Search
You have no alerts.

    LU’U LU’U

    💎 L U’U L U’U
    (The diamond)💎

    H U G U M A

    FREE PAGE 1



    Bismillahir rahmanir raheem

    Shimfida

    _Lu'ulu lu'ulunne dai ya yardar Allah,shimfidaddiya kuma miqaqqiyar tafiya dake dauke da wani sabon zubin labari_

    manyan qasashe guda biyu da taurarinmu zasu kasance mallakin qasashenne,wasu abubuwa da guraren zasu iya sabawa da yadda ainihin zubi tsari da kuma yanayin da qasar ke rayuwa akai

    fatan shine cimma gaci…….fatan shine cimma anihin saqon da alqalamin HUGUMA ya sauka a kai

    wani sabon salon labarine dake dauke da sarqaqiya…….boyayyun qulle qulle da ZARGE wanda bahaushe kewa kirari da mugun qulli

    sarauta QASAITA DA IZZA ne zallarta take magana cikin wani irin salo me ban qayatarwa

    karki bari…….karki sake……kada kuma ki yarda a baki labarin tafiyar nan ya kasance ba dake aka yita ba

    Allah ya bamu sa’a,yadda muka fara yasa mu kammala a tare cikin qoshin lafiya arziqi da kuma wadata

    AGADEZ
    masarautar agadez
    Maison de i’emir

           Masarutar agadez,babbar masarauta ce data kafu tsahon shekaru masu yawa. Ta samo asalin kafuwarta tun daga wani qarni can baya daya wuce,wanda aka samu rarrabuwar kawuna gurin masu buqatar mulkar yankin daga kowanne gida iyali da kuma dangi. Rashin samun hadin kan fidda mutum daya yayi sanadin yanke hukuncin tafiya zuwa ga daular musulunci ta istanbul,mahukuntan yankin agadez kuma suka nemi agaji wajen basu wanda zai zama shike mulki da yankin,wannan shine ya haifar da samuwar sarki na farko dan asalin daular turkiyya istanbul *MUHAMMAD AGGA_ABBA BIN MUHAMMAD ALMUBARAK*.
    
           Sosai auratayya hulda na kasuwanci da cinikayya sukaci gaba da wanzuwa tsakanin qasashen nan guda biyu,wanda ta haifar da haihuwar mutanen da suka kasance *RUWA BIYU*. Wato halfcast inji bature.
    
           *BUZAYE* na daya daga cikin qabilun da suke da yawa sosai cikin qasar agadez,wasu irin launin mutane dake da wani kyau na musamman daya zame musu tambari na daban,ya kuma sanya suka zama na musamman. A cikinsun SULTANE MUHAMMAD HAMUD ya fito.
    
            Mahaifinsa buzu ne na asali,wanda jininsu ya gauraya da na turkawa,don kuwa mahaifiyar SULTANE MUHAMMAD HAMUD 'yar asalin garin istanbul ce......wannan ya sanya kyanshi ya zama wani irin nau'i na daban daya gadoshi daga bangare biyu wato UWA da UBA.
    
             SULTANE MUHAMMAD HAMUD......qasaitaccen sarkin da yake mulkin qasar agadez a yanzu. Wata irin hamshaqiyar sarauta dake cike da izza qarfin mulki dana iko gaba daya. Sarkin da yasha banban da dukka sarakunan da sukayi mulkin kafin shi......sarkin daya kawo gagarumin sauyi ya canza qasar agadez gaba daya daga fuska yanayi da tsarin da take a baya,zuwa wata sabuwar duniya datasha banban da kowanne yake na qasar NIGER gaba daya.
    
            AGADEZ din a yanzu ta zama wani yanki ko kuma gunduma ta musamman.......yankin daya fadada ta fuskar noma kasuwanci ilimi da sauransu. Wannan sauyin bai tsaya a iya yankin AGADEZ kawai ba......yayi mamaya har ya zuwa cikin ainihin gidan sarautar yankin. Komai ya canza daga inda yake zuwa wani bigire dake tafiya da zamani.....wani yanayi dake dauke da kowanne ci gaba na zamani,ya zamanantar da komai din da wani irin salo da dole kowa ya sallama. Cikin qauna ga sultane muhammad hamud da girmama duk wani motsi da aiki nasa suka bashi sunan ZAMANI GOMA.
    
          Qasaitaccen sarki,ma'abocin izzar dake barazana tare da kad'a zukatan abokan burminsa.......qasaitaccen sarkin da kwarjinsa ya keta ta cikin kowanne hijabin BARAZANA......qasaitar data dasa shakka tsoro da kuma kokwanto akan zuciyar duk wani dake da zaton yakai ya tsaya gurbi guda dashi......kwarjinin daya zama wanzajjen abu dake ea matuqar tasiri,ya kuma sanya zukata da yawa sallamawa.......
    
