GUDUN AURE
GUDUN AURE!
NA
BINTA UMAR ABBALE 🍒
M.W.A✍️
GODIYA!
Yabo da godiya su tabbata ga Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah suka kara ninkuwa ga shugaba Annabi Muhammadu s.a.w. Wannan littafi mai suna a sama ‘kirkirarre ne, ba a yi shi don wani ko wata ba, idan har ya yi daidai da yanayi na rayuwaka/ki a rashi ne. Haka zalika ban yarda a juya mini labarin littafin nan ta kowace siga ba. Yin hakan ba tare da neman izini ba ka iya kai mu ga hukuma a kiyaye!
Ina mik’a godiyata ga kafatanin masoyana a duk inda suke ina mutukar godiya tare da fatan alheri, ina fatan kuma wannan karon ma za ku kasance da ni a cikin wannan littafi mai suna gudun aure. Kamar yadda tsarin yake book1 zai zo muku kyauta anan Whatsapp yayin da book 2_3_4 zai zo a matsayin paid a manhajar talgram da arewa, ina burin samun goyon baya daga gare ku bakid’aya. Ga masu karatu a arewa books za su iya garzayawa can domin na yi nisa a can din.
Godiya da fatan alheri.
Fatima Musa nijar
Usaina abdulmalik kaita
Hairi
Aisha Aliyu
Munnira
Amina
Fadima sani
Prof Asabe
Sakina Mahmud
Zainab Yola
Amra
Fatima Gwaram
Giwar sarkin Sudan
Maimuna ramalan.
Shafin farko kyauta ne ga Jamila Adam namaska Hajjaju Ina godiya sosai.🥰💯
Book1
KANO STATE
‘KOFAR KABUGA
1
Sunana Amina Malam Salisu wanda ake kira da (Mai wankin hula) Ni tela ce k’wararriya sannan kuma malamar makarantar boko ce ta gomnati. Ina koyar da Yara harshen hausa a firamare ta gwale local goment. Bazawara ce ni a yanzu mai yara biyu dukaninsu maza. Babban sunansa Kamalu sai d’an’uwansa Yusuf wanda muke kiransa da Yusi. Mahaifinsu ya rasu shekaru hud’u da suka gabata tun lokacin Yusi din yana da shekaru bakwai a duniya. Tazarar da take tsakaninsa da d’an’uwansa Kamalu ta shekara daya ce. Ni da Babansu Allah ya jikansa da rahama muna hasashen daga yin arb’anin din haihuwar Kamalun ne na yi katari da cikin Yusuf din. Tsiran da yake tsakaninsu dai bashi da wani yawa. Yanzu Kamalu yana da shekara goma sha biyu, yayin da Yusi yake da goma sha d’aya.
Tun bayan rasuwar Yaya Aminu mahaifin yarana na koma gidanmu da zama domin dama gidan da muke zaune dashi na haya ne kasancewar akwai rashin ‘karfi da rashin ‘kwa’kkwarar sana’a daga ‘bangaransa. Cikin ikon Allah sai aka yi sa’a d’akin da muka yi ‘yan matanci ni da ‘yan’uwana yana nan sai dai shirgi da matan gidan suke ajiyewa. Anan na ra’kube da ‘yan kayana na zauna nake gurgura rayuwar kafin mu ga hukuncin da Allah zai zartar.
Zamantakewatar auran da muka yi ni da Yaya Aminu na tsayin shekara goma sha uku kusan ni ce ‘karfin gidan saboda Allah ya ri’ka mini Ina aiki, sannan ina d’inkin mata da ‘yan gyare-gyare, bayan haka kuma ana kawo mini aikatau na jaka ‘yar pose da huluna irin na yadin hijabai. Sosai Allah ya huwace mini. Duk wata zan d’auki albashi sana’ar d’inkin da nake yi kuma tana taimaka mana sosai har mu iske sabon wata ba mu galabaita ba.
