LABARI MAI DAƊIN SAURARE
Abinda ya faru shine
Jiya da daddare da misalin ƙarfe bakwai na dare wata lamba ta kirani cikin ikon Allah na ɗauka sabida ban fiye ɗaga waya ba nafi gane a turo mun saƙon karta kwana.
Sai tace dani
“Ƴata dan ALLAH hutun da kika ce zaki yi na tsawon kwana goma yayi yawa ki daure zuwa monday in dai da hali kici gaba da rubutun dan ALLAH. In ina karanta littafinki ina samun nishaɗi sosai. Ƴata Ubangiji Allah ya huwace miki baiwar tsara rubutu da fikrar hausa sosai. Ni tsohuwar ma’aikaciyar jarida ce, nafi shekara talatin ina karance karancen littattafan hausa irin nasu Ado gidan dabino, Balaraba Ramat, Anty Bilki funtua Amman Ƴata salon rubutunki ya bambamta da na ragowar marubuta. Hausarki, sunayen jarumai, da yadda kike amfani da daɗaɗɗun kalaman hausa, bugu da ƙari sunayen littattafanki sunfi komai burgewa.”
Mun yi maganganu da’ita sosai na yaba na kuma yi mata godiya dattijuwace sosai.
Na yi mata alƙawarin monday zanci gaba da posting da izinin Allah.
Maigidana daya dawo masallaci na bashi labari sai ya umarceni da yau lahadi in soma posting ɗin kawai.
Mamana gashi na soma posting sabida girman soyayyar da kika nuna mun
Masoyana a duk inda suke da bazarsu nake taka rawa. In babu ku babu BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.
001
SABUWA:.
Hannu na saka zan amshi ledar da Khalid yake miƙo mun ina murmushin cusa haushi. Ban aune ba naji an warce ledar tare da tunkuɗeni gefe naje na faɗi na dauje hannuna.
Babangida ashe ya fito a mota da gudu kamar mayunwacin zaki.
“Dan ubanki waye wannan, wanne kwarto fasiƙin maƙiyin Allah da manzonsa ne wannan. Au ashe Sabuwa har yanzu baki dena bin maza ba da gasken dai duk fitar da kike yi maza kike bi?”
Da sauri na miƙe ga mutane har sun soma taruwa”
“Malam koma me kake tunani bai kamata ka shiga ɗaga murya a hanya haka ba. Matarka ce fa, ya zaka tunkudeta haka”
Karku daɗa kar ku raga iyakar abinda Khalid ya faɗa kenan Babangida ya kucuneshi ya soma cunkusa mishi manyan ashariyar da kamar a bakin tasha aka haifeshi yana yi yana jijjiga Khalid idanunshi kamar gauta.
Ka sake shi Babangida, zanma baya”””
Hannu yasa ya zabga mun mari, ya sake marina bakina ya fashe.
Ya sake ɗaga hannu kenan Khalid ya riƙe hannun gam jikinshi na rawa yace.
“Kar ka sake dukanta in kai baka san darajarta ba ni nan nasan darajarta. Baby ashe ɗan balaja’u kike aure ban sani ba, madoki wanda baisan darajarki ba?”
Habawa Khalid bai rufe baki ba Babangida ya runtumashi da ƙasa, dambe ya kaure kica_kica jama’a suka haɗu kamar yaƙi mata sai tittiɗowa suke yi sada gidajensu.
Da kyar aka raba faɗannan Babangida ya shiga labartama jama’ar da suka taru.
“Matatace fa kwarto ya kawota har gida, har yana mata siyayya fa, saina kasheki Sabuwa wallahi, shima sai ya mutu. Mutuwa nima zanyi uban kowa ya huta. Yana faɗan haka ya cabke wuyana ina kakari yana dukana. Da ƙyar aka ɓanɓare Babangida a jikina. Duk ya fasa mun wuyana.
A guje na faɗa motar Khalid, ana in fito naki fitowa Babangida kamar zai haukace haka yake ji. A guje ya gangara.
“Malam ja motarka ka bar wajennan dutse yaje ɗakkowa zai ragargaje maka mota”
Da sauri Khalid ya buɗe motar ya shigo, yana ma motar key muka hango Babangida da ƙaton dutse a hannunshi, habawa a guje muka hau titi har muka kusan kaɗe wata baiwar Allah mai ciki, dutsen da Babangida ya harbo ya fashe ma Khalid gilashin bayan motarshi.taratsatsatsa
Gudu muke yi Babangida na binmu a mota.
Ka kaini gida Khalid, na gama auren Babangida na gama zama dashi kenan har abada.”
“Amman babu matsala Baby jini ne yake zuba a bakin ki da hannunki fa muje asibiti”
Idanu na lumshe na waiga Babangida na biye damu a mota.
A_a ka kaini gida kaga biyo mu yake yi, in kuka kuma haɗuwa zai iya maka komai”
Ƙwafa yayi yace
“Rabu dashi bai isa yayi miki komai ba, ni kuma daidai nake dashi. In yana jin shi tataccen ɗan iskane ni ubanshi ne a iskanci”