🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandycom.ng for your updated.
FIRST FAMILY…
*1…….* Ƙarfe biyar da minti arba’in da takwas na yamma, ta faka Motarta a parking space, ajiyar zuciya ta sauke ya fi sau uku, sannan ta kalli takardun da ke gefenta kamar mai tunani, daga bisani ta kai hannu ta ɗauka, ta buɗe motar ta fito.
Jiki a sanyaye ta nufi harabar gidan, gurin da Mahaifinta yake zaune yana shan iska, daman a al’adarsa ya kan zauna a habarar gidan da yamma, wani sa’in ya kan duba jaridu wani lokacin kuma ya leƙa yanar gizo, dan sanin me duniya take ciki.
Da kamar fargaba Namra ta doshi gurin da yake, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama.
talkamin ƙafarta ta fara cirewa tun kamin ta ƙasara kusa da carpet ɗin da aka saba shimfaɗa masa, sallama ce ta fito bakinta kanta na ƙasa kamar mai jin nauyin kallonsa.
“Assalamu Alaikum”
Bai amsa sallamar ba, sai dai ko kaɗan hakan bai bata mamaki ba, daman bata tsammaci zai amsa mata ba, sai kawai ta ɗora da gaisuwa.
“Abban sannu da hutawa ya aikin?”
Ya yi jinkirin amsa mata na daƙiƙon da zai kai ashiri zuwa ashirin da biyar, sannan ya amsa mata can ƙasan maƙoshinsa
“Al-hamdulillah”
Bata yarda wata kalmar ta ƙara fito daga bakinta ba, sai kawai ta tashi jiki ba ƙwari ta saka takalminta, ta nufi hanyar da zata sadata da part ɗin Mahaifiyarta.
Sai da ta share hawayen da suka zubo mata kamin ta kai hannu ta murɗa ƙofar falon ta shiga. Babu kowa a parlor sai air conditioner dake ta aikinsa, Kai tsaye ɗakinta ta wuce zuciyarta cike da rauni.
Saman gadonta ta zauna ta lumshe ido tana sauraren bugun zuciyarta, kalaman da Mahaifinta ya yi mata ɗazu da safe suƙa riƙa dawo mata, irin yadda ya riƙa aibanta ta, yasa ta ta yi saurin dafe kanta, sai kuma ta fashe da kuka tana murza zoben dake hannunta.
Haka ta zauna a ɗakin bata fito ba har sai da aka yi sallah Magariba, bayan ta yi sallar ta fito ta nufo parlor fuskarta babu yabo babu fallasa.
Duk ƙannenta suna zaune parlor suna kallon Dadin kowa, babu wanda ya lura da fitowarta sai Mahaifiyarta. can nesa da Mahaifiyarta ta zauna tana gaisheta.
“Anty barka da dare”
Bata amsa mata ba, sai kallonta take tana karantar irin halin da ƴarta take ciki.
“Tunda kika dawo daga makaranta Namra kina cikin ɗakin, so kike yi damuwa ta yi miki yawa ko? Yau ranar girkina ce amman saboda ke Abbanku bai leƙo nan ba, na shiga sashensa na rasa gane kansa, so kike ki kashe min aure ko Namra? kin fi son ki rayu da son zuciyarki fiye da farincikin iyayenki? bana ƙin zaɓin ki Namra, amman tun da mahaifinki ba ya so barin shi ya fi alheri”
Matsewa ta yi cikin kujerar tana wani irin kuka da ba zata iya fitarwa ba.
Sai yaushe Abbah ta zai fahimci halin da take ciki ne, sai yaushe zai tausayawa rayuwarta? ji take idan har ta yarda ta rabu da Asim zata iya mutuwa, bata jin zata iya rayuwa da wani Namji da ba Asim ba, kuma idan har bata aureshi ba, ta san Allah ba zai yafe mata ba, mutane zasu masa dariya, daman an daɗe ana masa kirarin ita ɗin ba sa’arsa bace, ta san irin son da Asim yake mata, ta ya zata iya sanar da shi ba zata aurensa ba? Yayyu ta Mata da Maza Tara Mahaifinta ya aurar, duk kuma a cikinsu babu wanda ya yi ma zaɓin miji ko matar aure sai ita.
Sallamar Barrister Yasmin da Mijinta ne, ya ankarar da ita ta yi saurin share hawayenta, tana gyara fuskarta dan kar su gane ta yi kuka.
Anty Amarya ce ta amsa musu fuska a sake kamar yadda ta saba tarbonsu.
“Maraba maraba da Lauyoyi, cikin daren nan ake tafe”
Yasmin ta zauna a kujerar da Anty Amarya take zaune, yayin da Uzair ya zauna a kujerar da ke kusa da ƙofa, idonsa na kan Namra wace ta banye ɗaurin ɗankwalinta tana ƙoƙarin magana da matarsa.
“Anty Barrister ina Afnan?”
