TURKEN GIDA.
SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY). NA GODE BISA KARAMCINKI GARE NI, UBANGIJI YA RAYA MIKI ZURU’A AMIN
KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
07045308523.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE
MANUNIYA
Jihar kano, jiha ce da take a arewa maso gabashin yammacin Nigeria. Tana da yawan faɗin ƙasa kimanin kilimota murabba’i 20,131 da yawan Jama’a miliyan sha ɗaya da dubu hansim da takwas da ɗari uku(a ƙiyasin 2011).
*
ENGR. YUSUF MUHAMMAD INUWA ya fito daga masallacin dake can gaba da gidan shi, lokacin misalin shida saura kaɗan ne na safe, tun da ya saba sai ya tsaya ya yi azkar da yan addu’o’in shi bayan nan kuma ya kan ɗan tsaya ya gaggaisa da mutane, duk da anguwan ta masu dashi ne amman akwai mutane masu mutumci da dattako mazauna a anguwa ko dai ba a haɗu a ko’ina ba magidanta na haɗuwa duk sallar asuba a masallacin, tunda wasu daga asuba sai asuban ake samun damar ganinsu saboda aiki, irin su injiniya Yusuf ma masu harkokin da yawa da baya ma samun zama ko yini a gida shi ko weekend ne yana fita tunda shi ba aikin gwamnati yake yi ba ma’aikaci ne mai aikin kai da kai da ya tsayu da kafafunsa tun da kuruciyarsa.
A ƙiyastin shekaru Injiniya Yusuf ba zai gaza shekaru 42 a duniya ba. Kuma ba zai iya haura haka ba, yana tafiya sannu sannu bayan barowan sa daga masallaci zuwa gidansa tunda kusa ne ba nisa, sanye yake da jallabiya baƙa mai kyau har tana kyallin sabunta kansa kuma da hula wata baƙar dara sannan hannunsa ɗauke da Casbaha. Dogo ne namiji ne a tsaye mai zati da haiba, a kallo farko in ka ganshi za ka shaida bafullatani ne saboda ya na da haske sannan sumar kansa za ta iya fallasa ko shi waye, duk da ba ma’abocin tara suma ba ne. Ba doguwar fuska gare shi ba tana da ɗan faɗi amman Injiniya Yusuf yana da kyau saboda yana da dogon hanci ga kwarjini da zatin na cikakkun maza.
Wani maidaidaicin gida ya nufa a anguwan Lodge road, gidan yana bakin titi ne saboda gabaɗaya anguwan tana shimfiɗe da kwalta ne. Fasalin gidan na ƴan gayu ne ko na ce ma tsarin gini ya sanu akan aikinsa. Sannan yanayin gidan daga waje zai iya shaida maka gidan ko ba sabo ba ne, to bai daɗe ba domin har a lokacin baƙin get ɗin dake gidan yana ta ƙyallin sabunta sannan fentin gidan daga waje mai ruwan ganye yana nan a sabuntar shi kamar yau aka yi shi, yana zuwa ƙofar gidan ya zura hannu a aljihun gaban jallabiyansa ya ɗauko key ya buɗe gidan ya shiga sannan ya maida kofa ya rufe, haraban shima ƙarami ne na zaman mota ɗaya zuwa biyu, sannan ga wata baƙar mota ƙiran TOYOTA C.HR. a fake a haraban gidan sannan haraban ya ƙawatu da filawoyi masu kyau da sha’awa suna fidda kamshi. Ƙofar da zai sada shi da cikin gida tana rufe ne itama sai da ya sanya key ɗin hannun shi ya buɗe sannan ya shiga kuma ya maida ƙofa ya rufe. > Janaftybaby: Falon gidan na farko ya fara iskewa wanda ba wani hayaniya daga kujeru sai ƙaton tibi dake kafe sai cafet ɗin tsakar ɗaki. Falon yana da girma sosai saboda daga can gefe ta hannun dama akwai dining mai zaman mutum biyar, falon kalan shi mai ruwan golden yellow mai haske, hatta labulayen da suka zagayen falon kalarsu kenan.
Daga falon ya fara cire takalmin kafarsa ya fara taka doguwar kafarsa mai cike da gargasa zuwa wata kofa dake fuskanta shi, domin falon shuru, ko’ina ya na rufe har wutan ma falon a kashe ne sai da ya yi amfani da hasken wayarsa duk da kuma akwai wutar nepa bai tsaya neman makunnin wutar falon ba, tunda ba zama zai yi a ciki ba.
Ƙofar da ya sake buɗewa bai saka mata key ba tunda ta na buɗene. Tura ta kawai ya yi ta buɗe sai ga shi ya ƙara bayyana a wani ƙaramin falo mai ɗauke da kujeru guda uku ba manya sosai ba, sannan akwai tibin bango ƙarami ba wani babba ba sai cafet da Fridge babba mai kofa biyu. Daga can gefe kuma akwai dispanser a kafe shi wannan falon kalan brown ne, hatta shima labulanyan nashi suma kalansu kenan, shima falon tsit ba motsin komai, sai da ya saka hannu ya kunna wutar falon haske ya bayyana ko’ina. Daga tsakiyar falon akwai wata kofa a rufe, daga gefe kuma korido ne dogo da zai sadaka da wata kofa amman daga gabas ɗin sa kuma akwai wata itama a rufe ita ya taka ya nufa.
Sai ya ƙwankwasa lokaci ɗaya da sallama saboda daga bakin kofar kana iya jiyo sautin karatun azkar da wasu muryoyi sirara ke yi.
