WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 1K MANHAJAR TALGRAM MASU KARATU A AREWA BOOKS KUMA AKWAI COMPLETE DINSA A CAN SAI A GARZAYA A KARANTA. DOMIN BIYAN KUDIN LITTAFIN 0542382124...Binta Umar gtbank MUTANAN NIJAR DALA DARI KATIN AIRTEL SAI A KANKARE HOTON A TURA MINI DASHI TA WHASAP DA WANNAN LAMAR A TURA SHEDAR BIYA KAI TSAYE. 07084653262 08089965176 *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A✍️* *GODIYA!* Yabo da godiya su tabbata ga Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah suka kara ninkuwa ga shugaba Annabi Muhammadu s.a.w. Wannan littafi mai suna a sama 'kirkirarre ne, ba a yi shi don wani ko wata ba, idan har ya yi daidai da yanayi na rayuwaka/ki a rashi ne. Haka zalika ban yarda a juya mini labarin littafin nan ta kowace siga ba. Yin hakan ba tare da neman izini ba ka iya kai mu ga hukuma a kiyaye! Ina mik'a godiyata ga kafatanin masoyana a duk inda suke ina mutukar godiya tare da fatan alheri, ina fatan kuma wannan karon ma za ku kasance da ni a cikin wannan littafi mai suna gudun aure. Kamar yadda tsarin yake book1 zai zo muku kyauta anan Whatsapp yayin da book 2_3_4 zai zo a matsayin paid a manhajar talgram da arewa, ina burin samun goyon baya daga gare ku bakid'aya. Ga masu karatu a arewa books za su iya garzayawa can domin na yi nisa a can din. *Godiya da fatan alheri.* Fatima Musa nijar Usaina abdulmalik kaita Hairi Aisha Aliyu Munnira Amina Fadima sani Prof Asabe Sakina Mahmud Zainab Yola Amra Fatima Gwaram Giwar sarkin Sudan Maimuna ramalan. *Shafin farko kyauta ne ga Jamila Adam namaska Hajjaju Ina godiya sosai.🥰💯* *Book1* *KANO STATE* *'KOFAR KABUGA* *1* Sunana Amina Malam Salisu wanda ake kira da (Mai wankin hula) Ni tela ce k'wararriya sannan kuma malamar makarantar boko ce ta gomnati. Ina koyar da Yara harshen hausa a firamare ta gwale local goment. Bazawara ce ni a yanzu mai yara biyu dukaninsu maza. Babban sunansa Kamalu sai d'an'uwansa Yusuf wanda muke kiransa da Yusi. Mahaifinsu ya rasu shekaru hud'u da suka gabata tun lokacin Yusi din yana da shekaru bakwai a duniya. Tazarar da take tsakaninsa da d'an'uwansa Kamalu ta shekara daya ce. Ni da Babansu Allah ya jikansa da rahama muna hasashen daga yin arb'anin din haihuwar Kamalun ne na yi katari da cikin Yusuf din. Tsiran da yake tsakaninsu dai bashi da wani yawa. Yanzu Kamalu yana da shekara goma sha biyu, yayin da Yusi yake da goma sha d'aya. Tun bayan rasuwar Yaya Aminu mahaifin yarana na koma gidanmu da zama domin dama gidan da muke zaune dashi na haya ne kasancewar akwai rashin 'karfi da rashin 'kwa'kkwarar sana'a daga 'bangaransa. Cikin ikon Allah sai aka yi sa'a d'akin da muka yi 'yan matanci ni da 'yan'uwana yana nan sai dai shirgi da matan gidan suke ajiyewa. Anan na ra'kube da 'yan kayana na zauna nake gurgura rayuwar kafin mu ga hukuncin da Allah zai zartar. Zamantakewatar auran da muka yi ni da Yaya Aminu na tsayin shekara goma sha uku kusan ni ce 'karfin gidan saboda Allah ya ri'ka mini Ina aiki, sannan ina d'inkin mata da 'yan gyare-gyare, bayan haka kuma ana kawo mini aikatau na jaka 'yar pose da huluna irin na yadin hijabai. Sosai Allah ya huwace mini. Duk wata zan d'auki albashi sana'ar d'inkin da nake yi kuma tana taimaka mana sosai har mu iske sabon wata ba mu galabaita ba. Ban ta'ba yin nadama ko na ji wani abu na 'kyashi a raina ba a duk lokacin da Ya Aminu zai nemi wani abu a wurina muddin ina dashi babu jayya ko gardama nake d'auka na bashi. Babban burina ace asirinmu ya rufu gabad'aya, kuma dama tun lokacin da muka yi aure na yi alkawari cewa 'In dai Allah ya ri'ka mini sai Ya Aminu ya fi karfin komai a wurina, sakamakon irin hallacin da ya yi mini a rayuwata. Duk da cewa albashina bashi da wani yawa kasancewar firamare nake koyarwa, amma ana yin salary nake ware masa kudin transport, tun bayan korarsa da aka yi a kamfanin da yake aiki sakamakon tashin ciwonsa, to sai ya koma kasuwa yake buge-buge. Dalilin da ya sanya kenan Ina kar'bar albashina nake ware masa wanda za su ishe shi zurga-zurga a wata saboda lalurarsa tunda bashi da abin hawa kuma daga unguwarmu zuwa kasuwar da yake hurd'odinsa akwai akwai nisa sosai. Ni da Gwaggwo mahaifiyarsa ba mu ta'ba sanin yana da wani ciwo ba sai da kawo shi ranga ranga daga wurin aiki tukkuna likita ya tabbatar mana da cewa yana da matsananciyar asma bayan ita ma har da sanyi wato limoniya sune suka tayar masa sakamakon yawan shiga ruwa da yake yi, da kuma shakar iskar asubahi. Tunda ana idar da sallah yake fita kuma a 'kafa yake tafiya dalili kamfanin babu nisa a tsakaninmu, bayan haka kuma Yana da matsalar k'afa guda d'aya a dogare take dunduniyar bata taka k'asa. Likitan ya tabbatar mana da cewa iskar da yake sha'ka da tafiyar da yake yi mai tsanani duk sune suka had'u suka tayar masa da ciwon. Sai sannan Gwaggo ta tuna a lokacin da yana yaro ya ta'ba yin irin haka da 'kyar aka shawo kan matsalar. Tun daga sannan ni dashi muke kaffa-kaffa. Ko fita ya yi ya manta da inhele sai ya dawo ya d'auka. Ni ma kuma kafin ya fitan na kan tuna masa sai ya d'auka ya sa a aljihunsa ya tafi. Tunda aka sallame shi daga aiki. Muke kame-kame, taimakon da Allah ya yi mini ina da hanyar samu da ban san ya za mu yi ba. Takaici da bakinciki ya hana shi sakat kullum idan muka zauna maganarsa Alhaji Tajo bai yi masa adalci ba. Ya sallame shi babu uzuri, sannan bai bashi komai ba duk irin wahalar da ya yi masa. Ni kaina sheda ce Yaya Aminu ya bautatawa mutumin sosai. Amma bai duba hakan ba. Na dinga 'karfafa masa gwiwa akan ya yi hak'uri ya cire damuwar hakan a cikin ransa. Idan ni ce ba zan ta'ba d'aga masa hankali ba, da dadi babu dadi zan zauna dashi. kuma ya je kasuwa ya nemi arziki, Allah ne mai bayarwa. Kalamaina suna 'kara masa karfin guiwa a lokacin zai shirya ya fita duk da bai san inda zai nufa ba amma zan ta 'karfafa masa guiwa. Wasu lukutan ya dawo da d'an abin sarrafawa, wasu lukutan kuma ya dawo sannu rabbana da kukan k'afafunsa na yi masa ciwo. Tashin ciwonsa na biyu shi ya kasance ajalinsa ya kwanta jinya a gida da tunani da takaicin abubuwa da yawa, domin har zuwa lokacin bai manta da wula'kancin da akayi masa ba. Da ba'kincikin Alhaji Tajo Yaya Aminu ya koma ga Ubangijinsa. Komawa ta gidanmu da zummar yin zawarci sai abubuwa suka ru'banya rinca'bewa. Kuncin dana riska na yanzu ya fi na baya inda Allah Ya taimakeni ina da abin yi sai na samu sassauci ta nan 'bangaran. Amma dai dukda haka wataran idan masifar ta ishe ni 'kunshe kaina nake yi a d'aki na ci kukana na 'koshi. Wata zuciyar ta dinga raya mini kawai na sanya dilallai su cigita mini gidan haya wanda ba zai gaza dubu hamshin ba a shekara na san tunda ba'a zaune nake ba Allah zai agaza mini, saboda wata masifar Kamalu ne yake janyo mini ita, yaron bashi da ha'kuri kamar d'an'uwansa gashi dai shine babba,amma kullum kuka ake yi dashi a gidan. Ya yi ta tsokanar yaran jama'a dana ma'kota Ya ci zalin wanda ya fi karfi. Iyayensu su fito su yi zage-zage da gore-gore. Da barazanar sanar da maigidan Babanmu akan ya tursasani mayar dasu dangin Babansu. A wancan zaman na baya na fuskanci uk'uba ba da 'kunci na garari. Farko na rashin uwa majinginta. Na biyu kuma yadda na zama 'yartsakargida wula'kantacciya wadda ba ta da 'yanci kamar sauran 'yan'uwanta. Na uku jarabbawar da Ubangiji ya yi mini a lokacin mun taso mu biyar duk 'Yan mata amma gabad'aya sai da aka aurar dasu ni ina zaune babu ma wanda yake sansanta. Sai da kaddara ta gifta tukkuna Yaya Aminu ya nuna sha'awar aurena muddin ina sonsa tunda dai shi ga yadda Allah Ya hallice shi. WANNAN KENAN. **** Kasancewar na raba dare ina yanka din'kunan mutane da suka jima a hannuna ban samu sukunin dinka musu ba sai da aka yi wa yara hutun makaranta tukkuna. Dalilin da ya assasa mini bacci mai nauyi kenan da k'yar na tashi na gabatar da sallar asubahi. Na tashi yarana sai da na tabbatar sun fita zuwa massalaci tukkuna na koma na kwanta baccin dai ya 'kara surata. Sai na ji sautin kukan Yusi a cikin kunnuwana na bud'e idona da saurin gaske na tashi zaune sai na ganshi a ra'kube a jikin bango. Saminu 'kanina da muka had'a Uba d'aya dashi da tsintsiyar kwakwa a hannunsaa yana shaud'a masa. Da sauri na fizge ina fad'in." Kai akan me ka ke dukansa, me ya yi maka?" Ya ce.'' Kashi ya yi a bakin masai. Cike da b'acin rai na ce." Saboda ya yi kashi a bakin masai sai ka dake shi Ina ce kai ma kana yi, ko kai kake wanke bandakin ne?" Cikin rashin kunya ya ce.'' Ai bayan haka ma d'azu kina bacci Kamalu ya tsinkawa Ashiru mari, babu abinda aka ya yi masa, shine nake ramawa a kan 'kaninsa ni ma." Cikin takaici na ce." Dallah fita ka ba ni wuri shashasha kawai." Ya kama hanyar fita yana wa'ke-wa'ke. Na girgiza kai tare da mayar da hankalina kan yaron na ce." Yusi ban ce idan za ku hau masai ku dinga nutsuwa ba?" "Mama matso ni ya yi. Kuma Saminu ne a cikin bandakin da yaga ina jin kashin sai ya'ki fitowa daga band'akin, yana leko ni yana yi mini dariya. Na fadawa Ummansu ta yi mini banza. Sai da Yaya Usaini ya yi masa magana sannan ya fito na shiga ban san na yi bakin masai ba." "Yanzu ina Kamalun yake?" "Ya d'auki kudi a jakarki ya tafi sayo kunu da awara." Na kalli agogon da yake bangon d'akin, takwas saura mini goma. Na ce." To tunda an yi hutun boko sai ku yi shirin allo idan kun karya ba zan iya cecekuce da rabon fad'a ba." Ya ce." To Mama." Kamalu ya shigo da jug din kunu da awara a bakar leda Yana cewa." Mama na d'auki dari biyar a jakarki na sayo awara ta d'ari uku kunun dari biyu, yanzu darin sukari za ki bayar." Na ce." Kamalu kai kullum burinka ka janyo mini magana ko? kullum sai na zaunar da kai na yi maka fad'a, amma magana tana shiga ta kunnan dama ta fita ta kunnan hagu ko? Ba za ka ri'ke maraicinka ba Kamalu abinda kake yi fa shi d'an'uwanka zai kwaikwaya, ba za ka barni na ji da abu daya ba sai ka jefa mini damuwa da zullumi a cikin raina ko Kamalu." Ya zauna jiki a sanyaye ya ce." Mama don Allah ki yi hakuri kin ji, ba zan kara ba." Na ce." Haka kullum kake fad'i Kamalu amma kana fita zaka sanya kafa ka shure maganata, me yasa kake dukan yaran mutane kana d'auko mini magana, bakin jama'a a kanka, kowa Kamalu kowa Kamalu, so kake yi baki ya kamaka ko?" "Mama ki yi hakuri ba zan sake ba." Girgiza kaina kawai na yi cikin zuciyata nake masa addu'ar shirya. Na ce." Ka je ka zuba mini ruwa a buta zan wanke bakina." Da sauri ya tashi ya d'auki buta ya fita. Sai gashi ya dawo yana cewa."Mama sun d'auke gugansu. Na tambayi Ummansu Saminu ta ba mu aro wai ba zata bayar ba tunda kina sana'a ki saya mana." Kaina ne ya d'aure da jin maganar. Na ce." Umman Saminu ce din ta fadi haka?" Ya ce." E, wallahi." Ban yarda ba sai na tashi na fita da kaina na tsaya a bakin kofar dakinta na ce.''Umma ina kwana?" Tana rabawa Yara karin kummalo ta amsa a dakile. Na ce." Guga za ki d'an ban aro zan ja ruwa." "Amina ki sayi guganki don Allah, kullum sai kin ara, bayan Allah ya hore miki, kada ki ce za ki yi gadara domin ba babanku ne ya saya ba, kowa da kud'inta ta saya. Yawan jan ruwan da Kamalu yake yi miki, duk gugana ya fatattake." Kafin na ce wani abu. Ummansu Hadiza ta le'ko tana cewa." Kin ga zo ki d'auki nawa ki yi abinda za ki yi gugan me da har za ki tsaya ana yi miki gori akansa." Hakan sai ya fusata Ummansu Saminu. Kamar dama kiris take jira, ta fito tsakar gidan tana cewa." Aikin banza da wofi. Murja sai yanzu ne za ki nuna mata k'auna waye bai san irin jifan da ki ke yi mata ba. Ba zan bayar da gugan ba, tunda ba ubanta ne ya saya ba.'' Ni dai ban ce komai ba na je na d'auki gugan na wuce bakin rijiya ina jin su suna ta masayar yawu. Na kud'ire a raina idan na fita kasuwa sayo kayan d'inki zan tsaya na siyo gugana da duk abinda na san za a yi mini gori akansa. Babanmu ya fito daga d'akinsa da shirin fita hannunsa da hulunun mutane da yawa. Ya tsaya yana tambayar ba'asin hayaniyar da suke yi. Babu wadda ta ba shi amsa a cikinsu. Kamalu ya ce." Saboda gugan jan ruwa ne, Ummansu Saminu ta c... Na daka masa tsawa sai ya yi shiru yana kallona. Na ce." Wuce ka je ka d'auko mini d'an bokitin nan.'' Ya bar wurin da sauri. Na dan risina a lokacin da ya kusa karasowa bakin rijiyar da niyyar fita. Na ce." Baba ina kwana" Ya amsa ya dan tsaya yana kallona kafin ya ce." Ko zan sami dari biyar a wurinki Amina yau haka na wayi gari babu ko kwabo, wad'annan matan kuma suna nema su tona mini asiri da sanyi safiyar nan." Na ce." Ina da ita Baba." Sai ya ce." To ki aiko Kamalu ya kawo mini, zan aike shi ya sayo mini shayi." Na ce." Baba don Allah ka rage cin borodin nan kwanan nan fa ka tashi daga lalura basir ne da kai mai muni." Ya ce." Ai kad'an nake ci, kuma shayin tsura nake sha ba madara. Na ce." Dukda haka dai Baba, hanyar lafiya a bita da shekara." "Amina abinda ya tashi basir din nan fa zama ne, da kuma cin rogo da gyad'a dana dimanta amma zan kiyaye dai." Ya kama hanya ya fita yana gyara tarin hulun nan da suke hannunsa. Sai da na cika butocina da babban bokitina mai murfi sannan na mi'ka mata guganta. Muna karyawa na ce." Wallahi Kamalu duk lokacin da ake hatsaniya a gidan nan na ji ka kara sanya bakinka sai na sanya an zane mini kai, kaine mai bakin magana ko?" Shiru ya yi. Na k'araci yi masa fada bai ce uffan ba. Na kunna kurfoti na d'ora musu ruwan wanka suka yi suka tafi makaranta. Na had'a wankinmu da ya taru, na sanya sabulu a ciki na daure. Sannan na juye ruwan dana dora na je na yi wanka a gurguje na shirya da zan fita na yi musu sallama. Kafin na wuce kasuwar sai da na tsaya a shagon Babanmu na bashi dubu daya kamar yadda na yi masa alkawari kafin ya fita. Da ya tambayeni Ina zan je na ce." Kasuwa zan je na sayo kayan d'inki. To da yake motar sabon gari bata wahala ina fita titi na samu. Sai dai gosolw da ya ri'ke mu a hanya daidai sabon titi gidan 'kankara. Na rasa cunkuson menene direban da yake jan mu ya ce.'' Rasuwa akayi nan cikin Sani mainagge shine Alhaji Tajo ya zo gaisuwa wad'annan zungura-zunguran motacinsa ne da jama'arsa." Na ce.'' Na d'auka ai dan kasuwa ne ba 'dan siyasa ba ne." Ya ce." E, d'an kasuwa ne sosai, ai ba sai lallai d'an siyasa za a yi wa wannan cunkoson ba. Shi ma babban mutum ne a garin nan." Na girgiza kaina. Ban yi mamaki ba tunda sananne ne. Akwai d'aruruwan mutane dake 'kar'kashinsa. Bayan haka ma har kalandarsa na ta'ba kafewa a d'akina a lokacin da Abbansu Yusi ya yi aiki a kamfaninsa na sarrafa robobi. Kafin ya sanya soke sunansa daga jerin ma'aikatansa... ✍️ *Garkuwar mata Bintuumarabbale* *08089965176* *07084653262* [11/11, 7:38 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *Marubuciyar* *Yar bangar siyasa* *Ba'aboren namiji* *Madadi* *Ga irinta nan* *Goje* *Babban yaro* *Sadauki Omar* *Nida Yaya sadam* *Da sauransu..!* *@Arewa Books* *Bintuumarabbale* *2* Matar da take zaune a kusa da ni ta ce." Kai gaskiya ban yarda ba domin kuwa wannan bawan Allan ya ma fi wani dan siyasar. Yadda yake taimakon jama'a shi zai nuna maka cewa adali ne yana kuma da tausayi, tabbas da zai fito takara ina ganin zai iya lashewa muddin jama'a sun san ciwon kan su to shi zasu dangwalwa kuri'arsu. Ni dai ko yanzu ya fito takara shi zan za'ba." Cike da karsashinta tare da kwarin guiwa ta dire maganarta. Yadda ta ha'kik'ance take bayar da sheda akansa shi yake nuni da cewa lallai akwai abinda ya ta'ba yi mata a rayuwa ko wani da ya danganceta. Tunanina ya katse a lokacin da na ji direban namu shi ma yana ce wa." Gaskiya ni ma 'kuri'ata tasa ce, domin yayyuna biyu a kafamninsa suke aiki, sun yi gida, sun yi aure kuma suna ri'ke da iyalinsa. Ko yau zai sallameka daga aiki zai baka kudin da za su isheka jari domin yin wata sana'ar, ai mutumin kirki ne mai dattako wallahi." Na ce" Ban tari numfashinka ba, irin wad'annan mutanan fa suna zama da mutum ne idan sun ga zasu amfanu. Babu yadda za a yi ku ce lallai ya cika cif kowane d'an adam za ku same shi da da aikata wasu kusakuran. Ni dai wallahi duk inda za a je ba zan bayar da sheda a kansa ba. Domin ni ma mijina ya yi aiki a kamfaninsa na robobi kafin rasuwarsa, kuma daidai gwargwado ya yi masa bauta. Amma tashi d'aya ya sallame shi bai duba uzuri da lalurarsa ba. Kuma bai bashi komai ba." Matar da take kusa da ni ta kalleni tana fad'in." Anya kuwa, gaskiya ban yarda da maganarki ba, mutumin nan adali ne, sai dai idan mak'arkashiya aka yi wa mijinki a kamfanin, amma zahiri daidai gwargwado yana yi wa ma'aikatasa hidima." Na ce." To ko annabawan Allah suna kuskure ballanatana mutum, ba wai na ce dole ku yarda ba ne, ni ma kuma babu lallai na aminta da hasashenku akansa ba domin lokacin da aka bawa maigidana takardar sallama mun shiga tashin hankali sosai, shiyasa duk lokacin da na ji sunansa sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi." Direban ya dinga dariya yana ce wa." Lallai hajiya kenan ko da zai fito takara ba za ki zabe shi ba?" Kai tsaye na ce." Babu lallai gaskiya." Har goslow din ya tsaigaita muna jayayya suna fad'in ra'ayinsu akan mutumin ni ma ina fad'in ra'ayina akansa. Direban dai in banda dariya babu abinda yake yi mana ganin yadda ni da matar dake kusa da ni fad'a ya kusa ya kaurewa sai ita ta gaji ta yi mini shiru, fad'i yake "Hajiya za ki yi kyau da aikin jarida na lura ba a kada ke a magana, ko dai 'yar siyasar ce ke me.'' Na ce." A a ban ta'ba sha'awar siyasa ba, asalima ni malamar makaranta ce. Ya ce." Haba koda na ji shiyasa duk maganganunki suke fita cikin azanci da hikima. To Ubangiji Allah dai ya yi mana za'bi nagari." Gabad'aya muka amsa da 'Amin." ** Cikin kasuwar sabon gari nake kutsawa na sayo kayan dinki cikin sau'ki da rahusa. Shiyasa nake rufe fuskata da nikabi gudun had'uwa da idon sani, wasu mutanan basu da gadonka amma suna da gadon magana akanka. Na kammala duk abinda zan saya da ya danganci sana'ata. Na fito bakin kasuwar na sayi kayan miya na k'arasa 'yan kura na sayi kifi d'anye da sauran abubuwan buk'atata. Na tari shatar adaidaita sahu muka tsadance zai kai ni har kofar gidanmu dake kofar kabuga d'ari takwas. Ya taimaka mini wurin sanya kayan a babur din. Na shiga na zauna babu jayayya domin na san ya yi mini adalci sosai a yadda mai yake tsadar nan wani ma zai iya cewa sai na bashi dubu daya da d'ari biyar. Gidan namu a bushe da alama Babanmu bai yo aiken kudin cefane ba, tunda sau tari sai ya fita abinda ya samu zai aiko musu su sarrafa. Kowacce tana dakinta. Yara kuma sun fita. Na bude dakina na shiga na zube kayan a gefe. Na cire nikab da hijabi na zauna ina mayar da numfashi. Yusi ya shigo a guje ya zube a jikina Yana dariya. "Mama mai ki ke sayo mini?" Tambayar da ya yi mini kenan. Na ce." Ina Kamalu yake? Ya zo ya d'auki wankin nan ya kai wa Halima tun jiya na fad'a mata zan kawo mata wanki." Ya ce." Muna tashi daga makaranta shi da Saminu suka d'auki buhu." "Suka d'auki buhu suka je ina?" Ya ce." Tsince-tsince suke yi a bola su kai kangon Jadda ya basu kudi." Raina ya 'baci ainun! Na ce." Yusi kada ka yi mini karya ka fad'a mini gaskiya tun yaushe suka fara jari bola." Ya ce." Ni dai na gansu kusan sau uku, ni ma na ce zan bi su, Saminu ya koro ni gida." Sai kawai na ji idona ya ciko da ruwan hawaye. Wato duk ko'karin da nake yi akan tarbiyar yarana Saminu sai ya rugaza mini. Ba na son yawon nan da suke yi lungu-lungu. Abin har ya kai su d'auki buhu su hau bola suna suna tsince-tsince bayan duk rintsi ana basu abinci . Na tashi na nufi wurin Ummansu Saminu domin na ji shin ta san abinda yake faruwa. Tana kwance a tsakiyar rumfa da mafici a hannunta. Ta tashi zaune tana cewa." Na sani wallahi, to ya zan yi Amina, ai sana'a ce, muddin ba za su d'auko abin wani ba to ki kyale su kawai, yanzu fa rayuwar sai an hadu karfi da karfe iyaye da Yara an taimaki juna, sabulun wanki kad'ai ma ya ishe shi bawa, to balle ma duk ba wannan ake yi wa ba, abinda za a ci shi ake fafutuka." Na ce." Ban 'ki maganarki ba Umma, amma ki yi nazari sosai akan hanyar da yaran nan suka d'auko, ban ce jari bola ba sana'a ba ce, amma ni wallahi a yanzu na fi buk'atar yaran nan su yi karatu, tunda daidai gwargwado ana yi musu hidima, basu rasa komai ba, to me zai sanya su dinga yawo da buhu suna hawa kan bola daga haka fa ba fata nake yi ba idan suka ga abin amfani su sai su d'auka su je su sayar kin ga wa gari ya waya." Ta ce." To ni babu yadda zan yi Amina. Yaron nan Saminu ya kan taimaka mini idan ya yi buga-bugarsa. Kin fi kowa sanin yadda rayuwar gidan nan take, wataran a baka wataran ace ba a samu ba. Kuma ko an baka ba za a baka wanda zai isheka ba. Ba ni da jarin yin sana'a balle ki ce. Amma duk ranar da Saminu ya fita gwangwan muna ragewa gaskiya kin ga yanzu sha biyu da rabi amma har yanzu babanku bai aiko ba, Yara kuma ba su san babu ba, lokacin cin abinci Yana yi za su fara kuka." Gabad'aya maganunta suka kashe mini jiki. Na ja k'afafuna da suka sage na bar bakin kofar dakinta. Na jima Ina tunanin hanyar da zan bi gurin ganin na janye Kamalu daga tarayya da Saminu kaina ya kulle gabad'aya. Babu yadda za a yi su rabu tunda suna kwana a gida daya. Saminu ya girmi Kamalu da shekara uku. Amma a haka suke cud'anya da gwagwarmaya tunda shi Kamalu duk abokanansa yawanci sun girme shi daga na makarantar har na cikin unguwar. Duk wani yun'kuri da zan yi a yanzu dan ganin na datse ala'kar dake tsakaninsu za a yi mini wata fassara ne. Ni kuma akwai dalilin da ya sanya bana son tarayyarsu. Ban dai ta'ba gani da idona ba, kuma bai ta'ba yi mini ba, amma a unguwar ana rad'e rad'in yaron yana d'auke-d'auke, idan kayi wasarare da abinka sai ya d'auka. Wasu lukutan ma yakan yi wa uwarsa ta kulle shi a d'aki ta yi ta duka. Ina jin tsoron yau da gobe mu'amularsu ta canza mini yaro. Tunda Kamalu ko nawa zan ajiye a gabansa ba zai d'auka ba. Yana bud'e jakata ya d'auki kudi idan ina bacci ya dawo da canjin ya ajiye mini, idan na duba kudina na gansu cif a yadda suke. Wannan dalilan ya sanya na ke fargabar abotarsu. Da yake idan na d'auki albashi abinci nake saya da d'an yawa. Dan sai na auno shinkafa kwano biyar na sayo 'karamin buhun taliya na auno garin towo. Da su mangyad'a da manja da hadin maggi. Da har buhun gawayi nake jinginewa, yau da gobe ta sanya na daina saboda idan na sa 'kafa na fita aiki sai na dawo naga an kwashe mini gawayin. Ba damar kuma na tambaya. Sai su ce na 'kala mu sata. Sai na daina sayan buhu nake aikawa gidan Mairo a sayo mini. Dana gama abinci na zubawa Ashiru tunda shine k'arami a dakinsu. Ita kuma Ummansu Hadiza bata da k'ananun yara duk sun girma tunda itace uwargida. Amma dai dukda haka ina zuba mata itama. To sai wajan biyu da rabi Babanmu ya Aiko musu da kudin abinci sannan Kowacce ta fara fafutukar abinda zata girka har zuwa lokacin Kamalu da Saminu Basu dawo ba. Raina ya baci ainun! domin lokacin makarantar allo ya kusa, ni kuma a rayuwata na tsani wasa da karatu ganin kamar shine gatan da za ka yi wa yaro, bayan haka kuma ni ma a yanzu karatun ne yake ri'ke da ni bayan d'inkin da nake yi.... Uku saura suka shigo gidan a firgice duk'un-du'kun 'kafafuwa da hannuwansu duk daud'a. Saminu ya yi d'akinsu da kud'i a hannunsa. Shi kuma ganina a bakin rijiya ina jan ruwa ya tsaya. Na kalleshi sama da k'asa kafin na ce." Daga ina kuke?" Ya yi shiru bai ba ni amsa ba. Saminu ya fito ya na cewa." Kai Kamalu ungo kudinka." Ya kar'ba da sauri yana fad'in." To ya na ga ka ba ni dari uku da hamsin, bayan gabad'aya abinda aka sayi kayan dubu daya da dari bakwai ne." "E, Ummanmu ce tace mu bata aron kud'in. Zan cika maka sauran tunda tace gobe za ta bayar." Cikin takaici na ce." Saminu yawon tsince tsince a bola kuke yi ko?" "E, ai ni, na kwana biyu ina yi, shine Kamalu shi ma ya ce zai dinga bina. Idan mun samo k'arafuna sai mu kai kangon Adahama ya saya." Hankalinsa a kwance ya ba ni amsa. Na girgiza kaina ban sake cewa komai ba, na d'auki botocina dana cika da ruwa na wuce na bar su a wurin. Kamalu Yana cewa ba zai kar'bi dari uku da hamsin ba. Ban iya jurewa ba. Haka nan raina idan ya baci ban iya duka ba. Sautari akan fad'a mini duka ba zai tarbiyantar ba. Cikin wayo da dubara da ja ajiki ake ladabtar da zuriyar yaro. Hakan ya sanya na rage dukansa. Nake yi masa nasiha da kuma kawo masa misalai da hadisai. Amma a yau, raina ya 'baci sosai, na gaza ha'kuri sai da na bari ya sakankace tukkuna na rufe d'akina na kamashi da duka. A lokaci Baba Sule ya shigo gidan. 'Kanin Babanmu ne. Ya zo ya tsaya bakin kofar d'akin Yana cewa." Amina an fad'a miki ki daina dukansa kin 'ki ji ko? Wato matan gidan saboda ba su suka haifeki ba shiyasa babu wadda za ta fad'a miki kiji. Dama tuntuni ina jin labarin abinda ki ke yi, kina yawo da mu a duniya kina cewa babu wanda yake taimaka miki dake da marayunki. To bari ki ji wad'annan yaran dole ne ki mayar dasu wurin kakarsu tunda tana raye, ba za su lalace a hannunmu ba, azo a yi kuka da mu. Wannan yaron Kamalu takad'iri ne, wa yasan abinda zai zama anan gaba tunda kowa baya furta alheri a kansa." ✍️ *GARUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* *07084653262* [11/12, 10:23 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *Marubuciyar* *Yar bangar siyasa* *Ba'aboren namiji* *Madadi* *Ga irinta nan* *Goje* *Babban yaro* *Sadauki Omar* *Nida Yaya sadam* *Da sauransu..!* 'Yan uwa Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS, duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali. Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su Sandal flakes Hawee Gabgab Halut Dorot Coconut chips Dufr(farce) Black khumra Brown khumra White khumra Oil perfumes da Body sprays Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku. Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka Call/WhatsApp 07037489958 Location:Gonan Ganye,zaria Kaduna state Nationwide Delivery *3* Na bude d'akin na fito ina kuka sosai na ce." Haba baba Sule wannan wace irin magana ce. Idan ba ku taimaka mini wurin kula da yaran nan ba ai ba za ku dinga furta munana kalamai a kan su ba. Wallahi ko kai ka ji abinda suka aikata sai ka yi musu hukuncu, a gaskiya maganganun nan da kake fad'a akan yaronan Kamalu sun yi tsauri da yawa." Sai ya harzu'ka yana ce wa." Rashin kunya za ki yi mini don ubanki, ni za ki nunawa ban san abinda nake yi ba, an fad'a din Kamalu takad'iri ne ba ya ji, ko za ki musanta mini ne? yaron da kullum cikin d'auko miki magana yake, kaf zuri'armu babu fitinanne a can dangin ubansa ya samo wannan bakin halin. Akan ya je yana d'auko abin mutane ai gwara ya d'auki buhun ya tafi ya yi jari bola, ai sana'a ce, yara nawa ne suke yi, ko za ki gaya mini naki yaron ya fi na kowa, akan hakan ki ka zage karfi akansa kina dukansa, Murja ta yi mini bayanin komai, to wallahi idan ba ki yi wasa ba da kaina zan d'aukesu na mayar da su can wurin kakarsu su je su 'karata." Cikin kuka mai cin rai na ce." To baba Sule duk mai ya kawo wannan maganganun? Wahalar nan wai wanene yake yi mini ita ne? yaran nan fa kwanciya kawai suke yi su tashi a gidan nan, duk d'awainiyarsu ni ce, na d'auka ai sai ana wahala da mutum tukkuna za a nuna gazawa akansa. A tsaye nake akansu ba zan iya bari su yi wannan sana'ar ba gaskiya magana kenan, Allah ma sai ya tuhume ni, tunda ya taimaka mini da yadda zany..... Ban yi tsammani ba na ji ya tsinka mini mari a fusace yana ce wa." Za ki nuna mini ba ni na haife ki ba kenan, tunda har zan iya fad'in Magana ki mayar mini da raddi, don ubanki ni ba kanin babanki ba ne, Ina ce ni ne na bada auranki ga uban yaran. Wato Ke har abada bakinki ba zai mutu ba ko?" Ummansu Saminu ta ce." Ni abin ne ya ba ni mamaki Sule ashe duk zaman da muke yi a gidan nan, Amina ta na yi mana kallon sakarkaru wad'anda ba su iya tarbiya ba. Wato yanzu na gane nufin ki kina so ki janye yaronki a ganinki kamar ana so a lalata shi ko?" Na ce." Ba haka nake nufi ba. Ni dai na ce ban yadda yarona ya yi jari bola ba, karatu nake so ya yi." Baba Sule ya ce." To ke ma don ubanki gidan za ki bari aure za ki yi, ai ba a ce don ubansu ya mutu ki sarayar da k'uruciyarki ba. Tun wuri ki fito da miji ki yi aure." Ban ce masa komai ba na bar wurin zuciyata a cunkushe da tunani da fargabar mummunan kalubalen da yake fuskantoni. Wannan ya wuce da kwana biyu wani abu bai sake faruwa ba. Kamalu ya ji fad'a da dukan da na yi masa. Ya rage wasu abubuwan mussaman da ya ga Baba Sule ya mare ni, sai ya dinga kuka a lokacin yana ba ni ha'kuri da al'kawarin ba zai sake ba. *** Ranar juma'a da wuri suka yi wanka suka shirya tsaf cikin kaya iri d'aya hula da takalmi ma duk iri d'aya. Yusi ya kalle ni a sanyaye ya ce." Mama me yasa ba za ki je ba, don Allah ki shirya mu tafi tare." Na ce." Yusi ba na jin dadi, zan bari zuwa wani satin idan muna raye sai mu je tare, idan kun je ku gaishe mini da Gwaggwo da kyau." Na kalli Kamalu dake tsaye a jikin bango sai 'bata rai yake yi, na ce." Kai na gane abinda ya sa duk lokacin da za ku je gidan Gwaggwo kake jin haushin saboda tana yi maka fad'a ko?" Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Na girgiza kaina tare da furta. " Ka d'auko ledar can shinkafa ce rabin kwano da taliya guda uku a ciki, ka kai mata, ungo wannan dubu biyu ce sai ka bata. " Ya kar'ba ya sanya a aljihu. Ya kama hanyar fita yana fad'in." Dallah malami taho mu tafi." Da sauri na ce." Wallahi tallahi ka ci zalinsa a hanya sai ranka ya 'baci, muddin ka ta'ba mini yaro kasan karon mu da kai." Ya zum'buri baki ya fita." Na kalli Yusi da yake ta walwala duk ranar da za su je wurin kakar tasu yana kasancewa cikin farinciki da nishadi. Sai na ji kwalla ta ciko mini a Ido. Yanayin sanyi da d'abi'a' sak mahaifinsa, mutum ne mai walwala da sanyi hali, baka ta'ba ganin fushinsa. Yusi kamar Yaya Aminu ya yi kaki ya tofar kamarsu d'aya. Kamalu kuma wasu suna cewa da ni yake kama. Na d'auki naira hamsin a cikin jakata nasa masa a aljihu ina fad'in." Idan ka ga wani abu a hanya ka saya. Ka yi kyau sosai d'an saurayina." Sai ya fashe da dariya yana cewa." Mama ki saya mini gilashi sannan ba ki fesa mini turare ba." Da sauri na bude 'yar sif dina na d'auko turare ina fad'in." Kash an yi tuya an manta da albasa yarona d'an gayu ne." Na fesa masa turare ko'ina a jikinsa. Na ce." Ku gaisa mini da ita da kyau." Yasa takalminsa Yana cewa.'' To zan fad'a mata Mama zan ce sai wani satin za ki zo." Ya kama hanyar fita da sauri. Na janye idona, a sanyaye na zame na kwanta kawai sai wasu hawaye masu d'umi suka fara sulmiyowa suna bin kumatuna. Ban yi yun'kurin gogewa ba tunda ni kad'ai ce a d'akin. Kukan kuma shi zan yi na samu sassaucin cunkusar da zuciyata ta yi. Abu biyu ne suka tarar mini. Duk lokacin da zan yi al'ada na kan kasance cikin k'unci da 'bacin rai. Sai kuma matsaltsalun da nake fuskanta. Matsalar Kamalu itace ta fi damuna a halin yanzu ba ni da wanda zai taya ni a gidan. Duk wanda zai bud'e baki sai ya ce masa fitinanne. Na san illar baki domin ana cewa har ya fi maita. So nake yi ni da yara mu yi nesa daga gidan da unguwar gabad'aya domin mu canza wata rayuwar, amma yin hakan ma kalubale ne mai zaman kansa. Na 'kudindine a cikin mayafi na ci kukana na k'oshi. Cikin zuciyata na dinga nanàta addu'ar nan (Rabbi Inni Lima Anzalta Ilayya Min Kairin Fa'kir) ina ta kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Har Allah ya sassauta mini k'uncin da nake ji a raina. Na tashi na juye ruwan wankan dana d'ora. A gurguje na yi wanka na shirya jikina tsaf. Lokacin na dan ji sassauci ciwon marar da ya matsanta mini kasancewar abin ya fara zuba. Na shirya na fito duk suna cikin d'aki. Na kulle 'kofata. Sannan na tsaya kowacce daga bakin kofarta na yi mata sallama. Har na kai bakin kofar fita Ummansu Hadiza ta kira ni. Na shiga na sameta tana d'aura dakakken yajin da take sayarwa na daddawa dana barkono. Ta ce." Ina ta zuci-zucin yi miki magana gashi kuma kin shirya za ki fita, Ina za ki je ne? Na ga an yi hutun makaranta ko kayan d'inki za ki sayo?" Na ce." A 'a ba kasuwa zan je ba, gidan Sahura zan je." Sai ta ce." Ayyo, to dama babanku ne ya ce na fad'a mini za ki yi ba'ko yau, Alhaji Mutari ne ya ce yana sonki da aure." Cikin fad'uwar gaba da tsananin tashin hankali na ce." Wanene kuma Alhaji Mutari Umma sai kuma akace masa ni aure zan yi, ko ni kad'ai ce bazawara?" Ta zuba mini ido na minti biyu kafin ta ce." Matsalarki kenan Amina rashin tauna magana, ni sa'arki ce da za ki ba ni amsa cikin gatsali." Na sassauta fuskata na ce." Umma zancen ne na ji shi kamar saukar aradu wallahi, ki yi hakuri don Allah." Ta ce." Alhaji Mutari Ubangidan Babanki Sule shine ya nuna masa hotonki, shi kuma ya yi Allaragaf dake." Na ce." To ba za ta yiwu ba, Umma ba aure zan yi ba, tarbiyar yarana ce a gabana a yanzu, kuma ko zan yi aure ni zan duba mijin da zan aura wanda ya cancanta babu ruwana da dukiya nagarta nake nema kamar dai Yaya Aminu, in sha Allahu zan samu." Ta ce." To, ni dai na isar da sa'kona Amina, amma ki yi nazari sosai akan maganar kafin ki yanke hukunci." Na yun'kura na tashi ina cewa." To zan yi, in sha Allahu Umma sai na dawo." Ta ce." Ki gaishe da Sahura da yaranta." Na kama hanya na fita ba tare da na sake cewa komai ba tsabar tashin hankalin da nake ciki. Cikin zullumi da tunani mai zurfi na isa gidan Sahura. Na same ta tana shirin fita. Ganina a hargitse ya d'aga mata hankali. Na nemi wuri na zauna kawai sai na rushe da kuka! Ta kid'ime ainun! Ta rirri'ke ni tana fad'in." Sis menene don girman Allah ki yi shiru kada ki jazawa kanki lalura, ba fa ke kad'ai ba ce, kuna nan da yawa iyayen marayu, kuma ki godewa Allah da ya ba ki sana'ar da za ki yi d'awainiya da yaranki, wallahi akwai wad'anda aka mutu aka bar musu marayun ba su da yadda za su yi, wasu ma sai sun yi bara da ro'ko suke samun abinda za su ci, ni kaina da nake da mijin kullum cikin fafutuka nake, kin san komai ba sai na fad'a miki ba, Abbansu Yasir bashi da tartibiyar sana'a, kasuwa yake shiga Yana tare mutane idan an yi katari sai ya kai su shagon da suke nema, da haka fa yake samun abinda zai kawo gida, ki yi hakuri ki godewa Allah, ki kuma cigaba da yi wa Mijinki addu'a, Allah Ya gafarta masa." Hannu nasa na goge hawayen da yake zuba. Na ce." Na san Allah Ya yi mini Sahura, ba zan butulce masa ba, yana taimakona ta fannoni da yawa. Amma sis ina da damuwa sosai, ba zan iya aure yanzu ba sai yarana sun yi 'kwari, sis Baba Sule kwana biyu ya sani a gaba, ga Kamalu Yana nema ya fi 'karfina." "Wace irin magana ce wannan Amina, ki haifi 'dan a cikinki sannan ki ce yana nema ya fi karfinki, me yake yi? kuma me Baba Sule yake yi miki, na ga dai ke kike hidima da kanki da yaranki, na d'auka ai ba ki da wani kalubale da mutanan gidanku." Naja majina cikin jin ciwon abubuwan da suke faruwa na fara bata labarin abinda ya wanzu kwanaki biyu da suka wuce. Ta ce." Ki yi hakuri, kada damuwar hakan ta janyo miki ciwo, aure dai a yanzu sai kin yi ra'ayi za ki yi tunda dai ke ba yarinya ba ce, bazawara ce muddin za ki ri'ke mutumcinki ki cigaba da sana'arki domin ki kula da yaranki, Ubangiji zai shige miki gaba, ki yi ta addu'a dai, sannan maganar Kamalu kada ki dinga yi masa kuka domin hakan zai sake jefa shi a garari, ki yi ta yi masa addu'a. In sha Allahu lamarin zai tsaya iyakacin 'kuruciya, kuma wallahi irinsu idan sun girma ba su iya hankali ba. Suna da biyayyar iyaye. Kowane yaro da irin 'kuruciyarsa. Zuciyata ta sassauto sakamakon irin rarrashi da tausasan kalamanta. Sahura k'awata ce tun ta k'uruciya tare muka dinga fa'di tashi muna 'yan mata. Daga gidansu na samu taimako sosai a harkar karatuna. Sai dai ta riga ni aure har sai da ta yi haihuwa ta biyu tukkuna Abbansu Yusi ya yi fito da zummar aurena. Ta ce." Tunda kin zo na samu abokiyar tafiya dama ba na son zuwa ni kad'ai wallahi, duk da hakan ba wani abu ba ne, amma dai bibiyu tafi dadi. Na kalleta cikin nazari sai a lokacin ma na hangi ramar da ta yi, yanayinta ya nuna tana cikin damuwa. Na ce." Da Ina za ki je ne?" Ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce." Hotoro zan je sabon kamfanin Alhaji Tajo na leda suna buk'atar ma'aikata. Maman Anisa makociyar nan tawa ta kar'bar mini form a wurin mijinta kin san shi ma yana aiki a 'karkashinsa amma dai Yana da matsayi ba 'karamin ma'aikaci ba ne, to shine suke neman ma'aikata da na gayawa Abbansu Yasir ya amince, yanzu na cike form din zan je na kai wata'kila ma a yi mini interview." Idona a kanta har ta ajiye maganar. Na ce." Sahura ba wai zan dakile ki ba, don Allah kada ki yi aiki a kamfanin nan, ki cigaba da neman aiki na gomnati, ni ma zan cigaba da nema miki har Allah Ya sa a dace, amma hankalina bai kwanta ba wallahi tunda Abbansu Yusi ya yi aiki a kamfanin mutumin nan aka zalince shi nake jin tsoro. Kin san suna amfani da lafiya da kuzarin mutum ne, duk wahalar da za ka yi musu da lafiyarka daga ranar da Allah Ya jarrabeka da ciwo ka kwanta sai suce ba su san wannan ba, 'karshe a rubuto maka takardar sallama kuma babu ko sisi." "Amina ni kaina akan dole zan yi wallahi, na fad'a miki tun farko Abbansu Yasir ne ya cuce ni, farkon auranmu na samu aikin rabon magani 'kauye-k'auye ya ce ba zan yi ba saboda mugunta. Gashi kuma yanzu muna nema Ido rufe dalilin hidimar gida da ta Yara tunda shi ba k'arfi ne dashi ba, wallahi idan lokacin biyan kudin makaranta ya yi hankalina yana tashi Amina, wasu lukutan Ina ji ina gani za'a koro mini Yara daga makaranta. Kin ga kuwa idan Ina aikin zan samu hanyar da zan dinga biya musu da yin wasu hidindimun babu fargaba." Na ce." To yanzu kina da tabbacin idan mun je za a d'auke ki, wulakanci nake gudu Sahura, shiyasa ki ka ji ina wannan maganar wallahi." "A a ai ina da hanya kai tsaye muna zuwa zan kira wayar mijin Maman Anisa d'in tunda shi ya kawo mini form din, in sha Allahu ba za a samu matsala ba." Na gyad'a kai tare da cewa." Daga nan ja'in zuwa hotoro nawa za ki kashe Sahura, kuma nawa ne kud'in albashinki komai fa d'an lissafi ne?" Ta ce." Gaskiya ba zai haura dubu saba'in ba, bayan haka kuma an ce sa'i da lokaci yana yi wa ma'aikatasa alheri, har da su kayan abinci Yana bayarwa." Na ce." To ni dai tsayin shekara biyu da Abbansu Yusi ya yi aiki a k'arkashinsa bai ta'ba gaya mini ya samu wani abu ba bayan albashinsa. Kin ga fa koda aka sallame shi ma fa ba'a bashi ko kwabo ba." A sanyaye ta ce." Zan dai jarraba na gani Amina, idan na ga babu ci sai na ajiye, don Allah ki taya ni da addu'a, ki kuma cigaba da nema mini wani aikin ko koyarwa ne irin naki." Cikin kulawa na ce." In sha Allahu rabbi, zan taya ki da addu'a kawata, zan kuma cigaba da yi miki fafutuka, Ubangiji Allah Ya sa mu dace gabad'aya." ✍️ *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* *07084653262* [11/13, 9:30 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *Marubuciyar* *Yar bangar siyasa* *Ba'aboren namiji* *Madadi* *Ga irinta nan* *Goje* *Babban yaro* *Sadauki Omar* *Nida Yaya sadam* *Da sauransu..!* *Tallah!* Albishirinku mata 'yan gayu yan gwalisa ku yi maza kugar zayo shagon (Aysha/Addah beauty saloon and spa). Shin kin taba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba ki yi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa Suna wanke kai(wash and set) suna wanke qafa(pedicure) And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University *GOMBE STATE* Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka, 08037925676 Or 08167764242 Whatsapp ko kuma Call we’r available 24/7.. Tabbas ni ma na shaida ingancin ayyuka da kayayyakin shagon anti adda mutuniyar kirki. Babu tsada komai ana samunsa cikin sau'kin farashi mutanan gombe kada ku bari wannan sau'kin ya wuce ku.🥰 *@Arewa books* *Bintaumarabbale.* *Free pege4* Ba mu fita ba sai da yaran suka dawo daga cefane tukkuna. To abin dai gashinan a hannu a hannu. Na ce." Yanzu Sahura shinkafa gwangwani biyu ce zata ishe su har su uku?" Tana gyara zaman hijabin wuyanta ta furta." To ya zan yi Amina, babansu da wuri ya fice don ma kada na tambaye shi kudi, ko sallama bai yi mini ba. Jiya dai da daddare na gaya masa zan fita. Wallahi dubu dayan kenan ta rage mini na ba su suka yo cefanan nan. Kudin mota kuwa dama cewa na yi zan kar'ba a a wurin Maman Anisa, idan na samu daga baya sai na bata. Na dubi Yusra dake juye shinkafar a faranti domin tsincewa. Na ce." Tashi ki je ki auno kwana daya sai ki dafa muku yadda za ta ishe ku. Ki karo man'kuli da maggi da wake." Na zuge jakata na d'auko dubu biyar na mi'ka mata." Duk abinda babu ki saya a ciki." Sahura ta yi sakato tana kallona. Na tashi ina fad'in." Wannan rayuwar Allah Ya magance mana. Ta ce." Sis, anya kuwa ina lefin ki bata kudin rabin kwano." Na ce." Don Allah kada ki bata mini rai Sahura." Yadda na fadi maganar cikin fushi shi ya sanya tayi shiru da bakinta ta juya kan yaran tana cewa.'' Yusra ki rufe gidan idan mun fita, duk wanda zai k'wankwasa kofa kada ki bude, ki ce bana nan." Ta ce." To Ummi sai kun dawo." Ba mu wani jima a bakin titi ba muka samu abin hawa. Ya ce sai dai mu bashi dubu daya da d'ari shida duk mutum daya d'ari takwas kenan. Na ce." Sahura shiga mu tafi a hakan ya yi mana adalci, tunda gaskiya tsakanin hotoro da ja'in akwai tazara mai tsayi. Wajan d'aya saura muka isa. Ya ajiye mu daidai bakin kamfanin duk da sabo ne hakan bai hana masu sana'ar adadaita sahu saninsa ba idan an yi duba da shuhurar mamallakinsa. Masu tsaron wurin ba su bari mun shiga kai tsaye ba sai da ta yi musu bayani ta fito da takardu ta nuna musu tukkuna suka bari muka shiga. Wurin ya yi sosai an ka'wata shi ga ko'ina a tsaftace ma'aikata na ta shawagi tare da tashin sautin injina. Sai dibi dibi take yi tana zare Ido. Na ce." To Sahura ina zamu nufa ne yanzu?" A rikice ta ce." Bari na kira Abban Anisa a waya." Na yi shiru ina kallonta ta d'auko wayarta ta kira shi bai daga ba har sau biyu. Jiki a sanyaye ta ce." Kin ga bai daga ba." Na ce.'' Na ji, wata'kila ko yana wani uzurin ne, kin ga yanzu lokacin shiga massalaci ne. Mu bari an jima kad'an sai ki sake kiransa." Muka je muka samu wani wuri muka zauna muna tattaunawa. Wani ma'aikaci da uniform ajikinsa irin na tsaro ya zo ya tsaya akanmu fuska a daure Ya ce.'' Me kuke yi anan?" Da sauri ta ce." Form din da aka ba ni na cike shine na kawo, ina neman Sulaiman sha'abu ja'in." Ya yi jim na minti biyu kafin ya ce." Ba anan yake dindin din ba. Amma yana iya zuwa da kowane lokaci. Ku tashi ku shiga cikin nan akwai wad'andasu a ciki irinku." Yadda ya fadi maganar cikin izgili shine ya bata mini rai. Na ce." Ranka ya dad'e. Ubangiji shi ya karrama dan'adam, ya kuma fifita shi akan kowace hallita. Kaga kuwa wani mahalu'ki bai isa ya 'kas'kantar dashi ba. Ba mu zo wurin nan a matsayin wulakantattu ba face neman dogo da kai." Ya yi jim Yana kallona kafin ya furta." Kada ki yi mini rashin kunya ko kin ji na fa'di mummunar magana akanku ne?" Na ce." Ba ka fad'a ba Yallabai." Sahura ta ri'ke hannuna muka tashi. Ya ja tsaki tare da nuna mana inda za mu shiga da hannuna. Muka kama hanya muna tafiya raina duk a 'bace. Ba na son raini ko kad'an. Kuma dai d'abi'ata ce rashin yin shiru idan an ta'bo ni. Shiyasa wasu suke yi mini kallon mara kunya tunda gaskiya ba na iya bari, duk girmanka ka nemi ka takani na kan nuna ban yarda ba. Dalilin da ya sanya kenan matan gidanmu suka tsaneni tunda kuruciya. Ba wai Ina yi musu fitsara ba ne, kawai dai ba na yarda da son zuciya. Mun zo shiga manager wurin zai fito a gurguje muka gaisa da alama massalaci zai je. Ya ce mu shiga mu jira shi. Mata hud'u muka samu a zaune a kan kujera. Uku duk da 'kwarinsu. Dayar kuma dattijuwa ce sosai shekarun girma sun cimmata. Muka gaisa kafin mu nemi wuri mu zauna. Wurin tsaf da sanyin Ac ga tibi falasma nan k'atuwa a bango tana aiki. Wajejan biyu da rabi wani ma'aikaci ya shigo ya dube mu kafin ya ce." Ga Yallabai nan zai shigo." Bai jira wata magana ba ya fice da gaggawa. Dattijuwar nan fadi take 'Alhamdullahi' bakinta ya gaza rufuwa. Sahura ta kalleni itama da farinciki a tare da ita ta ce." Lallai mun shigo da kafar dama 'kawata." Shiru na yi ban ce komai ba kawai dai na zubawa hanya ido. Ina mamakin yadda gabad'ayansu suka rud'e. Mutum uku ne suka fara shigowa kafin shi din ya shigo da masu tsaronsa a baya. Hakan ya nuna akwai masu kula dashi a gaba da bayansa. 'Kamshin turaransa ya gauraye wurin. Farin bafulatani ne mai madaidaincin jiki da manyan idanu kamar dai yadda hotonsa yake a kalanda Yana da kyau da fuskar salihai. Yanayin jikinsa shi ya b'oye shekarunsa. Amma dai da shekarun tunda ga tsalli tsallin furfura nan a gashin da yake kewaye da matsakaicin bakinsa, yana sanye da farar shadda babbar riga da 'yar ciki, da jar dara tare da farin gilashi a idonsa. Cikin 'yan sakwanni na karance shi. Gabad'aya muka mike tsaye. Cikin nutsuwa ya tsaya yana amsa gaisuwar da muke yi masa. Ya ce." Sabbin ma'aikata ne ?" Da sauri manager da shigowarsa kenan shi ma ya ce." E, Yallabai." Ya jinjina kai yana dubanmu ta cikin farin gilashin da yake idonsa. A nutse ya furta." Kun gama dasu ne? Ina nufin kowacce ta san matsayinta." Manager Ya ce." Ranka Ya dad'e. Wad'annan daga baya suka zo. Sulaiman sha'abu ja'in ne ya turo su. Yanzu Muna buk'atar masu shara ne da goge-goge." Ya juya Yana kallon dattijuwar nan. Ya ce." Mama za ki iya aikin nan kuwa?" Da saurin gaske ta ce." Zan iya Yallabai." Ya yi murmushi a tsanake Ya sake cewa." Aikin fa ba irin na gida ba ne Mama, kin ga wurin nan da girma ba ki dai da wata lalurar ko? don ba kasafai nake d'aukar dattijai ba, ai irin wannan yana buk'atar masu lafiya da k'ananun shekaru" Ta ce." Zan iya Alhji in sha Allahu." Ya juyo yana kallonmu ni da Sahura sai ya ce." Ina fatan za ku kula sosai, idan na d'auki mutum aiki ba na son wasa, shine dalilin da ya sanya ma na fi buk'atar zawarawa ko 'yan mata, irin wad'anda ba su da uzuri na miji da yara. A dinga zuwa akan lokaci in sha Allahu ni kuma za ku same ni da kyautata muku." Ba tare da rashin kunya ba na ce." Ranka ya dad'e ni babu ni a cikin masu neman aiki, ina da abin yi, ni ma'aikaciyar gomnati ce, sannan ina sana'ar hannu, wannan 'kawata ce Sahura ita na rako." Ya ce." Okey ita tana da aure ne ko bazawara ce?" Raina ya d'an sosu da maganarsa. Na ce." Tana da aure da Yaranta uku." Na dubeta tare da cewa." Sahura ki yi bayani mana." Ta ce." Ina da aure Yallabai, yarana uku ina zaune a unguwar ja'in." Ya ce." Wannan ba zai hana a d'auke ki aiki ba muddin za ki ri'ke shi da muhimmanci, sakarci ne dai ba na so a duk sha'anina. Na san duk dokokina kun karanta a cikin form din da kuka cike ko?" Gabad'aya suka amsa. Ya ce." To, Allah Ya yi mana jagora gabad'aya." muka amsa da "Amin." Ya juya domin fita mabiya bayansa suka take masa baya. Minti biyar sai ga d'aya daga cikin escort d'insa da kudi a hannu. Ya zo dukkaninmu ya bi mu da dubu biyar biyar Yana fad'in oga ne ya ce a baku kudin mota." Ya gama raba mana sauran ya zura a cikin aljihunsa ya fice da saurin gaske.....✍️ *GARKUWAR MATA.* *BINTA UMAR ABBALE* *07084653262* [11/14, 10:42 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *TALLAH!* 🌲🌳🌿☘️ *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* *@Arewa book* *Bintuumarabbale* *free pege* *5* Bayan an gama komai sai muka fito bakin titi muna jiran abin hawa. Na dubeta a nutse kafin na ce." Sahura kin fahimci azancin wannan mutumin ko?" Ta d'an yi shiru daga bisani ta ce." Na fahimta sis, amma kuma ban ga lefinsa ba, idan ba hakan ya yi ba sai a samu matsala. Kin san halin mutanan mu da son zuciya. Muddin dai zai kyautata kuma zai cika alkawari kamar yadda ya fada, ni kuma zan yi kokarin ganin na rike aikin da muhimmanci, ba za a samu matsala daga wurina ba." Na ce." Hakane, amma dai dole sai kin kiyaye Sahura, domin aure shi yake gaba da komai, yadda na fahimce shi kamar bashi da damuwa akan auran mutum hakkin mijinki da yara. Shi dai kawai ku fito aiki akan lokaci, ba ki ji abinda ya ce ba, ya fi buk'atar zawarawa da 'yan mata wad'anda ba su da nauyi kowa a kansu, sai ya yi amfani da kuruciyarsu da lafiyarsu, kin ga kenan hakan yana nuna duk ranar da kuka kuskure ba za ku wanye lafiya dashi ba, gaskiya ni ina ganin kamar akwai fa son zuciya a sha'aninsa." Ta yi murmushi tana ce wa." Ke dai Amina tunda aka kori marigayi daga kamfaninsa ki ka tsane shi, dukda cewa jama'ar gari na shelar mutumin arziki ne, amma ke ban ta'ba jin kin fad'i alherisa ba. Kwanaki fa har zagi ki ka d'ura masa, kin ala'kanta rasuwar mijinki dashi. Allah ina tsoron kada watarana ki yi su'btar baki a gaban jama'arsa su yi miki dukan tsiya." Na ja tsaki tare da furta." Sahura kin san Allah da sanya hannun mutumin nan wurin mutuwar Ya Aminu. Abban Yusi jajurtacce ne sosai ya yi masa bauta kwarai da gaske, kema kin san da haka ranga-ranga magashiyan aka kawo mini shi gida ciwonsa ya tashi sakamakon aikin da suka yini suna yi a kamfanin. Haka ya kwanta jinya, mutumin nan bai ta'ba zuwa duba shi ba, daga 'karshe ma sai kawai takardar sallama muka gani, wai an d'ora wani a madadinsa. Kuma babu ko sisi. Duk ranar dana tuna wannan wula'kancin sai na yi kuka. Sahura tun daga lokacin fa jikinsa ya sake rikicewa har sai da ya mutu. Ya ba zan tsane shi ba." Nasa hannu ina goge hawayen da suka zubo a kumatuna. Ta dafa kafad'ata cikin taushin harshe ta ce.'' Ki yi hakuri don Allah kin ga akan hanya muke, na yarda mutuwa d'aya ce, amma kuma tana da sanadi. Ki cigaba da yi masa addu'a. Sannan ki godewa Allah ni'imar da ya yi miki, ki tsananta da yi wa yaranki addu'a." Na ja hanci tare da furta." Sis, ba na sha'awar aure wallahi, ina jin tsoron mazan yanzu, ina ganin kamar ba zan samu mai nagartar Yaya Aminu ba. Sannan kin ga ina da yara ba kowane namiji ba ne zai yarda ya aure ni dasu ba. Ni kuma ba zan iya tafiya yawon aure na bar su a wani wuri ba." Ta tsayar mana da adaidaita sahu muka shiga. Ta ce." Kina da hujja Sis, amma fa kin san iyayenmu ba za su barki ki yi ta zama a haka ba, wand'anda suka fi ki shekaru ma suna yin aure ballantana ke da ki ke da talatin da wani abu. Kin ga a yanzu ne ki ke kan ganiyarki, amma zan yi miki uzuri idan kin ce ba za ki yi a yanzu ba sai yaranki sun girma tukkuna. Wannan kowanene zai iya duba hujjarki akan haka ." Kira ne ya shigo wayata dake cikin jaka. Na fito da ita da sauri ina dubawa sai na ga anti Yagana ce. Da sauri na daga tare da furta."Anti barka da Juma'a. Ta amsa tana fad'in." Mai yasa ne yanzu ba a samun wayarki ta dadin rai, sai a yi ta kira tana katsewa. Na ce." Sai dai idan matsalar network ne anti fatan duk kuna lafiya ya yarana?" "Kowa lafiya Lou alhmdullhi dama bikin babandi ne ya tashi satin da zamu shiga za a fara, na ce bari na gaya miki tunda an yi hutun makaranta ki zo ki shiga dangi, da yawansu suna tambayarki sai ki zo ku gaisa." Na ce." Zan zo kuwa in sha Allahu anti Babandi ai mutumina na ne, in sha Allah zan gayawa Babanmu idan na koma gida." "Kina Ina yanzu na ji kamar k'arar abin hawa." "Muna cikin adaidaita sahu ni da Sahura na rakata neman aiki a wani kamfani." Ta ce." To an dace dai ko?" Na ce." E, an dace anti." "Ki ba ni ita mu gaisa." Da sauri na mi'ka mata wayar. Bayan sun gama gaisawa ta mi'ko mini wayar muka yi sallama tana sake jadadda mini lallai na gayawa Babanmu maganar bikin da wuri idan da hali shi ma ya zo d'aurin aure. Ni ce na fara sauka a bakin titin gidanmu. Ita kuma aka wuce da ita. Ina sane ban kar'bi kudin da aka ba mu ba. Daf da zan shiga gida ta kira ni tana fad'in"Sis kudinki kin manta." Na ce." Ina sane Sahura ki ri'ke sai ki yi amfani da su." Ta ce.'" Amma ba ki kyauta mini ba wallahi. Kenan duk wahalar ke za ki yi mini." Na ce." Ina wahalar take ni ban ganta ba." Sai ta kashe wayar na san ranta ya baci da abinda na yi. Ina da kudi tunda ba a jima da yin salary ba, bayan haka kuma na yi jakkunkuna da yawa an kai mini kofar wambai. Don na barwa Sahura dubi biyar ba wani abu ba ne idan na yi duba da irin d'awainiyar da ta yi da ni a baya. Shaf na manta da maganar Ummasu Hadiza ina shiga gidan ko zaman minti goma ban yi ba ta leko tana cewa."Amina kin dawo?" Na ce." E, na dawo Umma." Ta ce." Babanku da ya shigo cin abinci ya sake jadadda mini maganar d'azu akan Alhaji Muktari." Na tashi zaune a nutse na ce." Umma ku yi ha'kuri don Allah ni fa ba aure zan yi yanzu ba, sai yarana sun girma tukkuna." Ta jim tana kallona kafin ta ce." Ni kuma sai na ke yi miki sha'awar auran Alhaji Muntari domin yana da rufin asiri gashi da kula da gida." Shiru na yi ban ce mata komai ba yadda zuciyata take tiriri zan iya furta wata maganar ta yi mata zafi. Sai ta juya ta fita tana fad'in." Wani lokacin arziki yana kiran mutum sai ya yi ta gudu, ina lefin Alhaji Muntari in banda abin Amina. Na koma na kwanta da nazarin yadda zan kawowa rayuwata da ta yarana cigaba. Da 'kyar na tashi na d'ora mana taliya Ina da miya dama na kan yi ta kwana biyu ko uku." Daf da magariba Yusi ya shigo shi kadai da ledar goruba a hannunsa. Na ce."Gwaggwo ce ta baka ne?" Ya daga kansa yana zaro kudi a acikin aljihunsa ya ce." Baba Hamusu ne ya ba ni dari da hamsin." Na ce." An gode masa, ina Kamalu yake?" "Mama tunda muka je gwaggo ta zuba mana abinci muka ci, sai aka neme shi aka rasa. Yanzu ma Baba Hamisu ne ya tsallako da ni titi, na 'karaso gida. Cikin fad'uwar gaba da fargaba na ce." Aka neme shi aka rasa kamar Yaya?" Ya yi shiru bai ce komai ba. Na d'auki wayata da sauri na nemi lambar Hamisu kanin Babansu ne. Muka gaisa na ce." Yusi ya dawo gida shi kadai, yana ce mini tun d'azu ba a ga Kamalu ba." Ya ce." E, wallahi ni ma dawowata gida kenan gwaggo take gaya mini, tunda suka ci abinci ya fita, amma ki kwantar da hankalinki zai dawo in sha Allahu, kin san halinsa ba ya zama wuri daya." Na ce." Hamisu Ya zan yi ne? Kamalu ne damuwata a halin yanzu, ka dubi shekarunsa ba su kai sun kawo ba, amma yana so ya fi karfina." Ya ce." Ki daina fad'in haka Anti Amina, duk yaran namu haka suke k'uruciya ce kawai, da ya kara shekaru zai daina. Sannan ki dinga tsinkaye kafin ki fad'i magana a kansa." A sanyaye na ce." Shikkenan Hamusu don Allah daga ya dawo ka kawo mini shi har kofar gida." Ya ce." In sha Allahu rabbi." Na kashe wayar na ajiye jikina duk babu kuzari na tace taliyar na juye a fulas. Idar da sallata kenan na ji kaya-kaya hayaniya na tashi a kofar gida. Yusi ya shigo da gudu yana fad'in." Mama wasu ne suka daddaki Yayana har sun fasa gefan ido suna ta ce masa 'barawo, 'yansanda sun riko shi." Gabana ya yi mummunar bugawa. Na tashi da azama na fita. Lokacin matan gidan da yaran duk sun yi waje. Kofar gidan namu ta cika da jama'a, ga Kamalu ri'ke a hannun 'yansanda da wasu yara su biyu a tsakiya. "Wacece mahaifiyarsa ne?" Muryar d'ansandan ta daki kunnane. Saminu ya nuna ni da hannu yana ce wa." Gata nan." Ya kalle ni." Yaron nan an kama shi ne yana yun'kurin 'kwacewa yaran nan kud'i an aike su sayan shinkafa a wurin mai awo na kan kwanar layin nan." Shiru na yi ban ce komai ba illa kaina da yake mugun sarawa. Ya cigaba da cewa." Ku dinga kula da yaranku, duk dai yaran yanzu sai addua amma dai duk da haka sai iyaye sun tsananta kula da addu'a. A dinga basu abinci duk rintsi kada a bar su da yunwa domin itama tana taka muhimmiyar rawa wurin gurbata tarbiyar yaro. Kasancewar shekarunsa basu kai matakin hukunci ba, za mu 'kyale shi. Amma da sharad'i idan ya sake shigowa hannunmu sai mun hukuntashi." Usaini 'kanina ce ya ce." Mun gode Yalla'bai in sha Allahu kuma za a kula, wallahi mahaifiyar yaron nan a tsaye take akansa maraya ne kuma mahaifinsa ya rasu, kawai rashin ji ne irin na mutumin yanzu." Ya zaro dari biyar a aljihunsa ya basu. Suka kama hanya suka tafi. Baba Sule ya 'karaso wurin Yana cewa." Tunda naga cincirindon jama'a a kofar gidan nan na san d'an iskan yaron nan ne ya janyo magana." Jin abinda yake fitowa daga bakinsa ya sanya na shige gida ba tare na tsaya gaishe shi ba. Gabad'aya suka shigo gidan har shi Kamalu da Yake rike a hannun Usaini Baba Sule yana kai masa duka yana ta zagi da aibata shi. Na kwanta hawaye masu d'umi suna bin gefen fuskata. Sai kawai na tsinkayi maganar Ummansu Saminu tana cewa." To dama ai ba dabararka ba ce ba kuma wayonka ba ne. Kullum dai ana ganin namu yaran sune lalatattu, to yau sai gashi kuma su Kamalu har da 'yansanda." Baba Sule ya ce." Shine dama d'an iskan cikinsu ai, za su zo su gurb'a ta mana zuri'a. Ita dai Ummansu Hadiza ba ta ce komai ba. Har ya gama zage-zagensa ya dago labulan dakina yana fad'in." Ke kina Amina." Shiru na yi ban amsa ba. Ya shigo d'akin sosai yana fad'in." Tashi zan yi magana dake." Na tashi ina goge hawayen da suka kasa tsayuwa. Ya ce." Ki mayar da yaran nan danginsu shi ya fi miki kwanciyar hankali, ki yi auranki tunda ba ki wuce ba, akan me za ki zauna ki lalata k'uruciyarki a banza, ba fa ke kike da hakkin kula dasu ba, dangin babansu ne suke da hakki a kansu. Ki kwantar da hankalinki, ki samu nutsuwa in sha Allahu idan ki ka auri Alhaji Muntari ba ke kadai ba, mu kanmu za mu ji dadi, domin mutum ne mai wadata da bushasha ko ni zan huta ta dalilinki." Na dube shi Ina 'kara ganin ba'kinsa a cikin raina. Na ce." Baba Sule ba zan yi aure ba, tunda ba farilla ba ne, musulunci da maslaha ya zo mana. Gaskiya yanzu Babu wannan ajandar a tare da ni, saboda inda da hujja. Bayan haka kuma ni ba yawon ta zubar nake yi ba balle ace ina neman janyo abin kunya, sannan ni nake wahala da kaina da yarana. Don Allah ku 'kyale ni da maganar auran nan haka." Cikin fushi ya ce." An ki a kyale ki din wallahi tallahi ba ki isa ba, sai kin yi aure Amina. Mu ba al'adar gidanmu ba ce haka iyaye da kakkani, ba za ki zauna mana god'od'o a gida ba." Na dube shi cikin rashin shakku na ce." To shikkenan zan nemi Babanmu da maslaha sai na je na kama haya, tunda ka ce ba zan zauna muku a g.......Ya bi kuncina da mari mai tsanani! Jikinsa na kyarma yake fad'in." Kin samu kudi ko Amina, kina ji babu wanda ya isa saboda ba kya nema a wurin kowa shiyasa ki ke gaya mini maganar da duk ta zo bakinki, wallahi ba ki wuce duka ba, zan zage gabad'aya karfina akanki na nakastaki muddin ba za ki bi umarninmu ba." Ina kuka haikan na ce." Zan fi son ka nakastani Baba Sule ni wallahi ka kashe ni ma, na gaji da wannan duniyar ba zan iya ba, me yasa lokacin da nake budurwa ba ku damu da aurena ba, sai a yanzu da Ubangijin da ya hallice ni ya ba ni za'bi. Ina da hujja Baba, ba wai ina gudun auran ba ne, akwai dalilina." Kuka nake tu'kuru Ina fad'in." Baba Sule ka dake ni, idan hakan zai sanya ka huce! ina so na mutu na riski Yaya Aminu a aljannar Firdausi." Kamalu ya zo ya ru'kunkume ni yana kuka. Shi ma dan'uwan nasa ya zo ya zube a jikina ya fashe da wani irin kuka mai soya zuciya....✍️ *1k on talgram via 0542382124..Binta Umar gtbank ko 7084653262...Binta Umar Opey bank mutanan nijar katin Airtel na dala dari* *08089965176* *07084653262* *What'sapp kawai!* [11/15, 9:38 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *TALLAH!* 'Yan uwa Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS, duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali. Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su Sandal flakes Hawee Gabgab Halut Dorot Coconut chips Dufr(farce) Black khumra Brown khumra White khumra Oil perfumes da Body sprays Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku. Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka Call/WhatsApp 07037489958 Location:Gonan Ganye,zaria Kaduna state Nationwide Delivery @Arewa books Bintuumarabbale. *Free pege* *6* Ya kama hanya ya fice daga dakin yana cigaba da fadin." Yadda ki ke ganin kin yi 'kwari a yanzu babu wanda ya isa ya gaya miki ki ji, to nan gaba idan ki ka fi haka za ki ce ba mu muka haifeki ba, ni Sule idan ni ne waliyinki to tabbas ba ki da miji sai Alhaji Muntari, domin ba za mu ta'ba bari wannan damar ta wuce mu ba." Duk cikin maganganusa babu wadda ta razana ni. Dole dai sai da yarda ta tukkuna za a d'aura mini aure, ba zan yi ba din saboda hujjata ta fi ta su karfi. Muryar Hamusu na tsinkaya a tsakargidan suna gaisawa da Ummansu Hadiza. Na ji dad'i da bai riski Baba Sule ba, lokacin ya tafi. ya shigo d'akin yana ce wa." Ina Kamalun yake?'' Jin haka ya sanya yaron da sauri ya zo 'buya a bayana ya fara kuka. Ya kuwa janyo shi ya fara gwaura masa mari wanda ya gigitashi ya k'wallara ihu! ya rike tsintsiyar hannunsa da kyau! yana fad'in." Mai kake so ka zama Kamalu? nawa shekarun naka suke a duniya da za ka dinga daga mana hankali, kai ba ka tausayin uwarka da take ta fadi tashi a kanku, ba zaka ri'ke maraicinka ba ko? idan ka yi wa Yaya Aminu haka ba ka yi masa adalci ba, sannan ba ka yi wa kanka adalci ba, kaf zuri'armu babu wanda ya ta'ba shiga hannun hukuma sai kai daga tasowarka zaka jaza mana abin bala'i da maganar mutane." Bai dubi ihun da yake kurmawa ba ya 'kara kai masa wani marin a d'aya kumatun. Ya kid'ime sosai yana fad'in." Don Allah Baba Hamusu ka yi hakuri ba zan sake ba. Wayyo Allah Ummansu Saminu ki zo ki cece ni." Ya rike shi da kyau! ganin yana ta kiciniyar fizgewa daga hannunsa. Ya ce.'' Wallahi ni ne maganinka Kamalu makaranta zan kai ka, a d'aure ka da sa-sari(mari!) ka je can ka zama almajira mahadaccin al'kur'ani, ba za ka d'orawa mahaifiyarka ciwo ba." Jin haka sai ya sake gigicewa yana fad'in." Na rantse da Allah ba zan sake ba, Baba Hamusu don Allah ku yi hakuri." Ya juyo yana kallona " Mama ki yi hakuri ba zan sake ba." Yusi yana kuka sosai kamar shi ya aikata lefin ya daddafa 'kafafuna har sai da na ji yadda jikinsa ya rawa. Ya ce." Mama ki yi hakuri, ki ce kin yafe masa, don Allah kada ki bayar dashi aka shi almajiranci kin ji mama." Wasu hawaye ne masu tsananin zafi suka kece mini. Tausayin yaran ya kara tsananta a cikin zuciyata. Haka suke yi a junansu mussaman shi Kamalun ya yarda ya ci zalin d'an'uwansa, amma bai yarda wani ya ta'ba shi ba. Ko a makaranta ne idan aka ci zalinsa a ajinsu ana tashi sai ya tare hanya har sai ya ramawa d'an'uwansa hankalinsa yake kwanciya. Duk lokacin da Kamalu ya yi lefi ina yi masa fada. Yusi shi yake shiga damuwa fiye dashi wanda ya yi lefin, ya dinga ba ni ha'kuri kenan. Ya je da rarrafe ya rike kafafun kawun nasa Yana cewa." Baba Hamusu don Allah ka yi hakuri ba zai sake ba, kada ka kai shi bara." Ummansu Hadiza ta le'ko tana fad'in." Hamusu ya isa haka, ai ya bada ha'kuri, dukan ba zai shiryar ba sai dai addu'a, kuma dai kowa da irin k'uruciyarsa. Tasa ce kawai ta fito fili, amma duk abokanan nasa haka suke da 'kin ji, ku yi masa addu'a kawai Allah Ya tsayar iya nan." Ya sake shi. A guje ya je ya ri'ke Ummansu Hadiza yana fad'in." Don Allah ki ce masa kada ya kai ni bara ba zan 'kara ba." Ta ri'ke shi tana cewa." Zan gaya masa, amma kai ma ka yi mini alkawari ba zaka sake k'wacen kud'i ba." Cikin kuka ya ce." Ba zan sake ba na yi alkawari." Sai ta ja hannunsa suka fita tana fad'in." Idan kuwa hakane ni ma ba zan bari a kai ka almajiranci ba." Ya juyo yana kallona a sanyaye ya ce." Anti Amina don Allah ki daina kuka, hakan zai sake jefa shi cikin wani yanayi. Ki dinga ko'karin sarrafa kanki. Wallahi tallahi ba ki fi mu shiga tashin hankali ba da damuwa ba, ba ki ga yadda Gwaggwo duk ta rud'e da jin abinda yaron ya aikata. Tana fad'in sai ta zo na ce ta zauna zan je ni na ji Ina aka kwana. Da kyar ta ha'kura. Ina zuwa kuma sai Usaini yake fad'a mini ai an kashe maganar. Ki yi hakuri ki cigaba da yi masa addu'a, in sha Allahu rabbi za ki huta da shi." Na yi 'ko'karin dakatar da hawayen da suke zuba. Murya a dashe na ce." In sha Allahu zan yi 'kokarin yin hakan Hamusu na gode sosai da kokarin'ka, Allah Ya shirye shi.'' Ya amsa da "Amin Ya Allah." Kafin ya yi mini sallama ya tafi. Da 'kyar na iya cin abinci saboda tsananin damuwa. Wajejan takwas da rabi. Babanmu ya shigo dama idan ya rufe shagonsa ba gida yake dawowa ba yana tafiya bakin titi wurin abokanansa tun na k'uruciya su yi hira. Ya shigo d'akin yana kiran sunana na amsa. Ya ce." Tun kafin na shigo gida jama'a suke yi mini jaje a hanya. Anya Amina yaron nan ba za ki mayar dashi hannun iyayensa ba, kada fa ya lalace a yi kuka da mu." Hanci na ja, a tausashe na ce." Baba ka yi hakuri da abinda zan fad'a maka don Allah ku bar ni na ri'ke yarana ba na so na yi ta jayayya da ku, Allah ne mai shiryarwa, in sha Allahu Kamalu ba zai lalace ba." Ya ce." Duk da haka dai. Kin san idan aure za ki yi babu namijin da zai ri'ke miki yara har biyu, ban 'ki ma 'karamin ba, shi wannan din da yake neman gagarar mutane ki mayar dashi can hannun kakarsa tunda tana raye." Shiru na yi ina nazarin