ʙɪsᴍɪʟʟᴀʜ
ᴘᴀɢᴇ 1✦5
Bai dai_dai parking ɗin ba ya fita motar da sauri kai tsaya babban palorn gidan ya nufa yana kiran’ Ammi Ammi am back to home..
Wata ƴar matashiyar mata ce wacce bazata gaza 45 years ba ta fito ta ce” oh ni Sadeeq sai kace makaho da zaka dinga ƙwalamin kiran nan haba”
Shagwaɓe fuska ya yi ya ce”Ammi nifa yinwa na ke ji yakama ta abani abinci na”..
Ammi ta ce” wai daman saboda abinci ne ka ke kirana haka to nagaji da wannan kiran ka zo kai aure nima na huta”.
Ya tsani yaji ance masa ya yi aure bai ce komi ba ya nufi bedroom ɗin sa bathroom ya shiga ya na mai watsa ruwa akan shi fitowa ya yi daure da tawol sai ƙarami a hannun shi yana goge kan shi…
“Mama kinga yanzu idan muka fara warar nan sai kiga ana samu ba kaɗan ba cewar matashiyar yarinya”
Mama ta ce”a’a hameeda kawai ki cigaba da zuwa gidan aiki na kada ki fara warar”..
Ƴar kwalla ce ta zubomata ta ce indai shine farin cikin ki zanyi hakan in sha Allah..
Yauwa “hameeda na Allah dai ya taimake mu, ya zaɓa maki miji nagari kiyi aure ki huta”!
Kuɗi ta bata ₦100 ce garin kwaki na hamsin sai sugar ta 30 gyada amaro ta 20 jiƙawa masu tai suka ci ita da mama, share gidan tai fes tai wanke wanke ta ta ɗauki Qur’ani tana karanta wa cikin murya mai daɗin sauraro..
Tunda safe 7:30 ta gama komi mama ce ta tara ka ta gidan aikin ta domin ta cigaba da yi a madadin ta, su na isa gidan mai gadi ya buɗe masu ƙaramar kofar saboda ya gane ita ce mai aikin hajiya gaisawa suka yi palon masu aiki suka nufa inda ta ce ai mata iso da hajiya kusan minti 30 sannan ta fito duƙawa sukai suna gaida ta ta ce” lafiya dai na ganku ku biyu”?
Kallon ta mama tai ta ce” hajiya yanzu yarinya ta ce zata cigaba da yi a matsayi na idan badamuwa”
Murmushi tai tare da faɗin au haba ai badamuwa ai ko baki faɗamin ba zata iya cigaba da yi, hakan ba komi bane..
Nan mama ta barta don ta fara aikin falon Hajiya ta nufa domin nan ne da sashen Sadeeq take gyarawa sai abincin sa domin ya fi son girkin [ maman hameeda ] palon ta gyara ta nufi sashen Sadeeq domin ta gyara yana gida bai fita ba tura kofar part ɗin nashi tai daidai lokacin yana zaune a 2sita yana latsa waya saurin komawa tai tai noking ya ce” ki shigo mana zaki dame Ni da noking”..
A sanya ye ta shiga ta ce” ina kwana ɗan laɓai”