Buɗe ɗakin ya yi lokaci ɗaya yana shiga sannan ya maida kofar ya rufe. Lokaci ɗaya mirmishi ya wanzu a saman fuskarsa lokacin da ya yi arba da kyakyawan ƴaƴan nashi dake zaune a saman karamin cafet ɗin da ya ɗan rufe tsakiyar ɗakin. Duka mata ne babban kimanin shekarunta na haihuwa 13 da kaɗan a duniya ta na sanye da Hijabi baki har kasa da littafin azkar a hannunta sai ƙaramar mai kimanin shekaru biyar itama da irin Hijabin ɗayar a jikinta itama da ƙaramin littafin azkar a hannunta.
Sanda ya shigo har ƙaramar ta yi ƙokarim milƙewa da sauri ya ɗaga mata hannu lokaci ɗaya ya na faɗin.
” Ku ƙarishe azkar ɗin ku Baby.”
Babbar ta kalleshi ta yi masa mirmishi sai shima ya maida mata, ya ɗan jima tsaye yana kallonsu kuma yana saurarensu suna rera azkar ɗinsu cikin muryoyinsu mai sanyi da karaɗi, kamar ma sun haddace a kansu ba gargada ba komai agogon wayarsa ya duba ya ga shidda ta wuce na safe sai kawai ya kaɗa kai kafin ya ce” Jidda kar ki manta yau Monday in kun gama azkar ɗin ku yi wanka ku shirya”
Da kai babbar ta amsa masa wacce ya kira da suna Jidda, ya juya ya fice ya na mai rufe musu ƙofar ɗakin a hankali kada ta ba da sauti, ɗakin daman ba shi da wani girma akwai tiolet a ciki sai ƙananun gadaje guda biyu kowani gefen shi akwai ƙaramin wardrope mai ƙofa biyu, sai daga can gefe ƙaramin dirowa in ds suke tara littafansu na boko da na isalamiya.
Yana fitowa ya nufi hanyar korido ya buɗe kofar ya shiga sai ga wani ɗan lungu ƙarami mai kofa na fuskantan shi, sai wasu kofofin na kallon juna. Ƙofar da ke hannun dama ya buɗe ya shiga da siririyar sallama a bakinsa daga bakinsa duk da ya san wacce ke cikin ɗakin ta na barci ba lalle ba ne in ta farko, ballatana ace ta ji shi amman tunda sallama wajibi ne ko babu kowa a ɗakin shi ya sa ya yi sallama sannan ya shiga lokaci ɗaya mai da kofar ya rufe.
Akwai hasken wuta a ɗakin ya manta shi ya kunna lokacin da zai fita sallar asuba.
Yanayin kwanciyar da Sadiya ta yi ne ya sa sai da ya kusa sakin dariya shi kaɗai a sannu sannu ya karisa bakin gadon dake bedroom ɗin kafafunsa suna mai nitsewa cikin ƙaramin cafet ɗin da ya yi ma bakin gadon kwalliya.
Sanye take da kayan barci riga da wando, masu taushi kanta ba ɗankwali ko ma ta saka wajen barci ya cire, kuma ba ta yi kitso ba duk gashin ya birkice duk da a kallon farko za ka fahimci ma mallakiyar gashin ta na da yawan gyara. Kwance take a kan gadon amman yanayin kwanciyar ne abin dariya kafarta ɗaya ta sauka ƙasa, ɗayan kuma ta yi can gefe da ita ta buɗe kafarta kanta ya sauka daga kan filo sannan kwanciyar rigingine ta yi hannunta ɗaya ya yi yamma ɗaya ya yi gabas ne. > Janaftybaby: Kai ya girgiza kafin ya saka hannu ya ɗago kafarta guda ɗaya da ta sauka ƙasa ya maida ta saman gado, sannan ya gyara mata hannuwanta ya jirkitata ta yi kwanciyar gefen dama, yana shirin rufa mata blanket ɗin da ta yi gefe dashi ne ta yarfa masa hannunta a fuska a cikin barci sannan ta yi wani juyi sai da ta ture shi ba domin yana da ƙarfi ba sai ya faɗi saboda da karfi ta yi juyin. Kai ya kara girgizawa ya ja blanket ɗin ya rufa mata daga ƙafafunta zuwa cikinta, ya san ta na fashin sallah sannan a satin da ya gabata kaf ba ta zauna ba saboda Rahila ta haihu sun sha hidima.
Wajen kanta ya koma ya tattara mata gashin kanta, rebon ɗin can ya tsince shi gefen da ya kwanta ya zura hannu ya ɗauko shi ya kama sumar kan nata duk da ba shi da cika amman akwai tsawo ya kama mata shi, sannan hular dake kanta a daran jiya mai taushi da ta yi wani gefe can ya ɗauko ya saka mata sai motsawa ta ke yi tana ƙananun kunƙuni na barci. Ba ta buɗe ido ba amman ta motsa kuma ta riƙe hannunsa mai cike da garsasa bakin ta ya motsa wajen faɗin
“Yallaɓai na.”
Ƙayataccen mirmishi ya saki kafin ya riƙe hannun ta na dama da ta riƙe shi dashi, ya kai bakinsa ya sumbata lokaci ɗaya yana faɗin” Na’am Sadiya ta.”
Sai kuma ya ga ta koma barci sai ya sauke mata hannunta ya ƙara gyara mata bargo sannan ya bar bangarenta.