maganarsa. Na san dama da wahala a samu namijin da zai aure ni da yara biyu. Wannan shine dalilin ma da ya sanya gabad'aya na ji auran ya fice mini daga rai, ba don komai ba sai don faruwar matsaltsalu bayan auran. Ba na jin zan yi aure a irin wannan yanayin gaskiya magana kenan. Maganarsa ta fargar da ni ashe yana tsaye bai fita ba. Ya cigaba da cewa." Alhaji Muntari yana kan hanya zai zo ku gaisa idan kin amince ba za a ja dogon lokaci ba, tunda dake dashi duka ba yara ba ne." Cike da tsananin damuwa na ce." Shikkenan Baba zan yi bincike a kansa, idan ya kwanta mini a rai sai a yi." Ya ce." Hurumin bincike ba a hannunki yake ba, mun riga mun gama bincike a kansa. Mutumin nan sananne ne, Ubangidan Babanki Sule ne, kuma yana da rufin asiri da dattako, sai ki godewa Allah wannan karon ba ki yi jinkiri ba. kuma ya ba ki miji mai wadata, idan Allah Ya yi ma don ya ri'ke miki yaran ba wani abu ba ne a wurinsa tunda yana da hali." Shiru na yi ban ce komai ba. Ya kama hanyar fita yana fad'in." Ba za mu bari wannan damar ta wuce mu ba, ni kuma ba zan zuba Ido na dinga ganinki a gida kina yi mini shige da fice ba." Shimfid'a na gyarawa yaran ina ta nazarin yadda rayuwar duniya take kwatantawa da ni. Babanmu da d'an'uwansa suna hango wadatar Alhaji Muntari. Suna ganin idan na aure shi zan huta suma za su huta, ni kuma akwai abinda nake hange. Tara saura na dare yaro ya shigo yana fad'in." Wai ana sallama da Amina." Ummansu Hadiza ta yi caraf ta ce." To gata nan zuwa." Na juya na dubi Yusi da yake bacci a shimfid'arsu har lokacin Kamalu bai shigo ba yana can wurin Ummansu Hadiza. Hijabina na zura ba tare da wata kwalliya ko fesa turare ba nasa takalmana na fita. Yana jingine a jikin motarsa babban mutum ne don zai yi shekarun Baba Sulen. Yana da ki'ba daidai misali da duhun fata Amma ba can ba. Ga dai tumbi nan ya ajiye irin na alhazawa. Yana sanye da shadda riga tazarce da hula a saman kansa. Hannunsa kuwa manyan wayoyi ne guda biyu. Cikin nutsuwa na iske inda yake tsaye. Ya saki fuskarsa Yana kallona tare da furta." Allah Ya sa ba daga bacci aka tashe ki ba." Na dube shi cikin tsanaki na ce." Bacci kuma karfe tara fa yanzu mun yini lafiya ya iyali." Ya gyara tsayuwa yana amsawa ya dora da cewa ." To ai ban sani ba ko kina da saurin bacci." Shiru na yi ban ce komai ba. Sai ya cigaba da cewa." Malama Amina na ji dadin ganinki a yadda nake hasashe. Sule ya jima yana ba ni labarinki. Na farko ha'kurinki da tarbiyarki, wannan ya kara kwad'aita mini jin sha'awar auranki a raina, ina fatan zuciyarki ta aminta da ni, domin ni ba da wasa na shigo ba." Ba tare da na dube shi ba na ce." Na gode sosai da yabo da fatan alheri, amma don Allah ka yi hakuri da abinda zan fada maka, wallahi ba zan iya aure yanzu ba sai nan da wasu shekaru tukkuna, idan ma Allah Ya 'kaddara ba zan sake wani auran ba hakan daidai ne a wurinsa. amma dai yanzu babu shi a lissafina ." Ya gyara tsayuwarsa a karo na biyu ya fuskance ni sosai Ya ce." Wace hujja ce dake da za ki furta wannan maganar. Amina guda nawa ki ke da za ki jingine maganar aure, ki ce ba za ki yi ba sai nan da wasu shekaru. lokacin kin tsufa kenan, babu namijin da zai yi marmarinki, ai aure rahama ne kuma ni'ima ne ba don komai ba sai don idan sha'awarki ta tashi ki samu wanda zai kawar miki da ita. Wallahi a shirye nake da na aureki, kuma na kula dake yadda ya kamata, idan matsalar yaranki ne, zan ri'ke miki su, ai d'a na kowa ne, ni ma ina dasu a gida sai mu had'a mu ri'ke gabad'aya." Ganin yadda ya rikice yana karyar da kai, da kalamai tausasa, sai jikina ya mutu. Na rasa abinda zan gaya masa domin ya gama kashe mini jiki, matsalata yarana kuma ya ce zai ri'ke mini su. A dan nazarin da na yi masa na hangi sona a tattare dashi. Kuma bai nuna 'kyama akan yarana ba kamar yadda wasu mazan suke yi idan suna son mace, sai su dinga k'yamar yaranta, suna nuna kishi, amma shi tashin farko ya amince zai ri'ke mini da alkawarin kula dasu kamar yaransa.. Jiki a sanyaye na ce." To na gode da nuna damuwarka, ina so ka ba ni lokaci zan yi shawara akan hakan, in sha Allahu duk abinda na yanke zan sanar da kai." Ya ce." Wannan ba matsala ba ce, amma ina rokonki don Allah ki yi shawara da mutanan arziki, domin kada ki yi da baragurbi su rud'a ki,wallahi da gaske nake auranki zan yi Amina, kuma zan kula da yaranki." Murmushi na yi na ce." In sha Allah, ni ba ni da k'awaye marasa tarbiya duk wad'anda nake mu'amula da su, sun san abinda suke yi, don haka kada ka damu." Ya ce." Ki ba ni lambarki zuwa gobe da safe idan Allah Ya kaimu, zan kira ki domin na ji Ina aka kwana." A nutse na fad'a masa lambar ya yi serving. Ya ce." Kin ga goma saura yanzu zan wuce gida, don Allah zuciyarki ta sa'ka miki alhari a kaina." Na ce." In sha Allahu, a gaishe da iyali." Na juya da zummar shiga gida ya dakatar da ni. Kudi ya d'auko a aljihunsa ya miko mini. Na girgiza kaina ina fad'in." Na gode amma ba zan kar'ba ba." Ya rausayar da kansa. " Don Allah ki kar'ba babu kyau mayar da hannun kyauta baya Amina, ki yarda da ni da alheri na zo miki." Hannu nasa na kar'ba tare da furta" To na gode sosai, A gaishe da iyalin." Ya amsa yana bud'e motar. Ni kuma da sassarfa na shige gida gaba na bugawa kad'an-kad'an. *1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank ko 7084653262...Binta Umar Opey bank* *07084653262* *What's app kawai* [11/16, 10:40 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A.* *TALLAH!* Albishirinku mata Yan gayu yan gwalisa kuyi maza kugar zayo shagon (Aysha/Addah beauty saloon and spa). Shin kintaba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba kiyi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu Wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa Suna wanke kai(wash and set) suna wanke qafa(pedicure) And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University gombe state Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka, 08037925676 Or 08167764242 Whatsapp ko kuma Call we’r available 24/7.. *@Arewa books* *Bintuumarabbale.* *Free pege* *7* Ko da na shiga gidan zaman minti biyar ban yi ba. Baba ya shigo yana fad'in." Kin je kun zanta to? Na fad'a miki da gaske yake, ina fata kun fahimci juna." Na ce." E, to Baba mun gaisa dai, amma fahimtar juna ai sai a hankali tukkuna, ina so ne komai a tafiyar da shi cikin nutsuwa Baba gaggawar auran sai ya haifar da d'a mara ido." Ya ce." Ki dinga kyautatawa kanki zato na alheri Amina, wannan mutumin na yarda dashi d'ari bisa d'ari, domin duk wanda zai bude baki zai fad'i alherisa." Shiru na yi ban ce komai ba. Ya juya zai fita yana cigaba da jaddada maganar. Na ce." Baba d'azu anti Yagana ta kira waya." Ya juyo da sauri yana ce wa." To, to Ina fatan dai lafiya? "Bikin Babandi ne ya tashi sati mai zuwa shine tace na gaya maka ko zaka samu zuwa d'aurin aure, ni ma zan yi kokarin halarta tunda an yi hutun makaranta." Ya ce." Zan je mana Amina muddin za ki yi mini kud'in mota me zai hana ni zuwa." Murmushi na yi na ce." To Baba zan yi maka kud'in mota sai ka zauna cikin shiri." Ya ce." Idan da kara itama Murja ki yi mata kudin motar mana sai mu ruguntsuma mu tafi tare." Na ce." Baba idan na biyawa Ummansu Hadiza kud'in mota hakan zai haddasa maka rikici, Ummansu Saminu za ta nuna rashin jin dadinta akan hakan, kawai dai mu tafi mu biyun." Ya ce." Hakane kuma, to babu damuwa Allah Ya nuna mana." Na amsa da '"Amin." Shi kuma ya juya ya fita daga d'akin. Na dubi shimfid'ar yaran nan ga Kamalu a kwance kusa da d'anuwansa. Na girgiza kaina, wato tsoron shigowa yake yi sai da ya tabbatar da na fita tukkuna. Na so a daran na rage d'inkunan mutanan da yake hannuna, amma damuwa da zullumin da nake ciki suka hanani katabus. Na yi zaune ina ta tufka da warwara akan lamarin da yake fuskanto ni. Na sake lissafa kudin da ya ba ni dubu goma sha uku ne, domin duntso su kawai ya yi daga aljihu bai lissafa ba ya mi'ko mini sabbi kar dasu. Mutumin nan da gaske yake aurena zai yi. To ni ba na hangen wadatarsa yadda rayuwar aurana da shi za ta wakana nake nazari. Ya ce yana da yara shin matansa nawa? wannan amsar dole tana wurinsa. Ya zanyi rayuwa a cikin gidansa da marayun yarana? Wace rayuwar zasu fuskanta. Wannan tunanin shi ya dami k'wa'kwalwata. Dukda Babanmu ya ce na dinga yi wa kaina zato na alheri. Amma ya zama dole ne na yi wannan nazari. Na dubi agogon da yake kafe a d'akin d'aya saura na dare. Gidan ya yi tsit. Na d'auki buta a nutse na fita Ina hirji. Na dauro alwala na ke'bance wuri d'aya domin kai wa Ubangiji kukana. Na jima Ina rok'onsa da ya kawo mini d'auki a rayuwata. Ya yi mini za'bi na gari. Na ninike daddumar cikin nutsuwa na shiga cikin net din yaran, na sanya a hannuna a cinyarsa na dan buge shi, ina kiran sunansa. Firgigit ya tashi zaune Hakan ya tabbatar mini da cewa dama bacci da yake yi rabi da rabi ne, a tsorace yake yi. Sai hawaye shaaa! suka fara bin kuncinsa. Na ri'ke hannunsa da yake ta rawa yana so ya fita daga cikin net din. A hankali na ce.'' Babu abinda zan yi maka Kamalu, ka samu nutsuwa tambayarka kawai zan yi, ga gaya mini gaskiya, idan kuma ka yi mini 'karya da kaina zan kai ka hukuma, idan sun hukuntaka sai na kira Hamusu ya zo ya tafi da kai tsangaya almajiranci." Hawayensa suka tsananta zuba. Ya had'a hannuwansa wuri d'aya yana fad'in." Mamanmu ki yi hakuri don Allah." A hankali saboda ina gudun kada sautin maganarmu ya fita. Na ce." Tona mini asiri za ka yi ko? me na yi maka kake kuka Kamalu, ni ce fa zan zubar da hawaye, amma ban zubar maka ba. Kana so mutanan gidan su ji abinda yake faruwa tsakanina da kai kenan?" Ya girgiza kansa alamun "A'a. Na ce." To maza goge hawayenka ka nutsu sai mu yi magana." Ya goge hawayen tare da rungume gwiwarsa da hannuwansa. Na dube shi cikin nazari da tsantsar tausayi da fargaba. Na ce." Bayan kun ci abinci a gidan Gwaggwo da ka fita Ina ka je?" A sanyaye Ya ce.'' bayan mun ci abinci sai Gwaggwo tace mu yi sallah. Bayan mun idar sai na ga tana gyangyad'i shine na fita. Ina tsallaka titi na ga Saminu ya ce na'ibawa zai je tsinto lemo ya siyar shine na bi shi muka tafi tare." "Kun tsinto lemon kenan?" "E, mun tsinto, amma ni ba'a sayi nawa ba wai duk ya ru'be ya lalace, shi kuma Saminu an sayi nasa amma ba duka ba shima akwai rub'abbu a ciki, ya samu d'ari shida, shine ya ba ni dari biyu." Na ce." To ya aka yi aka ganka za ka 'kwacewa Yara kudi an aike su auno shinkafa, Kamalu na yi maka sheda ko ni baka d'aukarwa kud'i idan ka gansu na ajiye, a garin yaya ka ke ko'karin jefa rayuwarka cikin wannan halin. Sata fa Kamalu kasan illarta kuwa?'' Hawaye ya kwaranyo masa ya ce." Saminu ne ya ce mini na je na k'wace musu sai mu raba, amma wallahi ban ta'ba yi ba Mama." Na zuba masa ido cikin nazari na ce.'' Kada ka yi mini 'karya fa Kamalu, ka san halin Saminu idan ya ji ka yi masa sharri ba zai yarda ba." Ya ce." Wallahi Mama shine ya tura ni. Shi yana samun kud'i sosai, haka yake yi, ko a makaranta sai an fita break idan wasu sun bar jakarsu sai ya je ya yi ta bincike idan da kudi ya d'auka idan babu sai ya kwashi littafai da biro. Muna tashi sai ya je ya sayar. Idona ya ciko da ruwan hawaye na yi kokarin dannesu saboda ba na son zubar masa dasu saboda kada masifar ta yi mana yawa ni dashi. Cikin wayo na ce." Yana baka kudin ne?" Ya ce." E, yana ba ni wataran kuma baya ba ni, amma dai idan mun je makaranta yana saya mana abubuwa." "A 'kafa ku ka je tsinto lemon har na'ibawa kuma ku ka dawo a kafa?" Ya daga mini kai alamun 'E' hawaye na zuba a kumatunsa. Na girgiza kaina jiki a mace na ce." To koma ka kwanta." Ya kwanta ya takure wuri d'aya Yana goge hawayen da suke karakaina a fuskarsa A hankali na fita daga cikin net din na jingina jikin bango(garu) ina nazarin abinda muka tattauna. Ba a shaidar d'an yau, Amma duk da haka zuciyata tana tabbatar mini da cewa Saminu Yana taka muhimiyar rawa wurin gur'bata mini tarbiyar yaro. Ya girmeshi ya fi shi wayo. Kuma muddin za su kwana a gida su wayi rabuwarsu za ta yi wahala. Duk lokacin da zan zauna da Kamalu na yi masa fada da nasiha yakan nuna nadamarsa ya yi ta kuka Yana ba ni ha'kuri akan ba zai sake ba. Amma ba a yin sati zai koma ya cigaba da d'auko mini magana. Babu yadda za a yi na fito na fadi wannan maganar a cikin gidan a yarda dalili kowa yana ganin fitinar Kamalu ta fi tsananta bayan ba haka ba ne. Ita Ummansu Saminu ta san yaronta ba ya ji, amma kullum cikin kare shi take ko abu suka aikata a tsakaninsu za ta cire shi tace ai lokacin da abin ya faru baya nan. Babban tashin hankali ne zai afku idan na fito na fadi cewa Saminu ne ya tura Kamalu yin 'kwace. Hawaye masu masifar zafi suka fara gararanba a kumatuna. Dole dai abinda ba na so shi zai faru. AURE Ina ganin shine zai nesanta ni da zaman gidanmu ko yarana za su samu ingantaciyar tarbiya. Ba na jin son mutumin a cikin zuciyata ko kad'an. A duniyar nan ma ba na jin akwai wani d'a namiji da zan so fiye da Yaya Aminu, zan aure shi ne domin katange kaina daga zargi da kuma tseratar da yarana daga rushewar tarbiya. Ina hasashen samun nutsuwa daga gare shi dalilin yadda ya nuna damuwa da kulawa da ni da yarana. Da kyar na runtsa saboda tunanin rayuwar da take fuskantoni. Ina idar da sallah na hau kan keke domin rage din'kunan da suke hannuna. Sai da na hada set uku tukkuna na sauka daga keken domin karyawa. Lokacin yaran sun tafi makaranta allo. Na karya a gurguje na yi wanka na nufi makarantar tasu. Bayan mun gaisa da malamin na fad'a masa abinda yake tafe da ni. Ina so a yi mini saukar al'kur'ani domin warwarewar matsalata. Dubu goma ya kar'ba a hannuna a matsayin sadaka za a dafa shinkafa da wake ga Wand'anda suka yi karatun. Cike da kwarin guiwa na dawo gida, a raina ina fad'in babu abinda ya gagari Allah komai da lokacinsa. Sai bayan na koma gida tukkuna na kunna wayata. Minti biyar a tsakani kira ya shigo. Sabuwar number ce. Ban yi mamaki ba tunda dama ya ce zai kira ni. Na daga a nutse da sallama ya amsa da sauri yana cewa." Ba kya kunna wayarki da wuri ne, ko ba ki da chaji ne?" Na ce." Ina da caji ba na kunnawa da wuri ne saboda wasu dalilai." Ya sauke ajiyar zuciya tare da furta." A a ranki ya dade ki dinga kunnawa da wuri domin kada wasu alheran su wuce ki, ba ki ji yadda na d'okantu da jin muryarki ba." Murmushi na yi na ce." Alhaji kenan, ina kwana ya iyali?" "Lafiya lau, iyali kuma duk suna nan lafiya, suna gaisheki da kyau, ina fatan yarana na wurinki suna cikin koshin lafiya?" Na ce." Suna lafiya, sun tafi makaranta." "To Allah Ya yi musu albarka, yanzu a Ina maganarmu ta kwana, ni dai da gaske nake, Amina ni ba yaro ba ne, ina da mata biyu Uwargidana tana da Yara biyar mata hud'u namiji daya. Ta biyun kuma tana da Yara hud'u duk maza, ke idan kin zo nawa za ki yi mini, domin har ga Allah ina so na hada garke da yawa, tunda Allah ya huwace mini." Jin maganarsa ta karshe sai jikina ya yi sanyi, domin har ga Allah ba ni da burin daga mun yi aure na haihu sai zama ya yi zama tukkuna na lura da kamun ludayinsa da iyalinsa. Shi kuma har ya fara maganar haihuwa. Ya yi gyaran murya yana cewa." Na ji kin yi shiru Amina, kada ki ce mini ba ki amince ba " Ajiyar zuciya na sauke na ce." Ba wai ban amince ba ne, ka d'an sake ba ni lokaci Alhaji zan je Maiduguri a can dangin Mamana suke zan yi shawara da Yayata, in sha Allahu zan kira ka na fad'a maka abinda na yanke." A sanyaye ya ce." Shikkenan, yaushe za ki tafi Maidugurin ne, sai na zo na kai ki." Dariya na yi na ce." Ka yi hakuri tare da Babanmu zamu tafi jibi in sha Allah." Ya nisa kafin ya ce." Da kin bari mu tafi tare sai dangi su gan ni, mu gaisa da juna." "Ka yi hakuri dai Alhaji a hankali za ku gaisa." Ya numfasa tare da cewa." To babu damuwa, amma zan iya bada kud'in mota ko?" Na ce." Ai ina da kudin mota ranka ya dad'e." "Ki ajiye na ki za su yi miki amfani ta wani gefan, ki turo mini acct d'inki zan sa miki kudin mota kin ji ko?" Cike da bada umarni ya kai karshen maganar. Na ce." To na gode sosai, Allah Ya kara budi, wannan lambar tawa Opey bank dina ne, idan ka cire ziron farko." Ya ce." To za ki ji ni, in sha Allahu rabbi." Yana kashe wayar ni ma na kashe na ajiye a hankali na lumshe idona ina ta so na tursasa zuciyata ta fara ganin haskensa......✍️ 1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank.. *07084653262* *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* [11/17, 9:51 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A.* *TALLAH!* 🌲🌳🌿☘️ *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* *@Arewa books.* *Bintuumarabbale.* *8* Duk yadda naso tursasa zuciyata ganin hasken Alhaji Muntari hakan bai samu ba. Domin na riga na gama amincewa da cewa da wahala na samu namiji da yake kaunata fiye da Yaya Aminu Ban sani ba ko saboda auran ya fice daga raina ne ya sanya nake ganin duhun duk wani namaji da zai ra'be ni. Shi kansa Alhaji Muntari zan aure shi ne domin kawar da 'kalabulan da yake tunkaro ni na rushewar tarbiyar yarona. Ina ganin idan muka bar gidan za a samu saukin wasu al'amuran. Da yamma ya kira ni yake gaya mini ya turo mini dubu talatin na duba na gani. Cike da mamaki na ce." Kudin sun yi yawa Alhaji jiya fa da ka zo ka ba ni wasu ." Ya ce." Babu matsala Amina ai ba rokata ki ka yi ba, ni na yi ra'ayi na baki, saboda haka babu Kalmar godiya a tsakaninmu." Jikina ya sake yin sanyi da sha'aninsa. Na ce." To na gode sosai, Allah Ya biya ka." Ya amsa yana cewa" Zan kira ki da daddare sai mu sake tattaunawa." Na ce." To shikkenan." Ya kashe wayar. Na yi shiru ina zullumi. Wato mai bushasha ne mutumin nan, wata'kila abinda Baba Sule ya hanga kenan ya rikice. Da daddare ilai kuwa sai gashi ya zo gidan. Ya shigo ya same ni a d'aki Ina aikin had'awa mutane d'inkunansu. Na gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake har yana tambayar su Kamalu. Na ce." Sun tafi makarantar dare. Ya nisa kafin ya ce." Ai yau Alhaji Muntari yake fad'a mini yadda ku ka yi, na yi miki murna domin mutumin kirki ne abinda nake miki sha'awa kenan, shiyasa na hadaki dashi, kuma ya tabbatar mini da cewa zai ri'ke miki yaranki duka biyun." A takaice na ce." E, haka ya fada." Ya gyara tsayuwa yana cewa." Yanzu yaushe ki ka yanke maganar d'aurin aure, kin ga shi fa babban mutum ne, ba na son shiririta." Na ce." Sai mun je Maiduguri mun dawo bikin Babandi." "To babu lefi, daga dai kun dawo din sai a yi magana, ba na so na zama dattijon banza ." Ni dai shiru na yi masa ban ce komai ba. Ya gama maganarsa ya kama hanya ya fita. *** Ranar da za mu tafi Saminu ya sanya rigima lallai sai an tafi dashi har da kuka. Babanmu to ya ce ya yi sauri ya shirya. Jin haka ya sanya na yanke shawarar barin Kamalu a gida tunda saboda za a tafi dashi ne yake rigima sai kace karamin yaro, gabad'aya haushi yake ba ni. Ba tafiyar da shi ne matsala ba halinsa ne abin gudu yaje garin mutane ya aikata son zuciya 'kan'kanin yaro dashi. Baba ya ce." Hakan ya yi, tunda tare suke wasa kin ga ba za a d'auke masa abokinsa ba. Shi ma Kamalun ya zauna. Ai ba wani jimawa za mu yi ba, kwana uku ne. Akan dole Kamalu ya ha'kura ya shige d'aki yana rusa kuka. Na rarrashe shi sosai tare da kwakwkwafarsa akan ya kula kada bayan bana nan ya d'auko mini magana. Da zamu tafi na bawa Ummansu Hadiza dubu uku nace idan za ta yi girki ta dinga zuba masa da kudin karin kummalo dana makaranta. Hakan ya 'bata wa Ummansu Saminu rai. Ko adawo lafiya ba ta yi mana ba har muka fita daga gidan. Yusi duk ya takura har da 'yar kwalla ganin mun tafi ba tare da d'an'uwansa ba. Anti Yagana ta yi murna sosai mussaman da ta ga har da Babanmu farincikina ya tsananta. A gidanta muka sauka tunda mijinta ba lefi yana da yar wadata direban babbar mota ne ta sauke mu da abinci mai rai da lafiya. Wajejen shida na yamma Babanmu ya fita zaga gari domin dama garin ba bakonsa ba ne, ya saba zuwa tun yana saurayi yake hada-hadar kasuwancin huluna tsakanin kano da maiduguri. Anti Yagana ta kalle ni a nutse ta ce." Na ga duk kwarmin Idonki ya zurma Amina ke da jikinki ya baya nuna rama amma wannan karon ya nuna wuyanki da yake cike da guru ya rairaiye akwai abinda yake damun ki ko?" Maganarta ta fama mini miki da yake yi mini ciwo hawaye suka fara kasa tsare a kumatuna. Ta ce." Ke dama can abin kad'an sai ki sa masa kuka, ba ki da juriya, idan matsalar gidanmu ce ya ci ace kin saba da ita, ki godewa Allah tunda baki rasa komai ba, kowane bawa fa da irin kaddararsa ." Cikin kukan da yake yun'kuro mini na ce." Anti Yagana ki sanya Kamalu a addu'a da sauran al'ummar muslimi bakidaya. Matsalarsa ce ta fi damuna a yanzu." Cike da damuwa ta ce." D'azu na so na hasashi wani abu da muna magana da Babanmu akan yaran gidan, amma ban kawo wani mummunan abu daga gare shi ba. Ki fad'a mini me yake yi da har zai zame miki matsala." Nasa hannu na gogewa hawayen da suke ta zuba a kumatunna. Na ce." Anti Kamalu da Saminu suna nema su fita zakka a zuri'ar gidanmu." Gabad'aya kaf na kwashe duk abinda yake faruwa na fad'a mata. Na cigaba da cewa." Auran dai da nake gudu shi zan yi anti saboda ina ganin kamar shine zai katange Kamalu da Saminu, tunda sun yi nesa da juna. Ta nisa kafin ta ce. " Kina da wanda ki ka tsayar ne? kuma kina da tabbatacin zai ri'ke miki yara har biyu Amina mazan nan fa basu da kirki kad'an ne suke iya kawar da kansu akan yaran da basu suka haife su ba, gashi idan suna nema sun iya dadin baki." Nasa hannu na goge hawayen kumatuna a sanyaye na ce." To anti ya zan yi ne? Baba Sule ya matsanta mini har dasu duka akan sai na auri Ubangidansa Alhaji muntari. Gashi kullum baya fad'in alheri akan yarana, zagi da gori irin Wanda baya yi musu." Cikin bacin rai ta ce." Kamarki Amina da shekaru talatin da yaranki zai fitar da hannu ya dake ki, me ya yi zafi, wai don Allah me yake damun Baba Sule ne, Ashe har yanzu bai canza d'abi'a ba, ai kin wuce duka." "Wallahi anti ba dukan ne ya fi damuna ba yadda yake zagin Kamalu Yana aibata shi da mugun fata shine abinda ya fi damuna." Ta gyad'a kanta cikin takaici ta ce." To yanzu me Babanmu ya ce akan maganar ni gaskiya lamarin bai kwanta mini a rai ba, na lura kudi ne suka rud'i Baba Sulen ya daga hankalinsa, ki nutsu sosai, kada ki yi gaggawa a zo ana lissafa miki aure Amina " "Anti Babanmu fa ya amince, kema kin san tuntuni kin sani bashi da katabus sai abinda Baba Sule ya zartar a gidansa. Kuma haka kowa zai ha'kura, tunda ya ji maganar Alhaji Muntari ya yi na'am da ita, yanzu maganar da nake miki daga mun koma gida za a yi maganar d'aurin aure." Ta zuba mini ido da damuwa mai yawa a tare da ita ta ce." To ke ya ki ke ganin kamun ludayin mutumin, ke ba yarinya ba ce Amina, ki zauna ki karance shi tsaf da dabi'u da halayensa sannan kuma na san ba zai rasa iyali ba." "Matansa biyu, da Yara takawas anti, ba lefi dai karon farko ya fito mini da kyawawan halayensa. Ya yi alkawarin ri'ke mini yara, sannan yana da sanyin hali da Kyauta, abinda na yi nazari akansa kenan. Anti kin san ai ba zai bud'e mini mununan halaye ba tunda nema yake yi zai danne sai zama ya yi zama tukkuna, amma ni shawarar da na yanke shine ba zan yarda na haihu ba tukkuna sai na ga kamun ludayinsa da zamantakewatarmu." "To kin yi shawara mai kyau anan, idan Allah Ya kaddara auran naku sai ki yi takatsantsan da kyau. Idan kin lura gidan zama ne, kuma tsayayye ne akan komai sai ki fara ajiye yaranki, domin yanzu mafi akasarin mazan yanzu auran dandano suke yi, ko kiga sun aureki da wata manufa, tafiya kad'an a fara samun matsala. Ba na fatan haka ta faru dake, sannan ki yi istahara akan sha'anin, Allah Ya tabbatar da alheri." Maganganunta suka sake karfafa mini gwiwa, na ji a raina zan iya auran mutumin koda ba na jin sonsa a raina zan zauna dashi muddin na fahimci cewa yana da nagartar da za a had'a zuri'a dashi zan saki jikina na haihu kamar yadda yake buk'atar Allah Ya wadata shi da zuri'a. Washe gari da wuri muka shirya muka nufi can family house su Mamanmu. Da yake 'yar dangi ce, gidan a cike mata da maza ana ta hidima. 'Yan'uwanta suka dinga murnar zuwa. Na shiga cikinsu sosai Muna gaisawa da tambayar bayan rabuwa. anti Falmata itace 'yar autarsusu sa'ar anti Yagana ce don Mamanmu da mahaifiyarta da muke kiranta da Dada sun had'a wankan jego tazarar da take tsakaninsu ta kwana tara ce. Ta shigo cikin irin shigarsu tana fad'in." Amina Idonki kenan ko? kin manta da mu a duniyar ko a waya ba kya kira a gaisa, duk wanda ya damu dake sai dai ya kira ki, idan kudin motar zuwa ne ba ki dashi ba sai ki fad'a a tura miki ba . Na ce." Wallahi ko daya antina, ayyukane sukayi yawa. Kin san ina koyarwa, Ina yin d'inki sosai na mata, bayan haka na kan yi huluna da jakunkuna akai mini kasuwa, ke har aikatau Ina yi wa mutane, wannan shine dalilin da ya sanya ba na samun lokacin kaina anti, ku yi hakuri." Dada dake zaune cikin kwalliya jikinta nanna'de da lifaya taci jan kunshi kafa da hannu. Ta harare ni tana cewa." Ke kya ji dashi dai, dama can ba kirki ne dake ba, kin fi karkarta can dangin babanki, sau nawa ana kawo ki nan tunda kuruciya ki dasa mana kukan safe daban na rana daban, ke sai kin koma cikin 'yan-uwanki da suke azabtar dake " Dariya na yi na ce." Dada ai lokacin da kuruciya. Kuma kin ga ku baku da k'ananun yara irina a lokaci sai Babandi, duk da ya girme ni dashi muke wasa. idan ya tafi makaranta ko gidansu sai na zama ni kadai, shiyasa nake yi muku kuka." Gyatsine baki ta yi ta kawar da kanta ba ta ce mini komai. Na yi dariya tare da mayar da hankali kan Ya Falmata dake cewa." Tunda kin zo kuma kin tabbatar mini dake tela ce, akwai atamfofina biyu da zaki dinka mini, sai dai fa kin san din'kunan mu sun sha bam-bam da irin naku." Ba tare da damuwa ba na ce." Nuna mini irin wanda ki ke so a waya, anti Allah ya yi mini fikira fa." Anti Yagana ta yi dariya tana fad'in." Lallai ni ma na yarda sai dai akwai saurin kuka." Ya Falmata tana dariya ta fito da wayarta ta fara nuna mini irinsu. Ban ta'ba yi ba don gaskiya zasu ja kayan d'inki da yawa a can idan na ce su biya ayi musu babu wadda za ta iya fitar da kudi kusan dubu ashirin da wani abu. K'arkari dubu uku dubu hud'u. Sai ta yi wuta tukkuna suke iya biyan dubu biyar ayi musu d'inki. Na ce." Anti an yi an gama in sha Allahu muddin akwai kayan d'inki ai abu ne mai sau'ki a wurina." Ta ce." Duk abinda ake buk'ata yanzu zan aika kasuwa a sayo." Na ce." To shikkenan ni kuma in sha Allahu rabbi kafin dare na kammala miki. Cikin farinciki ta ce." Zan yi magana da Maman Sabir yanzu ma'kociyata ce tana da keken d'inki sai ki shiga gidanta a nutse ki yi." Na ce." To shikkenan antina....✍️ *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* [11/18, 6:12 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A.* TEEMAH DATA SERVICES MTN 1GB @550 2GB @950 3GB @1450 4GB @1550 5GB @1700 CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306 8037026306 fatima musa ibrahim opay *@Arewa books* *Bintuumarabbale.* *Free pege* *9* A ranar yini na yi akan keke don duk wanda ya zo sai ya tambaye ni. Ango Babandi ya biyo ni har gidan muka sha hira irin ta zumunci. Shi din ba sa'ana ba ne, amma akwai sha'kuwa mai 'karfi a tsakaninmu kasancewar tun ina k'arama idan an kawo ni garin dashi muke wasa. Shine babban jika na d'a namiji a gidansu Mamanmu. Babansu shine babba a gidan, sai Baban Saude shine na biyu. Na saki jiki sosai ina tsokanarsa amaryarsa tafi shi kyau shi ba'ki ne kamar shuni ita kuma kamar ka matsa jini ya fito. Ya dinga dariya yana fad'in ." Ai ganganci ne na auri bak'ar mace, ba zamu haifo yara bakake ba gwara a surka." Na ce." Ai yanzu an fi yayin bakar mace, mazan ma duk sun gane, abinda wasu farin nasu na mai ne, ko da yake dai ita wannan amaryar taka ma tana yi mini yanayi da bafulatana." Ya ce." Fulani ne usul gabansu da bayansu. hausarta ma bata fita sosai." Na ce." Ai na ga alama, Babandi Allah Ya sanya alheri. Shekara mai zuwa mu dawo suna." Ya amsa da "Amin Yana gyara tsayuwarsa ya ce." Ke wai yaushe za ki yi aure ne, na san dai ba kya rasa mane ma." Hankalina yana kan abinda nake yi na ce ." Duk ranar da Allah Ya nufa zan yi, Babandi aure da haihuwa da mutuwa duk na Allah ne, amma ina mamaki naga ana titsiye mace wai ana tambayarta yaushe za ta yi aure, abin yana daure mini kai wallahi." Ya ce." Hakane gaskiya, amma fa sai kin sanya abin a ranki tukkuna. Allah Ya ce ka taimaki kanka ni ma zan taimake ka, Amina tunda mijinki ya mutu na ga take takenki ba kya son ayi miki maganar aure ." Dariya na yi na ce." To ai auran ne ya zama abinda ya zama Babandi, da wahala yanzu na samu mai sona tsakani da Allah kamar Yaya Aminu. Wallahi gabad'aya mazan basa burge ni balle na ji sha'awar auran, ko ka ga na yi to Allah ne ya kaddara." Ya dube ni a tsanake ya ce." Mu cire maganar wasa anan Amina, wanda ya mutu fa ya riga ya mutu, kada ki tauyi rayuwarki da k'uruciyarki, ki ce za ki zauna haka, ko bayan haka ma kina da sha'awa irin wadda Allah Ya 'kaddarawa bayinsa, aure shi zai katange ki daga fad'awa wani halin." Na numfasa tare da ce wa." Babandi ban san me yasa rashin aurena yake damun mutane ba wallahi. Sai na ga 'yan mata suna zaune a gaban iyayensu ba a matsa musu ba sai zawarawa. Duk wanda zai dube ka sai ya yi maka wata fahimta. Babandi ka ganni nan wallahi babu wanda yake yi mini wahala ni nake yi kayata. Kuma ina kula da kaina sosai bana taba barin wata kofa da zata janyo mini 'bacin suna. Sana'ata kawai na sanya a gaba, a yanzu burina yarana su yi wayo Allah Ya taimake ni su tsaya da kafafunsu, su samu ilimi da tarbiya. Sai na ji dadin auran." Ya harareni Yana furta." A lokacin kin tsufa kenan, kina maganar shekara ashirin fa anan gaba Amina. Lokacin kin yi hamsin, wane namiji ne zai yi kwad'ayin auran tsohuwa." Na fashe da dariya ina cewa." Shikkenan ka ga sai na k'arasa rayuwata a haka, dama ba na so na yi aure ranar lahira na tashi a matar wani, nafi so na tashi a matar uban yarana." Ya ce." Wannan ba hujja ba ce Malama sai kin yi aure fa, idan ba ki da tsayayya a cikin abokaina akwai wanda yake son kari, idan ma ba za ki auri mai mata ba akwai samari. Tunda Allah Ya sa kina da jiki mai kyau na san da gudu za a aureki." Na ce." A a ba sai ka kawo mini kowa ba. Na kusa in sha Allahu. Akwai wani mutumin Ubangidan Baba Sule a kasuwa, akan maganarsa muke ina fata zaka tayani da addu'a Allah Ya sa alheri ne. Wata'kila ma ina komawa gida da 'yan kwanaki ku ji labarin d'aurin aure." Cike da farinciki ya ce." To Alhamdullahi, ina taya ki murna da fatan alheri, Allah Ya sa idan kin shiga kin shiga kenan, Allah Ya kad'e fitina." A takaice na amsa da Amin." Maganarsa da muka yi yanzu ita ta tuna mini da wayata dake kashe. Jiya da daddare bayan mun gama waya dashi na kasheta ba don komai ba sai don gudun kada ya kira ni ina cikin jama'a, na lura kuma shi yana son yawan waya kamar matashin saurayin da yake da sabuwar budurwa. Ni Kuma sabgogina sun isheni zaman yin wayar nan ba ni dashi, don sai na ga kamar batawa kai lokaci ne. Sai da na koma gidan anti Yagana tukkuna na kunna wayar bayan na gabatar da sallar isha'i. Jikina ya yi tubus gajiya ta dirar mini, ta zaman mota da zaman keke. Bacci ya fara surata, Yusi Yana can cikin yaran anti. Da yake Yana da saurin sabo ya sake dasu duk inda zasuje sai su ja shi. Anti Yagana ta shigo tana fad'in." Ga abinci nan na tawo mana dashi, idan za ki ci sai ki fito ki d'iba." Na ce." To shikkenan anti Gajiya ce ta addabeni wallahi." Tana ko'karin fita daga d'akin take cewa." Ai dole, zaman mota da zaman d'inkin nan da ki ka yini kina yi. Ki sha Panadol mana." Ido a lumshe na ce." Anti ba na so na sabawa kaina da shaye shayen maganin nan, gari Ya na wayewa zan warware." Ta fita daga d'akin ba ta ce komai ba. Ina jin kiran waya na san wanda nake tsammani ne. A nutse na daure na daga wayar da sallama a bakina. Ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa." Wato saboda kin lura na kamu da sonki shine za ki yi mini jan aji ko Amina, da alheri fa na zo gare ki, ba zan cutar dake ba." A sanyaye na ce." Ba haka ba ne wallahi, yau na yi ina wani uzuri ne, shaf na manta ban kunna wayar ba sai yanzu, amma ka yi hakuri, kuma ai ka bari mu gaisa ko." Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu Ya furta." Dukda haka dai ba ki damu dani ba Amina, ai jiya kafin mu yi sallama kin yi mini alkawari za ki kunna wayarki, sannan Zaki sanar da ni shawarar da ki ka yanke akan sha'aninmu. Amma gari Yana wayewa na ji waya a kashe, yini na yi cikin zullumi wallahi." Yadda yake tausasa murya da lallashi. Sai Yaya Aminu ya fado mini a raina. Kwalla ta taru a idona. Shi ma haka yake yi mini wasu lokutan ma ni na ce da laifi amma sai ya mayar dashi kansa yayi ta rarrashina. Nasa yatsa na goge kwallar da ta fara zuba. A sanyaye na ce." Ai na bada ha'kuri Alhajina, a yi mini afuwa ba zan sake ba." Ya ce." Na yi miki afuwa, amma ki dinga kira na kina jin lafiyata Hakan shi zai tabbatar mini da cewa kin damu da ni." Murmushi na yi na ce. " In sha Allahu rabbi zan yi Hakan, sannan albishirin da zan yi maka shine na amince da auranka. Daga zarar na dawo sai mu tsayar da magana." Cikin wani irin yanayi na farinciki da karsashi yake furta." Alhamdullahi. Allahamdullahi, na gode Allah Amina, ni ma albishirin da zan yi miki shine idan an daura auranmu zamuje saudia mu yi godiya ga Allah." Cikin jin dadi na ce " Aikuwa na gode sosai da wannan karamcin, Allah Ya kara suttura, Ya kuma raya zuri'a." Ya amsa da "Amin cikin walwala da farinciki, yadda yake nunawa shi yake sake tabbatar mini da cewa 'Sona yake yi bilhaki da gaskiya' Ba auran dandano zan yi da ni ba. Zuciyata ta kara aminta da auransa na san a hankali idan da kyautatawa soyayyarsa zata shiga cikin zuciyata. Muka yi sallama cikin mutumci da kulawa. Bacci ne ya d'auke ni mai nauyin gaske anan na bingire ba tare dana hau katifar dake shimfide a gefe ba. Wajan sha biyu da rabi anti Yagana ta tashe ni. Wai na hau katifa kada jikina ya yi ciwo. Sama sama nake jinta na ja jikina na hau katifar na kwanta ta kashe fitilar d'akin ta fita. Gefin asuba na tashi na zauna gabad'aya dan'kon baccin ya saki idona. Gabana ya dinga bugawa. Wani mafarki na yi mara kyau wai ga mutane a kofar gidanmu a tsaye anata hayaniya. Wani Yana cewa a tafi a nemo Kamalun duk inda ya shiga. na sauka daga kan katifar na nufi bandakin da yake cikin d'akin cikin sanyi jiki da kiran Innalillahi wa'ina ilaihi! Ban kwanta da abin a Raina ba ballantana na ce. Gabad'aya sai hankalina ya yi gida don mafarkin ya tsorata ni sosai. Muna karyawa da Anti Yagana na ce." Jira nake Babanmu ya tashi daga bacci anti yau za mu tafi tunda an daura aure, na bar din'kunan mutane wallahi, ga Kamalu, kin san abin sai a hankali." Ta ce." Malama kya bari dai sai gobe wace irin tafiya ce wannan da gaggawa haka, Shi ma Babanmu haka yace sai gobe sai ku tafi a nutse, jiya ai mun jima dashi da daddare muna hira. Kiran waya ya katse maganar da zan yi. Ina dubawa na ga Usaini. Gabana ya buga. Hannuna na rawa nasa a kunnena. Ya ce." Anti Amina an tashi lafiya? Yau za ku dawo ko?" Na ce." Lafiya Lou, wata'kila yau ko gobe, ina fatan dai lafiya, ina Kamalu ka bashi wayar mu gaisa." Ya yi shiru bai ce komai ba." Cikin mi'kawa Allah lamarin na ce." Usaini tunda na ga Kiranka na tabbatar da matsala, ka fad'a mini kawai, abinda ba sabon abu ba ne, me ya faru?" A sanyaye ya ce." Anti abin ne babu dadi wallahi, da har na ce kada a gaya miki. Ummansu Hadiza ta ce a fad'a miki kawai, ki san abinda yake faruwa." Na daga kai ina kallon Baba lokacin yana ko'karin shigowa. Na ce." Usaini gaya mini don Allah, ba na son kwane kwane Kamalun mutuwa ya yi ne?" Ya ce." A a, da asuba ne da aka tashe su shi da Saminu domin su yi sallah, bayan sun fito daga massalaci sai suka je tu'ka-tu'kar kofar gidan Alhaji Lawan. Suka kwashe jarkokin mutane har da sababbi sun kai goma suka had'a da zungureriyar kurar ruwar wani dan garuwa. Suka nufi cikin kasuwa, su uku Saminu Kamalu da kuma Shamsu 'kanin Bashir abokina. To Allah dai Ya rufa asiri ba su sayar ba, Malam Maharazu na bayan gidanmu ya shiga kasuwar da wuri shine ya gansu a gurin masu sayarwa ana ta ciniki, to da yake akwai police station ana gane sato wa suka yi, gabad'aya su ukun aka kama su suna can a cell a kulle." Ajiyar zuciya na sauke na ce." To Usaini Allah Ya kyauta, idan hali ya yi za mu iya dawowa yau, idan kuma hakan bai samu ba sai gobe idan Allah ya nufa ." Ya ce." Shikkenan anti Amina, amma don Allah ki kwantar da hankalinki, na sanki da sanya damuwa a cikin rai, kin ga ba ke kad'ai ba ce, wallahi ba ki ga yadda Ummanmu take kuka ba yanzu ta yadda da cewar Saminu shine shugabaa cikinsu." Na ce." To, zan danne Usaini, ba zan sanya damuwa ba, na gode kawai zan kira ka idan an jima, yanzu ya mu tattauna da Babanmu." Na kashe wayar na dube su. Gabad'aya hankalinsu Yana kaina, ba sai na yi musu karin bayani ba sun ji komai tunda handsfree na sanya wayar rad'au duk sun ji komai. Anti Yagana ta fashe da kuka tana fad'in." Wannan wace irin masifa ce, yaran nan suke nema su janyo mana, jarkokin ruwa uban me za su yi da kudin idan sun sayar, Yara k'ananu dasu." Na bita da kallo ban ce komai ba, domin a lokacin ma ni kaina kullewa ya yi na rasa tunanin me zan yi, na san dai tun lokacin da Usaini ya fara yi mini bayanin abinda yake faruwa wani abu mai nauyi ya tokare mini a wuya. Babanmu ya dubeta Yana fad'in." Ai ba sabon abu ba ne Yagana ke yanzu ki ka ji shine dalili. Ki daina yi musu kuka, yi musu addu'a kawai, Allah Ya tsayar musu iya nan, kuruciya ce kowa da irin tasa." Tana goge hawaye wasu na sake zubowa. Gabad'aya ta rikice sai Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un take yi. Ya dube ni yana cewa." Tashi ki shirya mu tafi a samu a fito da su, zaman cell din ma wata masifar ce, bari na fita na yi sallama da jama'a." Ya tashi ya fita da saurin gaske. Na dubi anti Yagana da kanta yake a sunkuye hawaye na zuba tana sharewa na ce." Ashe ba ni kad'ai ba ce mai saurin kuka." Ta kalle ni, na yi murmushin da babu nishadi a cikinsa. Na tashi kafafuna na rawa na shiga d'aki na fara had'a kayana. Cikin zuciyata ina ta kiran sunan makagina da ya kawo mini d'auki *** Tafiya ce muka yi ta a gigice cikin rashin kintsi shiyasa ba kowa muka yi wa sallama ba. Allah Ya nufa muka samu mota mai kyau da rashin tsaye tsaye. La'asar sakaliya muka sauka a tasha nan kasuwar kwari. Na kira Usaini domin jin karin bayani. Ya ce mini ai har yànzu yaran suna can cell a rufe domin jama'ar unguwa sun ce sai an shiga kotu an hukuntasu tunda an jima ana sace musu kayan ruwa." Na ce." Kai kana ina yanzu, ko kana shago ne?" Ya ce." E, ina shago anti kin san Babanmu da zaku tafi ni ya barwa dan mukkuli, idan an samu aiki na yi, nake basu kudin abinci, yanzu haka ma akwai aikin mutane a hannuna." Na ce." To yi zamanka tunda kana da aiki, amma ka samu wani ka turo shi muna nan tashar kwari, ya zo ya d'auki kayan nan zan bashi kudin mota." Ya ce." To yanzu kuwa anti." Na kashe wayar. Na dubi Babanmu da yake tsaye a jikin wata tumba ta wutar lantarki, tausayi ya ba ni kwarai, haka dai na daure na yi masa bayani duk yadda muka yi. Ya ce." Ai dama da wuya jama'ar unguwar nan su ha'kura, kin san babu had'in kai, idan matsala ta faru a maimakon a had'u a kashe wutar sai a samu wasu a gefe suna rurata. Yaran nan kowa yana dasu sai addua." Na ce." Baba tafi gida ka huta, ni zan wuce station din, in sha Allahu abin ba zai yi girma ba." Ya ce." A'a, ba zan bari ki je ke kadai ba, mu je tare Amina, idan da namiji abin zai fi yin kyau." A sanyaye na ce." To shikkenan Allah Ya taikaita, su kuma Ubangiji Allah Ya shirya mana su." ya amsa da "Amin Ya Allahu......✍️ *1k on talgram* *0542382124...Binta Umar gtbank* *07084653262* [11/19, 9:07 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *Marubuciyar* *Yar bangar siyasa* *Ba'aboren namiji* *Madadi* *Ga irinta nan* *Goje* *Babban yaro* *Sadauki Omar* *Nida Yaya sadam* *Da sauransu..!* *TALLAH!* 'Yan uwa Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS, duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali. Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su Sandal flakes Hawee Gabgab Halut Dorot Coconut chips Dufr(farce) Black khumra Brown khumra White khumra Oil perfumes da Body sprays Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku. Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka Call/WhatsApp 07037489958 Location:Gonan Ganye,zaria Kaduna state Nationwide Delivery *Free pege* *10* *@Arewa books* *Bintuumarabbale* Lokacin da muka isa station din yaran suna cikin cell a rufe. Wani d'an-sanda ya ce maza a sayo musu abinci domin tunda aka rufe su da asubahin babu wani abu a cikinsu. Na fito da dubu d'aya na ba wa wani 'karamin ma'aikaci daga cikinsu ya je ya sayo musu abinci da ruwa ya shiga ya kai musu. wanda case din yake hannunsa ya yi mana bayanin duk yadda suka yi da mutanan unguwarmu. Shi ma ya so maganar ta mutu ganin yaran kananu ne amma wasu daga ciki suka ce ba su yarda ba, kamar dai yadda Usaini ya fad'a suna cewa an jima ana yi musu sace-sace a cikin unguwar. Babanmu ya ce bari ya je ya samu mai unguwa zai dawo yanzu. Ya tashi ya fita da saurin gaske. Ina zaune ina kallo ana ta shigowa da masu lefi har da mata daga cikinsu akwai wadda na kusa zubarwa da hawaye budurwa ce duka bata wuce shekara sha shida ba take sace-sace. Matar da suke zaune a gidanta haya tana sana'a idan ta fita unguwa yarinyar sai ta shiga d'akinta ta k'asan 'kofa da yake akwai rara ta sace mata kud'i sai yau da dubunta ta cika ta kamata. Da aka tambayeta tana kuka tace Mamanta ce take turata ta d'auko kudin sai su sayi abinci. Koda aka tambayi uwar ba ta yi jayayya ba tace hakane. Ita kuma matar da suke zaune a gidan nata tana ta rantsuwa wallahi sai ta yi 'kararsu a kotu tunda duk abinda take yi musu basa gani sai sun cutar da ita. Dubu hamsin da biyu ta d'auke mata Allah Ya sa ba su ci da yawa ba. Aka lissafa dubu hud'u suka ci, na zaro a jakata na bata. Na ce. " Don girman Allah ki dubi maraicin yarinyar nan ki rufa mata asiri, kada ki fitar da maganar nan, wanda ya suturta wani Allah zai suturta shi. Dan kuskure ta yi, haka nan mahaifiyarta amma ki yi hakuri, idan ya so sai ki tashe su daga gidanki, Amma dai maganar nan ta mutu anan." Ta yi shiru sai huci take yi. Uwar da d'iyarta Kuma sai kuka suke yi. Na ce." Ke kuwa baiwar Allah ba kya jin tsoron ranar da Ubangiji zai tuhumeki akan abinda ya baki kiwo. Kada fa ki manta yarinyar nan amana ce a wurinki ki bar ganin ke ki ka haife ta, tana da hakki a kanki, haka zalika ma Allah Yana da hakki a kanki, me yasa za ki dinga tura ta tana yi sata, ki lalata mata rayuwa. Ba zaku nemi taimako ba? Ke me yasa ba kya yi sai ita, ki ji tsoron Allah, kuma ki yi nadama akan abinda ki ka aikata." Ta share hawayen da yake gudana a fuskarta tana fad'in." In sha Allahu zan kiyaye wallahi rashin yadda zamuyi ne ya sanya shaidan ya ribaci zuciyata, amma na yi alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba. Na ce." To Ubangiji Allah Ya yafe mana gabad'aya, Allah Kuma ya shirya mana. Jami'in ya gama rubuce rubucensa ya tura su wurin d.p.o domin ya sake yi musu sulhu. Ina nan zaune suka shiga suka fito. Muka yi sallama suka fita. Jin shiru Babanmu bai dawo ba ya sanya hankalina ya tashi. Don ba na k'aunar yaran nan su kwana a wurin nan, ina so a samu maslaha. Na kira Usaini a waya domin jin Ina aka kwana nan yake tabbatar mini da cewa suna nan tafe gabad'aya har da mai unguwa." Na kashe wayar zuciyata gabad'aya babu dadi. Koda suka so station din zama aka yi sosai a office din D.P.O aka fito da yaran gabad'aya sun firgice yini daya da suka yi a rufe. Har da yar rama a tattare dasu. Gefan idon Kamalu ya dan tasa kamar duka kamar kuma alamun kuka. Kallo daya na yi musu na kawai kawar da kaina. Da 'kyar aka samu sasanci. Amma dukda haka d'angaruwar nan sai da aka biya shi kud'in taya da wili acewarsa ba a haka ya ajiye kurar ruwansa ba. Kudin beli dubu talatin. Suka buk'ata Kowanne dubu goma gabad'aya kudin hannuna basu wuce dubu sha uku ba. Babu yadda za a yi na yi belin mutum biyu na bar dayan. Tare suke shashancinsu, bayan haka ma iyayensa ba su da wani karfi ta abinda za su ci suke yi. Na bada abinda ya rage a hannuna na fita na ciro sauran na na cika musu sannan suka ba mu yaran muka kama hanyar gida lokacin tara saura na dare. Lokacin da za mu shiga gidan ne na lura da dinginshin da Kamalu yake yi shi da Saminu sai ra'be-ra'be suke yi suna bin bango. Usaini kuwa sai talle musu keya yake yi. A haka muka shiga gidan duk suna tsaye cirko cirko. Na bude d'akin na shiga na zauna 'kafafuna har yanzu ba su daina rawa ba. Tun ina jin hayaniyarsu har na daina ji tabbacin kowa ya watse ya kama abinda yake gabansa. Na tashi na le'ka tsakargidan ta tagar dakina. Sai na gansu su biyu a zaune a tsakargidan su kad'ai. Shi Kamalun Yana ra'kube a kuskurwa ya rungume gwiwarsa. Yusi din yana gurfane a gabansa Yana kuka. Na daure zuciyata sosai na ce." Kai Yusi kukan me kake yi ku taso daga nan ma." Ya kalleni da sauri yana cewa." Mama don Allah ki yi hakuri kada ki dake shi, jikinsa da ciwo da kafarsa ta kumbura, ya ce ba zai sake yi ba." Na ce." Ai ba zan dake shi ba, ku taso ku dawo d'aki." Ya riko hannunsa yana cewa." Yaya ta so mu je, ta ce ba zata dake ba." Ya dago kansa ya kalleni. Na ce." Ta so ku shigo ba zan dake ba." Sai hawaye shaaa! suka fara zubowa daga idonsa. Na d'auke kaina da saurin gaske na bar jikin tagar. Rigijib haka na zube kan tabarmar duk ko'karin da nake yi wurin danne masifaffan kukan dake ta damuna kasawa na yi. Ya kufce da karfin gaske na sanya hannu na toshe bakina. Na silale na kwanta ina kukan haikan tare da tunanin ranar da Allah zai yaye mini k'uncin dana ciki tunda ga kuruciya. MAFARI Malàm Salisu mai hula shine mahaifinmu. Mutum ne mai ha'kuri da sanyin hali. Uwa uba kuma mara son hayaniya domin da wahala wata hatsaniya ta tashi a cikin unguwarmu ka ji sunansa a ciki. Ya kan kokari wurin ganin ya kama girma da mutumcinsa. Yadda ake fad'a tun yana k'arami ya tashi da zuciyar neman na kansa . Dalilin da ya sanya ma kenan ya fara fatauci zuwa gari gari kai huluna. Sai da Iya mahaifiyarsu ta nuna rashin yardarta da hakan tukkuna ya ha'kura. amma dukda hakan fataucin ya janyo masa alherin arzikin had'uwa da uwargidansa wato Mamanmu kenan mai suna Saratu. Asali Maiduguri kowa ya san gari ne da ake sana'ar huluna irin daban daban. A nan garin Allah Ya had'a shi da Mamanmu a kasuwa ta je sayayya kusa da shagon da yake zama ya gudanar da sana'arsa. Ba a ja dogon lokaci ba da suka aminta da junansu soyayya ta kullu sai iyaye suka shiga cikin lamarin aka gudanar da bincike ta kowane bangare babu wata matsala waliyan Babanmu suke shige gaba har garin borno aka dauro aure. Babanmu bashi da matsalar wurin zama tunda mahaifinsu su uku kacal ya haifa kuma kafin rasuwarsa sai da ya bawa kowa wurin zama. A gidansa da yake unguwar kabuga cikin kwaryar birnin Kano Mamanmu ta tare da komai na al'adarsu. Sun yi farinciki sosai a lokacin da suka ga wurin zamanta ya yi kusanci da gidan aminiyar Dada wato mahaifiyarta. Suka dinga godewa Allah da ya sanya akwai wadda za su barwa amanarta a garin. To Gwaggo maihaifiyarsu Yaya Aminu itace ta zama uwardakin Mamanmu kuma uwa a gare ta. Mamanmu ta jima bata haihu ba. Hankalin Babanmu ya tashi don ganin yadda 'kaninsa Sule daga yin auransa har ya haihu. Kun san dai zama irin na Malam bahaushe. Babanmu ya fara wasu dabi'u. Ya canza gabad'aya. Gashi dai bashi da wani karfi kullum da 'kyar suke kai labari amma a hakan ya fara fafutukar kara auran wata bazawara. Ashe a lokacin Mamanmu tana da ciki ba ta sani ba, Shima bai sani ba. Tsabar tashin hankalin da take ciki ya gigitata ta kasa gane halin da take ciki. Ita macece mai bala'in kishi. Dalilin da ya sanya ma kenan ta figale ta lalace koyaushe ita da mijinta babu zaman lafiya. Shi kuma a lokacin idonsa ya rufe da son haihuwa. Sai ta tattara kayanta ta gudu gidan Gwaggo da kudirin ba zata koma ba ta gama auran gabad'aya. Ita ba zata zauna da kishiya ba. Gwaggo ta dinga rarrashinta Amma fafur ta ce ba zata koma ba. Shi kuma Babanmu kamar sammatace a lokacin baya ganin kowa da mutunci sai Ummansu Hadiza. Domin Iya mahaifiyarsa ma ta rasa gane kansa. Ta je gidan Gwaggwo akan Mamanmu ta koma dakinta. Gwaggo ta ce idan mijin yana buk'atar cigaba da zama da ita ya zo a samu sasanci. Ashe Baba Sule ne yake zuga shi akan kada ya je ya rabu ma da auran Mamanmu gabad'aya tana da farar kafa ba zai ta'ba cigaba ba. Auran Murja wato Ummansu Hadiza shine alheri a tare dashi tunda yayar matarsa ce, kuma gidansu akwai arziki na dukiya da kuma na haihuwa. Babanmu ya yarda da maganar d'an'uwansa. Ya jingine Mamanmu a gidan Gwaggwo ita ba mai aure ba ita ba mara aure ba. Lokacin da Gwaggo take yun'kurin sanar da su Dada halin da ake ciki a lokacin Mamanmu ta dinga wani irin ciwon kafa babu tafiya sai rarrafe. Gwaggo ta aika aka sanar da Babanmu halin da ake ciki. Ya ki zuwa tunda a lokacin ma har an d'aura aure ya tare da matarsa a daya daga d'akunan dake cikin gidan. Gwaggo ba miji ne da ita ba, ya rasu shekaru kusan biyar kuma ya bar mata marayu hud'u itace take d'awainiya dasu a lokacin inda Allah Ya rufa asiri tana 'Yan sana'oi na hannu a lokacin shiyasa asirinta yake a rufe. Haka ta yi ta jigila da Mamanmu asibiti akayi gwaje-gwaje likita ya tabbatar da ciki na wata shida kuma har ya juya shine sakamakon ciwon kafafun da take yi. Ba a mamaki da ikon Allah amma lamarin ya bawa kowa mamaki. Gwaggo ta sanya aka kira babamu a karo na biyu yaki zuwa. Sai ta shirya ta nufi shagonsa anan ta same shi da maganar ta kuma nuna masa sakamakon a rubuce. Ya tsorota sosai kuma ya yi mamaki da ikon Allah jikinsa ya mutu ya gaza had'a ido da Gwaggo ya dinga kame-kame Yana ko'karin kare kansa. Gwaggo ta ce to tunda haihuwa ce matsalar sai ka zo ka d'auki matarka ka kuma ji tsoron Allah ka yi adalci da ni da kai duka amana aka ba mu. Ta kamo hanyar gida ta bar shi da alhini. Baba Sule ya so ya zuga shi domin ya firje ya'ki amincewa da cikin akan ba nasa ba ne. Babanmu ya ki yarda da shawararsa saboda shi yafi kowa sanin yadda ya sami matarsa. To ashe haihuwar ra'kuma daga babamu ne. Domin itama Ummansu Hadiza duk da take bazawara kuma ta haihu a wani wuri ba daga shigowarta ta haihu ba sai da Mamanmu ta haifi anti Yagana da shekara biyar tukkuna Ummansu Hadiza ta samu cikin d'anta na fari, kuma cikin ikon Allah da ya ta haife shi kwana biyu Allah Ya kar'bi abinsa. Ta dinga kuka tana cewa Mamanmu ce ta 'kona shi da ruwan zafi tunda a lokacin da ya rasu Mamanmu ba ta jima da yi masa wanka ba. Dama zaman doya da manja suke yi. Mamanmu tana dannewa ne a matsayinta na Uwargida. Kada ace ita ce bata k'aunar zaman lafiya. Amma dai duk da haka watarana idan Ummansu Hadiza ta kai ta bango fitowa take yi su yi ta cacar baki. Tana da ha'kuri a wasu lukutan. Amma ba ta son raini. Shiyasa anti Yagana take fad'in halinmu daya da ita na rashin san wargi. Kusan lokaci daya aka samu cikinmu ni da Hadiza a yadda Ummansu Hadizan take ba mu labari tare suka dinga laulayi har Allah ya kawo lokacin haihuwar tazarata da Hadiza ta kwana tara ce. Ita aka riga haihuwa sai ni. A lokacin ita an yi mata hakika da tinkiya katuwa. Ni kuwa Babanmu ya ce bashi da kudi sai dai Mamamu tayi ha'kuri tunda ya yi mata na fari. Mamanmu ta dinga kuka tana fad'in ba ta yarda ba ai 'yar sunna ce, yadda aka yankawa kishiyarta tinkiya itama sai an yanka mata. Shi kuma ya ce Ai ba dole ba ne, shi dai ya rad'awa 'yarsa suna Amina. Kamar yadda ya rad'awa 'yarsa Hadiza. Can gidansu Mamanmu da suka ji labari abin bai yi musu dadi ba ko kad'an. Da yake Dada tana kiwon akoyiyi sai tasa aka yanka guda daya. Aka soye tsaf da zasu zo duba ni suka kawo mata da sauran abin buk'ata. Dukda haka abin bai saki Mamanmu ba, domin bambamci ko a kayan barka sai da Babanmu ya nuna na Hadiza sun fi yawa ni kuma nawa kad'an. Da ta yi magana ya ce ai ita ya yi mata ba fari. Wannan abin ya dinga haddasa rikici a gidan. Babanmu daga ya d'auko hanyar gyara idan ya gane kuskuransa sai Baba Sule ya rusa. Ya d'ora shi a wata hanya ta daban.....✍️ *1k on talgram via 0542382124..Binta Umar gtbank* *07084653262* [11/20, 1:17 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *TALLAH!* Albishirinku mata 'Yan gayu yan gwalisa kuyi maza kugar zayo shagon (Aysha/Addah beauty saloon and spa). Shin kintaba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba kiyi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu Wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa Suna wanke kai(wash and set) suna wanke qafa(pedicure) And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University gombe state Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka, 08037925676 Or 08167764242 Whatsapp ko kuma Call we’r available 24/7.. *@Arewa books* *Bintuumarabbale.* *free pege* *11* Sanyin halin Babanmu shine ya sanya Baba Sule yake yi masa kutse a cikin duk al'amuransa . Kwata-kwata Allah bai had'a jininsa da Mamanmu ba tunda ta zo gidan gaisuwar kirki ba ta had'a su ba. A wasu lukutan ma sai ya zo ya yi abubuwansa ya fita bai kulata ba kuma tana a matsayin matarsa d'an'uwansa ciki daya sai dai ita take ture komai ta gaishe shi. Idan kuma 'yan miskilancin suna kusa da ita kuma sai ta share shi har ya gama abinda ya kawo shi gidan ya tafi yana habaice habaice sai ka ce wani mace. To irin wad'annan matsaltsalun su Mamanmu ta dinga ajiyewa a ranta har ya haddasa mata ciwon zuciya wanda shi ya zama ajalinta duka ba a ankara ba, ta dinga ciwo a tsaitsaye har sai da ta fara kumburi tukkuna Baba ya farga suka nufi asibiti likita ya tabbatar da cewa zuciyarta ce ta ta'bu. Gwaggo ta shiga rudu sosài don har Mamanmu ta ma ta fita dauriya, ita ta dinga tausarta. A lokacin shi ma babamu ya tsorota sosai ya mayar da hankali wurin nemo mata magani na gida dana asibiti. Ya nemi alfarmar gwaggo akan kada ta sanar da gidansu halin da ake ciki. Kulawar da take dan samu dalilin ciwon sai Ummansu Hadiza ta sanya kishi a ciki. Itama koyaushe sai ta kirkiri ciwo ta kwanta tace bata da lafiya. Haka babamu ya zama kamar zautacce a wancan zamanin ga rashin kwanciyar hankali daga cikin gidansa ga neman abinda za a ci. Lokacin muna da shekara takwas a duniya. Ni da Hadiza tare muka tashi cikin ikon Allah suka sake samun ciki a lokaci daya. Abin ya had'ewa Mama laulayi da ciwonta da yake tashi a sa'i da lokaci don dai ma Gwaggwo da Babanmu a tsaye suke akanta duk inda suka ji magani mussaman na hausa suna ko'karin saya mata. Kuma idan an jarraba ana dacewa. Sai dai idan kwana ya kare babu yadda za a yi. Mamanmu ciwonta ya tashi da zafin gaske ga ciki na wata biyar a jikinta. Suna zuwa asibiti aka bata gado lokacin ma ba ta gane wanda yake kanta. Kwana biyu 'yan gidansu suka zo, domin duk abinda yake faruwa babu wanda ya sani a cikinsu. Gwaggo ganin yadda abin ya yi tsanani ya sanya ta sanar dasu. Wani d'anuwan Dada da yake da rufin asiri ya bada umarnin a d'auketa a kaita babban asibiti zai biya kudin da duk abinda aka buk'ata. Babu rabon shan wahala da asara rai ya yi halinsa a lokacin da ake yin cuku-cukun. Mamanmu ta rasu da cikin a jikinta a daran alhamis aka kaita Juma'a da safe. Alokacin da kuruciya ban fahimci mutuwa ba. Ni dai kawai na daina ganinta idan na tambayi Gwaggo sai tace mini ai ta tafi saudiya. Da aka share makoki Dada ta bukaci da Baba ya ba ta ni, tunda ni ce karama. Ummansu Hadiza ta ce a bar mata ni din za ta had'a ta ri'ke mu tare 'yarta idan an d'auke ni Hadiza ba za ta ji dadi ba. Ganin yadda ta nuna damuwarta akan hakan ya sanya Babanmu ya ce Dada ta yi hakuri ta d'auki anti Yagana idan ya so ni sa'i da lokaci sai a dinga kaini garin muna gaisawa. Haka kuwa akayi suka tafi da anti Yagana tana kuka Ina kuka haka muka rabu. Gwaggo ta rungume ni tana cewa na yi hakuri za a dinga kaini lokaci zuwa lokaci. *** Na koma hannun Ummansu Hadiza gabad'aya. Da farko kamar abin arziki sai daga tafiya ta mika tukkuna ta fara nuna fifiko da bambamci a tsakanina da yaranta Hadiza da Fati wadda ta haifeta bayan rasuwar Mamanmu. 'Kiri'kri take nuna komai. Ina kallo zata sayawa yaranta wanduna da 'yan kunnaye da kayan kwalliya ni ba zata saya mini ba. Sai dai na je gidan Gwaggo idan ta lura babu d'an kunne a kunnena sai ta saya mini ko ta cire na kunnanta ta sa mini. Wasu lukutan ma haka zata dafa ruwan zafi ta wankeni da wandon jikina wanda sai ya fi wata d'aya ban cire ba. Gwaggo itace take saya mini wanduna da kayan kwalliya sannan itace take tsefe mini kai ta ba ni kudin kitso na shiga nan makotansu a yi mini. Da Ummansu Hadiza ta lura da Hakan sai ta hana ni zuwa gidan gabad'aya. Idan mun taso daga makarantar allo Hadiza zata shige ta kwanta ni kuwa zan yi shara da wanke-wanke sannan na je wurin Babamu na kar'bo kudin cefene na je na yi. Tun ban kai shekara goma sha biyu ba na ke yi mana girki. Nasha k'onewa a hannu da k'afa wasu lokotan idan na nuna mata sai ta yi mini banza, sai ta ga dama za ta ce mini sannu. Haka nake warkewa. Kayan makarantarmu na boko ni nake wanke mana. Wani sa'in ma idan Ina wanki Ummansu Hadiza za ta de'bo 'yan k'ananun kayan tagwayen da take goyo Hassana da Usaina ta watso mini tace na wanke musu. Ba ni da lokacin kaina kullum idan naje makaranta na dinga gyangyad'i kenan, domin wasu lukutan ma da daddare har aikena take yi wurin masu awo da kantina idan tana buk'atar wani abu. Watarana mun dawo daga makarantar boko ni da Hadiza nuna tafiya sai ga Yaya Aminu akan Kekensa. Na dinga washe baki ya tsaya a gabanmu Yana murmushi. Hadiza ta murguda bakinta ta bar wurin bata gaishe shi ba. Ni kuwa muka gaisa sosai Yana yi mini wasa kamar yadda ya saba a lokacin da yake tambayata me yasa na daina zuwa gidansu ban rufe masa ba na sanar dashi Ummansu Hadiza ce ta hana ni. Ya rarrasheni sosai yana fad'in ki cigaba da ha'kuri dadin abin ma ke macace aure za a yi miki watarana sai labari. Ya d'auko dari biyu ya ba ni. Ina shiga gida Ummansu Hadiza ta rufe ni da fada wai na tsaya shiririta bayan na san akwai abinda zan yi. Na ce mata mun gaisa da Yaya Aminu ne shiyasa ban shigo da wuri ba. Hadiza tana daga cikin d'aki na ji tana cewa wannan cangal din ai dan'iska ne, ki cigaba da tsayuwa dashi zai lalata ki. Raina ya b'aci sosai. amma sai na share ta ban ce komai ba, itama Ummantasu bata kwa'beta ba. Na cire kayan makarantar jikina domin yin abinda yake gabana. Sa'i da lokaci Yaya Aminu ya kan ba ni dari biyu a duk lokacin da muka had'u. Ni kuma zan kar'ba da murna da farinciki domin wannan dari biyu da yake ba ni tana taimaka mini sosai a makaranta idan ana birek don ma wani sa'in Sahura tana zuwa da abinci sai mu ci tare ina rage yunwa mutuka. Su Hadiza Ummansu tana basu hamsin hamsin kullum. Ni ce dai bata bawa. To ashe tana lure da ni idan an fito birek din ina sayan Aya da gyada. Sai ta je ta gayawa Ummansu ita kuma ta titsiyeni tana tuhumata wai maza nake bi suke ba ni kudi suna tabbatani. Na dinga kuka ina gaya mata ba haka ba ne. Yaya Aminu ne yake ba ni dari biyu wasu lukutan. Ta dinga fad'in to shi ma ai d'an iskan ne garjejen tuzuru dashi yana zaune shekara arba'in babu aure ai dole sha'awa ta yi masa yawa ya dinga tare yaran mutane Yana tattabe su. Na ce wallahi babu abinda yake yi mini Umma ki aika a kira Sahura ma ki tambayeta ni ba na kula maza. Hadiza ta dinga fad'in itama Sahurar ai halinku daya haka take kashe kudi a makaranta. Da Babanmu ya dawo ta gaya masa. Ya yi mini fad'a sosai, amma shi bai zarge ni ba. Sai da Baba Sule ya zo Ummansu Hadiza ta gaya masa. Ya dinga zagina Yana zagin Mamanmu har sai da ya dake ni da igiyar da muke shanya, yana fad'in ba zan gurb'ata musu zuri'a ba. Ummansu Hadiza kamar wadda ta yi mini farraku da dangin Mamana ko an kai ni garin ba na dogon zango nake Sanya rigima sai na dawo Koda anti Yagana ta yi haihuwar fari ma da muka je da Gwaggo ta ce zata barni a can din na kwana biyu 'yan'uwa su gan ni. Kuka nasa sosai kan cewa ba zan zauna ba, kafata kafarta. Haka Dada za ta yi ta fad'a ta gaji ta ha'kura domin ba na iya sakewa dasu na dai fi son cikin wahalar kamar yadda Dada take fadi a koyaushe. Sai zuciyata ta sake 'ke'kashewa na ji a raina babu wanda ya isa ya raba ni da alhalin Gwaggwo domin sune suka tallafi Mamana a lokacin da bata da kowa yanzu kuma suna tallafata. Duk da basu had'a ji'bi da Mamanmu ba 'kawance ne kawai da zaman gari d'aya ya had'a su da Dada amma kusan koyaushe na dubi gwaggo sai na ga kamar dangin Mamana nake tare dasu gabad'aya. kuma ina zuwa gidanta Muna gaisawa sa'i da lokaci amma ban ta'ba bari Hadiza ta farga da hakan ba. Sahura k'awata ce sosai a bayan gidanmu gidansu yake. Ajinmu daya da ita a boko da allo haka zalika ma makarantar dare ajinmu daya da ita. Gidansu babane Babansu Yana da rufin asiri daidai gwargwado. Ya rasu ya dan bar musu d'an abin hannu kuma yana da akid'ar boko sannan akwai had'in kai a gidan zumunci bai lalace ba. Nan nake zuwa na huta a wasu lukutan na yi ta kuka tana tausata ina gaya mata ina so ko diploma ma ne na yi domin na samu aikin da zan dogara da kaina. Ita kuma ta yi mini alkawari za ta gayawa Baban yayansu a yi mana kokari a tare idan jarrabawarmu ta fito. Muka ta so a gidanmu 'yan mata mu hud'u. Hadiza ce babbar cikinmu sai ni, sai Fati wadda aka haifeta bayan rasuwar Mamanmu, sai kuma tagwayen da ta yi. Daga su ba ta sake haihuwa ba. Sai da Babanmu ya auro Ummansu Saminu mai suna Sakina. Tana zuwa ta fara da maza ta gwaye Hassan din ya rasu kwana biyu da haihuwarsu. Tsabar yadda nake wahala a gidanmu ya sanya na tsunbure jikina ya tsuke. Shekaruna suka 'buya. Sai ya zamana har su Hassana sun fi ni kyawun gani da 'kira ta 'yan matanci. Dama ba a zancen Hadiza da Fati tunda a lokacin Uwarsu a tsaye take a kansu da kayan ado da kwaliyya. Gasu da jiki ruguzaza irin nata. Babban burinta a lokacin miji ya fito ta yi musu aure gabad'aya. Ba ta damu ni da halin da nake ciki ba. Duk sai da suka riga ni fara al'ada. Na dinga nuku-nuku ranar da na fara na b'uya ina kuka. Da 'kyar na gyara kaina. Na bi duk matakan da ake koya mana a makarantar dare. Sai dai wandunana biyu ne kacal gashi ba ni da audiga ina dai ganin su Hadiza da ita suna amfani ni kuma sai na yagi dankwalina na kasa shi biyu nake kunzugu dashi. Su yi tayi mini dariya Usaina ce ma daga cikinsu ta mu ta zo daya itace a 'boye take d'auko mini audigar a cikintata ta kawo mini. Anti Sakina wato Ummansu Saminu itace daidai da Ummansu Hadiza domin dama ita a shirye ta shigo gidanmu. Kuma tunda ta ga ta fara da maza a gidan ta gyara zamanta. Itama Ummansu Hadizan tunda ta lura da cewa 'yar bana bakwai ce ta shafawa kanta lafiya. A wasu lukutan tana yi magana idan ta ga son zuciyar da ake yi a gidan. Ta dinga fad'a tana cewa su yaranki shafaffu ne da mai ne da ba za su yi aiki ba. Wannan ba gata ki ke nuna musu ba Murja aure za ki yi musu ba kuma ki san inda zaki kai su ba. Ita wannan din ki kewa gata. Wahala dai mai shigewa ce, kuma shi da ba a yi masa mugunta domin ba kasan ranar da zai yi maka ba. Makamantan maganganun take yi mata a duk lokacin da ta su ta had'o su a gidan. Ni dai ba na cewa komai sai dai na yi musu shiru su yi su gama. Na dai ajiye a raina cewa watarana sai labari. Daf da za mu yi saukar al'kur'ani a makarantar allonmu wani Alhaji Halilu mai kudi da mata biyu ya fito fagatatan Yana son auran Hadiza wata uku kacal yake so a sanya a d'aura auran Babanmu ya ce bai shirya ba domin bai ajiye komai ba. Mutumin ya ce gidansa akwai duk abinda ake buk'ata ba sai an wahalar da kai ba. Babanmu ya ce za a yi bincike tukkuna ya jira shi. Baba Sule ya yi tsalle ya shiga sha'anin bai bari an tsananta bincike ba ya ce tunda yarinyar tana so a maganata ta 'kare. Kuma dai yanzu a sha'anin aure kawai a binciki aljihun mutum, idan zai iya ri'ke iyali ai an yi barka. Balle ya ji labarin mutumin da rufin asirinsa harkar motoci yake yi. Babanmu Ya ja bakinsa ya yi shiru bai sake magana ba. Baba Sule shi ya yi ruwa da tsaki ya kar'bi kudin auran dubu dari masu danko irin na da. Gari ya d'auka an kawo kudin auran Hadiza dubu dari. Makaranta ma a ajinmu zancen ake yi, ai Hadiza aure za ta yi kuma mai kudi ne wanda za ta aura. Hadiza da Ummansu sun samu abinda suke so. Sai ta fara jiji da kai gabad'aya ma ta daina zuwa makaranta daga ta bokon har ta allon. A lokacin ajinmu uku a boko za mu yi jarrabawar shiga aji hud'u. Allo kuma duk da ba kokari ne da ita ba amma tana cikin 'yan sauka. Ko da ta daina zuwa malamin ajinmu ya tambayeni dalili na ce wallahi ban sani ba. Ya samu Baba da maganar yana gaya masa ya kamata ta cigaba da zuwa domin a hada saukar da ita idan ya so ranar d'aurin auranta sai a bata allonta. Da ya samu Ummansu da maganar sai ta ce tunda aure za a yi mata bai yiwuwa a hada gudu da susar duwawu, auran shine yake da a hakku. Karatun kuma ko Yaya ne ta samu ya isheta. Shima Babanmu bai damu ba ya rabu dasu. Bikin Hadiza ya hade da hidimar saukarmu. Hidima ta yi wa Babanmu yawa ta ciyar da 'yan biki da sauran abubuwa. Bai biya mini kudin allo da ankon saukar ba. Gabad'aya abinda kowa ya biya dubu goma sha bakwai gashi kullum idan na je makarantar sai an yi mini magana na kawo. dana sake tuna masa maganar a lokacin suna tare da Baba Sule suna shirya yadda d'aurin aure zai wakana. Baba Sule ya buga mini tsawa kan cewa na tashi na basu wuri. Shi kuma Babanmu bai ce mini komai ba. Na kwana da tunani da fargabar tunda na san idan ban bada kudin ba wata'kila za a iya cire sunana. Washe gari na shirya da wuri na fita gidansu Sahura na nufa aron wayar babarsu na yi bayan mun gaisa. Muka shiga d'aki ni da Sahura duk na fad'a mata yadda akayi. Sai ta kara k'arfafa mini guiwa akan na sanar da dangin Mamana ko za su taimaka mini. Lambar anti Yagana ce da ni a kaina. Na kira ta ba tare da ja'inja ba ta d'auki muryata muka gaisa. Na gaya mata halin da nake ciki. Ta ce tana nan tafe a cikin satin amma kafin nan zata turo mini abinda yake hannunta na fara biya kafin tazo, tace babu wanda za a gayawa daga cikin dangin Mamanmu abin kunya ne. To ashe a ranar ma Yaya Aminu ya je ya biya mini ya samu labari ne a bakin Hamusu 'kaninsa tunda ajinmu daya dashi kuma tare zamu yi saukar ya san ina daga cikin wad'anda ba su biya ba. Ya zo har gidanmu Yana gaya mini ya biya mini don haka na kwantar da hankalina. Amma bai fad'a mini keken da yake hawa ya sayar ba. Da anti Yagana ta zo na fad'a mata. Ta yi ta godiya ta ce na ajiye kudin da ta turo mini a acct din Mamansu Sahura idan ina buk'atar wani abu sai na kar'ba. A daran muka je gidan Gwaggwo domin yin godiya. Ita kuma ta dinga yi mana fad'a tana cewa ai duk yiwa kai ne, kuma duk wanda ya yi wa al'kur'ani hidima a gidan duniya to babu shakka a lahira shi ma zai yi hidima dashi. *1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank. Mutanan nijar dala dari katin Airtel.