*TURKEN GIDA.* *SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY). NA GODE BISA KARAMCINKI GARE NI, UBANGIJI YA RAYA MIKI ZURU'A AMIN* KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *MANUNIYA* Jihar kano, jiha ce da take a arewa maso gabashin yammacin Nigeria. Tana da yawan faɗin ƙasa kimanin kilimota murabba'i 20,131 da yawan Jama'a miliyan sha ɗaya da dubu hansim da takwas da ɗari uku(a ƙiyasin 2011). * ENGR. YUSUF MUHAMMAD INUWA ya fito daga masallacin dake can gaba da gidan shi, lokacin misalin shida saura kaɗan ne na safe, tun da ya saba sai ya tsaya ya yi azkar da yan addu'o'in shi bayan nan kuma ya kan ɗan tsaya ya gaggaisa da mutane, duk da anguwan ta masu dashi ne amman akwai mutane masu mutumci da dattako mazauna a anguwa ko dai ba a haɗu a ko'ina ba magidanta na haɗuwa duk sallar asuba a masallacin, tunda wasu daga asuba sai asuban ake samun damar ganinsu saboda aiki, irin su injiniya Yusuf ma masu harkokin da yawa da baya ma samun zama ko yini a gida shi ko weekend ne yana fita tunda shi ba aikin gwamnati yake yi ba ma'aikaci ne mai aikin kai da kai da ya tsayu da kafafunsa tun da kuruciyarsa. A ƙiyastin shekaru Injiniya Yusuf ba zai gaza shekaru 42 a duniya ba. Kuma ba zai iya haura haka ba, yana tafiya sannu sannu bayan barowan sa daga masallaci zuwa gidansa tunda kusa ne ba nisa, sanye yake da jallabiya baƙa mai kyau har tana kyallin sabunta kansa kuma da hula wata baƙar dara sannan hannunsa ɗauke da Casbaha. Dogo ne namiji ne a tsaye mai zati da haiba, a kallo farko in ka ganshi za ka shaida bafullatani ne saboda ya na da haske sannan sumar kansa za ta iya fallasa ko shi waye, duk da ba ma'abocin tara suma ba ne. Ba doguwar fuska gare shi ba tana da ɗan faɗi amman Injiniya Yusuf yana da kyau saboda yana da dogon hanci ga kwarjini da zatin na cikakkun maza. Wani maidaidaicin gida ya nufa a anguwan Lodge road, gidan yana bakin titi ne saboda gabaɗaya anguwan tana shimfiɗe da kwalta ne. Fasalin gidan na ƴan gayu ne ko na ce ma tsarin gini ya sanu akan aikinsa. Sannan yanayin gidan daga waje zai iya shaida maka gidan ko ba sabo ba ne, to bai daɗe ba domin har a lokacin baƙin get ɗin dake gidan yana ta ƙyallin sabunta sannan fentin gidan daga waje mai ruwan ganye yana nan a sabuntar shi kamar yau aka yi shi, yana zuwa ƙofar gidan ya zura hannu a aljihun gaban jallabiyansa ya ɗauko key ya buɗe gidan ya shiga sannan ya maida kofa ya rufe, haraban shima ƙarami ne na zaman mota ɗaya zuwa biyu, sannan ga wata baƙar mota ƙiran TOYOTA C.HR. a fake a haraban gidan sannan haraban ya ƙawatu da filawoyi masu kyau da sha'awa suna fidda kamshi. Ƙofar da zai sada shi da cikin gida tana rufe ne itama sai da ya sanya key ɗin hannun shi ya buɗe sannan ya shiga kuma ya maida ƙofa ya rufe. > Janaftybaby: Falon gidan na farko ya fara iskewa wanda ba wani hayaniya daga kujeru sai ƙaton tibi dake kafe sai cafet ɗin tsakar ɗaki. Falon yana da girma sosai saboda daga can gefe ta hannun dama akwai dining mai zaman mutum biyar, falon kalan shi mai ruwan golden yellow mai haske, hatta labulayen da suka zagayen falon kalarsu kenan. Daga falon ya fara cire takalmin kafarsa ya fara taka doguwar kafarsa mai cike da gargasa zuwa wata kofa dake fuskanta shi, domin falon shuru, ko'ina ya na rufe har wutan ma falon a kashe ne sai da ya yi amfani da hasken wayarsa duk da kuma akwai wutar nepa bai tsaya neman makunnin wutar falon ba, tunda ba zama zai yi a ciki ba. Ƙofar da ya sake buɗewa bai saka mata key ba tunda ta na buɗene. Tura ta kawai ya yi ta buɗe sai ga shi ya ƙara bayyana a wani ƙaramin falo mai ɗauke da kujeru guda uku ba manya sosai ba, sannan akwai tibin bango ƙarami ba wani babba ba sai cafet da Fridge babba mai kofa biyu. Daga can gefe kuma akwai dispanser a kafe shi wannan falon kalan brown ne, hatta shima labulanyan nashi suma kalansu kenan, shima falon tsit ba motsin komai, sai da ya saka hannu ya kunna wutar falon haske ya bayyana ko'ina. Daga tsakiyar falon akwai wata kofa a rufe, daga gefe kuma korido ne dogo da zai sadaka da wata kofa amman daga gabas ɗin sa kuma akwai wata itama a rufe ita ya taka ya nufa. Sai ya ƙwankwasa lokaci ɗaya da sallama saboda daga bakin kofar kana iya jiyo sautin karatun azkar da wasu muryoyi sirara ke yi. Buɗe ɗakin ya yi lokaci ɗaya yana shiga sannan ya maida kofar ya rufe. Lokaci ɗaya mirmishi ya wanzu a saman fuskarsa lokacin da ya yi arba da kyakyawan ƴaƴan nashi dake zaune a saman karamin cafet ɗin da ya ɗan rufe tsakiyar ɗakin. Duka mata ne babban kimanin shekarunta na haihuwa 13 da kaɗan a duniya ta na sanye da Hijabi baki har kasa da littafin azkar a hannunta sai ƙaramar mai kimanin shekaru biyar itama da irin Hijabin ɗayar a jikinta itama da ƙaramin littafin azkar a hannunta. Sanda ya shigo har ƙaramar ta yi ƙokarim milƙewa da sauri ya ɗaga mata hannu lokaci ɗaya ya na faɗin. " Ku ƙarishe azkar ɗin ku Baby." Babbar ta kalleshi ta yi masa mirmishi sai shima ya maida mata, ya ɗan jima tsaye yana kallonsu kuma yana saurarensu suna rera azkar ɗinsu cikin muryoyinsu mai sanyi da karaɗi, kamar ma sun haddace a kansu ba gargada ba komai agogon wayarsa ya duba ya ga shidda ta wuce na safe sai kawai ya kaɗa kai kafin ya ce" Jidda kar ki manta yau Monday in kun gama azkar ɗin ku yi wanka ku shirya" Da kai babbar ta amsa masa wacce ya kira da suna Jidda, ya juya ya fice ya na mai rufe musu ƙofar ɗakin a hankali kada ta ba da sauti, ɗakin daman ba shi da wani girma akwai tiolet a ciki sai ƙananun gadaje guda biyu kowani gefen shi akwai ƙaramin wardrope mai ƙofa biyu, sai daga can gefe ƙaramin dirowa in ds suke tara littafansu na boko da na isalamiya. Yana fitowa ya nufi hanyar korido ya buɗe kofar ya shiga sai ga wani ɗan lungu ƙarami mai kofa na fuskantan shi, sai wasu kofofin na kallon juna. Ƙofar da ke hannun dama ya buɗe ya shiga da siririyar sallama a bakinsa daga bakinsa duk da ya san wacce ke cikin ɗakin ta na barci ba lalle ba ne in ta farko, ballatana ace ta ji shi amman tunda sallama wajibi ne ko babu kowa a ɗakin shi ya sa ya yi sallama sannan ya shiga lokaci ɗaya mai da kofar ya rufe. Akwai hasken wuta a ɗakin ya manta shi ya kunna lokacin da zai fita sallar asuba. Yanayin kwanciyar da Sadiya ta yi ne ya sa sai da ya kusa sakin dariya shi kaɗai a sannu sannu ya karisa bakin gadon dake bedroom ɗin kafafunsa suna mai nitsewa cikin ƙaramin cafet ɗin da ya yi ma bakin gadon kwalliya. Sanye take da kayan barci riga da wando, masu taushi kanta ba ɗankwali ko ma ta saka wajen barci ya cire, kuma ba ta yi kitso ba duk gashin ya birkice duk da a kallon farko za ka fahimci ma mallakiyar gashin ta na da yawan gyara. Kwance take a kan gadon amman yanayin kwanciyar ne abin dariya kafarta ɗaya ta sauka ƙasa, ɗayan kuma ta yi can gefe da ita ta buɗe kafarta kanta ya sauka daga kan filo sannan kwanciyar rigingine ta yi hannunta ɗaya ya yi yamma ɗaya ya yi gabas ne. > Janaftybaby: Kai ya girgiza kafin ya saka hannu ya ɗago kafarta guda ɗaya da ta sauka ƙasa ya maida ta saman gado, sannan ya gyara mata hannuwanta ya jirkitata ta yi kwanciyar gefen dama, yana shirin rufa mata blanket ɗin da ta yi gefe dashi ne ta yarfa masa hannunta a fuska a cikin barci sannan ta yi wani juyi sai da ta ture shi ba domin yana da ƙarfi ba sai ya faɗi saboda da karfi ta yi juyin. Kai ya kara girgizawa ya ja blanket ɗin ya rufa mata daga ƙafafunta zuwa cikinta, ya san ta na fashin sallah sannan a satin da ya gabata kaf ba ta zauna ba saboda Rahila ta haihu sun sha hidima. Wajen kanta ya koma ya tattara mata gashin kanta, rebon ɗin can ya tsince shi gefen da ya kwanta ya zura hannu ya ɗauko shi ya kama sumar kan nata duk da ba shi da cika amman akwai tsawo ya kama mata shi, sannan hular dake kanta a daran jiya mai taushi da ta yi wani gefe can ya ɗauko ya saka mata sai motsawa ta ke yi tana ƙananun kunƙuni na barci. Ba ta buɗe ido ba amman ta motsa kuma ta riƙe hannunsa mai cike da garsasa bakin ta ya motsa wajen faɗin "Yallaɓai na." Ƙayataccen mirmishi ya saki kafin ya riƙe hannun ta na dama da ta riƙe shi dashi, ya kai bakinsa ya sumbata lokaci ɗaya yana faɗin" Na'am Sadiya ta." Sai kuma ya ga ta koma barci sai ya sauke mata hannunta ya ƙara gyara mata bargo sannan ya bar bangarenta. Ya koma ɗaya bangaren ya zauna lokaci ɗaya ya cire hula kansa ya ijiye nan saman Side drower ɗin gadon, daman casbahan hannunsa na cikin aljihun bakin wando ke jikinsa a ciki ya saka, miƙewa ya yi ya cire jallabiyan ya rage daga shi sai dogon baƙin wandon dake jikinsa. Babban wardrope ɗin dake ɗakin mai kofa shidda ya buɗe ya saka jallabiyan sannan ya saka hannu a aljihun wandon dake jikinsa ya cire casbahan ya juya ya ijiye saman makeken madubin dake bedroom wanda ke shaƙe da kayan kwalliya. Laptop ɗinsa dake cikin drower ɗin gefen gadon ya buɗe ya ɗauka akwai aikin da yake so ya kamallah kafin ya fita office. Kan gadon ya koma ya zauna ya jingina da jikin gadon. Sannan lokaci ɗaya ya mikar da kafarsa ya dora yar ƙaramar laptop ɗinsa ya fara aiki, lokaci bayan lokaci yana kai kallonsa kan Sadiya da ta cigaba da barcinta cikin salama. Sannan kuma wani lokacin sai ya ɗaga kansa ya na zagayen ɗakin da idanuwansa. Babban ɗaki ne domin bayan gado da wardrope akwai shuraf ɗin takalma mai hawa bakwai ne kuma dogo ne shaƙe da takalma na Sadiya da na Yusuf sai gefen kuma karfen sagala jakunkuna ne, ga su nan kala kala sama da goma, shi kalan ɗakin mai ruwan baƙi da fari ne ya yi kyau kwarai domin hatta zanin gadon fari ne da blanket ɗin su sannan haka labulan dake jikin window ɗin bedroom ɗin baki ne da fari. Yana cikin aiki ya shagala kawai sai ji ganin kafar Sadiya ya yi a kan hannunsa dake saman laptop ta mako masa da karfi. Sai da ya yarfe hannu ya koma yana kallonta, kai ya ƙara girgizawa sannan ya ɗauki kafarta ya maida mata kan gado ya na ƙokarin cigaba da aikinsa ta ƙara yarfa masa hannu ya rankwafa yana gyara mata hannunta guda ɗaya,ta ƙara saka ɗayan hannun ta zargo wuyansa wanda sai da ya yi sauri cewa"Sadiya.." Kamar ta ji sa sai ta sake shi, shi kuma sai ya koma yana kallonta bai san lokacin da ya kara sakin kayattacen mirmishi wanda Sadiya ce kaɗai in ya kallah ya ke iya yi ma wannan mirmishin. Fuskarta yake kallo yana jin wani farinciki daga ƙasan ransa, yar duma duman fuskarta mai ɗauke da kalan chaculate domin ba fara ba ce wankan tarwaɗa ne, mai ɗauke da doguwar fuska hancin ta ɗan madaidai ci ne da bakinta ƙarami mai ɗan tudu, ta haura talatin amman har gobe kamar yarinya yar shekara goma sha yake kallonta a kuma haka take a idanuwansa har gobe har kuma gaban abada. Hancinta ya lakuce lokaci ɗaya yana faɗin" Yar tekwando kawai." Leɓenta ya kalla har yanzu akwai danshin jan bakin da ta yi masa kwalliya jiya, hannunsa guda ɗaya ya saka ya shafi leɓenta nata lokaci ɗaya yana mirmishi da ya tuna ranar daran amarcin su ranar da shi da Sadiya suka zama Miji da mata. > Janaftybaby: Tun ta na jin ɗari ɗari ta dunkule waje ɗaya, bai raina kansa ba sai da barci ya kwashi Sadiya ranar duk jikinsa a gajiye ya tashi, Kafafunta da hannayenta ta rika yarfa masa kwana ya yi yana gyara mata kwanciya, tun daga lokacin yake zolayanta da yar Tekwandon dare, Sadiya tana da nauyin barci da mugun barci ta yi ta buge wanda suke kwana tare, in kuma ya yi magana da safe ta musa har sai ya samu wata rana ya yi mata video ta gani sannan ta gasgasta. Tun tsawon shekaru goma sha da auransu har gobe Sadiyarsa da ya aura yar ashirin ta na nan ba ta sauya ba, ba ya kuma tunanin ko tsufa ta yi akwai wasu hallayar ta da ba za su taɓa sauya wa ba. Vibration ɗin waya dake saman can side drower bangaren Sadiya ya katse masa tunaninsa. Wani gur gur sautin ke ba da wa ya ɗauka ma nashi ne sai da ya waiwaya sai ya ga ba tashi ba ce, sannan ya fahimci wayar Sadiya ce. Laptop ɗin dake saman jikinsa ya sauke nan saman side drower ɗin bangarensa. Sannan ya sauka daga kan gadon ya taka zuwa wajen wayar ya duba sai ga ALHAJINMU ke kira, ya na shirin ɗauka sai wayar ta katse, ya san password ɗin wayarta saboda date ɗin auran sune, ya buɗe yana shirin bin bayan kiran Alhaji ganin ko bakwai ba ta yi ba yana tunanin kamar ba lafiya sai ga wani kiran Alhaji ya ƙara shigowa sai ya ɗaga kiran da sauri lokaci ɗaya ya na faɗin. "Alhaji barka da Safiya.." Da yake wayar tana da ƙara ana jin sautin mgana ta cikin wayar. "A.ah Yusufa ne?. Mun tashi lafiya ya kwanan iyalan naka? Kamar yana ganin shi Yusuf ya rankwafa yana amsa masa da lafiya kalau. Shima ya tambaye shi ya su Gwaggo ya ce duk suna lafiya. Alhaji Sulaiman Yashe dagacan bangaren ya ce" ina ita DUBUN take? Ko ta na can wajen yaran ne? Kai tsaye Yusuf yace"A'ah ba ta tashi ba ne Alhaji amman in ta tashi zan sanar mata da ta kira ka." Alhaji cikin gamsuwa ya ce'"To to ba laifi daman ba wani abu ba ne. Kai ma daman ina son ganinka, in ka samu dama yau bayan sallah isha'i ina son ka zo gida kai da Dubu." Cikin ladabi Yusuf ya ce"To Alhaji in sha Allahu muna nan tafe" Da haka suka yi sallama, ya maida wayar mazauninta ya juya sai ya ciro karo da idanuwan Sadiya kaifaffu a kansa, mamakin yaushe na farka ya bayyana a saman fuskarsa cikin sanyin murya ya ce"Oh daman idanuwanki biyu kike ta buguna da sunan barci ko? Mirmishi na saki kafin na miƙe zaune lokaci ɗaya ina yaye bargon jikina. Hannu guda ɗaya na miƙa masa sai ya kama na jawo sa ya zauna a gefena ni kuma sai na yada kaina saman kafaɗansa lokaci ɗaya ina faɗin" Allah yanzu na tashi, mganarka naji sama sama a saman kaina." A tare na kuma kallonsa kafin na ce"Waye ya kira hala? Yana wasa da yatsun hannuna na dama da suka shan jan lalle, ya na faɗin" Alhaji ne." Cikin zaro ido na ce"Alhajinmu? Bayan na tada kaina daga saman kafaɗansa. Dariya ya yi kafin ya miƙe lokaci ɗaya ya miƙa mini hannunsa na kama ya miƙar dani tsaye ina miƙewa ya buɗe min hannuwansa na faɗa jikinsa ina sauken numfashin salama. Murya ƙasa ƙasa yace" Muna da wani Alhaji ne bayan Alhajinmu? Shi ne ya kira ya ce yana son ganin mu ni da ke. Yau da daddare" Ina lafe a jikinsa ban wani jin mamakin jin haka ba, daman nasan za a rina ai ni daman uwar laifi ce yanzu har an samu wata ta je ta gaya ma Alhaji faɗan da ya faru tsakanina da Ma'u a gidan Rahila. Ban da Allan misuri amman ina da tabbacin dalilin kiran Alhaji kenan, ƙaramin tsaki na saki abin na cin rai na har yaushe ne yan gidammu za su gane Ma'u makira ce ita da uwarta? Tun muna yara ita ke nasara a kaina saboda macijin sari ka noƙe ce ni kuma ina da baki shi ya sa take ta samun nasara a kaina har kuma yau din nan komai ya faru tsakanimu ni ce mara gaskiya fitinanniya. Ƙara sakin tsakin na yi wannan karon mai karfin har sai da ya ji, sai ya rankwafa da kansa dai dai kunnena yana faɗin" Me ya faru matata? Sai na ƙara shigewa jikinsa kamar wani zai ƙwace min shi kafin na ce"Ina kwana Yallaɓan Sadiya" > Janaftybaby: Duk da ba na kallon shi amman na ji sautin mirmishin kafin yace"Ina kwana Sadiyan yallaɓai." Atare muka saka dariya, sannan ya ɗago ni, ya sumbaci goshina ni kuma na sumbaci kumatunsa sannan na kalleshi cikin ido ina faɗin" ina sonka Yallaɓai na." Mirmiahi ya yi min sannan ya sumbaci lebunana ya ɗago ya na kallona na wani lokaci kafin ya ce" Nima ina kaunarki Sadiya ta." Komawa na yi na sake lafewa a saman kirjinsa ina faɗin"I miss u" Cikin ƴar shagwaɓa da har sai da ya yi mirmishi ya rumgumeni yana faɗin"Ba ga ni ba, ni naki ne har abada Sadiya ta." Ina jinsa ban yi mgana ba tsawon lokaci muna rumgume da juna, muna jin buguwar numfashin juna. Da sauri na ɗago kaina ina kallonshi shima kallona ya ke yi. "Yau wata rana Yallaɓai.? Gira ya ɗaga kafin ya ce" Monday mana." Da sauri na waro ido kafin nace"Monday fa ka ce? Ya na yar dariya ya ce"E, mi ye to? Gabansa na bari ina gyara zaman kaina na ce" Yallaɓai yau fa monday ka manta su Jidda na da makaranta." Riƙo ni ya yi na dawo gabanshi lokaci ɗaya yana faɗin" Ba matsala na faɗa ma Jidda su yi wanka su shirya." Wuya na karya a shagwaɓe kafin na ce"Breakfast fa Yallaɓai? Yana shirin mgana muka ji ana knooking shi ne ma ya ce a shigo, ko ban tambaya daga ni har shi mu san su waye. Buɗe ƙofar suka yi suka shigo a tare cikin shirinsu na kayan makaranta, Jidda riga da wando ne a jikinta da ƙaramin farin hijabi, sai Baby sanye da doguwar riga zuwa gwiwa daga kaɗan amman ta saka wando baƙi dogo. Itama da ƙaramin farin hijabi ita uniform ɗinta maroon ne da fari. Da sauri na buɗe hannuwana ina faɗin"My Babys" Da sauri Baby ta nufo ni na duƙa ta faɗa jikina tana faɗin"Good morning Umma" Ina shafa kanta na ce"Morning my princess" Sannan ta ɗago ta sumbaci kuncina nima sai na sumbaceta, Yusuf ta nufa tana faɗin"Good mornig Abba." Gefe ya yi ya na make kafaɗa kafin ya ce"Naƙi sai da aka gama rumgumar Umma sannan a ka tuna da Abba." Kafafunsa ta rumgume ta na faɗin"Abba" Lokaci ɗaya ta na dariya ni kuma sai na miƙe ina faɗin"Yallaɓai kishi kake yi da Umma yau? Hararata ya yi ba tare da ya yi mgana ba, cak ya ɗaga Baby sama. Ni kuma sai na ƙarisa na rumgume Jidda wacce ke faɗin"Ina kwana Umman mu." Ina shafa kumatunta na ce"Lafiya lau Jiddan Umma " Mirmishi ta yi irin na babanta kafin ta ce"Umma mun gama shiryawa, har na ɗumama mana sauran shinkafan da kika dafa jiya mun ci ni da Baby" Baki na washe kafin na ce"Good girl to lunch box ɗin ku fa? Kai tsaye ta ce" Na soya mana doya Umma sai na haɗa mana tea za mu tafi dashi." Farinciki ya cika ni domin na gaji har daman fargaban aikin safe nake yi na sake rumgume Jidda ina faɗin" Allah ya yi ma Jiddan Umma albarka. Ta amsa da Amin Umma bayan mun gama ta ƙarisa wajen Abbansu bayan ya sauke Baby itama ya rumgumeta bayan ta gaishe su. Ina dariya na ce" Yallaɓai ni fa yau Jidda ta fanshe ni bari na koma barci." Ya na kallona ya mele baki kafin ya ce"To daman Sadiya yar laushi." Ina shirin hawa kan gadon ban san lokacin da na fasa ba, hannu na saka na daki kafaɗan Yusuf ina hararansa kaucewa ya yi yana ƴar dariya idanuwana kamar za su faɗo wajen hararan shi, shi kuma yana ta faman dariya ya rike hannun Jidda da Baby yana faɗin"Mu je daga falo kafin mai mashin ɗin ku yazo. Mu bar Sadiya yar laushi ta huta dakyau.." Filon dake kan gadon na ɗauka na wurga masa ina faɗin"Tafida bana son sunan nan fa." Da gudu daga shi har su Jidda suka fice daga ɗakin suna min dariya, nima mirmishin na yi sannan na koma na kwanta na lulluɓa da blanket ina tuna sunan da ya kira ni da shi, ko a baya a gida in aka kirani da wannan sunan sai Alhajinmu ya yi sharia faɗan ke rabuwa, Allah ya jiƙan Mama da Rahama ita ta lanƙayamin sunan nan da har gobe bana kaunarsa. Ƙara gyara kwanciya nayi, ina tunanin me kuma wannan karon aka je aka gaya ma Alhaji akan abin da ya faru tsakanina da Ma'u? > Janaftybaby: Wayata na zura hannu na ɗauko na shigar da kaina cikin blanket ina duba wayar tawa, Missed calls na Rahila ba adadi tun jiya take kirana ban ɗauka ba har Yaya Murja na ga ta kirani har da Ma'u, kai matar nan ba karamar makira ba ce, uban ta zan yi mata da ta kirani bayan sun haɗu ita da ƙawarta sun ci mini mutumci? Kwafa na yi ni kaɗai na buɗe data ina ganin saƙonni na ta tururuwan shigowa, abin da ya fi jan hankalina ganin group ɗina gidanmu na S. YASHE'S sai faman tagging ɗina ake yi ko shiga ban yi ba saboda nasan zagi nake sha wajen su Yaya Abubakar tunda an taɓo yar gwal wacce ba ta laifi a wajensu, su na ba ni mamaki ta ya ya za ka yanke ma bangare ɗaya hukunci ba tare da an ji bayani daga ɗaya bangaren ba? Na rasa gane wani irin tasiri Ma'u ke da shi a wajen yan gidanmu da suke fifita damuwarta sama da damuwar ni da nake ƙanwarsu jininsu. Na ga Yaya Murja ta min Vioce note mai tsawo ko buɗewa ban yi ba, na ga ma mganar Yaya Abubakar naga dai a farko ya ce Sadiya ke wai ba ki jin mgana ko? Sai saƙon Rahila rututu wajen ashirin na tsaki ma na kashe datan ta je ga ta ga Ma'un ta zaɓe ta sama da ni yar'uwanta da muke uba ɗaya, wulla wayar na yi can gefe na sake gyara kwanciya ina tunanin abin da zan gaya ma Alhaji, ba ni da damuwa da Yusuf saboda nasan halin mijina ɗan ba ruwan shi ne duk abinda na ce masa zai ce ya yi dai dai ne, mutum ne mai ƙoƙarin girmama duk wani abu da nake so da wanda ba na so duk da baya sanin wasu rigimgimun dake tsakanina da Ma'u amman shi shaida ne ni da ita ba ma ga maciji. Rufe idanuwana na yi ina tuna abin da ya faru a shekaranjiya asabar wajen sunan ƴar ƴar'uwata da muke uba ɗaya Rahila wacce muka taso tare tun muna yara aure ma rana ɗaya aka yi mana. Tsabar baƙin ciki sai da na ji taruwan ƙwalla na yi saurin shanyewa, daga kan gado ina jin mganar Yusuf ta haraban gidan tunda window ɗakin na ta wajen haraba kenan su Jidda ya raka Salisu mai mashin ɗin da yake kaisu makaranta ya zo, ina kuma kwancen ba jimawa ya shigo ɗakin sai na yi luf kamar ina barci ina jinsa ya zo ya ɗauki wayarsa da laptop ɗinsa sannan ya kashe min hasken ɗakin ya fice bayan ya rufo min ƙofar. Sai na koma na ƙara lafewa na lumshe ido ina wani tunani a cikin raina ban sa na furta a fili ba sai da na riga na furta cewa" Ya Allah ka ƙara bani haihiuwa ko guda ɗaya ne na ƙara haifa." Idanuwana suna yi wani luu kamar zan fashe da kuka in na tuna wautar da kuruciyar da na tafka a zamanin baya gashi yanzu abin da na aikata na neman ya zo ya dame ni. Barci ya kwashe ni sama sama ban daɗe ba na tashi saboda na ji karan ruwa a Tiolet kenan Yusuf ya shiga wanka sai na miƙe duk da ina jin kasala na saka takalma na tsakar gida mai taushi na fita daga ɗakin na buɗe kofar kitchen ɗina na shiga mai girma ne, irin kitchen ɗin zamani amman ya yi kaca kaca saboda manya sun yi aiki mirmishi nayi Jidda, ba ni ta biyo ba karsashinta irin na Babanta ne amman da ni ta biyo ba za ta iya taimakamin kamar yadda take taimakamin yanzu ba, ta yi ma Baby wanka ta shiryata sannan ta shirya kanta ta kuma yi musu abin karyawa da na tafiya makaranta sai in naga dama na ke fitowa na yi wani abun. Gyara kitchen ɗin na yi sannan na dora ruwan tea bayan na saka haɗe haɗen ganyen shayi. Nima doyar na fere na soya mana sai na yi mana yar source ɗin miya ta albasa. Na kwshe komai zuwa dining kenan Yusuf ya fito cikin shirin fita, sanye da shadda mai ruwan ƙasa dinkin riga da wando tazarce da hula a saman kansa kuɓe takalmin kafarsa mai buɗewa ne baƙi A falon muka haɗu yana ta tashin kamshi sai na tsaya ina kallonsa har sai da ya tsole min ido kafin ya ce"Kallon fa? Na koma miki saurayi ne? Mirmishi na yi kafin na ce" Ko da yaushe Saurayi ka ke a idanuwan Sadiya Injiniya Yusuf, ina kallon ka ne kamar yau ɗin ne na fara ganinka a hanyar dawowata daga BUK a wata ranar laraba." > Janaftybaby: Na faɗa ranar ta na dawo mini a cikin tunanina a tare muka saki mirmishi, kujera na ja masa na dining ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin"Na ce ƴan mata doguwa sallamu alaikum ba, ki ka wani juyo kina min fari da ido kika juya kika cigaba da tafiyarki" Ina dariya ban yi mgana ba ina tsaye ina haɗa masa tea shi kuma yana faman kallona, basarwa na yi ina faɗin" Yau sai ka shirya ba ka jirani na zo na shirya ka ba ko? Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Na bar Sadiya yar laushi ta huta ne." Da gangan na ɗiga masa ruwan zafi a hannunasa dake ɗaure da agogon fata baƙi, da sauri ya cire hannunsa a wajen ya na yarfewa ni kuma sai na haɗe rai ban ma kalleshi ba, cikin kallona ya ce"Sadiya bayan Tekwondon ɗin dare kin fara na safe ne? Kafarsa na taƙa dake cikin Takalmi da sauri ya janje kafarsa ya na faɗin"Akwai matsala kam." Ina tura masa Mug ɗin tea ɗin gabansa da Doyar da na saka masa amman ban kalle shi ba. Na juya zan tafi ya riko hannuna amman sai na ƙi juyowa daman raina a jagule ya ke, amman sai ya yi tunanin mganarsa ne ya ɓata min rai, tasowa ya yi ya rumgumeni ta baya yana faɗin"Kin ji haushi ne? To Allah ya baki hakuri Sadiya ta." Mirmishi na saki ina riƙe hannunsa kafin na juyo da shi muna fuskantar juna, gemunsa na shafa zuwa sajensa kafin na ce"Ka ji ka wani haushi? Sadiya ce fa da Yusuf? Ka manta.? Sai ya duka ya sumabaci goshina tunda ya fi ni tsawo kafin ya ce"To ai na ga za ki tafi ki barni ni kaɗai ahalin ba haka muka saba ba." Da sauri na ce"Ruwa zan ɗauko kasanni da shan ruwa" Tuna haka yasa ya sakar min hannu na fice daga falon zuwa falo na biyu kitchen na koma na ɗauko karamin mug na koma wajen depenser na tsiyaya ruwa mai ɗan sanyi sannan na koma falon na ja kujera gefensa na zauna muka fara karyaawa. Amman ni ba wani ci nake yi ba sai juya cokali na ke yi yana ta min hira kan wani kwangila gina makaranta da aka ba kamfanin shi sun gina wajen shekaru biyu ba a biya su kuɗin aikinsu ba to daman an kira shi tun wancan sati ana saka ran payment ɗin shi ne ya ke ta mini surutu ba na wani fahimta gabaɗaya natsuwata ba ta tare da ni Sai da na ji ya na kiran sunana. "Sadiya." "Sadiya." Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalleshi idanuwana sun yi laushi kamar zan yi kuka. Daƙatawa ya yi da cin abincin ya na mai ƙure ni da ido kafin ya kira sunana cikin yanayin da yakan kirani a duk lokacin da ya ga na shiga damuwa. "Sadiya." Na kalle shi amman ban amsa ba cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce" Me ke damun ki ne? Tun fitowata na lura da yanayin ki ya sauya." Da sauri na yi mirmishi kafin na ce"Haba. Bakomai fa kawai ina tunanin kiran me Alhaji ke yi mana ni da kai? Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya saka hannu ya rike min hannuna guda ɗaya yana faɗin"In dai kan wannan ne karki damu ba komai, ina tunanin kawai kila Alhaji na son ganin ki ne, kin san fa ke dubu ce." Ya faɗa da sigan zolaya duk dai ya sakani dariya kuma sai da na dara, ya manta ko wancan satin ni da yara acan muka yi ni sai dare ya je ya ɗauko mu. Amman ba na son na kawo masa mganar Ma'u shi ya sai na bar shi a hakan na san halin shi in har bai ga na saki ba ba zai fita gidan ba ko ya fita to cikin damuwa ne shi ya sa na saki jiki muka karya muna mganganumu na soyayya da muradi kamar yadda muka saba. Bayan mun gama tare muka koma ciki ya wanke bakinsa nima na wanke duk da ban yi wanka ba. Yana riƙe da hannuna har falo ya ɗauki laptop ɗin sa na karɓa da wayarsa na rike masa shi kuma da key ɗin motarsa a hannu na rakashi har haraban gida na saka masa kayan a gaban mota bangaren mai zaman banza shi kuma ya je ya buɗe get sannan ya dawo ya rumgumeni muka sumbaci juna sannan ya sake ni yana faɗin"Karki damu in na dawo gida da wuri sai mu je mu ga Alhajin ko? Sai na gyaɗa masa kai, na buɗe masa gaban mota ya shiga ina ɗaga masa hannu yana ɗaga mini har ya fita daga gidan ya tsaya sai da ya fito ya rufe get ɗin ya ɗaga mini hannu nima na ɗaga masa a fili na furta"Allah ya dawo mini da kai lafiya yallaɓai na." > Janaftybaby: Cikin gida na koma na zauna a falo kawai rumgume da cussion ina tunanin rayuwa, na ɗan lokaci sannan na tashi na koma ɗaki na yi wanka na yi shigar doguwar rigar wani material mai maroon da baki sai na saka baƙar hula, ina cikin shiryawan na ji ana buga get daman na ce Saude ce ganin shuru ya sa sai ta kira wayata ina ɗauke da wayar na fita zuwa can haraban gidan na buɗe mata kofar, wata yar budurwa ta shigo tana a faɗin. " Anty hala barci kike yi ne ina ta bugu ba ki ji ba? Kai tsaye na ce"A'a na yi wanka ne ina kan shiri ne." Gaisheni ta yi na amsa ina faɗin" Ya su Balaraban ? Ta amsa min da lafiyan lau suna gaisheni. Ina gaba tana bin bayana har cikin gida falo na biyu na shiga bayan na kalli Saude ina faɗin"Akwai sauran abin ƙaryawa a dining ki ci sannan ki fara aikin" Da to ta amsa min sannan na shige ciki na rufe ƙofa. Saude kenan mai zuwa tana mini aikacen aikacen cikin gida. A can anguwan mu na Ɗorayi ta ke, makota suke da gidanmu. Saboda ba na son zaman shuru ya sa na kunna Tibin a tashar MBC3 ina ga Baby ta kunna sai ban sauya ba suna haska cartoon ina kallo saboda yara. Ya ɗan fara ɗaukan hankalina kiran wayata ya katse ni ina duba mai kira sai na ga RAHILANMU ce ke kirana. Karamin tsaki na ja har sai da ta katse ban ɗaga ba sai da ta ƙara kira gabda za ta katse sannan na ɗaga bayan na saka a amsa kuwwa a fusace ina faɗin" Wai me zan yi miki tun jiya kike ta faman kirana? Daga can bangaren Rahila ta ce" Kai Sadiya daman kina ganin ina kiran ki shi ne kika ki ɗauka? Kai tsaye na ce"To me zan yi miki? Rahila ba ta ji haushi ba ta ce" Yi haƙuri na ga jiya ba ki dawo ba ne Sadiya." Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" To na zo na yi miki mene Rahila? Ai Ma'u na nan za ta iya miki abin da ni ba zan miki ba ma." Daga can bangaren Rahila ta ce"Haba Haba Sadiya wai ke abu ba ya wucewa a wajem ki? Jiya nan fa Ma'u har da kukanta ta ce ita wallahi ba ta ji daɗin abin da ya faru a tsakanin ku da shema'u ba a gabanmu fa har da yaya Murja ta kira ki baki ɗauka ba, me kike so a yi miki Sadiya.? Karamin tsaki na ja kafin na ce" Munafuka kawai,." Rahila ta ce"Don Allah Sadiya ki daina wannan ƙiyayar ga Ma'u. Yar uwanki ce fa." Rahila ta magana kamar na kifa mata mari ta cikin wayar haka na riƙa ji. Wai Ma'u ta na kuka a gabansu Yaya Murja, takaici ya hana ni mgana ina jin Rahila na ta wa'azin ta na fama akan na manta komai na rumgumi Ma'u. A fusace na ce"Allah ya tsari Sadiya da ta rumgumi Ma'u. Kamar yadda ba na kaunarta itama ba ta ƙaunata amman kun kasa ganewa, shi ya sa har da Alhajimu kuka haɗa ni, ku kuka sani ga ku ga Ma'un nan tunda kuka zaɓe ta shikenan amman in dai ta na waje ina waje sai dai ɗaya ya hakura ya bar ma ɗaya." Rahila ta ce"Ni ban gaya ma Alhaji ba sai dai in su Yaya Murja ne." Baƙi na taɓe kafin nace"Koma waye ku kuka sani. Ai an taɓa yar gwal dole a je a kai ƙarana wajen Alhajin mu mana" Rahila ta sauke kai tana faɗin" To ki yi hakuri Sadiya don Allah." Kamar ba zan yi mgana ba sai can na ce"Uhm" Rahila ta yi dariya kafin ta ce"Sadiyar Dubu tawa, ga naman sunan ki a hannuna fa." Kai tsaye na ce" Ban so. Ki haɗa ma Ma'u duka ki aika mata." Ban ba ta ma zarafin mgana ba na yanke kiran ina ƙara jin takaicin kaina da na tsaya ma ina sauraranta alhalin nasan Rahila ta fi shaidar Ma'u sama da ni da muke jini ɗaya. Ƙwafa na yi a raina ina tunanin in muka je gaban Alhajinmu zan fito masa a mutum kawai gwara ya raba tsakani na da Ma'u kowa ya yi sabgarsa zai fi alheri. KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️02* Ina zaune a wajen Rahila ta ƙara kirana sai na danna mata busy. Ina mai ƙara sakin tsaki ni kaɗai ƙara miƙe kafata na yi a saman kujera mai zaman mutum biyun da nake zaune akai ina mai ƙara jin wani takaicin na ƙara cika min zuciyata. Rahila ba ta haƙura ba sai da ta ƙara kirana har wajen sau uku ina kashewa sannan daga ƙarshe sai ta turamin saƙo. Na ba ma Hubby saƙon ki da zai fita, zai biya gidan Bulo ya ba ma Musabahu. Zai kawo miki ko kuma in ya haɗu da Yallaban na ƙi ya bashi ya kawo miki. Ki yi haƙuri." Ba saƙon ne ya ba ni dariya ba sai Hubby da na ga Rahila ta rubuto mini shi ne ya sa ni tsintsirewa da wata dariya mai sauti wanda har sai da Saude da ke kichen ta leƙo tana faɗin"Lafiya Anty? Ina dariya na ɗaga mata hannu ina faɗin"Bakomai Saude. Ci gaba da aikin ki." Sai ta amsa min da kai ta maida ƙofar kitchen ɗin ta rufe ta bar ni nan zaune ina ta faman dariya. Wai Yaya Muntarin ne Hubby kai in na tuna da sunan ma sai na ji wata ƙarin dariya ni dai ban taɓa katarin Rahila ta kira shi da wannan sunan ba. Baban Islam na san tana kiran shi dashi ko Yaya Muktar ɗin da ta lankayamai amman yau shi ne karon farko da na taɓa jin ta kira shi da sunan Hubby. Ina dariya ina tuna wani zamani a can baya ina jin na kasa riƙe dariyata. Har sake karanta saƙon na yi ina dariya a fili na furta" Tab! su Rahila masu Hubby manya." Saƙon Rahila shi ya tafi da kaso mafi girman ɓacin rai na, har na ji zuciyata ta yi sanyi, ban jima a falon ba na miƙe dauke da wayata ta kitchen na bi saboda daga kichen ɗin akwai ƙofar da za ta sadani da ƙofar koridin Bedrooms ɗina. Saude na gani a rakuɓe kamar wata bakuwa tana cin doya, a tsugunne ba ta san ma na shigo ba a saman kanta ta ɗago kawai ta ganni harara na ɓalla mata kafin na ce" Wai ban hana ki wannan ɗabi'ar ba Saude? Nan gidan baƙon ki ne? Cin abinci a tsugunne kamar an hana ki zama a in da kika ga dama? Da sauri ta ɗago tana faɗin" Yi hakuri Anty, daman na ga ina sauri ne shi ya sa ban zauna ba." Ƙaramin tsaki na ja kafin na wuce ina faɗin"Ke dai kika sani, ki kuma cire hijabin nan saura na fito na ga kina aiki dashi kamar wata yar gudun hijira ki ga yadda za mu kwashe da ke a cikin a gidan nan." Dariya ta yi har ina jin sautin ta kafin ta ce" To Anty." Ni kuma Bedroom ɗina na koma kan Dressing ɗin mirrow ɗin da ke ɗakin na ijiye wayata na koma na kwanta har da shigewa bargo. Har ga Allah na ji ana ta kiran wayata amman ban mai da hankalina ba, na ɗauka yan gidanmu ne kan maganar ƴar gwal Ma'u shi ya sa ban ko motsa daga cikin bargon da na ke kwance ba afili ma sai da na yi ƙwafa kafin na ce"Ku ci kan ku." Na ƙara shigar da kaina cikin bargo ina ƙara gyara kwanciyata. Barci ya fara ɗauka ta domin har na fara wani mafarki mai ɗan karan daɗi, kamar daga sama na ji muryan Saude ta na kirana. "Anty. Anty.." A firgice na tashi saboda a saman kaina a can cikin barci na ji kiran sunan. Saude na gani a cikin Bedroom ɗina daga can baƙin kofa, tana ganin na tashi zaune da sauri ta ce"Anty kin yi baƙuwa." Yamutsa fuska na yi kafin na maimaita kalmar" Baƙuwa? > Janaftybaby: Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce"E. ta ce na faɗa miki Bahijja ce." Shuru na yi ina tunanin wace ce kuma Bahijja, ido na ɗan waro kafin na yi saurin yaye bargon jikina na sauko daga kan gadon lokaci ɗaya ina faɗin" Tana can falo ne? Saude ta gyaɗa kanta kafin Ta ce" E. tana can falon farko." Kai na gyaɗa kafin na ce" Je ki ce mata gani nan zuwa Saude." Ta amsa min cikin ladabi sannan ta buɗe kofa ta fita ta barni ina sauke numfashi. A gaban madubi na tsaya ina kallon fuskarta sai da na tabbatar da ba ni da wani abu da za ta kalla ta yi ƙorafi sannan na gayyato mirmishi da fara'a a saman fuskata sannan na zura takalmina mai taushi na zirga zirgan cikin gida, na zo zan gota ta jikin madubin sai da na ƙara tsayawa na kurama kaina ido ta cikin madubin ina jin gabbaina suna yin wani irin sanyi ƙalau, yanayin jikina na bi da kallo tabbas ina da son gayu da gyara ni macece da kana ganina kafin ma a faɗa maka wani abu akaina za ka sha shaida ina da son gyara, tun da ga kan gyaran fata na gashi da gyaran ƙasa na mace duka ba na wasa dasu bangaren gyaran fata kayan AISHA LAME +234 703 666 2633 na ke amfani da su, in kuma bangaren kayan ƙawa na gayu ne tun da ga kan atamfofi da abayoyi da takalma a wajen DIJA COLLECTION na kan yi siyayyata da ga ni har su Jidda shi ya sa kayana tare da na ƴaƴana muka fita dabam a cikin Dangi. Numfashi na ja sannan na ƙara fesarwa, wayata na ɗauka sannan na fice daga ɗakin ba ta kitchen na bi ba sai ta bi ta korido tunda falon farko zan je, ina tafe ne ina latsa wayata na ji na tsorata lokacin da na ga cikin waɗanda suka kirani har da Anty Bahijja, lalle yau Allah ne kaɗai ya isa ya cece ni daga ƙorafi da ƙananun mganganu sai wanda kunnena suka iya ji, ina tura ƙofar falon lokaci ɗaya tare da sallamata da kuma tahowa da fara'a a saman fuskata. +234 903 661 7473 Ta na hakimce kan kujera mai zaman mutum ɗaya, sanye da dogon hijabi mai ruwan kuka har da liƙabinta, kenan daga makaranta take, ta biyo ta nan ina nufarta ina washe baki lokaci ɗaya ina faɗin"Maraba da Anty Bahijja." Sai a lokacin ta ɗago kanta daga duba wayarta da take yi, sai da na kariso gabanta na zauna saman kujera mai zaman mutum ukun da take gefenta ina faɗin" Ina kwana Anty Bahijja." Sai a lokacin ta iya ɗaga likaɓin ta sama fuskarta ta bayyana. Cikin yanayin maganarta ta kalleni daga sama har ƙasa ni kuma ina ta faman yi mata mirmishi. "Barka dai ta tashi gimbiya ko na ce Sadiya yar laushi ba" Wani abu mai ɗaci ya taho daga cikina ya tokare a saman ƙirjina. Shi ya sa har abada ba zan taɓa ƙaunar Ma'u ba, kuma ni da ita ba za mu taɓa zama a inuwa ɗaya ba. Amman ban nuna mata ba sai ma na ɓige da yin wani kayattacen mirmishi kafin na ce"Kai Anty Bahijja, ki yi haƙuri kin kirani ban ji ba. Na ɗan kwanta ne." Baki ta taɓe kafin ta ce"Ai fa aikin kenan barci, kina ciki kin kwanta yar aiki na yi miki aikace aikace" Kai tsaye nima na ce" Saude ai tana zuwa tana taimaka mini ne, kinsan aikin gida da yawa Anty Bahijja." "Ina wani yawa a aikin gidan nan Sadiya? Kawai daman kin saba da hutu shi ya sa kike kallon shi a matsayin aiki." Ni ko sai na yi mata mirmishi duk da maganar ta na sukan zuciyata amman sai na ɓoye hakan a saman fuskata. Kai na kaɗa kafin na ce"Hutun ne ya zo Anty Bahijja amman karki manta a baya nima na yi aikin." Ta san magana na gaya mata shi ya sa ta yi mini wani kallo, ban bari ta samu damar magana ba na cigaba da faɗin" Kuma Anty Bahijja laifi ne in mace ta samu hutu ta huta a gidan mijinta? Kema fa kina da yar aikin nan sannan ki na fatan nan gaba in su Sulaihat suka yi aure suma su samu gidan da za su huta ko ba haka ba ne? Ba fa wanda ba ya son jin daɗin nan fa." Na faɗa ina kallonta saboda na ga kuma wata magana za ta ƙara faɗa mini, sai na ga ta juyar da kai ta na faɗin"Ba irin na ki ba Sadiya." Ban yi magana na nima sai na kauda kaina ina ɗan mirmishi, na rasa wani hutu suke hangomin a cikin wannan gidan? Sun manta a baya komai na gidana da mijina da ƴaƴana ni nake yi ma kaina? Saude ba ta fara zuwa mini aiki ba sai bayan mun tare a wannan sabon gidan amman gabaɗaya ƴan'uwan Yusuf gani suke > Janaftybaby: yi da kuɗin ɗan'uwansu na ke walwali ina haskawa sannan na samu duniya ina ta jin daɗina. Ban ƙara ce mata ƙala ba, amman ita sai faman kalle kallen falon take yi tana wani taɓe baƙi, ba yarinya ba ce tunda Yayar Yallaɓai ce, daga ita sai shi tana da manyan ƴaƴa amman ba taba aurarwa ba suna karatu ne. Can ta ga ji da zaman mulkinta ta kalleni ta na faɗin" Su Jidda suna makaranta ko? Sai na gyaɗa mata kai, kafin na yi magana ta rigani da cewa" Kuma sai satin nan ba ki kai su gidan Yaya Maimuna ba? Me ya sa ? Daman na san rashin zuwan su gidan Anty Maimuna sai ya zame min abin magana, zama na gyara kafin na fara faɗin" Ba su samu zuwa ba. Amman weekend ɗin nan in sha Allahu za su je." Anty Bahijja ta ƙara faɗin" Me ya sa na ke tambaya? Kai tsaye na ce"Gidanmu muka yini ranar asabar, lahadi kuma na ce su tsaya saboda shiryen shiryem makaranta, su goge uniform da homework lokaci ya ƙure shi ya sa sai na ce bari su bari wannan satin da sun dawo makaranta ranar jumma'a zan tsa yar mai mashin ɗin su, sai ya kai su in sha Allahu." Miƙewa ta yi, lokaci ɗaya ta na rayata jakarta, kafin ta kalleni tana faɗin"Kina da ƙulafucin ƴa'ƴan Sadiya. To ki yi zuciya ki sake haihuwa mana. Amman ace kamar gidan Yusuf shi da ke son yara a ce ƴaƴa biyu kaɗai gare shi kamar ba shi da wani zaɓi, yanzu in muka ce ya ƙara aure sai ki ji haushin mu ko? Ƙuramin ido ta yi saboda tana so ta ga yadda zan yi, sai ni kuma na nuna mata har yanzu ba ta gama sanin wacece Sadiya ba. Dariya na saki har ta na fidda sauti kafin na ce" Jin haushi kuma Anty Bahijja? Ai aure umarnin Allah ne shi ya ba su damar ƙarawa, wallahi tallahi na sha faɗa ma Yallaɓai in zai ƙara aure ya ƙara domin ni ba ni da matsala da ƙarin auransa tun da ba akaina za ta zauna ba, kuma ko ta zo sai dai ta zo a ta biyu kin ga kenan ko ya ya dai na ke na amsa sunan Turken gida. Haihuwa kuma ta Allah ce, in ya tsara min ƴa'ya biyu zan haifa shike nan, kuma ni ba zan yi ma Yallaɓaina baƙin cikin ya ƙara aure ya sake haihuwa ba, duk wani abu da ya fito daga tsatson Yusuf abin so ne a wajena." Kamar ba ta yarda da magana ta ba, domin sai ta ƙara kallona take yi, tana mirmishi, kallonta na yi domin har ta mirmishinta irin na Yallaɓaina ne. Ganin ta kama hanyar barin falon ya sa na miƙe na bi bayanta dai dai lokacin da na ji ta na faɗin"Ke fa kika tsaida haihuwan da kanki Sadiya kin ga ko, ko auran Yusuf ya ƙara bai yi miki rashin adalci ba." Ina bin bayanta na yi mirmishi amman ban yi magana ba. Ni ce har haraban gida na rakata, ina ce mata"Ba ki zo da mota ba ne Anty Bahijja? Kai tsaye ta ce" Tana waje." Sai na gyaɗa kaina fulawowin gidan ta bi da kallo kafin ta ce" Fulawowin nan sun ƙara ma gidan nan kyau fa." Na biye mata ina cewa" Sosai ni ko ma da farko ban so Yallaɓai ya saka su ba sai bayan sun fara girma sai na ga sun yi ma wajen aiki." Wani kallo ta yi min ta cikin likabinta da ta saki kafin ta ce"To gidan ki ne? Da sai kin zaɓi abin da zai saka ma gidan shi? Dariya na yi kafin na ce" Gidana ne mana Anty Bahijja, ko kwatance za a yi gidan Sadiya za a ce ko Maman su Jidda, kamar yadda kema a ke kwatancen gidan mijin ki da gidan Malama Bahijja." Kallona ta yi ido cikin ido ni ko sai na waske ina dariya. Sai ta bige da yin mirmishi kafin ta ce"kin samu dai kan Yallaɓai ta bakin ki kina yadda kika ga dama, to tunda ya yi miki gida saura mota ko? Ina riƙe baki na ce"Ni Sadiya? Ai ko kuɗin ya samu kuka ji zai siya mino mota hana shi za ku yi Anty Bahijja" Kai tsaye Ta ce"Tabbas. Gwara ya yi aure shima ya tara zura'a kar ki manta a gidasu mata huɗu cif ne da kimanin ƴaƴa 21 ban da waɗanda suka rasu." Ni ko da gayya na ce"Allah ya bashi kuɗin da zai wadatamu. Sannan sai ya yo auran miye a ciki? Anty Bahijja ta san halina ko Hajiya Maimuna ba na raga mawa, in suka faɗa min cuta zan faɗa musu mutuwa, duk da suna yayyen mijina, saboda suna da ƙananun maganganu sannan sun sakama rayuwata ido, a wasa ne za su yi ta faɗa minI magana > Janaftybaby: Nima ko a wasa na ke maida musu martani. Anty Zuwaira ce kaɗai ba haka a tsakanin mu saboda ita tana kama girmanta, da yake yar boko ce ga isa da gadara ba ta da ma lokacin tsayawa ƙananun maganganu. Har makaranta private nata na kanta gare ta, sannan ita ma ta kai matsayin Principal a wata makaranta ƴan mata ta cikin gari, sannan uwa uba mijinta a Mininsty of education reshen jihar kano ya ke aiki. Ban bar jikin get ba sai da Anty Bahijja ta shiga motar ta ta tafi, ina ɗaga mata hannu bayan na ce ta gaida su Suhailat, sannan na rufe get ɗin na koma cikin gida a falon da muka zauna na koma na sake zama. Duk a cikin maganganun Anty Bahijja magana ɗaya ta fi tsayamin a rai. Wai da ta ce ni na tsaida haihuwa da kaina, tuni na ji kaina ya fara sarawa abin nan mai ɗaci ya tokaremin a cikin kirjina ya kasa wucewa, wani tuƙiƙi kawai na ke ji kamar zan shiɗe. Har yau na kasa aminta da ba Yusuf ba ne ya je ya kwance min zani a kasuwa a gaban ƴan'uwan shi ba, tunda ya na da wani hali na faɗi ba a tambayeka ba, sai sai Ma'u ita ce abin zargina na biyu saboda tana auran yaron mai bi ma Mijin Anty Bahijja ma'ana suna aure a dangi ɗaya duk wasu maganganu da suke samu a kaina ta bakin Anty Bahijja ne, ko sunan Sadiya yar laushi da ke bakinta ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba daga baƙin Ma'u ne. Wannan yarinyar tun zuwanta gidanmu na san annoba ya zo cikin zuru'armu, idanuwan kowa ya rufe sun kasa gane tsabar makircin Ma'u da ta yi gadon shi wajen uwarta Baaba Asiya ta tsotsa a nono, ban san ina hawaye ba sai da na ji danshin saman kumatuna. Baƙin ciki ya cika min zuciya, me ya sa mutane suke kasa gane wani abu. Mace da Namiji waɗanda ke zaune ƙarkashin inuwa ɗaya ta ma'aurata tsakaninsu sai Allah, ba za ka ji bangare ɗaya ka yankema bangare ɗaya hukunci ba saboda Ubangiji ne kaɗai ya san mai ya ke faruwa tsakaninsu. Ƴan'uwan Yusuf suna ganin kamar komai na ke da shi sanadin ɗan'uwansu na samu Allah na tuba ba kyau tone tone in har da abin da nake dashi ya zauna a hannuna da yanzu na wuce matsayin da nake a yanzu, sun manta a yadda na auri ɗan'uwansu bashi da komai sai kwalin Degree da Masters sun manta gwagwarmayan da muka shafe shekaru sama da goma muna yi tare dashi rana tsaka saboda ya ɗan samu rufin asiri har ana tunanin ya ba ni duniya ina kwance a gida ina hutawa. Hawayena na share ina jan ƙaramin tsaki, ni ba domin Yallaɓai ya hana ni aiki ba da tuni ba su ganni ina zaman gidan ba, amman in har ya biyani kuɗina da nake bin shi ina nan da tunanin buɗe shagon Saloon kamar yadda na ke buri. Suna alfahari da wannan gidan su a tunanim kamar ya gama mini komai tunda ya gina min wannan gidan sun manta tsawon shekarun da na kwashe ina zaman haya. Maganar auran sa ba ta gaba na ta lafiyata na ke, na riga na shafa faɗama Yallaɓai cewa ba zan taɓa baƙin ciki domin zai ƙara aure ba amman ya sani kafin ya yi tunanin ƙara aure ya yi tunanin mu ya wadatamu da komai na rayuwa da ni da ƴaƴansa ba kuma mu ba mu wadatatu ba, ya je ya ɗauko mata ta zo ita a wahale mu a wahale. Jikina ya yi sanyin da na ƙasa tashi daga kan kujeran da nake zaune. Yallaɓai na kira domin na tuna masa maganar da muka yi na komawata ganin Gynea Asibitin ABU SHIKA. Ya sake kiran Uncle Abba mu ji yadda suka yi da wani abokin shi da ya ce zai kira a can Zaria zai taimaka mini. Amman ban same shi ba daman wani lokacin wajajen office ɗin sa ba Network a yi ta neman wayarsa ba a samu. A shekarun baya wani babban asibitin kuɗi ma'ana private Hospital na yi ta wahala da jelangen zuwa ba wani cigaba sai cin uban kuɗi sai aka bani shawara na koma babban asibiti ko Aminu kano ko ABU Shika da ke Zariya. Yallaɓai ya so na zaɓi Aminu kano, ban san me ya sa tunani na ya fi karkata da gwara na fara ganin likita a Asibitin Shika ba. Shi kuma daman Yallaɓai ya na girmama ra'ayina da buƙatuna shi ya sa bai hana ni ba. > Janaftybaby: Daga nan sai na sake buɗe data Group ɗin mu na BUK ya fara ɗaukan Hankalina saboda na ga ana ta massages da yawa kuma ni dai nasan tun da muka gama makaranta ba wani mgana ake yi sosai ba. In magana ta yi yawa to ɗayan biyu ne ko rasuwa ko an samu ƙaruwan aure ko na haihuwa. Ina shiga ko sai na ga Hauwa Jamilu ce ta haihu ƴ'a mace, ƙawarta Samira Aliyu ne ma ta tura hoton Baby da sanarwan haihuwan, na ƙurama hoton Baby ido mai kyau da ita. Ina son haihuwa ina son na ƙara haihuwa har a cikin raina, ko a ina naga an yi haihuwa sai na ji dama ni ce ko da ace daga shi in na yi ba zan ƙara haihuwan ba. Tagging na yi sai na yi mata barka a ƙasa kuma nace zan kira wayar ita Hauwan, duk da ban da wata ƙawa sanda muka yi BUK amman kuma ina gaisawa da mutane. Daga baya ma bayan mun gama makaranta na fi zumunci tun da in aka yi rashi ko ƙaruwa ko ban je na kan kira waya in kuma za a haɗa gudummuwa na kan tura nawa. Ina yin maganar Samira na Online ta yi min Reply. "Amin Amin. S Yashe ku kam dai kun gama ko? Sai na ba ta amsa da cewa" Mun gama me Samira Aliyu? "Haihuwan mana, kin daɗe fa ba ki ƙara haihuwa ba ina jin" Emojin mirmishi na tura mata ban yi magana ba. Ina gani Maijidda Bala, ta yi tagging ɗin maganar Samira da cewa" Ƴan boko ne matar Injiniya guda ko matar Yallaɓai zan ce? Sai da na yi dariyan Sarari saboda ko username ɗina Sadiyar Yallaɓai ce a rubuce. Kuma Maijidda Bala anguwanmu ɗaya, ta san gidanmu na san na su , duk halina na rashin son sakewa da mutane amman Maijidda na zuwa gidanmu saboda Rahila, to daman duk wanda ya zo gidanmu saboda Rahila ce ko Ma'u su ne masu jama'a. Ba zan taɓa mantawa da maganar Mama tun muna ƴan mata ta sha ce mini" Ke kam Sadiya da wuya ki ta shi aure ki ga jama'a. A yi mutum ba shi da son shiga jama' a kwata kwata." A lokacin dariya na kan yi kafin na ce"Shike nan sai ke da Gwaggo ku ci min ƙawayen amarya." Allah Sarki Mama Allah ya sa kina aljannah. Ban biye ma mangaganunsu ba na sauka saboda kar na manta nan take na kira Hauwa na yi mata barka, har tana mini tsiyan ni na gama na ji daɗi na. Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba. Saboda ko me zan ce ba za ta gane ba sai da na ji tana faɗin"Nima daga wannan na faɗa ma Baban Afnan na gama wallahi. Allura zan je a yi min na shekara biyar." Da sauri na ce"Kul ɗin ki Hauwa. Karki yi wannan gangancin, in kika tsaida haihuwa na shekara biyar to za ki yi ta nadama har na shekaru ashirin ba ki daina ba. Saboda lokacin da kike son ki ƙara haihuwan ba za ki samu wannan damar ba." Na faɗa ina jin raɗadin abin a cikin raina Hauwa ko cewa ta yi" Ko Sadiya? Sai kawai na rausayar dakai kamar tana ganina kafin na ce" Ku yi na gargajiya ko na musulunci Hauwa. Saboda haka ina gargaɗin ki in ba so kike yi ki ƙare a zuwa gaban Gynea ba." Hauwa na jin haka sai ta ce to shike nan za ta yi magana da Daddyn Afnan duk yadda ta so na yi mata wata mgana ban yi ba saboda ba close na ke da ita ba, rayuwa ai darasi ne amman da zan buɗe mata cikina sai ta ji tunanin da ke cikin ranta ya fita ba domin komai ba sai tsira daga faɗawa irin halin da ni na faɗa. Ina nan zaune ina ɗan duba wayata amman ban shiga group ɗin gidanmu ba sannan ban shiga na ɗaiɗaikun su da suka yi min magana ta private ba saboda nasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Fita na yi zuwa Instergram ina kallon kwalliya domin ni Allah ya yi da son abu fashion. Domin har certificate gare ni akam koyon kwalliya ba ma ɗaya ba sannan ina da na koyon saloon da gyaran jiki, shi ya sa wayata cike suke da ire iren su. Ban san na ɗau lokaci haka ba sai da Saude ta zo ta ce mini ta gama da ciki za ta gyara falo sannan na ba ta waje, bayan na ce in ta gama ta ɗora min ruwa a gas ta dafa taliya fara tunda ina da miya a firiza. Bedroom na koma na yi zama ma ina ta kallon Videos ɗin yadda ake kwalliya da na ɗaurin ɗan kwalli a istergram daman ni can na fi auki, kiran sallar azahar ya tada ni na ijiye wayar na je na yi sallah lokacin har Saude ta tsane taliyan da na ce ta dafa guda biyu, ni na karɓe ta na ce ta shiga ɗakin su Jidda ta yi sallah ni kuma sai na fito da miyar na > Janaftybaby: ɗumama. Na saka ma kaina sauran kuma na bar shi a cooler. Ƙaramin falo na koma na kunna kallo sai na sauya tasha zuwa Mb2 na iske a wani film mai kyau sai na barshi, filet ɗin abincin na kan jikina ni kuma na miƙe kafata saman cafet ina cin abinci ina kallo har Saude ta fito sai na ce ta ɗauko kofin ta tsiyayo mini ruwa a Dispenser. Sai ta kawo mini sannan na kalle ta ina faɗin" Ki ɗiba abinci ki ci sai ki zo ki wuce gida kin san kina da makaranta." Da toh ta amsa min ta wuce kitchen ta diɓo taliyan ta zo ta zauna a kasa ta na ci, ba hira muke yi ba sai ni ce ma ke mata tambayoyi. "Babanku ya dawo? Sai ta ce min a'a sai na girgiza kai kawai, lagos ya ke zuwa kwadago in ya tafi sai ya yi rabin shekara bai dawo ba ya bar iyalansa da wahala. Ni na riga ta tashi, na tafi da filet ɗin hannuna da kofi zuwa kitchen na saka a sink ɗin wanke wanke. Leda na samu na buɗe drower ɗin cabinet ɗin kitchen ɗin na auna mata shinkafa tiya biyu sai taliya da maracaroni da na diɓar mata tunda nima abincin nawa ya yi ƙasa. Bedroom na koma na ɗauko mata 2k daga cikin jakata sannan na dawo falon lokacin ta gama cin abincin sai na ce ta wanke hannu ta zo. Ina zaune ta zo ta zauna gabana ta na faɗin" Ga ni Anty" Ledan na tura mata gabanta lokaci ɗaya ina mika mata kuɗin hannuna ina faɗin"Ki kaima mamanku kin ji ko? Ta karɓa tana faɗin"An gode Allah ya saka da alheri." Na amsa da Amin ina faɗin"Ki yi sauri ki hau mashin ne biyu ta kusa." Sai ta amsa minI, tare muka fita saboda zan rufe gida tana fita na maida gidan na rufe na dawo falo ina kallo, film ɗin horror ne ya ɗauki hankalina sai da aka gama shi amman za a yi part 2 ɗin shi. Uku na rana na koma ɗaki na kwanta sai barci ban ta shi ba sai huɗu da rabi, sai na yi alwala na yi sallah na ga tunda huɗu ta wuce sai kawai na ce bari na yi azkar ɗina. Ni kaɗai a gida kamar mayya na matsu su Jidda su dawo sai shidda suka dawo saboda biyar da rabi ake tashin su kafin ya je ya ɗauko su shidda ta yi tunda makaranta boko da isalamiya ne. Dawowarsu ne ya sa na fito falo suna bani labaran makaranta suna cin abincin, Baby ce mai surutun Jidda irin Babanta ne tana da sanyi sosai ba kamar Baby ba. Suna gama cin abinci suka sauya kaya zuwa na gida. Unform ɗin Jidda ta ce za ta wanke na ce yamma ta yi, tunda suna da guda biyu ta bari zan wanke musu gobe da safe Tare muka yi sallar mangariba, muna idarwa a ƙaramin falo muka fara karatu. Jidda na suratul maryam ne Babby kuma tana ƙasa ƙasa sai da suka biya na jiya na ƙara musu sannan muka yi azkar tare. Muna gamawa sai muka miƙe muka yi isha'i tunda an kira. Muna idarwa na bar su a falo suna kallo ni kuma na shiga kitchen na dafa ma Yallaɓai tea daman na dafa masa farar shinkafa tunda shi taliya ba ta dame shi ba, ina gamawa na shiga wanka ina wankan ma na ji shigowar motar Yallaɓai. A gurguje na shirya cikin riga da wando, wandon plazo ne mai buɗewa ta kasa. Rigar kuma Top ce mai wuya ta kama jikina sai na gyara gashin kaina na tufke a tsakiya na saka wata hula mai love a saman kaina kalan pick . Tsakiya babu komai, kwalliya na yi kamar yadda na saba na saka jan baki na kamar yadda na saba. Na ji ƙaran bude ƙofa ganin bai shigo ba ya sa na san ya shiga tiolet ne. Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ina zaune a gefen gado ina bin shi da mirmishi bayan na amsa sallamarsa. Hannuwana ya buɗe minI na tashi da sauri na faɗa masa ya rumgumeni. Nima sai na ƙamƙamesa ina fadin"Barka da dawowa Yallaɓai na." Ya na shinshina ƙamshin humran dake jikina ƙasa ƙasa ya ce" Uhm. I like it." Ɗagowa na yi muna kallon juna kafin na ce'Me? Yana mini wani kallo ya ce"ƙamshin ki mana." Far na yi masa da ido kafin na ce"All is yours" Kumatuna ya shafa kafin ya ce" Allah ya yi miki albarka." Na amsa da Amin. Ruwan wanka na ce zan haɗa masa ya yi wanka sai ya ci abinci. Shi kuma sai ya ce"E. sai mu ta fi wajen kiran Alhaji ba" > Janaftybaby: Gyaɗa masa kai na yi ba tare da na yi mgana ba. Sanda ya shiga wanka ni kuma na je haɗa masa abinci bayan ya fito ya sauya kaya zuwa wani yadi riga da wando ɗinkin zamani. Falon farko mu ka je saman dining ya ci abinci su Jidda kuma suna ƙaramin falo Bayan mun gama ba mu tsaya ɓata lokaci ba ya ce na saho hijabi mu ta fi, daman na fito da Hijabin jalbab mai ruwan ƙasa har ƙasa sai na saka takalmina iri ɗaya da wanda Yallaɓai ya saka daman tare ya siya mana. Na ce musu Jidda su kula da gida za mu je gidansu Gwaggo mu dawo. Baby taa saka rigiman sai ta je Babanta ya tsaya yana lallashinta da zai siyo mata ice cream sannan ta yarda na ce in za su kwanta su kashe komai za mu fita da key da toh Jidda ta amsa da yi mana a dawo lafiya. Sai da muka fita da motar sannan Yusuf ya koma ya rufe get ɗin Sannan ya dawo muka kama hanya mun ɗauki hanya kenan na kalle shi kafin na ce" Na gwada kiran ka yau ban same ka ba." Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Nima na kira ki ban same ki ba." Sai ya kalleni kafin ya ce"Me ya faru? Kai tsaye na ce"Kan mganar komawata Abu shika ne, Uncle Abba bai ƙara kiran ka ba? Sai a lokacin ya tuna ya ce"Kash! Ya kirani amman shaf na manta ba mu yi mganar ba. Amman bari yanzu zan kira shi." Ni ya miƙa ma wayar ya ce na kira shi, Kawu Abba daman ya saka masa da na kira sai na saka a speaker har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. "Kawu barka da dare." Shuru bai yi mgana ba. "Uncle Abba barka da dare" Wata murya a dakushe ya ce"Yusuf in ma bashi kake nema na kuɗi ba ni dashi wallahi. Wanda ma nake binka EFCC ne za su ƙwatar mini haƙƙina." Daga ni har Yusuf sai da muka kyalƙyace da dariya. Ni ce na ce"Haba Uncle Abba ba amana yanzu sai ka kai mini Yallaɓai EFCC? Jin muryata ya sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce" Sadiya? daman kina kusa? Na amsa masa da e, sannan muka gaisa dashi. Shi kuma sai ya bige da faɗin"Yallaɓan nan naki ya ci bashina kamar gadon ubansa yaƙi biyana. Gwara babbar hukuma ta shiga ciki, in na je gaban manya sai a saka sanayya a ciki gwara a kame shi ko amansu ne sai ya yi." Yusuf na dariya ya ce" Na ci fa halas, abin da ya yi Nene shi ya yi ka fa Kawu Abba." Kai tsye ya ce"Ko? To ai ko ita Nenen ta ci kuɗina sai ta biyani ballatana kai." Ni dai ina ta dariya ganin sun sarƙe da gaddama shi Yusuf ya na faɗin ya ci halas kawu na fadin shi ba ƙanin Uban shi ba ne na uwarsa ne bashi da gadonsa. Zungurin kafar Yallaɓai na yi sannan ya yi gyaran murya yana fadin"Sadiya ta ce a yi maka tuni ka yi mganar da Dr Fadil ɗin? Kawu Abba dagacan bangaren ya ce"Kash na manta. Amman bari na kira shi na ji yadda muka yi zan kira ka." Sai ya kashe wayar, dai dai Yusuf na faɗin" Kina ganin komawarki can da ganin likitan ba damuwa? Sai na gyaɗa mai kai ina fadin"E, ba matsala can ma ƙwararru ne. Tunda na yi ta nan ban dace shi ne aka ban shawara na gwada can ɗin." Sai ya jinjina kai, bai yi magana ba sai ni ce na cigaba da faɗin"In ina da appoitment na ganin likita tun ana gobe zan je zariya na sauka gidan Ya Hamza bayan na gama ganin likitan sai na dawo." Kai tsaye ya ce"E hakan ma ya yi. Allah ya sa a dace." Na amsa masa da Amin. Mun shiga anguwan ɗorayi kawu Abba ya sake kira ya ce sun yi mgana da abokin nashi Dr Fadil shi likita ne a bangaren zuciya amman ya ce ya yi ma wata Dr Nayami mgana musulma ce amman ba bahaushiya ba ce, ya ɗan yi mata brief na matsalata ta ce zuwa sati mai zuwa za ta iya bani appiotment in har ya tabbata zai kira Kawun ya sanar dashi. Jin haka ya sa sai na ji daɗi kamar na je ta shaida mini zan iya sake samun wani cikin haka na riƙa ji. Daidai lokacin Yallaɓai na gyara parking a kofar gidanmu da ke anguwan Ɗorayi. KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️03* Gidanmu na nan a farko layin shiga anguwar Ɗorayi. Yanayin fasalin gidan babba ne sannan tun daga waje za ka fahimci tsarin gidan na tsohon ɗan boko ne. Domin Alhajinmu kafin ya yi Ritire(Ritaya) sai da ya riƙe mukamin babban darakta na kamfanin wuta na jihar kano(KEDCO). Bayan kasancewarsa manomi. Kuma gidanmu na da ga cikin rukunun gidajen da suka daɗe a anguwar tun da sama da shekara ashirin duk da ko mu kanmu muna da wayau lokacin da muka dawo gidan tun a wancan lokacin zamani na kwance. Sai dai yanzu lokaci bayan lokaci yana samun ƴan gyare gyare da kwaskwarima daga su Yaya Hamza. Ni na fara fitowa daga Motar. Yallaɓai na kuma an kira wayarsa ya tsaya a mota ya na mgana. Kofar gidan namu tar da hasken wuta gabaɗaya ma anguwa akwai hasken ƙwakwayen da suke kofar gidajen wasu mutane dake cikin rukunin anguwan ta Ɗorayi. Gidanmu na ke kallo ina tuna wasu shuɗaɗɗun al'amura da suka faru damu a cikin gidan masu daɗi da akasin su. Yallaɓai ne ya katse min tunani da cewa" Kin ga ko na manta ɗazu musabahu ya zo offishina ya bani saƙo ya ce in ji Yaya Muntari mijin Rahila." Sai a lokacin na ɗago ina kallonsa ya fito daga mota ya na nuna min kullin abu a baƙar leda, yadda ya ga na taɓe baki ya sa ya san tabban nasan da saƙon. "Bar shi a motan kawai." Bai yi musu ba sai ya koma cikin motar, ina hangensa daga waje ya buɗe akwatin motar ya jefa sannan ya fito yana ƙoƙarin rufe motar hasken wata mota da ke tunkaromu ta kashe mana ido daga ni har shi sai da muka saka hannuwammu muka kare fuskokin mu dashi. "Kai. Waye wannan da ba zai rage filita tunda ya shigo cikin anguwa ba." Na kasa magana ne saboda mamakin ganin motar ba wucewa ta yi ba, kusa damu itama ta gyara parking, tun kafin ma na ciki su fito na shaida su waye tun daga cikin motar akwai hasken fitila. "Ma'u ce.." Haka na faɗa a cikin raina dai dai san da ta buɗe murfin mota ta fito shima mijinta ya fito daga can bangaren direba. "Alhaji Mustapha ne, da Ma'u ashe." Yusuf ya faɗa ya na sakin mirmishi, na kalle shi wani abu ya yi mini tsaye a zuciyata. Lalle Alhajinmu wato zaman yau bayan ni da Ma'u har da gayyar mazajen mu kenan? Kara haɗe rai na yi, ganin Ma'u na nufoni shi kuma Yusuf ya nufi Alhaji Mustaphan shi adole ya ga ɗan'uwan mijin yayarsa. Ƙaramin tsaki na ja dai dai lokacin da Ma'u ta ƙariso kusa da ni ta na faɗin"Sadiya kema Alhajinmu ya kira ku ne ke da Injiniya? Ta faɗa lokaci ɗaya ta na ɗora hannunta saman kafaɗata. Sai na ji kamar ta ɗora min cuta da sauri na kauce ina yi mata wani irin kallon ke ki kiyayeni. Ita kuma ta na bi na da wannan munafukin mirmishin nata na yaudara. Ƙoƙarin sake matsowa kusa da ni take tana yi min mirmishinta da ba alheri a cikin sa. Tsaki na ja mai karfi na juyawa na fara tafiya zuwa ƙofar da za ta sada ni da cikin gidanmu na ji muryan Ma'u da ɗan karfi ta na faɗin"Haba Sadiya. Ke shike nan abu ba ya wucewa a wajen ki? Na yi ta ba ki haƙuri fa? Sai da na kai kofar gidan sai na juya ina kallonta sai na ga har su Yusuf ma sun dawo da hankalunsu kan mu, dariyan gefen ba ki na yi. Ni ai sai dai na rubuta littafi guda akan maƙircin Ma'u daman ta yi ne domin hankulansu ya dawo kan mu, shigewata cikin gida na yi ina ji Yusuf na kiran sunana na yi masa banza na yi shigewata na bar su nan ƙofar gida. Dogon korido ne mai ɗauke da ɗakuna uku na waje, biyu suna rufe ne sai guda ɗaya ne a buɗe. A raina na ce kila Datti ya zo gida ko kuma an yi baƙin maza daga Yashe ko Yan tumaki. Ban gama mamaki ba sai ga Datti ya fito daga cikin gida sai muka ci karo da juna. "Datti.." Na kira sunan shi, sai ya kalleni domin fitowarsa daman hankalinsa na kan wayar hannunsa. Daga shi sai baƙin wando da farar singileti. "Yaya Sadiya? A daran nan? Ya faɗa yana kallona, jiyo muryoyinsu Yusuf suna ƙokarin shigowa ya sa na raɓa ta gefensa na wuce, ina jin sa ya na tambaya ta. > Janaftybaby: "Ke kaɗai kika zo? Ina Yallaɓan da su Jidda? Ko juyowa ban yi na faɗa tsakar gidanmu da sallama. Gwaggo na Madafi na kuma nasan shayi ta ke dafama Alhajinmu da tun tasowarmu nasan ba ya iya barci sai ya sha wannan ruwan zafi. Ita ta amsa min sallamata tana kuma leƙowa muka ci karo da juna tsakar gidan tar yake da hasken gulop. "Maraba da Hajiya Dubu." Sai na sa ki mirmishi ina faɗin"Kai Gwaggo ni dai wannan tsohuwar ta mutu ba ta bar mini gadon komai ba sai na sunan ta." Gwaggo na dariya ta ce"Ka ji min ƴar nema. Ai ko ita ta bar miki gado tunda ta bar miki gadon suna mai daraja irin Halimatussadiya." Ya na iya?. Domin in dai Gwaggo ce ta riƙa sharhin sunan kenan da kawo tarihi. Gaisheta na yi cikin girmawa ta amsa ta na faɗin"Na gan ki ke kaɗai ina shi Yusufan? Na rausayar da kai kafin na ce"Ga shi nan shigowa." "Oh. To ina yaran suke? Ko can gida kuka baro su? Ban amsa mata tambayarta ba. Sai na bige da faɗin"Alhajinmu na ciki ne Gwaggo? Na faɗa ina kallon ƙofar falon shi da na hangi hasken wuta. "E. ya na ciki tun ɗazu ya dawo. Zaman jiran ku yake yi. Domin nima sai yanzu ya ke yi min taɗin kuna tafe ke da Ma'u" Ta na dire maganarta sai ga sallamar Ma'un ban tsaya ba ni kuma na kara sauri zuwa falon Alhajinmu. Da nesa kaɗan dashi ɗakin Gwaggo ne shima akwai hasken wuta daga cikin ɗakin, kusa da shi kuma ɗakin Mama ce a sakaye, daman in dai ba mu ne muka zo gida ba, ɗakin Mama yana yini a sakaye ne Ɗakin na kallah ta window ya yi duhu alamun an kashe hasken ɗakin gabaɗaya ƙwallah suka taho min na yi saurin shanyewa amman a fili sai da na furta" Allah ya yi miki Rahama Mama." Lokaci ɗaya na cire takalmina akofar ɗakin Alhajinmu na shiga da sallama a bakina. Alhaji Sulaiman Abubakar Yashe(Alhajinmu) na zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu cikin jerin kujerun da suka yi ma falon kwanya. Falon da na girma sosai shi ya sa sai kujerun suka zama a can tsakiya. Alhajinmu ba tsoho ba ne, ko na ce yanayin jikinsa na ɓoye shekarunsa. Ya mori jiki saboda bashi da kiɓa tun zamanin samartakansa har kuma girmansa. Dattijo ne wankan tarwaɗa, mai matsaikacin faɗin fuska da furfura ta gama zagayewa. A shekarunsa zai iya haura 65 amman kuma ba zai ga za 67 ba. Cikin yanayin maganarsa da zafin murya irin ta Alhajinmu ya amsa min sallamata. "Amin wa'alaikis salam. Dubu ce tafe? Sai da na ƙarisa gabansa na zauna ina faɗin"Ni ce Alhajinmu barka da dare." Yana yar dariyansu ta manya ya ce"Barkan mu dai. Yana ganki ne kaɗai ko Yusufan ya na waje ne? Ko kafin na samu zarafin magana Ma'u ta yo sallama ta shigo bayan ta kuma mijinta ne Alhaji mustapha da Yallaɓaina Injiniya Yusuf. Itama gaban Alhajin ta zo ta zube ta na gaishe shi, ni dai na matsa can gefe na jingina da kujera suma su Yusuf nan kasan cafet ɗin da ya malale ɗakin suka samu mazaunin zama cikin girmamawa suna gaishe da Alhajinmu ya amsa cikin sakewa da dattako, sai ya karkata kansu yana tambayan su aikinsu da sauran harkoki. Ni kuma kaina sai na dukar da kaina ina duba wayata ganin har tara na dare ta gota da kaɗan. Ita kuma Ma'u sai ta tankwashe kafa kamar mutuniyar kirki kanta na ƙasa ban san abin da ta ke yi ba. Shigowar Gwaggo ɗakin dauke da shayin Alhaji ya katse hiran ta su, ta miƙa masa a wani ƙaramin mug ya karɓa ya na faɗin"Na gode Maimuna. Allah ya yi albarka" Ta amsa da Amin. Sannan ta juya suna gaisawa da su Yusuf tunda da suka shigo ta ce su shiga itama ga ta nan zuwa. "Ma'u ya gida ya yara? Ina su Alhaji karami? Gwaggo ta faɗa ta na kallon Ma'u. Ita kuma sai ta ɗago ta na faɗin" Lafiyan su lau Gwaggo na baro su gida tare da Zainab" Gwaggo ba ta yi shuru ba sai ta kara cewa" Ya gajiyan ku? Kun sha suna. ke ce kawai daman da Sadiya ba ku biyo ta nan ba ranar sunan" Gum na yi da bakina saboda daman in dai Ma'u na magana ba na saka baki, can na ji ta na ce ma Gwaggo wai mun yi dare ne shi ya sa ba mu biyo ta gidan ba. Shi kuma Alhajinmu sai da ya yi rabin da shan shayinsa sannan ya kalli su Yusuf ya na faɗin"Ban yi muku ta yi ba, ko Maimuna ta haɗa muku shayin ne? > Janaftybaby: Alhaji Mustapha ne ya yi saurin cewa" Mun gode Alhaji." Yusuf dai bai yi magana ba saboda na ji an kira wayarsa bai ɗauka ba ina jin sai ya sakata a silet. Ficewa Gwaggo ta yi daga Falon zuwa ɗakinta. Ta bar mu daga mu sai Alhajinmu sai da ya gama shan shayinsa sannan ya kalleni yana faɗin"Dubu kai kofin can madafi" Ya faɗa yana mika min mug ɗin hannun shi da ya gama shan tea, sai na miƙe da sauri na karɓa na fita zuwa tsakar gida na tura kofar madafin tun da har Gwaggo ta sakaya ban ijiye ba sai na diɓi ruwa a katon botoki mai murfin ɗin dake cikin madafin na tara a sink na wanke shi, tunda madafin gidanmu ya daɗe da komawa na zamani na kife kofin saman cabinet ɗin kitchen ɗin sannan na fito na sakaya shi kamar yadda na ga Gwaggo ta yi. In da na tashi nan na koma na zauna. Sai sannan Alhajimu ya gyara zama ya na sanye da jallabiya mai ruwan madara kansa ba Hula sai furfuran da suka masa kwanya daga kansa suwa gemunsa da sajensa. "Ma sha Allah, na ji daɗin yadda bayan na kira ku kuka amsa kirana. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya." Muka amsa da Amin gabaɗayanmu. Alhajinmu ya kalleni sai ya kira sunana da sai irin haka mgana mai muhimmanci ya ke kiran sunana bayan Dubun da yan kirani. "Halima.." Sai na ɗago na kalle shi lokaci ɗaya ina mai amsawa. "Na'am Alhajinmu." Sai ya karkata kan Ma'u itama ya kira sunanta. "Asma'u.." Itama ta amsa da na'am Alhajinmu Sai ya cigaba da faɗin" Kusan dalilin da ya sa na ce ina son ganin ku wannan karon tare da mazajen ku? Dukkanmu muka girgizanmu kanmu kafin mu haɗa baki wajen faɗin"A'a Alhajinmu." Kai ya gyaɗa kai kafin ya ce"To ba saboda komai ba ne sai dalilin bayan ni kuna da wasu shugabbanin da in kuka yi ba dai dai ba, za su iya yi muku faɗa akan ku gyara kamar yadda ni zan yi muku. Mazajen ku su ne alhakin duka rayuwarku da tarbiyansu yake hannunsu bayan na aura musu ku, shi ya sa wannan karon ganin wannan rigimar da sheɗan ya ba da gudummuwa wajen gina ta a tsakaninku da ta ƙi ci ta ƙi karewa na yi tunanin saka mazajen ku a ciki, saboda ba na so na faɗi na mutu a zaman makokina ke Sadiya da ke Asma'u a ce bakwa yi ma juna mgana akan abin da bai kai ya kawo ba." Sai ya dakata ya na nazarin mu, dukkanmu kan mu na ƙasa ba wacce ma ta ɗago. Sai ya karkata hankalinshi zuwa ga mazajen mu. "Yusufa. Cikin ladabi ya ce"Na'am Alhaji" "Mustapha." Shima cikin ladabi ya amsa da Na'am Alhaji. Sai Alhajnmu ya gyara zama ya na faɗin"Ban sani ba ko kun taɓa sanin tsakanin matayen ku ba a ga maciji? Ma'ana ba sa haɗuwa waje ɗaya su yi rabuwan lafiya? Wataƙila za ku iya fahimtar ba sa shiri da juna amman na san ba su taɓa zama sun warware muku lamarin yadda za ku fahimta ba. Wannan karon Alhaji Mustapha ya fara faɗin" Haka ne Alhaji. Ban dai san me ya ke haɗa su ba amman Sadiya ba ta zuwa gidana sannan ko haɗuwa muka yi ni da ita in dai ba ni na yi mata mgana ba. Ba za ta yi mini ba, na taɓa tambayan Ma'u ko akwai wani abu a tsakaninta da Sadiya ne amman ba ta ce komai ba" Ya karishe faɗa yana kallona, nima ko na ɗago muka kalli juna na kauda kaina domin ba ƙarya ya faɗa ba mun sha haɗuwa da shi gidan Anty Bahijja sai na yi kamar ban gan shi ba in har bashi ya yi mini mgana ba. "Kai fa Yusufa? Ka taɓa fahimtar wani abu? Cikin girmamawa ya ce"E. Na fahimci ba shiri tsakaninsu. Amman na ɗauka faɗa ne kawai na ƴan'uwa ba mai tsananin da zai haifar da matsala ba ne Alhaji." Alhajinmu sai ya sauke numfashi kafin ya ce"Kowa ma haka ya ɗauka daga farko farko. Amman suna ƙara girma lamarin na su na ci gaba, tun suna yara har suka girma na aurar da su gare ku, suka hayayyafa suka zama iyaye sun tashi daga yara sun koma uwaye waɗanda ba zan ce ba su san ciwon kansu ba. Sun sa ni tunda Tarbiya ne ma a ƙarƙashin ikon su, daga lokacin ne na fara fahimtar lamarin ya wuce tunanin zai tsaya anan ina tsoron kada su mutu su bar ƴaƴansu cikin muguwar gaban da sheɗan ya kulla a tsakanin su." > Janaftybaby: Dalon sai ya yi shuru, Alhajinmu kuma bayan ya yi shuru na wani lokaci kafin ya cigaba da faɗin"Ba yau ne na saba sulhu tsakanin Halima da Asma'u ba, tun yan'uwansu na yi musu ban sani ba har ya fi karfinsu suka dangana da ni, na yi nasihan da ban baki sai sun ce sun bari amman ba a daɗewa sai an zo an faɗa mini sun haɗu kuma sun yi faɗa. Wannan zaman saboda dalilin faɗan ne da suka haɗu shekaranjiya a gidan sunan ƴar Rahila. Murja ta zo har gida nan ta na faɗa mini a gaban mutane ke Halima kika yi ta ma yar uwanki ɗiban albarka, ita kuma an ce Asma'u haƙuri take ba ma Sadiya amman dai sun sanar dani faɗan dalilin ita ƙawar Asma'un ce da ta je sunan ƴar Rahilan" Yusuf ya ce"Subhanallah" Shi kuma Alhaji Mustpha ya kaɗa kai kafin ya ce"Asha. Abu bai yi daɗi ba." Ni ko kaina na ƙasa a raina ina mamakin Yaya Murja, ko miye riban ta na zuwa ta karantama Alhaji komai? "Wannan dalilin ya sa na ce zan saka ku a ciki. Gani ga ku zan tambayesu ɗaya bayan ɗaya menene haƙikanin matsalansu da ko da yaushe suka haɗu sai sun yi faɗa? Ko sun manta su ƴan uwan juna ne dangi ɗaya? Ko ke Sadiya kin manta matsayin Asma'u a gare ki ne? Ko ke Asma'u kin manta matsayin Sadiya a gare ki ne? Ya ƙarishe faɗa ya na bin mu da kallo, kowaccen mu ta kasa ɗagowa saboda nauyin idanuwan Alhaji a kan mu. "Ke Sadiya ke ce Babba da ke zan fara. Ɗago ki kalle ni" Ba ni da mafita illa ɗago kaina ina kallon Alhajinmu cikin muryansa a kaushashe da ɓacin rai ya ce"Halima na san halin ki, kina da tsiwa da mgana sannan ke ce daman ko faɗa aka yi dake ko an yi sulhu ba kya hakura ki yi ta gaba saboda daman gaba ba ta yi miki wahala. Ki faɗa mini gani ga Asma'u da mijinki wani irin abu ne Ma'u take yi da ba ki so? Ki faɗa mana sai ta ji ta ba ƙi hakuri ta kuma ɗauki alkwarin za ta daina yi miki saboda ku samu zaman lafiya" Shuru na yi na wani lokaci kafin na ce"Alhajinmu ba fa ni kaɗai na tsani Ma'u ba. Itama ta tsane ni tun zuwanta gidan nan ba ta sona nima ba zan maka ƙarya ba ba na sonta Alhaji. In kuma ana son a samu zaman lafiya to Ma'u ta daina bin hanyata ni daman ba ta gabana domin na fi ƙarfinta Alhajinmu ka raba tsakanina da Ma'u don girman Allah." Na karishe faɗa har ina haɗa hannu alamun roƙo, gabaɗaya ni suke kallo har Ma'u sai kawai na ga ta fashe da kuka, ban ko razana ba domin kaɗan daga cikin makircin Ma'u kenan. Yusuf kuma ni ya ke kallona, saboda ya san halina ina da taurin kai, in na kuma ce na tsani abu to da gaske na ke yi ba na son shi. "Innalillahi ni ko Sadiya me na taɓa miki a rayuwa da kika tsane ni haka? Kai tsaye na ce" Ban sani ba. Ke za a tambaya abin da na yi miki kika bi kika addabi rayuwata kina yi mino bita da kulli a wajen iyayena da ƴan'uwana wannan bai isheki ba kin fara yi min ta bangaren dangina mijina wannan bai isheki ba sai kin je kina yamaɗiɗi da ni cewa planning na yi shi yasa har yanzu na ke neman haihuwa ido rufe ban samu ba, har wannan matsiyaciyar ƙawar na ki ta kalli tsabar ido na tana gaya mini mgana." Na ƙarishe faɗa cikin tsawa domin nima raina ya ɓaci. Tuna abin da ya faru da a gidan Rahila kaɗai kan haifar mini da ƙuncin zuciya. Daga Alhajinmu har su Yusuf shuru kawai suka yi suna kallon mu. Ma'u ta na kuka ƙaryan da ta saba na yaudaran mutane ta fara rantsuwa ta na faɗin" Wallahi tallahi in kin yarda dani Sadiya ban san a ina Shema'u ta ji wannan labarin kuma, a gabanki na yi mata mganar ban ji daɗin abin da ta yi ba, saboda haka ya sa ko yau ta zo gida ta na faman bani haƙuri ban saurareta ba. Har a waya tana ta kirana ban ɗauka ba domin na faɗa mata ba ke ta tozarta ba ni ta tozarta domin abin da ya yi ki shi ya yi ni Sadiya da ni da ke bamu da bambamci" Ta ƙarishe faɗa tana shesshekan kuka sai kuma ta kalli Alhaji tana cigaba da faɗin"Alhaji wallahi Allah ɗaya kenan ba ni da wani mugun nufi kan Sadiya. Ina son ta kamar yadda na ke kaunar yar uwata Zainab, ina son ta ƙwatankwacin yadda nake son su Rahila. > Janaftybaby: Amman ban san me ya sa Sadiya ta kasa fahimtata ba, Alhajinmu ko rashin fahimtar da ta faru a baya ta maganar aurena da Yaya Hamza tabbas raina ya ɓaci kuma na ji haushin Sadiya amman har ga Allah daga baya na cire abin a raina ban taɓa kallon Sadiya dashi ba. Ni ko me ya sa zan yi haka? Alhaji Sadiya ce ba ta sona ban kuma san me na yi mata ta tsane ni ba tana hulɗa da kowa Alhaji ban da ni in dai abu ya shafe ni Sadiya tsame hannunta ta ke yi a ciki ba ta zuwa gidana ni in na je wallahi ko bare Sadiya ba ta yi masu abin da ta ke yi mini, in muka haɗu a gida ko gidajen ƴan'uwa Alhaji ko na yi ma Sadiya magana ba ta yi mini ta yi ta gaba da ni. Na zauna ta yi ta tunanin abin da na yi ma Sadiya ta tsane ni amman na kasa ganewa, daga baya sai na fara tunanin ƙila saboda Alhaji ka ɗauke ni ka sanyani cikin Iyalanka ne, ita kuma Sadiya ba ta so wani daga waje ya raɓe ta, sai kuma daga baya na kwaɓi kaina da cewa ai ni ba bare ba ce Alhajinmu ni ma ƴarka ce kamar Sadiya" Ta faɗa har ta na riƙe kafar Alhaji, tana kuka, gabaɗaya na san ta gama cika zuciyar Alhaji da tausasa kalamanta. Ni ko a raina ban ji na yi nadama ba, kallonta na ke yi ina mamakinta har ta manta mganganun da ta gaya mini a lokacin da aka fasa auranta da Yaya Hamza? Har ta manta? "Tashi. Tashi Asma'u. Ke kam ba bare ba ce ke ƴa ce kamar Sadiya. Ta shi daina kuka kin ji bari kuka nan" Ya faɗa cikin sigan lallashi, Alhaji Mustapha har da mika mata wani farin hanky, ya na faɗin"Ki share hawayen ki Ma'u" Ba wanda ya fi baƙanta min rai irin Yusuf har da shi a masu ba ma Ma'u hakuri daman halinta ne ta shirya makirci a raja'a a kanta. Tsaki na ja mai ƙara kafin na ce" Ke dai Ma'u wallahi an yi baƙar munafuka kuma makira, ke wai kina kuka saboda ki zama abin yarda ni kuma na zama victim kamar ko yaushe ko? Har kin manta? Har kin manta maganar da kika faɗa mini lokacin da aka rushe maganar auran ki da Yaya Hamza? Na ce kin manta? To wallahi kamar yadda baki ƙaunata nima abada ba..' "HALIMA..." Alhajinmu ya katseni tare da kiran sunana a tsawa ce, ban kalle shi ba na cigaba da faɗin"Alhajinmu cewa ta yi fa sai ta rama abin na yi mata sai ta kun samini kwatankwacin baƙin cikin da na kunsa mata kuma.." "Na ce ya isa ko Halima? Ko so kike yi na saɓa miki? Alhaji ya faɗa ransa ɓace, sai na yi sansarai rai, ganin ya koma ya ba ma Ma'u haƙuri tana shessheƙan kuka. Baƙin ciki da ya tokare mini zuciya ya ta so mini ba kasafai na ke kuka kan abu ba amman daman Ma'u ta saba cin nasara a kaina akan kowa ko da yaushe ni ce victim ita kuma mai gaskiya. Ban san nima na fashe da kuka ba, sai kawai na miƙe zan fita daga falon ina faɗin" Shike nan ai daman ita mai gaskiya ce ita ce ba ta laifi ni ce fitananniya. Alhajinmu ni fa ƴar ka ce Ma'u fa? Bai kai kamar ni da ka haifa da gudan jinin ka ba." "Ke ke Sadiya ina za ki je? Alhajinmu ya fada saboda na juya ina kuka zan fita ne. "Wallahi zan saɓa miki in kika fita Halima." Shi ya sa na fasa fita amman sai na coge a tsaye ina sharan kwalla. Ran Alhaji ya ɓaci ya ɗaga murya ya na kiran sunan Gwaggo. Sai gata ta shigo da sauri ta na sanye da Hijabi a jikinta. Gani na tsaye ina goge idanuwana sannan ga Ma'u na ta shesshekan kuka Alhajinmu na faman ba ta haƙuri. Cikin mamaki da damuwa a saman fuskarta har kuma ya bayanna a muryanta ta ce"Subhanallah. Alhaji lafiya? Me ya faru ne? Duk da ta san dalilin zaman amman shi dailin koken koken namu ne ba ta sani ba. Yusuf ne ya tashi daga in da ya ke zai iso in da na ke tsaye amman Alhajinmu sai ya dakatar dashi. "Dawo ka yi zaman ka Yusufa ƙyaleni da ita." Sai ya koma ya zauna a inda ya tashi amman gabaɗaya hankalinsa na kaina kamar yadda hankalin Alhaji Mustapha ke kan matarsa. "Taho min da Halima nan gaba na Maimuna." Umarnin da Alhajinmu ya ba ma Gwaggo kenan sai ta riƙo ni lokaci ɗaya ta na faɗin" Mu je Sadiya. Mu je Alhaji na kiran ki." Ban isa na yi musu ba sai na bita har gaban Alhaji ta kuma zaunar da ni a gabansa a kuma in da na tashi, jan majina na ke yi ina ƙokarin shanye takaicina. > Janaftybaby: Gwaggo ta kalli Alhajinmu kafin ta ce"Daga sulhun ne suka fara koke koke kuma Alhaji? Bai amsa mata tambayarta ba, sai ma kallonta da ya yi kafin ya ce" Samu waje ki zama, saboda abin da zan faɗa ina so kema ki zama shaida." Sai Gwaggo ta koma ta zauna a kujeran mai zaman mutum biyu dai dai lokacin da ta ke kallon Ma'u wacce ke ta faman tsane hawayenta da hanky ɗin da ke hannunta. Sannan lokaci ɗaya ta na cigaba da shessheƙan kukanta. "Ke ma Ma'u ki bar kukan ya isa haka nan." Ta fada cikin wani yanayi, a cikin ranta tana tunanin komai Alhaji zai yi ba za a taɓa samun daidaito ta bangaran Ma'u da Sadiya ba. "Halima.." Kamar daga sama na ji Alhajinmu ya kira sunana a kausashe kuma da karfi jikina da zuciyata suna rawa na ɗaga kai ina kallonsa cikin ɓacin ran da ya bayyana har a saman fuskarsa na ga ya nuna ni da yatsar sa manuniya da ya hana ni ma iya amsa masa kiran sunana da ya yi. "Yau ce rana ta farko kuma ta karshe da zan ji ƙin ƙara kiran Ma'u da bare, yau ce rana ta ƙarshe da za ki ƙara yi mata kallon wata ba ƴar uwanki ba. Na san halin ki saboda ni na haifeki da gaske ki na da fitina da rashin haƙuri sannan ba ki da yafiya da barin abu ya wuce, sannan kina da nacin faɗa, kowa sai ya manta amman ke zuciyarki ba ta iya mantuwa. " Ya ƙarishe faɗa da karfi, kamar zai kai mini duka daman Alhajinmu akwai faɗa in ran shi ya ɓaci. Kuma ka da ka ba ri faɗan shi ya faɗo ta kanka domin ba za ka taba jin daɗi ba. Shi ya sa na ji zuciyata ta karye na fara kuka, kenan har a yau ma Ma'u ce za ta sake yin nasara a kaina? "Kar na kuskura na kara jin kin danganta Ma'u da bare, ita ba bare ba ce. Jinin ki ce domin in aka tsaga jininta za a ga na ki jinin haka itama in aka tsaka na ta jinin za a ga naki, bari na tunasar da ke abin da nasan ba ki manta ba, ni na saki nono mahaifiyar Asma'u ta kama Asiya ƙanwata ce uwa ɗaya uba ɗaya. Me ya sa kike da tunanin banza ne? Me ta yi miki? Tana bin ki amman kina ƙara nuna mata tsana? Ina ce har hakuri Murja ta ce ta yi ta ba ki kika tafi kina ta cin mutumci? Ke sheɗan ce da ba ki jin bari Halima ko so kike ki zama sheɗaniya a cikin mutane? Kuka kawai na ke yi, wannan karon kukan da na ke yi ya fi na wanda Ma'u ta yi fidda amon sauti, falon ya yi tsit sai tashin faɗan Alhaji kawai ake ji har Gwaggo tana zaune ne amman ba ta iya dakatar da Alhaji ba. Ma'u ce ta ɗago kanta tana kallon Alhaji kafin ta ce" Alhajinmu har a waya na kira ta bata ɗauka ba sai na yi mata saƙon murya ta WhatApps bari ma ka ji." Nan da nan ta ɗauko wayarta ta shiga ta duba sai ga shi ta kunna muryanta tarwai ta na fadin"Ki yi hakuri Sadiya da abin da Shema'u ta yi miki. Har ga Allah ban san a ina ji maganar ba. Na nuna mata ban ji daɗi ba na kuma ce sai ta ba ki hakuri saboda haka zan tura mata lambarki sai ta kira ki ta baki hakuri." Alhajinmu ya girgiza kai kafin ya kalleni ya na faɗin"Ta yi ta ba ki hakuri akan laifin da ba ita ta yi miki ba amman kin kasa hakura. Tabbas na fahimce ke ce sheɗaniya sannan ke ce ke hassada duk abun da ke faruwa." Ina rawan muryan kuka na kwashi rantsuwa ina faɗin"Wallahi Alhajinmu..." "Rufe min ba ki, ki kuma tsaya dakyau ki saurareni. Ga uwarki nan ta zama shaida ga mijin ki nan ya zama shaida, daga yau ina mai ba ki umarni a matsayina na mahaifinki, ki ijiye duk abin da ke cikin ranki game da Asma'u ki rumgumi ƴar uwarki. Sannan ki yi zumunci da ita ki je gidanta in abin farinciki ya same ta ki taya ta murna. Sannan ki je a lokacin jaje domin ki ta ya ta jimami. Sannan in ku ka haɗu ke za ki fara yi mata magana, ki bi ta a inda ta ke ku gaisa cikin zumunci da ƙaunar juna. Gargaɗi na ƙarshe a gareki shine ki bi umarnina ya zama wannan shi ne zama na ƙarshe da zan yi a kan wannan mganar, na ƙara faɗa miki ki yarda makaman yaƙin ki ki bi Asma'u sannan ki yi zumunci da ita, in kika saɓa ma ko ɗaya daga cikin umarnina zan yi fushi da ke fushi mai tsananin da ba ki taɓa tsammani ba Halima. Saboda haka in kina so ki rabauta har a ranar gobe ƙiyama ki yi gaggawan bin umarnin da na ba ki." > Janaftybaby: Alhajinmu na mgana ina jin kamar zuciyata za ta faso ƙirjina ta fito tsabar baƙin ciki tuni kukana ya ɗauke. Saboda ban ga amfanin ina zauna ina kuka saboda Ma'u. Na yarda ta yi nasara a kaina kamar ko yaushe. Muryanta na rawa na ce"Na ji Alhaji in sha Allahu zan zama mai bin Umarnin ka." Na faɗa ina sauke numfashi saboda na ji kamar numfashina na shirin kwacewa. Alhajinmu ya gyaɗa kai kafin ya ce" Kin yi kyan kai. Ki sani ko da rana ɗaya na ji labarin kin bambanta Asma'u da Rahila ki sani kin ɓata mini sannan zan daɗe ban iya kallon ki ba, zan daɗe ina miki kallon wacce ta gagare ni." Da sauri Gwaggo ta ce" Haka ma ba zai faru ba. Sadiya kara ba ma Alhaji haƙuri." Kaina na ƙasa na ƙara faɗin" Allah ya huci zuciyarka Alhaji. In sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba." Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso mini daga ƙasan zuciyata. Sai ya saussauta fushin sa jin har Yusuf ya rankwafa ya na neman min afuwa har da Ma'un da mijinta sai Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce" Bakomai. Na tsorata ne sabo da halin rayuwa. Ka da na faɗi na mutu na bar baraka daga zuru'a ta, na ji daɗin da kika hangi kuskuranki kika kuma yi aniyar gyarawa. Ki yi ma Asma'u sallama ta amsa miki tare da musabaha yanzu a gabana Dubu." Ban yi musu ba na juya ina miƙa ma Ma'u hannu lokaci ɗaya ina yi mata sallama. Ta miƙo min hannunta ta na yi min wani irin mirmishin da ni kaɗai nasan ma'anarshi lokaci ɗaya tana amsa sallamata tare da sarƙe hannun juna. Ni ma sai na yi mata mirmishi kwatankwancin mirmishin da ta yi mini, ai ba Ma'u kaɗai ita iya bariki ba nima na iya tunda na fahimci ta na cin nasara a kaina ne ta hanyar amfanin da makirci. "Ki yi hakuri Ma'u. Ki yafe mini sharrin sheɗan ne." Haka na faɗa ina mai gayyato mirmishi da rahama a saman fuskata, ko ta yi mamaki ba ta nuna ba sai ta waske, kafin ta ce"Bakomai. Na ji daɗin haka Yar'uwata." Daga zaunen na matsa na rumgumeta, sai da ta yi wani sansarairai kafin ta rumgume bayana ta na ɗan mirmishi nima mirmishin na ke yi sannna muka saki juna bayan mun kalli juna kowaccenmu ta yi mirmishin da bai kai zuuci ba. Gwaggo ta yi hamdala Alhajinmu ma haka ya ɗora da cewa" Na ji daɗin haka. Allah na gode maka da korar min sheɗanin da ya shigo cikin zuru'ata. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya, ku kuma na ƙara ɗora muku nauyi ku yi musu gyara in sun yi ba dai dai ba. Sannan kuma ku gaya musu su sada zumunci a tsakaninsu saboda samun falala wajen ubangiji irin ta masu sada zumunci." Suka amsa ma Alhaji da In sha Allahu. Ganin har sha ɗaya ta yi na dare sai ya ce mu ta shi mu ta fi gida mun bar yara su kaɗai a gida. Dukkanmu a tare muka yi ma Alhajinmu da Gwaggo sallama muka fita, muna gaba ni da Ma'u su kuma mazajen namu suna bin bayan mu. Ni ce na fara kallon Ma'u dai dai mun fito kofar gida, ƙasa ƙass na ce"Kin iya acting kyan shi ki faɗa harkan film za ki ci kuɗi sosai" Dariya ta yi kafin ta ce"Ko Sadiya? Ke ma ashe kin san na iya acting sosai." Sai na gimtse fuska kafin na ce"Kin sha yin nasara a kaina Ma'u kamar baya yau ma kin ci nasara. Amman ina mai ba ki tabbacin daga yau ba za ki ƙara samun nasara a kaina ba har abada." Cikin reni ta ce"Kai don Allah? Da gaske? Ban tsaya sauraranta ba na ƙarisa jikin motar Yusuf,ganin sun kariso suma ya sa na ɗaga murya ina faɗin" Sai da safe Ma'u. Alhajin Ma'u mu kwana lafiya a gaida yaran." Shi ya amsa min cikin sakewa, ita kuma Ma'u sai ta bige da mirmishi kafin ta ce" A gaida min da yarana Sadiya." Kai na jinjina mata a saman leɓena na amsa. Mu muka fara yin gaba sannan su, a juctiion muka rabu mu muka ɗau hanyar Lodge road, su kuma suka ɗauki hanyar Rijiyar zaki in da gidan Alhaji mustapha ya ke. Tun da muka ɗau hanya ban yi magana ba. Hawaye na ke yi a ɓoye ina sharewa da gefen jijabina jikina. Yusuf sau ɗaya ya yi min magana na ce ya rabu da ni, sai ya maida hankalinsa kan tuƙi amman rabi da kwatan hankalinshi na kaina ganin yadda hawaye ke kwaramyamin wani na korar wani, ba wanda zai iya fahimtar yanayin baƙin cikin da na ke ciki, Ma'u ta daɗe ta na gigita duniyata ba tare da an sani ba amman komai > Janaftybaby: ya zo ƙarshe. Na fahimci ni nake ba ma Ma'u daman da ta ke cin galaba a kaina to in haka ne zan dakile wannan damar zan toshe mata duk wata hanyar da za ta ƙara kuntatamin. Sanda muka isa gida ko jiran Yusuf ban yi ba, na yi shigewata cikin ɗaki na barsa yana leƙa ɗakin yara. Bedroom ɗin mu na shiga na faɗa kan gado na saki kukan da na ke ta riƙewa tun dazu har da fitar da sauti. Ina ji Yusuf ya shigo ganin ina kuka ya sa ya nufeni da sauri ya na faɗin"Haba Sadiyata, ina raye kike kuka? Ko za ki yi kuka ba za ki yi kuka a saman kafaɗata saboda na ji daɗin lallashin ki ba? Ya faɗa ya na mai hawa gadon ya tarairayoni jikinsa, sai na faɗa masa muka durkushe saman gadon ina wani irin gunjin kuka shi kuma yana ta ɗan tapping ɗin bayana alamun lallashi bai hana ni kuka ba sai da na yi ya isheni sannan ya ɗago fuskata ya saka hannuwansa ya na share min hawaye lokaci ɗaya yana faɗin. "Ya isa. Ki daina kuka ka da kanki ya fara ciwo. Shii.. is ok kin ji ko? Haka ya ke faɗa, cikin sanyin murya, buɗe idanuwana da suke rufe ina kallonsa da jajayen idanuwana kafin na ce" Ka yarda da cewa Ma'u makira ce? Ka ga fa ta haɗa ni da mahaifina a gabana na kasa wani abu Yusuf, ta haɗa ni da kowa nawa.' Sai na ƙara fashewa da kuka ina faɗin" Na rasa me na yi mata ta ke yi min haka? In saboda fasa auranta da Yaya Hamza ne ban yi nadama ba, saboda in da na bari da tuni ta haɗa mana yaƙi a gidanmu. " Shi dai yana ta faman ba ni, ba ki ya na cewa na yi hakuri na daina kuka tunda Alhaji ya yi min faɗa na bi umarninsa. Ƙura masa ido na yi kafin na ce"Haka ne zan bi umarninsa. Bakomai." Daga haka na tashi daga saman jikinsa na sauka daga kan gadon lokaci ɗaya ina cire Hijabin jikina. Fita na yi zuwa toilet ina wani tunani a cikin raina. Ba haka zan zauna Ma'u ta cigaba da cin galaba a kaina ba, tunda har ta riga ta samu magoya baya, ni kuma daman ba ki na yasa ko ina da gaskiya na ke zama mara gaskiya gwara na yi amfani da fatar bakin nawa domin ka da Alhaji ya sake yin fushi da ni gwara na cigaba da tafiyar da Ma'u kamar yadda nima ta ke tafiyar da ni. KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️4* Sanda su Ma'u suka ɗau hanyar gidansu da ke Rijiyar zaki. Zaune ta ke a bangaren mai zaman banza, kamar ba ita ce ta gama kuka wurjajan ba. Wannan karon mirmishi ne da Annuri ke fitowa daga ƙarƙashin zuciyan Ma'u kuma har ya ke iya bayyana a saman fuskarta. Mijinta Alhaji Mustapha na tuki, sai ya waiwayo da hankalinsa zuwa kanta a tunaninsa har a lokacin ba ta bar kuka ba, amman ga mamakinsa sai ya ganta zaune tana mirmishi. Cikin mamaki ya ce"Har kin huce kenan Hajiyata? Kallonsa ta yi ta na ɗan mirmishi kafin ta ce"Me ye a ciki? Ba fa komai Alhajina. Farinciki na ke yi yau Sadiya ta kalleni a matsayin ƴar'uwa. Zuciyata na cike da farincikin da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba." Ta ƙarishe faɗa fararan haƙoranta na bayyana a waje. Ma'u Fara ce farinta mai irin ja ja ɗin nan ne, taNa da fadin fuska sannan ba ta da tsawo kuma tana da ɗan jiki, sai kibar ta yi mata kyau sosai. "Ni fa Sadiya ce ke ba ni mamaki har yanzu. Kina ƴar'uwanta haba. Sai ka ce bare ko bare ce ke ai wannan ƙiyayyar ta yi yawa Asma'u. Ni ko da muke haɗuwa ba ta son yi mini magana ban kawo haka ƙiyayyar nata a kan ki ya yi ƙamari ba, na fi danganta haka da halinta ne tunda ko Anty Bahijja za ki ji ta na complain da Matar Tafida ba ta son mutane, ga shi kuma ta auri ɗan dangi." Maganarsa ya katse mata tunanin da ta ke yi, kallon shi ta yi mirmishin da ya ke so game da ita. Asma'u ba ta fushi ko an ɓata mata rai yanzu yanzu za ta huce ka ga har tana mirmishi. "Bakomai Alhajina ai komai ya wuce yanzu. Kuma da man ko lokacin muna gida ni da Rahila mun fi Sadiya son mutane, ita haka take ba ta cika son mutane ba gaskiya." "Amman ko halinta ba mai kyau ba ne. Ina mamakin yadda Injiniya ke iya zama da ita da wannan murɗewan na ta." Mirmishi Ma'u ta yi masa ba tare da ta ƙara magana ba. Ta gaji da bashi amsa tana Allah Allah ya yi shuru ya maida hankalinsa kan tuƙinsa amman sai da ya juyo da niyar ƙara yin wata mgana sai kuma wayarsa da ke gaban Aljihunsa ta fara ɗaukan sauti alamun ana kiran shi, shi ya katse masa mganarsa sai ya maida hankalinsa kan wayarsa. "Alhaji Garzali ne.." Haka ya faɗa sannan ya ɗaga wayar. Mirmishin gefen kawai ta yi, ya na waya hannunsa ɗaya na saman sitiyari hankalinsa rabi na kan waya rabi na kan tuƙi, shi ya sa ma ya rage gudun motar sai aka ci kuma sa'a dare ya yi sosai ba yalwar giftawan motoci sosai. Ƙuri Ma'u ta yi masa da ido, tana ƙare masa kallo. Alhaji Mustapha ba zaɓin ta ba ne, ba kuma shi ne muradinta da mafarkinta ba. Ba domin Sadiya ba da ƙila yanzu ita ce a gidan Yaya Hamza kuma ita ce mahaifiyarsu su Afnan ba Khaleesat ba, ba domin Sadiya ta yi mata baƙin ciki ba da yanzu ba ta auri wannan magidajen kanon ba. Shi ya sa har gobe wannan dafin da Sadiya ta bar mata ya kasa ɓacewa daga cikin zuciyarta. So ta ke yi ko da ƙwatanƙwacin irin baƙin cikin da ta ji ne, itama Sadiya ta ɗanɗani irin shi ta ji in da daɗi. "Ma'u..Ma'u.." Muryan Alhajin nata ya katse mata tunani, sai ta dawo da ƙwayan idanuwanta a kansa, daman can sunan ta na kallon shi ne amman tunaninta da hankalinta ba su a kansa kwata kwata. "Tunanin me kike yi haka? Ina ta magana kin yi shuru? Basarwa ta yi kafin ta yi mirmishin da ta san ya na sace zuciyansa. "Tunaninka na ke yi mana My Alhaji." Ta faɗa lokaci ɗaya ta na yi masa fari da wani kallo da shi kaɗai ta san yana kunna shi, aiko sai ga shi ya ke ce da wata dariyan nishaɗi kafin ya buga sitiyari lokaci ɗaya yana faɗin" Ma'u. Ma'u na, ba ki da dama." Mirmishi ta sake yi tana kara narke masa, dariyan ya sake yi kafin ya ce"Alhaji Ghali na gaishe da Amarya Ma'u." Cikin yar dariya ta ce"Ina amswa. Ya iyalan nasa? Ya amsa mata da suna lafiya kafin ya ɗora da faɗin" Kin san ko har gobe in na je gidan sai Hajiya Fati ta yi mini tsiyan ba ki zo mata Allah ya sanya alheri ba, lokacin bikin ƴa'ƴanta." > Janaftybaby: Kai tsaye Ma'u ta ce"Ayya. Ba ka gaya mata bana nan ba ne lokacin? Kuma ai Hajiya ta je ta wakilceni" Ya na dariya ya ce"Nima haka na ce, da Hajiya da Ma'u duk abu ɗaya ne a waje na." Taɓe baki ta yi, a farko sannan ta ɗan saki fuska kaɗan. Hira ya cigaba da yi mata, sai faman taɓe baki ta ke yi, in zai juyo sai ta sakar masa lallausan mirmishin da ta san ya na kunna sa har cikin zuciyarsa. Kanta ta maida jikin window din motar tana kallon hanya har ga Allah ba ta son surutu, surutun ma a wajen Namiji, ba haka ta so mijin auranta ya kasance ba, ta na son namiji mai Aji da kamewa amman mai ake yi da gidahumin namiji, waiwayawa ta yi ta na ƙara kallon Mijin nata wani abu da ya daɗe da tokare mata zuciya duk sanda ta kalleshi a matsayin mijinta ya sake ta so mata. To ta san ba ta san shi me ya sa ta aure shi? Ba saboda kowa ba ne sai Saboda da BAABA. da kuma KUƊI. Ba domin kuɗin Alhaji Mustpha ba, da ko hanya ba za ta iya haɗawa da shi ba, tunda ya yi yamma da irin zaɓin mijin da ta daɗe tana mafarkin samu. Alhaji Mustpaha irin ƙauyawan kanawan nan ne, shi bai yi boko ba sai arabi, amman fa ya san kan kasuwanci yana kasuwancin Fata sannan kuma ɗan chajin ne, yana da kuɗi sosai. Kuma mahaifinsa ma har ya mutu sana'ar fata ya ke yi, shi ya sa zuru'arsu ke da kuɗi, amman bayan nan mugun bagidajen ƙauye ne, mara lissafi. Sannan ita ba ta taɓa hango kanta a matsayin macen da za ta yi aure ta zo a mace ta biyu, ta tsani zama da kishiya a rayuwarta saboda mahaifiyarta tun auranta na fari ba ta ji daɗin kishiya ba, kafin ta zo ta auri mahaifinta mutuwa ta zo ta raba, sannan a auranta na uku ma gidan kishiyiyon ta je, da har gobe ba ta huta ba. Shi ya sa ta yi fatan samun gidanta ita kaɗai ta gina shi duk yadda ta ga dama ba wai ya kasance ita ce zata shiga gidan da wata ta gina ba. Amman kaddara ta riga fata, ko da ya ke Sadiya ce ta sauya mata kaddaranta. Domin saura ƙiris ta cika mafarkinta ta yi sanadiyar lalata komai, shi ya sa itama ba ta da wani buri sai na ganin ta lalata ma Sadiya jin daɗin duniyarta ta gigita mata rayuwarta yadda ƙwatankwacin yadda ba ta samu abin da ta ke so ba, itama ba ta fatan Sadiya ta cigaba da samun abin da ta ke so, in ma ta samu to za ta yi sanadiyar lalata shi ya zama baƙinciki a gare ta. Tana da burika da dama akan Sadiya waɗanda ko kwatansu ba ta cika ba. Nasara a kan Sadiya yanzu ta fara yi in a baya ita ta ta yi kuskuren barin Sadiya yin nasara a kanta wannan ƙarnin baya ne da ya shuɗe. Wannan ƙarnin na yanzu ita ce za ta cigaba da samun nasara akan Sadiya daga nan har abadan. Ba ta ma san sun iso gida ba, sai da ta ji yana hon sannan ta farga da har sun iso gida, gidan Asma'u ƙaton gida ne mai kama da Aljannar duniya, amman duk wannan daular ba ya gabanta matukar ba ta ɗanɗana ma Sadiya irin ɗacin da ta ke ji a cikin zuciyarta ba, ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba. Ita ta fara yin gaba zuwa cikin gida. Ta bar Alhajinta na magana da megadi, a falon gidan ta ci karo da ƙanwarta Zainab ƴar kimanin shekaru 16 zuwa 17, da ke hannunta tana zaune ta na kallo, abin sai ya ba ta mamaki ta na ganinta ta yi saurin miƙewa tana sosai ido, wani kallo Ma'u ta yi mata kafin ta ce"Uban me kike yi har yanzu ba ki yi barci ba? Cikin In ina Zainab ta fara faɗin" Ina. Ina. Kallo ne." Kafin Ma'u ta samu zarafin magana Alhaji Mustapha ya shigo falon kawai sai ta fasa maganar da za ta yi sai ma ta kalleta tana faɗin" Kin tabbatar da kin saka su Baba ƙarami sun yi fitsari kafin su kwanta ko? Da sauri ta ɗaga kanta, Alhaji Mustapha na tambayan me ya faru? Ba ta tsaya bashi amsa ba ta kama hanyar ɗakinta lokaci ɗaya ta na faɗin" Ki kashe kallon nan ki je ki kwanta." Daga haka ta shihe koridon da zai sada ta da ɗakin barcinta a ƙasan ranta ta na ji kamar ta ce Alhaji ya je gidan Hajiya yau ba ta cikin Mood ɗin da za ta iya dauriyan kwana dashi. > Janaftybaby: Shi ya sa ta na shiga ɗakin barcin na ta ta maida ƙofa ta rufe. Wayarta ta sauke nan saman gadon da mayafinta sannan ta buɗe kofar tiolet ta shiga wanka za ta yi, ta na cikin wankan ta ji Alhajin nata na ƙwanƙwasa mata kofar, tsaki ta ja a fili da ɓoye wani abu na suƙan zuciyarta dagacan ƙasa. Ta na fitowa ɗaure da Towel, har lokacin bai tafi ba ko ya tafin ma ya sake dawowa. "Ma'u. Ma'u ta,..' Tsaki kawai ta ƙara ja a fili sannan ta isa ga kofar ta murza key, ta na buɗewa kawai ta juya ta dawo cikin ɗakin gaban madubin da ke shake da kayan kwalliya ta tsaya shi kuma cikin jallabiya ya shigo yana mai washe baki. "Au wanka kike yi ne? Juyowa ta yi sannan ta gyaɗa masa kai tana mirmishi, shi kuma sai ya rumgumota ta baya fuskarsa da nata na bayyana ta cikin madubin, Asma'u ta yi mirmishi, mirmishin da a saman leɓenta kawai ya tsaya, tana kallon Alhaji Mustapha kansa har ya fara furfusa ga uban sauƙo, a fuskarta mirmishi ne, amman a ƙasan zuciyarta ƙuna ne da wani irin turiri da ya ke ta so mata. Ita ko za ta iya yafe ma Sadiya? Kai ina sai ta gigita rayuwar Sadiya. Sai ta yi sadiyar zama sanadin da farincikin Sadiya zai yanke na har abada. Yadda ita ba ta zauna ita kaɗai ba, itama Sadiya burinta ba zai cika ba, sai ta gayyato mata damuwowi masu tarin yawa a rayuwarta wannan alƙwarin ASMA'U SULAIMAN YASHE ce. ** *BAYAN KWANA HUƊU* LODGE ROAD. JUMMA'A. Karfe 7:40am na safe Salisu ya zo ya ɗauki su Jidda zuwa makaranta. Suna tafiya ban huta ba na shiga ɗakinsu ina haɗa musu kayansu, na zuwa gidan Anty Maimuna ko jiya sai da ta kirani a waya tana gwaɓa mini magana wai wannan satin ma hala gidanmu za su je? Ban biye mata ba na ce yau in sha Allahu za su zo. A ƙaramar jakar baya na Jidda na haɗa musu kayansu da duk abin da za su buƙata, tiolet na shiga na ɗauko musu brush na fito kenan sai na ga Yusuf zaune a gefen gadon su Jidda. Sanye yake da jallabiya. Tun bayan dawowarsa sallar asuba ya kwanta ban ma san ya tashi ba. Tsayawa na yi sororo ina kallon shi kafin na yi mirmishi na ƙariso ina faɗin"Har ka tashi? Miƙewa ya yi ya zo gabana ya buɗe min hannuwansa na faɗa ya rumgumeni yana faɗin" Ina kwana Sadiya ta." Na amsa ina sakin sa kafin na ce"Na ga barcin ka ya yi nisa shi ya sa na ce su Jidda kar su tashe ka, su tafi kawai." Ya na tsaye ya harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ni kuma sai na duka ina saka musu brush ɗin su a cikin jakan da na haɗa musu kaya. "Kayan me ye wannan? Ina duƙe na ce" Kayan su Jidda ne. "Na zuwa ina kuma? Sai da na ɗago sannan na kallesa kafin na ce"Gidan Anty Maimuna. Wancan satin kasan ba su samu zuwa ba." Sai a lokacin ya ce"Oh. Na tuna ko jiya da na je gida Nene sai da ta yi min magana. Wai Anty Maimuna na ta faɗa." Ina kallon idanuwansa na ce"Wai faɗan me? Taɓe baki ya yi kafin ya ce"Ban sani ba, amman ta tambayeni me ya hanasu zuwa wancan satin na ce ma Nene ban sani ba." Baki kawai na saki ina kallon shi, wai bai sani ba, Me ya sa Yusuf ya ke yi mini haka ne? Yadda ya ga ina kallonsa ne ya sa ya fara dariya, ya matso ya riƙeni na matsa baya ina haɗe rai kafin na ce"Ba ka sani ba ko? To ai ya yi kyau." Ina gama faɗin haka na juya na bar masa ɗakin. Wai ni haka maza suke ko nawa mijin ne haka? Sau tari wasu laifuffukan da danginshi ke kallona da shi har da laifin shi, sai a yi abu kuma ya san dalilin faruwan shi amman in suka tare shi da maganar sai ya ce bai sani ba, kuma na yi masa ƙorafi har na gaji ya kasa dainawa, in na yi magana sai ya ce ai bai sani ba ne, ko game da zuwa sha'anin dangin shi, gajiya suka yi suka ƙyaleni, da suka fahimci ba ma su kaɗai ba hatta nawa dangin ba kasafai na ke shiga ba, ganewan suka yi ko gajiya suka yi da abu ɗaya suka kyaleni ban sanin musu ba. Kitchen na koma, daman yara saboda yau jumma'a ne drink suka tafi da shi da Bicuit, sai tea da suka sha da biredi kafin su tafi, doya na fara ferewa zan soya mu sha tea da shi, ina feran doyan ya shigo kitchen ɗin yana faɗin"Fushi kika yi? Banza dashi na yi, saboda ya ba ni haushi, burin sa na yi ta laifi a idon danginsa shi kuma ya na jin daɗi. > Janaftybaby: Zuwa ya yi ya rumgumeni ta baya. Lokaci ɗaya yana ɗora kansa saman kafaɗana bayan ya rankwafa. "Sorry, kin ji ko? Taɓe baki na yi kafin na ce"Ba dai da man so kake yi ko da yaushe na zama mai laifi a wajen ƴan'uwanka ba? To ai shikenan." Matse cikina ya yi da hannayensa da ya saƙalo ta cikina. Sannan da ƴar murya ya ce" To ai na ce ne ban sani ba, kin sani da yawan mantuwa." Mirmishin gefen baki kawai na yi, ba tare da na yi magana ba ya yi ta taƙalan mgana da ni na yi masa gim daga e, sai a'a kawai na ke amsa masa, sanin halina ya san in raina ya baci haka na ke yi sai ya sake ni yana faɗin" Bari na je na yi wanka. Zan je Rano." Sai da na ji ya ambaci Rano sannan na ɗago ina kallonsa kafin na ce"Uncle Abba bai kira ka ba? Kai ya girgiza kafin ya ce" Ya kirani amman bai yi mini maganar ba, amman in mun haɗu zan tuna masa." Kai na jinjina, ba tare da na yi magana ba shi kuma ya fice daga kitchen ɗin, bayan ya rufo mini ƙofar. Na bi shi da kallo kawai, a baya ne ba na ƙaunar na ji ya ce zai je Rano duk da tushen shi ne, saboda GIMBIYA, amman tunda yanzu ta yi aure ban damu da yawan zuwan shi ba, in na yi duba da irin ayyukansa na kwangilan gine gine in an samu yana zuwa ko Uncle Abba ya yi masa hanya, tun da shi har gobe ya na garin Rano kuma a nan ya gina ƙaton gida duk da bai yi aure ba. Gun bayan lamarin da ya faru tsakani na da Ma'u da yadda Alhajinmu ya goya mata baya. Tun da na dawo gida ban wani saki ba, ko Jidda sai da ta ce Umma ko ba ki da lafiya ne? Gabaɗaya zuciyata ba ta mini daɗi, ballatana da gabaɗaya ƴan gidanmu suka goya ma Ma'u baya, Yaya Hamza ne kaɗai bai shiga maganar ba shi daman sai a yi abu goma bai saka baki ba, mutum ne mai fahimta shi ya sa ko a baya nake ƙaunar Yaya Hamza saboda hallayarsa ɗaya ne a cikin dubu. Shi da Yaya Auwalu za a daɗe ana abu ba su maida kai ba. Yaya Abubakar har sake kirana ya yi, bayan na ɗauka zagina ne kawai bai yi ba akan Ma'u. Su Yaya Murja kar a ji labari. Yaya Aina har cewa ta yi za ta iya yanke ni akan Ma'u. A group ɗin Gidanmu an fi kwana uku maganar kawai ake tattaunawa. Ban san ina suka samu cikakken bayanin abin da ya wakana tsakaninmu da Alhajimu ba, sai ga shi Yaya Murja na maida yarda aka yi, to har na yi mamaki Ma'u ce ta faɗa mata ta na jin daɗi haka. Yaya Aina har ta na cewa gwara da Alhajinmu ya yi min haka ƙila zan shiga tairayina. A mganar nan mutane biyu ne suka ce nima ya kamata a duba maganata ƙawar Ma'u ta yi magana domin tozarci. Yaya Balki da Amina. Sauran kuma duk iyalan Ma'u ne, shi ya sa nima na sauya musu matsayi. Rahila dai ba ta saka baki ba wannan karon, domin ta san halina wallahi sai na yanketa. Sai na yi amfani da shawaran da na yanke a cikin zuciyata akan na shiga na yi magana na ƙara ba ma Ma'u hakuri a gaban kowa kamar yadda take yi min amman munafuki shi daman a koda yaushe yana shirye ne. Sai kawai ta rigani shiga ta yi magana, hakuri ta ba ma kowa sannan ta ce a bar maganar daga karshe ta yi tagging ɗina kafin ta ce"Komai ya wuce, zumunci da ni da Sadiya har aljannah ko ƴar'uwata? Ban yi wani mamaki ba, sanin ba tun yau ba Ma'u ta kware a iya acting ba sai nima na fito muka yi acting ɗin a tare, kai tsaye na ce"Kowa ya yi hakuri mun daidaita barakan dake tsakaninmu da ƴar'uwata Asma'u." Sai gashi sun fito suna murna, Yaya Murja ni kaɗai nasan haushinta da nake ji, har da cewa Allah Sarki Ma'u mai hakuri ce daman, ke kuma Sadiya a rage zafin zuciya. Ita da Yaya Abubakar Ma'u kamar ƙanwar uwarsu, ko da ya ke shi Yaya Abubakar akwai tsohuwar soyayya, ita kuma Yaya Murja har da son abin duniya, tunda Mijin Ma'u na da kuɗi ana zuwa ana maula dole ta riƙa zama mai goyon bayanta, ni fa a gidanmu na riga na san halin kowa sannan na yi ma kowa wajen zamansa wallahi. Har na gama soya doya raina a ɓace ya ke, na kwashi komai zuwa Dinning, sannan na koma Bedroom sai na iske Yusuf suna waya da Uncle Abba sai na ce ya ba ni mu yi magana kan dai maganar fara zuwa na ganin likita asibitin Shika dake Zaria ne. Sai ya ce sun sake magana da Dr. Fadel ya ce in ta bashi lokaci zai kira mu ya sanar da mu. > Janaftybaby: "Ki kwantar da hankalinki Sadiyan Yallaɓai. Da zaran ta saka lokacin ganin ki zan sanar ma Tafida kin ji ko? Sai na gyaɗa masa kai kamar ya na ganina sannan muka yi sallama na miƙa ma Yusuf wayarsa. Tiolet na shiga nima na fara wanka ko da na fito baya falon. Sai na samu daman shiryawa a tsanake. Riga da wando na saka na material Daman ni in dai ba fita zan yi ba, ba na saka kaya masu nauyi. Kalan kayan maroon ne, sai na yi amfani da bakar hula mai raga raga, kaina har lokacin ban yi kitso ba mai zuwa har gida ta yi mini kitso ta yi tafiya ne, ni kuma ko sake wanke shi a gida ban yi ba, tunda na iya ina da kayan wanke kan, har su Jidda ni nakan wanke musu kai na gyara musu. Takalmin gidana mai taushi na saka bayan na fesa turare mai ƙamshi na fita zuwa falo Yusuf na jira na mu karya sannan ya fita. Ni na zuba masa doyan sannan na haɗa masa tea ɗin, sannan na haɗa ma kaina na zauna kujeran gefensa. Ban ɗaure fuska ba amman ban kuma saki fuskar ba, ganin yanayina yasa sai ya rika takala na da magana sai dai in bishi da ido kawai. "Ko za ki shirya yau ki je ki gaida Nene, in na dawo daga Rano sai na biya ta gida mu dawo tare." Kai na gyaɗa kafin na ce"To shikenan sai na shirya na je ɗin." Yana mirmishi ya shafa kumatuna kafin ya ce"To a saki fuskar, shan kunin ya isa haka." Kalamansa suka ba ni dariya, sai na murmusa, mun cigaba da karyawa mun gama kenan na kallesa ina faɗin"Wata kwangilar a ka samu a Rano kuma? Ya na miƙewa ya ce"Ban sani ba. Abba ya ce na shigo mu je mu gani." Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya sa a dace? To su dai waɗancan masu payment ɗin shuru ko? Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Wallahi shuru. Amman ban cire rai ba tun da sun ce ko da yaushe zan iya jin su." Fatan alheri na yi masa amman ban yi ɗoki ba domin ni nasan yanayin aikin shi, sai a yi shekara ana cewa za a biya shuru amman fa aka biya muna warkewa masha Allah tunda kuɗi ne ba kaɗan ba, kuma in aka samu aikin ana yin shi muna shiga hali tunda kuɗin shi zai ɗauka ya yi amfani dashi a karkashin kamfaninsa na HM. TAFIDA AND SON'S LIMITED. office ɗinsa na can hanyar zoo road kan titin Zaria Road. Ni na raka shi har bakin mota kamar yadda muka saba, ya ba ni 2k ya ce na hau adaidaita zuwa gidansu da ke Gwammaja, muka rabu bayan ya rumgumeni ya sumbaceni, nima na maida masa martani, yana ɗaga min hannu nima ina ɗaga masa da fatan Allah ya kai shi lafiya ya dawo mini dashi lafiya. Bayan tafiyarsa na koma cikin gida, falon farko na zauna saboda ka da Saude ta zo ta yi ta buga gida ina ciki ban sani ba, sai na kunna kallo tunda akwai wuta a tashar arewa 24 suna haskawa wani film hausa mai suna Ahalil kitab duk da na kalli Film din amman ina son waƙoƙin ciki sai na zauna ina kallo har na ji buga gida na je na buɗe ma Saude muka shigo tare, na zauna na cigaba da kallona ita kuma ta fara aikinta. Kafin azahar ta gama min komai, ni har barci ma na yi a saman kujera anan falo da za ta tafi na ba ta 500 na ce ta hau abin hawa, tafiyarta ba dadewa su Jidda suka dawo daman na yi ma Salisu maganan zai kai su Alu Venue anguwan su Anty Maimuna sai ya ce mini bari ya je ya yi sallar jumma'a ya dawo kan nan sun shirya. Sai murna suke yi tunda na ce can za su yi Weekend,tunda akwai jikokin yarta na fari Mardiya suna wajen Anty Maimunan ne sa'anin Baby ne, sannan autan ta ma sa'ar Jidda ne Afiyatu. Ban yi musu girki ba, Coorfleck na ce su sha bayan sun sauya kaya sun yi sallah. Kayan su suka saka iri ɗaya shadda mai ruwan ƙasa da na ɗinka musu da sallah da ta wuce da mayafansu, iri ɗaya har takalminsu iri ɗaya ne, na faɗa ma Jidda su yi kitso a can saboda na san ba da wuri za su dawo ba. Ban san me ya sa Anty Maimuna ta ke kulafacin su Jidda ba, ko don Baby ita aka yi ma takwara? Ko kuma daman can ita mai son yara ce gaskiya. > Janaftybaby: Ɗaya da rabi na rana Salisu ya dawo ya ɗauke su suka tafi. Suna tafiya nima na shirya na saka wata atamfata hollad mai ruwan ganye, sai na yi amfani da green ɗin mayafi jaka da takalmina kuma na saka baƙi, key ɗin gidan da na ɗauka sai da na tabbatar da na kashe komai na wuta sannan na fita na rufe get ɗin da makulli, ban samu adai daita ba sai da na taka zuwa babban titi, anguwan shuru daman haka take to ta masu kuɗi ce, kowa na gidajenshi shi ya sa ƙawa ko ɗaya ban da shi a rukunin nan sun shigomin lokacin da muka tare amman ni da ya ke halina sai ni sau ɗaya na taba shiga gidan gefen mu gidan maman muhsana, da ta haihu na yi barka. Allah ya halliceni mace mara sson shige ma mutane, ko yan gidanmu in ba wani abu ya faru ba, ba kasafai nake zuwa ba, gwara na yi zama na a gida in yi barci ya fiye minim Drop na ɗauka zuwa Gwammaja. Muna tafe na ji wayata na ringing a jaka na ɗaukota na duba sai na ga Zaituna ce Matar Yaya Abubakar. Na yi mamakin ganin kiranta domin ni dai ban wani yi da ita na fi yi da Anty Khaleesat ɗin Yaya Hamza. Ita Zaituna akwai kwaɗayi da surutu da an ce kace kace shi ya sa ban cika sakin mata ba, sannan daman ina jin haushin mijinta shi ya sa na ɗauka a dakune ban sakar mata fuska ba. Bayan mun gaisa, sai na yi shuru ina jiran abin da za ta ce. "Kina gida ne Sadiya? Yamutsa na yi kafin na ce"A'ah me ya faru? Kai tsaye ta ce"Ayya daman ina kusa da anguwarku ne, mun zo suna gidan wata ƴar'uwarmu ne, na ce bari in kira ki in kina gida, sai na biyo." Daga yanayin yadda take magana kamar a wahale, na fi tunanin ƙila sun je ne ma ba abinci za ta ce ina kusa bari ta kirani ta daɓo gayyar danginta su zo min gida, na ji daɗi da ba na gida saboda ita ma Zaituna ƴar ƙashin bayan Ma'u ce. "Ai ko ba na gida, ina hanya za ni Gwammaja gidan su Yallaɓai." Sai ta ce to shike nan, daman ta ɗauka ina gida ne, daga nan muka yi sallama. Na kashe wayata ina hararan wayar kamar ita ce a ciki, na tuna ko faɗan da muka yi da Ma'u a gidan Rahila, suna yan gaba gaban saka bakin cewa ni ce ba ni da gaskiya. Wayata na mayar jaka, ni kaɗai ina ƙunƙuni ni fa su san halina duk wanda ya ci tuwo da ni wallahi miya ya sha, ga su ga Ma'un duk za su ci ubansu. Mai adaidaita bai direni ko'ina ba sai ƙofar gidan Iyayen Mijina da ke Anguwan Gwamnaja. Na sauko daga adaidaitan ina miƙa mi shi kuɗin shi na ji an kira sunana. "Anty Sadiya.." Ina juyawa sai na ga Adnan ne, sai da na sallami mai adaidaitan ya tafi sannan na nufe shi, ya na tsaye a ƙofar gidan shi da abokonsa guda biyu sun sha manya kaya ƙila daga masallacin jumma'a suke. "Adnan manyan kasa, yaushe a gari? Na faɗa ina kallonsa yana dariya ya ce"Jiya na shigo garin. Ina su Jidda? Ina amsa masa da cewa sun tafi gidan Anty Maimuna, abokansa suka gaisheni na amsa, jakar hannuna ya karɓa muka jera zuwa get ɗin gidan. Gidan Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa babban gida ne, mai bene sama da ƙasa. Ko haraban gidan wargajeje ne, duk da mai gidan ya fi shekara ashirin da rasuwa, gidan bai rankwafa ba, saboda ya hayyafa, kuma ƴa'ƴa sun tasa, in wannan bai kawo ba wannan zai kawo, shi ya sa ƙyallin gidan har gobe bai daina haskawa ba. Muna tafe ne zuwa cikin gida Adnan na yi min hira makaranta. A ABU ZARIA ya ke karatunsa na Engniaring, a tsakar gidan muka ga Jawahir na shanyan ƙananun kayanta da ta wanke. Tana ganina ta washe baki ta na faɗin" Anty Sadiya." Na amsa ina faɗin"Au kema kin zo hutun ne? Ko guduwa kika yi? Dariya ta saka tana faɗin" Kai Anty Sadiya, da ne fa yanzu ai mun zama ƴan makaranta." Adnan ya ce"Tunda ba ki son bokon ki yi aure mana ko Anty Sadiya? Kai na gyaɗa ban yi magana ba Jawahir ta balla ma Adnan harara lokaci ɗaya ta na faɗin" To ai sai ka zo ka yi min auran ubana." Yana ƴar dariya kafin ya ce"Ko ba ki faɗa ni ubanki ne, domin zan iya ɗaura miki aure." Suka kacame da gaddamansu na saƙo da saƙo ni kuma ina ta dariya. Jakata na karɓa hannun Adnan ina faɗin"Bari na karisa, su Hajiya Iya ba sa nan ne na ji gidan shuru? > Janaftybaby: Jawahir ta ce" Maman Farko ba ta nan an yi musu rasuwa, Iya kuma ta kwanta ne Nene kuma ki haura sama ta na ciki." Wuce su na yi, na bar su suna musu, ya na cewa shi ubanta ne, ita kuma ta na cewa Allah ya kyauta ya zama babanta. Shashen ƙasa Hajiya Iya ne da Mahaifiyar su Jawahir marigiyayiya Hajiya karima Allah ya jiƙanta, sama kuma Hajiya Nene da Maman Farko suke bangaren sama, amman a ƙasa akwai ɗakunan baki daga can haraba kuma akwai ɗakunan mazan gidan. Sama na haura, ƙofar shashen Nene ne a farko tun kafin na shiga na jiyo hayaniya, ina sallama bayan na cire takalmi na sannan na shiga babban falon na Nene. Hauwa na gani zaune a falon sai fama take yi da yara, Hauwa matar ƙanin Yusuf ne mai bi masa, Muttaƙa. Sai ƴaƴan Halima da su ban ga uwarsu ba, ina ga su kaɗai aka kawo Nene ba ta falon ma gabaɗaya. Hauwa na ganina ta tare ni da mirmishi, karamar ƴarta, Sahla ta nufoni ta na min oyoyo na taro ta ina ƴar dariya saboda yarinyar ta gane ni, duk in da ta gani ta riƙa gwarancin mgana kenan, suna zuwa gidana sosai nima ina zuwa saboda Hauwa tawa ce, duk cikin Facalolin gidan ba ni da kamar Hauwa. A bangaren Matan gidan ba ni ba ce Babba ba, akwai Matar Yaya Usman Zabba'u, sai ni sannan Muniran Yaya Nasir sai Hauwa da tsakanin auren mu da na su shekara shidda ne. Amman ina son Hauwa saboda muna da kamaceceniyar hallaya, ba ruwanta tana da sanyin hali duk da yar uwa ce tun da ƴar rano ce a can Mutaƙƙa ya auro ta. Gaisawa muka yi faram faram kamar yadda muka saba in mun haɗu. "Ina Nene? Sai ta ce mini ta shiga ciki ta kwanta. Yaran Halima na kallah kafin na ce"Tare da Haliman suke? Na ga ban ganta ba? Sai ta ce mini "A'a su kaɗai baban ya kawo ya ce Haliman ba ta jin daɗi" Sai na ce Allah ya sauwake, sai da na ji Hauwa na faɗin ƙila ma Haihuwa ce. Baki na saki domin ni har ga Allah ban san tana da ciki ba, har sai da na furta ma Hauwa. Ta na dariya ta ce" Kin daɗe baki ganta ba ne? Ni mun haɗu a walimar sabon gidan Anty Suwaiba, a can ne na ganta da cikin". Kai na jinjina kafin na ce" Ni kin san ban samu zuwa ba." Sai ta gyaɗa min kai, hira muka cigaba yi, amman hankalin Hauwa na ga yara, ita yayanta huɗu, sauran ta ce suna gida tare da babansu da Sahla kawai ta zo amman sai wahala take yi da yayan Halima da ba sa jin mgana. Muna zaune muna hira Walid da wayonsa ya fi shekara biyar ya yi fitsari a cafet, mamaki ya isheni ganin Hauwa ta miƙe jikinta na rawa ta na masa faɗan me ya sa ya yi fitsari a zaune bai zai yi magana ba? Sai kawai yaron nan ya fasa kuka ya nufi bedroom ɗin Nene, na saki baki galala ina kallon abin mamaki. Ina kallo Hauwa ta je ta diɓo ruwa ta zo da towel tana tsane fitsarin ina zaune ko motsi ban yi ba, na yi wannan wahalar a baya amman ban yi wahalan ƴaƴan ƙannen miji da yayyensa ba, na yi dai na uwar mijina a baya amman a yanzu wallahi na daina, in ba a gode na baya ba a barshi. Falon duk sun yi kaca kaca dashi sai da ta share, sannan ta dawo ta zauna Walid dai tun da ya shiga bai fito ba, Salha da Afra kuma Hauwa ta ce su sauka kasa su je wajen Anty Jawahir. Sai da suka bar falon sannan na kalleta kafin na ce"Wai sannu da aiki." Mirmishi ta yi mini ba ta yi magana ba..ni kuma da ban iya shuru na ce"Ke wai har yanzu ba ki daina wannan wahalan ba? Uwarsu na can gida tana hutawa, ke kin baro na ki yayan wajen ubansu, kuma kin zo nan kina hidiman na wasu." Dariya ta yi kafin ta ce"Kai Anty Sadiya ba ki da dama." Daman haka ta kan kirani, kai na girgiza kafin na ce"Tab. Wallahi Hauwa ba ƙanwar miji ko y'ar mijin da zan yi ma bauta, na yi ma mahaifiyarsa ita ce dole na, ko ita na yi a baya yanzun ma sai abin da ba a rasa ba." > Janaftybaby: Ni ba kaina na damu dashi ba saboda ban samu miji ba daman kuma ni burina sai na gama jami'a zan yi aure. Muna gabda gama zana jarabawarmu kawai Yaya Abubakar ya fara wani ciwo har da kwanciya a gadon asibiti ganin haka yasa na ce ba zan bari Ma'u ta kashe mini ɗan'uwa. Ni na je na samu Hajiya Dubu na faɗa mata duk abin da na sani. Ita kuma ta samu Alhajinmu ta faɗa masa abinda ke faruwa ni na ba da shaidar Gwaggo ma ta sani da aka kirata sai ta amsa amman ta ce Abubakar ɗin ya ce a bar mganar kar kowa ya sani kuma itama tana ta tabbacin ciwon nan saboda Ma'u ne. Alhajinmu bai yanke hukunci ba sai aka sallamo Yaya Abubakar daga asibiti Alhajinmu ya taramu a gaban kowa da kowa har da masu auran da Yaya Hamza da Alhaji ya sa ya dawo garin. A gaban kowa da kowa ya tsitsiye Yaya Abubakar sai da ya faɗi gaskiyan yana son Ma'u duk yadda ta yi ta masa inkiya da ido kar ya faɗa. Har Baaba an kirata tana wajen jin haka shima Yaya Hamza ya ce ya bar ma ɗan uwansa shi daman baya sonta. Hankalin Ma'u da Baba ya tashi saboda Alhajinmu ya ce an maida auran Ma'u akan Yaya Abubakar kuma ya yi ta faɗan cewa ba domin na zo na faɗa ba da an yi auren kuma azo ana neman mafita. Ban manta kallon da Ma'u ta yi mini a wannan lokacin ita da Baaba. A kuma nan take ta fashe da kuka ta ce ba ta son Yaya Abubakar Yaya Hamza take so shi kuma ya ce a ƙanwa ya ɗauketa. Alhaji ya rasa mafita yace zai yi mgana da sauran yan uwanshi. Har sai da su Baba Aminu su ka zo garin. A ɗakin Hajiya suka zazzauna suka tattauna Hajiya Dubu saboda samar da masahala sai ta kalli Alhaji kafin ta ce "Sule a shawarata kar ka matsa ma Ma'u ko Hamza. Tun da Hamza ya ce baya so. Abubakar ma yace ya hakura da ita to mu fasa wannan al'amarin kowanensu ya nemo mata itama ta nemo nata mijin mu aura musu sai na ke ganin kamar in muka yi haka za a samu mafita." Su Baba Aminu ma sun aminta da shawaran Hajiya kuma ita Alhaji ya ɗauka aka warware mganar auran Ma'u da Yaya Hamza har da Yaya Abubakar ɗin bayan an ce kowannen su ya zaɓo na shi matar daga waje. Wannan lamarin shi ya ƙara rura wutar kiyayya tsakani da Asma'u. Kwana biyu da faruwan lamarin na samu salama saboda ko banza itama ba ta samu abin da take so ba. Sannan Yaya Abubakar ba zai ga laifin Yaya Hamza ba. Ina kwance a saman gadon Hajiya ba ta ɗakin tana makewayi Ma'u ta shigo har ɗakin ta tsaya a kaina. "Lafiya Ma'u? Idanuwanta jajir ta kalleni kafin ta fara mgana cikin zafi." "Wallahi na tsane ki Sadiya. Na tsane ki." Nima kai tsaye na ce" To ai nima ba sonki nake yi ba Ma'u." Sai kawai ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Tun da kika zama silan rasa burina Sadiya ina so ki rubuta ki ijiye na rantse da sarkin da ke busamin numfashi sai na kuntata ma rayuwarki sai na saka ki a uku fiye da yadda kika sakani ko kin samu farinciki sai na yi sanadiyar lalatashi zuwa baƙin ciki. Kamar yadda na saba cin nasara akanki haka zan cigaba da nasara akanki har ƙarshen rayuwarki.". Kai tsaye nima na kalleta kafin na ce"To in kin fasa. Ta Allah ba ta ki ba. Aniyar ki sai dai ta biki. Kuma ban yi nadaman abin da na yi ba. Da ki ɓata mana zuru'a gwara ke ki rasa na ki burin na zalunci." Sai kawai ta yi kwafa ta fice a ƙofar ɗaki suka haɗu da Hajiya tana kiran sunanta ta yi banza ta wuce da ta shigo sai ta tambaye ni ko mun yi faɗa da Ma'u ne? Ina komawa na kwanta na ce" Ni ina ruwana da ita." Hajiya na faɗin" Sai hakuri ki rika kyaleta yanzu kin san ga abin da ya faru.' Ina jinta ban tanka ba. Tun faruwan lamarin bayan wani lokaci Ma'u ta warware Yaya Abubakar ɗin ma da sauƙi. Ta nuna ma kowa ba komai amman ni nasan ba ta hakura ba. Tsakanina da ita sai ya ƙara lalacewa. Ko da yaushe in ta fakaici idon mutane sai ta gaya min mgana nima sai na rama haka dai muka yi rayu cikin bata sona nima bana sonta. Jarabawar mu ta fito cikin ikon Allah ni da Ma'u muka samu ban da Rahila ba ta damu ba tunda aure za ta yi ni kuma ina ta murna zan fara jami' a. > Janaftybaby: Alhajinmu ya so ya hana Yaya Hamza ya matsa masa aka nema min gurbin karatu a jami'ar bayero a shashen tsumi da tattalin kasa economics. Ma'u kuma ta ce bording za ta yi sai aka nema mata Federal University Minna ko na ce ita ta nuna tana bukatar can ɗin. Saboda lamarin da ya faru bikin Rahila da Yaya Muntari ba a ma ƙara mganar shi ba sai zuwa gaba in zukata sun huta. Yaya Auwal kuma yana can keffi sai salla sallah ma ya ke zuwa ganin gida wani abun ma sai dai ya ji labari bai san faruwan shi ba. Na fara zuwa jami' a farkon shekaran 2002. Ma'u ma a shekaran ta tattara ta tafi Rahila kuma tana gida amman auran su da yaya Muntari ana tunanin karshen shekara tun da shima ya cigaba da karatunsa. A kuma lokacin ne Allah ya yi ma Hajiya Dubu rasuwa. Rasuwan da ta gigitani matuka. Na yi kuka domin har daren da za ta rasu mun kusa raba dare muna hira sai dai mun wayi gari ba ta raye tabbas ni aka yi ma mutuwa. Rasuwar Hajiya dubu da wattani uku lokacin muna jarabawar semester farko a makaranta na haɗu da Yusuf Muhammad Inuwa(Tafida) kuma mun yi aure da shi a ƙarshen shekaran 2002 rana ɗaya aka yi bikin mu tare da Rahila da Yaya Muntari. Kuma ana saura kwana talatin da biyar auran mu Allah ya yi ma Mama rasuwa daga kwanciya barcu ciwon ciki dare zuwa asuba ta ce ga garin ku nan. KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️13* Tun ranar farko da na fara ganin Yusuf na ji a raina tabbas na haɗu da namijin da ya gama cika zaɓina. Sannan na san tabbas zai iya yin katanga da cikar burina na sai na gama Jami'a na samu aiki zan yi aure. Saboda in na bari ya suɓuce mini samun kamarsa zai yi mini wahala Tun da gashi tuntuni ina tsumayen shi. Shi wanda ya dace ɗin amman ban samu nasaran haɗuwa dashi ba sai a wata ranar laraba. Daga cikin BUK na ke mun gama lacture tun safe har yamma na sha wahala ina tafe kamar zan faɗi, ba zan mata da kayan da ke jikina a ranar ba. Wata atamfa ce mai ruwan ganye hijabin jikina fari ne sai takalmin dake kafata mai saukaƙƙen tudu. Daga bakin get ɗin jami'ar da na fito ni kaɗai ce. Ko anan ɗin ma ban yi wata ƙawa da na saki jiki da ita ba a dai gaisa kawai. Ina tsaye ina neman abin hawa ba ni da masaniyar tun a lokacin Yusuf ya ganni kuma Allah ya haɗa zuciyarsa da tawa a waje ɗaya. Hauwa'u Jamilu ta fito tare da ƙawarta da tare na gansu Samira. Na gansu amman sai na ɗauke kaina kamar ban gan su ba, lokacin duniya na kwance sannan abubuwa duk ba su zama gari kamar yanzu ba. Ko wayar hannu nan sai wane da wane ke riƙe shi ko a ajinmu akwai ma su ita handset amman sai ɗaya ɗaya nima dai ina cikin mara shi. "S. Yashe sai gobe." Haka Hauwa'u ta faɗa sai na kalle su kafin na ɗan gyaɗa kaina. Ganin ina ta tsaye ban samu abun hawa ba sai na fara tafiya zuwa bangaren yamma su kuma su Hauwa sun yi gabas. Ina tafe ina sauri saboda yamma ta fara sauka biyar za ta iya gotawa a lokacin. Ban san ya na bina ba. Saboda ban ji takun tafiya ba sai da na ji sallamarsa cikin muryansa mai zaƙi da haiba ta maza masu kyau da Aji. " ƴan mata doguwa Salamu Alaikum." Haka ya faɗa da farko ban yi niyyar na juya ba amman yanayin muryansa da salon da ya yi magana su suka rinjayi tunanina da zuciya na ɗan waiwaya na kalle shi yana daga bayana kaɗan ina juyowa sai kawai ya yi mini mirmishi irin mirmishinsa da na ke matuƙar so a tare dashi. Na yi saurin ɗauke kaina na cigaba da tafiya amman na sauya takuna. Gaba na ta faɗuwa ban san so ba amman ina tunanin nima na fara son Yusuf a wannan ɗan kallon da na yi masa. Lokacin da na yi gaba ina ta fargaban Allah ya sa ya cigaba da bina ya yi mini magiya sai na yi masa kwatancen gidanmu. Har ɗan rage sauri na yi ina jinsa ya na cigaba da bina lokaci ɗaya yana sake faɗin. "Haba ƴan mata. Ina ta mgana shuru" Ɗan sake kallon shi na yi. Kai ya haɗu! Haka na faɗa a cikin raina ban wani saki fuskar da zai fahimci yanayina ba amman tabbas Yusuf ya shiga cikin zuciyata a karon farko da muka haɗu. Cigaba da bina ya yi yana min mgana amman ban tanka shi ba sai dai kuma tuni na gama haddace kamaninshi da kayan dake jikinsa. Tun a wannan ganin farko ni na san Yusuf ɗan gayu ne kuma yana da ilimi kuma shi ɗin daga ganin ɗan manyan mutane. Yana sanye da ƙananun kaya. Jeans baki ne sai T. Shirt fara ta na da zanen baki a jiki amman ban iya ganin me aka rubuta ba. Takalmin ƙafarsa mai rufi ne sannan akwai wasu takardu a hannunsa. Ta gefen ido na gama ƙare masa kallo a cikin zuciyata kamar in yi ta tsalle saboda murna. Tsayawa na yi ina taran abun hawa shi kuma sai ya ƙara marairaicewa yana faɗin. "Tafiya za ki yi ko muryan ki ba ki bari na ji ba? > Janaftybaby: Sai na kalle shi kafin na ɗan ɗauke kaina ina faɗin" Ya dace ka tari budurwa a hanya kana yi mata mgana? Da sauri ya ce"Afuwan. to ki faɗa min sunan ki sai ki bani lambar wayarki sai na samu lokaci na zo gida mu yi mgana." Kallonsa na yi sai ya yi wani sanyi kafin ya ce"Please." Sai kawai na rausayar da kai kafin na ce"Sunana Halima. Amman ana kirana da Sadiya." "Wow.! Nice name Sadiya ta." A karon farko da ya fa kirana da Sadiyarsa. Sai na yi mirmishi ina so na tambaye shi sunan shi amman na kasa. "Ba ni da waya. Gidanmu kuma na Ɗorayi in ka ce gidan Alhaji Sulaiman Yashe za a nuna maka." Ƙuramin ido ya yi kafin ya ce" Sadiya kin tabbata zan same ki in naje? Sai na samu kaina da ɗaga masa kai kafin na ce" In sha Allahu." Mirmishi ya yi mini nima sai na maida masa martanin mirmishi. Shi ya taran min motar haya na hau sannan ya ɗaga mini hannu kafin ya ce"Bye. See you " Ina so na ɗaga masa hannu amman sai na fasa sai dai na gyaɗa masa kai ina ɗan mirmishi. Na koma gida a ranar cikin farinciki har sai da Rahila ta fahimci yanayina. "Sadiya karatun yau hala ya fi miki daɗi ne? Sai na kalleta lokacin ina tsaye ne a tsakar ɗakin mu ina mirmishi ni kaɗai ban sani ba har Rahila ta shigo ta kama ni ina ta mirmishi ni kaɗai. "Me kika gani? Na faɗa ina kallonta sai ta ƙara matsowa kusa da ni cikin raɗa ta ce"Ko dai? Da sauri na matsa baya ina faɗin" Ko dai me! Ni matsa ki ban waje." Na faɗa ina tureta ina mata dariya. Daga tsakar muka ji Gwaggo na gaisawa da Ya Muntari. Sai na ga Rahila na mirmishi a raina na ce daman haka ake ji in ka haɗu da wanda kake so. Sai na daina ganin laifin Rahila akan Yaya Muntari saboda na fahimci haɗuwar jini ce. "Uhm kin ji muryan Yaya Muntari kin kasa sukuni." Sai ta harareni tana faɗin" Ya Muktar dai ko Sadiya? Ta faɗa ƙasa ƙasa. Ni ko ina ta dariya da gayya na fita tsakar gida dai dai zai koma can waje in da ɗakunsa suke da sauri na ce" Ya Muntari ina yini." Sai ya juyo yana amsawa kafin ya ce" Sadiya yan makaranta an dawo." Sai na amsa masa ina kallon Rahila ta cikin ɗakin mu tana faman harara ta. Ni kuma ina dariya. Yanzu saboda makaranta an ɗauke mini aikin gida sai in ranar weekend ne. Rahila ce da Amina ke yi tun da Ma'u na Minna sai an yi hutu ta ke zuwa ganin gida. Haɗuwata da saurayin da ban san sunan shi ba sama da sati ɗaya bai zo ba kuma ban ƙara ganin shi ba. Har in na fito daga cikin Jami'a. Na yi ta tsayawa ko da yaushe ina hasashen zan ƙara ganinsa amman shuru sai na fara damuwa. Ko ya zo ne bai gane gidan ba? Ko kuma dai! Na kasa iya fassara yanayin da na ke ji amman na rage walwala da fara'a kamar dai ina so na bayyana damuwar haka. In na kwanta sai na riƙa mafarkin shi tabbacin dai ya samu matsugunni a cikin zuciyata. Har na fara fidda rai domin an fi kwana goma da haɗuwarmu . Kamar wasa ranar da ya fara zuwa kofar gidanmu muka san juna sosai ranar laraba ne da yamma da wuri na dawo daga makaranta bayan na yi sallar la'asar na ci abinci sai na ɗan kwanta amma ba barci na ke yi ba. Na ji dai yaro ya yi sallama amman ban maida hankalina a wajen ba. "Wai Sadiya ta zo in ji wani a waje" Haka na ji an faɗa. Kamar an jeho ne sai gani a tsakar gida ina faɗin" Waye? Haka na faɗa ina kallon yaron Rahila na kan kujeran tsakar gida tana gyaran wake Gwaggo da Mama suna can ƙofar shashen Alhajinmu suna hira Amina na bakin ma zubar ruwa ta na wanke wanke. Gabaɗaya suka juyo suna kallona cikin mamaki. "Ni ma ban san shi ba." Sai da na juya ina kallon su Gwaggo sannan na dawo hayyacina. Sai kuma na yi sanyi na kasa motsi. "Je ka ce tana zuwa." Mama ta faɗa tana kallon yaron. Ya juya ya fita amman ni na kasa motsi daga in da na ke tsaye.. Rahila na dariya ta kalleni ta na faɗin" ki koma ciki ki ɗan gyara mana! Ko haka za ki fita? Sai na dawo hayyacina na koma ɗaki da sauri na sauya hijabina na duba madubi na gyara fuskata duk ina tunanin shi ne ko ba shi ba ne? Sai dai zuciyata na ta rawa. Na saka takalmina na fito tsakar gida bakina na rawa na ce" Zan je waje." Gwaggo ce ta tanka ni Mama ba ta ma a wajen ta shiga ɗaki. "To Sadiya. Amma kar ki daɗe saboda Alhaji." > Janaftybaby: Sai na amsa mata na juya na fita Rahila na yi mini dariya ganin yadda na yi wani sanyi ina tafe kamar ba na son tafiyar. Lokacin da na fita na ci karo da shi a tsaye a ƙofar gidanmu yau ya yi shigar manyan kaya ne. Yana tsaye ya na fuskantar ƙofar gidanmu hannayensa harɗe ƙirjinsa. Na ji lokacin da zuciyata ta ta yi tsalle ta dawo waje ɗaya lokacin da na ganshi. Sannan farinciki ya bayyana a saman fuskata lokacin da muka haɗa ido ya sakar min mirmishi nima na maida masa martanin mirmishinsa lokacin da na ke tafiya zuwa in da ya ke tsaye ya na kallona. Bayan mun gaisa ina noƙewa kai tsaye ya fara faɗin" Sunana Yusuf Muhammad Inuwa. Ni anan garin aka haife ni amman mahaifina da mahaifiyata mutanen Rano ne. Na yi karatuna har matakin Masters ranar da kika ganni ma a Buk na je ganin supervisor ɗina ne akan project ɗina. Sadiya da gaske na ganki kuma sonki sannan ina son in mun gama fahimtar juna iyaye su shiga ciki domin maganar aure." Bayan takaitaccen bayanin da ya yi min ban ja aji ba na bashi dama mun ɗan jima muna hira har Yaya Abubakar ya dawo ya ganmu suka gaisa da juna. Daga wannan lokacin ba a ɗauki wata biyu ba hatta Alhajinmu ya san da Yusuf sannan in ya zo zence a wajena a cikin gida muke yi. Zuwa lokacin kuma ni da shi mun gama shaida muna son juna sannan mun aminta mu zauna kan inuwa ɗaya ta aure. Na gama mutuwa a kansa kamar yadda shima ya gama mutuwa a kaina, kowa dake gidanmu na gidajen auran su da mazan gabaɗaya su san labarin YALLAƁAI da tun a lokacin na laƙaba masa wannan sunann tuni na watsar da tunanin sai na gama Jami'a zan yi aure ba zan iya jira ba gwara na yi auren sai na cigaba da karatuna a ɗakin miji. Ban taba sanin daga ɓarayin Yusuf zamu fuskanci barazana daga dangin sa ba. Duk da ya sha bani labarin gidansu da yan uwan shi na san suna da yawa tunda mata huɗu babanshi ya yi kafin rasuwarsa. Lokacin da muka haɗu da Yusuf a shekaru iyakarsa 27 to 28 ni kuma ina cikin shekarata ta ashirin na kuma san ya karanta Architecture ne masanin zane zane bai samu aiki ba amma yana buga buga. Mutum ne mai sabgogi da yawa da kuma ƙoƙarin neman na kansa. Yusuf ya turo magabatansa daga Rano. Ya ce mini ƙanin mahaifiyarsa ne da ƙanin mahaifinsa sun zo sun gana da su Baba Aminu an ba su damar dawowata ta gaba za a tsaida mgana. A wannan gabar ne Alhajinmu ya gudanar da bincike a hakan Yusuf har na samu cikakken bayanin waye shi da asalin shi. * Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa kafin rasuwarsa ya yi aiki a Ministry of Agriculture and natural resources. Ya rasu a shekaran 1999. Ya bar mata huɗu da tarin ya'ya guda 21. A kimanin ƴaƴan da haifa ashirin da takwas ne bakwai sun rasu. Sannan bayan rasuwarsa da wattani matarsa ta huɗu ta bi bayan shi Hajiya karima. Ɗan boko ne da ya yi shura tun a zamanin baya da boko bai yawaita ba. Sannan sun shiga gwamnati an dama da su sosai ta sanadin wani amininsa Alhaji Yusuf wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Rano. Shima ya rasu tsakanin shi da abokin nashi shekara ɗaya ne shima ya rasu ya bar mata biyu da yaya maza da mata. Alhaji Muhammad Inuwa da Alhaji Yusuf Tafidan Rano sun fito daga jiha ɗaya ne. Wato Rano sai kuma suka haɗu a makarantar kwana ta Barewa collage dake zariya. Ajin su ɗaya sannan ɗakin kwanan sy ma ɗaya ne. Daga lokacin suka fara aminta bayan sun gama sun nemi jami'a ɗaya ta Usman ɗan fodiyo University. Kowanne ya karanta bangaren da ya zaɓa shi Alhaji Inuwa sai ya yi karatunsa kan harkan Noma da tattalin ƙasa shi kuma Alhaji Yusuf Tafida sai ya kan harkan sanin Siyasa. Bayan sun gama karatun su sun samu manya ayyuka. Shi Yusuf a matsayinsa na jinin sarauta na Tafidan Rano yana da hanyoyin isa ga Gwammatin kano a lokacin. Dukkansu kowanen su ya je ya ƙaro karatu kuma dalilin Alhaji Yusuf Tafida rano Alhaji Inuwa ya tsinci kansa a Ministry of Agriculture na gwammatin Jihar kano a wancan zamanin. > Janaftybaby: Alhaji Muhammad Inuwa ya fara aure da Hauwa'u(Nene) wacce haifaffiyar Rano ce kuma duk an san juna. Kuma a sha'anin bikin ne Alhaji Yusuf Tafida ya haɗu da ƙawar Nene Aminiyarta Fatima Binta(Hajiyar Tafida) Sai Aminan junan suka aure ƙawayen junan. Dalilin haka sai zumumcin su ya ƙullu a tsakaninsu mai ƙarfi. Kuma ya samu kafuwa har zamanin ƴaƴan su. Shi dai Alhaji Yusuf Tafida kafin rasuwar ya ƙara mace ɗaya Hajiya kaltume. Ita ce ke da jibi da masautar kano kuma har ya rasu ƙaton gidan shi na nan a Rano. Amman dai yana da gida a cikin garin kano shi kuma Alhaji Inuwa a cikin garin kano ya gina ƙaton gida a gwammaja mai shashe da yawa daga nan Nene ta fahimci Mijin nata yana da ra'ayin zama da mace sama da ɗaya. Ya kuma tabbatar mata tun da sai da ya yi mata huɗu jeras sannan kuma dukkansu matan sun haifa masa zuru'a. A bangaren ɗakin Nene Zuwaira ce Babba sai Maimuna. Sannan ta yi Bahijja. Sai da ta yi mata uku sannan ta samu namiji sai Alhaji Inuwa ya cika burinsa ya sanya masa sunan Amininsa Yusuf suna kiran shi( Tafida) a kuma a tsukin Hajiyar tafida itama ta sauka an samu namiji itama sai kawai shima Alhaji Yusuf ya saka masa sunan Amininsa Inuwa suna kiran shi(,Tariq) a kuma lokacin a gidan su Nene mahaifinta matan shi biyu mahaifiyar su Nene Innayi ta daina haihuwa amman abokiyar zamanta Hannatu( Inna) ta haifi ɗan ta Namiji sai ya ci sunan mahaifinsu Abdulmu'iz sai suna kiran shi da Abba shi ne kuma auta a gidan su Nene sai ya kasance waɗanan mazan guda uku sun tashi tare sun girma tare sun kuma ba da misalin kyakyawan zumunci juna a tsakanin su. Bayan Yusuf sai Muttaƙa sai auta Halimatu. Sai Maman Farko(Hajiya Saliha) ita yar kano ce ita ta ɗan fi Nene yawan ƴa'ƴa domin ƴaƴanta bakwai ne. Usman shine Babba wanda Zuwaira da Maimuna ne ke gaban shi a tsarin manyan gidan sai shi. Bayan shi sai Nasaratu ita sa'ar Tafida ne sai Nasir sai Jafar sai Suwaiba da Jamila autar ta mai suna Hindatu. Daga ita sai Hajiya Zaliha(Hajiya iya) ita ƴaƴanta huɗu ne. Hafsat ce babba sai Saffiya sai Muhammad kabir sai Musbahu. Sai ta