“Yanzu na biyo uban daren nan na miƙe hanya ki rasa wanda zaki tambaya sai Afnan? amman yarinyar nan akwai ki da rainin hamkali”
Kusa da ita Namra ta dawo ta zauna tana faɗin
“Kaji Anty da wata magana, toh ai ita ce Ƴata dan haka ni ita zan tambaya”
“Idan kina son ganinta kawai ki je gidan Gwaggo ki ganta, amman indai tambaya zaki yi, ki riƙa cewa ya na ke ni da Mijina”
“O’oh masu miji manya, toh ni ban ga mijin na ki ba ai”
“Ni ai na ganki”
Uzair ya amsa daga inda yake zaune yana kallon ƙugunta zuwa saman ƙirjinta.
“Jar uban nan, ka ji min wata magana! saboda ke fa muka biyo ta nan amman zaki wani ce baki ganshi ba”
Duk suka sa dariya Maryam ta ce
“Toh mijin na ki ai tsoron mutane yake shiyasa ya maƙure gurin kamar wani ɗan fashi”
Anty Amarya ta kai mata dudu
“Wai dan kun ga baya magana shiyasa kuka raina shi ko?”
Dariyar suka sake yi, sannan Anty Amarya ta shiga tambayar Barrister ya aiki. Namra kuma ta nufi hanyar kitchen dan ta ɗauko musu ruwa, tun da ta tashi Uzair ya bi bayanta da kallo har ta shige kitchen ɗin.
Bayan sun sha ruwan ne Barrister ta ce
“Anty Mun zo aron Namra ne, Uzair zai yi ɓaƙi daga Abunja,kuma yana son ayi musu wainar kaza kinsan Namra ce ta iya shiyasa muka zo mu faɗa miki”
“Aa ni ba ruwana ga ku ga Namra”
Cewar Anty Amarya tana kallon Namra da ta ɗan ɓata fuska kaɗan, dan sam yanzu bata son zuwa gidan Yasmin, Hakan kuma ya samo asali ne tun lokacin da Uzair ya soma nuna mata maitarsa a fili.
“Kai gaskiya na so nayi tilawar haddata, dan Saturday nan ne walimar mu fa”
Yasmin ta ɗan zungureta
“Ke uwar kuiya, just for one day ne fa zaki mana, ai yau Wednesday, zaki iya yi Friday”
“Haba kije mana idan kin gama musu da wuri ma ai zaki iya dawowa”
Anty Amarya tasa baki. Yasmin ta ce
“Kuma ni kin ga fita zan yi ba gida zan wuni ba, ina da cases har huɗu ƙila sai yamma zan dawo balle ki ce zan dame ki da surutu, Uzair kuma sai biyar yake dawowa, ke kaɗai ma za’a bari a gidan”
Ta amince ba dan ta so ba, sai dan babu yadda zata yi, indan har ta ce ba zata je ba, Yasmin zata zargeta, Anty Amarya kuma zata mata faɗa, sa’arta ɗaya gobe ba su da lacca.
ba su wani daɗe sosai ba, suka yi ma Anty Amarya sallama suka fice. Har gurin Mota Namra ta rakasu, Yasmin na laƙame da kafaɗarta tana mata tambihi game da haƙuri, dan ta fi ƙowa sanin halin da Namra take ciki, kasancewar shaƙuwarsu, Namra bata ɓoye mata ƙomai.
Bayan sun wuce ne ta dawo jiki a sanyaye ta shigo parlor.
“Ni wallahi bana son zuwa gidan Anty Yasmin”
Ta faɗa tana ƙoƙarin zaunawa saman kujera. Maryam ta kalleta ta ce
“Saboda me?”
Kamar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru ta kalli tv.
“Tashi kije ki ci abinci”
“Bana jin yunwa”
“Ai gaki nan, duk kin bi ki koɗe sai fama kike da rama kamar wata marar lafiya”
“Wallahi Allah bana jin yunwa Anty”
“Ta ya zaki ji yunwa kin ɗauki damuwa kin sawa ranki, Allah ya sauwaƙe miki wannan rayuwa”
Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, dan ta dan duk yadda zata yi ma mahaifiyarta bayani, ba ganewa zata yi ba.
Annur ne ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa hannunsa riƙe da lemu ya ce
“AntyAmarya wai Abbah ya ce ki zo tare da Anty Namra”
Gabamsu ya faɗi dukansu, bama kamar Namra data ja wani dogon numfashi ta sauke, kamin ta kalli Mahaifiyarta. Ba tare da ɓata lokaci ba suka tashi suka nufi part ɗinsa, kishingiɗe suka tararda shi, kofin tea na gefensa yana sanye da madubi fuskarsa babu annuri yana duba wasu documents.
Namra ta zauna ƙasa cikin ladabi, Anty Amarya kuma ta zauna saman kujera tana faɗin
“Annur ya ce kana kiran mu!”
Bai ce uffan ba, har sai da ya ƙare duba takardun da yake sannan ya cire gilashin idonsa, ya kalli Namra babu alamun wasa a tare da shi ya ce
“Kin san Alhaji Madu Sanusi?”
“Eh”
Ta amsa ƙasa-ƙasa gabanta na ɗan faɗuwa, aikan ta san Alhaji Madu akan farin sani, mutumen da kwana biyu, uku yana gidansu, aminin mahaifinta.
