'ad wadanda suke gida da wadanda suke kan hanya sanda abun ya faru. Iya su uku suka shigo,don ko amna ya hanata zuwa asibitin gudun kada su hadu suyita yiwa mutane kuka. A sannan anni na gaban gadon sabreen din,tana ta neman yadda zata sanyata taci wani abun komai qanqantarsa. Karon farko da magana me zurfi ta hada alhaji hamza da sabreen. Shi ya tsaya kan saita saka wani abu a cikinta. Tana kuka hawaye daya bayan daya haka ta dinga karbar tea din daga hannun momma bahijja wadda ta shigo daya baya. Sai data soma yunqurin dawo dashi sannan ta barta,ta wuce da mug din ta daurayeshi sannan ta dawo dashi ta ajiye. Shuru ya ratsa dakin na wani lokaci,kowa ka kalli fuskarsa cikin nazari da kuma alhini yake. Alhj hamza ne ya fara magana. "Toh.....bamu da abinda zamu cewa ubangijinmu sai godiya.....kafin ya jarabcemu da wannan ya mana tarin baiwa da ni'imomin da ba zasu irgu ba....cikar iko da adalcinsa ne ya jarrabi bawa akan dukkan abinda yaga dama a sanda yaso.....to mu ba zamu butulce masa ba,alhamdulillah da duk yadda yayi damu......mun tattauna da masu ruwa da tsaki cikin sha'anin tsaro na qasar nan dama maqwaftanta,kuma suna bamu tabbacin lalubo inda suke ko wani abu daya shafesu cikin qasa da awanni ashirin da hudu in sha Allah......su kansu guard da suke aiki qarqashinsa dukkaninsu basuyi bacci ba,ba wanda ya zauna ko ya kwanta,aiki suke akan batun ba qaqqautawa....kuma ana samun haske sosai,su kansu na yadda da qwarewarsu in sha Allahu komai zaizo cikin sauqi" Ya qarasa maganar yana basu tabbaci a maganarsa dama fuskarsa. "Ubangiji ya amince....Allah ya bayyana gaskiya a duk inda take" Momma ta fada cikin sanyi jiki da tashin hankali. Sunan sabreen ya kira,ta amsa masa ba tare data iya dubansa ba,don kuwa ita kadai tasan abinda takeji. Nasiha sosai yayi mata me ratsa jiki da hankali akan imani da qaddara da daukarta. "Zan dauka abba in sha Allah.....zan dauka" Ta fadi kawai tana sauke idanunta saman tafin hannunta daya wani qara dashewa yayi haske kaman ba cikakken jini a jikinta. Da daya da daya suka fara juyawa suna fita. "Saddiq" Ta kirashi abinda ya dawo da hankalin anni kanta don wNi abune da bata taba yi ba. Shima a mamakance ya juyo yana kallonta,sai ta sanya hannu ta yafitoshi. Dawowa yayi a nutse,y jawo kujerar da momma ta tashi akai ya ajiye daura da ita. "Gani adda" Ya fada yana mata duban mamaki. "Akwai labari da nakeso na fitar kashi uku......kashi daya gidan tv radio dana jaridu......kashi biyun da yayi saura tv radio ne kawai zaiyiwu su haskashi" Ta fada tana dubansa. Magananta taja hankalin anni,ta kuma tuna mata da duk tattaunawarsu da maamah ta jiya. Sakin kayansu da take kwashewa tayi wanda za'a koma dasu gida,ta tako a hankali har inda suke. Duban saddiq anni tayi fuskarta ba walwala "Tashi kaje parlor.....idan na gama hada kayan zan kiraka" Fuskarsa da mamaki da kuma wani zumudi nason jin qarashen maganarsa da sabreen ya miqe,saidai babu yadda zaiyi anni ta katsi hanzarinsa. Inda ya tashi ta koma ta zauna tana duban sabreen. "Wanne labari zaki fitar sabreen?" "Yadda akayi uwa ta zama me dillancin yaronta don kawai ta mallakeshi......yadda wata uwa ta zama azzaluma wadda batasan ciwon 'ya'yan cikinta bama bare na wasu....yadda wata uwa ke burin murqushe 'ya'yanta ta gaji abinda suka bari......yadda akayi sabreena ta zama matar muhammad jadda ta hannun mahaifiyarsa" Sabreen ta fadi muryarta nason karyewa amma tana bawa kanta da kanta qwarin gwiwa,tana jin babu wani abu da zai hanata aiwatar da wannan abun,daga nan zuwa dare muddin bataji komai dangane da muhammad dinta ba. Koda sabreen bata fayyacewa anni komai ba.....annin da kanta ta gama fahimta.....wani tsohon zargi da shakkunta kan maamah lokacin aurensa shine yakeso ya tabbata bayan wani lokaci. "Akwai kuskure cikin aikata haka sabreen......kinsan wanne kuskure?" Anni ta tambayi sabreen tana son qwato hankalinta da nutsuwarta,domin kuwa ta hangi abubuwa masu tarin yawa cikin idanun sabreen din masu kaifin gaske suna kai kawo. "Mariya bata da asara.....domin kuwa tata rayuwar tazo qarshe idan aka dangantata da taku......mariya bata da wata asara me yawa,kece kike da jini a jika.....kace kike tara zuri'a yanzu.....domme zaki yiwa kanki wannan barnar?" Anni ta fada tana kallon idanun sabreen tanason taga iya dadin yadda maganar ta shigeta. Kai sabreen ta mirgina gefe....kamar anni ba zata fahimci nata shimfidadden takun ba.....wannan abun wani taku ne kuma tarko ne me kyau idan anyi amfani dashi ta hanyar daya dace......tarko ne da zata kama kowacce kurwa ta maamah din. "Kinsan wace mariya ta gaske?,kinsan yadda me babban suna suka rayu?" Haka kawai taji tanason ta sakeji daga bakin anni,ta tabbatar koda shi ya gaya mata.....koda shi ya labarta mata bazai gaya mata yadda anni zata sanar mata ba,don haka ta kadawa anni kai a hankali tana dubanta. A nutse anni ta warewa sabreen komai.....rayuwar fu'ad tun kafin tafiyar mariya da kuma tafiyartata,yadda ta samesu da irin wahala da tasha kafin ta maidashi kalar mutumin da yake a yau,duk wani qalubale da kuma gwagwarmayar rayuwa tasa. Hannu kawai sabreen ta saka ta lullube fuskarta da tafin hannuwan nata,sai takejin a wancan ranar a Maldives tamkar bai gaya mata komai nasa bama.....kaman ba wani abu daya gaya mata daya shafi rayuwarsa. Ta yaya zata iya controlling hawayenta a fuskarta?,ta yaya zara iya.hana kanta zubar hawaye?,wacce irin asararriyar uwa suka samu?,wacce irin uwace wannan wadda da ita gwara babu?. Lallai ba shakka zatayi komai.....har fiye da abinda take hasashe a baya ma zatayi. Amma da irin wannan abun nata har anni ke duban ta qyaleta?,me yasa anni ba zata fahimci cewa ita sabreen dama mutuncinta bararre ne a idanun mutane da yawa?......me yasa anni ba zata Fahimci zata iya saudar da komai wa fu'ad ba?,don don mutuncin nata da iyakarsa idanun fu'ad dasu anni?,duk da yafi qarfin D'A tunda wata yarda ce da sassanyan aminci ta samu a muhallin da yafi kowanne daraja. "Ban gaya miki don kiyita kuka ba.....ban gaya miki don kiyita damuwa da sanya bacin rai ba.....na gaya miki ne saboda ki sani........ba kowanne mutum kake qarar da energy dinka a kansa ba". Kai sabreen ta jinjina tana sauke hannuwanta. "Taso nayi tarayya da ita wajen raya zunibinta anni......ta kawoni da qarfi da yaji da'irar da ban shirya shigota ba.....saidai a yanzun ina kallon juyewar al'amarin daga sharri zuwa alkhairi...." A nutse itama ta gayawa anni yadda duka komai ya kasance tsakanin ta da maamah a wancan lokacin. Tayi shuru anni tana jin komai yana kwaranye mata,lallai duk inda xa'a qaunaci juna saboda Allah dole a dinga ji a jiki a duk lokacin da wani abu zai kasance da dayan biyun. Ashe ba'a banza ba ta dinga jin wani baqin abubuwa dangane da auren?,ba'a banza ba ta dinga jin rashin gamsuwa da komai?. Al'amarin maamah sai taji yana sake girma a zuciyarta. Mamakinta tana jin kaman zai fasa ko ya kashe zuciyarta gaba daya. *_WANI DARE!_* Ranar ta kasance musu wani dare da dukkaninsu suka kwana suna juyayi da mutuwar mamaki kan halayyar mariya da komai nata.....daren ya zame musu wani dare da sabreen ta kwanta tana jin zata dan dagawa maamah qafa saboda anni data buqaci wurga lamarinta a kwandon shara abita da ruwan addu'a,saidai kuma wannan daren ya zama daren da yayi silar da sabreen ta soma sakin UPDATE akan maamah......wanda batayi tunanin akwai wani abu da zai dakatar da ita ba ko waye ko meye shi!. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 122 122 Har qarfe sha daya na dare anni tana zaune gaban sabreen,lokacinne kuma Dr mubeena ta gama daura mata wani ruwan daya zama shine abincinta yanzu saboda ba wani abu da yake iya shiga cikinta ya zauna,koda ya shiga dimma sai ya fito. Rubuce rubuce Dr mubeena ta kammala yi cikin file din sannan ta rufe,ta ajiye a gefe tana sanya idanunta kan sabreen dake kwance da shirin yin baccin da ta tabbatar qaryarsa ya shammaceta......saidai tasan zaizo ne kadai ta hanyar sinadaran da suka zubawa ruwan dake shiga jikinta,wannan ne kadai yake bata daman yin baccin daya kasance ba natural na qashin kanta ba. Tausayi sabreen din take bawa Dr mubeena,tako wacce fuska ta kalleta tausayi take bata. Hannu ta miqa ta dauki abun gwajin BP din data gama gwada mata ta riqe a hannunta,tadan sakar mata murmushi wanda sabreen qarfin hali kawai tayi ta maida mata. "Kiyi bacci sosai Mrs jadda......fi amanillah.....in sha Allah boss yana cikin aminci,Allah baya bari bayinsa na gari su wulaqanta kosu tozarta ko su wofanta" DR mubeena ta fada cikin kwantar mata da hankali. Murmushi ta tattaro da qyar ta samu ta maida mata martani,Dr mubeena ta kalli anni dake zaune gaban gadon kaman ko wanne dare tana riqe da tasbaharta. "Yau ba checking din dare,BP dinta ya kusa dawowa daidai da yadda nake buqata,kuyi baccinku,idan Allah ya kaimu qarfe shida ko biyar da rabi zan shigo". Ta fada cikin girmamawa itama tana jin alhini har cikin qasusuwanta na rashin labarin komai akan fu'ad din. Murmushi kadan anni tayi tana sauke qafafunta daga saman kujerar,yau momma ta dage lallai a bawa anni 'yar tayin kwana ko huda ko ma'u. Ta karbi ma'u saboda ta matsanta dole gobe su wuce mali huda taje tayi ton print dinta duk da a goben zasu rufe. "Sannunku da qoqari kuma,Allah yayi muku albarka" "Ameen,Allah ya qara lafiya saida safe" Tayi musu sallama tana fita daga dakin. Idanunta a lumshe suke kawai,ita kadai tasan me yake yawo tsakanin qirjinta da zuciyarta,a duk sanda kwanyarta zata harba da lafazin. "Sun harbeshi.....ba'asan inda suke ba!" Sai taji kaman zata mutu......sai taji kaman ba wata tazara tsakaninta da tashin alqiyamarta. Takanji faruwar komai kamar a mafarki.....daddadan farinciki da wata iriyar tsaftatacciyar kulawa tana shirin rikida zuwa tashin hankali da firgici.....wannan kusancin tashin farko ya juye ya koma kewa da tsananin buqatar makusanci izuwa zuciyarta. Duk dare kafin alluranta su dauketa zuwa duniyar bacci.....duniyar dasu Dr mubeena suka matsanta mata zuwanta badon son ranta ba.....sai rayuwarsu tsakanin Maldives da madeena tayita dawo mata tamkar a faifan CD,takanji inda ana maida hannun agogo baya tabbas data maida.......tabbas data hanasu dawowa nigeri da tana da masaniyar ibtila'in da zai fada musu kenan. Tun tana iya jin muryar anni da ma'u sama sama har ta daina ji,ganinta da ruhinta suka koma zuwa ga wanda ya yisu nadan wucin gadi. Shuru da anni taji ma'u tayi shi ya bata tabbacin bacci yayi awon gaba da ita,saita gyara zamanta saman kujerar tana ci gaba da jan tasbaharta,tunanuka kala daban daban suna hana idanunta tafiya duniyar barawo wato bacci da itadinma duk dare satarta yakeyi,bata kuma fiya dogon zango ba yake sakinta,takan farka da mafarki ki razani duk dare,saidai ko sau daya bata taba farkawa ba ba tare da ambaton hasbunallanu wani'imal wakeel a bakinta ba. Batasan baccin yayi awan gaba da ita ba,har tasbhar hannunta ta sulale ta fadi da hasbunallanu wani'imal wakeel data kasance ta qarshe a harshenta. Dukkanin daukacin asibitin harda dakin ya dauki shuru,dare ya fara nutsawa awanni suna gudu......a irin lokacin da bayinsa nagartattu ke neman kusanci dashi saman darduma,ashararan mutane kuma suma ke nasu aikin saboda neman duniya da abinda yake cikinta. Daya daga cikinsu ta samu nasarar kunnowa dakin,ta murda handle din a hankali cikin sanda. Sanye da suturarta ta dazu,suturar qarshe data shigo dakin dasu babu abinda ya canza,daidai da takalminta da kuma dan qaramin hijabin kanta,saidai a yanzu akwai baqin face mask saman fuskarta koma bayan dazu. Kai tsaye ta wuce parlor din ta kuma tunkari dakin da sabreen ke kwance,ta saka hannu ta bude qofar dakin tana shiga. Daga bakin qofa ta tsaya,ta qarewa kowa kallo,ta kuma tabbatar dukkansu sunyi nisa a baccinsu. Ajiyar zuciya ta saki hakan yana bata nutsuwa da kuma qwarin gwiwar aiwatar da abinda ya shigo da ita,taci gaba da matsawa zuwa gadon da sabreen ke a kwance. Daidai inda ruwan dake saqale a hannunta ta isa,ta tsaya ta zuba masa idanu. Bisa qa'ida ruwan yake diga kaman yadda ya dace,aiki biyu zatayi a ciki,ta gaurayashi da sinadarin dake aljihun rigarta,ta kuma qara gudun ruwan dake shiga sassan jikinta,wannan shi zai saurin hautsina tsarin jikinta,ya kuma taimakawa sinadarin wajen yin aiki a jikinta da gaggawa. To amma ta wani bangaren tafison ta fara tabbatar da inda wayar take......wayar itace babban burinta na farko,wanda iya ita kawai idan ta mallaka kaman yadda akayi mata alqawari ya isheta kudin aikinta koda ba'a qara mata komai ba. Ta tsakanin annin da sabreen ta wuce tana miqa hannunta locker gefen gadon,durqusawa tayi ta soma binciketa a hankali. Sai data hautsine komai bata ganta ba,wannan ya qara gudun jinin jikinta energy dinta ya qaru fiye da yadda ya kamata ya kasance. Tana bala'in son wayar,don itace cikar burinta. Miqewa tsam tayi ta sake wucewa ta tsakaninsu,hannunta gefe da gefen sabreen din ta soma lalubawa ko a nan ta ajiyeta. Kaman wadda aka tasa ta dinga jin wani sauyin yanayi tattare da ita tamkar wadda aka canzawa muhalli daga wanda take ciki,jin hannu ta gefan kafadarta ya sanyata murmurewa daga yanayin bacci zuwa rayuwar zahiri. Baqon turaren da takeji a hancinta ya sanyata budewa idanunta qanqanuwar qofa da zata iya ganin wanda waye haka keda kusanci sosai a kusa da ita?. Dr mubeena kamar take gani,amma kuma qamshin da yanayin nutsuwar sam ba ita bace......saidai a idanu a kallon dake a fusge tabbas Dr mubeena ce. Tabo wayar da hannunta yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya,ta saka hannu ta jawota ta jefata aljihun lab coat din jikinta,sannan ta fiddo hannun da syringe da wani irin ruwa a wata mitsitsiyar roba. Tas ta soma zuqe ruwan a syringe din,wanda tana dab da kammalawa anni ta motsa bakinta dauke da HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL Tana shafa fuskarta da tafin hannunta. Fitar hasbunallahu din ya daki qirjinta,ya kuma sabbaba mata faduwar allurar dama robar ruwan,abinda ya sake sakawa sabreen matuqar ankara da ita,ta sunkuya da sauri ta dauki syringe din qirjinta yana dokawa. Idanu anni ta zuba mata a mamakance,duk da ta juya mata baya bata iya ganin fuskarta. Mamakin yadda suka canza tsari ne na Shigowar likita dakin mara lafiya haka kai tsaye?. Kaman Dr mubeena take gani......amma kuma abun da mamaki,Dr mubeena da ta musu sallama sai bayan sallar asuba?,me ya dawo da ita?,kuma ta shigo dakin ba tare da sanin kowa ba?. "Dr akwai allurar data rage ne?" Kai ta gyada mata kawai tana qoqarin qarasa zuqe ruwan a syringe din a gaggauce don ta qarasa cika aikinta. Hakan bata samu ba kuwa,don hannu sabreen takai mata cikin shammata ta daki hannunta,da syringe din da ruwan sukayi gefe suka watse,abinda ya darsa wani abu da gaggawa a zuciyar anni,ta miqe sa wani irin zafin nama ta damqo kafadarta tana juyo da ita. Kallon kallo suka yiwa junansu,tana shirin kubcewa anni,annin ta saka hannu ta yage face mask din fuskarta ta. Baquwar fuska ce da bata santa ba.....kaman yadda ya bayyana fuskar bata Dr mubeena bace. "Wacece ke?!" Tambayar da anni ta mata cikin madaukakim sautin tsawa daya qarasa farkar da ma'u ta miqe ta zauna sosai ta yunqura ta tashi. Kai matar ta girgiza,ta juya da gaggawa tana nufar qofa,saidai tuni ma'u ta rigata isa qofar ta danneta ta kulle ta zare key din. Raba dubanta take kan fuskar anni tana zaro ido waje,hankalinta ya soma tashi tana tunanin girman hadarin da zata shiga muddin ta bari taje hannu. "Kiban hanya na fita ko kuma na illataku!" Ta fada da wata gurbatacciyar hausa da zata baka tabbacin wani yaren ce daban ba cikakkiyar bahaushiya ba. Daga annin har matar ba wanda ya zaci haka,saukar kakkauran plastic plate din da sukaci abinc dashi dazu ma'u ta sauke mata a tsakiyar kai,sai gata ta zube qasa warwas zubewar data sanya wayar sabreen silalowa daga aljihunta. A hankali sabreen data sauko daga gadon ta dauki wayar tana juyata,iya daukar wayar kawai ta bata kowacce irin amsa da take buqata koda matar batace komai ba. Matsawa anni tayi da hanzari tana kiran security emergency line cikin qasa da minti daya sai gasu sun bayyana a dakin. Kiran security din ya tayar da kusan duk wani security alert na asibitin,kasancewar dakin babban daki ne,yana cikin VIP rooms da asibitin yake dasu. Cikin qanqanin lokaci qofar dakin ya cika da security da wadanda ihun security alert din ya tashesu. Kusan kowa yasan wacece a dakin a cikinsu,suna da masaniyar mahaifiyar wace a dakin,don haka fitar security alert daga dakin ya zamana kaman tashin hankali a wajen kowa. Sanda chief of security service na asibitin ya shigo dakin yana neman ba'asin abinda ya faru ya girgiza. Cikin matuqar tsoro da kuma kaduwa ya shiga bawa anni haquri. "Am sorry maaa.....muna dukkan iyawarmu wajen bawa madam tsaro,bamusan ya haka ta faru ba.....amma ni da kaina banyi minti talatin da shiga office ba bayan ba gama zagaye na tabbatar kowa yana kan aikinsa,hatta shige da fice na asibitin nan tun bayan faruwan abun muka sake saka ido akai....amma zamu duba in sha Allah,zamu kuma binciketa har sai mun tabbatar daga ina take?,meye kuma ya shigo da ita dakin......muna masu bada haquri". Kai kawai anni ke jinjinawa tana duban matar wadda tuni ta jiqe da fitsari,ainihin mummunar suffarta dukka ta fito saboda yadda tayi wurjanjan da kuka da tsananin tashin hankali. Haquri kawai take bayarwa hannuwanta a sama kaman me addu'a. A haka suka jata suka fice da ita,sabreen ta koma gefan gadonta ta zauna kawai rungume da hannayenta kanta yana cakudewa. Dr mubeena ta qaraso inda allurar da robar suka fadi ta sanya hand gloves ta daukesu,har yanxu ita kanta a tsorace take jikinta kuma rawa yake. Mamaki ne yake qara kasheta na yadda akayi amfani da kamanninta da komai nata aka shigo dakin za'a cutar da iyalin jadda. "Zanje dashi lab mu gwada muga meye ma taso zuba mata cikin drip din". Dr mubeena ta fada tana duban securities din guda biyu da suka rage a dakin. Juyawa tayi ta kalli anni da sabreen. "Ku kwantar da hankalinku,babu abinda zai faru in sha Allah,zasu dan xauna kadan daku kafin daga waje kafin security dinku na gida su iso....don anyi alerting nasu abinda yake faruwa". "Sannu Dr" Kawai anni ta iya fadi Dr mubeena ta juya ta fice da sauri Dr kamal da yake on duty yabi bayanta abun shima yana girgizashi. Case ne da makamancinsa bai taba faruwa cikin asibitin ba,sai gashi yau yana shirin faruwa akan matar mutum mafi girma da kima cikin idanunsu banda Allah ya kiyaye. Ajiyar zuciya me nauyi sabreen ta sauke tana dora hannunta saman cikinta a hankali. Wat qqqarfar soyayyar abinda take dauke dashi ya ratsa mata zuciya irin wadda bata taba ji ba,wato tako ta ina farautar rayuwarsu akeyi?,so ake a salwantar dasu gaba daya?,kowa rayuwarsu ta tsone masa idanu ta kowacce fuska?. "Nayi alqawarin baku kulawa da dukkanin qarfina da kuma iyawata.....nayi alqawarin kula daku har zuwa sanda zaku taka doron qasa......da ran mahaifinku ko babu.....da kulawarsa ko babu......zamu zame masa madubi kuma ababen alfahari in sha Allah" Tayi maganar ita daya tana sakejin kaman wata sabuwar alaqa na qulluwa tsakaninta da abinda ke cikinta da batasan meyeshi ba. Batasan hawaye takeyi ba saida muryar anni ta ratsata. "Ki rage damuwa da gaske sabreen ko don diyoyin cikin ki.....karki cutar dasu....Allah shike riqe da kowanne bawa yake bashi kariya....musamman idan ka sallama masa ka kuma miqa masa al'amarinka". Tayi maganar a tausashe tana goge mata damshin fuskarta. Ba wanda ya iy komawa bacci,abinda ya sanyata yanke shawarar yin alwala,ta daura alwalar ma'u ta shimfida mata abun sallah. Ta jima tana kaiwa Allah kokenta wanda tayi Imani shine sarki guda daya da baya maida hannun bawansa ba tare da ya amsa addu'arsa ba. Sanda ta idar tana zaune kanta a qasa,tana jin tattaunawar guards din fuad daga parlor din dakin. Kusan kowannensu zuciyarsa a kusa take,muryar abdulgafar ce ta qarshe. "Daga yau koda wasa ba wanda zai sake gigin zuwa kusa da inda take ma......daga gobe zuwa jibi ko da numfashinmu da jinin jikinmu zai qare sai mun lalubo duk inda oga yake,a cikin qasar nan ko africa ko a wacce nahiya ta duniya ma". Numfashi ta sauke a hankali,ta jawo wayarta tana lalubo number musaddiq. Dole ta fara taba mata nutsuwa kaman yadda tayi musu,dole ta taba kwanciyar hankalinta ko yaya ne,saboda itama tasan kifi na ganinka me jar koma. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 123 123 Cikin qasa da awa daya ta gama turawa saddiq komai da komai da take buqata,sannan ta sauka tana lalubo rubutaccen qur'ani dake kan wayarta. Ko yaya ne tanaso ta karanta ko zata samu sassaucin zugi da radadin da zuciyarta take mata,don ta dade da fahimtar babu wani abu dake bawa jiki da zuciya nutsuwa irin karatun alqur'anin. ★Zuwa sanda gari ya qarasa haske abba ya iso,already su musaddiq dama tun cikin daren suka qaraso,saidai da safen musaddiq yadan fita sannan ya dawo. Dr mubeena ta shigo da sakamakon gwajin,a sannan sabreen din tana zaune ana gyara mata cannula dinta data goce. Idanunta a runtse tana jin radadin yadda ake luguiguta qarfen allurar cikin Jikinta. "Guba tayi attempting zuba mata.....wadda take bin jiki a hankali ta lalata kowanne organ na jikin dan adam......alhmdlh da ubangiji bai bata nasara ba......inda hakan ya faru to fa da saidai addu'a kawai....poison ne da bashi da magani a nan qasar ko makari kwata kwata". Kai kawai sabreen ke gyadawa tana sake girmama rashin imani da rashin tausayi irin na wanda ya dauki nauyin abun. Zuciyarta tayi wani mugun karyewa fu'ad jadda yana fado mata. Allah ne kadai yasan a wanne yanayi yake a yanzu?,a wanne irin hali yake?. Da sassarfa take saukowa daga saman nata kaman zata hada matakala bibbiyu. Duk sanda taga kiransa tasan tabbas lamari ya baci,ba kasafai take sanyashi ayyuka ba.....ba kuma kowanne lokaci bane take bashi aiki na sai aikin daya kasance babba. Yana tsaye tsakiyar falon,hannunsa goye a bayansa yayin da idanunsa ke lullube da baqin gilashi. "Me ya faru?,ya ake ciki?". Baqin hannunsa ya saka yana cire glass din nasa,bakinsa da yake baqiqqirin ya motsa. "Aiki ya baci,kuma komai na iya faruwa saboda ta fado hannu a sanda kowa yake abun zargi ne". Hannuwa bibbiyu ta sanya yana dafe qirjinta dake wani irin buga mata,duka idanunta a warwaje tana jin tashin hankali yana zagayata. Wannan shine aiki na qarshe da take sanya ran samun nasara a kanshi,aiki na qarshe da take da kyakkyawan fata da hasashen indai ya tafi daidai ta gama da matsala daya cikin matsalolin rayuwarta guda uku,aikin data kwana jiya batayi bacci ba tana jiran jin kyakkyawan sakamako a kansa. "Waye ka bawa aikin?,ina fatan sunana bazai fito ba?" Ta tambayeshi zufa tana yanko mata tana jin kan an mata wanka da ruwan zafi. Kai ya girgiza yana dubanta. "Ko sunan wanda na bawa aikin bazai fita ba bare sunanki bare nawa,don da kika bada aikin na bawa wani shima ya bawa wani shima wancan wani ya bawa sannan aka bawa yarinyar......nasan yarinyar amma ban bata aiki kai tsaye ba saboda gudun qwacewar rana irin wannan......amma.abinda yafi bani mamaki,itadin expert ce,bata taba missing target ba tunda ta fara aiwatar da irin wadannan ayyukan sai yau ta silarki" Yayi maganar abun yana tsananin bashi mamaki na yadda ta fadi warwas a qaramin aiki irin wannan. Ajiyar zuciya ta sauke,ita komai ba damuwarta bane......kama yarinyar ko tsallakewarta,nata damuwar shine samun tabbacin nata kubutar da kuma tsiran. Kujera ta samu ta zauna tana juya tambayarsa. Me yasa rashin nasarar yarinyar da faduwarta bai tashi afka mata ba sai da aiki yazo kansu?. Tambayar data kasa samun amsarta kenan,saidai kawai ta sakawa ranta akwai wani boyayyen abu na daban da sabreen din ke amfani dashi. "Labari na gaba" Ya fada yana fiddo jaridar dake hannunsa. Kamfanin jaridar yafi kowanne kamfani fidda adadin jaridu siyar dasu da cinikinsu,saboda yafi kowanne gidan jarida fidda labarai latest masu daukan hankali,labarai na gaske da suke daukan hankali tsakanin kwanaki da makonni. Hannu ta saka ta karba tana dan mita,saboda a yanzun ba abinda tafi buqata irin ya barta ta zauna tayi nazarin hasarar data sake fada mata. Kudade masu ciwo ta biya don wanzuwar aikin,sai data siyar da bangles dinta na gold sannan ta biyashi kudin aikin. Wareta tayi tana mita a ranta,saidai bata samu sukunin sauke mitar ba tafkeken hoton farko daya mamaye jaridar ya dauki hankalinta. Hoto ne da alamu suke nuna daga cikin video aka ciroshi,fuskar hajja sosai ya fita,yayin da ita dake gefen hajjan kwata kwata fuskarta bata fita ba bata kuma nuna ba. Bata sani ba.......ta gurin bugun jaridar aka samu akasi tayi damage?ko kuma ana sane aka lalata gurin?. Kayan dake jikinta a jikin hoton tabi da kallo,sune dai......sune dai wadannan kayan data sanyasu a ranar da zasuje gidansu sabreen zuwa na farko......gabanta yayi wani mahaukacin faduwa sanda wani abu ya darsu a ranta. "Na shiga uku?!,me zan gani wannan?" Ta tambayi kanta da kanta hannuwanta suka dauki rawa,da wani irin sauri ta maida dubanta saman manyan rubutun da suke saman newspaper din da aka yisu in bold style yadda zai dauki hankalin harda na nesa. _CIKIN WADANDA AKE ZARGI KENAN DA SACE SHARARREN ATTAJIRIN KASUWAR GOLD DA DIAMOND KENAN MUHAMMAD JADDA_ Dukka hannunta suka dauki rawa,wata kidima ta saukar mata,ta dubeshi gumi yana sake tsatstsafo mata,yau itace buge cikin calendar da sunan wadda ake tuhuma da satar d'anta?,ba wanda zai aikata wannan sai yarinyar.....don kuwa ita daya take videos din ta tabbatar. Kamar wadda kuka zai qwacewa cikin rawar murya da qwacewa dukkan wani hanzari daga gareta tace. "Yaushe aka buga wannan labarin?,har ina kuma labarin yakai?". Gyara tsaiwarsa yayi da fuskarsa da bata nuna wanzuwar imani a zuciyarsa ko kadan yace. "Tun da sassafe....nima a teburin me shayi naga wani yana karantawa,sai naga kaman nasan fuskar,koda na duba sai naga fuskar hajja harira ce.....wannan ta kusa da ita dince dai ba'a gane fuskartata". Wata gauruwa ajiyar zuciya ta sake,tabbas zai wahala a gane fuskartata,amma ga wanda yayi mata farin sani hakan bazai bashi wahala ba sam. Qarar wayarta ya sanyata zabura tana dubanta,don sam bata tsammanin kiran wayar kowa a irin wannan lokacin. Hannu ta sanya ta dauka tana duba me kiran,hajja harira ce,tayi kaman ba zata daga kiran ba amma sai taji tana buqatar sanin waye. Karata tayi a kunnenta,tana shirin yin sallama sai sallamar tata ta maqale. Muryar hajja harira ce wadda ta fara da sauke mata zazzafan ashar. "Ni zaki wulaqanta a duniya?,ni xaki toxarta mariya?,meye ban miki ba a rayuwa?,saboda kin asircemin yarinya na miki shuru?,an gaya miki shuruna yana nufin tsoro ne?,bakisan ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne?,ni xaki buga a jarida akan abinda bani da masaniya?,ke bakisan kuskure bane tarar fada da wanda yasan sirrinka ba?,ganganci ne tarar rigima da wanda yasan waye kai ba?......to kin tara kin samu....mu zuba,dani dake shege ka fasa,hoto na gaba idan kika tashi tsirara zaki sakani......hukuma kuma ina nan ina dakon isowarta gidana,qarqari idan sun kamani su kulleni......idan kuma ya tabbata bani ke da hannu ba dole su sakeni". Daga haka hajja harira ta katse kiran. Wani tashin hankalin na daban maamah taji yana sauko mata,har numfashinta taji kaman yanason riqewa. Sam ba wani motsi data sakeyi akan hajja harira saboda dalilai.guda biyu. Dalilim farko ita daya ce mutum guda daya data mallaki sirrikanta ciki da bai,birnannun sirrikan da babu wanda ya sansu,babu wanda yasan da zamansu sai ita din tak!. Dalili na biyu laila dake hannunta,tasan wannan kadai ya isa ya zame mata daukan fansa game da cin amanar da hajja taso tayi mata,to amma ko a yanzu ikirari da kurarin da hajja tayi mata bazaiyiwu ta barta ba,don haka ta share gumin fuskarta ta soma tura mata gajeran saqo. _"kiyi komai harira,bazan hanaki ba,amma kada ki manta a hannu kike,laila tana gaidaki da kyau da kyau,tace kuma na gaya miki ki kula,ki kuma kula da kanki"_ Kamar jira shigar saqon yakeyi wani kiran ya sake shigo mata. Baquwar number ce da haka kawai ta sanya gabanta faduwa,ta dinga bin number da kallo tana raba daya biyu. Special number ce,simple da bata cika tarkacen lambobi da yawa ba,ta jima tana kallonta kafin daga bisani dab da xata tsinke ta daga. Karo na farko da muryarta kawai ta saukar mata da wani mummunan faduwar gaba da bata taba jin irinsa ba. "Ina fatan saqona ya riskeki zuwa yanzu?,idan ma bai iskeki ba to na tabbatar yana dab da iskeki......somin tabi ne kenan wannan din.....iname sake aike miki da gargadi.....ki nemo min mijina kuma uban 'ya'yana a duk inda kika kaishi.....ba sassauci ba daga qafa.....idan nar yakai awa saba'in da hudu.......abinda zai faru na gaba yafi qarfin wannan......yanzun ba irin wancan lokacin bane.....lokacin da zaki zubdasu ki watsar dasu a duk inda kikaga dama,yanzun rayuwarsu gewaye take da masoyansu......rayuwarsu gewaye take da rayukan dake buqatar su,suke da muhimmanci a wajensu.....suke muradi da mararin ci gaba da wanzuwa tare dasu,da dadi ko ba dadi.....da dukiya ko babu,da lafiya ko babu,saboda su din akeso.......zallar su din ba abinda ke tattare dasu na ni'ima ba". Har sai da maamah taji numfashinta ya sarqe guri daya da zafafan maganganun data soka mata,to amma zuwa yanzun ko taqi ko taso tana ji a jikinta itace a hannu,duk da tana ji nadan lokaci ne hakan zata kasance,sai maganan harira da suka gama yanzu ta dawo mata. _"Kuskure ne tarar fada da wanda yasan sirrinka.....yasan waye kai ciki da bai"_ tabbas a dazun kawai.harira ta bata wani darasi daua kamata ace kanta ya kawo mata,amma ko banza a yanzun ma ta zamu wani ajiyayyen darasi da zai zame mata makamin yaqi tsakanin ita hariran da sabreen. "Sabreena......ki saurareni kiji.....kuskure kikeso ki aikata wanda zaki dana sani daga baya.....ta yaya zan zama silar batan yaro na kamar a film ko a rubutaccen wasan kwaikwayo?" Wani numfashi sabreen ta sauke sannan tace. "Komai da kika taba aikatawa a kansu a baya din ai hankali bazai dauka ba......hakanan idan ka saurari labaran ba abinda zai hana kace cikin litattsfan labarai ne ba cikin rayuwarmu ta zahiri ba....." "Ba maganar baya akr ba......maganar yanzu akeyi sabreen" Maamah ta fada karon farko tana sassauta muryarta gudun ballewar sabreen din. "Da da da yanzun duka daya ne......ba wani abu da zai canzaki......ko a yanzun akwai wani abu da kikeson cimmawa shi ya sanyaki tsaiwa kina bayanin nan,bawai don kinga ya dace kiyi ba,ba kjma wai don kin damu da batan dama faruwar komai ba......kawai abjnda nake buqata daga gareki shine......ki sakarmin mijina.....ki fice a rayuwata.....kije kiyi taki rayuwar duk yadda kk so kika kuma tsara" "Bani da masaniyar komai sabreen,karki manta mana.....nifa uwa ce" "Ni kuma me shirin zama uwar,uwarma kuwa ta gaske ba MUNA UWA BA,uwar data shirya tsaf don bawa rayuwar yaranta kariya.....wadanda zasu zo dama wadanda basu taho ba.....kariya daga dukkan wani kalar farmaki daga miyagu da mafarautan mutane,irin kariyar da sunanta zai tumbatsa da tambarin SADAUKARWA.....sadaukarwa mafi girma kuwa cikin rayuwar 'ya'ya akan iyayensu.....irin sadaukarwar dake sanya kowanne yaro cikin alfahari da kasancewar iyayensa su suka haifeshi". Wani irin nannauyan abu kalamanta suka sauke mata......ta kuma isar mata da saqonni masu yawan gaske da.maganganunta masu harshen damo. "Ki huta lafiya" Magananta ta qarshe kenan da ita tana yanke kiran. Mayar da dubanta tayi kan huda dake zaune a gabanta. Tun dazu da abba yazo asibitin yace bai gamsu suci gaba da zama ba,Dr mubeena ta sallameta bisa alqawarin zata dinga zuwa ganinta kullum don samun cikakken kulawa fiye da asibitinma. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 124 124 "Zaku wuce kaman yadda ani ta buqata.....komai bazai fasa faruwa ba huda....komai kuma bazai sauya ba sai abinda qaddararmu ta tanadar mana". Hawaye sosai huda keyi,duk da yadda take qoqarin riqe kanta daga aikata hakan a gaban sabreen. "Zamu tafi adda da ciwo da firgici.....zamu tafi ba tare da taqamaimen masaniya akan ina hamma yake ba......yadda ya kula da lamarinmu muma ba zamuyi qasa a gwiwa ba wajen addu'ar bayyanarsa........da kuma tonuwar asirin duk wanda keda hannu wajen kitsa komai da zai illata rayuwar kamilin mutum me taimako irin hamma fu'ad". Ba qaramin jarumta sabreen din ta nuna ba a sanda suke sallama dasu nadra din da yammacin ranar,sai takejin kaman zata sake tabbatuwa cikin kadaici,ta dinga jin kamar ita daya ta rage a duniyar zata ci gaba kuma da rayuwa ne ita kadai. *11:30 pm* A hankali ta farka daga wani nannauyan bacci daya saceta saman abun sallah bayan ta kammala sallar nafilfilu da dukka addu'o'inta,ta kuma cika da sallar nan me matuqar fa'ida da kuma alfanu wato sallar wuturi. Hijabin da dardumar dukka suna jikinta,alqur'aninta yana ajiye a gefe yayin da tasbahar hannunta ta sulale ta fadi a qasa ba tare data sani ba. Ta qarasa bude idanunta da fadin "Alhamdulillahi ala kulli hal" Cikin kowanne lokaci idan ta bude ido tsammani takeyi zata ga komai ya wuce tamkar cikin duhun mafarki ne da hasken rayuwa da idanu biyu ya ratsata,saidai duk sanda zata farka din tana samun komai a inda ta barshi,komai yana nan yadda yake. Fitsari ne ya cika mata mararta,ta sanya hannu ta zare hijabin jikinta idanunta yana sauka saman tray din dake table din gefanta. Komai an shiryashi akai,tasan kuma wannan aikin ma'u ne bisa umarnin anni. Hatta da dakin suna dawowa annin ta saka aka shiryashi yadda ya dace saboda jin dadinta. Qafarta tadan riqe saboda yanayin zaman da tayi a wajen na wani lokaci,ta miqe a hankali tana nufar toilet. Ba jimawa ta fito daure da sabuwar alwala,tun daga sanda ta fahimci muhimmancinta ta daina zama babu ita,musamman ita din da tasan akwai mutum irin maamah dake gefe tana farautar rayuwarsu ta kowanne fanni. (Koda baka da masaniyar takun saqa tsakaninka da wani wanda kake kyautata zaton yana 'yan biye biyen shirkarsa,ka tabbatar baka zama ba tare da alwala ba,koba komai ita din haske ce a gareka,ga kuma kariya da zata baka daga dukkan sharrin me sharri). Wani sauqi sassauci da kuma rangwame take ji duk sanda ta tuna ta sakarwa maamah wani tsoro da firgici,don tana zaune ta shiga shafukan sada zumunta,kai tsaye ta dinga cin karo da labarin yanata trending,ga 'yan qarawa miya maggi da gishiri sunata qawata topic din da kalar qarairayinsu. Har ta gama shawagin ta sauka labarinne ta kowanne handle na bloggers da gidan jaridu mujallu harma da celebrities. Har zata koma ta zauna taji qishirwa sosai ya kamata. Koda ta duba tray din ba zam zam ma'u ta saka mata ba,ruwan gora ne,tana kyautata zaton kuma batasan ba kowanne ruwa take iya sha din ba sai zam zam shi yasa,don haka sai kawai ta maida hijab dinta ta zura flipp flops dinta ta nufi qofar. Sanda take takawa zuwa parlor din sai ta dinga jin wata kakkaurar murya tana magana,kaman tasan muryar,kafin ta qarasa tunaninta kuwa tuni ta fusgo mata cewa muryar abdulgaffar ce. Sunan fu'ad da taji an ambata ya sanya gabanta wani mummunar faduwa,qafafunta suka fara slow suka gaza ci gaba da tafiya da ita,sai kuma suka tsaidata cak qirjinta kaman zai fito waje. "Mun samu nasarar gano inda yake.......farouq da pilot dinsa sun fitar dashi daga qasar.......suna taipei capital na taiwan,asibitin taipei wellness hospital and resort,mun samu magana da farouq,saidai na lokaci kadanne ya datse kiran,alamu sun nuna bayason kowa yaji.....kuma haka mukayi dashi,ya bani information dinne nima na through waya ba,yace idan zaiyiwu kada kowa ya sani sai abba" Muryar anni rawa takeyi sosai,yayin da sabreen taji wani murdewa da mararta tayi,tanaso taji ya fu'ad yake......tanaso taji halin da yake ciki,muddin ta bayyana ba zasu fadi komai a gabanta ba ta sani.....muddin sukaji motsinta kuma nan ma ba qarasa maganar zasuyi ba bare tasan me ake ciki,don haka salin alin ta sulale tayi zaman dirshan a nan tana dafe hannuwanta jikin wata kujera qwaya daya da aka ajiye a wajen. "Me ya samesu abdulgaffar.....kada kace zaka boyemin komai" Shuru abdulgaffar yayi yana sadda kansa qasa,har sai da abba ya qagu shima yace "Zauna ameena.....kaima zauna abdulgaffar....." Dukkansu suka zauna sannan abban yace. "Dani da ameena bana jin muna cikin mutanen da zaka boye mana komai,shi kansa farouq din nasan bazai taba lissafamu a ciki ba,koda zaice kada a fada din zai fada ne saboda matarsa......tana cikin lalurar da ba komai dama ya kamata a gaya mata ba". "Ba gatan da zakuyimin abba sama daku gayamin halin da hamma yake ciki" Sabreen da jikinta ya soma daukan wani yanayi ta fada cikin zuciyarta,tana jin kamar ta jawo abdulgaffar ya gaya mata komai da gaggawa. "Haka ne,sun hari boss ne,a sannan yana tsaye suna magana da jordan,ya kauce basu sameshi ba,yana daga kai kuma ya hangi wanda yayo harbin,baice da kowa komai ba ya soma dosar inda yake hangoshin,daga can sama ne wani guri da ba kasafai aka fiya amfani da wajen bama,ganin ya hangoshi kuma ya nufeshi sai ya sake yin harbin a jere har sau biyu don kada ya samu isa gareshi,to amma kuma baiyi nasara ba,don harbin daya ne ya sameshi a damtsansa,dayan ya sake wuceshi,harbin bai hanashi qoqarin cimma mutumin ba,ganin yana dososhi da gaske kuma dab yake da riskarsa,jordan da farouq na biye dashi a baya sai ya fara hade kayansa zai gudu. Har yayi taku biyu ana ukun ya damqeshi yanason cire hular fuskar daya saka ya rufe idonsa,juyowar da zaiyi kawai sai ya shaqa masa wani abu a handkerchief din hannunsa yana qoqarin zamewa ya gudu,saidai kafin abinda ya shaqa masan ya kama jininsa su jordan sun qaraso,qarasowar tasu kuma yayi daidai da zubewarsa a wajen,basusan waye da waye a wajen yake tare dasu ba,basusan kuma waye ya aikoshi ba,wannan ya sanya kawai suka yanke shawarar komawa dashi su fitar dashi daga qasar,shi kuma mutumin sun sakashi hannun hukuma,He's unconscious har yanzu,wannan dalilin ya hana oga farouq bayyana ko bayyana komai". "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Shine kawai abinda anni ke maimaitawa. Komai jinsa sabreen tayi kaman tana saman gajimare ko iska yake faruwa,ta dinga kokawa da numfashinta tanason kamoshi ta kuma kama ayoyin Allah da zasu taimaketa,saidai ta gaza hakan har sai da sautin muryar anni ya bayyana. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Tabi bayan ta anni tana maimaitawa,saidai tata da wata madaukakiyar murya ce data fusgo sautinta da qyar daga maqoshinta,sautin kuma ya iske anni dake zaune tana maimaitata. Cak anni ta dakata tanaso taji sautin daga inda yake fitowa,jin daga inda sautin yake ya sakata waiwayawa tana duban fuskar abba wanda shima ita din yake kalla. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!!" Kalmar data sake maimaitawa da wani irin gunjin kuka shiya ankarar da anni daga inda sautin yake fitowa. Da wani gudu anni ta miqe tana nufar wajen hankalinta yana tashi,bai kamata sabreen taji wannan mummunan labarin ba,bai kamata ba,labarin da aketa boyonshi ta yaya ta jishi?". A zaune ta sameta tanata maimaitawa,wasu irin hawaye sun wanke fuskarta,jikinta kawai rawa yakeyi,durqusawa tayi a gabanta tana kamata yayin da Alhaji hamza ke tsaye a kansu shima yana tayata maimaitawa. "Me kika fito yi sabreen?,me yasa kika fito?" Anni ta maimaita a gigice tana riqeta cikin tsananin tsoron abinda zai iya faruwa da ita. Numfashinta yana wani iri,ta tabbatar kuma tana da asthma ne irin nata,tana tsoron kada ta sarqeta cikin wannan daren. Zuciyarta taketa qoqarin bawa dakiya da juriya.......tanata qoqarin maido wannan qwarin gwiwar juriya da jarumtartata,tanason dawo da old version of sabreen dinta. A yanzu bata da wani buri daya wuce ta bude idonta taga fu'ad din,ko a yaya yake......ko a wanne irin yanayi yake sai yafi mata nutsuwa akan zamanta a nan. "Ruwa zan sha anni" Ta fada muryarta tana rarrabuwa. Da kansa Alhaji hamza ya koma ya dauko mata ruwan,ya miqawa anni ta bude ta bata sannan yace. "Maidata daki ameena,muje na bude miki qofa". Riqeta anni tayi har yanzu suna maimaita hasbunallahu wani'imal wakeel tare. Saman gadonta ta ajiyeta tana jingina mata pillow "Anni" Ta kira sunanta kai tsaye tana jin wani jarumta yana shigarta. Kai kawai anni ta tada ta kalleta,don bazata iya tuna yaushe ta kira sunanta haka ba. "Kunason nutsuwata da kwanciyar hankalina?" Ta tambayi anni still tana dubanta. Alhaji hamza dake tsaye daga bakin qofa anni ta kalla,sai ya gyada mata kai,tasan umarni yayi mata sai ta dawo da dubanta kan sabreen. "Sosai sabreena.....sosai". Idanunta da takeji hatta su sun mata nauyi a jikinta ta lumshe sannan ta bude. "Abu daya nakeso anni da zai bani wannan nutsuwar......abu guda daya take nake da buqata....." Ta fada tana daga yatsanta daya,idanunta nayin wani iri kaman wadda tasha abun maye ta maku....... *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 125 125 "Mene sabreen?" Anni ta sake tambaya tana zama gefanta,tana jin kamar an salube qashinta daga cikin tsokokin jikinta,tana fata ba abinda bazai yuwu bane sabreen xatayi magana akai. "Anni ku kaini wajensa" Ta fada a taqaice hawaye suna cika fararen idanunta da tuni kalolinsu na fari da baqi ya jima da sauyawa daga idanunta. Da hanzari anni ta kalleta,kai ta dan girgiza mata. "Kiyi haquri ameenatu......ta yaya kina cikin irin wannan yanayin zaki tafi ki ganshi a yanayin da yake ciki?,ba abinda yafi buqata illa kiyi masa addu'a ki kuma kula da abinda yake cikinki......bazai taba iya mantawa ba muddin kika kasa riqe abinda yake cikinki kika kasa rainan masa su....." "Bazan iya rainonsu ba anni muddin babu shi a kusa dani.......zan fara lissafin yankewar numfashi daga gangar jikina daga yanzu zuwa fitarsa na qarshe" Ta qarasa maganar hawayen da take tarewa suka gangaro saman kuncinta. Wani abu ya ratsa anni da Alhaji hamza tun daga saman kansu zuwa tafin qarfinsu. Tsahon rayuwarsu zasu iya cewa basu taba ganin zazzafar soyayya irin wannan ba.....soyayya da qauna me wani irin zafi da radadi,soyayya da qauna ta gasken gaske......soyayya ta a mutu da kowanne motsi da yanayi na abokin soyayya ya tsayema dan uwansa a rai. Rasa bakin magana anni tayi,ta daga kanta tana duban Alhaji hamza da shima ya gama sallamawa. Kai kawai ya jinjinawa anni sannan ya dubi sabreen. "Indai don wannan ne ki kwanta kiyi baccinki sosai,daga gobe zuwa jibi in sha Allah zan siya mana tickets na fita taiwan......zakije ki ganshi....amma sai kinyimin alqawarin daga yanzu harmu tafi ba zaki sake damuwa ba......kuma zaki sakeyimin alqawarin idan munje ba zaki daga hankalinki ba.....ko a yaya kika sameshi zaki sawa zuciyarki nutsuwa da kwanciyar rai har ya samu lafiya kamar yadda muke kyautata zaton hakan". Kai ta shiga jijjigawa a jejjere. "Nayi maka alqawari abba.....nayi maka in sha Allah". Kai ya gyada shima,wani irin tausayinta yana kamashi,ya yiwa anni alama da hannu sannan ya juya yana fita. Saida anni ta tabbatar ta kwanta ta kuma nutsu,sannna ta saka mata karatun qur'ani qasa qasa kusa da ita,ta kira mata ma'u suka kwanta tare sannan ta fice. Tana jin fitar annin,saita runtse idonta tana jin wani rauni yana saukar mata,kuka takeso tayi wanda batasan iyakarsa ba,amma kuma sautin qur'anin da yake shiga kunnenta ya bata wata irin cikakkiyar nutsuwa,a hankali ta sake maida idanunta ta rufe,saita dinga jin kaman wani tabbaci take samu daga zuciyarta na samun nasara da sauqi a dukka al'amuranta,ta sake imani da wannan ayar da take cewa. (Ku saurara,da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa). A dan gaggauce anni ta qarasa dakin Alhaji hamza,ta dubeshi,waya yakeyi yana daga tsaye a daren,batasan koda waye yake wayar ba duk da dare ya soma nisa,sai ta zauna tana jiransa ya kammala. Ba jimawa ya kammala din,ya dubeta yana aje wayar "Na saka su dubamin tickets ne xuwa taiwan.....na gobe ko na jibi,ina zaton kuma sai jibi ma za'a samu". "Amma abba.....kana ganin ya kamata mu dauketa mu kaita ta dinga ganinsa cikin engine da tashin hankali?kasan tabbas sai muhammadu yafi son rayuwar yaran nan da nashi rayuwar?,kasan sai yafi qaunar ta kula da kanta da lafiyarta akan tashi?." Dan murmushi ne ya subucewa abban,sai ya zauna gabanta yana dubanta. "Ameenatu.....zuciya da ruhin soyayyarsu ba gama gari bace irin ta kowa.....karatun da na yiwa soyayyarsu shine.....suna sake qaunar juna da tsananin son kasancewa da junansu a sanda jarrabawa ko musiba ta samu daya daga cikin su,sunfi qaunar duk tsanani su kusanci juna akan suyi nesa da juna......sabreena ba zata taba samun nutsuwa ba.....ba zamu taba samun yadda mukeson gani ba muddin bamu sadata da barin ruhinta ba.....xakisha mamaki idan kikaga tafi nutsuwa a can fiye da anan din duk da unconscious yake?" Ya qarasa maganar da tambaya yana duban idanun anni. Shuru annin tayi tana juya maganar abban. Ta jima bataga soyayya me zafi jini da hanta da zuciya harma da b'argo irin tasu ba. Kanta ta gyada a hankali bayan ta gama nazarin,ta kuma yarda da maganganun abban dari bisa dari don itama taga hakan. "Allah yayi mana jagora,ya taqaita dukkan wahala da sharrin masu sharri" "Allahumma ameen" Ya amsa mata yana miqewa. _TAIWAN_ _TAIPEI_ *_Taiwan Taoyouan international airport_* Yammaci ne sosai sanda suka sauka a taiwan,misalim qarfe hudu na yammaci,wanda yayi daidai da qarfe sha daya agogon nigeria. Da yake tafiya ce bata shiri ba,cikin motocin da gwamnati ke ajiyewa saboda baqi da wadanda ke buqatan hayar da zaiyi driving da kansa,ya gama adadin kwanakin ka maida inda ka karbo ita suka karba. Abdulgaffar ke driving din,yana yi yana duba map da address din da ya samu da zai sadashi kai tsaye da asibitin. Duk yadda garin yakai ga kyau tsaruwa da daukan hankali ba wannan bane a gabanta,bama kasafai take iya fahimtar inda suke wucewar wa,burinta kawai.shine su isa asibitin,burinta kadai shine ta ganta a gabanshi,burinta ta ganshi a gabanta ta daina jin cewa yayi mata wannan nisan da kowacce rana zuciyarta da gangar jikinta suke jiye mata. Tafiyar mintuna arba'in suka fada ainihin titin asibitin,ba wani wanda yake iya cewa da danuwansa komai. Saddiq musaddiq abba da anni......ballantana sabreen da take ganin kaman laqai laqai kawai abdulgaffar yakeyi bawai tuqi ba,kaman tafiyar kunkuru yakeyi,kamar ma bayason ya sadasu da asibitin. Mintina sha biyar map ya nuna musu suna daidai asibitin,suna shiga titin shine gini na farko daga hannun dama. Idonta ta daga a hankali tana kallon tsararre kuma ajiyayyen ginin asibitin,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan cewa gurine me cike da tsari da tsananin kulawa,guri ne kuma da lafiya ke tsaye da qafafunta. Karo na farko data soma yarda da gaske ko a qasashen waje akwai rayuwar masu hannu da shuni akwai ta tsaka tsaki akwai ta talaka. Tun kafin sukai ga shiga asibitin checking nasu da akeyi kadai ya isa ya tabbatar maka akwai tsaro sosai cikin asibitin. Checking da ya sanya ta dinga jin kaman wani salo ne na hanata isa garesa.....kafin yafi tsaye mata a rai sama da zaman da sukayi cikin jirgin kafin isowarsu taiwan. A muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci abdulgaffar ya tsaida motar sannan ya kasheta. Ta daga idanunta tana jira taji wani a cikinsu ya bude motar da zummar fita amma bataga kowa ya motsa ba. A nutse Alhaji hamza kibiya ya fiddo wayarsa sannan yayi kira,kiran da duka duka bai wuce minti daya ba "Muns parking lot" Abinda ya fada kenan ya yanke kiran yana dubansu. "Muje ko.....ga Jordan nan zuwa". Kiran sunan Jordan kadai ya sanya jikinta ya fara rawa,a kasalance ta sanya qafafunta waje tana ambatar sunan Allah bayan musaddiq ya bude mata murfin motar,sai taji jikinta kamar yayi nauyi ta dafa murfin tana fitowa. Komawa gefenta anni tayi tana saka hannuwanta cikin nata,ta daga kai suka hada ido da anni. "Karki manta alqawarinmu,kada ki sabashi......be strong please ameenatu......na sani ke din jaruma ce" Kai ta gyadawa anni,bawai don a yau tana jin wannan jarumtar ba,ta dade da sani da kuma fahimtar indai akan fu'ad dinne bata da wani sauran jarumta daya rage,ita din raguwa ce ta qarshen qarshe. A hankali suka fara takawa suna dosar main entrance na asibitin,wanda basuyi taku goma cikakke ba saiga Jordan din,sukayi kacibus dashi a hallway din yana fitowa daga elevator. Kallo kawai sabreen take qarewa Jordan,abinda bata taba yi ba,saidai koda bata taba qare masa kallo ba amma ta sani yana da qiba da kuma tsaho gami da murdewar jiki,amma a yanzun abinda idanunta suke iya gane mata shine zubewar da yayi. Ya rame sosai duk da har yanzu wannan kuzarin yana tattare dashi,abinda ya sanya dukka gwiwoyinta yin bala'e'en sanyi tana jin tabbas ko meye ya faru da hammanta ba qaramin abu bane,abun har ya taba jordan har haka?. "Welcome madam" Ya fadi mata yana tsaye daga gefanta cikin tsananin girmamawa tausasawa da kuma kulawa. Bata iya amsa masa ba,sai idanunta data zare daga kansa gudun kada taje ta rasa ragowar qwarin gwiwar data rage mata. Musaddiq da abba da jordan su suka fara wucewa saman,kafin su kuma su kuma da saddiq su kira wani elevator din suka shiga suka bi bayansu. Farouq ne mutum na farko data fara hangowa yana fitowa daga wani balcony na daban bayan doguwar hanyar da kebantattun amenities suke. Faduwar gabanta ya sake tsananta saboda ganin irin zubewar da jordan yayi akan fuskar farouq. Ta kasa dauke idanunta a kanshi,kaman yadda ta lura shima din ita yake kallo. Suna takawa zuwa inda yake shima yana matsowa garesu,har suka riski juna a hanya. "Adda......haka kika koma?" Farouq ya fadi a raunane yana jin wani irin tausayinta yana ratsashi. Karo na farko da yaji yarda dari bisa dari yau yayi ido da ido da salon soyayyar da yakeji a ransa a baya cewa babu irinta a duniyar zahiri......saidai a duniyar litattafai da kuma fina finai. Kanta ta dauke tana qoqarin hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya.....tambayarsa kulawa ce ta kawota.....amma da zaiyi mata wani abu da yafi wannan tambayar faranta mata rai. Ya sauketa da labarin halin da hamma fu'ad yake ciki.....ya gaya mata yanayinsa shi zaifi komai mata dadi. "Kaima bakaga yadda ka koma ba BB?" Ta qarashe tambayar tana kallon fuskarsa kai tsaye muryarta tana rawa,tana fatan ganin wani mode da zai bata haske akan yanayin da fu'ad din yake ciki. Wani busashen murmushi yayi yana kada kansa,sannan ya maida dubansa gasu anni. "Sannu da zuwa abba.....anni sannu da zuwa". "Muje farouq ciki....muje dakin" Anni data kasa haquri ta fada tana yin gaba sabreen kuwa ta sanya qafafunta ta rufa mata baya kai tsaye xuwa dakin da sukaga farouq din ya fito. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 126 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 126 Daga balcony din ma'aikatan lafiyar wajen suka tsaidasu,kowanne aka bashi riga da hula ya sanya,sannan suka musanya takalman qafarsu zuwa wasu ajiyayyun tsaftatattun fararen Crocs da suke wajen. Lafiyayyen parlor ne wanda aka tsarashi cikin wani irin yanayi da zai bawa me jinya dama wanda ake jinyar yanayi me kyau,bisa wadatacciyar iska da haske,irin iskar dake fitowa daga tsirran da aka wadata bayan dakunan dasu,wanda kana iya hangen komai tarwai ta gilasan da dakunan ke dashi daga gaba. Sam parlor din baiyi kama da asibiti ba,an saka sofas set guda,tv plasma freezer da side tables da babba guda daya,curtains da komai na parlor din fari ne qal tamkar hannu baya tabawa saboda tsananin kula da tsafta,hakanan qamshi ne me kwantar da hankali kawai yake fita. "Akwai likita a ciki a tare dashi,bibbiyu bibbiyu nake ganin ya kamata a shiga......" Farouq ya fada yana rarraba idanunshi tsananin fuskokinsu. Sulalewa tayi ta zauna saman sofa din,koda farouq yace ta fara shiga batajin zata iya hakan,gwara a cikinsu wasu su fara shiga din,yanayin fuskar kowannensu shine zai bata qwarin gwiwar shiga ko akasin hakan. Kaman anni zatayi magana sai kuma ta fasa,ita da abban sukayi gaba farouq yana musu jagora suka buda qofar suka shige. Zaman jiran fitowarsu annin ba wani abu bane me sauqi a wajenta,sai ta jita tamkar tana zaman jiran isowar layin mutuwa kanta,kanta a qasa ta saka hannuwanta dukka biyun ta dafe kanta tana jin yadda zuciyarta ke harbawa kaman zata fado qasa. Wani motsi takeji mararta tanayi,baqon abune da bata taba jinsa ba sai a ranar kamar ana d'allinta da yatsa. "Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta dinga maimaitawa labbanta kadai ke motsawa. Da yatsunta ta dinga irga kowanne wucewae second,tanajin kaman suna wucewa da kowanne dama na rayuwarta,tana jin kamar suna wucewa ne da farincikin rayuwarta gaba daya. Sai da su abba suka kwashe mintuna kusan goma harda doriya kafin taji fitowarsu. Duk yadda taso daga kai ta kalli reaction na fuskarsu ta gaza yin hakan,ta kasa koda motsawa,tana jin tsoron abinda zata daga ta gani tattare dasu. Saidai takum tafiyarsu su biyun bata tsinci komai a ciki ba,karsashi ko akasin hakan,wanda hakan ya sake sanyata a taraddadi me yawa da kokwanto. "Ni zan shiga" Ta fada da wani irin fusgar kalma cikin ba zata a sanda saddiq da musaddiq ke takawa zuwa qofar dakin. Miqewa tayi ta zauna sosai tana dubansu sanda suka dakata daga shigar da juyyayyun idanunta,tana jin kamar kafin su shiga su fito zata iya rasa numfashinta da rayuwarta gaba daya,koma meye gwara ta shiga ta gani ta kuma fuskanceshi da.dukkan iyawarta,da wannan qudurin ta taho,ba kuma zata iya canzashi ba. Da baya suka dawo,ba wanda ya musanta mata ko yace wani abu,saita miqe a hankali tana jin kamar qafafunta ba zasu dauketa ba ta doshi dakin. Ta kusa sakkani talatin riqe da handle din ta kasa murzawa,har sai da muryar farouq dake bayanta ta dawo da ita daidai "Are you okay?" Ya tambayeta yana leqen fuskarta. Kai ta gyada masa. "Ko na bude miki?" Ya sake tambaya cikin kulawa saita girgixa kanta ta kuma tattara gaba daya qarfin daya rage mata ta murda qofar tana shiga. Jijiyoyin jikinta ne taji tamkar suna tsinkewa,numfashinta kamar an musanya mata da wani abun daban me tauri bawai lallausan iskar da kowanne me rai yake shaqa ba. Ta dinga ganin idanunta kaman gizo suke mata,ba ainihin abinda zata gani bane take gani......gani take zolayarta kawai idanun nata sukeyi saboda abinda take kwana ta tashi da fatarsa kenan.....abinda take kwana ta tashi tana mafarki da burin ya kasance kenan. Yana zaune saman gadon da aka tallafo bayansa aka dago kan gadon sosai yadda zaiji dadin zama. Jikinsa sanye da rigar asibitin ruwan sararin samaniya me haske sosai. Lallausan blanket ne lullube da qafafunsa zuwa qugunsa. Fararen idanunsa tarr bisa fuskarta,idanun da suka dan rusuna kamar wanda bacci yake cike a idanun nasa. Kallon kallo ya wanzu a tsakaninsu,zukatan kowannensu yana bugawa da sauri da wani irin doki da zumudin ganin daya bangaren zuciyar tasa. Wasu irin abubuwa ya dinga sakar mata suna ratsa sassan jikinta......wani irin shauqi mahaukaciyar soyayya da zazzafar qauna ke kurdawa ta kowanne lungu na zuciyarta. Kewarsa me matuqar qarfi ta taso ta lullube zuciyarta ta sakata jin wani rauni na mamayarta,take idanunta suka cika da hawayen da bata da ikon tsaidasu. Hannunsa daya ya miqa mata yana ware mata su alamun marabtarta yakeyi,cikin wani irin zaquwa da dokin isowarta gareshi,batayi wata wata ba ta soma takawa da sassarfa zuwa inda yake tana jin kaman lokacin isarta inda yake ma ya mata yawa.....inama zaiyiwu ta zama walqiya cikin qiftawar idanu ta samu isa gareshi. Jikinsa ta fada gaba daya kuka yana qwace mata,tsam ya riqeta cikin jikin nasa yana mata kyakkyawan masauki zuciyarsa na tsananta bugu cike da wani bahagon so,idanunsa suka dinga lumshewa da kansu,dumin jikinta yana ratsa qashinsa bargo harda jinin dake harbawa kowanne sashe na jikinta. Hannunsa daya ya sanya ya riqo fuskarta,idanunta yake son kallo,qwayoyin idanun nan nata da yayi matuqar kewa yakeson gani. Bata hanashi ba,ta daga oily eyes dinta masu sheqi da suka jiqe da hawaye tana kallonsa. Nutsewa idanunsu sukayi cikin na juna,wani irin feeling ke ratsa kowannensu wanda yafi qarfin baki ya bayyanashi. Wani deep connection ya qullu a tsakaninsu,magana ce tsakanin zuciya da zuciya kawai wadda tafi qarfin baki ya bayyanata. Idan ya motsa labbansa sai yaji sun masa nauyi.....sai yaji kaman sunyi kadan su isar da saqon da zuciyarsa keson fadi "Sabrrrr" Ya samu ya fusgi kalman da qyar zuciyarsa naci gaba da bugawa. Itama kaman zai bace mata takeji daga qiftawa qwaya daya tak da zata yiwa idanunta,don haka ta motsa labbanta ba tare da amsar NA'AM din da takeson furtawa ta fita a bakinta ba. "Love is in the eyes.....eyes don't lie.....sabrrrr.....kalli idona.....me kika gani?" Ya motsa labbansa ya fada da wata irin narkakkiyar murya irin wadda soyayya ta yiwa lahani. Inda yasan yadda qwayoyin idanunsa suke narka mata bargo da bai buqaci ta kallesu har haka ba....saidai kuma kallon nasu wani abune na musamman cikin ruhi da zuciyarta. Ci gaba tayi da kallon idanun nasa.....taga abubuwa masu tarin yawa.....taga abubuwa masu yawan da sai da taji kaman zata zauce,duka ita daya?,duk ita daya muhammad fu'ad kewa wannan zazzafan son?. Hannu ya kama ya riqe kumatunta yana aza shimfidadden murmushi kan fuskarsa. "You're a thousand miles away.......but no one else is closer to my heart than you are" Ya qarasa fada yana kama fuskarta sosai gami da hade goshinsu guri daya. Musayar numfashi suka fara yi a tsakaninsu,kowanne yana shaqar numfashin da dan uwansa ya fesar,hakan na sake qara musu wani qaqqarfan alaqa tsakaninsu data tsananta bugun zuciyarsu duka su biyun. "Zan iya mutuwa.......Allah zan iya mutuwa idan ka sake matsawa daga gareni irin wannan matsawar da kayi.......zaka iya rasani......ka rasa kuma babies dinmu gaba daya" Ta qarashe maganar tana sakar masa kukan da ya koma zuwa na shagwaba kuma a wannan lokacin. "Nayi alqawari DUNIYATA.....nayi alqawari bazan qara ba,i promise" Fuskarta ta qwace ta cusata cikin qirjinsa tana shaqar wannan tattausan qamshin nasa da tayi matuqar kewa kamar zata zauce. "I pray to god that you will stay permanently in my life". "I pray too my world" Ya fada yana kissing tsakiyar kanta. Qanqameshi tayi da kyau don sake bawa kanta tabbacin reality ne bawai mafarki ba. Kalmar "wash Allah na" Daya fada ita ta sakata saurin sakinsa tana kallon fuskarta. Idanunan dai nashi ya zuba mata murmushi na fita a fuskarsa,sai ta tabe baki kaman zata saki kuka. Da sauri ya mata nuni da hannunsa,ta waiwaya a hankali zuwa sashen da yake nuna mata din. Miqewa tayi ta zauna da sauri saidai ya hanata hakan,ya jawota jikinsa ya maidata sosai yadda zaici gaba da jin qamshinta da duminta. "A nan suka harbeka?" Ta tambayeshi a sanyaye da wani irin emotion na bacin rai saman fuskarta. Girarsa kawai ya dage mata yana dubanta har yanzu fuskarsa da murmushi duk da yadda yadan fada kadan. "Allah ya isar mana....Allah ya saka mana" "Very soon duniyata......mu ajiye wannan maganar yanzun......i need you duniyata.....kaman dazu naji kince babies instead of baby right?" Ya tambaya yana tsareta da idanunsa. Tsam tayi tana dubansa,sai kuma ta saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu. "Yes......twins n....." Bata qarasa fada ba taji yana lalube rigarta,saidai jikin ba qwari kwata kwata da alama don haka ya ajiye hannun nasa yana maida numfashi. Koda ta kalleshi kwantaccen hawaye ta gani saman idanunsa,batasan me yasa akan duk abinda ya shafeta ba shi rago ne na gasken gaske. "Please sabrrrr......ki dagamin rigar na gani,haka Allah ke sona?" Yadda yayi maganar da gaske abun ya taba ranshi,ba zata iya hanashi ba,don haka ba musu ta miqe ta yaye abayan jikinta,tayi qasa da under wear dinta take farar fatar cikinta ta fito. Jawo qugunta yayi sosai,a hankali ya aza labbansa saman mararta. Har tsakiyar kwanyarta taji wani yaarrrrr,wani abu ya tsarga mata ya saukar mata da wani irin yanayi a sassan jikinta. Lips dinsa nakan marartata ya daga idanunsa ya kalli yanayin fuskarta,kunya ta sakata runtse idanunta sai ya aje mata tattausan kiss sannan ya janye bakinsa ba tare daya saki rigar ba. Batasan me ya karanta ba,amma ya kusa mintina biyu bakinsa yana motsi kafin ya matsa kusa ya tofa mata abinda ya karanta din,ya sake kai hannunsa ya aza akai ya sake karanta wasu addu'o'in sannan ya sake mata rigar. Still hankalinta yana kan hannunsa,tayi taku biyu zuwa wajen ya sake jawota jikinsa "I really missed you......kiban koda 10minutes naji duminki......ban taba zaton zan sake rayuwa ba......dazu na tashi daga suman da nayi duniyata" Yayi maganar yana aza kansa saman kafadarta,yana jin ya samu wani peace daya dauke masa duk wani abu da yakeji a jikinsa da zuciyarsa. Idanunta sukayi rau rau da hawaye "Ko waye wannan bazan taba yafe masa ba.....ko wayeshi" Ta fada muryarta tana rawa. Ya buda baki zaiyi magana muryar farouq ta ratso dakin,yadan bude qofar kadan amma fuskarsa da idanunsa sun basu baya. "Su musaddiq kuwa zasu samu yin dubiyar nan?,ko kuma su koma kawai sa dawo?". Sassanyan numfashi ya aje kafin ya motsa labbansa. "Bansan me yasa baka da imani ba farouq....aidai ka tausayamin ko?.....na yafe dubiyar,kaima ka bisu kuje ku huta......thanks so much dude". Baki kawai farouq ya sake,ya dauka fu'ad din zai tuna dasu anni a wajen ya sakaya zancansa?. " Dama shi dan adam butulu ne ai,na maka welcome to the world ai ko?,alright.....but kasan hannunka yadda yake......yana buqatan a kula dashi.....still itama me jinyar taka ba'a dade da sallamarta daga asibiti ba.....banajin she can take good care of you". "I can BB.....i can wallahi" Sabreen ta samu kanta da fadin haka ba tare da wani kunya ko d'arr ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 127 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 127 "Pay no attention to him,brush him off" Fu'ad ya fadi yana lalubenta,abinda ya dameshi kawai shine yaga abinda ya sameta don yaji farouq yace bata da cikakken lafiya. Fes farouq yaji abinda dukkaninsu suka fada,ya jijjiga kai yana mamaki "Fu'ad......farouq ne fa?,lafiyanka nake magana kana gwaleni?". Hannun sabreen ya kama ba tare daya waiwaya sashen da farouq ke tsaye ba,a yanzun baya buqatar kusanci da kowa idan ba ita ba.....idanma akace wani zaya zauna dashi a dakin ai yana ganin an gama zaluntarsa. Yasan tsiyar farouq tsaf zaice shine zai zauna dashi saboda mugunta,yadda ta gayawa farouq kai tsaye zata iya kulawa dashi ya matuqar burgeshi,don haka ya qara encouraging nata. "Take what he says with a grain of salt,dont let him get to you" Ya fadi yana sake juya hannuwanta yana dubawa. Salin alin farouq yaja qofan yana wucewa,saidai a ransa ya ayyana dashi fu'ad din yaci tuwo,zaisan kuma miya yasha "What's wrong with you my world?" Ya tambayeta yana tallafo fuskarta,yaga alamun bata fahimta ba sai ya canza salon tambayar. "Farouq.....yace baki da lafiya.....da gaske ne?" Murmushi ta sakar masa,ta miqa hannunta a nutse tana kama habarsa me cike da kwantaccen gashi. "Kana tunanin zan iya lafiyayyar rayuwa sanda ake shaidamin muffin dina yayi batan dabo cikin DUNIYARSA?" Tambayar ta sanya murmushi kubce masa shima,ya girgiza kai yana kallon zara zaran eyelashes dinta. "Wannan ciwon nayi.....amma daga yau na warke in sha Allah". Knocking na qofar da akayi shi ya katse musu wannan daddadan tattaunawar,ya kalleta yana dan hade rai da alamun gajiya da rashin jin dadi a fuskarsa. "Inda zai yiwu.....zan sanya a sauyamin dakin da babu wanda ya sanshi bare a dameni" Idanu ta waro waje tana miqewa a nutse. "Da BB yace na hure maka kunne....kuma daka cika me butulci". "Kibar ganin farouq haka duniyata....zai iyayin abinda yafi nawa" "Qarya kakemin......kunyarka tafi tawa yin qaranci" Muryar farouq din ta ratsa dakin sanda sabreen ta bude musu,itadai sai tayi baya tana boye fuskarta. Da idanu kawai ya bita yana sake ganin ta canza masa,ko takan tsiyar da farouq keyi masa da raddin da yake maida masa baibi bama sam sam. Likitansa ne ya shigo a bayan farouq din,sai fu'ad ya kimtsa yanayin fuskarsa ta hanyar rage fara'arsa yana duban sabreen. "Ki shiga toilet ki gyara lullubin kanki sosai.....banaso ko gashi daya ya fito" Ya qarasa fada yana maida dubansa ga likitan wanda dauke idanunsa kenan daga kan sabreen din. Fuska a hade fu'ad din ya kalli farouq sanda likitan ke buda qirjinsa yana auna gudun zuciyarsa. "Ka gaya masa,He should look down when she's around,matar aure ce". "Tashin hankali" Farouq ya fadi,yasan ba qaramin daru za'a sha ba.....kowa ma sai ya shiga uku muddin duniyarsa tazo......wannan ya sanya yaso ya boye har sai ya fara samun lafiya da kuma sauran dalilai na tsaro da sukeso su gama binciken duk wanda keda hannu a cikin attack din ba tare da kowa ya ankare ba. Yasan da biyu ya fadi ragowan maganan da turancin englishi,dole yasan likitan zai fahimci wani abu. Sanda ta dawo daga toilet din gyaran mayafin kujera farouq yaja mata yace "Zauna a nan" Ya fada yana ajiyeta kusa dashi. Likitan yaci gaba da duk wani dube dubensa,ya kammala yayi rubuce rubuce ya ajiye file din ya fita farouq ya bishi. Idanunta still akan hannun,har yanxu tana jin ciwon kaman cikin jikinta,yanzu kenan ida harbin ya subuce ya sameshi a inda ba'aso yanzun da wani zancan daban kenan akeyi?. "Subhanallah" Ta samu kanta da furtawa tana dauke idanunta sai caraf suka fada cikin nasa. Abinda bata sani ba kallonta yakeyi da duk wani motsi nata. Ya miqa mata hannu yana daga kwance rigingine. Kafadarta ta noqe tana dubansa a shagwabe. "Kasan wadanne irin wahalallun kwanaki na dinga yi cikin duniya kuwa?" Idanunta suna tara hawaye har batason tuna wannan kwanakin. "Inda nine inajin da tuni fargaba ya kasheni.......kinsan adadin son da nake miki kuwa?" Kallonsa take har bata qiftawa,tanason gwada ma'aunin sonsa a zuciyarta da yadda yake iqirarin nashi yafi nata. "Kina tantama ko?" Ya tambayeta da murmushi,kafin wani ya sake cewa komai a cikinsu an sake shigowa. Anni ce da musaddiq saddiq abba da farouq gaba daya,kunya ta lullubeta,tayi qasa da kanta tana niyyar tashi a wajen anni tace "Yi zamanki" Suka koma saman ragowar sofas din dake dakin suka zauna. Duk budurinnan gogan idanunsa yana kanta bai iya dauke idanunsa ba sam sam. Sabuwar gaisuwa da jaje suka sake yiwa juna,dakin yayi shuru sanda farouq yake bada labarin yadda abun ya kasance. "Kaman gawa mukazo dashi abba......dazu da safe ya farka......amma ko jiya da daddare bayan an gama wasu test likitan ya sake jaddada mana abinda suka shaqa masan guba ce me qarfi....kuma idan ya wuce yau bai farka ba ICU zasu maidashi.....cikin hukuncin Allah sai gashi ya farka da yake yaji a jikinsa duniyarsa tana hanyar zuwa gareshi". Kunya sosai ta sake kama sabreen,tayi qas da kanta tana jan mayafinta. Abba da annin duka dariya kawai sukayi,saddiq ya bude abincin da sukayi takeaway da complete set da plate da spoons ya soma zubawa kowa ma'u tana tayashi. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 128 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* ___________________________ 128 ma'u tana tayashi. Parlor abba ya fita don amsa waya,sai sukaci gaba da tattaunawa a tsakaninsu. Zukata sunyi sanyi sun kuma samu nutsuwa daidai gwargwado,sauran abinda ke cikinsu bashi da yawa,godiya kawai sukema Allah daya tsallakar dasu daga fuskantar wannan bala'in. Idanunsa yake saukewa a kansu,kowa cikin walwala yake da farincikin samun kubutarsa.....kowa kuma a cikinsu soyayya da qauna ce irin ta fil'azal tsakaninsu,amma abu guda dake taba zuciyarsa shine sam ba MAAMAH ba dalilinta. Maman daya kamata itace a gaba kafin kowa?,maman daya dace a bisa mizani na hankali dacewa da kamata ace itace damuwarta ta dara ta kowa.....ta d'ara ta babarsa anni.....ta d'ara ta 'yan uwansa,ta kuma d'ara ta matarsa......saidai sabanin hakan maamah din itace halittar da tafi kowacce halitta rashin damuwa da yanayin nasa,sai ya maida idonsa ya rufe yana jin wannan zafin har tsakiyar zuciyarsa. Saddiq ya gama da kowa farouq ya dubi musaddi "Zubawa dude ka bashi ko kadanne ko zai karba". Harara fu'ad ya zubawa farouq,yaso ace su anni basu wajen da ya bashi amsa daidai dashi. Idanunsa ya juya a hankali inda sabreen ke zaune tana juya zoben dake yatsanta,don ita ba kowanne abinci take iya ci ba. "Ke ba zakici abincin ba?" Ya fadi da wata murya can qasa yana mata kallon qurilla. Sau daya ta dago kai ta kalleshi ta mayar qasa tana ci gaba da juya zoben hannun nata. "Na qoshi". Motsawa yayi kadan yana son gyara zamanshi. "Zubo kizo nan" Ya sake fada ba tare daya dubi inda anni take ba. "Yauwa....gwara ka tilastata taci,ko ba yawa aizai zauna,ta yaya kina da lalura amma cin abinci ya zama yaqi ameenatu?". Idanunsa ya sake maidawa kanta,sunan ameenatu yana masa dadi sosai,idan ya kalli fuskarta yakuma ambaci sunan sai yaji tayi bala'in dacewa da sunan,musamman idan ya tuna tarihin asalin me sunan. A kunyace ta miqe,ta zuba komai dan kadan kadan sannan ta dawo. "Zauna a nan" Ya nuna mata gefansa. Dan satar kallon anni tayi kafin ta zauna din tana bada tazara kadan tsakaninsu sannan ta ajiye plate din a tsakiyarsu. Spoon ta zura masa a ciki ta kalleshi,sai ya langabe kai yana bata fuska. "Bazan iya ci ba.....aikinsan bani da lafiya ko?" Sai kuma yayi qasa qasa da muryarsa yana satar kallon farouq. "Idan kuma so kike farouq yayi mana dariya ya yadda da gaske ba zaki iya bani kulawa ba to". "Anni muffin.....anni a gurin" "Kada ki damu,ita hirartama take dasu saddiq,ita kanta zatafison taga kina kula dani......oya bani abinci" Ya fada yana lumshe idanu saboda yadda yakejin wani yanayi yana ratsashi. A d'arare ta debo abincin ta taho dashi bakinsa,sai ya kauda kai yana kallonta. "Eat first" Ya fadi yana tsareta da ido. Fuska ta bata,batasan ta shagwabe masa ba tace "Hamma.....bazan iya ci ba". "Zaki iya.....zakici in sha Allah,kada kiji tsoro" Ya bata tabbaci yana kallonta. Da kadan da kadan ta dinga miqa cokalin bakinta har ta juye abincin,ta soma taunawa tana rolling idanunta cikin tsoron kada amai ya biyo baya,sai taji zuciyarta ko cikinta basu wani hautsine ko juya ba yadda suka saba ta hadiyeshi tsaf. "Good girl.....am next" Ya fada yana gyaran zamanshi. Debowa tayi ta miqa masa,ya bude baki ya amshe kaman qaramin yaro. "Hmmmm........dadin abincin daya fito daga hannunki daban yake......ban taba jin abincin da yayi dadin wannan ba......Allah ya qarawa hannuwanki da rayuwarki albarka". Ya fada yana lumshe ido a kanta. "Ameen" Ta amsa tana sadda kai tana satar kallon dakin. Wayam ta gani,ba wanda ta samu a dakin duka sun fice ba tare da tasan sanda suka fice ba,saita dawo da dubanta kan fuskarsa idanunta a warwaje. Dariya me qaramin sauti ya saki "Sun gudu......they can't wait to see" Fuska ta tabe ta kyabe baki kaman zata saki kuka "Kaga irinta ko?" "Wayyo Allah hannuna" Ya fada shima yana karyar dakai gami da riqe hannun da daya hannun. Tuni ta watsar da komai tayi wajen tana riqe masa a rude. "Sannu.....da zafi ko?,fama maka nayi?,yi haquri.....ko a kira Doctor" Yadda ta fadi doctor din sai labbanta suka masa wani mugun kyau. Lallausan kiss ya saukar mata saman lips din yana dariyar yadda ya cita wasan,ya samu hanya mafi sauqi na sake kusantar da kanshi da ita. Sai kusan dare can sosai sannan su anni sukayi niyyar wucewa masaukinsu. Ya tsareta da ido ganin tana hada jakarta da tarkacenta,a ransa yakejin muddin tace zata wuce tabi su anni saidai su tafi tare,don kuwa bazai zauna ba shima tana wani gurin yana wani muhallin na daban. Kamar anni tasan abinda yake tsarawa,ta ciro wani babban envelope ta aje mata a gefanta. "Ga magungunanki nan.....kada ki kwanta baki sha ba.....mun wuce gida mu,sai gobe idan Allah ya kaimu.....saiki kula dashi....muhammad Allah ya qara afuwa,sai da safe". Har baisan sanda murmushi ya kubce masa ba,yasa hannunsa me lafiya ya shafi kansa. "Ameen anni,na gode sosai,Allah ya qara girma" Ita kanta annin tasan godiyar da biyu ake mata ita,batace komai ba dai ta shanye,har sunkai qofa ta waiwayo. "Ki kula da kanki da kyau,kada ki manta da abinda likita ya fada" Ta qarasa maganar tana sauke dubanta kan fuskar fu'ad. Ko batayi maganan kai tsaye ba ya fahimci shi anni ke ajiyewa saqon,saboda haka suna fita ya jawota jikinsa yana cewa. "Ni za'a yiwa gulma?,wai anaso ana kaiwa kasuwa......kinsa anni ta tsareni da warning,wannan maganar da biyu aka yita,kuma dani ake nasan......ita anni ta jikokinta kawai take bata ta d'anta" Ya fadi yana sansana kunnenta,abinda ya sanya tsigar jikinta xubawa,ta yunqura da niyyar gocewa a jikinsa,sai ya fake kaman yadda ya saba. "Wayyo hannuna" Dawowa tayi da sauri ta zauna tana masa sannu. "Muga hannun.....idan yana ciwo a kira likita mana" Ido daya ya kashe mata yana kallonta. "Kece likitan ai.....jeki kulle qofan da key ki dawo na nuna miki abinda zakimin ya rage zugin da nakeji" Ya fada yana karya wuya kaman da gaske zugin yake. Da zuciya daya taje ta rufe din ta dawo,saidai kafin ta ankara ya jawota jikinsa ya matseta da kyau,kota ciwon ma bayayi. "Kada ka fama ciwonka fa.....hannunka muffin" Taketa fada cikin damuwa,bata kula sam da yanayinsa ba sai daya riqe fuskarta da hannunsa daya,sannan ta maida dubanta fuskarsa. Gaba daya idanunsa sun canza launi zuwa kalan ja,kaman yadda numfashinsa yake fita a wani hautsine,take ta fahimci inda lamarin ya dosa. "Sabrrrrr" Yadda sautin ya fita saida tsigar jikinta ya tashi,ta runtse idanunta tana jin ya saukar mata da wani azababben yanayi a dukka sassan jikinta. Sunan da muddin ya kirata dashi tabbas akwai wani abu me girma akanta cikin zuciyarsa kenan. Idanunta da sukayi laushi ta zuba masa tana kallonsa itama,tana jin wani abu yana tasiri sosai a jikinta da ruhinta "I can't hear you,you have too many clothes on" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi. Idanunta ta maida ta lumshe,ta gani rigima ce fal idanunsa,ta yaya kuma zai nema rigima irin haka a irin wannan yanayin da suke ciki?. "Please ki rage wannan kayan.....hutawa nakeso nayi". Maganan ya sake mata nauyi,ta bude idanunta a kansa. "Hamma......asibiti muke fa?" Ta fada a narke da wata irin shagwaba data sake kunnashi. "Shshshsh" Ya fada yana dora yatsansa akan lips dinsa,idanunsa suna sake narkewa. Sake zuba masa ido tayi har sai daya karya lagonta,a hankali ta motsa labbanta. "Me kakeso?" Tafin hannunta ya kama sosai ya saka cikin nasa yana murzawa,laushin tafin hannuwansu ya ratsa juna da wani irin dumi da jikkunansu sukayi. "A lot things duniyata...i missed you badly.....but ukunnan....long hug....deep looks....slow kisses,i want you in the worst way...." Can qasa yayi da muryarsa cikin salo na rad'a "Your taste....scent,and feel of your skin next to mine,Duniyata......our bodies could be skin on skin.....i want it all tonight,karki hanani yin komai.....if not" Sai ya girgiza mata kai yana kada mata yatsansa. Gaba daya kalamansa sun gama tsumata,sun gama tafiya da tunaninta da nutsuwarta,sai ta zame hannayenta a hankali daga nasa,ta fara tafiya da baya da baya kafin ta juya tana fadawa toilet. Tsaiwa tayi na wasu sakanni tana maida numfashi......tana sake ji da gaske fu'ad DUNIYARTA NE. "Nothing is hotter than a romantic man" Ta furta tana sakin murmushi ita daya gami da rungume hannayenta a qirji tana jin duniyar tana shawagi da ita. Cikin nutsuwa ta fidda kayan jikinta ta shige jacuzzi ta sakarwa kanta ruwa me dumi bayan tayi brush,koda ta gama cikin tattausan babban towel ta lullube jikinta ta yafa wani saman kanta. Dole ta fita a haka saboda kayanta suna dakin,ta soma takawa a hankali tana ficewa. Zaune ta sameshi saman zagayyar sofa din da aka aje don hutun majinyaci. Kwarjini ya mata da yawa,don ba komai a jikinsa sai boxer. Faffadan qirjinsa me cike da gargasa da dukka muscles dinsa a bayyane suke,saita danji nauyi ya kamata,qafafunta suka dan fara rawa. Ya gani,ya kuma lura,saboda tunda ta fito idonsa yana kanta,ta masa wani irin kyau,kyan da bai taba lura dashi ba sai yau. "Sabrrrr" Ya kirata a hankali sanda take kici kicin neman kayan da zata saka. Waiwayowa tayi a kunyace ta dubeshi,yantsansa ya kada mata yana lumshe idonsa. "We don't need any night wear.....skin to skin contact....it's where words fade and our souls speak" Ya qarasa maganar yana shafa qirjinsa saitin zuciyarsa idanunsa suna sake rusuna.. Ba musu ta watsar da kayan,ta jawo hijab ta zura tana jan under wear dinta sama. A hankali ta tako inda yake,qamshinta yana kado masa har saman fuskarsa tun kafin takai ga qarasowa. Idanunta taketa kaudawa gefe,batason su hada ido. "Ka shirya na taimaka maka ka kwanta?". Shuru ya gifta na wasu daqiqu,har tayi tsammanin amsawa ne bazaiyi ba,saidai sanda ta daga kanta sai taga iya ya zubawa ido yake kallo idanunsa a kanta kaman zai cinye namanta. "Am ready my world.....but kafin sannan ki kashe duka wutar dakin.....ki ragemin AC dinnan,ki ajemin ruwa saman drawer dincan......sai kizo ki taimakamin din" Ya fadi yana canza ma'anar maganar daga qarshe. Duka ga ganoshi amma tayi biris,tayi dukka abinda yace din sannan ta tako gabansa a hankali tana miqa masa hannunta. Ido ya zuba mata,shi kadai yasan kalar soyayyarta sake dawainiya dashi......ya yadda da gaske so zai iya zama ajalin mutum.......yana kyautatawa Allah zato.....yadda ya yiwa soyayya mummunar qi da mummunar fassara da kuma mummunan zato......baya saka ran sabreen zata zama cikin jerin jarrabawarsa a rayuwa. Sai daya gama qare mata kallo sanna ya dora hannunsa saman nata a hankali,ta hada qarfinta tana jin zai iya dogara da ita ya miqe,amma inaaaa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa..gaba daya ta rikito jikinsa wanda yafi kyautata zaton da gayya yayi mata haka. "Subhanallah" Ya furta da raunanniyar muryarsa yana boye dariyarsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 129 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 129 Tashi tayi tana zumbura baki alamun fushi "You do it knowingly" Sosai ya sake boye dariyarsa,bayaso ya bata rawarsa da tsalle da wuri,sai ya daga hannunsa irin na surrender. "It won't repeat itself" "You're not kidding right?" Kai ya gyada mata kawai dondai yasan wannan alqawarin bazai dauku ba. Sake bashi hannun tayi,ya miqe din saidai ya maqale a jikinta yana narke mata. "Hamma?" Ta kirashi a shagwabe. "Sabreen" Shima ya kirata da salon data kirashi,abinda ya sanya ta saki dariya kenan ba tare data shirya ba. A hankali ya haura gadon,ta saka masa pillow daidai da yadda taga yafi kwanciya ya maida bayansa ya kwanta a hankali,tana niyyar janyewa ba zato ba tsammani ya jawota gaba daya cikin jikinsa tamkar baya tuna akwai ciwo a hannunsa,take ta samu kyakkyawan masauki a jikinsa. "Karkimin musu....karkice komai.....wannan shine cikakken ma'anan jinyan da nakeso kiyimin......that's why nace banason jinyan kowa sai naki,am craving you so bad....you're my place" Ya qarasa fada sanda yake zame Undearwear din da ya rage a jikinta,sannan ya sabule hijabin jikinta ya maye gurbinsu da jikinsa. Bata hanashi ba,saboda tasan zai wahala a yadda hannunsa yake ya iya wani abu me dogon zango,ta barshi yayi birgimarsa yayi rigimarsa yadda yakeso,skin to skin connection ya sameshi har fiye da yadda yake buri,saidai dukkaninsu ya jefasu wani irin yanayi da ya sanya da qyar suka iya bacci,kowa na qoqarin kai zuciyarsa nesa. ★Wani zazzafan mari ya saukewa fuskarta,yana dubanta da wani mahaukacin fushi da bata taba gani kan fuskarsa ba "How dare you zaki hari mutum kaman muhammad jadda?,have you lost your mind?" Ya qarashe maganar jijiyoyin kansa suna tashi,yana jin kaman zaiyi qaramin hauka. Da zallar mamaki ta dora hannunta saman fuskarta tana duban mahaifin nata,karo na farko daya taba dora yatsunsa biyar saman fuskarta kenan da sunan mari bada sunan soyayya da lallabawa ba,wani abu da bai taba shiga tarihin rayuwarta ba sai yau.....yau ita mahaifinta ya daka saboda fu'ad?. "Abba?.....maman naka ka daka saboda wani?" Ta tambayeshi tana nuna qirjinta da yatsanta cikin jinta cikin zallar tozarci dumu dumu "Wani?,wani fa kika ce?,shi wannan din da kike kira wani kinsan wayeshi?,nace kinsan wayeshi?,kinsan rufin asirin da ya yiwa.mahaifinki?,kinsan cewa banda shi da baki isa ki tsaya a inda kike tsaye ba a yanzu?,kinsan waye boss na mahaifinki?,to MUHAMMAD FU'AD JADDA NE!". Shock taji sosai irin wanda bata taba ji ba,ta cire hannunta daga kan fuskarta tana dubansa idanunta dukka a warwaje. "Kinsan tsakanina da talauci a yanzu takun taqi kadanne zan afka cikinsa!......kinsan anyi freezing duk wani account nawa....anyi banning all my properties?,duba nan...." Ya fada a hargitse yana cilla mata wata takarda. "Takardar sanya hannu ne na dukkanin wanda keda ruwa da tsaki na saukeni daga muqamina.....duk a silarki fareeda!!!,ki gayamin meye ya rage mana yanzu?!" Ya tambayeta a tsawace yana watsa mata jajayen idanunsa. Wani irin tashin hankali taji yana sauko mata,kalar tashin hankalin da bata taba jin makamancinsa ba,ta koma da baya ta zauna tana jin ta fara gani.bibbiyu. Anyi banning duka properties na abbanta,harda motarta suturunta,gidansu da suke taqama da alfahari dashi.....anyi freezing accounts dinsa yana nufin harda nata daukacin accounts din......an sallameshi daga muqaminsa yana nufin daga yanzu an cire mata tittle na diyar AMBASSADOR KHALED MUSTAPHA?". "This is insane.....unbelievable" Ta fada tana girgiza kai da qarfi don kwanyarta ba zata iya daukan wadannan abubuwan duka lokaci guda ba. "Ba zaki gane insane bane sai lokacin da arrest warrant ya iso cikin gidannan da zummar kamaki a mazaunin masheqiya.....don tabbas!.....ina me Tabbatar miki jadda baya shurun banza......all these yayi ne tauna tsakuwa kawai don aya taji tsoro.....ina me Tabbatar miki bazai raga miki ba......kinyi yunqurin yin kisan kai......kuma bazan goya miki baya ko na hana a hukuntaki ba". Kowanne halitta na cikinta sai data kada tsananin tsoro "Dad......na dauka ko meye na dauko kai me tsayamin ne?,abba yau da kanka kake wannan maganar?". Wani banzan kallo ya watsa mata,ya matso gabanta yana dubanta sosai. " Ki taba kowa....ki tsokano kowa amma banda muhammad jadda.....mayunwacin zaki ne......damisar da tafi qarfin wasa......fareeda!!!!!.....wai mema kika sha?,still kina shaye shayenki da alama har yanzu ko?,magana ake miki na talauci yana bakin qofa yana qwanqwasa mana qofa fa!" Ya sake fada a gigice kuka na dab da qwace masa. "I can't take it......bazan iya jura ba......rasaki da hukuncin duk da jadda zai dauka a kanki yafimin sauqi akan rasa dukiyata". Sai ya jawo wayarsa yana lalubar number muhammad jadda yana fatan samunsa ya nemawa kansa gafara da sassauci. Zata iya cewa kaf tsahon rayuwarta bata taba jin wani abu daya gigita hankalinta irin wannan maganar ba,duban dad din nata takeyi ta koma kaman gunki,kowanne sashe na zuciyarta ya cika da tsoro da nadama da tashin hankali,ta yaya zata tunkari wannan babbar musibar dake tunkarota?. ★Tare sukayi sallan asuba shi da ita,ta lafe a jikinsa suna azkar tare ita dashi,a haka a haka har bacci ya saceta ba tare data sani ba. Bakwai da rabi ta bude idanunta a hankali,qamshin jikinsa ya tunasar da ita a jikin wanda take. Murmushi ya qwace mata,ta furta "Alhamdulillah" Tana tuna daren jiya,yadda ya baibayeta da wata zazzafa kuma tsumammiyar soyayya......tana kuma tuna yadda dare daya ubangiji ya tsamesu daga taskun da akaso jefasu,amma har yanzu ta gaza ajiye tunanin Who's the one behind the scenes?. Bataso ta zama mace me yawan sanya ido tambaya ko bin qwaqwafi akan kowanne lamura,wannan ya sanya bata tambayeshi akan hakan ba,ta sani koma meye ba wannan ba kadai,akan komai da komai ma idan ta cancanci taji zai gaya mata. A hankali a hankali ta dinga zame jikinta daga nashi. Daren jiyan tasan baiyi wani bacci me yawa ba,ta dade tana jinsa yana mutsu mutsu kafin baccin ya daukeshi. Tas ta samu nasarar zare jikinta daga nashi,ta kuma maida gurbinta da pillow,saita waiwaya tana kallon fuskarsa kawai. Wata fuska dake dauke da tarin nutsuwa da kamala.....wata fuska dake da wani irin sassanyan kyau da zata iya rantsuwa bata taba ganin irinsa ba.....wata fuska da Allah yayi mata baiwar kwarjini da haiba. Samun kanta tayi da addu'ar Allah yasa yaranta suyi kamanninsa.....zatafi son haka akan su dauko nata kamannin. A hankali ta dora hannunta saman mararta da yau takejin kaman an ajiye mata dutse a ciki,ta motsa labbanta tana karanto addu'o'in tsari sannan ta sauka a hankali daga kan gadon. Dakin ta kintsa duk da dauda ko tarkace,still ma akwai masu aikin da zasu shigo suyi maka duk abinda kake da buqata. Ruwan zafi ta kunna a dispenser incase ko zaya buqaci wani abu,duk da shima akwai kitchen da zaka kira direct a kawo maka komai da kake buqata. Wanka takeso tayi,amma saita zauna ta tura list na breakfast din da suke buqata zuwa kitchen sannan ta dawo ta shiga wanka. Tunic blouse ta saka da straight leg trousers,sannan ta saka madaidaicin Malaysian hijab da ya qawata fuskarta da wani irin calmness. Luggage dinsu ta gyara ta maida cikin cabinet,a hankali ta waiwayo sai idanunta suka sauka cikin nasa. Mamaki ya kamata,tun yaushe ya farka amma baiko motsa ba bare ya nuna mata?,wataqila a gabansa ta saka bra ta saka kayanta ta taje gashinta duka. "Kinyi kyau" Ya furta yana motsa labbansa a hankali,wanda banda tabi motsin bakin nasa ba lallai ta gane me yace ba. Kunya ta sakata kau da kanta ta soma takawa zuwa wajen sofa ta rusuna tana fadin. "Ina kwana?" "Kin tashi lafiya my super girl?" Ya fada cikin kulawa yana jin kwadayin jin dumin jikinta da kuma qamshinta gaba daya,tsumin daya tayar musu jiya yana qoqarin kunna kanshi a yanzu. "Alhmdlh...jikinka fa?" Ido ya lumshe mata sannan ya bude "Am fine and good....tunda gani ga duniyata" Murmushi ta sake sakar masa. Shi duka hakan bai masa ba,ya fahimci idan ya barta kuma a banza wannan kyan saidai ya ganshi a ido,don haka yace mata. "Zaki taimakeni ki daga ni?". " Why not?" Ta fada da tattausar muryarta tana isa gareshi. Gadon ta haura,kaman jiya ta bashi hannunta saiya noqe kafada yana kallon idonta. "Ki hada hannu biyu.....baki da wani qwari.....ina tsoro kada ki Fadi nayi laifi ace da fuska biyu nayi hakan" Yadda yayin ya bata dariya,saidai ta karkada kanta. "Zan iya" "Really?" Ya tambaya yana daga girarsa,saita jinjina masa kai alamun bashi tabbaci. Kai tsaye ya miqa mata hannunsa guda daya,ta cafe a nata,saidai kuma tashin farko tayi kyakkyawan masauki a qirjinsa. "I love you" Ya fadi da sauri cikin wani karyayyen amo cikin tsakiyar kunnenta. Murmushin dole ya qwace mata,ta yadda da gaske da ake cewa duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,ta kuma sallama fu'ad daga jiyan har yau wayau ne kawai yayi mata,don haka bata da sauran inkari itama ta motsa pink lips dinta da suka fusgi hankalinsa tace "I.....love you.....more" A rarrabe da wani sound daya sanya ya gaza jurewa yakaiwa lips dinta kiss. Janye fuskarta tayi tana cewa. "Asibiti ne fa hamma.....yanzu ida....." Bata qarasa ba aka murda qofar,abinda ya sanyata hantsalawa gefe tana neman maboya. Maida qofar akayi da hanzari aka rufe,muryar farouq ta bayyana. "Na shiga uku....wallahi daga yau bazan sake zuwa asibitin nan ba". Maganar tayi tsananin bawa sabreen dariya,ta cusa kanta a kafadar fu'ad tana boye dariyarta. "Rabu da tuzurun banza......waya aikeshi?...sa'idon farouq yafi qarfinsa" "Hamma baka kyauta ba gaskiya". "I'm only selfish when it comes to you.....zakiyimin wanka?" Ya fada a narke a kuma shagwabe. Ido ta zaro waje,tanason duban idanunsa tana tsoron kada ya narkata da kallon nan nasa. "Please" Kai ta girgiza. "Why?" Ya sake jefa mata tambayar a tausashi. boye fuskarta ta sakeyi cikin pillow. "I can't.....bazan iya kallonka ba". Wani murmushi yayi mara sauti yana fidda idonsa shima "Am all yours babe....alright,hadamin komai i will do it by myself" Hakan taji yafi mata,saita tashi da sauri ya wuce toilet din don ya gama shiryawa da wuri kada subar su farouq a parlor suna jira,ya bita da kallo yana jin kamar zuciyarsa ce a waje take tafiya da qafafunta. Har cikin toilet din ta rakashi sannan ta fito tana ja masa qofar. Tana tunanin yadda zata fita su gaisa da farouq da wanne ido zata kalleshi taji an bude qofar toilet din. Ido ya zuba mata ba tare da yace komai ba,har sai daya gama tsumata da kallonsa yadda yakeso sannan ya motsa labbansa. "Towel madam" Janye kallonta tayi zuciyarta na qara gudu,tanajin kaman akwai towels a bandakin,amma bata da energy din masa bayani,don haka ta taka a hankali hannun sofa ta dauko masa wani. Miqa masan da zatayi ya hado harda hannun nata ya jawota cikin toilet din ya maida qofar ya kulle. Sabon wanka ya sakata ta sake bayan ya gama jagwalgwalata. Tabbas banda ciwon hannunsa ta Tabbatar barna za'ayi a asibitin ba jinya ba. Ya aza mata wani nauyi da ta sakejin ta gaza dubansa harta kammala shiryawa ta canza wasu kayan zuwa riga da wando saqar india. Rigar ta kawo gwiwa haka wandon budadde ne sosai,yalwataccen mayafin kayan ta ware tana rolling dashi,sai ya tako a hankali ya tsaya a bayanta. Hannunsa guda dayan ya dora saman qugunta,ya daidaita tsahonshi da nata hana dora fuskarsa a kafadarta. "Ki bani lokacinki.....ko zana rayu a duniya.....ki bani tabbacin zamana dake kinji masoyiya....nidai nidai nida nake son ki nafi kowa jinki a zuciya" Murmushi ya qwace mata,ta rufe idanunta tana miqa hannunta ta shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Muryarsa ta mata wani mugun dadi,asalin sound din yana tasowa daga parlor dinne yana ratsowa ta cikin dakin,tsakaninsu musaddiq batasan waye yakejin waqar ba,shi kuma yabi waqar da tattausar muryarsa da tafi ta mawaqin dadi. "Am starving" Ya fada yana sansanar wuyanta. Muryarta da mugun sanyi tace "Muje parlor na baka" Kai ya girgiza da sauri yana dauko wayarsa dake saman table din ya soma budeta. "Farouq ya fusata.....idan kikaji yana jin waqoqi definitely ya fusata......yana kewan fannah dinsa" Ya fada yana dan jin wani sashe na zuciyarsa yana tausayin farouq din,don ya yarda da gaske soyayya mahaukaciyar abace....kewar masoyi kuma wani abune daka iya kassara mutum komai jarumtarsa. Murmushi me sauti ya kubcewa sabreen,batace komai ba don fu'ad da farouq sunfi kusa. Ya cika da mamakin ganin tarin uban miscalls din ambassador khaleed mustapha,ba kiran bane ya bashi mamaki,saboda yana expecting hakan dama,yawan adadin kiran da ya masa na fitar hayyaci shine abun mamakin. Qaramin tsaki yaja yana share dukkanin kiran,ya lalubi number saddiq. "Shigo dasu ciki" Kawai yace yana kashe wayar. Cikin second uku ya turo ya shigo dakin da wani kyakkyawan basket. A girmame ya gaida sabreen ya gaida fu'ad yayi masa sannu da jiki,sannan ya ajiye basket din ya juya ya fice. Mayafin data rola ya saka hannu ya cire pin din sannan y wareshi tas yana dubanta. "Let me behold this beauty....i want to take a look at this loneliness....i wannan see this " Ya qarasa fada yana shafar sumarta zuwa gefen fuskarta. Zamewa tayi tana murmushi,ta qarasa gaban basket din ta tsugunna a nutse ta fara zuba komai yadda ya dace,har zuwa sannan kunnuwansu na sauraron waqoqon soyayyar da farouq ya ware volume abinsa yanaji. Fes waqar ke fita da baituka na zallar soyayya,su duka kunnuwansu suna jinsu,har ta gama ta tako a nutse tana juyawa a hankali da wani irin nutsatsen taku dake bayyana surarta da zubin halitta me kyau da Allah ya azurtata dashi. Sosai ta ajiye plate din a gabansa,ta zauna kaman yadda taga yayi ta tanqwashe qafafunta. Hannu ya saka ya cire spoons din,ya gyara hannun rigarsa yana fadin. "Oya bismillah" Idanunshi zube a kanta. Zobanta ta canzawa yatsa sannan ta saka hannun nata kaman yadda ya buqata. Wani irin shuru ne ya ratsa tsakaninsu,sai kallon kallo da yaren zukata da suke fitarwa ta cikin idanunsu,irin yaren daya gagara zuciya ta furta. Zuwa lokacin waqar abdul hassan ta meerah ta soma tashi. Komai sunaji kaman a nan aka kunnata. Kowanne baiti dake fita daga bakin mawaqin sai yakejin kaman ya wakilceshi ne.....tamkar furucin da rarraunanniyar zuciyarsa ta gaza bawa bakinsa daman furtawa ne yake fiddasu daga zuciyar tasa. Ita dinma waqar ratsata take,ta daga fararen idanunta tana kallonsa. Ya dakata kwata kwata da cin abincin,ita yake kallo. Karon farko data yarda da cewa,da gaske ne idan soyayya tayi qarfi masoyi yana iya qoshi daga jin yunwa daya ganin masoyinsa kawai(kin taba fuskantar hakan?....musamman irin yunwar da batayi worst ba....da gaske ne hakan yana faruwa). Qarar wayarsa ta katsesu dukkaninsu shida ita,ya sauke nannauyan numfashi yana saka qwayar idonsa kan wayar. Ambassador ne,sam bashi da niyyar sauraronsa a lokaci na kusa har haka.....saidai kuma yana jin baida lokacin da zai bashi da zaiyita damunsa har hakan,wannan ya sanya ya daga kiran ba tare daya dauki wayar ba ya sakata a hands free yana maida idanunsa akanta don bai gaji da kallon kayarsa ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 130 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 130 "Ex ambassador khaleed mustapha" Kalma ta farko da fu'ad ya fara fada bayan ya daga wayar. "Ranka ya dade sir......tuba muke.....tuba muke,ayimana afuwa,ayi mana rai" Ambassador khaleed ya fada cikin matuqar qanqantar da kai da kalmasa harshe. "Wani abu ya faru kenan" Fu'ad ya fada cikin halin ko in kula,abinda ya sake daga hankalin ambassador kenan. Yafi kowa sanin illar wannan shariyar tasa,har gwara ya fito maka a mutum,yayi maka duk yadda yakeso,yayi maka kalar hukuncin da yaga dama. "Ranka ya dade sir.....ina me baka afuwa......ina me baka haquri......don Allah.....don Allah a dubeni,ayimin rangwame". Gyara zamansa yayi tare da yiwa sabreen inkiyar ta matso taci abincin. Kai ta langabe masa,sai ya matsa da kansa ya soma diban abincin ya miqa mata yana tambayar ambassador. "Hala bakasan abinda yarinyarka take aitawa ba.....bama a kaina kadai ba,har kan mutanen da take taqamar matsayinka da matakin da kake kai sun tsaya mata sun kuma siya mata ticket na cin mutunci da qasqanci ga kowa?". Ya masa tambayar sanda sabreen ta saka hannu ta karbe spoon din ta maidashi bakinsa,ya bude bakin ta saka masa abincin sannan ya mata sign na itace next da zataci. Shuru ambassador yayi,yana juya irin amsar da zai bawa muhammad jadda. Yasan wayeshi farin sani ma tass kuwa.......yi masa qarya tamkar tafka wani babban kuskuren ne,hakanan gaya masa gaskiya kuma bazai taba zama mafita ba. "Ko ka sani ko baka sani ba wannan kai zaka bawa kanka amsa......". "Am really sorry sir......ayimin afuwa.......na yarda da kowanne hukunci ya kamata kayi mata koka dauka a kanta,na aminta da hakan ranka ya dade sir". Fareeda dake durqushe waje daya ta daga kanta da sauri,a mamakance tana duban mahaifinta. Shi da kansa yake sallamawa me jadda ita?,shi da kansa yake miqata izuwa gareshi kan yayi duk kalar hukuncin da yaga dama?. Ci gaba yayi da cin abincinsa yana kuma morewa kallon duniyarsa. Kaman bazaice komai ba....kaman bazai amsa ko ya sake magana ba......har ambassador ya fara sarewa gami da fidda rai kafin yace. "Zabin dawowar dukiyarka qwaya daya ne tak........tsaffin kudaden qasar nan da ka danqaresu a France.......zamuyi yarjejeniyar dawo dasu gida kuma qasata Nigeria don amfanin al'ummar qasar". Wani razani ya sake kama ambassador,wanne irin mutum ne fu'ad din?,kamar wani maye me gani har hanji?,kudade ne masu ciwo nauyi da yawa da yayi imanin koda iya su kadai iyalinsa suka tsira sun rabauta,amma har ya akayi ya ankara dasu?. "Ina fata kana saurarena?" Fu'ad ya tambayeshi yana cirar tissue yana goge bakinsa don abincin ya isheshi haka. Sai daya goge gumin fuskarsa da habar rigarsa sannan yace. "Ina jinka......na fahimta" "Good......secondly diyarka......rashin kyautata tarbiyyarta wannan matsalarka ce.....damuwarka ce.....haduwarka da Allah kadai ya isheka barazana.......tayi attempting kasheni......inaso ta gaggauta fita da kanta media television da magazines ta tabbatarwa duniya da tayi yunqurin aikata hakan,tayi apologize nawa......tayi na matata.....ta tabbatarwa da duniya cikakken mutunci da darajar da iyalina ke dashi.......wannan muqulli ne kawai na budewar daskararru da kuma qwatattun dukiyoyinka......hukuncin yunqurin kisan kai kuma ita da hukuma.....sunsan matakin da yafi kamata su yanke a kanta". Ba fareeda kadai ba.....hatta da sabreen hukuncin ya mata nauyi,tayi zaton iya hakan da zatayi ya wanke duk sauran laifukanta... "Amma sir.......na dauka duka hakan zai wakilci kowanne laif......" "Khaleed!" Fu'ad ya kirashi a tsawace cikin fushin da har sabreen dake zaune a wajen sai data daga kai tana kallonsa,tana kallon yadda kamanninsa ke sauyawa alamun bacin rai ya fara tasiri a zuciyarsa. "Magana ake ta kisan kai bisa ganganci da niyya......magana ake ta bata mutunci da daukan hayar gidajen jaridu suyi batanci ga iyalina......kasan nawa ta kashe don kawai a buga sunan matata ta sunna da sunan KARUWA?,waye yake bata kudin?,a ina take samosu?,a gaban waye take dukka kalan rayuwar da taga dama?......wannan hukuncina ne ba wai shawara bace ko alfarma.....kana da right na cewa ba zatayi ba gaba daya......wannan ya rage naku.....dont contact me again indai akan wannan issue dinne.....i finalized the matter" "Please sir......please....." "Khaleed,Not my problem to solve......Could you please stop calling me?". Shuru ambassador yayi,ya tabbatar ba wani abu da zai sanya fu'ad canza wannan hukuncin nasa,abinda ya bawa fu'ad daman yanke kiran yana jan wani dogon tsaki kaman zai tsinke harshensa. A tausashe ta karbe wayar,ta sakata a DND mode ta ajeta gefe. Kamo lallausan tafin hannunsa tayi ta saka cikin nata tana lalubar qwayar idanunsa,cikin nasara ta samosu,saita kafeshi da idanunta tana kallonsa tana kuma murza tafin hannun nasa. Cikin minti biyar ya sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,abinda ke tabbatar mata ya samu relief na bacin ransa. Hannunta ta dora saman cikinta tana nake fuska a shagwabe. "Suna tsorata sosai idan abbee dinsu yana cikin irin wannan fushin......sunce na bashi haquri,na gaya masa komai me wucewa ne,komai watarana zai zama sai labari". Murmushi ya subuce masa yana lumshe idanunsa,ya saka hannunsa ya dagota,ya dorata saman cinyarsa,tura hannunsa yayi saman cikinta a nutse ya aza tafin hannunsa akai. "Dukiya jarrabawa ce me zaman kanta....kaman yadda talauci take shima jarrabawa ne,duk wanda Allah ya jarrabi bawa dashi akwai nasa kalan qalubalen.....ki fadi musu daddynsu yana nan yana fighting akan yadda zasu rayu cikin aminci ba tare da sauran qaya ba akan hanyarsu.....i love them more than i love myself....." "I hope I'm still your number one?" Ta fadi a narke tana kyabe baki. Dole ta sanya wani murmushi me sauti ya subuce masa,ya kama kumatunta yadan riqe yana girgizawa. "You're filled with jealousy......madam.....ke din DUNIYATA ce fa gaba daya". Murmushi tayi yana boye fuskarta a kafadarsa. " Kiraminsu Musaddiq" Ya fada yana komawa normal mode dinsa. Zamewa tayi a jikinsa a hankali ta miqe,ta taka tana fita zuwa parlor din. Dukkansu suna zaune,kowa kusan wayace a hannunsa yana dannawa. Farooq kuma ya koma amsa waya. Rusunawa sukayi suka gaidata cikin girmamawa,ta amsa musu da danjin kunya da nauyi sannan tace musu. "Hamma yana kiranku" Miqewa sukayi suna wucewa ciki,banda farouq daya daga musu hannu alamun yana zuwa. So samu su shiga ciki duka ta zauna ita a nan,don wala'alla wata magana zasuyi data shafesu,to amma farouq yana nan,ita kuma yanzu kunyarsa takeji,dole ta juya ta koma dakin. Yana zaune still saman kujerar,ya miqe qafafunsa hannunsa da cup din ruwa yana sha. Gaidashi sukayi shima cikin girmamawa kaman yadda suka saba,ya jiye glass cup din yana amsa musu. "Anni bata shigo ba?" Ya tambaya yana dubansu. "Eh sai zuwa anjima kadan,abba ne yadan tashi da ciwon kai". "Subhanallah,amma ba wanda ya gayamin a cikinku?" Ya fada cikin dan nuna bacin rai. Idanu kawai suka hada kowa ya sadda kansa,kota yaya zasu gaya masa bayan ko ganinsa basu samu yi ba. waya ya dauka ya kira abban,suka gaisa yaji jikin bawai tsanani ko yawa yayi ba,yace suyi xamansu yau su huta,tunda komai yana tafiya lafiya alhamdulillah,sannan sukayi sallama ya aje wayar yana dubansu. "A cikinku akwai wanda yayi magana da wani cikin abokai ko 'yan uwa sanda zamu baro madeena mu sauka a nigeria?". Daga kai sukayi suna dubansa,don tambayar tashi ta musu wani iri. Kai ya jinjina musu. " Eh ina nufin ko a hira ba wanda ya bawa wani full details na ranan dawowarmu da inda zamu sauka?" "Full details?" Musaddiq ya tambaya yana kallon hamman nasa. Kai fu'ad ya jinjina yana maida hankalinsa a kansa. "Eh" Fu'ad ya jaddada masa. "Akwai hamma" Musaddiq ya fada abinda ya faru a wancan ranar yana dawo masa. Ido fu'ad ya lumshe sannan ya budesu. "Waye?" Ya tambayeshi kai tsaye. "Maamah ta bani wani number na tura mata details din.....ban kawo komai a raina ba hamma......ban kuma yi tunanin akwai wata matsala da hakan zai haifar mana ba" Ido sosai ya zubawa musaddiq din,yana jin kanshi ya masa nauyi da ambatar sunan maamah a lamarin. Tsoro ya kama sha da fargabar kada sunanta ya fito cikin jerin sahun sunayen mutanen da suke da hannu a faruwar al'amarin fa. "Me yasa zakayi haka musaddiq?......me yasa baka kiyaye wasu abubuwa?,kana tunanin ni dakai saddiq farouq amna dama duk wanda yake under jadda family ordinary human ne?" . Shuru yayi jikinsa yana yin sanyi. Tun sanda abun ya faru wannan abun yake a ranshi,jiki da zuciyarsa duka suna gaya masa akwai alaqa tsakanin abun da kuma wancan address din daya bada,wannan ya sanyashi tilastawa kansa zama tuno digits din daya turawa address din,ya kuma sake zaunar dasu tsaf cikin kansa. "Baka riqe name din dake jikin contact din ba....koda bincike ne ta yaya kake tunanin za'a iya yinsa?" Fu'ad dake kallonsa da takaici ya fada. "Na riqe digits din...." Shuru ya danyi yana ci gaba da kallonsa "Really?" Kai ya jinjina masa,sai ya waiwaya ga saddiq. "Ya baka digits din ka turawa saleem.....kace masa injini" Ya fada yana maida bayansa jikin kujera yayi relaxing. Wani irin bacin rai ne yake ratsashi,maamah itace silar faruwar wannan abun?,to hadin baki sukayi da fareeda kenan wajen kasheshi ko goyon baya ta bata?,hakan yana da alaqa da hallarar kowa a asibitin da nuna zallar damuwarsa a kansa amma banda ita?. Kanshi ya samu da girgizawa,yana jin cewa sam maamah din ba zata aikata haka ba. "Amma ta taimaka wajen kauda abbanku daga duniya?" Tambayar da tazo daga qasan zuciyarsa kenan,ta kuma sake taso masa da wani irin bacin rai. ★A hautsine take duban mahaifin nata bayan ya gama gaya mata hanyar mabudin arziqinsa da yake hannunta,bisa tsari da kuma dokar da fu'ad ya bayar. "Yanaso yayi humiliating dina ne abba......ta yaya zan fita gaban 'yan jarida na tonawa kaina da kaina asiri?....hakan kuma ba yana nufin na wanke kaina da kaina bane?,tamkar kenan na bawa shari'a daman yankemin hukunci da daukan mataki a kaina ta sassauqar hanya?" Ta fada tana jin cewa aikata hakan wani abune da bazai yuwu ba. "Kina tunanin kina da wani sauran amfani a wajena ne fareeda muddin dukiyar dana kwashe shekara da shekaru zata salwanta ta sanadinki?......ruwanki kimin hanyar dawowar arziqina nasan hanyar xa zaki samu Sasaaucin hukunci.....ruwanki kiqi ni kuma da hannuna zan miqawa hukuma ke......daga rana irin ta wannan lokaci kuma ki tabbatar na cireki daga jerin 'ya'yana.....sunan.Khaled mustapha kuma ya saraya daga wuyanki.....na haramta miki amfani dashi haramtawa na har abada". "Bazanyi abinda yace ba daddy.....hakanan kaima dukiyar ka zai dawo hannunka" Ta fada tana rarumar wayarta. Number maamah take nema,hanya guda daya tilo da take tunanin zatabi don samun warwarewar komai. Daidai lokacin da mota ke tsula gudu da ita saman kwalta,hankalinta yayi nisa yayi kuma zurfi a tunanin tun sanda ta baro wajen boka. Kora yayi mata fata fata akan kada ta sake zuwa masa muddin da maganar data shafi taurari biyu ne sabreen da fu'ad. Ya gama aiki a kansu har abada saidai ta nemi wani. Sanda ta lallabashi da batun wata buqatar daban tazo da ita ba irin ta baya ba.....buqatarta dankwafar da cikin sabreen yayita zama a mararta ba tare daya girma ba bare a haifeshi,wannan kuma zai zama silar da zai zama karo na farko kuma na qarshe data samu ciki da fu'ad din,a sanya masa shakka kan qaryar ciki tayi dama tun asali.....maganar rabuwarsu kuma ita zataji da sauran. Har ya soma buga qasa yayi wani zabura da saida qoqunan gabansa gaba daya suka hantsila,yaja baya yana gurnani da wasu surutai kafin daga bisani ya dubeta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 131 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 131 "Kinsan aikata hakan daidai yake da kiran mutuwarki da kuma gaggauto da ajalinki tu lokacin mutuwarki baiyi ba?" Sosai abun ya daure mata kai itama,tana kuma buqatar qarin haske. "Kamar yaya?,ban fahimta ba?". A fusace yake.magana wannan karon fiye da fusatarsa ta dazu. "Wannan yaran da suke cikinta......bake bama......duk wanda keda qudurin cutar dashi to tabbas ajalinsa yake kira......fiddasu daga mahaifarsu ko hanasu wanzuwa suyi rayuwa irin ta kowanne jariri kuwa,daidai yake da kiran ajali yayin da yake nesa da ruhi.....ki fita daga harkar wadannan taurarin......suna dab da karo da naki taurarin.......tazarar dake tsakaninku kadance,faruwar hakan kuma daidai yake da LALACEWAR RAYUWARKI!.......SAURA QIRIS!.....KI KAUCE KI BASU HANYA.....BA WANI ABU ME CUTARWA DA YA ISA YA TARE HANYAR SHAWAGINSU!" ya fada a tsawace yana nunata da yatsa. Tashin hankali!,kanta taji ya wani irin sarawa.....muddin ya kasa mata wannan aikin duk duniya bata jin akwai wanda zai iya yinsa "Kayimin rai.....zan ninka maka abinda ya kamata a......" "Dakata!" Ya fada a gigice. "Wannan aikin ba kudi yake buqata ba.......aiki ne na tsira da rai........ran da muddin aka barshi ya dulmiya babu me iya fitowa dashi........KIBAR DA'IRATA HAR ABADA....KARKI SAKE DAWOMIN DA MAGANAR TSARARRUN TAURARI BIYU". Wannan tunanin yana mata shawagi kiran fareeda ya shigo,ta saka idanunta akan kiran da wani irin yanayi,mamaki ya sanya batayi wani dogon nazari ba ta daga kiran tana sakawa a kunnenta. "Ina kika shiga fareeda..... Ko kina shirin janyewa ne saga qudurinki?" Ta fadi tanajin kamar idan ta hada kai da fareeda din nasara zata zo mata da gaggawa cikin sauqi,dole tana da buqatar me tayata wannan yaqin. Ba kalar neman da bata yiwa zuwaira ba amma ta kasa samunta......duk inda take tunanin idan taje zata sameta ta aika ba labarinta,abun yana daure mata kai. "Ban fasa ba.....kuma sauka daga kan nufina ba.....hasalima tsakiyar aikin da nakeyi aka samu matsala da kuskure". Kanta ya sake sarawa,ta zauna sosai tana riqe wayar a kkunnenta sosai. " Me ya faru kuma?". Sai data gyara muryarta da kyau sannan tayi magana. "Nasa anyi attacking na matarsa.....cikin rashin sa'a aka sameshi.....yanzu haka anyi freezing komai na dukiyarmu......yasa kuma an dakatar da dad daga muqaminsa......yana maganar saina fito nayi iqirarin nina aika a kasheshi.....na bada haquri a media sannan zai sakar mana komai.....abinda yasa na kiraki.....inaso ki sakashi ya warware komai......ya janye kuma komai.....muddin wani abun ya sameni duk wani mmuradinmu zai tsaya cak.....don ina da babban shirin da zai kauda mana damuwoyinmu ni dake gaba daya". Dif maamah din tayi,kwanyarta suna juya mata maganganun fareeda. Haka kawai taji hankalinta kamar ya kasa kama maganganun fareeda din,kaman akwai wani abu da ba daidai ba. "Fareeda.....bansan qasar da suka kaishi ba.....yanzun haka matarsa ke dauke da cikin da nakejin gwara na nakasa da wanzuwarsa a tare da ita.......bansan inda suka ajeshi ba". "Taiwan......yana wani asibitu na Taiwanese a taipei......ki kirashi tabbas zaki sameshi". " Ki dakaceni tukunna.......fu'ad baya cikin mazan da akewa gaggawa haka kuma su karba da sauri". "Me kike fada mariya?!" Fareeda ta fada a tsawace,a yanayin da take ciki bata qaunar sharhi qarin bayani ko dako......isar da saqonta da cimma burinta kadai take da buqata. "Kinsan a wanne yanayi muke ciki da har zaki saka bataun JIRA a wannan zancan?......kinsan kowacce daqiqa guda da zata shude muna sake shiga hadari ne nida duk wanda ya dangancemu?......buqata ta gaggawa ce......kiyi hanzarin dakatar da d'anki daga aikata abinda yayi niyyar aiwatarwa......idan kuma ba haka ba to tabbassss bazan shiga uku ni kadai ba......zan shaidawa duniya da hannunki a cikin komai......dollars dina da kika karba kuma.....kada ki manta akwai evidence na amount account details date da time na yadda na saka miki komai.....saiki shirya maidosu" Daga wannan fareeda ta yanke kiran. Wani sarawa kan maamah taji yayi......lallai idan fareeda ta ambaceta a wannan badaqalar ba abinda zaya hana mutane aminta dasa hannunta.....musamman mutanen dake da issue da ita irin ameenatu da sabreen.....sabreen din da har yanzu tana qarqashin awa saba'in da biyun data bata,awannin da batasan ta yadda zata fiddo fu'ad ba banda yanzun da kiran fareeda ya sanya tasan inda yake. Karasashinta ya dawo da wani irin sanya ran lallai tana da dama.....damarmaki har guda biyu.....damar sanyashi ya janye kaman yadda fareeda ta buqata,a yadda duk wata kadara tata data mallaka ta narke daga auren fu'ad da sabreen......da kuma neman hanyoyin da zata rabasu batajin tana da adadin dollars din da zata maidawa fareeda kudinta. Lalubar number dinsa ta fara yi tana jin yadda kanta yaketa sara mata da ciwo. Kira uku tayi,ana hudun sabreen data dauke wayar don ya sake samun nutsuwa taga kiran. "Maamah" Da sunan yayi serving ba kaman sunan anni da yake suna na daban cikin wayar tasa ba. Qaramin murmushi ta saki,sannan ta taka zuwa bandaki a hankali ta maida qofan ta kulle. "A yanzun yana buqatar hutu daga dukkan wata takura da zullumi na rayuwa.....yana buqatar yin nesa da kowacce kalar damuwa" Kalaman sabreen kenan da suka sauka a kunnenta suka sanya wayar hannun nata kusan subucewa daga hannun nata,kanta kuma yayi wani dummmm na wucin gadi kafin ta tattara qarfin halinta waje daya. Magana takeson mata amma ta kasa furta komai,wacce irin HATSABIBIYA ce yarinyar?,a yanzun haka kenan tana taiwan tare dashi ta barta bata cikakken bacci?. "Duk yadda kike tunanin cin nasara.....kina yiwa kanki qarya ne.....ni mariya a duk sanda nayi nufin cimma nasara akan wani abu.....ba wani wanda ko wani abu daya isa ya dakatar dani daga wannan nasarar....." "Sai ubangijin da yayi ni yayi ki,ya kuma halicci nasarar........shin da gaske ne kuwa?.....anya ke kika haifi muhammad da musaddiq?" Sabreen tayi mata tambayar da bata taba tunanin zata iya mata ita ba....amma yau ta tsinci kanta da tambayar tata. Wutace tsaf ta daukewa maamah tana jin jiri yana kamata daga zaune. "Idanma ya tabbata ke dince.....to ki saka a ranki kin haifawa masoyansu ne su.......sun tashi daga mallakinki.....sun tashi daga ababen kulawarki,ubangji ya musu musaye da masoyansu na haqiqa....." "Ki dakata da wannan shirmen......ki hadani da d'ana dashi nake buqatar magana" Sabreen bata tsaya sake sauraronta ba ta kashe kiran,ta kuma kashe wayarma gaba daya. Iska me zafi ta furzar daga bakinta,mamakin maamah yana sake kasheta,a yanzun dai ya tabbata dari bisa dari......dukiya takeso......arziqin take da buqata bawai 'YA'YAN BA. Mummunan tashi hankalin maamah yayi,ta soma sake gwada kiran number amma a kashe. "Allah ya tsine miki......muddin banyi sanadinki ba a rayuwa nayi asara" Shine abinda maamah take maimaitawa sanda take yunqurin sake maimaita kiran number fu'ad din ana gaya mata a kashe layin yake. Sam Allah ya dauke mata basirar kiran musaddiq......tunaninta yafi karkata ga ME ZAI FARU bayan awannin da fareeda ta debar mata tana jiranta?. *_Hajja_* Tun sanda suka gama wancan wayar da maamah ko sau daya taqi bawa kwanyarta hutu na neman mafita da hasashen abinda zai wakana......hakanan ta gaza dauke kunnuwanta daga jiran isowar jami'an tsaro gareta suyi awon gaba da ita kaman yadda take hasashe,duk kuwa da bokanta ya shaida mata ba wanda ya isa ya shigo ya kamata muddin ta tabbata a cikin gidanta,saidai idan qafa ta sanya ta fita. Ta sake amanna da maganarsa ganin kwana dayar har biyu shuru,sai wannan ya bata daman zama tana tunanin matakin da zata dauka akan maamah. Laila itace burinta......laila da ita take kwana take kuma tashi,yantuwar laila shine muradinta kafin ta waiwayo ga hanyoyin tozarta mariya. Tsai tayi da ranta tana bitar kalaman da sukayi musaya a wayarsu ta qarshe,ta tsinci tsoro kadan da razana a muryar mariyan,ta yiwu akwai wani abu daban da batasan dashi ba.....ta yiwu ba mmariya bace ta fidda hotonsu.....ta tabbatar tunda hoton maqale yake da nata....duk da fuskarta bata fito sosai ba amma zai wahala mariyan tabari ya fita. Wata shawara ta tsirga mata.....taji a wannan karon ta shirya ayi tone tone tsakaninta da mariya muddin autarta zata dawo cikin hayyacin rayuwarta,wayarta ta dauka kanta tsaye ta fara kiran layin wayarta. Kamar ana jira ta tsagaita da kiran fu'ad wani kiran ya danno mata waya. Hajja harira,ko kadan kiran bai sakata fargaba ba har sai data daga wayar suka fara musayar magana. "Da baki wahalar da kanki kina tambayata meye yasa nayi kiranki ba......fuskata da sunana sunyi tambari a bakunan al'umma da kuma kowacce jarida......kina tunanin akwai wani faruwar abun kunya da zanyi shakkar fitarsa?....abun da koda ya fita tawa kunyatar qarama ce akan ta mahaifiyar data sadaukar da mutuncinta da rayukan 'ya'yanta saboda ta mallaki abun duniya?". Kaman babu jini cikin jikin maamah haka takeji......a yanzu takeson solving wannan issue din batabataso hajja ta afko cikin wannan da'irar.....tanaso a sanda hajja zata buqaci a fafata yaqin ta gama da issue din fareeda dana sabreen harma da ameenatu,a sannan zata gwadawa hajja yadda ake wasan kura da rayukan dan adam. "Hajja......karki tunkari.fadan da bazaki.iya qarasashi ba......ki lallaba masarautar cikin gidanki dake gareki,ki qarasa mulkinki sannu a hankali,ki kuma jirayi randa naga damar 'yanta miki d'iyarki" Wata dariya data saka numfashin maamah tsaiwa na wucin gadi ta saki,sai da tayi me isarta sannan tace. "A a'ah......mariyatul kibdiyya......wai ni bakisan abokin mutuwa nake nema ba?....,to bari kiji.......daga yau zuwa gobe na baki ki maidomin da d'iyata gaba na,ko kuma wannan boyayyar fuskar dake gefena a bugun shafin farko na jarida da kowa keson ganinta ta bayyana kanta da kanta.....aikin fahimta ko?" Daga wannan hajja bata jira komai ba ta kashe kiran. Daga zaunen da take amma sai taji tana jin jiri.......me yasa komai yake neman ya kwabe mata lokaci guda?,kowa adadin awanni yake deba mata cikin umarni da kuma gadara?,wai me yake faruwa ne?. Daidai nan taji muryar driver dinta yana fadin. "Mun iso gida.hajiya" Kanta ta daga tana kallon gidan,batasan sanda suka iso ba kaman yadda batasan sanda suka shigo gidan har ya iso parking lot ya tsaida motar ya kuma kasheta ba. Hannu ta saka ta bude murfin motar,a hankali taja jikinta tana fita a motar,saidai ko Cilakken tsaiwa batayi ba ta yanke jiki ta fadi a wajen hankalinta yana gushewa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 132 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 132 Da sallama farouq ya shigo,sabreen dake tsugunne gaban fu'ad din tana gyara masa nails dinshi na qafa duk da fes suke.....amma tsabar bayason tayi nesa dashi ya tsiro mata aikin ta matsa kadan tana amsawa. "Sannu da aiki addanmu" Ya fada yana jawo kujera ya zauna yana dubanta. Murmushi tayi a kunyace tana amsawa. "Yauwa BB....sannu da qoqari....Allah y qara zumunci.....ya saka da alkhairi". " Ameen dai.....dama wani abun saboda ke akeyinsa ai ba don mutum ba" Ya qarasa fada yana jifan fu'ad da harara wanda yayi relax abinsa jikin kujera kaman badashi yake ba. Miqewa tayi da zummar basu guri. "Kin gama ne?" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi. Kai ta girgiza tana satar kallon farouq tana masa alama dashi. Ya fahimci me take nufi amma ya basar,don haka ta buda baki. "Zanyi waya dasu huda kafin ku kammala". Agogo ya kalla da narkakkun idanunsa. " Minti goma ki dawo ki qarasamin" "Okay sir" Ta fada a girmame ta qarasa tana daukan wayarta ta fice. Farouq bai jira ta kammala fita din bama ya soma fesar da abinda ke ransa. "Zuwa nayi na maka sallama". Dariya ya taso ma fu'ad amma ya danneta,sai ya miqe sosai ya zauna yana ware idanunsa akan farouq "Ina zaka kuma?" "Gida zanje ayimin aure.....bazan zauna na mutu na tashi a gafiyar lahira ba". Wannan karon dariya ta gasken gaske ya bawa fu'ad,har wanda ke parlor din zai iya jin sautinta,kalan dariyar daya jima rabonshi da irinta. "Bafa inda zakaje dude.....ko zaka hadiyi zuciya saika gama jinyata ka cikasa ladanka". "Lada irin naka ne banaso......ina samun ladanka kaima kana samun naka ladan ko?....bazan iya ba....ni yanzu wallahi kafi qarfina" Kai ya jinjina yana shafa sumarsa. Da gaske yasan farouq aure yakeso.....kuma koda shine yake a matsayin farouq din yana sanya auren mace kaman sabreen bayajin zai iya haqurin da yayi ma.......baiga abinda zaiwa farouq ba sama daya tabbatar da aurensu a daidai date din da aka saka.....baya jin zai yarda ya zama silar daga bikin farouq koda na kwana daya ne. "Ka yiwa pilot nassar magana......ayi booking barinmu taiwan zuwa Nigeria.......inaso larabar nan mu koma gida". Waiwayowa farouq yayi yana kallonsa da mamaki. "Ina zakaje kana jinya?,ina zakaje bincike kuma bai kammalu ba?". Murmushi ya saki me taushi yana duban farouq din,duba irin na 'yan uwantaka ta jini me cike da dumbin qauna. "Bincike ya gama kammala farouq......fareeda keda alhakin komai......ta samu nasarar aiwatar da komai dinne ta silar maamah data bata full details din......abu daya da ban sani ba shine.....bata da masaniyar abinda fareeda zatayi dashi?,ko tana da masaniya?,tayi hakanne dukka cikin tsare tsarenta data dauki shekara da shekaru tana gudanarwa?" Ya qarasa maganar duk wata walwala da yake ciki tana sulalewa daga jikinsa. Ba farouq kadai ba,hatta sabreen data dawo da niyyar daukan slipper dinta ta zagaya koda veranda din dakunan saita tsaya tana komawa da baya. Wani irin tausayinsa yana sasuqar zuciyarta. Yadda walwala tayi qaura daga fuskarsa karo daya ya tabbatar mata a yanzu a rayuwarsa bashi da sauran wani ciwo daya wuce MAHAIFIYARSA. A jikinta ta dinga jin cewa......She has to put in effort to help him overcome his past,ya kamata ta sake matsawa sosai cikin rayuwarsa.....yana buqatarta fiye da yadda take hasashen zai kasance. "No dude.....no.....kada kayi wannan tunanin.....ko yaya ne.....ko yaya kuke da maamah uwa ce.....bana tunanin kowanne kalan hali ne da ita zata iya bada qofa ko daman rabaka da rayuwarka". Idanunsa da suka sauya kala ya maida kan farouq yana dubansa. "Farouq.....duk yadda zan gaya maka abinda ke nan gurin..." Yayi nuni da qirjinsa da yatsansa. ".....ba zaka fahimta ba.......mun rasa MAHAIFIYA.....MUN RASATA RASHI NA HAR ABADA......saidai na yadda nayi kuma imani,yana cikin rashin cikar kamalar ni'imar mutum cikin DUNIYARSA......cikakkiyar ni'ima tana lahira". "Duk da haka dude please......ka ajiye wannan a side" "Na ajiye farouq......fareeda zata girbi duk abinda ta jima tana shukawa.....she must pay.....bawai iya kaina kawai ba". Kai farouq ya jinjina,wani aikine daya shirya gudanarwa da kansa,sai gashi fu'ad din ya rigashi. "But dude.....inaga kaman ka qarasa warkewa....." "Noooooo......dole farouq dina ya shiga qwaryar manya as soon as possible.....ta iya yiwuwa ya rage zargina.....ta iya yuwuwa kuma ya daina katsemin muhimman lokuta na da DUNIYATA". fuskewa farouq din yayi yana sosa kanshi "Eh to.....kaman tafiyanma zaifi mana Alkhairi gaba daya.....don bana tunanin idan ka zauna a nan dinma warkewar arziqi zakayi,gadon ya muku kadan gwara a koma gadon gida". Toshe bakinta sabreen tayi,salin alin ta debi kayan kunyarta taja jikinta tana barin gurin tun wani a cikinsu bai ganta ba. ★Salati drivern ya saki,hannuwansa bisa saman kansa yana sake sakin salatin gami da cewa. "Ku kawo dauki bayin Allah......hajiya ta zube". Dukka hankalin ma'aikatan gidan ya tattaru a kanta,saidai har matan ciki tsoro da shayin dagata suke,basusan haqiqanin abinda zai biyo baya ba idan suka dagata bayan ta farka. "Dole haka za'a ceci ranta,kome zai biyo baya ai ba za'a barta ta mutu ba ko?". Malam sa'adu me gadi ya fada. "Matso ke raliya ki kama musu ita" Ya fadi yana matsawa baya. "Gashi ba kowa gidan Alhaji hamza ballantana muji ina ake kaita" Malam sa'ad ya fada yana duban driver din. "Kowanne asibiti ma kaita za'a yi tunda abune na gaggawa.....ki shigo mu tafi" Yace da raliya yana shigewa cikin motar. Tuqi yake a gaggauce yana tsoron kada ta mace a hannunsa,babar babban mutum irin me jadda ta mutu a hannunsa tabbas ba qaramin tashin hankali bane. Tafiyar minti shabiyar suka samu wani private suka tsaya a nan,aka dauko wheelchair aka dauketa akai,har a sannan bata dawo daidai ba. Sai da suka kashe minti kusan sha biyar a kanta sannna ta farfado,suka cire mata oxygen suka daura mata ruwa da suke saka ran minti talatin ya qare sannan likitan yace zaije ya dawo kafin ruwan ya qare. Kanta kawai take mirginawa tana jin qirjinta yana mata wani ciwo,duk inda ta juya fuskar raliya data drivernta kadai take gani,har bacci ya saceta. Still data farka din ba wasu sabbin fuskokin saisu din dai. Wani abu ya tsaye mata a wuya,wasa wasa tana shirin kamanceceniya da tsintacciyar magen da bata da wani gata. A hankali ta sauke dubanta kan wata mata dake kusa da gadonta,wanda su biyu ne kacal dama a dakin. Yara hudu ne tsaye a kanta,tana zaune saman gadon,daya a hannun damanta.....daya a hagunta,dayan yana tsaye saman kanta yana bare mata ayaba yana bata tana ci,dayar tana saman kujera gaban gadon nata riqe da robar yoghurt tana jira ya gama bata ta miqa mata. Hira suke a tsakaninsu,kowanne fuskarsa dauke da walwala duk da cewa jinyar mahaifiyarsu sukeyi. Tana gama ci ya karbi bawon ya jefa a Dutsbin,zai karba yogurt din daga hannun ta zaunen ta hanashi. "Saika kwashe ladan duk kai kadai,nima inaso" Ta fada tana kai roban bakin mahaifiyartasu. Idanu maamah ta dauke tana runtse idonta,wani irin bacin rai yana ratsata. Tasan koda kwatar kwatar kwatar kudin fu'ad duka yaran matar basu kai ba.....amma yadda suke tattalinta da nuna mata qauna da kulawa kadai abun kallo ne.....ita gata ta qare da zama 'yar kallo,cikin rayuwar kadaici da rashin wani sashe da zai tallafeka. "Allah ya isa ameenatu.....Allah ya isa" Ta fada a sarari tana ji har zuciyarta anni ta mata cutar da bazata taba iya wankuwa daga ranta ba.....hakanan kowacce kalar fansa data shirya dauka ba zata iya ramawa daidai da abinda tayi mata ba. Daga raliya har driver din da kallo suka bita,saidai babu bakin magana,daidai nan likitan ya shigo. "Ta farka ko?" Ya fada cikin kulawa yana dauko file din gami da sake duba abinda ya rubuta,ya qara wasu rubuce rubucen sannan ya ajiyeshi yana dubanta. "Hajiya ki rage saka bacin rai a zuciyarki.....ki rage saka damuwa a ranki,kina da hawan jini bai kamata ki dinga zama cikin damuwa ba.......irin wannan gaskiya yana iya haifar da matsala kala kala,ba'ason abinda zai dinga sanyawa jinin yana hawa haka ta farat daya....kuyi qoqarin ganin ta kiyaye" Ya qarasa maganar yana dubansu raliya ganin maamah din taja idanunta abinta ta kulle. "Tom.....in sha Allah" Raliya ta fada a sanyaye a ranta tana cewa mu asuwa?,indai taji da kunnenta ai shikenan mun kubuta. "Kuna iya tafiya gida.....amma da zarar taji wani abu daban ayi hanzarin dawowa,saboda yanzun takai matakin da dole a dinga yawa checking up nata". "Mun gode likita" Driver ya fada bayan ya karbi takardar magungunan daya rubuta mata. Yana shirin tada motar ya dan waiwayo "Ya za'a yi da magungunan nan hajjaju?,zamu siya ne a hanya ko za'a kawo?". "Kai sagiru" Maamah dake a qufule da yadda suke jaddada mata cutar hawan jini ta kira sunansa. "Naam hajiya". "Ka fita daga ido na......hawan jinin banza hawan jinin wofi?,maqaryatan banza wanda mutum baya ciwon Allah da annabi?,shekarata nawa a duniya hawan jinin bai sameni ba sai yanxu ina fafutukar cika burikana?,Allah ya tsinewa wanda ya fasa cewa ina da hawan jini.......hawan ruwa ne dani.....bani takardar nan nan" Ta fada cikin fada tana miqa masa hannunta. "Hajiya......ki tsaya ki duba maganarnan,don bakiga yadda kike bane dazu.....bai kamata ki wasa da magani ba....." Kai ta jijjiga. "Lallai sagiru wuyanka ya isa yanka.....ashe kana dab da rasa aikinka" Ta fada cikin mamakin tsaiwa.musu da yayi da ita. "Ka bata mana sagiru" Raliya tayi saurin tunasar dashi,salin alin ya miqa mata yana cewa. "Tuba nake,Allah ya baki haquri". " Idanma hada baki kukayi dasu saboda ku manna min ciwo ku kasheni to ta Allah ba taku ba.......rayuwa a duniya yanzu na farata,maqi gani ya kauda idonsa" Ta fadi tana yayyaga takardar ta watsar ta window tana cewa "Muje gida" Tana jin lallai tana buqatar tayi magana da fu'ad da gaske. Ya gama shirin kwanciya tsaf sanye da pyjamas masu taushi farare qal,yana zaune saman yalwatacciyar sofa yana binta da kallo sanda take qoqarin gyara masa gadon don yaji dadin kwanciya. "Sabrrrr" Ya kirata da sautin da ya sanya taji tsigar jikinta ta zuba. A nutse ta waiwayo tana kallon lumsassun idanunsa. "Yau bazan kwanta kan gadon nan ba". Da dan mamaki take kallonsa,kafin takai ga tambayarsa dalili sai musaddiq yayi knocking. Sabreen ta sauka a nutse tana nufan qofan da dan mamaki,don yanzun sukayi sallama dasu zasu wuce gida. Kanshi yadan rusunar yanajin nauyinta da tsoron kada hamman ya fatattakoshi. "Maamah keson magana da hamma" Ya fada yana miqa mata wayarsa. Bin wayar tayi da kallo kafin ta matsa tana baiwa musaddiq hanya. Dubanta yayi saita daga masa kai alamun ya shige,a sanyaye yake takawa ciki itama tabi bayansa da nufin gama gyara gadon ta fita ta bashi waje don ya samu amsa wayar sosai. Wani yawu musaddiq ya hadiye yana duban hamman nasa daya tsareshi da ido. "Maamah ce tace lallai na kawo......" Hannu ya daga masa yana amsar wayar,sai ya miqa masa yana fita daga dakin a gaggauce yana jin bazai iya jiran ma ya gama amsa wayar ba ya karba sa hadu gobe,don haka kai tsaye ya wuce inda cab ke jiransa. Handsfree ya sanya wayar,ya kuma ajiyeta a gabansa kawai yana zuba mata idanu,irin yadda yakeyi idan ranshi yana bace kuma baya da buqatar amsa wani kiran amma tilas ta sakashi amsawa. "Ina kyautata zaton kana jina?,ko yanzun ma 'yar mulkin taka ce ta daga kiran?" Tayi maganar da wata irin hasala da fusata. "Muhammad fu'ad jadda ne" Ya amsa mata da wani irin nutsuwa yana zubawa sabreen ido wadda ka ta ke duqe tana gyara bedsheet din gadon da pillow case din. "Naji dadin jin hakan......umarni ne daga uwa zuwa shashan danta wanda baisan inda yake masa ciwo ba.........ka kama dukiyar mahaifin yarinyar dake mutuwar sonka ka garqame.....ka masa sanadin aikinsa duka saboda kana hannuwan mutanen da suke riqe da ragamar rayuwarka......sai abinda suka ce.....ni mariya dana dauki cikinka daga gudan jini har zuwa tsoka.....harka zama mutum.....saboda lalurar rayuwa ta nesantani daku shikenan yanzun nice wulaqantatta a wajenka......to indai nice mahaifiyarka ina baka umarni cikin qasa da awa daya komai na ambassador khaled ya koma kan aiki daidai". "Tom" Kawai yace da ita yana sanya dukkanin wani qarfi na qwanjinsa dana ruhinsa yana danne zuciyarsa. Wasu irin abubuwa ke taso masa......yana rantsuwa da ubangijin ka'aba......banda da gaske ya ratsa jikin maamah ya bullo zuwa cikin duniyar da yake rayuwa a yanzu a cikinta......babu wani halitta kaf duniya daya isa yayi masa quarter quarter abinda tayi masa a yanzun. Hannunsa yake mutstsukawa yatsunsa suna wani irin qara,yana jin wadannan mutanen guda biyu sun fara kai masa ko ina a rayuwarsa. Kunnuwanta ne taji ba zasu iya dauke maganan maamah din ba,saita saki gyaran gadon ta soma nufar qofa tana takawa a gaggauce. "Sabreen.....dawo" Ya fadi kansa tsaye ba tare daya damu maamah zata iya ji ba. "Ina magana da kai kana kiramin sunan wannan yarinyar?,annamimiyar karu....." Ya riga ya shanshano abinda take da muradin fada,sai kawai ya sanya hannunsa da wani irin zafi ya datse kiran yana kashe wayar gaba daya. Da gaske wani irin abu sabreen keji,wani yanayi taji yana tsarga mata,ba zata iya zama ba da gaske,ba zata iya jura ba.....don haka ta sake takawa zata fita,sai kawai ya sanya hannunsa me ciwon dake nade ya fusgota sai gata ta fado zuwa jikinsa yasa hannuwansa duka biyun ya lullubeta cikin qirjinsa kaman ya manta ko baisan ciwon dake hannunsa ba ko kuma wani sassauqan rauni ne da bashi da radadi ko zafi ko kadan. A zafafe yake kiran wata number,tsoronsa a karon farko ya kamata ganin yadda numfashinsa yake fita da sauri,zuciyarsa na wani irin bugawa. "Haka fushinsa yake?" Ta tambayi kanta da kanta,daidai sanda kiran ya shiga aka daga. Ko muryar dake wancan bangaren bata jiba ya soma sauke musu umarni. "Inaso a daren yau basai gobe ba.....fareeda khaleed mustapha ta kwana a a cell......ba ita kadai ba,da duk wanda ya kawo wargi ko yunqurin hana fita da ita" Abinda yace kawai kenan yayi wurgi da wayar. Matseta yayi so sai a jikinsa,yana daga idanunsa da suka kada suka sauya launi yana zubesu cikin nata...... _tofa.....ran 'yan maza ya baci.....an manta da ciwon da ake jinya......ko sabreen zatayi aikinta?🫣,zamu gani_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 133 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 133 Sasai taji wani abu yana ratsa jinin jikinta game dashi......wani narkakken tausayinsa yana taso mata yana kuma mamaye ilahirin jikinta. Ta yarda dari har bisa dari cewa......da uwa irin maamah gwara ka rayu cikin maraici......da uwa irin maamah gwara ka zamana cikin layin yaran nan da ko dumin iyayensu basuji ba ubangiji ya karbi rayukansu......ta sake yarda da cewa.....komai ubangiji ya tsarawa bawa tabbas akwai manufa da alkhairi a ciki. "Ya zakayi haka?" Ta fada tana sake saka idonta cikin nasa sosai tana kuma riqe da fuskarsa cikin tafukan hannayenta. Kaman wanda yasha wani abu ya maku yake magana "Ya bazanyi haka ba.....ta yaya zanyi wasa da duniyata?.....ta yaya zan bari a taba duniyata?" Numfashi taja me zurfi wanda ya shige jikinta da wani irin mahaukacin sonsa da kowacce safiya yake qaruwa cikin ruhinta,ta sake bude idonta a kansa tana kallonsa. Taga abubuwa da yawa cikin idanunsa......giyar soyayya da qauna.....da kuma wani irin fushi. Ji tayi kaman bata da wani sauran aiki daya rage mata a duniya a yanzun banda ta kwaranyar da wannan fushin da kuma damuwar daga wannan ruhin daya gama macewa a soyayyarta. Ba zato ba kuma tsammani yaji ta hade bakunansu guri guda. Wani irin zazzafan kiss ta soma ajiye masa kafin ta tura harshensa cikin bakinsa ta soma sarrafashi kaman yadda yake mata. Cikin qasa da second biyu kowacce wuta dake jikinsa ta dauke,ya soma kokawar qwato numfashinsa,wanda bata daga masa qafa ba ta fara aike masa da qarin wasu saqonnin da suka birkitashi......suka sakashi ya soma mance wayeshi?,a wacce DUNIYAR yake?,meye matsalarsa a rayuwama gaba daya?. Tayi masa ba zata ta qarshen qarshe......ta kuma tashi kansa da wasu irin zafafan salon da suka saka har ya manta meye ma yakeyi?. Wani irin saqo take aike masa me cike da jan rai......sai taji ya gaza jurewa ya juyeta ya maidata qasa. Nutsuwarta taso maidawa jikinta,ta dafe qirjinsa a sanda yayi mata rumfa tana kallon narkakun idanunsa da suka sauya launi. Dubanta yayi shima yana neman qarin bayani,saita masa nuni da hannusa me ciwo da ya dafesu ya aza masa nauyi kaman ya manta yana da rauni. "Kina tsoron jini ne?" Ya tambayeta ha tare daya kalli inda take nuna masa din ba. Fuska tadan bata daban,ta sani ba'a fiya son yayi wani aiki sosai da hannun ba,saboda a samu ya warke da wuri.....kuma wannan fitinar da yakeso yayin tabbas zata iya maida ciwon danye. "Alright" Ya fadi da hanzari cikin qasa da second daya yana hautsinata ya koma qasan ita kuma ta koma sama ta maye gurbinsa. "You're in charge now" Ya fadi yana dage mata girarsa. Wani kunya ya kamata,ta cusa fuskarta cikin ni'imtaccen qirjinsa da bata gajiya da wanzuwa akai. "I give my self to you....i surrender to your will....play your role well" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi. Duk yadda yake buri hakane ya kasance,duk yadda yake da buqata haka tayi masa. Abun ya gigitashi ya sanyashi fita a hayyacinsa,wasu maganganun daya dinga yi sai sukayi mata mugun nauyi,har ta dinga jin daga wannan ranar kaman ba zata iya sake hada ido dashi ba. Wani sabon amarcin aka balle a asibitin tsakanin fu'ad da sabreen din,ba tare da kowa ya kula da lalurar da yake tare da shi ba. Hankalinta ya tashi bayan komai ya lafa da taga bandages din hannunshi sunyi staining da jini. "Ka gani ko?,dama bana gaya maka ba?" Ta fada a narke muryarta tana rawa tana shirin sakin kuka. Hannun nasa ya kalla ya saki murmushi yana jawota jikinsa sosai,duk qoqarin sauka da takeyi daga jikin nasa amma ya hanata. "Please stay with me.....i could use some relaxation time......sai muyi wanka" "Ciwonka fa?" Ta tambaya a mamakance tana kallon fuskarsa da tuni ya maida idanunsa ya lumshe yana fidda wani sassanyan murmushi. "Forget about.....zasu gyara zuwa safe" Ta sake motsawa zatayi magana ya dora yatsansa akan labbansa. "Shshshsh" Yace da ita,dole ta maida kanta ta kwantar,saidai hankalinta gaba daya yana kan ciwon. Bayan sun idar da sallar asuba,tana kammala azkar dinta ta koma toilet don yin fitsari saiga jini. Ta razana sosai ta ware dukka idanunta tana duban jinin. Jikinta ta dauki rawa gaba daya,bata da wani qwarin daga murya ta kirashi,tana ma ganin kaman bata lokaci ne,sai kawai ta fito a toilet din da wani irin sauri. Kansa ya daga yana kallonta sanda ta fito din,sai shima ya ware idonsa yana dubanta kafin ya miqe da sauri ganin yanayinta. Sosai ya riqeta yana tambayarta "What's happening?.....relax.....gayamin" Pant dinta kawai ta daga masa,sai ya zare idanunsa waje kaman zasu fado. "Oh shit......subhanallah" Ya fadi yana jin gaba daya ya gama firgicewa. Cikin kula da takatsantsan ya maidata gadonsa ya kwantar da ita. "Lemme call a doctor" Ya fada yana fita a dakin da sauri don yana ganin tsaiwa kiransa ta landline ma bata lokaci ne. Su biyu suka shigo,shi da wata likitan mace daban,yanata masa magana akan hannunsa amma bata wannan yake ba. "Scan zamu fara yi mata don tabbatar da lafiyar babies din" Likitan ta fada tana qarasawa gaban gadon sabreen din. Maida dubansa likitan yayi a kansa. "Hannunka ya akayi yayi staining haka?" Ya tambayi fu'ad din wanda hankalinsa duka yake kan sabreen wadda dr din ta fara jawo na'urar scan wanda take a dakin permanently. Kafin yace komai anyi knocking qofar an turo an kuma shigo. Farouq ne shida musaddiq dauke da breakfast da anni ke dafa musu. Likitanne ya amsa sallaman,farouq ya qaraso dakin fuskarsa dauke da alamun tambayar abinda yake faruwa. "Lafiya dude?" Farouq ya tambayi fu'ad yana qarasawa kusa dashi. Bai amsa masa ba,ya taka ya matsa gaban inda su sabreen suke ya jawo curtain divider ya rufesu daidai sanda yaji tana tambayar sabreen din "Kinyi wani aiki me nauyi ne sosai?" Amsa mata tayi da a'ah....still ta sake tambaya. "Ko kunyi mu'amala?". Shuru tayi tana jin kunya na dawainiya da ita,fu'ad da hankalinsa ke wajen ya sauke hannayensa daya goya a qirjinsa yana fadin. "Kiyi checking baby din kawai madam" "Okay sir" Ta amsa masa a ladabce. Daidai lokacin wani ma'aikacin jinya ya qaraso yana tura medication cart dake dauke da bandages da sauran kayan dressing. "Your hand sir" Dr din ya sake fadi yana duban fu'ad tare da masa nuni da abun zama. Sai daya waiwaya zai zauna din suka hada idanu da farouq,kai ya dauke yana hade rai,sai shima farouq din ya basar yana girgiza kai. Ana mata scan din likitan yana ware wancan bandage din a hankali,farouq yana daga zaune a gabanshi yana danne dariyarsa. Ya wani maze sai cin magani yakeyi?,karon farko da ya fuskanci fu'ad din baya son kallonshi. Koda ba'ayi bayanin komai ba farouq din ya fahimci aika aika akayi a dakin a daren jiya,saidai fatarsa daya babies dinsu ya zaman lafiya suke. "Wow......unbelievable" Muryar likitan ta fita da wani irin sound da yaja hankalinsu su duka. Kasa jurewa fu'ad din yayi,ya dagawa likitan hannu. "Wait..." Sai kawai ya miqe yana danne sauran bandage din da ba'a gama cirewa ba. Kai tsaye ya kutsa tsakanin curtains din ya shiga. "Triplets ne sir" Likitan ta sake fada da wani kwantaccen murmushi saman fuskarta. Idanu kawai ya zurawa na'aurar qirjinsa na harbawa,wani bahagon farinciki yana son bugar dashi. Zooming na scan din tayi,sai gashi ya nuna wasu gurabe guda uku. "Gasu a nan sir......congratulations" Ta fada tana sakin dariya cikin nishadi. "Alhamdulillah.......alhamdulillah" Farouq da yakeji kaman yayi tsuntsuwa ya shigo a nuna masa shima ya fada yana murza hannayensa bakinsa ya gaza rufuwa. Idanunsa ya lumshe sannna ya budesu,yana so yaji mafarki yakeyi ko kuma idanunsa biyu. "Subhanallahi wabu hamdih.....subhanallahilazeem,Alhamdulillah......alhamdulillah hamdan kaseeran dayyiban mubarakan fihi....." Ya fada yana yin qasa da kansa yana jin wani abu yana taso masa. Wanne abu zaiyiwa Allah ubangiji da zai da dadawa Allah?,wanne abu zai yiwa Allah mafi soyuwa a wajen ubangiji.....duk da ya ambaci wadancan kalmomin,masu sauqi a harshe.....masu nauyi a mizani.......masoya a wajen Allah(subhanallahi wa bi hamdih,subhanallahil azeem,kada ki wasa da yawan maimaitasu,kalmomi ne masoya a wajen Allah,wato wadanda Allah yake sonsu qwarai,ga nauyi a mizani,zasu qarawa ayyukanki nauyi ranar qiyama,ranar da ake auna ayyuka akan ma'auni). "Thanks.....thank you so much" Ya fada yana isa inda sabreen din take. Hannunsa ya dora saman kanta yana ranqwafawa a samanta,sai a sannan ya dauke idonsa daga kan screen din yan jin kamar zaiga yaran be baro baro a ciki. Idanunsu suka hadu waje daya,saita fara sakar masa murmushi. Kai yake jijjigawa kawai ya kasa magana,sai ta miqa masa hannunta shima kai tsaye ya bata nashi,ya sunkuya yana sumbatar mararta. "You're my world sabbrrrr.......da nace ke DUNIYATA ce da gaske ke din duniyata ce.......ya rabbb......ka tsaremin wannan baiwar taka da irin tsaronka ita da duk abinda take dauke dashi......yadda mahaifanta suka haifamin alkhairin rayuwata......ubangiji ka shimfida musu aljannarka cikin qaburburansu........" "Allah ya hada da abba daya zama nagartaccen uban daya nunawa yaransa muhimmancin mace" Ta tari numfashinsa tana jin zuciyarta na karyewa da irin addu'arsa akan mahaifanta wanda bata taba jin irinta ba. Wata kyakkyawar runguma yayi mata wadda ta sanya likitan ficewa daga cikin labulen ta basu guri. Wannan karon ba fu'ad kadai ba.....hatta da sabreen saida fuskarta ta jiqe da hawayen farinciki. Ya fita jarumta a wannan karon,don shi ya soma janye jikinsa yana goge mata fuskar. "Kada ki tashi hankalin babies dinmu......ya isa.....is okay ko?" Ya fada bayan ya gama goge mata fuskar ya sunkunya ya sumbaceta a goshi. "Sir......zaa qarasa duba ciwon?" Likitan yace dashi,sai ya miqawa sabreen daya hannun nasa ya dagata ta zauna ya yaye labulen bayan ya tabbatar ko ina a jikinta a rufe yake. Hugging nasa farouq yayi wanda ya kasa zama saboda farinciki,fu'ad ya dan bubbuga bayansa yana murmushi "Congratulations dude....." Kai tsaye ya taya farouq din murna,don ya sani suna raye ko basa raye,zai amsa sunan mahaifinsu ne kawai wanda yayi cikinsu,amma sunan uba farouq keda wannan matsayin. "Thank you dude.....na gode" Farouq ya fadi murmushi yana qin barin fuskarsa. Likitan yana duba ciwon daya doctor din tana sake yiwa sabreen bayani. "Duka fetuses din suna lafiya qalau,ki zauna sosai ki huta yau gaba daya,zai tsaya nan bada jimawa ba....sai prenatal medication dinki da zaki ci gaba da sha da kula dasu.....ina miki fatan haihuwa sassauqa da lafiyayyun Yara". "Na gode" Sabreen din ta fada tana murmushi. A yau din jinta take wata ta daban,jinta take ta musamman,yau ita sabreen itace a mazaunin uwa?,wadda zata kawo wasu rayukan cikin duniya?,wasu halittun da suka kasance jininta?,jinin muhammad fuad dukka a cakude a jikinsu?. Duk bayan minti daya sai ya daga kai ya kalleta,daga qarshe parlor suka koma don Dr din ya qarasa dubashi,sai yake jinsa ba tsaro,gani yake kaman yana kalle masa ita. "Amazing....haka kake da quick healing?" Likitan ya tambaya da mamaki yana murmushi sannan ya dora. "Nayi mamakin ganin saurin warkewar ciwon,kadanne ya rage banda an bashi pressure me yawa ba da bazai fidda jini ba.....za'a maida sabon bandage amma dan kadan.....please next time kada a matseshi da yawa hakan zai bashi daman warkewa da wuri". " Ai basai ka fada bama likita,ni nan zanwa tufkar hanci" Farouq ya fada yana bubbuda hanci. Harara fu'ad ya watsa masa,sannan ya maida harshensa zuwa hausa. "Kada kiyi gigin cewa zaka kai qarata wajen anni....muddin ka rabani da duniyata saina maida maka naka hannun agogon baya" Ya fada sounding seriously. Dariya farouq ya tuntsure da ita,baisan ya akayi ya dagoshi haka da wuri ba "Ko bankai qararka wajen anni ba nasan nayi dakai ai" Ya amsa masa yana miqe qafafunsa nishadance yana duba saqon fannarshi daya shigo masa. Sai da likitan ya kammala komai ya fice sannan ya kalli farouq. "Bani abinci malam.....haka ake jinyar?" Ya fada yana hararasa. "Zan baka mana....kai banda ka fanshi kanki jiya zaka sake ganin face din angon fanna ne?" Yadda yayi maganar ya sanya murmushi subucewa fuskar fu'ad,yakau da kansa kawai yana murmushi. Ya zuba masa komai amma sai yaga yayi gefe da wani babban mug. "Wancan meye a ciki". Da hannu farouq ya nuna masa. "Wannan?,maca and ginseng tea ne". "Zubashi a nan" Ya fada yana nuna masa wani glass mug. Nesa farouq ya qarayi dashi. "Kai ina......kaida wannan ai ba yanzu ba wallahi......kana wannan barnar xan barka kaci gaba da shan wannan?,kayi haquri ku haifemin yarana lafiya....to daga nan har china kuje saikun dawo". Idanunsa ya janye kawai bai ko musawa farouq ba ya dauki mug din daya zuba masa normal black tea ya fara kurba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 135 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 135 So take ta zama kaman kowacce mace.....wadda ke dauke da responsibility na mijinta,kula da duk wani welfare nashi da al'amuran da suka shafeshi,bawai ta barshi shi yayita hidima haka da ita ba,don haka koda suka qarasa bedroom din towel ta ajiye masa sannan ta zarce toilet din. Water heater ta kunna wanda in minutes ta kashe kanta da kanta alamun ruwan ya tafasa,saita kunna tap din duka guda biyu na famfunan,ta cika masa bathtub da ruwan me dumi sosai sannan ta saisaitashi ta health faucet saboda kama ruwa da sauransu. Ta kammala tana waiwayowa da nufin fita tace ta gama sai ji tayi an sake sama da ita an tsumbulata cikin ruwan sannan ya biyo bayanta. "Bansan sai yaushe zakiyi nauyi ba....kosai kin fara turtsi bulli irin na masu ciki?" Ya fada yana qanqameta cikin ruwan. "Me yasa da bakya hadamin ruwa me dadi haka?" Ya sake fada yana sake matso da ita yana shanshana sumarta data fara jiqewa. Bare baki tayi ta soma masa kukan shagwaba,akan meye zai jiqata bayan ba yanzu zatayi wanka ba. Dariya ya dinga mata kafin daga bisani ya fuskanci kukan ya koma na gaske ya lalace wajen lallashinta. Mintuna arbain kafin su fito,tayi daurin qirji da towel tanata goge kanta daya jiqe. Curling iron din data dauko ya karbe,ya soma tsaga gashin yana nade mata shi da style din da takeso. "Hamma.....ana jiranka fa" "Tare zamu sauka sabrrrr,bazan sauka na barki ba" Karbe curling iron din tayi ta ajiye "Mu shirya na rakaka kaci abinci ka fita.....kace kana da hidiman bikin BB naka.....yaushe ka gama ganawa da mutane ka maida hankalinka akai?". Hancinta ya lakace mata. "Yes maaa.....da alama ina da personal assistant me hazaqa,anya bazan sallami saddiq ba?" Murmushi ta saki tana cewa. "Ba ruwana,kada yace nasa an koreshi". Sai data tabbatar ya qoshi sannan ta taka masa har inda yake ganin baqin da suka zama dole,baqinsa na jikinsa sosai wanda ita kanta batasan da wajen ba sai a sannan. Zata juya kenan daya daga cikin guard dinsa suka qaraso. "Malam ne yazo" "Har sai an nema masa izini?,kace masa ya shigo qasan rumfar can" Ya fadi yana juyawa yana fasa shiga sitting room din. Hannunta ya kama. "Muje ku gaisa da malam.....mutumin kirki wanda ta silarsa ne na samu ilimin addini". Bata musa masa ba suka taka zuwa farfajiyar da aka qawata da kujerun zama. Tun daga nesa ta gane malam dinta,mutumin kirki na gasken gaske wanda kusan zata iya cewa tafi fu'ad sanin hakan. Mamaki sosai malam yayi sanda yake zama saman dayan kujerun dake wajen. Ta zame tana gaidashi kaman yadda fu'ad yayi. "Ashe da gaske rumaisa take?,sanda take gayamin ke kike auren muhammadu ba dauka shirmenta ne kawai.....muhammadu kayi sa'ar mata da gasken gaske" Malam ya fada yana maida dubansa ga fu'ad. Sabreen fu'ad din ya kalla sannan ya maida dubansa ga malam. "Tana da tausayi da taimako......tana da yawan sadaka da kuma kyauta,bata wata batayi sadaka ga mabuqata ba......marainiya ce muhammadu......nasan halinka kai dinma.....muna da kyakkyawan zaton nagarta daga gareka......ka riqeta hannu bibbiyu,lada biyu gareka,ladan riqon maraya,ga kuma ladan kula da iyali". "In sha Allah malam" Ya fada yana sadda kansa qasa. Inama ace malam yazo a sanda yake tsaka da fara cusgunawa rayuwarta?,inama ace malam yazo a sannan ya ceceshi daga feeling guilty da yakeyi a duk sanda ya tuna yadda ya mu'amalanceta a baya?. Duk da cewa ba laifinsa bane.......yayi dukkanin binciken da zai yi a matsayinsa na dan adam.....kuma abinda ya samu kenan. Da gaske ga a inda kudaden da duk take diba sukafi tafiya kenan fiye da jikin 'yan uwanta,sai yakejin wannan din dama ce ta sake samun wasu labaran a kanta ta wajen malam din. Hira kadan tayi da malam tana tambayarsa inna ta bada saqon gaisuwa ga rumaisa da shaida mata sun dawo sannan ta koma ciki. Da kanta ta shirya abun motsa baki ta kawowa malam din,duk da ma'u tace ta barshi amma tace sam malam yafi gaban haka. Qarfe tara tayi shirin bacci,don tunda ya fita ba sake jin motsinsa ba,ta tabbatar zai wahala idan ba baqin bane suka sha masa kai. Ta dawo parlor din farko da nufin daukan madarar shanu ma'u na fitowa a kitchen da alama ta gama komai na yau sai gobe kenan. Tana mata sallama amma idanunta akan kwalin hannun mau,tsirfa da tsarabe tsarabe irin na musu ciki haka kawai taji yawunta ya tsinke. "Amma fa ma'u meye wannan?" Kallon farin box din tayi tayi murmushi. "Wallahi amna ce ta aikomin dashi,wani doughnuts ne da ta taba ban guda daya ta yafi dani,sai tace zata sake sakawa a kawomin". "Mu gani" Sabreen ta fada tana matsowa,bude mata ma'u tayi take yawun bakinta ya qarasa tsinkewa gaba daya. "Don Allah ma'u ko guda daya ne" Ta fada tana narke fuska idonta akan doughnuts din da aka yiwa wankan madara. Dariya ta qwacewa ma'un,tasan halin ciki yafi gaban haka,bataga abinda zata samu ta hana sabreen din ba,bare wannan da nan da nan idan sunason wani za'a sake kawowa. "Jeki da kwalin gaba daya" Ta fadi tana tura mata kwalin. Har wani dan tsallen murna tayi,ta amshe tana godiya ta haura saman dashi. Gudu gudu ta gama shiryawa,ta ware gashinta saman bayanta ta haye sofa tana bude kwalin. Lashe baki tayi tana jin kaman ya mata nisa ta tsaya bude ledar a daidai kawai saita farke. "Uhmmmnnnnn" Ta fadi saboda yadda wata lafiyayyar madara ta hade da doughnuts din a bakinta "Ya salammmm" Ta sake fada sanda tayi gutsira ta uku,kawai saita kasa daurewa ta juya bayan kwalin ta kuwa dace da sunan mamallakiyar abun. *_Maman ummies delight_*+234 803 049 9555 A fili ta karanta komai tana lumshe ido,saita rasa wanne zata fara kira a tsakaninsu?. Landline kawai ta nufa ta soma kiran amna. "Addarmu" "Ba wani addarmu......yanzu amna harki samo abun arziqi irin haka amma ki kasa tunawa dani?". Tsam amna tayi tanaso ta tuna meye,ita ta dauka ma complain zatayi akan sun sauka bata nemeta ba " Adda mene?" "Doughnuts mana.....doughnuts din maman ummi". Dariya sosai ta zowa amna,duk yadda taso tareta kuwa sai data fito,karon farko data fara yarda masu cikin ajinsu da zasuga sun fiya fi'ili da neman fitina da gaske sukeyi bawai iya shege bane,yadda ta fadi doughnuts din maman ummin tar a bakinta saika rantse ta santa farin sani,kaman ba yaune cin farko ba. "To adda mu fara da bismillah mana.....dama anni ta gayamin triplets ne,suna sauka albishir din data fara yimin kenan da alama da abun take kwana tana tashi.....Allah ya bawa hamma juriya,ni dama guduwa zanyi na barku". Baki sabreen ta kama "Iyeeee,au gayamin kike aure zakiyi kenan" Kunya ta kama amna kaman sabreen tana gurin. "Ni na isa adda...." "Yanzu mu ajiye wannan maganar.....ina za'a samu doughnuts dinnan?,na kusa cinye wannan" Ido amna ta zaro. "Tana kaduna fa?,amma saga kaduna zuwa kano kawo doughnuts dinta kaman kina garinsu ne,sharp sharp ne.....idan ta kama sai asa hamma ya tashi jet a karbo miki" Dariya sosai maganan ta bawa sabreen,saidai da gaske dadin doughnuts din har cikin tsokokinta take jinsa. "Seriously amna.....am addicted to it......zan samu nayi breakfast dashi?" "Lemme call her......zaki samu koda wajen 10 ne haka in sha Allah.....ko duba flight din safe sai ayi idan akwai a sako miki.....amma indai shi zaki koma ci hamma yana kwale kwale" Amna ta fada tana qyaqyata dariya tayi kuma saurin katse kiran. "Kada fa haka ta kasance" Ta fada tana raba ido bayan ta lamushe taji bata gamsu ba. Ledar tabi ta tande madarar tasss ta saka kwalin a gaba har tana fatan inama tana sauran wani a ciki?. Bata ankara ba bacci yazo yayi awon gaba da ita sassaucin da aka samu kenan. Qarfe sha daya saura ya qaraso cikin parlor din,idanunsa a kanta,wani soyayyarta yakeji tana sake ratsa dukka qasusuwansa. Bayanan da ya sake ji daga bakin malam sai yakejin kamar ta cancanci sama da soyayyar da yake nuna mata.....kamar ta cancanci sama sa wannan rayuwar da takeyi a yanzu. Sai daya kammala komai a hankali don kada ya tasheta,ya dawo ya zauna da wayoyinsa. Su anni farouq da musaddiq duka yakeson kira,yanason komai ya kammala da wuri,don kwanaki hudu ne kadai suka rage daurin auren. Sai sannan idonsa ya sauka kan kwalin,ya jawo ya dudduba yana mamakin yadda aka yiwa ledar tasss,yadan girgiza kai ya kwashe ya zuba dustbin sannan ya dawo ya zauna yana sake duban fuskarta. Wani kyau take qarayi masa kullum,hakanan ba qaramin kyau bacci yakeyi mata ba,murmushi ya subucewa labbansa ya fara kiran farouq. Kira daya ya daga kaman yana kusa da wayar,muryarsa can qasa yayiwa fu'ad sallama. "Are you okay?" Fu'ad ya tambaya tana tsayawa cak. "Am okay dude" "Ma sha Allah.....ka karba envelope" "Na karba" "Ka bude?" "Na bude dude.....but I'm.....I'm speechless dude.......rubutun jikin invitation card dina da ruwan gold na ainihi?" Murmushi ya subucewa fu'ad. "Kafi qarfin wannan dude......kada ka sake magana akai.....akwai sadakin fannah a daga envelope din....have you seen it?" "What?,dowry fa kake magana dude?......wannan gold din ya ninka abinda suke karba a matsayin sadaki......babanta malami ne,kada yaga mun zura da yawa fa". "Fannah tafi qarfin haka a gurinmu....tunda takeson wannan tsohon tuzurun namu,ta kuma amince zata zauna mana dashi da zuciya daya.....sadakin mace baya yawa a musulunce,ko nawa aka bata yayi,saidai ma yayi kadan,yadda kace babanta malami ne nasan yasan da hakan,sayyadina umar yaso qayyadewa a zamaninsa,wata mata ta tunasar dashi annabi baiyi hakan ba, sai ya qyale shima.... Ka fahimta?" "Ya