             Yana da wani irinn qualities yana da wata irin ZARRA yana da wata irin jajircewa.......saidai duk da hakan akwai wani RAUNINSA guda daya.......RAUNI ne da ba zai taba canzuwa ba.......bazai kuma taba shafewa cikin rubutacciyar qaddararsa ba. RUHINSA ce ita......wani bangare ce ta RAYUWARSA.......GUDAR TSOKA daga zuciya da kuma jikinsa.......ita din wani abune me muhimmanci da ta zama shaida ga kowa cewar.......ba wani abu me tsananin muhimmanci da idanu ke iya ganin ya MALLAKA kamar ita. *_khadeeja(AKHNAN)_*

    Duk kuwa da tarin baiwar dake lullube da rayuwarsa……amma yana jin kamar daban TAKE cikin komai nasa. Tarin dukiya madararta,izzarsa……mulki da DAUKAKAR suna data mulkinsa wadda ta gangara cikin kowanne lungu da saqo na qasarsa…..qasashen africa GABA DAYA dama wasu daga cikin qasashen qetare

    EMIRE PALACE
    Palais de i’emir

            Wani bafaransen gine ne ko kuma mu kirata DUNIYA ta musamman dake zaman kanta tsakiyar bagargajiyen ginin masarautar AGADEZ din. Gini ne da dake tsakiyar manyan katangun masarautar agadez dake qara nuna qarfin iko dana izzar da masarautar ke dashi. Zaka tadda gine gine iri daban daban dake nuna gargajiya da kuma ainihin al'adar gidan sarautar dake bisa tsari da kuma zamani......zamanin da bai sanya alamu ko burbushin gargajiyar bacewa ba saidai ya gyarata daga ainihin asalin GARGAJIYAR zuwa GARGAJIYARZAMANI.
    
               Wani taswira ce da aka tsamota kacokam daga qasar France,qasar da a baya ta zama uwa kuma uwar goyo ga qasar ta nijer,aka kawoshi aka ajiye cikin gidan sarautar sultane muhammd hamud. Katafaren VILLA ce wadda ita ke zama mafaka kuma mazauni ga iyalan SULTANE MUHAMMAD HAMUD. Duk kuwa da cewa matanshi na auren biyu ne........amma kuma villa din na dauke da sassa guda shida ne.
    
              Sassa uku dake cikin villa din tafi kowanne sassa na ginin girma kyau fadi tsaho da kuma tsaruwa,biyu na matansa ne daya mallakin me alfarma sultane muhammad hamud,sauran an ajiyesu ne saboda baqi da kuma hadimai. Duk sashe daya yakai girman wani mansion House na mutum guda,wannan ya sanya akwai tazara sosai tsakanin wane da wane,kuma kowa yake rayuwarsa ba tare da damuwa ko takura daga dan uwansa ba.
    
               Bata baki ne kawai a gareka a wannan rana ta juma'a tsaiwa tambayar wani

    “Akwai wani gagarumin taro ne da zai gudana?” Domin kuwa tun daga gate din farko da zai fara kawowa farfajiyar farko da zata kaika farfajiya ta biyu wadda zata sadaka da villa din mai alfarma sultane idanunka zasu iya ganin komai. Yawaitar zirga zirgar hadimai maza da mata………canje canje da sauye sauyen da akewa wash flowers da sauran kayan alatun da suka zama cikar ado da qawar villa din,duk kuwa da cewa wannan din ba baqon abu bane,kusan koda yaushe wannan villa din cikin tsari take da kuma gyara bisa kulawar manyan jakadun guda biyu da villa din ke dasu AYAANA da kuma ME WADA.

           A qarqashin ayaana da me wada kuwa tarin bayi ne.......dogarai da kuma ma'aikatan da kowanne yake jagoranci da rarrabuwa ayyuka iri daban daban,wadanda sune suke tafi da kowacce rana da wuni na villa din. Iyakar nan dinne kawai tasu iyakar da hurumin,kaman yadda kowanne dogari da bawa yake da nashi iyakar da hurumin cikin gidan.
    
               Duk da yawan canzawar motsi da kai kawo dake wanzuwa a villa din harma da gidan gaba daya,hakan bazai hanaka ganin daga bangaren da wannan motsin yafi yawa ba.
    
              Sashe ne da yake mallakin hajiya *ZAITUN* uwar gidan me alfarma sultane hummad hummad wanda ke amsa sunan *UWA*  ga *AKHNAN*. Duk kuwa cewa ba itace matar farko ga sultane muhammd hummad ba.......amma a yanzun sunan uwar gidan ya zama shine TAMBARINTA........uwa ce ga AKHNAN amma akwai wani dalili daya hanata amsa sunan MAHAIFIYA. Dukka wadannan dalilai hakan bai samu qarfin iko dana dantsen togacewa ko rabata da wadannan *LAQABI* guda biyu ba da take matuqar ji dasu.....fiye da yadda uwa ke ji da jaririnta sabuwar haihuwa UWARGIDAN SULTANE kuma UWAR AKHNAN.
    