“Shekaran jiya ya yi min magana akan ki, saboda yana son ƙara aure dan ki zame masa first lady tunda sauran matansa basa jin turanci, kuma a takarar da yake akwai buƙatar ya auri mace ƴar boko, mun gama magana da shi gobe da dare zai zo ku gaisa”
Tun da ya soma maganar hawaye ke zuba a idonta har ya ƙare, daker ta iya amsawa da
“Allah ya kai mu”
Anty Amarya ta amsa da “Amin” Tana sauke ajiyar zuciya, sam bata jindaɗin yadda Abbah yake yi ma ƴarta sai dai babu yadda zata yi, ko magana ta yi cewa yake ita ke ɗaure mata gindi tana yadda take so.
Cikin sauri Namra ta taso, ta baro falon zuciyarta cike da zulumi, tana tsaron abunda zai je ya dawo, ta rasa ƙwaƙwaran dalilin da ya saka Mahaifinta ba ya son tarayyarta da Asim.
Har ta shigo ɗakinta kalmar Alhaji Madu ce take mata yawo a kunne, saman gado ta kwanta hawaye na bin fuskarta, sai ta kai hannu ta janyo wayarta, gallery ta shiga ta kamo hoton Asim tana kallo.
“Miyasa Ƙaddarata zata min haka? kin san ba zaki barni na yi soyayyah da shi cikin kwanciyar hankali ba kuma kika haɗa mu? kinsan ba zan auresa kuma kika sa na sansa, Allah kayi min mafita karka ka bar ni da kaina”
Rumgume wayarta ta yi sosai tana kuka da tuna kalaman daya faɗa mata yau a makaranta.
‘Ina son ki sosai Namra duk da jikina yana bani lallai ba zaki aure ni, saboda ni da ke ba ɗaya ba Namra, ga shi mahaifinki baya son na, Mahaifiyata tana yawan faɗa min wai zaki ɓata min lokaci ne kawai ba zaki aure ni ba, Namra ina gudun ranar da zan wayi gari kin zama matar wani magauta suyi min dariya…’
Kuka take sosai har da karkarwa, tana matsar idonta da buga ƙafafunta.
**********
Manjo Usman Zamau tsohon soja ne, mai mata biyu Hajiya Barau wanda ake kira da Mama da kuma Hajiya Larai wanda ake kira da Anty Amarya. Gidan Alhaji Usman babban gida ne mai ɗauke da part uku, part ɗin uwargidan sa da kuma na Amaryarsa sai nasa.
Uwargidansa na da ƴaƴa tara hudu mata biyar maza kuma dukansu sun yi aure, wasu suna tare da ita wasu kuma aure ya kai su nesa, a yanzu bata da ɗa ko ɗaya a gidan sai jikoki da ƴaƴan ƴan’uwa.
Anty Amarya ce aka auro daga baya, ita ce mai yara huɗu dukansu mata, Namra ce babba sai Maryam dake binta da kuma Hindatu da Aisha. cikakkancen sunan Namra shine Khadija mahaifiyarta ta kan mata Alkunya da Namra ne kasancewarta ita ta fari gareta. Namra na 100l a jami’ah ta haɗu da Asin, suka ƙula soyayyar da babu wanda ya sani har suka kai 300l, sai a yanzu ne abun ya zame musu matsala kasancewar Asim ba ɗan kowa bane face talaka mai neman abunda zai sa a bakinsa.
Ita kuma ƴar masu arziki ce musamman yanzu da Mahaifinta yake takarar Senator, daman can mutun ne mai abun hannunsa dan yana da kamfanoni da dama ciki da wajen ƙasar nan.
A duk familynsu da shi suke tinƙaho dan Allah ya yi masa rufin asiri ta ko ina.
Gashi shi ƙaɗai mahaifiyarsa ta haifa a duniya, a duk familynsu ya fi shaƙuwa da Mahaifiyar Yasmin da Kuma Mahaifiyar Uzair kasancewar kakanninsu guda, kuma yana ganinsu mata, yana tausayinsu sosai.
WANNAN KENAN
*********
SECOND FAMILY…
Tun da ta dawo daga aiki take cikin damuwa, abun duniya ya fara isarta komai ya taru ya yi mata katutu a rai, kullum ta fita ta dawo sai anyi da ita a unguwa, ƙawayenta su zolayeta familynsu ayi ta tambaya, kamar ita ta ɗorawa kanta rashin aure.
Kallon kanta take ta madubi tana hawaye, ta ko’ina Allah ya yi mata sura, mace ce abunda ake cewa mace, amman babu mai neman aurenta sai mutanen banza, duk acikin manemanta babu na ƙwarai da zata ware da sunan wanda zata aura, duk wanda ta yi ma maganar aure ba zai sake dawowa ba, sai dai su nuna suna son jikinta.
Sa’aninta duk sun yi aure, sun barta sai kace wanda ta zagi maza, tun tana sa ran idan ta gama karatu ta samu wanda zata aura yanzu ga shi har ta gama ta samu aiki amman ba shiru, ada abun ba ya damun iyayenta amman yanzu ya zame tunaninsu, suna addu’ah amman kamar basa yi, sun aurar da ƙannenta biyu mata ita shiru, babu mashinsshini balle malashi.