ilahi dude.....am speechless seriously" "Zamuyi fada dakai......ina fata ka riqe data din....kwana hudu......saura kwana hudu dude dina ya angwance" Sautin murmushinsa ya riski fu'ad,hakan kuma ya masa dadi a haka sukayi sallama. A duniya bayajin yana da wani abu da zai iya sakawa farouq dashi koda meye yayi masa. Musaddiq ya kira wannan karon,shima dai kaman yana kusa da wayar ya daga. Muryarsa da mugun sanyi ya amsa sallamar,still shima tambayarsa yayi lafiya yake?. "I'm fine hamma" "Maamah ko?" Shuru musaddiq yayi yana mamakin yadda ya gano haka ta farat daya. Shurunsa ya bawa fu'ad tabbaci,ya sauke numfashi. "Idan ka dorama kanka daukan damuwoyinta ba inda zakaje a rayuwa,zakayita zamane kamar a inda ta tafi ta barka ba tare da damuwan yadda rayuwa zata kasance maka ba.....na kiraka na gaya maka,kayi magana da musaddiq kai dashi ku duba gidajen nan dana bashi details dinsu ku zaba,za'a hade bikinka sana farouq in sha Allah,so ka ajiye damuwan da bata cancanci damuwarka ba.....ka fuskanci rayuwa da reality dinka.....but kada ka sake ka manta da wannan......ka riqe mana amna sai mutuwa ce zata raba". Mutuwar daya fada ta saukar masa da wani irin matsanancin faduwar gaba......ta kuma tuna masa da maganarsu ta dazu da maamah. "Mutuwa hamma?". "Yes.....mutuwa,saboda ita kadaice ta isa ta raba Soyayyar masoya" Shuru ne ya wanzu tsakaninsa da shi,har sai da fu'ad din yace. "Kana layi?" "Inaji hamma" "Good......komai da amna zata buqata ka rubuta ka turamin.....bance ko sisinka ka saka a bikinka ba" Baima jira ya masa godiya ba ya katse,saboda baya buqatarta,yanajin wani wajibinsa ne ya saukeshi. Anni ce ta qarshe daya kira,amna na kusa da ita ta miqa mata wayar. Ban gajiya suka yiwa junansu,sannan itama ya buqaci ta bada duk wani abu da take buqata. "Muhammadu kabar 'yan uwanka suyi wani abun mana?" Murmushi yayi "Anni sai idan bana raye.....ki fadawa amna ta rubuta komai da take buqata na lefe.....idanma ba zata iya ba tazo nan gidan su hadu ita da duniyat....." Saurin katsewa yayi bai qarasa ba,kunya ta kamashi ya aza hannunsa aka yana sosa sumarsa. Murmushi me sauti ya qwacewa anni "Ita da duniyarka ameenatu" Murmushi shima ya saki. "Su rubuta komai,bance ta dauke masa komai ba". Kaman sauran bai jira ta masa wata godiya ba ya katse wayar,ya zubawa sabreen ido wani abu yana yawo cikin ranshi. Da alama baccin ya mata dadi sosai,amma dole ya tasheta don akwai magana me muhimmanci da zasuyi da bata buqatar takai safiya,yana ganin kaman tayi nisa. Wayar anni ta ajjiye gefanta,tana jin wani abu yana sauka a ranta. Tabbas fu'ad din wani kyautar Allah ne a garesu,bawai don dukiyar da yake da ita ba.....aah....ta jima da sanin haka tun yana fu'ad dinsa dan makaranta secondary school,fu'ad dan bautar qasa. Wata irin zuciya ce shimfide a qirjinsa,wani irin dattako daya girmi shekarunsa......wani irin halin girma me dumbin yawa. "Tabbas mariya inda kinsan irin kyauta da alkhairin da Allah yayi miki a rayuwa da baki gudu kin bar muhammad ba.....da baki gudu kinbar musaddiq ba". A tattare dasu gaba daya tana ganin wata irin nagarta ta musamman. "Hammanki yace ki rubuta ko kije gurin addarki ki.masa list na kayan lefe duka" Anni ta fada tana nazarin amna data fahimci ta yawaita shuru shuru tun daga yammacin yau din. "Lefe ann?" Amna ta tambaya da wata sassanyar murya "Wani abun daban kikaji na fada?" Anni ta fada tana nazarinta. Kai amna ta girgiza,haka kawai taji hawaye sun cika idanunta,sai anni ta kasa jurewa. "Meya kuma?" "Tsoro nakeji anni......gabana yanata faduwa" Sai hawayen da take maqalewa ya gangaro mata. "Tsoro?" Anni ta maimaita,kai amna ta gyada mata. Yankewa gaban anni yayi ya fadi,ta sauke numfashi tana ambaton sunan Allah. "Tashi kije kiyi alawala,ki karanta hasbunallahu wa ni'imal wakil qafa dubu kafin ki kwanta". Kai amna ta gyada sannan ta miqe a sabule tana fita a dakin zuwa nata. "Addanmu" Fu'ad dake tsugune gaban sabreen da bacci yaketa danneta ya fada yana leqa fuskarta. Da qyar ta sake bude idon nata a karo na uku. "Adda sabreen.....tashi don Allah" A cikin baccin taketa mamakin kiranta da adda din da yaketa yi,saita miqe tana daquna fuska. "Hamma.....bacci" "Zakiyi,na miki alqawari,amma kafin sannan jeki wanki fuskarki ki dawo". A daddafe ta miqe saboda nauyin bacci,ta lalubi toilet din ta shige. Ba jimawa ta fito,fuskarta tayi fresh da digo digon ruwa,idanunta sun dan tashi kadan alamun bacci,ta zauna saman sofa tana dubansa. Ajiye abinda yakeyi yayi ya taso,ya iso gabanta ya tsugunna a hankali. Hannuwansa yakai ya kamo tafukan hannayenta a tausashe. "Adda sabreen" Ya maimaita fadi yana murmushi. Idanu tadan ware tana dubansa wani malalacin murmushi yana qwace mata. Kai ya jinjina mata. "Kin bamu daman neman auren sister huda?.....kin bamu izini mu nemawa musaddiq auren sister huda?". *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 136 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 136 Wani saukar ba zata zancen yayi mata,wani irin zuwa ya yiwa kunnuwanta. "Saddiq kuma?,saddiq dai hamma?" Ta fadi da sautin muryar bacci da har yanzu bata gama warwarewa ba,banda ta zuba ruwa saman fuskarta da sai tace cikin jerin gwanon mafarki kawai wannan maganar take dibanta. Murmushi ya saki me sanyi yana jinjina mata kai. "Eh......saddiq dinmu addanmu......inaso ya zama mijin huda nan da kwana hudu,kaman yadda farouq zai zama mijin fannah in sha Allah" A hankali ta daga ido tana sake duban fu'ad din,sai takeji kaman wasa yake mata da hankali kawai ko tsokana,saidai kuma ko daya bataga wannan a cikin idanunsa ba. "Hamma.....huda fa?.....ka manta mudin ba kowa bane hamma.... Mu din ba wasu madaukaka bane,ni din kawai a cikin family dinku ya isa,basai huda ta shigo ba...." "Shshshsh" Ya fada yana dora yatsantsa akan lips dinsa. Bayason wannan karayar da take nunawa,bayason wannan raunin da yadda har yanzu ta kasa jinta kaman kowa.....bayason yadda ta kasa daina tuna wacece ita a baya "Damu daku dukkaninmu abu daya ne yayimu.....jirgi daya ne ya kwaso mu.....ki manta akwai wani lokaci da abinci da sutura suke gagarar muhammad fu'ad?....ki manta akwai wani lokaci daya shude da yunwa take saka musaddiq kwana yana kukan yunwa?,kin manta wani lokaci daya shude fu'ad dan jari bola ne?......kin manta sanda saddiq ke kwana da yunwa saboda ba gatan uwa a gefansa?,duka damu daku ki gayamin meye banbanci a ciki?" Shuru tayi tana tuna komai kaman yadda yake tunasar da ita yanzu. "Hamma.....amma huda batayi qanqanta ba?.....yanzu zata gama secondary school fa......a haka an sanyata a makaranta da wuri kaman yadda abbanmu yake mana....." Murmushi ya saki yana dan jan kumatunta. "Qanqanta?.....ke din kanki duka duka shekara nawa kika bata?,banajin yakai biyar,ba gashi muna zaune ba?". "Hamma karatunta fa?" Hannu ya sanya yana dungure mata kai da sauri "Lallai dai sai an ja mana aji kafin a bamu auren sister huda.....lallai ko yaya wai sai an wajiga mu?.....me huda zatayi da karatu duniyata?,ba huda ba.....ko wanda ke rayuwa qarqashin inuwar jadda banajin zai buqaci karatu saboda ainihin buqata ta lalura.....saidai duk me sha'awa yayi karatun don dai sunansa ilimi.....ba abinda huda zatayi da takardu.....saidai.idan har tanason karatu saddiq bazai hanata ba.....za'a dauko mata duk kalar malamin da takeso ya koyar da ita matakin ilimi daga na college har zuwa university har PhD ma.......idan kuma makaranta takeso......ta zabi duk makarantar da takeso a fadin duniya cikin jerin qasashe da muke dasu a duniya 195 zuwa 200....kowacce take so zataje in sha Allah......sai me kuma......a shirye muke mu karba duka qorafinki" Ya qarasa fada yana tsareta da ido tare da jiran abinda zata sake fadi. A hankali ta jinjina kai "Na amince hamma.....na bada izini bisa sharadi da alqawarin zai bata dukkan wata kulawa data dace koda bayan raina". Wani zazzaro idanu wajen fu'ad yayi yana dubanta. "Kul.....karki sake zancan bayan ranki my world......waye ya gaya miki fu'ad yana da sauran rayuwa bayan babu taki?". Idonta ta maida ta lumshe a hankali tana murmushi. " Zamu rayu tar in sha Allah......zamu kula da yaranmu mu kuma basu tarbiyya tare" Ya fada yana sumbatar hannunta a tausashe. "Na gode sosai duniyata.....na gode sosai da sadaukarmana da daya daga cikin abubuwan da kike matuqar so a duniya.....kika yarda ta zama abokiyar rayuwar saddiq" "Kafi qarfin komai a wajena duniyata.....kafi gaban haka muffin". Ta fada itama harshenta da sautinta cike da qauna da soyayya. " Bayan gidan malam......sai ina da ina kike kai taimako?" Ya sake soko Mata tambayar da bata taba kawota ba. Fararen idanunta ta daga ta kalleshi,sai kuma ta sauke idanun nata qasa tana jin nauyinsa. Batason abinda zai sanya ya dauko mata wannan zancan na abinda ya wuce a tsakaninsu. "Ki bani dama.....inaso ki dore da aikin ladan da kikayi niyya in a halal ways.......inaso na miqar dake kici gaba da abinda kika fara a baya". Sake kallonsa tayi a karo na biyu......tana jin yana sake shiga rayuwarta yadda ya kamata. Soyayyarsa tana sake hudata,wani mafarki ne wannan nata,dasu take kwana dasu take tashi.....hayewar su huda kawai bai sanya zuciyarta ta kwanta d'ari bisa dari ba.....bai sanya zuciyarta ta samu nutsuwar da take yunwar samu ba. A yanzun a kuma wannan lokacin sai gashi ya gama qarasa karanta tunaninta kafffff yana son xike mata ragowar gibin da ya rage. "Me yasa a kowacce rana kake sake karantar zuciyata?,me yasa a kowacce rana kake abubuwan da suke sake haukatani a kanka muffin?". Idonsa ya lumshe yana budesu duka a lokaci guda. Yanason irin wannan yanayin.....yana son irin wannan lokacin da zaiyi zaune kawai a gabanta yana tana tona masa asirin zuciyarta. "Sabrrrrr" Ya sake kiranta a tausashe. "Haqqina ne.....kuma cikar kamalar kowanne d'a namiji kenan,ya karanci wace matarsa.....me tafi so?,me tafi buqata?,me zaiyi ya mallaketa?". Mallakar daya fada ta sakata fashewa da dariya tana zaro ido. " Hamma.....mallakata kakeso kayi?" "Nama mallakeki duniyata.....na mallakeki....kedin tawa ce ni kadai har abada" Ya fada yana daga yatsunsa guda biyu. "Gidan marayu.....gidan gajiyayyu.....yaran da iyayensu suka mutu suka barsu kuma babu me tallafa musu irinmu" Takai qarshen maganar muryarta tana karyewa. "Ki zauna ki tsara dukkanin burinki akan wadannan gidajen". Ya fadi yana miqewa tsaye. Wani irin sanyi taji yana sauka saman zuciyarta "Ina fata ubangiji ya lullubeka da dukka rahamarsa......ya yaye maka damuwarka.....ya kyautata qarshenka.....na gode da karamcinka karimin mijina.....na gode da wannan halin dattako naka uban 'ya'yana". Murmushi me sanyi ya kubce masa,yanajin alfahari da wannan addu'ar tata. "Allahumma ameen matata 'yar aljanna.....amma saura abu daya da baki roqamin ba". Idanunta ta juya,abinda ya sake tafiya sosai dashi " Me kenan muffin?" "Baki roqi Allah ya qarawa wannan ameenatun so na ba.....so nake ameenatu ta soni fiye da yadda takeson kanta,don kuwa ta samu wanda zai kula mata da kan nata" . Kunya ta sakata sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kafin tace. "Inda ana iya bude zuciya ko qirji a nunawa wani.....tabbas da na bude maka tawa zuciyar kaga abinda yake ciki a kanka,wataqila zakafi gasgatani.....don maganar fatar baki tayi kadan" Rasa me zaya ce mata yayi,sai kawai ya tsugunna yana kissinh forehead dinta a tausashi. Yana dauke labbansa tana daga idanunta da sauri,sai ta soma rarraba idanun nata tana a narke. "Kai.......ina doughnuts dina?" . Dubanta yayi "Wanne doughnut?". Ya tambaya yana tunanin ko mafarki tayi a dazun kafin ya tashera. Tambayar tata da yayi sai taji kaman zata saki kuka "Doughnuts dina mana da ma'u ta bani......a nan fa na ajjiye naci kadan na ajiye sauran". Qaramin murmushi yayi. "Kin cinye madam....ni na tattara kwalin na zuba a dustbin". Idanu ta waro waje tana dubansa sosai da salon rigima a muryarta. "Ka sakamin a shara?,wallahi ban cinye abuna ba,akwai saura" Ta fadi tana miqewa zumbur gami da nufar dutsbin din. Da mamaki yake binta da kallo ganin yadda ta bude dustbin din tana ciro kwalayen. "Kai?,ka cinyemin?" Ta fada cikin sanyin jiki hawaye yana taruwa cikin oily eyes dinta. Dariya ma abun ya bashi,ya daga hannunsa alamun surrender yana dubanta. "Innalillahi,Allah ba ruwana,sanda nazo ba komai a ciki sai boxes din da leda". Dariyar tasa ta qular da ita,sai kawai ta fashe da kuka tana sakin boxes din. "Wallahi kaine.....kaine ka cinyemin kuma bazan yarda ba" Mamaki sosai ya kamashi ganin yadda ta zube tana kuka bilhaqqi,hawaye shabe shabe ta dage wai shine ya cinye mata. Da sauri ya isa inda take yana miqa mata hannu. "Yi haquri ki tashi.....eh na yarda nine na ci". Ya fadi hakan don ya lura qaryata ba shine yaci din bama qular da ita yakeyi. "Dama kai dinne ko?" Ta fada tana watsa masa harara da jiqaqqun idanunta,sai ta sake fashewa da kuka sosai kaman wadda aka yiwa dukan tsiya harda shashsheqa. Ya rude sosai don ta maida abun serious matter. Ya sulale ya tsugunna a gabanta yana cewa. "Am really sorry my world......taso muje ki gayamin a inda aka siyo a sake nemo wani". Sai data galla masa harara sannan tace. "Kaduna.....kaduna ne wajen maman ummi". "Kaduna?" Ya maimaita. "Eh" Ta fada cikin son jiran mutum yayi wani abun ta sake barke masa. Kansa ya daga ya kalli agogo yana duba lokaci. Qarfe goma na dare,wa zaya tasa zuwa kaduna yanzu. Idonsa ya mayar kanta,saiya taras ta zuba masa ido tana kallonsa,dukkan alamu kuma sun nuna rigima ce a kwance idan ya musa. "Is alright.....bani details na masu abun". "0803 049 9555,wallahi tunda ummee ta haifeni ban taba cin doughnuts me dadin nata ba" Ta fada bilhaqqi da gaske har zuciyarta tana jin tun kafin ya kawl ma yawunta ya tsinke. Idanu warwaje yake kallonta. Tashin hankali!,ya fadi saboda yadda yaga tsaf ta haddace number,yaushe hakan ta faru oho shima bai sani ba. "Ina zuwa" Yace mata yana takawa a hankali yana sauka qasan. Shi kam yasam yanzu ba lallai a bawa jadda wings daman tashi ba,kafin ma su nemo umarni,pilot din ya isa su tashi ai asuba yayi,saidai duk da haka bai fasa kiran number din ba. Ainihin sunan daya fito ameena sai yaji kimar me number ya qaru a idonsa tun ba'a daga kiran ba. Bugu na uku aka dauka da cikakkiyar sallama ya amsa shima. "Am sorry,na kira late at night......i don't know ko matar aurece.....am sorry idan hakanne" "Ba komai" Matar me kirki ta fada. Bayanin dalilin kiran yayi sannan ya dora. "If possible goben zan aiko a taho dake,kizo kiyi mata sai a maidaki.....kiyi naming price dinki,kada ki damu ko nawa ne ki zaba i will pay it". Murmushi tayi. "Ba matsala.....ko goben da safen ma ana iya samun ko pieces nawa takeso.....akai akai sai a dinga zuwa ana karba mata,Allah ya raba lafiya,kowanne ciki da yadda yake zuwa ma mace,sai haquri". Yaji dadin magananta sosai,don daga yanayinta ya fahimci ba yarinya qarama bace,yayi godiya sannan ya kashe ya kira farouq. Bugu daya ya samu farouq,da alama bacci ya fara daukansa ma. "Farouq akwai matsala fa" Maganan da ta saka farouq miqewa ya zauna "Me ya faru?" Ya tambaya. Ajiyar zuciya ya saki ya masa bayani a nutse. "I don't know ina zan samu doughnuts?.....kune masu zuwa irin guraren nan". "Ba damuwa......bari na duba wani guri kusa damu......sun iya sosai zataji dadinsa". "Thank you dude.....you save me" Ya fada yana dan dafe goshinsa sannan suka yanke kiran. Lallabata ya dinga yi har aka gaya masa ga saqo daga bakin gate. Sanda yaje har farouq din ya aje saqon ya juya,ya yaba masa sosai irin saurin da yayi don duka duka mintuna talatin ya iso,ya tabbatar wannan gudun nasa ya zuba. "Ga doughnuts din" Ya fada da murmushi yana aje box din a gabanta. Da zumudi ta jawo ledar ta bude. Tun a yanayin packaging din ta tabbatar akwai matsala,banbamce babance take gani iri iri da wancan,ta danne tana bude doughnuts din. Kanta ta daga ta kalleshi,ya dage mata gira yana qoqarin lallabata,can qasan ransa yana fatan kada ta ballo rigima kuma. Kanta ta mayar kai,ta gutsira tana kaiwa bakinta. Taunawa daya biyu ta furzar,muryarta tana rawa ta kalleshi "Wannan bashi bane.....Allah bashi bane". " I know sabrrrr.........kiyi haquri kici wannan din,i promise you da safe wancan din zakici as breakfast" "Really?" Ta tambaya tana tsareshi da idanu. "In sha Allah" Ya fada yana bata assurance. Hankalinta taji ya kwanta,amma duk da haka ta ture wancan din "Banasonshi....nata yafi dadi yafi madara" Dariyarsa ya boye,yana mamaki ashe da gaske masu juna biyu suna haka?,idan madara takeso suna da ita kala kala har sai ta ture,amma ya tabbatar yace tasha din ba sha zatayi ba. ★Tun sanda amna tabar dakin sai taji ta gaza nutsuwa sam sam,hankalinta ya kasa kwanciya,itama sai ta samu kanta da rashin nutsuwa da kokwanto. Toilet ta wuce,ta daura alwala,ta dawo ta shimfida abun sallah. Raka hudu tayi ta zauna ta fara karanta hasbunallahu wani'imal wakil qafa dubu. Ko kadan batajin bacci a idanunta,haka kuma batasan meye ya dauke baccin a idanunta ba. Bayan ta gama ta sake gyara tasbaharta. Bismillah hirrahamanir rahim 450 ta karanta,sannan tayi salati 450 shima. Bayan ta gama ta karanta (Allazina qala lahumunnasu innan nasa qad jama'u lakum fakshauhum fa zadahum imanan wa qalu hasbunallahu wani'imal wakil zuwa fanqalabu bini'imatimminallahi qafa 45(ko 450 idan zaka iya),ta sake karanta salati 450,sannan ya azizu ya khafi ya qawiyyu ya ladifu 450,duk inda takai guda 100 saita tsaya ta jaddada roqonta ga Allah,neman tsari daga dukkanin wani mummunan abu ko abun qi da zai iya samunta ko ya samu wani cikin ahalinta,ta sake zurfafa addu'ar samun albarka da sanya albarka a dukkanin wadannan aurarraki da akayi dama wadanda suka wuce.(addu'a ce me kyau da tsananin tasiri wajen samun biyan buqata wajen Allah,in kin zama me riqe addu'a da barwa Allah lamuranki kin huta da gasken gaske,shi zai miki komai daidai da yadda ya dace dake,sadaka ce na baku sai a sanyani a addu'a,ubangiji ya bamu dacewa). Shafa addu'ar tayi tana jin wata nutsuwa tana saukar mata,ta miqe a nutse ta shirya don wucewa gurin abba. Sai data gama shirin sannan ta zauna saman stool,ta debo ruwa a wani babban mug ta soma karanta ayatulkursiyyu qafa ashirin da daya ta fita da mug din a hannunta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 137 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 138 Zuwa takwas da rabi na dare ya shigo gida. Tun kafin ya shiga din ya sallami kowa,don ragowar lokacinsa yana jin cewa na duniyarsa ne. Yau din sai take jinta a cikakkiyar matar aure kaman kowacce d'iya mace. Ta shirya sosai tayi kwalliya da wani farin tattausan lace,fari ne qal babu sirkin komai a jikinsa. Ya kwanta mata sosai a fatarta,ba makeup a fuskarta,daga powder data dace da skin dinta,sai wheat lips da ya sanya pink lips dinta suke wani glowing me daukar hankali. Sau daya tak ya kalleta yaji tana son raba masa hankali,sai yake ganin kamar canzata akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,kaman yadda yaji qamshin gidan gaba daya ya sauya. Qugunta ya kamo,ya kasa cewa komai sai daya sada lips dinsa da nata,ya tsotse lips gloss din da kyau kaman bata taba shafa komai akai ba da wani zazzafan French kiss. Bakinsa ya zare yana sauke numfashi,idanunshi akan fuskarta,yana jin yadda fatarta dama kayam jikinta suke fidda wani daddadan qamshin turaren kabbasa. Idan baiyi kuskure ba har gashinta data harshi baje saman kafadarta qamshin yake fiddawa. "Those sweet lips sabrrrr....." Ya fada yana zagaye yatsansa akan shape na lips din nata,yana jin wani shauqi yana fusgarsa. Murmushi ta saki tana dan kauda kanta tanason ta karbi wayoyin hannunsa da wata 'yar kyakkyawar briefcase dinsa. Hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta da sauri. "Nooo......my lips missed yours sabrrrr......" Ya fadi yana sake hade bakinsu guri daya. Wani yanayi ya fara saukar musu shi da ita,har qafafunta suka fara rawa ta fara jin ba zasu iya ci gaba da daukarta. Shi dinma hakanne,don gaba daya jikinsa ya dauki shock har sai da suka zube saman sofa sannan ya zare bakin nasa. "Your lips are the ones.....i want to kiss forever" Ya qarasa fada yana tura hancinsa wuyanta qamshinta yana bugar dashi. "Sabrrrr.....so kike ki haukatani da alama ko?" Ya furta yana Dubanta da juyayyun qwayar idanunsa kaman wanda yasha wani abu. Fiddo idanu waje tayi tana dubansa,hakan sai ya qara mata bala'in kyau saboda yadda sukayi wani haske,eye lashes din kuma suka zame musu tamkar wani ado. "Muffin.....me kuma nayi?.....idan na kasheka kuma na zauna da wa?" Tayi maganar ne cikin wata irin shagwaba. Hancinta yaja kafin ya lakuce mata kumatu. "Fisabillahi zan fadi gaskiyata.....wannan qamshin lallai idan kina tare dashi zanfi tape da taya maqale miki......komai kuma zai iya faruwa ako ina sabrrrrr.......daga ina wannan qamshin?" Ya fada yana kashe mata ido. Murmushi ne ya subuce mata sosai,harga Allah da farko ta dauki turaren ne kawai saboda amna tace ta dauka,cikin irin turarukan da akayi musu ita da huda wanda.ta bakinsa tasan huda sun iso,saidai tana sakawa a burners dake lungu da saqo na gidan ta gama giving up. Lumshe idonta tayi wani farinciki yana saukar mata,ta bude idanun nata ta saukesu akan kwalbar LAB_LAB da tayi amfani dashi,wanda daga saman kwalbar manyan rubutu ne b'aro b'aro dake dauke da sunan INCENSE BY KABO DAUGHTER. (Kunsan ni ma'abociyar son qamshi ce😄,na muku tallan turarukan matar nan TASTED AND TRUSTED ne,duk irin turaren da kike siya ina baki shawara ki gwada nata,yayi yayi yayi,zaki kuma bawa wani labari,muddin kina da dama amma baki siya ba ina me tabbatar miki kin loser😂😂,confirmed🙌🏽🙌🏽,ba kuma bala'in tsada gareta ba.....sai sirrin sanin kan turaren,nima dai 'yar gidan malam shehu ce bare ace na manya muke using ahto😂😂,ki gwada hajjaju zaki godemin,don tabbas idan me tsoron Allah ce ke kikayi kabbasarta kika saka humra ko lab lab dinta ba zaki iya fita unguwa ba saboda fitinannen qamshi suke bayarwa,ki gwada ki godemin +234 803 211 9803). "Saboda kai ne muffin......saboda kai ne". Idonsa ya lumshe yana sake zuqar qamshin,har cikin zuciyarsa yake sauka,wani nutsuwa qamshin yake bashi,kamar wadda aka tsoma a bahon turare. "Kiyimin rai please sabrrr" Ya fadi yana sake cusa kanta tsakanin dukiyar fulaninta. "Name?" Ta tambaya tana murmushi. "Don Allah kada ki bari wani yaji wannan qamshin idan bani ba". Ya qarasa maganar yana dago kansa gami da sanya idanunsa cikin nata don ta gane har ranshi,da gaske kuma yake maganar. Tafukan hannayenta dasu kansu qamshin suke ta saka tana dago kansa sosai. Zuwa yanzun tuni ta fara fahimtar yanayinsa....da yayi magana ko baiyi ba....idan yayin daga ina ta fito?. "Muffin.....kana tunanin zanbar wani hanci ko wani d'a namijin daban bakai ba ya samu wannan nutsatsen qamshin?.....har abada idan kace bakaso ko farfajiyar gidan nan qamshin nan ya fita bazai fita ba......a yanzun hatta da rai ka bani DUNIYATA......Ka bani rai tunda ka kusanto da makusantana kusa dani......dame ne zan saka maka ni ameenatu?" Ta qarashe maganar zuciyarta tana karyewa da wani irin rauni. Idanunshi cikin nata ya dora hannunsa saman mararta. "Kin gama sakamin ameenatu.....kin gama sakamin sabreena.....kin gamamin sakayya duniyata da kika bani iri.....yara uku fa?,lokaci guda?,a qaramin lokaci har haka?,kika cikamin muradin zuciyata?......abu daya ne ya rage kiyimin,karki guje ni tsanani ko dadi.....karki bari tarbiyyar yarana ta zama abun Allah wadai......ki soni irin son da ba wanda zaki bawa katankwacinsa.....that's all" Ya fada yana dage hannuwansa sama. Hannunta ta saka daga qeyarsa sannan ta hade goshinsu guri daya suna musayar numfashi. "Ka samu muffin.....ka gama samunsu.....amma zan qara da addu'a ga Abba......mutumin da yayi sanadin haifamin irin wannan mijin.....ubangiji ya jiqa kabarinsa ya kuma lullube kabarin nasa da dukkanin wani nau'i na rahamarsa" "Allahumma ameen" Ya fadi muryarsa qasan maqoshi yana sake jin ta masa kima sosai. "Abinci ko wanka?" Ta tambayeshi ba tare data dauke goshinta a nasa ba still kuma tana zaune saman cinyarsa. "Cin abinci sannan kazo kayi wanka yana raunana jiki my world" Idanu ta fitar tana dubansa bayan ta janye fuskarta. "Muffin.......da gaske komai naka dabanne,tsarukanka dabanne kaman yadda naji ana gulmarka......kasan duk wani abu da zai kiyaye lafiyarka" "Wait" Yace yana hade ransa da wasa. "Wake gulmata?,farouq ko?" Dariya sosai ta kubce mata har tana sake riqeshi don kada ta fadi. "Komai farouq?,komai farouq?.....BB ya kusa hutawa dai,nasan fannarshi zata siya masa 'yanci". Murmushi shima yayi yana kama hannunta suka miqe,shi kansa baisan ya wannan ranar zata kasance ba.....kowa ma ya shiga uku. Tsaf ya janyeta suka shiga wanka kaman yadda rules dinshi yake,har ya fara zame mata jiki,ya gaya mata sunna ce kuma bazai gaji da rayata ba,don duk wanda yayi koyi da wani abu cikin abinda manzan Allah yakeyi da zummar koyin yake dashi,to tabbas yana da ladan koyi dashi. Cikin wasu sauqaqan couples pyjamas suka shirya dukkanin farare da adon black wuya da hannu da qafan wandon da bai qarasa idon sahu ba. Kamar wasu ma'auratan daga wata qasar,suka sauka qasa tare. Bayan kammala cin abincin basu kwanta ba,dukka maganganu ne da shirye shiryen biki yaketa fama. Itadai tana gefe tana kallon zallar aikin zumunci irin ma fu'ad din,ta sake tabbatarwa bawai a banza Allah yaa sanya wannan dukiyar a hannunsa ba(Tabbas idan har Allah ya baka wadata fiye da sauran abokai ko 'yan uwanka,to ya baka ne don ka taimakesu,wala'alla duka harda arziqinsu ya saka a hannunsu don ka zama.silar ciresu daga matsi ko matsala,Allah yana sonka da yayi maka wannan baiwar,don zaka samu lada sanda kake basu ita ta hanyar data dace,don ka zama kamar wakilin Allah a bayan qasa,idan kuwa ka riqe ka hanasu yana kallonka.....tabbas! Kuma sai yayi hukunci akai, 'yan uwa dukiyarka kenan fa.....inaga wanda zai danne haqqin wani?,ina ga wanda zai cinye dukiya ko gumin wani?,Allah yasa mu dace,ya rabamu da taba abinda ba namu ba ya hayyu ya qayyumu). Ganin ta langabe masa zata yi bacci ya katse maganan da yakeyi da kowa ya dubeta. "Gate up ameenatu.....naga list na amna.....ke banga naki ba" Ido ta zaro,cikin muryar soma jin bacci tace "Muffin.......nawa name?" "Naki lefan.....naki lefen sabrrrr" Ya fada yana kama hannunta. "Banda wanda akayimin hamma?" Ta tambaya tana dan dariya saboda ta dauka zolaya ne. Kai ya girgiza. "A yanzun ke din cikakkiyar zabin MUHAMMAD FU'AD JADDA ce,sabon lefe sabon sadaki daga hannun jadda" Ya fada yana zame hannunsa a nata. Qasa ya saka hannunsa ya fiddo wata kyakkyawar leda ya zube kayan ciki. Kyawawan akwatuna ne har guda shida masu daukan hankali,iya akwatun kawai abun kallo ne,ba zaka gane kuma kallo ya koma sama ba sai daya bude abun ciki. Wasu irin sabbin designs ne na gold masu matuqar daukan hankali. Uku gold ne uku kuma diamond,wanda ta gane haka ne ta qaramar takardar dake maqale a ciki. Uku ya ware a ciki ya tura gabanta,ya bude wani jaka qarama dake gefan system dinsa ya ciro sabbin rafas na dubu d'aya d'aya na dollars a miqe kar dasu ya dora a sama. "Wannan shine sabon sadakin ameenatu muhammad jadda.....idan tana buqatar sama da haka tayi magana......wannan kuma" Sai ya tura sauran boxes din "Wannan kuma ladan rainon cikin da za'a yimin....duk da nasan ban isa na biyasu ba.....duk boxes daya a madadin yaro daya yake.....shima idan baiyi ba kiyi naming price dinki". Kaf jinin jikinta taji ya daskare na wucin gadi,uwar dukiyar daya zube mata kawai take.kallo tana jin zuciyarta tana raurawa,sarqoqi shida masu qololuwar darajar da batasan ya zata kimanta kudinsu ba?,ga tsabar kudi daya kusa naira million dari da sittin?. Tsoro ne kawai taji yana shirin kamata,tsoron ta yaya diyar ahmadu kamarta zata mallaki dukiya dare daya irin wannan?. Tana shirin zamewa tayi kneeling a gabansa ya dagota. "Kul karkimin godiya....karki qorafi,kinfi qarfin komai da zan baki,don kema kin bani abinda ban isa ni kadai na bawa kaina ba......kin soni da zuciya daya,kin tsallake duk wani gwaji da nayi miki da zummar gano dukiyar kikeso ko bata gabanki,a yanzu ba abinda bazan iya sadaukar miki ba...bare wannan da ba komai bane cikin abinda Allah ya mallakamin ba.....so komai na dauka na baki kin cancanceshi ne,addu'arki da soyayyarki kadai su nafi buqata a halin yanzu a rayuwata,Allah ya yimin komai". Qasa tayi da kanta tana jin hawaye yana sauka a idanunta,sai ya buge da tsokanarta har sai daya rakata daki,ya tabbatar ta kwanta ya lullubeta da duvet ya tofeta da addu'a. Sai daya tabbatar bacci ya soma cin qarfinta sannan ya dawo falon ya zauna yaci gaba da aikinsa. ★Sake juya rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan gold tana bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne zube a jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo anata yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah maisharif babaghana . Sake buda katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a yi komai,shima abu qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a hada da zaman ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba za'ayi ta'adin dukiya ba qarya ne. "Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da ameenatu?" Ta furta ta daga kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya jinjina mata "Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje tana ajiye katin. "Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita gidanta.....sai washegari da ameenatu zata gudanar musu da walima haka ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci. Wannan karon qaramar dariya ta saki. "Hakan nima yayimin.....amma kuma dan jahannama.......bazan iya jiran washegarin ba......inaso ranar juma'ar ta zama rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso ranar ta juye musu daga farinciki zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar tonon sililin baqincikinsu". Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi. "Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai zame musu abun lissafi da irga har qarshen kafuwar zuri'ar" "Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake wuyanta. Sarqa me tsananin kyau tsada da daraja. "A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka ne......bayan kudaden da zaku cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace masa bayan ya karbi sarqar,ko a hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar kudade ne masu nauyi akan sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin dadin yadda zai rabauta da riba biyu. _uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye zaiyi farinciki waye kuma zai shiga sasarin baqinciki?_ _Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana dab da fitowa fili_🥹 *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 139 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 139 *_WEDDING VIBES_* *_KANO & MAIDUGURI_* Idan aka ambaci umar farouq kibiya,wani mutum ne me wasu irin halaye nagartattu,iya mu'amala da mutane da kuma Tarin abokai,duk da kusan kowanne aboki da zai shigo rayuwarsa yana qoqarin tantance cancantar wanzuwarka a rayuwarsa. Bikin ya karade kafofin sadarwa masu yawa,ya kuma shiga jerin sahun bukunkunan da kowa yayi amanna zai bada wani irin salo me qayatarwa,duk da ba wani abu me yawa aka tsara za'ayi ba. Tun lahadi ya yiwa maiduguri tsinke ta jirgin jadda wings,yayin da ya saukewa fuad saboda yanayin hannunsa. Su ahsan da sauran abokansu sune suka zame masa groomsmen. Duka komai dasa hannun fuad aka kammalashi da wani irin dattako da nuna tsantsar 'yan uwantaka,sunyi fuad din zai taho ranar zaman ajo sai kuma da farouq ya sanya ya masa alqawarin zaije har gurin,saboda yasan halinsa,tun asali dama shi bameson ire iren wadannan abubuwan bane. ★A nutse suke takowa zuwa farfajiyan da motocin da zasu masa rakiya zuwa airport daga can su zarce Maiduguri. Hannunsa sarqafe cikin nata,kwana biyu din da zaiyi sai yake jin kamar wanda zaiyi shekara biyu ne. Ita kanta duk sai takejin kamar ta sake masa kuka,kewarsa takeji tun bai tafi ya barta ba,duk da takan ji dama dama idan ta tuna in ya tafin itama zata wuce gidan anni don shirye shiryen biki,wanda idan an dauko fannah an kawota nan din,walima za'ayi gagaruma guda daya da anni ta shirya,zasuyi yini randa za'a sauka da fannah,walimar kuma washegari ce,to amma ita din a yanzun ta zama kamar auntyn amaren gaba daya da angwayen. Tuna su huda na tare da itan yana rage mata wani kadaicin,duk kuwa da cewa ba wanda ya isa ya cike wannan gurbin nasa. Baiko kulaa ko damu da mutane a wajen ba,ya ajiye mata tattausan kiss a goshinta bayan duka sallamar da akayi a ciki. "Saina dawo?,ki kulamin da kanki sosai,if possible ki dawo gida ki kwana,banaso na tuna cewa baki dakinki kinji please" Kai kawai ta iya gyada masa,don idan tace zatayi magana kuka ne zai qwace mata. Har ya fara takawa zuwa motar da Jordan ya bude masa ta jawo yatunsa,ya dawo da baya yana kallonta da narkakkun idanunsa. "Yadai?.....ko na fasa ne?" Kai ta maqale sannan ta girgizashi. "BB ne fa......idan banda BB dinne ba wanda zan bawa aronka....." "Nima banda ina kishin a kallemin ke.....banda ina tattalin 'ya'yana ba abinda zai sanya na tafi na barki" "To amma...." Ta fada tana turo baki ba tare data qarasa magana ba. Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana kallonta,ya mata alama daka akan ta fada. "Banason ka kalli kowacce mace please...." Tayi maganan tana juya masa baya alamun kunyarsa takeji. Qaramar dariya ya qwace masa,yasa hannu.ya juyo da ita yana fadin. "Say it mana.....Louder please!,with all your might" Ya furta yana mata sassauqar runguma ta baya,yadda ta nuna kishin na faranta masa kaman farincikin na neman masa yawa. Kai tsaye ta juyo ganin abun na masa dadi,ta saka idonta cikin nasan tana dubansa. "Your eyes belong to me,don't look at any other women please,na maka alqawari a karan kaina.....my gaze is fixed on you alone,bana ganin kowai sai jadda na" Ta fada tana rungume Hannayensa". Sulalewa yayi sai gashi saman gwiwarsa a gabanta,abinda ya sanyata zaro ido ta fara kallon mutanen dake wajen. Dukka guards nashi sun juya bayansu,ba wani guda daya da yake kallonsu,saima kaman katanga da sukayi musu ta yadda ba wani a farfajiyan gidan da zai ganin ainihin abinda ke faruwa. "Karki damu,My men are extremely competent" Yana kaiwa nan ya kamo yatsuntsa masu kyau da taushi. Kafin yace komai wayarsa ta dauki tsuwwa,yadan yamutsa fuska yana cirota a aljihunsa. CP ahmad nuhu ne,don haka ya daga kai tsaye ya sanya a kunnensa. Cikin ban girma suka gaisa,kafin ya soma gabatar masa da bayanai. "Sir dukkaninsu a yanzu sunyi taushin da kowanne bayanai muke buqatar tatsa daga wajensu zamu sameshi in sha Allah,don yanzu haka bibo da zuwaira ma mun samu dukkanin bayanan da muke da buqata,ban sani ba ko zamu iya aike maka ta email?" "Good job sir.....thank you,basai ka turo ba,don yanzu haka mun fara hidimar bikin dan uwana.....but zuwa Monday dukka zamu zauna dasu,akwai yiwuwar wanda za'a sallama a cikinsu.....thank you sir" "Okay sir.....in sha Allah" Cp din ya fada suna sallama cikin farinciki da mutuntawar yadda dukiyar FU'AD din bata sanya yana musu kallon na qasa dashi ba. Ya basu dukkan wani girmamawa da dama na gudanar da ayyukansu. Kashe wayar yayi duka ya sanya a aljihu don kada wani ya katse masa shauqinsa,sannna ya sake riqo tausasan tafin hannunta da har yanzu yake jiyo wannan sassanyan qamshin na jiya (incense by kabo daughter+234 803 211 9803 Da gaske turarenta kwana yake a jiki,kama gida kuma da wuri yake,khumrorinta dukka na dabanne bare akai ga turarenta). "Ni muhammad FU'AD jadda,an halicci ruhi Zuciyata dama gangar jikina gaba daya saboda ameenatu sabreen........har abada gangar jikina da zuciyata sun haramta ga wata diya mace ba ita ba......mata gaba dayansu wallahi wallahi kallon maza nake musu 'yan uwana,daga kanki an gama haifar wata diya mace har abada,amana daya ce......kuma kin sameta,bana canza magana,bana sauya alqawari" . Tasha jin ana cewa maza basu da magana daya.....ta gani da idanunta yadda maza suke zama wasu ababen tsoro game da mata,amma a yanzun saita samu kanta da amanna da maganganunsa. Tana tsaye har dukka motocinsu suka bar harabar gidan,sai ta juya ta koma a hankali tana jin kaman ita kadai ce ta rage a duniya. Bata dauki lokaci ba itama sai kawai ta shirya,ta yiwa securities din daya bar mata magana suka shirya motoci ta fice zuwa gidan anni. Ta samu amare sunata wani glowing kaman wadanda anni ta dauka ta jefa cikin engine aka sauyo mata da wasu,duk da dama daga amna har huda kyan fata garesu. "Aah,mrs saddiq and musaddiq" Sabreen ta fada cikin salon tsokana. Abun mamaki wai yau ita suke kunya,kowacce sai ta sadda kai,saidai kuma yanayin amna data gani kaman ba yadda ta saba ganinta ba. Duk da akwai surukuta sosai tsakaninta da anni,amma ta dan sake wasu abubuwan da ba zasu zamto zaqewa ba ta shiga anyi da ita. Lefen data gani wajen anni akwati ashirin da hudu na huda ashirin da hudu na amna,guda biyu arba'in da takwas kenan. Daki daban anni ta saka ta shiga tana nuna mata wasu designers akwatunan guda sha biyu samfurin shekara mai zuwa,wanda akayi lunching nasu a dubai cikin satinnan. Ita tsoro ne ma ya kamata da anni take gaya mata wai nata ne,ya ilahi ina zatakai wadannan?,kada ya jawo mata baki fa na jama'a. A daren suna video call take jeranta masa kalaman godiya,kalaman da suka sake kashe masa jiki da zuciyarsa,yaji kaman zai narke saman sofa din da yake kwance akai. "Sabrrrr" Ya kirayeta,wanda kiran kawai ya gaya mata yanayin da yake ciki. "Anya ba gobe zan taho ba?,anya duniyata?". Dariya ta qyalqyale masa dashi tana tsokanarsa. "So kake BB da fannah suce nice na hanaka?,kayi haquri please,awa arba'in da takwas ne kawai". "Allah ka bani juriya" Ya fada yan lumshe ido,yana jin wata kewarta tako ina,tattausan skin dinta me qamshi laushi da santsi. ★Randa FU'AD ya sauka ranar fanna tayi bridal dinta,baije ba farouq ma bai matsa ba tunda yasan bame son zuwan bane. A rana ta biyu ne akayi zaman ajo,wanda a wannan zaman kudi sukayi rana.....dukiya tayi kuka da idanunta,ya nunawa BB dinsa qauna irin wadda ta sanya farouq tara hawaye sosai a Idanunshi. "Karka yadda kayi mana kuka gaban mata da tarin mutane,idan kayi hakan bamu yafe maka ba.....wannan kukan ka riqeshi sai sanda kuka kebe......idan ba haka ba za'a dauka lusari ta aura" Ya fada kadan a kunnen farouq bayan ya gama zazzage pound cikin abinda aka ajiye saboda zuba ajo din,don yana gama zubawa aka dauke abun,ya riga ya cika sai wani aka sanya. Tofa......nan idanu dama hankulan 'yammata dama zaurawa masu lokaci yayo kan FU'AD din,taron mayu bawai na maita ba......mayun mata.....ma'abota son kyakkyawan namiji me abun hannunsa hankulansu ya tashi. Kowacce isassace me aji tana jin takai,don me qaramin class ma baya suka dinga ja suna rufawa kansu asiri,saboda sunsan kalar zaren ba kalar yadin bane......saidai su kansu isassun sai rab'e rab'e,an rasa zaqaqura me qarfin halin tunkarar me jadda din.....kwarjini yanata aikinsa. Mota ya koma yayi zamanshi suns hira da duniyarsa,video call kaman ko yaushe,ta daga masa hannuwanta da sukasha wani irin jan lalle,tun daga tafin hannun har zuwa bayan hannun nata. "Ya salam" Ya fada yana jin wani abu ya harba a jikinsa. "Nawa me qunshin nan takeso a bata?". "Anni ta biya mana ni dasu amna.....beside ma ai ka ban kudin da zai isheni kalar kowacce hidima". "No....kudin dana baki ban bakishi bane don kiwa kanki komai ba,na baki shine don ki wata hidimar daban,zan saka miki a dollar account dinki,saiki cire". "Allah yabarmin kai jadda na.....Allah yajamin da ranka uban 'ya'yana" Ta fada tana jin kanta yana fasuwa,bada komai ba kuma,da zallar kulawa.....da kalar mijin kuma data samu. Sanda suka koma guest in dinsu farouq shine qarshen shigowa,bai kuma tashi shigowa ba sai daya na dare. A sannan FU'AD yana zaune saman abun sallah yana addu'o'insa,wanda duka ta neman dacewa da alkhairai ce duniya da lahira shida 'yan uwansa dama dukkan wani masoyinsu(harda ku fans na DUNIYATA😄🫶🏽). Ido suka hada FU'AD ya janye idanunsa yana hade rai. "Wanne irin abune wannan?,zaka ajiye.mutane kuma ka tafi,baka tashi shigowa ba sai tsakiyan dare kaman wani barawo?" Wani dariya sosai Farooq ya saki yana qoqarin cire babbar rigar jikinsa. "So sorry dude.....kasan abinka dame iyali kuma farin shiga.....inacan ina lallashinta wai yatsunta sun gaji......ga tafiya kano gobe donma flight ne.....". " A gidan ubanwa ta zama iyalin naka?" Ya fada adan fusace,don ya kira sabreen yaso suyi hirar dare bai sameta ba. "Ka rabo mutane da iyalinsu kuma kazo ka ajiyesu?". Ido farouq ya fiddo,yanason fashewa da dariya amma ya danne "Ikon Allah....to ni me zan muku idan nazo din?,qarqari muyi hira fa?,kuma yanzu tsakani da Allah saboda rashin imani wanda keda sabuwar amarya ai abun a masa uzuri ne ko?.....to kuma ma naga wancan lokacin naka daurin auren.....qasarma ka bari kaqi dawowa ka barni da amaryar da abokan gaba daya.....wannan rashin adalci ne dason kai dude". "Farouq....gori zaka yimin?....gate out please ka barni naji da damuwana" Wannan karon duk yadda yaso boye dariyar ya kasa,sai kawai ya saki abarsa yana nufar toilet. "Bani nakar zomon ba.....ratayar ma ba'a bani ba.....iyali me dadi.....ashe haka lamarin yake dama" Ya qarasa fada yana shigewa gami da turo qofar. Qwafa fuad ya saki,sai kuma murmushi ya qwace masa. To meye ma laifin farouq a ciki?,ita kanta sabreen din bata da laifi tunda tace masa zata aje wayarta dama,kawai dai iya shegensa ne ya motsa,da alama kuma ramuwa yakeson yayi masa. *_ALQAWARIN ALLAH baya tashi_* "An daura auren umarul farouq hamza kibiya,da fannah maisharif babaghana......jama'a kun shaida?". Sautin daya sanya fu'ad sakin tattausan murmushi yana furta. "Alhamdulillah......alhamdulillah" *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 140 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 140 Daga nan inda yake yana hangen sadakin fannah dake bada tabbacin ta zama ta farouq dinsa halak malak......hakanan yana iya hango farouq dake tsakiyar abokansa wanda shigarsa bata da maraba data jikin fu'ad din,sak da sak kaman yadda sukayi a bikin fu'ad din. Lafiyayyen walima aka gudanar a gidan gwamnatin jihar borno bayan kammala daurin auren da tarin abokansu masu jini a jika,wanda kowannensu wani ne shi ta fannin ilimi da abun duniya. Ana gamawa fu'ad ya wuce masauki yabar farouq da tarin abokanshi,don shi bazai iyama wannan iya shegen nasu ba,sun sanyashi a gaba sunata abubuwansu daya tabbatar sai yayi trending a social media. Tunda akayi hotuna wajen reception din yayo gaba,don akwai shirin da yakeso yayi. Ruwa ya fara watsawa ya fidda wayarsa,kai tsaye ya kira duniyarsa. Daidai lokacin tana zaune suna kallon reception da daurin auren da ko awa guda ba'ayi da yinsu ba amma har an warwatsa a media. Kishin fu'ad ke taso mata sosai saboda ganin tarin comment din yammata a kansa. Shi kadai amma ya fita daban a cikinsu,komai nasa daban yake,wani irin kwarjini me hade da nutsuwa da suka qarawa fuskarsa kyau da kuma kamala. _"Lallai baaba ma da babansa fa.....duk kyan azurfa bata kai ya gold ba.....the jadda.....guy dinnan daban yake fa🔥❤️‍🔥"_ comment din wata daya gilma kenan daya sanya zuciyar sabreen quntata,ta kuma ture screen din daga fuskarta tana jan wani qaramin tsaki,can qasan ranta kuma tana mita. "Bansan me yake damun 'yammatan yanzu ba,kamar mayunwata suke akan maza.....idan suka saka namiji a gaba baji ba gani?,ba kunya ba aji ba kamun kai?" Daga huda har amna sun fahimci me takewa qunquni,sai suka qunshe dariyarsu saboda zuwa yanzun suma suna jin tasu soyayyar da angwayensu har cikin jininsu. Kayanta take hadawa dama,saboda tanason wucewa gida ne kafin su qaraso,tanaso ta kimtsa ta tarbeshi da kyau,idan yaso gobe sai ta dawo gidan annin. Kiran wayarsa ya sanya ta ajiye duk abinda takeyi,ta kuma daga kiran tana samun wajen zama. "A ina kake?" Tambayar data fara masa kenan wadda ta bashi mamaki. "Na dawo guest house masauki.......me ya faru?" Wata sassanyan ajiyar zuciya ta saki,tana jin dadi daya dawo din,at least ya tsira daga kallace mata shi da wadancan mayunwatan 'yammatan sukeyi. "People are commenting about you everywhere You're all over social media muffin" Ta fada da wata irin narkakkiyar shagwaba. "What?" Ya fadi dariya nason qwace masa. "Like nine angon?" Ya sake tambayarta. "Am serous muffin" Ta sake fadi tana narke masa. "Am all yours......am yours forever my World" Ya fadi da wani irin calmness daya bawa zuciyarta nutsuwa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma gaidashi. "Ya taron?" "Alhmdlh.....but babu dadi coz bakya kusa dani". "Nan da awanni kadan zamu kasance tare in sha Allah" Ta fada tana bashi confidence. "In sha Allah" Shima ya maimaita. Lafiyan yaranshi shine next abinda ya qara tambaya,tayi murmushi tana dora hannunta saman mararta data fara tasawa tana bashi amsa. "They're fine.....suna gaida abbunsu.....sunyi missing nasa" "Me too my world.....akwai kyakkyawar gaisuwa tsakaninmu idan na dawo.....so get ready,be at home as soon as possible" "Yanzun nake shiri in sha Allah" "But.....karkice zaki fita da mota daya....ki jira su abdulgafar zasu kaiki har gida.....and nace su qara yawan security na gidan". Ya fada da serious murya. "I hope komai lafiya ko?" Kai ya jinjina,kawai yana jin wani abu daban a jikinsa. "Lafiya.....in sha Allah" Ya fada yana son tabbatarwa da kansa haka. Cikin nuna tsananin kewa da qaunar juna sukayi sallama shida ita,kai tsaye kuma ya kira abdulgafar. "Zamu qaraso gurin qarfe biyar......get ready please,a qara yawan security a airport da gida na harda gidan anni......har gidan farouq.....if possible inaso kowa cikin ku ya zama ankare da kowanne parts". "As you wish sir" Ya fada cikin girmamawa. "Ku rakata gida safely abdulgafar......bazan iya jurewa ba if something happen". "Bazai faru ba sir in sha Allah" "Good abdulgafar" Ya fada yana yanke kiran. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana dan wani gajeram tunani da shi kansa baisan na meye ba,sake daukan wayarsa yayi ya tura rubutaccen saqo ga duk wani guard da suke tare dashi a halin yanzu haka a maiduguri,sannan ya sauka yana laluben wayar farouq don jin yadda zasu shirya tahowa kano kada lokacin tashinsu ya fita. ★ Daga samanta tana iya hangen yadda duk wani shige da fice yake gudana cikin gidan hamza kibiya. Wani ajiyayyen qullutun baqinciki ne yake tsaye a wuyanta,shi bai fita ba shi bai sauka ba. Idan akace mata a baya nasararta zatazo da irin wannan salon tsaf zata qaryata......a irin wannan yanayin zata iya cewa bikin d'anta akeyi.......amma koshi yaron nata bata samu martabar ganinsa ba bare ta shiga lamarin bikin,balle kuma ta samu girma da daraja irin na kowacce uwa. Agogo ta kalla,tana jin ta matsu ta kuma qagu komai ya faru,tana jin a ranta afkuwar komai din shine zai bawa abinda ya tsaya mata a wuyan damar fadawa. Knocking akayi sannan aka turo qofar dakin. Bata damu ta waiwaya kota tambayi waye ba har zuwa sanda ta fara magana. "Maamah ga abincinki fa,tun na safe bakici ba.....na rana ma haka,ga na dare a hanya,kuma likita yace ki dinga kula da abinci ko don yanayin ciwon...." "Ciwon ubanki?.....nace ciwon ubanki?". Ta fadi tana katse laila da dukka tashin hankalinta ya tattaru ga ganin alamun maamah din tana cikin damuwa,tashin hankalin da takeji tana jin yafi wanda maamah dimma ke ciki. "Maamah kiyi a hankali ki daina fushinnan ko don lafiyark......". "Waini sa'arki ce?,to kiji na gaya miki na rantse da Allah kika qara Dangantani da wani cutar hawan jini saikin gwammace uwarki hajja bata haifoki na......idanma qullawa kukayi don ku cuceni ku kasheni saboda ba idon 'ya'yana ko to?,to kunyi qarya kun kwana da yunwa,ni mariya warki ce daidai qugun kowa.....ni mariya kuma ni kad'aice gayya......fita kiban guri" Ta dakawa laila tsawa tsawar da har saidata zabura. "Allah ya baki haquri" Ta fada ta juya tana fita a dakin kaman zata kifa. Fitar laila sai ya zama kamar ta fita da iskar da take shaqa ne,take taji iska tana mata kadan,wuyanta ya soma riqewa iskar bata samun daman isa ga hunhunta. A daddafe ta samu waje ta zauna tana qara gudun fanka da Ac din dakin,wani irin haki yana sarqeta. Likitan ya gaya mata,kada ta yarda ta fadi muddin irin hakan ya sameta tana a tsaye,idan ba haka ba komai zai iya faruwa. Ta kusa mintuna talatin a haka kafin taji a hankali numfashinta yana daidaita har ya koma normal. Wayarta ta jawo,ta kira number wayar da take sanya ran shigowar kiranta tun dazu. "Baki da damuwa.....muna ankare da kowa da kuma komai.....ki jira jin sakamako daga yanzu zuwa gobe da safe".. "Godiya nake" Ta fadi tana ajiye wayar tana kuma sake jin relief sosai a ranta. Cikin wani irin mugun matakan tsaro jirginsu ya sauka,yayin da baqaqen motocin dake dauke da tambarin JADDA kimanin ashirin sukayi convoy cikin wani irin tsari me daukan hankali da kuma matakan tsaro sosai bisa umarnin fu'ad. Lafiya lau suka qaraso unguwar,suka kuma jera kansu zuwa kyakkyawa kuma makadediyar harabar mansion House din alhj hamza kibiya. Duk wani dake da jibi da ahalin alhj hamza kibiyan yayi tattaki ya fito daga cikin gidan,yayi tsaye a farfajiyar saboda girmamawa ga fannah,wadda aka fito da ita nannade cikin wata lafiyayyar Cotton lafaya butter colour da ratsin maroon. Yana daga cikin motar amma yana iya ganin komai,yabi kowa da ido da yadda abun ke kasancewa,sai yaji wani abu yana taso masa,don haka ya maida idanunsa ya lumshe. Lallai babu wani babban arziqi a duniya irin uwa ta gari......babu wani babban jin dadin rayuwa irin samun uwa ta gari.......alhmdlh yana godiya ga Allah a bisa dukkan ni'imomin da yayi masa,kuma ya karba cewa tasa qaddarar tana kan MAHAIFIYARSA tasa jarrabawar tana kan UWA da Allah ya bashi. Amna dake nade cikin tata lafayar sai wani irin farinciki taji yana lullubeta,tana jin kamar suna dab da gina wani babban ahali ne,yau BB farouq dinta.....ya saddik,ya musaddiq da hammanta dukkaninsu yana da matar aure,wadannan matan kuma kowacce ana sanya ran zata basu baby,babies din da zasu taru su zame musu wata tawaga kuma family na musamman. Kasa jira tayi a qaraso da fannah,saita taka da dan hanzarinta tana cimmata ta riqe hannunta,abinda yasa matar dake riqe da fannah din sakin hannunta taja baya,wannan ya bawa amna daman magana da ita qasa qasa. "Welcome to alhj hamza family,welcome to jadda family adda fannah......bansan ya kuke cewa adda da kanuri ba.....anyway muna miki maraba". "Na gode" Siririyar muryar fannah ta fita wanda ta tabbatar ita daya ta jita. Cikin girma da martaba dangin anni dana abba suka amshi fannah aka qarasa ciki da ita,bayan anyi addu'a an kuma bawa su anni amanarta,sai annin ta sanya aka ware daki daban aka bawa fannah din ta huta suci abinci sannan sai a wuce da ita gidanta,hakanan danginta suma aka basu wani dakin daban. Sai data tabbatar babu kowa a dakin sannan ta yaye lafayar dake kanta. Amna da huda ke dakin,hudar da sam ta kasa sakewa,ta hana kowa ma ya ganta throughout saboda surukuta da takeyi da dangin anni. Musayar murmushi sukayi,amna ta nuna huda. "Wannan itace huda.....qanwar adda sabreen,matar ya saddiq" Lokaci daya huda ta yiwa fannah,ta miqa mata hannu sukayi musabaha. Ita da amna sai take jinsu karon farko kaman qannenta,don ta tabbatar ta girme musu,saidai ba wani da yawa bane. Qaramar walima akayi cikin gidan,baqi sukaci suka qoshi suka huta,sannan anni ta bawa fannah kyauta irinta surukuwa kaman yadda ta yiwa sabreen. *_ME FARUWA!_* Tun bakwai da rabi aka soma shirye shiryen qarasawa da fannah gidanta. Musaddiq da saddiq ne akan komai na game da shirya motocin da za'a dauketa a qarasa da ita ainihin gidanta dake maqociyar unguwarsu. Tunda aka fara jera motocin daga harabar gidan zuwa qofar gidan amna ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana bala'in son zuwa gidan ya farouq,wannan yana daya daga cikin mafarkanta tun kafin tasan rayuwa zata juya lokutan aurensu guri guda,tun kafin ta taba tunanin zata kasance qarqashin igiyar auren yaa musaddiq a wannan lokacin. Yadda kowa ya shirya haka ta shirya,tanason ta tambayi ya musaddiq ko shi ya dauki mota subi ayarin kai amare,a qalla tana tunanin bazai hanata ba,tunda zai wahala idan ta shiga nata gidan ya barta fita da wurwuri,don musaddiq din wani irin tsaro ne dashi tun wancan lokacin ballantana yanzu data zama mallakinsa. Zaune tayi tana gwada wayarsa,sai data kirashi a qalla sau hudu sannan ya daga. "Ya akayi baby doll?" Cikin shagwabar nan tata ta narkar da kai. "Besty.......gidan amarya please,don Allah muje" Idanunsa ya waro waje kaman tana gabansa. "What?.....aah karmu fara haka dake babe.....zakije amma bayan munyi wasu watanni" . Kukan shagwaba ta sakar masa wadda ta qarasa susutashi,da qyar da ban baki ta shawo kansa. "Amma kinsan anni zatayi fada ko?". "Karka gaya mata please,nayi alqawari muna zuwa zamu dawo". Shuru ya danyi,bayan wasu sakanni yace. "Ban miki alqawari ba gaskiya babe... Kema amaryarce kaman kowa,kodon kinga ban tada rigima a kaiki yau ba?" "Am sorry besty....don Allah" "Nace banyi alqawari ba,but ki jirani idan hali ya yiwu zan miki magana saiki fito" A haka suka rabu da musaddiq,duk sai taji ranta ya jagule,tunda taji ya fadi hakan probability na rashin zuwanta yafi na zuwan nata yawa,saita buga tagumi tana zaman jiran tsammani,har sanda aka shigo aka fita da fannah alamun tafiya zasuyi. Kasa zama tayi,ta lafe a farfajiyar gidan tana ganin yadda motocin suke tashi suna ficewa. Ta duba agogo,ta tabbatar tunda har musaddiq yakai wannan lokacin baice ta fito ba to tayi loosing chance dinta,tabbas bazai kaita ba. Hawaye taji ya silmiyo mata,daya daga cikin talalar aure kenan,idan dane anni kawai zata gayawa ta fice abinta. Ko a yanzun ma ji tayi ba zata iya haqura ba,tunda duka motocin gidansu ne zata iya basaja ta bisu,idan an tashi dawowa da dangin amarya ta biyosu ba lallai a gane ta fita harta dawo din,don haka ta silale a hankali tabi ta jikin motar dake fita daga gidan ta saje a jikinta suka fice tare. Sai data fita din tahau raba ido,ba wata mota a wajen duka sun dauki hanya wata nabin wata,caraf idanunta suka sauka kan wata baqa guda daya dake fake a gefe,sauri take kada musaddiq ya cimmata yace ta koma gida,don haka bata lura da number ba irin ta gidansu bane kawai ta doshi motar kai tsaye. Sosai abun ya musu dadi,ya kuma yi musu sauqi na ganin ta kawo kanta da kanta,sai ya bude motar kawai yana jiran isowarta,wanda tana isowar ta bude bakinta da zummar tambaya sai kawai ji tayi luuuu an jata cikin motar an maida qofa an rufe. A gaggauce ta bude idonta tana son gani ko musaddiq ne yake mata wasa?,saidai fuskar data gani din a gabanta ba wata alaqa ta kusa ko ta nesa da imani a tare dashi bare a alaqantashi da sunan musaddiq ma.....kafin kuma ta sake tantance komai,sun badeta da wani abu da ya sanyata atishawa,cikin qasa da second biyu ta daina fahimtar komai. _masu karatu kuyi haquri nayi baqi ne yau din,mu tara gobe in sha Allah......sai ince kowa ya shirya,ranar da kuke jira ce ta tunkaro mu_ Sonso🫶🏽🥰🥰 *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 141 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET........siya ko saidawa,reposting ko sari_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 141 Tsararren gida ne da akayi masa wani irin qawataccen gini mai dauka hankali. Tun daga qofar gidan zuwa cikin gidan dole ya burge me kallo saboda yadda komai yake a tsare da wani irin yanayi me jan hankali. Komai favourite na farouq aka saka,fu'ad yayi masa ba zata kaman yadda shima yayi masa. A hankali ta rufe turaren data gama fesa masa tana dubansa,yayi masifar kyau cikin wani lallausan yadin vicuna da aka yiwa riga da wando da wata 'yar sama me kama da alkyabba. Tsadajjen dinkin hannu da aka shiryashi da zare me daraja. "Kayi kyau muffin" Sabreen ta fada tana lumshe idonta gami da budesu akan fuskarsa. Hannunta ya riqo a tausashe yayi kissing dinta "Soyayyarki ce ta saka my world.....but bakisan kin fini kyau ba?" Ido ta zaro waje kana ta saki dariya tana girgiza kai gami da ja baya "Zolayata kake muffin.....ta yaya haka zai kasance?,kar ka tsaida BB hamma......yau ranarsa ce aje a miqawa sister fannah shi" Murmushi ya subuce masa ya soma zura rufaffun takalmansa tana daga tsaye tana morewa kallon abinta. Sai ya fito fes kaman wani shaihin malami. Har bakin mota ta masa tattaki,bayan ta tabbatar an saka komai a motar daya dace a kaiwa amarya da angon. A yau kadai data sanya order Youghourt da sauran wasu snacks daga wajen deeja beerva aka kawosu tsaf.......sai ta dinga jin sha'awar koyon duka nau'in wadannan abubuwan. Ta duba handle dinta na tiktok da Facebook,ita dai a rayuwarta zata iya cewa batasan mace kamarta ba. Komai ta iya,idan nace komai ina nufin komai da komai din,kama daga kayan gashe gashe,girke girke,kayan mata da na mazan ma da zaki hada da hannunki.....kayan maqulashe,man kitso,man shafawa kai duk wani abu da dan adam zai buqata musamman mace cikin rayuwarta. Hatta fannin gyara mu'amala da zamantakewar auratayya ta hanyar shawarwari. Kai tsaye ta nemeta ta number dinta ta yanke yin register da ita,kafin ta qara nauyi tanason ta zama cikakkiyar mace tako ina,itama ta hada wadannan baiwawwakin.+234 907 927 4454 (Ba sabreen ba,ni kaina magana ta gaskiya na jima banga mutum irinta din ba,akwai qaruwa sosai tattare da ita,in sha Allah bazan gajiya da kawo muku duk wani mutum da zamanku tare dashi zai amfaneku kuda iyalinku ba). Home service takeso sukayi tsada ta gama komai. Tun bata ganta ba kirkinta a iya waya kawai yasa hankalin sabreen sake kwanciya da ita. A nutse ya kashe motar gaban gidan,duk da mai tsaron gate din gidan ya dage qofar tun isowarsu. Ango farouq dake zaune a seat me zaman banza.....sanye da wata danyar dakakkiyar shadda da iya kallo kawai da idanu zai ganar dakai kudin data lashe. "Ya ka tsaya a nan kuma?". Girarsa kawai ya dage masa yana zare key din. "Muje na taka maka kawai.......sabrrrr tana jirana" "Muma dai Allah ya kawomu dadin abun ko?" Farouq ya fada yana bude side dinshi ya fice. Da ido farouq yabi kyakkyawan kwandon da fu'ad ya dauko da kansa. "Da alama wannan aikin adda ne ko?" Farouq din ya fada yana jin wani girma da kimar sabreen suna hauha a ranshi. "Eh.....ai ta rantse sai wannan tsohon tuxurun ya morewa angwancinsa". "Ta fiyemin kai ai hundred percent" Farouq ya fadi yalwataccen murmushi na subuce masa. "Thank god da babu yadda za'ayi dani ai" Fu'ad ya fadi yana yin gaba yana barinsa da wani nannadadden kwali da shima ke cike da tarkacen kayan qwalama. A veranda din farko fu'ad ya cake yana miqa masa kwandon. "Meye haka dude.....ka qaraso ku gaisa mana" "Da wa?" Ya fada yana zaro idonsa waje. "Fannah" Ya amsa masa kai tsaye. "Allah you're mad farouq.........kawai sai in shiga gidan mutane kai tsaye har can ciki?.....kaga forget about it please...........ka shiga da cikakkiyar sallama please.....don't forget to recite addu'an da miji yakewa amaryarsa a daren farko......don't forget to pray two Raka'at........fatan alkhairi ". Wani qaunar dan uwan nasa yaji yana kamashi,sai kawai ya rungume fu'ad din cikin jikinsa yana fadin. " Thank you dude.....thank you,Allah ya cika maka muradinka". "Kukan zakayi tun yanzun?,akwai sauran awanni" Ya fada jin muryarsa kaman ta karye. Dariya farouq ya saki da risunannun idanunsa yana janye jikinsa daga na fu'ad. Hannu fu'ad din ya sanya yadan daddaki kafadarsa,ya zura hannunsa a aljihu ua fiddo wayoyin farouq din. Latsesu dukka yayi ya kashesu sannan ya miqa masa su yana masa magana da ido akan "Ka barsu a kashe,kada ka kunna". Sannan ya juya a nutse yana fita a gidan gami da bawa guards umarnin su kulle ko ina a gidan. Yana takawa zuwa cikin gidan yana jin wani yanayi yana ratsashi. Wani yanayi daba kowanne zai fahimta ba sai wanda yake a matsayi irin nasa. Da cikakkiyar sallama a bakinsa,tare da qarin addu'ar "Allahumma adkhilni mudhkala sidqin,wa akhrijni mukhraja sidqeen,waj'alni minladunka suld'anan naseera,rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzileen" (Addu'ace me kyau ga amare ko angwaye yayin shiga gida,ko idan kunyi sabon gida a sanda zaki shigeshi). Yana yaye curtain din falon duk wani colors da tsari na dream parlor dinsa ya bayyana,lafiyayyen murmushi ya subuce masa. "My dude.......miskili kafi mahaukaci ban haushi" Ya samu kansa da yiwa fu'ad kirari qasan zuciyarsa. Kowanne taku nasa sai yakejin wata rahama da nutsuwa tana saukar masa,wani irin farinciki yana lullube ilahirin zuciyarsa. Qawatattun bedrooms din nasu har guda hudu ya dinga budewa daya bayan daya,sai ana biyar din sannan ya ganta. Nannade cikin laffayar nan da zata baka tabbacin asalin kanuri dince ita,turararren qamshinta daya dumame dakin kuma ya sake gaya maka still KANURI CE. Sallama ya sake jaddadawa,can qasan maqoshi ta amsa,saidai shi yaji abarsa,murmushi ya sake subuce masa,sai kawai ya duqa yana sabule rufaffen takalmin Gaziano & Glirling dake qafarsa,ya rage saura socks kawai wadda ita tayi masa jagoranci har zuwa bakin gadon da take zaune. Hannuwanta dake lullube da kyakkyawan zanen lalle ya kalla,baisan sanda ya ajiye wayarsa da keys dinsa gefe ba,ya miqa hannu yana dora tafin hannunsa saman nata tafukan hannayenta ba ya riqesu sosai. Wata sheshsheqa ya saki gami da nannauyar ajiyar zuciya duka lokaci daya,wanda suka fito tare da kalmar "Alhamdulillah". Karon farko a rayuwarsa da hannunsa ya soma taba na fannah bayan ta zama halalinsa......karon farko da sukayi kusaci da juna har irin haka,duk da yadda yake tsananin sonta,yake kuma shauqinta,itama kuma haka,amma dukkaninsu sun killace hakan,sun kuma boyeshi qasan ransu,ba wanda ya bari dan uwansa ya fuskanci hakan.(qalubale ga matasanmu) "Babarbariya ta" Ya fada a tausashe da wani taushi da baisan yana dashi ba. Wani suna qwaya daya da ba soyayya ba da yake kiranta dashi,yake kuma mata tsananin dadi. "Taimaki wannan dan bawan Allahn a bude masa wannan fuskar mutanen maidugurin ya kalla" Ya fada yana zamewa,sosai ya zauna a gabanta gami da komawa kalar tausayi,ya koma kaman wani dan almajiri,sai yakejin tun yanzun kaman zai fara sakin kukan da fu'ad ke cewa ya riqeshi tukunna. Kafada ta maqale ba tare datace komai ba,sarai ya gani,duk saita rudashi. "Roqo nake badon halina ba" Ya fada yana riqe hannayenta da kyau cikin nasa. Murmushi ya qwace mata,duk da fargabar da take ciki,sai ta zame hannunta daga nashi a hankali ta sanyasu tana janye lafayarta baya ba tare data daga kanta ba. "Kan uba!....subhanallah" Ya fada yana wani wantsalawa cikin wani irin mamaki. Fannah ta shammaceshi,tunda suka fari soyayyarsu har suka qare bazaice ga wani shape nata daya taba gani ba,koda da wasa kuwa,a yanzun saiga wata ajiyayyar kyakkyawar halitta kuma dukka mallakinsa ce?,yayi yadda yakeso?. Hannu ya miqa zai zame lafayar daga kafadarta,yanason ya sake ganinta sosai sai ya janye hannun da sauri yana murmushi,yana jin kaman wani shock ke jansa. "Dan sake budemin please fannah.....i wanted to see you all". Wuyanta ta langabe alamun aah,ai baibi ta kanta ba sai gashi ya dawo gabanta. Hannuwansa duka ya sanya ya dagata,ya miqa hannunsa gefan qugunta inda ta daure lafayar ya wareshi,ya kuma zarce da wareta gaba daya daga jikin nata. Tsaf ya ware kayarsa,sai yakejin wani abu yana ratsa sassan jikinsa. "Subhanallazi lam yattakiz waladan wala saheeba" Ya tsarkake girman zatin Allah a abinda idanuwansa suka gane masa karo na farko(qalubale gareku mata,wata sai ran bikinta ma take fidda shape din gaba daya mazan duniya dana media su tayashi kalla). Ji yayi idan ya qara koda second daya bai sanyata a jikinsa ba kaman zai mutu,sai ya jawota gaba daya cikin jikinsa yana lullubeta da hannuwansa,qamshin jikkunansu suna cakuduwa guri guda. "Alhamdulillah,first halal hug" Ya fadi a bayyane yana sake godewa Allah da yadda ya bashi iko ya tsare mutuncinsa. Sai da yayi da gaske ya zame jikinsa,don ya fahimci wannan al'amarin bame sauqi bane,idanma har za'a biyewa ta zuciya da gangar jiki,tabbas dukka addu'o'innan da musulunci ya koyar da sallolin ba zasu samu ba. "Ki shiga toilet ki daura alwala,ki rage wannan nauyin na jikinki kizo muyi sallah" Ya fada yana tattare mata lafayarta guri daya. Dama gurin tsira take nema,don haka da sauri da sauri ta wuce bandakin ta turo qofar. Wani wawan tsalle ya buga bayan ya isa dakinsa. "Alhamdulillah" Ya sake maimaitawa yana sauraren bugun da zuciyarsa keyi,sai ya miqe ya soma shima rage kayan nasa jikin sannan ya wuce bandaki. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 142 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.....siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashin da babu irinsa_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 142 Sai da suka tabbatar an kai amarya,an kuma dawo,kowacce mota an ajiyeta a muhallinta sannan sukabar farfajiyar gidan shi da saddiq suna wucewa sassansu da tuni kowannensu shima ya kwashe komai nasa banda furniture din ciki,aka kuma shirya a tagwayen gidajensu masu tsananin kyau da fasali. Saida musaddiq din yayi wanka don yaji dadin jikinsa,ya kuma canza kayansa zuwa sassauqar jallabiyya ta maza. Har zai tada sallah sai kuma ya fasa,ya koma da baya yana dauko wayarsa da tunda suka gama waya da amna ya sakata a charge ya kulle ya barta a dakin. Yayi hakanne don kada ta matsa masa da kira da magiya,taje ta karya masa zuciya yayi abinda baiyi niyya ba. Sam bayajin zai barta fita a gidan,fita daya yakeso tayi,daga gidan sai gidanshi a gobe in sha Allah. Ya tarar kuwa da miscal dinta har guda biyar. "Rigimammiya" Ya fadi yana murmushi sannan ya koma ya zauna yana yunqurin kiranta. Kiran farko aka gaya masa layin a kashe yake,mamaki yadan kamashi,don zai wahala ka kira amna wayarta a kashe,tunda dai su ba rashin wuta sukeyi ba,inverter ne 24/7 a gidan. Sake gwadawa yayi aka sake gaya masa hakan,sai ya haqura ya kira saddiq zuciyarsa na raya masa tayi fushi ne dashi bai kaita ba,shi yasa ta kashe wayar don ta rama,shikam bazai iya jura ba,gwara ya lallaso abarsa, "Huda zaka kiramin,kace tace da amna ta bude wayarta badon halina ba". Dariya saddiq ya bushe da ita. "Man.....wannan karyar da kai haka?,'yan mazan anni na dab da zubewa" "C'mon saddiq.....zaka taimakamin ko na shiga gidan da kaina na nemota?". "Ni na isa?,bari na kira maka ita.....hold on kada ka kashe". Ya fada yana hada conference call . "Hubby..." Ta furta da shagwabar data sanya musaddiq jin kunya ta kamashi. "Love ya akayi?". "Ina kewarka hubby" "I know love......but mun kusa kasancewa da juna in sha Allah,awanni kadan suka rage.....kina ina?" Ya tambayeta calmly. "Na boye a daki hubby.....kunyar anni nakeji". "Anni love?....." Ya fada dariya na subuce masa. "Anni ai bata da surukai sai 'ya'ya,tasha fadin hakan.....fell free please". "I will tray hubby" "Good girl....amna fa?" "Tun dazun da muka karbi adda fannah ban sake ganinta ba,ina tunanin tana wajen anni". "Thanks......bari nayi wanka.....get ready zan kiraki ki rage....." Bai qarasa jinsu ba ya yanke kiran,kada suje suyi masa baranbarama a kunne. Still ya sake kiran saddiq. "Ina kunyar tambayar anni please saddiq tambayar min ita" "A nawa?" Ya sake zolayarsa "Ka fadi price dinka" Ya fada yana jin zaquwa. "Bari na kira maka din sai mu tsadance" Ya fada yana yanke kiran. Minti daya kacal saiga kiran saddiq din. "Anni tace suna tare da huda,gashi kuma huda tace tana wajen annin". Gaban musaddiq ne yayi wata irin mummunar faduwa,haka kawai yaji fargaba tana ratsashi. "Ya akayi haka?....amma,ina zuwa" Musaddiq ya fadi yana yanke kiran,sai ya zura flip flops dinsa yana fita a dakin. Kacibus sukayi da saddiq wanda ya fasa wankan shima ya zura tasa rigar. "Ko wani dakin ta shiga bacci ya dauketa" Saddiq din ya fada shima yana jin haka siddan tsoro yana kamashi. "Haka nake tunani" "Muje cikin gidan" Saddiq ya fada yana yin gaba musaddiq da yakejin kaman an sabule masa gwiwoyinsa ya bishi a baya. Harabar gidan ba kowa don kowa ya gaji ya wuce makwancinsa,baqi suna can shiyyarsu a bangaren baqi na gidan,a haka suka kutsa sassan anni. "Kira anni kice ta sauko" Saddiq yace da badawiyya me aikinta,ta amsa da to. Harta fara haurawa saddiq ya dakatar da ita yace ta dawo sai ya haura da kansa. Ya samu annin tana cire dankunnayenta da sarqa,saita juyo da mamakin ganinsa a irin wannan lokacin tana kallonsa. "Ya akayi saddiq?" "Amna fa bata wajen huda anni,kota gaya miki tana wani gurin?,dakunan wajen nan kuma mun duba kafin mu shigo,wayoyinta switched off". Yankewa gaban anni yayi ya fadi,hannuwanta data miqa kunne don cire dan kunnenta sai taji sun mata nauyi dole ta ajesu tana dubansa. "Kun gama duba gidan nan gaba daya?". Kai ya girgiza. "Kusan ko ina dai anni" Hannu kawai ta miqa ta dauki mayafinta ta yafa tana cewa. "Muje". Tare suka sauko dashi,ta dubi musaddiq. "Qarfe nawa ta kiraka kira na qarshe?". "Takwas da rabi anni mukayi waya,tace zataje gidan BB nace ta bari if possible zan dauketa na kaita taga gida mu dawo....idan bai samu ba tayi haquri,na saka wayar charge saida muka gama komai na koma daki na samu miscal dinta me yawa,na kira kuma wayar a kashe take". Wani abune ya tsargawa anni,a jikinta kawai taji wani baqon abu yana shirin faruwa,don amna bata taba irin wannan ba. Koda garden na gidan zata shiga saita gaya ma anni ballanta ace ta fita ko tayi nisa da gida irin haka. "Kiramin duk masu aikin gidannan" Anni ta buqata tana duban badawiyya. Da sassarfa ta juya,ba jimawa sai gasu kafataninsu,annin ta leqa daga qofar falon ta gaya musu,matan su bincike cikin gidan,mazan kuma wajen gidan dama kewayensa,saita koma cikin falon ta zauna kawai tana jin qafafuwanta suna dab da gagara daukarta. Kimanin mintuna biyar matan suka dawo,saidai kowacce abinda take gaya mata shine. "Bamu ganta ba" "Ba kowa a dakunan" "Bata nan". Shuru kawai annin tayi tana jan hasbunallahu wa ni'imal wakil tana dakon dawowar mazan. Jimawa kadan suka kammala nasu duban suma,har zuwa qofar gidan. Kasa tashi annin tayi,don haka tace musu su shigo parlor din kawai. " Mun duba duk inda ya dace ace mun duba din,tun daga cikin gidan nan har street din daga farkonsa har qarshe amma bamu sameta ba,bamu samu kuma komai nata ba" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,hasbunallahu wa ni'imal wakil" Anni ta fada tana runtse idanunta,fargaba tana kamata. Gaba daya rasa abun yi tayi,hakanan kuma ta rasa abun fada kwata kwata,kwanyarta ta daure tamau kamar bata tunani me kyau ba tunda take. Fu'ad da farouq dukkaninsu suna gidajensu da matayensu,abba kuma baya nan,a yadda sukayi magana a safiyar gobe qarfe takwas zuwa tara jirginsu zai sauka. Kai ta girgiza,ba wanda zata bari ya sani a cikinsu,ba wanda zata dagawa hankali. "Anni ko su yaa fu'ad za'a kira?" Saddiq da tuni hankalinsa yayi qololuwar tashi ya fada. Kai ta girgiza tana miqewa. "Ban yarda ku gayawa kowa komai ba a darennan,don ba abinda hakan zai amfanar saidai ku daga musu hankali,bayan koda sunzo ba zasu yanke abun yanzu yanzu ba,sai wanda ya qaddara faruwar hakan ya qaddara warwarewar lamarin...." Ta fada cike da tauhidi da qarfafa imaninta,duk kuwa da cewa ita kadai tasan abinda takeji. "Kuje kuci gaba da kula da aikinku....kuma ku wuce zuwa safiya ko asuba muga abinda Allah zaiyi" Annin ta fada tana duban kowa. Kowa din ya juya ya fice,amma banda musaddiq dake qame a wajen,tamkar ma baisan abinda yake faruwa ba. "Musaddiq" Anni ta kirashi cikin dakiya. Kansa kawai ya daga ya kalli annin,don yasan baida sautin da zai iya amsa mata. "Kayi haquri kaje ka kwanta" "Kwanciya anni?" Ya tambayeta kaman baya fahimtar hausa. "Ta yaya zan iya kwanciya bansan halin da take ciki ba?,anni ina aka kaita?,waye ya dauketa?,me tayi musu?,me sukeso?,amna ce fa?.....kwata kwata shekararta nawa?,waye ta tsarewa wani abu?" A nutse anni ke karantarsa,ta fahimci kaman abun yanason fin qarfin kwanyarshi ne,don haka ta kira saddiq. "Ko baka kwanta ba kaje kayi addu'a musaddiq mu barwa wayewar gari" Tsam.ya miqe ba tare daya kalli koda saddiq dake jiransa ya tashi su tafi ba. "Ina zaka?" Saddiq ya zaburo yana tambayarsa gami da shan gabansa. "Zan fita nemanta ne,tunda kai baka damu da ita ba" Ya fada da alamun tashin hankali muraran akan fuskar sa. Kai saddiq ya girgiza "Akwai hadari a fitarka musaddiq,tunda ko su waye sukayi hakan bamu sansu ba,bamusan dalilin daya sanya suka aikata hakan ba,bamusan kuma meye manufarsu ko target dinsu ba". "Ko report sai naje na shigar,ba zasu dauke mana mutum.sukutum da guda mu kulle qofofinmu mu kama bacci ba kaman kaza suka dauka" Anni ta fahimci da gaske abun ya soma haurawa tunaninsa ne,don haka ta tako gabansa tana kiran sunansa. "Kanason jefa amna a hadari bayan wanda take ciki?" Kai ya girgiza da qarfi. "Yayi....to kada ka soma wani motsi ko aikata komai har sai munji daga bakin yayyenku.....qila fitar da zancan shine zai zama namu kuskuren.....kayita karanta ya hayyu ya qayyumu birahmatika astagis". Kafin ta dire ya kama,a hankali sai yaji hankalinsa yana daidaita,ya miqa hannu ya kama hannun saddiq da kanshi yana cewa "Muje". A parlor dinsu ya zaunar da saddiq shima ya zauna yana matsowa dab dashi,ya kalli saddiq din sosai muryarsa tana Rawa "Saddiq tsoro nakeji su waye?,tsoro nakeji karsu cutar da ita,saddiq munaji muna gani a hannunsu zata kwana?,wanne irin gurin kwanciya zasu bata?" Wanne kalan ruwa da abinci zasu bata?" Sosai saddiq ya riqe hannunsa yana fadin. "Kayita maimaita fadin ha hayyu ya qayyumu din kamar yadda anni tace......bamu zalunci kowa ba in sha Allah ba wanda Allah zai dorashi a kanmu". Sun jima yana riritar musaddiq kafin ya samo nutsuwarsa 'yar kadan,saidai ko cikakken zama ya kasa bare ayi maganan kwanciya,kai kawo.kawai yake tsakanin qofa window zuwa farfajiyar gidan,yana jin kamar ya zura da gudu ya tafi neman amanansa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 143 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 143 ★A nutse ya shafa addu'a daga sallar asubar da suka idar shida fanna din tasa,koda bai kalli madubi ba yana iya jin yadda qwayar idanunsa suka tasa,wanda bana komai bane saina kukan farinciki daya dinga yi a daren jiya. Yaso yayi haquri ya kauda kai saboda walimar da za'a gudanar a yau,amma inaaaa.......ya gaza jurewar,har sai da yakai ga inda zuciya ruhi da gangar jiki suke muradi. Juyowa yayi gaba daya gareta,tana zaune a takure,kanta a qasa tana duban yatsun hannuwanta. Ita dinma fuskarta duk ta tasa,saboda kusan tare akayi kukan,tana yi yana tayata. Idanu ya lumshe ya budesu yana jin nishadi yana saukar masa. Kullum cikin zulumin yadda zai taddata yake,saboda ya sare da halayen 'yammatam yanzun duk da cewa yana da cikakken yarda da dabi'unta,to amma wani lokaci abun ba'a kama bane ko siffa. "Taho nan flower" Ya fada da sassanyan muryarsa yana miqa mata hannunshi. Bata wani musa ba ta miqa masa nata,don tana buqatar inda zata jingina taji dadin zaman. Jawota yayi zuwa jikinsa yana rungumeta tsam,yana jin wata shaquwa tana tsaga jikkunansu,yana jin kamar ta tabbata a rungume a jikinsa kaman haka. Qoqarin gaidashi takeyi,ya amsa mata yana shafa kanta ya amsa cikin kulawa. Sosai ya dinga jero mata addu'o'i,kanta a qasa tana amsa masa da matuqar alkunya. Mintuna kusan goma sha biyar suka debe a haka kafin ya gyara mata zamanta,ya ciro alqur'ani guda biyu ya bata daya ya dauki daya. "Ko na minti biyar ne flower,saboda mu bude wunin rayuwarmu na farko da neman albarka". Ya fadi yana miqa mata. Rainon anni ne wannan ta saba musu da farawa da qur'ani,kaman yadda yasan itama fannah din 'yar gado ce wajen iya sarrafa harshe a qur'ani. (Ina kira a gareku iyaye,kiyi qoqari a mazauninki na uwa ki wadata kwanya da harshen 'ya'yanki da qur'ani,su zama gwanaye wajen karanceshi daga bango zuwa bango,idan da hali suna karantawa suna fahimtar ma'anar,saboda hakan yana taimakawa wajen zaunar dashi a kansu yana kuma taimakawa wajen sake jin asalin gard'insa da dadinsa. Allah ya sani ina mamaki naga babban mutum babbar mace ko sangamemiyar buduwa musulma,amma ba zata iya karance miki qur'ani daga bango zuwa bango ba,ko ba zata iya biya miki wani adadi me yawa ba,don kwanyar da aka horata da qur'ani zaka sameta da kaifin basira da fikira me tarin yawa,Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da yaranmu akan hakan,ya shirya mana zuria kafatanin musulmi Allahumma ameen). Suna kammalawa kira yana shigowa wayar tasa. Fannah ce ta miqo masa da hannu biyu ya karba yana murmushi "Allah yayi miki albarka" Saidai sunan daya gani mamaki ya kamashi,baiyi zatonma zaa kirashi da safe da wuri haka ba shi yasa ya bude wayar. "BB ba'a ga amna ba tun daren jiya......ga musaddiq nan ya rikice mana,kaman yanason rasa nutsuwarsa,ka sanar da hamma don Allah" Abinda saddiq ya fada kenan yana katse Kiran. Innalillahi yakeso yaja,amma kuma bayaso yayi abinda zai tashi hankalin fannah daga wayewar garinta a rana ta farko,ballantana yasan mata da rudewa qwarai,dan qanqanin abu sai su maidashi babba,don haka ya miqe tsam da wayar a.hannunsa yace. "Ina zuwa" Ya soma takawa yana fita a dakin. Tadan bishi da kallo kadan,sai kuma ta miqe tana ninke abun sallar da suka idar. Wani dakin daban ya bude ya shiga,sannan ya fara qoqarin kiran fu'ad yana kuma laluban kayan da zai sauya a jikinsa,idanunsa akan agogo yana duba qarfe nawa. Su dimma rufe alqur'aninsu kenan,don a yanzun shine malaminta. Tayi sauka tun kafin rasuwar mahaifinsu,tana da tilawa a kanta,amma sai yanayin karatunsa da qira'arsa suke mata dadi,wannan ya sanya ya zame mata malami duk bayan sallar asuba suke tilawar abinda ya sawwaqa tare. Wani lokaci ido take zuba masa idan yana karatun. Komai Allah ya bashi,duk wata baiwa da take nuna cikar dan adam ya sameta,abu guda daya ne ya masa cikas da naqasu shine MAHAIFIYA. Kashingidar da yayi da wannan damar ta samu ta zame jikinta zuwa kitchen. Wata irin mahaukaciyar yunwa take fama da ita a dan tsukinnan,ko cikin dare ta tashi abinci takeci,ba jimawa kuma take rasa komai,cikinta yake yayewa tasss kaman an mata yasa. A tsaitsaye ta hada oats ta madara tasha,kafin sannan saiga ma'u ta shigo. A mutunce suka gaisa,zuwa sannan ta fara gane inda sabreen tasa gaba na bawa mijinta kulawa da karan kanta. "Me zamu dafa?" "Ummm.....bari muga.....bari na fara dafa masa paw paw tea tukunna" Ta fadi tana nufar tsararren store dinsu. Duk kusan ganyayyakin da yakesha akwai a ciki,busassu anyi packaging nasa cikin wani leda ta musamman da ake kawowa daga china. Packet na Paw paw leave din ta dauko ta dawo,ta wankeshi da kyau ta tafasa ta juye masa cikin wani Traditional English tea set sannan tace da ma'u. "Ki fiddo naman kai bari naje na dawo". Ta shiga daidai sanda ya fito daga toilet yana goge ruwan alwala. Idanunsu suka gauraya waje daya,kowannensu ya sakarwa dan uwansa lallausan murmushi. "Barka da tashi sleepy head" Ta fada cikin salon tsokana. Fadada murmushinsa yayi har fararen jerarrun haqoransa suna fitowa. "Barka kade my super girl" Ya bata amsa yana karbar tea tray din yana ajiyewa saman drawer. Hannunsa ya miqa mata yana jawota cikin jikinsa,saidai kuma sulalewa tayi ta tsugunna tana gaidashi. Amsa mata yayi cikin murmushi kafin ya miqa hannu ya sake jawota ya rungumeta tsam,fitinannen qamshin kabbasarta na incense by kabo daughter daya hautsina har cikin gashinta da kuma lab lab dinta suna tashi da wani sassanyan qamshi daya manne a fatarta. "Fatan shalelena ta tashi lafiya.....addarmu.......matar babban yaaya" Yadda ya fadi maganan ya sanyata tuntsirewa da dariya,ya sake kamota yana qanqameta a jikinsa. "Ina yara na?,fatan sun tashi lafiya?" Ya furta yana qoqarin dage rigar baccin jikinta. Da sauri ta damqe hannunsa tana duban tsakiyar idonsa,sai ya dage mata dukka girarsa yana tambayarta why?,da wannan kallon nasa. "Ba bra a jikina". " Good" Ya fada da hanzari yana daukanta cak ya azata saman drawer din,sannan yasa hannunsa ya dage rigar har zuwa inda yakeso. Da cikin nata ya fara wanda ya fara turo kansa,ya aza dukkanin hannuwansa akai. "Good morning my Angel's" Dubansa tayi. "What?" Yatsansa ya dora saman lips dinsa "Shshshsh" Ya fadi sannan ya maida hankalinsa kan cikin. "Eheeennnnn......hope you're doing well......am eager to meet you my life.......have a nice and great day" Sai ya sunkuya yayi kissing na cikin. Sama ya komar da fuskarsa tsakanin ababen dake matuqar janye hankalinsa,qanqameshi tayi sanda yake cusa kansa a tsakiyar su,sannan ya sakar mata wani kiss din me sanyi kafin ya janye fuskarsa da idanunsa suka fara canza launi. "Mun gama gaisawa.....me kike cewa?. Fuska ta bata. "Son kai hamma.....son kai" "Name?" Ya tambaya yana ware hannayensa. "Angels hamma?......ni nafison baby boys.....masu kama da kai.....masu quality dinka". Ta fada tana tura baki gaba. Kyau sosai lips dinta sukayi masa,yasa hannu yana taba lips din murmushi na qwace masa,ya motsa bakinsa cikin nutsuwa. "Nafison baby girls masu tausayi irin naki......masu tsananin zumunci irin na ummansu......masu qaunar 'yan uwansu.....kinsan ma haihuwar diya mace falala gareta me girma fiye dana d'a namiji?" Kai ta girgiza "Na sani,idan aka haifi uku aka musu tarbiyya aka aurar dasu zasu zama sanadin shigar mahaifansu aljanna,sannan haihuwar d'iya mace tamkar shigowar haske biyu ne cikin gida,saboda zata jawo wani namijin shima ya zama naku". Tafi sosai ya sakar mata yana murmushi "Bravo alaiki...." Ya furta yana kissing tafin hannunsa ya aike mata dashi. "Duk da wannan?,duk da wannan my world kikeson boys?" Kai ta gyada. "Na rigaka addu'a fa hamma......inaji a jikina Allah ya amsamin.......ina buqatar photocopies din muffin dina" Ta fada tana tsiyaya masa ruwan gwadar ta miqa masa. Karba yayi yana dubansa,sai daya qare masa kallo sannan ya kalleta da lallausan murmushi "Ya akayi kikasan ina sonsa?". Dukka girarta ta dage masa tana nade hannayenta a qirji,hakan ya qara mata kyau sosai. "Kana tunanin idan nace inasonka ina sonka ne da wasa?......duk wanda nace ina sonsa......ina sonsa da gaske.....ballantana kai...." Ta qarasa fadi tana nunashi da yatsa daidai sanda kira ya shigo masa. "Farouq?" Ya fada a mamakance,farouq dinne da kira haka da sassafe?,cikin jikinsa yaji tabbas akwai wani abu daya faru,ya miqa hannu yana daga kiran *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 144 *_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽 *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂 Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾 wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 144 Shuru kawai yayi yana sauraren farouq har ya gama gaya masa abinda zai fada din. Satar kallonta yayi sanda take qoqarin zuba masa wani tea din. "Ka kula please dude.....banaso adda taji maganar nan ko don lafiyarta.....itama fanna din ban gaya mata ba,zan wuce gidan yanzu" "In sha Allah" Ya fada yana sauke wayar daga kunnensa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Shine abinda yaketa maimaitawa can qasan zuciyarsa kafin ya samu ya miqe tsaye yana duban ta. "Adamamin tea din nan,abba ne ya kirani yanzunnan wai ya kusa sauka yanason nazo". Har ga Allah bata kawo komai ba,kawai mamakinta shine abban ke nemansu da safe haka?,kuma shida farouq?. Ba huruminta bane zafafawa kan sanin meye asalin ainihin kiran ba,don haka ta taimaka masa ya sauya kayansa ya fice zuwa ma'ajiyar motocinsa,inda ya taso jordan suka fice tare. "La haula wala quwwata illa billah" Shine abinda yake maimaitawa kawai akan hanya yana murza goshinsa. Wani irin tashin hankali ne yaji yana lullubeshi,duk irin tsaron da ya saka.....duk yadda yake kaffa kaffa amma daga gefe akwai wanda yake fakonsu?. "Su waye?.....su waye?" Ya furta a dan zafafe yana jinjina hannunsa yana duban titi,yana jin kamar ya tariyo daren jiya komai ya wakana a idonsa. "Waye ya rage?,waye yayi saura?" Ya fadi yanason tunawa ko akwai wani abu daya bari wanda ya kamata yayi baiyi ba. Wayarsa ya fiddo ya fara qoqarin gwada number amna da kanshi,amma switched off ake gaya masa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ya koma maimaitawa. Anni kawai yakeji.....ko musaddiq zai biyo bayan anni ne wajen shiga rudani,saidai ita anni ta fishi dauriya da dakiya. Tun daga harabar gidan daga kan fuskokin masu tsaron gidan ya karanci tashin hankali b'aro b'aro. Jordan na fakashi ya sauka da dan sassarfa ya wuce cikin gidan. Da batulu ya soma cin karo,shugaban ma'aikatan gidan. "Ina anni?" Ya tambayeta ba tare daya damu da amsa gaisuwarta ba. "Tana sama sir" "Okay.......Inaso kowanne baqo a gidan nan a kula dashi yadda aka saba,a kuma sallamesu ba tare da kowa yasan halin da ake ciki ba......a shaida musu an soke walimar saboda annin batajin dadi,likita kuma yace a barta ta kwanta ta huta sosai,saddiq zai sallami kowa,masu tafiya a jirgi da masu tafiya a mota,inaso nan da azahar gidan ya zamana daga mu sai mu,na tabbata ku kudai kukasan abun.....daga haka banaso labarin ya qara gaba" "In sha Allah yallabai za'ayi duk yadda kace" Ta fada cikin girmamawa. Yana shirin haurawa saman yaji muryar farouq,waiwayawa kawai yayi ya kalleshi yana amsa sallamar saiya juya yana haurawa saman. Hankalinsa duka yana kan anni,don haka ita ya fara gani a sanda ya bayyana a parlor din saman. Kallo daya tak yayi mata yaga wata irin rama ta bayyana saman fuskarta,daga daren jiya zuwa yau?,idan kuma abun ya shallake haka kuma fa?,fu'ad ya tambayi kansa da kansa hankalinsa a tashe. Sauke dubansa ya sakeyi ga huda,wadda ke cure waje daya taci kuka har ta soma jin ba dadi,saddiq na zaune kusa da ita,da alama qarfin gwiwar lallashinta yake neman tattarawa kuma bai samu hakan ba. Musaddiq kuwa yana zaune kaman zane,ramarsa har taso wuce ta annin da wani taqi na musamman. Kallon da yayi musu dukkaninsu a lokaci daya sai yaji zuciyarsa na nufin karyewa kaman yadda ta anni ta karye. Ganinsu sun biyun sai takejin dukka qarfinta ya tattara a nan....kaman sune duk wani hope nata a yanzun. Fu'ad ne ya lura da yadda jikinta ya soma rawa,ya qarasa da sassarfa ya riqeta yana zaunar da ita. Komawa yayi gabanta ya zauna sosai yana tanqwashe qafafunsa. "Kece qarfin mu anni.....don Allah ki sake bamu wannan qwarin gwiwar koda karo na qarshe ne....koda shine alfarmar qarshe da zaki mana mu 'ya'yanki". Duk yadda taso tsare hawayenta sai daya zarto,saidai tayi qoqarin saurin daukeshi,banda su farouq da fu'ad din ba wanda ya gani. "Allah shine qarfinmu muhammadu.....shine kuma zai tsaya mana" Ta fada tana tattaro jaririyar dauriyar data rage mata. Saidai shigowar abba a daidai lokacin ya sanya qwarin gwiwar nata ya sulale yabi ruwa,don nufarsa tayi hawaye yana tsinke mata,fu'ad ya yiwa saddiq alama daya sauko da huda ya juya yana sauka da sassarfa. *_BAYAN MINTI TALATIN_* Dukkaninsu suna falon daya dauki shuru bayan gama tattaunawarsu akan al'amarin. "Nayi alqawarin muddin ina numfashi......tsakanin yau da gobe.....idan yayi tsanani zuwa jibi,tabbas da ikon Allah,da kuma girman zatinsa amna zata dawo cikin ahalinta.....inason kowa a cikinku ya ajiyemin wayarsa.....BB harda kai,kubar security code dinku akai basai kun cire ba.....abu na biyu kowa inaso ya sanya ido akan motsinsa,da motsin duk wani mutum da yake mu'amala dashi komai qanqantarta.....anni ki saka taki wayar a ciki.....abba zanyi connecting kowanne kira da wayata basai ka bayar da taka ba.....but kowanne saqo ko.kiran duk da nayi connecting ka kula sosai yayin dagawa......zamuyi aiki da team dina na kwana biyu zuwa uku in sha Allah" Yadda yace din duka hakan akayi,har zai fita ya dubi huda. "Bani taki wayar" Saboda wani tunani da yayi. Throughout yau bayason yau sabreen tasan komai ko taji komai,idam ta yuwu ma har zuwa sanda zaa kammala abun,saidai yasan abune me wahalan gaske,karbe wayar hudan zai rage shigarta tashin hankali. Wunin ranar gaba daya bai zauna ba,dukkaninsu shi da farouq dinma,zirga zirga ce kawai ake yinta a sirrance. Hankalinsa dukka yana kan wayoyin daya karba,wai ko zaiga wani baquwar number ya shigo,saidai ko gilmawar saqo bai gani ba. Zuwa yammaci saqo da kiran sabreen ya cika masa waya,sai daya idar da sallar la'asar ya ciro wayar sannan ya tuna tunda ya fita a gida bai kirata ba. Da sauri ya maida kiran nasa zuwa ga wayarta,bugu daya ta dauka,muryarta duk tayi wani laushi sosai. "Am so sorry my world.....ayimin afuwa,munyi busy yau sabgogi sun riqe muffin sosai". "Hamma na dauka ka manta dani ne yau?,yau Walmar anni,ga lokaci yana shirin kufcemin,na gama shiryawa ban sameka ba,kasan bazan fita ba kuma bada izininka ba,still kowa a gidan na kira number dinsa bai daga ba,hadda huda ma,lafiya kuwa hamma?". Yadda tayi maganar ya tabbatar jikinta ya soma raya mata akwai matsala,muryarta tayi wani laushi. "Na saka an tsaida walimar nan sabrrr...zazzabi ne ya saukarwa anni,kinsan kuma tana da asthma.....so kiyi zamanki a gida.....i will tray my best naga na dawo gida da wuri". Dan jim tayi kadan kafin tace. "Anya baka boyemin wani abun hamma?,ko wani abunne ya samu annin?". Murmushi ya saki me dan sauti na qarfin hali. "Ba komai my world.....karki damu.....ki kulamin da kanki,ki gaidamin yarana". Ya fadi yana katse kiran. Lamo kawai tayi saman gadon zuciyarta na wani bugawa,bugun sam ba daidai take jinsa ba,hakan yana sake bata tabbacin akwai abinda yake tafiya ba daidai ba. Tayi juyi saman gadon har batasan adadinsa ba,a nan sallar magariba ta sameta taje ta bada ita,tayi isha'i ta sake dawowa ta kwanta. Indai ciwon anni baiyi tsanani ba ai ya kamata ace ta samu koda mutum daya ya daga kiranta,bawai kowa ta kira wayarsa zata yita ringing bai daga ba.....ciki harda fuad din kansa. Sanda tara na dare yayi sai taji hankalinta ya soma tashi,kiransa ne ya bata relief dan kadan. "Am sorry....on my way dear,karkiyi kewata da yawa". Maganan da sukayi kenan a taqaice. Yana ajiye kirannata wayar farouq ta dauki ruri. Da hanzarinsa ya ajiye tasa wayar y kuma daga wayar farouq din yana kallon screen din. Baquwar number ce da babu ita a jerin lambobin kan wayar,baiyi jinkiri ba yayi hanzarin hada abinda zai hada ya kuma daga kiran. "Farouqu hamza kibiya haka ne?" "Shine" Fuad ya furta kansa tsaye yana fatan hirar tayi tsahon da yakeso. "Yauwa......mune wadanda muka dauki qanwarka amna a jiya........saidai kafin mu tattauna komai daku muna buqatar kudi naira billon goma". Idonsa ya lumshe ya sake budesu,wani fushi yana taso masa yana lullube zuciyarsa. Ashar yakeso ya fara sake musu a matakin farko,to amma kuma har yanzu ba'azo gurin ba. "Ba matsala.....zamu saka muku......amma idan munyi hakan zaku sakar mana qanwa salin alin?". "Me yuwuwa....duk da bamu keda wannan hukuncin ba,wanda keda ikon fadin a saki ko a kashe daban.....wannan din ladan aikinmu ne muke buqata daga gareku". Bakinsa yaji yana motsi,amma sai yayi qoqarin danne zuciyarsa. "Zamu biya mun amince......ku fadi inda za'a saka kudin". " Zamu saka" Ya fada yana datse kiran. "Oh shirt" Fu'ad ya fada yana dukan seat din motar. Qiris ya rage mintunan su cika.....baici nasara ba...... Bayajin wannan daren yana da nutsuwar gyangyadi ko bacci komai qanqantarsa.....maganar kisa suke fa idan ta kama?. Baiko jira Jordan ya gama tsaida motar ba ya bude ya dira daga ciki yayi cikin gidan. Baiko tsaya tantance wanda yake parlor din ba ya ketashi ya wuce hallway,wannan qofar dake a kulle kullum ya danna ya budeta yana kutsa kansa ciki. Ajiyayyen gurinsa ne dake dauke da tarin na'urori,ba kuma kasafai ya fiya shiga wajen ba sai ta baci ko kuma yana da babban aiki irin haka. Gaba daya qwayayen ya kunna ya kuma kunna kowacce na'ura ya saitata kan aiki,ba dadewa komai ya daidaita,ya fidda gaba daya wayoyin ya zubesu ya riqe ta farouq a hannunsa yana kwafe numbers din zuwa allon screen din dake gabansa. Tiryan tiryan ya soma kurdawa cikin bincikensa,saidai kaman yadda ya zata komai ya tsaya daidai iya mintuna daya kashe kiran. "Ya salam" Ya fadi yana jin wani zafi da fusata. "Da gaske dai wani abu ya faru" Muryar sabreen ta ratsa kunnensa. Da sauri.ya daga kai yana dubanta. Tana tsaye daga bakin qofa,sanye da night wear baby pink masu daukan idanu masu hawa biyu,gashinta ta sakeshi saman kafadarta,yayin da jaririn cikinta ya bayyana sosai ta cikin rigar kasancewar ta lafe mata sosai a jikinta. Duk da yanayin da yake ciki na tashin hankali hakan bai hanashi hango kyawunta ba......hakan bai hanashi ganin wani kwantaccen kyau daga gareta ba. "Listen sab....." "Karka rufemin hamma.....na roqeka" Ta fada jikinta da muryarta dukka suna rawa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 145 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 144 "Is alright......zo ki zauna" Ya fada yana tashi da kansa,ya kuma tarbota yaja mata kujera ya zaunar da ita. Ta bashi dukkanin wata nutsuwa da hankalinta tana kallonshi. "Kiyimin alqawari ba zaki daga hankalinki ba....." "Nayi hamma.....nayi". Kai ya jinjina,ya sake riqe hannunta sosai yana duban tsakiyar qwayar idanunta. "Amna ce tadan bace jiya,amma yanzun haka ina kan gano inda take" "Amna ta bata ko kuma an saceta?,wanne ne daidai a ciki?". Ta tambayeshi tana jin wata kaduwa tana kama ilahirin gabbanta. Juya maganar tata yakeyi a ransa,ya sake kallonta yana ganin yadda ta kafeshi da ido kaman me tuhumarsa da aikata hakan. " Kowanne za iya zama daidai....." "Bazai zama ba.....inaji a jikina dauke amna akayi intentionally.....wallahil azeem" Tana kaiwa nan saita rushe masa da kuka gaba daya. Rudewa yayi,gaba daya kukanta ya dauke masa nutsuwa. "Bamuyi haka dake ba sabreen.......karki cutarmin da yara please" Ya fadi yana hade hannayensa guri guda gami da sanya nata hannuwan cikin nasan🙏. "Me yasa zaka boyemin hamma?......sai idan ta mutu sannan zaka gayamin?,ina huda?" "She's safe" Ya bata tabbaci. Kai ta girgiza,sam hankalinta bai kwanta ba. "She's not safe tunda aka dauki amna.....nadra haneefa dukkansu suna cikin barazana" "Like how?" Ya fadi yana dubanta da tarin tambaya gami da zama sosai a gabanta sabanin tsugunnon dazu. Tambayarsa ta dawo da ita cikin hayyacinta. A hankali ta sassauta sautin kukan nata. Zato bai zama gaskiya ba.....zatonta kuma a yanzu baida hujja ko dalili sai qwqwaran zargi,tana gudun ta furta abinda idan yaje ya dawo zai zama ba gaskiya bane,da wanne ido zataci gaba da kallonsa?.. "Kina da wani masaniya ko hasashe ne?" Kai ta girgiza "Babu....but duk wanda ya shiga ya dauki amna....nadra dasu huda ba zasu gagareshi ba" "A tsukinnan indai ba aljani ba,banajin akwai wani dan adam daya isa ya keta tsaron da gidan yake dashi ya dauki amna.....ina kyautata zaton fita tayi.....zan binciki duk wani CCT footages na gida.....naci alwashin amna ba zata kwana uku ba cikin iyalinta ba". Wani irin abu taji yana yawo da ita,ya jima yana qoqarin daidaita mata nutsuwarta,amma kuma hakan bai hanata kwanan kuka ba,bisa sharadin itama gobe ba zata zauna a gidan ba,ya kaita gidan anni.....anni bata cancani fuskantar wannan tashin hankalin ita daya ba. ★Taku biyu tayi ta sake juyowa tana komawa bakin window din. Sake riqe wayar tayi sosai a kunnenta tana jin wani farinciki yana yawo da ita,jinta take tamkar a saman gajimare. Karon farko data fara kasancewa cikin sa'a a rayuwarta,karon farko data aiwatar da wani aiki da yazo mata da nasara ba a karon farko ba sai wannan. "Komai kakeso zaka sameshi tunda har ka cikamin muradin raina,iya wannan nasarar daka tabbatarmin ta isheni farinciki......wannan yarinyar dake hannunku kadara ce.....kadara ce me girman gaske,kada kuyi wasa da ita har sai kun samu abinda kuke nema" "Na sani hajiya,daga adadin abinda muka fara tambaya kuma muka samu tabbacin samunsu nasan munyi babban kamu,munyi kuma babban aikin da zamu fita daga talauci har abada". "Qwarai da gaske" Ta fada tana jinjina kai. "Ina yarinyar take?" Ta buqata ganin amna,ba bata lokaci ya juya kiran video call ya kuma haska masa amnar. Tana ya she tun sanda suka sheqa mata abun bata dawo hayyacinta ba. Baki ta tabe "Wai wannan abarce zata cakuda jinina da nasu?....kuci gaba da aliyarta.....tabbas sai na sanya sunyi nadamar hada hanya dani da kuma sanina koda sau daya ne a rayuwarsu" Ta fadi tana dauke idonta daga kallon amna. Kiran ta katse tana sake murmusawa,idanunta kan farfajiyar gidanta. "Wannan wasan zaiyi dadin kallo.....zan samu farinciki matuqa idan naje idanuna suka ganemin jigatar da ahalin alhj hamza sukayi tsakanin jiya shekaran jiya da yau" Ta fadi a ranta,sai kawai ta fada wanka. A nutse ta shirya cikin qasaitaccen lace,lace ne na alfarma da ita kanta a jininta tasan ba qananun kudade fu'ad ya sanya ya siya mata shi ba. Laluba ma'ajiyar sarqunanta tayi,duka gold sun qare sai fashions masu tsada. Su ta sauko ta zuba tsakanin hannuwanta wuyanta da kuma kunnenta,ta bade jikinta da turare,ta kuma dauko tsadajjen mayafinta mahadin lace din ta yafa. Tunda tazo gidan taga yadda anni da musaddiq ke a birkice idanunta basu huta da zubda hawaye ba,ba iyasu ba.....hatta saddiq dimma da hudan gaba daya. Sak gidan ya koma musu kaman gidan makoki,sauqin abun daya duk an sallami kowanne baqo ba tare da an bari ya fahimci komai ba. Duk yadda anni keji daga qarshe ita ta koma lallashin sabreen,wani irin abu takeji daya kasa tsarga mata,qaqqarfan zato da zargi maras iyaka dake mata kai kawo,wanda tayi imanin wannan karon komai ya kawo qarshe muddin ya tabbata abinda take zato dinne. Cikin isa da izza take takawa zuwa ainihin babbar qofar parlor din. Iska take zuqa sosai d'ai d'ai tana fesarwa. A yau jin kanta dama duniyarta sabuwa takeyi,a haka ta isa qofar falon annin ta turata ta shiga tana rangada sallama da muryarta data fita fes. Sabreen ce mutum ta farko data fara daga idanunta ta kalleta,fes ta zube mata kallonta sanda maamah din ke takowa zuwa cikin parlor din. Kasa motsa bakinta tayi bare ta amsa mata sallamar,sai idanunta da suka zuzzurma saboda kuka data kafeta dasu. Anni wadda ke zaune saman abun sallah bayan ta idar ce ta daga idanunta tana amsa sallamar. A mamakance anni take duban maamah dake takowa parlor din,ci gaba da dubanta anni takeyi haka kawai tana jin wani yanayi daban yana shigarta game da maamahn. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 146 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 146 Murmushi ta saki tana sake takowa da wani irin qarfi da conference,laushin da take gani iya idanuwansu da fuskokinsu wani nishadi yake bata. "Barkanku da wannan lokaci" Maamah ta fadi tana yiwa kanta da kanta wajen zama gami da harde qafafunta guri guda. Idanu anni ta sake binta dashi,tana so tace mata ta tashi ta fita idan ba alkhairi tazo dashi ba,tana so tace mata ta fita salin alin bata buqatar dogon magana,tanaso ta gaya mata ta nesanta fuskarta daga garesu muddin ba zaman lafiya ya shigo da ita ba......saidai kuma shi wanda bai sonka,ba'a ko yaushe ba,ba kuma a kowanne lokaci bane kake bashi daman da zai fahimci wani yanayi da kake ciki na matsatsi ko tashin hankali ba. "Mun yini lafiya ameenatu?,ya taro kuma ya tashi?" Maamah tayi maganar data bawa anni mamaki sosai. "Lafiya alhmdlh" Anni ta furta tana tsareta da idanu. Wannan sauyawar yanayin daga Mariya baiyi mata ba,wannan sanyin da nuna kirkin gaisuwar bai gamsheta ba sam sam. "To ai haka akeso,yayi kyau....Allah ya maimaita.....nace ba fada me ya kawo gaba ameena?,ina cewa duk tsiya dai nice mahaifiyar musaddiq,har abada kuma tuwo sunansa tuwo,babu me canza masa suna......ace an tashi bikin d'ana na ciki na amma bani da masaniya?,haba ameena,son kan naki ai yayi yawa,ko a 'yan Allah ya sanya alkhairi ai nazo ko?". Idanu anni ta dauke tana maidawa wani guri. Ko daya bata tsinci wani abu me ma'ana a cikin zantukan maamah ba,hasalima ciwon kai kawai zasu qara mata ba wani abu ba. "Yanzunma bata baci ba.....baki kuma makara ba" Annin kawai tace da maamah. Wani murmushi maamah ta saki tana dan doka hannunta saman kujera,a nutse sabreen ta sake kai dubanta wajen tana aje wata qatuwar ayar tambaya a kai,sai kuma ta sake maida dubanta ga maamah din. "To Allah dai ya kyauta,amma ko don gaba ya kamata a dinga sanin matsayin kowa". "Idan kin gama zaman don Allah mariya in zaki fita ki rufe qofar parlor din" Anni da takejin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraren soki burutsun maamah ba ta fada,don bata da juriyar zama sauraren nata a yau. "Kwantar da hankalinki ameena......tafiyar zanyi don banga alamun ana maraba dani ba.....amma na miki uziri,duk da cewa idan naqi fita a gidanma banyi kuskure ba,wanda ya gina gidan daga jikin mariya aka ciri halittarsa ya zama gudan mutum abun mora a yanzu" Ta fada tana sake hakimcewa alamunta suna nuna bawai tafiya zatayi yanzu yanzu ba kaman yadda tace. Ko sau daya anni bata waiwayeta ba,ta dauki abun sallarta tana wucewa ciki. Daga yadda take bin anni da kallo tana sake sakin faffadan murmushi ya isa ya gaya maka cewa batasan da wani mutum daban cikin falon ba. Wani abu daya sake qarfafawa sabreen dukka wani zargi da tunaninta a kanta. "Dariyarku takan zam kuka gaba,da nadamar me qin gaskiya......" Furucin da ya fusgi hankalinta kenan,ta maida dubanta sashen da sabreen ke hakimce qafa daya saman daya. Wani zazzafan duba take binta dashi,wani mayunwacin kallo me dauke da tarin ma'anoni,wani irin kallo dake da wani irin zafi.....kallo ne na kota kwana,kallo ne na ko a mutu ko ayi rai da wadannan fitattun idanun nata masu zafi da basu da sauqi ko kadan. Kallo kallo akayi tsakaninsu na wani mintuna,cikin jinin jikinta maamahn ke jin bata aminta da wannan kallon ba. Wani kallo ne da tafi kowa saninsa......tafi kowa kuma sanin ma'anarsa......tafi kowa kuma fahimtar yaren dake cikinsa. "Akwai wani yare da ba kowa yake fahimtar sa ba sai me matsanancin hankali......akwai wani juyi da idan ya tashi juyawa yake watsi da dukka wani abu dake kusa dashi ko nesa dashi ma......." Ta fada tana juya idanunta sannan ta sake maidasu ga maamah "Na jima ina gurnani......na dade ina gargadi.....na dauki lokaci inata jirwaye me kama da wanka......amma inajin cewa lokacin yin wankan gaba daya yazo don a batad da sahun wannan jirwayen.....jirwayen dake cutar da farar tufa yake nakasa kuma lafiyar jiki......gargadi na qarshe da bazan sake irinsa ba.....saidai fallasa ya biyo baya.....ruwan kura ne ta fiddo ajiyayyen naman data aje....don kuwa yafi qarfin bakinta,kalar nama ne da bai ciyuwa a gareta kasancewarsa me dauke da wata babbar guba.....a wannan karon lokutan bada damar gaba daya awa biyu ne kacal....do or die" Tsam ta miqe daga kujerar da take kai still idanunta akan maamah da wani zazzafan kallo tana wucewa ciki itama. Haka kawai kowacce gaba ta jikinta tayi wani irin sanyi,bugun zuciyarta ya dinga qaruwa da wani tsoro da batasan daga inda yake ba. "Kada fa maganganunsa su tabbata.....kada fa lokacin da yake maimaitamin ne yazo" Take fadi a Karan kanta tana jin wani irin razanannen yanayi yana ratsata. Fes maganganunsa suke ratsata kaman a sannan yake furta mata su,tsoro ta sakejin ya saukar mata,ta miqe da zummar barin falon sai taji jikinta ko ina ya dauki rawa. Qoqarin daidaita kanta takeyi,batasan wacce irin matsoraciya ta koma har haka ba,batasan dalilin da ya sanya take yawan samun rawar jiki ba idan tashin hankali ya durfafeta(badai.baki yarda baki da hawan jini ba?). "Ita din ba komai bace.....ba zata iya aikata komai ba don bata da hujja" Abinda zuciyarta ta shiga maimaita mata kenan,abinda kuma yadan bata nutsuwa 'yar kadan,saidai ta gaza samun irin nutsuwar da take da buqatar samu. K'arfe goma na dare daidai take takawa a harabar gidan tana nufar motar da fu'ad ke zaune a ciki yana jiran ta qarasl su wuce gida. Ta madubi ya hangeta,sai ya ajiye wayarsa da system din daya wuni dasu yana aiki ya bude motara a nutse ya fito ya bude mata qofar yana jiran ta qaraso. Tun bata qaraso din ba ya karanci baqon yanayi a tare da ita,yadda yasan sabreen dinsa ba haka take ba,duk da yasan dole akwai damuwa da dukkaninsu suke a cikinta, Baice komai da ita ba har ta qaraso,ta shiga ta zauna ba tare da tace masa komai ba,wannan ma ya bashi mamaki,don komai runtsi.ba haka ta saba yi masa ba,sai ya rufe ya zagaya ya shiga yana bada umarnin tashin motar. Hannunsa ya miqa mata,ta dubeshi sau daya ta miqa masa nata,sai ya jawota jikinsa ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya. "Ina cikin matsi da tsanani sabrrrr,bana cikin nutsuwata da walwalata.....please karki bari ki wanzu cikin damuwar nan kema,domin ke kadai ce kika ragemin da zan samu sassauci da ita". Tausayinsa yayi tsananin tsarga mata,yana tare da abu mafi hadari da muni ba tare da ya sani ba.....yana tare da halitta mafi zamewa rayuwarsa barazana ba tare da yasan da hakan ba. "Zamu kasance tare cikin tsanani da sauqi......zan zame maka garkuwa alqawari ne wannan,your battle is my battle.....we fight together".ta qarasa fada tana matse hannunsa da kyau cikin nata. Sosai maganarta ta sake bashi nutsuwa,yadda ta sakashi a jikinta tana qoqarin bashi dumi daga dumin jikinta ya tattaro hankalinsa dake son kaduwa waje daya. "Thank you duniyata" Maganarsa ta qarshe kenan shuru ya biyo baya. Samansa kawai suka haura shi da ita,don gaba dayansu ba wani me cikakken kuzari. Yana ajiye wayoyin da yaketa dakonsu tun kiran jiya wayar farouq ta sake kadawa. Da wani hanzari yakai dubansa ga wayar. Number jiya ce,don already ya riga yayi marking nata,da wani irin zafin nama ya jona komai yana qoqarin turawa team dinsa saqon kartakwana don buqatar kasancewarsu dashi koma saman minotti sofa dinsa ya zauna yana aza kafatanin hankalinsa akan komai. A hankali ta samu kanta da dawowa da baya,ta samu hannun sofa din da yake kai ta zauna tana jin 'ya'yan cikinta suna curewa waje daya. "Mun sake kiranka a karo na biyu,kiran kuma da ba lallai muyi na uku ba,zamu gaya maka inda zaka ajiye mana wannan kudin....." "Ni kuma a ina zan karbi qanwata?" Ya tambayesu muryarsa a tsaye. Ya gama shirya komai,a yanzun bawai lallabawa yake buqatar yayi musu ba,ko na bayan dama akwai gacin da yaso ya cimma shi yasa ya biyo ta sigar lallami,a yanzun kuwa dole ya canza hannu ya gani ko zai samu kaiwa ga wannan matakin. "Au maganar karbar qanwarka ma kakeyi?.....muna maka maganar kudin aikinmu?". "Wanne aiki kenan kukayi?" Ya tambayesu cikin salon rainin hankalin da yana sane ya tsiro dashi. "Lallai kana buqatar mutuwar qanwarka a wulaqance kenan a hannunmu". "Da na sanya kunyi nadamar haihuwarku da iyayenku sukayi,dana sanya kun gane duniya sashe biyu gareta". Shuru ya ratsa tsakani kafin yaji an danqaro ashar "Kuna tunani kuna da qarfin kudin da zaku iya kamamu ko?,to zamu nuna muku kudinku bai isa ya saka muzo hannu ba.....don ita kanta wadda ta bamu aikin me kudin kanta ce....kuma tana da nata ikon da ko kamamu kukayi din a dole zaku sakemu". "Au Allah?,amma ta kasa baku kudi wadatattun da zaku rayu?,saita hadaku da aikin wahala aikin kidnapping?". "Bayau muka fara mata aiki ba.....kuma wannan bazai zama na qarshe ba,ko ta bamu ko bata bamu ba sana'a mukeyi,kuma ba zamu fasa ba...koda ita ko babu". "Koda ita ko babu din kuwa daga wannan karon ba zaku sake zaluntar kowa ba.....daga wannan lokacin kun daina aikin ashshsha" "Kaga dakata malam!" Ya daka tsawa daga daya bangaren,tsawar da har sai data sanya fuad lumshe idonsa sannan ya budeshi,yana ji a ransa inama ce gaba da gaba suke da wadannan qananun 'yan iskan. "Bama doguwar hira da kowa faruqu kake ko wa?,kuma ba zamu fara a kanka ba.......ka kawo kudi ko qarawa qanwarka tsahon kwana....ko kaqi muyi kaca kaca da namanta kaman yadda hajiyarmu ta buqata daga nan zuwa wayewar gari" "Kuyi duk yadda kukeso" Ya fadi yana tsinke kiran don ya kwashi mintunan da yakeso. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 147 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 147 "Ya zakace musu haka?,ya zakayi haka hamma?" Sabreen data barke da kuka cikin rawar jiki ta furta,sabreen din da baisan da zamanta a wajen ba sai a sannan. "Ba zasu aikata ba.....kudi sukeso,sunsan kuma kudi ba zasu karbu ba muddin suka tabata......sai hajiyar da....." Cak ya dakata da maganar yana nanata sunan hajiyarsu da suke fadi. "Hajiyarsu.....kasan wacece hajiyarsu?" Sabreen ta fada tana miqewa tsaye cikin wani birkitaccen yanayi. Gaba daya ji takeyi tayi loosing duk wani control nata da tunaninta......tana jin komai yazo qarshe,komai yazo gaba.....tana jin ko na minti daya ba zata sake iya ci gaba da rufe sirrin matar nan ba,duk wani signal ya kama ya kuma nuna kanshi......sannan ya bayyanar da komai da komai. "Nace kasan wace hajiya suke magana akai?" Ta maimaita tana ware hannayenta gami da fiddo idanunta waje kaman wadda ta zare. Bata jira amsarsa ba ta dora. "Ba kowa bace sai MAAMAH!" ta fada da wata irin tsawa da bata tashi tarwatsewa ba sai a tsakiyar kunnen fuad da wani irin nau'in mafi munin sauti. Idanunsa da yakejin sun masa nauyi ya aza akan fuskar sabreen da wasu manya manyan alamun tambaya a kansu. "Maamah?" Ya maimaita sunan da salon tambaya. "Eh maamah.......maamah itce ya dauke amna.....maamah ita ta saka a dauke amnah!" Ta sake fada kuka me qarfi yana kubuce mata. Daga zaune da yake amma sai yaji kaman duniya tana zpagayawa ba daidai ba......kaman akwai wasu sautuka da abubuwa da suke tafiya ba daidai ba. "Kinsan me kike fada sabreen?....maamah fa?.....rashin imani da qeqashewar zuciyarta har......" Bata jirashi ya qarasa ba wani sashe na zuciyarta ya soma gaya mata cewa,kariya yakeson bata,qaryatata ita kuma yakeso yayi. "Abun nata baikai haka ba ko?,haka kake zato?.....kana ina sanda ta tursasamin aurenka don kawai ta mallakeka......ta tsundumani a rayuwarku don kawai na zama silar mallakarka gareta ta hanyar yin garkuwa da 'yan uwana......ta sanyani a kwanaki mafiya tsaho da tashin hankali a rayuwata?......kana ina a sanda ta sake diban qannena ta riqesu don ta samu damar cimma burinta a kanka da kaina......ta tirsasamin lallai saina shayar da kai na kuma ciyar dakai da asiri?.....na tufatar da jikina da rigar da zata zama silar soyayyarka a gareni?.mashkur......dama sauran wadanda suka kawowa rayuwarmu farmaki kina tunanin yin kansu ne?.....fareeda data samu nasara a kanka kana tunanin haka siddan ta sameta?......." Dora hannunta tayi saman matashin cikinta. "Hatta da wadannan yaran da basuzo duniya ba kana tunanin sun tsira a hannunta?,banda kiyayewar Allah zuwa yanzu lissafin watana nawa da barinsu akeyi.........ka duba wannan" Sai ta ciro wayarta daga handbag dinta tana bude masa inda ta adana videos dinnan da sauri sauri ta dangwarar masa ta juya da sassarfa tana fita a parlor din tana sauka qasa. Wayar yabi da kallo yana jin yadda jijiyar kansa ke wani irin harbawa. Yanajin kira na shigowa ta wayarsa dama system din gabansa,wanda ya tabbatar team dinsa da suke bincike tare ne suke kiran nasa,saidai baida wani kuzari ko kadan. Hannu ya sanya ya dauki wayartata,ya kuma bude video din da ta ajiye masa. Murya da komai ya fita tassss.....baya buqatar neman qarin bayani,sai kawai yayi connecting wayar da system dinsa,ya shiga aikin duba ingancinsa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Yaji yana maimaitawa bakinsa yana rawa. Duk da ya jima yana hasashe.....ya jima yana kwana yana kuma tashi da tarin tulin lissafin meye da meye maamah zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya ba?,amma sai ya samu kansa da jin komai sabo a tattare dashi.....sai ya samu kansa da jin komai ya zame masa baqo. Kaman wanda aka yiwa allurar qaimi,sai ya zabura,ya hada connection da kowa dake cikin team dinsa suka fara aiki akan kiran mutanen. Koda kowa ya gaji....koda kowa yana ganin dare yayi a barwa safiya,shi bayajin zai iya hakan......baya jin akwai abinda zai dakatar dashi daga lalubo maboyarsu daga daren nan zuwa asubahi......baya buqatar a wuce haka. Sanda ake qwala kiran assalatu na farko signal ya harba sosai,kai tsaye kuma ya basu daidai direction na inda network da layin yake motsawa. "Alhamdulillah" Ya furta yana zarar wayarsa da sauri. Jordan ya soma kira yace ya yiwa su abdulgafar magana......su hadu yanzun a masallaci zasu fita ana idar da sallar asubahin. Sai daya tabbatar ya gama hada komai sannna ya miqe yana nufar toilet. Yadda yakejin jikinsa kaman yana dab da kasa responding komai......amma ya gayawa kansa sai ya qarasa aikin daya fara,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka. Cikin baqin shirt da wando ya shirya,ya jawo wani boots dinsa ya saka yana dora baseball cap a kansa. Duk wani abu da zai buqata ya hada a back pack ya rataye,ya maida baqin eyeglasses a idanunsa sannan ya fara saukowa a gurguje. Har yakai parlor din farko wani abu ya fusgi zuciyarsa,sai ya koma da hanzari yana dosar dakunanta. Bai sameta asalin dakinta ba,sai a daki na biyu ya sameta. Qudundune ya sameta cikin duvet,da alama baccin me jima da saceta ba,don ga cups nan da plate da tayi amfani dashi da sauran ruwa. Har ya qarasa gabanta bata motsa ba,alamu sun nuna baccin daya dauketan me nauyi ne. Saman kanta ya tsaya yana duban kyakkywar Fuskarta,wani matsanancin tausayinta ya saukar masa,ya tsugunna a tausashe ya sauke mata kiss a goshinta don baiso ya tasheta,ya miqe a hankali ya maida hankalinsa ga dakin. Plates din ya soma tattarewa da cups din,murmushi ya kubce masa. Da gaske ciki yana canza hali da dabi'a,matar da daqyar sai yayi fama da ita take cin abinci,yau itace anywhere anyhow kama abinci take bada wasa ba. "Allah ya qara lafiya" Ya fada yana ficewa dasu ya kaisu kitchen sannna ya fice daga gidan. Cikin dukkanin shirin daya kamata suka gewaye area din kafin su sanya kai zuwa ainihin inda na'ura ke basu direction a kai. Cikin qasa da minti biyar suka nannade qofar gidan suka nadeta tsaf da wani irin qarfe. Sake kutsawa sukayi da wata irin sassarfa suna bada sanarwar suna qarqashin kamen hukuma,kada kuma wanda ya motsa a cikin su. Tun kafin sukai ga qarasowa ciki sukayi surrender,ba yau suka fara irin wannan aikin ba,saboda haka sun tabbatar da cewa sun riga sun kamu,tunda kuma suka kai ga cimmasu har inda suke lallai ba makawa basu da sauran wani qofa na fita. Qoqarin dakatar da fu'ad sukeyi wanda shine na gaba sanda yake qoqarin doke qofar dakin. "Sir......it may b......." Bai iya bari sun qarasa ba ya yiwa qofar wata Kyakkyawar duka data sanyata bude kanta da kanta. Bindigarsa ya saita akan mutum na farko dake tsaye kafin sauran suma su saita ragowan na dakin. Ya jima da koyar harbi da bindiga,ya kuma mallaketa da license dinta da komai saboda dalilai na tsaro,amma ba kowa bane yasan da hakan. "Kowa ya cire abinda yake jikinsa,bindiga ko wani qarfe ku zube a nan" Shugaban tawagar ya fada yana daka musu tsawa. Jordan ne ya soke tashi bindigar sannan ya fara zagayasu daya bayan daya cikin qaqqarfan takun nan nasa don tabbatar da kowa ya cire komai dake a jikinsa. "Hamma....." Muryar amna ta daki kunnensa da wani irin sauti galabaitacce. Idanunsa ya daga da zafin nama yana maidashi inda sautin yake. Amna ce ke takowa a hankali jiri yana kwasarta daga wani daki dake cikin babban dakin. Maida bindigarsa yayi da wani mugun zafin nama yana dosarta,wanda baikai ga isa ba qarar sautin bindiga ya tashi a dakin. Cikin tsarewar ubangiji ya bashi ikon kaucewa ya kuma ture amna ya wuce ya bula bango ya nutse a ciki. Cikin qasa da second biyu Jordan ya masa wani irin duka,ya kama hannuwansa ya murdesu ya maidasu baya ya karbi bindigar,sannan ya daki gwiwarsa ya zube a qasa. "Zakasan kayi mistake........idiot!" Jordan ya fada cikin tsananin fushi yana masa wani mummunan dauri. Amna ya daga da hannu bibbiyu,ya cire rigar daya dora daga saman rigarsa yana yafa mata saboda yadda take gayarta haka,ba dankwali bare mayafi. Wani irin zafi zuciyarsa takeyi,ya riqe amna da kyau suna takawa kafin ya kalli jordan "A yau nakeso su fadamin waye ya sanyasu wannan aikin,a yau basai gobe ba!" Ya fada da tsananin zafin zuciya. Yau din ta koma masa lovey dovey dinsa,ta koma masa amnansa sak ta shekarun baya,ta mance da wani surukuta a tsakaninsu,ta lafe kanta saman kafadarsa tana rera kuka. Ita kadai tasan ya takeji a zuciyarta da qirjinta,nata duka me sauqi ne,tana tausayin fu'ad ne a sanda sakamakon binciken ya fito sunan MAAMAH ya zama suna na farko cikin wadanda suka assasa dauketa. A baya wani tsoron matar takeji......a yanzun kuwa sai zuciyarta gaba daya ta qeqashe a kanta. Tayita kwanciya ne bayan ta farfado saboda tsoro,saboda tanason ta tsira da mutuncinta. Tana tsoron ta nuna musu ta warke batasan meye next step nasu ba. Maamah tayi waya dasu har sau ba adadi......taji kuma muryarta ta sake tabbatarwa da cewa tabbas din itace. Abun ya matuqar bata mamaki ita kanta,ya kuma girgizata. "Wacce irin zuciya ce a qirjinta?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance. Wani abu me zafi da tauri ya dinga hadiyewa,kai tsaye ya bada umarnin wucewa da amna asibiti don a duba lafiyarta. Kasa zama yayi ko tsaiwa waje daya,yana jin kaman ya sanya kai dakin da likitoci suka rufu a kanta suna checking dinta. Bashi da wani qwarin gwiwar sanarwa kowa an samu amna din har sai ya tabbatar da cikakken lafiyar amnan,har sai ya tabbatar da cewa ta kubuta da mutuncinta da lafiya da kuma cikakken hankalinta. A qalla sai da suka kwashe awa guda kafin su fito,cikin lallashi Dr aswad yace mishi. "Karka damu sir.....komai nata lafiya yake,ba wani abu daya sameta,saidai jikinta da yayi weakening saboda hodar cocaine da suka shaqa mata me yawa.......but shima idan tasha ruwa sosai jikinta zai koma normal in sha Allah". "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya maimaita yana jin zuciyarsa tana quntata. Cocaine kuma?,abar da yayi imani ko a ido aka ajiyewa amna ita ba zatace gata ba. Dakin ya koma,tana kwance tana bacci,ruwan da suka saka mata saboda samun qarin kuzari yana shiga jikinta. Wayarsa ya laluba ya fara kiran number abba. Daidai lokacin yake rufe shafin alqur'anisa,inda yakai qarshen suratu yaseen daya dauki gabarar karantata tunda abun ya faru sau wani adadi. Ya samu wannan sirrin daga bakin malam,wanda fu'ad ya raba kudi sosai aketa addu'a da kuma roqon Allah akai. Bismillah yayi sanda yaga kiran daga fu'ad ne. "Abba......an karbo amna,lafiyarta qalau alhamdulillah,amma muna asibitinmu tana dan shan drip saboda jikinta ba qwari" "Allahu akhbar......alhamdulillah.....tabbas ubangiji yayi gaskiya da yace ku roqeni zan amsa muku,Allah kaine abun godiya,sannu sa qoqari muhammadu.......inajin bazan shaida musu ba sai wannan drip din ya qare tukunna ta farka,ni zan taho,kafin sannan ina sanya ran qila ta farka". "Hakanma yayi abba" Ya furta yana katse kiran. Farouq ya kira da temporary line din da yake using nashi a kwana biyun. Kalamansa dukka irin na abban ne......saidai ya cika da mamakin abinda ya sanya fu'ad ya tunkari gagarumin aiki irin wannan bai gaya masa ba. "Ba lokaci dude.....na matsu na dawowa da anni autarta....besides ma waye zaiyi gangancin dauko ango ya sanyashi a hadari irin wannan bayan bai gama tantance ma zaqin duniyar daya shiga ba?" Murmushi ya sanya dole farouq din ya saki,sai ya yanke kiran shima murmushi yana subuce masa. Saidai kuma cikin qanqanin lokaci murmushin ya tsaya masa cak,yaji gabansa yana faduwa,sai ya sake lalubar number wayar CP. Dab da zata tsinke ya daga,yayi apologizing na fu'ad. "Ba komai.....nace zaiyuwu zuwa nan da azahar na zauna da dukka mutanen nan?". "Yes sir......zai yiwu,a gida ko a nan?". "If possible akaiminsu gida,zanwa abdulfattah waya ya bude musu masauki.....waccan dayar matar dake wancan gidan....me take da suna ma?" "Bibo ko.....habiba mu'azu" "Yes......itama a daukota,a hadamin ita a cikin su". "Okay in sha Allah" Ya fada suna yanke wayar. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 148 *_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽 *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂 Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾 wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 148 Ba jimawa sai ga abba,shigowarsa kenan farouq shima ya shigo,abinda ya sake zaunar dashi suna tattauna yadda abun ya kasance. "Amma don Allah me babban suna......zuwa yanzu ya kamata ka daina tunkarar abubuwa haka kai tsaye,bakai kadai bane yanzun kaman baya daka saba abunka gaba gadi,yanzun akwai nauyi akwai iyali da suka dogara dakai". "In sha Allah abba" Ya fada ne kawai,amma bayajin akwai wani abu da zai hanashi sadaukarwa da iyalinsa ranshi da lafiyarsa muddin yana raye din. Lokaci ya duba,bayason ya saba magana idan ya yita,don haka ya miqe yana duban abban. "Abba zanje gida....don sanda na fita tana bacci ne,yanzun haka nasan tana can da tunanin inda naje da kuma inda amna take" "Maza ka koma kayi mata albishir,ubangiji yayi muku albarka,ya kareku daga dukkan sharrin zamani.....ya tsare gaba" "Ameen abba" Sai ya juya ga farouq yana bashi hannu,shima bashi yayi sukayi musabaha suna duban juna,a tare a kuma lokaci daya murmushi ya subucewa kowannensu. Farouq ya gode Allah da abba yake a wajen,ya tabbatar da sai fu'ad ya taba masa iya shege komai qanqantarsa. "Ka gayawa su musaddiq saisu dauko anni tazo ta ganta itama hankalinta ya kwanta" "In sha Allah oga" Harara yadan balla masa,yasan da biyu ya fadi kalman oga din,sai ya juya yana fita a dakin. Tunda ta farka daga baccin takejin ta samu sassaucin qunci da bacin ran da takeji. Kai tsaye daga gadon kitchen ta wuce saboda yadda yunwar data tasheta a baccin ke neman sabautata. Koda ta duba agogo sai taga ashe ta zarta lokacinta ne. Tana cin abincin tana sake sallamawa lamarin ciki,tayi imanin banda cikin a yanayin da take ciki a yanzun ba abinda zai sanya ta iya sakawa cikinta abinci. Tsaf ta cinye ma'u na satar kallonta. "Ko a qara miki?" Kai ta girgiza. "Doughnuts dina kawai nakeso......ya qare ragowan na cinye yanzu da tea,don Allah ma'u ki sakamin order,kwali sha biyu nakeso" Ta fada tana goge hannunta da towel jikinta sam ba wani kuzari sannan ta juya tana fita a kitchen din ma'u ta bita da kallon mamaki. Eh dole ace ciki yana saka wasu hauka,batasan ya zatayi da doughnuts kwali goma sha biyu ba,doughnuts din matar da madarar ciki kawai ta isheka ta sanya kaji ka qoshi koda kuwa rabin guda daya kaci,ba qaramin jarumi bane wanda zai iya cinye guda uku ba,komai cinka kuwa idan har kaci ukun nan ba sauran space nacin wani abincin saboda ka gama qoshi. "Allah ya raba lafiya" Ma'u ta fada tana jawo waya ta soma lalubar number wayar maman ummee kada a samu akasi. Wata lafiyayyar kasala ta saukar mata,sai kawai ta yada zango saman sofa din falon. Zuciyarta na cike da mamakin yadda bataji motsinsa ba ko kadan......hakanan kuma bataga alamun ma ya nemeta ba. "Kodai da gaske yana shirin rejecting maganata da kuma qaryatani kaman yadda mamansa tasha shan alwashin hakance zata faru?" "Ga alama kuwa.....ya fara doubting akan abinda kika fada". Fada ne ya kacame tsakanin sassan zukatanta guda biyu,daga qarshe taja qaramin tsaki,ta jawo landline ta soma neman number gidan anni saboda tata wayar a hannunsa ta barta. Daya daga cikin masu aikin ce ta daga,cikin girmamawa ta gaida sabreen. "Hadani da huda ko.nadra ko haneefa" "Okay maa" Ta amsa mata a ladabce. Dukkaninsu ta kawo mata,suka bata lokaci sosai suna hira kafin suyi sallama. Daki ta koma donyin wanka,sai a sannan ta lura an kwashe duk wani datti kwanuka data zubar. Mamaki yadan kamata,amma saita samu assurance na shine ya shigo din ya fidda kayan. Tsaf ta gyare dakin,ta wadatashi da qamshi daya qarawa dakin wani irin sukuni da nutsuwa,sannan saita wuce tayi wanka. Tsaf ta shirya cikin wata chiffon gown maras nauyi,ta lalubo Malaysian hijab ta saka sannan ta fita. Kaman ba zata haura saman nashi ba amma ta daure. Tasan bai kamata ta barshi haka bata gyara ba,kaman yadda bai kamata ta bari wani ko wata su hau ba. Tsaiwa tayi tana qarewa parlor din kallo. Komai yana nan a zube inda yayi amfani dashi,da alama ma a nan parlor din ya kwana,saita taka tana tattareshi tsaf,ta kuma sanya vacuum cleaner ta tsaftace saman dukka ta gyare masa toilet din. Sanda ta gama azahar ta kawo jiki,cikinta kamar an mata yasa,dole ta sauko dining din qasa neman abinci. Tunda lalurar nan ta kamata ma'u ta haddace,bata taba barin dining din wayam ba komai,kaman yadda bata barinta ta dawo sake cin abinci ta samu maimaici. A nutse ta zauna ta zuba da nufin soma cin abincin amma kuma sai taji ta kasa. Azahar ta sako jiki sosai,ina yaje?,abunda tun fara shaquwarsu bai taba faruwa ba. Ta juya abincin har batasan sau nawa ba amma ta kasa kaiwa bakinta,kaman ahakan ake jira ya faru sallamarsa ya ratso parlor din. Duk da hautsine yake amma kallo daya tayi masa shigarta taji ta burgeta ta masa mugun kyau. Baqi da baqi a jikin fari,saidai duk da hakan saita wani basar ta dauke kanta tana amsa masa sallamar tan jira taga da wanne irin yanayi ya dawo gidan. Tsam ta miqe sanda taji alamun takowarsa nan dining din,ta tura kujerar tana nufin wucewa,saiji tayi anyi mata wata Kyakkyawar damqa na tare da bata lokaci ba kuma ya mata wata Kyakkyawar runguma da ta sanya qamshin turarensa mai matuqar sanya nutuswa isa ga hancinta. Saman wuyanta ya aje fuskar ta,kullum alfahari yake d wannan qamshin nata da yasha banban dana kowacce mace. "Kina bisa wuyana oum triplets......a yafemin,na leqo kina bacci,banaso kuma na katse wannan daddadan baccin nan.....yaya babies dina" Ya fada yana zamewa ya duqa a gabanta yana yaye rigarta. Maganganunsa daya saba yi da cikin nata yayi da nufin da yaransa yake magana,ta dauka zai tashi kaman yadda ya saba,sai kawai ya jawota yana tsokanarta ta cibiyarta. Janyewa tayi da sauri ya saki dariya.yana miqewa. "Anga amna" "Serious hamma....serous?" Girarshi ya dage mata,saita sauke ajiyar zuciya tana fadin "Alhamdulillah alhamdulillah.....please hamma" "Bani hug daya kawai ya isa tukucin yi miki albishir......tausar dare kuma itace tukucin kaiki wajenta" "Zanyi hamma zanyi wallahi" Ta fada tana dan qaramin tsalle. Riqeta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanunta,da wata muryarsa can qasan maqoshi yace. "Bi a hankali.....yarana" Ya qarasa fada yana dora hannunsa saman cikinta. Kunya ta kamata,ta kuma sanyata janye idanunta da sauri,daidai sanda kira ya shigo masa. Bai fasa sakata a jikinsa ya matseta ba sannan ya amsa wayar da cp ne ya.kirashi. "Thank you.....gani nan fitowa" Sai ya katse wayar yana dubanta. "Zanga baqi my world.....zan dawo shortly in sha Allah....ki kulamin da kanki" Ya fada yana kissing kuncinta duka biyun ya juya yana fita farfajiyar gidan. Daki ne yalwatacce da aka shimfideshi da lallausan carpet milk color kaman kalan labulayen dakin. Daga damansa bibo ce ita da zuwaira,sake maida dubansa yayi ga gabansa,mashkur ne shi da dan uwan tasa ta'asar.....mashkur din da gaba daya ya fita a hayyacinsa,tsufa sosai ya kamashi,wani irin tsufa na qarfi da yaji wanda wawulonsa ya sake tsananta munin abun. Sauran duka ya bisu da kallo,amma kowannensu munin fuskar mashkur ta zarta munin da yake gani a fuskokinsu,bawai muni na fuska kawai ba.....aaah muni na zuciya. Ma'aikatan gidan jaridar ya fara nunawa. "Wadannan na gama da case dinsu......aje a hadasu da diyar ambassador......ranar shiga kotu a hadosu tare qarqashin shari'a guda daya,lawyer na zaiji da komai". "Wayyo Allah.....mun shiga uku,don Allah sir kayi mana afuwa ka yafe mana,wallahi bamusan a kanka tace a buga labarin nan ba". Wani banzan kallo yayi masa. " Okay,idan wanine bani ba kenan zaku iya tozarta masa iyali,idan wani ne bani ba kenan zaku iya wulaqantashi ku wulaqanta aurensa da shaidar zur.....CP.....bana son sake jin muryarsa a nan wajen" Ya fada yana takawa ya jawo wata kujera. Kiiiii ya ajiyeta gaban bibo wadda jikinta ketsa tsuma,ya koma ya zauna sosai yana dora qafarsa daya kan daya. "Nutsu sosai.....labari zan baki sannan na sallameki". "To....to Allah yayi albarka". " Ameenatu ahmad sabreen takai budurcinta gidan mijinta,wanda ni Muhammed fuad jadda na karbeshi da kaina....kuma mutanen dake rayuwa damu suka shaida hakan a lokacin". Dif wuta ta daukewa bibo duk yadda takeji da tsageranci sai taji maganar ta girmeta. "Ke din uwace ko?,a kamatance bai dace na gaya miki haka ba ko?,saidai kash.....nidin bana yafiya bana kuma ragayya ga duk wanda yace zai taba rayuwar duniyata.....sabreen,a inda kuma aka samu akasi shine.....tuntuni kika sanya qafa kika take wannan girman daya kamata ki samu......to ina me!miki albishir.....sabreen takai bantenta......ba wani matsiyaci ko lusarin daya samu damar tsallake wannan shingen......yadda kika dinga yada jita jitan mutuniyar banza ce......na baki dama na biyu kisan yadda zaki wanke wannan sunan daga kanta....ki maida gurbinsa da kyakkyawar shaida,idan hakan bata kasance ba kuwa,a karo na biyu idan na daukoki batar dake zanyi bat.....a bude mata ta tafi gida". Bata tsaya tunani ko waiwayen tazarar nisar tafiyar da zatayi a qasa,ba tare da abun hawa ko kudin mota ba ta fice,tunda har ta samu nasarar shaqar iskar 'yanci kuwa......bataga abinda zai hanata hada lecture din wayar da kan al'ummarta kan muhimmancin mutuncin da sabreen ke dashi ba. Idanunsa ya ware akan mutum uku.....mutum ukun da yakejin laifinsu yafi na kowa girma,ya sake aza idanunsa akan zuwaira wadda daga ita har bibo sunyi wani zuzzurmawa. Duk da ajiya ce kawai akayi musu irin ajiyar da take daidai da aljannar kare. "Kamata yayi kema a hadaki da wadancan.....sashen manyan laifuka ko?..." Kuka ta fashe dashi tana hurwa tana neman agajinsa. "Ki rufen baki,don duk yadda raina yakai ga baci bazan iya zabgawa fuskar dakeda furfura mari ba,koda furfurar ta banza ce" Gum ta koma tayi sannna ya bude idonsa yana sake dubanta. "Kina gidana kina qarqashin inuwata amma kina neman hanyar da zaa shigo a keta haddin iyalina?!.....abu guda ya rage miki ki gayamin......waye ya sanyaki boyesu a dakinki kika fiddosu da dare zuwa sassan matata!!!". Wata bahaguwar tsawa daya sauke mata sai data tattara gudawa me yawa a cikin mashkur,ya rasa wanne.ibtila'i da bala'i ne yake hanashi furta masa sunan.matar kowa ma ya huta?,fatansa daya wannan tsohuwar ta kira sunanta,wataqila ko kwatance da ka yayi akan shima ita ta dauki.nauyinsa duk da akwai nasa shirin. "Mmm.......maamah ce" Sunan ya saukar masa cikin ba zata. Fuska ya yamutsa yana dubanta. "Wacce kenan?" "Hajiya maamah.....mariya mahaifiyarka" Komai ya tsaya masa na wasu daqiqu,sai daya koma daidai kuma kwanyarsa ta cika da wasi wasi. "Cp.....janye matar nan,a hadata da wadancan mutanen". Kallo daya ya yiwa mummunar fuskar mashkur,wadda ta jima da tashi daga kyakkyawa zuwa asalin mummuna. "Mariya ce nima!.....maamah ake ce mata" Ya fada da sarqaqqiyar muryarsa da bata fita yanzu tartar saboda fitar haqora sha biyar daga bakinsa. Kaman ya dauki takobi ya jefeshi dashi haka yaji,duk wani jini dake jikinsa yaji yana neman daskarewa,kwanyarsa kuma tana shirin yi masa formatting da karan kanta irin na kota kwana,saidai kiran wayarsa yaso maida komai muhallinsa,ya daga kiran bawai don yana gane waye ke kiran nasa ba yana komawa kaman wani shashasha. "Jordan ne sir.......sir an jona musu na'urar fidda bayanai cikin sauqi,sun kuma yi bayanin komai...." "Me aka samu?" Ya tambaya cikin sarewa da jin komai. "Am sir.....kayi haquri.....gaskiya bayanansu na qarshe kaman na'urar ta samu matsala.....sunce zaa sake bincikawa" "Jordan please tell me.....ka gayamin ko waye ya sanyasu.....bana buqatar jinkiri a daidai wannan lokacin". "Sir....sir" Sai ya kama inda inda. "Tell me nace!" Ya fada a tsawace. "Mariya......mariya ce maamah". Iya abinda fuad yaji kenan wayar ta sulale daga hannunsa ta fadi qasa. Bai sani ba......jijiyoyin hannunsa ne suka daina aiki yadda ya kamata ko kuma qwaqwalwarsa ce?!. Tashin hankali! Allah ka rabamu dashi! Me karatu sai ince muje mu qarasa Hugumanku ce Na gode *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 149 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 149 Kowacce gaba ta jikinsa sai yaji tayi wani irin sanyi,sai ya dinga jin kaman bashi da wani sauran damar ya motsa ko ya sakeyin kuzari a daidai wannan lokacin. "Mariya ce.....maaamah ce......itace" Sautukan suka dinga haduwa suna masa amsa kuwa a tsakiyar kansa. "Are you okay sir?" Muryar cp tayi kutse cikin tunaninsa,wanda yaga lokaci daya fu'ad din yanayinsa ya sauya,wuta kuma ta dauke masa. Da qyar ya iya daga idanunsa ya kalli cp saboda wani dan banzan ciwon kai daya saukar masa lokaci guda. "Yes.....am okay,akwai wadanda sukayi kidnapping 'yar alhaji hamza kibiya......za'a canzasu daga can inda suke a kawosu nan a hadesu......duk yadda ta kama ayi musu hukunci". " Ma sha Allah....sunzo.hannu kenan?" Kai ya jinjina masa kawai. Bayason doguwar magana sam sam,don shi kadai yasan yadda kansa yake masa wani irin bala'e'en ciwo,yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa da wani irin mahaukacin fushi da yake tsoron kada ya illatashi shi a karan kansa. Da zafi zafi ya fita a gurin,ya samu abdulgaffar suna tsaye suna dakon fitowarsa. Hannu kawai ya miqa masa "Bani key" Ya fada ba tare daya dubu abdulgaffar ba. Baki ya saki yana kallon boss din nashi,baisan meye haka da zafi ya tunzurashi ba ko kuma ya sauyashi. "Sir.....muje na kaika duk inda zaka je.....like kaman baka cikin mode din da za'a barka kayi driving". "Just give me the keys abdulgaffar.......ko mutuwa zanyi a hanya kana da asara?........wanda ya kawoni duniya ma bashi da asara ballantana kai!" Ya fada da wata irin tsawa data bashi matuqar mamaki. Salin alin ya miqa masa key din,saidai kuma ya yiwa sauran team nashi alama da ido,don haka fu'ad din yana tada motar yana fita suka bishi a baya cikin salon da bazai gane shi suke ba. Suna matuqar qaunarsa da kula da dukka abinda zai cutar dashi,suna matuqar jinsa a jiki irin kusa kusannan,suna jinsa tamkar wani babban yayansu da yake da ruwa da tsaki a rayuwarsu,inda suna da hali tabbas ba zasu bari ba ko quda me cutarwa ya sauka a kansa ba. Wani mahaukacin gudu yake zubawa wanda ya sake tabbatar musu da ba lafiya ba,hankalin abdulgaffar akan motar yana duban wanda ya bawa yayi driving. "Ka kula sosai,kada ka matsi bayansa da yawa kada kuma ka bari ya kufce mana" Ya fada yana gyara zaman Bluetooth din kunnensa yana magana da na motar baya. Shi kansa yasan gudun da yakeyi ya wuce qa'ida.......amma a irin zafi da bugun da tasa zuciyar takeyi sai yakejin ba wani gudu yake ba shi din. Idanunsa fes bisa kwalta amma tunaninsa yayi nesa sa gangar jikinsa. Baisan kuka yakeyi ba saida yaji iska na fifita hawayen daya silmiyo masa,karon farko tun bayan tafiyarta ta barsu.....karon farko tun bayan wasu shekaru masu yawan gaske da ya share wani abu bai sakashi kuka ba......a yau a zagaye na biyu ta sake zama silar kukanshi. Hannunsa daya ya saki dava steering din,ya shafo hawayen yana kallon su,a wannan lokaci yana jin ta gama sanyashi kuka......yayi kuka qarshe a rayuwarsa saboda ita. Tsananin kunyar anni da abba yakeji,da wanne idanu zai kallesu ya shaida musu mahaifiyarsa ce ta aikata ma diyar cikinsu autarsu haka?,da wanne bakin zai musu bayani?,wanne shine kalar sakayyar da suka cancanci su samu makwafin alkhairin da sukayi mata?. Wani birkitaccen parking yayi qofar gidan,parking din da ya tada qura,ya kuma ja hankalin malam sa'adu dake zaune daga cikin gidan a bakin qofa yana jan tasbaha. Da sassarfa yake takun nasa,kaman me gaggawar cimma wani abun. Security na farko ne ya hangoshi,ya kuma taso ya bude masa da sauri kafin yakai ga qarasowa. Kusan ba sosai yake gani ba,fatansa kawai ya cimmata......fatansa kawai ya isa gareta......ya kuma tambayeta dukka akan me?,me yasa?. Da sauri me aikinta dake saukowa daga samanta taja baya tana zubewa sanda taga shigowarsa. "Barka da warhaka yallabai?" Sam ba gaisuwarta bace damuwarsa,bai kuma damu ya amsa ba "Tana ina?" Ya tambayeta kai tsaye yana jin jikinsa ko ina yana rawa. "Tana sama" Ta amsa masa tana rabewa ganin yadda ya nufo saman da sauri bata ko dire statement dinta ba. Matakala bibbiyu ya dinga hadawa har Allah ya kaishi saman. Dab da matakalar qarshe sautin muryarta ya sauka a kunnensa. "Ta yaya akayi saken da har wani yasan inda suka boyeta.....wanne irin hauka ne wannan?,baisan muhimmancin yarinyar nan a hannuna ba?,subucewarta da kuma kamasun da akayi yasan irin asarar da zai jawomin?.....bani da haufi akan zasu iya fadar sunana......duk da boka baiyi aiki a kansu ba amma kudin dana musu alqawari da alqawarin dana musu akan koda tsautsayi ta gifta zan fiddasu....iya wannan bazai bari su fadi sunana ba" Ta furta cikin bawa kanta tabbaci da yaqini da gaibu da qaryar daka iya fidda bawa daga ainihin imaninsa. Wani abune ya fusgeshi sosai,da sassarfar data jawo hankalinta daga wayar da takeyi. Wani irin duba take masa me cike da tsoro da kokwanton ya jita ko bai jita ba?,zuciyarta gaba daya ta kasa bata nutsuwar bai jita din ba saboda wani irin kallo dake fita daga idanuwan da suka sauya launi suka jirkice,daga fararen qwayar idanuwa zuwa kalar makuba kaman an diga jini. "Why maamah.....why amna?!" Ya furta da wani irin sauti me cike da razani mamaki dake cakude da karyewa yana wara hannuwansa da kuma watsasu kaman wanda yake dakon kama wani abu. Wani irin shock taji,wanda ya kusa sanya numfashinta dakatawa na wucin gadi. "Me yasa maamah?.....me yasa?,idan ni kinyimin.......d'anki ne.....idan kin yiwa musaddiq.......d'anki ne......amma amnah fa?!" Ya fada da wata irin murya dake neman fara rawa saboda tsananin sarewa da dukkan komai,ya kuma qarasa maganar yana nuna waje da yatsarsa. "Me amna ta aikata maamah.....meye laifinta?" Ya kuma fada da yanayin mutumin da ya soma zarewa. "Idan kika bada kai bori zai hau.....idan kuma baka iya kama barawo ba saishi ya kamaka" Wani sashe na rubabbiyar zuciyarta ya sake bijiro mata da wannan shawarar,shawarar data qarfafi dukkan gabbanta,ta soma qoqarin tattaro kowacce nutsuwa tata,sannan kuma ta hana kanta shiga d'imuwa. "Kai fu'ad.....kalleni nan da kyau,idan kana cin qasa ka kiyayi ta shuru....ni dinnan nice uwarka,baka da sama dani.....ohhhh,wato kaje an karanto maka abinda zakacemin da kalar rashin kunyar da zaka yimin.....dukka ameenatu ta yo maka katunsa shine zakazo ka saukemin?!" "Ameenatu ameenatu dai?,ameenatun da batayi miki komai ba face alkhairi?,ameenatun da ta rungumi yaran da kikaji cewa baki buqatarsu?,ameenatun data yarda ta zauna ta kashe tata rayuwar saboda ta 'ya'yan da kika watsarwa duniya?,akwai wani alkhairi sama da wannan?,akwaishi......wata can daban tayi abinda uwa ta gaza yi?,wata can daban tayi abinda uwa take ganin ya zame mata babban aiki?" Ya qarasa fada yana zuba mata ido,qirjinsa yana sama da qasa yana jin kamar ciwon zuciya ne yake shirin kamashi. "Kin dawo kin sake kashemu a karo na biyu bayan wancan kisan da kika yiwa rayuwarmu.......me mukayi miki haka?,laifinmu ne da kika haifemu alhalin baki buqatarmu?" Ya fada a tausashe da wani irin rauni daya sanya idanunsa fitar hawaye "Daga kowanne bangare......cikin binciken kowanne laifi Maamah dai mahaifiyar fu'ad?,mahaifiyarsa?.....maamah dai?,wadda tayi silar zuwansa duniya?,maamahn ita ta dauke amna?,amna diya ga hamza kibiya?,mutumin daya zame musu uba......bango madafarsu?,ya tallafesu a sanda duniya tayi watsi dasu,ya rungumesu,a sanda ita da take Mazaunin uwar data kawosu duniya ta sanya qafa tayi wancakali dasu?.....ya rungumi farincikinsu da baqincikinsu?,ya rabu da duk wanda zaice baya sonsu?,ya qara zafin nemansa saboda su.......yayi musu riga yayi musu wando?,yayi kawar da dauda da duhun jahilci daga qwaqwalensu?,ya daga darajarsu a idanun duniya ta hanyar haskasu da hasken ilimi?,ya maidasu mutane ta hanyar basu ilimin addinin islama?,ya karbesu a matsayin 'ya'yan da shine yayi silar zuwansu duniya bawai uban riqo ba?,yayi musu gatan da ko 'ya'yan cikinsa bai musu ba?.....amnan dai itace d'iya ga ameenatu......ameenatun data dawowa auren hamza saboda yaran?,ameenatun data sadaukar da duk wata kulawa da lokacinta akan yaran?,ameenatun da bata yarda da wani abu me cutarwa ya rabesu ba?,ameenatun da idan kanaso kaga farincikinta.....ko kaga kirkinta ka yabi musaddiq.......ka yabi fu'ad......idan kanaso ku bata alaqarku taja baya ka zagesu ko ka kushesu.....ameenatun da ta sadaukar da lafiyarta saboda su su rayu cikin aminci?,taqi kwanciya ta huta sabodasu?,taqi ci saboda saboda basuci ba?,taqi sha saboda basu sha ba?......" Ya sake tsayawa saboda yadda numfashi ke masa wahalar shaqa. "Laifin ameenatu rainon 'ya'yanki da tayi......laifin ameenatu inganta rayuwar 'ya'yanki.....idan duka haka ne ita kuma SABREEEN FA?!". Wannan tambayar daya jefa mata tafi kowacce gigitata. Sabreen?,ya tabbata ta qarasa bude mata aiki kenan kaman yadda taci alwashi?. "Ni na kawota rayuwarka.....kuma a yanzu bani da buqatar kasancewarku......na nuna maka ta dukka hanyar data kamata amma saboda banda kima da martaba a idanunka ka gagara fahimta". "Sai hakan yanzama license ya zama halaccin da zaki tura wani d'a namiji gidan aurenta.......dakin da d'anki ya gina saboda matarsa ta sunnah?.....yaje ya keta hurumin ubangiji?,.......kin auramin sabreen saboda ki.mallaki fu'ad......fu'ad din da bai mallaki wuta ko aljanna ba......fu'ad din da bai mallaki rayuwa ko mutuwa ba.......bai mallaki komai ba face wata aba da ake kira DUKIYA wadda ka iya zama fitina da jarrabawa ga bawa.......". Yana kaiwa qarshe ya jawo littafi da abun rubutun daya gani ajiye a gefe,ya jawo side table ya ajiye a tsakaninsu ya daga idonsa yana kallonta duba na kai tsaye. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 150 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 150 "Na baki dama......daga farkon littafin nan har bangonsa ki rubuta adadin kudin da kikeso......na baki dama ki rubuta adadin alatun rayuwar da kikeso......na baki dama ki rubuta tsarin rayuwarki na shekaru dari nan gaba idan har zaki kai sannan......ni kuma zan tabbatar miki da wannan mafarkin,muddin zaki zare kanki daga rayuwarmu.......muddin zaki fita salin alin daga rayuwarmu......muddin zakiyi nesa da rayuwarmu......indai kin amince zaki bar iyalin ameenatu su rayu cikin salama su kuma zauna lafiya........ina fada miki hakanne cikin harshe na girmamawa.......ina gaya miki hakanne saboda har yanzu sunanki MAHAIFIYARMU.......Duk da girman abubuwan da kika aikatawa mutanen da basuji ba basu gani ba......ina gaya miki wannan zabinne saboda shine zaifi mana sauqi mu dake" Ya qarasa maganar yana jin wani mulmulallen dutsen wuta yana tsaya masa tsakanin wuyansa da qirjinsa yana qoqarin turashi da qyar. Fata yakeyi inama ace wani ko wata ce can daban suka aikata musu wannan abun ba maamah ba?......inama ace wasu mutanen ne daban keda alhakin dukka wadannan abubuwan ba maamah ba?,ya rantse da Allah da sai ya ganar dashi kuskuren bari da yayi uwarsa ta haifesa zuwa gidan duniyar ma gaba daya. "Fu'ad!.....ni kake gayawa wannan maganar?,ni kake cewa zaka rabu dani saboda ameenatu?" Ta tambaya tana jin wani irin tashin hankalin jahiltar matsayin ameenatu da tayi a baya. Ashe har zai iya katse alaqar uwa tsakaninsu saboda ameenatun dai?. "Fu'ad!.....ka saurareni da kyau!......." "Jaffal qalam" Ya fada yana miqewa daga gabanta. Zuciya da shaidan dukka suna kusa,duk sanda zai kalli fuskarta fuskar mahaifinsa yake kalla a tayi watsi dashi cikin tsananin ciwo bayan ta gama illatawa luguiguita lafiyarsa cikin mugunta.......duk sanda zai kalleta saiya tuna sanda take cida Mahaifinsu da abubuwan da aka hanashi ci ko sha saboda hakan zai iya zama sanadin komai.....ciki harda MUTUWARSA.......duk sanda ya kalleta saiya tuna sanda JADDA ta mutu saman cinyarsu saboda rashin gata suka kwana da gawarta ba wanda ya ko leqosu sai bayan wayewar gari......duk sanda ya kalli fuskarta sai ya tuna sanda musaddiq ke kwana yana kuka harda shidewa cikin kewa da qauna yana kiran sunanta.....burinsa shine kawai ya ganta......har yanzu kunnuwansa sun gaza manta yadda aka saka abun rushe gini ake dukan ginin gidan da mahaifinsu ya wahala da dukka qarfinsa ya ginashi don su rayu a ciki......ta badashi a mazaunin jingina ta karbi kudaden ta nausa zuwa duniya "Wannan dama ce a wajenki cikin girmamawa da kuma baki abinda kiketa harin mallaka din tsahon shekaru kina fadi tashi.....ki rubuta!....ki rubuta!!.....ki rubuta!!!!....ki gayyato wasu ma su tayaki rubutun?!!!,wannan damar ce kawai ta rage......'yanci muke nema!!!!,yanci muke buqata....." Sai ya hade hannayensa alamun roqo "A wannan karon da kanmu muke roqarki ki tafi ki barmu kaman yadda kikayi a baya". Sai ya fara tafiya da baya da baya idanunshi a kanta yana barin falon. Irin kallon da ya jima baiyi mata irinsa ba. Ya dade rabon daya sanya idonsa cikin nata,ya dade rabon daya iya daga kai ya dubeta,tana hango abubuwa da yawa cikin idanunsa. "Idan kika rubuta hakan yana bawa ameenatu tabbacin kinbar mata su dama dukkan wata dama ko matsayi da zasu sake takawa a gaba.....kinbar mata su da dukka wani arziqi da zai sake habaka nasu......kinbar mata dukkan wata alfarma ta amsa sunan UWAR ME JADDA har abada......iya abinda kika samu daman rubutawa shine kawai naki rabon har abada.....baki da wani sauran dama ko rabo a jikinsu saidai idan sun rigaki MUTUWA" Maganar da shaidaniyar zuciyarta ke gaya mata kenan sanda yake dab da fita a falon,abinda ya sanyata zabura ta miqe,sai wani irin jiri ya taso mata,amma cikin tsananin taurin rai dana zuciya ta cije ta kuma soma takawa tana binsa da hanzari gami da qwalla kiran sunansa. Turus yayi ya tsaya gaban gate din gidan yana kallon tarin 'yan press da suka cika qofar gidan maqil. "Da gaske ne kenan yallabai.....mamarka itace tayi kidnapping d'iyar alhaji hamza kibiya dake kwance a asibiti a yanzu tana jinya?,yanzu haka ma akwai d'iyar qawarta a cikin gidan nan da tayi!kidnapping nata tsahon watanni ba'a sani ba me suna laila?" . Wani abu yaji yana neman kayar dashi,abu daya ya saka masa sassauci ganin yadda dukkaninsu suka sauke cameras dinsu a kanshi cikin nuna masa girmamawa. Kasa magana yayi cikin tsananin mamakin yadda akayi!maganan ya fita?,waye kuma ya gayyatosu?,amsar da ya sameta kai tsaye daga bakin wani dan jarida. "Mun samu half details na cikakken labarin daga wajen aminiyarta hajja harira......ta kuma bamu tabbacin zamu samu full din daga bakin hajiya mariya ahmad" Ya qarashe fadi sanda maamah ki fitowa da sassarfa tana qwala kiran sunan fu'ad din. Waiwayawa yayi ya zube idanunsa a kanta a sanda sam bata lura da taron da dama ita suke kwadayin gani ba.....malam sa'adu ya tsaidasu da qyar ba,sai kawai ya dauke kanshi ya kuma dubesu da dakakkiyar muryarsannan dake qara masa kwarjini,wadda a yau take cakude da bacin rai yace. "Ku bani hanya....bani keda labarin ba". Tsakiya suka buda masa ya fara wucewa da sassarfa,bayajin akwai wani abu da zaiyi mata.....ba wani abu da yayi saura da zai iyayi mata shi "Fu'ad......a matsayina na mahaifiyarka ina me baka umarnin........" "Yauwa.....shikenan ma.....gata nan ta fito" Yaji muryoyin wasu a cikin su suna fadi gami da kunna cameras dinsu suka saitasu sannan sukayi kanta. "Kada ki damu,wataqila sun soma fahimtar kece mahaifiya ga fu'ad din.....girman ya fara dawo miki,wataqila ameenatu ta sallama ne" Wata zuciyar ta gaya mata,don haka ta dake tana dubansu sanda suke yowa kanta yuuu. "Ranki ya dade......samun tabbaci da neman sahihancin rahotanni yasa mukazo gareki.....da gaske kece mahaifiyar muhammad fu'ad jadda?.....mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources?" . Wani murmushin alfahari ya kubce mata,murmushin da ya dusashe duk wani bacin rai da tashin hankalin data tsinci kanta yanzu yanzu a cikinsa. "Qwarai da gaske.....nice" "Ma sha Allah......kina tare da laila d'iyar qawarki kenan?". Da farko tambayar ta mata banbarakwai,amma zuciya batan basira da neman suna suka gina mata tunanin wataqila suna kallon ita din uwar kowa ce da take riqon yara turmus,don haka ta daga kanta kawai tana cewa. "Eh haka ne". "Yauwa.....mun samu cikakken labarin qawancenku......yadda kikayi silar hada auren d'anki da matarsa ta yanzu sabreen da dukkan wasu hujjoji na riqe qannenta a bisa cikar wannan buri naki.....kidnapping diyar alhaji hamza da kidnapping tata d'iyar wato laila da a yanzu kika bamu tabbacin kuna tare....". Wani jibgigen abu ne taji ya saukar mata tsakiyar kanta wanda ya sanya numfashinta yaso riqewa iya wuyanta. Ita hajja zata yiwa haka?,ita hajja zata wulaqanta?,ita hajja zata jajibowa taron manema labarai?,ita hajja zata tonawa asiri?,ya akayi ta manta da ita bata sanyata mutum ta uku daya kamata ta shafe labarin su ba,me yasa bata b'atar da ita ba?,me yasa ta barta taci gaba da shaqar iskar 'yanci?. Juyawa tayi kawai don komawa ciki,saboda tana jin bai kamata tace komai ba gudun tonuwar asirinta gaba daya wanda ta fahimci fiye da rabinsa ya yaye. "Ranki ya dade ya zaki koma kuma?" Zaqaqurin dan jaridar ya fada. Waiwayowa tayi ta zube masa wani kallo. "Ni ba uwar qaramin mutum bace,bani da lokacin magana daku kai tsaye haka.....idan ka matsa kuma kasan waye d'ana,ba aikinka kawai zaka rasa ba.....har....." Sai kuma ta dakata tana kwabar kanta duba da irin cameras din dake fuskantarta. Kallon kallon suka farayi tsakaninsu,don kowa da abinda ransa ke raya masa da yanke maganar da tayi bata qarasa ba. Ganin ta dauke musu wuta gaba dayansu saita taka tana komawa ciki cikin jan qaqqarfan tsaki. "Akwai batun aika b'ata gari da kikayi gidansa don yiwa matarsa fyade da sunan baki sonta.......wannan batun gaskiya ne?". Wani irin suka maganar tayi mata a qirjinta,har batasan sanda ta saka hannu ta dafe saitin zuciyarta ba. Haki ta soma yi tana jin kamar qafafunta ba zasu dauke ta ba,dole ta fara kiran sunan laila saboda tasan duk 'yan aikinta yau basunan cikin mancewa da tarin 'yan jaridar da suke neman tabbacin lailan tana tare da ita kaman yadda cikin rashin sani ta basu tabbacin. Kome takeyi,komai girman bacci ko uzurinta muddin maamah ta kirata saita bar komai. Kaman yanzun da take zaman cin abinci haka ta watsar dashi ta kwaso da gudu. Fitowar tata ta sake maida hankalin mutane kan laila din da dukkanin kamanninta da hajja harira da suka fito. "Lafiya maamah?,me sukayi miki?,me ya faru?". "Kamani muje ciki" Ta bata umarni a tsawace,abinda ya sanyata kamata dukka jikinta suna rawa. "Da gaske kece diyar hajja harira?" Wata cikin su tayi caraf ta jefa mata tambayar sunason tabbatar da maganar juya mata hankali da sukayi. "Eh 'yarta ce......amma yanzun daidai nake da baiwa wajen maamah......yadda takeso take buqata haka zanyi,koda ya kama na rabu da ita hariran" "Ke laila kama bakinki mu wuce ciki!" Maamah ta fada da hanzari gudun kada tsananin mallaka ya sanyata nunawa duniya abinda zai sake zame mata abun fada. "Laaaaa haila ha'illallahu.....muhammadurrasulillahi" D'aya daga cikin mata 'yan jarida dake wajen ta kasa daurewa abinda ya farun ta saki kuka tana tafa hannu. "Wallahi 'yar hajja harira ce,da gaske ne,da gaske aikin juyar da hankali tayi mata bayan tayi kidnapping nata......da gaske ne,gashinan diya tana neman mancewa da uwarta?" Wannan kalaman sun sauka daidai kunnen maamah,wanda hakan ya sanyata runtse ido,tsananin jin zafin hajja yana sake ratsata tare da alwashin daukan fansa a tare da ita. "Ki gayawa malam sa'adu ya fidda mutanen nan,idan ba haka ba zai fuskanci fushi na" Umarnin data bawa laila kenan,ta kuma saka kunne tana jiran daina jiyo hayaniyarsu daga nan inda take. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 151 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 151 Tsahon mintuna talatin ta sauke idonta akan takardar da fu'ad ya ajiye mata,ta zubawa littafin idanu tana lissafa adadin yawan shafukan da yake dasu. Ya fadi cewa zata iya cika littafin harma ta qaro wani....tayita rubuta dukkanin abinda takeso.......wannna babbar dama ce a gareta kenan na zama Mulitibillonier?. Murmushi ta saki ta soma yunqurin daga hannunta ta miqashi don dauko littafin,amma abun mamaki sai taji hakan ya gagara. Ta sake yunqurawa a karo na biyu da zummar gwada daukar nan ma shuru ne hannun yaqi sarrafuwa. A zabure ta maida dubanta ga hannun nata cikin wani irin kidima da dimuwa tana kallonsa. Hannunta ne dai......hannunta ne data sani shekara da shekaru......hannunta ne da ba wani abu daya canzashi.........amma meye ya kawo qin daguwarsa?. A karo na uku ta tattaro dukkanin qarfinta zata dagashi ya sake motsuwa koda wasa,a birkice ta maida hankalinta kan daya hannun tana qoqarin motsashi shima. Still shima abinda dan uwansa yayi shi yayi mata. Matuqar qololuwar tashin hankali taji ta shigeta,wani irin mahaukacin gumi ya yanke mata. "Me hakan yake nufi kenan?,wani ne yayi min asiri?,ko wani ne yayi min tsafi?" Ta tambayi kanta da kanta. "Kai inaaaa.....a irin wannan lokacin?,a lokacin da dama tazomin?" Ta sake tambayar kanta a fili kaman wata tababbiya. "Bazai yuwu ba" Ta fada tana qoqarin miqewa don ta gani ko qafafunta suna aiki?. Miqewar datayi aniya jikinta ya gaya mata bashi da wani sauran motsi me qarfi,qafafun suma suka shaida mata basu da wani sauran qarfin da zasu dauki nauyin gangar jikinta ta hanyar warbar da ita ta zube a qasa tana kifawa saman fuskarta. Wani irin matsanancin ciwon kai yakeji,wani irin yanayi da yakejin kamar jikinsa yana dab da gazawa. Yana dafe da kanshi tsahon mintunan da suka dauka suna tafiya a motar,har zuwa sanda ya buda bakinsa a hankali yayi magana da driver din "Badawa zaka kaini......ba gida ba" A yanzun ba abinda yafi buqata irin ya kebe,so yake ya kebe shi daya,bayason magana da kowa bayason kuma hayaniya. Karya kan motar yayi suna komawa daya hannun. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu m,already yasan gidan,gida ne madaidaici daga waje,saidai kuma daga cikin yana da yalwa da wani irin yanayi da aka tsara me tsananin burgewa. Yakan jima baizo gidan ba,yana ma mantawa dashi sau tari,saidai duk sanda yake buqatar ya kebe ko ya huta a nan din yake zama har zuwa sanda ya gamsu da yanayinsa ya koma normal mode dinsa. Tun a parlor din ya zube,karo na farko da yaji yana buqatar yayi kuka,karo na farko da ya buraci inama ace shi din yana cikin sahun mutanen da hawaye ke fita a fuskarsu da wurwuri?. Hawaye yake da buqatar ya zubar sosai saboda qirjinsa dama zuciyarsa sun gaji da daukan abinda suke dauka din. Koda zai iya hana kanshi fitar dasu to ba a irin wannan lokacin ba,a yanzun kuka yafi buqatar yayi bawai yaci gaba da nuna jarumtarsa ba. "Astagfirullah ya Allah......astagfirullah" Shine abinda labbansa dake motsawa suke maimaitawa yana jin yadda qirjinsa ke sake suya idanunsa suna sake d'aurewa da wani irin zafi da kuma radadi. Wani sabon babi ya bude na tariyar rayuwarsu,tun daga sanda ya bude idanunsa ya zama mutum cikakke zuwa yanzu. Bai tsinci komai tattare da maamah ba banda haihuwarsu da tayi......ko a sanda take rayuwa tare dasu,yadda take mu'amala dasu haihuwarsu ta zame mata kaman wani nauyi wahala ko dawainiya.....abbansu kusan shine komai nasu......abbansu shine duk wata wahala da dawainiya tasu,abbansu shine wankansu abincinsu,shirin makarantarsu da komai na dawainiya......yayi a gida ya fita yayi a waje ya kawo musu. Zuwa yanzu baisan sadaqaul jariya na abubuwa daban daban dubu million nawa yayi saboda shi ba......yana fatan ko a ina yake ya bishi cike da samun salama cikin kabarinsa da rayuwarsa ta barzahu. Da taimakon ambaton sunan Allah da yakeyi ya samu nutsuwa ta fara dawo masa. Yayi amfani da wannan damar ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala. Dawowa yayi ya kunna ya kunna TV din dake kashe,ya lalubi tashar saudi qur'an ya qaro volume din ya karade parlor din gaba daya. Cikin kujera ya nutse,idanunsa a lumshe yana sauraren karatun gami da bin ayoyin tare da shaik abdurrahman assudais. Yana karatun yana fahimtar ma'anar ayoyin,abinda ya sake taimakawa wajen bawa zuciyarsa da ruhinsa nutsuwa. A nan gurin yayi sallar la'asar,magariba ma ta ruskeshi duka ba tare da ya sani ba. Itama magrib din a nan yayita,ya jima saman abun sallah yana addu'o'i har baisan adadin lokutan daya shafe ba,yadai duba ya tarar da lokacin isha'i har ya shiga. Isha'i dince ya fita a daddafe zuwa masallacin dake cikin layin cikin shiga ta bad da kama,baya son kowa ya tsaidashi don bazai iya dogon magana ba. Ana idarwa ya taso shida jordan sukayo gida,jordan din ya dan dubeshi cikin matuqar jin tausayinsa qauna da kuma kulawa. "Sir......ko za'a aika a karba maka abinci gurin madam?,if not a maka order daga wani eatery din?". Kai ya girgiza,a halin yanzu bayajin yunwa,still kuma bayaso ma sabreen ta ganshi a yanayin da yake ciki. Tashin hankalin da take fuskanta ita kanta yayi yawa,tunda ta dauki cikin nan bata huta ba,tana stressing kanta da yawa akan duk abinda ya shafeshi......is over,ya kamata ta huta hakanan,ya kamata ta samu peace of mind......yana shawarwarin yin nesa da ita har sai abubuwa sun lafa,shi kansa yana jin zaya dauki hutu har sai komai ya koma daidai. "Sakamin order lite abu please" Yace da jordan din yana wucewa cikin gidan. Saman sofa ya zauna,ya dauki wayarsa dake yashe a wajen wadda sam yama mance da ita. Saqonni da miscalls rututu,amma duka na sabreen din yafi yawa. Ya saki dan qaramin murmushi bayan ya gama karanta wani saqonta na qarshe.....finally ya samu wata kyakkyawar zuciya data damu dashi da gasken gaske,finally ya samu wani ruhi dake craving for him.......finally ya samu wannan madadin da yake qishirwar samu. _"na kiraka na maka saqo har sau babu adadi amma babu guda daya daka amsamin.....tom.....Even if you're ready to live without me,I'm not ready to let go,ko yaushe zan kasance a tare da kai,koda hakan baida tsada ko daraja a wajenka,bana saba alqawari,forever. Yours mom of triplet"_ Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar da saqon yayi masa. Wata soyayya ta musamman tana sake huda zuciyarsa,qaunar 'yan tayi guda uku dake kwance a cikinta suna sake lullubeshi. _You're the missing piece that makes me whole,without you,life wouldn't be the same,forever with you is where i want to be.....you're my forever adda sabreen......am safe.....karki damu da yawa,ki bani aron wadannan awannin,zamu kasance tare da juna in sha Allah,ma'u zata kasance tare da ke,ayimin afuwa"_ sai kawai ya tura mata,yana buqatar isashen time da zaiyi healing daga nan zuwa safiya,bayaso ya jefata a damuwarsa,wadda batasan sadda ta samo asali ba,yana ganin kamar yin hakan rashin adalci ne kawai. Yanaso yaji muryarta shima......yana kewar wannan lallausan sound din nata wanda koda fada takeyi ko masifa laushinsa sai ya bayyana,but definitely idan taji muryarsa saita gane damuwarsa. Cikin taqaitaccen zaman kusa da kusa da sukayi da juna,yana mamakin yadda take da saurin karantarsa,sauyawarsa ko damuwarsa,walwalarsa ko akasinta. Abu daya daya sani shine baiwa ce,ba duk namiji Allah kewa baiwar mace me kula da dukka damuwarsa da matsalolinsa ba. Sauran kiran da saqon nasu farouq ne,duka sai ya share,saidai akwai saqo guda daya daya dauki hankalinsa. "Maamah is sick,she was admitted to the hospital" Idanunsa yaja ya lumshe,baisan me zaice ba?,me zaiyi?,sai kawai ya kashe wayar gaba days ya cillata gefe. Ya samu yaci abincin kadan,sai ya maida hankalinsa kan tataccen ruwan blood orange natural da aka hado masa dashi,da kuma wadatar kayan fruit,cherry pear jujube sai gooseberry da suka hado masa dashi. Dasu ya danyi fresh up,yadan jira abincin ya narke kadan sannan ya wuce bedroom Kai tsaye. Duk wani haske da komai da zai bashi sauti sai daya kasheshi,ya zamana daga zallarshi sai sautin alqur'ani da yake tashi kadan kadan ta wata qawatacciyar fitila dake tsakiyar gadon,wadda ke zuwa da qaramar fanka me bada sanyi kwatankwacin na ac da Bluetooth da zaka iya using nashi,sai ya kashe hasken fitilar dake jikin yabar iya sound din. Yayi lamo saman gadon kaman dazu yana bibiyar karatun,bai tashi gane kuskurenshi ba sai da bacci ya qauracewa idanunshi fafur. Juyi ya dinga yi saman gadon shi kadai yana jin yadda kadaicinta yake neman hallakashi,kowanne sashe a jikinsa sabreen din yake buqata,kowanne bangare na jikinsa kewarta yakeyi. "Ya salam ya al-hadi". Yana sawwara ta yadda zai iya yin nesa da ita dalilin tafiye tafiye na kasuwanci......ta yaya hakan zata yiwu?" Ya tambayi kansa da kansa. Daga qarshe dai ya tabbatar hakan bame yiwuwa bane,ya tashi zaune yana duba qaramin kyakkyawan agogon dake saman side drawers na gadon. "Oops" Ya furta yana dafe goshinsa,dare yayi,yayi imanin zai wahala idan bata fara bacci ba yanzun,idan kuma har ya zama silar tadata a baccin bazai yafewa kansa ba,sai ya maida kansa ya cusa tsakiyar pillow din yana qagara asuba tayi. ★Tunda ya dawo sallar asuba ya wuce gym,yana fatan hakan ya dawo masa da kuzarinsa daya rasa a kwanakin nan saboda tashe tashen hankulan da suka durfafoshi. Waya ya dauka kai tsaye ya kira Jordan ya bashi umarni ya koma gida ya dauko masa duniyarsa. Yana so nan din ya zame musu wani kebantaccen guri da ba kowa bane yasan da zamansa,da qwaqwalensu zasu huta na koda kwanaki uku ne kafin su koma cikin jama'a. Sanda ya kammala shiryawa cikin sassauqar shirt da trouser sai ya wuce parlor. Da kansa ya shiga kitchen ya tafasa madarar shanu fresh one da turmeric dan kadan ginger da cloves ya dawo falon yana sipping kadan kadan yana kamo tashoshin daya saba kalla a lokuta irin wadannan da ake labarai na qasa. Tashar farko cikin headline na news din hoton maamah ya gifta da anyo briefing na case dinta daga qasa. Zuciyarsa ta motsa tana bugawa da wani irin yanayi,sai kawai ya matsa remote din yana canza tasha. Channel din daya kama sun fara news tuni,the next abinda ya faru shima dai hoton maamah ne da title tafka tafka na zargin kidnapping.....wannan channel din sun samu nasarar saka wani d'an yanki na tambayoyin da 'yan press din sukayi mata a Farfajiyar gidanta,wanda kusan duk me hankali idan ya kalla yasan maganganu ne kama kai. "Subhanallah" Ya fadi yana sauke canza channel. Already su sun gama,saidai.maimaicin kanun labarai da shima hoton maamah dana hajja harira harma dana fareeda da suka cika screen din. A nan ma baida buqatar yaji komai,yasan tunda haka ta faru duk inda zai kunna ma abinda zasu nuna masa kenan tamkar sunsan yana da alaqa da ita. Wani zafi zuciyarsa ke mass,wani irin kud'a da quna take masa. Ya dauka ko meye maamah tayi....kuma ko meye akayi mata ba wani sauran abu daya rage da zai tada masa hankali a kanta ko ya qona masa rai,sai gashi bayyanarta a screen na TV dinsa yana neman hana mishi nutsuwa. Har addu'a yakeyi......har fata yakeyi ta zabi adadin abinda take buqata daga gareshin.....mutanen dake kewaye dashi a yanzun,mutanen da yake rayuwa dasu a yanzun suna da matuqar muhimmamci a tattare dashi,mutane ne da bayajin idan wani abu maras kyau ya samesu ta sanadinsa.....ko ta sanadin arziqinsa lallai ba shakka bazai yafewa kansa ba,bazai iya jurewa ya rasa koda rai guda daya a cikinsu ba. Koda maamah ta karbi abinda takeso ta koma inda ta fito,har kullum,muddin da numfashi a gangar jikinsa bazai fasa mata addu'a ta shiriya ba darajar haihuwarsu da tayi. Idanunsa basa wajen,amma tsaiwarta a bakin wajen yaji a jikinsa,don haka ya daga risunannun idanuwansa yana dubanta. Tayi wani irin kyau da shigar mutanen turkey,wasu irin riga da wando da dan hijab dinsu me suturce jiki. Ya sauke idanunsa akan cikinta,sai yaga kaman ya qara tasawa,kaman ya qara girma a kwana daya tak da yayi bai ganta ba. Wani sanyi da rahama yaji yana sauka a zuciyarsa,sai ya miqa mata hannuwansa yana lumshe idanunsa,abinda ya bata tabbacin lallai yana buqatarta kusa dashi. A nutse ta tako,wanda tun kafin ta iso inda yake qamshin nan nata,qamshin kabbasar nan tata ya soma kasheshi daga inda yake a zaunen(incense by kabo daughter....duniya ne sis,ki gwada ko sau daya,basai nace miki gobe ki koma ba,wannan tasted and trusted ne,bawai just normal tallan da bakasan ya kan abun yake ba(+234 803 211 9803). Kasa dauke idonsa yayi daga kanta saboda wani salon tafiya da takeyi da yake fusgar hankalinsa,har ya qagu ta qaraso inda yake ya shaqi ni'imtaccen qamshin nan da yakejin inama kowanne second da zai shude a rayuwarsa zai samu daman shaqarsa?. Kaman tasan da hakan,tana zuwa dab dashi saita cake ta tsaya,ta yamutse fuska,ta turo lips dinnan nata ta kuma juya masa qeya. Ya masa nisa ya tsaya tambayarta abinda ya faru,don haka kanshi tsaye ya miqe,ya taka ya zagayo gabanta. Tsaiwa yayi yana duban kyakkyawan fuskarta data soma nuna yanayi na masu ciki,yasa hannuwansa duka biyun ya kama kunnensa. "Na tuba......bazan qara ba" Kafadarta ta maqale. "Ni saidai kayimin tsallen kwado". "Done madam" Ya fada yana dan ja da baya still idanunsa a kanta. Hannuwan rigarsa ya tattare,ya durqusa a nutse ya tattare qafafuwan wandonshi,sannan yayi bismillah ya tsugunna ya fara. Da idanu take binsa,tanaso taga alamun ya gaji amma saita lura kaman ko a jikinsa. Bata rai tayi ta soma buga qafa. "Ni ban yarda ba Allah.....so nake ka gaji fa". Murmushi ya kubce masa,da gaske mata rigimammu ne,suna kuma rigimar da ba dalili,musamman masu juna biyu,don haka yana kaiwa qarshen bangon ya zube warwas yana numfarfashin qarya gami da jujjuya kanshi. Dariya dole ta kubce mata da abinda taga yana yi din,ta qarasa gabansa tana dan dukan qirjinsa a tausashe. "Wannan duka cuwa cuwa ne......kawai yi kayi kawai badon haka bane". Dariya me siririn sauti ya saki,sai kawai ya jawota jikinsa,yayi mata kyakkyawar runguma yana fadin. "Na gaji da wannan qwalelen da kikemin,qamshi duka ya buwayi hancina,amma kin hanamini jinsa yadda ya dace?,haka akeyi?" Ya qarasa fadi yana yaye hijabinta ya salubeshi ya wurgar gefe sannan ya cusa fuskarsa tsakanin wuyanta da qirjinta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 152 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 152 ★K'arfe goma da rabi na safe motocinsa suka shiga farfajiyar harabar asibitin. Shi da duniyarshi ne,wadda tayi kyau abinta cikin wata tsadajjiyar cotton lace lafaya me asalin tsada da taushi. Butter color ne da aka yiwa adon maroon da golden,wannan ya saka takalmi da handbag da earrings data sanya duka suka kasance maroon color,kalar daya zauna sosai a farar fatarta dake glowing saboda cikin dake manne a jikinta. Wani lafiyayyen yadi ne a jikinsa fari qal me taushi,wanda baida kauri ko nauyi ko kadan,hasalima kana iya hangen fara qal din vest din dake sanye a qasan rigar. Kusan komai nasa fari ne yau,hatta da takalmi da kuma agogon da yayi amfani dashi dukka farare ne,sai wata hula saman kanshi irin ta mutanen qasar Morocco wadda itama fara ce kaman kayan jikinsa. Tunda suka fito daga gida take satar kallonsa,ya mata wani irin fitinannen kyau kamar yau ta soma ganinsa,sun maidashi kamar wani jarumin fina finan india. Waiwayowa yayi gareta sanda motar ta qarasa tsayawa sai suka hada idanu. Ta janye lumsassun idanunta daga kanshi tana sauke boyayyen murmushi da wata 'yar kunya can cikin idanunta. "Sabrrr" Ya kirata a tausashe da wani kwantaccen sauti yana dubanta duk da data dauke fuskarta a wajen. "Na'am" Ta amsa masa ba tare data waiwayo ba. "Sabrrrr" Ya sake fadi yana jin shauqin kallonshi daya samu tana yi. "Na'am hamma" Ta sake amsa masa still ba tare data waiwayowa din ba. "Please mana sabrrr" Ya fadi a shagwabe har abinda ya fusgi hankalinta ta waiwayo tana sakin dariya. "Hamma shagwaba?" Ta fada pink lips dinta dake qyallin man lebe yana fadada da fara'arta. Girarsa dukka biyun ya daga mata yana duban qwayar idanunta. "Kina kallona ina jin dadi.....kuma sai kawai ki dauke kanki?". Murmushi ta sakeyi,a hankali ta motsa labbanta. "Kayimin kyau muffin,kayimin kyau sosai......kyanka da kamalarka suna sake tsananta kishinka a raina.....wani lokaci ni kadai ina tunani......ina tunanin ranar da zaka raba wannan soyayyar......wannan qaunar......wannan kulawar......wannan jikin........wannan baiwar da wata diya macen......iya tuna haka kawai idan nayi sai naji kaman zan zauce,sai inji kaman numfashina zai tsaya,sai naji komai ya dainamin dadi.....kokwanto me yawa sai ya cika zuciyata......iya tunawa kadai idan nayi nakejin haka.......ta yaya zan iya fuskanta da d'aukan haka a gaske?" Ta qarasa maganar tana maida dubanta cikin idanunsa. Idonta kawai ya kalla ya fahimci ainihin zallar gaskiyarta......idanunta kadai sun gaya masa da gaske take......duk abinda take fada din ainihin gaskiyarta kenan. A hankali ya miqa hannunsa daya ya kamo fuskarta yana dubanta da kyau,yanayin fuskarsa ya sauya zuwa ga yanayin wanda zaiyi magana me muhimmanci. "Kin aminta daga wannan tsoron,kin aminta daga wannan firgicin har abada.......bazan taba iya jurewa ba naga ruhin da yake tsananin sona yana wahala har haka akan abinda nake da ikon yi masa ko bashi ba......sabreenn,mace daya tak qwaqwqqara na roqi Allah ya bani......nagartacciyar mace na nacewa Allah da roqo ya bani,koda zanci wahalar samu ko nemanta.....koda zan jima banyi aure ba amma dai ta gari nakeso......nasha wahalar.....na kuma fuskanci qalubale.....kuma Allah ya bani ke.....ke kadai kin gamsar dani,bana buqatar qari......kece reality na......bana buqatar gaibu.....muhammad fu'ad naki ne ke kadai har abada........muddin kina nan a sabreenn dinnan dana sani baki sauya hali da dabi'a ba....." "Koda na tsufa?". Ta fada idanunta suna rau rau da cika da hawayen farinciki "Ko deboki akeyi a shanya a rana sai yamma tayi a maidaki daki.....ballantana ma ina miki kyakkyawan fatan tsufa me kyau.....baka mummunar tsufa....baka tsufan banza muddin ka riqe Allah kayi rayuwa irin wadda Allah da manzonsa suka tsara". "Haqiqa ba wata kyauta da zaka bani a rayuwa bayan wannan......ba wata kyauta da tafi wannan.....ka amintar dani daga tsoro na.....na gode.....na gode". "Ni banason godiyarki" Ya fada yana zare jikinsa daga rungumar data masa,ya kuma zura qafafunsa ya fita waje,saidai ya babbake bakin qofar motar ya zube hannayensa a aljihun rigarsa ya zube mata fararen idanunsa. "Me kakeso hamma?" Ta tambaya a sanyaye. Yadda tayi sanyin ya bashi dariya,ya kalli qasa ya dara kadan sannan ya dubeta. "Kici gaba da haifamin yara turmus....bibbiyu uku uku hurhudu harma biyar biyar". Idanu tadan waro waje kafin murmushi ya subuce mata,kyau tayi masa sosai,sai ya miqa mata hannunsa yana duban idanunta. "Me kika ce?" Dora hannun nata tayi saman nasa ya taimaka mata ta fito sannna ta amsa masa. "Ka tayani da addu'a Allah ya bani masu sauqi,kuma Allah ya bani ikon tarbiyyantar dasu" "Zakk iya in sha Allah......am by your side.......na tsaya miki akan komai sabreen,na tsaya miki,duk wani kalar jin dadi kulawa da riritawa kikeso....duk wani kalar rayuwa ko kalan abu da kikeso a rayuwa umarni kawai zakiyi yazo gareki......kaman yaddana taba yowa kaina alqawari saina cikashi in sha Allah.....zan maida matata ta zama sarauniya cikin mata....zan sakata da kanta ta dinga jin ita din ta dabance a cikin mata....zata zama wata gimbiya tauraruwa me haskawa.....shalelen mata wadda mata zasu dinga jin duk ita suka rako duniya....komai mulkin mace dukiya ko nasabarta idan tazo inda kike zataji ta koma tamkar baiwa a gabanki......abu uku zuwa hudu ne kawai nake buqata. Ki soni har abada har Qarshen numfashi so na fisabilillahi.....wuya ko dadi kar ya zama silar rabuwarmu. "Na biyu kiyita haifamin yara kina basu tarbiyya,sahihiyar tarbiyya data dace da addini." "Na uku ki bani kulawa.....idan zai yuwu ki fifitani sama da kowa harda yaran da zamu haifa ma". Wannan gabar sai data sakata sakin dariya. "Daddyn yara yada haka?" Sassanyan Murmushi daya qara masa kwarjini da kyau ya saki,kafin ya bata amsa wannan karon sai daya jawota jikinsa suna iya jin hucin numfashin juna. "Saboda shi daddyn yafi yaran son mamar tasu.....sannan shi daddyn yafi yaran sanin tsadarta da kuma darajarta......abu na qarshe shine ki tsaremin kanki.....ki tabbata a matsayin DUNIYAR MUHAMMAD FU'AD JADDA har Qarshen rayuwarmu". Tun b'a je ko ina ba da wannan kalaman nashi na qarshe ya qarasa tashin kanta. Tun ba'aje kuma ko ina ba ta dinga jin kaman zata narke da wata irin soyayya da qauna me tarin yawa. Tun a nan wajen tasan tabbas tayi sa'ar miji.....an haifota cikin sa'a.....kalar sa'ar da sai mace me tsananin sa'a take samunta. Baya yaja kadan,yasa hannuwansa yana gyaggyara mata lafayar jikinta. "Banaso ko ina ya fito.....komai nawa ne.....you're mine and only mine,all rights reserved". "Kowa ma ya sani.....basai ka yita maimaitawa ba yallabai" Muryar farouq ta sauka daga bayansa. Baiko waiwaya ba,kaman ma bai fahimci farouq dinne ba yaci gaba da gyara mata lullubin,a nutse yace. "Har yanzu ba zaka daina yimin kutse ba kenan farouqu.....wannan....." Bai qarasa ba saboda idanun da sabreen ke juya masa tana masa nuni da bayansa. Da ido shima ya tambayeta,tayi qasa da muryarta kamar me rada. "Like kaman shi da fannah ne hamma" Shuru ya danyi sannan ya dage girarsa yana sauketa,yaja da baya daga gabanta sannan ya waiwaya. Fannah dince,tana a gefensa kanta a qasa,kunya kaman zai kasheta. Tasha labarun soyayyar sabreen da dude enshi,amma bata dauka haka sukejin DUNIYOYIN nasu daga su saisu ba sai a yau din. Tun daga nesa data hangi yadda guard dinsa sukayi musu qawanya take mamaki,ta dauka zallar tsaro ne suke bashi,ashe su suna qarfafa tsinkar fule da fulawar da akeyi ne daga tsakiya. Abun ya bala'in burgeta,sun kasheta sun kuma tashi kanta,har ta dinga murmushi duk da kunya da nauyin FU'AD da take danji,don yana mata kwarjini sosai. "Qaton banza......ka taho da diyar mutane amma ba zakamin magana ba?" FU'AD ya fada yana hade girar sama data qasa shi a dole babba. Fannah ta qwaci farouq da dariya ta hanashi bashi amsa. "Barka da yamma hamma". Qasan ranta tana mamaki dama yana taba barkwanci haka?,idan kaga face nashi a news ko a news paper ko a wani taro na kasuwanci ba zaka dauka yana murmushi bama bare akai ga barkwanci,kaman bashi ba. "Barka kade amarya.....ya baqunta da sabon guri?" Ya fada cikin kulawa da girmamawa. "Alhamdulilah hamma....yame jiki?,Allah ya qara lafiya yasa kaffara ne" Fannah ta hada duka ta fada don kwarjininsa ya mata yawa. "Ameen" Ya furta yana jin kalmar kaffara din data fada tayi daidai da a roqawa maamah ita din. Gaba yayi suna jerawa da farouq bayan fannah ta qarasa wajen sabreen suka jera suma suna gaisawa. Karon farko kenan da suka fara ganin juna face to face,saidai kowaccensu yanayin nutsuwar dayar tayi mata. "Ayi mana afuwa,bamu samu haduwa ba,yanayin yazo da ciwon boss,ba daman nayi nisan zango na barshi,sai yau Allah yayi muka hadu" Sabreen ta fadi tana dan murmushi. "Aiba komai.....ana tare ai,shekaru masu yawa a gaba muna fatan hakan,yana da kyau a kula da boss sosai ai.....kema kuma dole ki rage zirga zirga ai saboda naki yanayin" Fannah ta fada tana murmushi. Mamaki yadan kama sabreen,wai cikinta ya soma fitowa ne?duk da fannah din midwifery ta karanta dama,saita dora hannunta saman cikinta. "Cikin 'yan uku daban yake ai adda.....sauri girmansa da kuma yawan satittikan da yake dauka a haifeshi,baya kaiwa dadewar cikin twins ko single baby" Ta fada da muryarta maras hayaniya. Kai sabreen ta girgiza,bayanin na fannah ya gamsar da ita,ta kuma fahimta,da alama kuma zata amfana da ita sosai. A hankali suke takowa shida farouq din suna tattaunawa. "Mun jima a asibitin,gida zamu wuce.......amma kunyi cikakken magana da likitan da yake ganinta?" Farouq ya tambaya da dan alamun damuwa kan fuskarsa. "Banganshi ba.....bansan wanne likita ke ganinta ba.....sai yau na samu shigowa asibitin". " Why?" Farouq ya tambayeshi yana nuna rashin jin dadinsa,duk kuwa da cewa yasan komai,saidai muddin dai maamah tana raye....muddin dai maamah din sunanta mahaifiyarsu ko sau daya bayajin akwai Randa zaice yayi mata wani rashin kirki ko me tayi. "Farouq.....Allah ne ya kiyayeni......da taimakon Allah da taimakon sabreen,banda hakan nima da tuni yanzu ina nan inata checking BP na......saura kadan jinina ya hau,ciwo zuciyata ta dinga yi,banda dauki da Allah ya kawomin na bani mace ta gari......hutawa nayi na kwana uku farouq,bansan da wanne fuska zan kalleku ba kuda anni.....mahaifiyata ta zama silar da saura kadan anni ta rasa diyarta......wannan sakayyar ya kamata ta samu ta bangarenmu?" Ya qarashe maganan da alamun abun yana masa mugun d'aci. "Dude.....na taba zaginka?.....inajin zan fara wannan karon" Farouq ya fada ba tare daya dubi FU'AD ba. "Ashe har akwai banbanci tsakaninmu da ku?,ashe har akwai abinda zamu yiwa anni ta tsanemu kenan indai zata tsaneku ko.taji haushinku akan abinda baku kuka aikata ba.....ka saka a ranka ma tun wuri ka sake gayawa kanka cewa....ni dakai mahaifa daya muka kwanta aka haifomu tare,kaman yadda musaddiq da saddiq suka kwanta mahaifa daya aka haifosu tare......har abada ba wani banbanci". Shuru kawai FU'AD yayi,har abada baisan da meye zaiwa wadannan bayin Allah sakayya ba. "Ya kamata ka duba yanayin jikin nan nata da kyau,anni nata yimin fada tun jiya......ina ganin ma kamar qasar ya kamata a fidda ita....saidai kaje zaka gani,hawan jini yayi mata mummunar kayarwa" Ya qarasa fada da sautin jimami a muryarsa. Kai ya kada yana nazarin abun,hawan jinin da baida labarin sadda ta sameshi,ya sake kada kai yana tuna wata kalma data taba fadawa abbansu randa ya dawo result din kamuwa da hawan jini. "Kadanma ka gani......shi talauci in gaya maka idan ya samu ciwo yaga gurin zama kenan....duk talaka da hawan jini yake qarewa,kaga somi somin daukan hanyar mutuwa kenan,ciwon qoda,hanta,zuciya,lalacewar hanji duka daga hawan jini yake farawa......bari na fara tanadi don kaina" Tayi maganar tana miqewa abinta ta barsu a dakin da takardarsa da magungunansa a leda. Bai amsawa farouq ba,illa wani nannauyan numfashi daya sauke bayan ya gama tuna wannan,sai shima farouq din bai sake cewa komai ba. Ya sanshi,a dabi'arsa ba komai yake baka amsa ba,idan kuma kaga bai baka amsar ba to lallai baka da buqatar bada amsar ne. Dab da zasu shiga reception na asibitin da zai sadasu da sassan asibitin,sanda guard dinsa ke clearing masa hanya ya tambayi farouq. "Inasu saddiq?" Harara ya balla masa. "Zama zasuyi jiranka?,kwanan amna daya a asibiti abba yace kowa ya dauki matarsa su wuce gida". Ido yadan fitar. "Me yasa abba bai bari amna jikinta yayi qwari ba?" Ido farouq ya zuba masa sannan ya bushe da dariyar mamaki. "Kana tsoron kada ayiwa qanwarka abinda ka yiwa diyar mutane ko?,to abba yace ta qarasa warkewa a dakinta.. ..kaga malam ka barshi shima ya shana......wannan lamari baya buqatar shamaki ko shishshigi fa" Farouq ya fada yana dan shafa gemunsa cikin nishadi. Dunqule hannu FU'AD yayi yakai masa duka "Sai yanzu kasan haka kenan?" "Fes kuwa" Ya amsashi yana dariya. Mur FU'AD yasha ganin su sabreen sun kusa da inda suke,farouq kuma yaja tunga. "Wucewa zamuyi gida.....zamuzo muku ziyara once kafin mu wuce honeymoon" Ya fada cikin salon tsokana yana bawa FU'AD hannu. "Sai kunzo....Allah yasa muma ku samemu" Ya amsa masa yana bagararwa. "Iyeeee.....lallai mutumin nan.....baku gaji ba?" "Kai ka sani" FU'AD ya fada yana danne murmushin daya taso masa. Tsayata yayi a bakin qofar amenity din,suka gama sallama da fannah,sukayi exchanging phone numbers sannan ta tako ta sameshi. Hannunsa ya sanya cikin nata ya riqe gam kamar wadda za'a qwacewa ita,har sai data daga idanunta ta kalleshi suka hada idanu,idonsa ya dauke,sai mamaki kadan ya kamata,kaman ya manta gaban surukarta maras lafiya zasu shiga?,bazaiyi alkunya tafin hannunsa cikin nata ba,ta bishi kawai yana tura qofar gami da sanya qafarsa a ciki. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 153 *_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽 *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂 Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾 wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 153 Har yanzu da take zaune saman wheel chair din bata daina qoqarin motsa kowacce gaba ta jikinta ba,duk da hakan baida wani amfani ko qanqani a tattare da ita,kaman yadda bai kawo wani ci gaba a yanayin da takejin jikinta ba. Ta sake tattara duk qarfinta a karo na babu adadi don ta samu koda bakinta ne ta motsa tayi magana,amma kamar dai mintunan da suka shude ko motsi bakin baiyi ba bare akai ga fitar wani sauti. "Innalillahi......na shiga uku!" Shine abinda ta furta cikin zuciyarta,don babu damar yin magana a bayyane bare wani yaju furucin nata. "Wai da gaske ne?,da gaske ne ni mariya?,bazan iya yiwa kaina komai ba?,da gaske ne ni mariya bazan iya tafiya ba?,da gaske ne ni mariya bazan iya yin magana da kowa ba bare a jini ko a fahimceni?" Tambayoyin kenan da suka cika mata kwanya da qirji tsahon kwanaki ukun kenan,kuma bata da wani me iya jin tambayoyin bare ya amsa mata. Tun daga kwanaki ukun zuwa yau ko sau daya bataji ta gamsu ko ta nutsu da maganganun likitocin ba da suketa maimaita maganar hawan jini ne wai ya kamata ba. Tafi amincewa da cewa tabbas wannan abun daya sameta jifa ne......asiri ne kawai akayi mata saboda kada taci arziqin d'anta. Mutum biyu take zargi,hajja harira ko ameena hamza kibiya. Duk duniya wadannan mutanen biyu bata da wani abokan adawa sama dasu,bata da wani abokin takun saqa sama dasu. Duk da kuma tana zargin ameena din,amma zargin nata yafi qarfi akan hajja. "Na rantse da Allah na warke hajja bazaki sha ba.....ba zaki tsira ba....ko ke ko ameena duk wanda yake da hannu cikin maida rayuwata abun tausayi cikin qididdigaggun daqiqu" Taci alwashin cikin ranta tana jin wani abu yana tokare mata a wuya me tsananin zafi. Checking nata likitan yakeyi yana rubuta bayanan cikin folder dinta yana hada mata da bayanai duk da yasan bawai zata iya bashi amsa bane,amma yasan tana ji tana kuma fahimta,maidawar ne ba zata iya ba. Duk abinda yake fadi sam bata bashi hankalinta bama bare ta tantance ma'anarsa,a nata ganin maganin warware sihiri tafi buqata fiye da wadannan tarkacen na'urorin da aka zube mata aka. Tayi imani ba wani hawan jini daya sameta,kawai komai da akeyi din wani bata lokaci ne na daban,tunda ko hanyar bakin zaren bata ganin alamun daukoshi. Kaman kowanne kebantaccen dakin asibiti me cike da tsari shima haka yake. Gadaje guda biyu qananun sofas guda uku da plastic chairs guda biyu suma. Yadda idanunsu suka sauka a kanta haka itama idanunta suka sauka a kansu. Wani zazzafan abu ya taso ya lullube mata zuciya. Sosai ta kafe sabreen da idanu tana dubanta ba tare data dauke dubanta daga kanta ba ko na second guda. Ita kadai tasan me takeji akan yarinyar......tana kallonta a matsayin silar komai.....tana dubanta a matsayin wadda ta assasa mata dukkan wata musiba da take ciki. Gaba daya maganganu akanta da boka ya gaya mata suka fara dawo mata d'aya bayan d'aya. "KINYI KUSKURE!" Kalmar farko da ya fadi mata kenan a kanta,ashe tabbas da gaskiyarsa......da gaske yake kuskuren tayi.....to amma koma meye wannan kuskuren zata tabbatar ta maidashi kansu muddin lokaci da dama suka sake waiwayarta. Abubuwa ne da yawa suke yawo a zucoyarsa da idanuwansa sanda suka iso gabanta. Kallon da take binsu dashi tana raba idanunta tsakanin fuskarsa da tata kadai ya gaya masa komai. Akwai maganganu masu yawa saman harshenta,akwai saqonni masu nauyi cikin zuciyarta wanda dama bata bata daman furtasu ba......saidai duk wani yanayi nata.....duk wani motsi nata karantaccen abune a wajensa da koda da idanu tayi magana zai wahala ya gaza fahimta. "Sannu" Ya furta mata yana dubanta. Ido ta lumshe sannan ta budesu,qwaqwalwarta na dawo mata da haduwarsu ta qarshe. Maganganunsa da sam basuyi mata ciwo ba kaman yadda babbar damar daya bata ta kubce mata tayi mata ciwo......wata irin gagarumar dama da bata tunanin zuwanta da subucewarta haka lokaci guda ba. "Barka da zuwa sir" Likitan ya fada cikin girmamawa. Waiwayawa fu'ad yayi ya kalleshi. "Yauwa sannu da qoqari" Ya fadi yana jawo kujera gaban gadon maamahn. Sabreen ya waiwaya ya kalla sannan ya kalli kujerar. "Zoki zauna" Ya fada cikin nuna kulawa. Nauyi abun yayi mata,sai takejin kamar idanuwa ne da yawa a kansu. A darare ta matso tana tsarkake sunan Allah ta zauna,tasbihin da tunda ta shigo dakin takeyinsa da kallo daya data yiwa maamah. Tsaf kamannin maamah din suyi wani irin juyewa,qasa da awa saba'in da hudu kacal?,iya wannan ya ishi bawa girmamawa ga ubangijinsa da kuma sallamawa lamarinsa. Tsoron Allah taji yana sake shigarta,wani bangare na tausayin maamah din ya karyo mata. "Sannu.....ya jikin?,Allah ya mayar kaffara" Ta furta a hankali tana son karantar yanayin kallon maamah din a kanta. Kafe sabreen din tayi da idanuwa,tana jin wannan dubiyar da addu'ar gaba daya akwai isgili a cikinta. Akwai maganganu masu yawa data jima tana tanadin gaya mata,akwai maganganun data tanada saboda rana irin wannan.....ranar sa sabreen din zata tona mata asiri,ta kuma yaye lullubin sirrin dake tsakaninsu wa fu'ad......a ranar ta tanadi abubuwan fada masu yawan gaske a kanta. Saidai kuma ranar tazo mata da wani babban akasi......akasin da babu daman cewa komai gareta,sai kallo da da idanu,dukkan wasu kalmomi nata suna mata kai kawo tsakanin qirjinta da wuyanta amma fitarsu ya zame mata wani jan aiki. Kallon fuskar sabreen din kadai wani gagarumin baqinciki yake ajiye mata,saidai sanda ta dauke idanun nata da zummar kauda kanta sai suka fada kan dan matashin cikin dake kwance a jikinta wanda batasan sanda har ya fara bayyana kansa ba. Kulle idanun nata tayi tana jin yadda bacin rai yake hautsinewa a qirjinta yana kuma bin kowanne sashe da jini ke gudanar mata yana aike mata da saqo kowanne sashe na jikinta. Batajin zata iya ci gaba da kallonta zaune haka a gabanta,inda tana da baki da zata gaya mata cewa ta tashi ta matsa daga gabanta ne,amma bata da wannan damar yanzu haka banda ta kulle idanun. Sallamar da aka sakeyi ita ta tilasta mata sake bude idanun nata. Musaddiq ne a gaba,amna na biye dashi a baya sanye da baqar abaya data fito da hasken amarcinta da kyau,duk kuwa da 'yar rama kadan dake tattare da ita. Kallo daya tak zakayi mata ka karanci a tsorace take,tana daga bayan musaddiq din,duk inda ya tsoma qafarsa ya dauke nan yake ajiye tata. Hannunta riqe da nashi hannun daya bar mata shi ta baya a haka suka shigo. Kan hannun nasu idanunta suka fara sauka,wannan karon yunqurin miqewa tsaye tayi ta gwada tata jarumtar na UWA kuma wai MAHAIFIYA,saidai kuma kash......ba wani abu nata daya motsa balle akai ga batun tashin. Gumi sosai ya dinga karyo mata saboda abinda takeji a zucoyarta,bala'i da masifa ne fal idanu da zuciyarta,donme musaddiq din zai debo mata diyar alhaji hamzan yazo mata da ita?,auren da sukayi kadai bai ishesu ba?,har sai sun qara qunsa mata baqincikin ganin kasantuwarsu a tare?. "Akwai buqatar ki saka nutsuwa da kauda duk wani bacin rai daga zuciyarki don a samu a ceto lafiyarki yadda ya kamata" Likitan ya furta yana dubanta,gumin dake fita a fuskarta kadai ya gaya mishi akwai wani abu daya motsa zuciyarta,duk da baisan ainihin meye ba. Tana labe a bayansa suka qarasa gabanta,ya gaidata gami da yi mata sannu. Leqowa amna tayi daga bayansa tana mata sannu itama,suna hada idanu ta koma bayan mijinta ta lafe. Ko kusa ko alama bata qaunar ganin matar,anni ce ta kirata ba tare da sanin musaddiq din ba tayi yaqi da ita akan ta bishi idan zaije ta dubata. "Komai lalacewar tuwo ba'a sauya masa suna.....musaddiq baida wata uwa bayan mariya,koda ya nuna miki baya sonta wannan wani yanayi ne ya kawo haka.....batun abinda tayi miki kuma darajar addu'a bata samu galabar komai a kanki ba,sannan kuma hakan ya zame mata wani sanadi ne na tonuwar kowanne sirri....kina tunanin ke kika yiwa kanki haka?,ko kadan,darajar addu'a ce da duban zukata da Allah S W T yayi". Wannan maganar ita ta sanya amna yin qundumbala ta biyoshi. "Any progress?" Fu'ad ya tambaya yana duban likitan. Ajiyar zuciya kawai ya sauke sannan yace. "Idan zai yuwu muje muyi magana daga office ko?" Juyawa fu'ad yayi ya yiwa musaddiq inkiya,shi kuma ya waiwaya yana duban amna. Muryarsa can qasa cikin sigar lallashi ya fara magana. "Calm down dear......ga adda sabreen ku zauna tare da maamah......ba abinda zai sake faruwa,yanzun zamuje mu dawo.....okay?" Ya fadi yana dage mata dukka girarsa gami da riqe fuskarta tsakanin hannuwansa. Kai ta gyada masa,sai ya sake mata murmushi yaja da baya yana juyawa gami da bin bayan fu'ad. Saura kadan numfashinta ya qwace mata,wani tashin hankali ya sake sauko mata. "Shima musaddiq din haka yake?" Maamah ta tambayi kanta. Wani irin yanayi ne da batasan musaddiq dashi ba,soyayya muraran da mace a gabanta?.....wacce irin baqar rana ce wannan take gani?. Dukka yaranta guda biyu da iyasu ta mallaka a duniya,kowannensu ya dulmiya cikin soyayyar wata diya macen daban ba ita ba?,wani irin so me zurfin da bataga kwatankwacinsa a kanta ba a cikin idanunsu?. Shuru dakin ya dauka,sabreen tayi qarfin halin sakin murmushi ta kalli amna. "Ga guri ki zauna amarya.....kada angonki yazo ya tuhumeni na bar masa me a tsaye" Ta fadi tana ganin yadda amna din taqi sakewa. Ita kanta ta zama tamkar baquwa a gurinta. Murmushi ta maida mata,ta tako a nutse ta samu gefan sabreen din ta zauna tana qoqarin sakin fuskarta. Ashar maamah keda muradin narka musu ganin suna hira qasa qasa a gabanta amma bakin yaqi buduwa,game kula kuwa zaiga yadda idanunta suka kada sukayi jajur,daga amna har sabreen ba wanda ya kula a cikinsu,don sabreen din nata qoqarin jan amna da hirar da zata sakata sakin jiki. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 154 "Shekararta nawa tana fama da hawan jinin nan sir?" Likitan daya gaji da ganin abun mamaki tsakanin kwanaki ukun ya tambayi fu'ad. Kafadunshi duka biyun ya dage yana son gano dalilin tambayar. "Ba wasu shekaru bane,idan ya dade wata daya....." "Hamma duka baifi sati uku bafa" Musaddiq ya fadi yana duban fu'ad. Dauke dubansa fu'ad yayi ya maida ga likitan alamun "Kaji amsar tambayarka?". Kai ya jinjina cikin matsanancin mamaki. Tunda yake kaf a tarihin aikinsa bai taba ganin mutumin da jininsa yahau har haka kuma yake iya ci gaba da rayuwa ba. Matakin hawan jininta yakai mataki na qarshe,wanda daga wannan stage din saidai mutuwa bama stroke ba.....uwa uba kuma tun a kwanakin da aka kawota yake ta qoqarin ganin jinin ya sauka amma yana nan a inda yake,ba wani ci gaba. Ya gwada duk wata basira tashi da dabarun aiki amma abun ya cimma tura. "Sir......munyi mata dukkan abinda ya dace amma ba wani ci gaba ko nasara koda alamunta kuwa,abinda yafi bani mamaki shine......yadda hawan jinin yayi mata wata mummunar rafkiya karo daya,nayi zaton tsohon ciwo ne ma,sa'annan duk wani hanya na sauke jinin wallahi yaqi sauka,abinda yake dada bani tsoro shine,ci gaba da qin saukar nasa zai iya zame mata sanadin matsaloli kala daban daban,don a yanzun haka tsoro nake kaman qodarta tana son harbuwa,bansan me yake faruwa ba,nidai ban taba cin karo da case me kama da nata ba tsahon shekarun dana dauka a bakin aiki.......amma abinda nake tunani.......anya ba wani abu babba data sanya a ranta?,ko wani goal da takeso ta cimma a rayuwarta?,wani matsala dake bata mata rai?". Wani murmushin takaici ne ya qwacewa fu'ad,wanda tunda suka shigo office din yana tsaye kawai hannayensa zube a aljihun wandonsa. Likitan yayi tambaya a muhallinta,duk duniya shike da amsar wannan tambayar tasa,saidai abune da bai shafeshi ba,koda ya shafeshi ma labarin zai zame masa wani baqon labari da ko a duniyar hikayoyi bai taba jin irinsa ba. Uwa nason mallakar d'a kota mallaki abinda ya mallaka kota halin qaqa?,uwa nason tarwatsa rayuwar 'ya'yanta ta hanyar rabasu da abokan zamansu?......rabo na jikokinta dake manne a mahaifar surukarta kuma fatanta yabi rariya?,BURIN UWA TARWATSA RAYUWAR 'YA'YANTA ta rabasu da uwa da uban goyonsu da suka zamewa rayuwarsu suttura?,wacce irin uwa kenan wannan?,baya ga wasu boyayyun al'amura da fadinsu ma baida dadi koda a baki ballantana ga kunnuwa?. "Me take buqata?,me ya kamata ayi?" Ya yankewa likitan dogon tunani da zallar mamakin daya fada "Tana buqatar kulawa ta wurwuri......kulawa ta gaggawa saboda gudun rasa wasu bangarori na jikinta,kamar idanunta kunnuwanta ko qoda ko kuma hanta". "Yanzu me kake gani za'ayi?" Ya sake tambayar likitan,yana jin wani tsoron girman Allah yana kamashi. Amsa kuwwar muryarta yakeji a shekarun baya yanzu haka. "Shi hawan jini ai baka rabuwa dashi sai ya lalata maka ji gani qoda ko hanta.......kai kam gaskiya kaman bakayi sa'ar rayuwar duniya ba?,daga wannan sai wancan?" Tayi maganar tana tsaye a kan abban nasa sanda duniya tana tsaka dayi mata zaqi da gard'i. A lokacin shi kuma yana tsugunne a gabansa yana qoqarin ballo masa magungunansa saboda hakin daya sarqeshi ba qaqqautawa. "Ina ganin me zai hana ku fita da ita waje?,suna da kayan aikin damu bamu dasu,zasu sake bincikarta sosai ko akwai wani abun daban da yake jawo wannan matsalar bayan......." "Kayi magana da dukka asibitin daya dace ace an kaita din,ka tura adadin abinda za'a buqata daga dawainiyar asibitin da komai ka sanarmin ta waya" Ya fada kawai a gajarce. Yana ji a jikinsa komai daya kama na neman lafiyarta zaiyi mata shi,bayan ya tanqwara zuciyarsa wadda kowanne taqi tana tuna masa da yanayin nata action din akan mahaifinsa sanda yake jinyar ajali. Ya sani idan zai biya ta wannan ko paracetamol maamah bata cancanci tasha ba ta hannunsa.....to amma har yanzu huduba da tarbiyyar anni tana yawo a jininsa. "Uwa uwa ce fu'ad,duk lalacewarta ba wata madadinta" Wannan maganar ya jima da haddaceta daga bakin annin. ★Cikin sati guda komai ya kammala na fitar da maamah din qasar Egypt. Fu'ad da kansa yace musaddiq yayi zamansa su samu hutu sosai da amna,don itama amna din har yanzu yana ganin kaman bata gama sakin jikinta ba bata warware gaba daya ba. Sanda yake shirin tafiyar sabreen ta sameshi a daki,ya daga kai daga abinda yakeyi yana dubanta. Sosai cikinta yake sake bayyana kanshi kowacce rana. Sosai cikin ke qara mata wani kyau,shi kansa zamanta a jikinta kyau yake mata. Hannuwansa ya harde yana kallonta da sassanyan murmushin nan nasa. A kwanakin gaba daya ta sake sauya masa,wani abu me sunan tattali da kulawa da bai sanshi ba yake samu daga gareta. Wani irin respect take bashi,bai taba jin bashi respect yana burgeshi ba kaman a kanta,ta maida kanta qasansa sosai,komai zatayi tana nuna ita din a qarqashinsa take,ita din mallakinsa ce. "Sun hanaki bacci halan so abbee dinsu suke jira yazo tayasu hira" Ya fada yana bude mata hannayensa. Bata tsaya wani bata lokaci ba ta taho ta fada ciki,ta kuma lafe abinta. Ba wani guri da takejin tsananin aminci kaman qirjinsa,ba wani guri da take ji take kuma samun cikakkiyar nutsuwa irin qirjinsa,wani guri ne na musamman da takejin duk duniya bata da kamarshi. "Na gama shirya nawa kayan fa hamma" Ta fada a shagwabe. Dan dagata kadan yayi daga jikinsa yana duban fuskarta. "Zuwa ina kenan adda?". " Egypt mana" Ta fada a shagwabe tana maqale kafada. Kai ya girgiza yana sakinta sannan ya fara takawa yana barin wajen "No.....zaki zauna a nan har mu dawo,kinsan yanayin da kike ciki ai ko?,ko kin Manta wani hutun nake shirin baki ma?". Batace masa komai ba har ya qare zancen,saita sauke hannayenta data harde a qirjinta tana takawa a hankali zuwa inda yake zaune yana basarwa ta hanyar qirqirar wani aikin. Dab dashi ta zauna har jikinsu yana gogar na juma,tasa hannunta ta jawo fuskarsa zuwa inda take kaman yadda shima yakeyi mata. "Nasan me kake tunani,nasan abinda yasa ka fadi haka kuma.....amma kada ka manta.....har yanzu maamah uwa ce.....kuma nidin nayi alqawarin riqe hannunka gam,zamuyi tafiya bisa tafarkin rayuwa a tare,da dadi ko babu dadi right?". Kansa ya daga a hankali yana dubanta,ya rasa wadanne irin mutane haka Allah yayi masa rahama da ni'ima dasu?,sam basa duba sharri sai alkhairi a tare dashi,duk da irin uwar da Allah S W T yayi masa jarrabawa da ita. "Koda maamah zata kasance me laifi a waje na.....nikam na yafe mata,har abada babu wata uwar da zata iya haifamin muhammad jadda sai ita.....ta kuma haifamin din,ina da abinda zan iya saka mata dashi?". Idanunsa ya lumshe kawai yana jin yadda soyayyarta ke tsatstsaga jikinsa. Addu'ar mace ta gari da yayi Allah ya bashi ma sama da abinda ya roqa din,yana jin kunyar idanun kowa......yana jin kunyar sanyasu su yiwa maamah wani hidima bayan dukka tarin sharrance sharrancenta a garesu,wanda har zuwa yanzu shikam yana ji a a jikinsa maamah din bata hau sirad'al mustaqeem ba da gasken gaske. Hannunta ya riqe sosai cikin nasa da wani irin taushi. "Na gode sosai my world......na gode duniyata". Murmushi ta sakar masa "Ba godiya tsakanina dakai.....kome nayi maka kafi qarfinsa a wajena". Tafiyar sai ta kasance me sassauci a tare dashi,don kasancewar sabreen a tare dashi cikin kowanne motsi a rayuwa ba qaramin qarfafa masa gwiwa yakeyi ba. Sun isa Egypt bisa jagorancin Dr awwab,an kuma gabatar da maamah ga qwararrun likitocin asibitin,wadanda suka dauki kwanaki suna dukkan bincike da gwaje gwaje. To sakamakon dai guda daya ne,hawan jini ne me tsanani da har a Egypt dinma dai bai sauka ba,sai kuma wani abu data qulle a zuciyarta da suke ganin kaman shima yana barazanar taba lafiyar zuciyarta. Sabreen ta girgiza matuqa,jikinta kuma ya sanyaya,ta qara cika da mamakin maamah,ta kuma sake sallamawa lamarinta,ta qara yarda da imani da yaqinin lallai wanda Allah ya shiryayye......ba wanda kuma ya isa ya shiryar da wanda Allah ya batar. Daga idanun maamah da kallon da take binta dashi duk da kalar hidimarta gareta ta karanci ba wani rusunawa ko nadama a tattare da ita......qaddararren ciwon daya zama jarrabawa game hankali ne kawai yayi mata cikas ya hanata duk wani sukuni. Daga qarshe sun yanke zasu ci gaba da bata kulawa har na tsahon wata guda suga abinda hali yayi. Da taimakon qwararun nurses dake kula da maamah din aka soma dorata akan magunguna da therapy kala kala. Duk da akwai masu kula da ita din sabreen bata zauna ba,saidai ko yanzun sabreen ce zata bata abinci ba zata karba ba. Da idanu take kafeta,wani abu yana sake mata ciwo,duk sanda ta kalleta zuciyarta tana gaya mata. "Yarinyar tayi winning a kanki,ke gaki a zaune saman wheelchair ko yatsarki baki iya dagawa". Rana ta farko da zuciyarta ta gaya mata haka bayan sun gama zama da ita ne sun wuce masaukin da suke kwana. Kuka sosai ta dingayi,hawaye shabe shabe daya na bin daya,hawayen zallar baqinciki faduwa da kuma asarar da tayi. Hakanan nurses din dake kwana da ita suka taru a kanta suna lallashinta,amma taqi tsaida hawayen tamkar ma suna tunzurata. Haqurin da suke bata ma sake bata mata rai yakeyi,ta rantse inda bakinta yana magantuwa su kansu da sai sunji magana iya magana. Jirigi guda musaddiq da amna,farouq da fannah......saddiq da huda wadda ta soma murjewa ta fara qiba suka shigo Egypt duba maamah din. A ranar taga baqar ranar da zata iya cewa kaf fadin rayuwarta bata taba ganin irinta ba. Kowa yana zaune da qugunsa......yana takawa da qafafunsa....hannu kai da qafufuwansu dama bakunansu gaba daya suna aiki amma banda ita?,banda nata?,ita kadai dai komai a kanta ya qare?. Wannan tunanin ya sake sakawa ta dinga fitar da hawaye,har numfashinta ya sarqe saida likita ya shigo ya mata allurar bacci. "Har yanzu akwai wata danqararriyar damuwa a ranta.....kuma indai bata cireta ba treatment dinmu bazaiyi aiki ba,jininta bazai taba sauka ba.....tana da ciwon tun asali tayi wasa da magungunanta har sai daya zame mata haka,qodarta ta fara nuna alamun failure.....duk yadda zakuyi ta cire damuwa a ranta". Bayanan da likitan yayi musu kenan. Dukkaninsu sunsan wani abune me suna gaibu tilasta maamah ta cire damuwa a ranta,damuwar da dukkaninsu suka kasa gane ta meye idan ka dauke fu'ad sabreen da musaddiq. A nasu hasashen it's high time ace maamah ta cire komai a ranta,so ba damuwar dabi'unta bane na baya,saidai fu'ad sabreen da musaddiq sunsan cewa HALI ZANEN DUTSE......BARIN HALI KUMA SAIDAI MUTUWA. *_TURQASHI.....WAI ME KARATU NACE BA.....WAI SAI YAUSHE NE MAAMAH ZATASAN ANNABI YA FAKU?,SAI YAUSHE NE HALINNAN ZAI CANZA?_*155 ★Cikin wata gudar nan da suka dauka mata ba wani kalar treatment da ba'ayi mata ba. An kashe kudi sosai anyi amfani da engine da fikira da fasahar dan adam a kanta amma ba wani canji ko qanqani da aka samu. Duk wata lalurarta saidai ayi mata,bata tsinanawa kanta komai don ko yatsanta bata mallaka ba,bata isa ta juyashi ba bare sauran sassa na jikinta. Idanu da kunnuwan ne kawai suke aiki,banda su za'a iya cewa komai a jikinta ya tsaya a aiki idan ka cire ZUCIYA. Wannan zuciyar dai da annabi yake mana gargadi da jan kunne a kanta,wannan zuciyar dai da yake gaya mana idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci dukkan jiki ya baci. Wannan zuciyar dai wadda da ita ake gwada nagartar bawa.....wannan zuciyar dai wadda da ita ake ganin qarfin mutum,ba qarfi na jiki ba ko qarfi na dukiya ko qarfi na mulki ko qarfin iko ba. (Ubangiji don girman al'arshinka kasa mufi qarfin zuciyarmu,ya Allah kasa mu mallaki zukatanmu don hasken fuskar manzan Allah,wallahi wallahi duk wanda kaga yayi qarko to tabbas ya mallaki zuciyarsa ne......yafi kuma qarfinta,ya haneta aikata abubuwa masu yawa daba daidai ba,dukkaninmu kowa yasan daidai yasan kuma ba daidai ba,kubutacce a cikin mu shine wanda ya mallaki zuciyarsa yaji tsoron Allahnsa akan komai na duniya da lahira,yake kuma aiki da nasa hankalin). Dole hakanan don ba yadda za'ayi mata suka tattara suka koma gida nigeria da sauran tarkacen kayan therapy din da za'a iya siya mata,wadanda zasu dinga motsa mata gabbanta,kaman yatsun hannu da sauransu. Ma'aikata dole ya sanya aka samo masa ya dauka,wadanda zasu kula da ita da komai nata. Wankanta,cin abincinta,sallarta tsaftar kanta data jikinta. Already tana da masu aiki dake tsaftace gidan suyi girki,akwai guard kuma a gaban gida da farfajiya masu kula da gidan gaba daya. Rayuwa duk yadda kayi haka za'a yi maka,Allah da kansa yace wadancan kwanakin sune muke juyasu tsakanin mutane,kwatankwacin karin maganar bahaushe da yake cewa YAU GAREKA GOBE GA DAN UWANKA. Wata babbar dama ce ta samu ga wadannan ma'aikata da aka dauka,sabbi da kuma wasu daga cikin wadanda suke cikin gidan. Bude cin karensu babu babbaka sukayi,kowa yayi abinda yakeso a sanda yakeso,a kuma yanayin da yaga dama. Bata da bakin magana sai idanu,sai tarin baqinciki da takeji kaman zai kasheta. Idan tayi bayan gida ko fitsari,muddin fu'ad ko musaddiq basa nan sai ta gane kurenta. Don zasu barta da abinta sai sun gama sharafinsu sannan suzo su wanke su gyarata bayan sun gama tsaki toshe hanci da harara da baqar magana. Tanaji tana gani duk wani abu da yake mallakinta ita keda iko dashi sunayin yadda sukaga dama,da sunji alamun zuwan musaddiq ko fu'ad harma da sabreen......yanzun nan zasu dawo gabanta su zauna suna nan nan da ita. Takan yawaita kallon fu'ad din,tanason gaya masa irin abinda suke aikata mata amma ba wannan damar,ba bakin magana,tana ji tana gani zasu gama abinda zasu yi mata su fice,su kuma su dora daga inda suka tsaya. Duk abinda mutum yake akwai ranar da dubunsa zata cika,khairan au sharran......muddin kaga ka dade to Allah yana qara maka lokaci ne yaga ko zaka tuba?,ko zaka gyara kurenka?.....ko zaka gano kanayin ba daidai ba?....kaman yadda bahaushe yace komai nisan jifa qasa zai fado.....komai girma gona akwai kunyar qarshe. A irin wadannan ranakun Allah ya kawo sabreen katsam. Basuyi zaton zuwanta ba,don ba lokacin zuwan nata bane. Yanayin da taga sun watsar da maamah din ya daga hankalinta sosai. Hawaye kawai ta dinga yi tsoron Allah ita kanta yana sake shigarta,wato dan adam ba kowa bane.....kaman yadda yake ba'a bakin komai ba. Girman kai dagawa da mugunta dukka idan kaga mutum yana yi Allah ne ya ara masa lokaci,dama ce wadda idan yaga dama ya qwaceta shikenan ta tafi kenan har gaba da abada. Ko a mafarki akace mata maamah din zata dawo haka ba zata gasgata ba......ko da wasa aka ce mata akwai lokaci me zuwa kaman haka ba zata yarda ba......matar dakeji da dukkan wani izza taqama da gadarar qarfin iko,yau gata zaune waje daya,ko ruwa bata isa ta bawa kanta ba idan ba'a bata ba. Kaf ma'aikatan gidan ta tattara,bayan ta gama jin ta bakin amintaccen malam sa'adu,wanda ya gama karantar halin kowa. Da kanta ta yanke hukunci ta sallami dukkan wanda lambarsa ta fito na baqin hali da mugunta. A ranar tayi kuka tayi kuka,kukan tausayin kanta a matsayinta na 'yar adam wadda itama haka tana iya kasancewa a kanta. Tun fu'ad na lallashinta har ya rasa ta ina zai bullo mata. Ya dafe habarsa kawai yana kallon yadda tasa ciki a gaba tana kuka. Kuka akan maamah?,duk sanda ya tuna da wannan abun yana bashi mamaki. Baiyi zaton koda mutuwa maamah tayi ba hakan zai d'a d'a sabreen da qasa ba "Ya ilahi......wacce irin zuciya ce da ita?" Ya tambayi kansa da kansa yana sake jinta har cikin qasusuwansa. Ya tabbatar kyakkyawar zuciya kawai baiwa ce......baiwa ce da ba kowa Allah yake yiwa ita ba,baiwar da tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi. "Ya isa haka sabrrrr.......ya isa.....babies dinki karsu dauka nina taba musu maamah fa" Ya fada cikin damuwa. Shi kansa ba jin dadin ganin maamah a haka yakeyi ba,to amma yasan cewa duk wani abu daya dace suyi mata sunyi mata shi,hukuncin Allah ne kawai yake aiki a kanta. Duk runtsi duk yanayin aikinsa sau biyu shida musaddiq suke zuwa,da safe da kuma yamma wani kuma yaje da dare. Har yanzu wannan ruhin da wannan zuciyartata basu gama yin laushi ba,abinda yafi komai dagawa fu'ad din hankali kenan. Idan kaga tana gumi sosai to musaddiq yaje shida amna,ko ta ganshi tare da sabreen ko kuma ta zubawa cikin jikin sabreen din idanu. A yadda sabreen ta damu da maamah yayi tsammanin zuciyarta zata sanyaya da dukkan komai. A yadda ta wahal da amna ta nemi rayuwarta ya zaci yanzun zatayi nadamar aikata mata abinda ta aikata mata. Kai tsaye ya hana musaddiq zuwa da amna kwata kwata,don itama 'yace me cikakken 'yanci da iyayenta ke matuqar qaunarta,bai kamata a dinga razana rayuwarta da qananun shekarunta ba ta hanyar zuwa da ita inda takeji kullum bata da security. Wannan karon saida sukayi bincike sosai kafin daukan masu mata hidima,asalin garinta na haihuwa suka shiga tushenta,suka samo amintattun mata da suke da dangantaka da maamah din. Wasu ma cousins dinta ne......amma yanayin rayuwa ya sanya duk suke kaman sun girmeta. A asali nutumin karkara mutum ne me karamci mutunci da kuma martaba dan adam......mutum ne me juriya da amana,har yanzu akwai ire irensu.....cikin taimakon Allah suka samo mutum shida a cikinsu. Uku mata uku maza,da farko ma sunce kyauta zasu kula da ita,saboda Allah saboda kuma girman zumunci. Basuyi fushi ko zuciya da yadda ta watsar dasu ba,saidai fu'ad bai yarda ba,ya yankawa kowannensu albashin da iyalinsa zasu rayu cikin wadata da nutsuwa. A duk sanda yaje dubata,ya cire duk wani shiga nashi na office don gyarata ko mata wata hidima mamaki sukeyi. Babban mutum kamarshi?,wanda bai rasa komai ba?,amma yana iya tsaftace qazantar mahaifiyarshi?,ko yayi mata brush?,ko ya azata saman keken dake mata massage da sauran exercise na jiki?. Abu daya da yakan tuna a ko yaushe a kanta shine girman haqqin uwa......uwa uba kuma maamah din a yanxun abar tausayi ce ita,koda ita batasan hakan ba,koda har yanzu zuciyartata batayi laushi ba. Daya daga cikin ranakun da suka sake sanyaya jikin sabreen game da maamah. Ranar wata Wednesday ne,ranan kwanaki biyu suka rage ita da fu'ad din su koma madeena umra da kuma duba lafiyarta dana babies dinta,a asibitin da fu'ad yayi mata register na komai. Burinsa a duniya a haife masa yaran a garin manzon rahama annabi Muhammad,garin da jikin masoyi farin haske farin jakada yake kwance a ciki wato madeena. Tazo ta samu masu kula da ita sun gama mata komai. Ta qarasa kujerar dake gefan wheelchair dinta suna gaisawa da ma'aikatan,idanunta yana kan maamah din. Ta rame sosai,duka idan ka kalleta ba zakace mariya bace. Kwanakinnan da cikinta ya sake turowa ya fito sosai bata kallon nata. Kallo daya tak idan tayi mata to koda awa nawa zatayi da ita ba zata sake daga idanunta a kanta ba. Zama suke na kaman qawaye da masu aikin,don haka yawancin lokuta idan tazo cewa take su zauna ayi hira,a nata lissafin wai ko hirar zata daukewa maamah din kewa. Yanzun ma hira sukeyi lokaci lokaci suna kallon wani hausa film. Sunason kallo sosai,kuma bata hanasu ba indai sun gama duka ayyukansu. Musaddiq ne yayi sallama,suka amsa masa,ciki harda sabreen cikin mamakin jinsa a irin wannan lokacin. Kwata kwata ba lokacin zuwansu bane,saidai kafin ta dauke idanunta amna ta biyo bayansa. Doguwar riga ce a jikinta da qaramin hijab,kallo daya tayi mata taga kaman ta fada. Yau din ba wannan tsoron sosai a tattare da ita,ta tako kaman yadda mijinta yayi ta qaraso gaban maamah ta gaisheta ta kuma dubata sannan ta matsa gefe kusa da sabreen ba tare data damu da ko idanu maamah din bata daga ta kalli amna ba. Sun gaisa da sabreen kafin amnan tayi shuru. Sabreen ta daga kai ta kalleta da dan mamaki. Amna ba kasafai zata zauna tayi shuru haka ba,abune me wahala musamman idan akwai sabo tsakaninku. Dan tabota tayi,ta daga kai ta kalleta,sai ta sake mata murmushi,itama amnan ta maida ma sabreen "Lafiya kuwa auta?" Sabreen ta tambaya. Kaman jirar tambayar aman da ya taso mata yakeyi sai ya qarasa fitowa zuwa sarari. "Subhanallah" Sabreen ta fada a rude ta miqe tana riqe amna din dake sake galabaicewa. Kaman ya mance a inda yake,gaba daya yayo kan amna din yana rungumeta ta baya hadi da riqeta sosai hankalinsa yana tashi. Sannu kawai yake jera mata,har zuwa sanda ta kammala aman,daya daga cikin masu aikin maamah din tuni harta dauko kayan aiki tahau gyara gurin,sauran kowacce sai jera mata sannu suke cikin kulawa da tausayawa. Idanu maamah ta zuba mata tana jin qwayar idanun dama kewayenta gaba daya sun budade da yaji,tamkar an damqi garin yaji an watsa mata. Wani lafiyayyen gumi ya soma karyo mata,ta kasa dauke idanunta daga kanta zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa. "Da ka sani musaddiqu ai baku fito haka nan ba" "Daga asibiti muke......tun shekaran jiya bata da lafiya taqi kuma yarda aje asibitin saboda tsoron allura......ganin ban samu shigowa da safen ba sai nace bari mu shigo mu gaida maamah saimu wuce gida" Ya amsa mata yana goge mata jiki da tissue. "Allah ya sawwaqe.......Allah ya inganta......mu saidai mu tayaku da addu'a ai,shekara ashirin rabona da haihuwa yanzu haka" Ta fada cikin raha tana murmushi. Murmushi sabreen ta saki,sai a yanxun ta gano bakin zaren,wato shima musaddiq yayi nashi aikin. Murmushin da yazo wuyan maamah ya tsaye mata,sai taga kaman dariya sabreen take mata,kaman sabreen tana gaya mata KE DIN LOSER ce,kowa yaci nasara a kanki,abinda ya sanya wani tari ya sarqeta ta soma qoqarin zamowa daga saman wheelchair din saboda yadda zaman ya gagareta.156 "Subhanallah" Musaddiq ya fadi da sauri yana isa gareta ya tareta kafin takai qasa. Hawaye ne suka qwace mata,inama ace tana da ikon tureshi,ba shakka da sai tayi masa mummunar turewar da bazai sake sha'awar zuwa kusa da ita ko kawo mata dauki ba. Ciccibarta yayi yana maidata saman wheelchair din sannan ya daureta da belt din da suke jiki. Komawa yayi gabanta ya zauna yana duban fuskarta yana kallon gumin da yake tsatstsafo mata. Ba ita ba.....shi kansa radadi zuciyarsa take masa,saidai akwai banbancin radadin da yakeji da kuma wanda ita yakeji. Ita nata radadin na baqincikin rayuwar wasu ne,qyashi da kuma baqar hassada. Yayin da nasa radadin ya ta'allaqa ne da yadda kullum zuciyarta ke sake gurbacewa,duk da irin yanayin da take ciki,duk da irin qalubalen da take fuskanta amma hakan bai sanya ta haqura ta ajiye koma meye da yake zuciyarta ba. "Maamah" Ya kira sunanta kai tsaye da wani irin sauti bayan ya yiwa masu aikin alamar su fita. Jajayen idanunta ta daga ta kalleshi dasu,tana da magana fal bakinta saidai ba damar hakan. "Kiyiwa Allah.....kiwa manzon Allah......na roqeki ko meye muka yi miki a rayuwa.....ba domin kanmu ba don lafiyar jikinki ki manta da komai........ki duba girman Allah ki sassautawa zuciyarki......haba mana!" Ta furta da wani irin bacin rai da yakeji yana taso masa. Idanu tsaf ta zuba masa,abinda ke nuna inda bakinta a bude yake tabbas da yaji maganganu,saidai ko a iya kallonta a kansa kawai ya shaida masa maganarsa ta shigeta da wani kalar mamaki. "Ba wanda ya isa ya canza qaddarar wani.....ba wata qaddara da zata sauya kanta da kanta sai wadda ubangiji da kansa yaso sauyata.......ba wani dan adam da zai tsarawa wani rayuwarsa......kowa da yadda Allah ya tsara masa.... Me yasa ba zaki hutar da zuciyarki ba?" Ya sake fadi yau din yana jin zuciyarsa takai maqura.......a yau din yana jin yana yanke dukkanin tsammaninsa da sauyawar halaye da dabi'un maamah. "Ki yafe mana idan mun miki wani abun.....me zaki ragu dashi?" Ya qara tambayarta yana kallonta. Ba amsa,amma still hawayen basu daina fita ba "Ko bayan an cuceka ka yafe.....ba zaka ragu da komai ba sai qaruwar daraja a gunka......ki yafe mana indai mun miki laifi muddin kedin ke kika haifemu" Ya qara fada yana hade hannayensa waje daya alamun roqo. "Indai kun yadda ni din nice na haifeku me yasa ba zaku yimin abinda nakeso ba?,indai kun yarda nice na haifeku me yasa ba zakubi umarnina ba?,me yasa ba zaku kwanta nayi muku mulki irin na isassun iyaye ba?,me yasa ba zaku fahimci asiri akayimin ba?,me yasa ba zaku gane ba hawan jini bane wannan?!" Wadannan sune kalaman da suke ta kokawa a qirjinta suke koma neman hanyar da zasu fidda kansu,saidai kuma ba wannan damar,illa hawayen baqincikin rashin samun damar magana da batayi ba da suka sake wanke mata fuska. Tsam ya miqe kawai,ya kama hannun amna da jikinta ya sakeyin laushi qwarai bayan aman da tayi,ya miqa mata takalminta ta sakawa qafafunta suka fice a parlor din sabreen da maamah na binsu da kallo,kowa da mabanbancin yanayi cikin zuciyarsa. Tausayin musaddiq da hammanta kullum take kwana take tashi,bata tunanin duk yadda sukaso maamah ta shiryu idan har ubangijin daya halicceta bai shirya mata hakan ba saidai kowa yayi haquri. A zuwan da take dubata da duba yanayin gidan da masu kula da ita.....ba kalan lokutan da bata kebe ba zaune da ita,daga ita sai maamah din ta karanta mata dukkan kalar wata nasiha me ratsa jiki da zuciya......amma bata taba ganin alamun rusuna ko sanyi daga idanuwanta ba. ★"laila" Hajja harira ta sake kiranta karo na biyu. Daga kai lailan tayi wadda ke zaune qasan carpet din dakin ta kalli mahaifiyar tata. "Na'am hajja" Ta fadi dukkanin wani lungu da saqo na zuciyarta dama gangar jikinta suna azalzalarta,tana jin kaman wuta ake hurawa sassan jikinta dama zuciyarta. "Wacece ni?" "Mamana ce" Ta amsa mata Kai tsaye idanuwanta kafe a kanta. "Alhamdulillah" Hajja ta fadi tana sakin murmushi. Cikin zuciyarta cike fal da godiya ga bokan da yayi mata aikin farraqu tsakanin maamah da laila,ya gaya mata cewa wannan din qaramin aiki ne da zai iya aiwatarwa,ya mata alqawarin sai yazo duk duniya ba wanda laila taqi jini taji koda sunansa sama da hajiya mariya. "Zaki koma wajen maamah mariya?" Hajja ta gwada tambayar laila. Shuru ta danyi na wasu sakanni,sai kuma ta girgiza kanta da qarfi. "Bana so,bazan koma ba,ina wurin hajja na". Ta fadi bawai don tana nufin abinda ta fada din bane da gaske har zuciyarta. Da dariya ta qyalqyale sosai,farinciki yana cikata,lallai laila dinta ta dawo,ta dawo hayyacinta. " Na godewa Allah daya dawomin dake hayyacinki laila" Murmushin qarfin hali ta sakarwa hajjan,tanason ta sake bata tabbaci da yaqinin ta warke don ta ware mata takunkumin hana fita da sanya masu gadi su hanata fita ko nan da can. Ba abinda takeso irin taje wajen maamah,ta duqufa tayi ta mata bauta iyakar qarfinta. "Na warke hajja in sha Allahu,kawai zaman cikin gidan nan ne hajja na gaji.....ko cikin layinnan kya barni na tattaka da qafafuna ko?" Ta fada a shagwabe kaman yadda take mata a baya. Fuska hajja tadan bata tana dubanta. "Aah......ba yanzu ba laila,matar nan makira ce,duk da ance tana can tana jinya amma ba Allah a ranta,kina kallon yadda take kidnapping 'ya'yan jama'a fa?" Hajja ta fadi tana nunawa laila girman ta'addancin maamah. Wani irin tashin hankali da kuma bacin rai ne suka bijirowa lailan,ta tabbatar yau ko gobe Hajja ba zata barta ta fita ba bare ta koma wajen maamah,kenan ba amfanin rayuwarta ba tare da maamah ba?". Ta yiwa kanta wannan tambayar. A take taji indai za'a yanke alaqarta da maamah bata da wani amfanin rayuwa,don haka ta miqe tsam. "Bari naje kitchen nasha ruwa" "Ki tahomin dashi" Ta fada hankalinta kwance don tasan a kitchen din dai ba wata hanyar fita daga sassan ma bare akai ga gidan. Idanu kawai take warawa sanda ta shiga kitchen din,gaba daya kwanyarta a birkice take,neman abinda zatayi amfani dashi kawai take yi idanunta suka sauka kan gas. Da sauri ta qarasa wajen,ta saka hannu ta kunna dukka makunnansa guda hudun da yake dasu. Fita ya fara yi sosai,kafin kace meye wannan warinsa ya mamaye kowanne sashe na part din hajjan. Hancinta sosai hajja ta dinga budewa tanason tabbatarwa warin gas dinne?. Da wani irin sauri ta duro daga saman gadon tayi kitchen da mugun sauri. Duka masu aikinta ba kowa yau ballantana tayi tunanin wani ne a cikinsu,laila kawai tasan ta shiga kitchen din. Cak ta tsaya daga bakin qofar falon,qafafuwanta suna rawa zuciyarta na wani irin gudu mara fasali. Laila ce tsaye a kitchen din riqe da lighter,idanuwanta fes kan hajja dake tsaye daga can bakin qofar kitchen din. "Laila.....laila baki da hankali ne!!!" Hajja ta fadi a birkice ganin lailan tana qoqarin motsa yar robar data tare bakin lighter din wadda ita zata bata damar tashi. Wani kalar murmushi ta saki tana duban hajjan "Kina tunanin zan iya rayuwa ba tare da umarnin maamah ba?,ko kina tunanin zan iya rayuwa a inda babu ita?.....sai watarana hajja" Laila ta fada cikin qwarin gwiwa. A gigice hajja ta bude baki tana son gaya mata cewa. "Kada ki kunna laila.....indai mariya c na bar mata ke har abada,ki hada kayanki ki koma gareta" Saidai dukka wadannan kalaman basu samu damar fita daga bakinta ba sai hucin tsananin atsabar zafin wuta da qarar bindigar fashewar tukunyar gas din da suka cakude waje daya aka wullota waje,wanda daga nan bata sake sanin abinda yake faruwa ba. Qarar fashewar taja hankalin sassan matan 'ya'yanta da masu gadi dake waje,kafin balbalin wutar ya tashi hankalin kowa suka nufo sashen hajja din. Duk saurinsu turus kowa yayi,saboda wata irin muraddiyar wuta ce me azabar duhu da Zafar tana harshe ke cin kowanne sashe na hajja din. Babban sashe da yafi na kowa cikin gidan girma kyau da tsaruwa,sashen da idan ka kalleshi ka kalli na matan 'ya'yanta saika dauka su din duka sashen ma'aikatan gidanne wato boys quarters,duk kuwa da cewa mudin na mazajensu ne,dasu akayi wahalar nema da kuma samu. Tashin hankalinsu waye da waye a ciki?,suna tsaka da son tantancewa sukaci karo da hajja yashe a qasa,wadda babban jikanta ne kawai ya iya gane itace,saboda shi dinma ya shiga dazu kai mata wankinta ya gane atamfar jikinta,fuskarta kaf da kafadunta zuwa qirjinta sun koma jazur kaman an shafeta da jar hoda saboda yadda wutar ta kwaye asalin fatarta. "Na shiga uku......wayyo Allah na..... Wayyo laila......laila kada ki mutu ki barni......laila bansan kanki abunnan zai koma ba,wallahi laila bake nace a bawa kici ba......laila don Allah ki fito laila......naci buri a kanki,na shiga uku" Sune maganganun data dinga fada tana ihu tana kururuwa gami da zabura,azabar zuciya dana gangar jiki duka sun isheta aka wuce da ita asibiti cikin ambulance bayan anyi kiran fire service suzo su tsaida watar kada ta soma lasar sassan gidan. Abun kamar film kamar almara,ana fita da hajjan sanda wutar ta cinye sassan sarai,surukanta dukka dake tsaye a wajen sai kowacce ta dafe kanta. "Wayyo Allahna.....wash Allah na.... Wayyo kaina" Shine abinda suka fara fadi a jejjere,kafin kace meye wannan sai gasu duka su ukun a zube warwas a qasa sun sume. Akwai wani malamin makarantar almajirai dake a wajen,kallo daya yayi musu yace basai an kaisu asibiti ba,babban falon gidan yasa aka ajiyesu,ya karbi ruwa yayi musu tofi sosai ya bawa mazajensu yace a yayyafa musu idan sun farka a bawa kowacce tasha. Cikin qasa da minti biyar sai gasu a zaune,kowaccensu kuka takeyi wiwiwi "Wallahi saika sakeni......wallahi bazan sake zaman bauta ba..... Idan ta dawo kuma me ya rage mata?,inajin sujjada zata saka mu koma yi mata" Shine abinda matan kowacce ke gayawa mijinta cikin kuka. Duka falon sai ya rikice,ga gobara a waje ga tashin hankali a cikin gidan,su kansu mazan a rude suke,don sam duka abinda matan ke iqirari akai ba wanda yasan anyi a ciki. Gyaran murya malamin yayi ya kuma nemi su bashi hankulansu. Bayani ya musu me ratsa jiki game da lamarin,kusan abune da kaf unguwar ake magana akai yadda take bautar da uban kowa cikin gidan,kusan duk me hankali yasan aikin sihiri ne. "Indai har zaku yarda da shawarata ku yafewa mazanku,ku sake sabon zama dasu don ba cikin hayyacinku dukka kuke ba,wataqila wannan gobarar ta qone duk wani binne binne ne shi yasa komai ya warware kansa.....sai ku bita da addu'a Allah ya bata lafiya ya sake fahimtar da ita ainihin rayuwa.....". Da wannan bayanin nasa ya kashe wannan qurar,hankula kuma suka koma kan wutar dake ci wadda an fara samun daman kasheta.157 ★Tana kwance saman kyakkyawan gadon,sanye da fara qal din abaya har veil din da tayi rolling dashi,kaman yadda siraran abun hannun azurfa da zobensa da set din dan kunnensa suka sake qawata mata shigar tata. Duk da tsufa da nauyi da cikinta yayi hakan bai hanata ado ba......duk da yadda take komai da qyar amma bata yarda ta bari tayi mummunan kama ba. Ko a yanzunma akan gadon scanning take,daga daidai kanta kuma muhammad fuad jadda ne. Sanye yake da farar jallabiyya ta maza saqar morocco wadda ya yiwa ado da farin hirami daya zauna sosai a kansa,saika rantse da Allah dan asalin qasar saudiyyan ne. Wani irin ajiyayyen kyau na musamman shigar tayi masa,jikinsa da fatarsa dukka suna nuna zallar hutu da jin dadi gami da cikakken sukunin rayuwa da Allah ya bashi. Saman kujera hake,hannunsa cikin tsakiyar tafin hannunta,ya sarqafe yatsunta cikin nasa. Daga shi har sabreen din idanuwansu suna kan allon computer din,wanda balarabiyar ke yawo da kan na'urar saman cikin sabreen din da yayi wani irin girma. Sai data kammala scan din tsaf,sannan ta dora hannunta saman board din computer ta danna tana maidashi 3D scan gami da cewa cikin harshen larabci. "Sa'ureekum shai'an" Ta fada tana murmushi. "Na'am" Ya fada yana matse hannun sabreen cikin nasa. Maida mouse din tayi saman cikin sabreen din,ta matse hoton cikin take yara guda uku suka fito sosai. "Allahu akhbar.......subhanallah" Fuad ya fada muryarsa tana rawa. Damqe hannunsa sosai sabreen tayi itama cikin nata,ta kasa magana kaman yadda fuad shima ya kasa cewa komai face tasbihi ga Allah buwayi gagara misali. Yaran na kwance irin kwanciyar jarirai uku cikin mahaifiyarsu,kamanninsu sosai ya fito,har ya dinga jin kaman ya saka hannu ya daukosu. Cikin qwarewa take juya na'urar tana zoom in musu yaran daya bayan daya. Qosassu kuma lafiyayyu ko a ido,wanda ko daga yanayin girman cikin sabreen din shi kansa yasan qosassunne,duk da akance abun ba daga girman cikin bane. Murmushi ya subuce masa wanda ya taho da taruwar hawaye cikin idanunsa ganin daya daga cikin yaran da tayi zoom in din babban yatsansa na cikin bakinsa kaman me shan hannu. "Astgafirullah......alhamdulillah......subhanallah walhamdulillah wallahu akhbar" Abinda ya dinga fadi kenan,yana jin kaman kada ta daina nuna masa fuskokinsu,saidai kuma dole saboda ayyukan da suke gabanta. Sauke na'urar tayi itama murmushi yana qwace mata,ita kanta yaran sun burgeta,ta kuma jima bataji jariran da taji tanason ta gansu fuska da fuska ba irin yaran. Bata sani ba,ko hakan yana da alaqa da yadda ma'auratan suke burgeta?. Zata iya cewa tsahon shekarun aikinta,taga spouse kala kala,amma ba wadanda sukafi burgeta tare da qara mata son yin aure a kurkusa irin sabreen din da fu'ad. Da fari ma ita sam bata yarda daga nigeria suke ba,na farko dukkaninsu sunayensu batayi tunanin akwai masu irin sunan a bahaushiyar qasa ba,na biyu kuma yadda fatarsu keda wani irin haske da kadan tasu ta dara nasun,uwa uba yadda sukejin labarin Nigeria da yadda 'yan qasar suka zubda kansu a qasar saudiyya yadda ake binsu ana kamesu kaman kaji ko awaki,bata dauka akwai mutane masu qayatarwa da burgewa kaman wadannan mutanen ba,sam bata zaci zaa samu mutum irinsu a Nigeria ba. Hannun sabreen kawai ya juya ya dinga kissing,har sai da dariyar likitar ta dakatar dashi. Da kansa ya taimakawa sabreen din ta zauna sannan ta miqe tsaye,ya gyara mata rigarta da mayafin saman kanta,sannan ya taimaka mata ta zauna saman kujera tayi relaxing sosai,daidai sanda likitar ta dawo dauke da takardu zuwa gabansu. "Cikinta yanzu haka yana sati na talatin da uku,kuma yawanci 'yan uku bama bari su haura sati na talatin da hudu saboda nauyinsu......don haka ina tunanin mafi kyau sati me zuwa ayi mata CS a ciresu". Murmushi ya sake kubce masa,wannan nesar tazo kusa kenan,wannan lokacin na haduwa da yaranshi yayi kenan. Already sun yanke ayi mata CS din,saboda haka kawai yake tsoron tayi naquda,gani yake kaman zai rasata,tun randa sukazo anti natal suka samu wata mace ta rasu gurin haihuwar twins dinta. Koda ya shawarci sabreen din bata qi ba,don ita don ta ita bata da wani zabi,kome ya yankewa rayuwarta tasan bazai cutar da ita ba. Likitar kuwa dama kai tsaye ta gaya masa cewa. "Ba kasafai muma muka fiya so ko barin me haihuwar fari triplet ta haihu da kanta ba,akwai risk,CS is the best idan har ma'aurata sun amince. "Ba matsala,Allah yasa ayi a sa'a.......a turamin komai da asibiti keda buqata na komai da komai din,zamu shirya zuwa sati dayan in sha Allah". "To yayi.....zaku zo a day kafin ranar aikin,don bayan asuba koda sassafe zamu shiga da ita". Shi da kansa yayi driving nasu dama zuwa asibitin,yanzunma shi dinne,don wannan karon kwata kwata daga Jordan dan amanarsa sai abdulgafar,da iya mutanen daya taho kenan. Wani rayuwar 'yanci yake abinsa cikin garin madeena,kusan kullum saisun fita shida ita,strolling ko a mota,suci abinci su dawo gida bayan sun zazzagaya garin. Ya lura yadda yake qaunar madeena haka ita dinma,yanayin garin da calmness dinsa yana sakata nutsuwa sosai ya lura da wannan,don haka a yawan lokuta ma ba hira suke ba,suna tafiya ne kawai a low speed tare da madaidaiciyar qira'ar daya daga cikin malamanmu na addini,sai kaga duk jikinta yayi weak wani kwanciyar hankali tana ratsata. Yanzunma hakan yayi mata,saidai suna fara tafiya tace "Hamma" "Na'am adda sabreen" . Yadda ya fada din ya sakata sakin murmushi,muddin zata ce masa hamma,to shima fa zaice mata adda sabreen. "Umra nakeso nayi......". Kallonta kadan yayi sannna ya maida hankalinsa kan titi. "Yaushe kenan?". "Kafin ayimin