* *07084653262* [11/21, 9:33 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A.* *TALLAH!* 🌲🌳🌿☘️ *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* TEEMAH DATA SERVICES MTN 1GB @550 2GB @950 3GB @1450 4GB @1550 5GB @1700 CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306 8037026306 fatima musa ibrahim opay *@Arewa books* *Bintuumarabbale.* *free pege* *12* Duk sabgogin bikin Hadiza ba ta sanya ni a ciki ba. Ina dai kallo ita da 'yan'uwanta da suka fito ciki d'aya suna ta kai kawo amma ni ban san komai ba. Har 'kawayenta na waje da ire-iren yaran 'yan uwan Ummansu sun fi ni mutunci. Sai na zama kamar bare a gidan su kadai suke yin shige da ficensu. Ta inda Allah Ya taimakeni ma hidimar saukata ta d'auke mini hankali, amma dai duk da haka abin ya yi mini ciwo, haka zalika ma ya yi wa anti Yagana, don sai da ta gaza ha'kuri ta yi mini maganar. Na ce haka suke yi mini dama ba tun yau ba, suna had'e mini kai da b'oye mini abinda ya shafe su. Ranta ya baci sosai, ta ce sai ta samu Baba da maganar, na ce kawai ta bari yin hakan zai haddasa rikici domin cewa za a yi ta zo na kwashe 'karya da gaskiya na gaya mata. Ko kuma wasu su canza mata manufa a ce tana yin hassada ne domin ba ni ba ce zan yi aure ba. Haka ni da ita muka zama ware a cikin gidan. Dama a d'akin Anti Sakina ta sauka. Da yake ta iya zaman duniya ta rik'eta da kyau ta janyeta tunda dama ba wani shiri suke yi da Ummansu Hadizan ba. Aka yi hidimar biki da sauka lafiya kowa ya kar'bi sakamakonsa. Ni da allo da kyauttuka na mussaman. Ita kuma Hadiza aka kaita gidan mijinta mai wadata da abin hannu Allahu Halilu. Anti Yagana bayan hidimar da kwana biyu ta tattara kayanta ta tafi da takaicin abubuwan da suka faru a sha'anin da ya gabata. Ni kuma na cigaba da rayuwata da 'yan'uwana da muka rage mu uku a d'aki daya. Sai ya zamana raini ya shiga tsakanina dasu. Usaina ce kawai take girmamani, amma da bana kai zuciyata nesa da kullum sai mun yi fad'a, kuma babu yadda za a yi a ba ni gaskiya kasancewar ni ce babba a cikinsu. Ganin haka ya sanya na je na samu Maman bokola wata mata ce a bakin titin gidanmu take da shagunan d'inki. asalinta 'yar ghana ce ta zo ta kama haya a kusa da gidansu Sahura. To duk yawanci 'yan gidansu ita suke bawa d'inki, ni ma ta ta'ba yi mini sau d'aya amma kyauta ta yi mini, dalilin Sahura muke gaisawa idan na je gidansu. Da ban sameta a shago ba na je gida na sameta na ce don Allah zan dinga zuwa ina koyon d'inki idan na iya sai ta daukeni aiki ko kalmasa na dinga yi mata. Sahura ta dinga yi mini dariya tana fad'in ai ita ba za ta iya d'inki ba saboda wahalarsa. Ni kuma na ce ina da naci akan abinda raina yake so. Maman bokola ba ta da ganin 'kyashi ta amince mini tace amma ba shago zan dinga zuwa ba gida zan sameta duk ranar asabar da lahadi da safe take zaman yanka sai na zo na kalla. Ta yi mini alkawari kuwa daga na iya d'inkin za ta d'aukeni aiki. Ban yi kasa a guiwa ba na samu Babanmu na gaya masa. Ya ce babu damuwa amma lallai na sanar da Uwata yana nufin Ummansu Hadiza. Na gaya mata yadda muka yi tace tunda ubanki ya barki yawon gantali da sunan koyon d'inki ni menene nawa a ciki, Allah Ya bada sa'a. Abinda tace mini kenan hakan bai karya mini guiwa ba, kuma na dinga tunani akan lafuzanta bini-bini sai ta jefe ni da mummunar magana mussaman wadda ta danganci maza. Ni Kuma ba kulasu nake yi ba, asali ma a unguwar ba a taba cewa ana sona ba, yaranta ne kullum cikin zance da samari, amma ni babu wanda ya ta'ba zuwa wurina. Duk ranar asabar da lahadi da wuri nake zuwa gidan Maman bokola watarana ma ni nake yi mata shara da wanke-wanke kafin mu zauna ta fara gudanar da aikinta ni kuma ina ta nazari. Hakan bai d'auke mini hankali na mance da haddar da nake yi ba. Karatun boko na ma ina kokari sosai domin duk abinda na sanya 'kulafuci akansa ba na yi masa rikon sakainar kashi tunda yayansu Sahura ya yi mana al'kawarin shige mana gaba wurin samun diploma na ajiye a raina sai na ga abinda ya turewa buzu nadi. 'Bangaran Gwaggwo ma tana yi mini alheri sosai. Hakan nan Yaya Aminu wannan d'ari biyun da tun ina 'karama ya kafa mini adashinta yana ba ni a duk lokacin da za mu had'u. Tafiya ta mi'ka a cikin sha'anin auran Hadiza matsaltsalu suka fara kunno kai. Ashe da manufar da ya aureta, yana so ya mori kuruciyarta ne ba don ya haihu da ita ba. Matansa biyu na gida sun haifa masa yaran da ya 'kayyadewa rayuwarsa. Daga zarar ta samu ciki sai ya zubar dashi. Wannan shi ya fara kawo musu matsala wadda tun tana nuku-nuku har dai ta zo gida ta fad'a tana kuka, duk garin jikin nan babu ta rame saboda fargaba. Ta ji labari an ce yawan zubar da ciki ya janyo cancer da raunanar mahaifa, kuma dai zahiri itama tana so ta haihu. Suka dinga fa'di tashi a boye. Ummansu na yawon gidan malamai domin nemo mata taimako a juyo da hankalinsa. Amma a banza, idan ta yo yajin ta dawo gida baya zuwa biko da 'kafafunta take komawa dakinta. Babanmu kuma ya ce ba zai iya ba, dama can sune suke son auran, idan ba zata iya zama ba ta nemi saki. Ko ta sanar da Baba Sule waliyyanta. Shi kuwa Baba Sule da ya ga lamarin ya kwa'be ya dinga zamewa yana fad'in sabogogi sun yi masa yawa amma zai samu Alhajin su tattauna akan matsalar. Hadiza ta dinga rama a tsaitsaye duk wannan jiji da kan babu saboda babu kwanciyar hankali a gidan mijin, domin da ta daina bin umarninsa akan yadda yake so sakinta ya yi ta zo gida da takardar tana kuka. Satinta biyu a ka samu daidaito ta koma, ta cigaba da zama. Sai ya kasance koyaushe Ummansu sai ta fita kuma ba ko'ina take zuwa ba sai neman taimakon yadda za a mallake mijin. A haka rayuwar ta cigaba da gudana. Ni ina ta fafutukar ya za a yi rayuwata ta yi kyau. Sauran 'yan matan suna ta gasar tara samari. Karatu da koyon sana'ar da za a dogara da kai bai dame su ba, koyaushe idan sun zauna hirar samari su dai a yi musu aure. A haka wani ya fito a unguwarmu da zummar auran Fati. Yana da sana'a sosai manemi ni, Amma fa kaf gidansu basa karatu daga na boko har na addini mazansu da matansu an dai yi musu sheda wurin neman kudi. Ajinta hud'u a sakandire aka yi auran. Bata damu da guntule karatun ta ba, hakan Ummansu ma ba wannan ne a gabanta ba, a cewarta ba za ta bari dama ta wuce ta ba, tunda kaf unguwar yaron ita ya gani yace yana so karatun ba dole ba ne, auran shine yake da a hakku. Kamar dai yadda ta fada a lokacin bikin Hadiza. Aka yi hidimar biki sosai tunda shima ba lefi yana da rufin asiri a ka kaita gidanta dake karkasara. Sai na cigaba da rayuwa ni dasu Hassana da Usaina wanda suma a lokacin sun kere mini tsawo da girman jiki. Ni ba ni da wani girma A amma ba na cikin jerin masu tsamurmuri jiki. Daidai misali ina da tsayi da cikar kirji da baya don wuyana a cike yake kowane d'inki na sanya a jikina yana zama mussaman fittedgown da riga da siket. Irin jikin Mamanmu ne da ni, mai kyau da boye tsufa. Sannan ba ni cikin farare haka zalika kuma ba ni cikin ba'ka'ke wuluk ina tsakiya fatata tana da kyau sosai shiyasa bana Gigigin shafa mata mai in banda cocorbutter quin Elizabeth shine man shafawata har hazar yau. Su kuma suna da girman jiki kuma a sake yake sharkaf irin na Ummansu. A wasu lukutan ma mutane suna d'auka yaran duk sun girmeni ni sai dai kawai na yi ta dariya ina mamakin yaran da aka haife su a gabana ya za a yi a ce sun girmeni kawai dai idan kana da jiki mai kyau ne sai ka ci zamaninka ka ci na wasu haka abin yake. *** Hadiza ce koyaushe take cikin matsalar aure. Ita Fati tana zaune kalau. Sai narka ki'ba take yi. kuma shekara da yin auran ta haihu lafiyar Allah aka sha shagali. Ita kuma Hadiza ga dai gidan 'kato da kuma ci da sha amma babu nutsuwa. Bata sati daya sai ta zo gidanmu sun fita da Ummansu. A cikin wannan hargitsin Iya kakarmu ta rasu sakamakon ciwon wuya da ta kwana biyu ta na yi. Abin ya zo da 'karar kwana Allah Ya kar'bi abarsa. Muka ci kukanmu muka koshi domin ba 'ya'yanta kawai ne ba suka yi rashin har da mu. Saboda tsohuwar akwaita da dattako da k'aunar jikokinta. Kuma ba ta ta'ba nuna bambamci a tsakaninmu. Bayan an share makoki sosai na mayar da hankali wurin koyan d'inkin da na sanya a zuciyata. Allah kuwa ya taimaka mini na gwanance kamar wasa Maman bokola za ta yanka d'inki ta ba ni ta ce na hau keke na had'a. Duk wahalarsa kuwa haka zan hade shi tsaf. Ta dinga mamaki. Tana fadin kina da fikira da ko'kari Amina, za ki ci abinci da d'inki in sha Allahu rabbi. Idan na had'a mata riguna sai ta d'auki kudi ta ba ni, ni kuwa naki kar'ba na ce ai bata d'auke ni aiki ba tukkuna yanzu akan koyo ne don haka ba zan kar'ba ba. Haka za mu yi ta bugawa da ita har dai ta gaji ta ce to ta d'aukeni aiki na dinga zuwa shagonta. Na ce mata tunda daf muke da zana jarrabawa hankalina zai kasu gida biyu idan mun kammala sai na kama aikin gadan-gadan, yanzu sai dinga zuwa ina taimaka mata. Ta ce Hakan ya yi, ta yi mini addu'a da fatan alheri. Bayan mun yi jarrabawar fita daga sakandire da kwana biyu aka kawo kudin auran Sahura. Sai a lokacin ne jikina ya dan yi sanyi da abinda yake faruwa da rayuwata. Wato tunda na taso nake ganin yadda samari suke karakaina akan 'yan'uwana, amma ni babu wanda ya ta'ba sansanta da sunan so. Ban san wane irin bakin jini ne da ni ba, gashi yau an kawo kudin auran Sahura wadda muke fad'uwa tare mu tashi tare, sannan Hassana da Usaina su kansu akan hanya suke domin an gama magana da iyayen samarin da za su aure su, kudi kawai za su kawo a tsayar da magana. Sai na ji hankalina ya tashi, na fara tunanin ko dai Ina da matsala ne ban sani ba. Ashe irin tunanin da nake yi shi Gwaggo take yi. Watarana ta kawo mini magunguña da turare ta fad'a mini yadda zan yi amfani dasu. Ban yi kasa a guiwa kullum da magariba zan yi turaran. Har Ummansu Hadiza ta ankara ta tambayeni na gaya mata. Sai ta kama dariya tana cewa ai dole sai da turaran a lamarinki Amina. Ko a ina ki ka gado bakin jini oho. Ta wuce ta barni tana ta dariya. Na ji Anti Sakina tana cewa ko dai ki ka jefeta ai bata da makusa yarinyar duk tafi yaranki kyau, amma kin sanya gilli da bakin kishi a ranki, kowa ya ga wannan abin ya san jifa ne. Wannan furucin ya haddasa musu rikici a gidan suka dinga cacar baki ni dai na yi shiru ban ce musu komai ba har suka gaji suka yi shiru kowacce ta shige d'akinta. Haihuwar Fati ta biyu ta yi daidai da bikinsu Hassana. A lokacin kuma ni da Sahura mun samu damar shiga makarantar gaba da sakandire wanda ba yadda Ummansu Hadiza ba ta yi ba akan Babanmu ya hana ni, shi kuma ya ce ba zai yiwu ba tunda babu kwabonsa a ciki, ba zai dakatar da ni ba. Na je na yi karatun tunda mijin bai samu ba. Ta dinga jifana da mugun baki tana fad'in babu abinda ake koyowa a jami'a, sai Iskanci, ita ba zata bari yaranta su yi zurfin karatu ba aure shine gaba domin umarnin Allah ne. A wannan lokacin ne Babanmu ya yi mata jan Ido akaina ya ce duk lokacin da ta sake jifana da wata mummunar kalma sai ya yi shari'a da ita. Hakan ya sanya ta ce to ta zare hannunta daga kaina. Tunda ta gama wahala da ni, na girma za a nuna mata ba itace ta haife ni ba. Hakan ya yi wa anti Sakina dadi, sai ta fara jana a jikinta. Ban yadda na janyu ba saboda na riga na san hakan duk salon makirci ne, kadaran kadahan nake zaune da su. Ina basu girmamsu daidai gwargwado amma ba na yarda su taka ni, tunda na girma na san abinda yake yi mini ciwo. Aka yi bikinsu Hassana kowace aka kaita dakinta. Sai na zama ni kadai a d'akin, idan zan fita na kan kulle tunda anti Yagana ta saya mini keken d'inki. Akwai kayan mutane a ciki na aikatau huluna da jakunkuna. Da nake yi suna biyana. Sannan wasu lukutan na kan d'auko aikin da nake dashi a shagon Maman bokola na yi a gidan. Shiyasa na sayi katon kwad'o nake kullewa a duk lokacin da zan tafi makaranta. Muka dinga fa'di tashi da zurga-zurga makaranta tare da Sahura, kuma kamar yadda Yayansu ya yi alkawari bai bambamta ni da ita ba, duk abin buk'ata da ya danganci karatunmu tare zai saya mana Wanda ita a d'akinta ta kammala. Ni kuma har lokacin ba ni da wani tsayayye. Ina dai ta addu'a da neman yadda asirina zai rufu domin a lokacin na mayar da hankali sosai wurin neman aiki, da kuma fitar da style na din'kunan mata. Sosai nake neman kud'i a gidan. Hakan ya janyo mini kwarjini da mutunci a wurin matan Babanmu Mussaman Ummansu Hadiza da ta watsar da makamanta a kaina ta fara jana a jiki tana nuna mini k'auna. Hadiza da a can take ganin tafi karfin ma ta kula ni idan ta zo gidan sai ya zamana tana shakkata don ganin irin sutturar da nake sanyawa tana nema tafi karfinta ita da take da miji. Babanmu kuwa yadda nake taimaka masa shiyasa koyaushe cikin sanya mini albarka yake. Anti Sakina itace muke sama-sama Hakan ya samo asali ne dalilin 'kin auran 'kaninta da na yi saboda binciken da na yi akansa aka tabbatar mini da cewa ba shi da wata cikakkiyar sana'a sai maning, sannan uwa uba yana shaye-shaye, kullum yana shagonsa a kwance da waya a hannu wasu ma suna zargin yana harkar yahoo (damfara) ita kuma ta kawo mini shine a ganinta ta rufa mini asiri ganin yadda duk na tsofe a gida, an aurar da 'yan uwana, 'yan matan unguwarmu a yanzu duk babu sa'ata. Shine ta yi mini wannan gwanintar. Tabbarar mini da munanan halayensa ya sanya na ce ban amince ba. Babanmu ya goya mini baya, shine dalilin da ya sanya take jin haushina har tana fad'in dama can na yi masa girma tunda na girmeshi kawai dai ta tausaya mini ne shiyasa tace masa ya aureni . Maganarta ta ba ni dariya sosai a lokacin sai na shareta ban tanka mata ba, muka cigaba da zama a haka ina ko'karin kaucewa duk abinda zai janyo mini samun matsala da su a gidan, amma ba na yarda su zo mini da son zuciyarsu....✍️ *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* [11/22, 10:12 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *@Arewa books* *Bintuumarabbale.* *Na yi nisa a arewa idan ba kya son jira ki yi maza ki garzaya can Kisha karatu!* *Domin biyan kudin karatu a talgram kuwa 1k ne ga hanyar biya 0542382124...Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari ne katin airtel sai ku kankare hoton a turo mini sheda ta wannan lambobin* *Whasap kawai* *08089965176* *07084653262* Astagfirullah jiya na yi mistake typing error inda zan rubuta Alhaji Halilu wato mijin da Hadiza ta aura sai na rubutu akasin hakan. Wad'anda suke bibiyar littafin nasan za su gani bisa kuskure ne, ina neman afuwa. *Free peges* *13* Watarana katsam Yaya Aminu ya zo yana gaya mini ya sama mini offer ta aikin koyarwa. Saboda murna kamar na rungumeshi na rasa ina zan tsoma kaina. Na dinga yi masa godiya wanda har na gaza ha'kuri na tambaye shi yadda aka yi ya sama mini aikin da har na fitar da raina da samuwarsa. Nan yake gaya mini wani abokinsa ne da suka yi harkar siyasa. To shine mutumin da suka wahaltawa da ya samu kujera ya raba musu offer biyar domin su taimaki makusantansu. Cikin ikon Allah ya kaiwa kanwarsa daya ya rabar da sauran. Tunda lokacin shi yana aiki a karkashin kamfanin Alhaji Tajo. 'Kanwar tashi sai ta rasu, shine ya nema mini alfarmar maye gurbinta da ni. To komai dai rabo ne, kuma na tabbata addu'ar da nake yi ita Allah Ya kar'ba ya kawo mini aiki cikin sau'ki da rangwame. A daidai lokacin ne itama Sahura ta samu aikin rabon magani 'kauyika amma mijinta Idiris ana ta turzawwa dashi ya 'ki amincewa bayan kuma ba haka akayi dashi ba kafin auran. Cikin hukuncin Allah na fara zuwa aiki da zuciya daya. Sai dai yadda 'yan gidanmu suke ko'karin juya mini manufa shi ya fi damuna. Mutanan unguwarmu ma suna ganin kamar yanzu na yi karfin da babu wanda ya isa ya gaya mini na ji, tunda babu uwata a gidan matan Babana ban d'auke su a bakin komai ba. Wasu ma suna fad'in duk an yi wa 'yan'uwana aure ni kuma na tsaya za'be sai mai kudi. Kowa dai da irin kallon da yake yi mini akwai masu cewa ma zaman kaina nake yi, na fi karfin Babanmu tunda ina bashi kudi na toshe masa baki. Wannan maganar kuma daga bakin Ummansu Hadiza ta fita, domin itace mai yawan fad'in haka har jama'ar unguwa suka d'auka. To da yake komai ya yi farko yana da k'arshe. Idan kaddara ta gifta babu yadda bawa zai yi dole ya kar'beta hannu biyu, ya kuma roki Allah Ya sa alheri ne faruwar Hakan. Budurwar da Yaya Aminu yake nema da aure har an kai kudi da sa ranar d'aurin aure rana tsaka ta bijire tace ta fasa. Kuma kada ku d'auka lafiyayayyace kamar kowa. Bai yi gigin haka ba saboda shima ya san ga yadda Allah ya yi shi, sai ya nemi daidai dashi don har ya fi ta lafiya ma tunda shi yana yawo da 'kafafunsa, sa'banin ita da kafafun suke a nanna'de a keke take yawo. Sai dai kyakykyawar gaske ce fara tas da ita. A haka suka kulla soyayya har suka kai matakin aure rana tsaka wani gurgu d'an wani attajiri ya ganta a wani taro da suka yi irin nasu. Ya ce Yana sonta. Ganin daga gidan da ya fito ya sanya iyayenta da ita kanta suka dawowa da Yaya Aminu kudinsa wai ya nemi wata. A lokacin ya shiga rud'u sosài, domin ya d'okanta da auran da ya shafe shekaru sama da arba'in a kasa bai yi ba, har furfura ta fara feso masa, kuma a hakan ma bashi gwaggo ta fara Haifa ba, ta yi haife-haife kafin zuwansa yaran suna rasuwa. Sai da shekarun girma suka cimmata ta haife shi, Allah Ya raya shi tare da d'an'uwansa Hamusu da tazarar da take tsakaninsu take da yawa. Wannan dalilin ya sanya hankalinsa ya tashi. Ita kanta Gwaggo ta shiga damuwa. A lokacin ne ya zo har kofar gidanmu ya aiko nazo. Na fita na same shi muka gaisa ba yadda yake duk ya yi rama. Ya fara tambayata ko Ina da tsayayyen wanda zan aura. Na ce masa babu. Sai ya bijiro mini da bukatarsa akan na share masa hawaye, idan kuma da takura ko ba na sonsa kada na cutar da kaina na gaya masa sai ya ha'kura. Na ce wallahi ko ka fi haka nakasa da talauci zan aureka Yaya Aminu, kuma da zuciya daya, na amince Ubangiji Allah Ya tabbatar mana da alheri. Ba'a ja dogon lokaci ba iyaye suka shiga lamarin. Ummansu Hadiza ta dinga fad'in dama tuntuni na fahimci soyayya kuke yi, tun kina yarinya. To tunda shi ki ka gani, ai ba mu da abinda za mu ce akan haka. Anti Sakina kuwa dariya take yi tana fad'in. Ai ta gwammace ta auri nakasashe an kawo mata mai lafiya da aikin yi ta ce ba ta so. To za mu ga zuwan da dawowar ai. Duk maganganunsu akan lamarin bai dame ni ba. Kawai dai ni na tsananta da addu'a Allah Ya sanya mana alheri da albarka a cikin auranmu. Danganin Mamanmu ba su k'yamaci lamarin ba sanin wacece Gwaggo ya sanya suka nuna faricikinsu da hakan. Kuma suka yi mini shatara ta arziki a lokacin auran duk abinda ake Yayi da buk'ata sai da suka saya mini aka shirya mini dakunana biyu wanda Yaya Aminu ya kama hayar gidan a can sharad'a wajejen kamfanin da yake aiki ya yi hakan ne domin ya samu sau'kin zuwa neman abincinsa. Zaman lafiya muka gudanar a zaman auranmu, tunda aka yi babu wanda ya ta'ba jin kanmu, Muna ta rufawa juna asiri, duk wanda zai zo gidana sai ya yi sha'awa domin ba na yin girki lami sai da nama ko kifi, kuma idan mutan zai tafi na bashi kudin mota. Na ri'ke aikina da sana'ata hannu bibbiyu, muka dinga cud'a rayuwar har na yi haihuwar fari, wata matsala ba ta faru. Irin sa'banin nan na zama ba mu taba samu ba, tunda kowa yana ko'karin kiyayewa da kyautata mu'amula da abokin zamansa. WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA RAYUWATA TA BAYA. Saukar hannu na ji a kumatuna. Da sauri na bud'e idona, sai na ga Yusi a gurfane a gabana Yana kuka harda shashsheka. Gefe kuma Kamalu ne ra'kube a jikin kusurwa sai ajiyar zuciya yake saukewa. Ganin haka ya sanya na yi namijin ko'karin daidaita kaina. Na tashi na dan gyara abinda ya samu a d'akin. Na gyara musu shimfida kafin na kira Usaini na bashi kudi ya sayo mana abinci, don ba zan iya yin komai ba saboda gajiya da fargaba. Suna cin abincin na ce dasu su kwanta sai da safe kuma. Suka shiga net din a tare Ina kallon yadda Yusi yake ta rirri'ke dan'uwan nasa da har yanzu yake a tsorace Yana ganin zan shammace shi ne kamar yadda na saba na zane shi. Kiran anti Yagana ya shigo wayata dake cikin jaka. Na d'aga da sauke ajiyar zuciya. Tambayar da nake hasashe ita ta jefo mini. Na ce." Ai an gama komai sun ba mu yaran. Amma sai da aka yi dauki ba dad'i sosai da jama'ar unguwar. Ta ce." Ubangiji Allah Ya kiyaye faruwar hakan anan gaba, ki yi ta addu'a watarana sai labari." Na ce." In sha Allahu rabbi anti, sai da safe." Muka yi sallama na ajiye wayar na fita na d'auro alwala domin ban yi magariba da isha'i ba. Da kyar na iya tsakurar abinci, hakan ma don dai kada na kwanta ban ci ba, na cutu, shiyasa na ci kad'an, na zame na kwanta a kan daddumar ina lumshe ido. Bacci ya fara fizgata kira ya shigo wayata a karo na biyu, ban kawo kowa ba sai Alhaji Muntari, shine ya kan kira ni a irin wannan lokacin, sai na kan rasa azancin hakan, mutumin da yake da iyali ai a irin wannan yanayin ya kamata ace yana tare da wadda ta yi girki. Ban saki jikina ba sosai, dalilin damuwar da nake ciki, da kuma fargabar kada hakan ya haddasa masa rikici a cikin gida domin na san ba kowace mace ba ce za ta iya daurewa da hakan, na dinga yin hamma ina amsa masa magana a kasalance. Hakan ya sanya shi yi mini sallama yana fad'in da safe zai sake kirana mu k'arasa tattuna maganar tunda na dawo a satin yake so a yi komai a gama. Na ajiye wayar. Idona a lumshe na cigaba da nazarin yadda abubuwan za su kasance anan gaba, ko na'ki ko na so, dole na auri Alhaji Muntari domin katange kaina da mummunar kaddarar da take shirin rufto mini. A zahiri na furta 'Allah Ka takaita mini wahala' Ban yi wani baccin kirki ba dalilin tunanin da ya'ki barina, akan kunne da idona asubahi ta yi. Na yi sallah, yaran ma na tashe su kamar koyaushe suka daura alwala suka fita. Ban koma bacci ba domin na san akwai wad'anda za su dako mini sakammako abinda ban k'arasa ba, na kammala. Duk wadda ta zo kar'bar dinkinta ba na yarda na bata sai ta cake mini kudina tukkuna. Domin zurga-zurgar nan, da wannan matsaltsalun kudin hannuna duk sun kare, don dai ma Alhaji Muntari ya taimaka mini da wasu. Yusi ne ya shigo shi kadai jikinsa sanyi kalau saikace wanda ya tashi daga ciwo fatar samar idonsa duk ta tasa, tamkar shi ya aikata lefin duk ya shiga damuwa. Na kalleshi a nutse na ce ." Ina Kamalun yake?" "Yana can massalaci a kwance Yana bacci, wai kafarsa ce take ciwo. Mama kin ga har ta kumbura." Na ce." Je ka taso shi, ka ce ya zo in ji ni." Ya kalle ni. "Mama tsoro yake ji kada ki dake shi, shiyasa ya kwanta a can. Na ce."Ai da zan dake shi da tuni na dake shi Yusi, addu'a na ke yi masa, Allah Ya shirye shi." Ya saki ajiyar zuciya Yana fad'in." Bari na je na kirawo shi." Ya fita da sauri. Minti uku da fitarsa Hamusu Ya shigo. Muka gaisa ya ce." Tun jiya na so na shigo mu tattauna Allah bai nufa ba, da yake ban dawo da wuri ba, Gwaggwo duk ta sheda mini abinda ya faru, anti Amina jama'ar gari suna ta zaginmu akan mun sakar miki wahala, don Allah wannan karon kada ki ce a a, ki ba mu yaran nan, su koma hannunmu da zama, komai Yana da lokaci, kuma in sha Allahu yaran nan, sai duniya ta amfana dasu." A nutse na ce." Ban ki maganarka ba Hamusu, kuma ban ce kun gaza mini ba, ni dai har duniya ta nade babu kalmar zagi ko 'batanci akanku, duniya ban ga abinda za ku yi mini ba Hamusu, domin Iya k'auna kun nuna mini. Ba wai ba na son ba ku yaran nan ba ne, ina tausayawa Gwaggo da shekarun tsufa suka cimmata. Ta rainin yaranta cikin nutsuwa da kwanciya hankali, ba zai yiwu ace kuma yanzu da take buk'atar kulawa a kai mata wahala ba. Ku barni da yaran in sha Allahu babu abinda zai gagare ni." Ya ce." Ai kin san na kusa aure, zaman da yaran za su yi a hannun Gwaggo na hucin gadi ne, daga zarar na yi aure da 'yan watanni sai su koma hannuna da zama, in sha Allahu zan ri'ke su da kyau, haka nan yarinyar da zan aura na sanar da ita duk abinda yake faruwa kuma ta ce ta amince za ta ri'ke su." Na dube shi cikin nazari. Wato wasu lukutan maza suna da gajeran tunani. Ta ya za a yi amarya daga aure ta fara jigila da yaran ma da bana mijinta ba. Akwai matsala babba wadda shi ba zai fahimta ba a yanzu sai zama ya yi zama tukkuna. Yanzu yarinyar zata furta karya domin tabbatuwar auran, idan ta ga ta shiga daga ciki sai ta canza alkibula. "Hamusu wannan karon ma dai Ina ba ku hakuri, kuma ma dai har gida zan zo wurin Gwaggwo mu tattauna, aure zan yi nan da sati biyu in sha Allahu, kuma wanda zan aura ya amince mini, zai kula mini da yaran nan, ba ni na nuna ina son hakan ba, shi da bakinsa ya furta, ka ga kuwa bai kamata mu watsa masa kasa a Ido ba, sannan ina so da ni da yaran gabad'aya mu yi nesa da unguwar nan, Kamalu ya canza abokai, muna cigaba da addu'a sai ka ya dabi'un nasa sun canza gabad'aya. A sanyaye ya ce.' Anti Amina surutun mutane shi yake damuna wallahi, Baba Sule sai ka ce babu dangatanka duk inda ya zauna sai ya zagi Gwaggo, ya aibata mu, kuma kin ga ba lefinmu ba ne, duk talaucincmu ba zamu kasa ri'ke yaran nan ba." Cikin takaici da b'acin rai na ce." Ka yi hakuri Hamusu, don Allah kada ka sanya damuwar Baba Sule a ranka, ni kaina bai barni ba, kuma Allah da zuciya yake amfani, kai dai ka cigaba da yi musu addu'a. Komai zai zama tarihi." Ya ce." In sha Allahu rabbi anti." Yaran suka shigo d'akin. Gabad'aya muka dube su. Da gaske dai d'ingisa k'afar yake gefanta ya kumbura kadan. Ya zube a bakin k'ofa, murya na rawa yake gaishe da kanin Uban. Bai amsa ba hankalinsa yana kan kafarsa ya ce." Garin tura kurar ruwan ka ji ciwo, domin an ce kaine jami'i wurin d'aukar kurar ko? Ya girgiza kansa yana fad'in." Ba ni ba ne, Shamsu ne ya tura kurar ni kuma na d'auki jarakuna biyu, muka nufi kasuwa, sai Saminu da ya cire wili da taya ya sayar." Ya girgiza kansa tare da furta." Allah Ya shirye ku. Ya dube ni kaina a kasa domin duk sanda na kalli yaron Ina ji kamar na fasa ihu. Ya ce." Bari na je na kira Abdullahi mai chamis ya zo ya duba shi. Na ce." Anya Hamusu kafar nan, ba targad'e ba ne, dukansa fa suka yi 'yan sandan." Ya ce." Ai dole su dake shi tunda ya yi yun'kurin guduwa, idan suka riga suka kamaka, kawai ka mika wuya. Sai ya fashe da kuka Yana cewa." Ban yi yun'kurin guduwa ba, wani daga cikinsu ne ya rike ni ya dinga dukana da takalmin kafarsa." Babu wanda ya tanka masa a cikinmu. Hamusu ya tashi ya fita. Ni kuma na cigaba da abinda nake yi. Sai kawai na tsinkayi muryarsa yana cewa." Mama ina kwana?" Na dube shi a nutse na amsa. Ya yi shiru fuskarsa duk hawaye a bushe. Ya furta." Don Allah ki yi hakuri kin ji." Na ce." Ai na ha'kura tuntuni." Sai ya rarrafo kusa da ni, yana fad'in." Ki dake ni, idan hakan zai sanya ki daina damuwa a kaina, jiya na ga ba ki yi bacci ba, kina kuka." Na ce." Yaushe ka ga ina kuka Kamalu? Idan ka ce ban yi bacci ba wannan na yarda, amma ban yi kuka ba." Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya. Na ce." Na yafe maka, Kai ma ka yi mini alkawari ba za ka sake ba." Da sauri Ya ce.'' Wallahi ba zan sake yi ba, kuma ba zan kara kula Saminu ba." Na ce." Allah Ya kyauta, Kai be Yusi d'auko kofi a kwando ka je ka sayo kunu, ina da sugar, sai ka wuce gidan awara." Da sauri ya yi abinda na umarce shi, ya kar'bi kudin ya kama hanya ya fita da saurin gaske.....✍️ *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* [11/23, 10:21 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *TALLAH!* 'Yan uwa Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS, duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali. Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su Sandal flakes Hawee Gabgab Halut Dorot Coconut chips Dufr(farce) Black khumra Brown khumra White khumra Oil perfumes da Body sprays Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku. Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka Call/WhatsApp 07037489958 Location:Gonan Ganye,zaria Kaduna state Nationwide Delivery *DATA Mai karfi da quality 💯* TEEMAH DATA SERVICES MTN 1GB @550 2GB @950 3GB @1450 4GB @1550 5GB @1700 CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306 8037026306 fatima musa ibrahim opay *@Arewa books* *Bintuumarabbale* *Ga wad'anda ba su san jira akwai more peges a arewa na gode🙏* *Free pege* *14* Hamusu ne ya yi duk abinda ya kamata akan rauninkan dake jikin Kamalu. Abdullahi mai chamis ya zo ya duba shi sosai, ya bashi maganin da ya dace. Sannan ya bi bayansa yana tambayarsa abinda za a ba shi. Da k'yar na lallab'i Yusi ya shirya ya tafi makaranta. Babanmu ya leko yana fad'in." Ina Kamalun yake ne, ban ji motsinsa ba." Na ce." Gashi nan, a kwance yana bacci, Abdullahi ne ya ba shi magani. Ya shigo d'akin sosai yana duba kafartasa. Ya girgiza kansa babu kuzari a tare dashi ya furta." Allah Ya taikaita muku wahala." Na amsa da "Amin Ya Allah." Ya dube ni kafin ya ce." Maganarki da Alhaji Muntari tana nan ko?" Kai na d'aga a hankali na ce." E, Baba." Sai ya kama hanyar fita yana fad'in." Allah Ya tabbatar miki da alheri." Na amsa da "Amin." Cikin sanyin jiki. Ummansu Hadiza ta le'ko ta duba jikin Kamalu, mun d'an jima da ita muna tattaunawa kafin ta fita daga d'akin. Na dinga zuba Ido ko zan ga Anti Sakina ta le'ko, ta duba shi, tunda dai ta san bashi da lafiya, amma shiru ba ta le'ko ba, kuma ina jin kayaniyarta da yaranta a tsakargida. Na nemi wayar Sahura domin tunda na rakata neman aiki ba mu sake had'uwa ba, ko a waya. Tana d'agawa take fad'in." Kina raina wallahi sis, kuma yau nake cewa zan kira ki kwana biyu network Yana yi mana wahala a unguwarmu." Na ce." 