Ban ta’ba yin nadama ko na ji wani abu na ‘kyashi a raina ba a duk lokacin da Ya Aminu zai nemi wani abu a wurina muddin ina dashi babu jayya ko gardama nake d’auka na bashi. Babban burina ace asirinmu ya rufu gabad’aya, kuma dama tun lokacin da muka yi aure na yi alkawari cewa ‘In dai Allah ya ri’ka mini sai Ya Aminu ya fi karfin komai a wurina, sakamakon irin hallacin da ya yi mini a rayuwata.
Duk da cewa albashina bashi da wani yawa kasancewar firamare nake koyarwa, amma ana yin salary nake ware masa kudin transport, tun bayan korarsa da aka yi a kamfanin da yake aiki sakamakon tashin ciwonsa, to sai ya koma kasuwa yake buge-buge. Dalilin da ya sanya kenan Ina kar’bar albashina nake ware masa
wanda za su ishe shi zurga-zurga a wata saboda lalurarsa tunda bashi da abin hawa kuma daga unguwarmu zuwa kasuwar da yake hurd’odinsa akwai akwai nisa sosai.
Ni da Gwaggwo mahaifiyarsa ba mu ta’ba sanin yana da wani ciwo ba sai da kawo shi ranga ranga daga wurin aiki tukkuna likita ya tabbatar mana da cewa yana da matsananciyar asma bayan ita ma har da sanyi wato limoniya sune suka tayar masa sakamakon yawan shiga ruwa da yake yi, da kuma shakar iskar asubahi. Tunda ana idar da sallah yake fita kuma a ‘kafa yake tafiya dalili kamfanin babu nisa a tsakaninmu, bayan haka kuma Yana da matsalar k’afa guda d’aya a dogare take dunduniyar bata taka k’asa. Likitan ya tabbatar mana da cewa
iskar da yake sha’ka da tafiyar da yake yi mai tsanani duk sune suka had’u suka tayar masa da ciwon.
Sai sannan Gwaggo ta tuna a lokacin da yana yaro ya ta’ba yin irin haka da ‘kyar aka shawo kan matsalar. Tun daga sannan ni dashi muke kaffa-kaffa. Ko fita ya yi ya manta da inhele sai ya dawo ya d’auka. Ni ma kuma kafin ya fitan na kan tuna masa sai ya d’auka ya sa a aljihunsa ya tafi.
Tunda aka sallame shi daga aiki. Muke kame-kame, taimakon da Allah ya yi mini ina da hanyar samu da ban san ya za mu yi ba. Takaici da bakinciki ya hana shi sakat kullum idan muka zauna maganarsa Alhaji Tajo bai yi masa adalci ba. Ya sallame shi babu uzuri, sannan bai bashi komai ba duk irin wahalar da ya yi masa. Ni kaina sheda ce Yaya Aminu ya bautatawa mutumin sosai. Amma bai duba hakan ba. Na dinga ‘karfafa masa gwiwa akan ya yi hak’uri ya cire damuwar hakan a cikin ransa. Idan ni ce ba zan ta’ba d’aga masa hankali ba, da dadi babu dadi zan zauna dashi. kuma ya je kasuwa ya nemi arziki, Allah ne mai bayarwa. Kalamaina suna ‘kara masa karfin guiwa a lokacin zai shirya ya fita duk da bai san inda zai nufa ba amma zan ta ‘karfafa masa guiwa. Wasu lukutan ya dawo da d’an abin sarrafawa, wasu lukutan kuma ya dawo sannu rabbana da kukan k’afafunsa na yi masa ciwo.
Tashin ciwonsa na biyu shi ya kasance ajalinsa ya kwanta jinya a gida da tunani da takaicin abubuwa da yawa, domin har zuwa lokacin bai manta da wula’kancin da akayi masa ba. Da ba’kincikin Alhaji Tajo Yaya Aminu ya koma ga Ubangijinsa.