Ya koma ɗaya bangaren ya zauna lokaci ɗaya ya cire hula kansa ya ijiye nan saman Side drower ɗin gadon, daman casbahan hannunsa na cikin aljihun bakin wando ke jikinsa a ciki ya saka, miƙewa ya yi ya cire jallabiyan ya rage daga shi sai dogon baƙin wandon dake jikinsa. Babban wardrope ɗin dake ɗakin mai kofa shidda ya buɗe ya saka jallabiyan sannan ya saka hannu a aljihun wandon dake jikinsa ya cire casbahan ya juya ya ijiye saman makeken madubin dake bedroom wanda ke shaƙe da kayan kwalliya. Laptop ɗinsa dake cikin drower ɗin gefen gadon ya buɗe ya ɗauka akwai aikin da yake so ya kamallah kafin ya fita office.
Kan gadon ya koma ya zauna ya jingina da jikin gadon. Sannan lokaci ɗaya ya mikar da kafarsa ya dora yar ƙaramar laptop ɗinsa ya fara aiki, lokaci bayan lokaci yana kai kallonsa kan Sadiya da ta cigaba da barcinta cikin salama. Sannan kuma wani lokacin sai ya ɗaga kansa ya na zagayen ɗakin da idanuwansa.
Babban ɗaki ne domin bayan gado da wardrope akwai shuraf ɗin takalma mai hawa bakwai ne kuma dogo ne shaƙe da takalma na Sadiya da na Yusuf sai gefen kuma karfen sagala jakunkuna ne, ga su nan kala kala sama da goma, shi kalan ɗakin mai ruwan baƙi da fari ne ya yi kyau kwarai domin hatta zanin gadon fari ne da blanket ɗin su sannan haka labulan dake jikin window ɗin bedroom ɗin baki ne da fari.
Yana cikin aiki ya shagala kawai sai ji ganin kafar Sadiya ya yi a kan hannunsa dake saman laptop ta mako masa da karfi. Sai da ya yarfe hannu ya koma yana kallonta, kai ya ƙara girgizawa sannan ya ɗauki kafarta ya maida mata kan gado ya na ƙokarin cigaba da aikinsa ta ƙara yarfa masa hannu ya rankwafa yana gyara mata hannunta guda ɗaya,ta ƙara saka ɗayan hannun ta zargo wuyansa wanda sai da ya yi sauri cewa”Sadiya..”
Kamar ta ji sa sai ta sake shi, shi kuma sai ya koma yana kallonta bai san lokacin da ya kara sakin kayattacen mirmishi wanda Sadiya ce kaɗai in ya kallah ya ke iya yi ma wannan mirmishin.
Fuskarta yake kallo yana jin wani farinciki daga ƙasan ransa, yar duma duman fuskarta mai ɗauke da kalan chaculate domin ba fara ba ce wankan tarwaɗa ne, mai ɗauke da doguwar fuska hancin ta ɗan madaidai ci ne da bakinta ƙarami mai ɗan tudu, ta haura talatin amman har gobe kamar yarinya yar shekara goma sha yake kallonta a kuma haka take a idanuwansa har gobe har kuma gaban abada.
Hancinta ya lakuce lokaci ɗaya yana faɗin” Yar tekwando kawai.”
Leɓenta ya kalla har yanzu akwai danshin jan bakin da ta yi masa kwalliya jiya, hannunsa guda ɗaya ya saka ya shafi leɓenta nata lokaci ɗaya yana mirmishi da ya tuna ranar daran amarcin su ranar da shi da Sadiya suka zama Miji da mata. > Janaftybaby: Tun ta na jin ɗari ɗari ta dunkule waje ɗaya, bai raina kansa ba sai da barci ya kwashi Sadiya ranar duk jikinsa a gajiye ya tashi, Kafafunta da hannayenta ta rika yarfa masa kwana ya yi yana gyara mata kwanciya, tun daga lokacin yake zolayanta da yar Tekwandon dare, Sadiya tana da nauyin barci da mugun barci ta yi ta buge wanda suke kwana tare, in kuma ya yi magana da safe ta musa har sai ya samu wata rana ya yi mata video ta gani sannan ta gasgasta. Tun tsawon shekaru goma sha da auransu har gobe Sadiyarsa da ya aura yar ashirin ta na nan ba ta sauya ba, ba ya kuma tunanin ko tsufa ta yi akwai wasu hallayar ta da ba za su taɓa sauya wa ba.
Vibration ɗin waya dake saman can side drower bangaren Sadiya ya katse masa tunaninsa. Wani gur gur sautin ke ba da wa ya ɗauka ma nashi ne sai da ya waiwaya sai ya ga ba tashi ba ce, sannan ya fahimci wayar Sadiya ce. Laptop ɗin dake saman jikinsa ya sauke nan saman side drower ɗin bangarensa. Sannan ya sauka daga kan gadon ya taka zuwa wajen wayar ya duba sai ga ALHAJINMU ke kira, ya na shirin ɗauka sai wayar ta katse, ya san password ɗin wayarta saboda date ɗin auran sune, ya buɗe yana shirin bin bayan kiran Alhaji ganin ko bakwai ba ta yi ba yana tunanin kamar ba lafiya sai ga wani kiran Alhaji ya ƙara shigowa sai ya ɗaga kiran da sauri lokaci ɗaya ya na faɗin.
“Alhaji barka da Safiya..”
Da yake wayar tana da ƙara ana jin sautin mgana ta cikin wayar.
“A.ah Yusufa ne?. Mun tashi lafiya ya kwanan iyalan naka?
