LITTAFI NA UKU
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
SHAFIN FARKO 1
TSOKACI
*MU KULA A YAYIN DA MUKE KARATUN LITTAFI* *MUFI MAYAR DA HANKULANMU AKAN DARUSSAN DA LABARIN YA ƘUNSA, HAWA DA SAUKAN LABARIN DA YADDA MATSALTSALUN AKA WARWARESU*
*ABINDA AKA TSINTA MARAR KYAU BA’A KOYI DASHI MARUBUCI BAI RUBUTA DOMIN KAYI KOYI DASHI BA, YA HASKAMA WATA RAYUWACE MUMMUNA DOMIN KASAN ANA YINTA KUMA YAJA HANKALINKA DAN GUDUN AIKATA IRIN WANNAN LAIFIN*
*YA HASKAMA NE KA GANI WALA ALLAH KANA CIKIN IRIN RAYUWAR SAI KAGA HANYOYIN DA ZAKA WARWARE MATSALOLINKA CIKIN SAUƘI*
*MARUBUCI GYARAN TARBIYYA YAKE YI BA GURƁATA TARBIYYA BA*
*MARUBUCI MADUBINE DAKE HASKA RAYUWAR AL’UMMA ALƘALAMI YAFI TAKOBI*
Har zuwa wayewar gari Sabuwa bata san a wanne halin take ciki ba. Jakarta tana cikin motar Dr Kamilu, shi kuma tunda ya jefa jakar a mota bai sake tunowa da wata jaka ba a haka har wayar ta mace mus.
Dr Kamilu bashi ya shigo asibiti ba sai da yamma a lokacin Dr Mu’awiya na shirin tafiya yaje ya huta. Kai tsaye ofishin Dr Mu’awiya ya shiga ya taddashi a zaune dai amman ga jakarshi akan teburin gabanshi.
“Ah Dr ka shigo? Kaga yanzu nake ƙoƙarin nima in kashe na’urarnan in tafi in huta.”
Masauki Dr Kamilu yayi ma kanshi a kujera yace.
“Sai yanzu na samu shigowa. Nazo ne inji me yake damun mara lafiyan dana baka sannan yaya jikin nata?”
Sai da Dr Mu’awiya ya gyara zama kana ya soma da cewa.
“Tana cikin wani irin mawuyacin hali gaskiya. Ciwon damuwa ke ɗawainiya da’ita. Ga jininta ya hau sosai, sannan tasha maganin maye mai ƙarfin gaske. Kasan hawan jini da kayan maye, da damuwa abokan gabane? Halamu sun nuna tana cike da wata damuwa a ranta. Kafin nurse suyi mata allura sai sambatu take yi tana dai kiran wani suna da basu fahimta ba. Zai iya yiyuwa zafin ciwo ne. Zai iya yiyuwa kuma a bige take, zai iya yiyuwa ɗimuwace.
An dai mata allurar bacci tana kwance, sai kaci gaba da kulawa da’ita tunda kazo”
Kai kawai yaci gaba da girgizawa yana mamakin dalilin da yasa Sabuwa zata sa rayuwarta cikin haɗari irin haka. Allah yasa a hotel data faɗo jikinshi ya riƙeta da ƙila inta faɗi ƙasa ta samu mutuwar ɓarin jiki. Tabbas da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba, Allah ya turoshi domin ya zame mata garkuwa.
“Allah ya kyauta Dr Mu’awiya. Mata yanzu sun lalace da shaye_shaye kome yake jefa su a irin rayuwar sai Allah”
“Hmm Dr kenan. Kasanfa mafi akasarin masu shaye_shayen muyagun ƙwayoyi suna yine domin samun mafitar wata damuwa data tuƙe musu. Basusan jefa kansu suke ga halakaba. Yanzu baiwar Allahn daka kawo kyakkyawar mace kamarta bai kamata ace ta jefa rayuwarta cikin irin wannan halin ba”
Dr Kamilu ya miƙe tare da jan numfashi yace.
“Tana wanne room ne?”
“Tana room 4 gado na biyu anan take.
Ɗakin duk masu irin lalurarta ne shi yasa na haɗasu tare basa son hayaniya bacci wadatacce suke buƙata”
Kai kaqai ya gyaɗa tare da ficewa zuwa room 4 .
Ɗakin shiru babu kowa face majinyata huɗu da ko wacce take kan gadonta a kwance suna aikin bacci.
Ko wacce durowa ta gefen gado shaƙe da kayayyakin marasa lafiya dangin lemo ayaba, da filas na abinci dana shayi, harda ma gwangwamayen madarori.
Gadon sabuwane babu ko tsinke a kan durowar. Ƙura mata idanu yayi duk da ba saninta yayi ba amman da ganinta kasan tayi rama halamu sun nuna kamar dama a cikin ciwo take.
Bai jima a ɗakin ba ya fita ya shiga ofishin shi ya zauna. Sai zuwa lokacin ne ya tuno ai jakar Sabuwa na bayan motarshi. A zabure ya miƙe yana shirin zai fita Nurse Samira ta shigo da sauri.
“Dr akwai mara lafiyan daka Kawo jiya ta farka, batai magana na ba, amman sai hawaye idanta yake fitarwa.
SABUWA:.
A hankali naji idanuna na buɗewa tare da jin wani irin mugun nauyi a duk sassan jikina. Da ƙyar idanuna ya buɗe sai dai dishi_dishi nake gani na kasa tantance a inda nake. Na dai ji murya a kaina ta namiji yana cewa.
“Allurar baici ace ta saketa yanzu ba. Yaya akayi to ta farka? Muga allurar da kukai mata”
Daga haka banma sake sanin inda nake ba wani irin mugun baccine ya sureni farkon haɗuwata da Babangida yaci gaba da tariyo kanshi a ƙwaƙwalwata hankali da tunani basa jikina ina cikin halin da nayi imani ko maƙiyi sai ya zubar mun da hawaye.
CI GABAN WAIWAYE:.
“Kefa menene sunanki kyakkyawa?”
Sabida yadda Babangida hannunshi ke yawo a jikina saina kasa bashi amsa kan kari sai da nayi da gasken_ gaske kana na iya furta sunana.
“Sabuwa, ai kuwa sunan ya dace dake. Muje mu ɗan tattaka rawa. Bansan ko kina shan sigari ba balle insa a kawo miki ba”
Dama dai kunsan nayi kewar kayannan har wani tsinkewar yawu naji.
“Zo muje”
Ya riƙo hannuna muka shiga wajen da ake rawarnan a caccakuɗe cike da rashin daraja da rashin tarbiyya.
Abubbuwa a tsakanina da Babangida sun faffaru a wajen rawarnan sosai da sosai. Ga sigari bazan iya tuna kara nawa na sha ba.
Hannuna Babangida yaja muka fice daga cikin club din zuwa dogon falon da zai sadamu da ɗakunan zangon baƙin.
Wani ɗaki ya tura muka shiga anan muka tadda abokanshi. Mustapha, Gaddafi, Hannafi, sai Sani wanda shi Allah yayi mishi rasuwa.
Ko wanne budurwarshi tana gefenshi anata hira da cin nama da shaye_shayen sigari.
“Mazaje wannan mai zafin fa?”
Cewar Mustapha har yana zaro harshe yana lashewa
Kafaɗarshi Babangida ya buga.
“Kai dan abu ta kazanka. Wannan ba irinsu Karina bace. Dubeta fa da kyau ai kai da ganin kasan zata bada wuta.