huɗun da ta rasu Hajiya karima ita ƴaƴanta uku ne. Ummu Salama sai Adnan Jawahir ce ƙaramar su. Kuma bayan rasuwarta riƙon su Jawahir ya koma ya koma ƙarkashin kulawar Nene. Kaf ƴaƴan Marigayi Alhaji Inuwa kamar shi sun yi ilimi sun kuma tsaya da kafafun su. Ba matan ba sannan ba mazan ba wasu sai sun gama karatun suke auren wasu kuma suna cikin yi suke auren sai su ƙarisa a gidan mazajen su. Yusuf dai ya yi karatunsa na fimari kaf a garin Rano ne a gidan Alhaji Yusuf Tafida tare da Tariq da kuma Abba. Sannan bayan sun gama ya nema musu makarantar kwana a kaduna mai suna. Federal Sceince and tecnical collage (FSTC) Kafacan Kaduna. Su uku tare suka yi makaranta tun daga matakin fimari har matakin gama babban sakandiri daga nan sai Yusuf ya tafi Abu zaria. Tariq ya tafi jami'ar Ibadan shi kuma Abba ya tsaya anan BUK ya yi karatun shi. Sun gama degree farko kuma kowanne ya zaɓi in da ya ke so ya cigaba da karatunsa. Shi Tariq Jami'ar lagos ya koma ya yi masters ɗinsa shi kuma Yusuf ya dawo kano ya yin da Abba bai cigaba ba ya koma Rano ya fara kasuwanci da noma tunda abin da ya karanta kenan. Yawancin zaman Yusuf ba a kano ba ne ya fi zaman Rano shi ya sa akwai sabo na musamman tsakaninsa da yaran gidan Marigayi Tafida, kuma a gidan ba a kiran sunan shi sai dai Baaba. Ita kuma Hajiyar Tafida ta ce Tafida mutun ɗaya ce ke kiran shi da Daddy Saudatu(Gimbiya) ƙanwar Tariq ce. Kuma ta ci sunan gimbiya ce matar sarkin Rano a wancan lokacin. Mganar aurena da Yusuf ta yi barazana domin yan'uwansa sun ce ba zai yi ba ya yi gaggawa sannan bai gama karatu ba kuma ba shi da sana'a mai ƙarfi sai buge buge. Kuma shi Yusuf Mutun ne da ba ya son zama a ƙarkashin wani ya fi son ya zauna in his on. Ban taɓa ganin mutun mai tsari irin Yusuf ba ya karanta abin da ya shafi zane zane amman kuma ya na da sani kan abin da ya shafi gini da sauran su. > Janaftybaby: Tun kafin mu yi aure ya sha faɗa mini so ya ke yi ya buɗe kamfanin shi na kan shi ba ya ƙaunar aiki a ƙarkashin wani ya fi so ya cika burinsa na yadda zai gina kansa domin ƙara ma matasa karfin gwiwan kan dogaro da kansu. Bai taɓa faɗa mini yan'uwansa sun ƙi auran mu da farko ba sai daga baya saboda lokacin da suka ƙi sai ya kai su ƙara wajen kawun nan na su sna bangaren babansu da ke Rano su suka shige masa gaba akan mganar auran mu. Daga karshe da suka ga ya dage sai suka hakura suka bar shi ya yi. An saka rana ba lokaci mai tsawo ba sai aka sanya shi lokaci ɗaya da na su Rahila. Abu kamar wasa kamar mafarki sai ga shi abu ya tabbata kowa ya ji zan yi aure sai ya yi mamaki kamar irin su Ma'u da ba haka ta so ba sannan da ta ga Yusuf sai ta fahimci na tsere mata ko ba ta fada mini ba a fuskarta na ga hassada da kishina. Duk da rasuwar Mama ta saka an ƙara wata ɗaya kafin auran mu mutuwar da ta gigitamu har Alhajinmu da har gobe ya kasa manta rashin Mama. Da Gwaggo da ta daɗe cikin jimami shi ya sa a sha'anin bikin ba a yi wani taro sosai ba. Amma dai kayan ɗaki komai iri ɗaya ni da Rahila babu in da aka bambamta mu ni a anguwar Dakata muka fara zama ita kuma Rahila nan cikin anguwan Ɗorayi ne tana kusa da gida. A tsarina ban taɓa tsara ma kaina fara rayuwa a gidan Haya ba. Amman sai gashi nan ne muka fara shimfiɗa rayuwarmu ni da Yusuf. Ya san ina karatu kuma ya yi alƙwarin barina har na gama karatuna. Mun sha amarcin mu sosai na ke jin daɗin zama da Yusuf in zan je makaranta wani lokacin har rakani yake yi in bai da wajen zuwa in shima yana da shiga makaranta sai mu jira juna mu koma tare. Yana samun kira haka in ana son zane sannan tun lokacin yana karambanin karɓan kwangila gini sai ya nemo ma'ikata da injiniya. In na ce a zamana da Yusuf bai gatanta ni ba na yi ƙarya. Ya yi mini hidima da jikinsa da Aljuhunsa. Nene ta karɓe ni a matsayin surukarta. Amman ban da yayyen Yusuf da suke uwa ɗaya barin ma Anty Bahijjan sai bayan auran na ke sanin sun so hana auran mu a cewar su ya bari zuwa gaba sai ya auri Gimbiya. Sai daga baya na fahimci Gimbiya na son Yusuf soyayyar da ba ta iya ɓoye shi. Shi kuma ba ta gan shi a ƙanwa ma ya ɗauke ta. Suna son haɗa auren ne saboda amincin iyayensu amman kuma hakan bai yuyu ba. Farkon auran na yi musu biyayya kamar zan bauta musu saboda dai ina auran ɗan'uwansu. Kuskurena na farko shi ne na yi tunanin yin tsarin iyali saboda karatuna sai dai cikin Jidda shi ya zo ya shammace ni. Watanni tara da kwana huɗu da aurenmu na haifi Jidda da ta ci sunan Nene Hauwa'u. lokacin ina aji biyu ne zan shiga uku na sha matukar wahala ga ciki ga karatu ga aure shi ya sa ina yaye ta na nemi shawaran Yusuf akan ina son in yi tsarin iyali shi kuma sai ya ba ni goyon baya muka je wani asibitin kuɗi na fara karɓan allura duk bayan 6 months har na shekara biyar. Daga wannan alluran sai ta zame mini matsala. Na gama karatun kuma ina son na ƙara haihuwa amman shuru ko domin goron su Anty Bahijja tunda suna ganin na daɗe ban ƙara haihuwa ba bayan Jidda sun ta zargin ko planning na ke yi amman ban faɗa musu ba tunda kamar na tona asirin kaina ne. A kuma lokacin muka shiga rayuwa na halin babu. Yusuf ba aiki yake yi ba. Sannan aikin da ya kan samu ya ragu sai jifa jifa. Duk wani abin da na ke dashi sai da ya kare na zo da ɗan kunnen gold wanda na siya da sadakina amman sai dai na siyar da shi. Da cewar Yusuf in ya samu anam gaba zai siya mini. Saboda haka ya sa na nemi aiki a makaranta kuɗi anan kusa damu na fara koyarwa saboda mu rufa kan mu asiri. Ba zan raina ba in Yusuf ya samu na samu to amman yanayin aikinsa kafin ya samu fa? Kuma na yi na yi ya nemi aiki shi yaƙi a dole sai ya tsaya da kafafunsa. Ta ina za ka iya samar da kamfani baka da kuɗi? Zan iya cewa renon jidda ma tare muka yi tun lokacin ina makaranta tare muke zuwa ya rike mini Jidda har mu fito daga karatu ko ya kai ta gida wajen Nene. Da na fara Koyarwa shi na ke barin ma a gida kafin na dawo ya gama duka aikin gida har girki ma ya yi. Kuma albashina ba na iya cin komai dashi ɓukatunmu na ke yi mana dashi. > Janaftybaby: Sai dai yan'uwan shi duk ba su ga haka ba a tunaninsu na tsaida haihuwa ne saboda Yusuf bai dashi ni ma na fara damuwa sai na fara yawon private hospital ana ce mini ba matsala zan ƙara haihuwa sai da Jidda ta kai shekara Takwas da wattani na ƙara haihuwan y'a mace sai ta ci sunan Anty Maimuna muna kiran ta Baby zuwa lokacin kuma Yusuf ya samu buɗi tunda har ya siya fili ya fara gini muma kuma Alhamdulillah muna cikin ni'imarsa. Na sha wahala a haihuwan Baby C.S ma aka yi mini daga nan kuma sai na yi ta samu matsaloli na zubar jini da kasala sai juwwa. Daga baya sai na fara ramewa sannan haihuwa ta zo ta tsaya mini cak sai na fara jelen gen zuwa ganin likitoci a asibitocin kuɗi suna cin kuɗina suna gaya mini ba matsala in sha Allahu zan ƙara haihuwa. Tun ina ɓoye lamarin har ya fallasa ga dangin Yusuf tsarin iyali na yi ya ba ni matsala shi dai ya ce bashi ba ne ya faɗa sai na yi tunanin Ma'u tunda itama bayan ta gama karatu ta dawo gida ba daɗewa ta haɗu da Alhaji Mustapha cikin wattani kaɗan suka yi aure sai wayan gari na yi na ga Ma'u tsudum a cikin dangin mijina. Saboda sanin Yusuf a harkan kwangilan gine gine sunan shi ya ɓace daga Yusuf zuwa Injiniyan da ya yi ma haye. Sannan da tsarina da shawarata mu ka samar da sunan kamfanin shi. HM TAFIDA AND SON LIMITED." Hauwa' u and Maimuna kenan da sunana ya so ya saka saboda gudun mgana na ce mu saka na ƴaƴanmu. A can zariya road ya kama office ɗin kuma ya yi ma kamfanin sa rigister. Ya taimaka kwarai wajen samun kwangiloli masu tarin yawa. Kuma balle ya san jama'a connenction ɗin shi da mutane yasa har Gwamnati na bashi aikin kwangila. Akwai kwangilan da ya samu na gina wata makarantan koyon aikin Jinya ta ƙanin marigayi Alhaji Yusuf Tafida. Wanda shi ne yanzu a matsayin Tafidan rano yana aiki a ministry of education. Yusuf ya samu alheri sosai da shi ya ƙarisa mana gini sannan na bashi shawaran ya buɗe gidan buɗo saboda yanayin aikin shi. kuma ya yi na'am cikin lokaci kaɗan ya buɗe gidan Buɗo. Mun tare a sabon gida bayan ɗaukan shekaru sama da biyar ana ginin shi. Tsarin gidan da komai tsarina ne Yusuf kuma ya yi zanen sanan yan kwangilanshi suka gina gidan da jagorancin. Tarewarmu a anguwan lodge road. Yusuf ya hana ni aiki ya ce na zauna a gida na huta. Duk da ina da ra'ayin fashion na shiga makarantar koyon kwalliya da gyaran kai. Har zanen shagon da Yusuf zai buɗe mini ya zana amman har yau bai tabbata ba. Amman hidimdimu ba za su bari hakan ya samu ba. Tun da muka koma wannan gidan ƴan'uwansa suke tunanin ina can na samu daula kuma ban haihuwa sai kwanciya ina cin daula sun manta irin gwagwarmayan da muka sha a baya komai Yusuf ya samu ko ya mallaka tare da ni aka mallake shi. Ko bayan tarewarmu a sabon gida sun so ya ƙara aure domin Gimbiya ba ta yi aure ba har Masters ta yi. Da ta ga dai Yallaɓai na Sadiya ne ita kaɗai sai ta hakura ta auri wani tsohon sanata matansa uku ita ce ta huɗu. Ta na can Abuja kuma har ta samu aiki da NGO. A shekaru sama da goma sha huɗu da wattani da aurena da Yusuf na san me ake kira aure da gwagwamarya. Ba zan ce ba mu taba samun matsala ba mun sha samu tun da ni ina da saurin fushi ga baki shi kuma yana da sanyi wani lokacin amma in ya yi fushi ba shi da kyau. Mun sha samun matsala akan ƴan uwan shi mussaman Anty Bahijja da Anty Maimuna. Daga karshe shi sai ya bi bayan ƴan uwan shi ya bani rashin gaskiya. Nene dai ba na ce ta taɓa nuna mini kiyayya ba. Ban taɓa samun matsala da ita ba shi ya sa na ke yi mata biyayya iya iyawata. Sannan akan zamantakewa ma muna samun matsala amma sai mu shirya kan mu a tsakaninmu. Amman matsalan da muka sha samu da ya yi ƙamari shi ne akan Gimbiya. Ban samu salama ba sai da ta yi aure. Yusuf ya samu kusanci sosai da Gimbiya itama kuma ba ta sakin jiki da kowa sai shi in na nuna fushi ko kishi sai ya ce ina da matsala ina da zargi. Kuma sai ta zo gidan Nene shi kuma in ya je ya biye mata ya kai dare har kwalliyan da na yi sai ya lalace in na yi mgana sai ya ce bai san lokaci ya tafi ba suna can suna hira da Gimbiya. > Janaftybaby: Ban samu salama ba sai da ta yi aure sannan na ji hankalina ya kwanta amman fa da in na ji zai je Rano yini na ke yi zullumi. Da shekaru suka gangara haka sai nima na fahimci an gogi jigida. Na daina matsa ma kaina kan wasu abubuwan tun da na fahimci ni ba zan ga karshen su ba nima ba za su ga karshe na ba. Sannan irin wannan matsalolin ana samun su a kowani dangi. Sai dai na wata ta fi wata. Nene ce dole ne ita ne kawai ban daina yi ma biyayya ba amman sauran duk abin da na ga zan yi shi na ke yi. Na daina tsoron a ce na yi ko ban yi ba saboda shekaru sun gungura nima wuyana ya isa kaurin da na isa ga kaina. Shi ya sa na ke tafiyar da rayuwata da ga ni sai mijina sai ƴaƴa na. Sauran abin da ya fi ƙarfina na bar ma Allah ni yanzu abu ɗaya ne a gaba na. Ina son na ƙara haihuwa ko domin Yallaɓai mai son yara sosai. KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️14* Present. Da safen tea muka sha gabaɗayan mu amman ban da Yallaɓai saboda kamar akwai gajiya a tare dashi. Tun bayan da ya dawo daga sallar asuba ya kwanta yana ta barci sai na ƙyale shi tun da na ga har wayarsa ma sai da ya kashe. Da wuri Saude ta zo na saka Jidda ta fito da kayan na su. Daga kitchen ɗina akwai wata kofa dake fidda mutum ta can baya in da muke yin wanki ko shanya. Ko tara ruwan sama can na ce su je su yi wankin har da Baby da ta saka rigiman sai ta yi na ce a ƙyaleta ta yi. "Umma ba fa wanki ta iya ba. Ɓata jikinta kawai za ta yi da ruwa." Ina ɗakin na su ne a lokacin ina gyarawa saboda Saude ba za ta samu lokaci ba gwara ni na gyara gidan. Kallon jidda na yi da ta shigo kawo min karan Baby. "Bar ta yi. In ta jiƙa jikinta ai shike nan ta huta." Haka na faɗa ina mirmishi saboda ni dai na san ina kamar ta ban so aiki ba amman tunda tana so ai ba zan hana ta ba. Wucewa Jidda ta yi amman ranta bai so ba sai na bi ta da kallo ina dariya. Jidda akwai son aiki da karambani in da ta biyo ni da na shiga uku. Har yanzu da shekaru suka tura ba na son aiki barin ma girki, ko anan domin ya zame mini dole ne na ga ba mai yi mini. Saude daman in ta zo sai dai na saka ta yi ma yara. In da Allah ya so ni da Rahama Yallaɓaina bai da tsirfan cewa ga abin da zai ci duk abin da na kwaɓa na bashi yana maraba. A baya kafin na samu Saude na wahala sai dai in Marwa ta zo mini hutu. Marwa babbar ɗiyar Yaya Aina ce. Lokacin da ta ke gida kafin ta samu makarantar koyin aikin jinya a garin tsafe na more ta saboda yarinyar tana matuƙar sona. Shi ya sa nima na ke son ta ina kuma kyautata mata. Ba ta zuwa gidan kowa hutu sai gidana in ta zo ba na komai sai dai na ci na kwanta Yallaɓai ya yi ta mini tsiyan daman haka na ke so na kwanta na yi ta laushi ni kuma na ce na ji ba komai. Marwa ba ta da ƙiyuwa. In ta zo har wankin kayana da guguna tana yi min kayan su Jidda sai dai na fito na ga ta wanke ta shanya, budurwa ce mai kimanin shekaru 20 zuwa da ɗaya. Duk da ni da uwarta ba sosai muke yi ba amman kuma Allah ya haɗa jinina da Marwa kuma ina daraja haka saboda yaran Yaya Murja ba sa zuwa gida na amman gidan Ma'u kam suna zuwa mata hutu. Har gwarama Firdausi ta wajen Yaya Balki ta kan zo wajena ban da su Anti. (Aina) sunan Yaya Aina a ka sanya mata sai ake kiran ta da Anti ita ce babba a ɗakin Yaya Murja ƙannenta huɗu duk maza ne. Ni bai dame ni ba domin kowa ya san halina ka yi da ni, ya ka ƙare ballantana ma ba ka yi da ni ma gabaɗaya. Allah na tuba gari da yawa ai maye ba ya ci kansa ba shi ya sa ina yi ma Marwa abin alheri har ɗinkuna ina yi mata lokacin da ta samu makaranta tsafe siyayya na yi mata mai yawa kuma har da ni a masu rakata, sannan in dai ta zo gida hutu ko da ba za ta daɗe ba sai ta zo gidana ba ta daɗe ba ta yi mini sati ɗaya. Sau tari in zan siya abin mata na kwalliya uku na kan siya saboda Marwa. Ita tunda ta fara amfani da su bra da pad in dai na fita kasuwa siyayya ina siya mata na ijiye in ta zo hutu ko ba ta zo gidana ba ina aika mata dashi na ce Yaya Aina ta iijiye mata. Ban taɓa jin na damu da ta gode mini ba koma me na yi nima ai uwar Marwa na ke, kuma abin da ke tsakanina da mahaifiyarta ba zai taɓa shafanta ba. > Janaftybaby: Ko kafin in gama gyara gidan har sun gama wankin duk da bai da wani yawa daga uniforms ɗin su sai kayan barcin su. Ko daman ita Saude akwai ƙokari a shekaru iyakarta 17 ko ta gota da kaɗan ne. Na ɗan taya su shanya wajen sharce kayan. Bayan mun gama na ce Saude ta yi ma Baby tsifa ita ma Jidda ta kwance kan ta in wanke musu. Tun da ba su samu zuwa kitso ba sai in yi musu da kaina. In kana da ƴa'ƴa mata koyon kitso ba zai zama wani abu mai wahala ba. Kuma daman ina da mai kitson tun ta can anguwan dakata da muka ta so bayan mun dawo nan tana zuwa gida ta yi mana ina biyanta ranar da kuma ba ta samu zuwa ba na kan kira Salisu ne ya zo ya ɗauki su Jidda ya kai su. wani lokacin in ta gama yi musu kitson yarta ke dawomin da su ranar da ba su samu zuwa ba na yi musu da kaina tun ban ƙware ba har ba ƙware kaɗan kaɗan. Da na so sai la'asar zan je gida amman sai Amina ta sake kirana tana faɗa mini duk yau Yaya Hamza da Yaya Auwal za su koma sai na yi tunanin na tafi bayan azahar. Yallaɓai bai tashi ba sai da na gaji har wajen sha ɗaya saura bayan na wanke tiolet na jiƙo hannuna na zo na tura masa a cikin ƙirjinsa da sauri ya buɗe ido sai a cikin idanuwana. Ɗan ɓata rai ya yi irin na masu barci ni kuma sai na yi masa mirmishi. "Yallaɓai a tashi haka nan. Kalli fa rana ta yi." Na faɗa ina buɗe masa labulen window ɗin bedroom din. Ai sai ya kauda kai har ya na juyawa zai cigaba da kwanciya. "Yallabai. Haba mana" Na faɗa cikin yar shagwaɓa amman sai ƙara shigewa da kansa ya yi cikin bargo lokaci ɗaya cikin shaƙewar murya cike da barci ya ce. "Sai azahar za ki tashe ni. Kin ji". Ya faɗa ya wani ƙara sakin numfashi sai na saki baki kawai ina kallon shi na buɗe baki in yi mgana wayata dake kan dressing mirro ta ɗau kiɗa alamun kira sai na bar wajensa na isa wajen wayar. "FaridaAisha." Faridan Tariq ce. Haka na faɗa a fili kafin na juya ina kallon Yallaɓai lokaci ɗaya ina faɗin" Ka gani ko? Ƙila ma Tariq ke neman ka ka kama ka kashe waya kamar wanda ya kwana aikin gajiya." Na san ya na jina amman bai yi motsi ba sai ni ce na taka zuwa gefen gado na zauna sannan na ɗaga kiran "Maman biyu." Daga can bangaren ta ce"Matar injiniya." Da fara'a muka gaisa sai ta ke ga ya min sun shigo garin ita da Tariq suna Gwammaja suna son ƙarisowa gidanmu amma an kira wayar Yallaɓan nawa a kashe Da sauri na ce"Yau hutu ya ke ji tun da ya dawo sallar asuba ya kashe wayarsa. Amman ai yanzu yana jin mu. Za ku samu ƙariwan kuwa? "E. Amman a tsaye gaskiya saboda daga nan sai kaduna in sha Allahu " Ina buɗe baki kamar ta na ganina na ce"Kai. Yau kuma! Ba ku bari zuwa gobe? Tana yar dariya ta ce"Mai gayya ne ya ce yau za mu tafi" Ina dariya na ce"kuma an gama mgana ba." Sallama muka yi ta ce suna tafe. Muna gama wayar na juya ina kallon Yallaɓai amman bai tashi ba sai na miƙe ina faɗin" Yallaɓai ga su Tariq nan da iyalansa don Allah ka tashi ka yi wanka ka ƙarya kafin su kariso" Dakyar da soɗin goshi na samu Yallaɓai ya tashi. Hararan shi na yi lokacin da na ga ya miƙe ya na miƙa. "Gajiyar duk ta mene ne? Sai da ya sargafo hannayensa ta saman wuyana muna kallon juna kafin ya ce" To kuma me ye na tambaya? Duk tsawon gajiyar da kika tara min ne na wannan watan na ke safkewa" Ya ƙarishe yana ɗage mini gira. Ture hannun shi na yi daga kafaɗata na wuce ina faɗin" Ni ban ce ka tara min gajiya ba sai kai? "To ke wani ƙokari kike yi ban da abin ki. Ni ke fa aikin." Ya faɗa yana biyo bayana. Juyawa na yi muka haɗa ido kafin na yi masa wani kallo sai kawai ya fara dariya ni kuma sai na rausayar da kai lokaci ɗaya ina faɗin" "Au! Haka ka ce ko? Na nuna shi da yatsa kafin na cigaba da faɗin" Kai nan har wani ƙokari gare ka? Ba domin ni ba Yallaɓai uhmm." Na faɗa ina cije baki. Yana dariya ya ce" Sadiya ki ji tsoron Allah." Na juya zan fita ina faɗin" Za mu haɗu ne anjuma zamu ga mai ƙokari da mara ƙokari " Ta baya ya rumgumeni yana faɗin" Just a good morning Hug." > Janaftybaby: Dakyar na tura shi Tiolet ya yi wanka kafin ya fito na soya masa yar sauran doyan da ta rage sannan na dafa masa ruwan tea mai haɗin kayan shayi. Ƙananun kaya ya saka tunda yau ya na gida a saman dining na zauna har sai da ya gama karyawa. "Yallaɓai daga yau in dafa sauran shinkafar nan komai namu ya ƙare na kayan abinci." Na faɗa ina kokarin tattara kayan da ya yi amfani da shi. "Kafin Anjuma ɗin Allah zai kawo mafita. In sha Allahu." "Allah ya sa." Haka na amsa ina mai fita daga falon zuwa kitchen. Na leka su Saude na ga Baby tana hawaye ana mata tsifa daman ita akwai zafin kai ita dai Jidda har ta tsife nata. Ina dariya na ce"Baby ki bari a yi tsifa an juma Babanki ya ce zai si yo miki ice cream kin ji? Jin haka yasa ta washe baki. Sai na ce to a daina kuka in ta na son shan Ice cream. Fita na yi daga ɗakin na rufo musu kofa duk da na yi wanka ina bukatar na ƙara tun da tun safe ne. Ina wanka su Farida suka iso domin na ji lokacin da Yallaɓai ya fita ya buɗe musu get Tariq ya shigo da motarsa shi ya sa a gurguje na gama wanka na fito na shirya na saka riga da sikat na wani material sai ga Yallaɓai ya shigo. "Ke sun fa ce suna kan hanya ne." "Ga ni nan zuwa Sorry." Sai ya juya ya fita ya na faɗn" Ki taho musu da ruwa." Sai na amsa da to. Mayafi na saka na rufe jikina sannan na biya ta kitchen na ɗauko musu ruwan gora a fridge da kofuna guda biyu bayan na saka a faranti. Ina shiga falon Farida ta zo ta tarbeni. Falon ya yi albarka Baby ta ga yan biyu sai wasa suke yi, ƙila babansu ya kira su su gaida baban na su, Jidda ba ta falon tabbacin ta koma ciki. "Sannun ku da zuwa." Na faɗa ina sauke ruwan saman center table ɗin da ke gaban Yallaɓai da Tariq. "Yauwa Sadiyar Yallaɓai. Ai ina nan ina masa tsiyan yau ko ba ya so mu ganki ne ya ɓoye ki? Ina dariya na zauna a kujeran kusa da Farida. "Haba dai ko ɗaya. Ina wanka ne lokacin da kuka shigo." Tariq ya jinjina kai kafin ya ce" yan hutu. Shi ma ai yanzu ya ke faɗa mini bai daɗe da tashi barci ba." "Shi ne ɗan hutu. Amman ni tun asuba ban koma ba." Farida na hararan mijinta ta ce" Shima ɗin ya na fin haka ma yana barci." Yallaɓai ya ce" to daman mana. Ni da suka raina ne suka saka mini ido shi da kawunsa Abba." Tariq na dariya ya ce" Tafida yarinyar nan fa ta kirani. Ni dai kawun ka ya kusa kashe min aure. Madam fa ta ƙi yarda da rantsuwata shi ya sa na matsa mu zo ga ka ga Sadiya ƙila tafi yarda da mganar ku." Ina dariya Yallaɓai na dariya Farida ce ta haɗe rai kafin ta ce" To na sani ko sabuwar budurwa ya yi. Kira kan kira" Ina dariya ne amman ina auna wawancin Shema'u kina mace ki zama mai arha haka! Amman tuna wacece ita sai ban yi mamaki ba. "Maman biyu kar ki yarda. Tabbas ni ma kwanaki nan ban gane masa ba duk yadda aka yi ya fara neman aure a boye." Yallaɓai ya faɗa ya na haɗe ai sai Tariq ya kasa magana amman ya buɗe baki. "Uhm. To Allah ya ba shi sa'a." Farida ta faɗa kai tsaye ganin ta ɗan shaka sai na karɓi mganar ina faɗin" ƙyale Yallabai.' Nan na faɗa mata abin da ya faru a jiya duk da ta na nuna ba ta damu ni na san ta damu. "Ku kam ba abokan rufin asiri ba ne. Daga kai har tazurin kawun ka." Tariq ya faɗa yana ture hannun Yusuf dake saman kafaɗansa. Farida na dariya tana bamu labarin sun je gaida innayi sun haɗu da Uncle Abba shima dai tuburewa ya yi da bai san zencen ba shima Yusuf ga abin da ya ce. "Ai gaskiya ne. Mu ba mu san yadda aka haihu a ragaya ba." Yallaɓai ya faɗa yana dariya sai Tariq ya miƙe ya na fadin" Madam lokacin mu ya ƙare anan fa." Itama sai ta miƙe tana rataya jakarta. Dukkanmu sai muka miƙe gabaɗaya ina faɗin daga zuwa sai tafiya. "To ai zuwan daman na a gaisa ne. Muna nan muna jiran ku ke da Yallaban na ki dai." "In sha Allahu." Na faɗa, muka bi su har waje ina yi ma yan biyu wasa. Kamar na sani na sako yar dubu ɗaya daga ɗaki shi na bama yaran ganin Farida ta zo ma da su Jidda bickit mai yawa. Sun shiga mota ina bangaren Farida ina yi mata sallama. Yallaɓai kuma suna bakin motar shi da Tariq suna mgana. "Man sai yaushe kenan? > Janaftybaby: Tariq ya buɗe mota ya shiga lokaci ɗaya ya na faɗin" Ai ni ƙila sai ranar da tuzurin kawun ka ya samu matar aure in za mu je tambaya sai na shigo." Dariya suka yi har suna tafawa. Ni ko sai na ce" Kawun ku ke ma haka? To ai ba ku za ku yi masa tambaya ba." Tariq na dariyan mugunta ya ce" har auran ma za mu karɓa masa. Gaya min su wa za su je? To iyayen duk sun tsufa sun kare mu ɗin dai mune rufin asirin sa. Tafida ka bar gemun ka ya taru nima haka saboda na ga kamar kawun na ka ya fara maganar aure. Ko wani lokaci zai iya neman mu." Dariyan su suka sha suna tafawa nima ni da Farida muna ta ɗan dariya. "Sai mun yi waya. Allah ya kiyaye hanya." Yallaɓai ya faɗa bayan sun ƙara musabaha da Tariq. Shi ya bude musu get suka fita muna ɗaga musu hannu Allah ya sa baby ta samu biskit da ta yi rigiman sai ta je. Mun dawo cikin falo na kalli Yallabai ina faɗin" Duk abin da kuka faɗa akan Uncle Abba sai na faɗa masa." Yana ƴar dariya ya ce" To wai shi ne me? In ba ki da kati ki yi mini mgana sai na saka miki." Kafaɗansa na kai ma duka ina dariya shima yana tayani. Mun zauna kan kujera ɗaya muna hira nan ne na ke gaya masa zan je Ɗorayi da wuri saboda yau su Yaya Auwal za su koma wajen aikin su. "Ok. Zan kai ki ne da kaina? "No. Ka bari dai sai ka je ka ɗauko ni" Sai ya gyaɗa mini kai sai na mike na wuce da farantin ruwan da na kawo ina faɗin. " Bari na je na wanke ma su jidda kan su." Da kai ya amsa min, sai na bar masa falon gabaɗaya. Kitchen na biya na sauke kayan hannuna sannan na shiga dakin su Jidda na ga sun gama tsifan har Saude ta ƙara share ɗaki. "Saude je ki wanke min sauran kofunan da suka ɓaci bari na wanke musu kai tare za mu tafi ɗorayi." "Umma ba kin ce za ki yi mana kitso ba? Jidda ta tambaya ne, sai na kalle ta kafin na ce" Sai na dawo ko zuwa dare ne." Mayafin jikina na cire na shiga tiolet ɗin akwai mayukan wanke kansu a ciki tunda daman rabi na kan raba na su da nawa. Kuma daman na iya ni nake yi ma kaina wankin kai ni da yayana a gida tunda ina da handrayer. Ruwa na tara mai ɗumi sannan na kira Baby na fara wanke mata sannan jidda a karshe, bayan na gama na fito na jona handrayer na busar musu da gashin gabaɗaya na shafa musu man kitso Jidda ita ta ƙara taje kanta ta daure da band ni kuma na yi ma Baby duk da ana yi ta na kuka har sai da Yallabai ya leƙo yana faɗin" To a kyaleta mana tun da an gama" Ina kallon shi kafin na ce" Za a dai gama amma ba a gama ba." Sai da na matse na samu na daure mata gashin. Yallaɓai ya ɗauke ta yana lallashinta lokaci ɗaya yana share mata hawaye, domin har da majina saboda kukan. "Ba ki son gashin ne? Yallaɓai ya faɗa duk cikin sigan lallashi sai ta gyaɗa masa kai, da sauri ya kalle ni kafin ya ce" Sadiya to a yi ma Baby aski ba ta son gashi balle ta rika kuka ko? Sai ya kalleta kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin" Ba na son aski." Yallaɓai sai ya kalleni kafin ya ce" To a bar mata gashin ta shi ke nan? Ya sake kallonta sai ta gyaɗa masa kai, rumgumeta ya yi, ni kuma me zan yi in ba dariya ba. Jidda ma ta na ta dariya Yallabai ya sunkunci Baby ya fice ya na faɗin" Tunda kun yi faɗa da Umma sai a ji da Abba ko? Bin bayan su na yi bayan na ce jidda ta ƙara share ɗakin saboda gashi. Ganin har an kusa azahar sai na bi Saude kitchen na ce bari kawai na dora farar shinkafa ina da sauran miya sai a ci da shi kafin mu tafi. Ni da na so fita tun bayan azahar sai gani har karfe uku sai da muka ci abinci na sauya kaya sannan na bar ma Yallaɓai amanar gidana da yarana ina ta ƙara jadadda masa. Sai kawau ya ce" Na ji mai gida. Kina ta mini kashedi megadi ne ni? Ina dariya na ce" Kamar haka! Tun da ko a ina aka je gida na Sadi baby ne." Na ƙarishe faɗa ina masa fari sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce" Hausawa suna cutar mu. Kai da guminka sai ka ji ana gidan Sadiya." "Ko gidan Maman jidda ba." Na faɗa ina yi masa dariya. "To ba a cewa na Baban jidda." Yadda ya yi mganar ne yasa har ina riƙe ciki wajen dariya. Mun rabu sai mangariba zai zo ya dauke ni bayan ya sake duba Alhaji. > Janaftybaby: A daidaita muka samu zuwa Ɗorayi a kofar gida muka yi sallama da Saude bayan na ce ta gaida mamanta. **** Ɗorayi. Ko da na je gida cike da ƴaƴa da jikoki. Domin kaf su Yaya Murja da yaransu suka zo tun da yau lahadi ba makaranta. Na iske har Ma'u tare da Zainab da su Alhaji ƙarami. Rahila ce kawai ba ta zo ba wai ba ta jin daɗi Mutanen Abuja dai sun riga sun tafi saboda nisa. Sai Yaya Hamza ne shi ma lokacin da na zo suna sallama ne za su ɗau hanya. Amina kuma za ta bi su su rage mata hanya daga zariya sai ta hau motar kaduna. Da ta ce sai gobe megidanta zai zo su koma tare to shima sai daga baya ya kirata ya ce suna da taro a wajen aiki da wahala ya samu zuwa. Ya dai yi ma Alhajinmu sannu ta waya. Tunda mijin Amina lacara ne a jami'ar kaduna. Kallon ta na yi lokacin da muka samu keɓewa a ɗakin Mama ina faɗin" Ke yanzu da sai ki tafi ba mu yi sallama ba? Ta na yar dariya ta ce" Ai na san kina hanya." Gyara zama na yi kafin na ce" Tun da Datti ya koma ya zo gidanki weekend kuwa? "A'a ya ce suna ta test ne. Zai zauna a cikin makaranta ya yi karatu. Ƙila sai sun gama zai taho.' Sai na jinjina kaina. Saboda Datti a farkon shigarsa jami'ar a gidan Amina ya fara zama amman sai aka samu matsala tun da akwai wani ƙanin mijinta a gidan da suka yi ta samun matsala da Datti har lamarin na neman shafan auren Amina tunda kowa kanshi ya sani. Sai Yallaɓai ya ba da shawaran gwara ya samu hostel ya koma can da zama, Allah ya sa ma akwai wani abokin shi ɗan nan kanon ne shi ya bashi waje a ɗakinsa suka yi sukwatin. Sai dai ya na ɗan zuwa wani lokacin ya yi ma Aminar weekend. "Mubarak ɗin ma ba ya nan yanzu. " Ita ta katse min tunani Mubarak sunan kanin mijin na ta. "Me ya faru? Har ya gama karatun? "Ban sani ba. Amma ina kyautata zaton kamar ya samu matsala ne duk da yayan na shi baya son faɗa mini. na san ya na Aji uku ne sai ya tafi can zuntu sama da wata biyu bai dawo ba gashi ana ta karatu sai na yi zargin wataƙila ya samu matsala ne a can makarantar." Sai na gyaɗa kai kafin na ce" Za ta iya yuyuwa. Ke dai tunda ba a faɗa miki ba. To ba ruwan ki." Tana dariya ta ce" Haba. Kamar ba ki sanni ba' Aiko na san Amina miskila ce kafi mahaukaci ban haushi, mun ɗan yi hira sama sama kafin Khaleesat ta leƙo ta na fadin ta fito su wuce ni na riƙe mata karamin akwatin ta muka fito suna falon Alhajinmu muma sai muka shiga can. "Na gode ƙwarai. Allah ya kai ku lafiya." Alhajinmu ya faɗa ya na ɗan kishigiɗe a saman kujera. Ya na riƙe da Amna Tasleem na kusa dashi. Khaleesat ta duka a kusa da Mijinta ta na faɗin" Allah ya ƙara lafiya Alhaji sai mun ƙara dawowa." "Allah ya sa. Na gode Allah ya yi muku albarka gabaɗaya." Muka taya su amsawa da Amin mune rakiyar har waje bakin mota gabaɗayanmu ba mu iyayen ba, sannan ba yaran ba. Sai da suka ɗaga muna ɗaga musu hannu suna ɗaga mana. Har sai da motar su ta ɓace ma ganin mu sannan muka koma cikin gida. Aneesa ɗiyar Anty Balki ce ta tambayi su Jidda na ce suna gida, a ɗakin Mama muka yada zango gabaɗayan mu tun da an ce a bar Alhaji ya huta ɗakin Gwaggo kuma ta ce Baaba na ciki tana barci kar a dame ta. A kusa da Yaya Aina na zauna ina faɗin" Wai su Marwa ba su samu hutu ba ne? Kai tsaye ta ce mini" Sun kusa fara jarabawa. In ta dawo za su fara pratical a asibiti to babanta ya ce ta dawo gida ta yi kawai." "E. Gaskiya ai yafi. Ni ko wai ba ta da waya ne kwanaki ina ta kiranta a kashe " "Ta lalace tana saka layinta a wayar wata ƙawarta ce." Sai na kaɗa kai kafin na ce" Haba shi ya sa ba na samunta. Ta dawo sai a gyara in ba ta yi sai a siya wata amman ba ta zauna ba waya ba." Yaya Balki ta yi karaf ta ce" Tun da tana da uwa Sadiya ba" Sai na fashe da dariya kafin na ce" Kwarai kuma matar Injiniya ba." Yaya Aina na dariya amman ba ta yi mgana ba. Yaya Murja na zaune waje ɗaya da Ma'u sai da suka jiyo suna kallon mu, sai na yi kamar ban gansu ba muka cigaba da hiranmu da su Yaya Aina. Muna nan zaune sai ga Zaituna ta shigo fakam fakam kamar an jeho ta. > Janaftybaby: Yaya Balki ce ta yi mata mgana da cewa" Daga ina? Ɗazu mijin ki ya fita ya na cewa ba ki zo ba? Ruwa ta ce a bata sai da Aneesa ta kawo mata pure water biyu ta shanyen su tana maida numfashi. "Wallahi na ɗan je barka ne. Wata yayarmu ce ta haihu." Daga ji ƙarya take yi saboda sai wani faman kifta ido ta ke yi kamar wacce ta yi ma sarki karya. "Za ki ci abinci ne? In ji Yaya Murja ai da sauri ta ce" Wallahi kamar kin san ina jin yunwa. Can anguwa uku ne ba mu samu abin hawa ba sai da muka ci uban tafiya duk abincin da na ci ya gama zazzagewa." Su Ma'u na dariyanta ni ko ban yi dariya ba saboda ban ga abin dariya ba. Kallonta na ke yi kamar wata mahaukaciya ta hana kanta zaman lafiya saboda shegen shige shigenta ta kuma hana ɗan uwan mu ya huta. Firdausi a ka kira ta zubo mata jallop ɗin shinkafa da wake ta zauna ta na ci hannu baka hannu ƙwarya da Yaya Aina ta ce ta ci a hankali sai ta fake da cikin goyo tunda a lokacin ta na da goyon mai sunan Yaya Hamza. Ba ta lura da ni ba sai da ta ci ta koshi sannan ta ganni. "Sadiya daman kin zo? Yanayin maganarta sai ya yi kama da ta renin wayau. Amman ta juya ta na yi ma Ma'u magana. Sai na ji ya kamata na rama na nuna mata matsayinta, sai kawai na kalleta kafin na ce" To daman ina za ki ganni kin shigo kamar an koro ki" Na faɗa ina kallonta. A raina ina faɗin Yaya Abubakar ya haɗu da jarabawa na auran wannan matar, iyayenta talakawa ne ba su da komai Yaya Abubakar ne ke tallafe da su, yayanta namiji sai shaye shaye ƙannenta sai bin yan iskan anguwa amman ba ta duba haka ba ita ce yau cin bashi ita ce kafa adashe ta cinye ta sha shiga rigima Yaya Abubakar na fidda ta ina tsoron wata rana kar ta ɗauko abin da zai gagare shi ta saka a ɗaure shi. "E na shigo ban ko gani na shawo tafiya" Kai tsaye ina kallonta na ce" Wata tafiya? Ko dai yunwa domin daga ganin ki yunwar ce ke ɗawainiya dake daman." Yaya Balki na yar dariya ta ce" Da alama kam." Ita kuma sai ta wayance da cewa" Ban tsaya a gida na yi abinci ba ne, kuma can ɗin na kaɗan na ci kuma ga tafiya cikina duk sai ya zazzage" "Ke kam Zaituna me zai hana ki tsayawa a gida ki yi abinci? Shi ya sa Yaya Abubakar da ya shigo ɗazu ya ce a zuba masa abinci ashe da yunwa kike barin shi." Yaya Balki ta faɗa tana kallon ta kafin ta samu zarafin mgana Yaya Aina ta karɓe da cewa" To ta ina ma mace na da miji da ƴaya za ta fita ba ta yi girki ba? Ai ko fitar sassafe ce ka yi dai ko fara ba mai ne kafin ka fita." Ina gyara zama na ce" Ta saba ne. Ita fa Zaituna ba ta son komai ba sai shigen yawo da shige shige. Ko mu nan da kika ganmu sai mun yi abinci muke fitowa daga gidajenmu ballatana ke." Na faɗa ina kallonta sai tafara kame kamen wai ita ina ta ke zuwa karaf ko Yaya Murja ta ce" A a Zaituna. Kina da shigen yawo kullum ba ki iya zaman gidan ki. Na rasa gidan wa kike zuwa da ya fi gidan mijin ki? Har ta na rantsuwan wai ita ba in da ta ke zuwa ko da yaushe tana gida ba domin rashin lafiya Alhaji ai ta fi sati ba ta fita ba, Ma'u na dariya ta ce" Ko ana gobe rashin lafiya Alhaji kin biyo gidana kika ce daga anguwa kike hanya ta biyo da ke? Ko ba a yi haka ba? Ta faɗa tana kallonta ganin an ƙure ta sai ta wayance da cewa ta tuna sun je gaisuwa can ɓarayin su Ma'u shi ya sa ta biya ta gidanta. Ganin ta na neman sauya hirar ya sa na kalleta ina mai kiran sunanta. "Zaituna kenan. Ki daina ma karya kowa ya san halin ki nan kwanaki na ji an ce kin cinye kuɗin adashen mutane har da yan sanda suka dauko miki, to ni dai ba zan ce ki bari ba amman in kika ɗauko rigimarki ki riƙa tsayar da ita a kan ki ko akan dangin ki, ki bar ɗan uwana ya huta duk kin tsufar da shi kin saka shi a uku, kar ki kashe mini ɗan'uwa gwara ma ki daina abin da kike yi." Sai ta kasa mgana Yaya Balki ta ce gaskiya ne Yaya Abubakar duk ya fara tsufa saboda wahala da rashin kwanciyar hankali. > Janaftybaby: Yaya Murja sai ta taɓe baki kafin ta ce" Ai Allah ya bashi wasu kudaɗen sai na ce ya kara aure ita kuma ta je can ta ƙarata, ka rasa abin da take siya da kuɗin da ta ke rigima komai dai dai gwargwado ya na yi miki zaituna me kika nema kika rasa? Ganin mun yi mata taron dangi ya sa ta fara kuka tana murza idanuwana. Yaya Balki ke faɗin" Me ye na kuka? Domin fa muna sonki ne ya sa muke gaya miki gaskiya da wasu dangin ne wallahi sai dai ki ji wata maganar, to ki ɗauka mu muna sonki ne shi ya sa muke faɗa miki gaskiya domin ki gyara." Yaya Aina ta karɓe da faɗin" Kwarai da gaske in wasu dangin mijin ne ita kanta ta san ba za su ɗauka ba. Faɗan ke so kan ki muke yi miki ki gyara saboda ke ba yarinya ba ce kin san abu mai kyau da mara kyau, in kika bari ya yi zuciya ya ɗau wani mataki akan ki ba za mu saka baki ba to kafin akai ga haka ki sauya rayuwar nan da kike yi, ki zauna a gidanki ki fita daga shiga rigima tunda ba abin da mijin ki ya rage ki da shi' Kowa na ta tofa albarkacin bakin shi, Yaya Murja dai ta ƙare mganar da cewa" Ke ko koyi ba za ki yi da su khaleesat da Laila ba? Dube su kowacce tsaf ita da ƴaƴanta, kuma suna rawan jiki akam mazajensu suna tattalin su amman ke ba wannan a gabanki sai shirme, to ki fara gyara kanki da gidanki in kuma ba haka wata rana za ki yi nadama." Ma'u ta saka baki tana faɗin" Ki rika kwalliya Zaituna. Haba kamar ba mace ba, ba ki gyara balle ki gyara ƴayan ki? Namiji fa na son gyara kuma in kika gyara wallahi sai ya ji daɗi" Nima na yi mata nasihan ta daina zama kaca kaca ta zauna a gidan ta gyara kanta tana kuka tana mana godiya tare da alƙwarin ta daina muna mata fatan haka daga nan sai muka saki maganar muka shiga wata hira ana mganar Baba Sani zai tafi gobe su Yaya Hamza sun bar kuɗi a ba su Yaya Aina ta ce in muna da wani abu mu haɗa masa ko in akwai mai sabulai da omo mu kawo ni dai na ce ina da sabulai zan aiko da safe Ma'u ta ce za ta ga abin da za ta aiko, har da kaya ma Yaya Balki ta ce tunda wancan zuwan da suka yi Matar Baba Sani ta mata zencen kayan yara haka suna so. Yau dai zaman gwanin daɗi ba faɗa ba bakar magana kowa ya binne abin da ke ran shi, Yaya Aina ce ta kalli Ma'u lokaci ɗaya tana faɗin" Ke ko Ma'u dangin babanki na neman ki yanzu? Sai ta yi shuru kafin ta ce" E. Muna waya da wasu daga ciki can kwanaki ma wata wacce da mamanta da babana uwar su ɗaya uba ɗaya ta zo wajena har ta yi kwanaki. Ni dai na daɗe ban je ba amman Alhaji ya ce in ya samu lokaci za mu je mu gan su." Yaya Murja ta yi karaf ta ce" Ba dole su neme ta ba. Sun ji labarin ba ta wulakanta ba. Ta na da abin duniya." Yaya Balki ke faɗin" To daman ai sai an san kana da amfani ake nemnka. Lokacin da suka san su za su wahala da ita ai ba su damu ba. Sai yanzu da suka san za su more ta. Ba komai abin da ta ke dashi ta yi musu ba shike nan ba." Ni ko ina gefe na ce shiken nan kuwa. In kana da shi ka yi in baka dashi ne in baka yin ba matsala. Ita dai sai gyaɗa kai ta yi tana faɗin in sha Allahu. Sallar la'asar ya tashe mu a wajen, bayan mun idar da sallah na shiga ɗakin Gwaggo na gaida Baaba ta amsa kamar yadda ta saba amsa mini. Daga nan ɗakin Mama na yi shigewata ina duba wayata su Firdausi ne a tsakar gida suna shara wasu na wanke wanke su Yaya Murja na baro su ɗakin Gwaggo. Tun da su sun rigani zuwa karfe biyar Yaya Aina ta yi sallama ta wuce gida bayanta Yaya Balki tare suka fita da Zaituna ni ma sai na yi shirin tafiya har Ma'u na fadin ta ɗauka sai dare zan tafi, da haka na so amman sai na tuna zan yi ma su Jidda kitso ba zan zauna jiran Yallabai ba. "Tafiya zan yi. Na yi ma su jidda tsifa zan kama musu kai gobe makaranta." Yaya Murja na gefe ta ce" Da kin zo da su Firdausi ta yi musu." Sai na ce mata ban yi tunanin Firdausin za ta zo ba ne, ina shirin tafiya Munirra ta kirani a waya ta na tambayan muna asibitin ne ko gida? Sai na ce mata muna gida sai ta ce mini gata nan zuwa ita ta tsayar da ni na jirata har sai da ta zo na rakata falon Alhaji ta gaishe shi. "Matar ƙanin Yallabai ne Alhaji" "Allah ya yi mata albarka. Na gode.". > Janaftybaby: Har da kankana ta kawo masa Gwaggo na ta godiya, mun dawo ɗakin Mama sai ga su inna Mariya sun zo duba Alhaji ta ce Amina ce ta faɗa mata jiya shi ne ta ce bari ta zo ta duba shi, dalilin haka yasa na daɗe a gidan tun da sai bayan sun tafi tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u, sannan ita Munnira ta ce min ba daɗewa za ta yi ba na fito rakata har bakin gida bayan ta yi sallama da su Gwaggo ta ke ce min. "Ke na taɓa ki da alheri matar Yallaɓai. Kin ji Yaya Usman zai kara aure? Ban samu zarafin mgana ba ta cigaba da faɗin" To yanzu ma mganar da ake yi Anty Zabba na gidan su. " Cikin nuna mamakin na ce"Wai har yanzu ba ta koma ba? Munnira ta ce" Ina fa ta koma, a bakin Nasir na ji wannan satin mai shiga Yaya Usman ɗin zai zo, na so kiran Anty Zabba sai na fasa kar ta ce ina da son jin gulma" Ina mata dariya na ce" Wallahi haka za ta ce." Munnira ta kama haɓa kafin ta ce" Shi ya sa ban kira ba. " Na ce gwara hakan itama Munira ta na faɗin ba ta ji daɗi ba, koma mene da ta yi hakura ta zauna tunda matar na shi ba akanta za ta zauna ba. "Uhm ke dai Munira Allah dai ya kyauta ya dai dai ta su." Ta amsa min da Amin Amin daga nan muka yi sallama na koma cikin gida sai na ga Aneesa da wayata wai ana ta kirana ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne da sauri na ɗaga kiran. "Yallaɓai ka taho ne? Cikin wani irin murya ya ce min" Sadiya ta congratulation." Ina yar dariya na ce" Yallaɓai ka biya mini makka ne? Shima dariyan ya yi kafin ya ce" In sha Allahu ina saka ran haka, amman dai yanzu ina so na faɗa miki ne an biya ni half payment na aikin nan namu na Rano." Cikin murna na ce" Don Allah fa Yallaɓai" "Allah Sadiya ta. Yanzu kuɗin suka shigo sun kuma kirani sun faɗa mini." Ɗakin Mama na faɗa ina faɗin" Alhamdulillah mun yi kuɗi" Ya na yar dariya ya ce" In an yi mangariba zan fito sai na zo mu dawo tare" Da haka muka yi sallama, muna gama wayar na yi hamdala ina jin daɗi Allah ma ji roƙon bayin shi. Na ƙosa mangariba ta yi ma saboda murna, ina idar da sallar mangariba na shirya lokacin har Yaya Murja ta tara yayanta sun tafi gida ni da Ma'u kawai ne a gidan ita kuma tana tare da Baaba. Yallaɓai sai bayan isha'i ya zo, ya ƙara duba Alhaji sannan na yi musu sallama muka tafi gida. Muna hanya ya kalle ni kafin ya ce" Yanzu da me zamu fara Hajiya ta? Ina dariya na ce" Mu je gida mana Alhajina." Sai muka kalli juna kafin mu kwashe da dariya, ni ko har ina dukan kafaɗansa kafin na ce" Ranka ya daɗe mai girma Tafida." Shi dai ya na ta dariya ni kuma ina masa kirari "Angon Sadiya Ɗan gatan Nene, uban Jidda da Maimuna. Allah ya ƙara ja zamanin Tafida mai girma Injiniyan gine gine, mai muƙamin zane zane takawar ka lafiya" Ya na dariya ya ce" Me kike so Sadiya? Ina masa dariya na ce" Me kuwa na ke so? Yallaɓaina kaɗai na ke so." Gira ya ɗaga min kafin ya ce" Kin yi kyakyawan zaɓi kuwa." Muna tafe muna hira, har muka isa gida. Baby har ta yi barci, dole na tashe ta tana kuka tana komai na yi mata kitso, Yallaɓai na ta faɗan wai ban iya kitso ba ne na saka yarinya tana kuka. Baki sake na kalle shi kafin na ce" Au ban iya ba ko? Ya na kallona ya ce" To ni dai ban san lokacin da kika koyi kitso ki ka iya ba" Sai kawai na yi banza da shi Jidda dai lafiyan lau muka yi kitson mu, sai bayan na gama mu su ne na ce su yi shirin kwanciya Baby daman Babanta ya lallasheta har ta yi barci. Wanka na sake yi na yi shirin kwanciya Tea na haɗa mana muka sha sannan muka zauna kassafa kuɗi, abu na farko kayan abinci na yi masa mgana sai kuma na ce ya ijiye kuɗin makaranta yara tun da sun kusa fara jarabaawa. "A'a ki bari sai zuwa lokacin ai da sauran lokaci." Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda na san wataƙila zuwa lokacin ya zo babu, mun yi mgana ya cire wasu kuɗi saboda Gidan bulo da office sai na yi masa mganar Halima ta haihu ba a yi mata komai ba sai ya ce zai turamin 20k ya ce a siyi abin da ya kamata ina so na ce ya rage min ko kaɗan a cikin kuɗina amman ban yi ba kamar ya san me na ke tunani sai ya ce "Zan ba ki 50k ki rike a hannunki. Kuɗin ki kuma in gwammati ta biya mu sai na baki duka in sha Allahu." > Janaftybaby: Ina yar shagwaɓa na ce" Yallaɓai buɗe saloon ɗin fa? Da sauri ya ce" Wannan ni na ce zan buɗe miki, kuɗin ki kuma haƙƙn ki ne zan biya ki in sha Allahu." Sai ya ga na yi shuru sai ya shafa kumatuna kafin ya ce" Kar ki damu. In sha Allahu duk za a yi." Sai na gyaɗa masa kaina. Mun cigaba da lissafi ya ce 30k na kayan maggi da kayan tea, sai na ce ai ya haɗa gabaɗaya cikin na kayan abinci tunda tare muke siya a kasuwa a wani babban shago yana da lambar wayarsa list ɗin kawai zan rubuta ya tura masa da ƙudin har gida za a kawo mana kayan abinci. Har da sabule da omo, ni kuma sai ya ce zai ƙara mini 30k saboda siyayyarmu ni da yara su Unders da sauran kayan kwalliyan mata. Kuɗin asibiti kuma ya ce zai ware mini 50k saboda bamu san nawa za a nema ba sai dai goben in mun je mun gani. Sauran kuma ya ce zai yi amfani zai sallami sauran ma'aikata da shi ko da rabi rabi ne, ni na san har da kyatttuka sai ya yi in dai Yallaɓai ya samu kudi kamar suna masa kwaiƙwayi ni na yi masa mganar Nene, daman in za mu yi siyayya kayan abinci har da ita da kayan tea sai sabulan wanka sai ya ce na rubuta list ɗin gabaɗaya sai ya tura babban shago za a kawo kayan zuwa gobe in sha Allahu. Sai na ce to a daran na rubuta abin da na manta na ce zuwa da safe zan tuna. Saboda zuwana asibiti tun asuba na tashi na yi ma yara shirin makaranta Yallaɓai jiya ya siyo indomie da kwai , sai buredi sai na soya musu buredin da tea ɗin suka tafi da shi makaranta, ni kuma muka shirya daman tun safe na tura ma Dr Fatima saƙo sai ta dawo min da amsar za ta ƙara kiran Dr Aisha ɗin amman na je asibitin na siya kati za a kai ni gynea unit ɗin in ce dai Dr. Aisha na zo gani a shigar mata da Fayel ɗina za ta duba ni in sha Allahu. Tare muka fita da su Jidda muka kai su makaranta daga nan muka wuce Aminu kano. Da taimakon Yallaɓai nan da nan muka siya kati har aka yi mana hanya zuwa Gyea Unit da taimako irin masu zirga zirga rarraba katina Yallaɓai ya yi ma ihsani, ya faɗa mai mun zo ganin wata Dr Aisha bukar ne. Wajen ta zai kai mini Fayel ɗina sai ya ce ba matsala ba ta ƙariso ba amman tana hanya. Sai wajen tara da wani abu likitocin suka fara zuwa. Muna zaune da Yallaɓai bangaren yan jira aka shigar da Fayel ɗin mu, Saboda ihsanin da Yallaɓai ya yi mishi sai ya shiga ciki ya yi ma Dr Aishan bayani sai ta ce eh ta na sane fayel ɗina daman a sama ya saka min ni ce ta farkon da aka fara kira na shiga ganin Dr Aisha Bukar kamar yadda ke rubuce jikin Office ɗinta. KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️15* Aminu kano Teaching Hospital. Gynecologist Unit. Ina zaune a kan kujeran da ke fuskarta wajen zaman likita. Idanuwana kir a kan Dr Aisha Bukar ina ƙare mata kallo. Ta fi Dr Fatima shekaru ita babbar mace ce gaskiya a kallah in ba ta haura 40 ba za ta tsaya a hakan ta na da kaurin jiki, ga tsawo ga kiba sannan ba ta da wani haske sosai. Tana zaune tana duba fayel ɗin gabanta gefe ɗaya kuma hankalinta na kan system ɗin dake gabanta da alama dai akwai abin da ta ke dubawa a ciki. Fuskarta da gilashi siriri sannan sanye take da rigan likitoci kanta kuma ta sanya ƙaramin breziya Hijab fari. "Sadiya Sulaiman Yashe" "Maa." Ba ta kalle ni ba hankalinta na kan system ɗin gabanta ta ce" Ke ce wacce Dr Fatima ta yi transfer ɗin ki daga ABU KO? Sai na gyaɗa mata kai lokaci ɗaya da cewa" Yes" Saboda da turanci ta yi maganar. Tsayin mintina goma sannan ta ce" Ga Report ɗin ki da ta tura mini ina kan dubawa." Da hausa ta yi mganar wannan karon kafin ta dawo da hankalinta kaina. "Sunana Dr Aisha Bukar. Zan cigaba da jagorantar matsalarki har zuwa lokacin da za ki samu waraka in sha Allahu." Ba ta jira jin ta bakina ba kawai ta cigaba ta faɗin. " A yadda na ga ɗan brief na matslar ki, kafin mu je kan matakan da muke ɗauka ga masu irin laluran ki, kin san abin da ke damun ki? Ko dalilin da ya sa ba ki sake haihuwa ba? Na ɗaga mata kai zan yi mgana kawai cikin zaƙin muryanta ta ce. "SECONDARY INFERTILITY" Kai tsaye kuma ta cigaba da bayanin ta. "Kuma shi Secondary infertility ( rashin samun ciki bayan mace ta haihu ko hayayyafa) yana faruwa ne lokacin da mace ta haihu sai kuma haihuwa ta zo ta ɗauke kwata kwata ayi ta nemanta ruwa a jallo amma bata samuwa wani lokacin har sai an dangana da asibiti. Mace a haihuwar farko ta san lafiyarta lau saboda ta samu ciki ba tare da neman taimakon likita ko shan magani ba, amma kuma daga nan sai haihuwar tayi ɓatan dabo." Nan ma sai ta ɗan dakata kafin ta cigaba da faɗin. "Yawancin abubuwan da ke haifar da secondary infertility sun haɗa da low egg quality(wato kwan haihuwar mace ya kasance baida karfin haihuwar) matsalar mahaifa, matsalar rashin karfin maniyyi, yanayin abinci da wasu abubuwan wanda suka danganci rayuwar mace kama daga yanayin cututtuka da uwa uba Family Planning" Ta ɗan ɗago ta kalleni ganin ina kallonta sannan hankalina na kanta ya sa ta ɗan gyara zama gilashin ta sannan ta sake cigaba da faɗin. "Babban abunda ke kawo secondary infertility musamman a kasar hausa shine family planning wato tsarin iyali. Yawancin mata idan sunyi tsarin iyali yana haifar masu da matsaloli wanda cikin matsalolin nan babbansu shine sanadin family planning. Family planning na haifar da jinkirin rashin samu ciki da wuri saboda karfinshi da kuma aikin da yake a productive system na mace Kama daga hormones har zuwa Reproductive organs "Kuma kowani abu ya na da Siide effect, kuma shi planning yana ninka adadin shekarunsa sau ɗaya ma'ana zai iya haurawa da kashi ɗaya, wani lokacin har biyu, kamar ke ɗin nan kin yi na shekaru biyar amman ya haura ki har shekara tara ba ki haihu ba, sannan kafin ki samu ciki side effect ya taɓa ki kin ta samun matsaloli ko? Ba ta damu da na amsa ba ta cigaba da faɗin. > Janaftybaby: "Secondary infertility kuma mace ta taɓa haihuwa sai ta zo ta hanyar planning ko kuma haihuwar ta tsaya mata chak, shine za ta je asibiti ayi aune aune sai a bata maganin da zai dakile karfin planning din nan da kuma wanda zai taimaka mata wajen buɗe mahaifar ta da hormones ɗin don a samu cikin, kamar irin problem ɗin ki kin gane? Sai na gyaɗa mata kaina alamun gamsuwa. Tana mgana da hausa ta na haɗawa da turanci a maganarta kawai na fahimci ita ɗin kanuri ce saboda ba ta da hausa sosai. Fayel ɗina ta jawo ta fara rubutu kafin ta ce" Kafin mu kai ga ɗora ki kan mgani Akwai bukatar sai kin yi wasu gwaje gwaje kamar yadda tsarin mu ya ke." Mintina sama da biyu sannan ta sake ɗagowa tana kallona kafin ta ce" "Muna da gwaje gwaje a kallah guda tara waɗanda sai kin yi su gabaɗaya ne za mu iya gano ta in da matsalar ki take, da kuma hanyar da zamu ɗora ki kan mgani." Gwaje Gwajen da ake sun haɗa da 1.A semen analysis (mace da namiji zasu tara, sai a tara sterile container a debi sperm din daidai lokaci da namiji ke kawowa, da gaggawa ake yin awon sbd kada sperm cells din su mutu kafin ayi awon wanda hakan zai iya lalata sakamakon da ake bukata a wannan awon ne ake gane cewa sperm din namiji na active zai iya haihuwa ko aa. 2.Blood tests to look at hormone levels (zai nuna level din hormones, suna over secreting ne ko under secreting) 3.A transvaginal ultrasound 4.A hysterosalpingogram, a type of X-ray that allows your provider to see your uterus and fallopian tubes( wannan da x-ray machine ake yin shi,zai nuna cikin mahaifa da kyallemun mahaifa duka honestly speaking its painful) 5.Blood tests. Samples of your blood can be tested for a hormone called progesterone to check whether you're ovulating. ... 6.Chlamydia test. Chlamydia is an STI that can affect fertility 7.Pap smears 8.FSH follicle Stimulatiing Hormone 9.LH Luteinizing Hormones All these are the most common primary and secondary fertility tests for women." Ta na gama yi min bayanan ta miƙo mini takardan mai tambarin sunan asibitin a jiki, hannuna biyu na saka na karɓa ita kuma sai ta maida hankalinta a wajen system ɗin gabanta. "Ki je lab ki kai musu, za su yi miki cikakken bayanin a can" A sanyaye na ce" Yanzu Dr? "Yes. Ki je yanzu a can za su ƙara miki ƙarin bayani da yadda za a yi." Sai na miƙe ina mata godiya. "Sai an baki result sai ki dawo mun da shi , on Monday ranar da zai ma ranar clinic ɗin ki." Na yi mata godiya sai kawai ta gyaɗa kanta. Ina fita na nufi Yallaɓai ya na ganina ya taso, sai na bashi takardan ina faɗa masa yadda muka yi da ita sai ya ce mu je lab ɗin. Tare muka je lap ɗin amman shi bai shiga ba ni ce na shiga na ba su takardan, laboratory ɗin da ya karɓa ya duba takardan sai ya ce. "Muna bukatar ki zo da mijin ki " Haka ya ce mini wani ɗan baki ne, kai tsaye na ce" Tare mu ke yana waje." Sai ya ce na je na shigo da shi, bayan mun dawo tare sun bamu wajen zama, sai wani lap tecnicial ɗin ya fara mana bayanin gwajin da za mu fara yi a matakin farko wato Semi analysis na sperm ɗina da na Yallaɓai." "Ya za mu iya kawo muku samples ɗin? Yallaɓai ya tambaya sai ya kora mana jawabi a tsanake, yanzu dai ya ce za mu fara yin bucking ko gobe ko jibi za mu iya kawowa amman mu kawo shi cikin gaggawa. Kafin mu tafi sai da ya bamu sterile container ya ce mu yi amfani da shi, kafin mu baro asibitin har kuɗin test ɗin sai da muka biya suka samu takardan da cewar sai jibi in sha Allahu za mu kawo ya yi ta jadaddamana da kar mu ɓata lokaci ana son a yi awon da gaggawa ne. Mun fito daga asibitin muna hanya sai kawai na yi tunanin bari na tsaya a kasuwa na ƴan siyayya ta daga nan na tsaya in yi saloon kafin na koma gida. Nan take Yallaɓai ya tura mini 50k kuma ya ijiye ni a kasuwar Wambai. "Yanzu sai ina? Na faɗa ina ƙoƙarin buɗe motar na sauka bayan mun iso shagon da na ke zuwa gyaran kai kusa da kasuwar Wambai. "Office zan fara zuwa akwai mutanen da zan gani." Sai da na fita sannan na leƙa ta window motar ina faɗin" Ka tura list ɗin ga babban shago saboda su kawo mana da wuri" > Janaftybaby: Sai ya gyaɗa min kai kafin ya ce" Kin tabbata ba abin da za a buƙata daga baya? Jin abin da ya ce ne ya sa sai na buɗe motar na sake shiga na karɓi wayarsa na dubo list ɗin da na tura masa. Kallonsa na yi kafin na ce" Ina jin su kenan. Amman za ka iya ce ko zai duba wancan list ɗin? "In ya na da shi ba" Ina ƴar dariya na ce" Ya na da shi mana. Ai suna ijiye rocord saboda babban shago ne." Sai ya jinjina min kai kafin ya ce" ƙarfe nawa za ki koma gida? Ina gyara zaman mayafin jikina zuwa saman kaina na ce" Da na gama siyayya zan koma gida in sha Allahu" Hannuna ya riƙe ya sumbata kafin ya ce" Take care. Ki koma gida da wuri." Ni kuma sai na sunkunya na sumbaci ƙuncinsa ina faɗin" Allah ya ba da sa'a." Daga nan muka yi sallama ya sauke ni ya wuce, shagon wata Amesty ne anan na ke zuwa gyaran kai tun da daɗewa. Ina shiga ta na ganina ta tarɓeni saboda mun saba da juna har lambar wayar juna gare mu. "Hajiya zuwa ba waya? Ina zama kan ɗaya daga cikin kujerun dake cikin shagon na ce" Ba da niyyar zuwa na fito ba. Daga asibiti na muke sai kawai na ce Yallaɓai ya sauke ni anan, daman ina ta wa ƙen zuwa." Yaran shagon na ta gaisheni, ina amsawa ita kuma sai ta je ta ɗauko min ruwa. Ba musulma ba ce amman in ka ganta sai ka rantse musulma ce hausa a bakinta kamar jakar Kano dressing ɗinta irin na hausawa ne. "Na gode." Na faɗa lokacin da ta ba ni ruwa na karɓa na sha kaɗan saboda ina jin kishi. Amesty na zaune gefe na tana faɗin" Ina su Jidda kwana biyu? Ina Baby mai kuka." Ina dariya na ce" Duk suna makaranta." Saboda ba ko yaushe na ke yi musu gyaran kan ba, amma na fi kawo su lokacin salla ko biki saboda ba ni da lokaci tsayawa na yi musu. "Me za mu yi? Wankin kai ko Saloon? Sai na zare mayafina na tuɓe ɗankwalina na zame ina nuna mata kaina. "Saloon ko? Kamar wata biyu kenan ban yi ba." Ta na dubawa sannan ta kalleni ta na faɗin" Gaskiya. Bari mu yi Saloon ɗin" Daman in dai na zo da kanta ta ke yi mini saɓanin sauran da yaran ta ke yi musu, ni kuma muna yi duk abin da na gani ina mata tambaya saboda ɓarayina ne, na iya wankin kai Saloon ɗin ma na iya, Amesty na dariya ta ce" Hajiya wannan shagon na Saloon sai yaushe za a buɗe shi? Nima ina mata dariyan na ce" Yallaɓai ya ce Soon in sha Allahu.". Sai ta ce Allah ya nuna mana. Na yi awa ɗaya da wani abu a shagon Amesty, kafin a gama min Saloon kaina ya yi kyau. Ba ni da kuɗi a hannuna sai na ce zan tura mata ta banki in na koma gida da haka muka yi sallama ta rako ni har waje. Daga nan na samu Adaidaita zuwa cikin kasuwar Wambai akwai shagon da na ke siyan su bra da pant da kananun gajerun wanduna na yara nan na fara tsayawa na siya ma su Jidda pant da vest sai sikat na yara da ƙananun wanduna sai na siya ma Jidda da Baby dogayen wanduna baƙaƙe saboda makaranta. Har da safuna na siya musu farare da baƙake, nima na siya ma kaina pant da bra sannan na siya ma Marwa, daga nan na wuce shagon Musa mai kayan costimetic na siya irin su shampoo sai sabulin da su Jidda ke wanka, sannan na siya Veet da kayan wankin tiolet sai Moneyfresh saboda Mopping, na yi siyayya sosai na amfanin gidana har man kitso na siya mana. Saboda siyayya shago biyu ne kawai shi ya sa ban wani daɗe ba na dauki drop ɗin Adaidaita zuwa gida a ƙofar gida na ga Saude ta na jirana. "Shi ne ba za ki kirani ba?! In ban dawo da wuri ba fa." Kanta na ƙasa ta ce" Na kira ki ba ki ɗauka ba. Yanzu na zo fa daman." Sai da ta ce ta kirani sannan na tuna wayata na can cikin jaka, key na saka na buɗe gidan Saude ta taya ni ɗaukan kayan zuwa cikin gida duk na ji na gaji, ga cikina kamar an yi yasa kamar ban karya ba kafin na fita sai da na haɗa tea na sake sha sannan na dawo dai dai. Sai da na natsu sannan na kira Farida na yi mata ban gajiya da yadda suka koma gida. Sannan sai na kira Amina ba ta ɗauka ba sai na kira Khaleesat itama na yi mata ya hanya. Lailan ma Yaya Auwal mun yi mgana da ita. > Janaftybaby: Da rana tuwo na yi tun da shinkar tuwon kaɗai ya rage mana. Saude sai wajen uku na rana na bata kuɗin mota ta tafi gida, ni kaɗai a gidan jin an kira sallar la'asar sai na yi sallah sannan na kira Yallaɓai nan ya ke faɗa mini ya na Rano ya je duba aiki. Ni kuma daman na manta ne ban faɗa masa mganar a saka drinks ɗin yara na makaranta ba da kayan kamshin girki tun da shagon babba ne a can kasuwar Singer ba abin ba sa saidawa. "Ai na tura masa na ce kuma ya saka duk abin da ya kamata." Sai na ce ya dai sake kiran shi ya faɗa masa sai a manta wani abun sai ya ce to. Sai shidda saura su Jidda su ka dawo, na so na yi wanki gajiya ya sa sai na ce bari na bari zuwa gobe sai na yi wankin. Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya dawo gidan yana tambaya ta ba a kawo kayan abinci ba? Na ce ba su kawo ba nan ta ke ya sake kiran shi manager ɗin sai ya ce a ba' a gama haɗa kayan ba ne sai zuwa da safe in sha Allahu. Da wuri muka kwanta su Jidda daman ko da Yallaɓai ya dawo sun kwanta. Ina kwance a saman ƙirjinsa sai na kira sunan shi. "Yallaɓai." "Uhm" "Ba ka ga Saloon ɗina ba ne" "Na gani mana" Ya faɗa ya na ƴar dariya duk da ba na ganin fuskar shi amman ina jin sautin dariyan shi. Baki na tura kafin na ce" Shi ne ko ka ce ya yi kyau? Hannunsa ya kai ya zare mini hulan kaina ya na mai tura hannun shi a cikin gashin sannan ya kai hancinsa ya shinshina ya kuma sumbata da baki kafin ya ce" Kina da gajen hakuri. So na ke yi daman na baki kyakyawan tuƙwaici." Na ga ko kyakyawan tuƙwaici a daran nan sai da Yallaɓai ya saka ni jiƙa kai gabaɗaya kamshin Saloon ya bi ruwa ina tura baki na ce" Yallaɓai wannan tuƙwaicin naka ban yi maraba da shi ba." Yana min dariya ya ce" Saboda mene? Hararan shi kawai, na haye gado na shige cikin bargo ina tura baki, sai da ya tsane kanshi da danshin ruwa sannan ya hayo gadon ya na min dariya ni ko ko busar da kan ban samu na yi ba na dai tsane shi da towel. Har da asuba sai da ya ƙara jiƙa mini kai, lamarin yallaɓai ya ishe ni har sai da na tsare shi ina masa tambayoyi. "Yallaɓai ka faɗa mini gaskiya me kake sha ne a bayan ido na? Na faɗa ina mai tsare sa da ido. Muna dining ne bayan mun gama karyawa su jidda sun tafi makaranta. Wani kallo ya yi mini na bangane ba kafin ya ce" Kamar na me fa? Ina haɗe rai na ce" Ko ka siya manpower ne ka fara sha a ɓoye ban sani ba? Sai ya buɗe baki yana kallona kafin ya rufe ya na dariya. Ni ko ban yi dariya na tsare shi da ido ina faɗin" To Yallaɓai gwara na sani. Kana samu ɓarnan ruwa da yawa yanzu." Haɓa ya riƙe kafin ya ce" Fisabillahi Sadiya kamar ni na yi lalacewan da sai na sha wani abu za mu yi barnan ruwa? Kai na kaɗa kafin na ce" shi ne na ke tambaya." Miƙewa ya yi a kaina sai da ya yi mika sannan ya sunkuya dai dai kunnina na dama kafin ya ce." "Ke ba ki san muna girma ba ne muna ƙara sanin daɗin abin da darajarsa ba" Kallonsa na yi sai ya dage mini gira kafin na samu zarafin mgana ya sumbaci wuyana da sauri na ture shi na miƙe ina hararanshi. "Miye haka? Saboda na ga ya na ƙokarin riƙo ni kuma yana min wani kallon ƙasa ƙasa. "Allah zan busar miki da gashin da kaina." Ya faɗa ya na ƙokarin jawo ni ai da sauri na warce na fara zagayen dining ɗin ina faɗin" Bar shi kawai na yafe. Ina da hannu" Shima sai ya fara bi na ya na faɗin" Kai Sadiya ta. Guduna kike yi yau kuma? Ya faɗa har yana marairaicewa. Na san halin shi cikin sauri na ce" E wallahi yau na guje ka." Dariya ya yi min ni ko na haɗe rai, haka muka dinga zagayen falon nan daga karshe na fice da gudu zuwa bedroom ɗin ina shiga kafin na rufe ƙofa ya cimmin karfi ba daya ba turani ya yi kan gado ya biyo bayana ya na faɗin" Duk wayon Amarya dai." Ina ture shi ko gizau sai ya fara min cakulkuli ina ta dariya kamar zan mutu ina faɗin" Yallaɓai cikina don Allah ka bari." Sai da ya ga numfashina na sama sannan ya kyaleni ya na faɗin" Gobe dai dole ki bari na yi shagalina tunda kin ga asibiti na bukatar samples." > Janaftybaby: Ko mgana ban yi mishi ba ina maida numfashi shima sai ya yi rigingine ya na nishi, ina ganin haka na lallaba na haye kanshi na fara masa cakulkuli da ƙarfi tun yana daurewa har ya fara dariya yana hantsila kafa, karshenta dai muka yi biji biji da gadon fililluka duk a kasa in ya yi min cakulkuli nima na yi masa daga haraba ma za a iya jiyo dariyan mu. Har sai da muka gaji sannan muka koma muka kwanta muna hutawa. Karfe sha ɗaya Yallabai ya yi wanka ya fita ya ce zai je Gwammaja ne daga can zai ta fi office ya fita ba daɗewa Saude ta zo ita na bari da gyaran gida na kwaso under ɗin yallabai da nawa sai kayan barcin mu na fita can in da muke wanki na kafa kujera kayan ba su da yawa kuma ba su yi wani datti ba cikin lokaci na gama na shanya na saka abin matse shanya na kama dasu. Bayana sai da ya riƙe ina gamawa na yi wanka da ruwa mai zafi, sannan na gyara bedroom ɗin da muka yi kaca kaca dashi ni da Yallaɓai. Ina da sauran fulawa sai na tura Saude kasuwar ƴan kaba ta siyo min kayan miya har da kabeji, ƙuli kuma daman ina da sauran shi sai dai bai da yawa ne. Da ya ke ina son gurasa to ina yi da kaina lokaci bayan lokaci. Gurasa na yi mana. Ita kuma Saude ta niƙa min sauran kayan miyan a blander na saka su a cikin fridge bayan ta ci na saka mata guda uku a leda na ce ta tafi da shi gida. Da safen daman Yallaɓai ya yi mganar albashinta daman mu da kan mu mun kan je gidansu hannu da hannu mu ba ma mahaifiyarta haka tsarin ya ke, sai na ce mata ƙila mu shigo zuwa dare. Su Jidda suna dawowa su ka ga gurasa na yi suna ta tsallen murna. Kayan abinci ko sai bayan mangariba suka kawo mana. Yallaɓai baya nan dole su suka kwaso su zuwa cikin gida. Ma sha Allah na furta a raina komai an kawo har da su maclean da kayan maggi, ni da Jidda muka gyara komai a muhallinsa na Nene kuma na cire mata nata kayan Tea ne sai sabulan wanka da na wanki sai katan ɗin taliya da maracroni sai coouscous, tun da ta na so, shi ma saboda ya saba siya mata duk wata ne a matsayinsa na Namiji amman abincin gidan gabaɗaya yana Wuyan Yaya Usman ne gaskiya duk da sauran duk suna yi, matan ma kowacce tana iya bakin ƙokarinta. Kayan tea ɗin ma gida uku ne Nene da Hajiya Iya sai Maman farko. Da Yallaɓai ya dawo sai na nuna masa ya kalleni kafin ya ce" Ba matsala dai ko? Sai na rumgumeshi ina faɗin" Ba matsala mun gode Yallaɓai Allah ya ƙara buɗi da wadata." Sai shima ya riƙe ni yana amswa da Amin Amin. Ni nasan na yi dacen miji, in dai Yallaɓai ya na dashi ba zan taɓa neman wani abu na rasa ba. A daran muka fita mu ka je Gwammaja mu ka kaima Nene nata ya ƙara mata da 20k tana ta saka albarka farko ma ta ce ba za ta amsa ba ni na ce ta karɓa. Sai ta saka hannu ta karɓa tana faɗin" Komai fa suna yi min Sadiya to kuɗin kuma na mene ne? Ina mirmishi na ce" ki rike a hannun ki Nene kina yin baki da ga Rano ko na sallamansu kya samu." "Haka ne. Na gode Allah ya yi albarka" Muka amsa da Amin Amin muna gidan sai ga Mimisco(Anty Zuwaira) ita da mijinta itama kayan abincin ta zo da shi da kayan tea, sai mganar zuwa ganin likita ga Nene, tunda nauyin asibitin na ta Mimisco ce ta ce a bar mata za ta iya. Mun gaisa da ita kamar yadda muka saba ni dai ban taɓa samun matsala da ita ba. Tana da ilmi ta kuma san yadda za ta zauna da jama'a. Saboda zuwanta ya sa muka ɓata lokaci tunda Yallaɓai suna ta hira da mijinta. Sai wajen tara da rabi muka baro gidan bayan Yallaɓai duk ya shiga ɗakunan su Hajiya Iya ya ba su 10k kowacce suka karɓa suna godiya a hanya ne ma da za mu je Ɗorayi Yallabai ke faɗa, min Yaya Usman ya shigo garin jiya amman bai kwana ba ya koma a ranar. "To. Ya zo biko ne? Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce" Ban sani ba. Na san dai ba zai rasa zuwa gidan su ba." Sai na jinjina kai kafin na ce" Hmm. Allah ya kyauta.". Saboda ina so na yi magana ina tsoron kar Yallaɓai ya taso min shi mai ɗan uwa. > Janaftybaby: Mun fara zuwa gidanmu muka sake duba Alhaji 20k Yallaɓai ya ba ma Alhajinmu. Gwaggo kuma 10k suna ta saka albarka. A bakin Gwaggo na ji labarin yau da safe Baaba ta koma na ce Allah ya tsare. Daganan mun shiga gidan su Saude 50k Yallabai ya ba ma Balaraba daman a wata 30k kuɗin aikinta amman Yallaɓai na yi musu ihsani kuma kafim mu baro gidan sai da ya yi mganar ya na so ya saka Saude a makaranta bai da ce a barta haka ba karatun boko ba, ta gama firamari ba ta cigaba ba. Mahaifiyarta har da hawaye tana ta godiya zaman amana ne da maƙotaka ya haɗamu har na ga Saude na ce ta riƙa zuwa tana kama min aiki saboda na taimaka musu. Daga gidan su Saude gida muka dawo tun da daman mun yi sallama da su Gwaggo muna hanya Yallaɓai ya ce na tura mai acct number Datti zai saka masa wani abu ina ta masa godiya. "Tsakanin mu ba Godiya Sadiya ta." Haka ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na yi masa mirnishi kafin na ce" Duk da haka dai zan gode maka. Yallaɓaina Allah ya sa a fi haka." Sai ya amsa min da Amin muna yi ma juna mirmishi. * Washegari da sasaafe, bayan Yallaɓai ya ja mun yi ta barnar ruwa ni dai ai nace dole zan kira mai kitso kafin Yallaɓai ya sa gashina ya sauke ƙasa saboda jiƙashi da na ke da ruwa. Sai bayan su Jidda sun tafi makaranta a gurguje muka yi abin da aka umarcemu mu kawo daga Lab. Saboda yadda ya jadaddamana cikin sauri muka yi wanka Yallaɓai ya kai ni asibitin na kai musu da sauri suka karɓa bayan na haɗa musu da takardan da suka ba ni shekaranjiya. Suna karɓa suka ce mu jira a waje za su ba mu result ɗin. Tare da Yallaɓai muka yi zaman jira ana ta kiran shi ma a office bai tafi ba sai da aka gama test ɗin suka kuma bamu result ɗin da cewa zan kaima likita ranar clinic ɗina. Daga nan Yallaɓai ya dawo da ni gida ya ijiye shi kuma ya wuce office domin ya faɗa mini akwai kwangilan da ya samu na zanen wani kamfani da za a buɗe a kaduna ne. Na bishi da Allah ya ba da sa'a shi ya wuce ni kuma na buɗe gida na shiga. Ban san me result ɗin ya nuna ba tunda rubutun likitoci sai su sai na adata kafin ranar Monday. Ranar yini na yi gugan kayan under ɗin mu da na wanke mana na goge su tas na feshe da turare, na jera mana a cikin wardrope, ganin na samu natsuwa ya sa na ɗau wayata na kira Aisha lame na yi mata mganar ina son Body lotion, sau Face soap sai Fade cream sai showergel na wanka Sai ta ce mini za a kawo mini sai na ce kamar yadda muka saba zan tura mata kuɗin ta, Aisha Lame ba abin da ba ta saidawa na gyaran jikin mata. Kuma kayan ta suna da kyau da inganci su na ke amfani dashi shi ya sa kullum Yallaɓai sai ya ce ya na son taɓa fuskata saboda taushi da santsi sannan ba guraje, jikina kuma ya yi fresh ya yi taushi domin Showe gel ɗin ta ba baya ba yana bala'in gyara fata. Tana aikawa da kayanta ko'ina a faɗin Nigeria Daga ita sai na kira Surayya Dee mai kayan gyara na BOJUWA ta dalilin Aisha lame na san Surayya. Kuma na yi amfani da kayanta na yaɓa da ingancinsu. Ni duk bayan wata uku na ke shan mganin sanyi sannan na ɗora da na gyara Ni macece da ta yarda da gyara shi ne har gobe ya sa na ke da matsayi a zuciyar Yallaɓai. Duk da har kayan marmari ba na wasa da su da duk abin da zai kawo mini Ni'ima amman kuma ban zauna ba ina gyaran jikina tare da can ainihin majalisar ɗinkin duniyan gabaɗaya. Maganin infection na ce ina so Surayya ta aiko minibda shi in na gama zan siya kazan uwargida tana ta dariya ta ce" Hajiyar Injiniya ba a dai gajiya da gyara." Nima ina dariyan na ce" Ba a gajiya Hajiya Surayya. Gyara shi ne mace da gyaran ya sa har gobe muke ƙyalli a idanuwan mazajen mu." Tana ta dariya mun rabu akan yau ɗin nan mai kawo mata kaya zai kawo mini tun da ya san gidana, tun da ba yau muke tare ba, sama da shekara ɗaya tun da na gwada kayanta na san ingancin su. Domin ke ma ki dace da ingantattun kayan gyara contact Surayya Halin yau on +234 803 277. Kano Nigeria tana aikawa da kayanta ko'ina. > Janaftybaby: Zuwa yamma sai ga saƙon Surayya Halin yau, a daran kuma na tura mata har kudin kazar da zan siya. Mayuka na bangaren Aisha lame kuma sai washegari da safe ta aiko mini dashi. Ranar jumma'a gidan Rahila muka yini ni da su Jidda, Rahilar ba ta da lafiya zazzaɓi daga ita har Bbyn na ta sai dare Yallabai ya je ya dauko mu, mun sha hira mun yi tsiya mun yi daɗi ta ji sauƙi tun da har kitso sai da ta yi mini daman ta iya ta rufa mini asiri kafin Yallaɓai ya saka ruwa ya sauke mini gashi. mun rabu da Rahila ta roƙe ni ƙanwar mijin Ma'u za ta yi aure za ta biyo mini mu je tare kai tsaye na ce" In ta gayyace ni ba? In ba ta gayyace ni ba wallahi ba zan je gayyar soɗi ba." Rahila na dariya ta ce" Ki ji tsoron Allah Sadiya. Ke yanzu sai kin jira Ma'u ta gayyace ki." Ina hararanta na ce"Kwarai kuwa. Kawai tusa kai ba kwarjini in ta gaya min zan iya zuwa amman ba ta gaya mini ba sai dai na ce a sha biki lafiya." Washegarin asabar kamar ta san mun yi maaganar da Rahila sai ga shi ta tura mini katin biki sannan daga baya ta kirani. "Ina fatan za ki zo dai zo ko Sadiya? Sai na ce mata in sha Allahu tun da sati na sama ne. ** Ranar Monday, na koma asibiti na ga Dr Aisha bayan na ba ta sakamakon ta duba cikin ikon Allah ta ce da ga ni har Yallaɓai sperm din mu suna active matsalan ba daga nan ba ne yanzu tun da an yi wannan an tabbatar da ba matsala za su yi focusing a kaina ne. Sai ta rubuta mini blood tests to look hormone levels. Na je na kai lap aka ɗibi jinina suka ce na dawo nan da kwana biyu domin karɓan result. Tun ina hanya na kira Yallabai na faɗa masa likita tace matakin farko ba matsala yanzu dai sauran gwaje gwajen akai na ne. "Alhamdulillah. Suma sauran in sha Allahu ba matsala." "In sha Allahu." Na amsa masa cike da yaƙinin hakan A satin Hauwa ta zo gida na ta yini ita da yara a bakin ta na ke jin Anty Zabba ta koma amman sai bayan Yaya Usman ya koma ni ko sai na ce" Ya fi mata. Amma ba ta gina gidanta ta bar ma wata shi saboda kishi ba." Sai dare Muttaƙa ya zo ya dauke su. Washegari gidan Halima na je na kai mata Atamfar da na da siya mata a Dija collection+234 Domin kayanta ta na ba da su ne akan farashi sari mai sauƙi. Sai na siya rigar yaro ssi pampers da na je sai na ɗora mata 5k na ce nawa ne kuɗin kayan kuma daga Yallaɓai ne tana ta godiya a gabana ma ta kira shi tana yi masa godiya ya ce ba komai. Ina shirin tafiya sai ga Anty Bahijja wai sun zo nan kusa ne ganin gidan da ƙanwar mijin Ma'u za ta zauna shi ne ta biyo wajen Halima. Da gangan na yi ma Anty Bahijja taɗin bikin ina dariya na ce. "Anty Bahijja ashe biki gare ku ba gayyata." Sai ta kalleni kafin ta ce" Ba ni ya kamata na gayyace ki ba Ma'u ce." Ina mirmishi na ce" Ai fa ta gayyace mu muna nan zuwa." Na ga ta kalleni da mamaki amman sai ta shanye ta ce sai mun zo ni dai anan na barta na koma gida da wuri saboda yara. Ranar asabar da wuri na shirya daman na faɗa ma Yallabai tun kwanaki ya ce ya ba ni izini. Shi na bar ma yara a gida na ce in zai fita ya kai su Gwammaja wajen Nene, ni kuma Rahila ta kirani ta ce wai mu a haɗu a Ɗorayi ni kuma na ce ba zan koma baya ba tun da na san gida yayar mijin Ma'un ta taɓa rasuwa muka je gaisuwa na san iyayin Yaya Murja ce za ta ce a haɗu a gida a tafi gabaɗaya tun safe Rahila ke kirana nace ina dalili su yi gaba sai azahar zan taho. Ban ma samu zuwa ba sai bayan azahar ganin na yi rana kawai Yallaɓai ya ce na jira mu fita tare shima Alhaji Mustapha ya gayyace shi ɗaurin aure sai da muka kai su Jidda Gwammaja sannan muka wuce Maitama in da gidan iyayen mijin Ma'u suke, ko da na je su Rahila sun jima da tsufa da zuwa Ma'u har da rumgumeni can na ga su Anty Bahijja Hajiya sama Hajiya ƙasa tun da mijinta shine babba a ɗakin ita mahaifiyar Alhaji Mustapha kuma suna ji da shi, shi ya sa ita ke faɗa aji, ina ta mamakin yadda take ba da umarni a dangin mijinta an ce so so ne amman son kai yafi ita ta samu dama tana yadda ta ga dama amman idanuwanta na kan wasu kar su ji daɗi a gidan mijinsu sannan kar su zama masu faɗi a cika a dangi amman ita gashi tana yarda ta ga dama. *TURKEN GIDA.* KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️16* Mutuwa ɗaya ce haƙiƙa na tausaya mata ganin ko shekara biyu ba ta rufe da auran ba. Yallaɓai a ranar suka tafi Abuja tare da Uncle Abba da Nene, da Anty Maimuna Anty Bahijja za ta taho daga baya. Sai Hajiya iya Maman farko kaɗai aka bari a gida. Can suka kwana Tariq da Farida daga kaduna suka tafi. Ni kuma ranar litini na je ganin likita sai ranar na je lab na karɓo sakamakon test ɗina na kai mata shima ta ce lafiya lau ba wata matsala. Sai muka je matakin gaba na A transvaginal ultrasound. Ta ba ni nan da kwana shidda na dawo. A ranar su Yallaɓai suka dawo daga Abuja kwanan su ɗaya amman an bar Anty Maimuna acan tare da Nene da Hajiya Kaltume sai an yi uku za ta dawo. Ranar talata muka je Abuja gaisuwa. Ni da Hauwa da Munnira sai Jamila da Hindatu, Hafsat daman ta na can Abujan ne, sai Mimisco da direbanta ne ma ya tuƙa mu. Mun iske gidan Gimbiya cike da yan uwa da abokan arziƙi. Kaf yayyenta mata da matan mazan suna nan, Hajiya kaltume da Nene ne tare da ita a matsayinsu na manya. Har Sameena a can na ganta ta ce tun ranar da da aka yi rasuwar ta zo sai an yi bakwai za ta koma. Tariq ma na nan shi da Farida da yara. Amman dai shi ya ce min da zaran an yi sadakar uku zai koma gida. Ba Gimbiya ke bin Tariq ba akwai wata mace sannan ita a shekaru ba za ta gaza 33 ba ko na girmeta bai wuce da shekara ɗaya ba. Lokacin da nake yi mata gaisuwa ta yi matuƙar ba ni tausauyi ta yi kuka idanuwanta sun shige ciki, ba ta mgana sai dai ɗaga kai ba ta ci ba ta sha sai an yi da gaske ta ke tsakura da kuma ta ci sai ta amayar dashi. Ta rame sai farin fata da dogon hanci gabaɗaya sai ta bani tausayi har araina ina yi mata addu'an Allah ya ba ta dangana. A bakin Sameena na ke jin Alhajin na gidanta ne lokacin da ciwon shi ya tashi. Ashe yana da ciwon hanta a Egypt ya ke ganin likita a daran su ka kai shi babba asibiti a nan Abuja da niyyar kafin a fita dashi waje, da asuban ranar Allah ya yi masa rasuwa. Allahu akbar. Allah ka sa mu yi kyakyawan karshe. Mun je gidajen duka matan shi mun yi musu gaisuwa tun da dukkansu suna anguwa ɗaya ne asokoro. Kuma gidajen su ba nisa bai wuce ka ga gida uku a tsakani ba. Yana da manyan ƴaƴa ba shi da ƙananu da Gimbiya ta haihu ne zai iya samun yara. Ba kuma yaro ba ne don ko da ta aure shi ya yi shekara 60 Allah na tuba a lokacin har ina ma Hauwa gulma me za ta yi da tsoho mai mata da ƴaƴa haka? Ashe zaman ma ba mai tsaho ba ne. Duk da na zo garin da Yaya Auwal ya ke ban je ba. Saboda gaisuwa muka zo kar a ce daga zuwa ina yawo. Sai dai na kira Lailan na faɗa mata mun shigo garin, sai ta ce in da sarari za ta shigo ta yi musu gaisuwa. Yallaɓai na bari, a gida shi da yara amma mun yi mgana ya ce gobe ranar uku za su dawo sai na ce kawai in sun dawo daga makaranta ya faɗa ma Salisu ya kai su gidan Rahila tunda ya ce za su kwana washegari sai a haɗu gabaɗaya a koma kano. Shi ya sa na kira Rahila na ce, za a kawo mata su Jidda su kwana a wajenta kafin mu dawo tun da Salisu ya san gidanta. Saude kuma Yallaɓai baya nan ban taɓa kwatantan barin ta ita kaɗai da yara a gida ba. > Janaftybaby: Ma'u ta karrama mu ba zan raina mata ba. Shema'u sune yan gaba gaba Ma'u mijinta ne babba a maza duk da ya na da yaya mace, amman itama Anty Ma'u sama Anty Ma'u ƙasa sai abin da ta ce. Ina ta mamakin ina abokiyar zamanta Hajiya Zainab? Sai can na ganta ta ci kwalliyarta da kin ganta kin ga wacce ta gaji arziƙi ba haye ba. Ita ba ruwanta gaskiya ba ta son hayaniya ma Ma'u kuma da ya ke yar bariki ne duk ta siye dangin Alhajin da siyasar ta. Yaya Murja sai da ta yada mini mganar wai sai yanzu na zo biki da rana. Ni ko na ce Yallabai na gida tare muka zo dashi shima ya zo ɗaurin aure. Shema'u kuma ba ta mini magana ba ta yi wani ɗan iskan ɗinki duk ya kama jikinta fuska da jiki sun sha mai ta yi wani fayau saboda in rama wulakancin da ta mini sai da na bari ta shigo ɗakin da aka saukemu sannan na kalleta ina faɗin "Shema'u ranar da muka sauke ki a gidan Nene Tariq ke faɗin wai kin karɓi lambar wayar Uncle Abba." Ba ita kaɗai ba gabaɗaya waɗanda ke wajen sai da suka kalleni daman na yi alƙwarin yadda ta yi min cin mutumci a gidan Rahila sai na rama. Ina mirmishi na ce" Wai kin roɗa ne? To gwara ma ki bi wani sarki shi Uncle Abba mata har ƴayan sarakuna daga Rano an yi masa talla bai ɗaga kai ba ballanta ke, na san dai zuwa yanzu kin ma san ya fi karfinki tunda lambar wayar ma ba tashi ya baki ta Tariq ne." Ƙur ta yi min da ido, ni kuma sai na gauraye fuskata da mirmishi Rahila na ta mini sigina na yi kamar ban gani ba har Yaya Murja mai baki ta kasa mgana. Shema'u kuma dakyar ta iya yaƙe kafin ta ce" Oh. Wannan daman na karɓi lambarsa ne saboda na ga ya yi min kama da wani sai daga baya na gane bashi ba ne, ni fa Sadiya ɗan'uwan mijinki ya yi mini tsufa kaf ma a dangin sa ba wanda zai iya dai dai da Shema'u.' Ta faɗa cikin danne yanayinta ina dage mata gira na ce"Da gaske? Cikin renin wayau Anty Aina ce ta yi mgana. "Sadiya ki bar mganar don Allah." Sai na yi dariya kafin na ce" An barta." Shema'u na yaƙe ta fice amman ni kaina na san ta ji abin da ake ji in ka tozarta wani a cikin jama'a sai da ta fita Yaya Balki ta ce ya aka yi ne na gyara zama ina faɗa musu yadda aka ƙare. Yaya Balki na dariya ta ce" Wannan akwai ɗan jaka da rabi. Zai haɗa fada." Ina dariya na ce" Kaɗan daga aikin Uncle Abba kenan." Rahila ta ce ta gane shi ta taɓa ganin shi a gidana Yaya Murja ba ta ce komai ba sai daga baya ta ce" Ko ma dai menene ba kyau cin fuska a cikin jama'a." Kai tsaye na ce" Ba cin fuska ba ne. Ai naga nan duk ɗayan ne ko? Ta kalleni na kalleta sai kuma ba ta ƙara mgana ba. Ma'u ba ta ɗakin amman na san za ta ji labari Zaituna kam duk muna tare da ita amman ta ci abinci har da guzurin alale, ni da mangariba muka tafi ni da Rahila da Zaituna Yaya Murja ta ce sai ta kai Amarya amma Yaya Aina da Yaya Balki ban ji suna zencen ba amman dai can muka bar su. Na dawo gida da Waina da sinasir Ma'u ta matsa dukkanmu sai da muka taho dashi Shi na ci na sha ruwa tunda mai siga ne sai dare Yallaɓai ya je ya ɗauko su Jidda suka dawo gida. Su sun ci abinci Yallaɓai ne na dafa ma Indomie da ruwan tea ya ci kafin ya kwanta. Washegari Lahadi da asuban fari sai ga wayar Tariq Allah ya yi ma mijin Gimbiya rasuwa. *Janafty* > Janaftybaby: Duk anan gidan Gimbiyar muka kwana. Abinci sai dai a kawo shi a dafen shi komai ga shi. Saboda ya na da kuɗi dan kwangila ne ya tara abin duniya kuma a baya ya yi siyasa. Washegari ranar da aka yi sadakar uku da wuri su Yallaɓai suka iso shi da Uncle Abba da su Kawu Sa'adu sai Anty Bahijja. har cikin gida kuma sun shigo an yi ma juna gaisuwa. Ni ina can ɗakin da muka kwana ba mu haɗu ba sai can yamma ma. Mun dai yi mgana ta waya da daddare kuma sun ƙara shigowa, a bakin Munnira na ji ta na faɗin wai Tafida ne ma ya matsa ma Gimbiya da lallashi har ta amince ta sha tee ɗin da yawa kuma sannan sai yau aka ji ta taɓa buɗe baki ta yi mgana amman ga Tafida kaɗai. Ban yi mamaki ba sanin shaƙuwarsu kuma a lokacin ai abar tausayi ce. Washegari muka dawo kano amma mun bar Nene a can ita da Hajiya Kaltume da sauran ƴan uwanta. Mota ɗaya muka shiga da Anty Bahijja na ji suna mgana da Mimisco da cewa wai Gimbiya ba ta mgana da kowa sai Tafida sannan shi kaɗai ke ba ta abu ta karɓa ta sha. Su Nene haka suke yi kamar za su ari baki amman ba ta cin komai ba ta mgana sai kuka. Anty Bahijja ta ƙare maganar ta da cewa" Ga shi kuma kin ga ba gari ɗaya ba. Balle a ce ko da yaushe ya riƙa zuwa ya na matsa mata ta ci abinci" Ina kujeran zama ta tsakiya saboda motar irin babba ce ta yara ta mijin Mimisco ne. Ni da Hauwa muna zaune waje ɗaya har muna haɗa ido muka kalli juna amman ba mu yi mgana ba. "Ba matsala ba ne. Jiya mun yi mgana Hajiya ana tunanin da an yi arba'in Gimbiya za ta koma Rano." In ji Mimisco sai Anty Bahijja ta ce" Ai ya ma fi sauƙi. Allah dai ya ba ta dangana baiwar Allah." Mimisco ta amsa da Amin.sai ita Anty Bahijja ta ƙara da cewa" To Nene fa? Ko itama tare da Hajiya Kaltumen za su zauna har arba'in ɗin? Sai ta yi shuru kafin ta ce" In za ta iya sai ta zauna. Tunda na taho mata da magungunanta da ta manta. Gida daman ba wani abu take yi ba." Muna jin su suna ta tattaunawarsu har muka iso kano. Da ya ke mun iso da wuri Yallaɓai suna baya mun riga su yo gaba gaskiya. A bakin hanya na ce su sauke ni na samu adaidaita zuwa gida. Sai da na isa gidana na yi salla na dafa indomie na ci sannan na dawo hayyacina. Sannan na kira Yallaɓai sai ya ce min suma sun kusa ƙarisowa, sai na ce ya kira Salisu ya faɗa masa in ya dauko su Jidda daga makaranta gida zai kawo su na dawo sai ya ce to. Ni kuma sai na kira Rahila na ce mata na dawo sai ta ƙara min gaisuwa ni kuma na yi mata godiya har ta na cewa" Uban godiya ke fa ba ki da hali wani lokaci." Daga nan ta kashe wayarta ta bar ni ina dariya. Bayan Rahila da Laila ba wanda na faɗa ma an yi ma su Yallaɓai rasuwa sai gashi kwana ɗaya tsakani da dawowarmu daga Abuja a group gidanmu na ga Yaya Balki na yi min gaisuwa da na tamnbayi in da suka ji sai ta ce Yaya Murja ta faɗa mata da ta je gidanta itama ta ce Ma'u ce ta faɗa mata. Abin sai ya bani mamaki na ga ni dai ba tamin gaisuwa ba. Amman ta je tana faɗa, ban yi mamaki ba tunda tana tare da Anty Bahijja ta kuma yarda da ita shi ya sa wasu labaran na dangin mijina kafin ni na kai ga furta ma wani Ma'u ta yaɗa shi a gari. Tsaki na yi a fili kafin na ce" Wannan ai gwara ta kashe auran nata ta auri Nasir ko Musabahu da wannan bin diddigin na ta." A daren kuma sai ga ta ita da Alhajinta wai sun zo ma Yallaɓai gaisuwa. Kuma abin da ya ɓata mini rai shi Alhajin ya kira Yallaɓai ya faɗa masa za su zo amman Ma'u ba ta kirani ba, shima Yallaban ya kira wayata bai samu ba ƙwatsam na gansu lokacin shi bai ma riga ya dawo gidan ba. Da ɗan fara'ata na karɓe su. Bayan mun gaisa sun yi mini gaisuwa sai na ce ai Yallaɓan bai dawo ba sai ya ce ai sun yi mgana dashi ya na kan hanya. Kafin ya ƙariso na kawo muusu ruwa da lemu na yi shinkafa da miya na kawo musu suka ce sun ƙoshi sai da suka ci abinci sannan suka fito daga gida. Ba ko daɗewa sai ga shi ya iso. Saboda mu ba su waje sai na ja Ma'u zuwa falon na biyu na kora su Jidda ɗakin su bayan sun gaida Ma'u ta amsa cikin fara'anta har tana faɗin" Jidda idon ki kenan? Ina nan dai ina jiran ki a wannan hutun." > Janaftybaby: Sai Jidda ta fara kallo na, sai na yi saurin cewa" A'a ni ba ruwana ki tambayi babanki in ya barki in an yi hutu sai ki je." Da sauri Ma'u ta ce" Ai ni dai na san Yallaɓai ba zai hana ba." Sai kawai na ɗan yi yake. Muna zaune ba mgana sai baɓatun talabijin. "Ashe kin je Abujan kema? "Uhm" Na faɗa ina kauda kaina ba na son kallon Ma'u saboda kallonta ba alheri a cikin yanayin kallon ta. "Allah ya jikan sa." Na amsa da Amin shuru na wani lokaci sannan ta ce" Allah sarki ta ba ni tausayi rashin miji ba daɗi." "Ai fa kam." Na faɗa ban bama mganar muhimmamci ba. "Allah ya kawo mata kyakyawan zaɓi." Na amsa da Amin na ɗauka daga nan maaganar za ta tsaya sai kawai na ji tana faɗin. "Anty Bahijja na gaya mini halin da ta ke ciki kamar in yi mata kuka ta ce mini ba ta cin abinci sai kuka ba ta kuma mgana da kowa sai Yallaɓan ki" Kure ta da ido na yi domin na san daman sai ta zo wannan gabar." "Ta ce min shi kaɗai ke iya cewa ta ci abinci ta ci kuma shi kaɗai take yi ma mgana. Abun mamaki ko da ya ke na ji labarin an ce daman sun shaku da juna." Ta fada tana mini mirmishi. "Haka na ji." Nima sai na ba ta amsa amman ban nuna wani abu daga saman fuskata ba." "Allah sarki. To bakomai tunda na ji Anty Bahijja na faɗin ana arba'in za a dawo da ita Rano Sai na ce ai ko ga shi kusa ina Rano ina Kano? Yallaɓai sai ya riƙa zuwa yana kula da ita baiwar Allah abin tausayi.' Ta gama faɗa har tana bayyana jimamin a saman fuskarta. Ni na san da biyu ta yi wannan maganar sai kawai na yi mata mirmishi kafin na ce" Gaskiya ne. " Sai na datse bakina ban kara yin mgana ba amman ina kallonta ta gefen ido tana mirmishi kafa ɗaya ta ɗora kan ɗaya kamar falon gidan Alhajin na ta ne. Yadda ta ga na haɗe rai ina duba wayata ya sa ba ta ƙara mgana ba. Ba daɗewa ma sai ga shi Yallaɓai ya leƙo ya ce Ma'u ta fito za su wuce tsabar haushi iyakata a bakin kofa ban fita haraba ba Yallaɓai ne ya fita ba su shigo da mota ba sun yi parking daga waje ne. Kamar maganar Ma'u ba za ta dame ni ba, sai gashi kuma tana sukan raina ace wai komai ya faru a dangin mijina sai Ma'u ta sani in na ji haushinta ta wani fannin kuma ban ganin laifinta ba kowa ya ba ta dama ba sai yayar Mijina. Ta kuma wani bangaren itama Anty Bahijja sai na ke yi mata uzuri saboda in dai Ma'un da na sani ne makircinta zai iya siya mata kowa da kuma wannan makircin ta siye Anty Bahijja. Renin na ta har ya yi yawan da za ta zo har gidana tana gaya min mgana na ci ji yatsa da na ƙyaleta amman dai na san za ta ƙara wata rana dole za mu haɗu. Washegari na koma asibitin domin ganin likita. Wannan karon ma Dr Aisha ta ce vaginal ɗina komai lafiya lau sai matakin gaba na A hysterosalpingogram a type of X RAY, that allows your provider to see your uterus and follopian tubes. Dr Aisha ta faɗa mini scan ɗin is very painfull tunda na cikin mahaifa ne. Ta gaya mini zan iya bucking anan asibitin ko mu fita waje, da na kira Yallaɓai sai ya ce kawai na yi bucking anan asibitin, ban dawo gida ba sai da na yi bucking sun ba ni sati ɗaya na dawo su yi min scan ɗin. Ban damu da wahala ko wani abu ba babban burina na kai ga matakin nasarata shine a gabana. ** BAYAN SATI UKU. Bayan sati da huɗu rasuwar mijin Gimbiya a lissafi kuma bai fi saura kwana biyu ya yi arba'in da rasuwa ba. Kuma har alokacin Nene da Hajiya Kaltume ke zaune da ita sai dai yan'uwa da ba su samu zuwa ba sukan je domin yi mata gaisuwa. Har na ji Yallaɓai suna mgana da Mimisco akan a cikin satin su Nene za su dawo da Gimbiya gida. A cikin sati ukun da suka gabata lamarin Gimbiya ya fara ba ni mamaki har na fara tunanin ko ba ta da tawakalli ne kuma har sai da na furta ma Yallaɓai har ya ji haushina. Haba abun nata ya yi yawa ba kanta farau rashin miji ba Allah na tuba sauran matan shi da suka yi shekaru aru aru da shi ma sun ɗau dangana haka ma ƴa'ƴan shi da suka rasa uba suma sun dangana amman ita ba alamun dangana a lamarinta. > Janaftybaby: Na tuna ni kaina fa uwata ba ta a duniya nan na ɗau tawakalli Yallaɓai ba shi da uba shima ya ɗau dangana. Har wani lokacin in na jin masa shaƙiyanci ko ina son ya yi min wani abu ya ce ba zai yi ba sai na marairai ce ina faɗin." Yallaɓai ka tausaya mini ka ga ni fa marainiya ce.' In na ce haka a lokacin sai ya yi dariyan nishaɗi kafin ya ce" Au ke sai yanzu kika san ke marainiya ce? Mu ai mun daɗe cikin maraici kuma ba mu mutu ba." Ko kuma ya ce" Ke ba marainiya ba ce Alhaji ai bai mutu ba ko kin kashe shi ne? In ya faɗi haka daga ni har shi sai mun ƙyalƙyace da dariya. Saboda mun yi shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma Annabi muhammdu manzonsa ne, sannan rayuwa da mutuwa duk ta na hannun shi ne. Sai dai ta bangaren Gimbiya ba ta san wannan ba, tun da a ka yi rasuwar nan saboda ba ta jin mganar kowa sai na Yallabai a rana ban san adadin sai nawa ya ke kiran waya a ba ta ba, yana lallashinta ta samu ta ci wani abu. Ko in ta fara kuka sai su kira shi su ba ta ya yi ta mata nasiha, duk wannan ƙokarin da ya ke yi mata ba ta dangana ba. Bayan wanda yan'uwa ke yi mata shima duk bai sa ta dangana ba. Tun ina tausayinta har ta koma ba ni haushi. Na yi ta tunanin ita ko wani irin so ta ke yi masa haka. ko dai garken yaya ta tara da shi sai haka amman aure duka duka wata ashirin ba ciki ba goyo haba lamarin nata ya yi yawa har na fara gajiya da jin labarin halin da ta ke ciki a bakin Yallaɓai in yana faɗa min Daughter ta zama abin tausayi, tun in yana faɗa ina nuna jimami har na daina saboda lamarinta ya wuce na musulma mai tawakalli ya koma hauka da jayayya da ubangiji. Nan ko sati ba a yi ba sai da Yallaɓai ya koma Abuja ya kwana ɗaya sannan ya dawo. Wai ta shige ɗaki tun safe ta rufe kanta tana kuka kuma tun daren jiya ba ta ci komai ba su Nene sun yi sun yi da ita ta buɗe ta ƙi har azahar shi ne Nene ta kira Yallaɓai a waya ta ce ya bar duk abin da ya ke yi ya zo Abuja. Shi ne fa ya na ma office ya dawo gida ya na faɗa min tare da cewa na haɗa masa kayan tafiya na kwana ɗaya tun da ba zai yuyu ya je a yau ya kuma dawo ba. A lokacin ne na furta masa abin da ke zuciya ta. "Haba kamar dai ba ta da tawakkalli. Wai kanta farau mutuwar miji? Na faɗa ina mai sakin tsaki tun da shima yana kan aikinsa ne amman an wani ta da shi zuwa Abuja. Ni ina ganin gulma ne ace duk cikin yan'uwanta da suke uwa daya uba ɗaya mata da maza ba ta ga wanda za ta riƙa jin mganarsa ba sai Yallaɓai da zaman da ya yi a gidansu na ɗan lokaci ne, za a ce ya fi mata yan'uwanta da suka fito ciki ɗaya ne? Tsawa Yallaɓai ya daka mini kafin cikin ɓacin rai ya kalleni ya na faɗin" Sadiya wannan wani irin mgana ne? Kallonsa na tsaya yi saboda sai na ga kamar ban