RAYUWA DA GIƁI Batul Mamman💖 Bismillahir Rahmanir Rahim _In loving memory of Aisha Aminu Balbalo (mai lalurar numfashi da take sayen cylinder ɗin oxygen wadda aka fi sani da Carofee). Allah Ya jiƙanta Ya gafarta mata. Amin_ *** Wanki take a tsakar gida tana sauraron hirar mahaifiyarta da ƙanwarta Zee. Ba ta saka musu baki saboda tun ainihinta ba mai son hayaniya bace. Sai murmushi kawai idan sun yi abin dariya. "Wannan wankin naki zai sami shanya kuwa Hamdi?" Sararin samaniyar da Yaya ta kalla ita da Zee su ka zuba wa ido. Ga dai rana ana gani tana haska ko ina. Amma idan mutum ya miƙar da ganinsa zai yi tozali da baƙin hadarin da yake ta gangami daga nesa. Tunanin taƙaita wankin ta soma yi yadda wanda ta gama za su sami wuri akan ƙofofin ɗakunan gidan su ka ji sallamar wasu mata. Da farinciki Yaya ta tashi daga kan tabarmar da take zaune ta nufi zaure tana cangala ƙafarta ta hagu wadda shan inna (polio) ya cinye. Da alama baƙin da aka kwana aka wuni ana zancen zuwansu ne su ka ƙaraso. "Maraba lale da Altine." Shewar Yaya da baƙuwar su ka ji daga zauren da taje ta taro su kafin su dawo tsakar gidan hannun da baƙuwar a kafaɗarta. "Oh ni jikar mutum huɗu. Ashe rai kan ga rai Jinjin? Ya bayan rabuwa?" Matar ta jero mata tambayoyi su na daga tsaye. "Sai alkhairi. Rayuwar nan sai godiyar Allah." Su ka sake rungumar juna su na dariya. Ƴan matan da baƙuwar tasu mai suna Altine ta zo dasu da kuma Hamdi da Zee sai su ka tsaya kallon abin al'ajabi. Labaran da su ke ji game da juna ashe gaskiya ne don ga zahiri sun gani. Iyayen nasu sun yi zumunci sosai kafin a haifesu lokacin suna zaman Agege a Lagos. Abubuwa da dama sun faru waɗanda su ka yi sanadiyar dawowar su Jinjin garin haihuwarsu Kano. Ƙarancin hanyoyin sadarwa da faɗi tashin yau da gobe ya dakusar da wannan zumunta ta makwabtakar gidan haya ɗaya. Shekara bakwai kenan da dawowar su Altine Kano su ma amma basu taɓa haɗuwa ba sai da Allah Ya haɗa mazansu da wani da ya san duk su biyun. A wurinsa su ka sami labari harma da lambobin wayar juna. Altine kakkaurar mata ce mai fara'a kamar gonar auduga. Mijinta Maje mahauci ne yana sana'arsa ta fawa. Da yake kakanninsu ɗaya duk su na da billensu na gadon sana'ar a kuncinsu. Akwai ta da kazar kazar don in tana abu sai ka rantse wannan jikin ba nata bane. Da wannan yanayin nata ta ja Jinjin a jiki duk da farkon zuwanta saboda yanayin mijinta da lalurarta bata sakewa da kowa. A gidan nasu na iyali goma sha biyu ƴan ka zo na zo aka taso ta a gaba da tsokana. Don ma maigidan nata ba ƙyalle bane. Bakinsa kaɗai ya ishe su ƙwatar kai. Idan ya fita ne dai ko banɗaki ta fito zagawa an dinga dariyar tafiyarta kenan. Sai da Altine ta gama lura da ita ta gane tsoron ƴan gidan da su ke duk hausawa take yi. Sai ta zame mata baki harma da hannuwa. Don idan abin bawa hammata iska ya kama dukan tsiya take yiwa mace la'ada waje. Ɗan Altine ɗaya lokacin ita kuma Jinjin da ciki su ka rabu. "Ina Baballe kuwa?" Cewar Yaya cikin yanayi na kewa. Da jindaɗi Altine wadda ƴaƴanta su ke kira Iyaa (kamar yadda Yarbawa su ke jan sunan) ta bata amsa. "Ya tafi bautar ƙasa Binuwe (Benue)" "Allah Sarki. Shekara kwana. Yaron da na tafi na bari yana tatata" Dariya su ka yi farinciki da jindaɗinsu ba zai kwatantu ba. Duk wannan abin da su ke yi Hamdi da babbar cikin ƴan matan Iyaa kallon gane juna su ke yi. Ganewa mai cike da tsoro da fargaba a ɓangaren kowacce bisa dalilai daban daban. Kamar iyayen sun sani kuwa su ka zaɓi wannan lokacin wurin gabatarwa juna ƴaƴan nasu. "Kina nufin da cikin Hamdi ku ka taho?" "A'a, yayarsu dai Sajida. Tsiranta da Hamdi ma ya kai shekara biyar. Bata nan ne. Ta tafi Abuja gidan ƴar yayata da ta haihu." Iyaa ta murmusa "Allah Sarki" ta nuna babbar ƴar "Sajidan ce sakuwar Ummi kenan, don baku jima da tafiya ba na haifeta." Yayinda Yaya take da ƴaƴa huɗu, Sajida, Hamdiyya, Zinatu (Zee) da Halifa, na Altine uku ne. Baballe, Ummi da Siyama. Sai da su ka nutsu da gaishe gaishen Yaya ta aiki Zee. "Maza jeki gidan Lami ki ce ta baki lemukan da na bata ajiya." Ta yiwa Iyaa bayanin sace musu transformer da aka yi kusan wata uku babu wuta sannan ta fuskanci Hamdi "ke kuma ki je wajen babanku ki faɗa masa Altinen Maje ta iso." Iyaa ta sanar da ita ai babansu Ummi na sauke su a ƙofar gidan ya yi waya da maigidan nata. "Ina jin ya kwatanta masa wurin sana'ar tasa don ya ce can zai je sai su taho tare." Cigaba da hirarsu su ka yi wanda hakan ya bawa Ummi damar yiwa Hamdi inkiya da su tashi tana son magana da ita. Ita kuwa sai ta ɗauke kai kamar bata gani ba. Hakan ya tunzura Ummi matuƙa sai kawai ta miƙe tsaye ta ce tana son shiga banɗaki. Hamdi na jin haka ta san kwanan zancen. Cikin ɗakinsu ta gayyato ta ba don ta so ba. Duk da gidansu mai tsakar gida ne amma kowanne ɗaki da banɗakinsa a ciki. Wannan tsarin babansu ne da ya ce baya so ace komai dare, ruwa ko iska sai an fito tsakar gida idan za a zaga. Shigarsu ɗakin ke da wuya Ummi ta juyo fuskarta a murtuke. "Zan faɗawa Iyaa makarantarmu ɗaya amma kada ki kuskura ƙaiƙayin baki yasa ki faɗawa kowa sirrin rayuwata a makaranta" "To" ta iya cewa don hankalinta a tashe yake. Yau ruwa ya ƙarewa ɗan kada. Sirrin ɓoye zai fito fili. Rai a ɓace Ummi ta bangaji kwalarta yadda ta saba cin zalin ƴaƴan mutane a makaranta. "Bar ganin nan gidanku ne kin dai san an kusa komawa makaranta. Kin kuma san ko ni wace ce ba sai an faɗa miki ba." Ficewa kawai Hamdi tayi daga ɗakin wani abu na hawa da sauka a ƙirjinta. Barazanar Ummi ba ita bace damuwarta kamar yadda zuwanta gidan yake nufin tonuwar asirinta. Gudun rana irin wannan da wata ƴar makarantarsu za ta zo gidansu yasa ta zaɓi makarantar kwana. A can ɗin ma bata da ƙwaƙƙwarar ƙawa ko ɗaya. Tsakaninta da kowa mutumcin gaisuwa ne da kuma taimakon da take yi musu na ƙarin haske akan karatu. Allah Ya yi mata baiwar ɗaukar darasi da zarar an koyar. Bata taɓa tsallake matakin ukun farko ba tun shigarta. Sau biyu makaranta na neman iyayenta domin a karramata a gabansu tana daƙilewa. Na farko ta ce mahaifinta ya yi tafiya. Na biyu kuma ta ce yana kwance tun kafin ta taho ya yi hatsari ya karye. Da taga alamun za a bishi gida gayyatar Yaya ta nuna ai maman ke jinyarsa. Malamin ajinsu da kansa ya gane akwai abin da take ɓoyewa sai ya sanar da hukuma kada a matsa mata. Sun riga sun saba ganin abubuwa marasa daɗi game da dangin ɗalibai. Tunda dai ba karatu aka hanata ba sannan duk dawowa daga hutu da kuɗin makarantarta take zuwa ya ce a ƙyaleta kawai. Daga lokacin sai dai idan an yi taron ta taho da kyautarta gida. Bata tsoron duniya ta ga lalurar Yaya amma mahaifinta da shi ya ɗorawa kansa bata son ana alaƙanta su a waje. Sau tari ita da ƴan uwanta su kan zauna su kwashewa wanda ya haɗa auren mamansu da mutum irin mahaifinsu duk kirkinsa albarka. Fitowarta tayi daidai da dawowar Zee. Ta ajiye ledar hannunta ta tafi ɗauko tray za ta ɗora musu. Sai ga Ummi ta fito ta dubi Hamdi tana murmushi kamar gaske. "Don Allah ba ke ce Hamdiyya Habib ta Rumfa Hostel ba?" Murmushin dole Hamdi tayi ganin iyayen nasu sun dawo da hankali garesu. "Ni ce. Kema kamar na gane ki." "Ummi ce, Ummi Maje. A 'F class' nake shi yasa ba lallai ki sanni ba." Iyaa ta hau murmushi wanda kuma da wuri ya koma shan kunu da ta gane me hakan yake nufi. "Kin dai ji kunya wallahi. Karatu kamar cin ƙwan makauniya. Ƙanwar bayanki ma ajinku ɗaya?" Ta gyara zama ta yiwa Yaya ƙarin bayanin asalin daƙiƙanci irin na Ummi wanda ya janyo ake ta yi mata repeating. Wannan shekarar ma don an riga an saka ranarta ne babansu ya roƙi alfarma aka kaita aji shida saboda ta gama a aurar da ita. Basu san rashin ƙoƙari ba shi kaɗai ne matsalarta ba kamar yadda Hamdi ta sani. Idan kana neman irin ɗaliban nan da ko bayan shekara ashirin in ka tambayi abokan karatunsu game dasu sai dai su bi su da 'Allah Ya isa' ko ka ji ana cewa 'a dai yi shiru' idan mutum ya riga ya mutu to Ummi Maje ce. Bully ce lamba ɗaya! * Lokaci guda rana ta ɗauke, hadarin ya sake duhu ga iska mai ƙarfi tana kaɗawa. Babu shiri hirar ta koma cikin falo. Zee ta ƙarasa shanya wa Hamdi kayanta ita kuma ta shiga kitchen ta haɗa salad bisa umarnin Yaya. Abu ɗaya hakan yake nufi. Abbansu yana tafe da abinci kuma tabbas a yau Ummi za ta sami makamin cutar da ita. A baya ko kallo basu ishi juna ba tunda duk jarabar mutum dole ya haƙura indai Hamdi ce. Bata shiga sabgar kowa balle a kai ga yin faɗa da ita. Tsananin faɗuwar gaban da taji lokacin da aka yi sallama daga zauren gidan yasa ta sharɓe hannu wurin yankan albasa. Yayyafin da aka soma bai hana kowa jin sallamar mace ba. Yaya da Iyaa su ka amsa da fara'a yayinda Ummi ta ƙagu ta ga wace baƙuwar akayi mai zaƙin murya haka. "Za mu shigo da Alh. Maje" su ka ji muryar ta faɗi. Sai kuma dariya ta biyo baya inda Baba Maje yake cewa "ai ka rigani indai amsa sunan Alhaji ne." Kan Ummi da Siyama ya ɗaure. Zee kuwa duk abinta na rashin damuwa yaƙe ta kama yi da taga yanayin fuskokinsu. A kitchen kuma numfashin Hamdi ya kusa ɗaukewa da Yaya tayi musu izinin shigowa. Abbansu ne a gaba. Sanye yake da jallabiya yana tafe jiki na rangaji irin na riƙaƙƙun mata. Ga hula zanna bukar da ta ɗan sha jiki ya kafa a karkace. Shigarsa dai da ta sani ta yau da gobe. A bayansa wani mutum ne mai jiki wanda da alama shi ne baban su Ummi. Suna shiga falon ta leƙa ta tagar kitchen ta hango yadda yake magana yana tafa hannuwan mamaki yadda mata su ke yi harda riƙe haɓa. "Altine kece haka? Ikon Allah." Ya zauna a kujerar kusa da matarsa. "Gaskiya rabuwar zumunci bata yi ba ko kaɗan." Fuskar Iyaa wasai ta amsa gaisuwarsa sannan ta mannawa yaran nata harara. Ba shiri kowacce ta miƙa gaisuwa da girmamawar dole. Ga mamaki ƙarara bayyane a fuskokinsu. Namiji har namiji Ummi ta ayyana a ranta. Dogo ne don sai yau ta raina tsayin babanta. Jikinsa babu rama amma yadda yake karairaya shi yasa babu mai cewa jikin namiji ne da ya amsa sunansa. Fatar nan dabbara dabbara alamun an sha bleaching a shekarun baya. Yana buɗe baki kuwa haƙoran Makka ne na azurfa a sama har biyu suna maraba da baƙi. "Kan uban can...ƊANDAUDU ne?" Ta yiwa kanta tambayar a zuci ba don tana neman ƙarin bayani akan zahirin da idanuwanta su ke gani ba. Abba kuwa da zafin nama ya fita shigo da kulolin abinci ita kuma gwanar ta ɗauko ƴar wayarta tamkar mai duba wani abu ta soma yi masa hoto a fakaice. Sautin wayar ma a silent ta saka don kada kowa ya gane. Siyama ce kaɗai ta kula kuma a take jikinta ya yi sanyi don ta sani babu ko tantama irin murmushin fuskar yayarta a lokacin na nufin abin da take yi ba na alkhairi bane. RAYUWA DA GIƁI 2 Batul Mamman💖 Banda hotuna har sautin muryarsa Ummi ta ɗauka daidai inda yake kiran Hamdi ta kawo salad. Tana jin kiran ba amma saboda tsoron yanayin da za ta tarar da fuskar Ummi na farincikin samun lagonta sai ta kasa amsawa. "Abba bari na kira ta." Zee ta miƙe tsaye. "Matso mu su da plates bari naje." Tashi ya yi ya tattare gefen jallabiyarsa ya riƙe da hannu ɗaya ya fita. Ya samu ta gama haɗa komai ta lulluɓe da clig (farar leda ta rufe abinci) kamar yadda ya koya mu su. Haɗin ya yi kyau gwanin ban sha'awa. Ya murmusa cikin jindaɗi yana ɗaukan tray ɗin. Ko ƙanƙani bai san wani abu girman kai ba musamman a tare da iyalinsa. "Allah Ya yi albarka Hamdi. Mu je a ci abinci." Jingina tayi da sink ta juya masa baya kamar wani abu za ta wanke ta gyaɗa kai. Amsawa da baki zai iya ankarar dashi kukan dake barazanar ɓalle mata. Shi kuwa kamar ya sani ya ajiye tray ɗin ya juyo da kafaɗunta. "Hamdi?" Ai suna haɗa ido sai kawai ta fashe da kuka. Zuciyarta tamkar ta fashe saboda baƙincikin da take ji. Wani abu mai masifar ɗaci ya dinga kai komo a cikin ƙirjinta. Duk gidan tana da yaƙinin tafi kowa takaicin fita tsatson bawan Allahn nan. Ranta yana ƙyamarsa. Albarkacin karatun addini yasa ta daina danganta shi da munanan kalmomi da fata a zuci kamar yadda take yi a baya. Asalin da mutane ke tutiya dashi Yaya ta janyo sun rasa ta da haifesu tare da tubabben Ɗandaudu. Mutumin da har yau idan aka yi rashin sa'ar gamuwa da tsofaffin abokansa sai kaji ana kiransa Simagade. Hankalinsa tashi yayi da ganin hawayenta ya dinga tambayarta damuwarta. Da bata ce komai ba ya yi yunƙurin rungumeta domin rarrashi amma sai ta banƙare jiki ta ja baya. Dama can ta saba yi masa haka don shi tarairayar yara sai dai wani ya koya a wurinsa. Na yau ne da ya sanya masa shakku tunda ya san ta kan bari sai dai ta zare jiki da wuri. Kallon tuhuma ya bita da shi sai ta wayance ta ɗago hannun da ta yanke ta nuna masa. "Ya Salam" ya ce da ƙaramar muryarsa "Sannu. Jeki falo ki jira ni." Tray ɗin salad ɗin ya ajiye ya fita cikin ruwan nan mai ƙarfi ya shiga ɗakinsa. Haƙƙin iyaye da a kullum shi ne jigon dake hanata fito masa da zahirin abin da take ji game da shi yasa ta ɗauki tray ɗin. Idonta da na Ummi su ka haɗu taga abin da take gudu muraran a tare da ita. Jikinta ya sake yin sanyi. Sallamar Abba ta dawo da ita duniyar mutane. Ya zauna akan hannun kujera ya ce ta kawo hannunta. Ɗan akwati gare shi irin na gidan ƴan boko da ya adana magunguna da kayan taimakon gaggawa. Ya umarci Zee da zubawa kowa abinci shi kuma ya zauna bawa ƴarsa kulawa. Spirit ya dangwala a jikin auduga ya goge ciwon. Ga azabar zafi saboda ba ƙaramar yanka bace amma ko uhumm ta kasa cewa. Allah Ya sani zafin da take ji a zuciyarta yafi raɗaɗin ciwon. Saboda yadda ta ƙyamaci rayuwar mahaifinta bata ƙaunar gabaɗaya abokan sana'arsa. A son ranta namiji ko ruwan zafi aka ce ya dafa ya dawo ya ce ya ƙone saboda rashin iyawa. Namiji mai shiga kitchen ba zai taɓa yi mata kwarjini ba balle har taga ƙimarsa. Dressing sosai ya yi mata ya kawo auduga ya ɗora ya manne ta da plaster. Gwani ne sosai ta wannan fannin wurin son ganin komai ya tafi daidai kamar wani bature. Ire iren abubuwan nan harda Abban da yasa su ke kiransa kamar ba talakawa ba duk bata so. Cikakken namiji bahaushe a wajenta ai Baba ake kiransa ba wani iyayin Abba ko Daddy ba. Kowa sannu yake mata tana amsawa da ka. Da kuma wannan damar ta samu ta gudu ɗaki ta kwanta. Ba ita ta sake fitowa ba har sai da baƙin su ka tafi bayan Iyaa da su Ummi sun leƙo sun mata sallama. *** "This is crazy Taj. Waye yake tattara duka ƙwansa ya sanya a kwando guda?" Wata kamilalliyar dattijuwa sanye da doguwar rigar bacci da ƴar hula ta furta da takaici. Huci take cikin ɓacin rai tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune yana murmushi kamar abin da take faɗi da wani take a talabijin ba shi ba. "Tajuddin!" Ta kira shi da ƙarfi da gargaɗi. "Yes Ma" ya miƙe tsaye gami da sara mata. Ta sake tamke fuska. Shi ma da alama ya gama shirin bacci ne don wandon jikinsa three quarter da singileti basu yi kama da kayan mai shirin fita ba. "Ina wasa da kai ne?" Ya girgiza kai. Abin da ta san za ta yi ya dawo da hankalinsa gareta yadda take so ta aikata. "Ko don kaga ba ni na haifeka ba? Shi yasa ban isa..." "Amma gorin haihuwa kuma za ki min. Has it realy come to that?" Ya yi ƙwalƙwal da ido. Jikin Amma a take ya yi sanyi. Taj ya yi wani ɗan banzan murmushi a bayan idonta sannan ya cigaba da magana. "Idan baki aminta da abin da nake so ba ai ina ganin ba sai kin tuna min cewa ni ba ɗanki bane." "Ba haka nake nufi ba. Kai ma ka sani." Marairaice mata fuska ya yi sosai ta yadda ya san hankalinta zai tashi. Ya kuwa yi nasara don faɗan da ta ɗauko da gaske sai ya koma laluma. "Taj bana son kayi abin da zai zama ganganci. Bayan duk irin abubuwan da ka jure a baya kada wannan step ɗin ya bada ƙofar da za a yi maka dariya." "Amma da Happiness mu ke komai. Mun yi survey na yadda malls su ke saurin dakushewa..." "Durƙushewa dai ko?" Ta ci gyaransa ba tare da ta ɓoye takaicinta ba. "Yeah, durƙushewa. So after the survey mun gano wasu reasons da suke kawo failure na business ɗin." Zama tayi bayan ta gama sauraronsa tayi ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa take guje masa wanda idan ba ɗan fito dasu tayi ba da wuya ya gane inda ta dosa. "Shekararka nawa a ƙasar nan Taj?" "10 years" ya amsa kai tsaye. "And for those years you have been working non-stop kana tara kuɗi. Cikin ikon Allah kuma ka sami nasarar cin gasar nan ka sami maƙudan kuɗaɗe da sponsorship. Sai kawai na yarda da shawarar gina ƙaton mall irin wannan lokaci ɗaya da duka kuɗin? Kai baka hango ganganci a cikin yin haka ba?" Ta nuna zanen ƙayataccen ginin da yake kan laptop ɗinsa wanda nuna mata da ya yi ne ya kawo rigimar. Marairaice fuska yayi "Tafiya ce ba kya so nayi ko Amma? Nayi miki alƙawarin zama har ki yi ritaya." "Bani da son kan da zan yi amfani da gudun zaman kaɗaici na daƙile maka rayuwa." Bakinta kawai ya kalla ya yi murmushi. Wata hausar idan ta ɗauko duk nacinsa sai ya tsinci kansa da rashin ganewa. Laptop ɗin ya rufe ya fuskanceta. "Yanzu me kike so nayi?" "Ka fara da restaurant ɗin mana. Idan kaga riba sai ayi planning for expansion." Tana gama magana ya sake buɗe laptop ɗin ya nuna mata sakamakon bincikensu. Tabbas akwai ƴan kasuwa da yawa a Kano. Tada ginin mall ba wani abu bane a wajensu. Kuma yana samun karɓuwa sosai. Ayi ta tururuwa ana zuwa. To amma fa bayan lokaci ƙanƙani yawanci da wuya ka sami motoci biyu sun ziyarci wurin. Wasu ma kayansu har ƙura su ke suna expiring saboda rashin zuwa. Da wannan su ka haɗa bayanai wurin yin abin da ya saɓawa wanda mutanen su ka saba dashi. "Kinga na farko zamu yi shi a wurin da bai yi nisa da talaka da mai kuɗi ba." Bata ce komai ba. Ya ƙura mata ido sai ta gyaɗa kai don ya cigaba. "Dole zamu dinga canjawa with current trend. Idan ban yi shi da girma ba chanjin zai dinga bani wahala. Maybe wani ya saye space ɗin kusa dani in rasa hanyar expansion. Sannan yin babba da zan iya bada hayar shops for diverse businesses zai taimaka. Idan mutum bai je don cin abinci ba maybe yaje wurin tailors, grocery shopping, wasan yara and the likes." Taƙaita masa bayanin tayi ta hanyar nuna masa ta gane. Yana son yi mall mai ɗauke da shaguna daban daban amma na brands da suka yi suna. A haka nasa ɓangaren wato wurin abinci ko bai yi kasuwa sosai ba zai dinga samun kuɗin haya daga waɗanda suke ciki. Burinsa talaka da maikuɗi kowa ya ɗanɗana ababen more rayuwa a ƙasarsa cikin jindaɗi. Goyon baya ta bashi amma ta yi masa hannunka mai sanda akan tsoron da take ji da kuma ƴan gyare gyare. "Kamal jininka ne. Kuma na san irin shaƙuwar dake tsakaninku. Amma kada ka manta mutane irinmu da yawa living in diaspora (ƙasar waje) muna fuskantar matsala guda. Sai mu tura kuɗi gida domin wani aiki musamman gini. Idan mun koma mu tarar babu aikin babu kuɗi. Kuma family su nuna basu yarda muyi ƙarar wanda ya cucemu ba." Da rashin jindaɗi ya ce "Amma Happiness ne fa." "Shi ɗin fa. Ka tafi gida ayi komai a gabanka. Sayen fili, kafa foundation da dukkan wani abu da ya dace ka sani. Daga cikin abubuwan da su ke durƙusar da business harda rashin kulawar wanda ya samar da shi. An bar komai a hannun ma'aikata. Sai abu ya lalace a zo ana complain." Sai kuma ta bashi shawarar maimakon mall ita dai tafi son ya yi ƙaton restaurant tunda da girki ya yi fice. Idan an gina sai ya ware wurin wasan yara domin janyo mutane. A ɓangare guda ya yi wurin da masu gashin nama ko tsire zasu iya haya. Da kuma inda masu kayan fulawa kamar cake da su meatpie zasu yi nasu. Maimakon mall indai akwai wurin da aka keɓe domin yara to fa tabbas iyaye za su zo. A ƙarshe ta ce ya tabbatar wurin an yi shi yadda zai burge mai kuɗi sannan bai yiwa talaka tsadar zuwa ba. Sosai yaji daɗin shawararta. Ya ce zai sa a sake yi masa wani zanen. Amma fa dole zai samarwa Happiness wurin da zai kafa nasa shagon. Addu'a tayi masa da fatan Allah Ya ɗorar da zumuncinsu shi da yayan nasa. Sai da su ka tabbatar sun daddale komai ya ce, "Ni fa nafi son mu tafi tare." "Ya kamata kaje gida uwayenka su ganka haka nan." Tashi tayi ta juya masa baya amma bata tafi ba. "Tajuddin ka sani cewa if your intension is not honourable (idan niyarka ba mai kyau bace). Ina nufin in kana son fara business ɗin nan ne kawai domin ka nunawa Yaya Hayatu cewa kayi nasara duk da yadda ya nuna ƙiyayyar sana'arka, to lallai Allah zai kunyataka. Domin Ya karrama darajar iyaye. Saɓanin fahimta da rashin goyon baya daga garesu ba dalili bane da zai sa mu nuna musu raini." "Korata fa ya yi" jijiyar kansa da idanu su ka firfito a lokacin da yake maganar. "Shi kuma Allah Ya zaɓa maka a matsayin uban. Ya kuma rayata haƙoƙin junanku a kan ku. Idan ya take nasa kada ka kuskura kayi nufin binsa da ƙulli. Wallahi duk wahalarka ta shekarun nan sai ta tashi a banza." "Amma..." "Ka tsaftace niyarka Taj. Everything will just fall into place. Goodnight" Juyowa tayi ta sumbaci goshinsa sannan ta ɗauki wayarta ta shige ɗaki ta bar shi a tsaye yana kai gwauro da mari. Maganarta a kullum umarni ce a gareshi. Ta san yana yi mata biyayya gwargwadon iyawarsa. Me yasa bayan tsayin lokacin nan don zai tsaya da ƙafarsa za ta ce ya tafi gida? RAYUWA DA GIƁI 3 Batul Mamman💖 Masu tambaya littafin ba na kuɗi bane. *** Auren Habibu da Jinjin ba na son zuciya bane kamar yadda ƴaƴansu suke hasashe. Yar mahaifinsu da suka fi ɗorawa alhakin saboda sunanta da Zee tace wato Anti Zinatu ma ba laifinta bane. Abu ne na karamci da sanin darajar wanda ya kiyaye taka darajar. Aure ne na zumunci domin kuwa kamar yadda Iyaa da Baba Maje suka fito daga zuri'a ɗaya su ma iyayensu mata shaƙiƙan juna ne. Mahaifiyar Habibu ita ce babba. Tayi aure a Kano da ƴaƴanta maza uku da mata biyu. Shi ne na biyu. Ita kuwa mahaifiyar Jinjin a garinsu Ɓatagarawa dake Katsina tayi aure. Bata sami haihuwar ba da wuri sai akanta. Ta haifota kyakkawa mai kama da dangin mahaifiyar. Idan ka ganta da ƴaƴan Inna Batulu za ka rantse ita ta haife su duka. Sunanta Khadija amma ake kirantan Jinjin (jinjinniya don ƙauna). Soyayya da gata gwargwadon hali ta taso tana gani wurin uwa da uba kafin Allah Ya jarabceta da cutar shan inna tana da shekara biyu da rabi. Lokacin da iyayen su ka farga ƙafar ta mutu ba ƙaramar damuwa su ka shiga ba. Idan tana tafiya kafaɗa da ɓangaren ƙirjinta na dama sai ya ballaƙo waje. Wannan abu ya tsayawa uban a rai. Har ta kai indai yana wajen da ta miƙe zai ce, "Don ubanki koma ki zauna. Kina faman tafiya kamar wata tsuntsuwa babu kyan