Kamar yana ganin shi Yusuf ya rankwafa yana amsa masa da lafiya kalau.
Shima ya tambaye shi ya su Gwaggo ya ce duk suna lafiya.
Alhaji Sulaiman Yashe dagacan bangaren ya ce” ina ita DUBUN take?
Ko ta na can wajen yaran ne?
Kai tsaye Yusuf yace”A’ah ba ta tashi ba ne Alhaji amman in ta tashi zan sanar mata da ta kira ka.”
Alhaji cikin gamsuwa ya ce'”To to ba laifi daman ba wani abu ba ne. Kai ma daman ina son ganinka, in ka samu dama yau bayan sallah isha’i ina son ka zo gida kai da Dubu.”
Cikin ladabi Yusuf ya ce”To Alhaji in sha Allahu muna nan tafe”
Da haka suka yi sallama, ya maida wayar mazauninta ya juya sai ya ciro karo da idanuwan Sadiya kaifaffu a kansa, mamakin yaushe na farka ya bayyana a saman fuskarsa cikin sanyin murya ya ce”Oh daman idanuwanki biyu kike ta buguna da sunan barci ko?
Mirmishi na saki kafin na miƙe zaune lokaci ɗaya ina yaye bargon jikina.
Hannu guda ɗaya na miƙa masa sai ya kama na jawo sa ya zauna a gefena ni kuma sai na yada kaina saman kafaɗansa lokaci ɗaya ina faɗin” Allah yanzu na tashi, mganarka naji sama sama a saman kaina.”
A tare na kuma kallonsa kafin na ce”Waye ya kira hala?
Yana wasa da yatsun hannuna na dama da suka shan jan lalle, ya na faɗin” Alhaji ne.”
Cikin zaro ido na ce”Alhajinmu? Bayan na tada kaina daga saman kafaɗansa.
Dariya ya yi kafin ya miƙe lokaci ɗaya ya miƙa mini hannunsa na kama ya miƙar dani tsaye ina miƙewa ya buɗe min hannuwansa na faɗa jikinsa ina sauken numfashin salama. Murya ƙasa ƙasa yace” Muna da wani Alhaji ne bayan Alhajinmu? Shi ne ya kira ya ce yana son ganin mu ni da ke. Yau da daddare”
Ina lafe a jikinsa ban wani jin mamakin jin haka ba, daman nasan za a rina ai ni daman uwar laifi ce yanzu har an samu wata ta je ta gaya ma Alhaji faɗan da ya faru tsakanina da Ma’u a gidan Rahila. Ban da Allan misuri amman ina da tabbacin dalilin kiran Alhaji kenan, ƙaramin tsaki na saki abin na cin rai na har yaushe ne yan gidammu za su gane Ma’u makira ce ita da uwarta? Tun muna yara ita ke nasara a kaina saboda macijin sari ka noƙe ce ni kuma ina da baki shi ya sa take ta samun nasara a kaina har kuma yau din nan komai ya faru tsakanimu ni ce mara gaskiya fitinanniya.
Ƙara sakin tsakin na yi wannan karon mai karfin har sai da ya ji, sai ya rankwafa da kansa dai dai kunnena yana faɗin” Me ya faru matata?
Sai na ƙara shigewa jikinsa kamar wani zai ƙwace min shi kafin na ce”Ina kwana Yallaɓan Sadiya” > Janaftybaby: Duk da ba na kallon shi amman na ji sautin mirmishin kafin yace”Ina kwana Sadiyan yallaɓai.”
Atare muka saka dariya, sannan ya ɗago ni, ya sumbaci goshina ni kuma na sumbaci kumatunsa sannan na kalleshi cikin ido ina faɗin” ina sonka Yallaɓai na.”
Mirmiahi ya yi min sannan ya sumbaci lebunana ya ɗago ya na kallona na wani lokaci kafin ya ce” Nima ina kaunarki Sadiya ta.”
Komawa na yi na sake lafewa a saman kirjinsa ina faɗin”I miss u”
Cikin ƴar shagwaɓa da har sai da ya yi mirmishi ya rumgumeni yana faɗin”Ba ga ni ba, ni naki ne har abada Sadiya ta.”
Ina jinsa ban yi mgana ba tsawon lokaci muna rumgume da juna, muna jin buguwar numfashin juna.
Da sauri na ɗago kaina ina kallonshi shima kallona ya ke yi.
“Yau wata rana Yallaɓai.?
Gira ya ɗaga kafin ya ce” Monday mana.”
Da sauri na waro ido kafin nace”Monday fa ka ce?
Ya na yar dariya ya ce”E, mi ye to?
Gabansa na bari ina gyara zaman kaina na ce” Yallaɓai yau fa monday ka manta su Jidda na da makaranta.”
Riƙo ni ya yi na dawo gabanshi lokaci ɗaya yana faɗin” Ba matsala na faɗa ma Jidda su yi wanka su shirya.”
Wuya na karya a shagwaɓe kafin na ce”Breakfast fa Yallaɓai?
Yana shirin mgana muka ji ana knooking shi ne ma ya ce a shigo, ko ban tambaya daga ni har shi mu san su waye. Buɗe ƙofar suka yi suka shigo a tare cikin shirinsu na kayan makaranta, Jidda riga da wando ne a jikinta da ƙaramin farin hijabi, sai Baby sanye da doguwar riga zuwa gwiwa daga kaɗan amman ta saka wando baƙi dogo. Itama da ƙaramin farin hijabi ita uniform ɗinta maroon ne da fari.