Cs.....ban sani ba ko itace ta qarsh" "Ameenatu!" Ya kirata da wani irin sauti kaman kan motar zai subuce masa kafin ya daidaitata. "Don Allah ki rufan asiri karki qara fada,kinsan tsarki da darajar garin nan kuwa?,kinsan ko ina kayi addu'a indai a cikinsa ne ta musamman ce?,kin sani ko muna tare da mala'iku?" Ya qarasa fada kaman zaiyi kuka. Sanyi itama jikinta yayi,sai tayi qasa da kanta tana fadin. "Kayi haquri,bazan sake ba in sha Allah" Shuru yayi kaman bazai amsa ba kafin ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya. "Allah yayi miki albarka,ya rayamu a tare" "Ameen" Ta amsa tana satar kallonsa tausayinsa yana ratsata. Hanyar komawa gida taga ya canza sai kuma yace mata. "Jibi in sha Allah zamuje kiya umra......amma muje in nuna miki wani abu" Kai ta gyada,sai ya qaro sautin qur'anin kadan yaci gaba da tuqin a nutse. Sosai karatun yake ratsata,qasan zuciyarta kuma tana jaddada godiyarta ga Allah. Haqiqa tasan bata da haufi.....bata kuma da tsoron kalar uban data zabawa 'ya'yanta. Nagartar fu'ad kawai wata baiwa ce me zaman kansa,ballanta zallar tausayinsa da jin qansa akan 'ya'ya mata......especially matarsa. Ita kadai tasan wanne irin kalar miji take aure.....a father...a mentor.....uwa uba Selfless partner ne. Batasan yawan addu'o'i da take sha ba daga wajensa.....ita take dauke da cikin kawai,amma ya fita damuwa da kan kanta. Bai taba barinta ta kw ata ba addu'a ba alwala ba,bai taba barinta tana kallace kallace ko jin kade kade ba,duk da dama ita din ba gwanarsu bace,saidai akance dan adam ajizi. Da yawan lokuta yakance. "Tun a ciki kana iya koyawa yaranka dabi'a me kyau da maras kyau.....tun a ciki kana iya debewa yaranka albarka kana kuma iya sama musu albarkar.....me ciki kullum so ake ta zama cikin d'a'a da bin Allah.....ta zama very attached to her rabb,yawan sadaka.....yawan kyauta,karatun qur'ani ko sauraronsa,ambaton Allah da istigfari,ta guji gulma zagi mugunta tuggu makirci da qarya......wannan zai sanya ta samu nagartattun yara in sha Allahu". Kai ta jinjina,kuma tun daga wannan lokacin bata sake bari ya mata gyara akan duk yadda yakeso ta kasance ba. Bata tashi bude idanunta ba sai a gaban wani gida,wani irin qawataccen gida daya fusgi hankalinta tun a waje. Ya bude mata motar ta fito,suka zagayo a tare,sai yayi tsaye gaban gidan yana zura hannunsa a aljihun rigarsa ya fiddo key. "Wannan gidan na siyeshi ne da sunan yarana......mallakinsu ne halak malak cikin wannan garin na madeena,ya Allah ka shaida" Yayi maganar yana damqa maqullin a hannun sabreen. "Bude mana" Ya furta yana sakin murmushi. Sanda take budewa dukka hannunta rawa yake,idan tace bata taba ji ko ganin matar data samu tsananin soyayyar miji ba irinta batayi qarya ba. "Kawo nan raguwa ce ke wani lokacin" Ya fada yana tsokanarta sanda ya bude gidan. Da bismillah da kuma sallama suka sanya qafafunsu. Tun a parlor na farko tasan sun shigo aljannar duniya ne kawai,wani irin gida me cike da tsari da nutsuwa ta daban. Tiryan tiryan yake nuna mata kowanne sashe na gidan har zuwa sanda sukazo kan daya cikin bedrooms biyar da gidan yake dasu. Murmushi ya sakar mata yana mata nuni data bude dakin,ta maida masa sannan a hankali ta saka hannu ta murda handle din ta tura. "Wow......ya subhanallah" Ta fadi tana ware idanunta da kyau. Wani irin lafiyayyen dakin yara ne dake dauke da wasu irin designers gadaje masu dan karen kyau. Komai na dakin an shiryashi da wani irin hikima da tsari me tafiyar da hankali. Komai na dakin guda ukune tabbacin ana welcoming yara uku kenan. Curtain rug da duk wani furniture na dakin abun kallo ne. Bango zuwa bango na dakin dauke yake da frames masu rubutattun ayoyin qur'ani na tsari kala kala,sunayen annabi da sunayen Allah. Daga cikin dakin akwai wata qofa,banda tasan cikin gida suke ba abinda zai hana ta kira da dakin baby shop. Komai akwai a ciki,babu ce kawai. Tarkacen kayayyaki Cots,baby bassinet,portable cribs kala kala. Kayan sawa kuwa cikin wasu irin kwalaye na alfarma suke me dauke da wani tambari na musamman da zai tabbatar maka musamman aka yosu. Tun idanunta na iya fahimta har ta daina gane wasu kayan ma,don wasu abubuwan ko sanin mene ne batayi ba ballantana amfaninsu. Idan tace babu ce kawai babu cikin abinda ya shafi tarkacen jarirai sabuwar haihuwa batayi qarya ba,tun daga nan ta sallama,ta yadda lallai 'YA'YAN GATA zasu shigo duniya. Fuskarta kawai ta rufe da tafukan hannunta kuka yanaso ya qwace mata,komai tana kallonsa ne kamar a mafarki ba a zahirin rayuwa ba,sai ya jawota ya sanyata cikin jikinsa yana bubbuga bayanta. "Wanne irin so kake musu haka hamma?" "Beyond imagination sabreen.......ina dreaming gina big family duniyata.......inaso nayita tara yara nayita tara yara,wadanda zasu zamemin sanyin idaniya" Ya furta yana hadiye wani abu. Shuru kawai tayi tana sauraren bugun zuciyarsa,ta wani bangaren kuma zuciyarta ta cika da tarin addu'o'i da fatan samun rayyayun 'ya'ya masu albarka. ★ *_LOKACI TAMKAR TAKOBI YAKE_* Kamar yadda yayi mata alqawari ya cikashi,kwanaki biyu rak suka sauka a makka ta sauke umrarta a ranar. Tayi matuqar qoqari shi kansa ya yaba,duk da nauyin da cikinta yayi amma tayi addu'o'i sosai tayi ibada a kwana biyu kacal da sukayi. Ranar da suke sanyan rai zasu dawo sai ga uban 'ya'yan BB farouq da amarya fannah. Dukkaninsu sunyi wani irin kyau shi da fannah din,sunyi bundum abinsu gwanin sha'awa. Yayi mamakin saurin qarasowarsa,don dai kawai ya gaya masa saura kwana biyar ayi CS din sabreen baiyi zaton zai taho da wuri haka ba. "Dole muzo mu yiwa adda addu'a,sannan so nake a matsayina na uban 'ya'ya na riga kowa daukarsu" Murmushi fu'ad yayi,yana jin wannan qaunar har cikin jininsa,farouq na dabanne a rayuwarsa. Su suka tsaidasu suma saida suka sauke tasu umarar,sannan suka tattara suka wuce madeena. A kwanakin sosai sabreen taji dadin zuwan fannah,ta qarfafa mata gwiwa sosai ta kuma bata shawarwari a matsayinta na wadda bangaren ta karanta. Akwai fargaba kadan da takeji,amma tana dannewa saboda fu'ad din. Dukka tunaninsa da hankalinsa yana kanta,burinsa na duniya gaba daya ya tattara a kanta da abinda yake cikinta. Ta san ko yaya ne sai damuwar ta tabashi,shi yasa taketa qoqarin nuna komai normal ne. Ranar da zasu wuce asibiti da azahar,ko kara fu'ad qin yiwa fannah yayi,ya hanata hada kayan tafiyar,sai list data musu ya zage da kanshi ya hada komai. "Zo mu tafi daki abunmu.....muje na baki labari me dadi" Farouq ya fada yana janye fannarshi. "A dawo lafiya......Allah ya bada lada" Fu'ad yabi farouq dashi ba tare daya kalleshi ba,don idan kaga yadda yayi maganar zaka dauka badashi yake ba. Qaramar dariya sabreen tayi,kominsu yana burgeta,tsakanin farouq da fu'ad ba wanda ya isa ya shiga,idan ka shiga ma zaka fice da qafafunka don kunya zasu baka. Ba'a wuce awa daya ba ya dawo ya janye dude dinshi,can ta hangosu suna qus qus kafin ya juya ya fice. Idanunta ta lumshe,tana jin wani sanyi qasan ranta,koda ta mutu wajen aikin,fu'ad yabi bayanta,tayi imani da Allah muddin farouq yana raye yaransu ba zasu tashi a maraici ba,yaransu ba zasu wulaqanta ba,yaransu ba zasu fuskanci kalar rayuwar da ita da abbensu sukayi a duniya ba. Sallamarsu anni kawai sukaji,anni huda da saddiq. Mamaki ya kama sabreen har ta gaza daurewa,ta taka a hankali ta isa ga anni,sai annin ta rungumeta tana mata sannu,lamarin da ya sanya sabreen din sakin kukan da batasan meye dalili ba.158 Hannu anni ta dora saman bayannata tana shafawa a hankali gami da fadin "Ya isa haka mana.....kukan na mene ummmm sabreen?,habba addarsu.......bakya gani duka qannen naki suna kallonki?" Annin ta fada cikin murmushi. Kunya kadan ta kama sabreen,saita boye fuskarta saman kafadar annin tana murmushi. Qarfe takwas na dare suka shirya suka wuce asibitin bisa jagorancin tuqin BB farouq,wanda a yau yake jin kansa kamar yafi kowanne mutum farinciki a duniya. Shi yake driving din fu'ad yana gefansa,a haka suka qarasa asibitin. An shirya mata lafiyayyen daki kafin isowarsu wanda aka zuba komai da zai sakasu su jisu comfortable sosai. Sosai qwalla ta cika idanunta sanda ta bude qofar dakin,wanda aka tsarashi da gadajen jarirai har guda uku,gadajen da taji zuciyarta na bugawa,yaran zasu hau?,ko gawarsu ce zata hau?,zata bude ido ta gansu su duka ukun akai?,ko kuma za'a rasa wani ko ita a rasata?,dukka wannan Allah shi ya barwa kansa sani. Sukam gaba daya tsarin dakin ya burgesu,sunbar anni a gida saboda yanayin tafiya da zaman jirgi,don haka har huda da fannah suka samu sakewa abinsu. Huda kam kaman taso tafi kowa gaza boye farincikinta,idan triplet sukazo zanyi kaza......ni zanyi kaza.....ni zanyi kaza,har tana dariyar sai ta riga haneefa da nadra daukansu. "Idan kika kira kika tsokanesu fa zan iya daukanki mu koma salin alin.....musamman kika saka mana haneefa auta kuka" Saddiq ya fada qasa qasa yana jifanta da wani irin kallo da kana gani kasan na shauqin soyayya ne. Kukan shagwaba ta saki masa,Allah yasa fu'ad a lokacin ya fita magana da likita. Kunya ta kama sabreen,sai dauke kai tayi tana ajiye kayan kunyarta,sai yanzu ta fahimci haka sukeyi ashe suma?,kuma ko yanxun ba fasawa akayi ba. Fu'ad din baya gane kowa baya jin maganan kowa bare ya fahimta a sanda suke tare da ita. Tana jinsu ta gama,ya lallashi abarsa,koda ta dawo kusa da sabreen harara ta balla mata. "Ke bakijin kunya ne?,wannan tabarar da kikeyi ko haneefa sai haka". Dariya sosai ta ballewa hudan,tadan matsa baya kadan. "Adda.....bamayin komai fa a kanku keda hamma......adda kinsan kuwa yadda kuke komawa keda hamma?.....wallahi idanunku ma narkewa suke su juye idan kuns tare,har wani laushi jikinku yakeyi baki taba lura ba?" Daquwa sabreen ta watsawa huda da sauri. "Qaniyarki huda.....kakarki ce ni?" "Barta ta fadi fa......sister gaskiya ta fada,Allah na tuba waye yayi yaku?,har yanzu gani nake BB bai kamoku ba,in kuna wani abun sai inga tabbas mu dukka 'yan koyo ne" Cewar fannah tana dariya bayan ta gama duba bayanan asibitin da yadda zasu gudanar mata da aikin. Kai kawai sabreen ta girgiza,bata iya ce musu komai ba don bata da abun cewar. A fakaice take bin huda da kallo,ranta fari tas tana godewa Allah,tana tuna shekarun baya......tana tuna nasir,wanda tabbas inda yakai ga cimma gaci qila yanzun huda ba'a wannan matsayin take ba. Yadda ta mori miji haka tayi imani huda ta mora,ta lura da yadda hudan ke qara mulmulewa abinta,jikinta kuma ya bata juna biyu ne,fadi ne kawai basuyi ba saboda kunya,uwa uba kuma sai Allah yayi mata baiwar juna biyu maras laulayi sam sam sam,kawai dai ya sakata mugun cin da ya sanya taketa qiba. Amna ce tayi fama da laulayi,yanxunma dai daya girma sai a hankali,abinka da auta shagwaba ga quruciya,duk da shekarunsu kusan daya da huda amma rainon ma ba daya bane,amna bata saba da wahala ba,huda kuwa ta daku da wuya iya wuya,qilan ma shi yasa yazo mata ba'a wani kayan wahala ba,duk da cewa asali halitta halitta ne. Aikam zancansu dutse,don sanda fu'ad yake shigowa dakin duka kasa zama suyi,kowa yaja matarsa,daga qarshe ma sallama sukayi musu akan gobe zasu dako sammako don ayi aikin a gabansu. A hanya suke gulmarsa,fannah tace. "Kasan Allah mine......nasha gulman dude dinka,nakance wadda ta aureshi zata wahala,miskilancinsa yayi yawa,duk yadda kuke dashi sau daya ya taba rakoka zance,koda yaxo ma sai naga magana wahala take masa,nace wannan ina za'ayi walwala a gidansa?,ashe expert ne......Shahrukhan ne" Dariya sukayi gaba dayansu. Huda ta karba itama. "To ai har yanzu adda fannah....." Harara fanna ta aika mata. "Nifa ba fulbe bace.....ki daina kirana da addan nin.....bayinmu fulani ke amfani dashi" Dariya ta sake sosai. "Adda kin riga fa kin shigo cikinmu,kema kin zama bafulatana daga yau......" Jujjuya kai fannah tayi alamun ya zata iya?,anfi qarfinta. "Ko yanzun ba boss yake,yanzu fitowarmu daya shigo yana taku yana shan qamshi in ke baquwa ce ba zakice haka yake ba.....amma yana isa gurin matarsa ya koma wani mutum na daban" Huda tace tana dariya abinta. Da irin wannan hirar ta qawatacciyar soyyarsu suka qarasa gida. *WELCOME TO THE WORLD* *_The jadda's triplet_* *_a bundle of joy_* *_three little miracles_* Idanunta tsakiyar nashi,ta kasa banbance tsakanin ita dashi waye yafi wani fargaba,waye yafi wani tsoro?,waye yafi wani shiga yanayi na zaquwa da kuma shauqin ganin yaran da har a sannan basusan wanne jinsi bane?. Cikin tsararren dakin aiwatar da tiyatar,kwance saman gadon wanda likitoci ke kewaye da ita. Aikinsu suke daga qasanta,sun saki koren labule daga saman cikin nata zuwa kanta bata tare dasu......amma muhamma fu'ad jadda.....rauninta kuma qarfinta yana tare da ita. Yana zaune daga saman kan nata saman kujerar da tsahonta yakai daidai kanta,sanye yake da wasu kayan green color shima da irin hular dake kawunan likitocin. Hannunsa cikin nata hannun,ya sarqafe yatsunsu guri guda,idanun kowannensu cikin na dan uwansu. Qur'ani yake karanta mata qasa qasa,cikin wani irin daddadan sauti daya sanya hatta da likitocin sauraronsa babu shiri,idan kaji sunyi magana ya kama ne. Sosai takejin wani nutsuwa yana saukar mata,idanunta kan labbansa dake motsawa cikin gwanancewa da qwarewa cikin karatun qur'ani me girma. Daidai sanda yakai kan ayar qarshe ta cikin suratu yaseen "Innama amruhu iza arada shai'an an yaqula lahu kun fayakun,fasubhanallazi bayadihi malakuti kulli shai'in wa'ilaihi turja'un". Sound din kukan baby na farko shine ya biyo bayan saukar nashi muryar. Sake sarqewa idanuwansu sukayi cikin na juna,zukatansu na wani irin bugawa da wani irin madaukakin farinciki. "Second baby" Muryar likitar ya baqunci kunnensu da kuma wani sabon kukan jaririn. "Third one" Suka fadi sanda sabreen din ta sauke wani nishi saboda fitar yaron daga cikinta da ya sanya qirjinta fadawa sosai.(wannan wani irin yanayi ne da kowacce uwa da aka taba yiwa CS ta sanshi,wani yanayi ne da bakya taba mantashi,ya Allah ka taimaki duk wasu uwaye musulmi,wanda CS ya zame musu abu na ko yaushe yayin haihuwa ya rabbi ka basu da sauqi,ka tsallakar dasu dukka wani hadari da wata wahala dake cikinsa,masu haihuwa da kansu don isar annabin rahama ka basu naquda me sauqi,masu neman haihuwa ya Allah don hasken fuskar manzan Allah ka azurtasu da ita,ka basu masu albarka wanda zasu iya dasu ameen). (A wannan gabar nima nake barar addu'arku da bakunanku masu albarka😄,Allah ya azurtani da twins ko triplet nima🙏🏽🙏🏽,the dream of my life,ina fatan zaku sani a addu'arku,akwai wadanda suke qasa me tsarki duka ina fatan zaku jefani a Addu'arku,na gode). A lokacin fu'ad ji yake kaman bazai iya jira su zagayo da yaran su nuna musu su ba,duk da yasan definitely zasuyi hakan. Bai jima da sauke tunanin ba kuwa mutum uku suka daga musu yaran yadda mahaifiyarsu ta haifesu suna tambayar sabreen meye gender dinsu. "Boys" Ta fada muryar ta na rawa da wani irin narkewar zuciya. Shikam kasa magana fu'ad yayi,sai sake damqe hannunta da yayi cikin nasa,ya maido idonsa cikin nata yana dubanta da wani kasantaccen shauqi. "Thanks hamma......na gode sosai hamma......inama ummeena tana raye?,ka bata jikoki da jinsin da har ta mutu ake mata gorin bata haifa ba.......ka bani wata kyauta da bazan taba iya mancewa da ita ba". Hannu ya dora saman lips dinta yana fadin. " Shshshsh.....ki huta my world......ki huta duniyata" Ya aza hannunsa saman kanta yana shafa mata a hankali. Bayaso taci gaba da magana,don ya tabbatar muddin zataci gaba din to tabbas zata karya masa zuciya ne,zuciyarsa a kusa take da sakin kukan farincikin da a yau bayajin yana da nutsuwa idan bai dangana da masallacin ma'aiki ya miqa godiyarsa ba. Yana iya hangen yaran bayan an gama tsaftacesu an kuma shiryasu cikin kayan jarirai,kowannensu ya cika kayansa,kaman ba jiriri ba,abinda yake bashi mamaki yadda cikin duniyarshi ya dauki manyan yara kaman haka,yana hangensu suns wutsil wutsil,yana jin shauqinsu daga nan inda yake zaune,amma kuma bazai iya sakin hannunta ya barta yaje wajensu ba. Tana ankare da hakan,saita saki tattausan murmushi ta kuma matsa hannunsa,wanda hakan ya jawo da hankalinsa kanta "Tashi kaje hamma....tashi kaje wajensu" Kai ya girgiza mata yana sakin murmushi,qwalla cike da qwayar idanunsa. "Bazan iya motsawa daga inda duniyata take ba....until you feel okay" "Am okay hamma.....am okay" Ta bashi assurance,amma sai ya maqale kafadarshi yaqi tashi. Cikin minti arba'in gaba daya aka kammala gyarata tsaf ita da yaran,sannan aka tura gadonta zuwa dakin da zata huta. Tsaiwa nurses din kawai sukayi da yaran suna dariyan ganin drama din da akeyi tsakaninsu BB farouq huda anni saddiq harda fannah ma. Shidai abba Alhaji hamza kibiya da isowarsa kenan asibitin baya yaja ya tsaya yana dariya,don baisan shi kansa ya zaiyi musu ba,kowa so yake shi za'a fara bawa,wannan ya sanya kawai suka zarce wajen Alhaji hamza suka miqa masa daya,sauran biyun wuka sanya masa su kan cinyarsa. "Shikenan sun raba rigima ko?" Abba ya fada yana dariya gami da zube idanunsa akan yaran.159 "Ma sha Allah,tabarakarrahman.......alhamdulillah.....alhamdulillah" Abban ya maimaita yana jin wani qaunar yaran sabuwa fil tana taso masa. Har ransa yakejin alfahari da samun yaran,har cikin jininsa yake jinsu tamkar amna ko farouq ne ya haifesu,wani irin rahama yaji kaman ta sauka a family din nasa,samun qananun yara har qwaya uku a lokaci daya,a sanda suke kewan yara qananu din. Baisan wani abu da yakeso yake kuma matuqar alfahari dashi ba irin iyalin nasa......irin family din nasa ba,wani baiwa da kyautar ahali Allah yayi masa,badon yafi kowa wayo ko dabara ba. Addu'a sosai abban ya dinga musu a sarari a bayyane,su anni suna amsa masa da ameen,duk kuwa da cewa kowa ya qagu abban ya gama ganin yaran ya basu su. Na hannun nasa da suka ce masa shine babba ya juya,yayi masa kiran sallah a dama,sannan yayi kasa iqama a hagu,bai ambatar masa sunansa ba,don shi din ba mutum bane me yawan kutse ga al'amarin yaran sa ba,muddin basu sabawa al'ada ko addini ba yana barin kowa ya zabi abinda yakeso ne. Anni ya fara miqawa sannan ya dauki na biyun ya maimaita masa abinda yayiwa na farko ya sake miqawa anni,wadda ita kuma ta miqawa huda na farkon. Tana ganin irin zaquwar da huda ke ciki,ta kasa zama ta kasa tsaiwa. Hannu biyu anni ya karbeshi shima,sai ga hawayen da taketa riqewa sun soma diga saman lallausan abun daukan jariran,sai sautin kukan huda itama ya soma tashi. Murmushi abba ya saki yana tsokanar annin. "Da alama wannan kukan za'a yimin tawaye kenan,banda haka nine ya cancanci nayi kuka ai,nida aka yiwa kishiyoyi?,har uku rigis a rana daya a lokaci daya?,to ki daure zuciyarki dai karsuce matar tasu raguwa ce" Ta tsakiyar hawayen nata murmushi ya subuce mata,daga ita sai Allahnta su kadai sukasan irin farincikin da yake dawainiya da ita,yaran wani baiwa ce da rahama daga ubangiji zuwa garesu,lallai bawa ya kamata ya zama me yawan imani da qara girmama zatin mahaliccinsa. Duk wanda ya dauka kaman kada ya sauke a cikinsu,sun karade wajen har basa ganin wani bare a wajen,ganin yara uku ya janyo hankulan mutane,duk wanda zai wuce sai ya tsaya ya kalla ya musu addu'a kuma. "Wai ina muhammadu ne?" Abba da baiga fu'ad ba tun zuwansa gurin ya tambaya. "Yana can wajen matarsa......inajin ko yaran bai dauka ba" Anni ta fada tana nannade yaro daya da yake hannunta. "An kaita dakin hutu ai,inaga ya kamata sukai masa yaran.......kai saddiqu" Ya kira saddiq da suka lafe shida hudarsa suna tattauna yadda nasu yaran zasu kasance kyawawa kamar haka,sun saka yaro daya dake hannunsu a tsakiya sunata murmushi kaman wasu shashashai. Kai anni ta dauke tana sakin murmushi gami da girgiza kai,daga hudan har saddiq din akwai wauta tamkar 'ya'yan fari. Saida zamansu ya miqa ta fahimci lallai halayyarsu ta dace da juna sosai,shi yasa har yau bata taba jin kansu ko cikinsu ba. "Karbeshi kuje kukaiwa babbansu su" "To abba" Ya fadi yana sanya hannu ya karbeshi daga hannun huda,ji tayi kaman kada ta bada shi,shima ya karanci haka,sai ya saki murmushi murya qasa qasa yace "Namu yana hanya in sha Allah". Murmushi ta saka cikin tsananin jin kunyarsa ta kauda kanta,tana ganin kamar su anni zasuji abinda ya gaya mata. Dashi da BB farouq suka isa dakin,farouq yara biyu ne saman kafadarsa,yayin da saddiq din yake dauke da guda daya. Wani irin nutsatstsen yanayi dakin ke dashi,ba yawaitar haske kuma ba yawaiyar duhu,wataqila sun barshi a hakanne saboda cikakken bacci da sukeso sabreen din ta samu. Yana zaune gaban gadon saman wata farar kujerar,hannunsa cikin tsakiyar nata hannun,ya tattara dukakanin hankalinsa a kanta cikin matsananciyar kulawar da ko cikakken motsi baya so tayi. Da alama magana sukeyi qasa qasa,wanda a tsakaninsu ne,don kana dakin babu lallai ka iya jin komai. Motsin shigowarsu ya sanyashi daga kanshi,ya zube idanunsa akan yaran dake hannunsu yana jin wani irin abu me nauyi na sauka a qirjinsa. Cakudadden farinciki ne daya gauraya da nutsuwa da godiya da rahamar Allah a kanshi. "Wannan duniyar taka ba zata taba barin yarana suyi farinjini a gurinka ba da alama......kawai dadin abun......uba da yawa maganin kukan d'a" BB farouq ya fada yana isa gabanshi ya jeresu daga gefen sabreen din duka su ukun. "Minti kadan na baka ka gama kallonsu zanzo na debe kayana" Farouq ya fada da wani irin cin serious harda duba agogon hannunsa. Murmushi kawai faud ya saki,zuciyarsa na karyewa,nauyi da kunyar ubangiji tana kamashi,yana jin kaman baiwa Allah komai ba daya cancanci irin wannan kyautar da baiwar ba. Har yayi taku biyu farouq din ya dakata,ya waiwayo yana dubansa. "Ko barka kayimin ba.....kuma duk wanda baimin barka ba yana cikin black book dina" Murmushi ya sake qwacewa fu'ad,ya motsa labbansa a nutse. "Congratulations BB farouq......ina tayaka murna da samun 'ya'ya da kayi". Wani ni'imtaccen murmushi ya bayyana a fuskar farouq din,sai kawai ya dawo da dan sassarfa,kafin yakai ga qarasowa kuwa fu'ad ya rigashi miqewa suka rungume juna sosai. "Barka da arziqi dude......ina maka fatan alkhairi,ina tayamu murna mu gaba daya.....Allah yasa mu da musulunci gaba daya muyi alfahari dasu" "Ameen dude......ameen na gode" Fu'ad ya fada yana jin jinin 'yan uwantaka yana yawo a jikinsa. Zare jikinsa farouq yayi,yaja da baya yayi saluting sabreen da sai a sannan ya lura idanunta biyu. "Well done addarmu......" Ya fada yana qamewa. Murmushi ta saki idanunta na lumshewa saboda nauyi da sukayi mata,ta girgiza kai murya can qasa ta furta. "Na gode BB". Gira ya dagawa faud tare da babban dan yatsansa sannan ya juya yana fita. Da fari idanu suka zubawa yaran su duka shida ita,dakin yayi tsit sai qarar na'urar kadan kadan. Gaba dayansu bacci sukeyi,sunyi wani irin matuqar tafiya da zukatansu da wani qaqqarfar soyayyarsu data fusgi zuciyarsu lokaci guda. Tare suka kai hannuwansu kan yaran,sai suka kalli juna kuma kowannensu ya sakarwa dan uwansa murmushi. Tsam fu'ad ya miqe tsaye,ya gaji da bugawar da zuciyarsa keyi,ya dauki.yaron farko ya mannashi a qirjinsa sosai yana jin dumin jikin yaron da qamshin sabbin tufafinsa. "My heart beat" Ya furta a sanyaye har na tsahon second sittin sannan ya daukeshi daga qirjin nasa ya maida dubansa kan fuskarsa. "Wannan hamza ne.....hamza ne wannan,jarumin sadaukin nan,baffan manzan Allah......kuma ubana abbana daya bani sabon ruhi da sabuwar rayuwa" Yayi maganar daga qasan zuciyarsa yana jin soyayyar yaron. Idanunsa ya cire ya maida kanta,tana daga kwnace tana kallonsu da wani azababben kallo me cike da qauna. Rayuwarta take gani a tattare dasu,ruhinta dama komai nata.......daga sabreen ita daya ya daga darajarta ya maidata me rassa har uku. Kadan ya Matso gareta,ya manna mata yaron itama a qirjinta. "Ki masa addu'a.....hassan shine hamza" "Allah kasa ya biyo halin asalin me sunan" "Ameen" Ya amsa yana lumshe ido. Juyawa yayi tana nufar gadonsu,ya kwantar dashi sosai yana gyara masa lullubarsa sannan ya dawo kan yaro na biyu. "My world......dukkansu kamarsu daya.....kama suke da juna ta sosai da sosai......kinga har wani digo dake fuskarsu ma iri daya ne" Ya furta yana dubanta. Ajiyar zuciya ta sauke,ta gani itama,ta gani fadi ne akwai batayi ba. "Wannan babban aminina ne,dan uwana kuma masoyina.....umar alfarouq" A wannan karon ita kanta saida murmushi ya subuce mata "Wai Allah hamma......zaka kawo rigima fa.....tabbas BB bazai boye soyayyar hussain a zuciyarsa ba". "Na sani ameenatu" Ya amsa mata shima yana imagining fuskar farouq,don ba zata yayiwa kowa,shi kansa baisan gender na yaran ba sai bayan an haifesu bare wani yaji sunan da zai sanya musu. Shima sai daya mannashi sosai a qirjinsa sannan itama ya saka mata su,ya kuma sanyata ta masa addu'a kaman dan uwansa sannan yaje ya hadashi da dan uwansa ya dawo kan na ukun. "Gamboliya gambo" Ya furta da wani irin nishadi a muryarsa daya sake saka sabreen din ita kanta a nishadi,duniyar duka sai take jinta kamar tasu ce su biyar dinnan suda yaransu. "Shi wannan......abbana ne......sanadi na.......masoyina almustapha muhammad jadda" Ya qarasa fada yana kissing nasa sannan ya maidashi qirjinsa yayi masa kyakkyawar runguma. Tana iya hangen hawaye qasan idanunsa,wanda ta tabbatar na rauni ne. Wani tsohon miki ko rauni dake danqare qasan zuciyarsa. Tanaso ta sassauta masa don haka tagi gyaran murya kadan,sai ya ware idanunsa da suka canza launi akan fuskarta. "Amma hamma.....anya ba za'a samu jam'iyyu ba.....zakaso abba da yawa fa....." Murmushi ya qwace masa,ya dauke almustapha daga qirjinsa yana cewa. "Wadannan dukkaninsu masoyana ne......idan kika cire daya daya daga cikinsu to tabbas babu fu'ad......tarihin muhammad jadda bai kammala ba,bazai kuma taba zama kammalalle ba". Ta aminta da maganarsa dari bisa dari,ya matso ya aza mata almustapha din saman qirjinta,shima ta bishi da addu'a. Dawowa yayi saman kanta,yana shafa doguwar sassalkar sumarta a hankali. "Kiyi bacci my world.....yi bacci duniyata.....kin cancanci ki huta,kiyi bacci me dadin gaske,mijinki yana daga bakin qofa yan gadinki,ko yatsarki kika motsa zan jiki......ki raya a ranki duk duniya ba wata mace me gatanki......ke 'yar gatan mijinki ce......mata tabbas rakiya sukayo miki zuwa duniya". Wani sassanyan ruwan nutsuwa maganarsa ta sakar mata a tsakiyar zuciyarta,ta lumshe ido tana sakin murmushi bar batasan sanda baccin yayi awon gaba da ita ba. Ai duk yadda sabreen ta wassafa za'a sha drama da farouq sanda yaji an masa takwara abun ya wuce nan. Gaba daya farouq ya koma qaramin nanny........dariya kawai data sha banda Allah yasa tana qoqarin kiyayewa saboda dinkinta ma da batasan adadin yawanta ba. Duka sunqi gida,asibitin ya zame musu a kwanaki hudun da sukayi,kafin likitoci su taru suyi qaramar walima cikin asibitin da yaran da iyayensu dasu anni,sannan aka musu takardar haihuwa,da shaidar zama cikakkun 'yan qasa......daga bisani kuma suna shirin tafiya saiga galla galla motoci na billions of naira guda uku kyauta daga masarautar saudiyya,saqo daga sarki abdul'azeez zuwa ga d'iyoyin muhammas fu'ad da aka haifa a qasarsa. Labari ne daya zama abun dauka ga kafafen yada labarai na qasar saudiyya,labarin kuma ya lula ya dira kai tsaye akan akwatin talbijin din da aka kunnawa maamah saboda debe kewa da zaman tunani. Tana daga zaunen jikinta dukka ya dauki kyarma. A sanda sukayi waya da fu'ad din don yaji lafiyarta,ya gaya mata sabreen din ta haihu,amma batasan me ta haifa ba,mace ne ko namiji,in fact ma ita bata dauki abun serious ba,sai yanzu da idanunta ke nuna mata kyawawan yaran tamkar photocopy na muhammad din sanda ta haifeshi akayo aka manna musu. Maida idanunta ga rubutun dake wcewa tayi. "Yara maza!!....Yan ukun shahararren attajirin dan kasuwar sarrafa gold da diamond da qasar saudiyya garin madeena ya zame musu mahaifarsu". " Tayi nasara a kaina......taci nasara kaman yadda boka ke gayamin,dukiya ta zama tata......Muhammad fu'ad ya zama nata" Abinda take maimaitawa kenan jikinta dukka yana rawa kamar wadda aka sawa shocking. Gumi kuwa tuni ya jiqa gaban cotton gown din dake a jikinta,numfashinta tana jin yana mata nauyi har tana zuqarsa da qyar. Tashinsu kenan a wajen masu kula da ita zasuyi sallah wasu kuma su hada mata abincin rana,me sallar tana dawowa ta sameta a haka tana qamewa kamar wadda aka hadawa shocking. Hankali a tashe ta dauki wayar da fa'ad ya nuna musu yadda zasu kira likita,musamman aka hadata kawai saboda yiwa likitan kiran gaggawa. He's always available likitan,saboda albashi kawai jadda ya yanka masa yake biyansa monthly,ko yayi aikin duba maamah ko baiyi ba,kawai buqatar fu'ad din shine ko yaushe ya zama available duk sanda aka kirashi. Ba jimawa ya iso,ya kuma bata dukka taimakon da zai bata aka samu ta dawo da qyar,saidai danci gaban da ake sanya ran samu komai ya dagule ya koma baya. Shi mamaki matar take bashi,ba abinda ta rasa na kulawa daga 'ya'yanta,jin dadin rayuwa iya jin dadi,amma taqi kwantar da hankalinta ta warke. Guri yasa aka basu daga shi sai ita,da zuciya daya yakeson mata fada wala'alla zataji. "Hajiya.....kiyiwa Allah ki rufawa kanki asiri kaman yadda Allah ya rufa miki......ko kinaso kikai kanki lahira ne?,kina sha'awar kwanan kabari da maqabarta?,wacce irin damuwa kike da ita haka a zuciyarki data hanaki sukuni?,anya ba ciwon hassada bane silar damuwarki?,to amma idan hassadar ce ma waye zaki yiwa ita?,mutum nawa kikafi a rayuwa amma ke baki gani ba?,to na rantse da Allah muddin baki sassautawa wannan zuciyar taki ba zakita shan wahala ne,ana aiki yana dawowa baya ba wani ci gaba" Ya fada cikin jin haushinta da takaicinta ya miqe yana barin parlor din bayan ya ajiye duka magungunan da zasu bata. Idanunta suna kan likitan har zuwa sanda ya kammala ficewa. Numfashi taja sosai tana saukeshi,wani bacin rai yana qoqarin taso mata amma tana danneshi. "Ba yanzu ba mariya......ba yanzu ba,ki danneshi don ki samu lafiya......ki danneshi don jikinki ya daidaita,akwai abubuwa da dama da kike buqatar aiwatarwa,lafiyarki kuma ita ce jagora,idan babu ita ba abinda zaki iyayi" Ta yarda da wannan sashen zuciyar dake mata wannan bayanin,ta aminta da abinda yake gaya mata. Maganganun likitan sun tsaye mata a rai,lallai ne baisan wacece ita ba.....baisan wacece mariya ba,wato kawai idan baka da lafiya sai abinda ka gani?,idan ba zaka iya yiwa kanka komai ba......idan ba zaka iya cewa komai ba kawai sai abinda ka gani?. Maganar da take nanatawa kanta kenan tana tuhumar wannan ciwon.....ciwon da yayi mata dirar mikiya a sanda ya kasance takun taqi kadanne tsakaninta da arziqinta,takun taqi kadanne tsakaninta da cikar burinta fa......to kuwa me zai hana su kasa fahimtar asiri akayi mata ba hawan jini bane. Duk inda ta juya ya waiwaya fuskokin yaran take gani,ba daman ta rufe idanunta sai taga yaran guda uku sak masu kama da fu'ad,ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana jin wani razana yana kamata. Fu'ad ya riga daya samu magada,ko mutuwa yayi a yanzu ba a abinda mutuwarsa zata qara mata illa tsira da kaso daya bisa shida na dukiyarsa.......babban sake da kuskuren shine barin yaran suka iso duniya.....kuma duniyarma ta shaida. Ko sanda ta samu bacci yayi awon gaba da ita su ta dinga mafarki,a mafarkinma su shida suka koma,wani akan qafarta wani a bayanta,wani a zaune saman kanta,wani a gefenta haka dai,na saman kan nata ne ya sheqo mata kashi daya rufe fuskarta da jikinta gaba daya,abinda ya sakata farkawa kenan. Jikinta rawa yakeyi sosai,ta jiqe da gumi cikin tashin hankali,takai idanunta inda su sahura ke bacci,tanason tashinsu amma bata da wannan ikon. "Meye fassarar kashi a jiki?,anya ba ajalina aka haifo yaran nan suyi ba?" Ta tambayi kanta da kanta can qasan zuciyarta. Juya mafarkin taci gaba dayi da ma'anoni daban daban,hankalinta kuma yana sake tashi,har sanda Allah ya tashi sahurar ta dubata ta bata ruwa ta sake gyara mata kwanciya. Tanata kallon sahurar,tanaso ta tambayeta fassarar mafarkin kashi,amma ba bakin magana,haka ta maida idanunta ta kulle tana jin zuciyarta tana mata quna,tana Allah wadarai da rashin damar yin magana da bata dashi. "Mafarkin kashi fa arziqi ne....alheri ne" Wata zuciyar ta gaya mata tana tunasar da ita shekarun baya can sanda fu'ad yana yaro. Tasha yin wannna mafarkin a kanshi,duk sanda ta farka kuwa an yita tafka tsiya kenan ita da abbansu. "Ni wannan yaron bansan meye tattare dashi ba......kai baka da aiki saidai ayita mafarkin ka shafe jikinka da kashi koka shafeni?,inda Alla yake taimakona wankewa nake zuwa ni nayi a mafarkin ina dalili?,kai kuwa kaida Musaddiq duk yadda zan jaku ku wanke qi kukeyi.....kashi ai masifa ne qazanta ne". Tofa a ranar haka zata yita maganganu,hantara da kyara kuwa ranar fu'ad ya gamu dashi kenan har sai ya fita a gidan ya wuni a layi sannan hankalinta yake kwanciya. Ba fadan da abban baiyi mata ba amma bata ji ba,dole ya kawo idanu ya zuba mata,shi kuma bai taba gaya mata cewa ana tunanin arziqi bane. Abun ya tsaye mata akan jariran,tanason gasgatawa amma kuma tana qaryata hasashen nata. ★Sati biyu sukayi a madeena kaman yadda fu'ad ya tsara. Cikin sati biyun yake sanya ran sabreen taji qarfin jikinta,hakanan yaran sun sake qwari. Hakanne kuwa ya kasance,zuwa lokacin sabreen din ta warke sosai saboda irin kulawar data samu daga kowanne bangare,duk da cewa anni tun suna da sati guda ta koma Nigeria. Tana da buri sosai na hadawa yaran gagarumar walima,saidai taje ta tarar amna ta gama shirya komai da taimakawar musaddiq. Wani irin gagarumin suna da akayi sati guda ana shelarsa,sunan da duniya ta jima bataga irinsa ba. Cikin sati gudar nan fadin irin dukiyar da fu'ad ya sadaukar ma bata baki ne,irin yawan kyauta da yayi abun ba'a cewa komai,mutane da dama ya fidda da prison,mutane masu yawan gaske ya biyawa bashi,mutane masu yawa ya siyawa gidajen zama,mutane masu yawa ya dauki nauyin aurar da 'ya'yansu,a cikin dangi kuma ya sake ninka adadin mutanen da ake bawa kujerar hajji da adadin ninki uku. Mutane da yawan gaske ya dauka nauyin maganinsu da samar musu lafiya,hakanan ya qara yawan adadin marayun da nauyinsu ke wuyansa. A sannan sai ya ke qara jin yana da kyau idan sabreen ta koma hankalinta su zauna,foundation yake da sha'awar ya bude mata saboda taimakon iyayen marayun da marayun kansu. Yayi kyautar kudaden da shi kansa baya lissafawa. Duk duniya sai data shaida muhammad jadda an haifa masa abinda yafi so.....muhammad jadda ya samu abinda yafi qulafuci,duka kuma yayi ne saboda nunawa ubangiji godiyarsa a gareshi. Kwanaki uku kawai da suka rage suna suka baro birnin madeena da boundles of joy dinsu,suka sauka kanon Nigeria. Tun a airport tasan lallai haihuwa wata baiwa ce,wata abace ta daban dake cike da ni'ima baiwa da kuma tarin albarka da bata da iyaka. Tamkar tawagar matafiya haka sukayi zuga zuwa gida,ko dama fu'ad din idan yana qasar motocinsa sukan kasance ne cikin convoys koda yaushe......saidai a yanxun yawan adadin ya ninku. Sanda suka isa gida ma mutane 'yan sannu da zuwa da barka suka samu,saidai kusan duk wanda ke cikin gidan me fada aji ne,don haka cikin gayu da nutsuwa komai ke gudana,don sai data shiga daki ta sake wanka ma,aka warware yaran suma aka sakeyi musu wanka aka shiryasu cikin wasu lausasan kaya masu zuwa complete set dinsu ruwan sararin samaniya me haske. Nannys ya dauka musu qwararru tun daga madeena din,wadanda raino suka karanta gaba daya. Salwa da sameena,ba cikakkun larabawa bane,saidai acan aka haifi iyayensu suma aka haifesu,har kuma suka soma girma a yanxun,don kowacce tayi shekara kusan talatin da biyar biyar. Asalin kakanninsu 'yan nigeria ne......mata ne kamilallu da suka san rayuwa,sukasan kuma raino da abinda ake nufi da tarbiyya. A iya rayuwarta idan aka gaya mata akwai ranar da rayuwa zata sadata da manyan mutane irin wadannan zata qaryata.....mummunar qaryatawa kuwa,don tasan tabbas wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa idan har ba ta dalili ko silar fu'ad din ba. Allah ya zuba mata wani iri kwarjini da cika ido sabreen din tun asali,tana kuma da wata irin nutsuwa da kamewa......wannan ya sanya ta saje sosai a cikinsu. Irin gifts din data karba a ranar kadai sai daya sanya kanta ya kusa kullewa. Da gaske masu kudi suna sha'aninsu,da gaske masu arziqi suna sha'aninsu......da gaske rayuwa mataki mataki ce. Gifts data samu a yau idan a rayuwarta ta baya aka gaya mata ana kyauta da irin wadannan kudaden ko kayan zata qaryata,zata kalli wanda ya bata wannan labarin tace masa ya rage qarya......ya kuma ji tsoron Allah,sai gasu zube a wani daki daban,wanda ma'u tace a nan zata tarawa yaran komai nasu. Ana magariba ta rufe ganin kowa don tanaso ta bawa fu'ad lokacinsa.......tanaso ta bashi kulawa kaman yadda ta soma tsarawa rayuwarta. Yaran ta sama su salwa suka sake daukewa,aka sake fesa musu wanka da wasu baby set din da akayi musu order dinsu musamman daga wani babban kamfani dan qasar turkiyya. Akwai wani tambari na musamman jikin rigunan dake dauke da THE JADDA'S jikin rigar Kowannensu,hula da takalmi da safan hannu dana qafa duka irin guda sak da kayan da abun daukan nasu dake da adon gold a jiki. Daga wanka ta fito itama,wanda take lullube wajen dinkin da wani leather haka tayi wankanta sannan ta tsane jikinta da kyau kafin ta bude. Tururin zazzafan ruwan dake tashi da wani sassanyan qamshin turaren wanka na incense by kabo daughter jikinta yake fiddawa. Wani irin nishadi takeji......tana masifar son qamshi har batasan waye yafi wani ba tsakaninta da fu'ad din. Duka gidan a dumame yake da qamshin incense by kabo daughter,wanda kowanne sashe da daki na gidan qamshinsa daban yake fiddawa. Manyan mahaukatan botikai tasa akayi mata kusan kala goma,kowanne kuma qamshinsa daban yake fiddawa. Kanta ta busar ta kuma turareshi da kabbasar gashi duka daga kamfanin incense by kabo daughter,ta tajeshi tana qoqarin kameshi da banda taji an riqe hannayenta a tausashe ta baya. Murmushi ya subuce mata jin yaqi magana,ya kuma tsaya cak yaqi ya bata alamun da zata gane shine. Motsa labbanta tayi a hankali tana dora hannunta ta baya saman nashi. "Koda bayan na dauki shekaru da mutuwa ne......koda bayan na zama qasusuwa ko qasa cikin qabarina......muddin zaka wuce ta gurin zan fahimci cewa kaine ka wuce,don takun takalmanka zai zama ya fita daban dana kowa". Wani irin abu yaji yana ratsashi,sabreen dinsa ta fita daban da kowa.......ta iya kalaman da suke sanyashi kullum kwanan duniya yake jin kansa yana sake kumbura,kullum kwanan duniya yakejin yafi kowanne d'a namiji sa'ar mace.....kullum kwanan duniya yakejin ba za'a sake haifan mace kamanta ba. Juyo da ita yayi suna fuskantar juna,idanunsa cikin nata yana ganin ta sake masa wani ajiyayyen kyau. "Na dauka zaki tsorata ai" Ya fada a tausashe yana sanya hannunsa ya matsar mata da wani siririn gashi daya fito ta gefen fuskarta gefe. Murmushi ta kuma sakar masa tana juya idanunta. "Tsoro?" Ta tambayeshi tana murmushi,sai kuma ta miqa hannunta gefan fuskarsa tana shafa kwantacciyar sumar dake wajen. "Wannan jarumin mazan......wannan uban na 'yan ukun nan masu sunaye masu daraja......ya fidda kalmar tsoro kwata kwata daga rayuwar marainiyar nan.....ya cikata da qauna da aminci da soyayya.....ya sanyata cikin wata masarauta dake cike da tsaro......ya kewayeta da amintattun mutane......ya kuma sake bata wasu ruhikan har uku da zasu rayu da ita" Kasa magana yayi illa jawota da yayi ya rungumeta tsam cikin jikinsa. "Me zan mallaka miki my world......me zan miki da zai sake fahimtar dake girman matsayinki a raina.....me zan miki?". "Kaci gaba da sona saboda Allah,kaci gaba da qaunatata don girman zatin Allah,ka kula dani......ka kula da yayana da rayuwata.....sannan ka rayu dani ni kadai". Dagata yayi.yana murmushi gami da duban fuskarta,kafin yace komai ta rigashi. " Ina da.tsananin kishi.....amma akanka kadai.....banajin zan iya rabaka ko sharing dinka da wata". "Kin riga kin sameni.....kin sameni har abada ke kadai sabreen.....xanta maimaita miki hakan har sai ranar da kika gamsu dari bisa dari". "Na yarda dakai" Ta furta tana kallon tsakiyar idanunsa "Na yarda dake fiye da yadda kika yarda dani" Ya fadi yana sauke mata tattausan kiss. Knocking din qofar shi ya maida hankalinsu kan qofar. "Xan iya shigowa hamma?" Muryar amna ta qaraso dakin bayan tadan buda qofar kadan "Bismillah" Ya fadi yana takawa zuwa qofar dakin. Babies biyu ne rungume a kafadarta,ya miqa hannu ya karbi daya yana tayata dashi. Tare suka shigo dakin,ya qarasa gaban sabreen ya tsugunna zai miqa mata shi,kaman yasan an iso gaban mamanshi ya saki kuka. Murmushi ya saki yana bude fuskarsa,ya kalleshi da kyau sannan ya daga kansa yana dubanta. "Farouq ne......" Murmushi itama tayi tana maida kallonta kan fuskarsa. "Gyara zaman na baki shi". Saman cinyarta ya dora mata shi sannan ya saka mata pillow yadda zata jita comfortable. Baya ya koma ya zauna sosai yana kallonsu cikin burgewa,yadda take shayar dashi hamza yana gefanta hannunta saman sumar kan hamzan. "Hamma" Ta kirashi a shagwabe. "Giwar hamma" Ya amsa mata har cikin ranshi yana jin ta cancanci wannan sunan. "Nifa na shirya" "Zuwa ina?" Ya tambaya yana kallonta. "Zamuje ni dakai mu kaiwa maamah yaran nan ta gansu......bata gansu ba bata sansu ba". Shuru ya danyi yana juya maganarta,hakan ya kamata suyin,to amma shi yana tsoron dabi'ar maamah,baisan da wanne irin kallo zata dubi yaran ba,yana tsoro kada kallonta kadai ya cutar masa da yaran. Saidai kuma ya tabbatar sabreen din tana da zurfin tunani da hangen nesa,ba zata yi abinda zai zamewa yaran cutarwa ba......hakanan ya yarda da ita dari bisa dari.....161 "Is okay" Ya fada a taqaice yana miqewa "Bari na watsa ruwa kafin lokacin ki sallami sojojina ko?abbana ne kawai ba'a kawo ba" Ya fada yana kashe mata ido daya. Rolling nata idanun tayi tana murmushi. "Ba laifi" "Wannan abun yana kasheni my world......anya zaki taimakamin na barki har ki warke?" Ya fada yana karya wuya. Yadda yayi wani kalan tausayi ya sakata sakin dariya "Eh to,ai anni tana nan dai......sannan momma ma gobe zata iso". Sarai ya fahimci me yake nufi,sai yadan bata rai,ya tako zuwa kusa da ita. "Karki yadda a zame mana katanga tsakaninmu......bazan iya jurewa ba,idan kuma har na gaza jurewar komai ma zai iya faruwa" Ya qarasa maganar yana aje mata wannan zazzafan kallon nasa da taji ya tsarga mata itama tun daga tsakiyar kanta har tafin qafafuwanta. Daidai sanda kira ya shigo wayarta,ya matsa a hankali ya dauko mata wayar. "Bibo da yarinyarta sunzo,saidai na hanata ganinki,don har yanzun ban gama nutsuwa da ita ba,bazan kuma bari kowanne abu da ban gama nutsuwa dashi ba ya iso gareku" Ya furta yana saka mata wayar a hannunta. "Na tabbatar maka bibo tayi nadama zuwa yanzu,don ba komai yake damunta ba tuncan baya sai kishi da hassada" "Zan duba na gani" Ya amsa mata yana takawa a hankali zai fita a dakin,ta maida kallonta kan wayar. Kawu rufa'i ne,ta dan saki murmushi tana daga kiran. "Sannu d'iyar arziqi......sannu d'iyar albarka......wadda aka haifa tsiya tana bacci". Dariya sosai kawun ya bata. "Ina wuni kawu barka da dare" "Barkanki kadai,an samu kai qalau?" "Alhamdulillah kawu" "Ubangiji ya rayasu yayi musu albarka......ai nace kinyimin daidai da kika bugo yara uku tun a karon farko......wa yaqi arziqi?,waye zaiyi sanya a gidan arziqi?,ina me miki wasiyya,duk sanda kika tashi haihuwa dinga ajiye masa hudu hudu uku bibbiyu,idan da hali karkiyi d'an d'aya ma sam". Dariya ce taso kubce mata,amna ta danneta,saidai hakan ya nuna a muryarta. "To ai kawu abun na Allah ne,shi yake bada iya adadin da yakeso". " Eh amma ai yace ku roqeni zan amsa muku ko?,qarshen watannan zamu shiga qasa me tsarki,farouqu xai fara cika alqawarinsa.......zam zage nayita roqo miki.haihuwar haka haka din" Wannan karon saida tayi dariya sosai. "Kawu Allah ya bamu masu albarka wadanda zamu iya dasu". "Ke!,kana da wadata da arziqi irin na mijinki harka dinga tunanin kalar yaran da zaka iya dasu?,yo ko yawan taron arfa kika haifa masa ai yana da abinda zaiji dasu". Kai ta girgiza tana murmushi. "Kawu......tarbiyya ba'a nan take ba,kace ameen kawai" "To ameen sarkin tsari......nace ba?" Ya fada yana komawa serious. "Ina jinka kawu" "Ina iya tahowa zaman dab'aro?". Idanu sosai sabreen ta bude dariya tana son qwace mata. "Kawu kaifa kawuna ne,kuma namiji ne kai,ai mata suke zaman dab'aro,inama laifin ace inna A'i?(matarsa)". "Ke komai yanzu a zamanance akeyinsa,ta yaya zan turo A'i gani?,bayan ba abinda bazan iyayi miki ba?,ni damuwata na kula da d'iyar ahmadu,na rama halascin da ya yiwa rayuwata" Ta fuskanci da gaske kawu yake,saita gyara muryarta. "Kawu kada ka damu,mun dauko masu kula da yaran musamman,sannan kuma ga masu aikin gidan na ainihi". "Duk da haka ba za'a barki haka ba,xan aiko A'in ta zauna miki kona kwana arba'inne na al'ada" "To kawu Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci" Ta fada tana jin dadi qasam ranta. Ko ba komai zata ce ga wani daga dangin mahaifinta,duk da zuwa yanzu 'yan uwa ne kowa keta kutsowa da b'arkowa don nuna kulawarsa da bajintarsa akan haihuwar,tun suna madeena ma kafin sukai ga dawowa. Wayar ta sauke tana murmushi sanda take tuno baya,drama dinsu da kawu wadda kusan kullum sai an yita,rayuwa kenan.....komai yayi farko said qarshe,kuma dukkan tsanani yana tare da sauqi tabbas. Farouq yayi bacci,saita ajiyeshi kusa da dan uwansa hamza,ta miqe ta soma shiryawa,tana yi tana duban fuskokinsu. Ita kadai murmushi yana subuce mata,tana jin qaunar yaran har a cikin jininta. Duk sanda ta kallesu su ukun a jere reras saita samu kanta cikin mamakin yanzu wadannan din daga jikinta suka fito?,yanxu wadannan din 'ya'yanta ne?,mallakinta ne?,yanzu wadannan din jininta ne?,jinin muhammad fu'ad ne?. Sanda ya shigo tsaiwa kawai yayi yana qare mata kallo,tayi wannan sassanyan kyau cikin shigar atamfar data yafawa mayafi onion color. Sautin sauke ajiyar zuciyarsa shi ya dawo da hankalinta,tadan juya ido a shagwabe "Ka tsoratani hamma.....ka iya sanda ka tsaya kayita qaren kallo.....so kake kyauna ya qare?". Bai amsa mata ba har sai daya iso inda take,ya rungumeta ta baya sassanyan turarukansu suna gauraya waje daya. "Bakisan kina sake qara shekaru kina sake qara kyau a waje na ba?,tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan halittar ya kuma mallakamin ita a matsayin halaliyata......kuma uwar 'ya'yana" Luf tayi itama a jikinsa,tana jin yadda soyayyarsa take hudata tako ina. Mota uku kawai tayi musu rakiya zuwa gidan maamah din,wadda tun a bakin gate masu da guards na gidan suka taso,kowa barka yakeyi masa da nuna farincikinsa. Shi ya dauki farouq da hamza,ita kuma abba ne a hannunta wato almustapha. Yana gaba yayi sallama tana biye dashi. Mutum daya suka samu a parlor din wato saratu,ta miqe tana musu sannu da zuwa,ta kuma karbi yaro guda daga hannun fu'ad din tana musu barka da addu'o'i sosai. "Yanzu muka kai hajiya ciki,munga kaman ta gaji da zaman bacci takeso tayi" "Har yanzu ba batun magana?". Kai saratu ta girgiza cikin jimami. "Ba abinda ya canza har yanzu" Shuru kadan yayi yana juya al'amarin,a irin kulawar da take samu physically and mentally yaci ace an samu ci gaba sosai,amma yana mamakin yadda komai yaqi canzawa koda qanqani kuwa. Daga saman gadon da take zaune jingine da fuskar gadon ta daga idanunta sanda suke sallama cikin dakin. Idanunta ta zube fes a kansu kowanne dauke da yaro guda. Saratu ce ta fara isa gefanta ta aje hamza tana juyawa ta fice a dakin. Da wani irin kallo taci gaba da binsu ba tare data dora idanunta akan yaran ba da takejin ba zata iya kalla ba,zuciyarta ta fara zafi tana jin gumi yana fara keto mata. Kaman hadin baki suka isa gabanta a tare,fu'ad ya ajiye mata farouq a gabanta,ya karbi almustapha ya ajiyeshi shima kusa da farouq,ya dawo da hamza kusa da yan uwansa still idanunta akan fu'ad din yake. Yatsarsa ya sanya ya nuna hamza. "Ga hamza......wanda ya zamemin tsanin zama muhammad jadda din da ake kirana dashi a yanzu,hamzan daya bani dakin kwana......ya bani sabuwar rayuwa,ya bani sabon ahalin da zan rayu dasu,na kuma kallesu a mazaunin nawa,ya kashemin kudinsa,yayi amfani da lafiyarsa don sama mana abinda zamu rayu dashi cikin aminci.......ga farouq,wanda ta sanadinsa nakai ga hamzan daya zama qashin bayan ilimina da tarbiyyata gaba daya........ga kuma abbana..." Ya nuna almustapha yana tsagaitawa wanda da alama wani abun ya hadiye. "Abbana.....sanadi na......abbana da bani da wani abban daya haifeni wanda zai sake maimaituwa irinsa sak" Yana kaiwa nan ya miqe,ya damqi hannun Sabreen "Gasunan maamah.......gasunan ki kallesu,kiga waye bakiso a ciki?,waye yayi miki wani laifi na rashin kyautawa?.....ki.kallesu jikokinki ne......yaran da suka fito daga tsatson fu'ad.....dan da kika dauki cikinsa wata tara,d'an da kikayi naqudarsa tsakanin mutuwa da rayuwa" Yana kaiwa nan ya fara jan sabreen din suna fita a dakin. Bugawa kawai zuciyar sabreen takeyi,don tace akai mata yaran ba hakan yana nufin su fita a dakin subar mata su ba,zuciyarta ta kasa nutsuwa ko amincewa da hakan "Hamma......" "Shshshsh" Kawai yace da ita da qarfi. "Hamma yara na....." Ta sake fadi a gigice wanda sautin da reaction din yakai kunnen maamah dake zaune a dakin. Suna fita a dakin ya kama kafadunta dukka biyun ya riqeta da qarfin gaske. "Relax sabreen.....ba abinda zai faru......ba zata iyayi musu komai ba......inason zamansu a dakin ya wanke duk wani daci da tsanarsu da zata iya ji a nan gaba......ban isa na sanya ta soki ba kota soni......amma definitely!.....dole!......dole taso wadannan yaran" Qwarin gwiwar da take gani tsakiyar idanunsa shine ya bata relief,ta bishi xuwa falon suka zauna. Tana iya jin zaman yaran kusa da ita har cikin jikinta,tana iya jin wanzuwarsu sosai a tattare da ita,saidai kuma ta gaza daga idanunta ta kallesu. Zafi takeji a ranta,zafin sabreen sosai takeji,tana ganin kamar itace silar komai da komai. Sun dauki mintuna masu yawa a haka,iyayen basu dawo sun daukesu ba,abinda ya dinga bata mamaki kenan. Me yasa suka iya dauke idanunsu akan yaran?,me yasa suka iya bar mata su suka fice abinsu?. Motsin da hamza ya fara yi shine ya fusgi hankalinta ba tare data sani ba takai dubanta kansu. "Subhanallahi" Ta fadi a ranta tana mamakin zallar kamannin dake fuskar yaran. Kamannin da suka tuna mata da fu'ad din sanda yake tsumman goyo kaman haka. Idanu ta zuba masa shi kuma yana ci gaba da motsinsa,a hankali har ya fara qushin qushin din kuka,abinda kuma ya tashi sauran 'yan uwansa kenan. Mutsu mutsu suka fara yi su duka ukun,kafin kuma a hankali su kece da kuka.162 Hannun fu'ad ta riqe da kyau tana ji kaman ana matsa zuciyarta sanda sautin kukan nasu ya isa ga kunnuwanta. Jikinta duka ya dauki rawa,ta daga idanu tana kallon fu'ad. Qin kallonta yayi,kuma kaman ta fahimci yana sane yaqi kallon nata,sai kawai ta sadda kanta qasa tana sake jin yadda zuciyarta ke tsananin bugawa. Cika mata kunne sosai kukan nasu yayi. "Ya isa....kuyi shuru" Ta fadi tana jin ciwon yadda furucinta baya fita a sanda ta yishi,saidai kuma ga mamakinta sai almustapha ya fara rage sautin kukansa,a hankali dukkaninsu suka rage kukan kafin kuma suyi shuru. Mamaki taji ya kamata,ta sake xuba musu idanu wanda kaman sunsan da hakan sai hamza ya soma bude idanunsa. Tarwai qwayar idanunsa,kai ba zakace jariri bane dan sati biyu kacal,tana waiwayawa ga sauran suma duk idanunsu sun bude,kuma ita suke kallo. Batasan me yasa ba ta samu qaramin murmushi ya subuce daga fuskarta,ta samu kanta da yunqurin miqa hannunta ta kamo hannun koda d'ayane a cikinsu. Cikin wani irin ba zata da mamaki sai ga hannunta ya motsa,ta maida dubanta ga hannun,ta sake gwada dagashi xuwa gaba,ga tarin mamakinta sai hannunnata ya isa ga almustapha ta riqe yatsunsa hannun nata yana wani irin kakkarwa. Wani abu da batasan meye ba ya soma ratsa zuciyarta,hawayen da batasan daga ina suke ba suka tsinke mata. Wacce irin baiwa ko hukuncin Allah ne tattare da yaran?,abinda ta dinga maimaitawa kanta da nacewa da tambaya kenan idanunta akan fuskokinsu dukka su ukun. Sun zame mata waraka daga wani bangaren ciwon ta kenan?. Tambayar da tana ajiyeta fu'ad ya murza qofar ya shigo a hankali shidaya,don gaba daya sabreen ta gaza miqewa bare tayi jarumtar biyoshi,kawai zuciyarta tana gaya mata shikenan,shurunsu wani abun ne maras kyau ya samesu. Hannun nata yabi da kallo yana mamaki shima wanda har yanxu yana cikin yatsun almustapha,ya qarasa gabanta ya tsugunna yana duban hannun yana kuma duban yaran. "Hannunki ya motsa yau?" Ya tambayeta,saita gyada kai a hankali hawaye yana silmiyo mata daga idanunta. Qasa yayi da kansa yana tasbihi ga Allah,sun jima a haka sannan ya fiddo wayarsa. "Ubangiji ya tabbatar da lafiya" Ya fadi a taqaice yana kiran sabreen zuciyarsa ta nauyaya da girman zatin Allah. Tana kallo suna ficewa da yaran a dakin,sai ta samu kanta da gaza dauke idanunta a kansu har suka kammala ficewa. Tafi qarfin awanni uku bacci bai dauketa ba,tana jin kamar dakin nata ya koma kango bayan fitar tasu,kamar ba wani abu daya rage a dakin sai ita kadai. Abun mamakin shine,kwana tayi tana mafarkin yaran,cikin mafarkanta na daren gaba daya sune kewaye da ita,harda wanda suke magana da ita,saidai ta kasa bambance me suke fadi. Ajiyar zuciya kawai ta dinga saukewa sabreen din tana tariyo abinda fu'ad ya gaya mata na yadda ya shiga ya samu maamah din. "Ya Allah.....ka jefa matsananciyar soyayyarsu a zuciyarta ninkin ba ninkin yadda ta tsani mahaifiyarsu" Ta samu kanta da wannan addu'ar. *_NAMING CEREMONY_* Katafaren kuma qawataccen guri ne na alfarma,aka aka shirya sannan aka tsarashi musamman saboda gabatar da radin sunan. Komai na gurin kusan fari ne,farin ma irin qal dinnan me daukan hankali da kuma daukan idanu. Tun daga farkon shiga gurin har zuwa ciki wasu irin manyan hotunan ne na jiraran design daban daban suke welcoming naka. Kana shiga gurin zakasan guri ne bana wasa ba.....guri ne da akayi barin dukiya,irin barin da zai gaya maka ba'asan zafin kudin ba,don an nemesu a sanda ya dace an kuma tarasu. Komai a tsare yake,don guri na musamman aka tanada saboda ajjiye yaran. Kowa xai qarasa ya gansu,me buqatar basu gift ko wani abu makamancin hakan amna da huda suna kusa,don sune iyayen yaran gaba daya. Cikin tsari aka soma gudanar da taron,sabreena maman yaran wadda ta koma hajiya sabreen,tayi wani irin razanannen kyau cikin wani dan banzan lace da aka warewa milliyoyin kudi aka bada order saqashi a india. Ba iya lace din jikinta kawai ba......hatta da lace da atamfofi da manyan luxury warmers da aka raba a gurin duka container guda akayi musu. Tun kana lissafa adadin kayan ciye ciye da shaye shaye da aka tanada a wajen zaka gaji ne kawai,don kuwa tsarin serve yourself kawai akayi,debi da kanka,kaje ka zaba ka zuba koka aika a debo maka,ko ka kira daya daga cikin ma'aikatan dake wajen ka bashi order din abinda kake da buqatar ci. Guri na musamman aka tanadarwa jama'ar DUNIYATA,don a idanun sabreen mutane ne masu kima mutunci da daraja,wadanda suka taimaka qwarai wajen bawa dangantaka dama soyayyarsu gudunmawa. A gurinne fannah ta gabatar da kyautar da BB ya yiwa takwaranshi,wato kyautar sabon company dinsa na sarrafa auduga da fiddashi qasashen waje.....daukan nauyin duka wani abu da ya shafi rayuwarsa,tun daga karatu lafiya sutura da sauransu,yace kawai abbanshi ya zuba masa idanu,don shi aka haifawa umar din. Bama umar duka ba.....dukkanninsu yana jinsu a zuciyarsa,saidai yace bazaiyi qarya ba umar din na dabanne a wajensa. Abba baiyi qasa a gwiwa ba shima ya aiko da nashi saqon ta hannun amna,estate guda ne me dauke da gidaje dari ya mallakawa nasa takwaran. Ihu aka dinga yi a wajen,saboda yadda abun ya qawatar da mahalatta taron,wato dai gasa ce ta gasken gaske tsakanin kowa da takwaranshi. A sannan fu'ad din yana daga can gidan hutawarsa,yana kallon yadda taron yake gudana kamar a gabanshi,ta hanyar cameras da ya saka aka zuba sosai a wajen,aka kuma miqa ragamar monitoring dinsu a hannun qwararrun security dinsa. Saidai duk da haka yaji yana sha'awar zama,yayita kallon duniyarsa da yanzun ta rarrabu da wasu hadakar qananun duniyoyin har guda uku. Murmushi ya saki yana gyada kai,shi za'a yiwa wariyar launin fata kenan a ware masa abbansa?,kawai sai ya dauki waya ya kira musaddiq da nashi saqon. Sanda musaddiq ke sanar da bada kyautar JADDA WINGS ga almustapha kusan kowa sai da yaji shock,kafin daga bisani gurin ya kaure da tafi. "Sannan nima ina gabatar da tawa qaramar kyautar motar" Ya fadi yana fiddo maqullin motar daga aljihunsa ya dagashi sama ya kuma isa gaban abban nashi almustapha ya ajiye. Motace me bala'in tsada new model,wadda har yanzun ko cikin masu kudi ba kowa bane ya samu nasarar mallakarta ba. Tabbas abban abba ne,kusan yafi kowa a cikinsu tashi da gwaggwabar kyauta. Kafin abar gurin fu'ad ya sanya qaramar musabaqa ga yara masu haddan qur'ani a wajen,daga shekara goma sha biyu zuwa qasa,koda izu uku ke gareka kuwa. An gwabza musabaqa me kyau,abinda ya sake janye hankalin sabreen taji a duniya bata da burin daya wuce yaran nata su zama mahaddatan alqur'ani. Sai da aka kammala komai sannan anni itama ta gabatar da nata kyautan. Motoci ne masu kyan gaske guda uku iri daya sak,dukkaninsu farare qal,amna kuwa wani babban box ne da ba wanda yasan ainihin meye a ciki. Fannah ma ba'a barta a baya ba,itama da nata gift din,haka dai kusan duk wanda yazo wajen da nasa alkhairin da zai gabatar, Muhammad fu'ad jadda ba qashin yarwa bane,komai arziqinka komai kuma babunka ba zaka taba cewa baka amfana dashi da komai ba,wannan ya saya ma yaranshi dama matarsa wata irin soyayya da qauna. Taro ya tashi lafiya,yara kuma sun tabbatar da sunayensu na ALMUSTAPHA MUHAMMAD JADDA(FAWAD). HAMZA MUHAMMAD JADDA(FAUZAN). da babban aboki amini kuma dan uwa UMAR MUHAMMAD JADDA(FAWWAZ). Yaran sunzo da wani irin yanayi a dangi gaba daya,yan uwa dama wadanda ba 'yan uwa ba kowa ya tafi da fawwaz fauzan da fawad a bakinsa. Kusan gaban idanunshi aka gama komai,koda ya dawo gidan wajen sha biyun dare yayi mamakin haurowarta samanshi batayi bacci ba. Daga qofa ta tsaya ta langabe kafada,ya saki murmushi yana cewa. "Qaraso ciki........kinsa yau duka kishi ya kamani......na kasa sukuni sam". Ido ta zaro,ya sakata sakin murmushin da bata shirya ba. "Hamma.....kishin me?,duka mata ne fa a wajen,yaran dake wajen under age ne fa?". Idonsa ya lumshe yana duban dukiyar fulaninta da suka tutturo kaman suna tsokanarshi ne ma,lafiyayyar farar fatarta dake samun kulawa tana sake qawata su,uwa uba kuma yanayin rigar da tayi amfani da ita V neck ne da aka shimfidawa lace. Wani abu ya hadiye a maqoshinsa kawai ya miqa mata hannu,tana mamakin maganarsa ne,don haka sam bata lura da mayataccen kallon da yake watsa mata ba. Tanata masa surutu na labarin taron suna,har sai da yayi mata wata kyakkyawar runguma sannan hankalinta ya dawo jikinta,dif surutun ya dauke,shuru ya wanzu a dakin,sai sautin bugawar zuciyoyinsu. Duk wani gaba ta jikinsa sai data amsa,ya sake cusa hancinsa cikin jikinta yana jin qamshinta yana birkitashi. "Sati uku adda na......sati uku da haihuwan su fauxan right?" Kai ta gyada masa,sai shima ya jinjina kansa yana dan zame jikinsa kadan daga nata. "Naga kaman kinyi sallah daxun da asuba ko?". Qirjinta ya buga tsoro ya saukar mata. "Hamma.....nayi sallah......amma fa three weeks....." Yadda ya zuba mata jajayen idanunshi ya hanata qarasa magana,ta maida abinda takeson cewa.163 "Yayi wuri?,nasan haka zakice.....amma bakisan me nakeji bane sabrrrr". " I know hamma......na sani,ba wani motsinka da zan kasa gane manufarsa.......I will always be ready to accept you.....amma yanzu hamma,dr tace ina buqatar time kafin wannan abun,yana da kyau nayi healing sosai". Zame jikinsa yayi yana lumshe idanunsa ya koma wata kujerar daban ya zauna yana dafe goshinsa. Tausayinsa taji ya kamata,ta tako a hankali zuwa gabansa ta tsugunna tana dora hannuwanta saman cinyarsa. "May I help you?.bette" Idanunsa da suka sauya launi ya bude a hankali yana kallonta,saita sake gyara tsugunonta "I will help you to feel better" Idanunsa ya ware a kanta yana dafe hannuwanta. "No.....ba abinda hakan zai qara bazai magani ba.....komai zai iya faruwa don qishirwa kawai zaki qaramin......dawo nan ki zauna muyi hira" Abinda yace kenan da ita yana ture mata pillows din da suke gefanta. Hirar kuwa tayi masa sosai,ta dinga bashi labaran abinda ya faru a wajen. Tun yana tsume har ya ware,ya soma dariyan abubuwan da take bashi labarin,qarshe dai a nan suka bingire yana rungume da ita,basu tashi farkawa ba saida kiran wayar tashin triplet ya farkar dasu. ★Sannu a hankali kwanaki suka dinga tafiya,abubuwa da yawa sun lafa kuma sunyi sanyi,kaman darajar haihuwan yaran yazo musu da abubuwa ne masu yawa. Amna da fannah harma da huda dukkaninsu goyon ciki sukeyi,amma hakan bai rage musu kwadayi ko sha'awar yaran ba. Babu wanda ke iya kwana biyu cikakke ba tare daya kira yaji lafiyar yaran ba. Farouq kuwa da aka jarabceshi da son takwararsa gidan ya zame masa kaman hanyar wucewa,sai aiki yayi mugun cude masa yake kwana uku bai shigo gidan yaga yaran nashi ba,ya kuma kebe takwaransa sunyi ganawa ta daban da sauran. Ta bangaren maamah kuwa.....tun ranar daya kai mata yaran suka kasa bacewa daga idanu da kunnenta. Cikin awanni ashirin da hudu na yininta kowanne awa bata rufewa ba tare data tunasu ba. Sannu sannu sai takejin kamar tanason ta sake ganin yaran,kaman tana kewarsu,idan tana dakin bata da aiki sai kallon muhallin da ya kwantar dasu a waccan ranar. Wani abu takejin kamar yana shirin kamata me kama da hauka hauka akan yaran,tana yawan jin irin kukan da sukayi a waccar ranar,tana yawan jin muryoyinsu kaman suna wajen. Daga qarshe dai ta fahimci son ganinsu takeyi,saita ta rasa kuma yadda zata fahimtar dasu saratu tanason ta sake ganin yaran,don iyasu kadai kawai takeson gani banda mahaifiyar tasu. A hankali sabreen din cikin salo da hikima ta soma gyaran jikinta ta hannun dattijuwar matar nan da tasan jiya tasan yau kuma har gobe ake tafiya da ita wato Bgawos kitchen and aphrodisiac. Ingantattun kayan gyara natural na matan da suka jima a duniya kusan shekaru hamsin.08127084190/08104553105(tasan sirrin gyara sosai,gyara irin na dauri na tsaffin mata bana zamani ba,bana gama garin masu magungunan matan yanzu ba,bama gyaran kadai ba,hadda duk wani nau'in abinciccika,na biki ne suna taron sauka walima da sauransu,ko kuma kawai akwai ranar da zaki tashi bakya sha'awar shiga kitchen?,kinaso kuma abincin gidan ki ya zama ready a tsaftace kaman ke kika shiga kitchen din kikayi da kanki?,karki tsallake wannan). A jikinta kawai taji canji me matuqar yawa,ta sake jinta tana sake kintsuwa tako ina. Har ta soma gyaran jiki ta watsar,don ta tsorata sosai ranar da fu'ad ya rutsata,da qyar tasha,amma daga qarshe ya gaya mata yana lissafe da satittikan da suka rage. Tunani ta shiga sosai na yadda zata kubce masa,tanaso ta sake warkewa sosai,uwa uba kuma sunyi hira da fannah,har suka gangaro kan tsarin iyali. "Muddin period dinki ya dawo to duk sanda kuka kasance tare xaki iya daukan wani cikin" Idanu sabreen ta waro waje. "Ciki fannah......" Ta danyi dariya. "Satinsu fauzan nawa?" Dariya fannah tayi. "Shi ba ruwansa da satin yaranki nawa......indai har period ya dawo daidai shikenan magana ya qare" "Fannan BB...." Sabreen ta fada tana cin serious. "Adda sabreen" Ta amsa mata tana dariya qasa qasa. "Kibar zancan nan tukunna......me zaki bani na gyara tsarabar bare bari" Gyara zama fannah tayi. "Kamar kuwa kinsan mu bare bari ba wasa bane" Sai suka saki dariya a tare. "Bari na gutsira miki kadan.....ki samu 'ya'yan habbatussauda da dabino ki dinga ki tsaga dabinon ki cire qwallon ki zuba yayan habba din ki dinga taunawa kullum safe da dare". Da daya da daya ta dinga bata sirrikan da na barebari ne,ita kanta ta qaru ta kuma sallama (sai damu wallahi😂🥱). A tsorace take har zuwa sanda suka cika sati shida,ganin sun tsallake ranar baice mata komai ba,don washegari qaramar tafiya ta kamashi zuwa branch dinsa na lagos,don haka kawai tayi amfanin da wannan damar ta tayar da yawon arba'in. Dabara tayi,ta kira anni tace mata tana son zuwa din,amma bata samu hamman ba,tunda tasan wani lokaci idan tafiya me muhimmanci wadda take ta gaggawa irin haka ta taso masa yakan saka layinsa a flight mode ne "Yana da kyau ai,ko don a sake ganin 'yan uwa,zan gaya masa da kaina" . Hankali kwance tahau shirinta,so samu ma ta wuce mali wajen mommanta,to amma mali din tasan tayi nisa ta tsallake zuwa can,don haka kawai saita shirya zuwa abuja gidan yayan ummeenta da bai jima da dawowa Nigeria ba,ta shirya su fauzan duka da masu aikinta,ta siya musu ticket suka wuce abinsu. Sanda anni ta gaya masa harda 'yar mitarsa,yana tunanin cikin kano ne zasuyi ziyaransu gidan kawu rufai da gidansu da sauran wajen 'yan uwa su dawo gida su kwana. "Anni kina ganin ba zata debowa yaran nan iska ba?,40 days fa kawai sukayi,nima kwana uku kawai zanyi fa na dawo,meye na fitan?" Ya kasa boyewa sai daya furta. "Banda abinka fu'ad ai sada zumunci ne,kuma a al'ada ai dama ana yin wannan zagayen,kaman ba gajiya ne da kuma nunawa dangi lafiya kuke ne" Shuru ya danyi,dondai anni ce,yana kuma kunyar jayayya da ita. "Shikenan,Allah ya kiyaye hanya" "Ameen ameen" Anni ta amsashi suka dan sake tattaunawa sannan suka shiga wani maganan na daban. _Yawon arba'in ko?....hmmmm😂😂......._ _get ready muna pages din qarshe ne fa in sha Allah_🥰🥰🥰 ★Kwanansa uku a lagos,kwanan sabreen biyu a Abuja ya dawo kano. Har ya iso gidan baiyi wani tunanin abuja ta tafi ba,sai bayan ya shigo ne yadda gidan yayi masa shuru da yawa ya sakashi ya fara kokwanto. Tun a parlor na biyu ya soma da duba kitchen. Ba alamun dazu ko jiya anyi amfani dashi,kai tsaye kawai ya wuce bedroom dinta. Yadda yaga komai a killace ya bashi amsar cewa ba mutum a gidan,mamaki ya sanyashi zama gefan gadon nata,yana kallon inda aka shirya qananun gado saboda su fauzan idan a dakin zasu kwana. Sai lokacin yayi noticing wani abu,tunda ya tafi shi yake kiranta,idan ya kunna wayar yana tunanin zai samu saqonta ko miscal dinta sai ya tarar wayam,idan kuma ya tashi kiran nata sai ya kira sau nawa ana gaya masa isn't reachable,sai daga baya ya sameta. Jiyama kwata kwata basuyi waya ba,don ya shiga cikin qaguwar kammala aikin daya kaishi ya juyo gida. Ya manta rabon da yayi nesa da ita har haka.....bare su yaran da dama bai taba nesa dasu ba sai a wannan karon. Koda ya ciro wayarsa sai ya rasa waye zai kira?. Anni dai ya tabbatar bada cikakken saninta akan baisan nesa zasuyi ba akayi tafiyar ba........ita kuma sabreen ya kirata yace mata me?. Wani mummunan baci yaji ranshi ya soma yi,zuciyarsa ta soma tafasa sosai,sai kawai ya fara maimaita "A'uzubillahi minashshaidanir rajeem.....innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". A hankali a hankali yaji zuciyarsa tana yin sanyi,gefe guda kuma yana tunawa kansa maganganun malamai da yawa da kuma abbansa,hadisin manzan Allah S A W da yake gayawa maza su waye mata?.....karkatacciyar halitta da aka halicceta da qashi mafi karkacewa na haqarqari,da wannan ya danne zuciyarsa badon ranshi ya daina baci ba. Samansa ya haura yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin shigar wani tattausan yadi ruwan sararin samaniya,kawai sai ya dauki key da wayarsa ya fice a gidan,duk da cewa yunwa yakeji. Da kansa yake driving,kanshi cunkushe da tunanin ina zata je?,ina zataje da har bai sani ba?,ya miqa hannunsa ya dauki wayarsa da daya hannun dayan kuma yana riqe da steering ya soma kiran anni. Bugu uku annin ta dauka,yana iya jin maganarta da su nadra,yaran da qiri qiri tace nata ne.....bama tun ya zu ba,tun a baya inda tasan dasu da tuni sun jima da zama a hannunta,dole kowa dake da kwadayin daukarsu ya haqura yabar mata su. "Barka da dare anni" Ya furta muryarsa ba wani karsashi yana rage gudun motar. "Barka kade me babban suna,abban abbobinsa" Ta fada da dan tsokana kadan a muryarta. Duk yadda yakejin muryarsa a jagule saida sabon sunan data sanya masa ya sakashi sakin murmushi. "Mun yini lafiya?" "Alhamdulillah.....ka dawo ne?". Sai daya hadiye wani abu sannan ya amsa mata. " Na dawo dazun,bai wuce awa daya ba". "To ma sha Allah,Allah ya bada abinda akaje nema da nasara me yawa" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" Sai kuma ya danyi shuru. "Da wani abune?" Ta tambayeshi,kaman yadda ta saba da saurin gano damuwarsa tun baikai ga furtata ba. "Cewa nayi anni......wanne waje ne su fauxan suka je?" Banbarakwai anni taji maganar "Abuja mana.....ina cewa kun fara magana dama tun kafin ka tafi?". Kai ya girgiza a hankali,ya fahimci inda maganar yanzun ta dosa. Idan ya cewa anni baisani ba hakan bai dace ba,zai zamana kaman ya nunawa anni wani laifi nata da wala'alla zai saka annin jin wani iri a kanta,don haka sai kawai yace. "Ba komai anni......na dauka sun canza booking ne" "Aah abujanne dai,gidan uncle mubarak ko". "Ba matsala.......sai na shigo". "To Allah ya kawoka lafiya" Har zai yanke kiran ta rigashi. "Me kaci daka dawo?" Tayi tambayar ne don bata gamsu da yanayin muryarsa ba,kuma wani tunani ne yazo kanta a sannan. "Ba komai anni....amma zanci". " Ka qaraso ga favourite dinka anyi". "In sha Allah,godiya nake" Ya fadi yana yanke kiran. Cilla wayar yayi seat me zaman banza yana jin wani bacin rai yana taso masa. Duk wani dalili na kiranta yakejin babu shi yanzu a tattare dashi. Gudun na meye?,kaman wadda yake sarar naman jikinta?,ko soyayyar daya bata ne ta mata yawa takeson ta fara karya alqawarinsu,ta kuma fara wahal dashi kaman yadda sauran mata sukeyi a sanda suka samu soyayyar d'a namiji yadda sukeso?. Shikam yana jin bazai dauki irin wannan ba,ya tsare mata dukkan komai,itama ya kamata ta tsare masa. _hausawa sukace zo mu zauna zo mu saba,ran maza ya baci_ _wanne hukunci kuke ganin ya kamata jadda ya yiwa sabreen?