gani." Ko ya ce "wannan da ma ciwon tafiya ya yi dake kika huta. Meye haka don Allah?" Da bata da wayo uwar ke kuka idan yana wannan rashin albarkar. Ƙarshe ma yayi aure shi da matar da lafiyayyun ƴaƴan da su ka haifa su ka taru su ka mayar da rayuwar Jinjin ƙuntatacciya. Yanzu ita ke kukan uwar na rarrashi. Watarana Inna Batulu ta kawo musu ziyara ta tarar da ƴaƴan kishiyar ƙanwarta suna dukan Jinjin. Abin takaici uwarsu da ƙanwar na kusa amma wai kawaici ya hana ta ƙwaci ƴarta. Garin cangala ƙafa ta kifar da garin masarar tuwon dare. Kuma gudu ma take saboda an biyota za a ci zali. Inna Batulu na gani tayi kukan kura ta damƙo yaran nan su uku ta bi kowa ta feffela musu mari. Ta ƙare musu zagi irin nasu na Katsinawa. "Banda raini ba yayarku bace?" Ta juya ga ƙanwarta "shiga ki haɗo min kayanta yanzu zan wuce da ita tunda ba kya so." "Ba haka bane Yaya." Da takaici takalleta "kunyar marasa kunya asara ce Luba. Gidan nan kaf har mijin naki ban ga wanda ya dace ki ragawa akan kyautar da Allah Ya yi miki ba." Jijjiga Jinjin tayi a gabanta ta ƙara da cewa "don bala'in gidan nan ƴar shekara goma sha uku ji ƙirjinta kamar anyi daɓen siminti." "Kai Yaya Talatu?" "Allah kuwa. Zuwa yanzu ai yaci ace an fara ganin..." Da ɗan gudunta Jinjin ta bar wajen don bata son ƙarasa jin hirar iyayen. Kamar wasa maigidan na dawowa Inna Batulu ta sauke masa nashi kwandon masifar ta ce kuma jiransa take a bata ƴa. "Gata nan har abada da gaban abada na bar miki." Ya furta ko ajikinsa. Luba sam bata ji daɗi ba amma haka ta shirya mata kaya su ka tafi. Bata da wani farinciki ko nishaɗi a gidan idan ba Jinjin take gani ba. Da ita take hira tunda miji ya juya mata baya. Sauƙinta ɗaya ta san cewa yanzu za ta sami ƴanci ta wataya kamar sauran yara. A Kano tabbas taga gata da soyayyar da tasa har take manta da nakasar dake tare da ita. Inna Batulu da maigidanta harma da yaransu sun mayar da ita ƴar gata. Matsala guda ta kula akwai a gidan ita ce ta yayanta Habibu. Lokacin yarintarsu tana iya tuna shi da yawan wasa da dariya. Yanzu kuwa kullum iyayensa cikin kukan sabuwar ɗabi'arsa suke yi. Shi ne tafiya yana rangwaɗa da karairaya jiki kamar mata. Ga uwa uba muryarsa da bata san ya aka yi ta motse ba. Idan ya yi magana sai ka rantse wata budurwar ce. Duk wasu take taken daudanci yake nunawa. Indai zai yi sallama a gidan daga su Inna Batulu har ƴan uwansa basu da nutsuwa. A yau da take da kusan wata biyu a gidan sallamar wata matashi suka ji a gaggauce. Babu kowa a gidan sai Jinjin da ta dawo daga makarantar islamiyya. Fita tayi ko kaya bata cire ba ta sami wani mutum da bata sani ba. Da gani magidanci ne ya sha shadda wagambari da ɓakar ɗara a ka. "Inna Batulu ko Baba nake nema" ya ce kafin ta gaishe shi. "Duk basa nan." Kallonta ya sake yi ya tuna sun taba shiga gidansu wurin iyayensa da Inna Batulu tace ƴarta ce daga Ɓatagarawa. Shi yasa kawai ya faɗa mata abin da ya kawo shi. "Ki ce musu Habibu na gani a gidan abincin wasu ƴan daudu yana girki a kasuwa." Rasa abin cewa tayi don fuskar mutumin tayi nuni da matsanancin ɓacin ran da ganin hakan ya janyo masa. "Kin fahimci abin da nace kuwa?" "Eh, zan faɗa musu in sha Allahu." Juyawa ya yi babu sallama zai tafi ta tambaye shi wa za ta ce musu. "Hayatun gidan Alh. Sule." Sunan da taji bayan tafiyarsa ya dawo mata da hirar da ta taɓa tsinkaya daga mutan gidan. Akwai gidan wani mai kuɗi nan kusa dasu wanda aka ce ɗansu Hayatu ya ɗauki Habibu tamkar cikinsu ɗaya. Saboda ladabi da ƙoƙarinsa a shekarun baya ya kasance duk wata lalurar karatunsa Hayatu ya ɗaukarwa kansa. Irin abin nan na maikuɗi ya cicciɓi talaka domin inganta masa rayuwa. Ance da Habibun ya fara canja akalar rayuwa Hayatu ya shiga ɓacin rai sosai. A son sa yaron ya ginu ya zama mutum amma kullum ana yi masa faɗa yana daɗa kangarewa. Me za ayi da namiji mai girki a ƙasar hausa? Har dukansa taji ya taɓa yi watarana da ya ganshi da ɗaurin zani a ƙirji ya fita. A ƙarshe ya ce masa zai iya tsaya masa ya koyi girkin harma ya mayar dashi sana'a amma sai ya ajiye duk wani abu da yake kamanceceniya da mata. To Habibu dai ana faɗa ta kunnen dama zancen na ficewa ta hagu. Da Inna Batulu ta dawo ta sanar da ita sai da tayi kuka. Shi yasa ba a son zama unguwa ɗaya da wanda ake ganin zai iya jan ra'ayin yaran unguwa. Daga yawan aikensa siyan abinci a wurin wasu ƴan daudu dake bakin titi ita dai bata san yadda aka yi ya dinga rikiɗewa ya koma wannan Habibun na gabansu ba. Ranar anyi masa faɗa sosai. Baba ya zage ya yi masa dukan mutuwa. Garin Allah na wayewa aka neme shi aka rasa. Wurin wata uku ana nema kafin daga bisani su sami labarin ya tafi Saudiya da wani ubangidansa. Sana'ar abinci su ke yi a can ɗin. Akwai abubuwa da kan sami bawa ya rasa silarsu. Ka haifi ɗa kayi masa duk iyakar ƙoƙari amma idan ƙaddara ta faɗa masa kana ji kana gani zai zaɓi hanyar ta bata ɓullewa. Irin haka ta sami Habibun Inna Batulu. Dangi su ka sanyo su a gaba da yawan magana da famin ciwo. Wasu in sun sami zuwa ƙasa mai tsarki a unguwar su yi ta kawo labaran yadda aka ganshi ya ɗashe saboda shafe shafe. Zantuka barkatai harda wanda ya ce wai an faɗa masa ya yi aure da wani ɗan daudu irinsa. Zancen da ya tayar da hankalin Baba fiye da kowanne kenan. Ya sayar da gonarsa da wani gidan haya ya haɗa kuɗi a shekarar ya tafi Hajji. Bai wani sha wahala ba aka sada shi da gidan da Simagade yake haya da abokan sana'arsa. Lokacin shekararsa tara baya gida. Jinjin ta gama sakandire har ta fara sana'ar kitso a gida tunda aure ya gagara. Ta kai matakin da kowane iri tana son samu saboda yadda mahaifinta ke jifanta da maganganu idan taje gida. Baba fashewa yayi da kuka da yaga ɗan nasa sanye da jallabiya ya ɗora zani da ɗankwali. Ga haƙoran Makka har biyu. Tamkar ba a Jidda ba suna ta ƙazaman zage zage shi da wani da suke faɗa. Ganin mahaifinsa ne ya sagar masa da gwiwa ya yi shiru. Sai hankalin kowa ya kai kan tsohon dake zubar da hawaye. "Shiga ka sako kaya ka zo ka rakani masallaci." Ba Habibu ba hatta abokan zamansa duk jikkuna sun yi sanyi. Ya shiga ciki ya samo aron wasu pakistan na maza ya saka. Ya fito tafiyar nan babu dama ne. Masallaci mafi kusa Baba ya shiga dashi. Ya umarce shi da yin sallah raka'a biyu sannan ya fuskance shi bayan sun idar. "Saboda ka taka dokar Allah Habibu yau alwala da sallarka ma in ni nake karɓa ba za su bar rufin masallacin nan ba zan jeho maka kayarka." Kai ya sunkuyar cike da kunyar kansa. "Daga wannan rana ba zan sake yi maka faɗa ko nasiha ba. Zan kuma roƙi Batulu da kada mu sake zubar da hawaye a kanka. Na barka da duniyar da ka zaɓa wadda nan da kwanaki kaɗan za ta daina yayinka. Idan tayi maka rawar ƴan mata ina jin za ka yi hankali har ma kayi tunanin dawowa gida. In na mutu tun yanzu ka sani na yafe maka. In kana da rabon shiriya ka zo gida kafin baƙincikinka yayi ajalin mahaifiyarka." Yana gama faɗin haka ya tashi. Habibu zai bi shi ya ce baya so. Haka ya koma ya gama kwanakin da su ka rage ya dawo gida. Habibu kuwa komai ya daina yi masa daɗi. Nadama mai raɗaɗi ta shiga ɗawainiya dashi. Ana gama kwaso mahajjata ya tattara komatsansa ya dawo gida. Bai fi wata biyu ba Baba ya kama cuta har ya cika. Yayi kuka kuwa kamar ba gobe. A gefe guda yana godiya ga Allah da Ys bashi damar dawowa. Tun daga lokacin ya soma neman gyara rayuwarsa. Sai dai kuma jama'a da dama suna gagarar yiwa mai laifi uzuri ko ya tuba. Da yake har yanzu in ba jallabiyar nan ya saka ba sai yaji kamar yayi tsirara, amma yana bakin ƙoƙarinsa wurin yin abin maza. Matsalar dai an bar kari tun ran tubani. Murya ta gama shaƙewa. Karairaya ta zame masa jiki duk da ya rage. Ya yi ta neman aikin yi ya rasa. In ya kasa kayan sayarwa irinsu kayan miya babu mai saye. Har wurin Hayatu yaje amma yaƙi taimaka masa ya zama yaron shago kamar yadda ya nema. Allah Ya ɗora masa ƙyamar ƴan daudu sosai. Da ya rasa yadda zai yi ne ya roƙi Inna Batulu ta yarje masa tafiya Lagos sayar da abinci. Ya tabbata a can da babu wanda ya san shi kuma girki ba a ɗauke shi sana'ar mata kaɗai ba zai sami sauƙi. "Idan ka tafi Habibu ina jin tsoron kada ka koma ruwa. Gashi nayi imanin babu mai baka mata ka aura a halin da kake ciki." Ta goge hawaye. "Ki yafe min Inna. Na san na cuci kaina amma nayi miki alƙawarin ba zan komawa waccan rayuwa ba." Duk zancensu a kunnen Jinjin. Kafin tafiyarsu ta sake jin maganar ana yi tsakaninsa da ƴan uwansu. Ta kula Inna tana cikin damuwa. Barinsa babu abin yi matsala ne. Sannan zuwansa shi kaɗai akwai haɗari. Bayan dogon nazari irin na yarinta ta nemi izinin zuwa gida ta shawarta da mahaifiyarta. Luba ƴar halak ko mijinta bata bi ta kansa ba ta sako ƴarta a gaba su ka taho Kano. A gaban ƴaƴan gidan da mahaifiyarsu ta ce ga amana ta sake damƙa musu. "Jinjin miskiniya ce na sani. Ban sani ba ko bawa Habibu ita zai zama gwaninta ko abin ɓacin rai a gareku." "Allah Ya kiyaye Gwaggo Luba" cewar yayar Habibu tana taya Inna Batulu kuka don ta kasa magana. Sun yiwa uwa da ƴar godiya kamar su ari baki. A wata guda aka yi komai aka gama su ka koma Lagos da zama. Rayuwar ta fara daɗi Allah Ya karɓi ran Innarsa. Shi ne dalilin dawowarsu kuma ya kasa komawa. Habibu yana ƙaunar ƴaƴansa kamar rai. Yafi kowa sanin akwai lokutan da basa son nuna shi. Shiyasa ya kan kame daga zaƙe musu don kada ya ɓata rawarsa da tsalle. Matarsa Jinjin kuwa duk duniya baya haɗata da komai. Shi ya sani cewa tayi masa alfarmar da da ace ana auren ƙanwa ko ya nasa ba za su taɓa aurensa yana ɗan daudu ba. ** Alh. Hayatu Sule Maitakalmi mashahurin ɗan kasuwa ne a Kantin Kwari. Takalma dai na mata da maza daga shagunansa an gama magana. Karansa ya kai tsaiko a kasuwanci. Sunansa ya zaga duk inda ya dace a dama da shi. Mutumin cikin ƙwaryar Kano ne daga unguwar Soron ɗinki. Yana da kirki da ƙoƙarin cicciɓa na ƙasa da shi sai dai akwai tsatstsauran ra'ayi kuma baya tanƙwaruwa. Duk wanda ya san shi ya san kaifi ɗaya ne kamar bakin wuƙa. Matansa huɗu kuma duk a gida ɗaya suke. Ƙaton gini ne na masu kuɗin da wanda yake yawan shan gyara domin ya tadda zamani. Ainihin gidan akwai ƙaton falo wanda in an shiga da ƙofofi huɗu a jere a ɓangaren dama. Kowacce in ka shiga falo ne babba da banɗaki da kuma ɗakuna biyu. Nan me ɗakunan matansa. Bangon dake kallon ɗakunan kuwa kitchen ne makeke da store sai ɗakin masu aiki dake haɗe da banɗaki. A jikin bangon tsakiya ne da matattakalar bene inda ɗakin maigidan yake da falonsa. Sai kuma ɗakuna biyu na ƴan mata suma kowanne da banɗaki duk a saman. Sai an fita daga bayan ainihin ginin ne kuma za a tarar da ɓangaren samari. Ta gaba kuma aka jona ginin falo da banɗaki inda yake ganawa da baƙinsa. Duka gidan ƴaƴa ashirin da takwas ne kuma a ciki biyar ne kaɗai maza. Sai ƴaƴan ƴan uwa da yake riƙo da ƙannensa. Shi yasa kullum gidan yake a cike. Uwargidansa ta lalle Haj. Gambo da ake kira Hajiya kaɗai tana da goma. Ta biyun Mama A'i tana da uku. Sai Umma Jamila mai takwas. Sannan amarya Inna Abu mai shida. Ya taɓa sakin mace ɗaya wadda ta kasance ta uku a jerin aurensa. Ɗa ɗaya ta haifa kuma shi ne babban namiji a gidan mai suna Ahmad. Da fitina ta zo shi kuma ba zai lamunta ba. Tun yana lallaɓawa da yaga za ta wargaza masa tsari ya sallameta ya bawa Mama ɗan. Tun daga lokacin babu wadda ta sake gigin tayar masa da hankali. Zaman lafiya ake da ƙullewar zumunci. Har ta kai idan mace ta haihu wani zubin ɗan cikinta ma sai ya yi mata ƙyuya saboda kulawar da yake samu a wajen yayyensa da sauran matan. Irin rayuwar nan ta daga ni sai ƴaƴana bata da muhalli kwatakwata a gidan Alh. Hayatu. Bayan Ahmad an ɗauki lokaci kafin a sake samun ɗa namiji. Don a haihuwa ta tara Hajiya ta haifi Kamaluddin. Yana da wata biyar Inna ta haifi Tajuddin. Bayansa tayi mata biyu sannan ta ƙara da maza biyu Sulaiman (Abba) da Bishir sai ta rufe da mace kuma autar gidan. Wannan yasa mazan su ka tashi a ƙarƙashin yayunsu mata tunda sun zo a sahun ƙarshe ƙarshe. Kamal da Taj sun tashi tamkar ƴan biyu sakamakon rashin tazarar haihuwarsu. Wasu har basa gane su don hatta pant duk mai sayawa ɗaya za ta sai wa ɗayan. Bambancinsu da aka fi ganewa shi ne doguwar fuskar Taj da gashin fulanin Kamal wanda su ka gado daga uwayensu. Da yake jinin Alhajin akwai ƙarfi duk inda ƴaƴansa su ke basa ɓoyuwa. Musamman da cikakkiyar girarsu da ta zama wani sirri na ƙarin kyawunsu. Mama uwar riƙon Ahmad ita ce maman mazan gidan. Duk abin da ya shafesu ita ce a kai tun ana goyonsu. Ita take yayesu shikenan yaro ya koma ɗakinta. Za a iya cewa Taj da Kamal wasu manyan jigo ne na farincikin gidan Alhaji. Indai suna gida to in sha Allahu dariya da nishaɗi baya yankewa. Zolaya da wasa duk halinsu ne. Har suna su ka sanyawa juna. Kamal ya kira Taj Happy, shi kuma Taj ya kira shi Happiness. Irin faɗan nan na sakonni da wuya kaga sun yi. Sannan daga yayyensu har ƙanne ba za ka ji wanda ya kai ƙararsu akan sun masa ba daidai ba. Duk kuwa da kasancewar Taj mai tsokana lamba ɗaya. To amma yana da tsoron yin laifin da za a hukunta shi. Shi kuwa Kamal dama green snake ne. Sai ya yi abu ya koma gefe kamar ba shi ba. Tun tasowarsu akwai wata irin shaƙuwa ta musamman tsakanin Alhaji da Taj. Shi dai da zarar mahaifinsu ya dawo to ya gama wasu wasanni. Yana daga cikin lokutan da akan gansu wuri daban daban shi da Kamal. A gefensa yake zama yana yi masa tambayoyi musamman akan kasuwanci. Nan da nan ya zama sunansa abokan harkokin Alhajin su ka fi sani. Kowa ya buɗe baki sai ya ce Taj. Har dai aka fara hannunka mai sanda a gidan ana cewa da alama shi zai gaji Alhajin. Yawan maganar yasa Inna ta fara jin abin yana damunta. Bata son rigima ta ɓullo daga ɓangarenta. Shi yasa wata rana su na zaune su biyu da Alhajin ta tayar masa da zancen. "To ke banda abin ki mene ne a ciki? Duk uba ai yana son magaji a fannin da ya yi zarra musamman idan halattacce ne." Wasa taga ya mayar da zancen ta girgiza kai. "Kaga yana da yayye. Idan ana cewa magajinka wani zai yi zaton irin abin nan ne na son ture wasu don wata manufa." Kallonta ya yi yaga sosai ta shiga damuwa. "Ku mata sai a barku. Tunaninku kullum babu nisa. Musulunci dai ya riga ya gama mana komai. Yau ko dama na kwanta yadda shari'a ta tsara haka za a raba abin da na bari a bawa ƴaƴana. Babu wani fifiko." "Na sani" "Amma duk da haka kina damuwa saboda kada a ce Hayatu ya fifita ɗanki akan na sauran. Ƙila ma kina ƙarawa da cewa za a zargi ko don mahaifiyarki ƙanwar mahaifina ce." "A'a wallahi" ta ce da sauri. Ya sake yin murmushi sannan ya ɗan tuna mata baya. A gidansu cikin maza su goma sha uku shi kaɗai ne ɗan kasuwa kamar baban su. Sauran duk aikin gwamnati su ke yi. Shi kuwa ya ajiye kwalin tun daga degree na farko ya rungumi sana'ar gidan ba tare da an tauye ƴan uwansa da komai ba. Duk abin da ya tara yanzu arziƙinsa ne na guminsa. Ya ma zamana duka ƴan uwan nasa duk wanda ɗansa namiji ya gama sakandire sai ya tura masa shi kasuwa na shekara ɗaya. A haka yanzu akwai mutum bakwai cikin ƴaƴansu da su ke jikinsa. "Zan yi maganin damuwar nan anjima idan an zo cin abincin dare." Bai manta ba kuwa. Dama al'adar gidan idan ba baƙi gare shi ba duka tare ake cin abinci a babban falo. Ƴan shekaru kusa da juna ake haɗawa a kwano guda. Matansa ma yawanci tare su ke ci. Ana gamawa yaran za su nufe shi da buƙatunsu. Ko fensir ne ya karye sun fi gane su sanar dashi. Yana daga zaune zai sa a bashi reza don yafi gane mata ya fiƙe. Wasu ya koya musu homework. Masu buƙatar kuɗi ko wani abu makamancin haka duk a wannan zaman ake yi. Ana gamawa zai ja su sallar Isha sannan ya tashi. Su kuma daga nan za su ɓalle da hira. Ƙananun da duk mai ra'ayi su tarkata su koma wurin Hajiya indai ba girkinta bane domin jin daɗaɗan tatsuniyoyi. "Mal. Bishir wai me ka ke son zama ne idan ka girma?" Bishir ya ɗago kai daga rubutun da yake yi na homework ya kalli baban nasu. "Shoe shiner." Falon gabaɗaya aka bushe da dariya harda Alhajin. Shekarar Bishir bakwai a lokacin. Kuka ya soma yi yana cewa "Alhaji kaga suna yi min dariya ko?" "Rabu dasu. Tambayar ma ta saraya a kanka sai ka ƙara girma. Duk wanda ya sake dariya kuma bana bashi da takalmin sallah. Dama kai zan bawa ka raba." Da haka ya kawo ƙarshen kukan nasa. Ya mayar da tambayar ka ga Abba. "Babana fa?" Murmushi ya yi "Alhaji ni police zan zama." "Ni dai bana son khaki Abba. Don Allah ka zaɓi aikin da ba zai dinga hana ni bacci mai daɗi ba" cewar Mama. Alh. Hayatu ya ce a ƙyale yara a bisu da addu'a. "Taj kuma fa?" Abin nema ya samu. Kowa ya zuba masa ido ana jiran a ji ya ce kasuwanci irin na baban nasa sai ya basu mugun mamaki. "Chef! Mai girki." Ya ce hankali kwance yana murmushi. Da yake yafi kusa da Umma a inda yake zaune bata san ma lokacin da ta buge bakinsa ba saboda wani hargitsatsen kallo da Alhaji ya watsa masa. "Bar dukansa Jamila. Barshi ya maimaita." Ko ɗar bai ji ba ya sake faɗin abin da ya ce da ƙwarin gwiwa. "Chef. Mai dafa abinci a restau..." "TAJUDDIN!!!" Tsawar ta gigita kowa. Ƴar autarsu ma kuka ta saka harda zubar da abincin da aka ajiye a gabanta tana ci da kanta. "Ku tashi ku bani wuri." Ya faɗa a fusace. Da yake a lokacin sun kai shekara sha huɗu shi da Kamal duk da hankalinsu. Shi yasa Taj ya gane abin da ya faɗa bai sami karɓuwa ba. Bin sahun ƴan uwansa ya yi ya tashi. "Ina za ka? Zama zaka yi ka faɗa min me ya burge ka da daudanci har kake tunanin kawo min wannan shaiɗancin cikin gida." A tsorace ya zauna yana kallo kowa ya tashi har iyayensu mata. Alhaji ya ɗan sausauta murya don ji yake kamar ya fara duka akan ɗan da yake matuƙar danne soyayyarsa. Ya tambaye shi ko ya taɓa yin girki a rayuwarsa. "Abincin da aka gama ci yanzu ma ni nayi miya. Wallahi Alhaji na iya girki sosai. Indai babu islamiyya ni nake na dare." Sai da ya cije leɓe don wani irin sarawa kansa ya yi sannan ya ce "kirawo min uwayenka ka ce su same ni a ɗaki." *** A ɗakin Hajiya su ka tare su huɗu ashe suna ta caccakar Mama. Musamman Umma wadda ta jima da hango ɓacin rana a dalilin wannan abu. "Na sha faɗa miki ki hana yaron nan shiga kitchen ki ka ƙi. Tun ana ɓare maggi har ta kai yana ɗora sanwar gidan nan." Mama da karayar murya ta ce "saboda Allah yanzu a ce mutum yana da yaro amma ba zai koya masa ayyukan cikin gida ba? Girki ai ba lallai sai mace ba. Kuma ra'ayinsa ne tunda duk yadda su ke da Kamal shi ko magin baya ɓarewa." Hajiya ta ce "Amma tun farko kin san Alhaji yaƙi jinin ganin mazan gidan nan da tsintsiya ma balle girki. Yana gani yake cewa a daina saka su kada su zama ƴan daudu. Ko kin manta tashin hankalin da aka taɓa yi akan gugar kuɓewa?" Wata rana ne kusan shekara uku da su ka wuce mai aikinsu ta fita bata dawo da wuri ba. Girkin Hajiya ne ita ma sun fita dubiya dukkansu. Suna dawowa taga ba'ayi tuwon dare ba. Shi ne ta rabawa Ahmad, Kamal da Taj gugar kuɓewa ita kuma da taimakon yan matan gidan ta ɗora tuwo. Alhaji da ya shigo yaga suna aikin nan a falo ya dinga faɗa ba ji ba gani. Sai da ya yi sati baya cin abincin gidan yana kuma gargadi da tuna musu aikin namiji da mace a gida ba ɗaya bane. Mama ta ɗan kalli Inna da tayi shiru kawai tana kallonsu. "Ki ce wani abu mana. Ko kema laifina kike gani?" "Laifi kamar yaya? Neman mafita kawai zamu yi kafin ya tasa mu a gaba don na san..." Laluben ɗakin da Taj ya ɗaga da sallama ya katse mata magana. "Alhaji yana kiranku a samansa." Hajiya kiransa tayi ganin jikinsa duk ya yi sanyi. "Girki ko a gidanka kana da damar yi Taj amma kada ka sake cewa za ka zama mai abinci ko daɗin ji babu. Duk wani namiji mai sana'ar abinci ɗan daudu ne. Su kuwa Allah baya son su tunda sun zaɓi jinsi kishiyar wanda ya basu." Kai ya gyaɗa kawai ya fice. Sanin cewa zai haɗu da Ahmad da Kamal kuma lallai ba za su goyi bayansa ba sai ya gudu ɗakin Inna. Wuri ya samu ya kwanta ya rufe idanunsa yana tunani. Kasuwanci da yake nacin koyo a wurin Alhaji ba don komai bane sai don yana da muradin buɗe gidan abincin da yake son ya yi suna. A rayuwarsa babu inda yake shiga yaji kamar an sabunta masa duniya kamar kitchen. Kuma a iya saninsa maza da yawa su na girki. Suna da shekara goma Alhaji ke kai yara Umra. Idan mutum ya yi shabiyar a kai shi Hajji. A Saudiyya in ka cire Takaru babu inda ya ga mata suna sayar da wani abu na ci. Maza ke girkawa su sayar. Maza musulmai magidanta waɗanda basu da wata siffa da duk hangen mutum zai danganta su da mata. Idan sana'ar haramtacciya ce ga namiji da waɗannan basu kai labari ba. Shi kam yana son girki kuma in Allah Ya so ita ce sana'ar da zai yi. A ɗakin Alhaji kuwa faɗansa har falon ƙasa. Don ma ƴaƴan kowa ya shige ɗaki. Manyan sun haɗe kawunansu da ƙananan a ɗakunan iyayensu a ƙasa. Ya fusata sosai don ko da su ka shiga ɗakin maganinsa na hawan jini yake sha. "Ni za ku ha'inta? Girkin nan ba yau ya fara ba tunda ya ce shi ya yi miyar dare. Ace ko sau ɗaya idanuna basu taɓa gani ba. Abin da mamaki." Mama ce ta fara bada haƙuri "na bari ne kawai saboda ganin yawanci gidajen da su ke da yara maza duk ana koya musu girki. Hakan bai sa sun yi koyi da ɗabi'un mata ba." Cikin faɗa ya ce mata gidansa babu maza da yawa. A cikin mata ashirin da uku a rasa me yin girki sai maza? Shi yasa yake sanya ido sosai saboda idan ya yi sake tabbas mazan za su iya jin cewa kwaikwayon yayyensu mata ba laifi bane. Ko ɗankwali ya gani a hannun ɗansa ya dinga faɗa kenan. "Da irin wannan sakacin wani yaro a unguwarmu ana ji ana gani wallahi ya zama cikakken ɗan daudu. Gidansu akwai mazan ma amma daga sai ga Habibu ya koma Simagade a unguwa." Gashi dai faɗa yake yi amma faɗin wannan suna sai da ya sanya Hajiya da Mama yin ƴar dariya. Umma da Inna dai a murmushi su ka tsaya. Ai kuwa sun janyowa kawunansu sabon faɗa. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Musamman Mama da a yau tayi nadamar amsa sunan uwar maza a gidan. "Dole ki yi dariya mana tunda ba ɗanki bane. Da alamu da gangan ma ki ka nemi ɓata min rayuwar yaro saboda baki san daɗin haihuwar namiji ba." Ba ita da ya yiwa gori ba, dukkaninsu hankulansu tashi su ka yi. Mama ta saka kuka, Umma da Inna su na taya ta. Hajiya kuwa fiƙe idanu tayi ta ɗauki ragamar girmanta. "A'a fa Alhaji. Akan ƴaƴanka ba za mu lamunci irin wannan ba. Kai ka koya mana zama da juna. Tunda mu ka kai yanzu kuwa wallahi ba za mu yarda ka haddasa mana rigimar da bamu yi da ƙuruciya ba." "Ba akan ƴaƴana za ki ce ba. Ki fito fili ki faɗa min cewa akan Taj ba za ku yi min biyayya ba." Ya dubi Inna ya cigaba da sababi "wato sai da ki ka ga lamari ya lalace sannan ki ka ankarar dani riƙon sakainar kashin da ake yiwa ɗana don kawai ana ƙyashin kusanci na da shi." "Na shiga uku. Alhaji yaushe mu ka yi haka?" Ta faɗi a ɗimauce ganin ƴan uwanta sun zuba mata ido. Shi a ganinsa babu dalilin da zai sa taji wani ɗar a zuciyarta. Ya riga ya santa da kawaici saboda haka don ana yabon ɗanta a tunaninsa bai isa dalilin maganarsu ta ɗazu ba. Tabbas ganin rayuwarsa ta ɗauko hanyar gurɓacewa a hannun uwar riƙonsa shi yasa tayi magana. Su Hajiya ficewa su ka yi aka rasa mai tambayarta abin da ya faru ma. Tana kuka ta tashi za ta bisu domin kwance wannan ɗauri da maigidan ya yi mata ya hanata fita. Dama girkinta ne. Sai kawai ya ce idan ta fita daga ɗakin ba da yawunsa ba. RAYUWA DA GIƁI 4 Batul Mamman💖 *** Manyan gidan a wannan rana basu ga bambancin dare da wuni ba. Kusan babu wanda ya runtsa tsakanin maigidan da matansa. Abin da yake faruwa baƙo ne a wurinsu. Basu saba da rigima ba sai gashi dare ɗaya ana gab da samun gagarumar ɓaraka. Ita dai Inna daga sallar asuba ta fake da ɗora kunun karin kumallo ta sauko. Bata zame ko ina ba sai ɗakin Mama. Akan sallaya ta sameta idanu sun kumbure. Jikinta a mace ta fita ta kira Umma da Hajiya su ka dawo ɗakin tare. Kai a ƙasa ta labarta musu ainihin yadda su ka yi da Alhaji jiya. "Ni wallahi ba da wata manufa nayi maganar ba. Na tashi gidanmu babu ƴan uba amma tsakanin yayyena sai babba ya kau ta hanyar aure ko barin gari sannan mai bi masa yake ɗaukar ragamar gidan. Ban san gudun kada a gaba yaran nan su sami raunin zumunci a dalilin haka ni zai jawowa matsala ba." Umma ta kalleta babu wannan fara'ar ta kodayaushe "To amma me ki ka gani a gidan nan da yasa ki tunkarar Alhaji da zancen? Cikinmu wata ta canja miki ne kuma ta nuna saboda kusancin Alhaji da Taj tayi haka?" "Ko kusa. Nayi masa magana ne kawai akan ya dinga nuna sauran ƴaƴan musamman Ahmad da Kamal da su ke manya kamar yadda ya nuna shi." "Maganar girkin fa?" Umma ta sake tambaya don ita so take a warware komai. "Yadda ba ku ɗauke shi laifi ba nima ban ɗauka ba. Wallahi ko kusa ni ban yi masa zancen da ya shafi haka ba. Ba gashi a ranar girkina ya yi miyar ba?" Wata tambayar Umma ta so yi Mama ta katseta. "Ni ban sakawa raina komai ba. Jiya Hajiya ta ƙara min nasiha akan idan muka bari wannan maganar ta girmi haka to zaman gidan nan zai daina yiwa kowaccenmu daɗi. Saboda haka zance ya wuce." Inna sai godiya da farinciki. Bata fita daga ɗakin ba sai da su ka koma wata hirar ana ta dariya. Da rana su ka kira Taj cikin lumana su ka rarrashe shi akan ya yar da wannan buri don ba mai yiwuwa bane. Mama tayi masa nasiha sosai akan yiwa iyaye biyayya. "Ka cigaba da bin Alhaji kasuwa ranakun da babu makaranta amma daga yanzu tsakaninka da kitchen sai hange. Don Allah kada ka bari zancen nan ya koma tasowa a gidan nan." Nuna musu ya yi kamar maganar ta mutu, ashe suma tayi. Shi da Kamal sun kammala sakandire suna da shekara goma sha shida da sakamako mai kyau. Alhaji kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha ranar da su ka kawo takardunsu. Dama tuni ya tura Ahmad ƙasar India inda yake haɗa degree ɗinsa a fannin Computer Science. Zaɓi ya basu tsakanin Dubai, India ko China. Burinsa su zaɓa cikin ƙasashen da su ke cibiyar kasuwanci. "Alhaji mun fi son zuwa wurin Yaya." Cewar Taj. Kamal ya yi Taj wani irin kallo sannan ya ce "ni dai Dubai." Kallonsu ya yi a tsanake. Da wuya zaɓinsu yake bambanta. Bai kuma saka ran samun haka ba ta ɓangaren karatun da zai rabasu na ƴan shekaru. "Anya kuwa Happy da Happiness za su iya rabuwa na shekara huɗu? Ku dai sake shawara ku zaɓi waje ɗaya." Kamal ya kalli Taj da sanyin jiki. Ya ɗauka sun gama magana akan za su zaɓi Dubai. Burinsa ya koyo larabci banda karatun da za su yi. Sannan idan da faraga ya sami wani balaraben malamin ya danɗaƙi haddarsa da kyau ta ƙara zama. Kuma lafiya ƙalau Taj ɗin ya amince har da cewa shi ma zai yi. To me ya kawo wannan sauyi? Alhaji bai ce musu komai ba amma ya fahimci akwai matsala tsakanin yaran. Sai bayan kwana biyu ya kira kowannensu gefe don jin me yake faruwa. A yadda ya fahimta zaɓinsu bai zo ɗaya ba. Kuma kowanne yana so ɗan uwansa ya bi ra'ayinsa. Kamal sai daɗa kwaɗaitawa Taj koyon larabci yake. Shi kuma duk da yana so amma haka kawai zuciyarsa tafi kwantawa da India. Sulhu ya yi musu da alƙawarin kowa zai sami inda yake so. Harka ta kuɗi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci an gama yiwa kowa cuku-cukun samun gurbin karatu har ana shirin tafiya. Iyayensu mata su ka sha kuka kamar lokacin tafiyar Ahmad. Ƴan uwansu hatta na gidan miji don an fara aurarwa a gidan duka aka haɗu a filin jirgi wurin rakiya. Alhaji da kansa zai kaisu makaranta. Dubai su ka fara zuwa saboda karatun Kamal saura kwanaki a fara. Ya biya komai ya tabbatar ya yi settling sannan su ka wuce India. Ahmad ya taho Mumbai ya tarbesu su ka rankaya Hyderabad tare. Gari daban za su zauna da Taj amma haka ya zauna da shi aka gama komai. Bayan sun raka Alhaji filin jirgi ya sake bin Taj har hostel ɗin makarantarsu, Osmania University ya tabbatar babu matsala sannan ya wuce makaranta. *** Washegari Taj ya fita ganin gari. Karatunsu sai nan da kwana goma masu zuwa. Yana cikin yawo ya ci karo da wani katafaren ginin gidan abinci na alfarma. Mutanen dake shige da fice a wajen ba za su ƙirgu ba. Murmushin takaici ya yi. Ina ma iyayensa sun bashi goyon baya. Da watarana idan Allah Ya albarkaci nemansa zai iya mallakar wuri irin wannan. Baya tare da yunwa amma yana son ganin wurin. Musamman kitchen da masu girki. Wurin shiga ya lura layi ake bi. Gashi ginin hawa biyar ne amma ko ina ka kalla tunda zagaye yake da gilas kana hango cikowar mutane. Da kansa ya haƙura da shigar ya kama zagayen ƙayataccen ginin yana mai son ganin iya faɗinsa. Ƙamshin girki mai tada kwantacciyar yunwa gami da muryoyi da ƙarar kayan kitchen yaji yana cikin tafiya. Da sauri kuwa ya manna goshinsa da gilas ɗin wajen yana ganin yadda ake kai kawo a wani makeken kitchen cikin tsari duk a ƙoƙarin ciyar da kwastomomi. Zuciyarsa a take ta soma harbawa. Yaji saukar nishaɗi da farinciki a ransa. Bai san minti nawa ya kwasa yana bawa idonsa abinci ba sai da yaji an taɓa kafaɗarsa an yi magana da yaren punjabi, guda cikin yarukan ƙasar. Da sauri ya juya yaga wani ɗan dattijo sanye da t-shirt da wando ya ɗaure ƙugunsa da apron mai tambari da sunan gidan abincin. Kansa wata irin hula ce kamar ta wanka amma ita mai laushi ce. Ana amfani da ita domin hana zubar gashi cikin abinci. A shekaru a ƙiyasin idonsa zai yi sa'an Alhajinsa. Daburcewa Taj ya yi ya matsa baya a tsorace yana cewa "I'm sorry. Sorry. Sorry." Hanyar komawa yake nema don tsoronsa ɗaya kada mutumin ya haɗa shi da security a ce me ya kawo shi nan. Murmushi mutumin ya yi ya ce "hungry?" Don dama ita ce tambayar da ya yi masa da farko. "Come inside" ya umarce shi da yaga yana neman guduwa. "Am sorry Sir. Please. I won't come again." Ya ce zuciyarsa na faman lugude a ƙirjinsa. Ko sauraronsa mutumin bai yi ba ya riƙe hannun ƙofar da ya biyo ya fito zai koma. Buɗewarsa ke da wuya wani jibgegen mutumi ya tare ƙofar ya yi magana da yarensu yana kallonsa. Dattijon sai ya amsa da turanci yana yiwa Taj kallon in kuma ka musa babu ruwana. Nunawa ya yi ciki za su shigo da shi sannan ba laifi ya yi masa ba. Ƙuttt ya haɗiyi yawu sannan kamar mai taka iska ya bi su ciki. Ƙofar na rufewa gabansa ya sake faɗuwa. Sai dai duk wannan tsoron ya kau lokaci guda da ya ƙarewa kitchen ɗin kallo na kurkusa. Aiki kowa yake yi da sauri-sauri ga magana ana yi wadda ya fahimci karanto odar masu jiran abince ce ko bada umarni. A gefe guda kana iya ganin wasu suna ta jere plates ɗin da aka gama haɗawa a wani abin turawa za a fita da shi. Ga masu girki sun duƙufa suna yi. Wuta da mai da cokula sai chuu...chauuu su ke. Ganinsa ya ƙare akan masu yanke yanke kamar inji. Wasu su na yanka albasa, caras, da ma nau'ikan kayan lambun da bai taɓa gani ba. Wani haɗaɗɗen murmushi ya saki sai ga ƙaton mutumin ya dawo da tray shaƙare da kwanukan abinci. "Eat." Mutumin tsoro yake bashi amma duk da haka ya faɗa masa gaskiya "Am not hungry." "Taste our food and we talk, okay?" Juyawa ya yi yaga dattijon farko ne ya yi magana. Musu ma wuri yake samu. Karɓar tray ɗin ya yi babu shiri ya zauna a inda aka nuna masa. Ƙamshin abincin ya tafi da tunaninsa. Shinkafa ce da kaza. Ga kuma wani haɗin albasa, cucumber da tumatir da wani ganye mai tsami tsami da daɗi kamar kunne zai fita. Wani ɗan kwano mai zurfi a gefe kuma miyar naman sa ne wanda ya dahu ya yi luguf. Sai wani abu kamar bread ko gurasa mai faɗi. Abu ɗaya ya kula shi ne babu cokali. Ya ɗaga kai ya tambaya dattijon nan shi kuwa ya ce masa. "We eat with our hands here." Taj ya gyaɗa kai ya miƙe yace zai wanke hannu. Sink ya nuna masa ya wanko ya dawo. Yana zama ya yi Bismillah ya fara ci. Miyar ya ɗauka zai zuba a shinkafar da wani ɓangaren nata ya yi jaja-jaja, wani fari-fari, wani kuma yellow. Mutumin ya nuna masa ai gurasar nan ake ci da miyar. Shinkafar kuma ya zuba salad ya dinga haɗawa da nama. Ya tambayi sunan abincin aka ce masa chicken biryani ce da kuma chappati da beef curry (miyar). Tunda ya saka hannu bai cire ba sai da abincin ya rage ɗan kaɗan. Yana ture plate kawai yaji mutanen kitchen ɗin suna ihu harda masu rungume juna. Ashe duk sun ankara da tsayuwarsa tun farko. Shi ne ogansu mai wurin ya shigo da shi. Farincikin fuskarsa a matsayinsa na wanda su ke da yaƙinin ranar ya fara cin abincinsu ne yasa su murna. Sai da kowa ya nutsu aka cigaba da aiki sannan mutumin ya tambaye shi sunansa da dalilinsa na leƙensu. "Kenan kana son girki" ya tambaye shi da turanci bayan ya yi masa bayani a taƙaice. "Sosai." "Ka taɓa yin makarantar girki ko ka koya daga wani professional?" "A'a." "Muna da makarantu a nan inda za ka iya yin degree." Taj ya yi murmushi da ya hango fuskar Alhaji idan ya je gida da kwalin degree a fannin girke girke. Sanar dashi ya yi cewa karatu zai fara kuma banu damar canjawa. "Idan ka tabbata kana da ra'ayi ni zan iya koya maka a nan. Ka je ka duba tsarin karatunka. Ranakun da baka da aji ka zo nan kayi aiki." Baki ya buɗe da tsananin mamaki. "Aiki?" "Baka so ne?" Da sauri ya ce yana so. Ya dai yi mamakin samu ne kafin ya nema. Ƙaton mutumin nan ya sakar masa fuska ya ce. "Dukkaninmu a haka yake ɗaukar mu aiki. Ra'ayin yi kawai zai gani daga gareka sai ya ɗauke ka yaronsa. Wurin nan nasa ne. Idan ka bada himma tabbas za ka ji daɗi. In kuma yaga baka da ƙwazo a wata ɗayan farko zai sallame ka." Kamar wasa daga wannan rana Taj ya fara karatu kuma yana zuwa koyon aiki a ROYAL CUISINE. Abin farinciki shi ne kasancewar dattijon da ake kira Paaji (ɗan uwa ko yaya) musulmi. Yawancin ma'aikansa musulmai sun fi yawa ma. Komai na wurin halal ne. Sai da ya yi wata guda cur babu abin da ake koya masa a kwana ukun da yake zuwa duk sati sai sanin sunaye da amfanin kayayyakin abinci da kayan ƙamshi (spices). Hancinsa ya aikatu don ko abu na kama da ɗan uwansa idan bai tantance ba maimaici za ayi ta yi. Wasu abubuwan kuma a ido su na kama amma a zahiri ɗaya nada amfani ɗayan kuma guba ne. Dole suma sai ya gane bambancinsu don kada a bashi a kasuwa ya cutar da masu sayen abinci. Bayan nasararsa a wannin fanin kuma aka koma koyon ɓare tafarnuwa da yankanta ƙanana. Kan kace meye wannan hannunsa ya cika da plaster. Irin wannan yankan na mugun sauri ake so ya iya. Da ƙwararre a wurin aka haɗa shi. Daga nan aka koma albasa. A haka, a haka ya ƙware a yankan kayan lambu da kayan marmari. Yankan nama ma zaman kansa yake. Sai da ya koyi haɗa mince meat ko babu na'ura da wuƙa kawai da ƴar muciya. Shekara guda ko mai ba a taɓa bari ya soya ba sai da ya zama zakara a fannin ƙananan ayyukan da su ne ƙashin bayan kowane girki. Bayan an dawo hutu wanda yaje gida ya yi da kyakkyawan sakamakon ƙarshen shekara ta farko aka kai shi gaban wuta. Zo ka ga farincikinsa da na abokan aikin. Mutane ne ƴan asalin garin Punjab masoyan duk wani abu na farincikin al'umma. Su dai ayi nishaɗi a zauna lafiya. Shi yasa Taj ya saje cikinsu. Happy Taj su ke kiransa tun ranar da ya yi skype da Kamal su ka ji yana kiransa Happy. Da yake anfi samun ƴan ƙabilarsu mabiya addinin musulunci a Pakistan, shi yasa Paaji duk inda ya sami ƴan uwansa musulmi yake basu aiki. Taj da wani Uygur Chinese (wata ƙabilar musulmai a China) Aynur kaɗai ne baƙi. A cikin shekara ukun farko Taj ya ƙware a girke girke da dama na yankin Asia. Banda na Indiyawa an koya musu na Larabawa da duk wani yankin Asia da su ka yi fice ta fannin abinci. Duk kuma wannan badaƙala ko sau ɗaya Ahmad bai taɓa sani ba har ya gama ya koma gida. Taj ya ci karensa babu babbaka ya haɗa riba uku a zaman nasa. Bai manta da ƙudurinsu na bitar hadda ba shi da Kamal shi yasa ya shiga wata makarantar ƙarshen mako da ake yi a masallaci. Kamal ne kaɗai ya san me yake ciki kuma ya bashi goyon baya tare da nanata masa mahimmanci barin abin a matsayin sirri. A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Taj da Kamal sun ƙarƙare karatunsu a cikin shekara uku da ƴan watanni. Kowanne akwai taron convocation da za ayi a makarantarsu. Kamar yadda aka fara kai Kamal, ranar nasu taron ta zo sati uku kafin na su Taj. Alhaji sai ya ɗauki Hajiya da Umma su ka tafi Dubai. Satinsu biyu a can su ka koma gida tare da Kamal ɗin. Bayan kwana huɗu ya juya da Ahmad, Mama da Inna zuwa India. *** Gagarumar gasar girki ce Culinary Academy of India ta saka domin samun zakarun da za ta bawa tallafin yin karatun degree na tsahon shekara uku a fannin Catering Technology and Culinary Arts. Makarantar reshe ce ta Jami'ar da ya kammala wato Osmania University. Kuma ɗalibanta ta buɗewa gasar masu ra'ayin girki waɗanda ba ƴan asalin ƙasar ba. Paaji na samun labari ya saka shi a gaba a gaban kwamfutar restaurant ɗin nasu ya cike komai online. Abokan aikinsu su ka yi ta murna domin da fari har ya soma yi musu sallamar komawa gida da zarar an yi convocation. A kwana biyar za ayi komai a gama. Taj bai san da tahowar su Alhaji ba kamar yadda Kamal bai san ya shiga gasa ba. So ya yi ya yi surprising ɗan uwan nasa. Wanda kuma da ya faɗa masa zai gargaɗe shi da tahowar tasu. Duk wayarsu da gida ana ta ɓoye masa don an san ba ƙaramin farinciki zai yi ba idan su ka zo. Tahowar Ahmad kawai ya sani saboda zai zo registration na masters tunda ya gama bautar ƙasa. Sun iso ƙasar awa guda kafin a shiga gasar a rana ta huɗu wadda ta kasance alhamis. Zuwa yanzu team ɗin Taj da aka haɗa da wani banufe ɗan Nigeria mai suna Wakili su ne su ke jan ragamar muƙami na biyu. Wasu wa da ƙani ƴan Indonesia kuma a sahun farko. Wayarsa Ahmad ya kira ya faɗa masa sunan hotel ɗin da su ka sauka. "Yaya ka daure ka ƙaraso Uma Nagar cikin Culinary Academy." Ya ce da farincikin isowar ɗan uwansa. Don dai yau ɗaya yana ganin ba komai bane idan an sani. A tunaninsa nasararsa ta karatun da Alhaji yake so za ta sa ya bashi damar cika nasa burin. "Me ake yi?" "Gasar girki na shiga." Gefe Ahmad ya matsa hankali a tashe. "Ashe ba ka da hankali Taj? Tun yaushe Alhaji ya soke maganar nan?" Da yanayi na ban tausayi Taj ya ce "Yaya ina so wallahi. Domin neman amincewarsa na dage sosai a makaranta. Kana ganin yanzu ba zai sauko ba tunda nayi karatun da yake so?" "Baka da hankali." Ahmad ya sake faɗi yana jin zufa na karyo masa. Duk abin da yake yi hankalin Alhaji dake magana da su Inna yana gare shi. Sauke wayar daga kunnuwansa ke da wuya yaji ya ce masa, "Me ku ke ɓoyewa da har za ka tashi ka dawo nan?" "Babu komai Alhaji. Ya ce min baya hostel ne." Rashin gaskiya ya gani ƙarara a fuskar ɗan nasa shi yasa ya ce, "Kai ni inda yake!" RAYUWA DA GIƁI 5 Batul Mamman💖 "Alhaji..." "Zan saɓa maka." Ba yadda ya iya. Cikin minti shabiyar ya sama musu tasi su huɗu suka kama hanya. Mama da Inna ba su san me ake ciki ba. Shi kuwa Alhaji tunda yaga sunan makarantar a bakin gate jikinsa ya soma tsuma. Ahmad dai jikinsa duk ya mutu. Ya yi kiran Taj ɗin da su ka shiga bai ɗauka ba. Da tambaya su ka ƙarasa wurin da ake gasar inda mutane su ka yi dafifi kamar ƙudaje. Basu wani sha wahala ba su ka hango tebura huɗu na ƙasashen da su ka rage a gasar. A yau za a fitar da wani team ɗin sai ya rage uku. Washegari idan an yi na ƙarshe a fitar da na ɗaya, na biyu da na uku. Cikin wata irin nutsuwa da tsantsar ƙwarewa Taj yake aiki. Shi da Wakili girkinsu cikin tsari yake kamar sun manta da lokacinsu na tafiya. Wannan nutsuwar ita tafi burge alƙalan gasar. Masu sauri saurin cimma lokaci kuwa daga kwano ya faɗi ya fashe sai ka ji su na washhh, mai ko ruwa mai zafi ya fallatso mu su saboda garaje. Tunda Alhaji ya yi tozali da ɗan nasa wani abu mai masifar ɗaci ya sami wurin zama a maƙogaronsa. Taj yake gani sanyi da dogon wando baƙi da riga yellow mai tambarin makarantar sai apron fari tas ɗaure a ƙugunsa. APRON!? Inna kuwa tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi. Tunda ta nunawa Mama shi bata sake iya cewa komai ba. Maman ce ma ta iya yin magana da ƙyar. "Ahmad me idona yake gani?" "Gasar girki ce" ya bata amsa a sanyaye. "Ku zo mu koma." Alhaji ya ce da matansa "Kai kuma ka jira ya gama ka taho min da shi." Ahmad ya so raka su amma ya nuna masa yawo a ƙasar da ba tasu ba, ba baƙon abu bane gare shi. Haka su ka tafi babu mai cewa komai. Da isarsu Alhaji ya ɗauko magungunansa na hawan jini ya watsa sannan ya ce kada wanda ya tashe shi sai Taj ya iso. Dama ɗaki uku ya kama musu. Sai su ka koma ɗayan. Ido cike da ƙwalla Inna ta ce "Yaron nan so yake ya jaza mana tashin hankali ko me?" Kallonta Mama tayi ta girgiza kai. "Matsi da takura yaro bai fiye haifar da ɗa mai ido ba. Taj ya yi masa biyayya an sami abin da ake so. Mene ne aibu don ya ɗan waiwayi burinsa? Don fa mun haife su ba yana nufin dole su rayu kwatankwacin tamu rayuwar ko ra'ayi ba." "Kayya dai Mama. Rayuwar yara sai da nuna hanya daga iyaye." "Nima ban musa ba. Amma babu inda addini ya bawa iyaye damar tauye ƴaƴansu akan abin da bai saɓawa addinin ba. Baki ji malamai suna faɗin ko sakin aure indai ba bisa adalci ba, iyaye basu da hurumin tilasta shi ba? Girkin nan kuma maza nawa ke yi? Mene ne aibu a ciki tunda ba daudu yake ba?" Inna dai duk a tsorace take ta ce "tunda mahaifinsa ba ya so sai ya haƙura ko don neman albarka." Mama gani tayi cigaba da nunawa Inna illar takura tayi yawa ga ɗa mai biyayya bata da amfani ba sai taga Innar ta kasa fahimta. Idan ta matsa kada abin ya yi kama da tana son sanya shi yin bore. Zaman jiran tsammani su ka yi har bayan Isha. * Sakamakon gasa yau dai da su Taj ya tashi. Cikin nasara da taimakon Allah su ne su ka yi na ɗaya. Yawan makinsu idan an haɗa da na kwanakin baya ya basu damar iya yin na ɗaya gobe in sun dage. Banda ihun murnar ƴan Nigeria da su ke makarantar ba ka jin komai. Yanzu ya rage teams uku. Gobe za a fitar da na ɗaya, biyu da uku. Da su ka fito za su tafi Wakili ya tare shi da godiya. "Ban san a ina ka koyi girki wanda yasa talent ɗinka ya zarce na kowa a nan ba. Your are truly amazing." Taj ya yi murmushi "ai ban kai ka ba." "Magana ta gaskiya ake yi. Idan muka yi nasara na san albarkacinka na ci. Saboda haka ina roƙonka don Allah gobe ka dage fiye da kullum. Samun karatun ya fiye min akan kuɗin da za a bawa na biyu ko na uku." Murmushi Taj ya sake yi da alƙawarin in sha Allahu gobe zai yi bakin ƙoƙarinsa. Da tallafin gwamnati Wakili ya sami tahowa karatu. Ya gama degree kamar Taj amma yana tsoron komawa gida yanzu. A ƙauye su ke. Gashi samun aiki yanzu ya koma wa ka sani, wa ya san ka. Tunda yana aiki a wani gidan abinci a nan yana samun abin turawa mamansa da ƙanne ba zai so ƙarewar visa yasa shi komawa gida a sake naɗe hannuwa ba. * Murnarsa ta koma ciki da Ahmad ya faɗa masa tare da su Alhaji su ka zo akan hanyarsu ta zuwa hotel ɗin. "Yaya don Allah kada ka sanar dashi zancen competition ɗin nan." Cije leɓe Ahmad ya yi wanda yasa Taj tambayarsa ko ya faɗa hankali a tashe. "Tare mu ka shiga inda ku ke girkin. Ya riga ya gan ka." Bayan karanto duk wata addu'a da ya sani ta neman sauƙi, bai sake cewa komai ba har su ka isa hotel ɗin. Kai tsaye ɗakin Alhaji su ka je su ka tarar da Inna da Mama a zaune jigum. Jikin Alhaji har ya soma tsananta saboda damuwar da ya sanya a ransa. Wuri ya samu kusa da Mama ya zauna jikinsa a matuƙar sanyaye. Shiru yana jira a fara yi masa faɗa amma babu wanda ya yi magana. Cike da fargaba ya rarrafa gaban Alhaji kai a ƙasa. "Don Allah..." Tassss. Alhaji ya tsinke shi da marin da ya gigita shi. Inna tsam ta miƙe ta fice daga ɗakin don ba za ta juri gani ba. Ko da ta koma ɗaya ɗakin fashewa tayi da kukan da bata san na mene ne ba. Tana tausayin ɗanta. Tana kuma son ya sami damar cikar buri sannan kuma tana so ya yiwa mahaifinsa biyayya. Sake ɗaga hannu Alhaji ya yi zai kuma marinsa cikin zafin nama Mama ta riƙe hannun da sauri. "Ka dubi Girman Allah kayi haƙuri." "Ki sakar min hannu" ya miƙe tsaye da fushin da yafi na farko yana mai fincike hannunsa. "Haba Alhaji. Mene ne aibun girki a wurin namiji da har za ka kasa bawa yaron nan damar cikar burinsa." "Buri? Buri fa ki ka ce A'i?" Ya nuna ƙirjinsa "ɗan cikina ki ke so na bari ya yi daudu?" A hasale ta bashi amsa saboda har ga Allah tana ganin da gangan kawai yaƙi fahimta balle ya sassautawa ɗan. "Mece ce alaƙar girki da daudanci? Maza nawa ka gani da wannan sana'ar kuma ba su lalace ba? Ka kyautata masa zato mana ka bi shi da addu'a." "Ni ki ke ɗagawa murya?" Ko ɗar bata ji ba ta ce "Gorin haihuwar namijin za ka sake yi min?" Ahmad ya fice kiran Inna. Taj kuma jin yadda rigima take son tasowa tuni ya dawo daga duniyar raɗaɗin marin da aka yi masa. "Mama bashi haƙuri mu fita." Ya durƙusa a ƙasa "in sha Allahu nima ba zan sake tada maganar nan ba." Hannun Mama ya ja su ka haɗu da Inna tana dawowa ɗakin da jan ido. Ganin sun fito ita ma ta bi bayansu ita da Ahmad. Kamar wancan lokacin yanzu ma nasiha game da mahimmancin yiwa iyaye biyayya su ka yi masa. Ya kuma karɓa hannu bibbiyu da