Komawa ta gidanmu da zummar yin zawarci sai abubuwa suka ru’banya rinca’bewa. Kuncin dana riska na yanzu ya fi na baya inda Allah Ya taimakeni ina da abin yi sai na samu sassauci ta nan ‘bangaran. Amma dai dukda haka wataran idan masifar ta ishe ni ‘kunshe kaina nake yi a d’aki na ci kukana na ‘koshi. Wata zuciyar ta dinga raya mini kawai na sanya dilallai su cigita mini gidan haya wanda ba zai gaza dubu hamshin ba a shekara na san tunda ba’a zaune nake ba Allah zai agaza mini, saboda wata masifar Kamalu ne yake janyo mini ita, yaron bashi da ha’kuri kamar d’an’uwansa gashi dai shine babba,amma kullum kuka ake yi dashi a gidan. Ya yi ta tsokanar yaran jama’a dana ma’kota Ya ci zalin wanda ya fi karfi. Iyayensu su fito su yi zage-zage da gore-gore. Da barazanar sanar da maigidan Babanmu akan ya tursasani mayar dasu dangin Babansu.
A wancan zaman na baya na fuskanci uk’uba ba da ‘kunci na garari. Farko na rashin uwa majinginta. Na biyu kuma yadda na zama ‘yartsakargida wula’kantacciya wadda ba ta da ‘yanci kamar sauran ‘yan’uwanta. Na uku jarabbawar da Ubangiji ya yi mini a lokacin mun taso mu biyar duk ‘Yan mata amma gabad’aya sai da aka aurar dasu ni ina zaune babu ma wanda yake sansanta. Sai da kaddara ta gifta tukkuna Yaya Aminu ya nuna sha’awar aurena muddin ina sonsa tunda dai shi ga yadda Allah Ya hallice shi.
WANNAN KENAN.
Kasancewar na raba dare ina yanka din’kunan mutane da suka jima a hannuna ban samu sukunin dinka musu ba sai da aka yi wa yara hutun makaranta tukkuna. Dalilin da ya assasa mini bacci mai nauyi kenan da k’yar na tashi na gabatar da sallar asubahi. Na tashi yarana sai da na tabbatar sun fita zuwa massalaci tukkuna na koma na kwanta baccin dai ya ‘kara surata. Sai na ji sautin kukan Yusi a cikin kunnuwana na bud’e idona da saurin gaske na tashi zaune sai na ganshi a ra’kube a jikin bango. Saminu ‘kanina da muka had’a Uba d’aya dashi da tsintsiyar kwakwa a hannunsaa yana shaud’a masa.
Da sauri na fizge ina fad’in.” Kai akan me ka ke dukansa, me ya yi maka?”
Ya ce.” Kashi ya yi a bakin masai.
Cike da b’acin rai na ce.” Saboda ya yi kashi a bakin masai sai ka dake shi Ina ce kai ma kana yi, ko kai kake wanke bandakin ne?” Cikin rashin kunya ya ce.” Ai bayan haka ma d’azu kina bacci Kamalu ya tsinkawa Ashiru mari, babu abinda aka ya yi masa, shine nake ramawa a kan ‘kaninsa ni ma.”
Cikin takaici na ce.” Dallah fita ka ba ni wuri shashasha kawai.” Ya kama hanyar fita yana
wa’ke-wa’ke.
Na girgiza kai tare da mayar da hankalina kan yaron na ce.” Yusi ban ce idan za ku hau masai ku dinga nutsuwa ba?”
“Mama matso ni ya yi. Kuma Saminu ne a cikin bandakin da yaga ina jin kashin sai ya’ki fitowa daga band’akin, yana leko ni yana yi mini dariya. Na fadawa Ummansu ta yi mini banza. Sai da Yaya Usaini ya yi masa magana sannan ya fito na shiga ban san na yi bakin masai ba.”
“Yanzu ina Kamalun yake?”
“Ya d’auki kudi a jakarki ya tafi sayo kunu da awara.”
Na kalli agogon da yake bangon d’akin, takwas saura mini goma. Na ce.” To tunda an yi hutun boko sai ku yi shirin allo idan kun karya ba zan iya cecekuce da rabon fad’a ba.”
Ya ce.” To Mama.” Kamalu ya shigo da jug din kunu da awara a bakar leda Yana cewa.” Mama na d’auki dari biyar a jakarki na sayo awara ta d’ari uku kunun dari biyu, yanzu darin sukari za ki bayar.”