Faɗi tashi na neman magani babu irin wanda bata yi ba ita da iyayenta, amman ba wani labari. Yanzu kan har ta fara fidda rai daga samun mijin aure.
Kallon kanta take sosai da sosai a gaban madubi tana mamakin yadda take ƙokarin kare kanta daga zina da alfasha, tana ƙokarin sallah dare da sadaka, amman ta kasa samun mijin da zai aureta.
Hawaye ne suka zubo mata tana tuna irin yawan ƙawayenta, amman babu ko ɗaya duk sun yi aure sun barta.
Ƙarar da wayarta ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, sai ta kalli Screen ɗin wayar Salma ce rubuce a fuskar wayar, cikin sauri ta share hawayenta ta ɗauki wayar ta kara a kunne.
“Hello Salma”
“Na’am Kalsoom ya kike?”
“Lafiya ƙalau, ya Ahmad?”
“Lafiyarsa ƙalau, idan kina da time gobe ki shigo da wuri zamuje wani guri”
Da toh kawai ta amsa mata ta aje wayar, ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ko bata faɗa ba ta san ba zai wuce ta kai ta gurin wani Malamin ba, dan duk cikin ƙawayenta ita ce ta fi kowa damuwa da rashin aurenta, ita ce take ta faɗi tashi akan taga ta yi aure.
Kiran da ta ji ana mata downstairs ne yasa ta motsa ta tashi ta nufi ƙofar fita. Karo suka yi da Momy sai ta ja baya da sauri tana faɗin
“Kirana kike yi?”
“Eh yanzu mijin Zainab ya kira wai bata da lafiya tun shekaranjiya”
“Subhannallah miye same ta?”
“Wai maleria ce, amman dai na san ba zai wuce ciki ba, shine nace ki shirya gobe kije can ki yi mata ko da kwana uku ne idan ta ɗan sarara sai ki dawo”
“Haba Momy ni kuma? miyasa Saleena ba zata je ba ni fa yayarta ce kuma ace na koma can na zauna”
“Toh miye a ciki? ai ansan lalura ce ta kai ki, Saleena Exam za su fara gobe kinga ba zai yiyu ta je can ba, amman ke tunda aiki ne ai idan kin dawo sai ki ɗan taya ta aikin gidan da dafa musu abinci”
“Amman Momy ai yana da ƙanne mata kuma za a iya ɗauka mata ƴar aiki”
“Ya san da ƙannensa amman ya zo nan ya faɗa mana, idan mutum yana mutunta ya kamata kai ma ka mutun tasa, kwana uku kawai zaki yi ki dawo kin ji?”
Ta ɗaga mata kai alamar toh, zuciyarta cike da damuwa.
“Allah ya yi miki albarka”
“Amin”
Daga haka Momy ta juya ta sauka ta barta a gurin tsaye. Jinginawa Kalsoom ta yi jikin ƙofar tana addu’ah
“Ya Allah idan mijina yana nesa da ni Allah ka kusan to dashi a gare ni, idan yana kusa da ni Allah ka haɗa mu”
Juyawa tayi ta shiga ɗakinta tana cika ma bakinta iska.
***********
THERD FAMILY….
A-hankali ya ke shafa lallausar fatar jikinta da hannunsa, idonshi a lumshe yana hura mata iska a kunne, daga bisani ya fara tsosar kunnen nata hannunsa ɗaya yana saman ƙirjinta. A take ta lumshe ido tana maida numfashi, tana ƙoƙarin mayar masa da martani, hannayenta tasa cikin gashin kansa kamin ta juyo ta soma masa kiss a ƙirji, ɗayan hannunta na cikin cibiyarsa, da sauri ya kwantar da ita ya zare tawul ɗin jikinta ya soma murza fatarta bakinsa cikin nata suna maida numfashi. Ringing ɗin wayarta ne yasa ta walƙato shi cikin dabara ta dawo saman ta, sai ta yi saurin sauka tana dariya
“Am sorry Sweetheart na yi latti, ka ga har an fara kira na”
Daker ya iya ɗaga jajayen idanunsa ya kalleta yana haɗiye yawu
“No Please karki min haka Ammyn Rafiq, i need you”
Tawul ɗinta ta ɗauka ta ɗaura tana faɗin
“I need you too Babe, but there’s nothing i can do, you know how my work is”
Babu abunda zai ce mata, haka take masa time to time, ta kan hana sa haƙƙinsa saboda aikinta, idan ta dawo da dare ta ce ta gaji bachi idan kuma da safe ne ta ce zata yi latti, babu kuma yadda zai yi ya hanata aikin tun da mahaifinta ya tsaya kai da fata akan lallai sai ƴarsa ta yi aikin banki.
Yana kwance a gurin har ta yi wanka ta shirya yana kallonta, sai daf da zata fita sannan ta zo daidai kunnensa ta yi masa kiss
“Take care of yourself okay, idan Rafiq ya tashi ka shirya shi idan zaka je aiki ka aje shi kurin Hajiya, zan ɗauko shi idan na dawo, idan kuma su Ulfah sun dawo abincin su na nan a flask, love you my hubby my Doctor”
Daga haka ta fice tana murmushi, da kallon ya bita har ta fice, sannan ya ɗauke kansa yaja bargo ya lulluɓe ya soma sana’arsa.