faɗi wani abu mara kyau ba. "Me na ce? Gasikiya na faɗa hakuri ake yi. In ta na wannan abun kamar tana faɗa da Allah ne." Kawai sai Yallaɓai ya fara faɗa ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Wai na san zafin mutuwan miji kuwa.? Ni ko kai tsaye na ce" Ban san na miji ba. Amman ai na san zafin mutuwar uwa ko? Na faɗa ina kallon shi saboda na ga zai wani hau kaina daga faɗin gaskiya saboda ma na ƙara kunsa ma sa kai tsaye na sake faɗin" Kuma na tabbata ba yau aka saba mata rashi ba. Ai ta rasa uba da yan'uwata me ya sa ba ta yi haka ba sai yanzu? Gaskiya ku yi mata faɗan ta zama mai tawakkalli kuka ko rufe kai a ɗaki ba shi zai kawo mafita ba." Ni kaina tsaye na ke mgana kuma shi kan shi Yallaɓan ya san ni. Amman a mamakina kai tsaye ya kalleni kafin ya girgiza kai ya na faɗin" Na yi miki uziru saboda ba ki san zafin mutuwar miji ba. Amman ba shi zai hana na ce ba ki da tausayi ba Sadiya." Baki buɗe na kalli Yallaɓai ya na sauya kaya cikin nuna kaina na ce" Ni ce ba ni da tausayi Yallaɓai? Kai tsaye ya ce" Ƙwarai da gaske. Domin duk mai tausayi tausaya ma halin da Daughter ta ke ciki zai yi ba maganganun banza marasa tushe ballantana makama ba. Shirme kawai." "Daga faɗin gaskiya? "Ki riƙe gaskiyan ta ki ba a so." Haka ya maida mini amsa a fusace. > Janaftybaby: Ajiyar zuciya kawai na sauke domiin na ji raina na tafarfasa zan iya maida masa martani amman sai na ƙyale shi, ɗakin na bar mishi kayan na shi ma ban gama haɗawa ba na ce ya haɗa da kan shi tun da da ga faɗin gaskiya sai na yi laifi ya je can ya tare saboda kula da ita. Da zai tafi ko sallaman da muka saba ba mu yi ba, shima fuska a haɗe nima na haɗe nawa ko haraba ban raka shi ba, daga falo na yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya. Amman Yallaɓai ya ba ni mamaki, yadda ya wani ɗau zafi daga fafin gaskiya. Wani abu ke tsaya min a maƙogwaro in na ji yana ambaton ta da Daughter ƙatuwar mace shima ya na namiji magidanci da wani sanabe da iyayi. Har ya je ya yi kwanan ɗayansa ya dawo ba mu yi waya ba. Ya san halina yadda bai kirani ba nima ban neme shi ba su Jidda suna ta tambayan Abba na ce ya ta fi Abuja. Da ya dawo ban yi masa tarban da na saba ba. Ni ban haɗe rai ba sannan ban sakar masa ba, sai dai lokacin da ya dawo sai bai dawo da fushin ba. Shi ya fara saki sai nima na saki amman na so ya cigaba ya sanni ni sai na iya gaba dashi ba wani abu mai wahala ba ne a wajena. Amman kalmar ba ni da tausayi da ya kirani da shi ya taɓa ni kuma sai da na yi masa mgana sai ya ce na yi hakuri amman nima ai bai dace na ce haka ba, kenan har a lokacin bai ga gaskiyan abin da na faɗa ba to ai shike nan ni kuma na saka a raina ba zan kara mgana ba. Abin da ma ya faru a can ɗin ban tambaye shi ba shi da bakin shi ya ke faɗa mini Ulcer ta kama Gimbiya sannan kuma jininta ya hau sai da likita ya zo gida ya duba ta. Bakina ƙanin kafata na ce Allah ya ba ta lafiya domin na fahimci Yallaɓai kiris ya ke jira da ni ya yaɓa mini mgana. Bayan arba'in da kwana uku Gimbiya ta dawo Rano. Mimisco ta je tare da ita ma aka maida ta rano. Sai yayyenta maza da suka je saboda sun gana da yan uwan marigayin da yaran shi. Farko sun nuna ba su so tafiyar ta ba sun nuna gwara ta zauna a gidanta ta gama takaba sai su kuma ƴan uwanta su kawo dalilin halin da ta ke ciki in ta koma gida ta na ganin mutane za ta samu ta dawo dai dai ba kamar zamanta anan ba, da haka suka amince ta koma gida amman sai da aka kai ta duka gidajen matan ta yi sallama da su. Suna kuka tana kuka an kwashe mata duka kayanta a ka rufe gidan aka mika makullin ga iyalanshi tunda sun ce suna kan tatrara abin da ya bari ne bayan an gama za a bincika in da baahi a biya in babu kuma in lokaci ya yi za su nemesu domin rabon gado. Gimbiya ta yi sallama da garin Abuja, aikin nata ba mganar shi daman tun da aka yi rasuwar ba ta je ba. Ana tunanin in komai ya lafa a yi mata transfer ko zuwa cikin garin kano ne. Kwana biyu tsakani da dawowarta na je yi ma Nene bangajiya tun da sai da ta ƙara kwana a Reno sanman ta dawo gida ita ce ma ta ke bani labarin abin da ya faru kafin ta tahowar su. "Allah sarki. Allah ya yi mishi Rahama ita kuma Allah ya ba ta dangana." Nene ta amsa da Amin kafin t ce" Ai an fara karɓa mata rubutu wajen wani malami a can rano. Da safen nan mun yi mgana da Hajiya ta ce ta fara sha da safe. To Saudatu ta rame ta lalace ta fita hayyacinta. Rayuwarta akwai tausayi sosai." Nene ta ke faɗa cikin rawan murya. Ni kuma sai na ce" Har yanzu ba ta fara dangana ba Nene? Sai ta ce a hankali dai amma in na ga Saudatu sai na tausaya mata. A gidan na yini ina nan Hauwa da Munirra suka zo da su Suwaiba domin yi ma Nene gaisuwa da barka da zuwa kaf ahalin gidan nan Yaya Usman ne kawai bai zo ba da Anty Zabba amman dai sun yi gaisuwa ta waya, har Muhammad Kabir da Nafisa sun zo gaisuwa daga katsina. Sati ɗaya da dawowarta Yallaɓai ya ce na shirya muje Rano domin na ƙara yi musu gaisuwa ban yi musu ba na shirya ashe tare da Mutakƙa ne da Hauwa sai na ji daɗi a motar Yallaɓai muka je ranar weekend yara kuma wajen Nene muka bar su gabaɗaya. Mun je mun iske mutane cike a gidan a kallah dai ba za ta yi kaɗaici ba. Sannan ga babbar Aminiyarta babbar ɗiyar Anty Zuwaira Naja'atu duk da ita Gimbiya ta girmi Naja'atu amman kuma Allah ya haɗa wannan kawancen lokacin da aka yi rasuwar ita da mijinta ba sa ƙasar suna Italy. > Janaftybaby: Kuma lokacin da aka yi rasuwar ta so dawowa sai matslan visa ya hana ta sai dai su yi mgana a waya to faa sai cikin satin nan ta dawo. Amman a kano take aure da yaron wani mashuririn ɗan kasuwa a garin kano mai suna Buhari manga. Ba su cika ma zama a Nigeria ba yawancin kuma duka yayan da Naja'atu ta haifa guda uku a kasar waje ta ke zuwa ta yi renon cikin ta ta haihu. Ita muka iske tare da Gimbiya wacce ta faɗe ta rame sai dogon fuska da hanci bakinta duk ya bushe idanuwanta duk sun zurma. Tana sanye da hijabi da caabaha. Mun gaisa da Naja'atu duk ba wani damuwa da mutane ta yi ba, irina ce shi ya sa na ke yi mata uzuri ban cika damuwa da halinta ba ammam duk in da muka haɗu za ta gaisheni da tambayan su Jidda. A ɗakin Hajiyar Tafida muka zauna ita kuma Gimbiya da ƙawayenta suna ɗakin Hajiya Kaltume kamar acan aka sauke ta tana takabar nata. Muna Rano har bayan la'asar na yo alwala daga bayin waje Hauwa ta rigani yin na ta shiga ɗakin Hajiya ni kuma lokacin da na yo tawa sai na ga maza sun shigo yan gaisuwa sun shiga ɗakin sai na wuce ɗakin da Gimbiya ke ciki Naja'atu ma ta bani darduma na shimfiɗa na ta da salla. Na kai raka'a ta biyu na miƙe a raka'a ta uku Yallaɓai ya shigo na ji muryan Mutaƙka da na Uncle Abba sai na wasu mazan amman tun da ina salla ba zan iya sanin su ba. Ina ji Mutaƙka na yi ma Gimbiya sallama daman kuma Yallaɓai ya ce bayan la'asar za mu tafi. Daga nan sai kowa ya fita har Naja'atu aka bar Yallaɓai da Gimbiya. Ban sani ba ko shi ya gane ni ce ke sallah ko kuma bai gane ni ba amman ita ta san nice na ke yin salla a wajen Suna ta gefen damana ne, ina kai sujjadar ƙarshe na ga Yallaɓai ya duƙa a gaban Gimbiya yana mai kiran ta da sunan da ya saba kiran ta dashi. "Daughter." Sai ta ɗago ta kalle shi a marairaice kafin ta amsa murya shaƙe. "Daddy." Dai dai lokacin da na ce" Assalamu alakum waramatullah Hagu da dama da kuma ƙarfi, ina juyawa bangaren dama muka haɗa ido da Yallaɓai har da ita Gimbiyan Ina salla ne amman kirjina na wani irin suya ne. Kallon yadda ya gurfana na yi a gaban Gimbiya har gwiwar kafarsa na gugan kafafunta da ke tankwashe sai kawai na kauda kaina na miƙe ina na ɗe darduman da na yi sallah da shi. Ko kunya ya ji da ya ganni sai ya yi saurin matsawa baya ya na mai miƙewa tsaye. "Da man ke ce ke salla? Ya faɗa ya na kallona sai kawai na kalle shi kafin na ce" E" Sannan na ijiye darduman a saman hannun kujera kafin na kama hanyar barin ɗakin ina faɗin" Ku cigaba da mganar ku." Ban san ko sun bi ni da kallo ba saboda ni ban juyawa ba har na fice daga ɗakin. Ba dota ba doya ba daddy ba Dada. Tun daga lokacin na rage fara'a har Hauwa sai da ta tambayeni ko lafiya na ce lafiya lau kila Yallaɓai ya tsargu ne ya sa bai daɗe a ɗakin ba ya fito ya leƙo nan ya na cewa mu fito za mu biya gidan su Nene kafin mu wuce. Sallama muka yi musu, sannan mun kara shiga wajen Gimbiya muka ƙara yi mata Allah ya jikan rai ya ba da danganta ta amsa a hankali. Daganan sai gidan su Nene muka je muka gaida Innayi ko minti talatin ba mu yi ba muka kamo hanyar gida. A cikin zuciya na ga to damuwar ta mace ce, namiji fa sunan shi Namiji ba abin da ba zai yi ba sai kawai na watsar da abin na ɗan saki fuska Yallabai daman suna hira da Mutaƙƙa ya nna ta faman sako ni a ciki da a shake na ke amsa masa sai daga baya na saki jiki muna ta hira. Sai da muka biya Gwammaja muka ɗau yara sannan muka kai su Hauwa gida muka wuce namu gidan Yallaɓai dai kamar ya kama kan shi ni dai ƙala ban ce masa ba sai shi ne da za mu kwanta ya ɗauko mganar. "Dazu Allah ban san ke ce ke sallah ba." Na yi kamar ban ji sa ba sai ya ƙara cewa" Kin san da ya ke sai a hankali. Na shiga yi mata sallama na ke ƙoƙarin lallashinta ta riƙa cin abinci." "Haka fa. Ai ka kyauta." Daga nan na juya masa baya na ja bargo. Ban sani ba ko yabi ni da kallo amman ina da tabbacin ya yi haka. Bai takuramin ba amman ya raɓo ta bayana mun kwanta. * > Janaftybaby: Haka rayuwar ta cigaba da tafiya. Wattani wajen biyu sun zo sun shuɗe kamar tafiyar iska. Har su Jidda sun yi jarabawa 3rd tearm sun yi hutu. Jidda Gidan Mimisco ta tafi hutu ita kuma Baby gidan Yaya Maimuna gida tsit daga ni sai Yallaɓai sai Saude da ke zuwa yi min aikace aikace. Bangaren asibitina kuwa tuni na yi nisa a gwaje gwajen da ake yi minib wanda na yi na ƙarshe shi ne Pap smears ne kuma har na karɓi result ɗin wannan satin da ya wuce na kai ma Dr Aisha cikin ikon Allah ta ce mini shima ba wata matsala. In da na ke ɗan samu salama kenan kuma ta na bani hop ɗin duk da saura gwaje gwajen ba mu gama ba, ba ni da watsala lokaci ne bai yi ba in ya yi zan ƙara haihuwa. Zuwa lokacin shiryen shiryen bikin Yaya Usman ake yi domin cikin watan da za mu shiga kafin azumi za a yi bikin na shi. Anan Gwammaja za a yi bikin tunda ɗaurin auran ma a kaduna ne. Yadda Yallaɓai ya faɗa mini gabaɗaya da Anty Zabba da yaran za su zo kamo sai an gama biki za su koma fatakot har da amaryan. Har anko ƙannensa su Nasara sun fidda Atamfa ce mu ma duk mazajen mu sun yi mana mu da yara. Aure dai ya tabbata ba fashi amarya na dawowa daga london aka tsaida date ɗin biki. A kuma tsuƙin ne na kirga za mu yi 15 years Anniversery da aure ni da Yallaɓai zuwa bayan sallan azumi da kwana shidda kenan. Ni kaɗai a raina na shirya za mu yi walima tun da tun na 10years ba mu kara ba lokacin Baby ta cika shekara ɗaya sai muka haɗe da birthady ɗin ta. Ba mu kara yi ba sai wanman karon na ke fatan mu sake yi. Daman a gida ne daga ni sai shi sai yara muka yanka cake ɗin mu sha hotunan mu da ciye ciye washegari kuma Yallaɓai ya fita damu mu wajen wassani da sauran su. Tun tuni na so na yi masa mganar amman bai samun lokaci Alhamdulillah yana ta samu kwangila bayan gama gina gidan buredi a Rano dalilin haka ya samu kwangilan gina bayuka na wasu makaratun sakandiri a garin na Rano sai ya kasance zamansa a nan office ba sosai ba sai dai Musabahu ya zauna wani lokacin gidan bulo kuma daman sun ɗauki yara ma su kula da shi, shi dai Musabahu manaja ne kawai. Abin da na fara lura da shi shi ne Gimbiya ta fara ƙoƙarin takura ma rayuwar aurena ta na daga can gidansu tana takaba. Ni na san cewa Yallaɓai na zuwa ganinta tun da yana yawan zuwa Rano. Ban kuma taɓa nuna damuwata ba ko na nuna fuska ban ji daɗi. Sai dai na ga ba ta da hankali in ya dawo gida sai ta kira shi a waya ta ji wai yadda ya koma gida. Da safe kuma ta iya kiran sassafe tsirfa kala kala daga ta ce Anty Bahijja za ta ba da saƙo a kawo mata sai ta ce Nene sai ta ce Anty Maimuna wani lokacin ita ce ma za ta ce ya siya mata abu kaza ya taho mata dashi tsirfa kala kala ranar da bai je Rano ba ta riƙa kira kenan ta na korafin me ya sa bai zo ba? Abin da ke ba ni mamaki shi kuma sai ya na biye mata sau ɗaya na yi masa mgana da cewa wani lokacin ta na kiran shi a waya ba ta da abin faɗa sai kawai ya ce min abar tausayi ce kuma ga shi ta samu hawan jini dalilin rasuwar nan shi ya sa ba a son ana ɓata mata rai. Na ga ƙoƙarin Yallaɓai da ya iya faɗa min haka amman kuma ta wanni fannin ban yi mamaki ba mun taɓa samun matsala da shi a baya tun ban haifi Baby ba akan Gimbiya muka yi faɗa da Yallaɓai na ce in son Gimbiya ya ke yi me ya sa ya aure ni bai aure ta ba saboda na ga bin binin ya yi yawa amman sai buɗe baki ya yi ya ce mini" In da bai haɗu da ni har Allah ya haɗa zukatanmu ba to ya ba ni tabbacin bashi da mata sai Saudatu." Har Gimbiya ta yi aure ban daina fargaban wata rana zan ta shi na ga Yallaɓai ya auro min ita ba na huta da ta yi aure amman yanzu kam bayan ta zama bazawara ta sake dawo mini cikin rayuwata ta na yi min barazana. Akwai wata rana baƙin ciki kamar na kama Yallaɓai da duka da asuban fari fa, ya je sallar asuba bai dawo ba ta yi ta kiran wayarsa ina ganin an saka Daughter na san ita se sai ban ɗauka ba. > Janaftybaby: Sau uku ta na kiran sa har wata zuciya ta ce na ɗauka sai wata ta kwabe ni sai da ya dawo na ce an kira shi a gabana ya ɗaga waya ya kirata bayan sun gaisa shi ya ma ɗauko ko wani abu ne ya faru ya na tambayanta ko akwai matsala ne ina jin muryanta ta cikin wayar tun da wayar da ɗan kara ta na faɗin. "Daddy yau za ka shigo? Sai ya ce ya na sa ran yau sai kawai ta ce" Ka taho mini da tsaraba." Shi kuma ya ce me take so ta ce duk abin da ya ke so. Tsabar takaici na kasa mgana. Sai na shanye takaicina na kalle shi ina faɗin" Wai ta gama takaba ne? Kai tsaye ya ce min" Cikin wata nan za ta fita in sha Allahu." Sai kawai na girgiza kaina, ina so na yi mgana amman kuma sai na fasa saboda maganar ba ta da amfani sai kawai na yi masa shuru kuma ya je Ranon a ranar kuma ina da tabbacin ya yi mata tsaraba tunda bayan ya dawo gida muna tare ta kira tana yi masa godiya. Ƙarin abin haushin ma wani lokacin in dai ya kai dare a can abincina sai dai ya zama kwantai sai ya ce Hajiya ta matsa masa ya tsaya ya ci abinci. Kuma Yallaɓai na ganin ina nuna damuwar hakan a saman fuskata bai taɓa damuwa da ya ba ni haƙuri ba shi a wajen shi ba a yi komai ba sai kawai na koma gefe na na zura masa ido ina ganin gudun ruwan shi amman dai ni na san ko na ƙi ko na so ai ƙarshen alewa daman ƙasa ne. KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 07045308523. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *🅿️17* Shirye shiryen biki Yaya Usman kawai ke kan layi yanzu saboda bikin ya rage saura kwana takwas. Kuma da ya ke bikin anan Gwammaja za a yi ita kuma Amarya a Kaduna gidan kakkaninta wanda ya haifi mahaifinta. Shima tsohon Soja ne mai ritaya amman ya rasu. To nan za a ɗaura aure ranar asabar amma taron biki ranar jumma'a ne asabar da an gama ɗaura aure amarya da tawaganta za su sauka a Kano sai ranar litini ango zai ɗau amaryansa da iyalansa su hau jirgi zuwa fortacol Kuma auran daman na yan boko ne lefe ma kuɗi kawai ya tura ma Amaryan aka ce ita ma uwargidan an ce ya ba ta kuɗi bayan ya biya mata Hajji shi da ita da Amarya bayan sallah da an fara tafiya za su ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Zuwa lokacin hatta abincin da za a dafa Yaya Usman ya saka an kawo. Biki dai za a yi na masu da shi, ba talauci a ciki ba kuma ɓarnan dukiya dai dai ruwa dai dai tsaki. Gimbiya ta gama Takaba tsakanin bikin Yaya Usman saura kwana goma ne. An yi walima da taro a can Rano amman ni dai ban je ba. Na ga dai su Anty Bahijja sun ta ɗora ta a status suna mata addu'an Allah ya kawo wani mijin na alheri ya kuma ƙara mata dangana. A cikin hotunan akwai wanda aka ɗauke ta a ranar da ta fita takaban ta yi kwalliya amman ta yi rama duk da dai haka a raina na ce dangana ai ta riga da ta samu ko Yallaɓai bai mini mganar ba nima ban yi masa ba. Na kuma ƙara ganin ƴan'uwan suna yi mata addu'a a group ɗin iyalan Marigayi Muhammad Inuwa 02 wanda muke ciki gabaɗayanmu har mu surukan gidan da a can Ranon gabaɗaya amman kuma suna da wani wanda ba ma ciki shi kawai na iyalan gidan ne gabaɗaya shima na sani ne saboda ina gani a wayar Yallaɓai. Kuma shi wannan da muke ciki daga baya aka saka mu, sannan ba a cika ma mgana ba sai ta kama ina ga sun fi yin ɗan sirrin su a can ne saboda ire iren mu da suke gani kamar bare. Yallaɓai kuma daman shi harkan chart ba wani damun shi ya yi ba. Yana yi ba wai ya yi ba ne, saboda harkokin shi da jama'a amman sai ya yi wata biyar bai saka status ba. In ma ya saka sai mutuwa ko in ya nishaɗu ranar Jumma'a ya saka salatin Annabi. Amman ni na san yana kiran Gimbiya a waya tun da ina yawan ganin sunanta a call long ɗin shi ba da kuma Niyyar bincike ba sai saboda wayarsa ba ta da shamaki a hannuna kamar yadda nima tawa ba ta da shamaki a hannunsa. To a irin haka ne ranar da ta yi fitar Takaban wayar na hannuna da daddare Yallaɓai ya shiga Tiolet saƙon ta ya faɗo Allah na gani ban buɗe ba amman daga sama na hango godiya zuwa ga Daddy na, na gode bi sa ɗawainiyar da ka yi ta yi da ni. Daga nan saƙon ya yanke gudun shiga hurumin da ba na wa ba sai na kauda kaina ban buɗe masa saƙo ba saboda ba ni aka tura mawa ba da ya fito kamar in faɗa masa an tura masa saƙo sai kuma na fasa na ajiye masa wayarsa a raina na ce ai zai gani. Yadda na gani ban nuna na gani ba, nima kuma bai nuna mini komai ba, sai kuma da safe kafin ya fita na ji suna waya lokacin muna dining ina haɗa masa abun kari, alƙwarin da na yi ma kaina shi ne zan zura masa ido na ga iya gudun ruwan shi daga shi Gimbiyar. Amman abin na sukan raina ganin gabaɗaya idon ta na kan mijina kamar shi kaɗai ne a dangi? Sai wata zuciyar ta tunasar da ni a lokacin." Kin manta ba namijin da ta yi ma so irin mijin ki? To ko dai angulu ne ke marmarin son ta koma gidanta na tsamiya? ** LARABA." Yau mun wayi gari ranar laraba. Kimanin jibi Jumma'a taron bikin a can Kaduna, mu kuma nan sai ranar asabar tunda mu za mu tarbi amarya. Ita kuma Anty Zabba ta iso kano ita da ya'yanta amma a gidansu ta sauka ta ce ita a can za ta yi nata taron biki. Mijin ta kuma ya amince shi ya sa ma kowa bai damu ba. > Janaftybaby: Sai dai wanda ya ga zai iya bin ta can sai ya je, ni tun da na ji haka na ce me zai kai ka? Ai sai a ce ka je ganin gulma ne gwara mu tsaya nan Gwammaja in ta zo ma haɗu a gaisa. Tun safe na tashi ina aikace aikace saboda mun yi da su Hauwa a Gwammaja za mu yi ni saboda aiki. Tun asuba da na tashi ban koma ba, tun watan da ya gabata hutu ya ƙare mini Yallaɓai ya cika alkwari ya saka Saude a makaranta wata private school ce mai ɗan sauki sauki a nan kusa da anguwar Ɗorayin ta ke da kafa ma Saude ke zuwa shi ya yi mata komai har uniform da jaka da takalmi an saka ta Jss2 saboda ta yi girma a jss1. Tun da ta fara zuwa makaranta shikenan aikin gidana ya dawo kaina saboda ba ta samun lokaci sai biyu suke ta shi in kuma ta dawo da la'asar ta na zuwa islamiya. Sai alhamis da jumma take zuwamin in ta dawo daga makaranta tun da ba islamiya weekend kuma sai ta je Allo ta dawo. Aiki duk ya yi min yawa rabo na da barcin safe har na manta da su Jidda sun tafi makaranta zan fara gyaran gida ina gamawa na je na tada Yallaɓai ya yi wanka ya zo mu karya to sai ya fita ne nake samun daman kwanciya na huta bayan azahar irin uku saura na miƙe na shiga kitchen na ɗora girki saboda yan makaranta. Kibar da na fara yi saboda hutu duk ta zazzage ga shi daman ni ba gwanar aiki ba. Ina yi ina jin na gaji kai har gobe ba zan kaunaci aiki ba. Ga shi yanzu Yallaɓai ya lalace ba iya taya ni da komai ko da ya na gida ne sai dai ma ya yi ta mini dariya in ya ganni na yi shigar aiki na tsuke cikin Boom short da ƙaramar riga sai ya hau tsokanata. "Sadiya ƴar laushi barka da aiki." Ranar haka ya ke shan harara ba na ma tanka shi domin na biye masa sai ya ɓata mini lokaci shi kuma bai tayani ba, ballatana ya rage min wani aikin Ahalin na san ba abin da bai iya ba shima kuma ya san na san ya iya komai. Yau dai aiki ya kacame mini ga wanke wanke jiya ban yi da yamma ba. Jidda ta so ta yi lokacin an kusan mangariba sai na ce ta barshi sannan ga shara na gama sai na yi mopping tunda na ɗan kwana biyu ban yi ba sannan na saka turaren wuta a burner gidan ya ɗau kamshi. Na riga na wanke tiolet ɗin su Jidda saura na mu shi na shiga na wanke ban gyara Bedroom ɗin mu ba Yallabai na kwance ya na barci har da minshari. Falon yara na koma na zauna ina maida numfashi. Na huta kafin na tashi na yi wanke wanke. Amman na so Yallaɓai ya ta shi ya yi wanka ya karya sai na haɗa komai na wanke domin da na fara shara na fara jin jiri tuni na je na karya cikina ya cika to ina zan zauna shi ya na can kwance ni kuma ina aiki yunwa ta far min a ciki na faɗi a sume tuni na nema ma kaina mafita na karya na barshi. Na yi hutun sama da minti talatin domin kallo ma ne ya ɗau hankalina wani film ɗin hausa da suke haskawa tashar Arewa24 na ga ya fara mini kyau sai na zauna ina kallo tuna ina hutun jaki da kaya a saman kaina ne ya sa na miƙe. Har na fara wanke wanke kuma sai na tsame hannuna a cikin ruwan omo na wanke da ruwa na fita zuwa cikin bedroom ɗinmu. Tsaye na yi kawai a gaban gado ina kallon Yallaɓai ina sanye da wando baki plazo rigar jikina vest ce ta lame min jiki kaina ɗankwalin doguwar riga ne na yi gammo da shi a saman kaina. Zuwa na yi kusa dashi, na fara jan bargon ina kiran sunan shi amman sai ya juya ya na jan bargon ina ja, alamun dai ba zai iya ta shi ba. "Yallaɓai.." Na faɗa ina dai dai ta saitin kunnuwan shi. A hankali ya buɗe idanuwansa da suka shige ciki saboda barci. "Mene ne kuma? Ya faɗa da muryan barci har ya na wani yamutsa fusaka ina ganin haka na saka hannuna na shafa kumatunsa sai ya ji sanyi da sauri ya ware ido yana kallona ni kuma sai na koma na riƙe kugu ina kallonshi rabi harara harara. Ɗan tashi ya yi kaɗan ya na jingina da jikin gado kafin ya kalleni daga sama har ƙasa sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Me kuma na yi! ? Baki buɗe na ce" Me ka yi fa ka ke tambayata Yallaɓai? > Janaftybaby: Ya na kallona ya ce" To ba dole na tambaya ba, kin ta da ni kamar yaƙi. Ga shi ke kuma kin riƙe kugu kamar mai shirin dambe." Yana cewa mai shirin dambe na dunkule hannu na ware kafa ina masa gusha gusha sai na kai masa hannu kamar zan naushe shi. Dariya ya ke ta yi kafin ya ce"Oh yau tekwando rana za mu yi kenan! To ai na iya irin wannan ba ri ki gani" Kawai sai na ga ya sauko ƙafafunsa ƙasa ya janye bargon sanin halin shi ya sa na yi saurin dawowa dai dai na riƙe masa hannu ya koma ya zauna na zauna a gefen shi na mararaice ina faɗin" Yallaɓai na." Na faɗa har ina masa fari, ina zan yarda ya yi wasan chinese da ni. Lokacin ina amarya sai ya ce mu yi daga karshe dai na gane ni ce ke shan wuya ya fi ni karfi awasa duk ya naushe ni in na yi shagwaɓa na ce da zafi sai ya ce wai saboda kashina ya yi ƙwari kuma nan gaba ya koya min faɗan kare kai. Daga baya na ce ni wallahi ba na so shi ya sa muka daina amman ina amarya ba wasannin da ba mu sha yi ba. Ko dawowarmu nan gida in ya na da lokaci muna yar gudu ni da shi da yara ranar weekend muna da kayan jugging. Daga baya na daina fita saboda na gaji ban iyawa shi kuma ya ce wai na tara kitse ne shi ya sa. Sai dai ranar da ya so ya na fita tare da jidda da Baby ya na kuma gaya musu motsa jiki na ƙara lafiya a jikin ɗan adam. Yadda na yi masa farin ne da yanayin maganata ya sa ya san akwai abinda na ke so. Cikin mirmishi ya ce" Me kike so ne Sadiya? Domin in za ki cuce ni haka kike yi." Hannuwansa na riƙe cikin nawa na marairaice ina faɗin" Haba Yallaɓai na wani rin cuta kuma? In miji ya taimaki matarsa sai a kira shi cuta? "Kamar wani taimako kenan? Ya faɗa ya na mai tsare ni da ido da sauri na marairaice kafin na ce" Yallaɓai na yi shara na yi mopping na wanke Tiolets baya na duk ya kage to kuma ga wanke wanke can ba a yi ba." "To shi me? Wai na je na yi wanke wanken? Ya faɗa yana kallona da sauri na ce" Ni ban ce ba." Sai kuma na saki hannun shi na miƙe ina tafiya daƙyar kafin na ce" Ka tausaya mini Yallaɓai Allah bayana ke ciwo." "Kina da ciwon baya ne ban sani ba? Ban juyo ba na ce" To ni dai ina tunanin tun lokacin haihuwan jidda na goce. Kasan kuma sai a hankali a hankali ya ke tashi." Da iya gaskiya na faɗa domin wani lokacin in na yi aiki bayana sai ya rike amman sai Yallaɓai ya ce" Ba shakka. To sannu." Yanayin mganar na shi ya sa na san bai yarda ba sai na juya ina faɗin" Fisabillahi Yallabai yanzu ka lalace sam ba ka son aiki." Me Yallaɓai zai yi ba dariya ba, ni ko sai na tsaya ina kallon shi da gaske fa haushi ya ke ba ni, ya na gida ace ba zan more shi ba. Sai kawai na tura baki kafin na ce" Ko a da ka fi tausayina ne! Yanzu kuma ka daina tausayina ko? Ganin yana kallona yana dariya yasa na fara matsan kwallar karya ina faɗin" Ko dai ka daina sona ne Yallabai? Na tsare shi da ido har lokacin fa bai daina dariya ba. Sai kawai na fashe da kukan da ba hawaye ina faɗin" Na shiga uku Yallaɓai na ya daina so na" Ya na dariyan ya ƙariso ya rumgumeni yana faɗin" Mamaki na ke yi da har yanzu ba ki san aikin da nake yi mai muhimmanci a cikin gidan nan ba? Sai na ɗago ina kallon shi kafin na ce" Wani aiki ne? Barci ko? Sai kawai ya kai hannun shi saman ƙirjina ya na shafawa ina kallon shi na ga ya dage min gira ai da sauri na kwace jikina ina faɗin" Ai daman anan kafi auki ba za ka zo ka tayani aiki ka motsa jikin ka ba." Na faɗa ina tura masa baki. Yana dariya ya ce" Ai abin da nake yi shi ne babban misalin motsa jiki." Sai kawai na jinjina kai kafin na ce" Kuma kana taimakon kanka ba." Sai ya daga hannu saama kafin ya ce" In ji wa? Taimakon kai da kai dai ko? Balla masa harara na yi na kama hanyar fita ina faɗin" Kai dai ka sani." Ina jin sa ya biyo bayana yana faɗin" Ciwon bayan ya warke ne? Sai na tuna da sauri na riƙe kugu na sauya tafiya ina cije baki. Yallaɓai dariya har tana sauti na yi masa banza na fice ina faɗin ai sai ya yi ta kwanciya. > Janaftybaby: Har na dawo zan cigaba da wanke wanke ya leƙo ya ce na zo na bashi abin karyawa. Dole na koma falo na haɗa masa tea na zuba masa ɗumamen tuwon da na yi jiya da daddare miyan allayu zama na yi sai da ya gama ci muna yi muna hira bayan ya gama na tattara komai zuwa kitchen sai ya biyo ni ya na faɗin" Je ki huta bari na yi " Ina jin haka na daka tsalle na rumgume shi na bashi sumba a baki kafin na ce" Yaron kirki Yallaɓan Sadiya." Kaina ya dankwanfar ya na faɗin" Sai na fasa." Da sauri na ce" Na tuba ranka ya daɗe ka yi mini rai." Yana dariya ina dariya ban kuma iya zuwa na huta ba saman cabinet ɗin kitchen ɗin na haye na zauna yana wankewa ina karba ina jera su a muhallinsu. Anan ne ma ya ke ce mini yanzu ya girma iyalai sun fara taruwa ba girman shi ba ne a ka ga yana aiki Ni ko sai na buɗe baki na ce" To mi ye a ciki? Ko ƴayan ka sun gan kana aiki ba abin kunya ka yi ba ka na koyi da sunnar ma'aikin mu ne kuma daman da shi muke koyi " "Uhm daɗin baki ko? Ya faɗa ya na kallona da sauri na ce" Haba Yallabai ai tsakanimu ba daɗin baki sai dai gaskiya da gaskiya." Na faɗa ina masa yar dariya sai kawai ya kalleni ya girgiza kai kafin ya ce" To ke ina wani aikin da kike ta zuzutawa? Tun auran mu tare muke aikin nan ban daɗe da daina yi miki girki kina kwance ba." Sai na buɗe baki ina kallon shi, ban rufe ba ya cigaba da faɗin" Kuma hatta renon su Jidda tare muka yi shi to ina aikin da kike ta kira? Sai na rufe bakina na kasa mgana sai da ya yarfa min ruwan wanke wanken da ke hannun shi yana faɗin" kin kasa mgana ne? Sai na kauda kai ina faɗin" To na ga abin ya koma gori ne gwara a bar mganar." Dariya ya yi yana ƙokarin sake mgana na yi saurin cewa" Yallabai yau ba za ka fita ba ne? "Zan fita mana. Zan je office akan mganar aikin nan na kaduna ki yi min addu'an Allah ya sa ta faɗa za mu samu alheri in sha Allahu.'" Da sauri na ce" In alheri ne Allah ya tabbatar in babu Allah ya kawo na alherin." "Amin Amin Abar ƙauna ta." Ya faɗa ya na min wani kallo sai nima na tsume ina masa kallon soyayya. Sai kawai Yallaɓai ya ce a hankali" Ko mu je mu yi ɓarnan ruwa ne mu dawo? Da sauri na ce" A'a. Fita fa za ka yi nima zan je Gwammaja." "To mu haɗa wankan mana ba shikenan ba." "Ba ko shiken nan ba.' Na faɗa ina haran shi, dariya ya fara yi min kafin ya ce" Me ke damun ki ne? Allah kin fara zama raguwa." Ko magana ban yi masa duk irin ƙokarin da nake yi wai na fara zama raguwa. "Na ƙosa ki sami ciki irin na Baby. Ko banza ki yi ta nema na ni kuma da sunan taimako ina shan Shagalina." Kafaɗansa na kaima duka ina faɗin" Ba Amin ba." Shi kuma ya na min dariya har ya na maƙale murya yana tsokanata. "Yallaɓai na. Uhm Uhm.." Kunya ta kamani na saka tafukan hannuna ina rufe fuska shi kuma ya na mini dariya. In na tuna lokacin har kunyar kaina na ke ji abu kamar cin tuwo na maida shi, ba na gajiya ni dai kawai a yi kuma da an gama sai na ji a lokacin nake son abin gaskiya ba zan so na samu ciki irin na Baby ba. Haka dai Yallaɓai ya gama wanke wanke sai na ce ya cika ladanshi ya wanke wajen ya goge mini kitchen ɗin harara ta ya yi ya ce" Shi wannan ɗin ba ni da lada ne ko ba ki gode ba ne? Da sauri na ce" Na gode. Allah ya ƙara girma mai girma Tafidan Rano." Kaina ya shafa ya na faɗin" Rayuwarki ta yi albarka ɗiyar ga." Ni da shi muka saka dariya gabaɗaya. Haka nan ya haƙura ya tayani muka gyara kitchen ɗin muka goge sannan muka koma ɗaki Yallabai dai sai da ya aikata abin da ya ce wato mu ka haɗa wanka Musbahu na ta kiran shi baƙi sun iso amman shi ya na gida yana shagali. Tare muka fita bayan mun shirya na rufe gida bayan na ɗaukan ma Baby dogon wando kawai suna da kayan sawa a gidan Nene domin wani lokacin in sun je sun kwana ba duka kayansu suke dawowa da shi ba, ni kuma ba na damuwa saboda irin haka suna wucewa daga makaranta ba ni da haufin kayan da za su sauya. > Janaftybaby: Yallaɓai na sauke ni a Gwammaja ko shiga bai yi ba ya wuce office ya ce mini sai ya dawo A can na samu Hauwa Munnira ce ba ta kariso ba. Gida cike da dangin Maman Farko sannan a bangaren ƴaƴa kuma su Anty Zulaihat da Nasara sune kan gaba su da su Anty Bahijja. Anty Zuwaira kuma da ya ke yar sabga ce ba ta zo ba ƙila sai yamma. Suwaiba, Jamila da Hindatu duk suna nan Safiya ma haka Hafsat ce tana Abuja ba ta ƙariso ba matar Muhammad Sani an ce sai Jumma'a za su taho tare da mijin nata. Ummu Salma ma da ke aure a Bauchi da wuri ta zo, na zo ba daɗewa Jawahir ta dawo daga makaranta sun samu hutun sati biyu. A ɗakin Nene na sauka. Tunda nan ne ɗakin Uwar mijina. Ana mganar abincin da za a yi su Anty Bahijja suka ce a yi tuwo da shinkafa sai alale sannan za a yi zoɓo duk da akwai lemuka da ruwa da aka sauke sai Nama da aka ce za a kawo naman sa da na rago za a gyara a soya domin a yi amfani da shi ga baƙi masu zuwa. Sai can bayan azahar sai ga Muninira Halima ma sai bayan la'asar ta zo. Mu surukan gidan muka gyara wake tunda an farke shi ya fara ƙwari bayan mun gama an kawo kayan miya da yawa ni dai daman yar laushi ce su Hauwa na bari da gyaran kayan miya ni dai na gyara albasa Munira na yi min tsiya gyaran albasa kaɗai ne aiki a wajen? Na ce shi ne na ga zan iya. Hauwa dai an yi dama dama cikin gyaran kayan miya ina zan iya. Ba zan yi ba ada dai kam na yi amman ban da yanzu. Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya zo muka koma gida washegari ma Alhamis mun koma ranar nama aka gyara aka soya sai kum an tafasa kayan miyan da aka nuƙo. A ranar baƙin Rano suka iso har da Gimbiya a ciki ban ɗauka ma za ta zo bikin ba amman sai na ji ana mganar har da cuku cukun transfer ɗinta ya kawo ta bikin. Sai can da mangariba ne ma muka haɗu muka gaisa. Baby dai ta kawo mini chaculate ta ce Anty Gimbiya ta ba ta, ba tun yau ba tana son su Jidda ba kyauttukan da ba ta yi musu tun tana gida ko bayan auranta da suka je honeymoon da mijinta Paris ta siyo musu kaya masu kyau da yarari. Can da dare ma tare na ganta da su Jidda da yaran Naja'atu. Sai ranar jumma'a Ango ya iso gida. Sai ihun ango ƴan uwa ke yi masa yana kamewa kusan Soja da tsare gida a ranar ma Tariq ya zo shi da Faridarsa. Muhammad Sani da Nafisa tun da safe suka iso shi Jafar ma da matar shi Nauwara ma sun iso ranar duk da Kaduna za a ɗaura auran amma dai ya zo gida shima. zuwa kuma yamma komai an kammale shi. Za a yi waina amma an ba da ne a yi sai dai Tuwon da miyan anan gidan za a yi shi kuma Alalen Anty Bahijja ta ce namu ne mu surukai mu za mu yi tsakani ga Allah ta na son ɗora mana wahala. Hauwa da Muniira na bar ma jagoracin su da ya ke a nan gidan suka kwana ni kuma gidana na koma na kwana na ce musu in sun ga ban zo da wuri ba kar su jira ni su fara aikin daman sun san halina ba da wurin zan zo ba. Jidda nan ta kwana tare da yara sa'aninta ita kuma baby ta na tare da Gimbiya Yallaɓai ke faɗa mini ta kira shi a waya ta faɗa masa ta tafi da Baby gidan Naja acan za ta kwana. Da safe sai da na sha barcina na gajiya. Yallaɓai ma a gida ya barni na dai shirya shi cikin wata dakakkiyar shadda mai ruwan ƙasa har da babban riga hula da takalminsa bakaƙe haka ma agogon fatan dake hannun shi na fesa masa turare na bishi da Allah ya kiyaye ba da motarsa ya je ba shi. Da shi da Tariq motar Uncle Abba za su bi zuwa Kaduna. Motar shi kuma Muttaƙƙa zai tukata zuwa Kadunan shima ɗaurin aure 11 ne na safe tun takwas suka ɗau hanya. Ni ina gida ma sai wajen goma da rabi na fita. Rahila ta kira ni ta ce za ta zo na ce sai ta zo domin ni ban gayyaci kowa ba Yaya Balki ma da ta yi mini mganar muna da biki ba gayya na ce ni ban yi gayya ba. Sai dai in sun zo domin Allah Gwaggo daman ta ce sai bayan biki za ta je Allah ya sanya alheri. Ma'u daman na san za ta zo balle Uwar ɗakin nata ne yan gaba gaba. Ko da na je su Hauwa sun gama alale Munnira na ta harara ta na ce su yi haƙuri na tsaya shirya Yallaɓai ne. > Janaftybaby: "Au to me Yallaɓai? Mu ma ai muna da mazajen da za mu shirya amman ba mu je ba sai ke mai Yallaɓai a 'a yallaɓiya" Munira ta faɗa ta na mai ƙara ɓalla minibharara. Ina dariya na ce" To ai ban hanaku ba. Da kun tafi kuma" Hauwa ta ce" Mu tafi Anty Bahijja ta tsire mu ko? Daman da ba ki zo ba ta ce Munirra ta ɗau girman tun da ke ba ki daraja girman da Allah ya ba ki." Ina dariya na ce" Ran Munirra ya daɗe. Zan zama mai yi miki biyayya." Kafaɗata ta daka tana dariya. Hauwa ke faɗa mini Nafisa ba ta da lafiya ta na ta amai ba ta yin komai ba na ce yanzu haka ciki gare ta. Nauwara kuwa gidansu ta gudu har na zo ba ta dawo ba. Shashen Marigayi Hajiya Karima muka gyara muka zauna tunda sauran duk ya na cike da jama'a Shashen Nene duk mutanen Rano ne Hajiyar Tafida ma da safe ta iso. Ni daman na yi wanka na a gida Jidda na nema na bata kayan da za ta saka da takalmi da mayafi saura na Baby ne an ce ba su dawo ba. Faridan Tariq kuma suna da ƴan uwa acikin gari can ta je ta kwana bayan ta dawo itama muna tare. Sameena ma sai a ranar ta so ashe ba ta nan ta je can Niger wajen dangin mijinta duk muna tare da su anan ɗakin. Karfe sha ɗaya da mintina goma Nasir ya kira Munnira ya ce an ɗaura aure acan ma cikin gida an kira su Anty Bahijja sai suka fara guɗa suna ta iface ifacen murna. Sai wajen sha biyu muka sake wanka muka saka ankom mu. Ni na yi kitso amman ban yi ƙunshi ba saboda wacce ke yi min kunshi ta yi tafiya kuma wacce ta yi ma su Hauwa na ga kunshinta bai yi min ba sai ban yi ba. Mu aka bari da wahalan raba abinci shi dai na yi saboda Mimisco ce ta kirani da kanta ta yi mini mgana shi ya sa na yi abin da ta ce. Kafin bayan azahar kowa ka gani ya ci kwalliya sannan wasu sun ci sun sha ko na ce ana kan cin da sha ɗin. Sai a lokacin su Baby suka dawo an saka mata wani leshi mai duwatsu dogowar riga sai da na natsu na fahinci anko ne irin shi ne a jikin Gimbiya da Naja'atu da ƴayanta sun kuma saka musu ƙananun hijabi a saman kansu har takalmin su baki mai igiya iri ɗaya ne. Baby na ta murna ta nuna mini na ce kaya sun yi kyau na kuma yi ma Gimbiyar godiya ta na mirmishi ta ce mini bakomai. A she ban sani ba har da Jidda sai can wajajen La'aaar na ga Jidda ta sauya atamfa ta saka kayan itama tana murna ta ce mini Anty Gimbiya ta yi mata na ce ta gode. Rahila da Yaya Balki ne suka zo min biki domin ba zan saka Ma'u da ƙawarta a lissafina ba. Ni fa ban ma san ta zo ba sai da Yaya Balki ta ce kafin su fito sun yi waya ta ce musu ta na gidan tun ɗazu na ce ni kam ban san ta zo ba sai da suka ci abinci na raka su ɗakin Maman Farko suka yi mata Allah ya sanya alheri daganan muka shiga ɗakin Nene nan na ga abin mamaki Ma'u da ƙawarta shema'u filet ɗin abincin su cike da kaji da nama sannan suna tare da su Gimbiya da Anty Bahijja ana ta hira ana shewa. Tana ganin mu ta tsargu ni ko da gangan na kalleta kafin na ce" Su Ma'u manya maso bare kiƙi dangi. Kin zo amman ba ki iya nema na ba? Sai ta fara kame kamen ta nemi ni ba ta ganni ba sai tana taɓe baki kafin na ce" Muna shashen su Jawahir tare da su Hauwa." Nan dai muka gaisa ni dai na kai su ciki su ka gaida Nene da Hajiyar Tafida bayan mun fito na ga sun tsaya suna mgana da Ma'u da shirina na yi tafiya ta. Allah ya so mu ma Mimisco ta ce mu ɗiba komai saboda namu baƙin kuma daman ina nemanta saboda ba a diɓar mana na mazajen mu ba, mun yi waya da Yallaɓai duk da sun yi reception a can akwai bukatar mu ijiye musu abinci. Anty Maimuna na tare da baƙin ta dangin mijinta. Sulaihat na gani na ce ina Mimisco sai ta ce mini tana bangaren Hajiya iya sai na kalli Anty Bahijja ina faɗin. " Anty Bahijja muna bukatar nama sannan da waina." Kai tsaye ta ce" Duk wanda aka ba ku fa? Nima kai tsayen na ce" To na mutane ne wannan, shi wannan da na ke magana na mazajen mu ne da suka tafi ɗaurin aure ne na yi ma Mimisco ma mgana." > Janaftybaby: Sai gabaɗaya suka kalleni har da Gimbiya. Sai Anty Bahijja ta riƙe baki tana faɗin" To ma su miji. Mu namu mazajen da suka tafi fa? Ba su da rai ne ? Ina dariya na ce" Kowa na shi ya sani Anty Bahijja. Ba zan hanaki ki ijiye ma Baban Sulaihat ba. Amma ni kam sai na ijiye ma Yallaɓai duk abin da na ci." Naja'atu ta buga guɗa kafin ta ce" Kin burgeni Anty Sadiya. Shi ya sa Kawu dai ya fara ajiyan tumbi." Ina mata dariya na ce" Ai na iya kiwo ne." Ta ce kwarai kam. Sai aka maida mganar dariya Anty Bahijja ta miƙe ta na faɗin. "Muje mai Yallabai." Ta faɗa tana riƙo hannuna sai aka kara saka dariya ni ko sai na rike ta muka fita daga falon muna tafe tana ce mini wai shi Yallaɓan nan ba zai ci abinci acan ba ne? Na marairai ce na ce zai ci amman akwai tafiya kar ya dawo ya na jin yunwa. A can shashen Hajiya iya muka je ta diɓar min waina da naman na je na kawo kula ta saka mini tana ta min tsiya Mimisco ta kare min da cewa abin da na yi mai kyau ne mata da dama in ana sha'ani sai su manta da mazajen su. Ni dai na wuce na barsu ina zuwa na ce su Hauwa sun ci sun ƙoshi suna sakin tusa sun manta da mazajensu to ni na yunƙura na samo ma mazajen namu abinci sai suka fara min dariya nace su gode minibko na fasa ba su Munnira ne wajen gaba gaban gode mini. Su Rahila da wuri suka tafi kafin mangariba Ma'u kam tana gidan tawagan masu ɗaurin aure da amarya suka dawo. A shashen Hajiya Iya aka safki amarya da tawaganta. Ana yin mamgariba na kira Yallaɓai na tambaye shi ko yana ina? Ya ce min suna cikin gida a ɗakin Musbahu da kaina na yi lulluɓi na kai masa abinci da ruwa da lemu na san daman shi da Tariq da Uncle Abba ne nama daman da yawa na diɓar musu sauran na bar ma su Munirra domin na ga su ba su damu da cikin mazajen su ba. Yallaɓai sai da ya rumgumeni ya ba ni sumbata a baki kafin ya ce" Allah ga baiwarr ka nan Halima Allah ka jiɓanci lamuranta kamar yadda take jiblɓanta nawa." Daman sun ce yunwa suke ji. Suna ma shirin tashi su fita su je su ci abinci a cikin gari ne sai ga ni, Tariq dai ba baka sai kunni ya fara cin nama Uncle Abba kuma sai ya kalleni kafin ya ce" Sadiya na ce wai ba ki da yar ƙanwa ne a gida? Gabaɗaya suka saka masa dariya nima sai da na dara kafin na ce" Babu Uncle Abba kana so ne sai a duba maka a dangi? Sai ya ɗau naman kaza ya saka a baki yana tauna kafin ya ce" Ina tunanin haka na gaji da wulaƙancin da yaran nan suke yi mini. Yusuf a gabana bai ji kunyar kama mace ba ina kawun sa." Yallaɓai na cin waina ya ce" Ba fa Mace ba. Matata na kama. Kawu kuma ai ban hana shi aure ba ko?. In ka ji haushi gobe a ɗaura ko Tariq? Ya faɗa ya na kallonshi Tariq ya gyaɗa kai sannan ya ɗaga hannu Abba ya zungure shi da ƙafa yana faɗin" Shege sarkin cin abinci." Ni dai gajiya na yi na fita na bar su domin ba za su fasa ba sai dai idan ba su haɗu ba. Farida dai na faɗa mata ba ta damuwa Tariq na tare da Yallaɓai. Su kuma su Hauwa suka ce wai na yi musu wayau na kwashe tsokoki na bar ma mazajensu kashi ina dariya na ce" To wai na hana ku diɓar musu ne da farko? Bana son son zuciya fa. Ku dai cigaba da zama." Ranar ma ban kwana ba gida na koma amman tare da Farida da Sameena su Munnira ma gida za ta koma ta kwanta Hauwa ce na ga tana shirin ƙara kwana na ce ta je gida ta kula da mijinta tun da ban ga abin da za ta yi ba in ta kwanan Uncle Abba da Tariq Rano suka koma suka kwana Yallaɓai kan gida ya dawo su Farida a ɗakin su Jidda na sauke su da safe bayan mun karya mun yi wanka muka koma Gwammaja. Sai a ranar muka shiga muka ga Amarya. Doguwa ce baka mai jiki. A shashen da muka zauna ajiya yau ma nan muka zauna da farko ba mu yi niyyar zuwa gidan su Anty Zabba ba sai da ta kira Munnira ta ce tun da mun zama yan amarya ta yafe mu shi ne yasa muka shirya bayan azahar muka tafi can anguwarsu ta Rijiyar zaƙi. Da muka ce ga in da zamu a gidan kafin mu tafi, sai da Anty Bahijja ta yi ƙorafin ne zai kai mu? Ita da Anty Zulaihat wai ai da gangan ta ki sauka anan a yi biki gabaɗaya Mimisco ta kashe bakin su da cewa" Ku bar su je yana da kyau haka a matsayin su na surukan gidan nan" > Janaftybaby: Dole suka yi shuru. Mun je ma Anty Zabba biki da muka je har tana cewa ta yi fushi nima ta ce ko waya ban kira ba na bata hakuri. Anty Zabba har ta ɗan rame amman kuma ta yi gayunta tsab da ita itama ta yi taro gidansu cike da mutane yaran nata sai a ranar da za mu taho suka biyo mu zuwa gidan kakaninsu a daran kuma aka zagaya da amarya duka ɗakunan gida mu ma aka tara mu aka yi mata bayanimmu ɗaya bayan ɗaya. Washegari litini da wuri Ango ya ɗau amaryansa da Rakiyan ƙannensa mata su Anty Nasara suka raka su gidan su Anty Zabba suka haɗa su suka yi musu nasiha daga nan sai filin jirgi suka ɗaga sai garin fatacol sai fatan Allah ya ba su zaman lafiya ya kaɗe fitina. Shikenan gida ya watse baƙi da nesa da na kusa zuwa talata duk sun koma gidajensu Gimbiya dai ta na nan amman na ji Hauwa na faɗin daga nan Abuja za ta wuce an kira su kan mganar rabon gado. Mganar aikin ta kuma Yallaɓai ya faɗa mini an dawo da ita nan office ɗin NGO da ke reshen Jihar kano. Amman sai ta dawo daga Abuja za ta fara zuwa aikin. A lokacin da ya ke gaya minibsai da na tambaye shi. "A wajen Nene za ta zauna kenan? Sai ya gyaɗa min kai har yana ce min" Nene ma ta karɓe ta. Ta ce sai kuma aure zai raba su." "Uhm! Kawai na ce a lokacin amman ban iya sake mgana ba. Sai bayan bikin Yaya Usman na samu damar yi ma Yallaɓai tuni kan Anniversery ɗin mu ya ce wallahi ya manta gwara da na tuna mishi. To shima zai ba ni kyakyawan surpise a lokacin in sha Allahu ina ta murna ina cewa ko Hajji za ka biya mini? Ya ce Allah ya sa haka. ** Bayan wata ɗaya da bikin Yaya Usman. Kuma a yanzu dai muna cikin watan ramadan ne har mun yi azumi takwas. Da azumi ya gabato Yallaɓai bashi da kuɗi a hannu ya samu kwangilan aikin nan na kaduna akwai kuɗin shi da ya saka a ciki, to kuma ya saba duk shekara ana yi masa kunin sadaka Maman Saude sannan yana rabama yaran dake ƙarkashin sa kuɗi ko kayan abinci. Wannan karon ma da bai da kuɗi kayan abinci mu a ciki ya ce. A ɗibar ma Mutakka da gidan su Saude. Yaran shi na Office kuma kuɗi ya ba su, sannan gidanmu kuma 30k ya ba ni na kai musu da ƙwai da yawa da dankalin turawa wanda Uncle Abba ya kawo mana an cire ƙwai a gidan gonan shi Dankalin ma shi ya kawo mana buhu a ciki na dibar ma gidanmu da Muttaƙa. Nene ma Uncle Abba ya kawo mata kwai da kayan gona muma ma mun shaida su kwaiba da mangaro har muna kyauta. Muttaƙa ma Hauwa ta ce ya samu alheri tunda shi kaɗai ne bai kai su karfi ba. Geron da Mijin Mimisco ya raba ma su Yallabai a ciki ya ce na diɓar ma su Gwaggo sauran kuma a ka kaima Balaraba na kunun Sadaka. Duk da daman a gidanmu