'Kwarai kuwa, kuna da matsalar network a nan wuraran, ya gida, da yara?" "Wallahi duk suna lafiya, ina su Kamalu fatan kowa lafiya." Na ce." Alhamdullahi wallahi, kin ga har na je bikin Babandi na dawo, anti Yagana tana gaisheki da kyau." "Ina amsawa wallahi, ina son zuwa garin nan k'awata." Na ce." Sai ki bari idan auran Fadila ya tashi sai ki je." Dariya ta yi tana fad'in." Ubangiji Allah Ya nuna mana, ai kaya ma zamu had'a ni da Yara mu je mu cashe da biki." Dariya na yi, a hankali na ce." Sahura aure zan yi nan da sati biyu masu zuwa." Da mad'aukakin mamaki a tare da ita ta furta "Aure sis!" Na ce." E, wallahi Sahura." "To ya aka yi ki ka canza shawara da gaggawa haka, wanene wannan da lokaci guda ya canza ki?" "Ba wani ba ne Sahura Alhaji Muntari ne dai wanda na baki labarinsa ranar da na zo gidanki...... Gabad'aya na kwashe duk abubuwann da suka faru na gaya mata, domin bahaushe yana cewa 'Abokin kuka shi ake fadawa mutuwa' A sanyaye ta ce." Sis, kin yi bincike sosai a kansa ko? Ni fa ba na son irin wannan gaggawar a sha'anin aure Amina, ki nutsu don Allah, kada wata matsalar ta sanya ki jefa rayuwarki cikin garari, na tsorata da na ji kin ce matansa biyu yaransa takwas, ba ki hango matsala ba." "Sahura ya zan yi? wallahi kaina ya kulle gabad'aya, gida sun takura mini, Kamalu Yana nema ya fi 'karfina, wannan ce kawai mafita a gare ni. Idan na ce ba zan yi aure ba, zan je na kama haya na zauna jama'a su canza mini manufa, ya zanyi ne Sahura, dole ko ba na so na amincewa mutumin nan domin na rufawa kaina asiri, yadda ya nuna alama kamar akwai nagarta a tare dashi, da bakinsa ya furta zai ri'ke mini yarana ba ni ce na nema ba, shiyasa na amince da auransa." "To, shikkenan sis, amma don Allah ki tsananta da addu'a akan lamarin, Ubangiji Allah Ya tabbatar miki da alheri, Allah Ya sa abinda muke hasashe a kan mutumin ya tabbata." Na ce." Amin Ya Allah Sahura na gode sosai, in sha Allahu ai kafin d'aurin auran zan zo mu tattauna." "To Allah Ya nufe ki, sai ki zo ranar da ba aiki, mu yini muna hira." Na yi dariya tare da ce wa." Sahura Ya aikin kuwa? Ina fatan babu wata matsala." "Wallahi babu matsala, ai na gaya miki na fara a sa'a, sati daya da fara zuwana ma'aikatar ya yi mana rabon kayan abinci. Harda kudin cefane. Na ce." A lallai, ma sha Allah, na taya ki murna, Allah Ya sa a d'ore." Na fad'a cikin barkwanci. Tana dariya ta ce." Za a dore in sha Allahu rabbi, ai kamar yadda ya gaya mana idan mun bi dokokinsa, zai kyautata mana, wallahi akwai alamun tausayi a tare dashi, shiyasa nake ko'karin ganin ban sa'ba dokokin aikinsa ba." "Ai kam Sahura ba girin-girin ba, Inji hausawa ta yi mai, Alhaji Tajo ne fa, ni dai ba na yinsa, tunda ya yi sanadin uban 'ya'yana." Ta dinga kyalkyala dariya tana fad'in." Ho 'kawata, idan ki ka tsani abu, duk inda makusa take sai kin nemo, wallahi mutumin arziki ne, ga kyauta da sakin fuska ga ma'aikatansa." Na ce." To a ba ni hakkin mijina kawai a zauna lafiya, shekara kusan goma yana yi masa bauta, ai ya ci ya bashi fansho." Ta ce." A rigimarki ba, ai ko gomnati ce sai mutum ya zartar shekara goma suke biyan fansho da garatuti, balle kamfani da babu wannan yarjejrniyar. Amina nifa na fi zargin akwai wad'anda suke cin amanar mutumin nan a bayan fage shiyasa ki ke ganin kamar bashi da Imani." Na ce." Ai duk wanda yake aiki a k'arkashinsa ba zai ga aibunsa, mussaman idan Ya na amfanuwa dashi, shiyasa idan na fadi abinda ya yi mana sai jama'a su karyata ni, ke dai kin sani, ba sharri ba ne ko?" Ta ce." Na sani, shiyasa ma ai ki ka ji na ce miki akwai masu ha'intarsa a bayan fage, wallahi na san da saninsa ba zai wulakanta wanda yake moruwa dashi ba." Na ce." Lallai Sahura harda rantsewa akan mutumin da ba ki jima da saninsa ba, to shikkenan mu bar maganar kawai, ba za ki fahimta ba ai." "Ai dole mu barta sis, tunda ba kya so, amma dai Ina kara tabbatar miki da nagartar mutumin, idan mu'amula ta had'aku, za ki gazgata cance na." "Uhm" Kawai na ce' "Kin ga gyaran jiki, nake so na fara tun yanzu, bahaushe ya ce' Idan kana da kyau ka kara da wanka, dukda breast dina ba sa samu wata babbar matsala ba, amma dai Yana da kyau na kara gyarasu, a cike suke sai dai sun dan rankwafa, nan ba sosai ba, Ina so ki bincika mini maganin gyaran nono mai kyau, dana sanyi, da na'ima, ina buk'atar na matsi sadidan, amma harbel nake so, ba na buk'atar na bature." "Aikuwa gyaran Yana da kyau kawata, don ma Allah ya yi mini kyawun suffa, wallahi da yawa wasu ba za su yarda kece ki ka haifi su Kamalu ba, kamar wata budurwa fa." Dariya na yi na ce. Lallai Sahura, ke ma abinda za ki fad'a kenan, to na gode sosai, dukda haka dai zan gyara jikina, kin ga ina da kishiyoyi, Yana da kyau na je gidan zam-zam." Ta ce." Kaya ya tsinke a gindin kaba, shekaran jiya na ji Maman Anisa tana waya da wata mai magani GARKUWAR MATA sunanta. Maman Anisa za ta cire yarinyar da take goyo daga nono shine tace ta had'a mata magani. Gaskiya duk abinda na ga Maman Anisa ta saya nagartacce ne, har take tabbatar mini da ingancinsa domin yawanci 'yan gidansu a wurin matar suke sayayyan kayan gyara, in sha Allahu zan karbo miki lambarta sai ki kira ta kuyi magana ko ta whasap ne, tana garin Kano tana kuma tura kayatanta kowane gari. Duk wani na'unin maganin matantaka idan kina bu'kata akwai wurinta cikin farashi mai sau'ki da rahusa, don har sari suke bayarwa.....08089965175 a yi magana kai tsaye ta wannan lambar.. "To yawwa, don Allah Sahura ki yi kokarin karbo mini lambarta yau din nan, sai ki turo mini, ina so mu yi magana da ita da wuri ta Aiko mini na fara amfani dashi." Ta ce." In sha Allahu rabbi yanzu zan shiga gidan da kaina na kar'bi lambar. Sallama muka yi, na ajiye wayar na tashi domin gyara d'akin, da tunanin lamarin da yake fuskanto ni, ina ro'kon Allah Ya wanzar mini da alheri. Ina tsaka da aiki Ya kira ni. Dama na yi hasashen hakan, wata'kila Yana ta kira lokacin muna waya da Sahura. Na zauna a nutse na daga wayar da sallama a bakina. Bai amsa sallamarba ya fara cewa." Na jima ina trying lambarki sai ace busy Amina ke da wa kuke wa da sanyin safiyar nan." Yanayin yadda ya furta maganar a cunkushe shi ya sanya jikina ya dan yi sanyi. 'Wato shi kuma mai titsiye ne' Na ce."Sahura ce kawata, muke tattauna yadda sha'anin bikin zai kasance." Sai ya sauke ajiyar zuciya. Ya sassauta sosai ba kamar farko ba. Ya ce." Ai na d'auka wani ne yake hure miki kunne da sanyin safiyar nan." Na ce." Wani kuma Alhaji, ai babu shi sai kai, domin zuciyata ta gazgataka akan abokin rufin asirina." Murmushi Ya yi wanda sautinsa ya fito har sai da na ji a kunnena, cikin jin dadi Ya ce." Kin gama faranta mini rai my love, ashe na samu wannan matsayin ba a gaya mini ba sai da aka gama ja mini aji ko?" Dariyar da babu nishadi na yi na ce." Ka kai makura a zuciyata, Kuma ina kyautata zato na alheri a kanka, ba zan yi kaico ba." Ya saki dariyar nishadi ya ce." Na yi godiya sosai da wannan yabo da na samu daga wurinki, Allah Ya ba ni ikon kula daku bakidaya." Na amsa da "Amin Ya Allah." Ya ce." Yanzu wace rana ki ka tsayar ta d'aurin aure?" "Juma'a ta sama ai hakan ya yi ko?". "Ya yi sosai, dama ke nake jira, don ni ko yau a daura ba ni da matsala a shirye nake." Murmushi kawai na yi. Ban ce komai ba. Ya ce." Zan tura miki kudin gyaran jiki, da hidimar da za ki yi, sannan na sanya miki kayan d'aki da labulaye, abinda dai da za ki zo dashi kad'an ne. Don gabad'aya na canza musu furniture din gidan. "Na gode sosai Alhaji Allah Ya 'kara arziki." "Amin Ya Allah, zan shigo yau da daddare sai mu sake tattaunawa ko?" "To shikkenan, Allah Ya kawo ka lafiya." Muna yin sallama da minti biyar message ya shigo a waya. Ina dubawa naga kudi ne ya turo mini har dubu dari da hamsin. Ban yi mamaki ba, tunda tun farkon haduwarmu ya nuna yana da kyauta da sakin hannu. Wani abin haushi da takaici, Ummansu Hadiza kuma sai ta tsiri jin haushina. Da farko duk abinda zan zartar sai na nemi shawararta amma ganin yadda ta fara nuna halin ko'in kula da lamarin auran ya sanya na janye jikina. Nake gabatar da abubuwana kai tsaye tunda ni ba yarinya ba ce. Abinda dai yake ba ni mamaki shine; Yadda take nuna mini hassada a duk abin alherin da zai tunkaro ni. Da farko ta nuna sha'awarta da lamarin, amma ganin yadda komai yake tafiya gwanin sha'awa sai bakinciki ya shigo ciki. Hadiza ta zo gidan tana fad'in "Dukda dai ba sanya mu a sha'anin ba, muna da abinda fad'a, mutumin nan dai bashi da wani kuzari a gidansa, matansa sun fi karfinsa, sannan kuma Yana neman mata, kowa ya san haka don har ciki ya yi wa wata yarinya, don dai yana da kudi ne maganar ta mutu." Ban girgiza ba, ban kuma tanka mata ba. Na cigaba da shirye-shirye na, ina kara mi'ka wa Allah lamarin, gefe guda Gwaggo tana kara kwantar mini da hankali da fatan alheri. Duk wani gyara na yi, na ciki da waje. Na sayi abubuwan da ba ni dasu. Domin da kansa ya dinga gaya mini idan kudin ba su isheni ba na yi masa magana zai kara mini. A iya tunanina dubu dari da hamsin da ya turo mini harda lefe, abin mamaki sai gashi saura kwana biyar d'aurin aure danginsa sun kawo mini akwatina uku cike da kaya manya da takalma da mayafai, wallahi ko wata budurwar albarka. Takaici ya kara cunkushe zuciyoyin massadana. Ita Ummansu Hadiza bakincikinta a kaina baya b:oyuwa, amma anti Sakina watsar da makamanta ta yi ta zo har dakina tana gaya mini idan na tashi fitar da kayan da zan bayar tana buk'ata. Na ce mata in sha Allahu zan zabar mata masu kyau. Ana jibi d'aurin aure, anti Yagana da Ya Falmata suka dira. Kaya sosai suka had'o mini na gyara dana sanyawa. Na yi farincikin zuwansu ba kad'an ba, domin dama kad'aici ya isheni. Sune suka je suka ga d'akin da zan zauna a unguwar Kawo Jirga. Su ka dawo suna 'kwarzanta gidan, da kuma sakin fuskar da suka samu daga matan gidan.. Hakan ya kara kwantar mini da hankali, na ajiye a raina in sha Allah zan yi iya iyawata wurin ganin na zauna dasu lafiya, zan kuma toshe kunnena daga barin jin gutsiri tsoma na jama'a.. Aka daura aure ranar juma'a, shedu suka shaida, kuma a ranar na tare a gidan. Inda na samu rakiyarsu Anti Yagana da Ya Falmata Sahura da kuma Anti Sakina. Ummansu Hadiza ita da yaranta babu wanda ya raka ni. Ita a ranar ma kwanciya ta yi a d'aki ta ce zazzabi take yi. Hadiza kuwa dama sai Yamma ta zo, Fati kuma tsohon cikine da ita ba ta fita, Hassana da Usaina kuma sam ba su zo ba, na fi zargin ba ta gaya musu ba, amma da ko Hassana ba ta zo ba, na tabbata Usaina zata zo, tunda muna shiri da ita. A ranar da na tare na d'auka zai tattaramu wuri d'aya ya yi mana nasiha, sai na ga akasin haka. Bai yi wannan ba, gabad'aya ya d'okantu sai barin jiki yake yi. Ya manta da sunnar da annabi ya koyarwa sabbin ma'aurata. Na gaza yin shiru na tunasar dashi akwai sallar nafila fa, mu yi da kyakykyawar niyyar domin wanzuwar farinciki a cikin auranmu. Kamar dai wanda na tilasta haka ya bi ra'ayina da yadda nake so, muka yi nafilar. Ina ta nazartarsa a tsanake na fara hangar wasu halayensa. Wato kowa dai ka ganshi kawai. Dama ana fad'in yawanci maza suna auran sha'awa ne, masu yi don Allah kad'an ne, na fara gazgata haka a dare daya da Alhaji Muntari, amma ba zan yanke hukunci kai tsaye a kansa ba tukkuna sai tafiya ta mi'ka. Yadda dai ya nuna zulamarsa a kaina shine abinda ya fi daure mini Kai, tamkar wanda bai da iyali haka ya kasance da ni a daran, ya gudanar da sha'aninsa, cikin nishadi da sambatu kala-kala. Muka wayi gari cikin aminci. Amma har yanzu ban daina mamaki a kansa ba. Da Ya tambaye ni Yara na ce " Suna can gidan kakarsu sai na yi sati tukkuna za a kawo su." Sai Ya ce ." To Hakan ba lefi, kema kin yi kyawun kai, na gama morewa ko?" Na yi murmushi ban ce masa komai ba. Ya ce." Za ki shiga ku gaisa da matan gidan hakan ya yi ko?" Na dube shi a tsanaki na ce." Ai na d'auka kai za ka yi mini iso a wurinsu mu gaisa sosai, idan da wani karin bayani a kaina da kansu sai ka yi mana." Ya girgiza kansa yana furta." A'a, ki je dai ku gaisa, ai kina fita kowacce ga kofarta nan. Ku dai zauna lafiya don Allah, ki ba su girmansu, tunda su ki ka samu a gidan, ki bi tsarinsu, muddin babu cutarwa. Suma na yi musu bayani akanki, ba ki da matsala, abinda dai na sani kansu a had'e yake, haka zalika ma yaransu, idan kin bi su a yadda suke so, za ku zauna lafiya da juna." Na jima Ina kallonsa da kuma nazartar maganarsa. Ai idan da wanda zan bi sau da k'afa shine, tunda shi ya ajiye ni, banga dalilin da zai sanya ace mini na bi wata ba, zaman aure ai ba wasa ba ne. Amma ban nuna masa damuwata akan maganarsa ba na ce." Babu matsala zan shiga mu gaisa da su zuwa an jima, amma wani hanzari ba gudu ba, wallahi abubuwa sun sha mini kai, tun farkon had'uwarmu nake so mu yi maganar da kai, Allah Bai nufa, amma wata'kila Baba Sule ya gaya maka Ina aiki ko? Ina koyarwa gwale firamare skull, sannan ina dinki sosai, ina so na cigaba daga inda na tsaya, ba don komai ba sai don kula da yarana, ba zai yiwu duk wahalarsu na sakar maka ba, ni ma zan taimaka da wani abun." Fuskarsa ta canza da wani yanayi da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Ya gyara zama Yana fuskatantata sosai Ya ce, "A gaskiya bai gaya mini ba, kuma kema kin yi ragwan azancin da ba ki sanar da ni ba tun farko ai da na fada miki ra'ayina, ba zan iya bari iyalina na fita aiki ba, bayan Allah ya yi mini komai, ba ni da wannan tsarin." Gabana na wani irin fad'uwa na zuba masa ido, Ina tunanin yadda zan yi don wallahi ban ta'ba tsammanin zan samu matsala a wurinsa ba. Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Ki ajiye maganar zuwa aiki Amina, babu ita a tsarina, sai dai ba zan katseki ba, adalci daya zan yi miki, ki cigaba da dinkinki, a cikin gida, ai aure ba wasa ba ne, da zan fita matata itama ta fita tana cud'anya da maza a waje, ba mu ta so da wannan akid'ar a gidanmu ba. Matayenmu suna gida a lullube mu ne muke fita mu nemo musu abinda za su ci, maganar yaranki kuma, ni na ce zan ri'ke su ai, kada ki damu zan miki kokari a kansu, a marayu ne, wata'kila sai na samu aljanna ta dalilinsu, in sha Allahu zan kula miki da su.......✍️ *1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank* *07084653262* [11/24, 9:34 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *TALLAH!* 🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨ 🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t *@Arewa books* *Bintuumarabbale* *Free peges* *15* Gabad'aya jikina ya mutu da kalaminsa na karshe. Dole haka na ha'kura tunda ya riga ya gama kashe mini jiki da tabbatar mini cewa zai kula mini da yarana, wanda dama duk abinda nake yi saboda su nake yi. Na kuma yi nazari sosai, akwai tazara mai mugun tsayi tsakanin nan kawo jirga da gwale makarantar da nake koyarwa, za a dinga samun tsaiko da tangard'a na makara da sauran matsaltsalu. Dole dai babu yadda zan yi na ha'kura, na ajiye aikin, na rungumi sana'ar hannun, tunda bai nuna mini keta a kanta ba. A d'akina ya shirya sosai, ya yi gayu, nan na sake fahimtar mutum ne shi mai son ado da nuna 'kawa, hatta waya da biyu yake amfani, kuma masu girma da kudi. Kafin ya fita yake gaya mini idan ya gama kwanaki ukun da musulunci ya ba ni, sai na fara binsa dakinsa kamar yadda sauran suke masa. Na ce." To shikkenan hakan ya yi." Sai bayan da ya fita da kamar minti ashirin tukkuna na zura hijabi na fito babban tsakargidan. Gashinan dai babu gyara, bakin kicin duk kwanuka. Da takalman yaran gidan a watse. Na dinga jin kayaniyar yara a d'akin da yake fuskanto ni. Kai tsaye can na nufa cikin nutsuwa na shiga da sallama. Tana kwance kan duguwar kujera, da kayan bacci a jikinta. fara ce gajera, kamar dai yadda ya nuna mini ita a hoto, ba ta da muni. yaran suna ta wasa, wasu daga ciki da littafain makaranta, wasu kuma game suke yi a wayar da nake tsammanin ta ta ce. Ta mike zaune da sakakkiyar fuska tana cewa." Shigo mana." Na saki fuskata sosai na shiga na zauna kan kujera, ina fad'in." Yaran duk suna nan kenan, ko da yake ai da sauran hutun tukkuna." Tana gyara zamanta ta ce." Ai hutu kuma ya kare tunda litinin za a koma, kada ki so ki ya yadda zaman nan nasu ya isheni, dan bacci nan na safe basa barina na yi." Dariya na yi, ina kallonsu yayin da suke yi mini wani irin kallo, na rashin sani, cikinsu kuma babu wanda ya yi tunanin ya gaisheni. Na ce." Ina kwana, ya yaran, fatan na sameku lafiya." Ta amsa a sake tana cewa." Lafiya Lou ki ka same mu, yanzu nan dama Babansu da ya shigo yake gaya mini za ki zo mu gaisa." Wani d'an matashin yaro da tun zamana a wurin na ji ana kiransa da Turmuzi Ya ce." Mama itace amaryar Babanmu ne?" Ta ce." E, ita ce" Shiru ya yi bai ce komai ba, sai kuma can ya tashi ya fita da sauri. Sauran yaran kuma suka cigaba da sha'aninsu babu wanda ya gaisheni a cikinsu. Na cika da mamaki sosai, kuma ita Anti Maimuna haka sunanta yake ba ta tsawatar musu ba. Minti kusan goma ina zaune muna dan ta'ba hira. Na lura tana da sakin fuska, kuma dai a haka kamar babu wani kulli a zuciyarta. Tana gaya mini yadda tsare-tsaren gidan yake. Sai dai yadda na fahimta tana da son jiki da kazanta a jikinta da falonta na lura da hakan, tafin 'kafafunta duk sun yi daud'a. Kuma kayan bacci ne a jikinta masu ruwan haske, Amma sun dafe, gashi dai safiya ce, amma kusancina da ita hancina yana ta sha'ko mini warin hammatarta, dukda hallita ne, amma dai akwai kazanta a sha'aninta, tunda mutum ya san yana da ki'bar da za ta ajiye masa gumi sai ya bi matakan gyarawa. Shigowa ta yi babu sallama tana cewa." Tun d'azu Turmuzi ya je yana gaya mini ga amarya nan a sashenki, anti Maimuna ai sai ki ce na zo ni ma a zauna da ni, a kalla fa kun fi minti ashirin a tare, ni ba fa na son haka." Cikin kausasa harshe take yin maganar. Ita kuma sai ta fara dariya tana cewa." Yanzu nan nake cewa Salima ta zo ta rakata wurinki ku gaisa, ai na yi tsammanin bacci ki ke yi ne." Ta zauna tana d'an kallona kafin ta ce." Ba bacci nake yi ba, kuma da ki ke cewa Salima ta rakota wurina makauniya ce ita, ai babu wanda ya yi mata jagora ta shigo wurinki, haka Turmuzi ya gaya mini. Anti Sakina ta ce." Ke fa matsalata dake Jamila gajan ha'kuri wallahi, wannan ba a bin damuwa ba ne fa." "Gajan ha'kuri kamar yaya Anti Maimuna, gaskiya na fada fa, kin san ni komai a bud'e nake yinsa." Na ce."Haba baiwar Allah, kya bari mu gaisa ko? Ai zan shigo har wurin naki dama bisa bin umarin maigidan, ina fata dai na sameku lafiya." "Lafiyarmu lau wallahi, ya hidima fatan an tashi taro lafiya." "Alhamdulillahi, na shigo cikinku da kyakykyawar zuciya, ina fatan zaku karbe ni hannu biyu." Ta ce." In sha Allahu rabbi." Falon ya yi shiru. Yaran duk sun zubo mana Ido. Sai na dube su a tsanake na ce.' Babu wanda ya gaishe ni a cikinku, kuma duk ku gaya mini sunayenku." Da yar dariya na yi maganar. Sai suka fara rige-rigen gaisheni, kowa yana ko'karin gaya mini sunansa. Na dubu Anti Maimuna da fad'in." Salima ce babbarsu ko?" Ta ce." E, itace gata nan sai tsawon kafar tsiya." Na ce." Ai girman 'ya mace ba shi da wahala, daga zarar ka fara da mace sai girma ya kamaka." Ta yi dariya tana cewa." Wallahi hakane. " Anti Jamila tasha kunu bata tofa mana ba. Ni Kuma ina sane ban sanya maganata da ita ba, saboda karon farko na fahimci bata da hankali, sannan yadda take nuna gadara akan Uwargidan, tana gaya mata magana kausasa bayan ko banza ta girme mata, to ni ba zan d'auka ba, duk cikinmu babu yaro, ba na tsammanin itama ta ba ni wasu shekaru da yawa. Shiyasa tun bayan gaisuwar da muka yi da ita, ban 'kara tanka mata ba, daga karshe ma sai na tashi na yi musu sallama na koma wurina da tunanin yanayin zamantakewar da suke gudanarwa mara kangado. Ciki da falo ne wadatattu, kuma kayan katakon da ya zuba mini masu kyau ne da tsada da manyan labuleye. Harda tibi irin ta bango. Na yaba masa sosai domin d'akin nawa ya yi kyau k'warai ko na wata budurwar albarka. Matsalar dai kawai babu bandaki a d'akin duk suna can waje. Dakinsa ne kawai dashi. Kicin din ma na had'aka ne. Amma gidan akwai yalwa irin gini ne na wadata babu takura. Har da wurin saukar baki a cikin gidan Na d'an gyara abinda bai yi mini, na ware kwanukan da zan zuba a kwando, da fulasai, da duk abinda zan nema domin ba na tunanin zan kwashi kayana na kai kicin din gabad'aya, domin fitar da na yi d'azu, na hasashi akwai gyara sosai a tare dasu, gidan gabad'aya babu tsafta har kicin din, kudaje sai bi suke yi, ban sani ba ko suna da mai aiki oho. Na zauna ina hutuwa amma gabad'aya hankalina na kan yaran, mussaman Yusi jiya ya sharbi kuka lokacin da za mu taho sai wayo aka yi masa aka fita dashi daga gidan. Gwaggo wayarta ta lalace sai na nemi ta Hamusu dukda ba ni da tabbacin Yana gidan, amma dai ai garin yanzu ya waye. Muka gaisa Yana 'yar dariya yake cewa."Amina Anya yau kin yi bacci arziki kuwa, na san hanalinki Yana kan yaran nan." Ni ma cikin barkwanci na ce." Ban yi ba gaskiya, ai shiyasa ma na gaza ha'kuri na ce bari na kira ka, na ji ya suka kwana." Ya ce." Suna nan lafiya lau, ga Yusi nan ya warware Yana ta wasansa. Shi kuma Kamalu gashi nan, Yana zubawa Gwaggo ruwa." Na ce." To fara ba ni Gwaggon mu gaisa tukkuna." Ya mika mata watar. Na ce." Gwaggo ina kwana, Kun tashi lafiya?". Cike da kulawa ta amsa tana cewa." Ya kwanan bakunta Kuma." Na ce." Alhamdulillahi Gwaggo. Sai ta dora da cewa ." Ai ana ta fad'in nagartar abokanan zamanki, an ce kansu a had'e yake ba su ta'ba fad'a ba, kema ki bi su a yadda ki ka gansu domin samun daidaito. Ubangiji Allah Ya sanya alheri." Na ce." Amin Ya Allah, ai kam babu lefi, akwai fahimta a tsakaninsu, in sha Allahu zan zauna dasu lafiya." Ta ce.'"To Allah Ya kad'e fitina." Hamusu Ya kar'bi wayar yana fad'in." Fita zan yi anti Amina, ga Yusi ku gaisa, idan na dawo da yamma zan kira ki sai ku gaisa da Kamalu, don ya fita yanzu, na ce miki dama Yana zubawa Gwaggo ruwa, yau me ruwanta ne bai kawo mata ba." Na ce." To shikkenan bawa Yusi wayar." Ya mika masa da zumud'i a tare dashi Yana dariya yake cewa." Mama shine jiya ku ka yi mini wayo kuka gudu ko?" Na sauke ajiyar zuciya a nutse na ce." Babu gaisuwa sai korafi ko Yusi." "Yi hakuri Mama, ina kwana ya kuke?" "Na ce." Ina lafiya lau, zaka zauna a hannun Gwaggo ko?" "Um-um!" Ya furta da sauri." Na yi dariya tare da cewa." Shikkenan zan zo na d'aukeku sati mai zuwa in sha Allahu." Farincikinsa Ya tsananta ya ce." To daga yau zan fara lissafi Mama." Na yi dariya tare da cewa." Ba wa Baba Hamusu wayar zan yi magana dashi." Yana kar'ba na ce." Don Allah da yamma idan babu takurawa kai da Usaini ku kawo mini kekunan d'inkina mana, akwai sauran kayan jama'a a hannuna. Maigidan Ya ce na ajiye aiki Hamusu, shiyasa gabad'aya yanzu hankalina ya karkarta wurin ganin na kafu anan din. Dukda na san da yawa wad'anda za su biyo nan din, amma ina so nan din ma a san ni akan sana'ata." Ya ce."Anti Amina dadina dake akwai himma, kina da zuciya da neman na kanki, Allah Ya dafa miki, in sha Allahu kuma daga na dawo daga kasuwa zan je can gidan naku na samu Usainin." Na ce." Shi ma na gaya masa Ya na jiranka." Ya ce." To shikkenan za mu zo in sha Allahu." Muka yi sallama na kashe wayar na ajiye. Ina sake nazarin yadda al'amurana za su kasance a sabuwar rayuwar da na tsinci kaina a cikinta. To cikin kwana uku kacal na fahimci yadda al'amuran suke gudana a gidan Alhaji Muntari. A kwai kusakurai masu girma da suka riga suka yi karfi a yanzu wanda idan an ce za a gyara su za a samu matsala babba, tunda tun fil'azal a haka suka gina gidan da kuma mijin nasu. Alhaji Muntari rayuwarsa yake gudanarwa irin ta bahaushe zalla, karin abin kuma iyakacinsa sakandire bai yi zurfin karatun boko ba, na addinin ma akwai matsala domin Yana tafka kusakurai a sha'aninsa, kuma yadda na lura dashi ba mutum ne mai so a yi masa gyara ba. Irin mutana nan ne da duk abinda suka yi daidai ne. Tun ranar da ya fara auratayya da ni, na fuskance dhi. Idan mun kammala yana kallona zan shiga bandakin da yake cikin dakinsa na tsarkake jikina, amma sai dai na fito na same shi Yana bacci tare da najasar a jikinsa. Abin takaici kuma da ban haushi baya tashi sallar asubahi. Har sai gari ya yi haske tukkuna zai yi sallah. Sun samu bambamci da Yaya Aminu ta wannan gefan, domin shi Abbansu Yusi akwai ibada. Ta inda dabi'arsu ta zo daya wurin mayatar yin jima'i, duk dare lokacin Yaya Aminu sai ya kwanta da ni, shiyasa da Allah Ya had'a ni da wannan din ban damu ba, tunda jikina ya riga ya saba da Hakan. Alhaji Muntari d'an sharholiya, aji dad'in duniya kawai. Addini bai dame shi ka'in da na'in ba. Ya yi ado da kwalliya ya ci abinci, sannan ya kwanta da mace, wannan shine abinda ya fi bawa muhimmanci. Gidansa babu yunwa da abinci, Yana kuma ko'karin tsarewa kowa mutumcinta. Sai dai 'keta da matan gidan suka sanya a zukatunsu. Abinci d'anye dai gashinan a store. To duk wadda take da girki idan zai fita zai bata dubu biyu kudin kayan miya kawai da markade, tunda Yana Aiko da nama ko kaji daga kasuwa. Ranar da na kar'bi girki, gabad'aya dubu biyun na karar da ita na yi komai a wadatace kamar yadda suke yi ba. Koda na dibi na maigidan da wanda zan ci sai na bar musu tukunyar domin ban san ya za a yi na raba.Na kira anti Maimuna ganin tana da sau'kin fahimta, na ce ta raba a hankali sai na koya. Sai suka fara hayaniya. Anti Jamila na fad'in." Akan me, za ki kwashe miyar duk ki juye a kwanukan yaranki, haba anti Maimuna, akwai son zuciya fa." Na yi shiru ina kallonsu da mamakin irin fitsarar da Jamila ke yi wa Anti Maimuna, ita kuma duk sai ta diririce, hannunta Yana kyarma tana raba abincin take cewa" Kowa za a zuba masa, Jamila ki kwantar da hankalinki." Ta kalleni tana cewa." Ke ma ai da ki ka yi girkin ke ya cancanta ki raba abincinki, tunda dai kin san gidan iyali ki ka shigo, mijinki ya gaya miki komai, to ba sai ki k'arasa ladanki ba." Uffan ban ce mata ba, na danne zuciyata da take shirin danna mata zagi. Anti Maimuna ta ce." Jamila, wai me ki ke nufi ne, na gaji fa da wannan iyashegen da ki ke yi mini, ki dinga yi mini tsawa, tunda Amina ta zo gidan nan, ki ke neman fitina, ina lefi don ta yi abincin ta ce mu raba, ai yaran mu ne gabad'aya. Kuma idan ta ce za ta yi rabon ba ta san ya za ta yi ba, komai sai a hankali. Amma kin zo kina ta yi mini rashin kunya, me ki ke nufi ne?" "To, ai gani na yi, kin fito da son zuciyarki 'karara, idan ke za ki yi miyar ai ba za ki saki jiki ki yi kamar wannan ba, kuma duk kin d'ibe kina zubawa a kwanukan yaranki, waccan ma da ki ka zuba a robar rufaida yogurt ta wacece?" Cikin bacin rai na ce." Wai ke don Allah menene haka? Ba fa girma da mutunci ba ne, ya za a yi mata tana iyakacin k'okarinta a gida, kina yi mata abinda ki ke so, ga yaranta suna jinki, idan kuma watarana suka yi miki fitsara fa, don Allah ki daina haka anti Jamila, mu yi hakuri dukanmu." "Kin ga, don Allah Ya isa, lefin ai na ki ne, me yasa ba za ki raba abincin da hannunki ba, ai mai iyali ki ka aure dole ki yi, ni ma kafin na ajiye nawa sai da na yi wannan bautar, ba zan yadda da sigar munafurci ba, shine za ki kira ta ki ce ta zo ta raba akan me?" Na ce.'' Babu dole Hajiya, ina lefin ma girkin da na yi, kuma ni dai ki dubi tsabar idona da kyau ki ga ni, ba zan lamunci wannan daga wurinki ba, ban shigo domin tashin hankali ba, amma idan kin ce ayi to a shirye nake, haba ina dalili, mata tunda na zo gidan nan ki ke ta hayaniya, ko kin d'auka hakan zai sanya na ji tsoronki ne." "To kada Allah Ya sa ki yi din mana, munafuka kawai, wallahi muddin ki ka ce ba za ki zauna lafiya da mu ba, ke ce a wahale, kuma maigidan zai dawo sai na gaya masa abubuwan da kuka fara yi mini. Ni ban iya rayuwar munafurci ba, kome za a yi to a fito fili a yi shi a gaban kowa." Na ce." Idan Ya dawo ki sanya shi ya sallame ni, tunda ke ki ka sanya shi ya aure ni. Kuma wallahi ki daina kira na munafuka idan ba haka ba, ni duka nake yi ban iya cacar baki, jikinki ne zai gaya miki." Turzumi babban yaronta ya ce." Aikuwa wallahi sai na kwala miki dutse' na fasa miki kai idan ki ka daketa." Yaran gabad'aya suka kwashe da dariya. wadda hakan ya kara kona mini rai! Anti Maimuna ta buga musu tsawa suka yi shiru, ta ce." Kowa ya d'auki abincinsa ya isa haka." Suna fara hayaniyar d'aukar abincin. Na bar wurin raina a kuntacce wannan wane irin gidane ...... *1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank* *07084653262* [11/25, 10:29 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *TALLAH!* *Gidan 'kawa ne da kece raini, abin ma sai wanda ya yi joning da su, nan zai kashe kwarkwartar idonsa ga sau'kin farashi!* 🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨ 🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t *@Arewa book's* *Bintuumarabbale* *Free pege* *16* Ta ina zan yi sake na samu ciki har na haihu a irin wannan gida na alhaji Muntari. Lallai dole na yi takatsantsan, domin tashin farko na lura gidan ba irin wurin da za ka saki jiki ka haihu ba ne, dalilin rashin saiti, da gurguwar rayuwar da iyalinsa suka kafu akai. Wannan marayan da Allah ya jarabce ni dashi ya ishe ni. Ina ro'kon Ubangiji ya ba ni ikon kula dashi tare da d'an'uwansa da kuma tarbiyarsu. Dole kuma koda yarana sun dawo gidan, na sanya ido kwarai a rayuwar da za su gudanar sabili da rashin gamsuwa da tarbiyar yaran gidan. lamarin dai sai da kawai mu ce Allah Ya magance mana. A daran ranan na fara had'iyar maganin hana d'aukar ciki. Dama na yi guzurin abina, zahirin gaskiya ba zan iya haihuwa dashi a irin wannan yanayin da shi kansa bai san menene rayuwa ba. Muka cigaba da tafiya a haka. Anti Maimuna macece mai sau'kin hali, kuma mara son hayaniya, yayin da ita Jamila ta kasance bagidajiya mara fahimta. Ko da yake babu mamaki idan an samu hakan daga wurinta domin a can karkara ya aurota wani kauye a karamar hukumar bichi, shiyasa komai nata take gudanar dashi cikin gidadanci, da kuma zargi. Gabad'aya jininmu bai hadu ba, tunda na fahimci halinta, sai nake takatsantsan, ban ta'ba yadda mun yi rigima ba, duk takalar da za ta yi mini, ba na nuna na san ta na yi. Sabgar gabana nake yi. Idan ba ranar girkina ba ma, ba na fitowa, ina ta sana'ata. Sai dai kuma zamansu a Kamalu a gidan yana nema ya zama d'an zani, domin ko kwana uku ba su yi da dawowa ba, matsaltsalu suka fara kunno kai. Yusi yaro ne mai son jama'a, ba shi da wahalar sabo, kullum Yana cikin yaran gidan su yi ta wasa. Amma ba a k'arewa lafiya sai ya shigo mini yana kuka, Turzumi ya dake shi. Idan na tambaye shi dalili sai ya ce babu komai, kawai dukansa ya yi. Sai dai kawai na rarrashe shi amma abin yana damuna mutuka. Kamalu ya yi ta kumbure-kumbure, yana jin haushi. Na hana shi motsi, domin dama tunda suka dawo gidan na zaunar dashi a gabana yana taimaka mini da wasu abubuwan na sana'ata Ba ni da matsala da maigidan, domin kamar yadda ya fad'a tunda yaran suka dawo hannunsa yake iyakacin bakin kokarinsa. Ya kammala musu komai na makarantar boko da Islamiyya wadda yaransa suke zuwa. Satin da za mu shiga za a koma makaranta gabad'aya. Matsalata yadda Turmuzi ke cin zalin Yusi. Wanda na tabbatar da cewa ba zai yi masa lefin da zai kai hannun jikinsa ba, face dai cin zali da ganin gidansu ne. Sai kuma rashin kwa'ba daga wurin uwarsa. Yau zai dake shi. Amma hakan ba zai hana shi komawa cikinsu gobe ba. Kullum dai sai ya je cikinsu, sai kuma ya dawo mini yana kuka. Ban ta'ba yun'kurin d'aukar mataki ba. Na d'auke kaina kawai, amma zahiri ba na jin dad'in hakan. Watarana ya shigo yana gursheken kuka wanda ya fi na koyaushe. Saman goshinsa ya kumbura har ya yi 'kululu! Na kama shi da sauri ina mulmula masa tare da tambayarsa. Ya ce." Mama Turmuzi ne ya buga mini kai a bango." Na ce." Me ka yi masa yau kuma?" " Ban yi masa komai ba mama, ball ya bugo shine don na mayar masa. Ya kama ni da duka Mamansu tana kallonsa." Kamalu da yake sanya mini zif a jakkunkunan da nake yi na sayarwa. yana huci Ya ce " Wallahi mama ba zan yarda ba dubi fa ki ga yadda ya lun'kuma masa goshi, na rantse da Allah sai na rama masa." Ya tashi da mugun sauri ya kama hanya fita. Na dinga 'kwala masa kira bai juyo ba. Na yun'kura na tashi da saurin gaske na bi bayansa. Sai kawai na same su a farfajiyar gidan suna dambe. Kamalu har ya kaishi kasa yana saman ruwan cikinsa yana ta dukan bakinsa. Kusan gabad'aya muka isa wurin da uwarsa da sauran yaran gidan. ihu! ta kurma ganin jini a bakin yaronta gashi a kwance a kasa yana kuka. Ta yi kukan kura ta janyo Kamulu. Na je na fizge shi daga hannunta. Sai ta hau d'ura masa ashariya tana fad'in " Kashe mini shi za ka yi a gidan ubansa, wannan wane irin samun wuri ne, agola da zage k'wanji akan d'an gida. Na rantse da Allah ba zan yarda ba." Anti Maimuna ta ce." To, wai me ya had'a su ne, Jamila, ba fa a shiga fad'an yarana, a bi komai a hankali." Na ce." Ka da ki yarda Jamila, don Allah ki yi duk abinda za ki yi, wato ke yaranki ba su lefi ko? Kin taba tuhumar dalilin da ya sanya Turmuzi yake dukan Yusi kullum, na san kin sani. Ki dubi goshinsa ki gani, a wurinki akayi kuma kuna kallo ya buga kansa da bango, ba ki mulmula masa ba. Yanzu kuma ko kunya ba ki ji ba kin zo kina kumfar baki, ki yi abinda za ki yi, ai ba tsoronki nake ji ba." Aikuwa zan yi wallahi, ba za ki kawo mana alakakai cikin gida ba, shi yaron naki ai ba mu muka janyo shi ba, rashin zuciyarsa ne yake kawo shi wurina, ban ga dalilin da zai sanya ki kawo mana masifa cikin gida ba, dama an ce yaron nan mugu ne, sannan kuma 'barawo ne, duk mun samu labarin haka. Wallahi tallahi sai sun bar gidan." Gabad'aya wurin ya yi tsit! domin Kalmar 'barawo da ta kira Kamalu ta girgiza kowa, har yaran. Anti Maimuna ta ce." Wace irin magana ce wannan Jamila, shin ke kin san me ki ka haifa, kada fa ki yi wa kaddarar wani dariya, tunda haihuwa ki ke, kuma kowa da k'uruciyarsa." Na ce." Rabu da ita Anti Maimuna jahilace ai, bagidajiya mutuniyar kauye. Don kin kira yarona 'barawo ba zai dame ni ba, tunda kema kin haifa, kuma sai dai idan ke ce za ki bar gidan, amma Kamalu da Yusi zama daram, tunda ba na ubanki ba ne." Wannan maganar tawa ta harzukata har sai da kwalla ta ciko a idonta. Muryata na rawa take cewa." An ce masa 'barawon, ai ba karya aka yi ba, ko za ki musanta ne, sau nawa ana kulleshi a Police station? Wallahi za ki ga matsayina a gidan nan na rantse da Allah sai kin yi dana sanin kirana da jahila, 'yar iska mai suffar karuwai." Na ce." Na ji dai, ni na je makaranta, kuma ba 'yar kauye ba ce ni, ina da ilimi, sannan ba 'kazama ba ce." Ta goge 'kwallar da ta d'igo a kumatunta. Ta tashi yaronta da yake kwance yana kuka ta ri'ke hannunsa suka kama hanyar barin wurin. Na dube ta tare da furta." Ina jiran matakin da za ki d'auka. Jahila bagidajiya kawai." Tunda na lura ba ta so a kira ta da hakan, ni Kuma na ri'ke. Sai ta yi wani kukan kura za ta kawo mini cakuma. Anti Maimuna ta shiga tsakani. Ta dinga d'ura mini ashariya sai ka ce bamagujiya. Na ce." Kin ga aikin jahilicin naki ko, a gaban ya ra ki ke wannan tumasamcin, ni ba zan yi kokawa dake ba saboda na je makaranta. Anti Maimuna fad'i take don Allah Amina ki yi shiru, wallahi mu ba mu taba fad'a ba, da dadi babu dadi muna zaune lafiya." Na ce." To ni ba sakarai ba ce, anti Maimuna ba zan zauna wannan bagidajiyar tana juya ni ba, ita din banza, ai ba tsoronta nake ji ba, kuma ba ita ta ajiye ni a gidan ba, wallahi daidai nake da ita, mu zuba shege ka fasa." Ganin babu sassauci a tare da ni ya sanya ta juya wurinta tana rarrashinta. Ta tura ta wurinta tana bata ha'kuri. Yaransu suka dinga ihu suna kiran Kamalu da 'barawo hooo! 