zuciya ɗaya. Ƙarfe goma da rabi na dare saƙon Wakili ya shigo wayarsa. Tuni akan fitowa da wuri ya soma yi masa. A ƙarshe kuma ya yi rubutu kamar haka. "...My mum said we should keep reciting this Du'a tonight being friday night and tomorrow when the competition begins. RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAYYA MIN KHAIRIN FAQIR. I will continue to thank Allah for bringing you my way no matter the outcome. Working with a pro like you is truly an honour. Thank you Happy Taj." Duk iya sata ta bacci daidai da sakan guda Taj bai runtsa ba. Shaf ya manta ba shi kaɗai bane a gasar har ya yiwa su Inna alƙawarin haƙura. Gashi daga cikin dokokin gasar duk wanda abokin girkinsa bai zo ba har aka fara da minti goma sha biyar sun zama disqualified. Anya zai iya samun kwanciyar hankali idan ya zama sanadiyar rugujewar rayuwar wani? Kafin asuba babu irin tunanin mafitar da bai yi ba. Yana idar da sallah ya fice daga hostel zuwa hotel ɗin su Alhaji. Bai tsaya neman abin hawa ba saboda ƙarancinsu a wannan lokacin. Sannan babu wata tazarar azo a gani ma. Da gudu gudu ya isa yana faman haki. Kai tsaye ɗakin Ahmad ya fara zuwa. Da ba a buɗe ba ya durƙusa a bakin ƙofar yana mayar da numfashi. Zaman kimanin minti shabiyar ya yi sannan Ahmad ya dawo. "Lafiya me ya fito da kai da asussuba haka?" "Alhaji yana ɗakinsa? Ya tashi?" Taj ya tashi ya ma manta da gajiyar jikinsa. Yanayinsa na rashin nutsuwa Ahmad ya fara dubawa kafin ya shige masa gaba zuwa ɗakin Alhajin. Shi kaɗai ne a ɗakin don matan nasa sun yi yaji saboda abin da ya faru jiya. Sanye yake da farar jallabiya yana fitar da daddaɗan ƙamshin turaren larabawa. Gemunsa mai sirkin fari-fari da baƙi ya ƙarawa fuskarsa kwarjini. Kamanninsa da samarin ƴaƴan nasa ta sake bayyana. Gaishe shi Taj ya yi ya faɗi buƙatarsa kai tsaye. Ahmad na ji ya fita da sauri ya kira su Inna don su dakatar dashi kafin maganar ta lalace. Sun shigo daidai lokacin da Taj yake cewa, "Ba don kaina nake son zuwa ba. Nayi maka alƙawarin ko na nawa mu ka yi ba zan karɓi komai daga gare su ba. Izini kawai nake nema kada rashin zuwana ya zama silar rushewar ...." "Tajuddin!" Durƙusawa ya yi duk da kiran sunan nasa ya kiɗima shi cikin ƙanƙan da kai ya shiga magiya kafin ma ya ji me Alhajin zai ce. Wannan ya ƙara tunzura mahaifin nasa sosai. "Indai ni zan yi maka izini to ka sani har abada ba zan taɓa yarje maka ka sake tsayuwa gaban murhu ba. Allah Ya yi min rufin asirin da ko mata cikin tsatsona ba za su nemi kuɗi da girkawa wasu abinci ba balle kuma namiji." Ƙwalla mai zafi ta shiga saukowa Taj a yayinda yake jin kamar da gayya mahaifin nasa yake tauye shi. To amma ko zai hana saboda baya son a haɗa ɗan cikinsa da sana'ar girki me yasa ba zai duba cewa rashin zuwansa zai salwantar da mafarkin cigaban ɗan marayan da bashi da gata ba. "Alhaji ka yiwa Allah..." "Na gama magana" Ya furta da izza sannan ya fuskanci Ahmad "ka canja mana booking idan akwai jirgi mu tafi yau da ƙanin naka. Takardunsa kuma ka tsaya ka karɓar masa." Hankalin Taj tashi ya yi ya miƙe da sauri "Alhaji na rantse maka ba don ni zani ba. Idan ban je ba za ayi disqualifying ɗinsa." "Wannan nauyin sai ya zame maka darasin rayuwa a gaba ta yadda ba za ka sake marmarin saɓawa umarni na ba." Inna da Mama har ma da Ahmad saka baki su ka yi wajen lallashin Alhaji akan ya amince amma ya yi biris da su. Taj kuwa kuka yake tamkar yaron goye. A wannan yanayin wayar Wakili ta shigo masa. Alhaji da kansa ya ce ya ɗauka kuma ya faɗa masa ba zai je ba. "Happy Taj yi haƙuri na kira ka da sassafe." Ya yi magana da ɗan jin nauyi. "Kada ka damu na riga na tashi." Wakili ya yi ƴar dariya "jiya wanda mu ka gaisa ka ce yayanka ne ko?" "Eh." Ya amsa da sanyin murya. "Breakfast na haɗa masa nake neman address ɗin ka. Na rasa da me zan karramaka. Ko a wannan matsayin mu ka tsaya kai ne sila. Zan so yin aiki tare da kai nan gaba." Ya sake dariya "kana burgeni ne. Ina son koyon girki kamar kai." Kasa cewa komai Taj ya yi sai ruwan hawayensa da ya ƙaru. Daurewa ya yi ya ce da Wakili zai tura masa address ɗin yanzu. Bayan ya ajiye wayar ya dubi Alhaji da ya gama jin komai. "Ka gani ko Alhaji? Yana da kirki kuma maraya ne. Cutar shi zan yi idan ban je ba." Gajiya Alhaji ya yi da magiyar dukkaninsu ya ɗaga murya ya ce ce "Ku fitar min daga ɗaki gabaɗayanku." Iko da izzarsa ba tun yau su ke damun Mama ba. Amma wannan ya fi ɓata mata rai. Wace irin zuciya ce da shi da za a dinga roƙonsa akan tallafawa rayuwar wani ya turje a kai. Sannan da girmansu ya haɗa su da ƴaƴan cikinsu ya yi musu kora irin wannan ta ƙasƙanci. Ta dubi hawayen Inna wanda ko ba a faɗa ba ta san na son share damuwar ɗanta ne. Bata cewa kowa uffan ba ta fita ta koma ɗaki inda ta baro wayarta. Kimanin minti goma ta ɗauka wurin yiwa mijin yayarta wanda ya kasance babban wa ga Alhaji ta fayyace masa komai. "Zan kira shi yanzu. Kashe wayar." Kawai ya ce bayan ya gama jin bayaninta. Da ta koma ɗakin yadda ta fita ta barshi haka ta same shi. Saboda halin da Alhaji ya sanya jama'ar ciki hatta iskar ɗakin bata daɗi. Shigarta ke da wuya Alh. Jafaru ya kira shi kamar yadda ya yi mata alƙawari. "Hayatu." "Na'am" ya amsa da ladabi domin ya yarda da aka ce babban wa uba, musamman wanda ya riƙe matsayin da gaskiya da amana irin yayansu. "Ni Jafaru na bawa Tajuddin izinin fita yaje ya ƙarasa abin da ya fara. Sannan ina mai umartarka da ka zauna har a sallame su daga makaranta ku taho tare." "Yaya Babba?" "Idan ban isa ba kana iya take umarnina ka ɗora naka." Bai bashi damar sake cewa komai ba ya kashe wayarsa. Alhaji ya kalli Mama da wani irin ɓacin rai mara misali. Sanin bata da gaskiya sai ta sadda kanta ƙasa kawai. "Tashi kaje wurin gasar." Iya abin da ya ce kenan ya fice daga ɗakin ya barsu. Taj bai ma gane dashi ake ba sai da Mama tayi masa magana. Ya kalli agogo yaga takwas saura mintuna ƙalilan. Gashi da ƴar tafiya zuwa makarantar. Tunanin wanka ko kusa bai zo masa ba ya fita da gudu-gudu ya sauka neman abin hawa. Ya isa tara saura minti bakwai. Har an gama shirya komai sauran teams biyun sun tsaya suna jiran lokaci. Wakili kuwa shi kaɗai ne a can gefe yana ta baza idanu cikin tashin hankali. Taj na shiga wurin aka kaure da ihu da tafi. Ashe ba Wakili kaɗai ke jiransa ba. Masu mara musu baya da dama sun shiga fargabar makomarsu da aka ga bai zo ba. Tara daidai aka buga wata ƙatuwar ganga wadda ta bawa participants ɗin damar farawa. RAYUWA DA GIƁI 6 Batul Mamman💖 *** Kyakkyawan envelop Yaya Babba ya miƙawa Alhaji ya kuma bishi da kallo a tsanake don son karantar yanayinsa. Kamar yadda ya yi tsammani duk wani annuri da walwalar da yake tare da ita a farkon zamansu tsaf ya kau. Duhun da yake zuciyarsa ya sami damar nuna kansa a fuskar. Disappointment ɗinsa akan Taj ya kashe masa jiki da zai yi magana. "Kawo maka ya yi?" Da Yaya Babba ya gyaɗa kai sai ya ce "to me yake so?" Kallon tausayi Yaya Babba ya yi masa. Mutum mai kafiya irin ƙaninsa yana da wuyar sha'ani. Wani zubin ya tabbatar yana sanin cewa ba a kan gaskiya yake ba amma don kada ya sauya baki sai ya cigaba da riƙo da hujjojinsa masu rauni. Sai dai a yau ya ƙudiri niyar amfani da girmansa karo na biyu ya tanƙwara ƙanin yadda yake so. A nutse yadda zai fahimta ya labarta masa zuwan Taj gidansa kwanaki uku da su ka wuce. A lokacin sun kusa wata biyu da dawowa daga India. Sakamakon gasar girkin nan ne Wakili ya taho masa da certificate ɗinsa na ɗaukar na ɗaya. Sannan ga admission letter kamar yadda aka yi alƙawari. Shi ne ya kai masa ya gani amma ya roƙe akan kada ya sanar da kowa domin ko iyayensa mata bai nuna musu ba. Ya kawo ne saboda ya nuna masa godiya akan shige masa gaba da ya yi har ya sami damar ƙarasawa. Sai kuma Wakili da ya nuna son zuwa ya gaishe da iyayensa kafin ya wuce Minna. Shi ne ya kai masa shi inda aka yi masa tarba mai kyau. Da yaji daɗi har mahaifiyarsa sai da ya haɗa da Yaya Babba su ka gaisa. Alhaji ya gama jin zancen da bai gamshe shi ba ko kusa ya ce "mece ce manufar nuna min tunda ya ce baya son na sani?" Yaya Babba dakewa ya yi babu alamun wasa ya ce "ina son ka sanya masa albarka ne domin idan Allah Ya kaimu lokacin fara karatun ni zan mayar dashi da kaina." "Kada mu yi haka da kai Yaya." Alhaji ya furta da ƙaramar murya yana jin wani irin yammm a sassan jikinsa. Yana matuƙar ƙaunar Taj sannan burinsa a duniya yaron ya gaje shi. Idan hakan bai samu ba ya yi zarra a duk sana'a ko aikin da ya nema amma banda GIRKI. Yadda rayuwar Habibu ta sauya salo a kan idanunsa ba zai taɓa lamuncewa ɗansa ya faɗa wannan hanyar ba. Shi fa ko duk jikinsa kunnuwa ne ba zai yarda girki ba wani nau'i bane na daudanci. "Idan Allah Ya bamu yara masu biyayya, amfani da ƙarfin iko wurin hanasu farinciki ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba Hayatu." "Haka ne." "Ka amince?" Yaya Babba ya tambaye shi yana murmushi. "Ai ka ishe shi uba Yaya Babba. Ba za ka taɓa faɗin magana na musanta maka ba in sha Allahu." Da zuciya ɗaya Yaya Babba ya miƙa masa hannu su ka yi musabaha cike da farinciki. Bai san cewa magana ce mai harshen damu Alhaji ya yi masa ba. "Allah Ya ja kwana baban Tajuddin. Nagode da karamcin nan da kayi min. Da yardar Allah sai mun yi alfahari da zaɓinsa." "Uhmm" kawai Alhaji ya iya cewa don bakinsa ya bushe kamar an shanya a rana. Samu ya yi ya bar gidan kamar babu abin da ya riƙe a ransa. Bayan fitarsa Yaya Babba ya kira Mummy (Ɗaharatu) matarsa kuma yaya ga Mama ya sanar da ita anyi nasara. Ta kama murna tana cewa hakan shi ne daidai. "A neman haram ake yin fito na fito da burin ƴaƴa. Yadda Taj ya rame ya sanya abu a ransa ko ya zauna ba daɗinsa za su ji ba. Allah Yasa matakin nasara da samuwar alkhairi mu ka ƙulla." "Amin" Yaya Babba ya faɗi yana gyara zaman gilashinsa. Duk cikin zuri'arsu shi da wata ƙanwarsu Jamila ne ake yiwa laƙabi da ƴan boko. Matarsa ɗaya da yara biyar waɗanda huɗu sun yi aure saura namiji ɗaya. Mutum ne da ya yarda da displine ɗin yaron da ya kauce hanya amma sam bai yarda a tauye haƙƙinsu ba. Ita kuwa ƙanwar tasu da yara ke kira Amma likita ce. Sai da ta gama karatu tayi aure har ana ganin da gangan taƙi yi tun farko. Mijin mazaunin Amerika ne a can yake aiki. Bayan aurensu da ta bi shi ita ma ya sama mata take aikinta a wani asibiti. Yaransu biyu mata. *** Ɗaki Alhaji ya kira Taj bayan ya koma gida. Ya yiwa ɗan nasa kallo na ka bani kunya sannan ya miƙa masa envelop ɗin. A take kuwa jikin Taj ya kama rawa. "Ba da wata manufa na kai masa ba Alhaji." "Ka ji na ce wani abu ne?" "A'a." "Madalla" ya gyara zama "Yaya Babba ya ce ka haɗa kayanka ka koma gidansa kafin lokacin fara karatun naku." "Wane karatun? Ba service zamu tafi ba?" Ya tambaya da faɗuwar gaba. A ransa Alhaji gani yake rainin wayo ne kawai Taj yake son yi masa amma ya san komai. Ƙarshenta ma shi ya roƙi Yaya Babban da ya taimaka masa ya sami komawa makarantar. "Idan ka dawo sai ka zo kayi service ɗin. Ina yi maka fatan samun nasara da alkhairi. Allah Ya yi maka albarka. Tashi ka tafi." Kansa sake ƙullewa ya yi amma babu halin tambaya. Sai ma ƙarin bayani da Alhajin ya yi masa cewa ya bari jibi zai kai shi da kansa don ya sami damar hađa kayansa. "Ba na kuma son jin zancen nan a bakin kowa har matan gidan don na san za su so hanaka tafiya." "To Alhaji" ya amsa a ladabce. Kamal kaɗai ya sanarwa abin da yake faruwa. Da taimakonsa ma ya gama haɗa kaya. Ranar da za su tafi Alhaji ya faɗa masa zai dawo daga kasuwa da azahar sai ya kai shi. "Happy" Kamal ya kira Taj suna zaune a ɗaki "ba ka mamakin chanjin ra'ayinsa?" "Ni fargaba ce ma tafi damuna. Naga ko kaɗan bai nuna fushi ba duk da Allah Ya sani ba da wannan manufar na kai wa Baba Yaya takardun ba." "In sha Allahu ma babu komai. Dama tsoron da naji da ka ce wai ya ce kada a faɗawa kowa." Bugun ƙofa gami da sallamar Bishir ce ta hana Taj sake yin magana. Saƙon Alhaji ne yana jiransa a mota. A take yaji gabansa ya yanke ya faɗi. Ya tashi jiki a mace sai Kamal da Bishir ɗin ne su ka ɗauko masa kayansa. Kowa yaga ana loda kaya a booth ɗin Alhaji sai ya yi mamaki amma an rasa mai tambaya don babu fuska. "Ka shiga ka yiwa uwayenka sallama." Alhaji ya umarce shi da ya fito. Inna bata gida. Sai su Hajiya. Su ka biyo shi waje kuwa su na tambayar Alhaji me ya faru Taj zai koma gidan Yaya Babba. Cewa ya yi su koma. Idan ya dawo zai yi musu bayani. A mota haka su ka tafi ko numfashi mai sauti Taj baya iya ja. Kamar tare su ke don ana buɗe musu gate su ka ga Yaya Babba yana fitowa daga mota. Dawowarsa kenan daga office. Yayi mamakin ganin Alhaji kaɗai ko direba babu da Taj. Sai dai wannan ba komai bane a yayin da yaga ya buɗe booth Taj na sauke kaya. "Hayatu me yake faruwa ne?" Ya matso kusa dasu don jiran su gama su shigo ciki ma ba zai iya ba. Alhaji ya dubi ɗan uwansa yana mai baƙincikin yadda yayi masa katsalandan a cikin harkar gidansa. Shi kuwa Taj yana jin haka wani irin tsoro ya kama shi. Kenan Baba Yaya ba shi ya nemi ya dawo gidansa kamar yadda Alhaji ya faɗa masa ba. "Ga Taj nan. Suna na ne kawai addini bai halatta min cire masa ba amma daga yau na bar maka shi." Yaya Babba ya girgiza da furucinsa matuƙa. Fuskar ƙanin nasa a haɗe take kamar baƙin hadari. "Me ya yi zafi? Don na ce zan mayar dashi makarantar da yake so?" "Ai ban hanaka ba tunda ka isa. Shi ma da na isa dashi ina mai umartarsa kada ya dawo min gida." "Hayatu bana son rashin hankali." Yaya Babba ya fara faɗa. "Ai kuwa bai kamata ka kira biyayyata gareka da rashin hankali ba." Ya cigaba da magana kai tsaye babu tauna lafuzza don yau dole ya amayar da ɓacin ransa "saboda gudun shiga haƙƙi ban taɓa yiwa kowa iko da ɗansa ba. Amma sau biyu Yaya kana bawa yaron nan abin da nake son hanawa. Hakan ba komai zai janyo min ba illa baƙin jini daga gare shi. Koda yayi min biyayya zata zama bisa tursasawa ba don son rai ba. Maganin kar ayi, kar a soma. Tunda ka nuna masa za ka iya bashi abin da na hana sai ka riƙe shi na bar maka." "Ni kake faɗawa magana Hayatu? Ashe zumuncinmu bai kai nayi umarni ko hani ga tsatsonka ba tare da ka ɗaga kai ba?" Yaya Babba ya faɗi yana mai jin ciwon maganganun da kunnuwansa ke ji. Musayar yawun da suke ba ƙaramin tadawa Taj hankali tayi ba. Ya durƙusa a ƙasa yana kuka yake roƙonsu da su yi haƙuri. "Wallahi ba zan sake tada zancen nan ba har abada. Ku yafe min don Allah." "Baka isa ba! Karatu ko ba kyauta aka baka ba sai kayi shi. Tunda ka iya raina ƙoƙarina akanka ka haɗani da ɗan uwana dole ka cika burinka." Taj na kuka ya riƙe ƙafar mahaifinsa yana roƙon yafiyarsa. Yaya Babba ma idanunsa sun kaɗa sun yi ja. A haka ya ja girmansa don gudun rigima ya bashi haƙuri. "Kayi haƙuri. Ban yi zurfin tunani ba, da ban shiga huruminka ba. Don Allah ka ɗauki ɗanka ku tafi." "Na gama magana. Wallahi daga yau Taj ya bar gidana..." "Kada ka rantse." Ya yi nufin dakatar dashi sai dai ya makara. Suna ji suna gani Alhaji ya juya ya shige motarsa yayi gaba. Taj ya bi motar a rikice kafin ya sami wuri kusa da akwatinsa ya zauna cikin wani irin yanayi na rashin kuzari. Zuciyarsa wani irin ƙunci kawai ke yawo a cikinta. Bai san lokacin da aka kwashe kayansa ba. Sai hannuwa da yaji na ɗan uwansa, ƙaramin ɗan Yaya Babba wanda ya kasance sakonsa ya tayar dashi. Da ƙyar ya yarda ya shiga gidan. Mummy tana kuka tana bashi baki tare da alƙawarin gobe Yaya Babba zai mayar da shi. *** A wannan rana ko gyangyaɗi Taj bai samu ba. Kuma haka ta kasance a ɓangaren Baba Yaya da Alhaji da Inna. Don bayan ta dawo gida da ya sanar dasu hukuncin da ya ɗauka har suma tayi. Gidan ya rikice da koke koke. Iyalin Alh. Hayatu su ka taru su ka juya masa baya daga matansa har ƴaƴansu. Hakan kuwa bai yi masa komai ba face ƙara tsanar turbar da Taj yake son bi. Da kuma abin da Yaya Babba yayi masa. Washegari duka ƴaƴan Marigayi Alh. Sule su ka taru a gidansu dake Soron ɗinki inda mata guda ɗaya da ta rage musu a matsayin uwa take. Ita ce mata ta uku cikin matansa. Zama irin na da yasa ita da ƴaƴan sauran abokan zamanta su ka cigaba da zumunci tamkar lokacin da mahaifinsu yake da rai. Ita Yaya Babba ya kaiwa ƙarar Alhaji tun a jiya. Tasa aka kira mata kowa dake kusa. Amma ma dake nesa dama ta iso kwana huɗu da su ka wuce hutun shekara. Tana Abuja da niyar tahowa bayan sati guda. Amma kiran Gwaggo yasa ta biyo jirgin ƙarfe tara na safe. Bayan an zazzauna Yaya Babba ya mayar da iya abin da ya faru ta ɓangarensa. Tun daga wayar da Mama ta yiwa Mummy da suna India har zuwa yadda ta kasance jiya. Aka tambayi Alhaji sai kaɗa baki ya yi ya ce bashi da abin sake tofawa. "Yanzu Hayatu har kayi girman da za ka nuna mana iko akan ƴaƴanka?" Yayarsa mace mai bin Yaya Babba wadda daga ita sai shi tayi maganar da ƙwalla a idonta "na zata za ka yi farinciki da zumuncin da muke dashi wanda mu ka ɗora ƴaƴanmu da jikoki. Kai ba abin alfaharinka bane ace ɗanka yaje neman sauƙi a wajen ɗan uwanka? Shi kuma bai bashi kunya ba ya share masa hawaye." Ransa sosuwa ya yi da har suke ganin laifinsa. "A cikinku akwai wanda zai bar ɗansa namiji ya ɓata lokaci a jami'a yana koyon girki da yadda ake sarrafa kayan abinci?" "Me zai hana tunda ba haramun bane" wani ƙaninsa ya amsa kai tsaye. Wasu duk su ka amsa da za su iya. "Wallahi ƙarya kuke yi. Ni ban taɓa ganin namiji a arewa mai sana'ar abinci ba wanda baya abin mata." "Saboda al'adar bahaushe ta mayar dashi aikin mata kaɗai ba. Amma a kudu da sauran ƙasashen duniya maza nawa ne su ka yi fice da girki kuma in ba faɗa su ka yi ba sai ka rantse ma ƴan dambe ne." "Ni yanzu me kuke so daga gareni?" Gwaggo ta dube shi. Haƙiƙa akwai ciwo wurin iyaye idan ƴaƴansu su ka ƙi bin umarninsu. Gashi mutum mai aƙida wanda baya son ko yaya aga gazawar nasa. Kuma dole yanzu yaga kamar an haɗe masa kai. Don ko ita idan zata yi rantsuwa ta san babu kaffara da matuƙar wahala in ka cire Yaya Babba da Amma a sami mai barin ɗansa namiji ya yi wannan karatun. "Hayatu kaje gidan Jafaru ka ɗauko ɗanka maganar nan ta mutu daga yau." "Ai nayi rantsuwa Gwaggo. Akan Taj wallahi ba zan yi kaffara ba." Cikin fushi Yaya Babba yace "Nima kuma wallahi ba zan zama silar raba ɗa da iyayensa ba. Idan rashin albarka ya bishi a dalilinka duniya ni za ta zaga." Gwaggo dai gajiya tayi da basu baki ta kama hawaye tana cewa don babansu baya duniya shi yasa su ke yi mata haka. Amma da bata ce uffan ba tun farkon zamansu ce ta katse musayar yawun da suke. "Gwaggo ki zama shaida. A gaban kowa duk sun yi rantsuwa ba za su zauna da Taj ba. To ni ina so kuma dashi zan koma. Zan taƙaita hutuna mu baku wuri ku sha iska." Kallonta kowa ya kama yi kafin kuma mazan su nuna a gidansu zai zauna. "Jamila zai bi domin babu amfanin ya zauna a nan kowa yana yi masa kallon wanda uba ya kora." Gwaggo ta kashe maganar. "Gwaggo ina so ki min shaidar ƙarshe. Yadda kowa baya son a shiga abin da ya shafe shi da đansa to nima kada wanda ya shigar min gonata. Zan yiwa Taj abin da zan yiwa ɗan cikina tsakani da Allah." Kafin kowa ya sake magana ta tashi ta fice daga gidan gabaɗaya. Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Da kaɗan da kaɗan zance ya zaga zuri'ar gidan kowa ya san me yake faruwa. Wasu na goyon bayan Taj wasu na ganin laifinsa. Inna da Mama sun fi kowa shiga tashin hankali. Sai Kamal da ya kwanta ciwo sosai. Alhaji kuwa tunda Amma tace za ta ɗauke shi ya san sai abin da Allah Yayi. Bai fasa ganin laifin Mama ba akan zama mutum ta farko wajen haɗa shi da ƴan uwansa da kuma raba shi da ɗansa. Irin abubuwan da ya dinga yi mata sai da ya kaita ga yin yaji. Tana ficewa kuwa Inna ma ta kama gabanta. Butulci ne zai sa ta cigaba da miƙe ƙafa a gidan da mai son ɗanta ta kasa zama. Hajiya da Umma da basu tafi ba ba daɗinsu Alhaji yake ji ba. Abu sai da ya kai anyi zama na musamman da dangin kowannensu. An sasanta dai amma tunda Taj ya bar gidan kaso mai yawa na walwalar gidan ya kau. *** Tafiya Amerika yana buƙatar visa da dogon cike ciken takardu wanda Amma take ganin ɓacin lokaci ne. Saboda haka ta nemi visar India da passport ɗinta na ƴar ƙasa na Amerika. Nan da nan ta samu. Cikin sati biyu suka bar ƙasar. Dama Abuja ta koma dashi. Ita ta kai shi makaranta ta jira komai ya kammala bisa tsari. Zai cigaba da aikinsa a wurin Paaji a duk ranar da bashi da lecture kamar yadda ya yi lokacin degree ɗinsa na farko. Da za ta tafi ta kawo kuɗi ta bashi. "Kada ka kunyata ni. Kada kuma kayi abin da zai ƙara girmama rigimar Yaya Hayatu da Yaya Babba. Ka kiyayi duk wani abu da Allah baya so. Shi kuma ba zai bari ka taɓe ba." Rufe ido ya yi yana kuka. Ta dungure masa kai "meye haka? Da Yaya Hayatu zai ga wannan kukan ai cewa zai yi abin da yake gudu ya faru." Dariyar dole Taj ya yi. Ta rungume shi tana rarrashi. Duk da yaji bambarakwai amma sai hakan ya sanyaya masa zuciya. "Bana son ragwanta. In shagwaɓa ce dai I will indulge you amma ragon namiji baya burgeni kaji ko?" Murmushi yayi. A rayuwarsa zai iya ƙirga sau nawa ya haɗu da Amma. Ya san tana da kirki amma bai san halayenta irin waɗanda yake gani yanzu ba. Uwa da uba ya samu a dunkule a tare da ita. Ta ƙarfafa masa gwiwa sosai sannan ta faɗa masa zata yi ƙoƙari kafin lokacin hutu tayi duk abin da ya dace domin ya sami visa. Wannan shi ne mafarin zaman Taj a Amerika. Ƴaƴan Amma sun yi aure. Su suna Minnesota babbar Anisa kuma tana aure a Florida. Iman kuma a Lagos take zaune da mijinta. Yayinda maigidan yake yawo tsakanin Nigeria wurin amaryar da ya yi bayan ya yi ritaya da Amerika. Sai ya kasance bayan Taj ya gama karatu shi da ita ne a gidan kodayaushe. Sun shaƙu matuƙa. Tana aikinta shima yana yi awani restaurant da ya yi fice a abincin Asia da Afrika. A wurin ma'aikatan wurin ya koyo nau'ikan abincin gargajiya na Nigeria na ƙabilu daban daban. Cikin ɗan lokaci ya yi suna sosai. Takanas aka zo aka gayyace shi gasar da ta ciwo masa wasu maƙudan kuɗaɗe bayan ya sami nasarar yin na biyu. Da kuɗin da kuma tanadinsa tun na India yake son buɗe mall a Kano. Rashin zuwansa gida bai hana shi mu'amala da ƴan uwansa da iyaye ba. Musamman yanzu da aka sami cigaban hanyoyin sadarwa. Suna yawan bidiyo call ana ganin juna musamman yayin aure da haihuwa. Alhaji ne kaɗai baya ɗaukar wayarsa har yanzu. Amma ta tilasta masa tura masa saƙon gaisuwa kullum rana ta Allah na kar ta kwana. Sai dai da yake zuciya bata da ƙashi, ya riƙe uban a zuciyarsa. Ya ɗora masa alhakin raba shi da ahalinsa. Da nesanta fuskarsa da ta mahaifiyarsa. Shi yasa ya ƙudurcewa ransa ba zai sake taka gidansu ba sai Alhaji ya neme shi da kansa. *** Hutu ya ƙare lafiya. Ranar da ƴan makarantar kwana za su koma Hamdi bata samu ta runtsa ba. Tana fama da tararrabin yadda Ummi za ta kwance mata zani a kasuwa. Duk siyayyar da Abbanta ya yi mata babu abin da ya burgeta. Rashin fara'arta ya dami Yaya har sai da ta kai ga yi mata magana kafin Abba ya kaita tasha. "Sai da aski ya zo gaban goshi nake ganin alamun rashin son komawa a tare dake Hamdi." Zee ma ta ce "Ya Hamdi ko kukan bodin za ki fara a term ɗin ƙarshe? In faɗawa Abba a dawo dake makarantarmu?" Duka Hamdi ta kai mata da wasa a ƙoƙarinta na danne damuwarta. Bayan fitar Zee daga falon Yaya ta muskuta kusa da ita. "Hamdiyya." "Na'am" ta amsa a raunane. "Na san baki so zuwan iyalin Maje gidan nan ba tunda aka zo da Ummi." A zabure ta kalli Yayan da tsananin mamaki. Ita kuwa tayi murmushi. "Kina mamakin yadda aka yi na sani?" Ta gyaɗa kai. "Kin guji gida saboda kada a san waye mahaifinki. Yanzu kuma gashi an zo an ganshi har gidan kina tsoron kada asirinki ya tonu." "Yaya..." ta soma faɗi cike da kunya. "Ki koyi son abin da Allah Ya baki sai Ya ninka miki da wanda baki zata ba." Yawu ta haɗiya "to." Yaya ta cigaba da cewa "Ban taɓa nadamar auren mahaifinku ba saboda bai bani wannan dalilin ba. Irin kulawar da muke samu daga gare shi wasu masu kuɗin sai sun yi kishi da mu. Zaman lafiya yafi zama ɗan sarki. Hamdi sandar hannunka da ita kake duka kin ji. Hangen ta hannun wani ba naki bane don baki sani ba ko duk ƙaya ce ko bata ma da ƙwari." Numfashi ta sauke ta sadda kai ƙasa ta bawa Yaya haƙuri. Ita kuwa da yake ba mace bace mai riƙo ko son ayi ta nanata zance sai cewa tayi a bar maganar. To a haka Abba ya dawo shabiyun rana ya sanar dasu Baba Maje na nan tafe zai kai su makaranta tare da Ummi. Ya ƙare da faɗin, "Tare zamu tafi." Albarkacin Yaya dake zaune a wurin da nasihar da tayi mata ɗazu ne kawai ya hanata fasa ihu. Ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi. Addu'a kawai ta kama yi Allah Ya kawo sanadin da zai fasa binsu don gudun kada ya dinga sakin baki a gaban Ummi. Addu'arta ta ƙarbu domin an fara zuba kayanta a motar Baba Maje sai ga wani dattijo yana sallama da Abba. Kana ganinsa baka buƙatar ƙarin bayani za ka gane ba mutumin kirki bane. Shadda ce yellow shar a jikinsa tana uban ƙyalli ga hula ya harbo gaban goshi irin na tsofaffin ƴan duniya. Taunar cingam yake cakakal-cakakal yana karkaɗa muƙullin mota. Ga wata uwar yatsina yana faman yi a yayinda idanunsa ke ƙarewa layin gidan kallo. "Maje anya ba za ku tafi ba kuwa? Ban san me ya kawo shi ba amma ina jin ba abu bane da zamu ƙare da wuri." "Ba dai abokin sana'arka bane ko?" Baba Maje ya tambaya don yanayin mutumin babu sha'awar son kusanci da shi. "Agent ɗin wanda nake hayar gidan abincina ne." "To ko dai mu jira?" Baba Maje ya sake cewa da ƴar damuwar yadda yaga abokin nasa kamar baya cikin nutsuwa. "A'a, ku tafi kawai." Godiya ya yi masa akan biyowa ɗaukar Hamdi sannan ya juya wajen mutumin su kuma su ka shiga mota. Akan hanyarsu Baba Maje yayi ta ƙoƙarin haɗa hira tsakanin Ummi da Hamdi. Da yake Ummi akwai wayo sai ta fishi jan Hamdin a jiki. Ya kuwa ji daɗin hakan sosai. Abba da baƙonsa kuwa ba komai su ka tattauna ba illa ƙarin kuɗin haya da aka yiwa gidan abincin nasa. Kuɗin ya yi biyun abin da yake biya. Ya fara roƙon alfarma mutumin ya ce sai dai ya tashi. Dama kuma ya samo mai biyan wannan farashin ne. Ya kuma san babu yadda za ayi Abba ya biya. Shi ne ya zo masa da dabara. "Idan na tashi yaya zan yi da iyalina? Don Allah ka rage min wani abu." "Sati biyu zan iya baka ka tattare komatsanka ka tashi. Idan kuma kuɗin sun samu kafin nan sai ka kawo a sabunta kwantiragi." Yana gama faɗin haka ya shige motarsa ya tada ƙura ya bar unguwar. Abba ya koma gida da sanyin jiki ya labartawa Yaya halin da ake ciki. *** "Ki fara kai min nawa kayan ɗaki don akwai abin da nake buƙata yanzu a ciki." Ko minti biyar Baba Maje bai yi da barinsu da kayansu da za su kwashe su kai hostel ba Ummi ta rikiɗa ta koma annobar ƴan FGC. Wani irin kallon mamaki Hamdi ta bita da shi "ban gane ba." "Au...kin daina jin hausa ne saboda mun shigo school? To jirani a nan. Zan aiko miki da yaren da za ki fahimta." Da tafiyarta ta ƙasaita ta wuce ta bar Hamdi a tsaye. Ita kuma ganin ta tafi ta fara ɗaukar kayanta ta nufi hostel ɗinsu. Tana ajiyewa ta koma da sauri domin ɗebo sauran sakamakon garin da hadari saboda damina da ta tsaya sosai. Da isarta ta iske wata yarinya da ta tabbatar cikin ƴan koran Ummi take. Wata tsadaddiyar waya ta fito da ita daga ƙasan hijab ta yafito Hamdi da hannu. Da taga bata matso ba kawai sai ta danna wayar. Nan da nan wurin ya karaɗe da muryar Abba inda yake cewa (Altine kece haka? Ikon Allah) da muryar nan tasa da ko ita ƴarsa bata so. Hankalinta ya yi masifar tashi. A take ta jiƙe da wani irin gumi. Ta miƙa hannu a firgice za ta karɓe wayar sai yarinyar ta ja da baya. "Ummi ta ce ki kwaso mata kayanta idan ba haka ba duk makarantar nan kowa sai ya gani" "To" ta amsa da sauri tare da duƙawa ta fara ɗaukar kayan. Yarinyar ta yatsina fuska "no, ta ce da ɗai-ɗai za ki ɗauka." "To" Hamdi ta sake amsawa da rawar jiki. Banda akwatuna biyu akwai manyan ledoji uku. Haka tayi sawu biyar tana zuwa hostel ɗin su Ummi. Bata ganta ba sai da ta kai ledar ƙarshe ta sameta zaune akan gadonta. "Ina za ki baki jera min ba?" Cak ta tsaya ta dawo da sauri ta jera kayan a kwanar Ummin. Ƴan ɗakin su ka zuba musu ido suna ganin ikon Allah. Bayan ta gama a gadarance Ummi ta ce mata gobe ta zo da wuri ta ɗebo mata ruwa. Ta amsa kawai ta fita. Da ta fita ko ganin hanya bata yi saboda hawayen da ya cika mata idanu. Da haɗa hanya ta isa inda sauran kayanta su ke ta kwaso. An soma yayyafi ga iska mai ƙarfi. Saboda haka akwatin da jakar sun yi buɗu-buɗu. Zuciyarta a ƙuntace ta tafi nasu hostel ɗin. Ajiye kayan kawai tayi ta hau gado ta dunƙule jikinta tana kuka. Nan da nan wurin ya cika da mutane ana tambayarta me yake faruwa amma ko ɗago kai bata yi ba. Sai wata ce da taga yadda ta dinga ɗiban kayan Ummi ta basu amsa. "Wannan hutun da alama ita Ummi Maje za ta takurawa." Alhini da tausayi su ka dinga nunawa bayan ta faɗa musu me ta gani. Abin bai yi musu daɗi ba domin kuwa Hamdi bata rigima. "Lallai Ummi bata da sauran rabo don ko mu masu baki da take zalinta bamu yafe ba balle mara baki irin Hamdiyya." Wadda tayi maganar tana rufe baki wata ma ta kama. Su ka taru su ka gama ɗebe mata albarka (mu guji irin waɗannan laifukan da bama ɗaukarsu a bakin komai. Babu wani haƙƙi abin rainawa) sannan su ka watse. RAYUWA DA GIƁI 7 Batul Mamman💖 Sanarwa In sha Allah post zai dinga zuwa ranakun Litinin zuwa Juma'a. *** Ummi dai baje kolin rashin mutumcinta tayi akan Hamdi har ya kasance sauran ɗalibai suna samun sararawa. Kowanne aiki Hamdi, kowacce bola da shara ma ita ɗin dai take nema. Wanki harda na su pant ita take mata. Su ɗebo ruwa da kwafar note dama tuni ta daina saka wasu. Kuma ko da wasa Hamdi bata taɓa faɗin wata kalmar neman sauƙi ba. Komai Ummi ta ce 'to' ce amsar. Ita dai burinta ta bar makarantar ba tare da kowa ya san ko waye mahaifinta ba. Da yake a cikin hutun da su ka aka yi jarabawar JAMB, yanzu ƴan kwanaki su ka rage kafin a fara WAEC. Kowa ya duƙufa da karatu ba ji ba gani. Waɗanda basu ɗauki karatun a bakin komai ba irinsu Ummi kuwa shagalinsu suke yi. Ranar wata laraba da safe aka tashi makarantar babu ruwa. Abin ka da lokacin zafi. Tsakanin April da May a garin Kano dama ba a cewa komai. Rijiyar makarantar mai dama dama ba a samun komai sai wani ruwan dauɗa wanda zai iya sati bai kwanta ba. Kowa ya shiga damuwa don ko darussan aji ba a shiga ba. Ga ɗan karen zafi ana ta zufa. Principal tun safe ta fice sai wajajen shabiyu ta dawo da tankokin ruwa har bakwai a bayanta. Yara sai murna. Aka umarci malamai da su kula da ɗaliban wajen bin layi ta yadda kowa zai samu. Sannan an ja musu kunne babu mai ƙarɓar ruwa sau biyu. Kuma bokiti biyu kaɗai za a cika wa kowa saboda kada wasu su rasa. Layi layi aka jera ɗaliban na ajujuwansu. A sammakon Hamdi ita ce ta talatin da huɗu a layinsu. Kafin a zo kanta rana ta gama dafa ta. Ana zuba mata taji wani sanyi ya ratsata. Ta ɗauki bokatan hagu da dama ta wuce ɗaki. Tun kafin ta isa bakin matattakalar hostel ɗin ta hango Ummi da ƙawayenta a zaune kan dandamalin wurin suna ta hayaniya ana dariya. Fuska a haɗe Ummin ta tarbeta da ta ƙarasa. "Kin daɗe a layi gaskiya. Ke ko irin turereniyar nan baki iya bane?" Take takenta Hamdi ta gane sai dai ta riga ta yiwa kanta alƙawarin ko me zai faru ba za ta bata ruwan da ta wahala wurin samu ba. Jikinta gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mata. Ga ƙishi ga yunwa. "Ban iya ba." "Mtswww, wuce ki kai min ruwan in samu nayi wanka kafin a gama abinci." Wata zaƙaƙura ta ce "Ummi kin ce fa nima za ki sa ta ɗebo min." "Ki bari ta juye min mana." Ta cewa wadda tayi maganar a wulaƙance. Juyawa Ummi tayi taga Hamdi ta ajiye bokatan ta sarƙe hannu a ƙirji. Rai a ɓace ta ce mata "Ɗauki mu tafi mana." "Ki je ki bi layi don babu wanda za a zubawa sau biyu. Har ticking suna ake yi." "To sai ki san yadda za ki yi. Ni ki wuce ki zuba min zafi nake ji." Hamdi ta rasa daga ina take jin wani ƙwarin gwiwa kawai ta ce "naga kamar baki gane ba. Wannan ruwana ne. Ki je ki ɗebo naki." Wata uwar shewa Ummi tayi tana dafa ƙirji "dani kike? Har kin manta abin da zan iya yi miki idan ki ka ɓata min rai?" Tunawa da alamun mutumcin su Iyaa tayi sai take ganin kamar duk haukan Ummi ba za ta fitar da bidiyo ɗin ba. "Kin daɗe baki nunawa duk makarantar nan waye ubana ba." "Kanbu, dani kike?" Ummi ta faɗi cike da mamaki. Sai kuma ta fasa faɗan ta ce ƙawayenta su ɗauko bokitin. Suna kai hannu Hamdi ta tare kayanta ta hanyar durƙusawa a gaban bokatan ta tarosu da hannuwanta. "Wallahi ba zan baki ruwan nan ba." Mamakin me Hamdi ta taka a yau ne ya kama Ummi. Taga gara ta nuna mata idan tace za ta yi abu lallai babu fashi. Waya ta ɗauko daga aljihun wandonta na kayan prep. Gaban Hamdi na faɗuwa amma idonta yau ya ƙeƙashe. Tana ji kamar kowa muryar Abbanta ta ƙarade wurin. Kan kace meye wannan ɗalibai sun taru suna jin bayanin Ummi na cewa wannan zuƙeƙiyar muryar fa ta mahaifin Hamdiyya Habib ne wanda ya kasance ɗan daudu. Aka dinga tururuwar leƙa bidiyon ana cewa ga kama nan. Kallon Hamdi aka fara ana zunɗe tayi kamar bata jinsu duk yadda ranta ke suya ta duƙa za ta ɗauke ruwan sai taji Ummi tayi wata maganar da ranta ba zai iya ɗauka ba. "Mamanta kuwa cangal ce mai ƙafa ɗaya da kwata" ta cilla ƙafa ɗaya ta banƙaro ƙirji ɓari ɗaya "idan tana tafiya sai ka rantse Awilo ne zai yi rawar waƙarsa." Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Hamdi ta iya faɗi don dariyar da aka tuntsire da ita a yayinda Ummi ke kwatanta tafiyar Yaya ta mugun baƙanta mata rai. Sakin bokiti guda tayi ta ɗaga ɗayan da hannu biyu ta juye shi tas akan Ummi. Kowa kuma sai ya bar abin da yake yi aka tsaya kallo. Ummi bata gama dawowa hayyacinta ba Hamdi ta cakumi wuyanta ta soma kai mata duka. Dambe sosai ya ɓarke a tsakaninsu inda Hamdi ta dinga tumurmusata da ƙasa. Tunda kayanta a jiƙe suke sai jikin ya yi futu-futu kamar an tonota daga rami. Ƙawayen Ummi da suka ji ta fara neman ceto ne su ka ƙwaceta sannan su ka yiwa Hamdi taron dangi. Mutum uku ne su ka danneta a ƙasa suna duka. Ƴan hostel ɗinsu na ganin haka su ma suka saka hannu wurin kai mata ɗauki. Wurin ya hargitse aka dinga ɓarin ruwa ana doke doke. Prefects ma basu iya yin komai ba sai malamai da aka kira. Duk wadda take waje a lokacin da ƴan kallo da ƴan dambe aka tasa ƙeyarsu sai ofishin Principal. Baiwar Allah ji tayi kamar ta fasa ihu da taga yadda yaran nan su ka ɓannatar da ruwan da ta wahala wurin nemowa. Ba'asi guda ta nema shi ne su waye su ka fara faɗan. Aka nuna Hamdi da Ummi. Ta karɓi bulala kuwa ta zane musu jiki ta zauna tana haki. Mataimakinta ne ya karɓi shari'ar saboda abin mamaki yau Hamdi yake gani kuma wai ita ta fara faɗan. Duk yadda aka yi a sanin da ya yiwa shaiɗanci na Ummi ya san laifin ba zai wuce nata ba. Masu tarar aradu da ka ya haɗa da displine master sannan ya zauna sauraron abin da ya haɗa yan matan. Ummi ta kitsa ƙarya da gsskiyarta ita kuwa Hamdi ko tari bata yi ba. Mutumin nan ya kaɗa ya raya amma ƙememe taƙi magana. Sai ajiyar zuciya kawai take saukewa. Waje ya tura su ya tattauna da malamai. Kowa ya riga ya san halin Ummi da Hamdi. Duk da haka tunda Principal tayi rantsuwa ya ce a dubo lambobin iyayensu a sanar dasu ana nemansu washegari Juma'a. Duk wanda bai zo ba ƴarsa ba za ta yi jarabawar da za a fara ranar litinin ba. Hamdi a yau ko a jikinta. Ta riga ta sanyawa zuciyarta ɓoyon uba bashi da wata fa'ida. Da tun farko ma an san shi Ummi bata isa tayi amfani da wannan damar akanta ba. A ɓangaren Ummi ne dai hankalinta ya nemi gushewa. Ƙaryarta ce za ta ƙare nannda ƴan awanni. Kiran iyayenta ba baƙon abu bane ko kaɗan. Inda gizo ke saƙar dai shi ne wani Sugar Daddy ɗinta ne yake zuwa a matsayin kawunta. Wai ita marainiya ce. Baba Maje da ke kawota kuma yaron kawun nata ne. Har ila yau baban nata yana karɓar wayarta duk ranar komawa makaranta tun da aka bata wayar. Wadda take amfani da ita ba tare da sanin hukumar makarantar ba wata ƙawarta take bawa ajiya. Babbar waya ce da wani saurayin daban ya saya mata. Tun kafin a dawo taje gidansu yarinyar ta tura wannan bidiyo ɗin da ta yiwa Abban Hamdi. Idan ta kuskura ta bari aka kira wani ba mahaifinta ba Hamdi za ta sami damar da ta zarce wadda ta samu ta cusguna mata. Gumin da ya tsatstsafo mata ta yarfe kafin ta tashi da rawar jiki taje ta sanar da Vice Principal numbar da zai kira a madadin wadda su ke da ita. *** Ɗokin da ya kama shi tunda aka yi sanarwar jirgi zai sauka nan da mintuna kaɗan ya bashi mamaki. Belt ɗin da aka ce fasinjoji su ɗaura ya gyara gami da leƙa tagar jirgin. Garin Kano yake gani da tsakar rana ƙarfe biyu da rabi. Tsirarun bishiyoyi da yalwar ciyayin damina sai gine gine marasa tsayi ba kamar inda ya baro ba. Tayoyin jirgin na dira ƙasa sabon yanayi ya baƙunce shi na farinciki da tarin fargaba. Uwayensa da ƴan uwa tun a waya su ke nuna farincikinsu. Alhaji ne damuwarsa. Zai karɓe shi ko kuwa yanzu ma zai cigaba da nuna masa ƙyama kamar wanda yake aikin saɓon Allah? * Kafin kowa ya kula wata matashiya dake tsaye tare da iyalan Alh. Hayatu Sule ta hango Taj ta cikin ƙofar gilas. Kyakkyawan saurayi ne wanda duk hangen mace indai ta same shi ta sake ɗaga ido neman wani dole a sanyata a sahun marasa wadatar zuci. Yana kama da ƴan uwansa amma akwai wani abu dake tattare dashi wanda ya bambanta shi dasu da take iya gani. Ba hasken fata bane domin wasu cikin ƴan uwan nasa sun fi shi haske. Haiba da cikar halittarsa su ne suka fi komai ɗaukar hankalinta. Tana can duniyar saƙe saƙe bata kula da yadda ƴan uwan nasa da ƴaƴansu su ka bar wurin ba domin tararsa sai daga baya. Idanu kansu su ka dawo ganin yadda ake pasin-pasin wajen rungumar Taj. Gashi taron mata don Ahmad da Kamal ne kaɗai maza in ka cire jikokin gidan da ba wani sabo suka yi dashi sama da waya ba. Bishir da Abba su na makaranta. "Aunty Salwa mu je mana." Wani yaro ne ya yi maganar yana jan hannun matashiyar budurwar da Taj ya sacewa zuciya farat ɗaya. Murmushin jin kunyar kanta tayi ta kama hannun yaron su ka matsa kusa dasu. Yaron ya saki hannunta ya koma wajen Ahmad yana cewa ya ɗaga shi zai ga Uncle Taj. "Daddy ni bai ganni ba. Ɗaga ni sama." Kamal ne ya ɗaga yaron ya miƙawa Taj. Ya karɓe shi ya rungume yana sumbatar kumatunsa. "Babana da kansa." Yaron ya girgiza kai "Uncle Taj sunana Hayat." "Ba Hayatu ba?" Taj ya ce da alamun mamakin da yasa yaron saurin cewa "Hayat yafi daɗi." Dariya kowa yayi sannan Ahmad ya ɗan turo budurwar nan gaba. "Ga Salwa ku gaisa." Taj ya sakar mata murmushi domin kuwa ƙanwar yayansa Ahmad ce da su ka haɗa uwa. A yanzu haka sakamakon karatu da ya kawota Kano daga Bauchi garin da mahaifiyar tasa ta sake aure shi ne take zaune a gidansa. Shekararta ta biyu kenan a Kano kuma iyalin Alh. Hayatu har matansa basu nuna mata wani abu da zai sosa zuciyarta ba. Ƙanwar ɗansu ita ma ƴarsu ce. Shi Ahmad matarsa ɗaya da yara biyu. Hayat da ake kira da sunansa bisa umarnin Alhaji sai jaririyar da ko arba'in ɗinta ba ayi ba mai sunan Mama wato Aisha. Ɗunguma su ka yi a motoci huɗu su ka nufi gida. Mazan motarsu ɗaya su kaɗai. Kamal ya yiwa Taj bayanin cewa sun canja shawara zai zauna a gidan Ahmad har lokacin komawarsa. Jikinsa a sanyaye ya tambaye su "Alhaji ya ce kada na zauna masa a gida ne?" "A'a" Ahmad ya faɗi da sauri. "Yaya ka faɗa masa gaskiya mana." Cewar Kamal dake tuƙi "ɓoyewar bata da wani amfani." "Faɗa min me ya ce Happiness." Tiryan tiryan kuwa Kamal ya faɗa masa yadda Alhaji yaje ɓangarensu har ɗaki ya ce yaga saƙon Taj na tahowa buɗe gidan abinci. Ba zai hanasu mu'amala da ɗan uwansu ba amma indai da niyyar cigaba da saɓa masa ya dawo ya nemi wurin kwana. "Amma ya amince ka shiga gidan ka gaishe da su Hajiya. Kawai dai kada ka bari ku haɗu." "Zan zauna a hotel." Dukkaninsu kallonsa su ka yi. Ba kuma don abin da ya ce ba, yadda muryarsa ta fito kai ka san ba ƙaramar dauriya ya yi ba. A shaƙe take da wani irin rauni daga zuciyarsa. "A gidana za ka zauna. Tun jiya nasa Salwa ta gyara maka ɗaki." Ahmad dake baya ya zura hannu gaban motar ya ɗan bubbuga masa kafaɗa. "Ba zan zauna na takura iyalinka ba. Infact mutumcina ma zai zube. Kawai bamu taɓa haɗuwa ba sai da aka koreni daga gida for the second time." Dariya Kamal ya yi "zaman hotel ɗin ba matsala bane amma ba mutumcin aljihunka bane gaskiya a garin da kake da gidan ƴan uwa sama da hamsin da za su so zamanka tare dasu." Kamar shi ya kar zomon, Taj ya ɗaure fuska ya ce masa "kawai ka faɗi abin da yake ranka. Kana tsoron kada naje ace na fara bin mata ko?" "Ba a ji mutuwar sarki a bakina ba, amma dai kai da kake kan tsini idan ka ƙara da kwanan hotel ban san yaya za ku kwashe da Alhaji ba." "Allah ni ba ɗan isk* bane. Saboda tsoron kada Alhaji ya yi min baki watarana na lalace ko girlfriend na kasa yi." Taj ya amsa defensively. "Daga budurwa sai lalacewa Taj?" Cewar Ahmad, shi da Kamal su na dariya. Shi kuma Kamal ya ce "dama me za kayi da busassun turawan nan da ba su da gaba da baya?" Haɓa Taj ya riƙe yana kallonsa kafin ya ce "Yaya kaji irin zancen banzan da Happiness yake yi ko? He is long overdue for marriage." "Da za ku yi auren maybe da ka samu daidaitawa da Alhaji." Hirar tasu sai ta koma ta dacewar Kamal da Taj su nemi mata su yi aure haka nan. Da haka su ka isa gida. Sai dai kafin maigadi ya buɗe musu gate motar Alhaji ta tsaya a bayan tasu. "Alhaji ne" Ahmad ya faɗawa Taj. Zuciyarsa ya ƙarfafa ya fita daga motar duk da tunin da yayunsa ke yi masa akan gargaɗin Alhajin na baya son ganinsa. Da sassarfa ya isa bakin motar da gilasanta duka baƙaƙe ne. Ba a sauke ko ɗaya ba a ciki amma ya tabbatar daga cikin ana ganinsa. Direba ke tuƙin motar amma da dishi-dishi yana iya hango Alhaji zaune a baya. Ya taka har bakin tagar ɓangaren nasa ya durƙusa cike da girmamawa. "Sannu da zuwa Alhaji." Tun a hanya jikinsa dama ya bashi zai ga ɗan nasa. Tunaninsa ne ma ya hana shi gama uzurin da ya fitar dashi. Yanzu da yake ganinsa kewar Taj ɗin ta mamaye zuciyarsa. Idanunsa su ka tara ƙwallar da yake jin abin kunya ne a ganshi da ita. Saboda haka bai ɓata lokaci ba wurin umartar direbansa da ya yi ribas su bar wurin. "Alhaji ka daure ka saurari yaron nan don Allah." "Koma na ce!" Direba ya so yin musu Alhajin ya manta da dattijantakar mutumin ya daka masa tsawa. Wannan yasa shi danna accelerator bayan yasa giya a ribas da ƙarfi. Ƙura kuwa ta tashi ta baɗe Taj da yake durƙushe har lokacin bai motsa ba. Ba shi ya tashi ba duk da magiyar su Kamal da wasu cikin matan da su ka riga su dawowa daga airport. Anyi a idonsu ne saboda an buɗe gate. Kuma dama Kamal na yin horn su ka firfito tare da iyayensu. Ahmad ne ya ɗaga shi zai shiga dashi gidan ya cije ƙafarsa. "Mu je gidan naka." "Kaga su Umma fa a tsaye. Mu ƙarasa ku gaisa sai mu tafi." Kai a sunkuye Taj ya girgiza kai. "Wallahi ba zan shiga gidan nan ba sai ranar da mai shi ya kirani ciki da kansa." Motar ya kama zai buɗe Kamal yayi saurin danna lock da muƙullin hannunsa. "Kada kayi taurin kai. Don Allah ka shiga ciki." Kai Taj ya ɗaga ya hango Salwa a tsaye tare da sauran. Bai yarda ya haɗa ido da kowa cikin matan gidan ba ya ƙwala mata kira. "Salwa..." Gabanta ya faɗi, zuciyarta tayi wani irin bugu. Sai kuma wani irin ɗumi mai daɗi ya lulluɓe mata jiki da ta tuna sunanta kaɗai Taj ya ambata a wannan yanayin da yake ciki. Ƙafafunta kusan da ikon kansu su ka ƙaraso da ita gabansa. "Kai ni gidan Yaya a rickshaw (haka ake kiran adaidaita sahu a India)." Alamun rashin fahimta ya gani a tare da ita ya nuno mata guda da ya shigo layin nasu. Kai Ahmad ya girgiza domin hanata sannan ya umarci Kamal da buɗe motar. Da kansa ya tura Taj baya ganin ƙanin nasa ƙiris yake jira ya saki ƙwallar da ta rufe masa idanu. "Kai shi gida zan taho." Haka kawai ya ce da Kamal ya buɗe gaba ya ce da Salwa ta ɗauki Hayat su bi shi. Suna tafiya shi da sauran suka koma ciki. "Korarsa ya sake yi?" Umma ta tambaya da kukanta. "A'a. Ku shirya mu je gidana ku gan shi." "Me ya faru Ahmad?" Mama da Hajiya duka kuka su ke yi. Inna kuwa jingina tayi da ƙofar shiga gidan ta runtse idanunta. Da yake duk da mayafi su ka fito Ahmad buɗe motarsa da ya bari a gidan ya yi ya ce su shiga. "Alhaji zai yi faɗa Ahmad." Da mamaki mai haɗe da ɗimbin takaici Mama ta kalli Inna da tayi maganar baki buɗe. "Sau tari damuwar uwa da jajircewarta na taimakawa wurin ragewa ƴaƴa raɗaɗin hukuncin uba. Kina tsammanin akwai riba idan duka ku biyun kun juya masa baya? Ko kuwa kina ganin yin hakan wata gwaninta ce da Alhaji zai yaba?" Umma dama tafi kowa zafi kuma maganarta indai akan gaskiya ne ba kasafai take taunata ba. Jiki ba ƙwari Inna ta ce "ba haka bane." Umma ta ce "to yaya ne? Sama da shekara goma rabon da