_______________________________
Hello my beautiful people, ina fatar kuna lafiya kuma ina fatar wannan tafiyar zata muku daɗi zaku kuma bani haɗin kai kamar ko yaushe.
Wannan tafiyar ba irin wacan bace ce, ba zan baku kunya ba In’shallahu, iyana gayyartar ku a sabon shafina wanda zan riƙa zuɓa duka littafaina a can, zan riga yin update a can sama da ko’ina zaku iya samun shafuka na akan kari Just click the for your updated.
www.khadeejacandy.com.ng
Zan cigaba idan na ji ra’ayoyinku 08036126660 na gode ☺
Best regards 💖
Khadeeja Candy🌺
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa03.html
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
*PAGE – 2*
NAMRA POV.
Yadda Namra ta ga rana haka ta ga dare, dan kwana ta yi kuka da tunanin Asim, da safe ma bata fito ba sai da ta yi shirin fita, sannan ta leƙa ɗakin Anty Amarya dan gaishe ta, daga bakin ƙofa ta tsaya tana miƙa mata gaisuwar tana ɗan kare fuskarta.
“Anty Ina kwana?”
Yanayin muryarta kaɗai ya isa ya karantar Anty Amarya halin da ƴarta take ciki, daman ta san za’a rina, ko babu dalili Namra ta kan yi kuka balle yanzu da kuka ya zame mata jiki.
“Ba zan hana ki kuka ba Namra, dan kina da dalilin yinsa, amman nasan kin sauke Alƙur’ane kuma kin haddace hizo arba’in daga cikin Alƙur’ane, ashe ko ya kamata a’ce idan kin shiga damuwa ki riƙa faɗawa Allah buƙatarki kina kai kukan ki a gareshi”
Daga inda take tsaye ta amsa da
“Na gode sosai Anty In’shallahu zan yi, zan je gidan su Anty Yasmin”
“Allah ya kiyaye hanya, amman ki tabbatar kin ci abinci ka min ki je”
“Toh”
Bayan ta amsa da to ne ta juya ta fice, dinning ta nufa ta haɗa tea kaɗan ta sha, dan bata jin cin komai, ta daɗe a gurin zaune sannan ta ɗauki handbag ɗinta ta rataya ta fice daga palour, direct ta nufi gurin da Motar ta take.
Bayan ta yi addu’o’in data saba, sannan ta yi ma Motar key ta yi horn Mai gadi ya buɗe mata ta fice.
Tuƙi take kamar marar lakka, gashi zuciya ba ƙwari, sai tunane-tunane take.
Hannu ta ga ana mata gefen hanya alamar ta tsaya, tana ganin Asim ta yi saurin taka burƙi ta yi ribas ta dawo dai-dai inda ya ke ta faka, buɗe Motar tayi ta fito jiki na rawa ta ga masoyinta.
Matsowa ya yi kusa da ita yana murmushi
“Namra”
“Asim”
Haɗa baki suka yi gurin kiran sunan, sai ko wannensu ya yi shiru yana kallon ɗan’uwansa.
Da sauri Namra ta kawarda fuskarta saboda hawayen da suka cika mata ido. Hankali Asim ya tashi sosai ganin hawaye a idon Sahibarsa.
“Jiya na kira ki ya fi a ƙirga amman baki ɗaga ba, yanzu kuma ga hawaye a idonki, hakan ya tabbatar min da akwai abunda yake damunki”
Ta share hawayen da suka zubo mata.
“Babu komai, ba abunda ya ke damuna”
“Kina ɓoye min wani abu Namra, kina son tunani ya yi min yawa ko, ina tunanin halin da muke ciki, ga halin talaucin da nake ciki ga rashin aikin yi da ke damuna, Namra da wanne zan ji?”
“Faɗa maka bashi da amfani Asim, zai ƙara maka damuwa ne kawai”
“Saboda ba zan iya miki maganinsa ba ko Namra?”
“Ba haka bane, Asim zan baka wasu kuɗaɗe da zaka ja jari da su…”
Hannu ya ɗaga mata
“Tun yaushe nake faɗa miki ba dukiyar ki nake so ba Namra, ke nake so ba abunda yake cikin gidan ku, ko abunda kika mallaka, kawai ina son ki yi min alƙawari duk rintsi duk wuya ba zaki rabu da ni ba, ki min alƙawarin zaki aure ni Namra shi kawai nake so”
Kai ta girgiza masa tana wasu irin zafafan hawayen
“Ba zan iya ba Asim, ka gafarce ni ba zan iya ba…”
Dammm! Ya ji kamar an jefa masa dutse a zuciya, a take idonsa suka rine suka cika da ƙwallah, sai ya yi saurin sadda kansa ƙasa yana zauke ajiyar zuciya.