ba mu da matsala komai akwai Yaya Hamza da Yaya Auwalu da suke da ƙarfi sun wadata su da komai, sai dai ihsani da kyauttawa namu amatsayin su na iyayenmu. Mijin Amina ma ya aiko da kuɗi sauran alherin da aka samu ta bangaren su Yaya Balki an tura shi can Yashe wajen su Baba Sani. Ko Mijin Ma'u mota guda ya kawo na kayan abinci Baaba ai tana cikin alheri shi ya sa Yaya Aina ta ce a can kura Baaba ce yar gaban goshi to tana da ƴa tana auren mai kuɗi kuma ana aika musu da alheri. Ni Rahila ke faɗa,mini har dangin Babanta da azumin nan ta kai musu alheri. Gimbiya ta dawo wajen Nene da zama saboda aikinta. Sun je Abuja tare da ƙanin mahaifinta Tafidan Rano an raba gadon dukiya ta samu gida biyi anan Abuja da kuɗi masu yawa na tumanin takaba dukkansu huɗun rabon su kenan. Su gwara su da ƴaya ita bayan tumin takaba ba ta samu komai ba. Yallabai na ji suna waya kan tana son a saida gida guda ɗaya a siya mata a fili anan kano kuɗin ta kuma Mota ta ke son siya. Da ya ke komai sai ta yi shawara da shi abin da ya ce kar a yi ta bar shi kenan wanda ya ce a yi kuma shi take yi. Ta ɗan yi facaka da ƙudin bayan Mota ta siya manyan suturu da gwala gwalai, har su Jidda ta siya ma Takalma da dogayen riguna daga Dubai oder ma ta yi, sai yan uwa suka yi mata faɗa suka ce ta fara tunanin kasuwancin da za ta fara tunda kuɗin gado kamar ruwa su ke za su ƙare ba tare da ta yi komai da su ba. *🅿️18* Azumi ya raba tsakiya, mun gama goma na marmari mun shiga goma na wuya kamar yadda hausawa ke faɗi. Yau in muka kai azumi mun kai sha biyar kenan, a duka shekarun da muka kwashe da aure ni da Yallaɓai na saba duk watan ramadana Yallaɓai ba ya kaiwa dare a waje a gida ya ke yin buɗe baki tare damu haka ya sabar mana kuma nima haka na saba. Amma wannan azumin sai al'amarin ya ɗan sauya. Saboda ya samu kwangila gina ma'aikatan nan na kaduna gabaɗaya ma'aikatan shi suna can kaduna shima yana zuwa har ya kwana ma kafin ya dawo sai ya zama na in baya gari sai dai mu yi buɗe baki tare da yara. Ranar da muka kai azumi na sha uku ya dawo daga Kaduna na yi masa har kunin tsamiya da ya ke matuƙar so, amman bai shigo gidan ba sai wajen tara na dare. Na kira shi a waya na ji ko bai dawo daga kadunan ba ne? Sai ya ce mini ya dawo ya na Gwammaja da ya faɗa mini haka har a cikin raina ban yi zargin wani abu ba, sai da ya dawo na kawo masa abin buɗe baki bai ci abinci ba,kunin ma kaɗan ya sha ya ce mini cikin shi ya cika a lokacin sai da na yi mamaki sanin Yallaɓai ba ya iya cin komai a waje sai ya dawo gida barin ma da azumi saboda ya san ina gida na shirya masa abin buɗe baki kamar yadda na saba. "Ka ci wani abu ne a can Gwammaja? Tambayar da na yi masa a lokacin kenan. Shi kuma kai tsaye ya ce mini Nene ce ta matsa masa sai da ya tsaya ya yi buɗe baki. Na ɗan yi mamaki saboda hakan bai taɓa faruwa ba ai Nene ta san ya na da mata me ya sa za ta ce sai ya yi buɗe baki a wajenta? Amma sai wata zuciya ta kitsa min kyakyawan Niyya cewa ita ɗin uwa ce a gare shi ta na da wannan damar kuma abu na rana ɗaya. Sai ko a fuska ban nuna masa damuwata ba na basar da komai ya wuce sannan ya faran tamin rai da ya ce da Asuba na ɗumama masa kuninshi ya na so ya yi sahur da shi. Haka ko aka yi da asuba bai ci komai ba kunin na ɗumama masa ya sha da buredi ni kuma da yara muka sha tea sai na soya mana ƙwai muka haɗa da shi. Ranar kuma da wuri ya dawo gida muka yi buɗe baki tare ana kiran sallar isha'i ya yi alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi sallar tarawihi kamar yadda ya saba ni kuma ni da yara daman muke yin namu a gida. Sannan da rana kuma da ba na komai sai na yi ta karatun Qur'ani tunda duk watan Ramadan in ya zagayo sai na yi sauka kamar yadda na saba. * Saude tana zuwa da safe ta yi min yan aikace aikace sannan ta ɗan rage mini aikin yamma tunda kafin la'asar ta ke komawa gida sauran aikin kuma ni na ke yi Jidda na kama min ɗan abin da ba a rasa ba. Yau alale na yi mana mai kifi da ƙwai sai na yi mana zoɓo, Yallaɓai ya aiko da kayan ciki sai na yi ferfesu shi kuma sai na dafa masa ruwan tea da ya ji kayan ganyen shayi na citta saboda ya na so duk dare Yallaɓai zai sha kafin ya kwanta. Muna da kayan marmari sai na ce Jidda ta raba biyu sauran kuma su yi fruit salat ni da Yallaɓai kuma sai na yayyaka mana tunda shi ya fi son cin su a haka. Bayan mun gama haɗa komai na bar ma Jidda gyara Kitchen ɗin amma bayan na haɗa duka kayan buɗe baki a falon su Jidda in da muke zama gabaɗayan mu a saman cafet mu yi buɗe bakin tare. Wanka na je na yi, saboda na gaji kuma yau ɗin nan ina ɗan jin azumin nan kaɗan ina fitowa wanka ana kiran salla daman ina da Dabino a ɗaki na yi buɗe baki Jidda ma na san ta yi na ta Baby dai daman azuminta rabi da rabi ne in ta ɗauka da ta yi rabi sai ta fara kukan yunwa Babanta kuma ya ce ta ci abincinta da cewa ta yi rabi gobe ma in ta yi rabi ɗaya kenan. > Janaftybaby: Sai da na saka wata doguwar rigata na Atamfa sannan na ta da salla daman na ɗauro alwala ina cikin sallar na ji ana kiran wayata sai da na idar na jawo na duba sai na ga Amina ce sai da na shafa salatin da fara sannan na kira ta daga baya. Mun gaisa ne ta yi mini barka da shan ruwa. Mu ɗan tambayi lafiyan juna kafin mu yi sallama Amina akwai ƙokari tunda aka shiga watan Ramadan duk bayan kwana biyu sai ta kirani ta yi mini barka da shan ruwa ita da Rahila suna da wannan ƙoƙarin a gidanmu. Ni ma dai farkon watan na kira duka yan gidanmu na yi musu barka da shigowa watan Ramadana wata mai albarka har Ma'u sai da na kira ban wareta ba wannan karon sannan Alhajinmu ma mun yi waya dashi sau uku kenan shi da Gwaggo saboda tun ranar da muka kai azumi na uku da na je gidan kai musu saƙon Yallaɓai ban ƙara komawa ba washegari kuma na je Gwammaja na gaishe da Nene tun daga kuma ranar ne ban ƙara fita ba. Wayar ta ɗan dauke min hankali na buɗe data ina ganin masu turamin saƙon Happy iftar group ɗin Gidanmu na shiga na ga Ya Abubakar ya turo addu'a daman shi ke da wannan ƙoƙarin Ya Hamza ya yi tagging ya ce Allah ya ba da lada. Sai ni ma na yi Tagging na ce Amin tare de cewa fatan mun sha ruwa lafiya? duk ba sa kusa da wayarsu tun da an sha ruwa ana can ana hada hadar buɗe baki sai nima na fita daga nan na ɗan duba saƙonnin private sai na ga Munnira ta yi min mgana da cewa Matar Yallaɓai sai na tura mata da amsa da cewa matar ƙanin Yallaɓai sannan na saka mata emojin dariya na fita. Datar na kashe na ijiye wayar saman gado sannan na cire hijabin jikina na ninke ina mamakin me ya tsaida Yallaɓai har yanzu bai dawo ba? Tunda Office ya je bai ma fita da wuri ba sai bayan da a ka yi sallar azahar. Falo na fita dai dai Jidda ma ta fito da Hijabinta alamun ta idar da sallah ne. "Barka da shan ruwa Umma." Ina kallonta na ce" Yauwa barkan mu dai Jiddan Umma. Ina Baby? Sai ta ce min ta na ciki ta na sallah, ganin ta juya za ta koma ɗaki ya sa na ce" Taho ki yi buɗe baki mana Jidda.' Cikin mamaki a fuskarta ta ce" Umma Abba bai dawo ba? Kai na kaɗa kafin na ce" Yana hanya in sha Allahu. Taho ko kunin ki zuba ki sha cikin ki ya warware." Sai ta amsa da toh hijabin jikinta ta cire ta zauna nima sai na zauna ta zuba mini kunun na ce kaɗan itama sai ta zuba nata sai ga Baby ta fito jikina ta faɗa tana faɗin" Umma azumi na goma.' Ina dariya na ce" Lalle Baby mai himma ce kai kai har azumin ki ya kai goma? Ta na washe baki ta ce" Umma ke guda nawa kika yi? Ina kallonta na ce" Ai muna tare da ke nima azumina goma." "Yaa Jidda fa? Ta faɗa tana kallonta ina dariya na ce" itama dai dai da naki." Sai ta miƙe ta na tsallen murna Jidda ta kalleta amma dai ba ta yi mgana ba saboda ba ta da hayaniya sosai. Har muka gama shan kunu ba Yallaɓai ba dalilin shi Baby sai cewa ta ke yi Umma ina Abba? Sai na tashi na shiga ciki na ɗauko wayata na kira shi bai ma ɗauka ba a lokacin sai da na ƙara kira sannan ya ɗaga wayar na ji hayaniya a in da yake amma ba sosai ba. "Yallaɓai na barka da shan ruwa." "Barka da shan ruwa Sadiya ta." Shima ya maida min martani. Mirmishi na yi mai sauti kafin na ce" Kana ina ne? Na ga an sha ruwa ba ka dawo gida ba." Sai kawai ya ce" Ina nan zuwa na ɗan shiga Gwammaja ne duba Nene Daughter ta kirani ta ce da zazzaɓi ta yi ni" Cikin jimami na ce" Ayya. Allah ya ba ta lafiya ka gaishe ta." Ya amsa mini da Amin sai kawai ya ce mu yi buɗe bakin mu kar mu jira shi in ya dawo sai shi ya yi na shi ban kawo komai ba na yi fatan Allah ya ƙara sauki mu ka yi sallama. Tare da yara muka yi buɗe baki ba mu ci abinci ba kawai kayan marmari muka sha sai ferfesu. Sai da muka yi sallar isha'i da tarawehi sannan muka ci abinci ni alale ɗaya na ci ma na ji cikina ya cika Jidda ta gaji da wuri ta kwanta Baby ne ma ta ɗan daɗe ba ta yi barci ba tana kallon cartoon sai da na kora ta na ce ta je ta kwanta saboda makaranta. Duk da ma yanzu 12pm suke tashi saboda azumi. > Janaftybaby: Tun ina saran dawowar Yallaɓai da wuri har na fidda rai sai na fara tunanin ko Jikin Nenen ne ya yi tsanani har sake kiran shi na yi ban same shi ba duk na damu. Ina ta tunanin Allah ya sa ba jikin Nenen ya yi tsanani ba ne kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tunda ni dai ba waya muke yi ba sai wani abu na jaje ko barka ni ba ma zan iya tuna last muka yi waya da ita ba gaskiya amma ina da lambarta kuma nima na san ta na da nawa tunda muna ganin status ɗin juna. Har na fara gyangyaɗi na ji ƙaran buɗe get sannan da shigowar motar Yallaɓai sannan na mike ina duba agogon wayata goma da rabi har ta gota sha ɗaya saura na dare. Ajiyar zuciya na sauke na fita zuwa falon farko dai dai ya buɗe kofar falon ya shigo muka ci karo da juna ni da shi. "Ya jikin Nenen? Da haka na tare shi domin a zato na jikin nata ne ya yi tsanani ya sa bai shigo gida da wuri ba. Lumshe idanuwansa ya yi daga gani a gajiye ya ke saboda ya na ƙarosowa gabana ya rumgumeni yana mai sauke ajiyar zuciya nima sai na rumgumeshi ta baya ina faɗin" Nenen na lafiya ko? Cikin muryan gajiya ya ce" Lafiya lau. Na gaji Sadiya ta ko'ina na jikina ciwo ya ke yi min." Ko bai faɗa ba na ga hakan a muryan shi da yanayin shi sai kawai na ce mu je na haɗa masa ruwan wanka ya yi wanka sai ya ji daɗin jikin shi. Muna riƙe da hannun juna har bedroom ɗim mu ina tambayan shi ya jikin Nene ya ce min da sauƙi likita ya zo gida ya dubata. Maleria ce ta kamata cikin tausayinta na ce" Allah sarki. Allah ya ba ta lafiya. Amma dai ta ijiye azumin ko? Sai da ya gyaɗa min kafin ya ce" Yau ɗin ma ta ɗauka da jikin ya zafi sai ta ajiye" Ina taya shi tuɓe kayan jikinsa ya ke tambayata su Jidda na ce sun kwanta. Kai ya kaɗa kafin ya ce" Na yo ma Baby tsaraba ya na mota na manta dashi." Ban maida masa martanin mganar shi na tura shi zuwa kofa ina faɗin" Ka yo wanka." Domin ni kaina na gaji barci na ke ji idanuwana har rufewa suke yi amma ban kwanta ba sai da na kwashe kayan da ya cire na zuba cikin kwandon kayan wanki na fito masa da wasu riga da wando masu taushi na barci. Lokacin da ya fito har na fara gangyaɗi sai da ya yarfamin ruwan hannunsa sannan na farka. "Ki kwanta mana. Kina barci a zaune? Ya faɗa ya na nufar gaban madubin ɗakin. Sai da na yi Hamma sannan na ce" Zan baka abinci ne shi ya sa ban kwanta ba." Bai juyo ba amma ya ɗau mai ya na ɗan shafawa ya ce" Yi kwanciyarki kawai na yi buɗe baki a gidan Nene amma zan duba na gani ko zan iya cin wani abu kafin na kwanta." Ban damu ba na ce to sai kawai na kwanta ina jin sa ya na faɗin" Haka za ki kwaanta? Tsabar barci umh kawai na ce masa. Daga nan ban san yadda aka ƙare ba sai dai can ina jin sa ya na cire mini rigan jikina ina ta masa magagi sai da asuba da muka tashi sahur ne na fahimci rigar barci ya sakamin kuma wani ikon Allah duk gajiya da zan ji da mugun barcina ta bakin Yallaɓai huɗu na yi na asuba na ke tashi wani lokacin ma kafin huɗun na tashi Yallaɓai ne sai na yi ta fama dashi kafin ya ta shi har mamaki na ke yi ina faɗin haka maza suke? Ni dai Yallaɓai sai na yi da gaske ya ke iya tashi Sahur in na tashe sa tun lokacin da na tashi sai ya koma barci da cewa in na gama haɗa abin buɗe bakin sai ya tashi, to fa in na gama sai na haɗa da jan hannun shi ya ke iya tashi in kuma zan kyaleshi sai an fara kiran salla zai tashi lokacin an gama ma Sahur ɗin. Kamar haka ne yau ma uku da rabi na farka barcin da gajiya duk sun sake ni na ganni na nannaɗe jikin Yallaɓai duk na yaɓa masa kafa. Sai da na yi mirmishi bayan na sauko daga kan gado na gyara masa bargo sannan na fita zuwa tiolet na ɗauro alwala na zo na shimfiɗa darduma na yi salla raka'a biyu na ɗan zauna na yi addu'o'ina sannan na miƙe na cire hijabin na nannaɗe tare da darduma na mayar ajiyar su ban ta da Yallaɓai ba sai na buɗe kofar bedroom ɗin na fita na bi ta cikin kitchen sai na ga Yallaɓai ya kwaso kololin da na bari a falo zuwa kitchen sai na bubbuɗe na gani bai ci alelen ba amma dai ya sha zoɓo kuma ya sha kayan marmari, ban damu ba tunda Baby ba ta azumi sannan nima zan ci alalen tunda jiya ban ci ba. > Janaftybaby: Gas na kunna na ɗora ruwan tea kawai. Muna da sauran buredi tunda jiya ya shigo da shi. Bayan na juye a fulas sai na ɗumama alalen sannan na soya ƙwai saboda Jidda da Babanta sai da na gama komai na kai falo sannan na shiga ɗakin su Jidda na tashe ta, ina tashin ta Baby na ji ta yi zaraf ta miƙe tana faɗin" Umma nima zan yi azumin." Kai tssye na ce" To ku wanke baki ku fito mu yi sahur." Daga nan na fice tiolet na shiga na yi brush ina fitowa hannuna da danshin ruwa na lallaɓa domin na shafa ma Yallaɓai ruwa a fuska saboda ya tashi sai dai ina zuwa dai dai saitin kan shi wayarsa ta kawo haske alamun ana kira ban saka hannu ba sai na leƙa sai na ga Daughter na kira. Mamaki ya kamani me ya sa ta ke kiran shi yanzu? Sai wata zuciyar ta ce min ko dai jikin Nene ne? Tunanin haka ya sa sai na yi niyyar amsa kiran sai na saka hannu na ɗauki wayar na buɗe bayan wayar ta yanke. Tunda na san password ɗin wayarsa ina shirin kiranta ne kawai sai ga saƙon ta ya shigo wayar har ga Allah ba halina ba ne duba wayar miji duk da wayar Yallaɓai ba ta da shamaki a wajena ban taɓa tunanin bin diddiginsa ba. Kuma har ga Allah lokacin da saƙon ya shigo hannuna ne ya faɗa kan saƙo sai ya buɗe kuma ban isa a lokacin na hana idanuwana karanta abin da ta rubuta ba. "Daddy na a tashi a yi sahur. Ko duk santin girkin nawa ne yasa ka kasa tashi? Na ga tuƙwaici na gode. Amma ka yi min laifi domin na ce ba zan karɓa ba yanzu haka ma za su dawo wajenka domin zan siya ma ƴaƴana kayan kwalliyar salla da su. Thank you so much for been their for me Daddy." Na yi ƙoƙarin bayan na gama karanta wannan na fita amma sai zuciya ta rinjaye ni na srolling sama ina ganin saƙonnin da ta ke tura masa. Tun da aka fara azumi ta ke tura masa saƙo da asuba a tashi a yi sahur sannan sai ta tura masa sakon barka da shan ruwa wani lokacin ya ba ta amsa wani lokacin ya yi shuru. Na duba saƙonin har wanda ta na Abuja lokacin da mijinta ya rasu. Wani saƙo da ya ba ni mamaki ya sa na ji kirjina sai da ya buga dam! Shine ta tura masa" Na yi kewarka Daddy yaushe za ka zo? Shi kuma sai ya ba ta amsa da Gobe in sha Allahu. Kirjina ne na ji ya fara suya, har ina ganin duhu duhu da ya sa ban ƙara gaba ba na ijiye masa wayar a nan saman side drower ɗin da ya ke kwance. Kallonsa na ke yi ina mamakin Yallaɓai ashe shima ya iya munafuncin maza? Ashe jiya ba Nene ba ce ta tsaida shi ba ashe Gimbiya ce ta tsaida shi, bayan ta yi masa girki ya ci har ya na santi daga karshe har ya na ba ta tuƙwaici ni kuma ko oho. Wani ƙululin abu ya tokaremin a kirji da wani haushin Yallaɓai don Allah menene na ƙarya tsakani ga Allah? Sai kawai na juya da na so na fita ne ba zan tashe shi ba sai dai yau ya yi ɗaure amma sai na danne zuciyata da na yi wani tunani sai kawai na dawo na fara buga gefen gadon yau ko sunan shi ban kira ba. Sannan ban taɓa shi kamar yadda na saba ba. Bai da wani nauyin barci sai gashi ya buɗe idanuwansa da suka yi nauyi yana kallona sai kawai na juya ina faɗin. "Ka tashi lokacin Sahur ya yi." Da ga haka na yi ficewata na bar shi a raina kuma na kudiri niyyar ko bai tashi ba na gama tashin shi. Daga yau sai ita wacce ke tashin sa sai ta cigaba da tashin shi. Ban da munafunci ta san ya na da mata amma wai ta ce duk asuba sai ta kira shi ya ta shi ya yi sahur? Ban taɓa lura ba saboda da na tashi na ke zuwa kitchen domin samar da abin buɗe baki ban taɓa cin karo da kiran nata ba sai yau. Tun da na zauna a wajen nan ban yi dariya ba. Tun kafin ya fito na ce ma Jidda ta zuba ma kanta da Baby sai ta kalleni kafin ta ce" Umma Abba fa? Wani kallo na yi mata kafin na ce" Kar ki ci ki tsaya jiran wani Abba." Ita kanta na san ta yi mamaki domin sai da ta kalleni ni kuma na kauda kaina ina cin alalen da ma ɗumama sai ruwan tea wanda ban saka madara ba na ke sha dashi Baby dai sai cin ƙwanta ta ke yi ba ta damu ba Jidda kuma jikinta a sanyaye ta ke kurɓan tea ɗin ta ke sha tare da buredi ni kuma a raina ina ta roƙon Allah ya sa kar Yallaɓai ya tashi yau sai dai ya yi ɗaure sai dai addu'ata ba ta karɓu ba sai ga shi ya fito ya na sanye da jallabiya mai ruwan ƙasa Baby > Janaftybaby: na ganin shi tana ƙoƙarin miƙewa ban san lokacin da na daka mata tsawa ba. "Ke koma ki zauna ko na saɓa miki." Haka na faɗa cikin zare mata ido. Daga Yallaɓai har Jidda da kallo suka bini, ita kuma sai ta kalleni ta ruɗe har ba ta san kafarta ya ture tea ɗin gabanta ba. Sai ga shi ya malale min a saman cafet kallon tea ɗin na yi yana gangarowa wani abu na tokaremin zuciya. Ganin irin kallon da na ke yi ma Baby ne ya sa Jidda ta yi sauri miƙewa ta na faɗin" Ki yi hakuri Umma bari na gyara wajen." Yallaɓai na tsaye hannunsa harɗe a kirjinsa yana bin mu da kallo barin ma ni. Kawai sai na yi kyafci ina kallon Baby da ta yi kamar za ta yi kuka na kaɗa kai kafin na ce" Lalle ko za ki ci ubanki Maimuna" Ta na jin abin da na ce ta barke min da kuka, tsawa na ƙara daka mata kafin na ce" Za ki yi min shuru ko sai na zo na tattaki a nan wajen? Na faɗa ina mata wani kallo, Sai kawai Yallaɓai ya kira ta sai ta kalleni ta kasa tashi shi kuma sai ya ce ta zo mana ya na kiranta ganin na kauda kai ne ya sa ta tashi ta nufe shi ta na kuka ta faɗa jikinsa ya rumgumeta yana faɗin" Shii Umma ce! Kyaleta kun kwance da ita ko? Kukan Baby ma ƙara harzuƙani ya ke yi amman ban yi mgana ba sannan ban ɗago kaina ba. Ina jin su yana ta lallashinta har sai da ta daina kuka sannan ya ce ta koma ɗaki ta kwanta ita kuma Jidda ta dawo da tsumma ta goge wajen tas ta gyara da na ce ta zauna ta ƙarishe shan tea ɗin ta sai ta ce mini ta ƙoshi. Uban gayyar kuma na tsaye ban kuma ce ya zauna ba sai da ya gaji sannan ya zauna a ƙasa kusa dani yana faɗin. "Zuba min tea." Da na so na ce ya kira Gimbiya sai kuma na fasa na haɗa masa tea ɗin na tura masa gabanshi da ƙwan da buredin ganin yadda na ƙi kallon shi ya sa cikin mamaki ya kira sunana. "Sadiya." Ban ɗago ba amma na amsa sai kawai na ji yana faɗin" Me ke faruwa ne? Sai a lokacin na yi masa kallon ƙasa ƙasa kafin na ce" Me ka gani? "Abubuwa da ya wa. Na ga kamar ranki yana ɓace ne me ya faru? Ke da yara ne? Ya faɗa yana kallona nima sai a lokacin na kalle shi sai kawai na kauda kai kafin na yi mirmishi gefen baki na miƙe ina faɗin" Bakomai." Abin ya bashi mamaki ganin na bar shi a falon na yi shigewata ciki kuma na san ya bi ni da kallo ban kuma ko waigo ba. Ban ƙara ganin Yallaɓai ba sai da ya zo daukan hula da carbi ina kan darduma ya ce mini ya tafi masallaci sai na gyaɗa masa kai kawai ba tare da na yi masa mgana ba. Da safe ma haka na tashi gim da raina ko fara'a ban yi masa ba daga shi har ƴayan shi Jidda dai ta ga har da safen ban huce ba sai ta sameni a falo ina zaune domin ɗakin na bar ma Yallaɓai gabaɗaya. "Umma ki yi hakuri don Allah." Har da Baby ma kamar ta yi kuka ta ce" Ki yi hakuri Umma." Sai suka ba ni tausayi laifin Ubansu ne ya shafe su sai na ɗan saki fuska na ce musu zo su wajena na haɗa su na rumgume na saki fuskata shi ya sa suka tafi makaranta suma sun warware. Amma shi kan Yallaɓai ya kasa gane kaina da ya matsamin sai na ce masa ban ji daɗi ne. "To ko mu je asibiti ne? Me ke damun ki? Kai tsaye na ce" Ba sai mun je ba. Ciwon kai ne kaɗan zai bari zuwa anjuma." Kasa fita ya yi saboda yadda ya ga ina basar dashi ya san halina dole akwai wani abu da ya yi mini ne. "Sadiya don Allah ki faɗa min me ya faru? Na ce masa bakomai ba sau adadi amma bai yarda ba. Ganin ya damu sai na ɗan saki raina saboda na ga ya na damuna da tambaya tun da ba gaya masa abin da ke danuna zan yi ba gwara na saki raina ko zai kyaleni da tambayoyin sa. Na ɗan sakin masa har muka zauna muna ta hira sai muka ganganro kan mganar kayan salla ya ce yana jiran cikon payment na aikin da suka yi a Rano ne a wannan sati sai a yi mganar kayan salla da ɗinki da sauran su ya so ba zai fita ba ne sai kuma Musbahu ya kira shi ya ce wasu mutane sun zo suna jiran shi. Da zai fita sai na ce bari na shirya ya sauke ni Gwammaja na duba Nene, da gayya na faɗi haka saboda na ji me zai ce sai kuma bai ba ni kunya ba. "Nene ta samu sauƙi fa. Ke da ba ki da lafiya, ki bari ko zuwa jibi tunda ba ki ji daɗin kema." > Janaftybaby: Kai tsaye na ce" Na ji sauƙi mu je ka sauke ni zan iya zuwa." Na ɗauka zai ƙara mgana sai kuma ya yi shuru sai da muka jira Saude ta zo na bar mata gidan daman mun yi wanka mun shirya ni shadda na saka da farim mayafi shi kuma sai ya saka kananun kaya. Da ya kai ni Gwammaja bai shiga ba saukeni kawai ya yi ya wuce office ni kuma na shiga ciki sai da na lelleƙa daƙunan su Hajiya iya muka gaisa sannan na ƙarisa ɗakin Nene na ganta garas da ita ita kaɗai ce a shashen ita ta ke faɗa mini Gimbiya ta leƙa wajen aiki. Da na yi mata ya jiki ta na mirmishi ta ce" Tafida sai da ya ta so ki? Ɗan zazzabi ne Gimbiya ta ɗaga masa hankali tun jiya ina shan mganguna na warware." Sai na yi mata fatan samun sauƙi bayan tambayan yara na ce suna makaranta mun ɗan taba hira da ita anan na yi azahar ina shirin tafiya sai ga Gimbiya ta dawo mun gaisa sama sama kamar yadda muka saba. Ta dai tambayi su jidda na ce suna makaranta. Ƙarfe biyu na koma gida na. Daga kuma ranar ko a fuska ban ƙara nuna ma Yallaɓai wani abu ba. Ban damu da ma ƙara saka masa ido ba saboda mu zauna lafiya amma ni na san ba ta fasa kiran shi da tura masa saƙo ba, amma dai bai ƙara buɗe baki a waje ba sai a gida mun shiga goman karshe an fara ibadar na tahujjud Yallaɓai masallaci ya ke zuwa ni kuma in ta da yara mu yi namu a gidaa. Ranar da za mu ɗau azumi na ashirin da 24 Yallaɓai ya dawo daga masallaci ya ɗan kwanta huɗu da rabi na tashe shi sai ya shiga tiolet yana wanke baki a lokacin na ga Gimbiya ta na kiran shi bayan ta katse sai ta tura mssa saƙo zuciya ta rinjaye ne na ɗau wayar na duba saƙon na ta. "Daddy jiya ba ka zo ba? Kuma fa na yi maka kunin tsamiya mai daɗi" Motsin fitowarsa na ji da na so na yi saurn ijiye masa wayar ne sai kuma na fasa sai da ya fito. Ya yi mamakin ganina tsaye da wayarsa sai da ya matso gabana sannan na miƙa masa wayarsa ya karɓa kafin ya samu sararin mgana na ce. "An tura maka saƙo." Ina gama faɗin haka na fice na san kuma bayan ya duba saƙon ya ji nauyi domin ba na ce kunya ba tunda maza ba su san kunya ba. Har ya fito muka yi sahur jikinsa a sanyaye ni kuma sai na yi masa bariki ban nuna masa ko a fuska na ji haushi ba sai ya ɗan saki jikinshi amma a raina na kudiri niyyar koya masa hankali daga shi har Gimbiyar ta shi. Washegari ya tura mini kuɗin kayan salla nawa da na yara sai na su Nene da na Gwaggo. Daman yana yi musu kaya duk shekara. Dija collaction na tura ma kuɗin daman mun yi mgana na zaɓi komai har Marwa na yi ma kaya da Saude saboda mun yi waya a gida za ta yi salla in ta dawo sai kuma ta gama pratical ɗin ta za ta koma makaranta. Kuma daman ta turo mini kayan na zaɓa tuni suna wajen ɗinki kuɗin ne sai da ya tura mini bayan mun gama lissafi na tura mata. Ni da yara kala huɗu ya yi mana. Leshi biyu atamfa biyu. Nene Atamfofi biyu su Hajiya Iya kowacce ɗaya sai Jawahir kala biyu Adanan kuɗi ya tura masa sai Gwaggo guda ɗaya Alhajinmu kuma shadda mai kyau. Sai ni mayafai guda biyu da Hijabi ni da yara sai takalman mu har Nene an siya mata takalmi da Hijabi gabaɗaya tun lokacin da a ka kawo kayan na nuna masa ya ce komai ya yi. Telanmu kuma daman na yi masa mgana kuma ga kuɗi har da na Nene na kai mana ɗinki tare da na Jawahir da Marwa Saude kuma na ta na bata mamanta na ɗinki ita za ta ɗinka mata. Gwaggo kuma da Alhajinmu na kai musu na su suna ta godiya duk da suma su Yaya Hamza duk sun yi musu. Nene ma na kai mata takalmi da hijabinta na ce kaya na wajen ɗinki ta na ta saka albarka. Ranar da muka ɗau azumi na ashirin da shidda Mimisco ta aiko da kaya yan kanti kala biyu biyu na jidda da baby. Anty Bahijja ma ta aiko musu da material a ɗinke sai Anty Maimuna itama kala biyu amma Bby uku ta yi mata har da wani riga da wando masu kyau da takalma. Gimbiya kuma Yallaɓai ta ba ma kayan ya kawo ma su, kayan kwalliya ne sai hijabai da mayafai sai takalma masu igiya sai abun hannu da ɗan kunne sai kwalban da ake kitso da shi kayan kuma ta ce suna wajen ɗinki duk Yallaɓai ne ya ke koramin jawabi nan yaran suna ta murna shima bakin shi ya ƙi rufuwa. Daga gani ya ji daɗi kuma har hakan ya nuna a saman fuskar shi. > Janaftybaby: Ni dai ban nuna masa komai ba na yi godiya har ya na saka min kati a waya ta ni kuma na san na kiran da na ce zan yi ma Gimbiya na yi mata godiya ne. Kai namiji munafuki ne wallahi. Ranar da muka ɗau azumin ashirin da bakwai ɗaure Yallaɓai ya yi saboda na zo tashin shi na ga Gimbiya na kiran shi sai kawai raina ya ɓaci ban tashe shi ba. Ni kaɗai na yi sahur saboda Jidda na ce ta huta jiya ta sha wahala. Yallaɓai bai tashi ba sai da aka fara kiran salla lokacin ina zaune na idar da raka'atul fajir, ya tashi ya na kalle kalle kiran sallar da ya jiyo ne ya sa ya kalleni cikin muryan barci ya na faɗin "Sadiya mun makara ne? Na ji kamar ana kiran salla? Sai da na kalle shi kafin na ce" Kai dai ka makara. Ni na yi sahur ɗina." Cikin mamaki da tuni barcin ya sake shi ya ce" Ban ga ne ba? Ni fa? Kai tsaye na amsa masa da cewa" Ba ka yi ba." "Me ya sa ba ki tashe ni ba? Sai da na yi shuru kafin na ce" Ban tashe ka ba. Saboda na ga wacce ka rabama girki da ita na kiranki sai na koma a tunanina ta tashe ka yau ɗin" Galala ya yi ya na kallona sunana ya kira na yi masa banza sai kawai na miƙe na kabbarta salla ganin haka yasa shima ya mike amma sai ya ya ɗau wayarsa ya duba sannan ya mike ya fita zuwa tiolet ya ɗauro alwala ya fita zuwa masallaci sanda ya dawo ina ji da na yi baricn ƙarya weekend ne yara ba makaranta sun ma yi hutu jiya jumma'a. Na san mganar da na faɗa masa na cin ransa bai iya hakuri ba ina barci ya tashe ni da mganar wai bai gane me na ke nufi da ya raba mana girki ba? Da wa ya raba mana girki? Kai tsaye na ce" Da wacce ta ke yi maka girki kana zuwa ka ci ka biya tuƙwaici mana." Wani kallo ya yi mini ni kuma ina shirin na juya na koma barci ya riƙo ni ya na kiran sunana. "Sadiya." Ido na sakar masa kafin na ce" Na'am Yusuf." Kawai sai ya girgiza kai bayan ya saki hannuna kafin ya ce" Sadiya karki fara abin da ba halin ki ba ne. Bincike mini waya kike yi yanzu saboda ba ki yarda da ni ba? Kai tsaye na ce" Allah shi kyauta. Kawai dai akasi aka samu na gani." Komawa na yi na kwanta ina faɗin" Karka damu ba wani abu fa." Miƙewa ya yi ya na kallona ni kuma sai na ja bargo har saman kaina. Hannu ya saka ya janye bargo ya na faɗin" Ki tashi mu yi mgana" Sai na ƙi tashi na riƙe bargon ina faɗin" Wata mgana? Ai mun gama mganar nan ko? Zura min ido ya yi kafin ya ce" E duk da haka na ce ki tashi mu yi mgana." Na ko ƙi tashi na juya zan gyara kwanciya a saman kaina Yallaɓai ya yi min tsawa. "Sadiya na ce ki tashi mu yi mgana ko? Kar ki bari raina ya ɓaci wallahi." Yadda ya yi mganar ne ya sa na gane ranshi ya ɓaci sai na miƙe na zauna a saman gado shima sai ya zauna ya na mai sauke ajiyar zuciya. "Sadiya wallahi ba komai tsakanina da Daughter fa. Kawai dai kin san am her favorite ne tun a baya. Kuma ni tana kira ne ba domin ta san ba ni da mata ko wani abu ba just normal na yan'uwan juna kin gane? Sai kawai na gyaɗa masa kai, domin ni na san kawai yana faɗa ne. "Kar ki ɗauke shi a wani abu don Allah. Ni ina mijinki haƙƙi ne a kanki ki tashe ni kamar yadda kika saba." "To ba za a ƙara ba." Na faɗa saboda na gaji da jin mgananunsa. "Kuma game da abinci in na je duba Nene sai ta yi mini ta yi in na ce ba zan ci ba sai Nene ta ce ko kaɗan ne na taɓa. Kin san dai ba zan yi ma Nene gaddama ba. Mganar tuƙwaici kuma wannan kyautatawa ce kema kuma ai ina yi miki ko? Ina ta kallon shi dai amman na kasa mgana. "Ba ki son kiran ne? Sai na ce mata ta daina Sadiya ta ba ta so." Wani kallo na yi masa kamar in yi dariya saboda na ga zai raina min wayau amma ban yi ba. "Zan faɗa mata ta daina kirana da asuba gashi yau ta ja mini yin ɗaure." Ya faɗa ya na yar dariya har yana shafa min kumatu. Yaƙe kawai na yi masa ban yi mgana ba. Hamma ƙarya na fara yi masa sai ya ce na koma na kwanta shi zai fita can falo akwai aikin da zai yi har ya ɗau laptop ɗin sa ya fice ina bin shi da kallon mamaki. > Janaftybaby: Ajiyar zuciya na sauke ko ba komai a zuciyar Yallaɓai game da Gimbiya ita har gobe shi ne zaɓin ta tsoro na ɗaya wannan karon mafarkinta zai iya zama gaskiya in dai ba wani ikon Allah ba tunda ba ta da shamaƙi da hakan ta kowanni fanni. Tun kuma daga mganar da muka yi ba mu ƙara tada mganar ba. Ita ma ta daina kiran asuba ina tunanin da gasken ya yi mata mgana sai na ji daɗi ko ba komai ya nuna mata ni matarsa ina da daraja. daga nan nima sai na watsar da abin da ke cikin zuciyata na kishi na rumgumi mijina. Sai cefanen salla tare muka je kasuwan muka siyo komai sauran kayan miya kuma Musbahu ya ce ya ba ma kuɗi zai kawo minibana gobe salla nama kuma daman a can gida sa suke yankawa a raba gabaɗaya amma dai ya siya mana na kasuwa kilo huɗu sai kaji muka haɗa da shi ni kuma a gida na siya fulawa zan yi cincin da cake da donut ga masu tayani Saude da Marwa da ta zo mini salla duk tare muke ayyukan gefe ɗaya kuma ina ta mana shirin Annirvesary ko Yallaɓai bai san shirina ba da ya tambayeni nace masa kawai ya tura mini kuɗi suprise ne shima ya ce a ranar akwai suprise ɗin da zai ba ni ina ta murna har ina zolayanshi na ce Yallaɓai ko ka biya mini Umra ne? Yana mirmishi ya ce in sha Allahu za mu je Umra Sadiya ta. Da ni da yara duk mun yi ƙunshi salla wata Hajjaju ce maƙoyar su Rahila na kira har gida ta yi mana kunshi na biya ta. kitso kuma mai yi mana kitso ta zo gida ta yi ma su Jidda har da Marwa da Saude bayan ni na wanke musu kan na su a gida. Ni dai ana gobe sallah na je shagon Amesty ta yi mini Saloon. Ban cika son yin kitso ba saboda Yallaɓai ya fi son in bar gashina a haka ta bakin shi ya ce ya fi mai daɗin taɓawa. *🅿️19* Mun yi azumi ashirin da tara 29 ɗaya ga watan shawwal ya kama ranar asabar ne a ranar muka sallaci salla ƙaramar salla. Mun je idi mun sallaci salla tare da al'ummar Musulman duniya gabaɗaya ni da Yallaɓai da yara sai Marwa da ta yi salla tare da mu. Bayan mun dawo idi na saka Marwa ta dafa jallop ɗin shinkafa mai nama. Tun a daran jiya muka gama duka soye soyen mu Saude da Marwa sun taimaka mini ƙwarai shi ya sa jiya da Saude za ta tafi da daddare Musabahu ya zo gidan da shi na haɗa su na ce ya kai ta gida tunda akwai motar Ya Usman a hannun shi tun lokacin biki bai koma da ita ba. Na dibar mata naman salla da kayan fulawan da muka yi sannen na ba ta ɗan kunne da takalmin sallar da na siya mata sai pant da bara da na siya musu tare da Marwa sannan na diɓa mata shinkafa kayan miya kuma na ba ta kuɗi na ce ta kai ma Mamansu ta siya kayan miya su yi abincin salla tunda na wajen nawa an niƙa gabaɗaya na tafasa. Yallaɓai na gida bayan ya ci abinci da nama yana falo yana amsa wayar ƴan'uwa nima 5k ya saka min kati ya ce na kira barka da sallah. Na samu kiran wasu yan gidanmu waɗanda ba su kira ba ni na kira su Alhajinmu dai da Gwaggo su na fara kira Nene itama na kira ta yi musu barka da salla sannan na kira Inna Mariya da su Kawu Nafi'u na yi musu barka da sallah. Har Yaya Murja ni na kirata Ma'u ce dai ita ta kirani kafin ni na kirata. Amma na kira Baaba ban ji mamakin da ta ce ba ta gane ni ba. Domin ba ta da lambata sai da na faɗa mata sunana bayan ma na faɗan sai da ta ce. "Wata Sadiyar? Kai tsaye na ce" Ta Yaya Sulen." Sannan ta ce au muka gaisa sama sama su Jidda ta tambaya na ce suna lafiya daga nan muka yi sallama. Da ga ita na kira Baba Aminu da Baba Sani suma na yi musu fatan an yi salla lafiya. Da ga su sai Rahila sannan na kira Yaya Muntari shima na yi masa barka da sallah. Bayan dangina sai na kira dangin Yallaɓai daman bayan su Alhajinmu na kira Nene na yi mata barka da sallah. Sai Mimisco Anty Maimuna na sameta mun gaisa amma Anty Bahijja ba ta ɗauka ba sai daga baya ta kirani. Na kira Faridan Tariq sai su Hauwa dukkansu na yi musu barka da salla Anty Zabba mutanen fatakol ita ta kirani muka gaisa har ta ke gaya min yara na nan gwammaja sun zo sallah. Da ya ke lokacin ya yi kusa an haɗu da biki ba lalle wannan sallan yan nesa su samu zuwa ba. A ranar Yallaɓai sai yamma ya fita zuwa Gwammaja kuma bai daɗe ba ya dawo washegari lahadi ban je ko'ina ba saboda ƴan yawon sallah. An kawo min su Sahla sai yaran Munnira sannan Jawaheer ta zo tare da ya'yan Anty Zabba da suka zo daga fatakol. Daga ɓarayina ƙannen Marwa ne kaɗai su ka zo min yawon salla daman su sun saba zuwa ban saka rai da su Antin Yaya Murja ba domin na san in da suke zuwa. Na ba su nama da kayan fulawa sannan na yi shinkafa da miya da salat suka ci da za su tafi da yamma na ba su kuɗin adaidaita sannan da kuɗin barka da sallah. Sun tafi kenan sai ga su Firdausin Anty Balki su biyu ita da ɗiyar ƙanwar babanta suka ce mini daga gidan Yaya Abubakar suke har ina yi musu tsiyan sai da yamma ne za su zo mini? Su bari sai gobe mana. > Janaftybaby: Suna dai sunne kai ba su ce komai ba, Allah ya taimaka bayan mangariba sai ga Musabahu da Adnan daman ina ta tunanin wanda zai kai min su gida tare da Yallaɓai suka shigo gidan. Ganin su ya sa na ce su jira su in za su tafi su a jiye min su a anguwansu ko daga bakin titi ne. Sai wajen tara na dare suka tafi tunda bayan sun ci abinci suna falo suna hiran su na ƴan'uwa acan falon shi. Amma sai da na kira Yaya Balkin na faɗa mata su Firdausi na gidana zan saka a dawo da su. Jidda da Baby daman a gidan Mimisco suka yi ni ta kira ni ta ce Direba zai dawo da su. Gwammaja kuma sai zuwa gobe za mu je can mu yini. Su Musbahu sun tafi da Firdausi ba daɗewa sai ga Direba ya dawo da su Jidda gida da Nama da yawa a leda da cake har da su lemuka da kuɗi da yawa sabbin yan ɗari ɗari suka ce Daada ne ya ba su wato mijin Mimisco daman sunan da ƴaƴan shi da ita kanta Mimiscon suke kiran shi kenan. Ranar litini ya kama ukun salla tun asuba na tashi ni da Marwa waina za mu yi saboda zan kai Gwammaja zan kuma aika da shi Ɗorayi da Gandun albasa. Saude na kira waya na ce ta zo da safe ta taya mu aiki. Saboda ina da mataya ko kafin sha biyu na rana mun gama toya waina duka miya daman tun safe na haɗa ta. Yallaɓai ya siyo mana manshanu daman na zuba a cikin miyan ga kayan ciki ga naman rago sannan ga ƙashi. Miya sai tashin kamshi ta ke yi Yallaɓai na sauri zai fita Rano zai je za su haɗu da Uncle Abba da Tariq da suka zo sallah sai na zuba masa ya ci ya na santi sannan ya tafi amma sai da ya ba ni goron salla ta na 10k sabbin yan 200 goron salla da kuɗin kwalliya domin na yi masa ado kuma ya burgeshi. Muna gamawa su Marwa suka gyara gidan saboda rage kaya Yallaɓai na ce ya yi mini gaba da su Jidda zuwa Gwammaja da wainar su ni daga baya sai mu taho da Marwa. Saboda daman ranar a can muke yini sai washegari yinin salla na huɗu kowacce sai ta je gidan su. Saude ma kuɗin a daidaita na bata bayan na diɓar mata na su wainar sai kuma na bata na gidanmu a babban kula na waina sai ledan da na saka Nama da kayan fulawa na ce ta kai ma Gwaggo in ji ni. Ni kuma sai da na sake wanka na sauya kaya na saka leshin da Yallaɓai ya yi mini na yi amfani da mayafi da jaka da takalmi kalan adon leshin jikina na saka ɗan kunnayena masu kyau da yarari na fito na yi ras da ni na san duk in da na shiga ba wanda zai raina ni. Da muka fito daga gida ba Gwammaja muka fara zuwa kai tsaye ba sai da na biya Gandun Albasa gidan su Mama na kai musu abincin salla da Naman salla sai kayan fulawan da na yi ban jima sosai a can ba duk na ga su Inna Mariya da sauran yaran su muka gaisa na yi musu rabon barka da sallah daman duk sallah ina kai musu abinci kuma ina zuwa tunda ni kaɗai ce mace a kano Amina ta yi nisa sai in wani abu ya faru ta zo. Ni ɗin ce na ke ƙoƙarin sada zumunci suma kuma suna da kirki duk abin da zai faru damu suna zuwa sannan Ya Auwal ma in ya zo garin ya kan je ya gaishe su kuma taimako dai dai gwargwardo ya na yi musu abin da bai gagara ba. A can Gandun albasa muka yi azahar sannan muka wuce Gwammaja. A can na iske su Hauwa da Munnira gida cike da ƴa'ƴa da jikoki. Domin kaf ɗin su yaran gidan sun zo sai dai waɗanda ke nesa irin su Jafar da Muhammad sani Yaya Usman daman sai yaran shi kawai ne suka zo. Su Anty Bahijja gabaɗaya suna nan da gayyarsu ban ga Gimbiya ba sai na ji Anty Maimuna na faɗin ta tafi Rano ɗazu da safe. Naja'atu ta zo amma ina gidan ta yi shirin tafiya gidan iyayen mijinta can za ta ƙarishe yininta Halima ma ta zo da yaranta ta yi kiɓa ita da jajariyarta mai kyau da ita har na ɗauke ta. Lokacin da na zo Nene ta kwanta sai da ta tashi muka shiga muka gaisa na kai mata Nama da kayan fulawan da na zo da shi ta yi ta saka mini albarka. "Sadiya Tafida ya kawo mana waina. Sannu da aiki Allah ya saka da alheri." Na amsa da Amin haka Nene ta ke komai sai ta yi maka godiya. > Janaftybaby: Daman su Hajiya iya duk na shiga mun gaisa na kai musu na su Naman salla, tunda haka na ke yi duk shekara sai dai Yallaɓai in ya je ya ji suna masa godiya nima haka suka yi ta min godiyar waina, Suwaiba har tana min tsiyan shi ya sa Yaya Tafida ya fara ijiye tumbi ashe daɗin girki na ne ina ta mata dariya. Maman farko ta ce ai ta diɓa ta boye za ta ɗumama ta ci da daddare wainar ta yi mata daɗi. Da ya ke shekara biyu kenan ban yi waina ba wancan shekaran tuwo na yi musu da miyar agushi wannan ne na ce bari na yi waina saboda a sauya baki. Kowa ya ganni tare da Marwa sai ya ce Sadiya ina kika samo yar budurwa mai hankali da kunya haka? Saboda da yara sun ɓata ɗakin Nene za ta ɗauko abun shara ta share. Ga shi ta na son yara goye take ma da ɗiyar wajen Halima har Nene sai da ta yi mgana na ce ɗiyar Yayata ce Marwa na tuna ma Nene ai ta na zuwa gidana hutu kuma na sha zuwa da ita gidan nan. Nene cikin mamaki ta ce" Allah Sarki girman ɗan mutu ba wuya. Ita ce ta girma haka? Ina dariya na ce ma Nene wallahi ita ce. Nene ta yi ta saka albarka Anty Bahijja ta saka mana baki da tambayan a ina take karatu na ce a tsafe makarantar koyin aikin jinya sai ta taɓe baki ba ta yi mgana ba ni kuma ban damu ba sanin halinta akwai son ta ji ƙwaf kuma in an faɗa mata ta nuna kamar ba ta so ta ji ba. Ganin ɗakunan su Nene cike da ƴayansu zuwa jikokinsu sai mu surukan gidan muka tsame kan mu zuwa ƙasa shashen su Jawahir ba ta nan ma tun safe an ce ta tafi can gidan kakaninta na bangaren uwa ita da Adnan. Da ni da Hauwa da Muniira muka zauna acan muna ta hira muna shewa. Muna ƙara ma junan mu sani kan abin da bamu sani ba. Muna mgana kan kayan gyara ne Munnira ke faɗin rabon ta da wani gyara tun haihuwan Mufeedan ta. Cikin mamaki na kalleta kafin na ce" Ke kam Munnira me ya sa me ki? Mufeeda yanzu ai ta shekara uku ko Hauwa? Na faɗa ina kallon Hauwa wacce kafin ma ta bani amsa Muniiran ta karɓe da faɗin" Shekaranta uku da wata biyu." Jinjuna kai na yi kafin na ce" Ki ce waje duk ya yi tsatsa. Gaskiya ba ki kyauta ma Nasir ba." Na faɗa ina hararanta ita kuma tana dariya kafin ta ce" Ke ni fa gani na ke yi duk ba sa wani yi asara ne. Kuma ni in dai ba shi zai ba da kuɗin a siya ba sai na ke ƙyashin fidda kuɗina na siya wallahi." Mamakin Munnira ya kamani daman har yanzu akwai mata masu tunani irin na Munnira? Ko dai ta yi ma kalmar gyaran mummunan fahimta kamar yadda wasu matan suka yi ma kalmar. Ban samu zarafin mgana ba Hauwa ta karɓe mganar da cewa" Haba Munnira ke da kan ki ma? Mata ai yanzu sun waye kowa ta san abin da za ta sha ya gyara ta ba wai kuma wanda zai zama cuta gare ta ba. Kuma kin manta hausawa na cewa in kana da kyau sai ka ƙara da wanka? Kina da yaƙinin tun gyaran da kika yi da haihuwan Mufeeda ya na nan a jikin ki? Haba ai yakamata dai ko yaya ne ki ɗan ƙara gyarawa ko dai baki sha komai ba yan kayan marmarin nan da za su ƙara miki cika da Ni'ima." Daga ni har Munnira baki muka saki muna kallon Hauwa. Sai da ta gama bayaninta ta ga irin kallon da muke yi mata sai ta ji kunya ta kauda kai tana faɗin" Me ya faru kuke kallona? Ko ba gaskiya na faɗa ba." Ina ɓoye mirmishina na ce" Kin faɗi gaskiya Hauwa uwargida a gidan Mutaƙƙa shi ya sa har gobe bai kallon kowa sai ke ashe sirrin da kika riƙe kenan? To mu ma a ɗan gaya mana sirrin mana ko Muni? Na faɗa ina kallon Munnira da ta kwashe da dariya har ta na bani hannu muna tafawa cikin dariya ta ce" Shegiya Hauwa ta zama yar gari. Maza gaya mana sirrin." Hauwa na dariya ta ce" Shawarwarin ku ne fa, sannan daga Rano akan ɗan aiko mini da gumba da sauran abin da ba za a rasa ba. Sai wacce Sadiya ta haɗa ni da ita na kan ɗan siya mganin infection sai kaza in na samu kuɗi kuma Alhamdulillah ina ta ganin canji." "Allah Hauwan Mutaƙƙa ? Na faɗa ina kallonta sai kawai ta ɗaga mini kai. Tare muka saka dariya Munnira har ta na ɗaga kafa saboda dariya kafin ta ce" Ke Sadiya yaushe Hauwa ta yi baki haka? Kuma abin ɗanwaken zagaye ne? Hauwa kaɗai kike so ta gyara ban da ni ko? > Janaftybaby: Ina ɗaga hannuna sama na ce" A'ah ita ta min mgana ta ce tana so saboda ranar tana gidana aka aiko min da saƙon. Sai ta ce min tana so sai na haɗa su kema in kina so ai ta kwana gidan sauƙi waya kawai za a yi mata." Munnira sai ta gyara zama kafin ta ce" To wai kuma yana yi sosai? Na kalleta ban yi mgana ba Hauwa ce ta ba ta amsa da cewa" To ai ke tunda kin riga kin saka wasi wasi ko kin siya ba zai yi miki aiki ba." "Ko? Haka ta ce tana kallon mu ni ko sai na gyara zama ina faɗin" Gaskiyan Hauwa. Kuma son kuɗi ne ba zai barki ki yi gyaran ba karki kashe kuɗi ko? Zauna Nasir ya samu wasu ƴan kudaɗe ya nemi chanji lokacin za ki yi bayani ne." Tana dariya ta ce" Haba. Ai ya yi ƙanƙanta da Mata biyu. Yallaɓai dai ke kan hanya daman ana ta cewa tunda Yaya Usman ya buɗe hanya Yallaɓan ki ne zai biyo baya." Wani kallo na yi mata sai ta kama dariya Hauwa na taya ta. Nuna ni take yi tana faɗin" Ta firgita ta. Kin gan fa Hauwa." Ta faɗa tana nuna ni ture hannunta na yi ina faɗin" Firgitan me? A kaina za ta zauna? Allah ya kawo ta lafiya." Hauwa da Munnira na ta danne dariya haushi ya kamani na ce" Wai dariyan na menene kuma? Ko kin ji labarin auren ne ni ban sani ba? Da sauri Hauwa ta ce" A ina? Wallahi wasa ne kawai ba abin da muka ji." Hararan su na yi domin na ga sun maida ni abin zolaya. Munnira ce ganin na haɗe rai ina faɗin" Ko za a mini kishiya sai an yi miki Munnira in sha Allahu." Da karfi ta amsa da cewa" Wallahi ba Amin ba. Cab" Ina mirmishi na ce" Au ashe ba daɗi? Sai ta marairai ce tana faɗin" Daga Wasa? To a bar mganar kawai." Ni kuma na ce sai an yi ta. Munnira uwar kishi ta ce ita fa ta tsani labarin kishiya. Ganin na na ce ina cewa Nasir sai ya yi aure nan kusa in sha Allahu Hauwa na taya ni sai kawai ta sauya mganar da cewa" Na ce ba ya mganar kayan gyaran can ɗin? Ina ga zan siya nawa nawa ne? Ni da Hauwa har muna tafawa saboda dariya sai da na gama ja mata aji sannan na yi mata bayanim ingancin kayan gyara na Hajiya Surayya Halin yau. Cikin mamaki Munnira ta ce" Da gaske suna da kyau? Ba su dai cutarwa ko? Kai tsaye na ce" In da suna cutarwa da tuni sun cutar da ni. Ke Munnira ki cire wannan tunanin a ranki na matan da ba su san kansu ba. Yanzu mata sun fahimci muhimmamci gyara a jikinsu wanda ba zai zama cuta a gare su ba. Kin ga mganin infection ɗin nan yana da kyau duk bayan wattani uki mace ta riƙa shan shi. Saboda shi infection 90% na mata muna dashi sannan mu ke zuwa gidajen biki da suna muna mu'alama da banɗakuna mabambamta. Kin ga kowani lokaci za mu iya ɗauka sai mun dage da mgani sannan maganar gyara Munnira ba wanda zai cutar dake ba yar gumbar nan ta mata ɗan kazan nan na haɗin uwargida ba komai a cikinta sai itatuwan maganin da zai ƙara miki Ni'ima. Bayan nan za ki riƙa gyaran ki a cikin gida kayan marmarin nan ki riƙa shan su madara su rage kayan ganye da sauran su duk suma suna taimakama wajen dawo da ruwan jikin mu kin gani nan duk bayan wata uku sai na siya mganin infection na sha sannan na bi da kayan gyara bayan kuma ina yin nawa dubarun a cikin gida hatta fatata ban zauna ba bayan wani lokaci ina siyan mayukan gyaran jiki domin kaina da kuma Mijina. Ba kuma domin shi ɗin ba sai domin ka riƙe wannan martaban da Allah ya ba ka na ƴ'a mace. Sannan yana da kyau ka yi gyara domin ka farantama mijinka Munnira ba sai an kawo maka wata ka haukace ba. Wanda ko da watan ta zo sai dai ita ta yi gasa da ke ba dai ki yi da ita ba tunda komai ta zo ta iske ki kin san shi kuma kina yi saboda haka ki yi ma kanki faɗa ki gyara jikin ki da kanki saboda martaban ki Munnira" "Gaskiya ne Sadiya mganar ki Haƙƙun." Hauwa ta faɗa tana mai jinjina kai. Munnira da ta yi tagumi ta na saurerena sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Kuma gaskiyan ku ne. To zan dage in sha Allahu. Kuma kamar na fara ganin wani alamu a wajen Nasir duk da bai yi mini mgana ba." "Alamun me? > Janaftybaby: Na tambaya ina kallonta. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Yanzu ba ya daɗewa da mun fara mintina goma sai ya sauka kuma da ba haka ya ke yi ba" Ni da Hauwa muka kalli juna kafin na maida kallona kan Munnira ina faɗin" You see. Akwai sanyi ajikinki kuma a yadda na fahimta ba ya wani jin daɗin ki yana dai yi ne saboda fita haƙƙi ki sai kin dage Munnira" Tuni ta natsu tana faɗin" To zan dage gaya mini mafita. Allah Sadiya ba na ƙaunar kishiya" Yadda ta yi mganar ne cikin tausayi ya sa muka tsintsire da dariya ni da Hauwa kamar za ta yi kuka ta ce" Don Allah ba dariya ba. Ku taimaka mini." Sai na gyara zama ina faɗin" Za mu taimake ki amman ke ma sai kin miƙe kin taimaki kanki." Sai ta ce ta ji duk za ta yi nan take na ɗauko wayata na kira Hajiya Surayya Halin yau. Bayan mun gaisa sai na ce zan haɗa ta da Munnira domin ta yi mata bayani ina ba ta wayar sai na ce ta shiga ciki yadda za ta samu damar yi mata bayani sosai. Sun ko jima suna waya sannan Munnira ta kawo min wayar nan Surayya ke faɗa min za ta fara shan na infection kafin haɗin kayan gyaran ya biyo. Mun rabu akan Munniran za ta karɓi lambar wayarta su ƙarishe mgana. Washegari ma ta ce za ta aiko ma da Munnira saƙon ko ba ta saka kuɗin ba tunda ta hannuna ne. Duk mai bukatar mganin infection sadidan, ko mganin gyaran uwargida da amarya contact Surayya Halin yau. +234 803 277 3332. Kano Nigeria. Nuna Gwammaja har wajen ƙarfe goman dare. Domin da mazajen namu suka shigo gidan can bayan sallar isha'i gabaɗyansu suna falon Nene da ƴan'uwansu suna ta hira a tsakaninsu. Mu kuma muna ƙasa mun yi sallah mun koma muna ta zaman hira. A lokacin mganar haihuwa muke yi sun sin ina son na ƙara haihuwa ko daga yadda na ke kan hanyar yawon asibiti. Hauwa ce ke tambayata ya ake ciki ne yanzu? Kai na rausayar kafin na ce" To ana dai kan gwaje gwaje duk da kamar guda biyu suka rage amma Likitan tana ta ba ni tabbacin ba matsala ko ma akwai ba wacce za ta gagare su ba ne." Tare da Munniran suka haɗa bakin faɗin" In sha Allahu ma ba wata matsala." Sai na amsa da Allah ya sa cikin wani yanayi na ce" Yallaɓai na son yara sosai. Biyu sun yi masa kaɗan ni na sani." Hauwa ta ce" Amma ai ba ya nuna damuwa ko? Sai na gyaɗa mata kai Munnira ce ta karɓe da cewa" Yallaɓai fa bai da damuwa. Damuwar su ne su Anty Bahijja. Ni da na ji ma wani batu amma dai ba ri na yi shuru." Sai na kalleta gabana ya faɗi saboda na san tabbas abin da ta ji ya shafe ni. Da sauri Hauwa ta ce"Gwara ki yi shurun Munnira. Ni ma da na je Rano cikin azumi na ji batun a gida." Sai kawai na kallesu kafin na yi mgana Munnira ta ce" Au kema? To me za a ɓoye mata ai mgana ce ba cewa muka yi ya tabbata ba. Kuma zaman tare kenan gwara mu faɗa mata ta san halin da ake ciki ko da ta faru ma ta san in da za ta bullo ma lamarin." Cikin ɗauriya na ce" Wai menene? Ku faɗa min ai ban isa na hana Allah ya yi ikon shi ba." Hauwa ce ta kalleni kafin ta ce" A bakin Autar gidanmu na ji wai ƙannen Gimbiya ke faɗin Tafida za ta aura. Da na ce ban san da wannan mganar ba Innamu ta ce itama ta ji kuma a bakin makusantan ita Hajiyar Tafidan an ce daman tun farko Hajiya Nene da Hajiya tafidan sun so su haɗa zumunci na auran Gimbiya da Tafida Allah bai yi a wancan lokacin ba. Mutuwar mijinta ya nuna cewa rabon Tafida ce." Ina kallon Hauwa amman na kasa mgana Munnira ta karɓe da cewa" Nima haka na ji wallahi. Kun san wacece ta min mganar? Hauwa ce ta girgiza mata kai ni dai ko motsi ban yi ba "Suwaiba ce fa kwanaki da ta zo gidana ta ke min zencen. Wai Anty Bahijja ta ce wannan karon Gimbiya Rabon Tafida ne. Shi ya sa ma wai ƙila aka dawo da ita wajen Nene." Hauwa ta ce" Ni kaina na yi mamakin dawowarta. In aiki ne ai ba kullum ta ke zuwa ba kuma tunda tana da mota za ta iya zuwa a ranar kuma ta koma gida." Munnira ta ce" Har Nasir na yi ma mgana ya ce mini shi bai sani ba gulma ce ta mu ta mata. Amma wallahi Sadiya na hango gaskiya ba rami me zai kawo mganar rami? Da man ta yi ta shige masa ni fa wallahi haushi ta ke ba ni." > Janaftybaby: Hauwa ta yi tagumi kafin ta ce" Ni kaina na fara hango hakan. Mganar fa daga bakin ƙannen Gimbiyar ta fito. Kin ga ko sun ji ana mganar ne." Ganin yadda na yi shuru kawai ina sauraran su ya sa Hauwa ta dafa kafaɗata tana faɗin" Kar ki damu Sadiya. Ni na san ko auranta Yallaɓai ya yi ba za ta sha gaban ki ba." Munnira ta taɓe baki kafin ta ce" Ni wallahi da wata ta waje ne wacce ba a sani ba. Amma wannan Gimbiyar fa ban so. Sai Sadiya ta zama mujiya Allah su Anty Bahijja ware ta za su yi daman ya ya a ka cika? Hauwa ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Da wannan kuma da wanman." Munnira cikin jin haushi ta ce" Har fa wani suna take kiran shi Daddy shi kuma ya ce mata me ne ma? "Daughter" Na faɗa ina kallon Munnira da ta yi tsaki kafin ta ce" Ke kuma wai duk kika ƙyale? Suna waya to? Sai na gyaɗa kaina kafin na ce " Suna yi mana." Gabaɗayansu suka kalleni cikin mamaki sai na yi mirnishi kafin na ce" To ai ban isa na hana shi yin waya da ita ba tunda yar uwanshi ne ko da na aure shi suna tare. Hauwa Munnira daman tun da na ji Mijin Gimbiya ya rasu da irin hidiman da ta ke yi ma yarana na san gwara na shirya domin watan wata rana ko Yallaɓai bai yi tunanin auranta ba za a tusa masa tunanin. Bakomai in ma ya auro ta fatana Allah ya zaunar damu lafiya abu ɗaya na sani ba zan yi ma Yallaɓai baƙin ciki domin ya ƙara aure ba. Sannan ba zan yi faɗa da dangin shi ba amma na kudiri niyar in sun yi mini hallaci na yi musu in ba su yi mini ba wallahi ba zan yi musu ba sai dai gayyar ta watse." Munnira ta ce Hmm! Ta ma kasa mgana Hauwa ce ta ƙara ba ni hakuri da cewa kar na damu tana da tabbacin Yallaɓai ba zai taɓa juyamin baya ba. Kallonta kawai na ke yi amman ban yi magana sai dai kuma a cikin raina sai da na ce Namiji ne fa mai chanza launi daga baƙi zuwa fari lokaci bayan lokaci. Muna cikin yin mganar ne Yallaɓai ya kira ni a waya ya ce na fito za mu tafi ya na faɗa min yara har sun yi barci. Jin haka yasa gabaɗayanmu muka fito zuwa ɗaƙin Nene muka yi musu sallama su Suwaiba nan duk anan gida za su kwana. Mu muka fara tafiya Hauwa Musbahu ne zai kai su gida ko a fuska ban nuna ma Yallaɓai wani abu ba har muka koma gida. Marwa na bari da Baby na ce ta yi mata shirin barci. Ni da Yallaɓai muka wuce bedroom ɗim mu kafin mu kwanta sai da muka yi soyyyarmu sannan muka yi wanka muka kwanta duk da yadda na ke jin wani abu ya tsaya min a ƙasan zuciya amman ban nuna masa ina ƙoƙarin gaya ma kaina gaskiya. Ban isa na hana shi abinda Allah ya ce ya yi ba. Sannan ba zan yi masa baƙin ciki domin ya ƙara aure domin samin wasu zuru'an ba. Amman a ƙasan raina ina tunanin saboda akwai ta in da na gaza ne. Na gaza ta bangaren ba shi zuru'a masu yawan da ya ke fata. Washegari tun safe muka shirya. Na yi abinci shinkafa da miya da nama sai salat ɗin da na saka shi a wani filet Babba muka rufe da leda Karfe goma a Ɗorayi ta yi mana Yallaɓai ya kai mu, ranar kaya iri ɗaya muka saka da ni da yara har Marwa Atamfar da Yallaɓai ya yi mana mai adon ja a jikin ta. Na yi kyau sosai gashi daman na ɗan rame kaɗan sai kayan ya zauna a jikina riga da sikat na yi. Duk sammakona sai da na tarar da Yaya Balki a gidan mun je ba daɗewa sai ga Ma'u itama da na ta gayyar yaran sai ƙanwarta Zainab sai Anti ƙila can ta yi mata salla Itama da abinci niki niki. Wannan sallar daman su Yaya Hamza ba su zuwa salla gida sun fi zuwa a sallar layya. Can ba jimawa sai ga Zaitunan Yaya Abubakar sai ga Yaya Murja ta ƙarshen ita ce Yaya Aina da ƙannen Marwa gifa fa ya cika ya yi albarka tun da kaf ɗin mun mun zo da yaran mu sannan har Datti a gida ya yi salla Alhajinmu ya ji daɗi bakin shi har kunnen gashi ga jikokinshi suna ta fira Gwaggo ma ta kasa zama sai ina za ta saka damu take yi. *🅿️20* Rahila ce jirgin danƙaro ita ce karshen zuwa har sai da na yi mata tsiyan tana kusa amma itace ƙarshen zuwa. Tana dariya ta ce " Ni fa na ɗauka ni ce ma farkon zuwa kawai sai na ga gida ya cika." Muna ta mata dariya ni da Ya Balki. Amina ta kira waya da ta ji gida cike kowa da kowa na nan kamar ta yi kuka ta ce ta yi missing. Ta so zuwa amma ba ta samu dama ba sai dai ta ce sallar layya in sha Allahu da ita za a yi. Ya Auwal kuma ni na kira shi a waya ya ce sun ɗan fita da laila ne da yara gidan shuru sallar duk ba daɗi sai ya ce na kunna data ya kira Video call nan ne fa suka gaisa da kowa har da Gwaggo da Alhajinmu an kai musu sun yi mgana da juna. Ya Hamza kuma na kira wayarsa ba ta shiga ba sai na kira na Khaleesat. Ita ke faɗin ya kwanta ashe bai jin daɗi zazzaɓi kuma ya hana a faɗa ma kowa. Muna cikin wayar ya tashi sai ta bashi wayar dukkanmu muka karɓa muka yi masa sannu da jiki ya ce ya ji sauƙi ya je asibiti maleria ne an yi masa allura kuma an bashi mganguna. Ba mu jima muna mgana da su ba tun da bai jin daɗi daga nan muka yi masa sallama da fatan samun lafiya. Datti dai za su fara jarabawa Jiya da yamma ya koma makaranta. Dukkan mu muna ɗakin Mama daman yawancin in dai mun zo gida mun fi zama ɗakin Mama. Gwaggo na ɗakin Alhajinmu suna ta fama da yara. Hira muke yi na can garin mu Yashe bayan sallar nan akwai bikin autar su Ya Muntari wato ɗiyar Baba Aminu kenan Yaya Aina ce ke mganar haɗa guddumuwa daman haka muke in sha'ani ya tashi sai mu haɗa kanmu kowa ta kawo abin da ta ke dashi mu haɗa mu ba ma Gwaggo ita kuma sai ta nuna ma Alhajinmu ya yi ta godiya kuma in sha'anin ya tashi ko ba dukkanmu. Yaya Murja da Yaya Balki suna zuwa ni ce ma ban cika zuwa ba sosai Rahila daman can ne tushen Mijinta tana yawan zuwa amma wannan karon tunda na ji bikin na ce sai na je Yashe na yi sati in sha Allahu tun da na daɗe ban je ba tun ina da cikin Baby da babbar ɗiyar Baba Sani ta rasu muka je gaisuwa kuma a ranar muka dawo ba mu kwana ba. Bikin bayan salla da sati uku ne. Yaya Aina ta ce ana jibi biki za mu tafi saboda Matar Baba Aminu magajiya mai yi ce ba ta wuce duk wani sha'anin mu ko ba ta zo ba ƙannen Yaya Muntari za su zo gaskiya tana da ƙoƙari daga ita har Baba Aminun suna da riƙo kan zumunci. Muna cikin hiran ne Marwa ta shigo sai dai ta ce sannanun ku gabaɗaya a ka amsa mata in da na ke zaune ta nufa tana faɗin" Umma Baby ta jiƙa kayanta da ruwa." (Daman Umma ta ke ce mini kamar yadda su Jidda ke kirana.) Kai na jinjina kafin na ce" To ai sai ta zauna dashi. Domin ban zo mata da wasu kayan ba." Da sauri ta ce" Gwaggo ta ce a cire rigar a shanya kar zazzaɓi ya kamata." Kafin in yi mgana Rahila ta karɓe da cewa" To ba wasu kayan? In sanyi ya kamata fa" Yaya Balki ce ta yi mgana wannan karon da cewa" Sadiya ce fa da tsiyarta. Ba za a rasa wasu kayan su Baby a gidan nan ba." > Janaftybaby: Yaya Murja na gefe ta ce" Ko ba na ta ba. Ba za a rasa kayan da za ta saka kafin na ta ya sha iska ba." Muna cikin mganar Marwa ta fita sai ga Gwaggo ta leƙo ta na faɗin ita ta ce a cire mata rigar a shanya ta samu wata riga ta ba ma Marwa ta saka mata na amsa mata da to Gwaggo. Yaya Balki ce ke mganar ta ga Marwa ta yi mata girma ne a ido ina mirmishi na ce" Ai na kusa yin suruki in sha Allahu." Yaya Balki ta amsa da Allah ya sa. "Aina can Marwa ta yi salla gidan Sadiya ne? Ya Murja ta faɗa ta na mai kallon Ya Aina wacce ta amsa da mata da cewa" E. Tun kafin ta dawo daga makaranta ta dame ni da ni Mama a gidan Umma Sadiya zan yi salla na ce to. Ta na dawowa ta gaya ma Baban shima yana dariya ya ce to yar gidan Umma Sadiya a dawo lafiya." Ina mirmishin jin daɗi na ce" Ai wallahi na ji daɗin haka. Ni da za ku bar mini ita a wajena Ya Aina." Yaya Balki na dariya ta ce" Topha ƴan mata ba su ishe ki ba ne Sadiya? "Ina fa suka ishe ni. Ban ƙi dozin ba Yaya Balki." Muka saka dariya gabaɗayanmu Rahila ce ta ce" Sai Ya Aina ta baki. Ki haɗa da Jidda ki riƙe gabaɗaya." Ma'u na gefe ba ta ce komai ba ta na latsa wayarta. Ya Murja na sauraran mu amma ba ta yi mgana ba Ya Aina ke faɗin Marwa za ta fara pratical a asibti kuma babanta ba zai bari ba amma don ta riƙa zuwa miki hutu lokaci bayan lokaci ba zai ce komai ba. na marairacewa na ce" Haba Ya Aina. In kika saka baki zai bari mana." Dariya kawai ta yi ba tare da ta yi mgana ba Yaya Balki ce ke faɗin" Topha! Lalle lamarin Sadiya azimin ne. "Da gaske take yi." In ji Rahila ni kuma na juya ina rantse musu da gaske nake yi. "To ke in kina son ɗauka shi Yallaɓan na ki na so ne? Ya Murja ta faɗa tana kallona da sauri na ce" Haba Ya Murja na ɗauka ke mai shaidar Yallaɓai na ne. Ba Marwa ba ko wacce bai sani ba ne na kawo na ce ina so zan riƙe wallahi ba zai ce komai ba. Ballatana ma Marwa shi ya fara cewa ko za mu karɓo Marwa ne ta dawo wajen mu da zama Sadiya? Shi ya sa ma kika ji na yi mgana." "Oh." Kawai ta ce ba ta ƙara mgana ba. Yaya Balki ce ta karɓe mganar da cewa" Kuma fa hakane. Yallaɓan na ki ba shi da matsala gaskiya." Rahila ma ta amsa da cewa" Shi da ke son yara. Allah ne dai bai bashi da yawa ba." Ita dai Yaa Aina ba ta ce komai ba sai dai ta na ta mirmishi daga karshe ta kashe mganar da cewa babanta ba zai bari ba ni kuma na ce zan sako Yallaɓai a gaba mu zo tambaya Rahila na dariya ta ce" Shike nan ma an kashe boss ɗin." Muna ta dariyan mu cikin nishaɗi. Daman fa ko haɗuwa aka yi waje ɗaya Ma'u da Ya Murja sun fi tsame kansu gefe ana hira sai jifa jifa suke saka baki tun ballatana ma in ina wajen. Ni kuma ban damu da su ba in suka sako ni na yi da su in ba su sako ni ba na juya na yi da waɗanda ke yi da ni. Zaitunan Yaya Abubakar tana ɗakin Gwaggo tun da ta zo sai barci kamar wata kasa Yaya Balki ta ce Allah ya sa ba ciki ne da ita ba Ma'u ta kwashe da dariya ta na faɗin" Kuma kamar kin san ta yi yaye ba." Ya Aina ta ce" Kai wannan mata ta Abubakar. Allah ya sauwaƙe." Ni kuma sai na kada baki na ce" Ku barta ta haihu. Iya rabon ta a duniya fa za ta haifa. " Sai Rahila ta ce kuma gaskiya ne. Gwaggo ce ta leƙo ta ce an kira salla ga ƴayanmu can har sun yi alwala mu ma sai mu tashi jin haka yasa muka firfito domin yin alwala ni ban samu buta ba sai na zauna ina jira Anti ta gama da na ta butan ta bani sai da ta idar da alwalan sannan ta kawo min na amsa ina faɗin" Su Anti an zama yan mata." Ta na dariya ta rufe fuska kafin ta ce" Anty Sadiya ina goron sallah na." Kai tsaye na ce" Gorom sallah kike so? Sai ta gyaɗa min kai. Ni kuma sai na rausayar da kai kafin na ce" Goron salla ai a gida ake ba da wa Anti. In kina son goron salla sai ki zo gidana ki karɓa. Yanzu ma kin makara salla ta wuce sai dai kuma ta layya in muna raye." Ita Anti ba ta damu da mgana ta ba cikin dariya ta ce" Kai Anty Sadiya." > Janaftybaby: Nima ina mata dariyan na ce" Ƙwarai Anti. Salla layya in kina son goron salla ki zo gidana da wuri ni kuma sai na cika miki jaka da kuɗi." Gwaggo na bakin famfo tana alwala ta na jin mu ta dai yi mirmishi ba ta saka mana baki ba. "To Anty Sadiya in sha Allahu zan zo. Wannan salla a gidan Umma Ma'u na yi shi ya sa." Ina mata mirmishi na ce" To ai shiken nan na ma san Ma'u ta cika miki jaka da goron sallah ba ki buƙatar tawa ko? Har ga Allah ni a wasa na yi mganar kawai sai gani na yi Ya Murja ta bankaɗo labule ta fito da hijabi a jikinta da alamun ta idar da salla ne kallona ta yi daga sama har ƙasa nima ko cikin mamaki na ke kallonta sai kawai ta daka ma Anti tsawa ta na faɗin ta wuce ta je ta yi sallah sai yarinyar ta wuce ɗakin Gwaggo da sauri. Kamar zan yi mgana sai na fasa na fara tafiya wajen famfo Gwaggo ta taso za ta shiga ɗakinta. "Ke Sadiya.." Ya Murja ta yi mini kira cikin gatsali sai na juya ina kallonta cikin mamaki. Ba ma ni kaɗai ba hadda Gwaggo. "Me ya faru Ya Murja? Na faɗa ganin kamar tana sakin huci kawai sai ta nuna ni da yatsa ta na faɗin" Daga yau in kina so ki yi min rashin kunya ki zo gare ni kai tsaye ne ba sai kin rakuɓe a jikin ƴa' ta kina gaya min mgana ba. Ba na son rashin kunya." Galala na yi da baki ina kallonta kafin na samu zarafin mgana Gwaggo ta tsawarta da cewa" Murja me kuma ya kawo wannan mganar? A fusace ta ce" Ba ki ji mganganun da ta ke faɗa ma Anti ba ne? Ta nuna kamar da gayya ne ban tura Anti gidanta ba na tura ta gidan maƙiyarta Ma'u ba. Duk na fahimci mganganunta." Gwaggo ta yi tsaki kafin ta ce" To ni ban ji haka ba. Mganar su kawai suke yi na tsakanin uwa da ƴa." Nan fa Ya Murja ta ce ita fa k a taufau da ita na ke yi. Ƙara nuna ni ta yi da yatsa kafin ta ce" Daman ba tun yau ba kin sha faɗan wai na fi son Ma'u da ke da ita kawai na ke shiri yayana ma gidanta suka sani. To yadda kika faɗan ne domin Ma'u ta fi ki ladabi da biyayya sannan ita ta ja ƴa'ƴana a jiki ke kuma da ba ƙi kaunar su ba ki ja su a jiki ba. Kin ga ko kar ki ga laifin su in ba su je in da kike ba. Gidan kuma Ma'u da ki ke jin haushin suna zuwa yanzu suka fara zuwa. Sai dai baƙin ciki ya kashe ki Sadiya" "Murja me ye haka don Allah.? Ya Aina bayan ta fito daga ɗakin Mama itama sanye da hijabi ita da Ya Balki da Rahila. Ma'u dai ba ta fito ba ni kuma tsabar mamaki ma na kasa magana. "Ya Murja Alhajimmu na ciki fa. Gaskiya wannan ba girman ki ba ne. Sadiya fa ba da ke ta ke mganarta ba." A fusace Ya Murja ta ce" Ba za ku gane ba ne. Ni na san ga in da ta dosa. To me ye na damuwa don ƴaƴana ba su je in da ta ke ba. Marwa da kika zaɓa kina so ita ai kin gayyaceta kuma ta je suma in kika nuna kina so su je ɗin za su je." Sai a lokacin na fahimci haushina ta ke ji saboda Marwa. Kai wannan mata ta ɗoramin karan tsana. Ba na so na yi hayaniya saboda Alhajinmu kawai sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Ki yi hakuri Ya Murja na ga ƙin ɗau zafi har ga Allah ba da wata munafa na faɗi mganar da na faɗa ba. Amma in ta ɓata miki rai Allah ya baki haƙuri. Mganar Anti na zuwa gidan Ma'u ban taɓa sawa a kaina ba domin da ni da Ma'u duk ɗaya ne. Ke ma kuma ina so ki gane wani abu da Anti da Marwa ɗaya suke a wajena ba Bambamci." Ina gama faɗin haka na juya na wuce wajen famfo ina taran ruwa a buta. Na san dukkansu sun yi mamakin sanyina har sai da Gwaggo ta ce" Shike nan Sadiya kin gama magana. Ke kuma Babba kwabo kin ji kunya tunda har yau Sadiya ta fi ki hangen nesa." Ganin ban kulata ba ya sa ta koma ɗaki fuu. Kuma kowa ita ya ba ma rashin gaskiya a wajen. Sai bayan da na ɗauro alwala na shigo cikin ɗakin ne Ma'u ta ke ce min" ki yi hakuri Sadiya ki fahimci Ya Murja don Allah itama ba da wata munafa ta yi miki mganar ba.' Kallonta kawai na yi ni kam wani makircin Ma'u ne ban gani ba sai kawai na ce" Bakomai. Ita za ki ƙara ba ma hakuri saboda na ga kamar ta ɗau zafi da ni." > Janaftybaby: Ina gama faɗin haka na saka Hijabi na ta da salla. Bayan na idar sai muka ci abinci na ga dai Ya Aina ta keɓe da Ya Murja na kuma san faɗa ta ke yi mata shi ne na ga ta ɗan saki ranta a raina na ce matar nan me na yi mata wai ta tsane ni ne? Muna cikin cin abinci sai ga Ya Abubakar ya shigo ganin abinci kala kala muna ci ya sa ya ce"Kai. A ina aka samo abinci nau'i nau'i haka kamar an samu sabon restaurant? Rahila ce ta faɗa masa kowaccem mu ta dafo abinci daga gidanta sai shima ya samu waje ya zauna ya na faɗin" To shi ne ana wannan shagali aka manta da ni? Ni ne fa the head of the family" Ya Balki ta ce" Mun ɗauka Zaituna ta yi maka kyakyawan beta kafin ta fito gida" Ta faɗa ta na kallon Zaitunan da ke ta cin abincinta jin an taɓo bangarenta ya sa ta yi saurin cewa" Laa shi ya ce in taho ba sai na tsaya na yi abinci ba." Rahila ta ce" Ehem daman na san za a rina." Yaya Aina ke faɗin" Ke kam Zaituna ban san yaushe za ki wayau ba. Ko mu kin ga mun taho ba mu yi girki ba? Ga shaida nan tunda gashi nan kina ci in da kin dafa kafin ki fito mijin ki zai zo ya na neman abinci? Kanta na kasa ba ta yi mgana ba Yaya Abubakar ya wani girgiza kai kafin ya ce" Ƙyaleta Aina ta yi lokaci ne." Daga haka kawai ya miƙe ya ce ya na ɗakin Alhaji a kawo masa abinci. Zaitunan Ya Aina ta tasa ta ce ta saka mai ta kai masa ta na fita Ya Murja ta ce" Mata kamar mai almatsutsai" Ya Aina ta ce" Lafiyan ta ƙalau iskanci ne kawai da ta samu shi Abubakar ɗin mai sanyi." Ni dai ina jin su ban tanka ba ina ta cin abincina ni shinkafa da waken da Rahila ta dafa na ke ci su kuma su Ya Aina sun ci nawa sun kuma ci na Ma'u ita waina ce da Sinasir. Mganar gaskiya duk cikin mu Mijin Ma'u ya fi kuɗi kowa kuma ya san haka amma duk da haka dukkanmu ba za a ce muna cikin halin rayuwa ba dai dai gwargwado mazajen mu na da rufin asiri. Mijin Ya Murja ne ma sai a hankali domin ya samu matsala can kwanaki an kore shi daga wajen aiki ya fi shekara uku a gida amma dai an ce ya koma shi ya sa Ma'u ta samu dama tana taimakonta ita kuma kwaɗayi ya sa idanuwanta ya rufe. Ni ba na kyautar ganin ido ko ka gode min in na yi niyyar yi maka alheri na yi, in ban yi ba shike nan ba zan yi domin duniya ko kai da zan mawa ka yabeni ba ita kuma Ma'u daman halinta ne ta yi alherin da duniya za ta sani a yabe ta a kuma san tana yi ɗin da son nuna ita fa mijinta na da kuɗi domin in dai Ma'u ta san za a zo gida a haɗu ƙarshen kayanta a kyau da tsada ta ke sakawa. A fuska ba ta nuna wani abu amma ga ni da na san halinta ni na san ta na da halin son a sani. Yanzu ma muna cin abincin ta na ba da labarin Alhaji Mustapha ya ce zai ba ta jari na miliyan biyar ta fara kasuwanci shi ne take neman shawarammu wata sana'a za ta fara. kowacce na faɗin albarkacin bakinta nima sai na tofa nawa na ce ta saro dogayen riguna da takalma da mayafai na mata ta fara saidawa mu gani ko za su tafi. Sai Ya Aina ta ce yauwa ta ƙara har da atamfofi da kayan yara ni kuma sai na ce kayan yara ta jinkirta tukunna zuwa gaba ta fara da waɗanan dai ta gani yadda kasuwan za ta kaya. Cikin mirmishi ta ce" Haka ma Shema ta ce. Da ya ke mun yi mganar da ita ta waya. Ya ce dai na tsaida shawara visa na fitowa Egypt za mu je a can zan yo sarin kayan nawa in sha Allahu." Ya Murja ta washe baki tana faɗin" Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ƙanwata." Ta amsa mata da Amin Amin. Ita kuma Ya Balki ta ce " Sai ki faɗa ma Gwaggo da Alhaji su suka albarka." Sai ta ce za ta faɗa musu sai mata fatan alheri suke yi nima na yi mata ta re da fatan Allah ya sa a fara a sa'a ta amsa lokaci ɗaya ta na kallona kafin ta ce" Amin Sadiya. Amma fa kema ya kamata ki zo ki fara wata sana'ar zama haka ba daɗi." Wani abu ya tsaya mini a maƙogawaro. Ma'u ta bala'in raina min wayau. Kuma kawai sai su Ya Balki suka amsa da wallahi kuwa Sadiya. Rahila ce ke faɗin" Ita fa Sadiya Shagon saloon da gyaran jiki take son buɗewa" > Janaftybaby: Ya Balki ta ce" To wannan ai lissafi ne me yawa. Ta dai yi tunanin fara wani abun kafin ta yi ƙarfin da za ta buɗe saloon ɗin." Duk yadda na so na yi mgana sai kuma na kasa. Da na so na mayar mata da martanin mganarta ne sai kuma na yi tunanin ina yi magana za a ce ni ce fitinanniya Ma'u ta yi min mganar arziƙi na maida shi ta tsiya Sai kawai na kalli Ma'u nima sai na mayar mata da martanin mirmishinta kafin na ce" Kar ki damu ki maida hankali kan naki. Nima soon in sha Allahu Suprise zan ba ku." Sai ta ce Allah ya yarda ta na min wannan dariyan na ta na mugunta. Ya Aina ko sai faman mgana take yi ta na cewa sana'a ita ce mace ko da mijinki na maka komai to ka yi dogaro da kan ka ko domin wata rana. Ya Balki ta ce" Har da ma rayuwa Ya Aina." Rahila ma na ji tana fadin itama za ta fara awo a cikin gida Ya Aina ta ce kasuwanci mai kyau. ita Ya Aina tana saida kayan miya da kayan nau'in ɗanɗanon girki ita kuma Ya Balki tana saida gwanjuna. Ni ce daman ban saida komai sai Rahila Ma'u kuma daman tana nuna mijinta na mata komai sai yanzu ne ta zo da labarin za ta fara na ta kasuwamcin. "Albishirin ku" Na faɗa ina musu mirmishi. Na gama cin abinci tuni har na sha ruwa na yi gatsa. "Goro fari ƙal." In ji Rahila da Ya Balki har suna haɗa baki. "Nan da kwana uku za mu cika shekara sha biyar da aure ni da Yallaɓai na. Haka ma Rahila da Ya Muntari." Na faɗa ina musu mirmishi. Ya Balki ta fara cewa" Ma sha Allah. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Kai ashe kun daɗe kamar jiya ne na ke ganin bikin ku fa ke da Rahila? Rahila na dariya ta ce" Sadiya ta na lissafi ni fa mancewa na ke yi. Ko da muka yi shekara goma sai da na ga sun yi walima ne na ce ma Ya Muktar yau auran mu shekaru goma Cif." Ya Aina ta ce" Shekarun suna gudu ba wuya. Allah ya ƙaro muku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya raya muku zuru'a." Muka amsa da Amin Ya Murja ma ta yi addu'a muka amsa mata. Sai Ma'u da ta gyara zama tana fadin" Ma sha Allah. Allah ya ƙara ɗankon kauna Mrs Yallaɓai da Mrs Ya Muktar." Ni ce na amsa mata Rahila ta na jin kunya Zaituna ce ta yi karaf ta na faɗin" Sadiya akwai walima ne? Ina mata dariya na ce" Akwai amma ta iya ni da Yallaɓai ce da yara." Ma'u ta ce" Allah? Ban damu kenan? Ina mata fari na ce" Ai kun gama na ku tunda kun yi addu"a. Ya Aina ta ce" Shi ne ko babban mgana." Zaituna na kallah ina faɗin" Tambayi Rahilan Hubby ƙila za su haɗa mana walima." Duka ta ɗaka min a cinya ta na faɗin" Sadiya ban son wulaƙanci." Kamar zan yi kuka na ce" Wai don na ce Rahilan Hubby shi ne har da duka? Rahila sai kawai ta balla min harara kunya duk ya kamata mu kuma gabaɗayanmu muka fashe mata da dariya. Sai ta ji kunya ta tashi ta fita, ta na fita Ya Balki ta ce" Daga Rahilan har Muntari masu kunya ne." Ya Aina ta ce" Wallahi ba su da hayaniya. Alhajinmu ya sha cewa tabbas an ijiye kwarya a gurɓinta." Ranar yini muka yi ana ta hira a yi daɗi a yi tsiya bayan mangariba Gwaggo ta ce Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shiri ta koma gidanta yinin ya isa haka. Jin haka yasa muka fara shiri saboda tun da Alhaji ya yi mgana to dole fa kowa ta kama hanya. Ni dai Yallaɓai na kira sai ya ce bari a yi sallar isha'i sai ya zo mu tafi gida. Ma'u ta fara tafiya Alhajinta ya zo ɗaukansu ita da yara haka ya yi mana yayyafim kuɗi goron salla damu da ya'yanmu ban sam kuma nawa ya ijiye ma Alhaji da Gwaggo ba. Su suka tafi da Zaituna da ƴaƴanta za su sauke su a gida daga can na ji Ma'u na faɗa ma Gwaggo za ta biya gidan su Shema'u. Kafin ya zo daman Ma'u ta sanar da Alhajimmu da Gwaggo mganar jarin da ya ce zai ba ta su ka yi ta masa godiya da saka albarka. Nima da Yallaɓai ya zo mun je gaban Alhaji na faɗa masa nan da kwana kaɗan auran mu zai cika shekara goma sha biyar da ni da Rahila. Alhajinmu ya yi mirmishi kafin ya ce" Ma sha Allah. Shekaru goma sha biyar masu albarka da tarin albarka zuru'a. Allah ya ƙara haɗa kawunanku. Haƙiƙa Yusufa da Muntari sun cika ƴaƴa tunda duk tsawon wannan shekarun ba su taɓa kawo min ƙaran ku da sunan kun yi musu wani abu ba hakan ma abin alfaharina ne. Allah ya yi muku albarka ya bar ku tare har jikokin ki." > Janaftybaby: Kan mu na ƙasa ni da Yallaɓai muna ta amsawa da Amin Amin. Gwaggo na gefe ta na ta saka albarka kafin ta ce" Jiya ba yau ba. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Na tuna da Mama itama shekarunta a ƙasa kenan Allah ya jiƙanta ita da Hajiya gabaɗaya." Muka amsa mata da Amin Amin da za mu tafi shima Yallaɓai ya ba ma yaran su Ya Murja goron sallah Marwa dai ta ce za ta bi Ya Aina zuwa gida amma jibi za ta dawo. Yallaɓai ya ba ma Alhajimmu kuɗi da Gwaggo amma ban sam ko nawa ba ne. Daga nan muka yi musu sallama ya ɗauke mu zuwa gida. Sai da muka koma gida har mun yi shirin kwanciya muna rumgume da juna Yallaɓai na shafa gashin kaina ya ce. "Sadiya ta." "Yallaɓai na" Na amsa masa cikin so da ƙauna. Sai kawai ya ce" Gani na ke yi kamar jiya jiya muka yi aure sai ga shi wai mun kusa cimma shekaru goma sha biyar da aure cikin yan kwanaki ƙalilan masu zuwa." "Nima haka na ke ji a zuciyata." Haka na faɗa masa na ke jin kamar jiya muka yi auran ashe shekarun sun tafi. Ƙara kamkameni ya yi kafin ya ce" Har yanzu ba ki sauya daga Sadiyar da na fara sani yar shekara sha tara ba." Nima ina mirmishi na ce" Kai ma har gobe baka sauya min a wannan gwarzon matashin da na aura a shekaru ashirin da bakwai ba." Sai kuma muka kalli juna ta cikin duhun ɗakin da ɗan hasken da ya kan shigo ta window ɗin cikin bedroom ɗin kafin ya sumbaci goshina ni ma sai na maida masa martani na sumbaci kumatunsa kafin mu koma mu kwanta yama ƙamƙame dani kamar za mu koma abu ɗaya. ** Wed.13 JULY 2015. Rana ta ƙara zagayowa ranar da a irinta ne aka ɗaura mana aure ni da Yallaɓai a irin kuma ranar ne muka zama miji da mata. Jiya Yallaɓai ya dawo domin tun washegarin ranar da muka dawo daga Ɗorayi ya je kaduna sai jiya da daddare ya dawo. Kuma yau tun safe ya fita saboda Nene ta kira shi a waya tana son ganin shi. Bai ko tsaya a gida ya ƙarya ba ya fita wanka kawai ya yi. Su Jidda sun koma makaranta tun jiya sun tafi gidan ba kowa sai ni kaɗai Marwa ba ta dawo ba amma na kira Saude na ce ta zo ta ta ya ni mu gyara gidan. Na ba da a yi mana cake babba sannan a gida na ce zan yi mana zoɓo muna da sauran naman sallah na ce kawai sai mu yi amfani dashi bayan haka na yi dambun nama da yawa ya na nan. Kawai dai yar walima ce daga ni sai mijina sai ƴa'yana. Saude ta zo da wuri tare muka gyara gidan ko'ina muka turare shi da turaren kamshi. Saude na saka ta dafa farar shinkafa tunda ina da miya da na yi a frigde sai na koma ɗaki na ɗau wayata na kira telanmu domin na ɗinka wani material mai kyau saboda wannan ranar na tuna masa yau zan yi amfani da shi sai ya ce zai aiko min da shi anjuma kaɗan. Sauran kazar da na siya wajen Surayya Halin yau na ce Saude ta ɗumama ta kai mini falon yara ni kuma sai na kunna data na shiga ina ganin saƙonni. Na ga group ɗin gidanmu ana ta tagging ɗina ina shiga sai na ga Ma'u ce ta sanar da Anniversery ɗin mu ana ta yi mana fatan alheri ni da Rahila da Ya Muntari. "Mrs Injinya Allah ya ƙara dankon ƙauna." In ji Yaya Auwal shi kuma Ya Hamza tagging ɗina ya yi kafin ya ce" Yallaɓiya an gangara a bautar ubangiji.. Allah ya zaunar da ku lafiya." Haka suka yi ta ma Ya Muntari shaƙiyanci wai ɗankwali ya ja hula. Nima na shiga ina amsawa cikin farimciki. Na je na yi status amma ban saka hoto ba na dai saka Alhamdulillah! Sannan sai na rubuta" "Shekaru goma sha biyar cikin farinciki Alhamdulillah." Duk da ban yi caption ba sai aka fara mini mgana ta private ana mana addu'a yawanci duk yan makarantar mu ne da muka yi BUK tare waɗanda na ke da lambarsu. Sai Adnan ɗin su Yallaɓai da ya gani ya ce min" Ma sha Allah Happy Wedding Anniversery Mrs Yusuf Muhammad Tafida." Musabahu ma haka ya ce mini" Ma sha Allah Allah ya ƙaro danƙon kauna ta Yallaɓai" Duk na amsa su. Sauran dai su Anty Bahijja ban ga sun gani ba. Zuwa na yi na zaƙulo hoton Rahila a waya na ranar sunan ɗiyarta da aka ɗauka na saka a status ɗina na c > Janaftybaby: " Happy 15 years Wedding Annivesary Mrs Muntari Amini yashe(Hubby)" Sai na ƙara da emojin rawa da murna da dariya. Ina ta dariya saboda na san in ta gani sai ta yi mgana Ya Hamza ya fara gani kawai sai ya yi tagging ɗin status ɗin da cewa. "Ina na ki hoton? Ina dariya na ce ni ban da hoto ya ce ban isa ba. Kowa sai ya ce wai ina hotona da na Yallaɓai tunda na saka na Rahila. Ganin sun dameni ya sa dauko hoton da ranar idi ne ma Marwa ta ɗauke mu da wayata ni da Yallaɓai yana tsaye ni kuma na jinginar da kafaɗata a saman kafaɗarsa. Shi waya ma ya ke yi bai san ana hoton ba ni kuma ina mirmishi. Hoton ya yi kyau sosai yana sanye da farar shadda mai babban riga sai dai ya cire babban rigan. Ni kuma na saka leshi mai ruwan haske akwai zanen marun a jikin leshin sai ya haskani gabaɗaya. Ina mirmishi shi kuma Yallaɓai ya ɗan sunkuya yana kallona aka ɗau hoton shi na saka a kasan hoton sai na saka. "Barka da shekaru goma sha biyar cikin Aminci, soyayya, sadaukarwa a gare ka ya amintattace na. MRS HALIMATUSADIYA YUSUF MUHAMMAD (YALLAƁAI NA)" Na ƙara da gayyar emoji kafin ka ce kwabo duk yan gidanmu sun ce na tura musu a group ɗin gida na tura hotunan tuni har sun sakamu a status daga ni har Rahila ni a bayan wannan sai na saka hoton Jidda da Baby shima da wannan sallan aka yi musu na yi mgana a ƙasa da cewa. " A shekaru 15 da auren mu ga albarka da Ubangiji ya yi mana nan. Allah ya raya ku HAUWA'U YUSUF MUHAMMAD(Jidda) DA MAIMUNATU YUSUF MUHAMMAD(Baby)." Kowa sai addu'a ya ke yi. Har ta Ma'u sai da ta ce na tura mata itama ta saka ta yi mana addu'a na amsa mata ko da bai kai zucci ba. Na duba Yallaɓai ba ya online na kuma kira layin shi ba ta shiga. Sai kawai na tura masa test massages. "Happy Wedding Anniversy Yallaɓai na" Na jira na jira amman bai turomin amsa ba sai na yi tunanin ƙila Network ya sa bai shiga ba. Da ya tafin na kira shi na ji ko Jikin Nenen ne ya tashi sai ya ce mini yanzu ya iso gidan lafiyanta ƙalau sai hankalina ya kwanta. Na yini cikin farincikina ina ta amsa wayoyin yan' uwa da abokan arzuƙa har mutanen fatakol Anty Zabba ta kirani ta na min fatan alheri Haka Munnira Hauwa dai wayar ta ya lalace ba ta sani ba. Amma har Nafisa Muhammad Sani mun yi mgana da ita, sauran yan gidansu Yallaɓai duk waɗanda suka ga status ɗina mun yi mgana hatta da Halima Autar su Yallaɓai amma ban ga Anty Bahijja ko Anty Maimuna sun gani ba Mimisco dai tana online amma ba ta duba ba. Ban damu ba, na cigaba da harkokina. Saude sai wajen uku ta tafi gida ni kuma salla kawai ke ta da ni a inda na ke Yallaɓai har lokacin bai dawo ba na kuma kira shi ta shiga bai ɗauka ba na ƙara kira shuru sai can ya turamin saƙon zai kirani ya je wani waje ne ni kuma sanin sabgoginshi sai ban damu ba. Na cinye sauran kazar hadin uwargida duka na sha gumba sannan na sha kayan marmari ranar ko abinci ban ci ba har Jidda suka dawo makaranta daman na gaya musu in Yallaɓai ya dawo da daddare za mu yi walima Jidda ta ce" Umma waliman mene? Ina mirmishi na ce" Na cikar mu shekaru sha biyar da aure ni da Abbanku." Da ya ke ta na da wayau sai ta ce" Umma Allah ya bar ku tare." Na amsa da Amin Baby kuma sai tsallen murna ta ke yi, ko kafin mangariba har ɗinkina an kawo min daman kunshin sallar da na yi bai fita kitso kuma daman bai dameni ba ƙara gyara kaina kawai na yi, na saka Jidda ta ƙara gyara gidan ta kunna turaren wuta. Ina da bloons na ma Baby ne jidda ta kama min muka hura su na ɗaura su a falon mu wajen guda ashirin kala kala. Sai falon ya yi kyau sai bayan mun yi sallar mangariba sannan mai cake ta aiko mini dashi da kwatance sai gashi a gidana ta online na siya ƙanwar wata mate ɗina ce da muka yi Buk ce ke yi. Sannan na siya ma Yallaɓai gift wani agogo mai kyau 25k shima a wajen wacce muka yi BUK na siya daman kayan maza take saidawa na saba siyayya a wajenta in dai zan siyam Yallaɓai wani abu na gift wajenta na ke siya. > Janaftybaby: Bayan mun idar da salla mangariba muka ƙara kawata falon a center table na ijiye cake ɗin sai muka zagaye shi da voul na nama da dambun nama cake, da donut sai lemuka da ruwa. wajen ya yi kyau muna gamawa na ce Jidda ta kashe hasken falon in an ji motar Yallaɓai yana shigowa sai a kunna daga nan na ce su je ta yi wanka ta yi ma Baby na ce su saka dogayen rigunan da na siya musu yan kati ita na Jidda riga da wando ne. Baby kuma doguwar riga ce kala ɗaya na siya musu mai kalan baƙi da fari. Nima na shiga bedroom ɗina na tuɓe na faɗa Tiolet na yi wanka amma a ƙasan raina ina tunanin ina Yallaɓai ya je? Ko kaduna ya je? Ya ce zai kirani amma shuru har na fito wanka ina wasi wasi. Daman na yo alwalata ana kiran isha'i na kabbarta salla bayan na idar ne na zo na zauna gaban madubi na tsantsara kwallya mai ƙayatarwa. Na gyara gashina na sake shi baya na yi ɗauri mai kyau ɗinki riga ds sikat ne sun kamani sun yi mini cif a jikina haka na yi ma kaina barin turaren humra ko'ina na gifta ina tashin kamshi na saka wani takalmina baƙi mai ɗan tsini kaɗan ina tafiya ya na ɗan ba da sauti kaɗan ƙwas! Ƙwas Falon yara na shiga na gansu sun yi kyau suma. Jidda ma ta ce" Umma kin yi kyau" na ce na gode sai na ja su muka yi ta ɗaukan hotuna sun ɗan yi ma duhu saboda dare tare muka zauna sun kunna cartoon ni kuma waya ce a hannuna ina ta kiran Yallaɓai wayarsa a kashe tun ina duba agogo ina saran dawowar Yallaɓai har na sare Baby ta gaji har ta fara barci ita kanta Jiddam ma barci ta ke ji. "Umma Abba bai dawo ba? "Yana kan hanya in sha Allahu." Na faɗa mata cikin karfin hali. Tashi na yi na fara zagayen falon ina yi ina duba agogon wayata. Tara da rabi ta yi shuru sai hankalina ya tashi na fara tunanin ba lafiya goma na yi na ce bari na kira Nene na ji ko yana can ai kuma ya san da ina gida ina jiran shi. Na latso lambar Nene kenan zan kira sai kira ya shigo mini na ɗauka Yallaɓai ne jikina na rawa na koma na zauna sai dai kuma sunan wacce ke kira ne ya sa sai da gabana ya faɗi Ras! Haka kurum na ji kamar ba alheri ba ne ya sa ta yi min wannan kiran karfe goma na dare. "Ma'u ce.' Jikina sai ya kama rawa har ta katse ban ɗauka ba. A ƙoƙarina na kira Nene amma ba ta bari ba kawai sai ga wani kiranta ya ƙara shigowa cikin dauriya da shahada na ɗaga kiran "Ma'u." Na faɗa kafin ma na yi mata sallama. Sai ta amsa mini cikin yanayin muryanta amma cikin farinciki. "Na'am Sadiyar Yallaɓai." Yadda ta faɗi sunan ne sai na ji ban yarda da ita ba. Kafin na samu zarafin mgana ta cigaba da faɗin" Na san za ki ce kira cikin daren nan ko? . Da sauri na ce" E ina fatan lafiya." Sai da ta yi wata irin dariya kafin ta ce" Lafiya sumul. Murna cika shekaru sha biyar da aure na kira na yi miki sannan tare da ba ki wani kyakyawan albishir." Sai kawai na ji zuciyata ta tsinke amma sai na ɗaure cikin karfi hali na ce" Na gode. Ina jin ki wani albishir ne wannan da ba za ki iya jiran safe ba ki ka kira cikin daren nan? Tana dariyan nan na ta na mugunta ta ce" Ba na so wani ya rigani ne. Na fi so ki fara jin wannan albishir ɗin daga bakina." Juyawa na yi sai na ga Jidda har ta fara barci daga kan kujera sai kawai na miƙe na buɗe kofar falon Yallaɓai na shiga na maida ƙofar na rufe a cikin duhun nan na lalubi kujeran dining na ja na zauna ina faɗin" Uhm ina jin ki Ma'u." "Zan kashe wayata yanzu. amma ki kunna data ki hau whatspp na tura miki saƙo." Ko kafin na ce wani abu ta kashe wayarta. Ni fa na gama sakankancewa daman ba alheri Ma'u za ta nuna min ba. Amman ban taɓa tunanin ganin abin da na gani ba. Jikina na rawa na buɗe data saƙonni na shigowa amma ba ta su na ke ba Ma'u na ke nema ina ko ganin ta tura mini abu kamar hoto na faɗa hannuna na rawa na danna sama yana buɗewa. Wallahi tallahi yana buɗewa ne amma kamar yana buɗewa da gudun numfashina ne. > Janaftybaby: Yana gama buɗewa na ji kirjina ya amsa. Kaina ya sara, hannunawana sun fara ƙarkawa saboda jikina da zuciyata suna rawa ne a lokaci ɗaya a lokacin idanuwana sun firfito ba domin na ji mamakin abin da na gani ba ne. Sai domin ban taɓa tsammacin shi a lokaci kusa haka ba. Ina wannan rawan jikin da na zuciyan kiran Ma'u ya sake shigowa ban ɗauka zan samu kuzarin ɗaukan wayarta ba amma sai gashi na ja na ɗauka na kuma ƙarata a kunnina duk da yadda zuciyata ke gudu da sauri da sauri. "Ina fatan kin ga irin kyakyawan albishirin ɗin da na ke so na gaya miki ko Sadiya? Runtse ido na yi zuciya na fat fat! Amma sai wata zuciyar ta ce Sadiya kar ki bari a ga gazawarki daman shi Ma'u take jira kamar an dake ni na dawo hayyacina sai na saki wani mirmishi wanda ya fi yin kuka daɗi na ce" Haba ai kin makaro Ma'u domin Yallaɓai ya riga ki yi mini wannan albishir ɗin' Shuru ta yi domin ni na san ta yi mamakin jin kalamaina. Ban bari ta ƙara mgana ba na ce" kin yi gaggawa Ma'u da kin jira da ni da kaina zan kira ki na faɗa miki Yallaɓai YA ƘARA AURE" Ban ƙara ba ta wata damar mgana ba na cigaba da faɗin" Walimar da na shiryama ma a gida saboda Anniversary ɗin mu ne da kuma taya shi Murnan ƙaruwan da ya samu na aure." Ina gama faɗin haka kit na kashe wayar saboda sai na ji kamar santsi na ja na ina shirin na sumulmiyo daga kan kujeran da na ke zaune. Sai na kama jikin kujeran da hannuna ɗaya na ƙanƙame jikina ba inda ba ya rawa. Zuciya ta da tunanina sun tsaya waje ɗaya cak na kasa yin ma wani tunani. Ji na ke yi kamar ina zaune ne amma jiri na ke gani shi ya sa na ƙamƙame kujeran da na ke zaune amma ban san lokacin da na ji na sulmiyo ƙasa ba. Sai ga ni zaune a kan mazaunaina a ƙasan tayel ina kokawa da numfashina wayata ta yi zaman dirshan a kan jikina na saka hannunawa da suke rawa na ɗauka na buɗe na koma whatpps na shiga kan sunan Ma'u ina kallon hoton da ta tura mini sai a lokacin na lura da in da Ma'u ta ga hoton. Sunan Anty Bahijja ne a saman sreenshoot ɗin da ta yi, sannan hoton na GIMBIYA CE(SAUDATU) tsohon hotona kamar ma a gidanta na Abuja ne kafin mijinta ya rasu. Tana tsaye a falon gidanta a lokacin ta na mirmishi ta saka wata doguwar riga ne a hoton. Abin da ya fi ɗaukan hankalina shi ne kalaman da aka yi amfani dashi a ƙasan hoton. "Allahu Akbar alƙawarin Allah ya tabbata. Congratulation Mrs Yusuf Muhammad(Tafida)." An ce wai ka yi ma hawaye rahama ne. Sai yanzu na amince da wannan mganar, na kasa jin kuka ya taho mini ma idanuwana sun ƙeƙashe. Shi kenan ta faru ta ƙare an yi ma mai dami ɗaya sata. Daman shi ne suprise da Yallaɓai ya ke ta faɗin zai ba ni? Lalle ko na karɓi kyakyawan suprise. Ban san lokacin da ya shigo gidan ba domin ban ji ƙaran buɗe get da shigowar motar sa ba ba. Sai da na ji lokacin da ya ke saka ɗan makulli yana ƙoƙarin buɗe kofar falon kamar an jani an mikar dani tsaye sai ga ni a tsaye a kan kafafuna. Wayata kuma tana jimƙe a hannuna. Ya buɗe kofar kenan ya shigo ni kuma sai na fara takawa ƙwas ƙwas ina ji jikina na rawa amma na daure na isa ga makunnin wuta na kunna dai dai yana ƙoƙarin ciro wayarsa daga aljihu domin haska fitila. Haske ya gauraye falon. Ya bi ko'ina da kallo dai dai lokacin kuma wasu daga cikin bloons ɗin da na saka afalon suka fashe ji ka ke yi tus! Tus! Sai da ya ɗan waiga sannan ya juyo yana sauke kallon shi a kaina dai dai ni kuma ina tsaye a gaban shi na harɗe hannayena a bayana. Na ƙasa takawa zuwa gare shi, saboda sai na ga kamar ba Yallaɓaina bane kamar wani ne wanda ban saba dashi ba, sai na ke jin kamar wannan Yallaɓan yanzu akwai wata tazara da ya shimfiɗa a tsakanimu daga yau. Kafafuna sun yi sanyi kamar gara ya kama su in na ce zan cire ƙafa zan iya zubewa saboda firgici. Shi ma sai na ga ya tsaya yana kallona amma kuma bai tsawaita ba da sauri ya kauda kanshi. Mirmishi ya ke gayyato ma fuskarshi sai dai ban bari ya gayyato ma kanshi ba ni na fara gayyato ma kaina mirmishi lokaci ɗaya ina faɗin. "HAPPY 15 YEARS WEDDING ANNIVERSARY YUSUF MUHAMMAD TAFIDA." > Janaftybaby: Na faɗa ina kallon ƙwayar idanuwanshi. Yadda ban je gare shi domin na rumgume shi ba. Shima bai yi saurin takowa gare ni ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana mai ijiye ledojin da ya shigo da su a hannun shi a ƙasa wanda ban san abin da ke ciki ba. Kafin ya ɗago kansa cikin ƙwayar idanuwanshi na ga rauni. Kasala tsoro da wani abu da na kasa ganewa. A kuma yanayin ya kira sunana cikin wata irin muryan da ban taɓa sanin Yallaɓai na da ita ba. "HALIMA." Zan iya kirga sau nawa Yallaɓai ya taɓa kirana da sunana Halima, a da in ya kirani ina jin kaina ya yi girma. Amma ban da yau domin sai na ji kamar ya kwarara min ruwan zafin a cikin jikina. Har ina jin tururunshi da hucin shi daga fatar jikina. Sai na ji kamar komai yana sauyawa kamar duk wata kyakyawan alaqan da muka gina ta tare da Yallaɓai tana zangayewa tana komawa ruwa. Kamar kuma ruwan ya fara zuba a ƙasa ya na kwarara da ƙarfin gaske wanda daga ni har shi ba za mu iya tare shi ba. *Ƙarshen littafi na Ɗaya*