ɗanki ya sanya ki a ido zahiri. Banda ma Allah Yasa Takwara (da yake haka su ke kiran juna da Amma) jajirtacciya ce da tuni ɗannan ya bi duniya. Uwa da uba a raye amma kun bar masa wawakeken giɓi mai wuyar cikewa. Baku san ku yabi ƙoƙarinsa ko kuyi masa faɗan kuskure ba." "Kiyi haƙuri don Allah" Inna ta ce tana kuka sosai. "Magana ce ta gaskiya. Kin goyi bayan miji kun mayar da yaro marayan ƙarfi da yaji. Yau ko ɗan kafin Fatiha ya kawo muku gida wannan hukuncin ya yi tsauri, balle girki. Mene ne aibun girkin nan ne? Har mamakin ki nake yi idan kina sha'anin gidan nan kamar babu abin da yake faruwa." "Jamila ya isa haka don Allah. Na tabbata tana da dalilinta na yin duk abin da tayi tunda ita tayi naƙudar Taj. Ta fi mu son sa." Hajiya ma ta gwaɓa tata maganar. Kukan Inna ya sake tsananta da wannan rashin fahimta da abokan zamanta su ka yi mata. Ita fa tun lokacin da taga auren Mama yana girgiɗi a dalilin Taj hankalinta ya yi mugun tashi. Balle da aka zo sulhun nan ta fahimci ashe su Hajiya ma dake gidan sun daina girki. Wannan dalilin yasa ta sauke dukkanin tijarar da ta tanadarwa Alhaji. Domin tana da tabbacin muddin ya sallameta akan Taj su ma za su gwada masa rashin goyon baya. Ƙarshenta cikin fushi aurensu ya sami matsala. Indai ba butulci ba kuwa irin zaman da su ke yi a gidan bata jin ya kamata ta yi musu sakayya irin wannan. Zafin da taga sun ɗauka ne ya bats damar yi musu wancan bayani yadda za su fahimceta. "Kuna ganin rayuwar Taj za ta yi albarka idan sanadinsa gidan nan ya wargaje? Fushi irin na Alhaji nayi imanin sallamarmu duka lokaci guda ba zai yi masa wahala ba. Sai dai ya yi nadama daga baya. Sannan gabaɗaya yaran gidan nan da wuya su sake yiwa ɗan uwansu kallon mutumci. Da farin gashinmu a ka ace muna zawarci." Allah Sarki. Tana rufe baki Umma ta rungumota. "Ki yi haƙuri Abullen Alh. Hayatu. Shaiɗan yaso amfani da ɓacin raina ya haddasa mana fitina." "Sunan da ki ka kira ni dashi na mene ne kuma?" "Na ƙaunar rigimammen tsohon nan mana." Dariya su ka ji an kwashe da ita. Shaf sun manta da ƴaƴansu dake wajen a tsaye. Kowa da jan ido an sha kuka suke dariyar daidaitawar iyayen nasu. Da wannan kuma babbar ƴar gidan Yaya Bintu ta sanar da ƴan uwanta cewa babu masifa da za su bari ta shiga gidan sama da rabuwar kawunansu. Don haka kowa ya shirya abin da zai iya domin taimakawa Taj. Haɗin kansu kaɗai zai iya sassautawa mahaifinsu haƙƙin ɗansa da yake ɗauka. Zaman lafiya aka ce yafi zama ɗan sarki. Alhaji bai san cewa duk cikim alkhairansa na duniya yadda ya gina gidansa shi ne mafi girman arziƙinsa ba. Gashi yana neman ɓata abin sa da hannunsa. Motar Ahmad su ka shiga ya kaisu gidansa. Sai ga Taj ya manta da dukkanin damuwarsa da ya ganshi tsakanin uwayensa. *** Abba ya maimaita zancen da yaji daga Vice Principal yafi a ƙirga a zuciyarsa bayan sun gama waya. Abin ne bambarakwai wai namiji da suna Hajara. Ta yaya ma za a ce Hamdi tayi dambe har ta kai rashin zuwansa akan matsalar zai iya jawo mata kora? Hamdi ce fa. Yarinyar da ko a cikin ƴan uwanta lokacin ƙuruciya da wuya a kawo ƙararta. Damuwar da su ke ciki shi da Yaya akan matsalar tashinsa da aka yi daga wurin sana'a sai ta zama ba komai ba. Fatan wayewar gari kawai yake domin yaje ya ji me yake faruwa. Sai dai kuma hantsi na soma leƙowa yaji wani irin tashin hankali. Da hankalinsa ya riga ya san yadda yaran ke kunyar nuna shi musamman ita Hamdi. Shin za ta yi maraba da amsa kiran nasa ko kuwa? RAYUWA DA GIƁI 8 Batul Mamman💖 *** Zazzaɓin gaske ne ya kama Ummi tun bayan ta saurari wayar Vice principal da mahaifinta. Aikin gama ya riga ya gama. Bayan ya ajiye wayar wani irin kallo ya yi mata ya jinjina ƙarfin halinta. Sannan ya ƙara tabbatarwa mace abar tsoro ce komai ƙanƙantarta. "Wannan mutumin shi ne mahaifinki Ummi?" Kai a ƙasa ta ce "eh." "Wanda yake zuwa kuma ya kuke da shi? Kuma me yasa ki ka zaɓi faɗin gaskiya yanzu?" Shiru tayi babu amsa tunda Hamdi ma taƙi magana me zai sa ta fara? Rai a ɓace ya ce "To kuwa ki kwana da sanin cewa yau ce ranarki ta ƙarshe a makarantar nan. Don ban ga wani dalili da zai hana a kore ki gobe ba ko da kece mai gaskiya. Sannan dole zan kira shi domin a warware komai gaban mahaifin naki." Yanzu ma kasa cewa komai tayi sai faman saƙe-saƙen neman mafita. Sannan a gefe guda babu irin ashar ɗin da bata saukewa Hamdi ba. Da farko ta san kawai jindaɗin samun mai yi mata bauta a makaranta tayi da sanin sirrin Hamdi. Yanzu kuwa wata irin tsana ce da za ka ji komai ma za ka iya yiwa mutum take ji akanta. Har lokacin bata saduda ba don tana jin da Hamdi tayi mata biyayya ta bata ruwan nan da bata ga wannan lokacin ba. Haɗuwarta da Baba Maje gobe ba ƙaramar tarzoma zai tayar ba. "Ki tashi ki fice min daga office nace." Tsawar VP ta dawo da tunaninta inda take. Ta miƙe za ta fita sai kawai wani tunani ya zo mata. Guntun murmushi ta saki wanda har ga Allah sai da ya VP ɗin tsoro da shakku akanta. Wurin ƙawarta konace babbar ƴar korarta Widad taje da saurinta. Sun gama nasu punishment ɗin na yau sai kuma washegari da ake sa ran samun ruwa. Za su wanke banɗakunan makarantar kaf har na malamai. Ga kuma sharar harabar makaranta da cire ciyayi. Widad na ganinta ta tashi zaune daga kwanciyar gajiyar da tayi. Ummi ko kallon arziƙi bata yiwa ciwon dake babban yatsan Widad na ƙafa wanda taji a wurin faɗan ɗazu ba. Kuma ta gan shi sarai amma ba shi ne a gabanta ba. "Bani wayarki in kira Uncle B" "Kuna can aka zo inspection ɗin bazata tun bayan an nuna wayarki a wajen principal. Yau wayar da aka fitar daga ɗakin nan tafi ashirin." Muguwar harara Ummi ta jefeta da ita sannan ta yatsina fuska ta ce mata "banza, me yasa ko a pant baki ɓoye ba?" "Korarmu aka yi waje bamu san dalili ba. Sannan aka yi searching ɗinmu da ɗai-ɗai." Widad ta amsa tana mai ɓoye zafin zagin da halin ko in kula da Ummin ta saba nuna mata. Plan ɗinta na farko ya faɗi tun kafin ta aiwatar. Dama niyarta ta faɗawa sugar daddy ɗin nata da take kira Uncle B idan an nemi numbarsa kada ya yarda ya zo. Shawara ta biyu kawai za ta ɗauka. Idan an zauna gobe kawai ta tada aljanu kuma duk yadda za ayi da ita kar ta yadda ta dawo daidai sai an koma gida. In ya so ko kasheta za ayi gara ayi a can. *** A hanyarsa ta zuwa tasha cikin adaidaita sahu Abba ya kira ƙaninsa a waya. Hankalinsa ne sam bai kwanta da zuwa makarantarsu Hamdi ba. Yana son kare martabar ƴaƴansa daga dukkan abin da zai iya janyo musu raini daga mutane. Ya tuna wani lokaci da Yaya Hayatu kamar yadda yake kiran Alhaji yayi masa wata magana a baya. "Habibu gaba nake jiye maka. Lokacin da za ka ji kunyar nuna kanka a wasu wuraren saboda kana ganin kamar darajarka bata kai ba. A lokacin ilimi ko rashinsa, talauci ko arziƙi ba su ne za su zame maka shamaki ba. Wannan mazantakar da kake gudu da Allah Ya karramaka da ita ce za ka so a baka aro ko na awa guda ne." Bai manta yadda ya murguɗa baki bayan wucewar Alh. Hayatu ba. Ya doka cinya harda tofar da yawu. "Aniyarka ta bika. Sa idawa, ana ruwa kuna ƙirgawa." Ya nuna ƙafarsa "wannan sayyara da Allah Ya bani babu inda ba za ta shiga ba sha Allahu." Ga ire iren ranakun sun zo. Ina ma ana mayar da hannun agogo baya. Da ya juya lokaci ya canja komai banda auren Jinjin. Matar da ta rufa masa asiri ta kuma bashi ƴaƴa mafi soyuwa a gare shi. Gaisawa su ka yi da ƙanin nasa da girmamawa sannan ya faɗa masa halin da yake ciki a kunyace. "Wallahi Yaya Habibu ka ganni a asibiti wani maƙocina ne babu lafiya. Daga shi sai matarsa ga yara ƙananu ta taho dasu. Basu da kowa a nan sai mu maƙota. Yanzu haka yayansa dake Zaria yana hanya. Tun asuba nake nan." "Ahhh, yi zamanka Abdulƙadir. Bari kawai naje." "Ka daina ɓoye kanka daga rayuwar yaran nan. Yau in dukkaninmu babu sai kai kaɗai shikenan sai ace zuri'armu basu da uba saboda abin da ya wuce?" Yayi maganar ne saboda ya saba ji daga yaransa cewa ƴaƴan yayan nasa suna kunyar alaƙarsu da shi. Bai ga laifinsu ba Fisabilillah. Amma kuma Allah da Ya haɗa alaƙar Shi Ya san yadda zai tafiyar da al'amura. Tayasu ɓoye kansa ba dabara bace tunda duk lalacewa da uba ake ado. Abba bai sake neman kowa ba ya tafi makarantar. Anyi sa'a yau shadda ya sanya ruwan madara, riga da wando harda hula. Da ya shiga makarantar bayan tafiyar minti arba'in tafiyarsa ya fara ƙoƙarin gyarawa. Sannan da zai tambayi masu gadi ofishin principal ya daddage ya kumbura murya. Amma kunne da idanu masu lafiya babu yadda za ayi su kasa fahimtar me ake son ɓoye musu. Basu dai nuna a fuska ba guda ya nuna masa hanyar office ɗin. A can gefe inda ake ajiye motoci ya ga wata kamar ta Baba Maje. Amma da yake baya tare da nutsuwa bai tsaya ƙare mata kallo ba. *** A rayuwa babu abin da yafi tashin hankali kamar a samu wani ya san sirri a kanka wanda baka so a sani. Kuma in anyi rashin sa'a ya dinga amfani da wannan damar wurin cusgunawa rayuwarka. A shekara shidan da Hamdi tayi a makarantar nan bata taɓa shiga matsanancin hali ba sai da Ummi ta fara blackmailing ɗinta. A jiya da abu ya fito fili waɗanda su ka sami ganin bidiyon nan su ka labartawa waɗanda basu gani ba, sai taji zuciyarta wasai. Abin ya matuƙar bata mamaki. Tayi zaton in an sani an tsokaneta za ta iya yin kuka. Sai gashi babu wanda ya tunkareta tunda aka ga abin da ta yiwa Ummi da kuma maganar da ta yaɓawa wata Metiron bayan ta dawo ɗaki. Da yake wasu manyan hankalinsu a ƙwauri yake, matar a gaban mutane ta tambayeta. "Hamdiyya da gaske ne babanki ɗan daudu ne?" A fusace ta amsa da "Eh, amma yafi uban wasu da yake zaman prison." Matar tayi matuƙar mamaki domin kuwa ba kowa ne ma ya san cewa mijinta yana prison ba saboda sata. Laƙwas tayi don babu halin sake magana saboda ƴan kallo sun sami sabon abin tattaunawa. Ƙarfe goma aka aiko kiransu. Tana zuwa ta sami Ummi tayi kneel down a gaban teburin Principal. Ga Baba Maje zaune akan kujera. Yana ganinta ya saki fuska sosai yana magana da Principal ɗin. "Yauwa ita ce kuwa." Principal ta dube shi da ɗan sakin fuska don taga sam bai fahimci zancen ba ta ce "Nima ita nake nufi Alh. Maje. Wannan Hamdiyyan ce dai su ka yi faɗa da Ummi jiya su ka yi sanadin hargitsa makarantar nan." "Na gane bayanin naki Hajiya. Dama abin da nake son fahimtar dake shi ne ina ganin ɗaya daga cikinsu ce ta shigar wa ƴar uwarta. Ba wai a junansu su ka yi faɗan ba." Ya yi mata bayani dalla dalla a ƙoƙarinsa na son ta gane. Murmushi tayi masa don yanzu bata jin za su fahimci komai sai yaran sun yi magana. "Ko me yasa ka yi wannan tunanin?" Ƴar dariya ya yi gami da gyara hannun rigarsa "mahaifin Hamdiyya abokina ne tun kafin a haifesu kin gansu nan. Shi yasa nake tunanin ko karewa juna suka yi. Ba kuma wai goyon bayansu nake ba. In sun yiwa makaranta laifi zan bada goyon baya ɗari bisa ɗari a hukunta su." Abin da ya fađa ya bawa Principal ɗin mamaki sai dai bata ce komai ba sakamakon sallamar sakatarenta da mutane biyu. Ɗaya wani ƙosasshen Alhaji ne ya sha babbar riga yana fama da kayan tumbi. Ɗayan kuwa Abban Hamdi ne. Su na shigowa VP da wasu manya cikin malaman su ka shigo su ma. Abba na ganin Baba Maje ya ce "da na san za ka zo ai da nayi zamana a gida." "Ko kuma da ni na zauna ba." Dariya su ka yi sannan aka yi musabaha tsakanin duka mazan wajen. Murya da yanayin mahaifin Hamdi kaɗai yasa malaman kallon kallo a junansu. Principal ta buƙaci a buɗe zaman da addu'a sannan ta ɗauko wayar Ummi ta miƙa mata. "Buɗe min wayar nan don na sami labarin ita ta fara janyo rigimar." Kai Alhaji mai ɗan tumbi wato Uncle B da baka gane Baba Maje ba tunda Ummin bata kama dashi sai ya kama faɗan bogi. "Ban hanaki zuwa da waya makaranta ba? Ke kenan kullum rigima ta tashi sunanki ne a sahun gaba." Baba Maje buɗe baki yayi don maganar ba tsoro ta bashi ba illa ruɗa masa tunani. VP na ganin haka sai ya taso har inda yake ya ja shi waje. "Duk abin da za ka ji ko ka gani kada kace komai don Allah har ka gama fahimtar inda zancen ya dosa." "To amma..." "Mu koma ciki. Komai zai warware kansa." Haƙuri ya bawa Principal na katse su sannan su ka jira Ummi ta buɗe wayar da rawar hannu. Jikinta babu inda baya ɓari. So take tayi aljanun ƙaryan tun yanzu amma bata da ƙwarin gwiwar pretending. Hamdi da bata san badaƙalar dake kwance ba kuwa ko a jikinta. Jikin kujerar da Abba ke zaune ta raɓa tayi kneel down abinta. "Kunna min abin da ki ka kunnawa ɗalibai a jiya." Nan fa ɗaya. Kasa kunnawa tayi. Displine master ya daka mata tsawa amma ko gezau. "Kin cika umarnin da aka baki ko sai na tashi?" Muryar Baba Maje ta fito da kaushi. Uncle B duk ya zata malami ne da ake tsoro shi yasa bai ji komai ba da yaga ta cika umarni da rawar jiki. Ofishin karaɗewa yayi da muryar Abba. Kunya tayi masifar kama shi. Idanunsa su ka yi jawur lokaci guda. Hamdi taji wani irin tausayinsa wanda yasa ta kuka. Baba Maje ya rasa me yake yi masa daɗi. Principal ta miƙawa kowa wayar ya gani da idonsa sannan ta umarci Hamdi da tayi magana. Ba tare da coge ba ta faɗi abin da ya faru tun ranar da su Baba Maje su ka zo gidansu har abin da ya faru jiyan. Irin cin zarafin da Ummi ke yi mata da takura kawai don ta mallaki sirrin mahaifinta. Kallon takaici kala kala ya dinga sauka akan Ummin bayan ra gama magana. "Ummi haka aka yi? A ina ki ka sami bidiyon?" Uncle B ya tambayeta har yana kai hannu zai ɗaga haɓarta domin kanta a ƙasa yake tana zubar da zafafan ƙwallar tsanar Hamdi. "Wai kai ɗin uban waye a makarantar nan da za ka taɓa baligar mace?" Baba Maje ya tambaye shi a harzuƙe bayan ya doke masa hannu. "Kai zan yi wa wannan tambayar." Ya kalli Principal ɗin "ya kamata malamanki su san aikinsu in ba haka ba zan cireta daga makarantar nan." Baba Maje ya ce "Kai a wa?" "Ni a mariƙinta" Uncle B ya bada amsa kai tsaye. VP gaban kujera ya dawo don yaga an zo inda yake jira. Cikin zafin rai kuwa Baba Maje ya ɗago Ummi tsaye ya dubeta. "Kalli ƙwayar idona ki faɗa min waye wannan." Numfashi ta fara ja tana shirin yin suman ƙarya taji Baban nata ya yi mata wata irin wawiyar jijjiga. Muryarsa tana rawa har wajen office ɗin kuma ana ji ya ce, "Idan ki ka ce za ki yi min ƙaryarku ta ɗalibai zan sabauta miki halitta a wajen nan. Ki faɗa min waye shi." "Saurayi na ne." Tasss, tass, tas ya ɗauketa da wasu gigitattun maruka. Abba ya yi saurin finciketa daga hannunsa ya tsaya a tsakani. "Haba Maje..." "Matsa min Habibu." Ya furta yana huci. Uncle B na ganin haka ya tashi zai sulale ya gudu sai dai babu dama. VP ya sanya securities ɗin makaranta a bakin ƙofa. Hasashen haka zai iya faruwa tun a jiya yasa ya ɗauki matakin da ya dace. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu Baba Maje ya zauna. Abba ya dubi Principal ɗin ya yi magana. "Da farko zan fara da baku haƙuri akan ɓarnar da yaran nan su ka janyo muku. Ummi tayi kuskure sannan ita ma Hamdi tayi na ɗaukar doka a hannunta. Amma fa duka abin da ya faru laifina ne..." ya sunkuyar da kansa. Principal ta kalle shi da tausayawa "bari na ɗan ce wani abu a nan." Ta kalli Hamdi "mu iyayenku da ku ke gani muma haifarmu aka yi ba da wayo muka zo duniya ba. Shekarunmu na hawa ne muna daɗa hankali. Duk wani kuskure da kuke yi a yanzu muma mun yi ƙila ma fiye da haka a lokacin tamu ƙuruciyar. Yanzu mun girma mun san illar abin shi ne dalilin da yake sa muke muku faɗa ma idan kun yi. Abin nufi a nan shi ne ƙuruciya da raunin hankali a baya yasa mahaifinki yin kuskuren bin rayuwar da kowa yake ƙyama. Gashi ita aba ce da ko ka daina da wahala đabi'unta su barka ɗari bisa ɗari. Amma tunda Allah Ya baki shi a uba ki rungume kayanki da godiya. Da baki ji kunya kin ɓoye shi ba, babu wanda ya isa ya ɗaga miki hankali akan shi. Ki nuna godiyarki ga Allah ta hanyar appreciating ɗin duk abin da Ya baki." Gyaɗa kai tayi tana goge hawaye "Abba don Allah ka yafe min." Da ƴar muryarsa ya ce "Allah Ya yi miki albarka Hamdiyya. Ki bawa iyayenki na makaranta haƙuri su ma." Ta kuwa bi umarninsa ta bawa kowa haƙurin abin da su ka yi jiya. Cike da kunya da jin nauyi Baba Maje ya bawa Abba haƙuri. Abba ya yi murmushi "Don Allah ka bar wannan zance." "Ta yaya zan bari? Bayan shekara sama da ashirin da rabuwarmu ace ƴar cikina ce tayi maka irin wannan tozarcin?" "Magana ni dai ta wuce don Allah." Abba ya sake maimaitawa. VP ya ce "yallaɓai ina ganin sanin alaƙar Ummi da mutumin nan shi ne abu mafi mahimmanci yanzu tunda an kashe wancan case ɗin." A lokacin aka fito da file na fitinannun makaranta inda sunan Ummi ya bayyana a kowanne term tun zuwanta a JS3. Bata fara laifin da ta cancanci a kira iyaye ba sai a SS2 da ta zama cikakkiyar senior. Kuma a lokacin ne duk sanda aka buƙaci iyayenta sai wannan mutumi dake zazzare idanu ya zo a matsayin kawunta. Ita ma aka bata dama ta faɗi yadda suke biyan maigadi su haura katanga ita da wasu. Samarinsu su kai su gari a shaƙata a sha ice cream da su shawarma a dawo. A rantsuwarta dai ta ce babu abin da ya taɓa haɗasu na fasiƙanci. Baba Maje kasa jurar jin maganganun ya yi ya finciki bulalar hannun wani malami ya shiga lafta mata. Da taron dangi aka raba shi da bulalar "Kanki ki ka cuta Ummi. Nan duka ɗaliban da ki ka zalinta in basu yafe ba sai kin gani a ƙwaryarki." Fuskarta yaɓe yaɓe da majina da hawaye ta ce "Baba ka yafe min." "Ba dole na ba? Idan nayi miki baki rayuwarki ai sai tafi haka lalacewa. Ki tashi ki haɗo kayanki don kin gama karatu kenan." "Alhaji ba ayi haka ba." Principal ta sa baki "ka bari mu ɗauki matakin da ya dace." "Maje kada ka ɗauki hukunci cikin fushi." "Kun san Allah ɗaya ne ko? To wallahi yarinyar nan ta gama karatu a ƙarƙashin ikona." Ya kalli Uncle B ya yi wani irin murmushi mai ciwo sannan ya ɗaga waya ya kira ɗan yayarsa police. Makarantar ya kwatanta masa. "Ku taho yanzu don Allah." "Yallaɓai da ka bari an kira masa ƴan sandan dake kusa da nan. Ka san kowanne laifi ana shigar dashi a unguwar da ya faru." "A kira su. Shi wannan ɗana ne saboda haka ina jiran zuwansa saboda ina son komai ya tafi da jagorancin wani nawa." Suna wannan zance Uncle B ya matsa gefe yana ta bige bigen waya da hargagin iska. Bayan ya gama ya cigaba da masifa yana doka teburin Principal. "Baki san ko ni waye ba a garin nan wallahi. Ina da damar sanyawa a rufe makarantar nan baki ɗaya a yau idan na so." "Ka daɗe baka aiwatar ba. Mutumin banza. Girma da matsayinka basu ƙara maka komai ba sai sanya hannu wajen ɓata tarbiyar yaran mutane." A cikin minti talatin motar ƴan sandan da VP ya kira ta iso makarantar aka yi awon gaba da Uncle B. Baba Maje da Ummi da VP ɗin su ka tafi tare dasu. Principal ta sanar da malamanta wajibcin neman iyayen yara a kurkusa domin tattaunawa da gujewa maimaicin abin da ya faru. Hamdi da Abbanta su ka fito tare fuskokinsu babu walwala sosai. Shi yana cikin damuwar halin da abokinsa ya sami iyalinsa, ita kuma tana cike da kunyar ya san irin matsayin da ta ajiye shi a matsayinsa na uba. Hannunsa ta riƙe ganin yana raɓewa gefe guda. "Abba in kai ka ka ga ajujuwanmu?" "A'a Hamdi." Ya zame hannunsa. "Ba ka yafe min ba ko?" Idanunta su ka kawo ruwa. "Ban taɓa fushi dake ba. Ba dai na son sake bar miki abin faɗi a cikin abokan karatunki." Ya ce a sanyaye. Wannan furuci nasa ya sanyata kuka sosai. Ta roƙe shi da ya jirata a nan inda yake za ta dawo bayan ya hanata kukan. Tana tafiya ta samu ɗalibai na dinning hall ana cin abincin rana. Duk da yadda take wasiwasi amma da ta tuno da maganar da Principal tayi mata sai taji zuciyarta ta daina tsoron komai. "SS3 A" ta ƙwala kira da ƙarfi. Tashi su ka yi wasu kuma su ka amsa da baki. "Ku zo ku gaisa da Abbana." Ai kusan rabin hall ɗin ne su ka fita a guje. Aka kasa controlling ɗin su. Tana gaba har inda ta barshi tsaye. Kawar da kai taga ya yi tayi murmushi ta zaga gabansa. "Abba an zo gaishe ka." Tunda yake kullum yaransa su ka zo gida da ƙawa basa taɓa cewa a gaisa da shi. Ƙawayen ma bai san kowa ba sai na dangi ƴaƴan ƴan uwa. Ya juya suna ta ina wuni shi kuwa ya kasa amsawa saboda kada jin muryarsa yasa a yiwa ƴarsa dariya. "Abba ka amsa mana" Hamdi ta ce tana dariya kamar ba ita ba. Yarinyar da kullum take cikin ƙunci da damuwa. Ya buɗe baki ya dinga amsa musu. Ƴan matan nan maimakon nuna ƙyama sai yake ganin kamar ya burgesu. Wasu basu taɓa ganin ɗan daudu a kusa haka ba. Kamar wani abin sha'awa su ka dinga girmama shi. Kan Hamdi ya kumbura suntum saboda daɗi. Ranar da taimakon malamai aka ƙora su duka har ita cikin makaranta sannan ya samu ya tafi wajen Baba Maje. *** Ganin su Inna ya yi saurin ɗaukewa Taj damuwar da ya shiga. Sai gashi ya zage yana ta hira kamar ba shi ba. A cikin hirar ne ya tambaye su ko akwai wani abu a tattare dashi da zai sa ayi masa kallon namijin da bai cika ba. Ya naɗe hannun rigarsa har saman kafaɗa irin yadda yara su ke yi. "Saboda son burge Alhaji har gym nake zuwa ina motsa jiki. Yanzu wannan..." ya nuna dantsensa "bai isa a kirani namiji ba?" Kamal kula ya yi da Salwa da ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci da yadda tayi saurin ɗauke ido daga kallon hannun Taj. Shi kuma gwanin ya kama ƙasan riga zai ɗaga wai ya nuna musu packs ɗin ƙirjinsa. Gudun kada ɗan uwansa ya kunyata shi ne ya kai masa duka a hannun. "Dalla malam rufe wannan sandar raken." Taj da yaji zafi ya rama dukan "ɗan baƙinciki in ka isa ka buɗe naka mai kama da taliya." "Mama kina dai jin abin da yake faɗa min ko?" Kamal ya faɗi yana miƙewa tsaye. "Laifinka ne fa Kamal. Kai ka fara dukansa" Mama ta goyi bayan Taj. "Saboda ya dawo daga America za ki nuna min wariya? Ke fa ki ka hana raini tsakaninmu." Su Hajiya sai dariya su ke yi. Taj ya sami goyon baya ya cigaba da tsokanarsa. "Ka ci sa'a ban auro baturiya ba da kaga asalin wariya. In taho da ƴan ƴaƴana farare su na Mom...Dad...who is this black man" ya nuna Kamal aka sake tuntsirewa da dariya. Ya cigaba da tsokanarsa "Duk ƴan uwa su taru a kansu ana son burgesu. Kai kuwa naka sai dai kaji ana cewa 'Sule maza tafi wurin babarka ta goge maka majina' " "Banza ƙazami. Wai majina kamar tashin Soron ɗinki. Kuma don wulaƙanci ba ma Sulaiman ba Sule zan haifa?" Kamal ya faɗi yana shure shi da ƙafa. Taj dariyar da ya san za ta ƙular dashi ya cigaba da yi. "Sule Kamalu Hayatu Sule. Irin ƴan chubby yaran nan masu ɗan ƙaton ciki ba." Ba ka jin komai a falon sai dariyar iyalin ta farinciki. Salwa da take