Da sauri na buɗe hannuwana ina faɗin”My Babys”
Da sauri Baby ta nufo ni na duƙa ta faɗa jikina tana faɗin”Good morning Umma”
Ina shafa kanta na ce”Morning my princess”
Sannan ta ɗago ta sumbaci kuncina nima sai na sumbaceta, Yusuf ta nufa tana faɗin”Good mornig Abba.”
Gefe ya yi ya na make kafaɗa kafin ya ce”Naƙi sai da aka gama rumgumar Umma sannan a ka tuna da Abba.”
Kafafunsa ta rumgume ta na faɗin”Abba”
Lokaci ɗaya ta na dariya ni kuma sai na miƙe ina faɗin”Yallaɓai kishi kake yi da Umma yau?
Hararata ya yi ba tare da ya yi mgana ba, cak ya ɗaga Baby sama. Ni kuma sai na ƙarisa na rumgume Jidda wacce ke faɗin”Ina kwana Umman mu.”
Ina shafa kumatunta na ce”Lafiya lau Jiddan Umma “
Mirmishi ta yi irin na babanta kafin ta ce”Umma mun gama shiryawa, har na ɗumama mana sauran shinkafan da kika dafa jiya mun ci ni da Baby”
Baki na washe kafin na ce”Good girl to lunch box ɗin ku fa?
Kai tsaye ta ce” Na soya mana doya Umma sai na haɗa mana tea za mu tafi dashi.”
Farinciki ya cika ni domin na gaji har daman fargaban aikin safe nake yi na sake rumgume Jidda ina faɗin” Allah ya yi ma Jiddan Umma albarka.
Ta amsa da Amin Umma bayan mun gama ta ƙarisa wajen Abbansu bayan ya sauke Baby itama ya rumgumeta bayan ta gaishe su.
Ina dariya na ce” Yallaɓai ni fa yau Jidda ta fanshe ni bari na koma barci.”
Ya na kallona ya mele baki kafin ya ce”To daman Sadiya yar laushi.”
Ina shirin hawa kan gadon ban san lokacin da na fasa ba, hannu na saka na daki kafaɗan Yusuf ina hararansa kaucewa ya yi yana ƴar dariya idanuwana kamar za su faɗo wajen hararan shi, shi kuma yana ta faman dariya ya rike hannun Jidda da Baby yana faɗin”Mu je daga falo kafin mai mashin ɗin ku yazo. Mu bar Sadiya yar laushi ta huta dakyau..”
Filon dake kan gadon na ɗauka na wurga masa ina faɗin”Tafida bana son sunan nan fa.”
Da gudu daga shi har su Jidda suka fice daga ɗakin suna min dariya, nima mirmishin na yi sannan na koma na kwanta na lulluɓa da blanket ina tuna sunan da ya kira ni da shi, ko a baya a gida in aka kirani da wannan sunan sai Alhajinmu ya yi sharia faɗan ke rabuwa, Allah ya jiƙan Mama da Rahama ita ta lanƙayamin sunan nan da har gobe bana kaunarsa.
Ƙara gyara kwanciya nayi, ina tunanin me kuma wannan karon aka je aka gaya ma Alhaji akan abin da ya faru tsakanina da Ma’u? > Janaftybaby: Wayata na zura hannu na ɗauko na shigar da kaina cikin blanket ina duba wayar tawa, Missed calls na Rahila ba adadi tun jiya take kirana ban ɗauka ba har Yaya Murja na ga ta kirani har da Ma’u, kai matar nan ba karamar makira ba ce, uban ta zan yi mata da ta kirani bayan sun haɗu ita da ƙawarta sun ci mini mutumci? Kwafa na yi ni kaɗai na buɗe data ina ganin saƙonni na ta tururuwan shigowa, abin da ya fi jan hankalina ganin group ɗina gidanmu na S. YASHE’S sai faman tagging ɗina ake yi ko shiga ban yi ba saboda nasan zagi nake sha wajen su Yaya Abubakar tunda an taɓo yar gwal wacce ba ta laifi a wajensu, su na ba ni mamaki ta ya ya za ka yanke ma bangare ɗaya hukunci ba tare da an ji bayani daga ɗaya bangaren ba? Na rasa gane wani irin tasiri Ma’u ke da shi a wajen yan gidanmu da suke fifita damuwarta sama da damuwar ni da nake ƙanwarsu jininsu.
Na ga Yaya Murja ta min Vioce note mai tsawo ko buɗewa ban yi ba, na ga ma mganar Yaya Abubakar naga dai a farko ya ce Sadiya ke wai ba ki jin mgana ko?
Sai saƙon Rahila rututu wajen ashirin na tsaki ma na kashe datan ta je ga ta ga Ma’un ta zaɓe ta sama da ni yar’uwanta da muke uba ɗaya, wulla wayar na yi can gefe na sake gyara kwanciya ina tunanin abin da zan gaya ma Alhaji, ba ni da damuwa da Yusuf saboda nasan halin mijina ɗan ba ruwan shi ne duk abinda na ce masa zai ce ya yi dai dai ne, mutum ne mai ƙoƙarin girmama duk wani abu da nake so da wanda ba na so duk da baya sanin wasu rigimgimun dake tsakanina da Ma’u amman shi shaida ne ni da ita ba ma ga maciji.