'barawo ne." Yusi ya fashe da kuka ya ruga da gudu ya shige wurina. Shi kuwa Kamalu Yana tsaye durmin danya babu alamun firgici, ko nadamar abinda ya aikata. Kuma ihun da yaran suke yi masa bai sanya zuciyarsa ta yi rauni ba. Na ja hannunsa muka bar wurin zuciyata na 'kuna, duk abinda yake faruwa a gidan, ban tana gaya masa ba, yau kam idan ya dawo zan zayyane masa, ba zan iya ba wallahi. A ranar dama girkin anti Maimuna ne, na yi ta Allah-Allah gari ya waye ya shigo domin da b'acin ran abin na kwana a raina. Ko da ya shigo da safe sama-sama muka gaisa gabad'aya na kasa sakar masa fuska. Ga yaran su ma duk sun damu ganin yanayina sun takure kansu wuri d'aya. Hakan ya kara dasa mini kunci tare da dakacen auran gabad'aya, domin da na tabbatar da cewa bai fi karfin gidansa ba wallahi ba zan aure shi ba. Yanayi na shi ya tabbatar masa da cewa akwai matsala. Ya fara tambayata. Na dube shi takaicinsa na 'kara nu'kurkusata. Na kalli yaran tare da cewa." Ku shiga d'aki." Suka tashi da sauri domin cika umarnina. Na sake kallonsa a karo na biyu Na ce." Ka zauna domin maganar tana da girma, kuma ni ban d'auketa karama ba." Ya dubi agogon da yake daure a hannunsa. "Ban 'ki zaman ba ai, ina da uzuri mai girma a waje, ba na son doguwar magana Amina kada dai ki ce mini kema fad'an yaran za ki shiga." Na ce." Ashe an gaya maka abinda ya faru?" "Kwarai an gaya mini, Ammaa ban d'auki hakan a matsayin komai ba face zaman tare, dole idan Yara suka had'u sai an yi wannan, muma da haka duk muka tashi, ki yi hakuri kin ji ko". Idona ya ciko da ruwan hawaye na ce." Ni fa ba wannan ne damuwata ba, yadda Jamila take Kiran Kamalu da b'arawo shine abinda ya bata mini rai, ai itama ta haifa, kuma ba ta san abinda za ta haifa ba nan gaba." Ya 'bata fuska yana cewa." Kin ga don Allah ki san irin maganar da za ki furta, wane irin lafazi ne wannan? kina fatan na haifi lalatacce kenan?" Hawaye suka fara gudana a kumatuna, na ce." Amma dai ka san da ciwo ko? kuma a'ina ta samu labarin tsalle-tsallen da Kamalu ya yi sai dai idan kaine ka tara su ka gaya musu." "Kada ki zarge ni akan abinda ban yi ba, me zai sanya na gaya musu yaronki ba ya ji, wata'kila ta samu labari ne a wani wuri, kuma kema tun farko sai da na gaya miki ki zauna lafiya da su, kuma ki bi duk abinda suke so domin samun daidaito, su ki ka zo ki ka samu, ba zai yiwu ace kin zo da wani tsari ba." Na dube shi raina a bace." Wallahi tallahi babu wadda zan bi a cikinsu, akan wane dalili? Ai lokacin da za ka aureni ba ka fad'a mini cewa matanka sun fi karfinka ba, ba zan jure ba, akan yarana zan iya komai, idan ba za ka siya mini mutunci ba, ka sawwake mini ba." Ya ja tsaki Yana fad'in." Ai aure ba wasan yara ba ne, duka sati hud'u kacal, kin fara bayyana mini halinki, ba zan sake ki ba, saboda ina sonki, Yara kuma ni na ce ki zo da su zan ri'ke, idan hakan be yi miki ba, ki tattarasu ki kai su wani wurin, ni babu rabuwa a tsakanina dake." "Cikin kuka sosai na ce." Wallahi ba zan iya ba, muddin ta kara aibata mini yaro sai na yi sharia da ita, ai tunda ya zo gidan bai ta'ba shiga wurinta ba balle ta ce ta nemi wani abu ta rasa, wallahi 'yansanda ne za su raba mu." Kuka nake yi sosai. Hakan ya sanyayyar masa da jiki. Ya ce." To na ji zan ja mata kunne, ki yi hakuri, sannan kuma ki bi shawarar da na baki, ki zauna lafiya da su, bayan wannan kuma idan kin yi girki ki dinga rabawa da hannunki, ki daina kiran Maimuna, duk abinda ki ka san zai janyo zargi kada ki yi shi." Na goge hawayen kumatuna tare da cewa." Ni fa na gaya maka babu wadda zan yi wa biyayya, Kai ka ajiye ni, kaine dole, tsakanina da su girmamawa ce kawai, amma ba zan bi son zuciya ba." "To shikkenan, ki daina kukan haka, ya isa." Ya fad'a da sigar lallashi. Sai da ya tabbatar na yi shiru tukkuna ya kama hanyar fita yana fad'in."Ashe haka ki ke da rigima dama. Tun daga ranar Yusi bai kara shiga cikin yaran Jamila ba. Ni ma kuma ban 'kara barinsa ya fita ba. Idan garin Allah ya waye muna tare a wurina. Kamalu na taimaka mini, shi kuma yana ta wasansa shi kadai. Anti Maimuna ta same ni kan cewa hakan da na yi bai dace ba, na takure yara wuri d'aya na hana su sakewa. Na ce mata yadda na yi shine kwanciyar hankalina. Duk da haka ba ta ha'kura ba sai da ta san yadda ta yi ta janye Yusi ya zama d'an dakinta. Ganin kwana biyu Yana zuwa wasa lafiya lau ba a dukansa, sai na kyaleshi, dama kamar yadda ta fad'a babu yadda za a yi yaro ya rayu shi kadai, ko shi Kamalu dana takure a wuri d'aya don ba yadda zai yi ne. Shiyasa lokacin da suka fara zuwa makaranta kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda murna. Na gargad'e shi sosai, akan ya kula. Inda hankalina ya kwanta ma direba ne yake kai su ya kuma dawo dasu, Islamiyya ce kawai suke tafiya da kansu tunda a cikin unguwar take. Yusi ya riga ya zama d'an d'akin anti Maimuna, don jininsu ya hadu da Salima, itace ta k'ara ri'ke shi, ko makaranta tare suke tafiya, ba ya jiran d'an uwansa, Yana shiryawa yake zuwa wurinsu, sai dai shi Kamalun ya tafi shi kad'ai. Hakan ya daga hankalin Jamila, macece mai zargi, ta hana mu sakat a gidan, neman rigimar yau daban dana gobe, fadi take na zo na rikita musu gida, ina ko'karin rabawa yaransu zumunci, tunda dalilin sha'kuwar Yusi da yaran anti Maimuna ya haddasa ba'kar gaba da rikici tsakanin yaran nasu. Turzumi da 'yan'uwansa, kaf sun daina shiga wurin Anti Maimuna, wanda dama can nan ne, dandalin wasansu, saboda ita tana da sau'kin hali, kuma tana jurewa hayaniya shiyasa kowane yaro yake da sakewaa wurinta, ba kamar ita jamilar ba. Ni dai tunda muka yi cacar baki akwanakin baya, ban sake bi ta kantaba, al'amurana sun sha kaina. Yanzu na ajiye d'inkunan jakkunkunan da nake yi, na durfafi manya dinkuna irin na mutan nijar mali, da sengal. Tun lokacin da na je Maiduguri bikin Babandi na yi wa Ya Falmata d'inki, Allah Ya haskaka al'amarina. Jama'a suka dinga kar'bar style a wurinta. Kawai sai ta yi tunanin sayan kayan aiki da irin sutturun da suke tu'amalli, ta kira ni a waya tana sheda mini, za ta turo mini da aikin, idan na kammala sai nasa a mata a mota, ita tana da masu saya a hannu. Na yi ta godewa Allah, saboda na san wani cigaba ne ya zo mini. Sai dai tunda na fara had'a-hadar ayyuka suka yi mini yawa, ranar girkina na kan sha wahala sosai, kuma wani aikin idan ta turo mini da sauri ake bu'katarsa. Kamalu makaranta dama shine yake taimaka mini da sanya zufa, jera stones kalmasa da sauransu duk ya iya wannan, Hamusu ko Usaini wani daga ciki ya kai mini tasha a dora a mota. Yanayin aikina ya fara ta'ba zamantakewata a gidan. Domin ranar girkina zahiri ni ma na sani, ba na gama abincin rana da wuri, Yara suna makara a makaranta, wasu lukutan ma haka suke tafiya ba su ci ba, sai sun dawo tukkuna. da daddare ma sai na kai bayan Isha'i, ban fito daga kicin ba, gajiya ta rafkar da ni, maigidan ya zo da buk'ata na kasa katabus, jikina ya mutu, babu wata kulawa da yake samu. Anti Maimuna dai tana yi mini kawaici ba ta ta'ba korafi ba. Jamila kuwa mun sha musayar yawu da ita, domin duk lokacin da ban gama abincin rana da wuri ba har yara suka tafi makaranta ta dinga mita kenan, kamar ta zage ni, tana fad'in ai ba neman kudi na zo yi ba, bautar aure na zo yi, akan me zan dinga azabtar dasu. Wasu lukutan shiru nake yi mata, amma idan ta kai ni bango kaca-kaca nake yi mata na ce ba zan yi girkin ba, ta yi duk abinda za ta yi.....✍️ *Gudun aure 1k on talgram via 0542382124....Binta Umar gtbank ko 7084653262 Binta Umar Opey bank. Yan nijar dala dari katin Airtel. Ga masu bin wannan book din ina miko gaisuwata zuwa gareku. Ina daf da kammala free peges tuntuni dai an fara payment labarin nan ba mu fara shi a hakan zan ce muku sharar fage ne. A hanzarta biya domin jin yadda za ta kaya. Na gode muku masu messages fatan alheri tare da yabo bisa wannan littafin Allah Ya saka muku da alheri🤲💝* *07084653262* *TALLAH!* 🌲🌳🌿☘️ *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* [11/26, 10:38 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* *TALLAH!* *Gidan 'kawa ne da kece raini.💯* 🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨ 🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t *@Arewa books* *Bintuumarabbale* *17* *Free pege* Ashe akan ga'ba muka yi wannan sa'insar. Sai maigidan gabad'aya ya d'auki laifi ya d'ora mini, yadda yake yin fad'a shi ya kara tabbatar mini da cewa a kufule yake da ni, dama yana Jin haushina. "Zaman aure ki ka zo gidana Amina, na gaji da rabon fad'a, kusan koyaushe Jamila sai ta kawo mini korafi akanki, na gaya miki tuntuni matan nam suna zaune lafiya, ban saba da irin wannan tashin hankalin ba, me zai sanya daga zuwanki ki d'aga mana hankali, muddin ba za ki bi umarnina ba, kamar yadda na sanya ki ka ajiye aiki, to d'inkin ma za ki daina yi mini a gida, domin ba zai yiwu ki zo kina neman kudi a gidana ba, kuma kina watsi da umarnina, ni kaina ba na samun kulawa a ranar girkinki, kin fi bawa neman kudi muhimanci, ki gyara muddin kina so ki zauna da ni." Ban katse shi ba har sai da ya kai 'karshen maganarsa na ce."Ka yi hakuri don Allah, in sha Allahu zan gyara, maganar kuma na zo zan lalata maka gida babu wannan ajandar raina, da zuciya daya na shigo gidanka, sai kaine ma ka 'boye mini wasu abubuwa, amma hakan ba zai sanya na ce ka sake ni ba. Abu na biyu kuma ina kara gaya maka babu wata mace da zan yi wa biyayya, idan lallai sai na bi tsarin da matanka suka ginu akai ne to lallai ba ka shirya zama da ni ba, zan dai yi maka biyayya tunda kai ka ajiye ni. Sannan don Allah ina neman alfarma a wurinka idan zan samu." Na kai 'karshen maganar ina dubansa. Ya ci kunu sai girgiza kafa yake yi da kyar ya ce."Wace irin alfarma ce?" "Ina so na nemi mai aiki 'yar matashiya wadda za ta dinga taimaka mini, ka ga Allah Ya sanyawa lamarina albarka, ina so na yi amfani da damar kafin ta kubce mini." Ya nisa kafin ya ce."Ita Iyami da take zuwa tana yi muku wanke-wanke da shara menene laifinta? Ba fa na son neman fitina Amina, idan ki ka ce zaki d'auki mai aiki ki ke kad'ai zai iya kawo hayaniya a gidan." "Ba ka fahimta ba, zan samu wadda za ta taya ni aiki ne ranar girkina, tunda kun ce yara suna makara a makaranta, kai ma baka samun kulawa daga wurina, shiyasa na yi wannan shawarar." "Ban yadda ba." Ya fada hankalinsa yana kan wayarsa. Shiru wurin ya yi gabad'aya raina ya gama baci da abinda yake yi mini. Ya ce." Sai dai ki dauko wata daga cikin yaran dangi, zan yi miki wannan alfarmar. Amma ban yadda da d'auko mai aiki ba, bayan kuna da ita, na gaya miki babu wani tsari da za ki zo dashi da zumar rusa mini zaman lafiyar gida." Ya tashi ya kama hanyar fita ba tare da saurari abinda zan ce ba. Yadda na fahimce shi ya fi tsoron Jamila fiye da anti Maimuna, ko meye dalilin haka oho! ko da yake 'yar kauye ce ai, Allah kadai ya san irin surkullen da take yi a gidan. Gabad'aya sai ya jefa ni a cikin tunani. Ba yarinyar da zan je na nemi alfarmar iyayenta su ba ni kai tsaye sai Yusura yarinyar Sahura. To kuma idan na yi hakan ban yi wa kawata adalci ba, itama tana zuwa aiki, kuma yarinyar itace take d'awainiya da 'kananta tunda ta yi wayo. Na yini ina nazarin yadda zan yi, domin fa zahiri idan ba mai'aikin nan na samu ba abubuwan ba za su gyaru ba, ni kuma ba zan fasa neman kudina ba, gashi daga farawa ta zuwa yanzu na samu kudi sun kai dubu dari biyu da hamsin, babu yadda za a yi na yi watsi da wannan damar da Allah Ya kawo mini, dole na yi wa marayun yarana digin da zasu amfana a gaba, ubansu bai bar musu komai ba. Da yamma bayan la'asar yara duk suna makaranta, ina kan keke Sahura ta yi sallama. Cike da farinciki na tare ta. Ina fad'in." Wallahi yau yini na yi da tunaninki." Ta zauna kan kujera tana cewa." Sai gashi Allah Ya kawo ni, daga aiki nake sai kawai na ce bari na karaso mu gaisa, kin san babu wata nisa fa tsakanin nan da wurin aikin na mu." Na ce." Aikuwa kin kyauta mini wallahi bari na kawo miki ruwa. Na kawo mata ruwa da d'an snacks da lemo na zauna ina fad'in." Me zan girka miki, na san kina tattare da yunwa daga ganinki." "Wallahi a koshe nake, ai ba daga wurin aikin nake kai tsaye ba, mun je can gidan ogan mun duba mahaifiyarsa bata da lafiya, yau kwana biyu kenan da dawowarta daga egypt ganin likita, shine fa muke tattara mukaje dubata, mun ci mun sha ba na tare da yunwa." Na ce." Ayya, to ko ruwa ai kya sha Sahura." Ta d'auki d'aya ta kai bakinta tana fad'in."To shikkenan." Bayan ta ajiye ragowar ruwan na dubeta a nutse na ce." Sahura ya aikin fatan komai lafiya, na ga fa kin yi kumatu, ko ya yi muku karin albashi ne ." Sai ta fashe da dariya tana cewa." Muna sa rai dai 'kawata, kin san ma na nemi alfarma a wurinsa za a mayar da ni daya daga cikin kamfanoninsa dake kusa da mu, saboda kafin na je Ina makara gaskiya, to da ya tambayi dalili sai na gaya masa, na kuma nemi alfarma." Na ce." Hakan zai fi miki gaskiya, to Ina yi miki fatan alheri kawata, Allah Ya hadamu da rabonmu na alheri ." Ta amsa da Amin tana bin falon da kallo. Ta ce." Su Kamalu suna makaranta kenan?" "Suna makaranta wallahi, kin san wani abu kuwa?" Ta girgiza kanta tare da mayar da hankalinta gare ni. "Alfarma nake nema a wurinki, ban sani ba ko Idiris zai amince buk'atar tawa dai ta wucin gadi ce, idan ma zan samu a ba ni duka har aure zan fi son hakan." "Wace alfarma ce wannan ki fad'a kai tsaye muddin Ina da iko, zan yi miki ai mun zama daya." Yadda ta fadi maganar da karsashi, shine ya bani kwarin guiwar fayyace mata halin da nake ciki. Na d'ora da cewa." Sai kuma na yi tunanin yarinyar tana taimaka miki kema, sannan tana kula da 'yan'uwanta a duk lokacin da ki ka tafi aiki, shine dalilin da ya sanya na janye maganar a zuciyata." Murmushi ta yi tare da dafa kafad'ata ta ce." Ki daina fad'in haka, idan ta ni ce yau ma Yusura ta dawo hannunki, ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, na san za ki kula mini da ita, maganar kula da gida da yara kuma, ba ki ji Ina gaya miki cewa wurin aiki za su dawo da ni kusa da gida ba, ai kin yi maganar akan ga'ba in sha Allahu kuma Abbansu ba zai k'i amincewa ba." Ajiyar zuciya na sauke mai sanyi na ce." Na gode kwarai da wannan karamcin kawata, in sha Allahu duk sabgar makarantarta zan yi mata kokari sai ta dora daga inda ta tsaya tunda akwai makarantu anan din." Ta nisa tana kallona." Kina ganin dai babu matsala a wurin abokanan zamanki ko?" "Babu wata matsala Sahura, ai tunda maigidan ya amince magana ta kare, Jamila ce matsalar gidan itama na san inda zan yi da ita. Ta sauke ajiyar zuciya a nutse ta ce.'" in sha Allahu rabbi ina komawa gida zan sanar da Abbansu duk yadda muka yi za ki ji ni a waya." Na ce." To shikkenan, ina godiya k'warai, Allah Ya bar mana zumunci." To cikin ikon Allah ba a sha wata wahala ba a wurin Idiris ba ya amince. Sahura ta kira ni a waya tana gaya mini na tura a d'auko yarinyar domin babanta ya amince tare da tabbatar mini da cewa ya yi farincikin hakan saboda shedar da ya yi mini yana da tabbacin yarinyarsa za ta samu ingantaciyar rayuwa." Na ji dadin dawowar Yusura hannuna. Dama tun fil'azal yarinyar ta horu da aiki, shekararta goma sha hudu ta iya komai, sai dai ba duka nake sakar mata aikin ba, ina sanya mata hannu saboda yawan aikin ba irin wanda take yi ba ne a gidansu, na nan da yawansa. Ranakun da ba ni da girki kuwa, idan na fita na gaisa da matan gidan na koma wurina ba na sake fitowa, za mu dukufa aiki ni da yaran gabad'aya, lokacin makaranta da sallah ne yake tashinmu. Kafin ki ce kwabo al'amurana sun 'bunkusa, duk sati sai na hada bacco na kaya sama da set talatin an kai Maiduguri. Tun ina lissafin dubu dari biyu uku hudu a cikin acct dina, sai na dawo lissafin miliyan. Al'amarin ya dinga ba ni tsoro da mamaki. Sai kawai na ajiye a raina cewa 'Allah ba yadda ba ya shirya lamarinsa' Ranar da muka wayi gari da Azimi na farko. Baba Sule ya dira a gidan. Dama ya kan zo sa'i da lokaci da matsalarsa na d'auki kudi na bashi. Wannan karan kuma da buk'atar na saya masa kayan abinci ya zo, saboda wai Usaini ya gaya masa harkokina sun bud'e yanzu, gashi babu abinda na nema a gidan aurena, tunda dai kowa ya sheda gidan Alhaji Muntari da kulawa ta fanni abinci da suttura babu yunwa. A cewarsa neman da nake yi sai na wahalta musu tunda suna raye sai na samu lada." Na riga na san son zuciyarsa sarai, idan ba haka ba mai zai sanya ya dinga zuwa yana cewa na bashi kudi, har binciken halin da nake ciki yake yi. Na dube shi a tsanake na ce." Baba ka koma gida in sha Allahu zan aiko muku da kayan abinci kai da Babanmu dama na yi niyyar hakan, amma don Allah ka dan rage zuwa, tunda ka ga ba ni kadai ba ce a gidan ina da kishiyoyi kada hakan ya janyo mini matsala." Ya ce." To, zan rage zuwa idan kin san abinda ya dace, ni dana had'a auranki da Alhaji Muntari ai kamata ya yi ace ina da kaso a wurinki, amma sai na ro'ka k'i, ki dinga tunani" Na ce." Ni fa ba wani abin nake samu da mutumin nan ba Baba, don Allah ka daina wannan maganar, duk alherin da nake yi muku daga aljihuna yake fitowa, saboda haka don Allah ka d'auke 'kafarka ba na so wani ya ta'ba muku mutumcinku." Da kyar na rarrashe ya kama hanya ya tafi bayan na d'auki dubu biyar na bashi a matsayin kudin mota. Kwana biyar da zuwansa na gama had'a komai. Sai na fara tunanin yadda za a yi a fita da kayan domin kuwa matan gidan za su iya zargin na mijinsu ne na d'iba tunda yana ajiyesu da yawa. Da daddare aka shigo mini dasu lokacin kowacce tana wurinta, sai na yanke shawarar kawai a fitar dasu da daddare. Na kira Usaini a waya na gaya masa ya zo da adaidaita sahu ya d'auka kowa ya kai masa, na dora musu dubu talatin talatin akai. Cikin rashin sa'a, lokacin da Usaini ya zo d'aukar kayan maigidan yana nan, tare da abokanansa a waje dama suna zaman shan ruwa idan sun yi asham sai su watse, abinda na cewa Usaini kenan bayan sallar asham zai zo. Minti goma da fitar Usaini ya shigo d'akin Muna zaune da yara gabad'aya a falo, ina yanka wasu riguna su kuma suna kallon tibi. Ya zauna kan kujera, suka dinga jera masa sannu da shan ruwa, ya amsa a takaice. Na daga kaina na dube shi. Babu fara'a, a fuskarsa, zaman da ya yi ya nuna yana buk'atar magana da ni, ga kuma yara. Na dubi Yusura a nutse na ce." Ku je d'aki ku yi kallon a can tunda da tibi. Suka tashi da saurin na ajiye almakashin hannuna. Na ce."Barka da shan ruwa." Ya dube ni. "Barka dai, wanene yanzu ya fita da buhunhunan shinkafa da su taliya?" "Usaini ne k'anina su Baba na sayawa." Ya zuba mini ido na minti daya kafin ya ce." A ina ki ka ga kudin sayan wad'annan kayan abincin Amina, rankatakaf fa komai akwai kayan sun tassama dubu dari uku a yadda rayuwar nan take tsada." Dariya na yi na ce.'' Ka raina wannan sana'ar da nake yi kenan, wallahi da ita na saya domin neman lada." Ya hade fuskarsa. " Gaskiya ban yarda ba, idan kin sayi wani abu da kudinki, to za ki ta'ba nawa da nake ajiye muku idan kin yi hakuri ma ai duk shekara ina fitarwa da surukaina abin bud'e baki." Cikin zuciyata na ce' an zo wurin' Zuciya ba ta da 'kashi zaman da ya yi, sai da na hasashi zargi a fuskarsa. Na ce." To, Allah ne dai shahidi kuma shine zai yi mana hisabi bisa zargin da ka yi mini, ba zan yi rigima da kai a wannan watan ba, amma na barka da Allah ." Daga haka ban sake magana ba, na d'auki almakashina na cigaba da aikin gabana. Jikinsa a sanyaye ya tashi ya fita bai sake ce mini komai ba. Duk yadda na so na daure zuciyata na cigaba da kyautatawa mutumin nan kasawa na yi. Da na kalleshi zan ji haushinsa ya turnukeni. Zama fa kawai nake yi dashi, har yanzu ba na jin sonsa a raina amma shine yake ko'karin gaya mini magana. Ya dinga raragefe neman shiri, na share shi, da kyar ya shawo kaina na ha'kura na sakar masa jiki yana ta fad'in shi fa ba zargina yake ba, kawai su'btar baki ce ya yi.....✍️ *Gudun aure 1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank* *07084653262* *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* *TALLA!* 🌲🌳🌿☘️ *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* [11/27, 10:17 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A* TEEMAH DATA SERVICES MTN 1GB @550 2GB @950 3GB @1450 4GB @1550 5GB @1700 CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306 8037026306 fatima musa ibrahim opay *TALLAH!* 🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨ 🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t *1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari katin Airtel. Ga masu karatu a arewa book akwai more peges domin na yi nisa a can din.* *07084653262* *08089965176* *@arewa books* *Bintuumarabbale.* *Free pege* *18* Wannan ya wuce da wasu kwanaki wani abu bai sake faruwa ba, tunda Ina iyakacin bakin kokarina wurin ganin na fita hakkin maigidan da abokanan zamana a duk ranar girkina. Sosai Yusura take taimaka mini da wasu ayyukan, itama Iyami tana nata bakin ko'karin. Goman karshe hada-hada ta yi yawa. Ya Falmata ta sake jibgo mini wasu ayyukan tare da sharad'in ana buk'atarsu kafin sallah. Babu abinda nake hangowa sai ruwan kudin da zan samu. Wannan dalilin ya sanya na hana kaina sukuni bacci arziki ba na yi. Yanzu haka kekuna biyu gareni ni na hau daya Yusura ma ta hau tunda ta fara iya wasu abubuwan ina nuna mata. Kamalu da Yusi suna aikin jera stone's da sauransu. Ranar girkina kuwa Iyami na sakarwa ragama duk da na san da cewa ba haka tsarin gidan yake ba. Iyakacinta shara da wanke-wanke, sai zuwa cefena da 'yan aike aike, amma ni kam har girkina na bar mata, muka yi da ita zan dinga bata dubu biyu kullum idan zata tafi. Ita kuma Yusura la'asar ta na yi zan tashe ta ta je ta feraye doya ta soya ita na dorawa alhakin hakan. Anti Maimuna ba ta ta'ba tankawa ba ila iyaka idan an kammala ta zo ta dibi abinci. Babu korafi a tsakaninmu tana dannewa koda taga abinda bai yi mata ba, gashi dai itace uwargida amma bata neman fitina da kowaccen mu, dalilin da ya sanya ma kenan na sayi shadda mai tsada yadi goma sha biyar na bada yadi bakwai a dinkawa Kamalu da Yusi sauran Kuma nake da kudirin yi musu d'inki na gani na fad'a ita da Yusura duk da cewa maigidan ya yi musu kala uku Yusura da su Kamalu bai bambamta da yaransa ba, hakan ya sake ba ni karfin guiwar yi wa 'yarsa duba da irin kara da kawaicin da uwarta take yi mini, uwa uba kuma yarinyar tana kaunar Yusi sosai, komai ka ji tace Yusifa. Yau bayan shan ruwa da kadan ina bandaki na ji sautin muryar Jamila a falona. Da sauri na cud'a jikina na zuba ruwa na fito. A gurguje nake yi komai dalili girkina ne, ba na so kuma maigidan ya shigo ya riskeni a hargitse, dama na fahimci kwana biyu a wuya yake da ni, dalilin baccin da yake riskata ina yi bayan ya gama zaman majalisarsa ya shigo, duk ranar girkina baya samun wani Abu a wurina saboda mugun gajiyar da nake yi. Shiyasa yau na sauka daga kan keke da wuri domin ina so na faranta masa. Tana tsaye sai fad'a take yi wa Yusura. Ita kuma yarinyar ta yi shiru idonta ya ciko da hawaye. Raina ya baci ainun. Na ce." Ke kuma menene haka don Allah za ki tasa yarinya a gaba kina fad'a mata wasu maganganu ko zamanki take yi ne a gidan?" Ta kalleni kafin ta ce." Amma dai kin san abinda ki ke yi ba kya kyautawa, ya za a yi ki dinga bawa wannan yar yarinyar aikin da bata iya ba, idan ita Maimuna ba zata iya yi miki magana ba to wallahi ni ba ki isa ba, ba zai yiwu mu dinga cin abu da 'karni ba, domin koyaushe doyar da yarinyar nan take yi ba ta soyuwa zubarwa muke yi ni da yara, wallahi ba zai yiwu ba dole maigidan ya ji abinda yake faruwa domin tun wuri ya yi wa tufkar hanci." Na ce." To sai ki bi shi ki gaya masa ai yana waje ba nisa ya yi ba, idan ya shigo sai ki sanya ya sake ni, ko ya kori Yusura tunda ta soya doya ba ta soyuwa ba." Ta bude baki kenan za ta yi magana ya shigo. Ganinta a tsaye ya sanya ya ce." Da azimin ma sai kun yi mini masifa a gida, menene kuma?" Ta fara gaya masa abinda ya kawota. Ya dube ni tare da cewa." Amina ba karya Jamila ta yi ba doyar nan bata suyuwa karni take yi yau ni kaina ban iya ci ba wallahi, bayan kunyar da ki ka ba ni a cikin abokai, ashe dama ba ke ki ke yin aikin nan ba?" Shiru na yi masa ban tanka ba. Ya dubeta tare da cewa" Tafi wurinki zan yi maganin abin." Ta juya ta tafi ba ta sake cewa komai ba. Yana shigowa falon na sake daure fuskata. Yaran suka tashi suka bar wurin. Bai ce mini komai ba, ya wuce cikin kuryar d'aki. Minti biyu na ji yana fad'in." Ina ki ka ajiye mini dabinon nan dana shigo dashi kwanaki?" A cunkushe na ce." Ka duba cikin doruwa." Gabana ya buga da karfin gaske tuna abinda na ajiye a dorowar. Da sauri na tashi na shiga d'akin na same shi a tsaye hannunsa rike da kwalin maganin, daya hannun kuma robobin dabinon ne. Jikina ya yi mugun sanyi. Kai a kasa na nufe shi. Ya dubeni ya jijjiga kansa. Cikin mamaki da al'ajabi ya ce." Maganin hana d'aukar ciki a gidana Amina, Ashe ha'intata ki ke yi dama, ina ta wahalar banza wuri zuba kwaya-kwayena ke kuma ki sha magani su tsinke su bi rariya, dama da wannan nufin ki ka shigo mini Amina? me ya sa ki ka yarda da haihuwa da tsohon mijinki wanda bashi da ko kwabo sai ni da Allah Ya rufawa asiri ki ke gudun had'a zuri'a da ni bayan tun kafin mu yi aure na gaya miki ni mutum ne mai burin tara zuri'a." Cikin sanyin jiki na ce." Wallahi ba haka ba ne, na yi hakan ne domin ni da kai mu huta, mu mori amarcinmu, amma mai zai sanya na guji haihuwa da kai bayan kana da nasaba, kuma Allah Ya rufa maka asiri, idan na yi haka ai na yi butulci ga Allah, don Allah ka yi hakuri." Babu sassauci a tare dashi Ya ce." Watanki takawas a gidan nan Amina don Allah ki gaya mini amarcin da ki ka bari na ci dake, tun baki fi sati biyu ba a gidan nan ki ka daina ba ni kulawa, bayan kin san ni din namaji ne mai buk'ata, kin fi bawa neman kudinki muhimmanci, a gaskiya wannan lamarin ba zai tsaya iyakacin ni dake ba, dole waliyinki Sule ya ji abinda yake faruwa domin akwai cutarwa a ciki." Jin haka ya sa na fashe da kuka ina fad'in." Don Allah kada ka fitar da maganar nan wallahi zan gyara, magani kuma daga yau na daina amfani dashi, ka yi hakuri ba zan sake ba." Kuka nake tukuru, harda face majina. Sai jikinsa ya mutu, ya riko ni muka zauna kan gado yana cewa." Tunda wannan shine karo na farko na yi hakuri, kuma kin yi alkawarin ba za ki sake ba, amma ina so yau ki ba ni kulawa ta mussaman domin a mutukar buk'ace nake dake." Da sauri na ce." In sha Allahu na yi alkawari ba zan sake shan magani ba, kuma san dinga baka kulawa." Ya girgiza kansa yana bina da wani shu'umin kallo. Saurin fahimtarsa da rashin riko ya sanya nake jin zan iya cigaba da rayuwa da shi duk da cewar har yanzu zuciyata bata gama aminta dashi ba. Dinkin da na yi wa Salimat ya d'agawa Jamila hankali, ta fito tana ta zage zage da neman fitina, tana kiranmu da munafukai ni da Anti Maimuna. Babu wadda ta kulata a cikinmu. Hakan ya k'ara yi mata ciwo, da maigidan ya dawo ta gaya masa. Ya shigo yana tambayata na ce masa hakane na yi wa Salimat da Yusura d'inki iri daya. Ya yi shiru na minti biyu kafin ya ce." Kema Amina ba ki so zaman lafiya, mai zai sanya ita jamilar ki kasa yi mata kawaici, itama ai sai kisa yaronta daya zata ji dadi." Saboda ba na so maganar ta yi tsayi na ce." Allah Ya kaimu wata shekarar sai ayi, amma ka gaya mata d'azu da ta fito tana zaginmu ba tsoronta ba ne ya sanya na yi shiru, saboda muna watan Azimi ne, wallahi ta kara zagin iyayena sai na yi mata duka." Yana dariya yake cewa." Ke yanzu kina ganin Jamila zata daku a hannunki?" Na ce." Abu ne mai sau'ki." Sai ya tashi ya fita yana dariya tare da cewa." Amina rigima kenan." Washe garin sallah Yusura ta tafi gidansu don tun kafin sallar take ce mini a can za ta yi. Kamalu har ya yi naci da magiya ya gaji, so yake na bar su su je gidan Gwaggwo su yi sallar a can na ce a a dalili ba na son abinda zai sake danganta shi da unguwar muddin ba da ni ba, balle har su hadu da Saminu. Haka nan ya ha'kura, gashi ba wani shiri yake yi da yaran gidan ba, sai ya sake takura sosai, shi Yusi Yana can wurin Salimat a can ma yake wanka kaf kayan sallarsa suna wurinta. Anti Maimuna ce ta tursasani barinsa ya bi yaran gidan zuwa gidan kakarsu uwar mijinmu Hajiya dogara. Ba yadda na iya da ita, saboda zahiri Ina ganin kimarta ganin yadda take mu'amulantata a gidan. Kamalu ya dinga murna da tsalle, Yusi yana kyalkyala masa dariya. Da zasu tafi sosai na yi masa fada akan ya kiyaye ya kula banda rawar kai, kuma babu ruwansa da Turzumi tunda ba shiri suke yi ba. Ya yi mini alkawarin zai kula. Sai dai kuma sai da na yi dakacen barinsa zuwa gidan Hajiya Dogara dalilin satar da tace ya yi mata. Suka dawo gidan kowa ransa babu dadi, domin tun a can Turmuzi ya Tara 'yan unguwa suka ture shi suna yi masa ihun b'arawo. Yadda ya shigo a firgice shine abinda ya tabbatar mini da cewa babu lafiya. Yana zama ya fashe da kuka! Hawaye masu tsananin gudu suka dinga tsere a kumatunsa. Ina ji yo hayaniyar yaran gidan daga waje muryar Jamila tana ta tashi. Salimat da Yusi suka shigo. Ta zauna a sanyaye tana cewa." Wallahi bai d'aukarwa Hajiya Dogara kudi ba, ni na rasa ma a inda ta ji cewa Yana sata. Abinda ma tunda muka je gidan bai zauna ba Yana kofar