            Wani qasaitaccen gine ne dake qunshe da dukkan wani kaya na qasaita da kuma alfarma,wanda iya su kadai sun isa gaya maka lallai QASAITA da kuma MULKI ne suke magana.
    
              Zaka wuce faluka bayan faluka,gurabe masu yawa kafin ka samu isa bangare ZUCIYAR MASARAUTAR kuma SHALELEN SULTANE take.
    
           Wani irin ni'imtaccen parlor ne dake da wani irin girma da kuma tsari......irin tsarin da yake zamewa abun kallo a idanun mutane masu yawa,saboda ba tsari ne da aka saba ganinsa ko ina ba......ba kuma tsari bane da aka saba ganinsa koda yaushe ba.
    
     Komai na parlor din ya kasance ruby red color and gold,tun daga kan lafiyayyun curtain na kamfanin NICETOWN dan qasar France,har zuwa Italian royal chairs da parlor din ya laqume har set biyu. Lausasan carpet dake nuna zallar alfarma da qasaitar falon dama dukkan abinda ya mallaka dake cikinsa......wasu irin qananun side tables mulmulallu dake daukan idanu wanda suke mahadi da Italian royal chairs din dake parlor din. Gypsum ceiling ne lullube saman parlor din,wanda aka qawata da wasu kyawawan fitilu da kuma crystal Chandelier daga tsakiyarsa. Iya su kadai abun kallo ne da zai daukeka shudewar wasu daqiqu kana mamakin yadda aka baje fasahar samar da ceiling na musamman irin wannan.
    
              Akwai qofofi kusan guda uku dake tattare da parlor din. Saidai qofa mafi daukan hankali itace qofar qarshe dake qunshe da wani kyakkyawan corridor maras zurfi da fadi sosai,saidai an qawatashi da wasu irin artwork frame da aka maqale a kowanne bango na corridor din a qalla frames shida. Kowanne frame yana dauke da zane mai daukan hankali na wasu irin furanni da qananun tsuntsaye a kansu,iyakar abinda yake jikin frame din kenan.
    
           Qofofi uku ne,abinda yake baka daman gane cewa bedrooms uku corridor din ya mallaka,kuma kowacce a qofa a rufw take ruf,sai guda daya da bata kai ga rufewa gaba daya ba.
    
       *PRINCESES* kamar yadda yake a rubuce a saman qofar dakin.....qofar dakin da idan ka samu nasarar budeta zai baka daman cin karo da wata ALJANNAR DUNIYA ta musamman.
    
             Komai na dakin na musamman ne da wani irin tsari da kalolin da kana ganinsu kasan cewa zabi ne na mamallakiyar dakin. Mutum shida ne cikin bedroom din masu mabanbantan yanayi kamanni dama matsayi na rayuwa.
    
              Zagayayyen gadon me suffar oval shape wanda yake lullube da rumfar net ta alfarma idanunka zai fara sauka. Kyakkyawar matashiya ce zaune a samansa......matashiyar da duka shekarunta ba zasu haura ashirin da hudu ba. Fara ce tas......irin hasken nan me fita sosai,ma'abociyar yalwar suma data bayyana harta qasan dankwalin lallausan material din dake jikinta. Tana kyan da a kallo daya zaka yarda da hakan,bata da jiki sam,siririya ce da rashin qibarta ya bayyana ta cikin lallausar doguwar rigar jikinta. Daga gefan gadon take a zaune amma qafafunta suna zube a qasa,gefan damanta kadan wani kyakkyawan table ne dake dauke da madaidaicin tray da aka shirya apple a ciki da grapes da basu da yawa sosai masu bala'in kyau........wanda sukan kasance zababbu cikin kayan marmarin da dukka za'a tsinko kuma a shigo dasu zuwa sassan AKHNAN.
    
           Qafarta daya saman daya,yayin da idanunta suke kan wata matashiyar dake tsaye dan nesa kadan da ita da alama magana take da ita me muhimmanci. Matashiyar da suka sha banban da wadda ke zaunen da wani nisan tazara me tarin yawa......wata irin tazara da babu shakka za'a jima ana ragaita cin neman halittar da zatayi tsara da ita. Bawai magana ake ta MATSANANCIN KYAU ZALLA BA.....aah...wani irin kwarjantaccen yanayi ne madararsa ke lullube saman zagayayyar fuskar da Allah ya horewa wani irin kwantaccen kyau daya cakuda daga mabanbantan qabilu guda biyu. BUZUWA CE ta wani fannin kuma jinin qabilar TURKAWA CE tsatson Istanbul.
    