Na ce.” Kamalu kai kullum burinka ka janyo mini magana ko? kullum sai na zaunar da kai na yi maka fad’a, amma magana tana shiga ta kunnan dama ta fita ta kunnan hagu ko? Ba za ka ri’ke maraicinka ba Kamalu abinda kake yi fa shi d’an’uwanka zai kwaikwaya, ba za ka barni na ji da abu daya ba sai ka jefa mini damuwa da zullumi a cikin raina ko Kamalu.”
Ya zauna jiki a sanyaye ya ce.” Mama don Allah ki yi hakuri kin ji, ba zan kara ba.”
Na ce.” Haka kullum kake fad’i Kamalu amma kana fita zaka sanya kafa ka shure maganata, me yasa kake dukan yaran mutane kana d’auko mini magana, bakin jama’a a kanka, kowa Kamalu kowa Kamalu, so kake yi baki ya kamaka ko?”
“Mama ki yi hakuri ba zan sake ba.”
Girgiza kaina kawai na yi cikin zuciyata nake masa addu’ar shirya. Na ce.” Ka je ka zuba mini ruwa a buta zan wanke bakina.”
Da sauri ya tashi ya d’auki buta ya fita. Sai gashi ya dawo yana cewa.”Mama sun d’auke gugansu. Na tambayi Ummansu Saminu ta ba mu aro wai ba zata bayar ba tunda kina sana’a ki saya mana.”
Kaina ne ya d’aure da jin maganar. Na ce.” Umman Saminu ce din ta fadi haka?”
Ya ce.” E, wallahi.” Ban yarda ba sai na tashi na fita da kaina na tsaya a bakin kofar dakinta na ce.”Umma ina kwana?” Tana rabawa Yara karin kummalo ta amsa a dakile.
Na ce.” Guga za ki d’an ban aro zan ja ruwa.”
“Amina ki sayi guganki don Allah, kullum sai kin ara, bayan Allah ya hore miki, kada ki ce za ki yi gadara domin ba babanku ne ya saya ba, kowa da kud’inta ta saya. Yawan jan ruwan da Kamalu yake yi miki, duk gugana ya fatattake.”
Kafin na ce wani abu. Ummansu Hadiza ta le’ko tana cewa.” Kin ga zo ki d’auki nawa ki yi abinda za ki yi gugan me da har za ki tsaya ana yi miki gori akansa.”
Hakan sai ya fusata Ummansu Saminu. Kamar dama kiris take jira, ta fito tsakar gidan tana cewa.” Aikin banza da wofi. Murja sai yanzu ne za ki nuna mata k’auna waye bai san irin jifan da ki ke yi mata ba. Ba zan bayar da gugan ba, tunda ba ubanta ne ya saya ba.”
Ni dai ban ce komai ba na je na d’auki gugan na wuce bakin rijiya ina jin su suna ta masayar yawu. Na kud’ire a raina idan na fita kasuwa sayo kayan d’inki zan tsaya na siyo gugana da duk abinda na san za a yi mini gori akansa.
Babanmu ya fito daga d’akinsa da shirin fita hannunsa da hulunun mutane da yawa. Ya tsaya yana tambayar ba’asin hayaniyar da suke yi. Babu wadda ta ba shi amsa a cikinsu. Kamalu ya ce.” Saboda gugan jan ruwa ne, Ummansu Saminu ta c… Na daka masa tsawa sai ya yi shiru yana kallona. Na ce.” Wuce ka je ka d’auko mini d’an bokitin nan.”
Ya bar wurin da sauri. Na dan risina a lokacin da ya kusa karasowa bakin rijiyar da niyyar fita. Na ce.” Baba ina kwana”
Ya amsa ya dan tsaya yana kallona kafin ya ce.” Ko zan sami dari biyar a wurinki Amina yau haka na wayi gari babu ko kwabo, wad’annan matan kuma suna nema su tona mini asiri da sanyi safiyar nan.”
Na ce.” Ina da ita Baba.” Sai ya ce.” To ki aiko Kamalu ya kawo mini, zan aike shi ya sayo mini shayi.”
Na ce.” Baba don Allah ka rage cin borodin nan kwanan nan fa ka tashi daga lalura basir ne da kai mai muni.”