_😂😂164 Karya kan motar tasa yayi zuwa unguwar tasu,yana jin ya kamata ya duba maamah,duk da ko bayan ya tafi kullum sai ya kira yaji ya suka kwana,ya kuma suka tashi. Tun daga gate masu aikin gidan suke gaidashi,har zuwa sanda ya isa qofar parlor din. Takalmansa ya cire,sam bashi da wannan dabi'ar na shiga guri da takalmi,duk da girman daraja da matsayin da Allah ya bashi,ya sanya kansa a parlor din a nutse bakinsa dauke da sallama,duk kuwa da yadda zuciyarsa ke a matuqar b'ace. Muryarsa ta sanyata daga kanta da sauri daga karbar madarar da saratu take bata. Idanunta ta kafe a kansa kafin ta maida dubansa zuwa ga bayansa kaman me neman wani abu. Ita shima yake kallo,yana mamakin yadda taketa kallon bayansa din,kwanyarsa nason lalubo masa dalilin kallon. Bugun zuciyarta yadan qaru,sai taji zuciyarta tana dan washewa daga sanda yayi sallama a parlor din. Can qasan ranta ta samu kanta da fatan Allah yasa tare yake da yaran,Allah yasa tare suke,saidai duk walwalar da taji ta sauko mata sai taji tana komawa sanda ya qarasa shigowa falon,ta kuma fahimci shi kadai ne. "Kawo na qarasa bata" Fu'ad yace da saratu sanda ta gama gaidashi yaja kujera ya zauna daura da maamah din. Amsa masa tayi cikin girmamawa,ta miqa masa hade da dan qaramin towel sannan ta miqe tana basu guri. Duk sanda ya miqa madarar bakinta sai yaga ta kafeshi da wani irin kallo,ya kasa gane abinda yasa take binsa da kallon,saidai yasan cewa lallai akwai wani abun a qasa. Wani irin boundaries takeji tsakaninta dashi,zamansa kusa da ita yana shayar da ita madarar sai taji kamar ana sauyata ana kuma sauya jiki da zuciyarta. Fuskokin yaran guda uku take gani a tasa fuskar,tanaso tace masa ina suke?,tanaso tace masa ina ya barsu?,tanaso tace masa yaje ya dauko mata su amma kuma ba halin hakan,ba kuma bakin hakan a tare da ita. "Akwai wani abu da kike buqata?" Ya tambayeta ganin yadda kallon yaqi qarewa yana kallon hannuwanta. Kai ta girgiza masa a hankali,amma still bata daina kallonsa ba. "Zaki iya rubutu?" Ya tambayeta bayan ya gama kallon hannunta guda daya wanda tun wancan ranar yaci gaba da motsi. Kai ta daga masa a hankali tana jin zuciyarta tana tsinkewa. Kowa da yake tare da ita ya gaza gano mata hanyar fadin abinda yake bakinta amma gashi daga zuwansa har ya gano hakan. Tana ji yana kiran saratu,sannan ya sakata taje ta dauko memo da sticky notes a ajjiye mata koda yaushe a kusa da ita. Sanda ta kawo din sai ya ciri sticky notes din guda daya da a biro ya dora saman cinyarta "Write it down" Ya fada a nutse yana kallonta. Gabanta ne ya fadi,jikinta kuma dukka yayi sanyi tana jin wani yanayi daya haifar mata da fara rawa da jikinta yayi. Sauke biron tayi tana jin ba zata iya rubuta komai ba. Tana jin kunyar tambayarsa yaran duk kuwa da yadda take bala'in son ganinsu......ba abinda ya dawo mata a lokacin sai gamuwarsu ta qarshe,daya ajjiye mata abun rubutu kaman haka,yace kuma ta rubuta dukka adadin abinda takeso zai bata don ta rabu da rayuwarsu har abada,kenan hakan yana nufin inda ta rubuta din sun rabu?,inda ta rubuta din da yanzu ko dan tsako bata dashi wanda zai zauna haka a gabanta ya damu da damuwarta?. Ga dukiyar ga komai tana gani......amma kuma bata wani jin d'andanonta sam a tattare da ita. Lumshe idanunta kawai tayi tana maida bayanta jikin kujera ta jingina,yadan tsaya yana kallonta saiya kalli saratu. "Idan bacci takeji a maidata daki a gyara mata gun kwanciya.....ni zan wuce,sai da safe idan Allah ya kaimu" "To ranka ya dade....Allah ya tashemu lafiya". Kai tsaye gidan anni ya wuce,ya sameta da 'yan matanta guda biyun,nadra da haneefa. Abinci sukeci,kai tsaye nadra ta shirya masa nasa abincin sannan sukayi qoqarin tashi su basu waje shida anni. "Kuyi zamanku" Fu'ad ya fadi yana ganin fuskar haneefa kamar sabreen ce a wajen saboda kamannin da suke da ita. Sosai yayi qoqarin share damuwarsa ta hanyar sakewa yayi hira da anni,saidai suna tsaka da hirar kiran sabreen ya shigo wayar annin. Bai sake cewa komai ba yaci gaba da cin abincinsa,saidai kuma yana iya dauko sound dinta ta cikin wayar. Abinda ya sake quleshi yadda yaji tana hira hankalinta kwance,suka gama maganganun da zasuyi da anni su haneefa suka karba suma suka dora. "Lafiya dai ko Muhammadu?" Anni tace dame babban suna wanda har ya kammala cin abinda zai iya ci ya miqe. Murmushi ya qirqira. "Ba komai anni......" Bata gamsu ba sam sam,saidai daga kiran da sabreen tayi kawai taga fuskarsa ta sake canzawa,amma kuma bataso ta zama me yawan sanya kai akan mu'amalolin gidajensu. Koda matsala ce tafison su koyi kasheta da kansu da kansu,hakan zai koya musu jarumta da kuma dabarun xama da juna da kuma sake samun shaquewa sosai da juna. Ya yiwa anni sallama ya fito zuwa parking lot na gidan farouq ya shigo shida fannah. Fanna ta gaidashi ta wuce ciki,shi kuma farouq din yayi tsaye daga wajen motar fu'ad na daga ciki ya zuro qafafunsa waje. "Inata tunanin kiranka ai" Fu'ad ya fadi yana dan shafa sumarsa,don duk yadda yakeso yayi avoiding damuwar amma har yanzu yana jinta cikin kansa. "Lafiya kake dude?" Farouq ya tambayi fu'ad din. Kaman zaice wani abu sai kawai ya basar,yanason koma meye ya ganar da ita kurenta da kansa,basai wani ya ji ba. "Share kawai......hannu nakeso ka sakamin a nan" Ya qarashe maganar yana miqaqa farouq din. Karbar takardar yayi yana dubawa. Takardar mallakar wani tafkeken fili ne me fadin qafa da tsaho me yawan gaske. Daga kai tukunna farouq yayi ya kalleshi. "Wanne company ne haka zai sake lashe girman filin nan?" Murmushi fu'ad ya saki a gajiye. "Ba wani company.........mafarkina nakeso na cika na gina mana gida guda daya amma me gidaje sassa daban daban a ciki,wanda zai qunshi duk wani jinin jadda......ina mana sha'awar mu rayu tare yadda yaranmu zasu tashi da zumunci fiye da namu in sha Allah". Kai farouq ya jijjiga,sai ya maida file din ya rufe. "Wannan burina ne.....ni na tanadar mana wannan filin,bazan kuma bari ka rigani ba......kayi haquri ayi amfani da nawa" Kai fu'ad ya girgiza yana dage glass din motarsa "Is too late dude........saidai ka dauki wani abun daban........amma wannan kam na riga na gama dashi,already ma yau nayi requesting ma wani company daga china zasu zo su fidda komai yadda nakeso ya kasance......idan ka saka hannun ka ajjiye documents din a hannunka,saida safe" Ya fada duka a dunqule yana jan murfin motar ya rufe abinsa sannan ya tashi motar da gudu yana fita a gidan. Da kallo farouq ya bishi har ga bace masa,sai kawai ya jinjina kai yana maida dubansa ga file din,sannan ya fara takawa yana wucewa cikin gidan. Ko sanda yaje lagos baiyi baccin wahalar da yayi ba a daren. Lagos yasan baqon guri yake,gurin da ba iyalin nashi,amma anan gurin a yanzun yasan cikin gidanshi yake,saidai ya kasance shi daya,don haka tunda asuba ya lalubi pilot nashi yace ya nema musu izinin tashi zuwa abuja a yau din. Sai wajen bakwai na safe ya kirashi,a lokacin yana cikin gym,ya sauko daga saman machine din da yake kai ya dauki wayar yana duba kiran. Zama yayi yana goge gumin jikinsa da qaramin towel. "Sir......mun samu izini,amma qarfe biyu daidai na rana suka bayar" "Good.....hakan yayi,zan kasance a airport din one din in sha Allah" "Yes sir" Ya amsa masa suna ajiye wayar gaba dayansu. Cikin wani baqin lafiyayyen yadi me tsada da aka yiwa dinkin kaftan ya shirya. Hularsa zuwa takalminsa dukkaninsu gray color ne,sosai yayi wani wani irin azababben kyau,kalar baqin kayan saman farar fatarsa ta zama wani abun kallo na musamman. Haibarsa da kwarjininsa sun ninka na koda yaushe saboda rashin walwalar dake shimfide saman fuskarsa. Shi da saddiq kawai suka tafiyar,sai jordan daya zama kaman aljihunsa saboda jajircewarsa da kuma qwarewarsa a aikinsa da kuma kula dame gidan nasa. Kasancewar juma'a ce,sai daya tsaya central mosque sukayi sallan juma'a. Yadan samu delay kafin subar masallacin,har la'asar saboda a ranar ana wani taro a nan a buja daya shafi qasa,kuma manyan mutanen daya jima basu hadu ba suka tsareshi a wajen. Daya daga cikin drivers dinsa ne ya iso da daya daga cikin motocinsa dake ajjiye a katafaren mansion dinsa na nan abujan qirar Lamborghini. Kai tsaye jordan ya karbi driving din daga hannunsa suka qarasa zuwa cikin maitama. Plate number dake jikin motarsa kadai ya sanya me gadin bude musu qofa,Kai tsaye jordan ya qarasa parking space na gidan ya ajiye motar. Bai fita a motan ba,har sai da daya daga cikin ma'aikatan gidan ya sanar da safuura matar uncle din sabreen zuwan fu'ad din. Tana kitchen tana hada abincin daren me gidan,tuni ta saki girkin tana cewa. "Ku bude masa seating room maza akai masa drinks da abinci,me gidan baya kusa,bari nazo mu gaisa". Fu'ad sunanshi kirkinsa dama kamanninsa duka ba baqinsu bane,wannan ya sanya suke matuqar girmamashi da yadda kuma ya riqe sabreen dama 'yan uwanta da kyau,duk da ba gazawa sukayi wajen riqesu ba. Daidai lokacin fitowar sabreen kenan daga wanka bayan ta murje hadin dilka dana gyaran jiki da akayi mata,tun daga ranar da tazo mummy safuura ta soma gyarata ta ciki da waje. Idanunta kan babbar TV plasma dake maqale a bangon dakin tana kallon waqar dani kake kama. Sosai waqar ke shiga ranta da wani irin yanayi daya sanya zuciyarta tayi wani irin laushi,zuciyar kuma ta fada wani matsanancin kewa da begen mamallakinta wato muhammad fu'ad jadda. Ajiye towel din hannunta tayi ta taka zuwa gaban mirror tana duban wayarta dake ajiye a kai. Yawancin lokuta tunda tazo a kashe take barin wayar,saboda tana tsoron ya kirata yaji inda take yace ta dawo gida. Tanason tadan sake samun lokaci kadan,duk da tayi kewar komai daya shafesa kewa bana wasa ba,amma a yau din sai take jin haqurinta ya gaza,koda muryarsa tana da buqatar taji. Kunna wayar tayi sannan ta zuba numbers dinsa da tuni ta jima da haddacesu,kiran ya fara gangarawa yana shiga wayarsa dake hannunsa a daidai wannan lokacin da suke gaisawa da mummy safuura. Fuskar wayar kawai ya kalla,yadan zubawa kiran idanu yana mamakin ya akayi ta kirashi a daidai irin wannan lokacin?. Yasan tabbas batasan yazo ba,don ga mummy din a zaune a gabansu ballantana yayi tunanin itace data shiga ciki ta gaya mata. Kife fuskar wayar yayi,har ta gama rurinta ta katse ba tare ma daya sani ba. Da dan mamaki ta sake daukan wayar tana sake kira,ta saka a handsfree ta ajiye tana jin yadda bugun zuciyarta ke daduwa. Still bai daga ba,abinda bai taba faruwa ba kenan a tsakaninsu. Komai yawan aiki ko uzurin dake gabansa kiranta na dabanne,to amma batasan wanne irin aiki ya samu da yawa haka a lagos din ba,don haka sai ta ajiye wayar ta miqe da nufin shiryawa,idanunta kan su fauzan dake bacci dukkaninsu su ukun abinsu.165 Tana bude luggage dinta hamra diyar mummy safuura ta tura qofar dakin da sallama ta shigo. "A tashi HAMFAAL(hamza/farouq/almustapha)". A marairaice Sabrina ta dakata da daukan kayan da take shirin yi ta dubi hamra,don tunda taji tace hamfaal to dukkaninsu take nufi. "Amma dai antynsu fawad ayimin rai don Allah......ina shirin karance littafin girke girken nan yau duka gaba dayanshi zaki jiqamin aiki?" Dariya sosai hamra tayi,don ita sam bata ma qaunar yaran suyi bacci. Bata gajiya da rainonsu,zuwansu ne yasa ta fara jin gidan nasu a mazaunin gida sosai. "Ayyah.....yau ba laifina bane......daddynsu ne yazo ganinsu". Dum!,taji qirjinta ya buga,gabanta yayi wani wawar faduwa,tsoro kuma taji ya saukar mata. Ta fidda idanu waje tana tambayar hamra. " Please hamra......banason wasa" "Serious adda......yana seating room,yanzun suka gama gaisawa da mummy" Ta fadi tana takowa ciki saboda shigowar me aikinsu da zata tayata daukan yaran. "Gasunan.......ga abun daukansu can" Sabreen ta fadi tana nuna mata tattausan abun daukan guda uku farare qal dake ajiye a gefe. Tsaf suka nadesu suka fice dasu,saita bisu da kallo har suka bacewa ganinta sannan ta maido dubanta cikin dakin tana sauke nannauyan ajiyan zuciya. Tsoron yadda zata tunkareshi takeji sosai,amma dole haka ta qarfafa gwiwarta ta som shiryawa cikin mutuwar jiki da rashin kasala. Dukkanin yaran ya aza saman qirjinsa ya rungumesu yana shaqar daddadan qamshinsu daya cakude dana mamarsu da yake iya jiyowa cikin jikkunansu (Shi yasa wannan yake zama babban abun kaico ga macen da take jego amma wai don wani kayan takaici da baqinciki ka rasa qamshi a jikinta,to wannan qarnin da qarin da kikeyi haka jikin yaronki zai zama,kada kiji haushi kada kuma kiyi mamaki idan kikaga yaronki sam baida farinjini duk da kuwa kyakkyawa ne,hakanan kada kiyi mamakin ganin ana rububin daukan yaron wata kuma bayan baikai yaronki kyau ko saka sutura me tsada ba,don Allah mu kula da wannan,qamshi rahama ne,koda kuwa iya keda hancinki ne ma 'yar uwa😂😂). Bugawar zuciyarsa ya canza sosai daga dumin yaran kawai,sai a lokacin ya sake fahimtar yayi kewarsu bata wasa ba. Ajiyar zuciya a jejjere ya dinga saki kafin daga bisani ya saukosu. Saddiq ya karbi abbanshi hamza. Da fuskarsa da tasu ya manne guri guda,ya basu tattausan kiss a goshinsu. Cikin wani tattausan milk material ta shirya,tayi wani irin sassanyan kyau,jikinta na fitar da tattausan qamshin nan nata na incense by kabo daughter da yafi qauna. Glowing kawai skin dinta yakeyi na masu danyan jego,ga cikakken hutu ga kuma gyara da takesha,wanda hatta da abun shanta mummy safuura na daban take bata na gyaran mata. Kanta ba dankwali sai qaramin mayafin material din data yafa saman kan nata,wannan ya bawa sumar kanta me sulbi daman fitowa ta gaban goshinta. A parlor ta samu mummy safuura,saita nuna mata wani kyakkyawan glass bowl me murfi "Dauki wannan ki tafi masa dashi......." "To" Kawai tace da mummy a sanyaye. Tun daga qofar setting room din ta lura ba alamun takalmin mutum ko daya,saidai duk da haka bata kawo komai a ranta ba ta taka a hankali ta shiga parlor din. Wayam ba kowa cikin setting room din,sai tattausan mayataccen qamshin nan nasa. Bugawa zuciyarta ta dinga yi d'ai da d'ai d'ai,indai batayi kuskure ba a nan din hamra ta fadi mata an saukesu,to amma ina suka shiga?. Mugun sanyi jikinta yayi,tayi taku biyu tana isa saman daya daga cikin kujerun ta zauna sannan ta ajiye bowl din hannunta. Wayarta data fito da ita ta zaro ta soma kiran mummy safuura. Bugu biyu ta dauka "Ya akayi sabreen?". " Mummy.....banga kowa a seating room din ba.....ba kowa" Ta qarasa fada a sanyaye. "Kaman yaaya?,yanzun hamra ta baro parlor din fa" Mummy safuura ta fadi da dan mamaki a muryarta. "Alla ba kowa mummy" Ta sake fada tana dora tafin hannunta saman goshinta,tsoro yana kai kawo a zuciyarta bayan wani hasashe da zuciyarta tayi mata. "Bari ina zuwa" Mummy ta fadi tana cike da kokwanton abinda sabreen ta fada. Wayar ta ajiye,tana shirin miqewa daya daga cikin yaran gidan ya shigo. Fuskarsa washe da madaukakiyar fara'a,hannunsa riqe da rafas na dubu daya sabbi kar a miqe. "Mummy.....baqonku ya tafi.......yace a baki haquri sauri yake,lokacin tashin jirginsu yana dab da qwacewa,yana gaidaki da kyau,ya mana kyakkyawar sallama,yau duka mu masu aikinki muna cikin alheri dumu dumu,yace a baki wannan" Ya fada yana miqa mata envelope din dake daya hannun nashi. "Waya bawa yaran ya dawo dasu?" Ta tambayeshi tana miqa hannunta. "Gaskiya dasu naga sun fita......ba da mamarsu suka tafi ba?" Batasan amsar da zata bashi ba,sai kawai tace dashi "Madalla.....ka dubamin idan uba ya gama wanke motarnan" Ta fada tana karbar envelope din. Budeta tayi a hankali,saiga sabbin dollars a ciki miqaqqu. Ido tadan fitar cikin mamaki,me yasa sam mutumin nan bai iya qaramar kyauta ba?. Komawa tayi ta zauna tana ajiye envelope din a gefanta,mamaki yana cikata. Ya zaiyi da yaran daya tafi dasu?,bai tsaya koda ganin mamansu ba?,bai kuma gaya mata zaije dasu ba?,kada dai ya zamana sabreen yaji tayi ita ta amsheta bata sani ba,ko kuma wasa takeyi da aurenta?. Kai tsaye ta dauki waya ta kira sabreen. "Dawo ciki ina parlor" Bata ko iya amsawa mummy ba,ta kashe kiran kawai ta miqa bata ko bi takan furar data ajjiye ba ta fice. '"Zauna a nan" Mummy safuura tace da sabreen tana nuna mata gefanta. Sam fuskarta ba alamun wasa a ciki. "Sabreen" Ta kirata a tsanake. "Na'am mummy" Ta amsa mata kowacce hanta dake cikinta tana kadawa. "Ki gayamin gaskiya,da iznin mijinki kikazo nan koba da izininsa ba?" Shuru tayi tana juya maganar mummy,nadama da tsoro suna cikata. "Ki fadamin gaskiya,don kinfi kowa sanin halina bani da sauqi,ba ruwana da wai kedin 'yar 'yar uwar mijina ce.....bata yadda za'ayi baban yarannan yayi tattaki yazo har nan,ya kuma dauke yara ba tare da sanin mahaifiyarsu ba" . Wannan abun wani baqon abune wajen sabreen din,ballantana ita din da sam sam bata son tashin hankali ko kadan. "Da saninsa,saidai baisan nan zamuzo ba,kuma har mu kwana" Take ran mummy safuura ya baci sosai,ta zubawa sabreen idanu tana jin kaman ta rufeta da duka. "Me yasa?" Ta tambayeta a taqaice,irin taqaicewar data nuna mata batason wani dogon sharhi ko dogewa. "Mummy tsoro nakeji". " Wani irin tsoro kuma?" Ta fada tana zare mata idanu waje. "Ciki mummy,inaso na huta......shi kuma haihuwa yakeso akai akai". "Haihuwarce ke bakiso saboda mamarki kuda yawa ta haifa?". Kai ta girgiza saboda tasan magana mummy ta gaya mata a fakaice. "Hutawa kawai nakeso na danyi mummy sab....." "Gafara can dalla ki rufemin baki malama,"Amma ban taba raina wayonki ba irin yau sabreen......ni'imar da Allah yayi miki kika sanya qafa kike shureta?.......ashe baki da hankali ban sani ba?,idan muhammad jadda beso haihuwa a dukiya da lafiyar da Allah ya bashi ba......ki gayamin me zaiso?,sometimes mata ku kuke kirawa kanku kishiya wallahi" Idanu a waje ta daga kai tana duban mummy jin ta ambaci kishiya. "Yes....kishiya,ga abinda mijinki yakeso amma ke kullum kina opposition party nasa.....me zai hana ya nemo wadda ra'ayinsu da komai nasu yake daidai?......to wallahi bari na rantse miki,nima yau dinnan basai gobe abbanku ya dawo ba,ba zaki sake kwanar mana a gida ba.......sauqinki daya na sakaki a jirgi na maidaki gida a ranar yau,muddin kika sake ya dawo yaji abinda ya faru saikin gwammace bakizo abuja ba....zan rufa miki asiri bazan gaya masa ba,shine kawai abinda zan iyayi miki" Kuka sosai ya qwacewa sabreen,komai ya dagule mata cikin lokaci qanqani. Kafin mummy ta nema musu ticket a gama komai nononta duka ya ciko yanata damunta,alamun dake nuna mata tabbas su fawwad sun tashi. "Me zai basu idan sun farka suna jin yunwa?,ta yaya zai iya kulawa dasu?" Tambayar data dinga yiwa kanta kenan,harta kasa jurewa ta tambayi.mummy safuura. Duk da yadda tayi laushi lokaci guda ta bata tausayi amma saita jefa mata harara sanda take hada mata sauran kayanta. "Ke kika sani,ban sani ba" Ta fada cikin jin haushi. Haushin kuma bai hanata ta hadawa sabreen din komai ba "Idan kinje kin nutsu kinwa kanki fada na miki bayani". Abinda kawai tace da ita kenan. Da kanta ta dauketa a motarta har airport,bata kuma dawo ba sai data tabbatar da jirginsu ya tashi qarfe takwas na daren ranar. K'arfe tara da minti ashirin da uku daidai na dare cave din airport ya saukesu a qofar gidan muhammad fuad jadda. Karon farko da taji tana fargabar shiga gidan,abinda bata taba ji ba tun bayan data amsa cikakkiyar sunan matar muhammad fu'ad jadda. Bata sake fahimtar waye take aure ba......bata sake fahimtar girman matsayin da Allah ya bata ba sai da suka tasamma shiga unguwar. Tun a main get na shigowa unguwar suka fara fama da tambayoyi na securities dake tsaron kowanne gate na unguwar. Yawancin gurare saita laqo tayi magana sannan suyi salute nata su dage musu su wuce,abinda bai taba faruwa ba kenan,don duk inda zasu plate number din motocinsu ne kadai amsarsu,amma yau din sai da tasha bayani kafin su samu su iso qofar gidan. Gaba daya masu gadin gidan mamaki ya kamasu ganin madam guda a cab. Cikin rawar jiki da kuma girmamawa suka bude motan suka shiga fidda luggage dinsu zuwa cikin gidan. Tun a veranda ta sallami nannies dinsu fawwaz,cikin fargaba ta dinga takawa zuwa cikin gidan,tana jin kamar ta kirasu su tayata bawa fu'ad din haquri. "Barka da dawowa......tun daxu nake zuba idanun ganin fitowarki ai" Muryar ma'u ta sauka a kunnenta. Dukka dauriyarta ta tattaro ta sakar mata murmushi "Yauwa ma'u......ashe kina ciki" "Eh na shigo ne na zare socket na freezer dincan,kayan ciki duka sun qanqare,kada mu tashi girki gobe qanqara ta hana ciro komai......ya hanya?,dazun na dan jiyo qushin qushin din mutanen nawa". Dan murmushin yaqe ta saki,ta san tana nufin su fauzan ne. "Kinsan basa rabo da rigima idan sukaso,duka su ukun saisun hade maka kai" Dariya ma'u tayi. '"Ai inajin sai wajen gobe zamu hadu dasu,Allah ya huta gajiya uwar dakina" "To ma'u na gode". "Ba'a buqatar komai ko?" Ma'u ta tambaya. "Babu ma'u,bari na qarasa ciki" Da haka sukayi sallama ta wuce parlor na biyu kai tsaye ya doshi hallway dinta.166 Wata matsananciyar kewar yaran takeji tana damunta,tanajin kaman ba awanni kadai ta dauka bata gansu ba,ji take kaman shekara bata gansu ba,wani qaunarsu tana sake taso mata kaman ba zata iya qara minti daya cikakke bata gansu ba. Kai tsaye dakinsu dake hallway din ta bude,bata gansu ba a ciki,hakan ya bata tabbacin suna samanshi kenan. Kaman ta wuce dakinta amma sai taji ba zata iya ba,ta soma takawa zuwa saman nasa tana qoqarin dake zuciyarta.. Ta kusa minti uku bakin smart door din sannna ta matsa inda tayi scanning nata,kai tsaye kuma ta bude kanta da kanta tana bata daman shiga. Scenes din watannin baya da suka shude ne suka shiga dawo kata kanta sanda ta hangeshi zaune saman minotti sofa dinsa.......watannin da take a matsayin sabreen dinta ta ainihin,wannan sabreen din wadda babu qaunar Muhammad fu'ad ko qanqani cikin rai da zuciyarta. Yana zaune gabansa ya bude apple system dinshi har guda biyu,da alama kuma aiki yakeyi sosai,koma ya jima a zaune a wajen,don ya saye idanunshi da farin glass din nan nasa dake bada kalan light blue sama sama wani lokaci wanda ke taimaka masa wajen zuqe hasken screen din. Kansa ya daga a nutse yana gyara zaman glass din a fuskarsa,lokaci guda kuma ya dauke idonsa daga inda take a tsaye ya maida idanun kan screen din yana taba Bluetooth din kunnensa "Am hearing you" Daya fada shi ya alamta mata cewa waya yake amsawa. Duk da haka bata fasa sallama ba don tasan ita din me laifi ce,ta taka a nutse tana shiga ciki idanunta nakan wani irin gado dake wani shiyya daban na parlor din. Kaman gado kama lilo haka aka tsarashi,amma idan kakalli cikinsa sosai zaka fahimci gado ne na 'ya'yan gata wanda aka yi masa lafiyayyar shimfida me tsananin taushi. Gaban gadon ta tsaya tana qare musu kallo,sai wani tausayinsu taji yana ratsata. Kayan jikinsu na dazun yanzun ba sune a jikinsu ba,an canza musu su zuwa kayan bacci masu taushi na jarirai farare qal dukka iri daya,hatta da socks na qafansu dana hannunsu,sai suka sakeyi mata kyau,taga kaman sun qara girma akan girman su na dazu. Kewarsu takeji sosai,don haka ta miqa hannu don fara daukan almustapha. A qirjinta ta sakashi,ta rungumeshi sosai tana shafa kan fawwaz. Ta jima a haka kafin ta sanya fawad a kafada daya,fawwaz a daya kafadar,ta fara takawa a hankali tana sauka dasu. Sai data kwantar dasu sannan ta dawo ta dauki fauzan. "Kinci darajar ma'aiki daya hana raba uwa da d'anta......banda hakan da daga yau ba zaki sake dora hannunki kan yara na ba" Maganar daya fada kenan wadda ta sanyata tsayawa cak. Batayi tunanin ya gama wayar da yakeyi ba,a sanyaye ta juyo zuciyarta na bugawa,saidai kafin ta gama ajiye kallonta a kansa tuni har ya wuce dakinsa abinsa. Jikinta a mace ta gama shirin kwanciya tana juya maganarsa a ranta. Tayi fakare tana jira taji ko zataji shigowarsa?,don ko dakin bata kulle ba,hakanan su fauzan duka akan gadajensu ta kwantar dasu,saidai harta gama zaman jiransa bacci yayi awon gaba da ita. Koda ta tashi har an gama sallar asuba. A gajiye ta miqe tana duba ko ina na dakin,ba alamun ya kwana a dakin,a haka taja jiki zuwa toilet tayi wanka sannan ta hada da alwala ta dawo ta bada farali. Shiryawa tayi cikin sassauqar doguwar riga data mata kyau ta fidda quruciyarta. Qarfe bakwai da ashirin ta wuce zuwa kitchen da nufin shirya masa breakfast,don bata da scheduled dinsa na satin gaba daya,amna ta tabbatar dole zai buqaci breakfast din. Kafin ta kammala har ma'u ta gyara su fauzan gaba dayansu,sai ta shiga wuce daki kawai ta gyara jikinta. Kwalliya tayi sosai data dace da safiyar,ta wadata jikinta da sassanyan qamshin nan da tasan yana masifar so. Bata ma dauki su fauzan ba kai tsaye ta wuce zuwa samanshi. Koda ta samu daman shiga parlor din bata wani ji motsinsa ba,don haka ta wuce zuwa master bedroom dinsa. Tun a nan ta fahimci tuni ya fita,don ga alamu nan sun nuna,comb dinsa da towel dinsa,da qaramin cup da yasha ruwan dumi duka saman mirror. Zama tayi gefan gadon tana maida numfashi,hakan yana nufin yayi fushi sosai da ita kenan?. Wayarta ta bude ta soma kiran numbers dinsa,saidai kowacce gaya mata akeyi a kashe take,dole ta haqura da neman nasa ta sauko qasa saboda kukansu fawwaz da yayi mata maraaba. Tana shayar da yaran amma duka hankalinta yana kan tunaninsa da tunanin abinda ya faru. Duk hankalinta a jagule yake gaba daya,ta dinga gwada kiran number dinsa amma bata shiga,tun tana sanya rai harta haqura ta daina neman nasa,sai gajeran saqo data tura masa,wanda shima har magariba tayi bata samu amsa ba. Magariba ta wuce,isha'i ta shigo itama ta wuce,shuru ba shi ba wayarsa ba dalilinsa. A haka ta samu su fauzan dukkaninsu sukayi bacci,don dama idan sun jima sukai bayan ishai'i,idan kuma suka kwanta matuqar sun tashi to yunwa ko qishirwa ya tashesu,basa farkawa yawanci da safen ma,sai sukai bakwai da rabi har takwas suna bacci abinsu. Baccinsu ya sake sakata ta dan qar samun nutsuwa. Wannan karon koda ta kirashi wayar yana shiga,amma haka ta qaraci b'urarinta ta katse bai amsa ba. Dole ta ajiye komai gefe,ta qarfafa jikinta ta shiga wanka. Saidai duk wata laka ta jikinta an zare mata ita. Batajin sam sam zata iya ci gaba da karbar wannan hukuncin nasa,batasan haka ya iya hukuncin 'yar shariya me ciwo ba sai yanzu. Zaifi mata sauqi ya kulata,yayi mata fada ma,idan ta kama ma ya zaneta ko ya zageta zaifi sauqi. To yau kam ma duk wani shirinta bata samu ganin shigowars gidan bama kwata kwata. Har sha daya na dare idanunta biyu,batasan kuka ta fara yi ba saida taji damshi saman fuskar fawwaz dake shan mama wanda ya tashi a sannan,daga qarshe ma tana tsaka da bawa fauzan mama bacci yayi gaba da ita,wanda a sannan sha biyu saura na dare. Washegari taga alamun gidan ya kaana,saidai duk saurint na ta sameshi bata iskeshi ba. Wunin ranar gaba daya dauriyarta a ya qare,wuni tayi a daki ma'au nata cigiyarsu,don batason ta fito ma'u taga canji a fuskarta ta zargi wani abu. Ranar ta rantse ba zatayi bacci ba sai taga shigowarsa,koda zata kwana ne a zaune,don haka koda goma na dare yayi ta tabbatar yaran sunyi bacci,goma da rabi ta sauya kayan bacci. Lafiyayyun kayan barci ne masu wani irin sulbi da yauqi,wadanda ta siya a HUGUMA CLOSET da sukazo kai tsaye daga Dubai. Suna da wani irin bin jiki da daukan hankali,lingerie ne sosai na isassun mata. Curling iron ta saka ta zauna ta yiwa gashinta wani irin nannadewa kaman macaroni,sannna ta tattarashi zuwa left side na kafadarta gaba dayanshi. Daga daya side din tadan tareshi da mabanbanta shapes na hair clips. Tattausan lips nata ta wadata da lips gloss daya qara masa kyau da sheqi,ta wadata kowanne part na jikinta da kalar turaren da musamman aka yishi saboda gurin,wannan turarrukan ta sansu da amfaninsu ne a wajen mummy sultana mummyn twins BATOUL DA BENAZEER(Gudun k'addara). K'awace ta mummy safuura,ranar da suka isa abuja tazo mata a gaggauce da nata twins din din batoul da benazeer,wadanda aketa shirye shiryen bikinsu dukka su biyun,duk da bikin saura watanni shida,amma tsananin gata idan kaga yadda aketa shiri saika dauja gobe ne ko jibi. Ita kanta ko yaya ta motsa qamshin jikinta burgeta yakeyi,ta tsaya gaban madubi taga yadda ta ajiye wani sassanyan kyau,ta gamsu da kanta da kanta,don haka saita tofe su fauzan da addu'a ta kuma wuce zuwa parlor na biyu. Ba sabonta bane kallo,amma yau da kanta ta kunna Tv din,ta kuma kamo tashar tumbin giwa ind suke wani hausa series. Rabi da rabin hankalinta yana kan wayarta,batasan adadin saqonnin data aike masa a kwanaki ukunnan ba,amma ko qwaya daya tal bata samu amsarsa ba. A baya ta shiga tsanani na rayuwa da barazana kala kala,amma bata taba jin tsananin da yakai mata wannan wahala ba. Bata taba jin nutsuwa da lafiyar zuciyarta tana mata barazana ba irin na wanann lokacin. A wannan lokacinne take tabbatar da ma'anar TASHIN HANKALI da kuma rashin sukuni da gasken gaske. Ba fahimta take cancan ba,saita yanke kiran fannah kawai suyi hira. A qalla sun kusa awa daya da fannah din,har sai da taji farouq ya iso kusa sosai,tana jinsa yana saka fannah din dariyar da bata shirya ba,dole ta yanke kiran. A gogo ta kalla,taji kewar nata mijin yana saukar mata,banda wannan matsalar data faru a tsakaninsu da tuni zuwa yanzun shima yana tare da ita,ta sauke idanunta tare da ajiyar zuciya zuwa saman Tv din,daidai sannan ya murxa handle din qofar parlor din ya shigo da sallama muryarsa can qasa,yanajin kowacce gaba ta jikinsa a mugun jigace. Idanunsa da sukayi laushi qwarai su ya fara zube mata,tayi masa wani irin fitinannen kyau,ya sauke dubansa kan gashinta da yasa kwalliya da wani irin salo,salon da hatta yanayin zamanta saman kujera yau din na musamman ne..... Cikin wani irin hanzari ya dauke kanshi daga dubanta sanda ta daga risunannun idanunta zuwa kanshi. Yadda ya dauke kan baima ko nuna ya ganta ba ya mata wani irin ciwo,duk da haka ta daure tace masa. "Sannu da zuwa". "Yauwa " Ya amsa still ba tare daya kalli sashenta yana takawa zuwa hallway din. Idanunsa ya lumshe,yana jin wani abu yana harbawa zuwa kowanne sashe na jikinsa. Ta masa kyau iyaka,ta fusgi hankalinsa qwarai,saidai har yanzu yana jin tasirin fushinnan da yakeyi da ita. Ta dauka masa yara sun fita daga gidan daya killacesu ba tare da yasan adadin nisan da zatayi ba,ta dauka masa yara ba wasu cikakkun masu tsaronsu......uwa uba ta taba masa martabar igiyar aurensa......tayi nisan da bai kamata ace ta yishi ba tare da muharraminta ba.....ba kuma tare da izininshi ba. Idan har ya sake mata haka da yawa gaba yana da guarantee din me zaya faru?. Iyali suke tarawa shida ita,fata yake kuma su gina iyalin da kowa zasu zame masa abun alfahari. Babban abun dake mintsinar zuciyarsa shine......tsoronsa daya karanta cikin idanunta tun wancan ranar,to meye yake mata a shimfidarsu da zai sanyata gudunsa har irin haka?. Ya sani......duk duniya ita zata fadi wayeshi a wannan fannin.......tafi kowa alfahari dashi........wani irin yanayine da take ji dashi cikin rayuwar aurensu,amma dare daya saita nema sauya hali?. Alqawari ne ya yiwa kansa tun first night nasu......bazai sake kasancewa da ita ba ta wani yanayi na daban har sai da shauqinta da cikakkiyar amincewarta,koda kuwa son kusancinsa da ita zai masa mene ne.......bare a yanzun da yake cikin fushi da ita.......banda wannan kallon daya mata na yanzu da yake shirin wargaza masa lissafin da baiyi niyyar wareshi a nan kusa ba. Dakinta ya wuce kai tsaye,kaman yadda ya saba shiga ya gansu suna bacci batasan ma shigar tasa ba bare fitowarsa. Ya qarasa gaban gadon,ya riqe yatsun yaran idanunsa a kansu. Wani sanyi yaji zuciyarsa tana yi.......da gaske da ake cewa yara sanyin idaniyar iyayensu ne. Yana iya jinta sanda ta tura qofar dakin ta shigo yana tsaka da musu addu'a,bai waiwayo ba,bai kuma tsaya da abinda yake ba har ya gama tofesu da addu'ar sannan ya juya a hankali da zummar fita a dakin. Dab da zai isa bakin qofar tasha gabansa,ta shiga ta tsakanin hannayensa ta tsaya a tsakiyarsa tana lalubar qwayar idanunsa ta saka nata a ciki. Narkakkun idanun nan nata da suke kasheshi......narkakkaun idanun nan nata da suke zare masa dukka wata laka tasa,su kuma kashe wutar fushi dake ruruwa a zuciyarsa,idanun da har yau wani haske da qyalli suke kasa kaman ranar farko daya fara ganinsu. "Zan wuce a gajiye nake.....bacci nakeji". Ya fada da wata maqalalliyar murya daga can qasan maqoshinsa,muryar da takeso lallai saita tona asirin dake danqare a zuciyarsa da gangar jikinsa. Qwalla sosai ta cika fararen idanunta,ta koma masa kaman wata yar shekara goma saboda yadda ta maqale.kafada. "Zakaje ka kwanta kayi bacci ko?,sabreen ita kuma ta mutu?". Sai kawai ta fashe masa da kuka. Cije labbansa yayi,yana jin yadda kukanta ke huda masa sassan jiki yanason kassarashi da kassara qarfin qwanjinsa dana zuciyarsa. Ya dake sasai yana fadin. "Nifa ba kuka na tambaya ba,hanya nakeso a bani......zancan sabreen ta mutu kuma ai bai taso ba.....ki bani hanya please" Ya fada a dake yana basarwa,yana fata ta matsa ta bashi hanyar kafin ya qarasa karyewa daga hawayen dake fita a fuskarta. _Wato dai da gaske kai ragon namiji ne indai akan sabreen ne?,zamu gani,zaka iya daurewa?😂😂_167 "Hamma" Ta sake kiransa muryarta a karye da sautin kuka. "Am really sorry hamma......Allah bazan sake ba" Tun daga tsakiyar kansa har tafin qafarsa yaji kiran sunanshi da tayi,zuciyarsa tayi sanyi amma tana gaya masa ba yanzun ba......da sauran karatun. "Naji na haqura.....matsa na wuce" Ya sake fadi yana kuma tsare gida. Fararen idanunta da suka dan surka kadan saboda kuka ta daga ta kalleshi,shima idanunsa suna kanta,amma koda ta kalleshin sai ya dauke kansa,saboda tsigar jikinsa ya da yaji gaba daya ta tashi. "Hamma baka haqura ba....." "Goyaki kikeso nayi?,shi zai tabbatar miki na haqura ko kuwa yaya?". Yadda yayi maganar da wani basarwa sai ya karya mata gwiwa,gaba daya sai taji kaman ya tozartata da yadda yake qoqarin tankwabe rarrashin da take masa. "Bani hanya please" Ya sake fada yana kuma hade gira. A hankali ta janye jikinta ta bashi waje,ya taka hankali kwance kaman wani abu be tsikareshi ba ya fice a dakin. Sulalewa tayi a wajen,sai wani sabon kukan ya tsinke mata. Tsoro taji yana shigarta,tsoron kada ya zamana fu'ad ya fara juyawa daga muhammad din data sani......zuwan mazajen yau da mata ke complain a kansu. Idan haka ta kasance a kanta bata jin zatakai labari.....don ta ta'allaqa dukka burinta da fatanta a kansa,ta karkatar da akalar rayuwarta a kansa,ta saka buri me yawa kuma akan nasa. Tas taci kukanta ta godewa Allah,sannan ta miqe tana qarfafawa kanta gwiwa. Ta shirya abincin duka cikin wani kwando na daban ta haura masa sama dashi. Ba kowa a parlor din,tafi sanya ran wanka ya shiga,don haka ta jera komai tsaf saman dining ta wuce bedroom dinsa. Kai tsaye ta murza handle na toilet din ta shige abinta gaba gadi. Cikin Jacuzzi ta hangoshi,ya sakarwa kansa ruwa wanda yake wanka duk kumfar daya sabawa jikinsa. Idanunta ta Maida ga bathtub din data cika masa d ruwa da kuma sassanyan turaren wanka,ba alamar ya taba ruwan ma bare akai maganar yayi wanka dashi,saita hadiye abinda ya taso mata ta nufi jazucci din kai tsaye. Zuge qofar tayi,ta taka a nutse tana shigewa ciki. Ya ganta sarai amma bai waiwaya ba,yaso ace sanda bai shiga azumin fushi da ita ba ta kawo kanta a irin wannan lokacin,lallai da ya samu ganima. Yana jinta ta gama tsokane tsokanenta bai nuna yasan tana ciki ba,ya gama ya nannade jikinsa da towel ya fito. Tana tsaye a nan kamar wata hoto har yabar toilet din,ranta taji ya soma baci,to amma ya zatayi?,duk ita ta jawo,ta tabbatar fushinsa lallai ba abu bane me dadi,tunda ya gwada mata ta gani. Ko data zuba masa abinci ma cewa yayi ya qoshi baya buqata,ta san halinsa koda yana buqatar abincin ma ba lallai yaci,zaice bazaici abinci bane late,don haka ta shiga kitchen ta hada masa fruit salad me kyau da nau'un fruit din da basu da matsala ga lafiya da dare,a cisu kuma a kwanta. "Ajiye a nan xanci" Ya fada kawai yana duba wasu file. Ajiye masan tayi,ta kuma sauka qasa tayi shirin bacci. Still cikin wasu red night gown ta shirya,ta saki gashinta kafadunta yanzun bayan ta tajeshi daga curling nashi da tayi a dazu. Sanda take kawo yaran zuwa gadonsa dake gefan dakin,yana kwance cikin duvet a qudundune amma tun shigowar farko sassanyan qamshinta ya ruskeshi har inda yake din. Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa,bai taba kawowa zai iya jure wadannan kwanakin ba.......bai taba zaton yana da haquri a kanta har haka ba sai yanxu. A nutse ta gama komai,ta sake musu addu'a,ta shiga toilet nashi tayi brush sannan ta hauro gadon tana rage hasken qwayayen dakin. Ya jita kusa dashi sosai,amma bai taba kawo zatayi abinda tayin ba a yanzun. Wata kyakkyawar runguma tayi masa ta baya,cikakken dukiyar fulaninta da shayarwa tasa y qara cika ya tokare a bayansa. Saura kadan numfashinsa yayi qaura daga gangar jikinsa,wasu irin kaifafan kibiyoyi ta sakar masa wanda suka ratsa sassan jikinsa d wani irin matuqar sauri suka aike masa da wani nannauyan yanayi daya sakashi takure jikinsa ba tare daya shirya hakan ba. Matseshi tsam tayi ta baya,tana bashi wata kyakkyawar runguma. Har cikin jininsa sai da yaji yadda dumin jikinta da tudun dukiyar fulaninta ya zauna sosai saman fatar bayansa. Sosai ya riqe numfashinsa don hana kansa jin abinda yakeji yana masa yawo a jiki,amma yadda zuciyarsa ke bugawa da sauti ya sanya ta kasa aiwatar da hakan,ya kamo numfashin da qyar sannan ya tattaro juriyarsa yana dan zamewa. "Stay away please" Ya fada da wata irin kasalalliyar murya. Maganan tashi tazo mata a bazata,tsam tayi da ranta tana dakatawa da komai,tana jjn yadda zuciyarta ke bugawa da sauri,tana kuma jin yadda itama a yau din take jin ta dokanta dashi. "Hamma" Ta furta a sanyaye. Qarasa janye jikinsa yayi,sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta "I'm not in the mode,im feeling off" Ya furta muryarsa tana qara yin can qasan maqoshinsa. Idanunta da suka fara lumsheea ta ware tana kallonsa. Yau ita jadda yake cewa he's off?,off for what?. Tana tsaka da wannan tunanin ta ganshi ya dauki babban blanket nasu da pillow ya aza saman sofa ya kwanta abinsa ya lulluba har saman kansa. Baki ta sake kawai tana kallonsa,abun gaba daya ya bata mamaki,yau ita abben su fauzan din ke yakicewa?,ita din yake dodging?. Wani matsewa zuciyarta dake qirjinta tayi,sannan a hankali wani hawaye me dumi taji kawai ya sauko mata saman fuskarta. Da hanzari ta sauko daga saman gadon kai tsaye,ko bedroom slippers dinta batayi ta kai ba ta soma fita a dakin da sassarfa. Komai da takeyi yana jinta,bai kuma motsa ba har sai da yaji fitarta,kunne ya kasa sosai,kusan mintuna biyar sannan ya yaye duvet din ya sauka a hankali yana fita a dakin. Bata duka bedrooms din hakanan bata parlor din,abinda ya bashi tabbacin sauka tayi gaba daya daga sassan nasa. Wani qaramin murmushi ya saki,qasan ranshi yana fadin ashe babu dadi. Maida qofar parlor din yayi ya kulle abinsa ya koma bedroom din duk da yadda zuciyarsa ke jin matsananciyar kewarta. Yaran gaba daya ya sauke daga nasu gadon,ya maidosu kan gadon nashi,ya bajesu ya shige cikinsu abinsa ya kwanta sosai yana sakin ajiyar zuciya,yana kuma jin kusancin dake tsakaninsa da yaran. Kwata kwata bacci qaurace mata yayi,batajin zata iya jurar wannan abun. Yayi mata komai zata jure amma banda nesanta kanshi da ita,ita kanta cikin tsananin buqatarsa take,don ya riga ya horata ta wannan fannin ya kuma maidata irinsa. Abu daya ne ya sanyata ta guje masa stitches nata na CS dinta da take ganin kamar zai farke. A haka bacci barawo ya lallabo ya saceta,cike da fata da sanya ran zai shigo har dakin ya nemeta,ko don saboda yaran ma. Sam baccin baiyi wani tsaho ba ta farka firgigit,ta shiga buda idanunta sosai tana sanya ran ganinsa ko yaran ko alamun ya shigo ya fita,amma bataga komai a ciki ba. Ranta taji ya bacu,zuciyarta ta quntata,sai ta shiga toilet tayi fitsari ta daura alwala,ta dawo tayi nafila raka'a shida. Tana saman abun sallan tana addu'o'inta wani baccin ya sake waftarta,wanda shine bacci mafi tsaho da tayi,don bata tashi farkawa ba sai da akayi kiran farko. Yanzunma bataga alamun ya shigo ba,kawai sai wata qwalla ta cika mata idanunta. Dama yake da ciwo kayi abandoning mutum?. Yaran sun tsaye mata a rai,tasan zai wahala ace duka tsahon daren ba wanda ya nemi nono,kawai saita sauka daga kan abun sallar ta soma takawa a hankali ta fice a dakin. A Hankali ta bude qofar bedroom din,mamaki da haushi ya cikata fam kaman zata fashe. Wato shi ya sanya yaranshi a gaba abinsa suna sheqa baccinsu ko a jikinsu?,ita gata nan wahalalliya ta hana kanta da kanta sukuni duka saboda yaran da nasa tunanin,kawai saita saki kuka me sauti,kukan daya tasheshi ya kuma saka yaran motsawa,daya bayan daya suka farkawa tarwai abinsu,sai kuma a sannan suka fara neman abincinsu ta hanyar fara cilla qafafu suna son fara sakin kuka. "Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihinnushur" Ya fada sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta inda ta zauna gaban gadon tana musu kuka. "Me akayi miki?" Ya tambayeta hankali kwance,tambayar data sakata sake masa hararar da batasan tayi ba,sai ya dauke kansa kawai yana sauka daga gadon a hankali ya wuce toilet don daura alwala yayi raka'atanil fajr kada ta subuce masa. Rigima ce fal idanunta yake hanga,shi kuma indai wannan rigimar ce a shirye yake da ita,ya fita jinta ma. Ko kafin ya gama alwala ya fito dakin duka ya karade da kukansu su ukun,ga mamar tasu zaune a gabansu itama tana hawaye sosai. Tausayi da dariya abun ya bashi duka lokaci daya,ya dake yana zura jallabiyyar jikinsa da sauri bayan ya tsane ruwan gargasarsa. "Baki gani kuka suke kika zauna kika sakasu a gaba kina kallonsu?". Kaman jira take yayi maganar ta miqe tana nufar qofar,kuka takeyi sosai,sai ya qarasa yasha gabanta yana duban idanunta. "Hamma raino kawai na iya dama?". "Ni me nace miki ne Sabreen?,me kikeso kuma ehmmm?" Yayi maganar da alama shima ranshi ya fara baci. Ta kalleshi sosai ta kuma fahimci kukan yaranshi ke dagula lissafinsa,kenan yafi jin kukansu a ransa sama da nata?,wannan ya sanya ta soma neman hanyan fita kawai. Hannu daya ya sanya ya jawota baya kafin ya saka hannuwansa duka biyun ya dauketa cak yana lullubeta a qirjinsa yana jin yadda sassanyan qamshinta ke bulale masa hanci,bai kuma direta ko ina ba sai tsakiyar gadon. Haurawa saman gadon yayi ya dauko farouq da nasa kukan yafi na kowa ya aza mata saman cinya,ya kuma tsare ta da idanun nasa. Zuwa yanzu qwayar idanun nan sun kuma na muhammadun sosai,me babban suna kuma shugaban kamfanonin jadda.168 "Feed him" Ya bata umarni nakai tsaye da husky voice dinsa. Duk wani annurin fuskarsa yana daukewa,kukan yaran yana jinsa kamar d'igar ruwan dalma saman tsokar zuciyarsa. Umarnin ya zarce har cikin kwanyarta,saita soma nuqu nuqun fidda maman. Gani yake bata masa lokaci takeyi shida yaran gaba daya,don haka ya buda hannayenta kawai ya balle duka button din rigar tata ya zameta daga kafadunta. Cikakkun dukiyar fulaninta da suke a tsaye,sun cika sosai irin na masu shayarwa ya bayyana,abinda yayi nasarar karya alwalar da yaketa faman tattalawa kenan. Hannunsa ya miqa cikin dakiya ya dagoma fauzan abincinsa,nan da nan ya kama,sannan ya saki ya koma wajen su fawwaz da kukan nasu ya sassauta. Bai nuna yaga hawayen da take zubarwa ba sam,yaci gaba da bata yaran suna sha,har sai kowannensu ya qoshi sannan ya janyeshi. Suna sha yana karbarsu daya bayan daya yana sauka dasu. Batasan inda yake kaisu ba,amma haka yake dawowa hannunsa babu su.v Almustapha ne qarshe,don kusan ya fisu haquri,sai daya tabbatar shima ya kama sannan ya tashi yayi raka'atanil fajr din. Sanda ya idar ya gama sha shima,ya miqa mata hannuwansa yana kallon fuskarta da tayi ja saboda kukan da tayi. Miqa masa shi tayi shima,sai ya karbeshi ya kuma ajiyeshi a gefe. Hannunsa yasa yana maida mata rigarta yadda take duk da qoqarin maidawa da takeyi da kanta. "Ka barmin abata zan mayar" Ta fadi cikin rawar murya. Wani kallo ya jefeta dashi. "Ina ruwanki?,wannan din ba jikinki bane.....jikin muhammad jadda ne.....naki jikin gashinan" Ya fadi yana nuna kansa da kansa da yatsa. Wani abu me sanyi taji ya sauka a zuciyarta,har sai data lumshe idonta kadan,ya kammala maida mata ita tsaf,ya saka hannu ya dauki almustapha fawad yana tafiya qofa. "Kiyi alwala kiyi sallah.....zanje sallah na dawo" Ya qarasa maganar yana qarasa fita. Tsaiwa yayi yayi locking qofar da new password ta yadda ba zata iya fita ba,sannan ya gangara ya miqawa salwa fawad yace a gyarashi shima kaman sauran 'yan uwansa sannan ya wuce masallacin. A sanyaye tayi alwalar tayi sallar,tayi addu'o'inta kaman yadda ta saba. Idanunta sun mata nauyi sosai,kuma da alama rashin bacci ne isashe na kwanakin,don haka sai kawai ta koma toilet ta hada ruwa me dumi sosai tayi wanka,ta kuma nade kanta da jikinta da towels dinsa wadanda qamshin jikinsa ya kamasu sosai. Idanu kawai take lumshewa,wanxuwar towel din me manne da qamshinsa sai ya xame mata kamar shine nannade a jikinta. Wani irin azababben shauqinsa takeji ta kowacce fuska,tana jin kaman takai kanta gareshi ta roqeshi. "Wanne irin abune wannan?" Ta tambayi kanta da kanta sanda tayi zaune saman stool a gaban madubi. Hirarta da fannah ta dawo mata fes a kanta. "Wata macen sai ta fara haihuwa take zama cikakkiyar mace me cikakkiyar buqatar namiji..sai a sannan komai nata yake qosawa yake kuma bunqasa" Dauke hawayenta tayi da yatsanta,tana raya cewa wataqila ita din tana cikin irin wadannan matanne. "Kamar ke kadai keda idanun kuka?,bakisan ni ya kamata na zauna nayita sheqa kuka ba?" Taji maganar sa daga gefanta wanda harga Allah batasan da shigowarsa ba. "Taso kizo nan" Ya bata umarni kansa tsaye yana nuna mata daura dashi. Da kallo yake binta sanda take takowa inda yake. Duk da yake shi ba ma'abocin kallon mata bane amma yayi imanin samun takun isa a wajen diya mace irin na sabreen dinsa zaiyi wahala,kaman yadda qirar jikinta tasha banban data dubban mata,don ko a yanzun da take tafiyar saika rantse ba wani yaro daya zauna a cikin ta tsahon wata tara,sai cika da komai nata ya sakeyi. Duk da yanayin halitta ma ya lura macace me gyara sosai(idan kina da kyau ki qara da wanka,karki yadda ki zauna a wargaje waike jego kike ko kin tara yara sun miki yawa,xaki banu zaki lalace fes wallahi). "Sabrrrr.......don ni bani da gata?,don ni bani da wanda zan gayawa damuwata......don ni namiji ne bani da idon kuka?" Yafada da wata raunanniyar muryar data tilasta mata daga idanu ta dubeshi. Wani irin tausayinsa daya tsarga mata ya sanya hawaye taruwa a idanunta. Miqewa yayi,da alama baiso maganar ma tayi tsayi can. "Alqawari nayi,tun a wancan daren bazan taba koda yatsarki ba muddin zamanmu sai kina cikin yanayin". " Ina ciki wallahi" Ta furta da wani irin sauri bayan ta yiwa kanta kyakkyawar masauki a qirjinsa tana cukuikuyeshi. Dariya ta kusa kubce masa duk da yadda sanyin hawayenta daya sauka budadden qirjinsa da wuyan rigan ya zama V shape ya taba zuciyasa sosai. "I can't live without you.....You're my everything,without you,I'm lost,i need you now and forever,you're irreplaceable hamma........ka yafemin hamma.....bazan sake ba hamma......na tuba" Ta qarasa fadi tana sakin masa wani kukan kisisina me tsayawa a zuciya. Hannunsa har rawa yake sanda ya riqeta,ya sake mata wani tsatstsauran riqo yana sanyata tsakiyar qirjinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Kasa magana yayi,kasa cewa komai yayi,kaman yadda shirunsa ya isheta amsa ta hanyar bugun da zuciyarsa takeyi. Ta yarda ta kuma amince tabbas taso ta zalunceshi,jikinta ya sake sanyi da kalar soyayyar da yakeyi mata. "Dukka wannan bugawar da Xuciyar nan takeyi tana yine saboda ke.....ke kadai sabreen,ban taba koda sha'awar daga kai na kalli wata macen ba bare har naji ta fusgi hankalina na ko ta dace da rayuwata ba bayanke". "Nayi maka alqawarin xame maka aljannar duniya koda shine xai kawo qarshen bugun zuciya dana numfashina" Lafaxinta na qarshe kenan daya iya tantancewa,ya dauketa cak ya ajiyeta inda yafi wayo sannan ya fara rabata da towel din jikinta. Wata irin sassanyan safiya ta bashi.....wata irin safiya me tsayawa a Xuciyar masoya..... "Can i have you for breakfast today?" Ya fada da wata narkakkiyar murya dake wani irin rawa. Yana dire tambayar ta tabbatar masa da abinda yake buri,abinda yake fata yake kuma tsananin buqata. Shi da ita kowannensu da zafinsa yazo,shi da itan gaba daya ba wanda bai gigita dan uwansa ba da wani irin zazzafan salo daya sake tabbatar masa itace DUNIYARSA shima shine DUNIYARTA. Gaba daya ta canza masa,ta kuma caza masa kwanya,yana jin tamkar yaune ranar farko a rayuwarsa daya fara kasancewa da ita. Ta gigita duk wani tunani nasa......ya sake fahimtar cewa lallai macen datasan kanta haihuwa ko shekaru basa saka kimarta zagwanyewa,a yanzunne ya sake gamsuwa da lallai sabreen dinshi ta zama cikakkiyar mace. Tana kwance luf saman qirjinsa sanda komai ya kammala,kalar alqawuran da yake zayyano mata ya sanyata sakin wani sassanyan kuka,nan ya sake lalacewa wajen lallashin kayarshi. Sanda taga lokaci bayan ta kalli agogo batasan sanda ta wantsalo daga gado ba ta nufi bandaki tana fadin "Su fawad" Miqewa yayi ya bita toilet din da towels dinsu. "Ina da nufina dana daukarwa su fawad nannies,kwanan nan kuma zan qara guda daya kowacce taji da guda daya,lokaci na lokaci na ne.....banaso nayi sharing nasa da kowa" Yaso ya bata dariya,saboda yadda yayi maganar da gaske. "Ayi musu afuwa naje na dubasu,don zuwa yanzun ya kamata ace an dubasun" Bai amsa mata ba ya turata cikin bathtub din kawai yana sake maqale mata. Tsaf ta shirya cikin atamfa riga da zani,shigar data jima bata yita ba. Shi kansa yau din saita masa kyau sosai,ta maqala wasu sabbin design na earrings na gold marasa nauyi a kunnenta da siriryar sarqarsu saman dogon wuyanta,abinda ya sake mata kyau kenan. Ido ya saka da baki yana kallon kyakkyawan dokin wuyanta,tunda aka fidda design din shi sai yau yaga kyansa saman wuyanta,ya tako a hankali ya sumbaci wuyanta nata,abinda ya dauke mata wuta na sakanni. "An bani izinin sauka na dubasu?". "An baki duniyata" Ya fada cikin kulawa da shauqin qauna. Basa dakinsu koda ta duba,don haka saita yanke duba parlor dinsu. "Salwa.....Allah yasa ba rigima suke miki b......" Bata samu daman qarasa fadin abinda yake bakinta ba komai ya maqale mata yadda ta zuba mata idanu itama haka ta zuba mata,cikin wani irin kallon me cike da matsanancin mamaki da gigita. Maamah ce zaune saman wheelchair dinta,an dora mata farouq fawwaz da almustapha fawad saman cinyar tata. Yatsanta cikin nasu yatsan tana tabawa a hankali,duk da bacci sukeyi amma idanunta yana kansu gaba daya. "Ba wata rigima hajiya......tun dazun suna hannun kakarsu,har sukayi bacci.......fauzan ne ma yaqi zama gashican an goyashi" Salwa ta bawa sabreen amsa. Maamah ce ta fara cire idanunta akan sabreen din sannan itama sabreen din ta dauke kallonta daga kanta cikin matuqar mamaki jikinta yayi wani mahaukacin sanyi. "Tun yaushe tazo?" Ta tambayi salwa da harshen larabci data tabbatar maamah bataji murya qasa qasa "Mintuna kusan arbain kenan,a rubutunta tambayeni ma haka kuke barin yaran a qasa gurinmu kuna sama?" Salwa ta fadi tana murmushi. Ta fada ne saboda yadda taga maamah din tana qarewa yaran kallo,kallon dake nuna zallar qauna da shauqi da kuma kulawa. Tunda tazo idanunta yana kansu,bata kuma saukesu ba ko sau daya. Kai sabreen ta jinjina,abun yana sake fadada mamakinta. "A samo mata abinci da abinsha" Ta fadi tana maida hankalinta kan maamah tana takawa cike da qwarin gwiwa. Ganin maamah a gidan nata ba abu bane me sauqi,ba wani abu bane da zatayi zaton zai kasance haka a nan kurkusa ba. Gabanta ta qarasa ta kuma tsugunna tana fadin "Sannu da zuwa maamah......barka rana,ya jikin?,Allah ya qara lafiya". Wani kallo ta dago ta dan watsa mata. Da tana da iko zata tambayeta ne uban me sukeyi a sama kusan sama da awa daya suka bar kula da yara hannun masu aiki?,haka sukeyi kenan cikin gidan?,shi ya ajiye fita office ita ta saki ragamar gida kamar su kadaine suka rage a duniyar?,kaman ba wani abu me rai da yake rayuwa a duniyar saisu?. Saidai ba wannan damar,sai dai kallon tuhumar data gabatar mata tana jin ya kawo mata dan sassauci a zuciyarta. Sarai taga kalar kallon,to amma ita kanta tasan yasha banban da kallon qiyayya da takeyi mata,wannan din akwai sassauci qwarai a cikinsa,duk da cewa akwai alamu na jin haushi a cikinsa da batasan haushin meye ba?,sai daga baya zuciyarta ke raya mata na barin yaranne a hannunsu salwa?. Saida salwa ta kawo komai sabreen ta jera mata a gabanta,sannan ta umarceta ta karbi yaran ta bata abincin taci,amma qememe taqi bayar da yaran. Sanda fu'ad ya sauko ana wannan drama din,don sabreen ta haqura ta koma gefe tana kallon ikon Allah,yadda ta tattara dukka hankalinta akan yaran,kamar bata da wani sauran abu me muhimmanci a duniyarta sama dasu,duk kuwa da cewa ita din daga wannan kallon guda biyu bata sake samun wani kallon ba. Shima nasa kallon aka aje masa,sannan ta kauda kanta bakinta yana motsawa kaman meson yin magana amma kuma ba dama. Mutuwar tsayen da yayi yafi na sabreen,don har sai da maamah din ta sake daga idanu ta kalleshi tana masa nuni da ya zauna ya tsaya mata a kai. Kaman yadda sabreen tayi mata shima still hakan,saidai shi dinma ba wani muhimmanci ta bashi ba. Ganinta riqe da yaransu kuma gudan jininsu cikin hannuwanta da wata qauna data gaza boyuwa daga cikin qwayar idanunta yafi komai yi musu dadi shida sabreen din. Suna zaune zaman kurame kawai,amma lokaci lokaci suna satar kallon juna shida sabreen din,har zuwa sanda tayi alama da hannu aka bata abun rubutu. "Ka kiramin driver ya maidani gida,kada ku sake barin yara har tsahon sama da awa a hannun masu aiki ba tare da kuna zagayosu kuna dubasu ba" Iya abinda ta rubuta kenan da rarrababben rubutunta. Ya dauka idanunsa ne suke masa gizo ko suke nuna masa ba daidai ba,sai kawai ya miqawa sabreen din paper ya qarasa ya karbi yaran ya ajiyesu sannan ya tura wheelchair din da take kai da kansa. Sanda yake turata da kansa sai taji wani abu yana sauka saman zuciyarta,tana iya qididdige takunsa da kuma yadda yake tura kujeran cike da karsashi,sai takejin kaman ba'a taba tafiya da ita saman wheelchair din irin haka ba.169 Koda suka isa key ya karba hannun driver din,yace su biyoshi a daya motar. Shi yayi driving nata har gida,ya kuma danganata da bedroom dinta. Tsugunnawa yayi a gabanta a hankali,yana jin wani abu me kama da qaqqarfan farinciki yana dawainiya dashi. "Zan koma......ba wani abun?" Kai ta girgiza masa alamun ba komai,sai ya miqe a nutse yana furta. "Sai da safe,Allah ya huta gajiya" Ya fada yana dan rage Ac din dakin. Idanunta ta lumshe,wasu hawaye masu dumi suna silmiyo mata wanda ba nace ga dalili ba,ta miqa hannunta da qyar dake yawan yo mata nauyi tana goge hawayen fuskarta. Riqe da paper din kuma a inda ya barta ya sameta a zaune tsakanin yaqini da kokwanto. Cak ya dagata yana juyi da ita sannan ya direta yana duban tsakiyar idanunta. "Na gode sosai duniya.....na gode da tayani siyawa yaran nan soyayyar maamah......koda ni ko ke mun rasa soyayyarta.......soyayyar da zata bawa su fauzan ta ishemu". Da mamaki take kallonsa,sai ya lakace mata hanci. " Ko an gaya miki bana sane da boyayyar addu'ar da kikewa iyalinki.....ni number one,addu'ar kariya samun nasara da cikakkiyar lafiya,yaranmu shiriya da zama nagartattu.....sai samun qauna daga wajen kakarsu" Kunya ta kamata,ashe dukka kukenta da fatanta cikin sallolinta na dare fakare yakeyi mata?. ★Cikin kwanakin kwanciyar hankali da nutsuwa ta samu ga kowa,ci gaba ta fuskokin rayuwa kala daban daban. Wata irin soyayya ake murmushewa cikin gidan me jadda me license,irin soyayyar da yaran da suka fito ma daga jikinsu saidai a sanmusu. Tsakanin DUNIYOYIN guda biyu wani irin dangantaka ce me qarfin gaske.....wadda ta gwada musu lallai WA YASAN GOBE? banda Allah?. Wata irin DANGANTAKAR ZUCI me tsakanin qarfi da power,wadda take sake basu yaqinin ABADAN ba wanda zai iya rayuwa ba dan uwansa. Sau da dama idan suka zauna labarin rayuwrsu ta baya suna jinjina lamarin ubangiji kan yadda ya tsara KUNDIN QADDARAr junansu,wani ALQAWARIN ALLAH ne wanda baya tashi. Komai na sabreen din tana qoqarin saitashi ya zama daidai da ALQIBLAr fu'ad din,komai nata tana qoqarin ganin bai saba da muradi da abinda me jadda yakeso ba. SIRADIN RAYUWArta kaf akan gidanta ne da yaranta,ta zage sosai wajen koyan abubuwa da dama da zasu maidata cikakkiyar matar gida,irin matar gidan da soyyayarta da kulawarta ke tsayawa a zuciyar mijinta. Duk wata DABI'AR ZUCIYA da tasan zata kawo rauni a mu'amalarta da fu'ad tayi qoqarin nesanta kanta da ita,ta sake qoqarin zame masa GURBIN IDO ta fannin mahaifiya dama mu'amalarsa tako da yaushe. Kusan duk bayan kwana uku ko zataje ko bazataje ba ta koyawa faud daukan yaran bayan sallar ishai suje su gaida maamah. Hakan yana sanya maamah cikin farincikin da har baya kasa boyuwa saman fuskarta,tana jin yaran a jikinta qwarai,can qasan zuciyarta kuma idan ta kalli mahafinsu takanji kaman ta zama butulu KUFAN WUTA a wani zamani can baya daya wuce. Tun zuciyarta bata gaya mata harta fara gayawa kanta da kanta cewa A RUBUCE TAKE qaddarar kowanne bawa,ba wanda kuma ya isa ya sauya qaddarar wani face marubucin qaddarar. Sabreen zata iya cewa ita din tana daya daga cikin matan da suka qaryata kalmar nan ta NAMIJI TABARMAR K'ASHI. Mu'amalar fu'ad da komai nasa na musamman ne kuma ya banbanta dana sauran maza. Duk da cewa GUDUN K'ADDARA GUZURIN TARAR DA ITA amma tayi imanin cewa addu'a tana iya sauya qaddarar bawa......tana fatan yadda ko yaushe ta sanya goshinta a qasa take roqar Allah madawwamiyar lafiya da zaman lafiya a gidanta.......ta kasance ita daya a rayuwar fu'ad din a matsayin matar aure,tana da yaqinin Allah bazai juyar da addu'arta ba duk da tabbacin data samu daga bakinsa. ★Cikin dim light din dake kai kawo a dakin ta qaraso gabansa,sanye da wata sassalkar rigar bacci data qawata surarta dama fatar jikinsa. Duk da sau daya ya daga kai ya kalleta amma sai data fusgi hankalinsa,ya kalli agogo ya maida dubansa kanta sanda take tsugunne gabansa tana zuba masa hadadden kunun ayar data koya,kunun da tunda ta koyeshi ya zame masa JARRABI kullum sai yasha shi. Sai data sake masa murmushi sannan ta miqa masa cup din,ya miqa hannu da nufin karba yana cewa. "Inda malami kika saka yayimiki aiki akan soyayyarki a zuciyata,tabbas dana qara masa kudi ya qara tsananta aikinsa,don nasan babu me mace irin tawa a duniyar nan". " Hamma....sonkai?" Ta fada da muryarta me sanyi,wadda shi daya take maidawa ita haka a kebantaccen guri irin wannan. Zai bata amsa zafin da bayan hannunta yayi ya dauki hankalinsa. "Subhanallah.....zazzabin nan wai bai tafi ba?" Ya tambaya cikin tsananin damuwa yana ajiye cup din hannunsa. Kai ta gyada masa a shagwabe "Bai tafi ba hamma....." "Bari na yiwa doctor mubeena waya ta shigo ta dubaki......zazzabin nan ya isa haka nan". Tasan koda tace masa ya bari bazai bari ba,yana damuwa da ciwonta fiye da yadda ita take damuwa da kan nata. Sannu kawai yake jera mata,tayi tayi ka yasha kunun yace ta maida fridge. Baa rufa awa ba doctor mubeena ta iso da kayan aikinta,kai tsaye suka wuce dan qaramin dakin daya zuba qananun kayan aiki a ciki saboda lafiyar iyalin gidan. Shi da ita duka idanu suka zuba mata sanda take duba gwajin data mata saboda ganin murmushi yana fita kan fuskarta. "Mr and mrs jadda......congratulations,madam nada juna biyu". Banda yasan doctor mubeena na tsananin girmamashi da sai yace tana wasa da hankalinsa ne,saidai duk da haka sai daya ce. "Say it again please". "I said madam nada juna biyu......she's pregnant". Suratul ikhlas kawai ya hau karantawa qafa uku,daga nan ya miqe ya sunkuci matarsa,daukan data saka Dr mubeena soma hada ya nata yan nata ta basu waje,saidai tana iya hangen tsoro sosai fuskar sabreen. Abinda kawai yake yawo a kanta shine watansu fauzan hudu,cikin week dinma duka duka aka fara koya musu zama......likita yace aqalla tayi shekara daya so samu har biyu bata dauki wani cikin ba saboda ta warke yadda ya kamata,yanzu kuma dr mubeena na gaya mata juna biyu ne da ita?. Cikin qasa da mintuna biyar dukka wannan tsoron yabi ruwa,cikin daqiqa kadan komai ya kwaranye daga zuciyarta. Yadda idanun fu'ad ke fidda qwallar farinciki......yadda bakinsa ya gaza hutawa dayi mata addu'ar "Ke 'yar aljanna ce in sha Allahu sabrrrr.......ke alkhairi ce sabrrrr......don Alla ki gayamin me kike da burin mallaka a rayuwarki bayan gidan marayu da gajiyayyu da tallafawa marayu?". Kai ta girgiza a hankali,lallai ta jahilci irin tsananin son da fu'ad yakewa haihuwa. "Babu.....babu muffin,iya wannan qaunar da soyayyar da wadatar......iya wannan shauqin na samun iri daga jikina ya isheni farinciki har qarshen rayuwata". Ta furta maganar da dukka zuciyarta tana tuna wata mata da mijinta yayi mata duka ya watsota waje ya kuma saketa dukka a iqirarinsa na ta fiya haihuwa......da an tabata sai ciki.....dukka ubangiji ita bai jarabceta da wannan ba?. Wani irin dare ne da bacci ya gagari idanun fu'ad,yayi sallah yayi addu'a har baisan iyaka ba. Itama da take kwance lamo kawai tayi,zuciyarta na sake cika da mamakin yadda yake tsananin son haihuwa,saita samu kanta da maimaita. "Alhamdulillah......alhamdulillah" Har sau babu adadi. ★Cikin lokacin wani kulawa yake bata data ninka ta baya,yana gida ko yana office dukka yana kula da motsinta. Ya sake qaro mata aminttatun masu aiki da suka sanya komai ya sake zame mata da sauqi,goyon ciki me 'yanci,kuma Allah ya bata da sassauci akan nasu fauzan,duk da cewa har a lokacin tana shayar da yaran,yace bai yarda ta yaye masa yara ba,idanma biyanta ne shi zaiyi a barsu susha nono su qoshi ko don saboda ginuwar kwanyarsu yadda akeso. To shi ciki dai d'an duma ne inji hausawa,a hankali jikinta da dabi'unta suka fara nunata,duk da yadda take gocewa shiga cikin mutane don kada su fahimci cikin. Kunyar cikin take sosai,sau tari idan shagwabarta ta motsa sai tayita masa rigimar banza akai. "Hamma don Allah kada ka gayawa kowa.....don Allah hamma kada ka fada,yayi wuri fa hamma.......duka duka watansu fawad nawa ne?,Allah kunya nakeji" "Sabrrrr" Ya kirata kai tsaye a lokacin tana saman cinyarsa yana raba mata doguwar sumarta biyu hagu da dama don ta dameta. "Wallahi wallahi ko cikin shege nayi miki bazan boye samuwarsa ba.....kuma zanso abina fiye da tunaninki,ballantana 'ya'yan halaliya 'ya'yan so". Yadda yace 'ya'yan so din har tsakiyar zuciyarta,tun daga ranar saita daina cewa komai akai,ta kuma tayashi da duk yadda yakeso. Tasha tsokana sosai wajen fannah wadda itama nata cikin ya fara girma,amna da huda kuwa dukkaninsu yaya take a Wajensu,ba tsokana sai gulmarta a boye,uwa uba suma duk ta kansu sukeyi don cikinsu ya tsufa sosai. Wata tara da bikinsu amna amna din ta dire nata yaron namiji. Maamah bata sanu ba sai bayan kwanaki bakwai,tana zaune saman wheelchair dinta sanda musaddiq ya ajiye mata goro da alewar radin suna. Hamza ya saka shima still saboda nuna yabawa bisa hidimar abban a kansu,sun masa laqabi da HILAL. Ba wani feeling data samu zuciyarta a ciki akan haihuwar,so ko qi itama bata san wanne layi take kai ba,saidai bata wani dorawa kanta tsananin tunani akan komai ba ta ajiye maganan,duk da lokaci lokaci idan aka kawo mata su fauzan yaron yana fado mata a rai. Tsakaninsu da huda wata biyu kacal itama ta dire nata sojan. Saddiq ya nuna kara sosai,ya sanya masa sunan mahaifinsu sabreen wato ahmad,suna masa alkunya da NASEEM. Ta kowacce fuska anni jinta take cikin alkhairin ubangiji,saidai a yanzun kwadayinta a samu 'yanmata kuma,don tana fatan samun garabasar nan na wanda ya raini diya mace biyu ya aurar dasu na alqawarin aljanna kai tsaye. Irin girman da nauyin cikin ya sanya fu'ad wucewa da ita a wata tafiya da yayi zuwa spain ya tafi da ita. Bawai don yana da nufin tayi anti natal nata a can ba,saidon kawai a duba mishi ita duk da bata da matsalan komai,saina wani irin cin abinci da takeyi,abinda shi kuma yakeyi masa dadi sosai,har yakan zauna yana kallonta abinsa. Scan din farko ya nuna twins ne a cikin nata. Wani iri ya dinga ji,tsoron Allahnsa yana sake kamashi. Dukka cikin addu'arsa ba wadda bai gani ta tabbata ba.....shin cikin ni'imomin Allah wanne ne a ciki zaiyi inkari?. _Allah ka wadatamu da dukka ni'imominka na zahiri dana badini,ya Allah karka jarabcemu da gushewar ni'imominka a kanmu_ _on our way to the last episode's in sha Allah_👏🏽👏🏽😄😄😄170 Tattalinta ya dinga yi,nan nan da ita yakeyi,baya yarda komai ya taba walwalarta ko kuma jin dadinta. Duk wani abu da yasan zata iya buqata ya ajiyeshi......komai da yasan zata iya nema kafin ma takai ga tambaya ya tabbatar da samuwarsa. Bata aikin komai,ba aikin fari bare na baqi,komai nata dana yara tana da amintattun masu aikin da take jinsu kaman 'yan uwanta na jini,musamman da suka kasance kusan dukkaninsu marayu ne wadanda basu watsar da maraicinsu ba. Duk wannan gatan data samu.....duk wannan kulawar bata sanya ta saki hidimarsa ki qwaya daya ba. Yayi yayi ta barshi amma ita kanta tasan ba abu bane me yiwuwa tabar kula da mijinta,sai ya qyaleta a bisa dole,amma duk wani motsi nata da zatayi shike tayata,shike kama mata. Misali wani lokacin yakan yi mata wayo ya rigata tashi da safe. A kitchen din sama zai hada breakfast abinsa ya aje mata nata,ya hada ruwan wankanshi da kanshi yayi,ya watsa undies dinsu cikin washing machine ya wanke musu,ya kwashe komai dake tsananin parlor zuwa Bedroom din da suka bata. Idan ta farka saidai ta taras da sauran aikin,wanda baya wuce shayar dasu fauzan da kuma qarasa kintsa saman nasa,sai tayi wanka shikenan ta zauna cikin masu aikinta. Idan ta gaji tana buqatar fita shike katse komai nasa ya dawo ya fita da ita,idan ma qasar ko garin takeso su danyi balaguro daukanta yake ita da duk wanda takeso su wuce suyi iya kwanakin da takeso. Irin gatan da yake gwada mata saita dinga jin kaman ya mata yawa,kaman bata cancanci tattali irin haka,ranar data fara magana a kai suna tsaye ne saman balcony na wani qawataccen madaidaicin gida daya siya a dubai a satin. Gidan yana area me tsada ne wanda yake da clear view na garin dubai da guraren kallo masu kyau. Ta baya ya rungumeta yana dora hannunsa guda daya saman qaton cikinta. Ta miqa hannunta ta bayan itama ta shafo sajensa tana sakin murmushi. "Tunanina kike?" Ya furta a tausashe,saita gyada masa kanta. "Ya akayi kasan sirrin zuciyata". "Ruhi daya......zuciya daya.....qwaqwalwa daya.....gangar jikince kawai guda biyu,to menene zai boye a wajena?" Ya qarasa maganar yana tura mata wani file ta gefan cikinta. Murmushi ta saki tana jin maganarsa ba wani kuskure ko gyara a ciki,ta karbi file din ta bude. Takardar shaidar mallaka ce ta wannan gidan da suke ciki,wanda ya rubuta da sanya hannunsa da komai kan ya mallaka mata gidan. Ganin komai take kamar a mafarki,batasan adadin gidaje da estate nawa ya mallaka mata ba.......amma wannan ya zama na daban. Mallakar gida sukutum da guda a dubai?,abun sai kanta ya kasa dauka,don a satin a gabanta ya bada izinin tura Dirham's masu nauyin gaske ga kamfanin da sukayi cinikayyar gidan. A nutse ta juyo suna fuskantar juna,hannunta yayi sanyi sosai ta riqe nasa hannun. "Hamma.......wannan kyautar tayi girma da yawa,wannan gatan yayi yawa". Sassanyan murmushin nan nasa ya saki,ya kama qugunta ya riqe yana mata wani tattausan kallo kaman zai hadiyeta. "Me akayi ma my world?,wannan gidan wai?,kinsan gidaje na nawa a qasar nan?,wannan din kuma dama tun asali saboda ke aka siyeshi.......sabreen" Ya kirata da wani sound yana kama fuskantarta cikin hannunsa. "Na'am muffin" Ta amsa masa idanunta suna cika da hawayen farinciki. "Komai na fu'ad naki ne.....komai na muhammad jadda kin cancanceshi.........gata kuma ban nuna miki komai ba sabrrrr.......bana buqatar komai a wajenki illa ki cikamin gida da yara......ki cikamin gida da zuri'ar da zasu zamemin ababen alfahari.....haihuwa nakeso kiyita yi......ni kuma nayi alqawarin bazan barki kisha wahalar komai ba banda ta basu tarbiyya". Rungumeshi ta matso zatayi amma cikin jikinta ya tokaresu,sai taja baya kadan,yana dariya ya nuna cikin da yatsarsa,sannan ya juyata yana baga kyakkyawar runguma ta baya. ★Wata takwas da sati biyu wanda yayi daidai da shekararsu fauxan daya da wata daya akayi mata wani CS din a garin madeena. Kyawawan 'yan biyu ya haifa dukkaninsu maza. Manya manya har sunfi su fawad girma da wani irin kyau me daukan hankali,don kuwa kamanninsu bangare biyu suka debo,fu'ad din da sabreen din,saika kasa tantance da wa suke kama?. Kasuwar 'yan uku ta tsaya,kowa so yake a bashi yaran,duk kuwa da cewa dasu aka tafi karban haihuwar 'yan uwansu. Amna naso,huda naso,fannah da farouq dinta sunaso,ga maamah a gefe da sai a ranar tayi kukan rashin magana da bata iyayi. Kuka tayi sosai me yawa,don kuwa taso tana da baki,da tabbas ko fu'ad baya so sai ta karbi wadannan yaran. Wani irin kwarjini yaran ke dashi kaman ubansu ya roqa musu,ga wani irin energy da suke dashi da wani girma kai zaka ce shekara biyu suke ba daya ba. Bugu da qari kowannensu tafiya yake sosai,don tun suna wata bakwai suka fara miqewa,yanayin kulawar da suke samu ya sanya ba wani wanda yayi wani abu wai kashin haqori,banda zazzabi da sukayi na wasu kwanaki,sai bullar haqora kawai a bakinsu. Energy dinsu ya sanya suke da fitina,haka suke fafatawa da anni. Gidan su kuwa tuni fu'ad ya sanya an dage komai sama wanda zasu iya jawowa ya illatasu,wanda bazai dagu ba yasa an daukeshi anyi replacing da wani abun na daban. An kwashewa sabreen flower verse dinta da yawa da take ado dasu,a ranar ta dinga fushi tana tura baki gaba. "Tsakani da Allah......haka kawai a hana mutum ado......". Duba daya yayi mata ya dauke kai yana ci gaba da yankewa fawwaz farce sanda yake bacci saman cinyarsa. " Yara dai da gidansu ba wanda zai hanasu sakewa,ni ba ta flower vase dinki nake ba.....ta lafiyan yarana nake,inda bazai cutar dasu ba zan bar musu suyita fasawa......qarqari ace dai mu biya ko?,mu kuwa baza'a mana gorin biya ba". Mamaki ya cikata,tayi sakato tana kallonsa yadda ya basar yana wani shan mur,ta danne dariyarta tana sake daure fuska "Amma dai ba haka akewa yaro tarbiyya ba,a barshi idan ya fasa a zane masa hannu don yasan ba abun tabawa bane". Nail cutter din ya subuce a hannunsa,ya waro ido yana dubanta. "Du me?,ke waye ya dakeki?,ashe kina so anni da abba su shigo sulhu kenan......wa yace miki akwai duka cikin tarbiyya?,wait.......tsaya ma......bakisan yaro muddin ba'a barshi yayi wasa yadda ya dace ba hakan yana zame masa naqasu a gaba?,ina manya da zakiga sun girma suna wasanni kaman yara?,har wata tsokanar idan sun maka ya baka haushi?,alhali bawai tarbiyya ne basu dashi ba?,to yawansu rashin barinsu suyi wasan da zasu qoshi ne". Dole dariya ta subuce sabreen ganin yadda ya gyara zama yake mata jawabi bilhaqqi da gaske. "Malam hamma....ban taba jin karatun nan ba sai a kanka". " Zaki jine da kyau.....nidai na fada abar yarana suyi yadda sukeso". Ya fada yana ci gaba da yanke masa farcen "Hamma" Ta kirashi a tausashe,kai ya daga ya kalleta ganin yadda ta kirashin. "Ina gudun kada soyayyar yaran nan ya rufe maka ido ka kasa tayani basu tarbiyya me kyau". Wani murmushi ya sakar mata yana ci gaba da aikinsa. "Zaki gani.....Allah ya bamu aron rai" Abinda ya fada kawai kenan. Shi kadai daga shi sai Allahnsa sukasan irin burin da yaci akan yaran,shi daya yasan kalar rayuwar da yayi musu tanadi.....ba iyasu fauzan ba,dukka yaran da zai samu daga nan har ya qare rayuwarsa. Ranar da zasu bar asibiti zuwa gida tana zaune suna hira da huda dake rungume da babynta wanda ya gama rigima bacci ya soma daukansa taji sallamar kawu rufa'i. Farar jallabiyya ce a jikinsa harda hirami,ga wani farin carbi a hannunsa. "Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu yake d'iyar aljanna mabudin arziqin ahalinta gaba daya". Bushewa da dariya huda tayi tana kallon kawun. Gaba daya ya canza,quruciyarsa kuma sai dawowa takeyi saboda wadatar daya soma tsumbula ciki. "Kawu waye ya kawowa madeena?,kamar bakafi wata shida da komawa bafa" Huda da dama can tasu bata jiquwa ta furta. Harara ya dalla mata yana neman wajen zama gami da kalmashe carbinsa. "Ni yanzu har ayimin maganar hawa gajimare da sauka......mutumin da yake da suruki irin me jadda gidan gold da diamond?,to bari kiji yarinya,a yanzu haka aminaina guda biyu dukkaninsu hajjin bana dasu Zamuyi gaba daya,albarkacin me jadda.....albarkacin d'iyar da aka haifa tsiya tana bacci kariris". Neman wajen zama huda tayi saboda kada dariya ta kayar da ita,kawun ya gama bata amsa daidai da ita,saiyayi banza da hudan yana maida hankalinsa kan sabreen. "Sannu d'iyata.....sannu 'yar nan.....ashe ni ahmadu da fateema suka haifawa ke ban sani ba?" Ya qarasa fada yana matse hawayensa da wasu sabbin qwalla da suka fara taruwa lokaci guda. "Dama na dade inaji a jikina zanyi kudi.....na dade inaji a jikina zanyi arziqi ashe ta sanadinki ne,ubangijin al'arshi yayi miki albarka,dukka gidanku yanzu ya koma qarqashin kulawarki,masoyanki da maqiyanki,harda 'yan uwanki na dakin aure,Allah ya qara miki riqonda zumunci da kuma zuciyar yafiya da afuwa" "Ameen ameen kawu" Sabreen ta fada tana murmushi. Gaba daya kawun nata ya canza kaman bashi ba,wata kamala duka ta saukar masa,ga alamun jin dadi da hutu duka tattare dashi. "Amma 'yar nan ya akayi haka?" Ya fada yana gyara muryarsa. Kai ta daga tana dubansa "Me akayi kawu?". " Kinyi qoqari dai.....amma ci gaba ya kamata a samu ai,'yan hudu ya kamata kiyi wannan karon,amma sai aka koma baya kikayi biyu,maimakon ki maimaita ukun?,kinsan innarmu sai da tayi 'yan uku da 'yan biyu kusan kashi biyar,duka rasuwa sukeyi,ni kadai da dan uwana ahmadu ne muka zauna,don ko babanki ai tagwaye ne,ni kuwa mu uku ta haifa,amma ni duka na fisu qwarin qashi ni kadai na zauna". "Kaine dai Allah baiyi niyyar kashewa ba kawu ba wayonka bane" Huda data goya baby naseem da baby carrier ta fada duka cikin salon tsokana. Daquwa ya watsa mata yana dubanta. "Kinci ubanki.....banda kinci darajar mijinki da ya bani kyautar gida harda mota satin nan daya wuce yau da sai na karbi goyon na aza a bayana naci qaniyarki sannan na baki danki kici gaba da tafiya" Daga huda din har sabreen sai a sannan sukasan saddiq ma yayi kyautar,ba zatar data kashe rigimar kawu da huda ya koma magana da sabreen. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 171 *_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_* https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1 171 "Allah ya sambada miki albarka,don Allah.........don Allah ki daure wata shekarar warhaka ki sake tunkudo wasu hudun" Ido ta zaro da mamaki "Da gaske fa kawu kake?". " To me zaki tsaya jira?,banda rainon cikin bakisan wahalar komai ba?,shi kuma iri kawai yakeso,ai faduwa tazo daidai da zama" Ya fada yana leqa fuskokin yaran. "Tubarkallah wallahi.....haihuwar masu kudi daban data talakawa,su kansu yaran daban naku suke da namu". " Wallahi idan banbar dakin nan ba sai kawu ya sanya cikina ciwo.....adda bari naje nima nayi sallah a masallaci" Huda ta fadi tana fita ta barsu. Wannan karon halastacciyar walima jadda ya fara hadawa a birnin madeena. Walimar maza daban mata daban. Jirginsa daya siya bayan wanda yayi kyautarsa na JADDA WINGS 002 kawai ya bayar akayi jigilar 'yan uwa da suke cikin list na zuwa umra a wannan watan aka gabatar da walimar tare dasu,ciki harda maamah,wadda akan idanunta aka gudanar da komai. Duk wani motsi na yaran nan guda biyar akan idanunta yake,ta saka damuwa sosai a kansu tana ganin kamar zasu bace ko zaa daukesu,saidai tana komawa daidai duk sanda ta tuna amincin da garin yake dashi. Wannan karon Sabreen itama ta samu mahaifinta,wato AHAMD(Amaan),dan uwanshi kuma yaci sunan muhammad da kanshi wato takwaran babansa (AMEEN). Tuburewan tsokana Sabreen tayi. "Hamma wannan son kai ne.....ni me yasa ba'a fara jira an saka me sunana ba?" Ta fada tana turo baki gaba. Dariya ya saki yana murza yatsunta sanda take zaune tana shayar da muhammad ameen din. "Ki haifomin baby girl ki gani DUNIYATA.....ke kika mana addu'an boys,gashinan ta shafi kowa cikin familyn jadda,duka maza suke haifa mana,muna da kwadayin mace dukkaninmu amma bansan kusancinki da Allah ba da addu'arki ta riga tawa tafiya ba.....at first nafison na samu daughters so samu.....don na basu tarbiyya na aurar dasu,na kuma rabauta da rabon aljannar da manzon Allah ya yiwa duk wanda yayi irin wannan aikin alqawarin samu". Dauke kai tayi tana sake tsuke bakinta cikin shagwabar nan da bata jin ta girma da yinta,kamar yadda shima baya ganin ta girma dayi masa ita. "Amma dai it's not fair hamma......sai a jirani sai sanda aka samu baby girl din aka saka ameenatu". "Ameenatu ta zama wajib akan dukka diya mace ta farko data fito daga tsatson jadda......take it easy maa.....ki qara himma next year by now ki ajiyemin girls" Idanu ta zaro ta bishi dasu,sai ya jinjina mata kai cikin bada tabbaci. "In sha Allah" Ya fada da yaqinin daya sanyata bata sake cewa komai ba. Sabreen bata yarda ta koma ba saida jini ya dauke mata,ta sauke umra. Addu'a tayi me tarin yawa akan rayuwarta data zuri'arta,addu'a ce me yawan gaske akan zaman lafiyarta dana familynta gaba daya,qannenta 'yan uwanta dama duk wanda yake da jibi dasu. Ta dade gaban dakin Allah tana neman me kyau a duniya me kyau a lahira(Rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati hasanatan wa qina azabannar/addu'a ce wannan me matuqar muhimmanci,ku dage kada kuyi wasa da ita). Ta roqi Allah dawwamammiyar soyayya a zuciyar mijinta,da kariyar Allah daga jinsa ganinsa da zuciyarsa dama al'aurarsa akan kowacce diya mace idan ba ita ba. Cikin wani irin aminci sakewa da walwala take kula da yaranta dukka guda biyar din. Tana da wadatattun masuyi mata hidima,yayin da ita kuma ta tattara damuwarta dama kulawarta dukka akan mijinta. Sai data warware sosai sannan yazo mata da komai da komai na kammaluwar ginin gidan marayu maka maka har guda uku a arewacin Nigeria,da kuma gina sabuwar foundation ta kula da marayu da zawarawa da yara marasa galihu. Kukan farinciki sosai ta dinga yi,saboda cikar ragowar burinta kenan a rayuwa. Wani irin katafaren gida ne da aka tsarasu bisa tsarin ginin unguwa guda wato estate. Da makarantunsu tun daga primary har zuwa secondry,jami'a kuwa a qasar waje yayi planning ya dinga turasu qasashen musulunci,don yana sanya ran a can zasuyi karatu me kyau,ba tsangwamar mutane ba takurawarsu. Komai an wadata gidajen dasu,abinci sutura wutar lantarki da kayan more rayuwa cikin kowanne gida da dakuna. Cikakken tsaro da tsari na addinin musulunci wanda aka ginashi bisa jagorancin malam da a yanzun shine babban me bawa jadda shawara akan duk wani abu daya shafi zakka da harkokin addini cikin rayuwarsa. "Wannan gidan da komai dake cikinsa kuma mallakin su ayshatu ne......na kusa dashi kuma na JIB ne,sai kuma guda dayan na busari" Ido ta waro tana mamaki,ya akayi yasan su jib?. "Maida idon ranki ya dade don ban gaji da kallonsu ba daga nan har qarshen rayuwata......karki ce komai,tun daga randa na sameki cikakkiyar mace na bibiyesu na kuma jawosu cikin rayuwata,yanzu haka busari shine shugaban drivers na kamfanina,Jib kuma yana jagorantar sashen tsaro na daya kamfanina dake lagos" A ranar idan farinciki yana kisa tabbas ta tabbatar sai buzunta. A yadda abubuwan sukazo tana buqatar ma'aikata ita kanta,tana buqatar su zauna su qarasa tsara komai kafin ranar da zaa qaddamar da qungiyar da kuma qaddamar da gidajen marayun dake kano kaduna da abuja. Sosai ta tsananta bincike cikin danginta na uba harna uwarma,ta kuma zabi amintattu da zasu dinga gudanar da komai,nata aikin kawai tana daga cikin gida xatayishi cikin system sai waya idan ta kama,sai kuma ziyara da duba gidajen lokaci bayan lokaci da zata dinga zuwa,da kuma wani taron idan ya kama,kamar ganawa da ma'aikatanta da sauransu. Abinda ya bata mamaki shine,albashin da fuad ya sanya mata na million din kudade. Abun ya qarasa kasheta da mamaki,itace shugaba,yayi dukka aikin ya mallaka mata,ya bata dama ta sakawa kowa albashinsa kuma zata dinga biyansa......sannan ita kanta kuma ya yanka mata albashin miliyoyin kudaden da batasan ma me zatayi dasu ba. Kuka kam wannan karon barinta yayi tayi abinta,ta shimfida fuskarta saman kyakkyawan qirjinsa tayi kukanta yadda takeso ta kuma zarce da godiya ta baki da kuma godiya ta aikace. A ranar ta saje yarda da kanta,ta haukatashi da wani irin salo......ta sake godewa Bgawo's kitchen and aphrodisiac. Mama macace dattijuwar qwarai data iya gyara a gargajiyance,saboda cikar hankali da shekarunta da takai matakin dattijantaka,bata taba ganin gyara irin nata ba,gyara na dattawan tsofaffi da babu side effects akai sai tsimuwa da jikinki zaiyi da kyau,wanda sun shigo duniyar gyara ne saboda bada gudunmawa ga matasan mata dake tasowa cikin rayuwar aure a yanzu.08127084190/08104553105. Yana jinta da kima a rayuwarsa fiye da duk wani abu me kima daya mallaka......yana jinta a matsayin abu mafi tsada da daraja a rayuwarsa,don haka komai nata ya zama na daban kuma na musamman. Wani tsaro yake bata,guards ya samar mata na musamman,wadanda suke tare da ita a duk sanda zata fita ko zata tafi zuwa wani gurin. Ya samar mata 'yan sanda mata biyu jajirtattu da zasu kasance da ita a motor din da take ciki,bayan 'yan aikinta dake kula da lamarin yaranta,sauran motocin kuma duka guards dinta ne. Cikin lokaci qalilan Sabreen din ta zama wata me tsada,komai nata kuma ya kuma sake zama na musamman,ya canza mata mota tata ta hawa da duka sabbin motocin da masu tsaronta zasu dinga using. *_BAYAN WASU SHEKARU_* *JADDA'S VILLA* JADDA'S VILLA shine sunan dake rubuce b'aro b'aro daga tsororuwa babban ginin gidan. Rubutun an yishi ne da ruwan GOLD jikin wani qawataccen allon qarfe da aka yiwa wani irin design me azabar kyau da daukan hankali. Wani irin shimfideden gida ne,wanda a qalla ya qunshi maka makan mansions a cikinsa guda shida. Kusan komai na gidajen iri daya ne,saidai banbancin girma da wani gidan yafi wani yawan dakuna da kuma qawatuwa da kayan alatu na rayuwa,daidai da yadda mamallakan gidan suke da buqata. Idan ka kira JADDA VILLA da aljannar duniya sam sam bakayi laifi ba,don inda akwai sunan da yafi haka nuna tsananin tsari da cikar suffa da haibar gida ya cancanci ka bashi. Gidane daya mamaye jadda street gaba daya daga hannun dama,sai hannun hagun dake dauke da qawatattun gidajen hamshaqai masu fada aji cikin unguwar da sai ka isa wane zaka mallaki gida a cikinta cikin birnin tarayyar abuja. Ba gidan kawai ba,unguwar kanta sai kabi matakai daya bayan daya kafin ka samu nasarar shigarta,bayan kuma ka shiga din zai zame maka barazana hanyar shiga JADDA VILLA. Birnin da ya shiga bakunan manyan masu kudin da suke ganin wuyansu yayi kauri a duniyar naira.....birnin daya girgiza zukatan al'umma da dama ciki harda manya manyan masu kudi na qasata dama qasashen duniya gaba daya. Manyan gate gate guda biyu da matsakaici guda daya dukka saika wucesu kafin kakai ga shiga BIRNIN JADDA kaman yadda aka rubuta daga cikin gidan gate din farko. Daga can cikin daya daga cikin gidajen dake cikin jaddas villa din,cikin tsakiyar wani qawataccen courtyard da aka shimfida hikima wajen gini da tsarinsa. Qawatattun shuke shuke ne masu dauke da mabanbantan furanni masu launikan dake kiran butterflies zuwa garesu,daga qarqashin shukokin wata 'yar qwarya qwaryar qorama ce ta zamani da aka qirqireta saboda wucewar wani ruwa me tsananin hasken da kake iya hangen wasu irin mulmulallun stones masu daraja da tsada dake zuwa a oval shape,amma suna da nau'in kaloli daban daban,kaman yadda madaidaita da qananun kifayen dake yawo a ciki suke da wadannan launikan. Wasu irin Kujeru ne sirara masu taushi aka qawata courtyard din dashi,wadanda suke farare qal,kaman ba'a tsoron kai kawon yaran da gidajen suka mallaka,yaran da suka tasamma rai ashirin da shida. Zafin rana ko sanyi duka basa rabar wajen,guri ne na musamman da kowanne gida daka cikin gidajen jadda villa aka tanadar dashi bisa tsari na musamman dake iya daidait weather na wajen. Idan zafi ne weather wajen na fidda iska me kyau da dadi,idan sanyi ne weather din wajen na bada temperature da zata dace da yanayin da mutum yakeso. Saman daya daga cikin kujerun dattijuwa anni ce,sanye da wata sassauqar riga mara nauyi ruwan madara,wadda take hade da hijabinta asalin saqar qasar Indonesia. Daga gabanta kuwa yara ne matasa maza da mata kusan guda biyar,masu kamanceceniya da juna,wasu kamanninsu sun fita sosai......wasu kuma kamanni ne na baya baya. Daga gefan daman annin wasu yara ne guda biyu da duka duka shekarunsu ba zasu haura takwas da tara ba,dukkansu share hawaye sukeyi fararen fuskokinsu sunyi jajur. "Kowa ya gama bayaninsa?"ta fada tana duban fuskokin su daya bayan daya. Da fari gurin shiru ya dauka kafin daga bi sani,ta sake bin fuskokinsu da kallo tana sake maimaita tambayarta. Kai suka gyada daya bayan daya. "Da kyau" Ta fada cikin cikakkiyar nutsuwarta dinnan tana ajiye littafin hallul masa'eel dake hannunta a gefe. "Ameen" Ta kira sunansa kai tsaye. Yaro da yaci sunan muhammadun ta hanyar fadin gaskiya akan komai da aka tambayeshi,koda hakan zai ja masa duka......yaron da kusan halayensu suke kamanni iri daya dana MUHAMMAD SAUBAN(Ku ajiye wannan sunan a next novel nawa idan rai yakai mana😄😄). Sauban din da shike binsu muhammad ameen da ahmad amaan.......amma halayensa sak irin na mahaifinsa......halayensa sak irin na ameen......shekarunsa duka duka basu wuce goma sha biyu ba......amma wani irin girma da dattako gareshi. "Me ya faru ameen?" Anni ya qarasa tambayarta. Bayani yayi mata na iya abinda ya sani,ya qara da cewa. "Amma a gaban sauban akayi.....ki tambayeshi". A nutse ta waiwaya ga sauban din,wanda yake zaune shi daya saman kujerar da babu kowa kusa dashi. Ita kanta kujerar tayi dan nesa kadan dasu,kunnuwansa manne da headphones wanda ko daga nan kana iya jin sautin qira'ar qur'ani na fitaccen shaik dinnan wato maheer almu'aiqaly. Duk wanda yasan sauban ya sanshi da yawan sauraren karatun shaik maheer duk sanda yake kebe shi kadai,wannan ne anni take kyautata zaton sanyashi ya zama na daban cikin 'yan uwansa......hasken alqur'ani kuma take tunanin ya qara sanyashi me tsananin nutsuwa,duk da tarin zuciya da yaron yake dashi. "Sauban" Ta kirashi tana yafitoshi da hannu. Kallo daya ya yiwa annin ya saka hannunsa ya cire headphones dinsa sannan ya taso ya qaraso wajen *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 __________________________ *_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽 *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂 Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾 wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 172 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 172 "Me ya hada arham da ahsan?". A nutse ya zube kyawawan idanunsa masu girma kaman na mamanshi akan dukkaninsu,sai ya matsa a hankali ya zauna gefen anni. Baiji tsoron idanun kowa ba ya zauna ya yiwa anni bayani filla filla har yakai qarshe. " Haka akayi?" Ta sake tambaya,dukka wajen ba wanda ya musa banda hilal da yayi shuru. Maida dubanta tayi ga hilal. "Allah yana cewa cikin qur'aninsa,yaku wadanda kuka bada imani da Allah.....idan fasiqi(mutum)yazo muku da labari,to kuyi bincike,gudun kada ku afkawa wasu mutane bisa jahilci(rashin sani dalilin rashin bincikenku).saiku wayi gari kuna masu nadama.......a duk sanda wani mutum yazo maka da labarin anyimin kaza,ko wane yayi maka kaza,ko kaza ya faru,dole ne akan musulmi ya nemi hujja ko dalili na abunnan ya faru,dole ne......muna da wata dabi'a ta saurin yanke hukunci,da daukan zance daga bakin mutumin daya fara zuwa mana da labarin wane yayimin kaza,wane ya batamin ko yayimin ba daidai ba.....nan da nan wannan daya fara zuwa da labarin saimu dauka shine me gaskiya,bisa jahilci irin namu na neman jin ba'asi daga bakin wani sashen,wanda muddin zaka kasance mutum irin wannan a rayuwarka,za'a yita sanyaka batawa da mutane masu daraja da kirki.....zaka yita fada da mutanen da basuyi maka komai ba.....za'a sanyaka ka yita yanke alaqa da mutanen da alaqarku keda matuqar amfani a duniyarku da lahirarku.......wannan ba halin musulmi na kirki bane a matsayinka na babba hilal.....ba kuma dabi'ar qwarai bace.....ba dattako sam a cikin ta,dukkaninku daga yau na horeku da zama masu bincike". "In sha Allah anni" Ya fada yana saukar da kansa qasa. Waiwayawa tayi ga yara biyun dake gefe tana dubansu. "Faarees da ra'ess ya tabbata kunyi qarya.....ku bawa Aadeel haquri,sakamakon qaryarku kuma wannan satin gaba daya kada naga uniform dinku a wash room,da kanku zaku wankesu duka satin nan.....sannan idan ummenku ta dawo......kune na qarshen zabar tsaraba har sai kowa ya dauka nashi" Ta fada tana nunasu da yatsa. Haqurin data buqata suka juya suna bawa wanda ake kira da Aadeel din haquri,ta kallesu daya bayan daya still tana cewa. "Ku kyautatawa junanku......kyakkyawar mu'amala itace mutum......girmankai na shashasha ne maras wayo.....hassada ta maras rabo ce,don tana cinye kyawawan ayyuka kaman yadda wuta takejin yayi.......shi kuwa sharri dan aike ne,daga inda aka aikashi duk daren dadewa nan zai dawo......alkhairi kuma danqo ne baya faduwa qasa banza.......komai dadewa ka shuka alkhairi shi zaka girba,kaman yadda komai dadewa idan ka shuka sharri cuta ko ha'ince sai ka girbeshi.....kyakkyawar dabi'a jari ce da babu kamarta,wadda duk dukiyar gidanku bata isa ta siya maka ita ba......hakanan duk talaucin gidanku idan ka sameta kaiba talaka bane har gaba da abada". Ire iren kalmomin kaka ta gari kenan a duk wani zama da zai hadata da yaran,bakinta sam sam baya gajiya da furta wadannan kalmomin a kansu,har sun fara haddacesu tun basusan ma'anarsu ba,zuwa yanzu kuma wadanda suka fara girma a cikinsu sun haddacesu tas a kansu. Basu fita a wajen ba saida kowa ya gaisa da kowa,kowa ya koma yanayinsa na dazun sannan. A sanda suke fita a lokacin sauban ya koma inda ya taso,ya maida headphone dinsa saman kansa yayi playing karatun yana ci gaba da ji hadi da lumshe ido. Kammaninsa da dabi'unsa kamar babansa,duk wani harka ta hayaniya ko fada babu shi a ciki,kaman ya yiwa kansa rigakafi daga fushi da zuciyar da yasan yana da ita. Dauke kanta anni tayi daga inda yake murmushi yana subuce mata. Tana ji a jikinta anya sauban din ba shine wannan HASKEN da take gani tsakanin iyalinta ba?,wannan mai riqon addinin ma'abocin cikakken ilimi daya haura na saura?. "Allah kayi mana zabi da mafita mafi alkhairi" Ta fada a nutse tana jawo hallul masa'il dinta tana dubawa. Tsaiwa Amaan yayi yana hango abokin tagwaitakarsa wato muhammad ameen dake fitowa daga sassansu. Sanye da fararen kayan da aka yiwa ratsin baqi sak irin kayan dake jikin Amaan din. Shima gunsa ya nufo kai tsaye yana dubansa. "Abbee fa ya shigo yanxun......kuma naga ya shirya.....ina kuma kyautata zaton ummee zaije daukowa daga airport......na tabbatar dukkaninsu sun manta da yaune wedding anniversary dinsu,15yrs" Ameen ya qarasa fada da faffadan murmushi daya qara masa kyau,yana kuma d'age dukka girarsa sama. "Na tuna......akwai wani abu ne?" "Yes" Ameen ya fada ya fada yana dariya. "Ya kamata muyi wani abu,yadda naga abbee yana wani shiryawa yanata duba mirror kaman wani dan saurayi,dolen saiya burge duniyarshi". Dariya suka saki lokaci daya,amaan yace. "Babu ruwana idan ummee ta jika.....let's go,mintunan zuwanshi da dawowarsa basu da yawa" Hannun juna suka riqe suna hirarrakinsu,wanda kana kallo zakasan akwai shaquwa da qaunar juna me tsananin gaske. Ita kadai yau take zaune saman wheelchair din nata,kusan awa biyu kenan. Mutum daya take sanya ran shigowarsa kaman yadda ya saba......yaro guda dayan da take mamakin yadda yafi kowa qulafucinta a gidan da qoqarin kula da duk wani motsi nata......yaro guda dayan da ita kanta yafi shiga ranta sosai wato sauban. Jifa jifa tana jin motsin yaran,guje gujensu kasancewar weekend ce.....amma yau ko wasan kaka da jikan data jima tana nuna musu bataso ba wanda ya leqota yayi mata,duk sai ta jita ba dadi. Sabreen ce ta fado a ranta,ba yadda za'ayi duk wuya.....duk runtsi idan tana nan ta barta ta zauna shuru haka,koda kuwa bata buqatar komai zata umarci biyu ko uku cikin haihuwa yara rai goma da Allah ya bata wani yazo ya zauna kusa da ita. Wani abu ta hadiye,karon farko da taji tana dokin ta dawo daga tafiyar kwanaki ukun da tayi zuwa qasar saudiyya. Daidai nan yayi sallama,sanye da dinkin kaftan da aka yishi da wani fari qall din yadi me daraja. Dinkin babbar riga ne da 'yar ciki dinkin da aka zamanantar dashi,ya kuma sake maida fuad din kaman wani qaramin matashi. Baiyi amfani da hula ba,sai farin rawani daya nada saman farar hular kanshi,sai ya fito kaman wani basaraken malami. Duk da ya dubata dazun yanzun bai gaza wajen dawowa wajenta ba,ya tsugunna ya gaidata,ta amsa masa da sautin da ba kowa yake iya fahimtar abinda take fadi ba idan ka dauke shi da Sabreen da suke iya fahimtar kusan komai tace. Nasarar fara fitar sautin nata ma gaba daya ya samo asali ne daga Sabreen,wani umra da sukaje,ta samu daman tara roba wajen indararon ka'aba ta tari ruwan saman dake sauka ta saitin wajen,ta kumayi tofin addu'o'i sosai data samu daga wajen mallam,ta durfafi bata. Wani abu ne daya tsayewa maamah din a rai,har yau ta kasa mantawa da abun,duk da sai bayan nasarar ta samu takejin daga ina ruwan ya fito,basu gaya mata ba gudun kada taqi sha. "Yau zata dawo?,daukota zakaje kayi?" Ta tambayeshi sanda ya miqe yana soma takawa da murdadden harshenta. A mamakance ya juyo yana duban maamah din,wai yau ita ke tambayar dawowar Sabreen?,wani farinciki yana sauka a zuciyarsa ya gyada mata kai. "Eh,saura mintunan kadan jirgin ya sauka". "A dawo lafiya" Ta furta tana jin wani dadi yana mamayeta . "Allah yasa" Ya amsa wata qwalla tana cika masa idanu. Yau maamah ke masa addu'ar da alamu sun nuna kai tsaye suna fita ne daga zuciyar ta?. Sai daya tsayar da jordan cikin motar ya daidaita kansa,ya kalli fuskarsa yaga ta koma ainihin mode dinta sannan yace suje. Bayason yaje da wani sauyi ko kadan saman fuskarsa,don yasan abune da tana masa kallon farko zata karanci hakan,shi kuma duka yau din yana buqatar kyakkyawan yanayi shida duniyarshi,wadda yayi missing nata tsahon kwanaki biyar kenan. Cikin hukuncin Allah JADDA MAJESTY JET ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake abuja. Mintuna kadan kafin jirgen ya sauke matakalarsa a hankali,tsakanin wasu mintunan kuma mutanen dake da iko da jadda majesty din suka fara fitowa. Da farko wasu matane guda biyu masu baqar fata,giant dasu,sanye da baqaqen abayas da mayafinta wanda sukayi rolling,sannan kuma suka manne idanunsu da baqaqe glasses. Mata biyun dake bayansu su dinma abayanne a jikinsu,saidai tasu ruwan wine color ne. Daya janye take da wata qaramar luxury luggage,yayin da dayan ke dauke da wata kyakkyawar jaka. Kyakkyawar halittar dake takowa daga tsakiyarsu ta dushe kowacce diya mace dake tafiya tare da ita. Mistress ameenatu ahmad mrs muhammad jadda......the lady of the house itace ke takawa d'ai d'ai cikin wani yanayi da zai tabbatar maka da cikar kamala da nutsuwa gami da kammaluwar hankali da nutsuwarta waje guda. Sanye take cikin wata Turkish gown ta wani lafiyayyen material,rigar ta bude sosai daga qasa,armless ce butter color me adon gray color da wasu manyan flowers masu ban sha'awa,wadda aka yiwa top gray color me dogon hannu da kuma sarqarta a jikin rigar ta yadda basai ta buqaci wata spare sarqa ba. Tayi rolling kanta da gray color din wani exclusive veil,qafarta na sanye da wani high hill daya kasance mahadin qaramar handbag din hannunta da batafi taci qananun abubuwa ba sai tsananin tsada da jakar ke dashi. Rungume take da wata baby girl wadda ke sanye da gown armless fara qal data kasance mahadin takalmin qafarta da kuma dan crown din dake saman kan yarinyar wanda ya hana sassalkan dogon gashinta bazuwa zuwa sassan fuskarta. Wani irin kamanni ne tsakanin ta da yarinyar na sak da sak.......abinda kawai ya banbanta su shine kasancewar yarinyar 'yar kululluba da ita. Ameenatu muhammad jadda kenan IFFA......shalelen family din jadda....diya mace qwaya daya da suke da ita cikin villa din tasu. Chubby din abbee......chubby din anni......kuma chubby din triplet da twins na jadda villa. Cikin kyakkyawar nutsuwar nan tata Madame kuma duniyar muhammad jadda wato ameenatu ahmad ke sauka da takalmin ta me tsini wanda zakayi tsammanin ba zata ita tafiya dashi ba,saidai caf caf take takawa da abinta cikin sani kan ado da gayu daya ratsa jini da jikinta gaba daya. Wani fitinannen qamshi take fiddawa wanda ya huda jikinta,irin qamshin da sai kazo kusa da ita kake iya jinsa a duk wani motsi da zatayi. Dawowarta kenan daga qasar saudi Arabia,bisa gayyatarta da sukayi don su karramata da lambar yabo da kuma girmamawa ta musamman kasancewar gidan marayunta gida na farko da kaf nahiyar africa dama wasu qasashen qetaren babu koda kwatankwacinsa. Gida ne daya fara bawa yara feature me kyau......ya fara inganta musu rayuwa da inganta mafarkansu bisa jagorancin me gayya me aiki muhammad fu'ad jadda mamallakin kamfani guda daya da baida kishiya dake sarrafa gold da Diamond a qasash kusan arba'in cikin qasashen da muke dasu a duniya sama da guda dari biyu. "Karbeta najma.....tayi bacci" Sabreen ta fadi a nutse tana miqawa nanny dinta ita gami da gyara rolling dinta daya dan cukuikuye. "Sarkin rigima" Nanny din nata ta fada tana rungumeta a kafadarta "Kunfi kusa,fadanki dana iffa ko waye ya shiga ma kunya zaiji" Sabreen ta fada tana murmushi. Murmushin daya samu isa ga idanuwan Muhammad fu'ad dake zaune cikin mota,ya kuma kori Jordan ya saita madubinsa yana qarewa duniyarsa kallo abinsa. Sam bata ganshi ba,bata kuma san yana mata kallon qurillar nan tashi ba,duk da cikin jikinta tana jin kamar wani kusanci yana wanzuwa tsakanin zukatan guda biyu. "Welcome maa" Shine abinda dukka ma'aikatan da suka rako boss jadda suke fada cikin rusunawa da girmamawa,yayin da ita kuma take amsawa cikin nuna kulawa da tambayarsu aikinsu. Abun yana bawa fu'ad mamaki sosai.....gaba daya ta zama tamkar wata uwa tsakanin kowanne ruhi dake rayuwa cikin jadda's villa. Ba iya yaran gidan su huda amna dasu saddiq ba......tsakanin kowa da kowa ma,muddin kana kwana kana tashi a jadda's villa. "Wannan tsadajjen murmushin rabonshi da akeyi ya isa haka please" Ta tsinci lallausan sautin nan nasa cikin kunnuwanta a sanda ya fito daga motar yana bude mata murfin motar yana kuma gyara babbar rigarsa da daya hannun. "Wow" Ta fada da wani boyayyen sautin da labbanta ne kawai zasu gaya maka abinda ta fada,tana fidda idanunta waje dukka a kansa. "Muffin......ka koma exactly ranar da ka zama angon ameenatu sabreen.......sak irin shigar". " Har yau har gobe har kullum ma cikin taya kaina murna nakeyi da mallakar mace irinki......ki taimakeni ki sakayamin kanki cikin motar nan kafin mazan dake airport dinnan kaf su qarasa kallemin ke" Kai ta girgiza tana dariya sanda ta fara takowa cikin jan aji. "Hammana yaushe xai canza ne?baya kallon madubi yaga yadda ya fara zama babban mutum?,babban mutum din daya ajiye yaran da sati me zuwa zasu kammala secondary school dinsu?" "Fu'ad bazai taba canzawa ba.....kishinsa da soyayyarsa game da Sabreen suna nan kaman yau aka ginasu" Ya amsa mata yana rufe motar,ya zagaya ya shiga nasa side din. _wacce addua kuka yimin littafinnan yaqi kammaluwa a yau?_🥹🥹🥹🥹 *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 *_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽 *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂 Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾 wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 173 *_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_* *follow us diaries*🥰🥰👏🏽👏🏽 https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1 173 Wani ajiyar zuciyar numfashi ya sauke yana lumshe ido gami da sauke nannauyan ajiyan zuciya. "Sai yanzu zuciyata zata koma aiki daidai......welcome home your royal highness" Ya fadi cikin salo na girmamawa yana hada hannuwansa guri guda. Murmushi tayi tana girgiza kai,kullum sabuwa ce a wajensa kaman yadda yake sabo a wajenta. "Giya nake roohi......hayaty kulliha" Ido ya fidda waje yana tashin motar tasa. "Wannan ranks din nifa bana gane musu sosai yanzu.......jira nake naga nan gurin ya tasa" Ya fada yana taba lafaffen cikinta kaman bata taba daukan ciki ba. Itama waro idon tayi tana kallonsa. Mamaki yake bata yadda har yanzu 'ya'ya basu isheshi ba,yara goma cas tara dukkaninsu maza mace daya?,me kuma yake da buqata?. "Muffin......fauzan fawwaz da fawad ba graduation dinsu next week immediately ana gama bikin nadra da haneefa?". Dubanta kadan yayi sannan ya tada motar hankalinsa kwance. "What's that supposed to mean? And what's the point?......kin daina haihuwa?". Ganin yadda yayi maganan yana nuna da gaske yake fadi,saita karya wuyanta tana narke masa. "Hamma......yanka sau hudu fa?...." "Yanka hudun yana nufin kin gama?" Ya sake tambaya yana tsume fuska. Sosai tayi calming down kanta tana saukar da kanta. "Ni na isa?" Ta fada a sanyaye. Wani abu data lura dashi yana da bala'in son tara yara,Allah ya taimaketa ya dinga bata bibbiyu har sau uku bayan ukun farko da tayi,iffa ce kawai tazo ita daya abinta,shi yasa idan suka tashi tsokanarta suke cemata me baqinjini,ita ba wanda ya rakota,su kuwa saida suka rako juna,duk da cewa a zahiri kusan farinjininta daban yake,kowa yasan wannan,farinjinin diya mace cikin yara maza. Shurun da tayi ya sanyashi satar kallonta kadan sannan ya kauda kai,bayason damuwa a tare da ita sam sam,don ta gama yi masa komai a rayuwa. "Bani labari.....How'd the trip go?". Numfashi ta sauke tana son wadata fuskarta da murmushi,saidai kafin tace komai ya sake magana. "Banga mamana bafa.....a ina kika barta?" "Tana hannun Nan najma(kaman yadda iffa din take kiranta)" Kai ya gyada "I missed her so much......da safen nan abinci sam bayamin dadi idan na kalli gurin xamanta naga bata nan". Baki Sabreen ta tura tana bata fuska. "I don't know me yasa kakeson min kishiya da iffa ne.......zan bayar da ita fa?". Ido ya waro kaman zai saki steering motar yana dubanta. " What?,yarona ko daya bazan iya badawa ba koda cikin gari ne dani......in fact ma ni koda mutuwa nayi ban yarda a rabamin yara ba bare ina raye". "Mu ajiye batun mutuwar nan hamma....." Ta fada tana maida aljihun motar data bude ta dauko mint sweet ta saka a bakinta. "Komai ya tafi daidai hamma......kuma dukka lambobin yabo dana karramawar da suka bayar naka ne....kaine ka cancancesu......ni 'yar tayi ce,Allah yakai kadan kabarin abba.....sun saka kudade masu yawa a asusun gidan,duk da nace bamu da buqatar wannan,amma sunce zasuyi don neman lada,sannan cikin daliban da muke yayewa duk shekara,a dinga ware mutum goma,maza biyar mata biyar yearly zasu dauki nauyin karatunsu har zuwa degree,har masters ma idan suna buqata har sama da hakan". Kai yake jinjinawa,ya jima yana ayyukan lada dana alkhairi kala daban daban,amma wannan din yafi kowanne yi masa dadi da qara masa walwala da nishadi. Uwa uba kuma wani abu daya lura dashi,tun daya sanda gidan ya fara aiki dukiyarsa kaman amai take,wani irin mahaukacin hauhawa takeyi,wani irin bangajejen budi yake qara samu da shi kansa kai tsaye yanzun bazaice ga adadin abinda ya mallaka ba. Ci gaba sukayi da tattaunawa shi da ita da wani irin yanayi da zai gaya maka zallar soyayya da tausasawa da jin qaine ke wanzuwa tsakanin ruhi da zukatan wadannan masoyan. Suna isa ya karbi mamarshi ameenatu iffa,don ta farka a sannan. Ita dinma da gudu ta nufoshi tana fadin. "Miss you abbee...." "Mamana.....My incomparable mother.....a mother without equal" Ya dagata yana juyata abinsa,ba ruwansu shi da ita da al'ummar dake farfajiyar gidan,wadanda kusan dukansu sun fito ne saboda tarbar Sabreen din,wanda wasu lokuta suke mata title da THE MISTRESS OF THE VILLA. K'ananun shekaru gareta amma ta zama babbar qarfi da yaji cikin gidan,duk da ta tasamma shekaru arba'in daidai a duniya......amma tsananin kula da kai da gyara jiki da kuma shan natural abubuwan gyara ga diya mace ya sanya zaka yita daukanta a shakarunta ashirin da biyar ko da takwas take. Bugu da qari idan ka kwatantata da su anni da suka kasance manya a gidan,ba laifi idan ka kirata da yarinya. Kusan duk wani dawainiya da matsaloli da zaa kaiwa annin ta hana isarsu Gareta,ballantana maamah da ba cikakkiyar lafiya gareta ba,yau da lafiya gobe babu. Girman ya karbeta da kyau,yadda ta tafi dashi kuma cikin adalci da mutuntawa ya sanya kowa yake biye da ita da tarin qauna. Ko a wajen bata wuce ba sai data duba lafiyar duka ma'aikatan,fuad na biye da ita dauke iffa yanata shan surutu,daya hannun nasa kuma handbag dinta ce. Wannan dabi'ar tasa kowa dake jadda villa ya santa,tun suna kunya har ya zame musu jiki. Ko zaman kwana uku kawai kayi cikin villa din zakasan cewa akwai wata mahaukiyar soyayya irin ta hanta da jini a tsakaninsu. Tare suka jera cikin gidan bayan gamawa da ma'aikatan yana tsokanarta. "Hajjaju da kanta......yau masu gidan sun dawo kowa ya shiga saitinsa" Yayi maganar yana maqalewa a bayan fuskar iffa yana mata gwalo. Murmushi ta saki tana mintsinar hannunsa. "Ka daina mantawa fa da cewa yanxun baban samari ne kai.....in suka ganka kana tsokanar ummensu tabbas xakaji kunya". "Suma sun jima da sanin cewa ba'a raba hanta da jini......yadda nakeso susan zallar madarar soyayyar dake tsakanin abbeensu da ummeensu alhamdlh sun fahimta" Kai ta gyada,ita kanta tasan da hakan,hakan kuma ya taimaka sosai wajen bawa yaran qwaqwalwa da rayuwa me kyau,hakanan kuma suma sai suka tashi da qaunar junansu sosai. "Banga kowa ba cikin dukka yaran gidan nan ba.....sauban dai ancemin yana gurin anni". "Kin rigani fade ne......duk da kaman su nadra sun tafi siyayya dasu sahl samr suhail duka sun bisu". Murmushi ta danyi tana jinjina kai,tana sake jin rayuwarta tayi mata dadi idan ta tuna yau zata aurar da nadra da haneefa gaba daya,ragowar abinda ya rage mata kenan take addu'ar Allah yakai mata ranta. "Kaman yaushe zaku fara bikin nan?" Fuad ya tambaya sanda suke dab da isa sassan maamah. Umarnin anni ne,duk sanda suka dawo daga wata tafiya ko kuma suka tashi da safe zasu shiga su gaisa ita ta yafe zuwan farko,su fara zuwa wajen maamah tukunna su dubata. "Don itace me lalura,tafi buqatarku a akaina,ni da lafiyata har yanzu da sauran qarfina.....kuma alhamdulillah zan iya yiwa kaina komai" "Hamma abubuwa kadan zasuyi fa......zasuyi the day of qur'an da dalibai da malamansu na mu'assas.......then zasuyi bridal shower.......sai waleema da anni ta shirya shikenan,dukkansu suda mazan basason dogon biki". Kai ya jinjina,yana jinjinawa yaran,suna da wani irin hankali da nutsuwa na daban,komai nasu moderate ne,shi yasa ya yuwa rayuwarsu wani tanadi na musamman da ba wanda ya sani sai ranar da aka daurawa kowaccensu aure. "Ma sha Allah.......Allahumma barik" Ya furta suna sanya qafa makekiyar balcony din da zata sadaka da falon. Idanunta akan tashar saudi sunnah da suke hasko masallacin ma'aiki tare da karanto hadisansa masu tsarki girma da alfarma,zuciyarta takejin tana tsananin kewa da qishirwan gurin,kaman bata taba zuwa ba tunda take a rayuwarta. Sukanje tana bin jama'ar gidan da suke da kebantattun lokuta da jirgin jadda majesty jet yake jigilar kowacce halitta dake birnin jadda villa din bayan kowanne hutun makaranta da za'ayiwa yaran. Wannan damar suke amfani da ita suke ziyartar fauzan fawad da fawwaz dake karatunsu a madeena king Abdul'azee international School wadda suka kammala kuma za'ayi bikin yayesu sati me zuwa. Kaman saukar nannauyan dutse daga qirjinta haka taji sanda sukayi sallama a tare,ta motsa bakinta tana amsa musu da sautin da ba'a fahimtar abinda take fada sosai sai wadanda suke da matuqar ganewa kaman sabreen din,don shi kansa fu'ad din sometimes sabreen ce ke gaya masa abinda tace din. Idanunta ta janye a kansu tana maidawa kan yarinya ta biyu da Allah ya jarabceta da masifar son yarinyar......yarinyar da duk gidan kowa qaunarta yakeyi saboda kasancewarta jika diya mace qwaya daya kaf cikin jikokin gidan ashirin da wani abu. Ameenatu iffa ta sakarwa maamahn murmushi tana zamewa daga jikin fu'ad ta tsallako da gudu tayo wajen maamah. "Har yanzu baki tashi kin fara tafiya ba?,kikace zaki fara tafiya kafin mu dawo?" Ta fadi cike da quruciya cikin maganarta. Murmushi kawai maamah din ta sake,yarinyar ta tattaka qafafun maamahn ta haye cinyarta tayi dare dare tana bata labarin su hamma fauzan suna gaisheta. Tayi kewar 'yan ukun sosai,su na dabanne a zuciyarta,duk da gidan cike yake da tagwaye amma nasu qaunar daban yake. Har yanzu suna iya kira video call su dukka ukun su sakata a gaba da hirarraki har sai sun sakata dariya sanna,har zaman jiran kiransu takeyi kulli yaumin,koda basu kira ba zata sanya a kira mata su. "Barka da warhaka maamah.......ya qarfin jikin?". " Alhamdulillah " Yau sautin amsa gaisuwar sabreen din ya fita da kyau har sai da sabreen ta daga kai ta kalleta a mamakance. "Ya taro?" Ta fada da sarqaqqen harshenta. "Alhamdulillah.....mun kammala cikin nasara" "Allah ya taimaka" Ta sake fada da qyar tana fuffusgo kalmar. "Ameen" Sabreen ta amsa tana sadda kanta tana tattalin hawayen farincikin dake son ballewa cikin idanunta. Kamar yadda maamah ta zata din,sabreen din saidata tabbatar komai yana tafiya daidai a sashen,daga masu kula da ita har kalar abincin da ake bata sannan suka wuce sassan anni. Suna zaune da mutuminta sauban a courtyard din da ya zamana shuru saboda fitar duka yaran da rashin motsinsu wanda anni batasan me ya kawo hakan ba. Murmushi ya sakarwa ummeen nasa da abbeen nasa,ya zare headphones din ya ajiye ya tako da nutsuwar nan tasa yana fadin. "Sannu ummee.....abbee sannu" Ya fada yana kamo iffa wadda tayi tsalle ta daneshi. Akwai sabo sosai tsakaninsu,don wani irin sassanyan kulawa yake bata ta hankali. "Anata karatun sauban?" Sabreen ta fadi bayan ya gama gaidasu,fu'ad ya dora hannunsa saman kansa. Yana jin yaron sosai a jininsa saboda yadda yake da maitar karatu,yana da buri sosai akanshi,kowanne yaro nashi yana bashi karatu daidai da abinda ya fuskanci yafi karkata akai.....kaman yadda ta fannin neman kudi ma yayi alqawarin zaibar kowa yayi kalar neman kudin da yafi sha'awa muddin bai sabawa addini ba. Da wani irin alfahari qauna da soyayya anni ke kallonsu a gabanta,har suka gama gaisawa suka fara taba hira "Kije ki huta takwara,anjima akwai general dinner a babban dining room na gidan nan,sai a qarasa hirar a can" Murmushi tayi a kunyace sannan ta miqe,fu'ad ya tayata da jakar suka rankaya dukkaninsu wannan karon har sauban suka fice. Tun kafin sukai ga bude qofar sassan taga kaman parlor din farko yayi duhu da yawa,bangaren sitting room ba ba wani wadataccen haske. Tanata so tayi magana amma kuma Allah bai bata iko ba har sai da suka shiga parlor din. Duduun ba wani haske,abun da ya basu mamaki kenan daga ita har fu'ad din,ta bude baki zatayi magana fitilan farko ta kama. Harafin H ne tafkeke,mamaki ya cikata,zatayi magana A ta bayyana,da wani irin sauri P ta bayyana a jejjere ragowar suka kama suka bada cikakken sunan HAPPY WEDDING ANNIVERSARY. Baki sake take kallon harufan,ta juya a hankali da zummar yiwa fu'ad magana ko yaga abinda take gani,sai gaba daya wutar falon ta kunnu hade da wasu abubuwa masu walwali da suka soma bude kansu da kansu daga jikin fitilun suna watsuwa a kansu,lokaci guda kuma muryoyin zuria'ar yara na jadda din ta hadu wajen fadin "Happy wedding anniversary" Sai a sannan suka ankara da komai da tsananin mamaki. Ameen,Amaan,hilal dan huda na fari,naseem dan amna na fari,sai yaron wajen farouq na farko shima Aleem,sai tagwayen sabreen na biyun masu bin su ameen Aabid da Aadil,sai wasu twins din masu binsu Aadil din,irfan da farhan wadda ameenatu iffa ita ta zama cikon ta gomansu. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 174 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX 174 Yara ashirin da daya ne idan ka dauke mutum biyar dasu nadra suka fita siyayya dasu.......sai fannah da huda dake tsaye a bayan yaran da alama su suka tayasu hada wannan surprise din. Inda Allah ya kawo ma sauqin abun amna bata nan,tare suka fita siyayyar dasu nadra tabbas da abun sai yafi haka. Kasa magana sabreen tayi,harga Allah tana sane da yau dinne suka cika shekara goma sha shida da aurensu,amma bata kawo zatayi wani abu da wani zai gane ba illa tsakaninsu ita dashi,sai gashi yaran sun rigata aiwatar da komai. "Ku ko?" Sabreen ta fada tana nuna fannah da huda,fanna din da amnar da dukkaninsu zuwa yanzu tana jinsu tamkar uwa daya uba daya suke. Tana nunasun da yatsa tana murmushi sai kuma kukan farinciki ya barke mata,ta aza kanta saman kafadar fu'ad din tana matsar qwalla. Irin wannan soyayya da suke gwada mata batasan wacce iri bace,bama ita ba.....kusan dukkaninsu ba zaka tantance wane da wane ga daga inda suka fito ba. Rankatakaf jikokin gidan dama iyayensu kallon uwa suke mata,kuma hakan baya rasa nasaba da yadda ta riqesu kaman ciki dayan suma fito. A cikin yaran ba wanda bata taba rainonsa ba,duk itama tata bataliyar,duk kuma da cewa kusan kowanne yaro yana da nanny dinsa a gidan,sai wanda suka kai shekarun girma irinsu ameen sannan ake barinsu su koyi rayuwa da hidimar rayuwar data zamewa kowa ya koyi yiwa kansa. Idanun yara kawai ya hana ya rungumeta,amma qasa qasa yake fadin. "Karki bata fuskarki,karki kashe mana farincikin yau" Ya fada yana dan bubbuga bayanta. "Kita fatan muci gaba da irga wadannan shekarun tare" Abinda ya rada mata kenan. Qaramin walima akayi a gurin da kayan maqulashe kala kala,kuma abunda ya bata mamakin shine,koda autar gidan iffa wadda tare suka shigo gidan sun tanadar mata gift din da zata bawa daddy jadda (yadda gidan suke kiransa kenan in general idan ba'a sassansa bane). Farinciki da walwala ne kawai ya wanzu a gurin,inda daga qarshe dai bata haura samanta ba kota wuce sassanta ta lalace a nan tana tsakiyar family din nata suka zarce da hirarrakin bikin da zaa fara jibi jibi. Wayarta ta ciro da zummar kiransu nadra taji inda suka dade haka da yawa sai taci karo da tarin miscal din jadda. Ta zaro ido tana mamakin tun yaushe yaketa kira bataji ba?,saiga shigowar wani kiran nasa. "Sabrrrr" Kawai ya fada a narke,take ta fahimci yana buqatarta a kusa dashi. "Banda abun hamma.....awa daya kawai ya rage ayi magriba fa?" Ta fada cikin mita tana tura katafariyar qofan master bedroom dinshi. Bata gama ajiye qafarta taji an ficikota ciki,a zafafe ya manne bakinsu guri daya ba tare daya jira komai ba. Har kullum har ko yaushe har kuma abada mantawa takeyi da shekarun dake wuyansu idan suna tare da jadda din. Wani irin mutum ne dake da baiwar narkar da zuciyar diya mace ya kuma mantar da ita komai. Abinda yayi imani dashi shine,yadda kowacce diya mace a kullum take fadi tashin neman hanyoyin faranta ran namiji da burgeshi,haka ya kamata kowanne namiji shima ya kasance cikin sanin hanyoyi da salon mallake zuciyar matarsa......wannan dabi'ar tasa ta sanya yayi zarra a zuciyar sabreen din. Sai data tabbatar ta samar masa da nutsuwa sannan ta baiwa kanta hutu tana aje numfashi,ya birkitota yana maqaleta a jikinsa bayan sunyi alwala sun dawo. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kafin daga bisani taji saukar numfashinsa a hankali bacci me cike da nutsuwa yayi awon gaba dashi. Sai bayan sallar isha'i ta samu saukowa daga wajensa,a lokacin ya fita sallar isha'i,da wannan damar ta samu tayi wanka tayi kwalliya kuma cikin atamfa kaman yadda ta saba idan zasuci abinci nasu duka. D'as d'as take takawa kaman ba wannan jikin bane ya fidda rai goma ba,har ta iso babban parlor din da anan aka gina katafaren dakin cin abinci. Ta samu kowa yana gurin,kowa kuma yasan mazauninsa yana kai a zaune,sauran wadanda basu hadu ba sai a sannan irin musaddiq saddiq da farouq duka a nan suka gaisa suna tayata murnar ci gaban da aketa samu. Kowa ya hallara kuma faud din ake jira,shine qarshen shigowa,yana takowa a nutse da wata irin haiba da kwarjinin da ya qara yawa sanadin shekaru da kuma riqo da addini da yake dashi,kwarjinin da yake hana mutum musu dashi ko yin abu ba daidai ba,kwarjinin da hatta sabreen a yawancin lokuta yakan daketa duk kuwa da cewa dazu dazu suka rabu a daki cikin wani sirrintaccen yanayi,amma yanzun data kalleshi kwarjinin nan ya dawo fes saman fuskarsa. Kusan yara yaran a tare suka gaidashi,su sabreen huda fannah da amna suka fara serving na kowa da kowa a nutse ba wani hayaniya kaman ba taron mutum kusan talatin ba. Cikin qauna da tsabar sabo da juna suke cin abincin,hirarraki suna gudana a tsakaninsu. Har yau har kuma gobe yana maintaining class dinta a idanunsa,bata duba an dade tare.....an jima da juna ta dinga wasu abubuwa da babu aji sam cikinsa a wajen diya mace( mata yana da kyau ku kula da wannan,stay classy please,karki dinga abu gaban miji wargazaza koda shekara dubu kukayi ki tabbatar masa ajin nan fa akwaisa,idan ba haka ba ya hango wadda bata kaiki ba nata ajin ya dinga dibansa yana burgeshi). Shi dinma satar kallonta yakeyi,yanason gano meye ya banbantata da sabreen din shekaru goma sha baya?. Ya dade yana against in din maza da yawa akan suna da babban laifi da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen wargajewar matansu,mace 'yar tattali ce.....'yar a bata kulawa ce,mace tamkar fure take,dole idan anaso aci gaba da ganinta sharshar a tsaya mata da ban ruwa,wato cima sutura muhalli abun sha me kyau,a debe mata damuwa daga zuciyarta. Ta samu daman zama da amaren nadra da haneefa har kusan sha daya na dare,don shima sun kebe dasu musaddiq suna tasu tattaunawar,har suka kammala ya dawo ta parlor din. Daga tsaye yake dubanta da lumsassun idanunsa,hannayensa cikin aljihun rigarsa. "Madame.....baa kammala bane?". "Saura kadan hamma" Agogo ya kalla sannan ya sauke dubansa. "Kubar addan nan ta huta mana.....da safe sai a qarasa" Dariya nadra da haneefa suka saki suna miqewa gami da tattare kayan da take dubawa,haneefa tace "Hamma babu ruwanmu fa,tun dazu mukace mata xamu qarasa gobe tace yau xaa gama.....saida safe" Ta shilla da dan qaramin gudunta tana bin bayan nadra da tuni ita ta fece. Ta dawo da idanunta daga kan haneefa tana murmushin wai auta itace yau da aure?,saiji tayi kawai anyi sama da ita. Wutsil wutsil ta fara yi da santala santalan qafafunta kamar qaramar yarinya. "Hamma......please mana,kada wani ya ganmu mana?". "Who cares?" Tunda taji ya fadi haka tasan zai wahala ya sauketa idan ba fita sukayi ba,don haka ta kwantar da kanta saman qirjin da duk duniya yafi mata ko ina dadi da samun cikakkiyar nutsuwa. ★Kwanaki uku kacal da dawowarta aka fara bikinsu nadra din,iya events din data fada din kusan haka aka yisu. Saidai fa tun ranar bridal shower fu'ad din bai sake barinta taje komai ba,saboda wani irin sassanyan kyau da tayi me daukan hankali cikin wata butter color gown ita da iffa da tayi order dinta tun daga Egypt,tana yawo kuma da tag din bride sister daya sake bata ranshi. Lallaba kayanta kawai takeyi,tasan halinsa sarai a kanta baida sauqi,ta samu ta saukeshi ta kuma kiyaye dukka dokokinsa har aka gama bikin lafiya. Saidai ko bayan bikin still mitar bridal shower day din ya dinga mata,saida ta samu ta bashi wani zazzafan dare guda daya sannan ta wanke kanta. *_GRADUATION DAY_* *@KING ABDUL'AZEE INTERNATIONAL SCHOOL* Triplet din 'yan qasa nigeria kuma haifaffun qasar madeenatul munawwara......wasu irin yara ne da sunansu dasu kansu sukayi fice cikin makaranta dama wajenta. Bawai don kawai farinjinin 'yan uku ba.....aah hatta da kaifin basira da Allah ya zuba musu,matsanancin nutsuwa da sanin ya kamata.....inda daga qarshe kuma suka zama dalibai madiya hazaqa da qoqari cikin daliban da makarantar ta fitar. Sanda makarantar ta tasosu ta tsaidasu saman stage tana wassafa kyawun dabi'u da hazaqar yaran sai sabreen ta kasa daurewa,ta kifa fuskarta tsakanin tafukan hannayenta tana jin wani irin alfahari da yaran da kuma qaunarsu tana ratsata.......wani irin farinciki da batasan yadda zata misaltashi ba na kyauta da baiwar yaran da Allah yayi mata,wanda a yanzun haka cikin amsa kuwwa ake sanar da kowa cewa su din cikakkun 'yan qasa ne.....gwamantin saudiyya kuma sun dauki nauyin komai da komai nasu saboda girmamawa da jin dadin yadda suka zauna da kowa cikin makarantar dama qasar lafiya. Da qyar ta iya isa tsakiyar yaran nata don karba musu kyaututtukan karramawa da suka samu,duk da jikinta a lullube yake kirif,baka ganin komai nata sai zagayayyar fuskarta,amma duk da haka wasu sun cika da mamakin cewa itace mamansu. Tun tana iya amsa har gifts din sukafi qarfinta saida jadda dake sanye cikin wata rantsatsiyar shadda ya tako da sanyin nan nasa da nutsuwarsa ya tallafeta da wasu kayayyakin. Ranar wata rana ce da bazata gushe ba a zukatansu,cike da tarihin da bazai kankaru ba cikin rayuwarsu. Already sun tsara ana kammala taron zasu koma makka su sauke umra gaba dayansu,saboda nuna godiyarsu ga Allah da kuma sake roqon ubangiji ingantacciyar rayuwa me dorewa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 *_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽 *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂 Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾 wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 175 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________ *_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*👇🏾👇🏾👇🏾 https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1 __________________________ 175 A maimakon jirgi a babbar lafiyayyar mota suka taho zuwa makka. Wata irin tafiya ce ta iyali me dadin gaske,hirrraki da labarai duka sun cika motar dake dauke da JADDA FAMILY. Saidai duk da hakan daga can seat din baya ita da fu'ad ne zaune,tadan dora kanta saman kafadarsa tana jin kasala da wani saqe saqe da cikinta yayi mata wanda batasan Meye dalili ba. A fili kuwa hotunan graduation din take kalla daya bayan daya. Duk inda zata wuce fu'ad da yaran sai tayi zooming ta kallesu sosai,tana jin kaman ba yaranta ba,kaman wani imagination ne a cikin duniyar mafarki ma,har sai da fa'ad daketa sauraron shirmen yaran daga gaban motar yana murmushi kadan kadan ya ankara da ita. "Kina mamaki ne?" Kai ta daga ta kalleshi sannan ta maida saman kafadarsa. "Ina mamaki mana hamma......yau sabreen da kowa ke mata kallon KARUWA da yara irin wannan?,sabreen din da kowa ya gaza janta a jiki yaji meye damuwarta,meye kuma uzurinta yau ita keda yarannan?......sabreen din da tafi kowacce yarinya nutsuwa da hankali saboda ita din rainon ummee ce yau ta zama haka meye sila?,ba hujja ba dalili sai yanke hukunci babu bincike". Bata tsaya jin ta bakinsa ba ta dora. "Alhaji ahmad me citta shine asalin sunan mahaifina,wanda ya shahara da sana'ar saida citta kanunfari da sauran kayan da suka danganci wannan da wasunsu ma daga qasar larabawa ake shigo musu dasu. Abbana ya auri ummeena ne a sanda yake da matan aure biyu da yara mata goma sha biyar,ummena ce ta uku,mace me tsananin haquri da kawaicin daya sanyata taci nasarar zama da sauran matan abbana,wanda cikin su take da babbar abokiyr adawa wato bibo,wadda ita ummee ke bi. Abban mu ya tsaya sosai a kanmu,shanmu cinmu tarbiyya da iliminmu,don har yanzu tasirin dagewarsa ce a jikina na ilimin dana samu daga private school daya sakamu me tsada,tun daga matakin free nursery har secondry,duk da cewa ina js 3 abbanmu ya koma ga Allah,ummenmu itace ta jajirce naci gaba da wannan makarantar har na shiga ss3 second semester,a lokacinne Allah yayi mata rasuwa,a lokacinne asirinmu ya tonu,maraici kuma ya afko.mana gadan gadan,ummenmu ba 'yar qasar nan bace,don haka bamu da kowa a kusa damu da zai tallafemu. Sh momma sunso tafiya damu amma kawu ya saka kuka,wai ya za'a tafi da zuri'ar ahmadu yana raye?,shi yayi alqawarin kula damu kaman yadda abbanmu ya kula da rayuwarsa. Abbanmu ne ya riqeshi bayan rasuwar iyayensu tun auren abban ma na fari,bai kuma qyale kawu ba sai daya aurar dashi ya hadashi da jari yana saka ran wasu halayensa da bayaso zuwa sannan kawun ya dainasu. Da wannan yaqinin suka barmu hannunsa,ashe kuma lokaci lokaci suna masa aike da sunanmu,amma ko labari bai taba bamu ba bare muga abinda suka kawo. ....... Tom ko bayan mutuwar abba kowacce mace ita ta koma hidimar kanta da kanta,to yanzun da bamu da uwa sai ya zamana ba wanda ya damu damu,ba wanda yake dubamu,ba wanda yake damuwa da munci bamu ci ba,munsha ko bamu sha ba,mun tashi lafiya?,waye baida lafiyar?,dukka ba wanda ya saka hakan a tsarinsa. Da farko na dauka abun na wasa ne,na dauka zasuji qanmu,saina fara nema mana abinci daga dakunansu kafin na fahimci ba wanda zai iya cida mu,don da zagi nake fita a dakin da qyama da tsangwama,daga bisani dole na koma roqarwa su huda a maqota,donni ban damu naci ba,muddin sukaci shikenan tawa me sauqi ce,zan iya kwana uku ma banci komai ba,saidai nasha baqin ruwa na kwanta. Sannu a hankali suma maqotan suka fara hanani,sai ya zamana mun qarasa galabaicewa,ciwon yunwa yanason kama huda da haneefa da bata gama sanin ma me ake ba idan yunwar taji ba. Ba wanka ba wanki don ba wanda zai bamu sabulu,saidai da yake ummenmu ta saba mana da tsafta hakanan mukeyi da zallar ruwa. Maqociyarmu kuma qawa ga bibo ita ta fara bani shawara. "Kina da kyau sosai sabreen,kaf gidanku ba yaro me kyanki.....me zai hana ki tallata hajar jikinki?,wallahi abinci ma saikun bawa wani" A ranar hankalina yayi mugun tashi,mukayi uwaka ubaka da ita,kaf kimarta ta zube a ido na,ita kuma ta kamani tamin shegen duka akan na mata sata kuma na mata rashin kunya. Ba wanda ya damu yaji ba'asi saboda basa sonmu bamu da gata,saima tayata da bibo tayi,haka nayi kwana uku kwance ina zazzabi ba magani a dole na warke. Sanda naga yunwa na neman rayuwarmu saina fara da tambayar alhaji baqo,aboki na kusa ga mahaifinmu wanda nake kyautata zaton zai iya taimaka mana" Shuru tayi tana hadiyar wani abu me ciwo. "Saidai abun mamaki abinda kuma ko yau na tuna yakemin ciwo,ya nemi yaci amanar amintaka,ya nemi na bashi mutuncina yaci gaba da ciyar damu duka. A nan ne naci masa mutunci saboda mamakin daya bani,kamar yadda mukayi da waccar matar shima duka yayimin ya hadamin da sharri,abu na farko daya fara qeqasarmin da zuciya,na fahimci kaman ba wanda zaiji tausayinmu a unguwar,binda yasa na kasa mantawa ko yafewa,na koma na kunna masa gobara a dakinsa data jaza masa asara me yawa,ya gano nice,yace zai kaini ga 'yan sanda,na gaya masa ina da shaidar cewa muddin ya aikata haka ni kuma nizan babbake gidansa duka da 'ya'yansa da matansa,abinda ya sakashi haqura kenan,tun daga ranar idan na ganshi sai tsaki habaici da tsartar da yawu,sai duka ya tsargi kansa yana tsoro kada na tona masa asiri,sai ya koma kaman sirikina. Daga nan saina fara yawon nema mana abinci,duk da ba cikin kyakkyawar kama nake ba,amma duk wanda ya ganni ringidi ringidi zai jani ya kaini gun cin abinci a zubamin,saina juyewa su huda a leda,sukance ki cinye,indai kin bamu hadin kai lallai abinci saikin ture. Mutun na farko daya fara nunan me hakan yake nufi na samu na gudu ina zaginsa,akayi na biyu na uku na hudu na biyar shida har goma,duk wanda yaga bazai samu abinda yakeso ba saiya qwace abincinsa. Maza da yawa haka muka dinga yi,abinda ya sake dasamin duniya ba imani.....babu me taimako don Allah sai don wani abu na daban,dana fahimci haka saina fara tunanin ta yadda zan amfana da kudadensu ba tare da mutuncina ya tabu ba. .....salis shine mutum na farko dana fara gwada hakan a kansa,na saka masa maganin bacci a lemo,na kuma debi kudade masu yawa na gudu. Wannan kudin su suka fara canza rayuwata,na siya mana abinci me yawa,suturu da komai na fara kwalliya muka fita daga qazanta. Da bincike salis yasa aka samoni,aka kamani,kamun da dashi bibo tayi amfani ta fara bugamin tambari da batamin suna,tunda tana baqinciki kwana biyu muna cikin abinci da duk kayan wadata na rayuwa,saita saka idon lallai sai tasan inda na samo,saiga case din salis. Sanda ake tuhumata na kasa bada amsa,na tsinci dai wata murya tana cewa. "Ku saketa fa,nine shaida bata da laifi,ya cinye kudinsa ne kawai zai laqabawa wata" Wani matashin dan sanda ne ya fadi haka. Wannan shine jib,silar haduwarmu kenan,mayen computer na gaske da salis da yake kawunsa yaqi taimaka masa da registration a shekarar qarshe da yake ciki saboda rashin kirki,wannan ya sanyashi rasa damar karatunsa,da cuku cuku ya samu aikin dan sanda da qaramin albashin da bai wuce ladan ganin ido ba. Haduwarmu uku da jib magana ta hadamu. Shima maraya ne,banda wanda nake gayawa damuwata amma ganin kirkinsa da yadda da nayi da nutsuwarsa a ranar mukayi dogon hira dashi. "Basa taimako Don Allah,ni shaida ne.....amma idan basu taimakemu don Allah ba,zamu diba ta qarfi da yaji" Da taimakonsa muka soma gudanar da plan dinmu,ranar farko na fadi,aka biyo sawunmu,Allah ya hadamu da busari ya daukoni kyauta,wanda tun daga ranar ya zama dan adaidaita sahuna,daga baya bayan uban gidansa ya qwace abun hawansa,na hada dukka kudina na siya masa wata,sanadin haka kwananmu biyu ha abinci,saboda shi dinma marayanne,kuma shike daukan nauyin tsohuwar mamarsa wadda shi kadai Allah ya bata a duniya" "Sannu a hankai aikinmu ya dinga tafiya daidai,indai zan fita sai nayi nasara,ina yin nasara ina gane cewa maza babu Allahba ransu,wasu mazan sukan daukaki matan bariki su wulaqabta iyalinsu,wasu mazan kuma saidai ki bada jikinki su baki kudi,don haka mukayi tsare tsaren da duk wayonka bani zuwa gurin da kakeso,saidai na sameka a guri public mu qarqareta a nan,na zare kudin ta hanyar taimakon jib dake sarrafa na'uarar,daga ranar kuma ba zaka sake jina ko ganina ba,bazan sake kuma zuwa duk wani guri da muka taba haduwa dakai ba. Nasha samun barazana amma Allah ya kiyeyeni,ban taba yarda ko farcena wani namiji ya tabamin ba duk kuwa iya wayonka,wanda ni nasan hatsari na saka kaina me girma,ba wayona ko dabarata bane kuma ya qwaceni ba,zuciyata akwai Allah ya duba. Duk namijin da zan hadu dashi ina fara karantarsa,adadin son matanka da fasiqancinka.....adadin barnar da zaka gani a dukiyarka......akwai nutsasun maza daidaiku dakeson aurena da tun tafiyar farko nake zamesu daga gareni saboda basu cancanci na cutar dasu ba,amma kuma bani da wani nufin aure kai ko sha'awa ma baya bani.....mazanma dukkaninsu haushi suke ban,saina sallamesu salin alin duk iya nacinsu kuwa. Yadda nake shiga me kyau nake fita da yadda duk wata buqata nake sauke mana ita ba tare da anga ina sana'ar komai ba sai bacin suna yahau kaina......yayin da shaidar zur dasu bibo ke qarawa 'yan waje ya sake basu qwarin gwiwar yadda da komai a kaina,ban damu sosai ba sai dana qara hankali,amma damuwata ta dadu qwarai sanda naga suna qoqarin brainwashing ma su hud akan qazafin karuwanci da zina. Kudi suka fara shigowa har suka fara fin qarfin buqatuna,sai a sannan na lura akwai tarin marayu a unguwanni daban daban,mabuqata marayu da iyayensun harma da marasa qarfi......saina saka marayu guda hamsin nauyin su saman kaina,duk wani abu da zan samu kuma kasonsu yafi nawa yawa,a haka na dinga kula dasu da nawa qannen......har xuwa sanda na hadu da mika'il komai kuma ya faru" Ta qarasa maganar tana sanya gefan mayafinta tana share qwallar data jiqa mata fuska. "Ki yafemin......ki yafemin sabreen don girman Allah......ku tayani roqar anni ta yafemin" Muryar maamah data sauka musu a baza wadda ta saka sabreen sake sakin kuka. Ashe dama akwai rana irin wannan da zatazo?. Sautin kukan ya taso anni tana dubawa ko cikin yaranne suke rigima,saidai sanda ta kawo qarshen motar taga sabreen ce saita zauna a wata kujerar tana shirin tambaya,amma yadda maamah ta riqe hannunta gam cikin nata ya tsoratata ya kuma bata mamaki. "Ameenatu ki yafemin........ki yafemin,iya abinda zan iya cewa daku kenan....kunyimin halaccin da bazan iya biyanku ba amma baqar zuciya da shaidan gaba daya sun sanya idanuna rufewa,kin yafemin don girman zatin Allah ta yadda idan na tashi mutuwa zan mutu cikin salama". Sosai qirjin fu'ad yayi nauyi saidai wani farinciki kebantacce yana dawainiya dashi. Har yanzu ya daina jin sautin kukanta na daren jiya,sanda ta sanyasu a gaba shida musaddiq akan su yafe mata. Wani irin kuka dake dauke da zallar nadama cikin ido murya da kuma lafazinta. Daga shi har musaddiq ba wanda baiyi kuka ba......wani hukuncin Allah da lamari na uwa kuma.......cikin awanni biyu kacal da sukayi zaune da ita tana qoqarin basu labarin komai da hardaddiyar muryar ta,saiga zukatansu dukka sunyi wani irin sawai. Basu bar dakinba saida tayi bacci tsakanin qafafunsa shida musaddiq,wanda ko bayan sun fito a dakin shi da musaddiq din ganin komai suke kaman mafarki,sai suka samu kansu da rungume junansu. Fu'ad ke lallashin musaddiq "Ba abinda yafi qarfin addu'a......ba wani lamari da yafi qarfin Allah,alhamdulillah da Allah ya qaddara mata shiriya tunda sauran damarta" Wadannan kalaman su suka tsagaita kukan musaddiq. "Anni ki roqamin hamza ma......na cutar da mutane da yawa ta fuskoki da dama......amma yanzu kune nake gani kune tare dani ku kuka rage.....ku yafemin naji dana sauran mutane.....hajja da laila dukkaninsu babu su bare na nema yafiya a garesu........fareeda ta haukace bata da cikakken hankalin da zamu yafewa juna nida ita". "Allah ya yafe mana gaba daya" Cewar sabreen qwallar farinciki na fita a idanunta. "Allah ya tabbatar damu kan hanya madaidaiciya.....Allah ya kyautata qarshemu" Anni ta qara da wannan tana goge Qwallar farinciki da Allah ya qaddarawa maamah shiriya bata mutu da haqquna ba saina wadanda suka rigata gidan gaskiya.𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 176 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _____________________________ *_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_* https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1 176 Zuwa yammaci sun daura niyyarsu suka kuma fara gabatar da umarar wanda cikin awa biyu suka sauketa. Itakam sabreen kusan duk sanda sukazo tana yin nesa ne da ayarin familyn jadda,don tana jin kamar tafi kowa yawan buqata a cikinsu. Sau tari bata sake haduwa dasu sai a masauki. Abinda ya gudana kenan yau dinma,don bata tashi komawa hotel dinsu dake daura da harami ba sai tsakiyar dare. A gajiye ta bude dakinsu wanda yake cikin jerin dakuna mafiya tsada dake hotel din da BB farouq ya kama musu. Kowa da iyalinshi,sai kuma babban daki dake dauke da bedroons guda biyu,anni ta dauki daya maamah ma ta dauki daya da jikokinsu da masu aikinsu. Da sallama ta shiga dakin,muryarta can qasan maqoshinta da wata irin gajiya a jikinta. Yana zaune da farin soft and cotton shirt me zagayayyen wuya,sai boxer da bai qarasa idon sawunsa ba. Littafine a hannunsa wanda yake bayani akan hajji da umra da kuma falalar madeena yana dubawa,ya daga kai a nutse yana amsa mata gami da zuba mata narkakkun idanuwansan nan. Qafafuwansa ya janye yana gyara mata pillow din dake wajen,da idanu ya mata nuni tazo ta zauna,saita qaraso tana zubewa saman kujerar. Hannu ya miqa ya zare mata hijabin jikinta bayan ya karbi handbag dinta da carbinta ya ajiye,ya zare mata hular saman kanta,wanda hakan ya bawa gashinta me sulbi daman bajewa. "Yanzun nan nake shawarwarin binki.......daren yayi yawa duniyata......me kiketa roqa hakane wanda Allah bai baki ba?" Ya qarasa tambaya da murmushi kan fuskarsa yana miqa mata ruwan daya tsiyaya mata a cup. Sai data maida masa murmushin sannan ta karba ta shanye,ta ajiye cup din tana dubansa. "Na godewa Allah......na gode duniyata......haqiqa Allah yayimin komai tunda ya bani kai......saidai 'ya'yanmu....uwa bata da wani sauran bacci a sanda ta tara zuria,kullum addu'arta shine yadda zasu samu rayuwa me kyau,ba irin rayuwar da iyayensu sukayi ba suka tsallake da qyar". "In sha Allah.....tun basuzo duniya ba tun iyayensu ma basu hadu ba muke roqa musu rayuwa me kyau......ubangiji yaji kuma ya karba da yardarsa" Kai ta gyada cike da gamsuwa,yayin da shi kuma ya miqe ya wuce toilet. Ruwa me dumi sosai ya hada mata,ya dauko mata towel ya fito. "Oya zaki wanka ki dawo ki kwanta ki huta,kin gama hidimar biki kikazo kikayi tasu fauzan.......ga kuma zaman mana addu'a dana tabbatar idan ba nigeria muka koma ba bazai barki ki huta ba". Murmushi tayi idanunta suna lullumshewa saboda tsananin gajiya,ta miqe da qyar ya taimaka mata ta cire kayan jikinta ta karbi towel din tana wucewa bandakin. Dumin ruwan ya hanata gama wankan da wuri,har sai da ta gasa jikinta sosai sannan ta fito,ta daura alwala ta tsane jikinta sosai,saita cire wata doguwar riga daya zaba mata me taushi dake jikin hanger ta zura sannan ta tako a nutse ta fito tana qoqarin daure gashinta da yayi mata damshi saboda ruwa daya taba. "Hamma yau ko yatsana bazan iya dagawa ba......am really tired" Ta fada tana jin idanun suna mata nauyi sosai. Shuru taji bai amsa mata ba,bayan tana hango qafafunsa daga qasan idanunta yana daga tsaye. "Hamma kaina ya jiqe,bazan iya busar dashi ba saida safe" Ta fada tana hayewa kan gadon,burinta kawai taji jikinta saman gadon. "Meye wannan?" Tambayarsa ta ratsa kunnuwanta gami da saukar wani abu a jikinta sanda take shirin kwanciya. Birkitacciyar fuskarsa ta kalla,yadda taga ya hautsine ya sanyata bin abinda ya jeho din da kallo da sauri. Tablet ne na family planning wanda har ansha rabinsa. Saita saka hannu ta dauka gabanta yana wani irin bugawa,ta miqe da sauri da maganin a hannunta a rude ta sauka daga saman gadon. "Magani ne hamma......" "Na tsarin iyali ko?!" Ya fada da wata gigitacciyar murya dake nuna tsananin fushin dake sauka saman zuciyarsa. "Eh hamma.....amma ka tsaya......" "Na tsaya sabreen?,na tsaya kiyimin me?" Ya tambayeta qofofin hancinsa da jijiyoyin kansa suna budewa. "Na tsaya ki gayamin ke kika tsaida haihuwa hakanan tun daga kan iffa?,na tsaya ki bani labarin yadda kika fara shan maganin planning?,ko na tsaya ki gayan kin gaji da haihuwa?" "Duka ba haka bane hamma!" Ta fada itama da muryar data dagu fiye da dazu. Kalamansa gaba daya sun firgitata da wani irin tsoro,lafaxinsa gaba daya ya gama rudata.....ya zaiyi hukunci irin haka?. "Duka ba haka bane to yaya ne?,kin taba samun tazarar haihuwa irinta iffa?,ko kin taba kaiwa haka?,shi yasa nayita tambaya ba bayani gamsashe?,ko shi yasa naketa magana ke sam ba damuwa a lamarinki!!!" Ya qarasa fada da wata tsawa data sanyata danne kunnuwanta tana fadin. "Ya isa hamma!!" Ta fada da murya me qarfin gaske saboda tsoratar da tayi. "Tsawa kikeso kiyimin?" Ya tambayeta yana nuna qirjinsa da yatsansa. "Kiyi kome kikeso sabreen.......sonki da nakeyi ne ya jawomin......ki jani da duk kalar abinda kikaga dama.....kiyi duk yadda kikeso!" Ya fada yana wurgar da daya kwalin dake hannunsa a qasa. "Karka qarayimin tsawa hamma" Ta fada tana jin fushi ya fara taso mata. "Karka qara zargina akan abinda ba haka yake ba......idan ba haka ba..." "Ba zaki yafe ba?". "Basai na fada da bakina bama......na gaji hamma na gaji,wanne irin 'ya'yane ban haifa maka ba?,wanne irin baiwa ce Allah bai mana ba na 'ya'ya,samun tazara tsakanin haihuwa da wata haihuwar lallai sai ace sai ya zama daidai dana baya!......ana yiwa Allah dole ne?,idan kuma yace gaba daya ka gama haihuwa fa?!" Ta qarasa fada kuka yana qwace mata. Wani malulun bacin rai ya taso ya saukar masa,donme zatace idan ya gama haihuwa fa?. "Ban gama haihuwa ba sabreen.......saidai idan kece zakiyi silar faruwar hakan" "Eh nice din.....nice hamma" Ta fada itama a fusace cikin gajiya da jin bayanansa. "Okay.....okay.......yanzu kika fitomin a mutum.....kin tabbatar min da abinda nake zargi kenan". " Ba zargi dama kakeyi ba.....kana cusamin laifin da bansan dashi ba......ko meye kake tunanin na aikata na aikata hamma!" Ta fada da wani irin kuka. "Don kin aikata sai me?,saboda kinga na damu dake?,saboda ina sonki.......saboda kina ganin bazan iya rayuwa ba tare da ke ba?........idan na daina sonki shikenan?" Ya fada da salon tambaya yana dage mata girarsa dukka biyun gami da bude idanunsa da suka sauya launi. Wani irin abu taji kaman an jibga mata a saman kanta. "Kana zaton nima bazan iya rayuwa babu kai ba?,bazan iya rayuwa ba soyayyarka ba?......ka daina sona din fine......sai me?" Ta fada da qarajin kuka. A gaggauce ta juya ta fusgu hijabin data cire dazu ta maida,ta juya ko wayarta dake kuwwa bata dauka ba illa jakarta data ajiye ta fice a dakin a gaggauce. "Kiyita tafiya.....zan iya rayuwa nima ko babu ke" Ya fada a birkice kaman wanda zai zauce. Komawa yayi ya fada saman gadon yana jin wani irin bacin rai yana saukar masa. Tayi masa laifi kuma sannan ta fishi fushi?,ya samu yara alhamdulillah amma arziqin da Allah ya bashi yana jin yana buqatar qarin wasu......yanason ya gina family din da aka jima ba'aga irinsa ba......yanaso ya gogewa maamah gorin yawan haihuwar da tace asali dangin babanshi na dashi,haifarsu su biyu da tayi daga jikin ubansu ne. Wani irin duhu da qunci dakin yaji yayi masa,tsahon awa guda da wani abu yana zaune guri daya batare daya ko motsa ba. Sake maida dubansa yayi ga sachet din maganin,ya saka hannu ya daga yana sake karantawa sai yayi jifa dashi wanda kai tsaye ya sauka a bakin qofa. Hannu bibbiyu ya saka ya dafe kansa yana jin yana wani sara masa,yaushe sabreen ta fara sha?,wanne lokaci ta dauka tana sha?,kada ya zamana ta illata mahaifarta fa?. Juyi kawai ya dingayi tsahon awa uku,sai daga bisani a hankali hankalinsa ya dawo gangar jikinsa,ya miqe ya shiga bandaki ya daura alwala. Saman abun sallah ya zauna yana karanta wasu addu'o'i hadi da sunayen Allah,A hankali sai yaji zuciyarsa tana saukowa tunaninsa yana daidaita. Sannu sannu sai komai daya faru tsakaninsu ya dawo masa fes cikin kanshi,wani sashe na zuciyarsa ya dinga masa zafi. Kwanciya yayi niyyar yi kafin ayi kiran sallar asuba,amma sanda ya isa gadon da zummar kwanciya sai maganarta ta fado masa. "Hamma na gaji.....bacci nakeso nayi". A nutse ya sauka daga saman gadon,ya koma saman kujera da nufin kwanciya,nan ma sai yaji ya kasa. Da daya da daya ya dinga sauya guraren kwanciya amma ko ina ya sanya kai sai yaji ya kasa,sannu a hankali ya fahimci zuciyarsa na neman 'yar uwarta ne.....zuciyarsa na neman mahadinta. Duk yadda yaso ga kafewa wajen fita nemanta amma sai zuciyar taqi bashi hadin kai,daga qarshe dai ya fahimci ba wata mafita da yake da ita illa ya fita ya nemo duniyarsa. Yana miqewa ana kiran sallar farko,don haka sai kawai yayi alwala,ya zura riga ya sanya flipp flops dinsa ya murza qofar zai fita a dakin. Farouq ya samu daga bakin qofar dakin "Yauwa dude......dan yiwa adda magana please ta miqo maganin fannah,jiya ta manta maganinta a jakarta duka biyun.....kasan ba'ason fashin shansa" Farouq yayi maganar hankalinsa yana wani gurin bai bada hankali ga fuskar fu'ad ba. Wani irin sanyi jikinsa yayi kaman an watsa masa ruwan qanqara,ya juya gwiwarsa a sabule ya koma dakin ya hada kan magungunan ya bawa farouq. Sanda farouq din ya wuce sai yaji kaman bazai iya sake taku ko guda daya ba,sai a sannan tunaninsa ya dawo,fannah tana shan maganin planning saboda matsala da take da ita a mahaifarta,dole take shan maganin sabida akwai buqatar ta huta sosai tsakanin kowanne ciki. Sam bai kawo hakan a ransa ba,ta yaya ma zaiyi tunanin maganin fannah zai shigo jakar sabreen?. Yana rangaji haka ya dinga takawa har yakai masallacin harami,daidai lokacin da ake dab da tada sallar,yayi raka'atanil fajr yabi jam'i aka tayar da sallar. Koda aka idar zama yayi yayi addu'o'i sosai,yayi istigfari akan zato da kuma yanke hukunci ba tare da bincike ba. Ya jima sannan ya miqe ya fara zagayawa guraren da yasan tafi zama ko zai ganta,amma har ya gama zagayensa ya koma duba guraren da ba wajen zamanta ba baiga koda me kama da ita ba. Zuwa sanda rana ta fito ya gaji sosai,dole ta sanya ya koma masauki. Ya samu yaran duka sun gama shiryawa,kowannensu kuma ummeensa yake da buqatar gani,musamman su fauzan dake jiran fitowarta su duba gifts da suka samu kafin su wuce harami. Baisan amsar da zai basu ba,saidai kawai ya zauna cikinsu ya sadaukar musu da wannan lokacin,amma dai duk da haka hankalinsu yana kan uwarsu. Har azahar shuru bata ba dalilinta,ga anni na nemanta,maamah ma da bata iya magana sosai sau uku tana tambayarsa. Zuwa la'asar hankalinsa ya tashi,don masu neman nata suna qara yawa ne,iffa ma dake da shekaru biyar neman ummenta takeyi bare sauran da suke da hankali. Ya kasa gayawa kowa abinda ya faru,yadai ce musu tana masallacine kawai. Sannu a hankali hankalin anni yakai kai,saboda yaran da suka matsa da qorafin taje ta dade a masallacin. Zaman jiransa sukayi har yaran sukayi bacci bai shigo ba,yana can yana dubata a ciki da wajen masallacin. Bai shigo ba sai daya baza masu duba masa ita,wai ko madeena ta koma daya daga cikin gidajensa?,saidai acan dinma duka daya ne bata koma ba ba wanda yaga gilmawarta. Nigeria ya karkata kiran nasa,tsakanin abuja lagos da kano,can dimma duka daya,don bata je musu ba. "Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Kawai shine abinda ya dinga maimaitawa,a rayuwarsa wannan shine ainihin color din tashin hankali tsurarsa daya taba gani ido bibbiyu. Yana kallon wayarsa na ruri da numbers na anni da maamah,kowacce kiranta yana katsewa na 'yar uwarta yake fadowa,amma ya gaza daga koda yatsansa ne bare ya amsa musu. A jikinsa yake jin bazai iya komawa masauki ba,idan ya koma da anni da maamah da dukka yaran me zaice musu?,sai kawai ya wuce bandaki ya sake alwalarsa ya dawo gaban ka'aba yayi salla raka'a biyu ya sake istigfari sannan ya zauna ya durqushe yana roqon Allah cikin qanqan da kai da neman afuwarsa da agajinsa. *_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽 *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*😂😂 Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*👇🏾👇🏾 wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 _Zafafabiyar_ ̶B̶O̶O̶K ̶2 ⱧɄ₲Ʉ₥₳ 𝙋𝘼𝙂𝙀 177 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _________________________ *_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_* https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1 177 Baisan adadin lokutan daya kwashe a wajen ba,baisan mutun dari nawa ne suka zauna suka kuma tashi ba a wajen. Har zuwa sanda ya soma jin wani siririn sautin kuka daga gabansa. Guri ne da mutane masu damuwa da buqatu kala kala ke zuwa,don haka baiko dago ba yaci gaba da abinda yakeyi,saidai kukan dayaci gaba da tashi ya fusgi hankalinsa don sautin Sabreen yake ji sosai. A hankali ya matsa zuwa gaba,ya kuma daidaita zamansa daidai da inda ta zauna. Jin mutum kusa da ita sosai ya sakata daga kanta,idanunsu suka gauraya dana juna,take kowannensu wani qaqqarfan abu dake riqe da zuciyarsa akan dan uwansa ya motsa. Fatali tayi da abun,ta kuma yi zumbur ta miqe kamar wadda cinnaka ya cijeta,saidai ko gama daidaita batayi saman qafafunta ba shima ya miqe,hakan ya sanyata ta fara hanzarin barin wajen,don tabbas inda tasan zai fito da tsakiyar dare irin haka ita ba zata fito ba. "Sabreen" Ya dinga kiranta da tausashiyar murya sanda suka fita a haramin gudun kada ya janyo hankalin jama'a kansu. Kaman ba zata amsa masa ba........amma wata raunanniyar zuciyar ta gaza jure jin yadda yake jera kiran sunanta da wata irin sassarfa wadda tafi qarfin tata tafiyar,saboda qoqarin tsere masa da takeyi sai data hada da gudu gudu. "Ki dakata sabreen". " Bana buqatarka" Maganar data cake masa a tsakiyar qirjinsa kenan. Bazai iya jure jin sake fitar wata magana haka daga bakinta ba,don haka yayi taku uku qwarara sai gashi a gabanta,baiyi wata wata ba kuma ya dagata cak kaman yadda ya saba yi mata. Ya raina jawota da hannu daya ko dagata kaman yarinya qarama,saita fara wuntsila qafafunta tana magana cikin kuka. "Ka saukeni......bana buqatarka,kace ka daina sona fa.....kai kacemin na tafi.....na tafi kenan bazan dawo ba,kuma nima na daina son......." Ai bai iya bari ta qarasa ba ya manne bakinsa da nata,wanda cikin second kadan qafafunsa suka soma qoqarin kayar dasu saboda wasu irin taurari da suka soma kewaya jininsa. Sauketa yayi ya hadeta da bangon wani gini dake kusa dasu,ya sake lalubar bakinta ya shigar dashi gaba cikin nasa yana aike mata da wani irin zuzzurfan kiss. Hawaye kawai takeyi,ta kasa hanashi,ta kuma kasa tsaidashi,kaman yadda zafin maganganunsa suka kasa cirewa daga kanta. Sai daya galabaitar da ita gaba daya,ya kuma zare duk wani tasirin fushi da yake iya hanga sannan ya zare kansa daga gareta. Hannunta yaja ya zaunar saman wata concrete chair dake wajen shi da ita duka suna sauke numfashi kaman wadanda sukayi tsere. A madadin ya zauna,sai ya zame yana tsaiwa saman gwiwoyinsa. Hannunta ya kamo ya sanya tsakiyar nasa hannun. "Sabrrr" Ya kirata da wani irin taushi daya sanya taji wani sanyi ya sauka tun daga tsakiyar kanta har tafin qafarta. "Sabrrr" Ya sake kiranta wannan karon saita lumshe masa kyawawan idanunta kawai da suka sanyashi yaji kaman ya hadiyeta ya huta "Ki amsamin don Allah.......kice na'am hamma idan baso kike na zauce miki ba". " Hamma" Ta furta tana ware idanunta da suka wani zuge saman fuskarsa. Sosai yaji abun ya sokeshi,me ya shigeshi ne haka jiya?. "Please forgive me my world......forgive me.....am mad duniyata.......i hurt your feelings......ki yafemin......bazai sake faruwa ba,ke na batawa amma ni na karbi hukuncin,'ya'yanki da iyayenki da qannenki dukka sun zuba mini ido ja fiddo musu madame dinsu......in fact ni kaina zuciyata da kanta fushi take dani,don na haramta mata ganinki.....na haramta mata kasancewa dake". Yayi dukka maganar yana dora hannuwanta saitin zuciyarsa dake fama gudu. Hannunsa guda daya ya zame a nata,ya danganashi da saitin ka'aba sannan ya fara magana. "Ni muhammad fu'ad......daga rana irin ta yau nayi alqawarin bazai sake bari hawayen bacin raina ya zuba a idanun ameenatu na ba.....idan har kuma hakan.......". Da wani irin sauri ta zame daga inda take zaune tana riqe dukka hannayensa biyun tana girgiza masa da sauri. "Kada kayi haka......kowanne zaman aure dauke yake da qalubale.....komai dadi kuma wataran sai an bata ran juna......nima ina bata maka rai fa hamma......sau nawa ma......amma saika dinga yi kaman ma ban bata maka ba......kawai abu daya ne banaso ka sake fada don Allah". Ta fadi hawaye yana silmiyo mata,da alama maganan ita daya tayi mata ciwo fiye da sauran komai. Kafin ma yaji abinda zata ce din ya dora kanta saman qirjinsa yana lallashinta "Mene ne?,me na fada sabrrrr?". " Kada ka sake cewa zaka iya rayuwa babu ni......don wallahi ni bazan iya rayuwar da babu kai a cikinta ba". Wani abu me nauyi yaji ya sake sauka saman zuciyarsa game da ita,ya runtse idonsa sannan ya budesu. "Sabrrr" Ya sake kiranta a tausashe. "Na'amm hamma" "Adda na" Ya sake kiranta yana jin kaman ya maida agogo baya ya shafe abinda yayi mata. "Muffin" Ta motsa labbansa tana kiransa da sunan da yafison ji a bakinta sama da kowanne suna "Wallahi Allah mugun maqaryacine ni indai akan wannan ne......zan iya rayuwa babu ke?,ko na daina sonki?,babbar qarya ce wallahi wallahi da babu ta biyunta a duniya". Sam sam ta mance da mode dinta sai wata irin dariya data kwashe da ita. Yayi matuqar bata dariya yadda ya taqarqare yake siffanta kansa da siffar da tasan yafi tsana guda uku a rayuwarsa. QARYA YAUDARA DA HA'INCI. "Mijina ba maqaryaci bane......ban taba ganin mutum me gaskiya irinsa ba........a shekara goma sha shida ban taba tuna wata tana daya batamin rai ba koda sau daya kuwa.....don me bazan masa shaida ta cikakken adali ba?,tabbas dana zama cikakkiyar butulu kuwa idan na tuhumeshi akan wannan laifin qwaya daya". Dagata yayi cikin jin alfahari da ita,ya kalli fuskarta sosai ya sumbaci goshinta. "Allah yasa ke matatace har a aljannah". "Haka nake fata ka zama mijina har aljanna.......amma akwai albishi daya" Ta fada tana murmushi. "Wanne kenan?" Ya fada yana dubanta cikin zaquwa. "Allah karimi ne me karamcin da babu irinsa kaf a halittun duniya.......Allah me boye baiwarsa ne ga bayinsa duk yadda yaso yayi hakanne zai faru.......bayan na fito sanda gari ya waye jiri ya daukeni,daga haram suka kaini asibiti don na huta,sunyimin gwaji abun mamaki sun tarar da cikin da ake rigima a kansa a jikina......kasan watansa nawa hamma?" Ta qarasa fada a mugun sanyaye tana aza hannunsa saman cikinta. Kai ya girgiza yana jinsa kaman a duniyar mafarki. "Wata uku hamma amma dukanmu bamu sani ba.....dama haka yana faruwa?" Wani irin rauni ya kamashi,ya daga tafin hannunta ya sanya saman bakinta wai yana qoqarin controlling farincikinsa kada murna tasa ya furta abinda bai dace ya fada ba. Sai bayan wasu wasu sakanni ya iya magana da muryarsa me rawa. "Yana iya faruwa saboda haka Allah yaso ya kasance.......astgafirullah......Allah ka yafemin bisa gaggawa da shishshigin da na yiwa lamarinka......tashi na maidaki cikin ahalinki don basu da wata madadinki" Ya fada yana dagata zuwa jikinsa gaba daya. "Da alama su suka sanya sabrrrr dina me ma'anar sunan haquri ta zama mafadaciyar qarfi da yaji?" Kunya ta kamata,ta shige jikinsa sosai yana boye fuskarta,ga kunyar albishir din da takeson yi masa. "Hamma two embrayos........ina fata su zama dukka baby girls,abinda na zauna na yita roqa maka kenan......sunan waye da waye zaka saka?". " Sunan maamah.......da kuma nagartacciyar surukar data haifamin wannan DUNIYAR TAWA" Ya qarasa fada yana matse hancinta me kyau. Dariya ta saki har fararen haqoranta suna bayyana,tana wassafa kuma irin soyayyar da yarinyar me sunan umminta zata samu daga gareta. "Godiya ga Allah daya bani DUNIYATA na haqiqa......ya fiddani daga wancan DUNIYAR me cike da rudani" Tayi maganar ne a zuci batasan ta fito ba har sai da suka hada idanu ya kashe mata ido daya,kunya ta sakata cusa kanta cikin qirjinsa tana boye fuskarta gami da shaqo tattausan qamshin nan nasa daya mata wani irin dadi kaman bata taba jin qamshin ba sai ranar,da alama za'a fafata kenan,da alama kuma wannan cikin meson zuminci da babansa ne,don dama tanata mamakin yadda cikin watannin ta sake zama very addicted da lamarin. *_Tammat bi hamdillah_* *_Alhamdulillah alhamdulillah,Allahumma lakal hamdu fil ula wal Aakhira_* *_lallai a rayuwa komai yayi farko yana da qarshe,doguwar tafiya me cike da tarin qalubale masu dadi da sauqi dalilin SUPPORT NA MASOYA_* *_sau tari wata rayuwa na zame maka mabudin alkhairan da bakayi zato ba🥰_* *_sau tari wasu dalilan ma zame maka falala me tarin yawa cikin hikimar gwani na gwanaye wajen iya tsara rayuwa da dukkan hukuncinsa da iyawarsa_* *_wata DOGUWAR TAFIYA da inajin bamu taba irinta ba😄,wadda a zahiri bazai yuwi nayi shuru ban yaba muku ba ku kanku_* *_kunyi yawan da bansan wasu bama a cikinku......masoyan da suka dora dambar bibiyar SAFIYYA HUGUMA badon tafi kowa ba.....ba kuma don tafi kowa iyawa ba,sai don saboda soyayya da qauna data zama SILA_* *_INA MUKU FATAN ALKHAIRI DA DUKKA FURUCIN BAKINA......INA FATAN ALLAH YA SAKE SADAMU A TAFIYA ME DADI IRIN WANNAN CIKIN QOSHIN LAFIYA AMINCI QAUNAR JUNA DA SUPPORTING JUNA_* *_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU A DUK INDA KUKE AREWABOOKS FOLLOWERS_* *_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU 'YAN WHATSAPP.....INA FATAN ALLAH YA AMINTAR DA KOWANNENKU YA YALWATA ARZIQINSA DON ALFARMAR SHUGANA S A W_* *_NAJI DADIN WANNAN TAFIYA MATUQA,NA SAMU SUPPORT DA SHINE QASHIN BAYAN NASARATA A WANNAN TAFIYA DAGA GURIN MABANBANTAN MUTANE,UBANGIJIN AL'ARSHI YA DAFA MANA GABA DAYA_* *_AMANA/GASKIYA/ADALCI/DATTAKO/KAWAICI SUNE TUSHEN KOWACCE NASARA_* *Darasin DUNIYATA* *_KOWACCE RAYUWA AKWAI NATA KALAR QALUBALEN,BA KOWANNE MUTUM BANE ZAKA GANI CIKIN INUWAR DUKIYA KA DAUKA SHIKAM BAIDA MATSALA BA,BA KOWANNE MUTUM ZAKA HANGA KA DAUKA YA SAMU DUKKAN WATA WATA NI'IMA TA RAYUWA BA_* *_KAYI RAYUWA IYA MATSAYINKA......KADA KAYI MIQAR DA ZATA WUCE TSAHONKA,DUK GAGGAWARKA RABONKA SHINE NAKA,BA ZAKA TABA CIN RABON WANI BA_* *_BAWA BAI ISA YA YIWA KANSA ARZIQI BA,SAI ABINDA BUWAYI GAGARA MISALI YA HUKUNTA MAKA_* *_KE UWA!.....BAKI DA KAMAR 'YA'YANKI.....SUNE RAYUWARKI.....KIYI AURE AMMA KARKI YADDA KI FIFITA KOMAI NAKI SAMA DA TARBIYYARSU DA KUMA RAYUWARSU_* *_AIKATA ALKHAIRI KA WUCE ABINKA KA BARSHI AGUN,ZAI CIMMAKA WATAN WATARANA.....KAMAN YADDA IN KAYI SHARRI HAKA WATARAN ZAI DAWO MAKA_* _Kusakurai da aka samu a ciki da abinda bai kammalu ba ayimin haquri,na rubutu matuqa har naji rubutu ya ginsheni😂😂😂_ _wanda na batawa ya yafen,na yafi kowa,kuskuren ciki ubangiji yayi afuwa,ya tattaramu a ladan,ya bamu ikon daukan me kyau a labarin mu watsar da shirme_ Every conclusion sparks a new inception Nothing lasts forever Every dawn has a dusk Ending are part of beginnings in sha Allah _subhanakallahumma wabi hamdika ashahadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika_ _Allahumma salli wa sallim ana nabiyyurrahmati_ S A W 08187255862