Rufe idanuwana na yi ina tuna abin da ya faru a shekaranjiya asabar wajen sunan ƴar ƴar’uwata da muke uba ɗaya Rahila wacce muka taso tare tun muna yara aure ma rana ɗaya aka yi mana. Tsabar baƙin ciki sai da na ji taruwan ƙwalla na yi saurin shanyewa, daga kan gado ina jin mganar Yusuf ta haraban gidan tunda window ɗakin na ta wajen haraba kenan su Jidda ya raka Salisu mai mashin ɗin da yake kaisu makaranta ya zo, ina kuma kwancen ba jimawa ya shigo ɗakin sai na yi luf kamar ina barci ina jinsa ya zo ya ɗauki wayarsa da laptop ɗinsa sannan ya kashe min hasken ɗakin ya fice bayan ya rufo min ƙofar. Sai na koma na ƙara lafewa na lumshe ido ina wani tunani a cikin raina ban sa na furta a fili ba sai da na riga na furta cewa” Ya Allah ka ƙara bani haihiuwa ko guda ɗaya ne na ƙara haifa.”
Idanuwana suna yi wani luu kamar zan fashe da kuka in na tuna wautar da kuruciyar da na tafka a zamanin baya gashi yanzu abin da na aikata na neman ya zo ya dame ni.
Barci ya kwashe ni sama sama ban daɗe ba na tashi saboda na ji karan ruwa a Tiolet kenan Yusuf ya shiga wanka sai na miƙe duk da ina jin kasala na saka takalma na tsakar gida mai taushi na fita daga ɗakin na buɗe kofar kitchen ɗina na shiga mai girma ne, irin kitchen ɗin zamani amman ya yi kaca kaca saboda manya sun yi aiki mirmishi nayi Jidda, ba ni ta biyo ba karsashinta irin na Babanta ne amman da ni ta biyo ba za ta iya taimakamin kamar yadda take taimakamin yanzu ba, ta yi ma Baby wanka ta shiryata sannan ta shirya kanta ta kuma yi musu abin karyawa da na tafiya makaranta sai in naga dama na ke fitowa na yi wani abun. Gyara kitchen ɗin na yi sannan na dora ruwan tea bayan na saka haɗe haɗen ganyen shayi. Nima doyar na fere na soya mana sai na yi mana yar source ɗin miya ta albasa.
Na kwshe komai zuwa dining kenan Yusuf ya fito cikin shirin fita, sanye da shadda mai ruwan ƙasa dinkin riga da wando tazarce da hula a saman kansa kuɓe takalmin kafarsa mai buɗewa ne baƙi
A falon muka haɗu yana ta tashin kamshi sai na tsaya ina kallonsa har sai da ya tsole min ido kafin ya ce”Kallon fa? Na koma miki saurayi ne?
Mirmishi na yi kafin na ce” Ko da yaushe Saurayi ka ke a idanuwan Sadiya Injiniya Yusuf, ina kallon ka ne kamar yau ɗin ne na fara ganinka a hanyar dawowata daga BUK a wata ranar laraba.” > Janaftybaby: Na faɗa ranar ta na dawo mini a cikin tunanina a tare muka saki mirmishi, kujera na ja masa na dining ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin”Na ce ƴan mata doguwa sallamu alaikum ba, ki ka wani juyo kina min fari da ido kika juya kika cigaba da tafiyarki”
Ina dariya ban yi mgana ba ina tsaye ina haɗa masa tea shi kuma yana faman kallona, basarwa na yi ina faɗin” Yau sai ka shirya ba ka jirani na zo na shirya ka ba ko?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce”Na bar Sadiya yar laushi ta huta ne.”
Da gangan na ɗiga masa ruwan zafi a hannunasa dake ɗaure da agogon fata baƙi, da sauri ya cire hannunsa a wajen ya na yarfewa ni kuma sai na haɗe rai ban ma kalleshi ba, cikin kallona ya ce”Sadiya bayan Tekwondon ɗin dare kin fara na safe ne? Kafarsa na taƙa dake cikin Takalmi da sauri ya janje kafarsa ya na faɗin”Akwai matsala kam.”
Ina tura masa Mug ɗin tea
ɗin gabansa da Doyar da na saka masa amman ban kalle shi ba. Na juya zan tafi ya riko hannuna amman sai na ƙi juyowa daman raina a jagule ya ke, amman sai ya yi tunanin mganarsa ne ya ɓata min rai, tasowa ya yi ya rumgumeni ta baya yana faɗin”Kin ji haushi ne? To Allah ya baki hakuri Sadiya ta.”
Mirmishi na saki ina riƙe hannunsa kafin na juyo da shi muna fuskantar juna, gemunsa na shafa zuwa sajensa kafin na ce”Ka ji ka wani haushi? Sadiya ce fa da Yusuf? Ka manta.? Sai ya duka ya sumabaci goshina tunda ya fi ni tsawo kafin ya ce”To ai na ga za ki tafi ki barni ni kaɗai ahalin ba haka muka saba ba.”
Da sauri na ce”Ruwa zan ɗauko kasanni da shan ruwa”
Tuna haka yasa ya sakar min hannu na fice daga falon zuwa falo na biyu kitchen na koma na ɗauko karamin mug na koma wajen depenser na tsiyaya ruwa mai ɗan sanyi sannan na koma falon na ja kujera gefensa na zauna muka fara karyaawa.
Amman ni ba wani ci nake yi ba sai juya cokali na ke yi yana ta min hira kan wani kwangila gina makaranta da aka ba kamfanin shi sun gina wajen shekaru biyu ba a biya su kuɗin aikinsu ba to daman an kira shi tun wancan sati ana saka ran payment ɗin shi ne ya ke ta mini surutu ba na wani fahimta gabaɗaya natsuwata ba ta tare da ni
Sai da na ji ya na kiran sunana.