gidan a zaune, sai da zamu ci abinci ne na ce a kirawo shi, wai amma tana bud'e jakarta ta duba ta ga babu dubu daya sai tace shine ya d'aukar mata. Sai da zamu tawo tukkuna tana daga kasan tabarma ta ga kudinta ashe anan ta ajiye. Amma sai ta yi shiru ba tace komai ba, kuma tana ji fa Turmuzi ya Tara Yara suna yi masa ihu amma bata hana shi ba, kuma bata gaya masa cewa taga kudin ba." Murmushin takaici kawai na yi na ce." Salimat tashi ki je kawai Allah Ya kyauta." Ta tashi jikinta duk a sanyaye ta fita. Yusi ya dube ni, murya na rawa ya ce." Mama me yasa kowa ya tsani Yayana ne?" Sai ya fashe da kuka ya kwanta kasan kafet yana rerashi." Na dubi Kamalun da lokaci guda ya firgice. Na ce ka gaya mini gaskiya ka d'auki kudin Hajiya dogara ko baka d'auka ba?" Ya sa hannu ya goge hawayen da yake zuba a fuskarsa. Ya ce." Wallahi ban d'auka ba Mama sharri ta yi mini." Na girgiza a kai, a raunane na ce." To shikkenan ni ma na aminta baka d'auka ba, yadda yanayinka ya nuna, ka share hawayenka ka ji ko." Ya sauke ajiyar zuciya tare da sanya duka hannuwansa biyu Yana goge fuskata. Koda maigidan ya dawo ban ce masa komai ba. ba wai don abin bai yi mini ciwo ba, sai don kimanta mahaifiyarsa. Amma zahiri da wata ce ta yi mini haka inaga sai na daureta. Kuma maganar ban san abinda zata haifar ba tunda Ina kan dokin zuciya, kuma uwa ta zarta komai. Ina fata hakan dai ya zama na farko domin idan ta sake faruwa ba na tsammanin zan yarda. Na san ya ji labarin abinda ya faru, amma bai tare ni da maganar ba, sai ya ja bakinsa ya yi shiru, hakan ya k'ara sanya ni karatun ta nutsu, tunda bashi ya haife shi ba, ai ba zai damu da abinda akayi masa ba, wata'kila shima ya yarda da zargin da akayi masa tunda shi Kamalu a kuyarsa ta riga ta yi kuka. Uku ga sallah 'yan gidanmu suka zo kaf dinsu har da yaran Baba Sule. Su Hadiza yanzu an yi hankali an daina giggiwa yadda na lura ma kamar shakka take yi ganin yadda Allah Ya rufa mini asiri. Zuwansu bai daga mini hankali ba tunda muna da abinci wadatacce kajin sallar da muka soya suna da yawa ko rabi ban ci a kasona ba. Ina gama yi musu abinci na d'auko musu naman gabad'aya na ce su juye akan abincin. Ruwa muke dashi babu lemo nasa aka sayo musu katon biyu. Suka yi facakarsu yadda ransu yake so ban hana su ba. Da za su tafi kowacce na bita da dubu d'aya sannan na bawa Hadiza atamfa turmi biyu iri d'aya dukda tace daga nan gidanta zata wuce na ce don Allah ta koma gidanmu ta kaiwa Ummansu da anti Sakina Ummansu Saminu, na so na dinka musu aiki ya yi mini yawa, na dora musu dubu bibbiyu akai kudin dinki. Alhamdulillahi shekarar ta zo mini da bud'i da nasara mai yawa. Domin ayyukan da na yi sun tara mini kudi masu nauyin gaske Ya Falmata tana da zuciya mai kyau bata ha'intata ko kad'an, duk wani matakin nasarar da zan taka a rayuwa zata kasance mace ta farko sai ko Sahura data ba ni gudumuwa daban daban. A maza Kam Yaya Aminu shine madubi na. Sati daya da sallah na shirya fita zuwa gidanmu da gidan Gwaggwo domin tunda na auri Alhaji Muntari bai fi sau uku kacal na shiga cikin garin ba. Gwaggo ta ji dadin ganina da yaran cikin koshin lafiya. Bakinta ya gaza rufuwa ta dinga murna. Ni ma kuma ban je hannu rabbana ba. Atamfa mai kyau da tsada na saya na dinka mata irin na manya, na hada mata da takalmi da mayafi, sannan na dora mata dubu biyar a kai. Ta dinga godiya har da hawayenta. Hakan ya k'ara karyar mini da guiwa ni ma hawayen suka ciko idona. Gidanmu kuwa da na je nan naga tsantsar kulawa ban yi mamaki ba saboda na riga na san a yanzu babu abinda ya fi saurin kankaro da mutunci irin kud'i. To Allah Ya hore mini shi a yanzu shiyasa kowa ke ganin girma na. Babanmu ma sam baya ganin aibuna duk sanda za mu had'u ya dinga fad'in auran naki ai Yayi albarka Amina. Ai na gaya miki mutumin kirki ne gashi bai yi miki keta ba ya rike miki yara sannan ya barki kina sana'a. Lallai Ubangiji Allah Ya yi mini sakayya. *** Na cigaba da rayuwa a gidan Alhaji Muntari da dadi babu dadi ana ta turzawa. Na dai ki yadda na samu ciki domin dabara nake yi a duk lokacin da ya yi auratayya da ni. Muna gamawa zan yi sauri na kada gishiri da ruwan dumi nasha. Kafin gari ya waye duk abinda ya zuba mini ya tsinke ya fito. Shi dai adduarsa Allah Ya tsananta rabo a tsakaninmu. Ni kuma ina jin na gama haihuwa da kowane namaji wanda Allah Ya ba ni sun isa. Yara suka koma makaranta. Ayyuka suka yi mini yawa. Sai na fara shawarwari mai zai hana na nemi shago a bakin titi na sanya Hamusu ya binciko mini kwararrun teloli maza na zuba kekuna kawai mu fara gudanar da aikin tare don gaskiya abin ya yi yawa sosai gashi koyaushe suna nake karayi a fad'in najeriya da kewayenta. Ban yi zaton maigidan zai amince mini da sauri ba, Ina gaya masa ya ce." Ai babu komai ke ma tunaninki ya dawo kan auranki, na yarje miki amma ki kula sosai da yaran da za ki zuba, a samu masu Amana wad'anda suka gwanance da aikin." Na ce." In sha Allahu za a samu." Godiya na yi masa sosai domin da ba na samun goyon bayansa da ban kai matakin da nake a yanzu ba. Amma har yanzu zuciyata ta kasa aminta da haihuwa dashi. Ina ta shirye-shiryen fadada harkokina, don har mun gama magana da Hamusu ya ce wannan duk ba zai zama matsala ba, zai tsaya mini akan komai. Wani mummunan lamari ya rikito mini wanda lokaci guda hargitsin ya gigita mini rayuwa. Na shiga halin d'imuwa da tashin hankali mai tsananin gaske......✍️ *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* [11/28, 9:51 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A.* TEEMAH DATA SERVICES MTN 1GB @550 2GB @950 3GB @1450 4GB @1550 5GB @1700 CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306 8037026306 fatima musa ibrahim opay *TALLAH!* 🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨ 🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t *@Arewabooks* *Bintuumarabbale.* *Free pege* *19* Tunda aka shiga hidimar sallar nan wata yarinya 'yar nan, ma'kotanmu ke shigowa gidan namu, a can wurin anti Maimuna take zama tunda nan din ne yara suka fi yawaita, tun kafin na ga yarinyar na ji sunanta a bakin Yusi Ihisan. 'Yar madamanciya ce dan bata fi shekara takwas ba, yawan ambaton sunanta da Yusi yake yi yasa nace idan ta shigo ya kawo mini ita na ganta, dan da alama jininsu ya hadu, yadda bashi da wahalar sabo ba haka itama take. Yarinya mai fara'a da ita. Na bata chocolate irin wad'anda nake ajiyewa suka fita tare da Yusi din. Can wurin anti Maimuna suka nufa cikin nishadi. Da yamma likis ina kwance gajiya ta kayar da ni, ina ta lissafin abubuwan da zan saya dangane da bud'e shagunan dinkin da zanyi. Anti Maimuna ta shigo a kid'ime tana kiran sunana. Na tashi zaune cikin tashin hankali don na d'auka mutuwa aka yi, ko maigidan na mu ne ya samu matsala. Ta ce." Yarinyar nan Ihsan akayi wa fyad'e." Gabana ya buga da karfin gaske na ce." Kada dai ki ce mini yar nan makota da take shigowa wasa wurin yara." Ta ce." Itafa, yanzu nan yara suka shigo suna fad'a." Na dinga nanata Innalillahi ina fad'in" Yarinya 'yar shekara bakwai, me za a samu a tare da ita, amma ya kamata ayi binkice akan wanda ya aikata wannan mummunan lamari." Anti Maimuna za ta yi magana kenan. Uwar yarinyar ta shigo tana kuka da yarinyar a hannunta tana cewa." Ai tace Yusi ne kullum yake cire mata wando." Cike da d'imuwa na ce." Yusi kuma? baiwar Allah wace irin magana ce wannan? Yusi me ya sani da har zai aikata haka." Anti Jamila da shigowarta kenan ta bude baki tana cewa." Ai ba a shedar d'an yau, yo shekararsa sha d'aya fa, ai daf yake da balaga, yaron da aka haifa yau ma gabansa yana tashi balle saurayin da yayi wannan shekaru." Na mi'ke tsaye da sauri ina fad'in." Karya kike yi munafuka yarona ba zai ta'ba aikata haka ba, a dai binkita a cikin yaranku." Uwar yarinyar tana kuka take fad'in." Wallahi ba zan yarda ba fa." Na dubeta tare da cewa." Kada Allah Ya sa ki yarda din, ki yi duk abinda za ki yi." Ta juya ta fita a fusace. Jamila ta bi bayanta tana kara zugata. Na zube a kasan wurin cikin tashin hankali. Anti Maimuna ta dafa kafad'ata tana cewa." Amina a bi komai a hankali, tabbas na sheda Yusi ba zai yi wannan sakarcin ba. Dole dai a tsananta da bincike. A cikin gidan nan fa akayi can koridon da yake bayan dakina. Na dubeta hawaye na ko'karin kwace mini na ce." Anti Maimuna lamarin nan ba na zama ba ne, ba yadda za a yi na yi lako-lako a d'orawa yaron nan abinda bai aikata ba." Ta ce." Ni ma ban ce ki yadda ba, amma dai abi a hankali." Ban ce mata komai ba har ta fita. Kamalu ya shigo yana nishi kafafun wandonsa duk a tattare. Sai gumi yake yi. Na dube shi zan yi magana ya katse ni Yana fad'in." Kokawa muka yi da su Turmuzi da Shahid Yayan Ihisan din, sun kama Yusi suna ta duka, sun d'auko almakashi wai zasu yanke masa wurin fitsari." Cikin kad'uwa da d'imuwa na ce." Ina Yusi din, don sai a lokacin ma na tuna da cewa ban ga gilmawarsa ba tunda lamarin ya fasu. Kafin yayi magana Salima ta shigo tana kuka. "Anti 'Yan-sanda ne a waje suka ri'ke Yusi gashi can a hannunsu. Suna neman Babanmu. yanzu Mamanmu ta kira shi a waya ya ce gashinan zuwa. Hijabina nasa da sauri na kama hanyar fita yaran suka rufo mini baya. Kofar gidan ta cika da mutane yara da manya. ga Yusi a hannun daya daga cikin jami'in yana kuka. Yayin da wasu ke ta tambayar abinda yake faruwa. Na iske wurin da yarona yake kai tsaye na ce." Sake shi domin ba shine ya aikata abinda ake zargi ba." Jami'in ya ce." Ai magana ta kare tunda yarinya ta ce shine yake cire mata wando idan suna wasa, kuma kowa ya tabbatar da cewa shi din abokin wasanta ne, ke kin san haka, sannan iyayen yarinyar ma sun sani." Wani zazzafan hawaye ya kwaranyo mini na ce." Wallahi ba shi ba ne, yaron ma guda nawa yake da zai aikata hakan, ku dai kara binkice, maraya ne, Allah ne gatansa, ni ce gatansa." Ya ce." Ai marayun sun fi iyashege, saboda haka ba zamu sake shi ba sai mun gama gudanar da bincike." Yusi ya rike gefan hijabina yana kuka, yana cewa." Mama wai me na yi?" Shi bai ma san akan me aka ri'ke shi ba." Jami'in ya fizgeshi hannunsa daga jikina ya kwada masa mari mai tsanani! "Tambaya kake yi me ka yi ko? za ka ci ubanka idan muka je station." Murya Kamalu na ji da k'arfi yana ce wa." Kai ma ubanka, shegu mugwaye sai Allah Ya saka masa." Sai kuka ya k'wace masa. Wurin ya cika da hayaniya! wasu na fad'in." Dama ai yaron bashi da kunya, dan iska b'arawo ne shima, wasu kuma sai jajantawa suke yi. Yayin da wani jami'i daga cikinsu ya yi kukan kura zai cafko shi. Ganin haka ya sanya ya fafara da gudu ya yi gabas! kaina na ya dinga bugawa kamar ana kwala mini guduma! Na dinga jin Hajijiya da kyar anti Maimuna ta zo ta janye ni daga wurin, rashin makama yasa na bi bayanta zuwa cikin gida tana rarrashinta tare da cewa na kwantar da hankalina inshallah gaskiya zata bayyana. Na zube kasa cikin sanyi jiki na ce." Anti Maimuna ya zan yi ne?" Ta ce." Addu'a za ki yi itace magani." Da karfin gaske na furta." Inna lillahi wa'ina ilaihi raji'un!" Tunda na dingi nanata Innalillahi na ji sauki yana saukar mini. Can kira ya shigo wayata dake uwardaki. Kafin na yi wani yun'kuri Salima ta shiga d'akin ta dauko mini da sauri ta ba ni. Hamusu ne ya kira. Na daga don ban yi mamaki ba tunda zan ce irin wannan sai ka tsince shi a wurin da baka ta'ba tsammani ba. Cikin damuwa yake tambayata labarin da ya samu gaskiya ne. Na ce." Kai wanene yake gaya maka?" Kai tsaye ya ce." Kamalu ne." Na girgiza kai, ashe yaron can ya nufa lokacin da ya yi wa 'yansanda rashin kunya. Na ce." Haka dai iyayen yarinyar suke zargi Hamusu Amma a duniyar nan me Yusi ya sani da zai yi haka." Ya ce." Wane police station suka tafi dashi?" "Ka bari kawai ba sai ka je ba, Babansu Salima Yana can, in sha Allahu abun ba zai yi tsanani ba gaskiya zata bayyana. Kada ka gayawa Gwaggwo." "Ba zan gaya mata ba in sha Allahu Amma anti Amina ki bari na je don Allah, kada duniya ta zage mu, wannan sharri ne?" Na goge hawayen dake zuba a kumatuna na ce." Hamusu muddin aka binkita lamarin ba Babu gaskiya bisa zargin da suke yi wa yarona wallahi sai na d'aukaka kara ba zan yadda ba." "Da damuwa mai yawa a tare dashi ya ce." Mu ma ba zamu yadda ba anti Amina, kawai ki gaya mini station din, zan je a yi komai a gabana." Na ce." Ka bari zan kira ka zuwa an jima, don a halin yanzu ni ma ban san station ba, amma na gaya maka maigidan Yana can zamu yi waya idan an jima." Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefana. Na kalli anti Maimuna tare da furta." Ba zan yadda ba wallahi sai na d'auki mataki akan wannan sharrin da aka yi mini." Shiru ta yi ba tace komai ba, gabad'aya duk jikinta ya yi sanyi, yanayinta sai ya nuna kamar akwai abinda ke damunta ko take 'boyewa, shine dalilin da yasa take ta cewa da ni na yi hakuri na bar maganar. Ni Kuma ba ta san yadda nake ji a cikin raina ba. Muna zaune ni da ita da yara cikin alhini maigidan ya shigo da Yusi a hannunsa. Gabad'aya muka zuba masa ido. Ni dai ganin yarona kalau, ya sanya na dinga godewa Allah, Amma yanayin mijin na mu shi ya fi d'aukar hankalina. Ya zauna kan kujera kamar mara laka. Ya dubi yaran tare da basu umarnin fita, Salima da yan'uwanta suka fice gabad'aya, Yusi din ma ya bi bayansu. Anti Maimuna ta ce." Da alama an samu maslaha sai dai yadda na ganka a sa'bule kamar akwai matsala." Ya ce." Matsala babba ma kuwa." Sai ruwan hawaye ya ciko kwarmin idonsa. Na ce." An gano wanda ya aikata kenan?" Kai tsaye Ya ce." Turmuzi ne!" Gabad'aya muka shiga gigita! hawayen da ya ciko kwarmin idonsa ya zuba a kumatunsa. Ya nisa kafin ya yakice kuttun takaicin da yake sasakarsa ya ce." Yaron nan Yusi bashi alhaki kuma dukan da jami'an nan suka yi masa sai Allah Ya saka masa, abinda ya faru shine; Wato rud'u da firgice da kuma tsoratarwa ya sanya yarinyar nan fad'in Yusi ne yake cire mata wando. Amma a zahiri Turmuzi ne, tun farkon fara shigowarta wasa gidan nan yake janta bayan korodo yana cire mata wando ya bata alawa. Mahaifin yarinyar shi ya yi mata wayo da daburu ya lallabata kan ta gaya masa wanene tana kuka tace Turmuzi ne ya ce duk wanda ta gayawa sai ya kasheta. Ya kunna mata wani film yana nuna mata irin kisan da zai yi mata da wuka. A ranar da ya cire mata wandon ya danneta." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! sai kawai ya fashe da kuka yana girgiza kansa, tabbacin abin yana susar zuciyarsa. "Yaushe Turmuzi ya lalace haka, yaushe ya balaga da zai iya haikewa yarinyar mutane. Shekara sha hudu me ya sani, a cikin gidana, ni ban kasance mazinaci ba, Allah kada ka jarrabe ni." Babban mutum Yana kuka tukuru!" Gabad'aya jikinmu ya yi sanyi. Kudirin da yi na d'aukar fansa akan haka na janye ganin irin gigitar da ya shiga. Anti Maimuna ta ce." Yanzu a wace matsayar aka tsaya?" Yasa hankice ya share fuskarsa." Maganar ta mutu, mahaifin yarinyar ya janye karar da ya yi. Yanzu sun kaita asibiti an duba wurin raunin kad'an ne, yarinyar ta yi bayani bayan gabansa da yake sa mata har hannu yana sa mata a wurin." Na sunkuyar da kaina k'asa kawai sai wasu hawaye masu rad'adi suka goce mini suka dinga fafara gudu a kumatuna. Yaushe rabon da na yi kuka irin wannan har na manta. Ba komai ne yake daga mini hankali ba yadda tarbiyar yaran k'ananu take nema ta gurbace. Wai kamar Turmuzi shekara sha hudu shine da aikata wannan lamari. Sai na ji anti Maimuna tana fad'in." Ban yi mamaki ba, dalili wayar da take hannun yaron babu abinda ba zata janyo ba. Tuntuni na gayawa Jamila cewa ta kwace wayar bata da amfani tunda ba aikin karatu yake yi da ita kallace kallace yake yi da, ya yaudareta ne kawai ya ce ta siya masa zata dinga taimaka masa bangaran karatunsa. A gabana akayi hakan, kuma ta saya masa. Na tabbata idan ka bincike wayar ba za a rasa fina finan banza ba, domin wasu lokotun idan ya shigo wurina Yana kallo baya barin kowa ya zo wurin da yake. Ya kan rage murya ko ya sanya airpix a kunnansa." Fad'a sosai ya shiga yi, domin shi duk abinda ake yi bai san yaron yana da waya ba, uwar bata gaya masa ba a lokacin da zata saya masa sai lefin ma yake ko'karin shafar anti Maimuna. Ana haka Jamila ta shigo. Ganinmu a hargitse ya sanya ta dan yi sanyi tana fad'in." Yanzu nan na ga yaron nan Yusi nace ashe an samu maslaha sun ba dashi kenan." Lokacin da take maganar hankalinta yana kan maigidan. Aikuwa tana rufe baki ya fara bata amsa, ya warwarewa mata zare da a bawa, har da barazanar saki muddin ta cigaba da yin abu ba tare da saninsa ba, domin ya tabbata wayar ta taka muhimiyar rawa wurin lalacewar yaron. Bata yarda ba don kuka ta fashe dashi tana fad'in an yi wa yaronta 'kage, wallahi ba zata yarda ba sai ta d'auki mataki. Ya kuwace sai dai ta d'auka a gidan ubanta domin idan tace zata yi wani yun'kuri na fitar da maganar sai ya sake ta. Jin haka yasa ta fita tana kuka. Ya tashi ya bi bayanta. Can muka dinga jin hayaniya a wurinta da kururuwar Turmuzi Gabad'aya muka nufi wurin. Ya samu narkeken itace yana dukansa dashi. Duk ya fasa masa hanci. Wahala ta sanya yaron fad'in shine ya aikata amma ba zai kara ba. Da kyar na kwace itacen hannunsa ita kuma anti Maimuna ta rirri'ke shi. Lokacin ne Jamilar ta dadi a wurin tana wani irin abu wanda ya tabbatar mana da cewa aljanune suka buge ta. Maigidan bai tsaya ba ya kama hanya ya fice da wayar da ya kar'ba a hannun yaron. Ni da anti Maimuna muka tsaya a kanta da tofi da addu'a har suka saketa bacci ya d'auketa. Lokacin da muka fito na kalli Anti Maimuna cikin sanyin jiki na ce." Dama anti Jamila tana da aljan u? Ta ce." Tana dasu amma ba koyaushe suke tashi ba, sun fi zuwa yayin murna ko bakinciki idan ta haihu ma haka suke tashi akai akai har sai an yi suna." Na girgiza kai ina mamaki, tabbas hakan zata iya faruwa idan aka yi duba da yanayin halayyarta. A hargitse take koyaushe kuma bata da yarda gata da mugun izza da girman kan tsiya. Sai bayan sallar isha'i tukkuna hankalina ya daidaita. Yusi ya shigo ya zauna kusa dani jikinsa duk a sa'bule. Na dube shi a tsanake na ce." Ka je massalacin ko?" Ya daga kansa alamun "E, sai ya ce." Mama ina Yayana yake? yanzu ina fitowa daga massalaci na ji wasu suna cewa 'yansanda sun kama shi saboda ya zage su." Na ce." Yana can gidan Gwaggwo k'arya suke yi yanzu nan zan kira Hamusu a waya ya kawo shi gida. Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin jikinsa. Na dau'ki wayata da sauri number Hamusu na nema. Ya daga muka gaisa Yana tambayata ya ake ciki. Na ce." Hamusu komai ya zo da sau'ki ga Yusi a gabana tun d'azu suka ba dashi saboda gaskiya ta bayyana kanta." Ajiyar zuciya ya sauke yana godewa Allah kafin ya cigaba da cewa." Yanzu dai an kama wanda ya aikata ko?" Na ce." E, ana kan binkice dai." Ba na so na fad'a masa yaron gidan nan ne, yin hakan kamar tozarta maigidan ne, kuma na ji dadi sosai da tsayuwar da ya yi akan sha'anin har gaskiya ta bayyana. Na ce." Don Allah tunda kana da abin hawa ka kawo mini Kamalu akan babur d'inka kada ka bari ya taho da kansa, dama akwai maganar da nake so mu tattauna dangane da bud'e shagunan da zan yi." Ya ce." A a, Kamalu ai baya nan, tun lokacin da ya zo ya gaya mini abinda yake faruwa ban sake ganinsa ba, bai dawo gidan ba ne?" Cikin faduwar gaba na ce." Bai dawo ba wallahi, amma don Allah yi maza ka duba gidanmu ko yana can." Da sauri ya kashe wayar. Yusi ya dube ni." Mama ya akayi, ina yayan nawa?" Cike da fargaba na ce." Yana can gidanmu, yanzu Kawunku zai je ya d'auko shi." Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu. Ina nan zaune ina sakawa da kwancewa. Hamusu ya kira ni yana tabbatar mini da cewa Kamalu baya can gidanmu. Na ce." Ka ga Saminu a gidan kuma?" Ya ce." Kwarai kuwa shine ma ya tabbatar mini da cewa baya nan, don koda sallah bai je musu ziyara ba. Jikina ya shika, sai fargaba ta yi mini sallama, da ban kawo komai ba a zuciyata, amma yanzu babu irin tunanin da ba na yi. Na ce." Hamusu bari na yi magana da maigidana yanzu zan kira ka zuwa an jima. Na kashe wayar da sauri na tashi na fita zuwa d'akin maigidan tunda ba girkina ba ne, Yusi ya biyo bayana da sauri yana kuka....✍️ *Gudun aure 1k on talgram via 0542382124....Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari katin Airtel a kankare a tura mini shaida ta wannan lambar* *07084653262* *TALLAH* 🌲🌳🌿☘️ *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* [11/29, 12:50 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *M.W.A.* *@arewabooks* *Bintuumarabbale* *Last free peges* *20* Abinci yake ci a lokacin dana shiga d'akin yana tare da anti Maimuna da alama maganar dai suke kara tattaunawa domin cikin alhini na same su. Shigowarmu d'akin ni da Yusi ya sanya suka bi mu da kallo bakidaya Na ce." Yanzu nan Hamusu ya ke gaya mini Kamalu baya can wurinsu. Tun fa da lamarin nan ya faru ya bar unguwar ni wallahi na d'auka Yana can gidan kakarsu ashe Yana gayawa kanin uban ya fita ba a sake ganinsa ba, duk inda ya kamata a duba mini Hamusu ya duba ba a ganshi ba." Hawaye ya zubo a kumatuna na sanya hannu na goge gabad'aya jikina Yayi sanyi sai nake ganin kamar akwai abinda yake shirin faruwa da yaron. Anti Maimuna ta shiga kwantar mini da hankali. Shi Kuma maigidan ya tsame hannunsa daga abincin ya d'auki wayarsa muna zaune ya kira station domin tambayarsu tunda ya ji labarin rashin kunyar da yaron Ya yi. Gabad'aya mun yi tunanin ko sun kama shi. Suka tabbatar masa da cewa baya hannunsu. Hankalina ya sake tashi. Gidajen redio uku ya kira ya bada cigiyarsa duk ya Basu bayanai akansa. Sannan ya waiwayo gareni ya shiga yi mini nasiha da kawo mini misalai na kaddarori na rayuwa. A wannan dare na yaba masa kwarai da gaske dashi da anti Maimuna sun yi mini kara, sai kusan sha biyu da rabi tukkuna na yi musu sallama na koma wurina jikina duk Yayi tubus. Yusi kuwa ya ci kuka ya koshi sai ajiyar zuciya yake yi. Yadda na ga rana haka naga dare. Ina idar da sallar asubahi na kira Hamusu domin tambayarsa ko ya samu wani labari akan yaron. Ya ce mini babu wani labari shima tun jiyan yake zaga gidajen masu unguwani. Da station da suke area ko an kai shi can. zuciyata ta dinga raya mini munanan abubuwa Ina ta tunanin ko wane hali yake ciki a yanzu. Fatana dai ace yana hannu nagari. Kwana uku babu wani labari babu Kamalu babu dalilinsa. A lokacin na gama gigicewa. Komai na rayuwata ya tsaya cak! Na kira anti Yagana na sanar mata da halin da nake ciki. Sannan na bawa Ya Falmata ha'kuri domin halin da nake ciki ba zai barni yin komai ba. Tsangayu uku na bada sadaka domin a yi mini ro'kon Allah akan lamarin Allah Ya bayyana mini yarona ko da rai ko a mace. Sahura zuwanta biyu ta ce mini muje gidan wani malami da rigar Kamalu zai yi aiki akai idan ma yana raye zai gaya mana, idan kuma baya raye nan ma zai gaya mana. Na ce ba zan iya zuwa ba, tunda na sanya a yi mini ro'kon Allah shikkenan. Zuwa lokacin na saduda burina ko gawarsa ce na ga ni. **** A ranar da Kamalu ya cika sati da 'bata Hamusu ya kira ni a waya da rana gatse gatse. Ina d'agawa ya ce." Anti an samu labarin Kamalu sai dai lamarin ba dadin ji wallahi." Na ce." Hamusu gaya mini idan mutuwa ya yi duk inda yake zamuje a ba ni gawarsa ko zan rasa komai." Ya ce." Yana nan a raye sai dai yana hannun hukuma tare da wasu matasan Yara 'yan nan gaba damu, wata'kila ma zaki san gidan Alhaji mato." Na ce." Na san gidan Hamusu mai ya had'a Kamalu da yaran gidan nan Kuma?" Ya ce." Neman mafaka ya yi dasu, ashe bayan ya zo ya gaya mini abinda ya faru, sai ya hadu da daya daga cikinsu yake gaya masa zai kwana a gidansu. Da ya tambaye shi dalili sai ya ce 'yansanda ya zaga shi kuma Yana jin tsoron komawa gida a kamshi. Shine da yaron mai suna Kamsusi ya bashi mafaka. A kuma washe garin ranar ya gudu dashi legos. Suka shiga wani kamfani sukayi sata aka kuma cafke su har da Kamalu. Inda nake jin dad'i kamfanin da suka shiga yana daya daga cikin mallakar Alhaji Tajo, muna sa ran yaran za su samu sassauci. Na ce." To Hamusu yanzu ya kake ganin za a yi? kana ganin zasu ba mu yaron nan cikin sau'ki idan an yi duba da irin yaran da suka ja shi, hukuma ba zata aminta da korafinmu ba, dole tunda tare suka aikata barnar a hukunta su. Ya ce." Ai Kamalu shine k'arami a cikinsu. Bai balaga ba har yanzu shekara sha hud'u, za a samu rangwami. Sauran kuwa duk sun haura ashirin. kwai dai hankalina yana tashi ne idan na tuna ta'adacin da yaran suka jima suna yi. Dama an ce hukuma neman su take ruwa a jallo, tunda basu jima da cinna wuta a wani a shago ba bayan sun kwashi kudi masu yawan gaske. Jiki a mace na ce." Hamusu duk yadda Allah Ya yi daidai ne. Zan yi magana da maigidana yanzu zuwa an jima abinda muka tattauna zan sanar da kai in sha Allahu rabbi." Ya ce." To shikkenan anti ni ma ta nan din zan cigaba da bincike akan lamarin in sha Allahu za mu sau'ki." Muna gama waya da Hamsu na kira maigidan na gaya masa. Sai ya ce ai ya samu labari don har gidajen jaridu sun buga da kafafen da zumunta. Shi ma a fece book ya gani. Ya kwantar mini da hankali kafin ya dawo har ya na fad'in lamarin zai zo da sauki tunda mamallakin kamfanin mutumin kirki ne. Tun kafin Azimi rabona da sa data a wayata saboda ba ni ma da sukunin shiga media kallace kallace dalilin ayyukan da suke gabana. Ashe lamarin har ya yi girman da gidajen jaridu ke watsa labarin. Ko da yake mutumin babba ne a kasar hakan ba zai zama abin mamaki ba tunda motsi kad'an zai yi media zata d'auka balle wani abu da ya shafe shi. Yanzu kenan hotonan Kamalu suna can suna yawo a duniya kowa yana fad'in albarkacin bakinsa. Da yamma Sahura ta kira ni a waya tana jajanta mini. Itama dai a fecebook din ta gani, maganar dai guda daya ce na kwantar da hankalina yaran za su samu sassauci saboda adalcin mutumin da suka yi wa ta'adacin. Ban iya ce mata komai ba saboda na san ta riga ta yi ammana da ubangidanta, ba ma ita kadai ba kowa alherinsa yake fad'a to ina addu'ar Allah Ya sa wannan karon ya gwada mini, ni ma sai na gazgata. Duk wanda ya jibance ni a wannan ga'bar sai da ya jajanta anti Yagana tana daga can duk ta damu, ni ce ma nake kwantar mata da hankali ina kara gaya mata ai mutumin da suka yi wa b'arnar Yana da kirki za su samu sassauci. Jin yadda jama'a suke fad'a ni ma sai na ara na yafa dukda a can baya bai kwatanta mana adalcin ba, amma ai ba ni da bakin bakin magana a wannan yanayin. Kwana daya zuwa biyu maigidan bai ce mini komai ba tun bayan tattauna yadda za a bullowa lamarin da muka yi dashi ranar da Hamsu ya kira ni a waya. Da ya dawo yake ce mini za su shirya zuwa Legos din da shi da wasu abokanansa wad'anda suka kasance 'yan unguwar da aka haifi Alhaji Tajo din wato 'Danbatta sun san shi sosai kuma sa'i da lokaci idan ya shiga unguwar tunda har yanzu anan mahaifiyarsa take zaune suna gaisawa har ya yi musu alheri, to Yana ganin za su shige masa gaba, domin komai ya zo da sauki. To tun ranar da muka yi wannan maganar bai sake ce mini komai ba, dan har Sahura ta kira ni a waya tana fad'in ta samu lambar wayar PA d'insa idan na amince sai ta kira shi domin ya sanar da ogan nasu muna san ganinsa, na ce ta bari tukkuna na ji daga maigidana. Da yake ba girkina ba ne a ranar bayan ya dawo sai da na tabbatar ya ci abinci tukkuna na same shi domin na ji Ina aka kwana. Sai ya ce na kara ha'kuri ashe duk abin nan da yake faruwa shi uban gayyar ma baya garin amma dai yana da labarin komai, ya ce a jiraye shi ya dawo tukkuna. Ni kad'ai na san irin fargabar da nake kwana na tashi da ita. Babu irin tunanin da baya zuwa k'wa'kwalwata akan yaron da yanayin gari, da wurin da aka ajiye su tare da garadan samari lalatattu wad'anda suka girme masa. Na gane kuka ba shine mafita a gare ni ba, domin ta wani gefan ma zubaar hawayen nawa zai iya janyowa yaron wata masifa. Wannan dalilin ya sanya na tsananta kai kukana ga Ubangiji akan ya gaggauta kawo sau'ki a cikin al'amarin. Kowa ya na ta sabgar da take gabansa ni kuwa komai na rayuwata ya tsaya cak! Abincin kirki ba na iya ci, ga yawan koke koke da Yusi yake yi mini akan rashin ganin d'an'uwansa. Ni dashi muka zabge lokaci guda tunda shi ma ba abincin yake iya ci ba. Sati daya sati biyu babu wani labari Hamusu ya kira ni a waya ya fi sau biyar ina dakatar dashi bisa bin umarnin maigidan wanda shi kuma tun ranar da muka yi magana dashi bai sake tayar da maganar ba. Da dai na gaji na sake tuntubarsa sai ya ce mini ya dawo amma baya hayyacinsa dalilin rashin lafiyar mahaifiyarsa. Sai na tuna wani zuwa da Sahura ta yi mini take gaya mini sun je dubata. A ganina hakan ai ba zai hana shi bin ba'asin abubuwan da suka faru bayan baya gari ba, idan ma ba zai saurari cas din ba sai ya wakilita wasu. Na kira Sahura a waya domin ta tabbatar mini da dawowar tasa ta kuma ba ni tabbacin cewa ai kwanansa uku ma da dawowa. Raina ya kai ma'kura wurin 'baci. Na fahimci ba kowa ne zai gane halin k'unci da fargabar da nake ciki ba, shiyasa duk a ka yi shakulatun 'bangaro da lamarin. Babu abinda ya fad'o mini a wannan ga'bar da zuciyata ta bushe sai yin amfani da social media domin tura sa'kona ga wanda al'amarin ya shafa. Idan hukunci zai sa ayi musu gwara ya fito ya yi magana, idan kuma zai yi musu afuwa sai ya fito ya sanar da mutane. Ban yi shawara da kowa ba na sayi data wurin TEEMA DATA SERVICES 08112392177///08037026306 domin dàtar ta akwai kyau da inganci tun a gida nake saye haka zalika ma mafi akasari na ga Hamusu da datar ta yake amfani a cewarsa nan da nan yake gudanar da komai babu wani jinkiri ko daukewar network. Fecebook na shiga. Duk da ba ni da wasu abokai da yawa amma na yi imanin rubutun da zan yi akan mutumin zai ja hankali mutuka har sa'kona ya iske shi. "Assalamualaikum warahamatullahi ta'ala wabrakatuhu. Jama'a sunana Amina Malam Salisu mai hula. Ni haifaffiyar jahar kano ce kuma ni uwar marayu ce. Jama'a ina so don Allah ku yad'a wannan sa'kon nawa zuwa wurin mutumin da duniya da mutanan cikinta suke yi masa kallon mutumin kirki. Kai tsaye sa'kona zuwa ga Alhaji Tajo Ibrahimu 'Dambatta ne na san kaf kasar nan babu mahalukin da zai ce bai san sunansa ba ko baku ta'ba ganinsa a zahiri ba ina da tabbacin kun ta'ba katari da hotonsa. Ina yawan ji jama'a na fad'in kyawawan halaye da nagartarsa sai dai ni Amina Salisu mai hula har yanzu na kasa aminta da hasheshenku. Ban fito duniya domin na zage shi ko na 'bata shi a idon duniya ba sai dai na fito ne domin na fadi ra'ayina. Mutumin nan bai san muhimmancin alkawari ba, wannan shine abu na biyu wanda ya yi mana wanda na kara tsanarsa a duniya. Ni ina daya daga cikin iyayen yaran da suka samu nasarar shiga d'aya daga cikin kamfaninsa dake Legos suka yi 'barna. Yarona Kamalu shine k'arami a cikinsu. An yi magana dashi kan cewa idan ya dawo daga inda ya tafi zai magantu akan sha'anin yaran amma yau tsayin sati uku kenan bai ce komai ba. Duniya ta yi masa sheda mutumin kirki ne har ana yi wa yaran murna cewa za su samu sassauci. Amma cikar kamala da mutuntaka shine cika alkawari. Ina so ya fito ya gayawa duniya abinda yake zuciyarsa a game da yaranmu. Ya yafe musu ne ko kuma zai bawa hukuma damar hukuntasu. A madadina da sauran iyayen yaran muna jira daga gare shi domin mu samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Jama'a da wannan nake yi muku sallama, kuma ina ro'kon alfarmar ku yi shearing din wannan sa'kon nawa har ya isa gare shi. Na gode sosai." Amina Salisu (Mai wankin hula.) ✍️ *Alhamdulillahi, anan na kawo k'arshen book 1 kamar yadda na fad'a muku kyauta ne ga kowa da kowa amma book 2-3-4 na kudi ne akan 1k a manhajar talgram ga wad'anda kuma suke karatu a arewa books akwai more peges a can domin na yi nisa. Ina fatan samun hadin kai da goyon baya daga wurinki. Littafin gudun aure yana 'kunshe da dambarwa daban-daban. Kada ku yi jinkirin wurin sayan littafin domin akwai darrusa masu yawa uwa uba akwai kuma irin soyayyar da kuke so mai sanyaya zukata😃 kun san dai yadda karshen book 1 ya kasance akwai rikice a kwance. Hanyar da za a biya kudin shine 0542382124...Binta Umar gtbank ko 7084653262... Binta Umar Opey bank. Mutanan nijar dala dari katin airtel sai ku kankare hoton a tura mini da sheda.* *07084653262* *GARKUWAR MATA* *BINTA UMAR ABBALE* *MAI MAGANIN GARGAJIYA* *TALLAH!* 🌲🌳🌿☘️ *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*