ganin duk motsin Taj wani salo ne daban mai tafiya da zuciyarta ce kaɗai ta ƙare da murmushi. Kamal da Taj su ka gaji da wasansu na dambe da girma bai hanasu yi ba su ka koma cin abinci daga plate ɗaya su na hirar da babu mai ji. RAYUWA DA GIƁI 9 Batul Mamman💖 *** Irin kukan da Iyaa tayi bayan jin tsiyar da Ummi take shukawa dole ya bawa mutum tausayi. Bayan an kai ruwa rana a station ɗin da su ka je Baba Maje ya gane duk inda yake tunanin Ummi ta wuce nan. Fitina da gagara ta ƴan matanci kam tana bugawa a bayan idonsa. Ya sake yarda ba a shaidar ɗan yau. Ba don da bakinta ta amsa laifukanta ba da ya yi rantsuwar sharri ake yi mata. Ummin da ya sani daban. Wadda ya dawo da ita gida daban. Abin baƙinciki shaiɗanin tsohon najadun da yafi kowa hure mata kunne Uncle B ashe makanike ne. Matansa biyu da ƴaƴa goma sha uku. Sau ɗaya ake ɗora tukunya a gidansa. Irinsu Ummi ke cinye ɗan abin da yake samu. Ita da yake tunanin raba hanya da ita saboda rashin bashi haɗin kai tuntuni ashe silarta asirinsa zai tono. Sai da ya yi sati guda a ƙulle kafin a yarda a bada belinsa. Shi ma kuma an haɗa masa da muguwar tarar da zai ji jiki wajen biya. Hantara da kyara su suka marabceta daga dawowarta gida. Ta zama mujiyar da bahaushe yake kira mai baƙin jini. Iyayenta ba su dake ta ba don ciwon abin da tayi ya kai maƙura. Yayanta Baballe ne dai ya kasa zama bayan yaji kukan Iyaa yayi yawa a waya da tana labarta masa. Ya niƙi gari ya taho Kano ya sakar mata ƙarfinsa. Zaneta ya yi ciki da bai babu wanda ya hana shi. Sai ma dare da jikinta ya yi mugun tsami ne Iyaa ta tada ta zaune. "Sau nawa ki ka zubar da ciki Ummi?" Duk soyewar zuciyarta da ya hanata kukan dukan da ta sha wannan tambaya sai da tayi sanadin zubar hawayenta. Hannu ta ɗora akan bakinta tana danne kukan. "Iyaa? Ciki kuma?" "To Ummi meye abin mamaki a ciki? Samarin da su ke kashe miki kuɗi ƙannen uwa ne ko na uba da za a ce zumunci suke yiwa?" Hawaye take ita ma ga tsoron kada Ummin ta amsa zargin da su ke yi mata ita da Baba Maje. "Wallahi Iyaa ban taɓa yarda na bada kaina ba." "To me ki ke basu ko me su ke samu a madadin kuɗinsu? Don dai bana jin shaiɗancin naki ya yi tsamarin da za ki asircesu su dinga bin umarninki." Shiru Ummi tayi. Hankalin Iyaa ya sake tashi ta dinga kai mata duka da hannu ta ko ina. "Ki faɗa min gaskiya kafin zuciyata ta buga." "Iyakarsu tattaɓani amma bana yarda da..." Da sauri Iyaa ta tashi don bata son kuma jin ƙarshen zancen. "Ya isa. Kin yiwa kanki." Fita tayi ta bar Ummi tana kuka. Kuma duk wannan abu bai zama ishara ya tuna mata yadda ta dinga cin zarafin mutane dole rana irin ta yau ta zo ba. Sunan Hamdi kawai ke yawo a zuciyarta. Ko harararta aka yi laifinta take ƙara gani. Musguna mata da ta dinga yi a makaranta ai bai shafi komai na karatunta ko rayuwarta ba a tunaninta. She was just having fun. Ba ita kaɗai bace senior mai yi wa na ƙasa da ita hawan karkatacciyar kuka, saboda haka bata ga dalilin da zai sa ita kaɗai ce rayuwarta ta kife irin haka ba. Da me ake so ta ji? Sanin waye Uncle B ko fitowar sirrinta? Ko kuwa rabata da makaranta a matakin ƙarshe da iyayenta su ka yi don ta ɗauki bidiyon ɗan daudu? "Wallahi sai na rama Hamdiyya. Babu wanda ya isa ya saka ni kuka ban saka shi ba." Da wannan kalaman ta goge hawayenta a fusace ta kwanta tana shure Siyama da ƙafa don ta ɗan matso ɓangarenta cikin bacci. *** Kwanaki sun ja inda a farko farkon watan August ɗaliban sakandire su ka kammala jarabawar fita. An yi WAEC har ta fito kafin a gama NECO. Da taimakon Allah da kuma dagewar karatu Hamdi ta sami kyakkyawan sakamako. Kwana biyu bayan kammala jarabawar makaranta ta shirya gagarumin taron sallamar ɗalibai. Iyaye da ɗaliban suna shiryawa wannan rana wasu tun farkon shiga SS3. Ɗinkin ankon wata shuɗiyar atampa su ka yi mai adon fari da yellow. Tun kafin hutu aka fitar amma lokacin Hamdi bata ƙarɓi ƙyallen ba. Saboda ko kusa bata sa ran zuwa. Sai bayan faruwar lamarin nan taji a jikinta ta daina ɗararewa. Allah Ya taimaketa kafin a gama jarabawar lokacin visiting da Sajida da Zee su ka zo mata ta basu. "Abba fa ya bar sana'arsa Hamdi. Ki haƙura kawai a kawo miki ko cikin kayan sallarki ne." Zee ta faɗi bayan ta gama kallon atampar. Mangareta Sajida tayi "Yaya bata gargaɗeki akan faɗa mata ba?" "Gaskiya fa na faɗa mata don kada ta sa rai." Zee ta bata amsa tana ƙunƙuni. "Ya Sajida me yake faruwa? Ba don saboda ni ya daina ba?" Hamdi ta tambaya hankalinta na tashi. Bayanin abin da ya faru su ka yi mata. Sannan Sajida ta ce kada ta damu in sha Allahu za a saya a ɗinka kafin ranar. "Na haƙura." Hamdi ta ce a sanyaye tana tuhumar kanta a matsayin wadda ta kasa godewa mahaifinta a lokacin da yake yi musu. "Anti Labiba ce ta bani kuɗi da zan taho. Allah zan iya saya miki." Sajidan ta bata amsa tana dariya. Daga nan su ka koma wata caftar mai daɗi. Sajida tayi saurayi a Abuja daga zuwa taya cousin ɗinsu zaman jego. Mutumin da gaske yake. Yana aiki da rufin asirinsa. Ƴan maza zar su ke da mijin Anti Labiban (ƴa a wurin babbar yayar Abbansu Anti Zinatu). Ƴan matan uku su ka haɗa kai su na ta murna kamar ma anyi auren an gama. Zee ce ta dakatar da shewar tasu "Kin dai yi masa bayanin Abba ko?" Fari Sajida tayi da idanu tana faɗaɗa murmushinta "Kada ku damu. Ya ce sai da su ka yi magana da mijin Anti kafin ma ya yi min magana. Yanzu dai ku sa rai da zuwansa nan da wata guda. Lokacin ma kin dawo gida ko?" "Su Ya Sajida an fara kashe murya a waya kenan." Hamdi ta tsokaneta. "Zan ɗauko rahoto kafin ki dawo. Dama bata yi na gani ba don kada na fesawa Yaya." "Kin fa raina ni Zee. Ni da na raineki." Dariya Zee da Hamdi su ka yi. Ita Zee SS2 take don tsiransu da Hamdi babu yawa. *** Aikin gini ya soma kankama son Taj ba ɓata lokaci ya zo yi ba. Shawarar Amma ya karɓa ya yi ginin a iya restaurant da shaguna ƙalilan. Wani Architect ya kwatantawa abin da yake so. Nan da nan aka zana masa plans kala uku. A ciki ya zaɓi ɗaya. Shi da Kamal kullum sai dare su ke komawa gida. Shi ya tafi gidan Ahmad, Kamal kuma ya koma don muddin ya kwana zai gamu da fushin Alhaji. Tsarin da aka ɗauko ya bada ma'ana sosai. Gini ne da aka yi ɓangare uku manne da juna. Na tsakiyar yafi girma da faɗi kuma shi kaɗai ne aka ɗorawa bene. Na hagu anyi kitchen ƙato da komai domin aikin fulawa. Cake, doughnut, meatpie, samosa, pies da dangoginsu. A wadace yake sai dai babu wurin zama a ci a ciki. Idan mutum baya son fita akwai ƙofa da za ta sada shi da tsakiyar wato ainihin restaurant ɗin. Ɓangaren dama wanda shi dama za a fara tararwa shi kuma kana gani za ka san na masu gashin nama da kifi ne. Ko yanzu da ake matakin gini kaɗai kana gani zai burge ka. A tsakiyar sama gabaɗayansa kujeru da teburan zama ne. Sai wasu ɗakuna biyu domin masu gudanar da taron da zai iya cin mutane hamsin. Meeting, seminar, reunion da sauransu amma banda biki. Ɗakunan ɗaya normal ne ɗaya kuma VIP. A ƙasa ma da wurin cin abincin sai ɓangaren masu haɗa natural juice da za ayi bayan kayi order. Saii kuma makeken kitchen ɗin Taj da ma'aikatansa. Har ila yau a farfajiyar wajen an keɓe wani waje da aka soma tayar da garden. Za a ƙawata wajen da liluka da wajen guje guje da wasan yara. Sai kuma cikon alƙawarin da ya yiwa kansa. Zai gina madaidaicin boutique da gininsa zai kallon restaurant ɗin ya bawa Kamal amma bai faɗa masa ba. Yau sun bar wurin duba aikin da wuri sakamakon zazzaɓi da ya rufarwa Taj gadan gadan. Kamar wasa ya ce kansa na ciwo, sai gashi kafin su isa gidan Ahmad yana rawar sanyi. Ɗauke hanya Kamal ya yi su na cikin tafiya. Taj ya ɗago kansa da ya yi nauyi da ƙyar ya dubi hanya. "Sayar dani za ka yi don kaganni haka Happiness?" Kamal ya yi murmushi "kwantar da hankalinka. Ai an taya kuma naji ba tsada za ka yi ba." "Ka ci bashi don sai na rama." "Allah Ya baka haƙuri. Yadda nake jin yunwa idan kayi fushi dani da alama Salwa ba za ta bani abinci ba yau." Wani irin kallo Taj ya yi masa na neman alaƙar fushinsa da cin abincin Kamal amma ya kasa ganewa. "Wani abu ne ya haɗaka da ita?" "No" Kamal ya bashi amsa mischieviously. "Meaning?" "A bar zancen sai ka warke." Taj bai matsa ba. Kansa kuɗa yake kamar zai cire. Asibiti Kamal ya kai shi duk turjiyarsa. Abu ya kai da ƙarin ruwa don likitan ya ce jikinsa babu kuzari. Gashi sakamakon gwaji ya nuna yana da malaria da thypoid duk shi kaɗai. Sun haɗe da rashin hutu sun kayar dashi lokaci guda. "Amma ba kwana zan yi ba ko?" Ya tambayi likitan bayan an gama saka masa canula a hannu. "Ka godewa Allah da ka iya shigowa nan da ƙafafunka. Your temperature is abnormally high." Da Kamal ya barshi ya rufe ido don ya gaji sosai. Bayan fitar likitan da Alhaji yaji Kamal ɗin yana waya. Ya sanar dashi halin da yake ciki. Ƙaguwa ya yi yaji me Alhajin zai ce don kamar ya ƙwaci wayar a hannun Kamal. Ya dai daure har su ka gama. Shiru bai ji Kamal ya isar da saƙon Allah Ya ƙara sauƙi ba. Sai da ya bari ya gama waya da su Inna da Ahmad sannan ya tambaye shi. "Bai ce komai bane?" "Yana hanya ne da alama ba ya ji na sosai" Ita ce kalmar da Kamal ya ƙirƙiro ya faɗa masa. "Hmmm" Kamal ya dawo kusa da shi "Happy kayi haƙuri sannan mu cigaba da addu'a." Abinka da ƴan dangi. Lokaci ƙanƙani asibitin ya fara cika da ƴan uwansu. Kowa ya zo faɗan rashin hutu yake yi masa. * Don son tabbatar da zarginsa, Kamal kiran Salwa ya yi ya faɗa mata bayan ya sanar da Ahmad. Tunda yaji ya ce baya gida shi ne ya kirata. Ai kuwa abin da ya yi tsammani yaji. Rikicewa tayi ba tare da ta sani ba. "Ya Kamal yana iya magana?" Ya yi murmushi "eh, ko in bashi ne?" Da sauri ta ce "a'a" kunya na lulluɓeta da ta fahimci za ta bada kanta. Awa guda bayan sun yi wayar ta kasa sukuni. Jira take Zahra matar Ahmad tayi maganar zuwansu dubiya tunda tayi arba'in yanzu amma taji shiru. Bini-bini ta ɗaga waya ta duba lokaci. Da ta kai matakin da ba za ta iya haƙuri ba sai ta tambayi Zahran. "Anti Zahra na ce ko sai Hayat ya taso in an kai shi islamiyya za mu wuce asibitin?" Zahra ta zaro idanu tana laluben wayarta "ba ki da lafiya ne Salwa? Ina yake miki ciwo? Bari na faɗawa Daddy." "Ƙalau nake Anti. Dama maganar duba Yaya Taj ne." Zahra tayi murmushi "lahhh kada ki damu. Daddy ya ce zai biyo muje yanzu. Ke kuma ki zauna saboda Hayat." "In zauna?" Salwa ta ce ba shiri. "Ina jin babu lallai ya kwana tumda yace min suna ta waya da Kamal. Meeting ne ya hana shi fita da wuri." Rasa bakin magana tayi ta fita kawai. Zahra ta bita da ido ba tare da kawo komai a ranta ba. Da Ahmad ya dawo ko shiga gidan bai yi ba ya kira Zahra ya ce ta fito bayan la'asar. Kafin ta gama shirya Aisha Salwa tayi saurin fita wajensa. "Ya Ahmad kana ganin daga gida ba za su fassara rashin zuwana duba shi ba ace don ba ɗan uwana bane?" "Ke, gidanmu babu irin wannan kin ji. Bana son Hayat yayi missing islamiyya shi yasa nace ki zauna." "Naga kamar zamu iya dawowa kafin ya taso." Wani irin kallo mai tattare da tuhuma ya yi mata. "To ko mu zauna ke ki je?" Diriricewa tayi don bata tsammaci furucinsa ba. Ta ce "Haba Yaya ba haka nake nufi ba." Su na tafiya ta sake kiran Kamal ya ce mata jikin Taj da sauƙi. Don ya ƙara rura wutar da ya fahimci ta soma cinta ya ce "Yanzu dai ya gama amai wallahi. Ya galabaita sosai don ko zama ya kasa. Amma dai da sauƙi za a ce." "Kace ina masa sannu don Allah" ta ce da muryar kuka. "Ban gane ba. Ba za ki zo ba?" Da sanyin murya ta ce "Ya Ahmad ya ce na zauna." Tausayi ta bashi ya daina ɗorata. Yana ajiye wayar ya yi murmushi "shege Happy. Daga zuwa ya yi ɓarna a zuciyar ƴar mutane." Wasa wasa sai da Taj ya yi kwana biyar aka sallamo shi. Kuma tun washegarin kwanciyar tasa kullum sai Salwa ta je. Duk wani motsinta Ahmad ya kafa ya tsare har ya tabbatar da zarginsa. Hankalinsa kuwa ya tashi don yana jiye mata abubuwa da dama. *** Takarda ce cikin foolscap Hamdi take ta karantawa tun wajen kwana uku tana son haddacewa. Speech ne malamar English ta bata wanda za ta yi ra ranar taron. Cikinta har ƙullewa ya yi yau da aka kira assalatu saboda tana da tsoron yin magana a gaban mutane. Har aka gama yayin monitoci da mataimakansu da ma prefects bata taɓa karɓa ba. Komai na mutane gudu take. Sai gashi wannan karon Principal da kanta ta ce a bata. Wai jawabin godiya ne a matsayinta na overall student ta makaranta. Da shawarwari ga ƴan uwanta ɗalibai akan hanyoyin bi domin samun nasara. Ga dai takarda ko daga bacci ta farka za ta iya kawota tas da ka, amma da zarar tayi tunanin mutanen da za ta fuskanta sai taji kan ya koma fanko. A haka ta janyo jiki ta zo wajen taron tamkar mara lafiya. Ana tsakar gabatar da shirye shirye ta tashi kafin a zo kanta. Bayan Admin block taje ta sami wuri ta zauna tana ta bita kamar mai zuwa musabaqa. * A cikin dandazon mutanen da su ka zo taron harda ƴaƴa da jikokin Alh. Hayatu Sule. Akwai jikarsa Firdaus ƴar wajen babbar ƴarsa Hajiyayye cikin masu fita. Yarinyar mutuniyar Taj ce sannan bata san ya zo gari ba. Rabonta da shi tun tana ƴar ƙarama. Shi yasa da Hajiyayyen ta gayyaci ƴan uwanta zuwa graduation shi ya fara amsawa zai je. A cikin hayaniyar programs ɗin da ake gabatarwa da hirar ƴan uwansa yaji wayarsa tana vibrating. Sunan Amma ya gani ba shiri ya tashi yana neman wurin da zai iya amsa wayar ba tare da hayaniyar ta hana shi jin me take cewa ba. Kamar ance ya kalli damansa ya hango wata yarinya tana tafiya da sauri sauri ta nufi bayan Admin block. Sanye take da ankon ƴan graduation ɗin da gown ɗinsu. Ta riƙe hular a hannu. Ɗaurinta na Maryam Babangida ya zauna đas a kanta. Sai ɗan mayafi da ta yafa a kansa ta rufe wuyanta da shi. Numfashinsa kusan ɗaukewa ya yi da ganin yarinyar kamar yau ya fara ganin mace. A kallon farko ya iya tantance tsayinta da yake matsakaici. Fatarta da yake iya gani a fuska tayi daidai da wankan tawarɗa da ake kiran masu sirkin fari da baƙi. Fuskar ya sake kallo wadda ta fizgi duk wani rational tunanin dake yawo a kansa. A cike take da duk wani abu da yake muradi a wurin mace. Ga ƙarin kwarjini da nutsuwa da yake da yaƙinin tana da su daga yanayin tafiyarta. Wayar da yake son ɗauka tuni ya manta da ita har ta katse. Kamar ana ingiza shi ya bi ta. Idanunta a rufe lokacin da ya hangota. Ta sanya hannu ta rufe kunne tana karanto abin da ta haddace. Sannu a hankali ya dinga takowa gabanta har ya rage babu nisan kirki a tsakaninsu. Ƙamshin da Hamdi taji yana ta kusanto ta ne ya hanata buɗe ido. A zuciyarta ta gama tsorata don an saba faɗin akwai ƙwanƙwamai a bayan Admin block. Wai ba a ganinsu sai dare. To me ya fito dasu da hantsin nan lokacin da ake ta kai kawo a makarantar? Taj na jin yadda ta ja numfashi ta kasa saukewa da ya matso. Ya saki murmushi. "Buɗe idonki." Hamdi ta tsuke baki don in ta sami wuri akwai tsiwa. To yau dai aljanu za ta nunawa bata tsoronsu don kada su maketa a banza. Ta sha jin labarin idan baka nuna tsoronsu ba, ba sa yiwa mutum komai. "Anƙi ɗin. Tsakanina da aljani nan gani nan bari. Na riƙe Ayatul Kursiyyu." Dariya Taj ya yi a hankali ya a jin wani irin abu na bin jikinsa. "Ni ba mai cutarwa bane so you can open your eyes." Ido ɗaya ta ɗan buɗe a hankali ta tabbatar mutum ne sannan ta buɗe ɗayan. A lokaci guda idanuwansu su ka sarƙe cikin na juna sai dai Hamdi bata iya zurfafa kallon ba ta kawar da kai. Babu abin da zai sa ta iya jurewa kallon idanun mutumin dake gabanta masu kaifi da su ka tsareta. A zuciyarta kuwa sai da ta kira sunan Allah saboda tunda take bata taɓa ganin wani namiji taji ina ma ace....ba sai a kan wanda yake gabanta. A daidai lokacin su ka ji sanarwa ta sipika. "Bayan wannan gajeriyar diramar da za ayi mana mai taken Ilimi a Karkara, za mu saurari speech daga bakin overall student ɗin makarantar nan Hamdiyya Habib." Wani haɗaɗɗen ruɗani Taj ya gani a idanun yarinyar gabansa. Da haka ya gane ita ce aka ambaci sunanta. Takardar hannunta yaga ta kalla kamar za ta yi kuka. "Kin taɓa ganina?" "A'a." "Good. Ki yi imagining ni ne duka mutanen wurin can sai ki yi speech ɗin naki na ji." Kamar ta ce a'a sai dai ta gyara tsayuwarta. Ta rufe ido. "Open your eyes and think of ..." ya kalleta "Wa ki ka fi so a duniya?" "Iyayena." "To ni ne su. Ki sa a ranki su kaɗai ne a wurin." Sallama tayi da rawar murya ta soma da gabatar da kanta amma ta kasa faɗin sunanta ma. Sai komawa baya take yi. Taj ya karɓi takardar ya dunƙuleta a cikin hannunsa bayan ya karanta a gurguje. "Bayan godiya ga school da iyayenki za ki bawa students shawarar karatu. Do you realy need a paper to say all that?" Hamdi ta ƙifta idanu "no." "Then say what you truly want to say from your heart. You will be fine in sha Allah." Haka kawai magana da shi ta sanya mata wata irin nutsuwa. Ta tattare doguwar rigarta sama kaɗan ta dube shi da murmushi a fuskarta. "Thank you." Ya so sake cewa wani abu amma tunawa da ya yi tana buƙatar nutsuwa kafin ta iya yin abin da ke gabanta sai ya barta ta tafi. Ya raya a zuciyarsa idan an gama taron zai nemeta. RAYUWA DA GIƁI 10 Batul Mamman💖 *** Numfashi ta sake saukewa a hankali bayan ta karɓi loudspeaker ɗin sannan ta rufe ido ta buɗe da sunan Allah. Da ido ta lalubo Taj wanda har ga Allah tayi matuƙar mamaki da ta iya gano shi a cikin mutane. Bata sani ba ko hakan yana da alaƙa da sahun gaba da ya dawo ya tsaya a jikin ƙarfen canopy bayan kusan kowa a zaune yake. Ya yi mata murmushi gami da gyaɗa kai kamar mai bata damar yin magana. Mantawa tayi da kowa da komai ta yi taƙaitaccen speech ɗinta mai ma'ana wanda kalmominsa su ka dinga zuwa kamar daga sama. Wuri kuwa ya kaure da tafi. Ɗalibai ƴan ajinsu su ka dinga kiran sunanta da ƙarfi suna tafi. Haka kawai tauraruwarta ta ƙara haske a idanunsu tun bayan da ta kare martabar iyayenta. Idanunta lokaci lokaci su na kan Taj har ta gama. Tana addu'ar gamawa taga Taj ya kalli wayarsa sai ya kara a kunne ya bar wajen. Za ta sauka aka dakatar da ita. Mai Girma hakimin Gabasawa da kansa ne zai bata kyaututukan da aka tanada dominta. Wani ƙayataccen kwando ne aka saka komai aka lulluɓe da ledar ado aka ɗaure. Ya miƙa mata aka yi musu hoto tare sannan ya ce tasa kyautar ita ce kujerar Makka a Hajjin shekara mai zuwa in sha Allah. "Allahu Akbar" Malamin da yake MC ya faɗi, sai ɗalibai da iyayen yara su ma su ka amsa. Murna a wajen Hamdi kuwa ba a cewa komai. Ta sauko daga stage ɗin idanunta cike da ƙwallar zallan farinciki. Wurin da su Sajida su ke zaune ta nufa da sauri. Banda Sajida da Zee harda ƴaƴan ƴan uwan Abbansu mata tsararrakinsu. Halifa ma ya baro ɓangaren maza aka yi murnar tare da shi. "Hamdi ina kayanki? Yaya ta ce kada mu yarda mu wuce ƙarfe biyu nan." Halifa ya ƙara da cewa "ana can ana haɗa miki ..." Kafin ya gama magana Zee ta dage ta doke masa ƙeya. "To fesal uban zance." Hannu Hamdi tasa ta saƙalo kafaɗarsa tana dariya "rabu da ita Halifa. Idan ka faɗa min me ake yi zan bar maka duk ragowar provision ɗina." Da sauri Zee ta riga shi faɗa. "Walimar ƴan gida za ayi miki" "Kin dai ji kunya wallahi. Da kayan ƙwalama za a sayeki cikin sauƙi" cewar Sajida tana taɓe baki. Kayan nata ta nuna musu su ka haɗu da cousins ɗin nasu aka kwaso cikin ƙanƙanin lokaci. Ta koma cikin ƴan uwanta ɗalibai aka yi hotuna harda malamai da musayar lambobin waya. Wasu harda kuka sosai. Ita dai bata yi ba don sabon da tayi da abokan karatun nata na iya lokacin jarabawa ne. Kewar rayuwar makaranta tafi damunta. Duk abin da take yi hankalinta yana komawa ga tunanin ina mutumin nan na ɗazu. Ta gaji da juyawa ko za ta gan shi Allah bai yi ba. Ga Sajida ta damu su tafi don ita za a yiwa faɗa idan su ka ɓata lokaci. Haka ta tafi zuciyarta tana begen sake ganin sa. * Wayar Amma ce ta sake shigowa, ita ce dalilin da yasa ya bar wajen. Kuka take yi wanda ya matuƙar tayar masa da hankali. Ta sanar dashi surukarta Hajjo ta ce lallai ta zaɓi tsakanin aure da aiki amma ba za ta haɗa biyu ba. Mijinta shekarsa huɗu da ritaya ya koma gida gabađaya. "Wai zaman me nake yi a nan. Taji an ce kai ma ka dawo." "Ba ki faɗa mata ba daɗewa zan yi ba?" "Nayi mata bayani duk taƙi ji. Yanzu don Allah 7 months to my retirement sai nayi resigning? An yi min adalci kenan?" Ta maza ya yi bai nuna mata damuwarsa ba ya dinga rarrashinta. Da ƙyar ta haƙura bayan ya yi mata alƙawarin zuwa Abuja ya sami Hajjo a gidan mijin Amma ɗin inda take zama da amaryarsa da yaransa. Yana dawowa cikin ƴan uwansa Firdaus ta janye shi tana ta nunawa ƙawayenta Uncle Taj. Daga hoto ɗaya sai da aka yi yafi goma. Masu ƙyasawa da yawa su ka kasa ɓoyewa. Shi dai ya biye mata ne kawai saboda ko a cikin jikokin gidan ita ce ƴar gaban goshinsa. Indai ana hutu tana yawan kiransa. Ana hoton da hayaniyar amma idanunsa yarinyar nan Hamdiyya Habib su ke nema. Da bai ganta zuciyarsa bata kawo komai ba tunda yana da yaƙinin Firdaus ba za ta kasa saninta ba. Bai san Hamdi bata da ƙawa ba. In ka cire sunanta ko sunan unguwarsu babu wadda ta sani. *** Washegari jirgin ƙarfe bakwai ya bi zuwa Abuja. Idan buƙata ta biya so yake ya dawo a ranar don yanzu ya matsu ya koma wurin Amma. Da yake tun dare ya sanar da Daddy mijin nata cewa yana tafe, yana isa direba ya zo ya ɗauke shi. Iyalan gidan ba baƙinsa bane tunda su na yawan kai ziyara America har Hajjo. Ƴan mata uku ne ƴaƴan kishiyar Amma da ake kira Anti. Su ma duka sun saba da shi. Dama tun zuwansa yana son tahowa Abujan su gaisa amma aiki ya hana. Tarba mai kyau ya samu daga Antin da ƴaƴanta. Sai da ya ci abinci ya ƙoshi sannan aka yi masa ido ɗakin Hajjo. A hakimce kan kujera ya sameta ta kashingiɗa tana danna remote. "Wannan zuwan na san na Jamila ne ba don neman albarkar tsofaffi ba." Taj ta sosa ƙeya "tuba nake Hajjo tawa ni kaɗai." Ƴar tsohuwar ta yatsina fuska "bana son daɗin baki. Ai da uwarka Jamila ce a gidan nan ba za ka saka aiki a gaba ka kasa zuwa ba." Anisa babbar ƴar Anti ta nuna rashin jindaɗin wannan furuci "abin kuma harda zagi Hajjo?" "Fita ko ban guri ai ba kiranki nayi ba." "Ya Taj na biyo." Hajjo ta haɗe fuska tana neman abin duka "Duk gidan nan babu wanda ya isa ya yi min iko da ɗaki saboda haka get out." Taj da Anisa su ka saka dariya. Ita tana cewa "yeeyyyy, Hajjo ta tuno zama cikin turawa." "Zan zagi babanki wallahi. Zo ki fice." Kafaɗa Anisa ta noƙe ai kuwa Hajjo ta bita da daƙuwa hannu bibbiyu. "Na iyayenki su uku." Alamun rashin