“Ashe gaskiya Umma take faɗa min, ashe yaudara ta kike ba zaki aure ni ba, amman kin ban mamaki Namra, ban tsammaci haka daga gareki ba”
Ta yi saurin kama hannunsa tana kuka
“Ba laifi na bane Asim, iyaye ne…”
Ya katsa mata tsawa
“Iyaye? Ni bana da iyayen ne Namra? Mahaifiyata bata son tarayyata da ke amman na tsaya kai da fata akan sai na aure ki, sai ke? kin fi ni sanin darajar iyayen ne ko me?”
Kasa cewa komai tayi, daman ta san ba zai fahimce ta ba, ba zai mata uzuri ba, zai zargera da da cin amana, ita kam ta san bata kyauta masa ba, sai dai babu yadda zata yi.
Hannunta ya ture, ya share hawayen da suka zubo masa ya juya a fuce ya kama hanya.
“Asim!Asim!! Asim!!!”
Haka ta bishi da kira tana kuka, amman ko waigowa bai yi ba balle ya amsa mata. Zubewa ta yi a gurin tana kuka, kukan tausayawa kanta da zuciyarta, dan ita ma kanta ta san tana son Asim, zata yaudari zuciyarta ne kawai idan har ta ce zata iya rayuwa da wani namijin da ba Asim ba.
Ta kusan minti goma shabiyar a gurin tana kuka, sannan ta buɗe Motarta ta shiga. Hanyar da zata sadata da gidansu ƙawarta Amira ta ɗauka tana wani irin gudu na fitar hankali.
Cikin ƴan mintuna ta isa gidansu Amira, daga wajen gidan ta faka motar ta dan ba zata iya jira mai gadi ya buɗe mata ba, sai ta fito ta taka da ƙafa ta shiga cikin gidan still tana kuka.
Mahaifiyar Amira ta yi mamakin ganin ta haka, sai tambayarta take lafiya, ita dai bata yarda ta faɗa mata komai ba, ta wuce ɗakin Amira kasancewar gidan ba baƙonta bane.
“Ke lafiya miya same ki?”
Amira ta tambaya cike da tashin hankali tana girgiza Namra. Bata ɓoye mata komai ba, tun daga yadda suka yi da Abbah, har abunda ya faru tsakaninta da Asim a yau.
Wani dogon tsaki Amira taja ta ɗauke hannunta daga jikinta
“Ke dan Allah duk kin tayar min da hankali, ni na ɗauka ma wani abun ne”
Kallon rashin fahimta Namra ta yi mata da idanunta da suka rine saboda kuka.
“Ban gane ba, Amira ko baki fahimci abunda na faɗa miki bane?”
“Na fahimta sarai, ai da hausa kike magana, naga dai babu wani abun tada hankali a ciki, tunda kina da mafita”
Namra ta ƙara kallonta
“Wace irin mafita? Ai nima mafitar nake nema”
“Kawai ki bishi ku gudu kuje can wani guri a ɗaura muku aure, daga baya iyayenki zasu yafe min idan suka fahimci irin son da ke tsakanin ku”
“Wannan ba mafita bace Amira, ni ba zan iya wannan ba, duk son da nakewa Asim bai kai wanda nake yi ma iyayena ba, ko wanne muhallinsa daban”
Amira ta taɓe baki
“Ashe ko ba son ƙwarai kike masa ba, tun da har ba zaki iya sadaukar da kan ki a gare shi ba”
Shiru Namra ta yi kamar mai tunani, sai kawai ta share hawayenta ta ɗauki jakarta ta rataya tana faɗin
“Bari na wuce akwai inda zanje, sai mun yi waya”
“Toh, Allah ya kiyaye hanya”
Lokuta da dama haka Amira take nata yaɓen maganar duk data zo bakinta, ta kan bata shawara tsaɓanin tunaninta, sai dai babu wanda zata faɗawa damuwarta kamar ita da Anty Yasmin.
Da wani mugun kallo Amira ta bita tana harararta, can kuma ta taɓe baki.
“Wahalalliya, ashe ƙaryar so kike tun da ba zaki iya barin iyayenki ba”
Wayarta ta jawo ta soma danne-danne, kamin ta tashi ta nufi ɗakin mahaifiyarta dan labarta mata abunda ya faru.
Har Namra ta fito daga gidan nazarin kalaman Amira take, sam bata ganin dacewa akanta guje iyayenta, saboda saurayin da zai iya barinta ya ɗauki wata, taya zata iya gudu mutanen da suka shekara ashirin da biyu suna bata gudummawa, akan saurayin da haɗuwarsu bata wuce shekara uku ba, idan har ta yi hakan ta yi babban butulci wanda ta cancanci ko wane irin sakamako. Sai dai wani ɓangare na zuciyarta, yana karantar da ita akan abunda Amira ta faɗa mata shine mafita, dan idan ba haka ba mahaifinta ba zai taɓa bari ta auri Asim ba.
Har ta isa gidan Barrister Yasmin wannan tunanin take, tana hangowa kanta illa da kuma alfanun da ke tare da ita idan har ta zaɓi guduwa ta bar iyayenta.
Ta daɗe a cikin motar tana kiran wayar Asim, amman yaƙi picking at the end ma sai ya kashe wayar gaba ɗaya, cikin rashin kuzari ta buɗe motar ta fito tana kallon balcony ɗin ƙofar Yasmin, sai a lokacin ta lura da Motoci uku da aka faka a gurin.