“Sadiya.”
“Sadiya.”
Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalleshi idanuwana sun yi laushi kamar zan yi kuka.
Daƙatawa ya yi da cin abincin ya na mai ƙure ni da ido kafin ya kira sunana cikin yanayin da yakan kirani a duk lokacin da ya ga na shiga damuwa.
“Sadiya.”
Na kalle shi amman ban amsa ba cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce” Me ke damun ki ne? Tun fitowata na lura da yanayin ki ya sauya.”
Da sauri na yi mirmishi kafin na ce”Haba. Bakomai fa kawai ina tunanin kiran me Alhaji ke yi mana ni da kai?
Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya saka hannu ya rike min hannuna guda ɗaya yana faɗin”In dai kan wannan ne karki damu ba komai, ina tunanin kawai kila Alhaji na son ganin ki ne, kin san fa ke dubu ce.”
Ya faɗa da sigan zolaya duk dai ya sakani dariya kuma sai da na dara, ya manta ko wancan satin ni da yara acan muka yi ni sai dare ya je ya ɗauko mu. Amman ba na son na kawo masa mganar Ma’u shi ya sai na bar shi a hakan na san halin shi in har bai ga na saki ba ba zai fita gidan ba ko ya fita to cikin damuwa ne shi ya sa na saki jiki muka karya muna mganganumu na soyayya da muradi kamar yadda muka saba.
Bayan mun gama tare muka koma ciki ya wanke bakinsa nima na wanke duk da ban yi wanka ba. Yana riƙe da hannuna har falo ya ɗauki laptop ɗin sa na karɓa da wayarsa na rike masa shi kuma da key ɗin motarsa a hannu na rakashi har haraban gida na saka masa kayan a gaban mota bangaren mai zaman banza shi kuma ya je ya buɗe get sannan ya dawo ya rumgumeni muka sumbaci juna sannan ya sake ni yana faɗin”Karki damu in na dawo gida da wuri sai mu je mu ga Alhajin ko?
Sai na gyaɗa masa kai, na buɗe masa gaban mota ya shiga ina ɗaga masa hannu yana ɗaga mini har ya fita daga gidan ya tsaya sai da ya fito ya rufe get ɗin ya ɗaga mini hannu nima na ɗaga masa a fili na furta”Allah ya dawo mini da kai lafiya yallaɓai na.” > Janaftybaby: Cikin gida na koma na zauna a falo kawai rumgume da cussion ina tunanin rayuwa, na ɗan lokaci sannan na tashi na koma ɗaki na yi wanka na yi shigar doguwar rigar wani material mai maroon da baki sai na saka baƙar hula, ina cikin shiryawan na ji ana buga get daman na ce Saude ce ganin shuru ya sa sai ta kira wayata ina ɗauke da wayar na fita zuwa can haraban gidan na buɗe mata kofar, wata yar budurwa ta shigo tana a faɗin.
” Anty hala barci kike yi ne ina ta bugu ba ki ji ba?
Kai tsaye na ce”A’a na yi wanka ne ina kan shiri ne.”
Gaisheni ta yi na amsa ina faɗin” Ya su Balaraban ? Ta amsa min da lafiyan lau suna gaisheni.
Ina gaba tana bin bayana har cikin gida falo na biyu na shiga bayan na kalli Saude ina faɗin”Akwai sauran abin ƙaryawa a dining ki ci sannan ki fara aikin”
Da to ta amsa min sannan na shige ciki na rufe ƙofa. Saude kenan mai zuwa tana mini aikacen aikacen cikin gida. A can anguwan mu na Ɗorayi ta ke, makota suke da gidanmu.
Saboda ba na son zaman shuru ya sa na kunna Tibin a tashar MBC3 ina ga Baby ta kunna sai ban sauya ba suna haska cartoon ina kallo saboda yara. Ya ɗan fara ɗaukan hankalina kiran wayata ya katse ni ina duba mai kira sai na ga RAHILANMU ce ke kirana.
Karamin tsaki na ja har sai da ta katse ban ɗaga ba sai da ta ƙara kira gabda za ta katse sannan na ɗaga bayan na saka a amsa kuwwa a fusace ina faɗin” Wai me zan yi miki tun jiya kike ta faman kirana?
Daga can bangaren Rahila ta ce” Kai Sadiya daman kina ganin ina kiran ki shi ne kika ki ɗauka? Kai tsaye na ce”To me zan yi miki?
Rahila ba ta ji haushi ba ta ce” Yi haƙuri na ga jiya ba ki dawo ba ne Sadiya.”
Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce” To na zo na yi miki mene Rahila? Ai Ma’u na nan za ta iya miki abin da ni ba zan miki ba ma.”
Daga can bangaren Rahila ta ce”Haba Haba Sadiya wai ke abu ba ya wucewa a wajem ki? Jiya nan fa Ma’u har da kukanta ta ce ita wallahi ba ta ji daɗin abin da ya faru a tsakanin ku da shema’u ba a gabanmu fa har da yaya Murja ta kira ki baki ɗauka ba, me kike so a yi miki Sadiya.?
Karamin tsaki na ja kafin na ce” Munafuka kawai,.”
Rahila ta ce”Don Allah Sadiya ki daina wannan ƙiyayar ga Ma’u. Yar uwanki ce fa.”
Rahila ta magana kamar na kifa mata mari ta cikin wayar haka na riƙa ji.