Ya ce.” Ai kad’an nake ci, kuma shayin tsura nake sha ba madara.
Na ce.” Dukda haka dai Baba, hanyar lafiya a bita da shekara.”
“Amina abinda ya tashi basir din nan fa zama ne, da kuma cin rogo da gyad’a dana dimanta amma zan kiyaye dai.”
Ya kama hanya ya fita yana gyara tarin hulun nan da suke hannunsa. Sai da na cika butocina da babban bokitina mai murfi sannan na mi’ka mata guganta.
Muna karyawa na ce.” Wallahi Kamalu duk lokacin da ake hatsaniya a gidan nan na ji ka kara sanya bakinka sai na sanya an zane mini kai, kaine mai bakin magana ko?”
Shiru ya yi. Na k’araci yi masa fada bai ce uffan ba.
Na kunna kurfoti na d’ora musu ruwan wanka suka yi suka tafi makaranta.
Na had’a wankinmu da ya taru, na sanya sabulu a ciki na daure. Sannan na juye ruwan dana dora na je na yi wanka a gurguje na shirya da zan fita na yi musu sallama. Kafin na wuce kasuwar sai da na tsaya a shagon Babanmu na bashi dubu daya kamar yadda na yi masa alkawari kafin ya fita.
Da ya tambayeni Ina zan je na ce.” Kasuwa zan je na sayo kayan d’inki.
To da yake motar sabon gari bata wahala ina fita titi na samu. Sai dai gosolw da ya ri’ke mu a hanya daidai sabon titi gidan ‘kankara.
Na rasa cunkuson menene direban da yake jan mu ya ce.” Rasuwa akayi nan cikin Sani mainagge shine Alhaji Tajo ya zo gaisuwa wad’annan zungura-zunguran motacinsa ne da jama’arsa.”
Na ce.” Na d’auka ai dan kasuwa ne ba ‘dan siyasa ba ne.”
Ya ce.” E, d’an kasuwa ne sosai, ai ba sai lallai d’an siyasa za a yi wa wannan cunkoson ba. Shi ma babban mutum ne a garin nan.”
Na girgiza kaina. Ban yi mamaki ba tunda sananne ne. Akwai d’aruruwan mutane dake ‘kar’kashinsa. Bayan haka ma har kalandarsa na ta’ba kafewa a d’akina a lokacin da Abbansu Yusi ya yi aiki a kamfaninsa na sarrafa robobi. Kafin ya sanya soke sunansa daga jerin ma’aikatansa…
✍️
Garkuwar mata Bintuumarabbale
[11/11, 7:38 PM] Aunty B: GUDUN AURE!
NA
BINTA UMAR ABBALE 🍒
M.W.A
Marubuciyar
Yar bangar siyasa
Ba’aboren namiji
Madadi
Ga irinta nan
Goje
Babban yaro
Sadauki Omar
Nida Yaya sadam
Da sauransu..!
@Arewa Books
Bintuumarabbale
2
Matar da take zaune a kusa da ni ta ce.” Kai gaskiya ban yarda ba domin kuwa wannan bawan Allan ya ma fi wani dan siyasar. Yadda yake taimakon jama’a shi zai nuna maka cewa adali ne yana kuma da tausayi, tabbas da zai fito takara ina ganin zai iya lashewa muddin jama’a sun san ciwon kan su to shi zasu dangwalwa kuri’arsu. Ni dai ko yanzu ya fito takara shi zan za’ba.”
Cike da karsashinta tare da kwarin guiwa ta dire maganarta. Yadda ta ha’kik’ance take bayar da sheda akansa shi yake nuni da cewa lallai akwai abinda ya ta’ba yi mata a rayuwa ko wani da ya danganceta.
Tunanina ya katse a lokacin da na ji direban namu shi ma yana ce wa.” Gaskiya ni ma ‘kuri’ata tasa ce, domin yayyuna biyu a kafamninsa suke aiki, sun yi gida, sun yi aure kuma suna ri’ke da iyalinsa. Ko yau zai sallameka daga aiki zai baka kudin da za su isheka jari domin yin wata sana’ar, ai mutumin kirki ne mai dattako wallahi.”