‘Waɗannan ba Motocin Ya Uzair bane, kar dai ace baƙin har sun iso, ko da yake abuja ba nesa bace idan sun shigo jirgi’
Shine abunda take rayawa a zuciyarta tana ƙoƙarin duba agogon hannunta, 11:23am ya bata hakan yasa ta saki jiki ta nufi ƙofar, tana isa ta kai hannu ta murɗa ƙofar. Abunda ta yi arba da shi yasa ta mutuwar tsaye, zaro ido ta yi ta rufe bakinta da sauri taja baya.
Cikin sauri Uzair ya ture Mutumen da ke samansa ya tashi ya nufi inda take, har ya iso kusa da ita jikinta rawa yake, gashi be da riga daga shi sai gudun wando. Shima hankalinsa ya tashi sosai bai tsammaci a buɗe ya bar ƙofar ba, mamakin kansa yake ma yadda bai ji buɗe gate ɗin gidan ba da fakawar Motar ta.
Da hannu ta nuna shi, sai kuma ta kasa magana. Cikin zafin hannu ya kai hannu ya cafko hannunta ya jefa ta cikin parlor.
Baya-baya tayi tana neman mafita sai kawai ta shige kitchen da samawa kanta makami, tana shiga ta nufi inda wuƙa take ta kai hannu ta ɗauka. Shi kuma ya kunno kai cikin Kitchen ɗin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.
“Ba zan miki komai ba Namra, matukar kika rufa min asiri, wallahi kuskure ne ba a son raina bane cilas ta ni suka yi”
Nuna shi ta yi da wuƙar da ke hannunta tana girgiza kai
“Ba zan rufa maka asiri ba Ya Uzair, tun da ba rufin asirin kake so ba, tun ba yau ba na taɓa ganin wani video a wayarka, Namiji na kissing ɗin Namiji ɗan’uwansa sai kace min sabon Memori ne ka siye baka san da video ba, yanzu kuma na kama ka da ido na.
Kai wane irin Namiji ne dan Allah? Matarka ta yarda da kai ta baka amana amman kana cutar, cutar ma bata tsaya akan ka har sai ka neme ni! Kuma miye abun son ga Namiji ɗan’uwanka? Tirrr da kai Ya Uzair, na yi baƙinciki da ka kasance mijin Anty Yasmi, sam bata cancanci zama matarka ba”
Murmushi ya yi ya jawo ƙofar Kitchen ɗin ya rufe.
“Na nemeki ne saboda naga abunda nake so a jikinki, lokacin da nace na aureki ai cewa kikayi kina da wanda kike so, daman nima ban shirya zama da mata biyu ba, shiyasa na nemi yin sex da ke.
Amman yanzu bari kiji na faɗa miki, duk kika kuskura kika bari maganar nan ta fita, kika faɗawa duniya cewar ni ɗan homo ne sai na tarwatsa rayuwarki, ki rubuta ki aje”
Ya faɗa mata haka fuska a ɗauri babu alamar wasa a lamarinsa, sannan ya buɗe ƙofar kitchen ɗin
“Zo ki fice, amman ki rubuta ki aje duk kika kuskura fitar da wannan maganar sai na salwanta rayuwarki”
Daga haka ya fita ya bar mata kitchen ɗin.
Ita kam bata yarda ta fito ta nan ba, sai ta buɗe ƙofar baya ta kitchen ɗin ta fita gabanta na mugun faɗuwa, har ta shiga Motarta jikinta rawa yake, zuciyarta na raya mata karta ɓoyewa ƴar’uwarta kuma aminiyarta abunda mijinta keyi, gani take idan har tayi haka bata yi mata adalci ba.
Tana fita daga gidan ta faka gefen ti-ti ta dannawa Yasmin kira, three miss call tayi mata amman bata ɗaga ba, ta san ba zai wuce tana cikin kotu ba, sai kawai ta yanke shawarar tura mata saƙo.
Ko da ta isa gida Anty Amarya bata nan, part ɗin kuma babu kowa, ƙannenta duk suna makaranta, hakan ya bata damar shiga ɗakinta ta baja kolin hajar tunaninta.
UZAIR POV.
Lokacin da Uzair ya ga Namra ta fita sai ya gargada ƴan iskan friends ɗinsa, ya gyara gidan tas kamar komai bai faru ba. Ba ayi minti Arba’in ba, sai ga Yasmin ta dawo gidan, cikin sauri ta shigo parlor tana dube-dube.
Uzair na zaune saman kujera yana kallonta, hankalinsa kwance kamar ba komai, sam be yarda ya nuna akwai wani abun a fuskarsa ba, tashi yayi ya tare ta, tare da rumgumeta yana kissing
“Lafiya wife?”
Ta sakar masa jikinta sosai
“Wallahi miss call ɗin Namra na gani da text ɗin ta, wai na yi sauri na zo gidana, shine duk hankalina ya tashi”
Dariya yayi sosai a zuciyarsa yana jinjina ƙarfin hali irin na Namra.
“Haba dai sai kace baki san Namra ba? Zata iya disgaki fa ai ba yau ta saba ba, karki tashi hankalinki”
Juyowa tayi sukayi kissing ɗin junansu sannan ta ce
“Ta katse min aiki na, ina fatar dai tayi maka kosan kazar?”
