ZAFAFAN LITTATTAFAN HAUSA GUDA GOMA [10] NA SHEKARAR 2024
Aduk lokacin da shekara ta zo karshe, kowane sashi na rayuwar yau da gobe na kokarin tantancewa da kuma fitar da jadawalin abubuwan da suka gudana a wannan shekara da ta gabata. Ta hakan ne za a gane nasarorin da aka samu da kuma kalubale, kamar haka ne muma a fannin mu na masu karatun littattafan Hausa muke iya bakin kokarin mu wajen fitar da zakaran gwajin dafi a karshen kowace shekara.
A wannan shekara da ta gabata ta 2024 ma baza muyi kasa a gwuiwa ba wajen yin hakan kamar yanda muka saba kawo muku su a kowace karshen shekara. Zamu gabatar muku da sunayen su ne da kuma dan takaitaccen bayani kan ko wane dayansu.
Sunayen littattafan da suka zama zakaran gwajin dafi a wannan shekara ta 2024 su ne kamar haka
10. Gargadan So
9. Kazamar Amarya
8. Sanyi da Zafi
7. Kwankwason Jimina
6. Matar Mutum
5. Gudun Qaddara
4. Mayrah.
3. Aminatu
2. Karfe a Wuta
1. Tsutsar Nama
TSUTSAR NAMA :- Littafin tsutsar nama labari ne da yake Magana akan wata matashiya mai suna SAMRAT . ita dai Samrat ta fuskanci tarin qalubale a rayuwar ta wanda ya fara daga rashin iyayen su da sukayi da ita da yan uwanta guda biyu wanda sanadin hakan ne riqon su ya koma hannun kawun su, zaman su a gidan kawun na su shi ne farkon fara fuskantar qalubalen su sakamakon rashin samun riqo mai kyau daga kawun na su da iyalan shi.
Sun sha fadi tashi na rayuwa sosai kafin daga bisani Samrat ta samu hayewa zuwa mataki na biyu a tarin qalubalen da ta fuskanta wanda shi ne haduwar ta da saurayin ta na farko mai suna Mansur da sukayi karatu tare kuma har ya samu nasarar samo mata aikin gidan jaridar da ya qara zama silar jefa ta a wani matakin rayuwar. Daga qarshe dai bayan tarin wahalhalu sun samu kwanciyar hankali da ingantacciyar rayuwa.
KARFE A WUTA :- Karfe a wuta littafi ne da yake dauke da labari mai sarkakiya kan wani Al’amin wanda ya kasance qasurgumin dan ta’adda a lokaci daya kuma ya kasance babban jami’in tsaro da yake ba qasar shi gudummuwa wanda rayuwar shi ya fuskanci kyara da tsangwama a hannun mahaifin shi sakamakon shu’umar mace da Allah ya hada mahaifin na shi da ita, hakan shi yayi silar jefa rayuwar shi cikin garari wanda sai da Allah ya hada shi da mace ta gari mai suna Jauhar sannan ya samu saukin kunci.
Sun yi rayuwa da jauhar na dan takaitaccen lokaci kafin rasuwar ta wanda sanadiyyar rasuwar ta ne qaddara ta qara hada shi da yar uwar tagwaitakar ta wadda bai taba sanin su yan biyu bane har matar shi ta bar duniya. Yar uwar jauhar mai suna Nabila ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar mijin yar uwar ta da bata taba sanin tana da itaba har ta bar duniya wanda daga bisani ta auri mijin yar uwar ta ta bayan gwagwarmaya da tasha ta hanyar bashi kariya a kan laifin da ake zargin shi wanda bai aikata ba.
AMINATU :- littafin Aminatu labari ne da yayi duba kan irin gwagwarmayar da masu sana’ar haqar ma’adanai suke sha da kuma irin rashin imanin da son duniya ke kawo ma wasu mutanen, ita Aminatu diya ce ga daya daga cikin wanda wannan sana’a ta say a samu abin duniya sosai wanda shi ma ya fuskanci matsaloli sakamakon dukiyar da ya tara har hakan yayi mishi sanadiyyar da ya rasa matar shi wato mahaifiyar Aminatu.
Rayuwar AMINATU diyar Aminatu rayuwa ce da taso cike da gata da sangarta a hannun yayan mahaifiyar ta kafin daga baya ta hadu da masoyin ta Haroon wanda sai a ranar daurin auren su qaddarar ta ta juye da auren dan uwan shi Jamal sakamakon hadarin da ya samu ya rasa ranshi sanadiyyar hakan, rayuwar Aminatu ta sauya zuwa wani bigiren da tayi ta fuskantar barazana da wahalhalu kafin daga bisani ta samu daidaito cikin rayuwar ta ta da farin ciki tare da kwanciyar hankali.
MAYRAH :- Mayrah labari ne kan wata yarinya da aka tsince ta takuma samu kyakykyawan riqo a hannun mariqanta har sai da ta girma ta samu mijin aure kafin wata diyar qanwar mariqiyar ta ta tona asirin cewar ita yar tsintuwa ce sakamakon ita wadda ta tona din tana son wanda zai auri Mayrah. Bayan Mayrah ta fahimci ita wacece sai ta fita duniya neman danginta inda acan ta hadu da yayar mahaifiyar ta amma ita Mayrah bata san wacece ita ba.
Mayrah ta dawo hannun mariqanta bayan ta nemi iyayen ta bata samu ba sai daga baya ita yayar mahaifiyar ta ta zo inda ake riqon Mayrah har ta bayyana mata asalin ta da danginta
.
