💦MALIKA MALIK💦..!*
(Sai na rama..)
By Janafty
1
Free Fage
KATSINA
"""Da misalin karfe 11:20pm na daren Ranar jumma"a Akan Titin dake tsakanin Dutsenmah da katsina wacce take gabda shiga katsina.
Adaidai kan Titin akwai yan Sanda wadanda suke patrole awajen,Suna tsatsaye ne Gefe kuma ga motocinsu guda biyu akallah yan sanda zasu kai su Biyar kowannesu, sanye da uniform dinsu bakake,da ganin kayan jikinsu basai ka tambayesu ba,zaka gane dukansu inspector ne,domin basu da kowani Rank ajikin kakin nasu,dukkansu fuskarsu sanye da Hula p-cap,da bakaken safan hannu sai manya manyan Tociloli masu bala”in haske kamar ta yan fashi,wanda in aka dallareka dasu, sai ka dakata saboda bala”in haskenta,Duk motar da tazo wucewa sai sun tsaidata sunyi bincikenta saboda tsaro dakuma bincike, wanda daga sama suka sameshi saboda masu shiga da fita da mugayen makamai wanda ake Shigo dasu daga bodar katsinar aboye.
Motocine jere guda goma sha biyu dukkansu 11 din iri daya ne Corollahx sai babban ciki wacce tafita dabam itace Range cover baka ce gabadaya motar Tinted ne gaba da bayanta kowacce mota bayan motan an saka musu Nomba mai dauke da Tambarin MALIKA MALIK1 har zuwa na 12,gudu suke ta shararawa bisa Titin Dutsenma zuwa katsina,Tundaga nesa Yan sandan suke Dalle su da fitila Tunda sukaga yadda suke gudun ganganci bisa Titi.
Sai da suka kawo gab kana suka fara slow,motar Farko Tana tsayawa Suma na baya suka tsaya,Wani inspector ne ya karisa kusa da motar yana kwankwansa glass din motar,sai da aka bata lokaci kana aka zuke glass din motar.
Wani Inyamuri ne zaune a mazaunin Direba sanye da wasu kaya brown colour Riga da wando da alamu dai kamar Uniform ne,Kallonsa yayi daga sama har kasa kamar yadda Dan Sanda ke karemasa kallo,Cikin gadara ya furta”Lafiya mallam.?.”Dan Sandan yayi mamakin jin Hausa abakinshi don akallon Farko bai yi kama da wanda yakejin Hausa ba.
Gyara tsayuwa yayi yana fadin”Zamu bincika duka motocinku ne,daga ina kuke da tsohon daren nan? kuma kuke gudu ba bisa ka”ida ba..?.”Yafada yana leka motocin dake bayansa Dan ware ido Direban yayi yana fadin”kai kana ko da hankali kasan motocin waye ka tsare kuwa? dariya Dan Sandan yayi yana fadin”Wannan bashi ne Abun da na Tambayeka ba,tambayanka nake daga ina kuke,? bai mai mgana ba kawai sai ya kada kai yana fadin”Zaka shiga mtsala matukar MADAM Ta fahimci meke Faruwa..”Yafada kai tsaye.
Dan Allah a saka mn cigaban ta wannan shafin mu cigaba da karantawa
mun kagu
pls