Na ce” Ban tari numfashinka ba, irin wad’annan mutanan fa suna zama da mutum ne idan sun ga zasu amfanu. Babu yadda za a yi ku ce lallai ya cika cif kowane d’an adam za ku same shi da da aikata wasu kusakuran. Ni dai wallahi duk inda za a je ba zan bayar da sheda a kansa ba. Domin ni ma mijina ya yi aiki a kamfaninsa na robobi kafin rasuwarsa, kuma daidai gwargwado ya yi masa bauta. Amma tashi d’aya ya sallame shi bai duba uzuri da lalurarsa ba. Kuma bai bashi komai ba.”
Matar da take kusa da ni ta kalleni tana fad’in.” Anya kuwa, gaskiya ban yarda da maganarki ba, mutumin nan adali ne, sai dai idan mak’arkashiya aka yi wa mijinki a kamfanin, amma zahiri daidai gwargwado yana yi wa ma’aikatasa hidima.”
Na ce.” To ko annabawan Allah suna kuskure ballanatana mutum, ba wai na ce dole ku yarda ba ne, ni ma kuma babu lallai na aminta da hasashenku akansa ba domin lokacin da aka bawa maigidana takardar sallama mun shiga tashin hankali sosai, shiyasa duk lokacin da na ji sunansa sai gabana ya yanke ya fad’i wallahi.”
Direban ya dinga dariya yana ce wa.” Lallai hajiya kenan ko da zai fito takara ba za ki zabe shi ba?”
Kai tsaye na ce.” Babu lallai gaskiya.”
Har goslow din ya tsaigaita muna jayayya suna fad’in ra’ayinsu akan mutumin ni ma ina fad’in ra’ayina akansa. Direban dai in banda dariya babu abinda yake yi mana ganin yadda ni da matar dake kusa da ni fad’a ya kusa ya kaurewa sai ita ta gaji ta yi mini shiru, fad’i yake “Hajiya za ki yi kyau da aikin jarida na lura ba a kada ke a magana, ko dai ‘yar siyasar ce ke me.” Na ce.” A a ban ta’ba sha’awar siyasa ba, asalima ni malamar makaranta ce. Ya ce.” Haba koda na ji shiyasa duk maganganunki suke fita cikin azanci da hikima. To Ubangiji Allah dai ya yi mana za’bi nagari.” Gabad’aya muka amsa da ‘Amin.”
**
Cikin kasuwar sabon gari nake kutsawa na sayo kayan dinki cikin sau’ki da rahusa. Shiyasa nake rufe fuskata da nikabi gudun had’uwa da idon sani, wasu mutanan basu da gadonka amma suna da gadon magana akanka. Na kammala duk abinda zan saya da ya danganci sana’ata. Na fito bakin kasuwar na sayi kayan miya na k’arasa ‘yan kura na sayi kifi d’anye da sauran abubuwan buk’atata.
Na tari shatar adaidaita sahu muka tsadance zai kai ni har kofar gidanmu dake kofar kabuga d’ari takwas. Ya taimaka mini wurin sanya kayan a babur din. Na shiga na zauna babu jayayya domin na san ya yi mini adalci sosai a yadda mai yake tsadar nan wani ma zai iya cewa sai na bashi dubu daya da d’ari biyar.
Gidan namu a bushe da alama Babanmu bai yo aiken kudin cefane ba, tunda sau tari sai ya fita abinda ya samu zai aiko musu su sarrafa. Kowacce tana dakinta. Yara kuma sun fita. Na bude dakina na shiga na zube kayan a gefe. Na cire nikab da hijabi na zauna ina mayar da numfashi.
Yusi ya shigo a guje ya zube a jikina Yana dariya.
“Mama mai ki ke sayo mini?” Tambayar da ya yi mini kenan. Na ce.” Ina Kamalu yake? Ya zo ya d’auki wankin nan ya kai wa Halima tun jiya na fad’a mata zan kawo mata wanki.”
Ya ce.” Muna tashi daga makaranta shi da Saminu suka d’auki buhu.”