Hancinta ya laƙata
“Namra bata ma zo nan gidan ba, friends ɗina kuma har son kama hanyar Abuja daman ɗaurin aure suka zo”
Da haka ya shammace ta ya cigaba da kissing ɗinta.
NAMRA POV.
Duk yadda ta so ta labartawa Anty Amarya abunda ke cikin ranta na game da Uzair sai ta kasa, haka ta wuni tana tunanin abunda ya faru tsakaninsu da Asim, da kuma shawarar da Amira ta bata, a ɗayan ɓangaren kuma ƙwaƙwalwarta na ɗauke da hoton abunda taga Ya Uzair yayi.
Har bayan Sallah Isha’i tana kiran wayar Asim amman ya ƙi ya ɗaga, ta tura masa massage no reply, abun duniya duk ya bi ya dame ta.
Shigowar Anty Amarya ne yasa ta tsaita natsuwarta, har tana ƙoƙarin gyara zamanta.
“Abbanki yace na faɗa miki baƙonki ba zai samu zuwa ba”
Anty Amarya ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zaunawa saman gadon kusa da ita. Namra ta ɗan kalleta kaɗan
“Miyasa?”
“Nima ban sani ba, amman na naji a waya yana cewa wai kin masa ƙarama, kuma yana jin nauyinki”
Namra ta ɗan yi murmushi ƙaɗan ta kwanta jikin Anty Amarya.
“Shima dai yasan ni ba sa’arsa bace”
Anty Amarya ta shafa kan ƴarta.
“Allah dai yayi miki zaɓin da yafi alheri, ya yaye miki damuwarki”
“Amin Mamana”
KALSOOM POV.
Around eight thirty Kalsoom ta fito ɗakinta, a lokacin Saleena har ta wuce makaranta. Ita ta haɗa musu breakfast bayan ta gama, ta zuba ma Dad da Momy nasu ta ɗauka ta nufi part ɗinsu.
Bayan ta gaishe su, ta aje musu abincin tana ƙoƙarin rasowa Momy tayi mata tuni da zuwa gidan ƙanwarta Zainab.
“Ban manta ba Momy, yanzu idan na shirya can zan fara zuwa na aje kayana sannan na wuce aiki”
“Hakan yayi Allah ya kawo miki naki mijin”
Sai da ta amsa sannan ta tashi ta fice. Kala biyar ta ɗauka a maimakon uku, dan tasan sai ta fi kwana uku a can, cikin ƙaramin akwati ta saka su, sannan ta shirya kanta ta fice.
Kamar yadda ta tsara sai da ta fara biyawa gidan ta aje kayanta sannan ta wuce gurin aiki. Biyu da rabi ta tashi daga aikin direct gidansu ƙawarta Salma ta wuce.
Ta taki sa’ah, tana shiga mijinta na fita. Sai da tayi Sallah Salma ta ɗebo mata abinci ta ƙoshi sannan ta ɗauko mata zance.
“Kalsoom wani gari ne nake son muje tare da Ruƙayyah ita zata kai mu, ance malamin yana aiki sosai dan mutane da dama suna dacewa”
Kalsoom ta sauke ajiyar zuciya
“Ni wallahi har na gaji da irin wannan shige-shigen, kullum ana abu kamar ba’ayi, wani gurin ace aljanu ne wani su kuma su ce sihiri ne, na rasa gane kan matsalar nan, Wani lokacin har ji nake kamar na kashe kai na”
Salma ta dafata
“Subhanallahi, haba Kalsoom ki daina wannan maganar mana, Allah ya baki aikin da zaki iya taimakon kanki, Allah ya rufa miki asiri aure ne kawai Allah bai kawo miki ba, shine kuma kike ƙoƙarin butulce masa, kina wannan maganar sai kace ba musulma ba?”
Kalsoom ta lumshe ido ta buɗe ta kalli Salma cike da damuwa ta ce
“Salma duk abunda Allah ya ban da wanda zai ban bai kai kamar aure ba, aure shine cikar mutuncin ko wace ƴa mace, ni fa ba dotse bace Salma ina da sha’awa ina tsoron abunda zai kai ni ga halaka”
Salma ta riƙata tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali.
“Roƙon Allah baya faɗuwa ƙasa Kalsoom, komai zai zo ya wuce kamar ba’ayi ba, kuma ba asan inda rabo take ba wata ƙila mu dace”
“Ni dai ba zan sake zuwa ko ina ba, na haƙura ballantana kinsan Ruƙayya ba a sirri da ita, kuma ko munje ba wani dacewa za muyi ba, tun da babu wanda zai iya matso maka da nesa kusa, babu wanda zai iya goge abunda Allah ya rubuta maka, sai dai kawai su ci kuɗinka, na fawwalawa Allah komai daman da shi na dogara”
Duk yadda Salma ta so ta lallaɓa Kalsoom su je, sai taƙi dan ita yanzu ta riga ta sadaƙar. Sai da Yamma Kalsoom ta bar gidan Salma.
__________________________________
How about dis journey?