Wai Ma’u ta na kuka a gabansu Yaya Murja, takaici ya hana ni mgana ina jin Rahila na ta wa’azin ta na fama akan na manta komai na rumgumi Ma’u.
A fusace na ce”Allah ya tsari Sadiya da ta rumgumi Ma’u. Kamar yadda ba na kaunarta itama ba ta ƙaunata amman kun kasa ganewa, shi ya sa har da Alhajimu kuka haɗa ni, ku kuka sani ga ku ga Ma’un nan tunda kuka zaɓe ta shikenan amman in dai ta na waje ina waje sai dai ɗaya ya hakura ya bar ma ɗaya.”
Rahila ta ce”Ni ban gaya ma Alhaji ba sai dai in su Yaya Murja ne.”
Baƙi na taɓe kafin nace”Koma waye ku kuka sani. Ai an taɓa yar gwal dole a je a kai ƙarana wajen Alhajin mu mana”
Rahila ta sauke kai tana faɗin” To ki yi hakuri Sadiya don Allah.”
Kamar ba zan yi mgana ba sai can na ce”Uhm”
Rahila ta yi dariya kafin ta ce”Sadiyar Dubu tawa, ga naman sunan ki a hannuna fa.”
Kai tsaye na ce” Ban so. Ki haɗa ma Ma’u duka ki aika mata.”
Ban ba ta ma zarafin mgana ba na yanke kiran ina ƙara jin takaicin kaina da na tsaya ma ina sauraranta alhalin nasan Rahila ta fi shaidar Ma’u sama da ni da muke jini ɗaya.
Ƙwafa na yi a raina ina tunanin in muka je gaban Alhajinmu zan fito masa a mutum kawai gwara ya raba tsakani na da Ma’u kowa ya yi sabgarsa zai fi alheri.
KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
07045308523.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE
🅿️02
Ina zaune a wajen Rahila ta ƙara kirana sai na danna mata busy. Ina mai ƙara sakin tsaki ni kaɗai ƙara miƙe kafata na yi a saman kujera mai zaman mutum biyun da nake zaune akai ina mai ƙara jin wani takaicin na ƙara cika min zuciyata. Rahila ba ta haƙura ba sai da ta ƙara kirana har wajen sau uku ina kashewa sannan daga ƙarshe sai ta turamin saƙo.
Na ba ma Hubby saƙon ki da zai fita, zai biya gidan Bulo ya ba ma Musabahu. Zai kawo miki ko kuma in ya haɗu da Yallaban na ƙi ya bashi ya kawo miki. Ki yi haƙuri.”
Ba saƙon ne ya ba ni dariya ba sai Hubby da na ga Rahila ta rubuto mini shi ne ya sa ni tsintsirewa da wata dariya mai sauti wanda har sai da Saude da ke kichen ta leƙo tana faɗin”Lafiya Anty?
Ina dariya na ɗaga mata hannu ina faɗin”Bakomai Saude. Ci gaba da aikin ki.”
Sai ta amsa min da kai ta maida ƙofar kitchen ɗin ta rufe ta bar ni nan zaune ina ta faman dariya. Wai Yaya Muntarin ne Hubby kai in na tuna da sunan ma sai na ji wata ƙarin dariya ni dai ban taɓa katarin Rahila ta kira shi da wannan sunan ba. Baban Islam na san tana kiran shi dashi ko Yaya Muktar ɗin da ta lankayamai amman yau shi ne karon farko da na taɓa jin ta kira shi da sunan Hubby.
Ina dariya ina tuna wani zamani a can baya ina jin na kasa riƙe dariyata. Har sake karanta saƙon na yi ina dariya a fili na furta” Tab! su Rahila masu Hubby manya.”
Saƙon Rahila shi ya tafi da kaso mafi girman ɓacin rai na, har na ji zuciyata ta yi sanyi, ban jima a falon ba na miƙe dauke da wayata ta kitchen na bi saboda daga kichen ɗin akwai ƙofar da za ta sadani da ƙofar koridin Bedrooms ɗina.
Saude na gani a rakuɓe kamar wata bakuwa tana cin doya, a tsugunne ba ta san ma na shigo ba a saman kanta ta ɗago kawai ta ganni harara na ɓalla mata kafin na ce” Wai ban hana ki wannan ɗabi’ar ba Saude? Nan gidan baƙon ki ne? Cin abinci a tsugunne kamar an hana ki zama a in da kika ga dama?
Da sauri ta ɗago tana faɗin” Yi hakuri Anty, daman na ga ina sauri ne shi ya sa ban zauna ba.” Ƙaramin tsaki na ja kafin na wuce ina faɗin”Ke dai kika sani, ki kuma cire hijabin nan saura na fito na ga kina aiki dashi kamar wata yar gudun hijira ki ga yadda za mu kwashe da ke a cikin a gidan nan.”
Dariya ta yi har ina jin sautin ta kafin ta ce” To Anty.”
Ni kuma Bedroom ɗina na koma kan Dressing ɗin mirrow ɗin da ke ɗakin na ijiye wayata na koma na kwanta har da shigewa bargo. Har ga Allah na ji ana ta kiran wayata amman ban mai da hankalina ba, na ɗauka yan gidanmu ne kan maganar ƴar gwal Ma’u shi ya sa ban ko motsa daga cikin bargon da na ke kwance ba afili ma sai da na yi ƙwafa kafin na ce”Ku ci kan ku.” Na ƙara shigar da kaina cikin bargo ina ƙara gyara kwanciyata.