“Suka d’auki buhu suka je ina?”
Ya ce.” Tsince-tsince suke yi a bola su kai kangon Jadda ya basu kudi.”
Raina ya ‘baci ainun! Na ce.” Yusi kada ka yi mini karya ka fad’a mini gaskiya tun yaushe suka fara jari bola.”
Ya ce.” Ni dai na gansu kusan sau uku, ni ma na ce zan bi su, Saminu ya koro ni gida.”
Sai kawai na ji idona ya ciko da ruwan hawaye. Wato duk ko’karin da nake yi akan tarbiyar yarana Saminu sai ya rugaza mini. Ba na son yawon nan da suke yi lungu-lungu. Abin har ya kai su d’auki buhu su hau bola suna suna tsince-tsince bayan duk rintsi ana basu abinci . Na tashi na nufi wurin Ummansu Saminu domin na ji shin ta san abinda yake faruwa.
Tana kwance a tsakiyar rumfa da mafici a hannunta. Ta tashi zaune tana cewa.” Na sani wallahi, to ya zan yi Amina, ai sana’a ce, muddin ba za su d’auko abin wani ba to ki kyale su kawai, yanzu fa rayuwar sai an hadu karfi da karfe iyaye da Yara an taimaki juna, sabulun wanki kad’ai ma ya ishe shi bawa, to balle ma duk ba wannan ake yi wa ba, abinda za a ci shi ake fafutuka.”
Na ce.” Ban ‘ki maganarki ba Umma, amma ki yi nazari sosai akan hanyar da yaran nan suka d’auko, ban ce jari bola ba sana’a ba ce, amma ni wallahi a yanzu na fi buk’atar yaran nan su yi karatu, tunda daidai gwargwado ana yi musu hidima, basu rasa komai ba, to me zai sanya su dinga yawo da buhu suna hawa kan bola daga haka fa ba fata nake yi ba idan suka ga abin amfani su sai su d’auka su je su sayar kin ga wa gari ya waya.”
Ta ce.” To ni babu yadda zan yi Amina. Yaron nan Saminu ya kan taimaka mini idan ya yi buga-bugarsa. Kin fi kowa sanin yadda rayuwar gidan nan take, wataran a baka wataran ace ba a samu ba. Kuma ko an baka ba za a baka wanda zai isheka ba. Ba ni da jarin yin sana’a balle ki ce. Amma duk ranar da Saminu ya fita gwangwan muna ragewa gaskiya kin ga yanzu sha biyu da rabi amma har yanzu babanku bai aiko ba, Yara kuma ba su san babu ba, lokacin cin abinci Yana yi za su fara kuka.”
Gabad’aya maganunta suka kashe mini jiki. Na ja k’afafuna da suka sage na bar bakin kofar dakinta.
Na jima Ina tunanin hanyar da zan bi gurin ganin na janye Kamalu daga tarayya da Saminu kaina ya kulle gabad’aya. Babu yadda za a yi su rabu tunda suna kwana a gida daya. Saminu ya girmi Kamalu da shekara uku. Amma a haka suke cud’anya da gwagwarmaya tunda shi Kamalu duk abokanansa yawanci sun girme shi daga na makarantar har na cikin unguwar. Duk wani yun’kuri da zan yi a yanzu dan ganin na datse ala’kar dake tsakaninsu za a yi mini wata fassara ne. Ni kuma akwai dalilin da ya sanya bana son tarayyarsu. Ban dai ta’ba gani da idona ba, kuma bai ta’ba yi mini ba,
amma a unguwar ana rad’e rad’in yaron yana d’auke-d’auke, idan kayi wasarare da abinka sai ya d’auka. Wasu lukutan ma yakan yi wa uwarsa ta kulle shi a d’aki ta yi ta duka.
Ina jin tsoron yau da gobe mu’amularsu ta canza mini yaro. Tunda Kamalu ko nawa zan ajiye a gabansa ba zai d’auka ba. Yana bud’e jakata ya d’auki kudi idan ina bacci ya dawo da canjin ya ajiye mini, idan na duba kudina na gansu cif a yadda suke. Wannan dalilan ya sanya na ke fargabar abotarsu.