             Wasu irin kyawawan idanu Allah yayi mata baiwa dasu,masu dauke da wani kebantaccen yanayi na kwarjini da wani irin kyau da ba zaka iya dauka idanun dan adam ya kebanta da irin wannan kyan ba. Idanun dake da girma da wani irin shape da ya sanyasu sukan lumshe karan kansu,lumshewar da yake dan rage girman da yake dashi.
    
             Matasan 'yammata ne guda daura da inda take tsayen,wanda dukkaninsu sanye suke cikin shigar wani olive green color din yadi,saman kansu kuma hijab ne Vshape apple green daya dace sosai da olive green din jikinsu.
    
             A shekarunsu dukkaninsu sa'annin juna ne......kowacce cikin tsafta nutsuwa da kuma tsari take,hakanan akwai alamun nutsuwa sosai saman fuskar kowaccensu. Kusan dukka su hudun kowacce aikin gabanta takeyi. 
    
               Guda biyu ne bayanta,ta farkon qoqarin zuge zip din gown din dake jikin AKHNAN takeyi cikin matuqar girmamawa da takatsantsan. Gown din da aka dinka da wani lallausan yadi da a kallo daya kawai zaka fahimci sutura ce ta alfarma......sutura ce kuma ta diyoyin isassu da kuma wadanda suka isa. Gown din ta zauna a jikinta tamkar don ita kadai aka halicci yadin,ta kuma sauka har saman dogayen yatsun qafafunta ta lullubesu. Zamanta a jikinta sam bai sanya halittarta fita ba,saboda abune sananne ga duk wanda yake da jibi da sanya suturarta,tun daga me dinkawa zuwa me sauyasu da kuma tsara closet dinta batason matsatsen tufafi sam. Duk da cewa abun a baya yana daya daga cikin tsarukan MAMMINA da wasu ke kira da GIWA a kebantattun lokuta.......amma ta wannan fuskar sai suka sha banban da AKHNAN........Banbanci qwaya guda tallin tal da har yanzu ba wani abu na biyu daya zama sabanin ra'ayi a tsakaninsu.
    
               Matashiya ta biyun kuwa tana kusa da waccanne,hannunta dauke da wani babban tray me ruwan gold dake lullube da wani tattausan yanki fari qal,wanda a cikinsa babu komai face kalolin ribbons da hair clip,ta tallafewa matashiya ta uku dake bangaren kafadar daman AKHNAN din tana tufke doguwar sumarta tare da qoqarin lanqwasata gami da qawatata da ado na ribbons masu zallar kyau da tsari.
    
           Matashiya ta hudu na daga gabanta a tsaye tana zuba warwaren dake qyalli a santala santalan hannuwan akhnan,wanda ta miqa mata su,idanunta dake dauke qwayar ido kalar baby blue zube saman fuskar matashiyar dake zaune gefan gadon. 
    
             Har yanzu tana riqe da apple din data gutsira sau daya bata kuma sake ba,still tana duban akhnan,kafin a nutse ta maida apple din tana sauke qafafunta data dora daya saman daya ga gyara zamanta tana cewa 

    “Il lui a vraiment fait du mal(yayi matuqar cutar da ita),har yanzun ta kasa mantawa……..ta kasa manta yadda relation dinsu ya taba gudana a baya”. Matashiyar ta qarasa fada muryarta tana yin qasa,alamun dake nuna kowacce magana ma sukeyi tana da girma a zuciya dama harshenta.

           Janye manyan idanunta akhnan tayi tana rufe blue eyes dinta,sannan ta dauke dubanta kacokam daga fuskar matashiyar tana maidawa ga bagaren hannun damanta,ta sake zube lumsassun manyan idanunta saman window size mirror din da da hadimarta data gama gyara mata gashinta ta dauko ta ajiyeshi dirshan a gabanta.
    
              A nutse ta sauke kallonta tana duban kanta,tun daga qafafunta da gown din ta lullube har zuwa sumarta me yawa tsaho baqi da kuma sulbi. Dakin ya dauki shuru,ta tsaida idanunta saman fuskarta.
    
           Kamar kowanne lokaci irin wannan......kamar kowanne zamanin me kama da wannan da yakanzo ya kuma wuce cikin rayuwarta. Ko daya......ko kusa kuma ko alama bata jin kowanne feelings game da lokacin......bata jin wani abune na musamman,hakanan bata jin cewa wani kebantaccen abune daya kamata ta jishi har cikin zuciyarta.

    “Birra” Ta kira sunanta da tattausan sautin nan nata da koda cikin fushi……koda cikin fada yake fita,wani irin sauti da baya buqatar hayaniya ko wahala.


    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!