GUDUN QADDARA :- Hausawa suka ce gudun qaddara….guzurin tadda ta, wannan gaskiya ne domin kamar haka ne yayi ta faruwa a cikin littafin gudun qaddara na yar mutan Huguma. Hajiya Hamdiyya Abdu diya ga shaharraren dan kasuwa a qasar Najeriya da Nijar kuma Mata ga Alhaji Hamid dan gidan Bibi ta yi ta qoqarin katange kanta da ahalin ta daga wata qaddara wadda a lokacin da take haqilo na ganin ta daqile afkuwar wannan abu, sai qaddarar faruwar shi ta gaggauto musu cikin yanayin da basu taba tsammata ba wanda hakan ya haifar da rudani mai tsananin gaske kafin daga qarshe aka samu maslahar da ta wanzar da zaman lafiya da jin dadin cikin ahalin baki daya.
MATAR MUTUM :- Littafin Matar Mutum ya tabo bangarori da daman a rayuwar yau da kullum a gidajen malam bahaushe.
Akwai rayuwar Audu bechi tun daga yarintar shi da kasancewar shi mutuum mai zafin nema da nasibi har zuwa girman shi inda ya auri mata dayawa cikin su hada wadda ta zama qaddarar rayuwar shi kasancewar ta gwana a tuggu da iya makirci, inda ta shiga ta fita sai da ta tabbatar da ta lalata rayuwar gida Audu bechi gaba daya ta hanyar hana shi gudanar da adalci atsakanin iyalan shi wanda hakan ya kawo rarrabuwar kawuna a gidan kuma kowa ya taso baya jin qaunar dan uwanshi cikin ranshi ganin kamar ana Fifita rayuwar wasu a gidan.
Akwai rayuwar Fatima [Afeeyah] wadda cikin rashin sani tayi soyayya da yayan Audu bechi guda biyu a lokaci daya wato Ahmad da qanin shi mafi soyuwa a gurin shi wato Jafar, kasancewar ance matar mutum kabarin shi, Fatima ta aurin Ahmad sukayi rayuwa ta tsawon shekaru kafin ya rasu kuma ta auri Jafar shi ma kuma suka rayu tare da yayan da ta Haifa da ahmad da kuma jafar din gaba daya.
KWANKWASON JIMINA :- Kwankwason jimina Hausawa sukace mai wuyar shafawa, labarin wata yarinya mai zuciyar manya wadda ta tsaya kai da fata gurin ganin an bi ma kisan da akayi ma iyayen ta da yayan ta haqqinsu wanda sakamakon jajircewar ta da kokarin ta yasa aka tabbatar da hukunci akan wanda suka ma baban ta da maman ta kisan gilla ba tare da sun aikata wani laifi ba. daga gefe kuma akwai Anees wanda ya fada a makauniyyar soyayya da Nawrah wadda bata ma san yanayi ba domin ta riga tayi zurfi a soyayyar abokin sa Marwan sai daga baya qaddara ta juya har Anees ya samu damar auren Nawrah suka shimfida soyayyar su mai cike da tsafta da kaunar juna.
SANYI DA ZAFI :- Littafin Sanyi da Zafi labari ne da ya zaqulo wani babban qalubalen da mutane masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki suke fuskanta a cikin alumma, sai kuma sakamakon da masu kyakykyawar muamala da mutane ke samu kamar yanda Rashida ta yi wanda har ya kai ta ga auren yarima mai jiran gado da ya zama sarki daga baya, gefe daya kuma akwai jajircewa da ita wannan Rashida tayi gurin ganin ta kula da kanta da kuma mahaifiyar ta wadda ta hadu da qaddarar samun cuta mai karya garkuwar jiki.
KAZAMAR AMARYA :- Kazamar Amarya wani dan gajeren labari ne da aka kirkire shi domin ya zama izina ga mazan da bas u daukar matan su na cikin gida da daraja, Hamid yana auren matar shi ta rufin asiri said ai kullum cikin korafi yake baya ganin kokarin da take yin a kula da shi da dangin shi har sai da yaje ya dauko kara da kiyashi da yake ma hangen dala wanda bai san ba shiga birni bane har sai da ta shigo gidan ta fara gasa mishi aya a hannun shi kafin ya shiga taitayin shi ya nemi yafiyar uwar yayan shi.
GARGADAN SO :- Gargadan so labari ne kan wata mata mai suna Hauwa wadda ta hadu da jarabawar jinkirin aure wato bata samu mijin aure da wuri ba hakan kuma ya sa ta fuskanci qalubale mai yawa kafin daga baya Allah ya tarfa ma garin ta nono ta hadu da Khalil dan gidan wani attajiri da ya kasance da daya tilo a gurin mahaifan shi, mahakurci kullum shi yake zama mawadaci domin kuwa, Hauwa ta samu kyakykywar rayuwa a gidan mijinta Khalil sukayin rayuwar su cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
KAMMALAWA
Zafafa goma suna zaqulowa ne cikin dubban littattafan da marubuta suka samu damar rubutawa a shekara domin fitar da zakaran gwajin dafi saboda a kara ma marubuta himma da hobbasa domin su qara dagewa da maida hankalin su suna rubuta abinda makaranta za su qaru, su kuma kura domin amfanin makaranta da marubutan gaba daya.
Naji dadin karanta wannan labarin, kuma muna godiya