Da yake idan na d’auki albashi abinci nake saya da d’an yawa. Dan sai na auno shinkafa kwano biyar na sayo ‘karamin buhun taliya na auno garin towo. Da su mangyad’a da manja da hadin maggi. Da har buhun gawayi nake jinginewa, yau da gobe ta sanya na daina saboda idan na sa ‘kafa na fita aiki sai na dawo naga an kwashe mini gawayin. Ba damar kuma na tambaya. Sai su ce na ‘kala mu sata. Sai na daina sayan buhu nake aikawa gidan Mairo a sayo mini.
Dana gama abinci na zubawa Ashiru tunda shine k’arami a dakinsu. Ita kuma Ummansu Hadiza bata da k’ananun yara duk sun girma tunda itace uwargida. Amma dai dukda haka ina zuba mata itama.
To sai wajan biyu da rabi Babanmu ya Aiko musu da kudin abinci sannan Kowacce ta fara fafutukar abinda zata girka har zuwa lokacin Kamalu da Saminu Basu dawo ba. Raina ya baci ainun! domin lokacin makarantar allo ya kusa, ni kuma a rayuwata na tsani wasa da karatu ganin kamar shine gatan da za ka yi wa yaro, bayan haka kuma ni ma a yanzu karatun ne yake ri’ke da ni bayan d’inkin da nake yi….
Uku saura suka shigo gidan a firgice duk’un-du’kun ‘kafafuwa da hannuwansu duk daud’a. Saminu ya yi d’akinsu da kud’i a hannunsa. Shi kuma ganina a bakin rijiya ina jan ruwa ya tsaya. Na kalleshi sama da k’asa kafin na ce.” Daga ina kuke?”
Ya yi shiru bai ba ni amsa ba.
Saminu ya fito ya na cewa.” Kai Kamalu ungo kudinka.” Ya kar’ba da sauri yana fad’in.” To ya na ga ka ba ni dari uku da hamsin, bayan gabad’aya abinda aka sayi kayan dubu daya da dari bakwai ne.”
“E, Ummanmu ce tace mu bata aron kud’in. Zan cika maka sauran tunda tace gobe za ta bayar.”
Cikin takaici na ce.” Saminu yawon tsince tsince a bola kuke yi ko?”
“E, ai ni, na kwana biyu ina yi, shine Kamalu shi ma ya ce zai dinga bina. Idan mun samo k’arafuna sai mu kai kangon Adahama ya saya.” Hankalinsa a kwance ya ba ni amsa.
Na girgiza kaina ban sake cewa komai ba, na d’auki botocina dana cika da ruwa na wuce na bar su a wurin. Kamalu Yana cewa ba zai kar’bi dari uku da hamsin ba.
Ban iya jurewa ba. Haka nan raina idan ya baci ban iya duka ba. Sautari akan fad’a mini duka ba zai tarbiyantar ba. Cikin wayo da dubara da ja ajiki ake ladabtar da zuriyar yaro. Hakan ya sanya na rage dukansa. Nake yi masa nasiha da kuma kawo masa misalai da hadisai. Amma a yau, raina ya ‘baci sosai, na gaza ha’kuri sai da na bari ya sakankace tukkuna na rufe d’akina na kamashi da duka.
A lokaci Baba Sule ya shigo gidan. ‘Kanin Babanmu ne. Ya zo ya tsaya bakin kofar d’akin Yana cewa.” Amina an fad’a miki ki daina dukansa kin ‘ki ji ko? Wato matan gidan saboda ba su suka haifeki ba shiyasa babu wadda za ta fad’a miki kiji. Dama tuntuni ina jin labarin abinda ki ke yi, kina yawo da mu a duniya kina cewa babu wanda yake taimaka miki dake da marayunki. To bari ki ji wad’annan yaran dole ne ki mayar dasu wurin kakarsu tunda tana raye, ba za su lalace a hannunmu ba, azo a yi kuka da mu. Wannan yaron Kamalu takad’iri ne, wa yasan abinda zai zama anan gaba tunda kowa baya furta alheri a kansa.”
✍️

0 Comments