jindaɗi Anisa ta nuna wanda Taj ya lura. Da ka ya yi mata ishara ta fita daga ɗakin. "Hajjo sai ki yi ta zagar mana iyaye saboda Allah? Kinga bata jidaɗi ba daga ɗan yin wasa da kakarta." Lura tayi shima kamar bai jidaɗin ba sai kuma ta saki fuska. Ita a dole Taj ne kaɗai jikanta namiji na wajen babban ɗanta. Tunda ya koma hannun Amma bata taɓa canja masa ba. Saboda tun asali dama kakarsa wadda ta haifi Alhaji da ita ƙawaye ne da su ka yi ƴan matanci tare. Ita ta fara zayyano masa ƙorafinta akan zaman Amma ita kaɗai a gida ga mijinta a wata uwa duniyar. "Saura bai fi sati uku ba na koma in sha Allahu. Kuma zan zauna har tayi ritayar. Ai na san zamana ne sharaɗin da yasa ki ka yarda ta cigaba da aikin." Hajjo ta ƙara sakin fuskarta saboda Taj akwai iya tsara zance. "Ka san ita mace bata tsufa da buƙatar kulawa. Yau ko ƙwan fitila ne ya mutu wata idan babu namiji a gidan sai dai ta zauna a duhu." Haƙuri ya sake bata da yaga ya samo kanta kuma ya yi mata bayanin gininsa da ya yi nisa. "Shi uban taurin kan har yanzu baku daidaita bane?" Dariya Taj ya yi. Kamar ba ita ta nuna ta daina ƴan mintuna ƙadan baya ba. "An dawo kansa kuma?" Ko a jikinta ta ce "Ai Hayatun ne akwai wuyar sha'ani sai ka rantse ni na haife shi. Don ita babar tasu haka take ba cas ba as." "Ahhhh. Ni fa Hajjo zan tashi wallahi. Harda kakata kuma." Yadda ya ɓata fuska sai da tayi dariya. Daga nan aka kashe maganar dawowar Amma. Sai kuma ta sako zancen da yake cin ranta. Dama can ba dawowar Amman bace a gabanta. Tafi kowa sanin halinta tunda a gabansu ta tashi. Ita ce ma ta haɗa auren nata da ɗanta. Da gangan ta tayar mata da hankali yanzu kawai don Taj ɗin yazo. Don tayi imanin indai yaji ba zai ƙasa a gwiwa ba zai zo neman sulhu. "Tajo." Babu yadda ya iya. Dole yake amsa sunan nan da baya son a faɗi indai daga bakinta ne. "Nace wai me zai hana ka nemi ƙanwarka Anisa ku daidaita? Karatunta sai gudu yake har an shiga aji huɗu a jami'ar nan." Gabansa yaji ya faɗi. Duk kirkin Hajjo kowa ya san rigimammiya ce ta buga misali. Yanzun nan sai ta yiwa mutum dabaibayin da zai sarƙe wuyansa bai sani ba. Ƙofa ya kalla tana gama maganar "Hajjo daina faɗa kada ta zata gaske ne ta soma jin haushina don na tabbatar ba za ta rasa masoyi ba." Shan kunu tayi harda yi masa daƙuwa. "Ƙaniyarka Tajo." Ya sunkuyar da kai yana sauraron sababinta. "Da akwai wanin ai ka san ni ba mai yiwa jikoki shisshigi bace. Sannan na tabbata da daga cikin Jamila ta fito ba ma za ka ce komai ba." Hankalinsa tashi ya yi ya miƙe tsaye yana ɗan tausar kafaɗarta. "Allah Ya huci zuciyarki. Ba haka nake nufi ba." "Za ka yi mata maganar ko na kirata yanzu?" Gani ya yi za ta rushe masa ginin da bai fara saka tubali ba akan yarinyar nan Hamdiyya. Shi yasa da saurinsa ya ce ta bari shi zai yi. "Alƙawari fa za ka yi min." "In sha Allahu zan yi mata magana." Tana jin haka ta washe baki hankali kwance. A ranar da washegari da zai taho bata sake tada wata rigimar ba. Daddy kawai ta kira ta ce masa tayi mai wuyar. Ya fara shiri don ba za ta zuba ido ya bar ƴan mata a gabansa babu aure ba. Da yaji waye zaɓin da ta yiwa Anisa sai taga ya fita farinciki. Kuma da murnarsa ya kira Amma ya faɗa mata. Sai ta nuna masa ta fishi jindaɗi domin ita ba butulu bace. Duk wata gudunmawa da ta dace financially da morally ya bata wajen kulawa da cikar burin Taj. *** Rayuwa ta fara tsanani ga iyalin Abba. Da yake mutum ne mai sakarwa iyali aji daɗi da abin da Allah Ya hore masa, yanzu da ajiyar ta soma ƙasa sai suke ƙuntata. Yawancin samunsa in ka cire buƙatun gida to anyi amfani dasu wajen tarin kayan ɗaki da yake yiwa ƴan matansa. Komai na mutum uku yake saya. Yaya bata san yiwa ƴaƴa komai ba ta wannan fannin don bata sana'ar komai. Tun da ƙuruciya babu irin nacin da bata yi ba amma sam yaƙi yarda tayi saboda a cewarsa ta gama aikinta da ta aure shi. Nan kuwa yana tausayin lafiyarta ne. A ganinsa rashin imani ne zai sa ya sanya rai da ta dinga neman kuɗi a yanayin da take ciki. Gashi dama bai tsira daga dariya da surutun mutane ba. Idan ya bari tana shiga jama'a da sunan sana'a babu mamaki a karyar mata zuciya da zancen lalurarta. Shi yasa ya yiwa tufkar hanci da wurwuri. Sauƙinsu ɗaya yanzu a gidan shi ne kitson da Sajida take yi. Hamdi kuma satinta biyu da dawowa gida Anti Labiban Abuja da ta zo Kano ta roƙi alfarmar tafiya da ita idan za ta koma. Kowa ya san miskilancin Hamdi idan ta so. Suna ta zaton za ta ƙi. Sai gashi da kanta ta amince za ta bita. Weekend na zagayowa kuwa su ka tafi. * Abin haushi da takaici da Taj ya tambayi Firdaus game da yarinyar da ta kasance overall a makarantarsu wai bata san komai a kanta ba. "Ba ƙawarki bace?" "Hamdiyya ai bata da ƙawa ko ɗaya. Sai da case ɗin babanta ya tashi ne ma ta ɗan sake da mutane." Interest ya nuna na son jin me ya faru da baban nata. Firdaus kuwa ta zage ta kora masa jawabi tiryan tiryan. Har hukuncin da makaranta ta ɗauka akan ƙawayen Ummi tunda ita an cireta. Tana gama jawabin ta tashi tayi gaba abinta. Ta bar shi da shiga ruɗani da mamaki. Ba kuma komai bane ya sanya haka illa tuna sunan mahaifin Hamdi da kuma sana'arsa da Firdaus ta faɗa. Tunani barkatai ya shiga yi game da yadda aka haihu a ragaya. Indai shi ne Habibun da Alhaji yake ƙyamar ya yi koyi da halayyarsa to yaya aka yi ya yi aure? Me ya faru da rayuwarsa? Kuma wace irin rayuwa yake yi yanzu? Tabbas zai so sani. Shi Tajuddin zai so ƙwarai ya shiga cikin rayuwarsa ba don ƴarsa kaɗai da ta tarwatsa masa zuciya ba. Wasu burika ne suka mamaye zuciyarsa wanda zai so ya cimma in har shi ne wanda Alhaji ya sani ɗin. Kwana biyar kacal su ka ɗauka shi da Kamal wurin neman Habibu Simagade na Soron ɗinki. Sai gashi an kai su har ƙofar gidansa. Mutumin da ya rako su magidanci ne amma har su ka isa hirarsa akansa bata wuce alkhairinsa da kyakkyawar tarbiyar ahalinsa ba. "Ai wato banda ance kowa da ƙaddararsa da in kaga wani aka ce maka zai sami sauyin rayuwa sai ka ƙaryata." "Me yasa ka ce haka?" Kamal da Taj bai ɓoyewa komai ba illa son Hamdi ya tambayi mutumin. Shi kuwa ya daina tafiya tare da binsu da kallon rashin yarda. Sannan ya nuna Taj. "Ka ce min kai sana'ar girki kake yi. Ɗan uwanka kuma kasuwanci." "Haka ne." Da faɗa-faɗa ya cigaba da magana "zamanin yanzu ai babu yarda a tsakanin mutane. Da naji aikin naka na zata taimakon Habibu ka zo yi. Shi yasa ma zan kai ku gidan." Taj ya yi murmushi "sana'ar girki yake kenan?" "Watannin baya ba. Kafin ƴan hassada su sako shi a gaba su ka ƙwace wurin da yake haya. Banda haka ko garau garau Habibu ya dafa maka wallahi sai ka ji bambanci." Duk surutun mutumin nan bai ƙara yarda ya đara daga inda yake tsaye ba yana jiran su faɗa masa gaskiya ko su waye su sai ga Abba ya fito. Daga yanayin tafiyarsa da kamanni da ya gani da Hamdi Taj ya gane shi. Kafin ya iso wurin da su ke ya tsaya ya fi sau huɗu yana gaisawa da mutane. Wannan abu ya sake burge Taj sosai har bai san lokacin da haƙoransa su ka bayyana da farincikin da ya shiga ba. RAYUWA DA GIƁI 11 Batul Mamman💖 Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya ɗagawa Taj da Kamal hannu yana ɗan ranƙwafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani. "Ƴan samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora." Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce "na barku lafiya." "Dakata Mal. Habibu. Waɗannan fa kai su ke nema." Tsayuwa ya yi ya sake kallonsu sai dai bai tuna taɓa haɗuwa dasu ba. "To Allah dai Yasa lafiya" ya ce muryarsa na raguwa saboda rashin sanin ko ba da alkhairi su ka zo ba. Kamal ne ya amsa masa "lafiya ƙalau." Sannan ya gabatar da kansa da Taj. Jin cewa Taj chef ne kuma a yanzu haka ginin restaurant yake sai Abba ya sami kansa da daina saurin zuwa uzurin da ya fito dashi. Zancen bai wuce fita nema ba dama. "Dama nayi tunanin maganar ba za ta wuce ta ɗaukarka aiki ba. Shi yasa na rako su. Bari na wuce." Abba ya yi masa godiya sosai sannan ya nunawa su Taj gidansa. "Ko mu ƙarasa daga soro mu zauna?" A duk lokacin da ya yi magana sai Kamal yaji zuciyarsa ta karye. Allah Ya sani a yau ya daina ganin baƙin Alhajinsu. Tabbas da wannan rayuwar Taj ya faɗawa da shi ma sai ya yi kuka ba iyayensu ba. Ta yaya zuciya za ta jidaɗin ganin namijin da ya cika a halitta yana irin wannan muryar? Don ma bai san lanƙwasar jikin da sauƙi yanzu ba. Gidan su ka bi shi. Daga soron ya ɗaga murya yana ta kiran sunan Zee amma sai da ya yi kamar sau biyar su ka ga ƴar budurwa ta fito a guje. Don shi Kamal ji ya yi kamar ya taya shi kiran saboda muryar ba ta tashi yadda ya dace. "Abba yi haƙuri ban ji ba ne." Mutanen da ta gani tare dashi ne yasa ta saurin komawa da baya don bata fito da lulluɓi ba. Ta bayan ƙofa ta gaishe su. Su duka biyun yadda tayi ɗin ya burge su sosai. "Tabarma za ki kawo da ruwa." Bata jima ba ta dawo da hijabi a jikinta ta shimfiɗa tabarmar. Abba ya sake gaisawa dasu sannan ya buƙaci jin neman da su ke yi masa. "Kamar yadda ɗan uwana ya faɗa maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana'arka." "Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya." Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce "hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?" "Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?" Kamal ya yi saurin katse shi. "Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?" Abba ya tambaya da sakin fuska. "Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faɗa maka. Ina so nayi recruiting ma'aikata da wuri kafin na gama ginin." Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman abin da zai ƙara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki? Abba ya ƙare musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo ɗaya ba don yaga irin kallon da Kamal yake yiwa Taj. "Samari nagode amma ina mai baku haƙuri. Ina da mata da ƴaƴa huɗu. Zama haka a yanzu ma yana damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma'aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara." Kuɗi Taj ya ciro daga aljihunsa da sauri. "Zan fara baka albashi tun yanzu kafin mu fara aikin." "Happy!" Taj ya yi biris da Kamal. Shi kuwa bai barshi ba ya dubi Abba da kyau. "Kayi haƙuri don Allah. Bari mu tafi." Taj ya ɓata fuska "Da gaske nake ina son aiki da shi Happiness." Abba sai ya nuna kamar bai ji haushi ba. Yana ƴar dariya ya yi musu godiya kawai ya tashi. Kamal kuma haƙuri ya yi ta bashi sannan ya janye Taj su ka tafi. A mota kuwa kafin su isa gidan Ahmad anyi faɗa kaca-kaca. "So kake Alhaji ya mutu da baƙincikin ka ko me? Kai yanzu rayuwarka tana yi maka daɗi?" "Kai baka ji komai ba da aka ce bashi da aiki yanzu?" "Sai ka taimaka masa da kuɗi." Kamal ya ce har zuciyarsa. "Are you serious? Yanzu da aiki da kuɗi wanne ya fi?" Da wannan cacar bakin su ka koma gidan. Don takaici Kamal ko shiga bai yi ba. A waje ya sauke shi ya tafi. "Masifaffe." Taj ya furta yana harar motar. * Ikon Allah Zahra ta gani yau tun dawowar Salwa gida. Kwananta shida a Bauchi da aka yi musu gajeren hutum mid-semester. Abin da aka bayar da kwana goma har weekend ya kama shabiyu, a daddafe tayi shida ta dawo. Ƙarya ma ta yiwa mamansu wai field work za su je. Da yake Agricultural Extention take karantawa. Nan kuwa kewar Taj ce ta isheta har tana neman zautar da tunaninta. Abin baƙinciki kuma shi ne tunda ta tafi ko sau ɗaya bai kirata ba. Ita ce ma da ta gaji tayi masa waya harda ɗan ƙorafi. "Idan mutum yaje gida baya son damu Salwa. Tunda ba daɗewa za ki yi ba gara duka time ɗin ki ya zama na family." Ji tayi kamar ya faɗa mata magana. Ta daure ta ce "Ba ka cikin family ɗina kenan?" "In ji wa? Idan kin dawo zan baki wayata ki gani a yanzu zan chanja yadda nayi saving sunanki." Zuciyarta ta harba da wani irin farinciki ta ce "me za ka saka?" "Ƙanwata Salwa. Yadda nake saving sunan ƴan gidanmu. Manyan kuma ina saka musu Yayata" Kuma bai barta ta gama jin haushin hakan ba kamar shi ys kira ya ce "bari na barki ki huta haka. Sai da safe." Azahar a Kano tayi mata. Tana zuwa gidan ko hutawa bata yi ba ta karɓi girkin dare. Zahra tana ta faɗa mata ta jira ayi la'asar amma ta ce gara tayi da wuri tunda tuwo ne. Daga nan ta haɗa juice ɗin abarba, mangwaro da ɗanyar citta saboda ta kula Taj yafi son fresh fruit juice. Da su ta taho tun daga Bauchi. Bayan tayi sallar la'asar ta shiga ɗakin Taj. Yana ƙullewa idan zai fita amma baya taɓa zare key ɗin. A cewarsa tunda masu gidan suna da kaya a ciki me yiwuwa za su buƙaci shiga idan baya nan. "Salwa me ki ke nema a nan?" Zahra ta taho da sauri da taji alamun buɗe ƙofar. Tsintsiya ta sameta tana gyarawa ɗauri. Tana ganinta tayi murmushi. "Anti Zahra gyara ɗakin zan yi." Curiosity yasa Zahra ta ɗan leƙa. Baya buƙatar wani gyara na a zo a gani. "Yana gyarawa. Ki fito don yayanki sai da ya yi min warning akan bari ke ko mai aiki ku shiga ɗakinsa." "Yau ɗaya dai Anti. Ai gara ayi masa gyara sosai. Tunda baya gida zan yi sauri." Tafiyarta tayi ta soma da wankin toilet. A sink inda ya tara boxers da singlets da socks ta haɗa komai ta wanke. Sai ta bar masa a bucket yadda zai shanya idan ya dawo. Wankin ma ana yi ana rurrufe ido saboda kunyar da ta dinga ji. Ɗaki ya fito fes dashi don har bedsheet sai da ta canja masa. Bayan ta gama komai ta rura gawayi akan gas cooker ta wuce da robar turaren wutan da ta siya online. Tun Zahra na bin ta da ido har tsananin mamaki yasa ta koma cewa 'uhmmm'. Yau ko ɗakin miji ne aka yiwa haka ai dole ya yabawa matar balle wanda a iya saninta babu soyayya a tsakaninsu. Ahmad ne ya fara dawowa gidan. Lokacin tuni Salwa ta gama har tayi wanka. Doguwar rigar atampa ta saka da ƙaramin mayafi ta zauna a falo tana ta ƙamshi. Wannan karambani duk aminiyarta ce ta kitsa mata. A cewarta da kyautatawa ake sayen soyayyar namiji. Jindaɗin yadda take kula da shi zai kwaɗaita masa mallakarta a matsayin matar aure. Wuraren ƙarfe biyar da rabi Taj ɗin ya shigo da sauran fushin faɗansu da Kamal. Sama sama ya gaisa da Ahmad. Ya ɗauki baby Aisha bayan gaisawa da Zahra. Salwa kuwa sai da tayi masa magana ya kula da ita. Ya dakata da tafiya "Har hutun ya ƙare? Ko dai kin dawo birnin da yafi ƙauyenku?" Ya ce da ita da zolaya. Murmushi kawai tayi. Ahmad ya girgiza kai. Dama tunda ta dawo da wurwuri ya san ba zai wuce saboda taji cewa Taj ya kusa komawa bane. Da Aisha ya shige ɗaki a kafaɗarsa ya kwantar da ita a kan gado. Ya yi mamakin yadda ya sami ɗakin. Waye ya gyara? Komai an killace shi gwanin sha'awa. Ya shiga toilet nan ma ƙamshi kawai yake tashi. Da sauri ya duba sink da ya tuna ya bar kaya da zai wanke sai yaga babu. Nan fa yaji wani abu ya taɓa masa rai. Yana duba bokiti kuwa sai gasu a wanke an matse. Ya fiddo gajeren wandonsa ɗaya ya tabbatar dai a wanke yake. Bai san lokacin da ya sake shi a bokitin ba. Ya ɗauki Aisha ya koma falo fuska babu annuri. "Anti Zahra waye ya gyara min ɗaki ne?" Ahmad ya yi saurin kallon Zahra ita kuma ta nuna Salwa dake faman doka murmushi tana sunkuyar da kai. Sauƙin hali irin na Taj bai hana shi nuna ɓacin rai ba kuwa. "Ke ki ka wanke min underwear?" Idanun Zahra waje su ka yo. Ahmad kuwa bai san lokacin da ya ce "underwear kuma?" Da me tambayar da kuma yanayin maganar Ahmad sai Salwa taji tsoro. Taj ya murtuke fuska. "You shouldn't have. Next time please kada ki taɓa min." Ya duƙa ya miƙawa Zahra ɗiyarta sannan ya dubi Ahmad "Yaya zan ɗan kwanta kafin magrib. Da headache na dawo." Shigewa ya yi ya barsu. Da Zahra taga irin kallon da Ahmad yake yiwa Salwa sai ta tashi tsam ta shige ɗaki. Ai kuwa kamar jira yake ya soma faɗa. "Wannan wane irin rashin daraja kai ne haka Salwa? Are you crazy or what?" Kai ta sunkuyar tana kuka. Ba kuma na faɗan yayanta ba. Fushin Taj da tsoron kada gwanintar ta tayi sanadin nesanta ta dashi kawai take gudu. "Ba tun yau na kula kina son Taj ba..." sai a lokacin ta kalle shi hankalinta na tashi. Ya taɓe baki "wanda bai damu da lamarinki bane kawai ba zai gane ba." "Yaya..." Tausayi ta bashi don ta soma kukan gaske. Amma hakan ba zai hana shi faɗa mata gaskiya ba. "Kin san komai dake faruwa a gidanmu da dalilin zamansa a gidan nan. He is trying his best ya daidaita da Alhaji. Kina tunanin soyayyar Taj dake, ƴar matar da ya saka zai faranta masa rai?" A tsorace ta kalle shi "Yaya ni meye laifina?" "Salwa kin fini sanin rigimar Mama tunda a gabanta ki ka tashi. Ke shaida ce irin yadda ta fitini Abbanku. Abubuwan da take yi bana jin akwai wanda Alhaji bai sani ba. Tun da in naso zuwa wajenta hutu baya son bari saboda yana gudun kada na koyo abin da zai haɗa rigima a gidanmu." Hawaye ta goge da mayafinta. Da muryar da kuka ya gama dusashewa ta ce "To ni yaya zan yi? Ba ni na ɗorawa kaina ba" "Kada ki yi komai sama da neman zaɓin Allah. Sai kuma tsare mutumci da darajarki ta mace. Ke kin sani da ina nan ko ɗakinsa ba za ki shiga ba. Ba kuma don ban yarda dashi ba. Amma wankin underwear...haba Salwa? It was totally wrong." Daga ƙarshe rarrashinta ya yi da jaddada mata lallai kada ta ƙwallafa rai akan Taj domin indai Alhaji bai amince ba da wuya ya aureta. *** Hutu yana ta daɗi. Hamdi ta zaga gari sosai da Anti Labiba da yaranta. Basu da ƴan uwa sosai a garin sai abokan arziƙi. Shi yasa yawon nasu yafi ƙarfi a wuraren shaƙatawa da ciye ciye. Wata rana sun dawo da yamma liƙis Anti Labiba ta ce da Hamdi ta ɗora abinci. Tayi tuƙi ta gaji ga bebinta na ta tsala ihu. Ɗaki ta shiga domin yiwa yarinyar tsarki amma har ta fito Hamdi bata ɗora komai ba. Gyaran kitchen ɗin take yi saboda ana gama cin abincin rana su ka fita. "Hamdi baki ji na ce ki ɗora jallof ɗin macaroni ba?" Murmushin ysƙe tayi "Anti Labiba don Allah ki ɗora. Duk wani yanke yanke zan miki." Ƙanƙance ido Anti Labiba tayi. Sai kuma ta tuna wata hirarsu da Sajida lokacin da ta zo mata zaman biƙi. Tabbas ta faɗa mata a duniya babu abin da Hamdi taƙi jini bayan namijin da ya iya girki kamar girkin kanshi. Ita duk abin da za ta ɗora akan wuta mai suna abinci zuciyarta bata son yi. Ba kuma komai ya janyo ba illa tsohuwar ƙiyayyar da take yiwa sana'ar Abbansu. Kuma fa da yake a wurinsa ta koya da wuya ka ci abincinta baka yi santi ba. "Baki iya girkin bane ko me?" "Idan na dafa ba lallai na iya ci. Don Allah ki ɗora kinji Anti..." Sosai abin ya bawa Anti Labiba mamaki. Hamdi bata taɓa yi mata ƙiwar aiki ba. Ga iya sammako ta gyara gida tun zuwanta. Amma fa duk cikin aikin nata bata taɓa yin girki. Ita kuma Anti Labiba bata damu ba saboda mijinta baya son cin girkin mutane musamman a gida. Abincinta tayi ta gama. Hamdi sai taji babu daɗi don sai da aka matsa mata taci abincin. Bayan sun gama ta bita ɗaki ta bata haƙuri. "Ni ban yi fushi ba. Kawai ina mamakin yadda aka yi ki ka zafafa akan harkar girkin nan." "Idan ina yi sai Abba ya dinga faɗo min a rai. Wallahi Anti Labiba bana son ganin shi a kitchen kwata-kwata. Yanzu ma ina ta fatan Allah Yasa ya sami wata sana'ar tunda an karɓe gidan abincin." Magana take yi muryarta tana rawa. Anti Labiba ta saƙala hannunta a kafaɗarta. "Nayi zaton kin daina abubuwan da ki ke yi da naga yanzu kullum sai kun yi waya dashi." "Ni me nake yi?" Ta tambaya da zumɓura bakin. "Babu komai." Ta shashantar da zancen "snacks da pastries fa? Su ma kamar girki ki ka ɗauke su?" "Don ban iya bane amma ina so." "Saboda basa cikin girkin da Abba ya koya mu ku ko?" Sunkuyar da kai Hamdi tayi a kunyace. Ita kuwa Anti Labiba sai wani tunani ya ɗarsu a zuciyarta. Ba dai za ta ce komai ba sai ta tuntuɓi ƙawarta Hauwa gobe. Idan Hamdi tayi sa'a za ta koyi small chops da youghurt from one of the best a garin Abuja. *** Kwana biyu Taj ya yi baya zuwa site ɗin aiki. Idan Kamal ya zo sai ya ce kansa na ciwo. Abu ya taru ya dami Kamal sosai. Lokacin tafiyar Taj na gabatowa amma ya sanyawa ransa wani abu daban. Shi kuma yafi son ko zai tafi ya zamana aikin da ya rage ba mai yawa ba. Gara aci ƙarfin komai a gaban mai wurin. Yau da ya bar gidan Ahmad wucewa ya yi gidan Abba Habibu. Bai wahala wurin gane gidan ba. Shaɗaya na safe ta ɗan wuce. Ya tura wani yaro ayi masa sallama da shi. Wata budurwa ba wadda ya gani a zuwansu na farko ba ce ta fito ta gaishe shi. "Abba ya fita amma yanzun nan zai dawo. Ba nisa ya yi ba." "Ke ma ƴarsa ce?" Kamal ya kasa daurewa sai da ya tambaya. Ita da ta rannan da ya riƙe Zee aka kirata su na kama sosai. Kyawawan ƴan mata ne masu nutsuwa. "Eh." "Yaya sunanki?" "Sajida." Ta amsa masa. Kujerar roba ta kawo ta ajiye masa a soron ta koma ciki. Kimanin minti goma a tsakani sai ga Abba ya dawo. Mamakin ganin Kamal ya yi sosai. Su ka gaisa sannan Kamal ya ɗan rissina kai. "Na san za ka yi mamakin dawowata bayan yadda nayi a wancan zuwan namu." "Babu komai. Allah dai Yasa lafiya." "Alhamdulillah" Shiru ya kuma biyo baya har sai da Abba ya sake tambayarsa sannan ya yi magana. Da farko ya fara da bashi labarin burin Taj tun ƙuruciya da duk wani abu da ya biyo baya. "Wallahi ban hana shi don ƙyama a gareka ba. Amma indai Alhaji ya sami labarin kuna tare bana jin zai zai yafewa Taj." Kallonsa Abba ya yi sosai yana jinjina kai "to amma a ina mahaifin naku ya sanni." "Soron ɗinki. Shi ma mutumin cikin gari ne." A karo na uku Abba ya sake ƙurawa Kamal idanu na wasu ƴan daƙiƙu sannan ya yi murmushi. "Yaya Hayatu ne mahaifinku?" Da sauri Kamal ya kalle shi "ya akayi ka gane?" "Da gaske ku ƴaƴansa ne?" Abba ya kuma tambaya yana miƙewa tsaye. "Ƴaƴansa ne." Ya faɗi yana gyaɗa kai. Jiki a matuƙar sanyaye Abba ya ce. "Ka faɗawa ɗan uwanka kada ya sake zuwa gidan nan. Kai ma ka tashi ka tafi." Kamal bai jidaɗin yadda Abba ya koma ba. Da alama ba mutum bane mai son hayaniya. Amma jin waye mahaifinsu ya canja yanayinsa. Hannu ya sanya ys fiddo dubu ɗarin da ya tanada tun a gida. "Ga wannan ka ƙara jari don..." "Ɗauke kuɗinka yaro. Bana so ko da wasa Yaya Hayatu ya yi tunanin da gangan na kusanci rayuwarku." Ciki ya shige ya bar Kamal riƙe da kuɗin yana fargabar yadda za su kwashe da Taj idan ya sami labarin zuwan nan nasa. RAYUWA DA GIƁI 12 Batul Mamman 💖 Wannan shafin yana ɗauke da tallan _LUCIOUSBITES_ gidan kashe ƙwalama. Mazauna garin Abuja ga taku ta fito da kanta ba saƙo. Taron biki, suna, conference, seminar ko reunion ne? Ko kuwa sha'awar kashe kwaɗayi ce ta tashi? To ku sha kuruminku. Hauwa aka luciousbites.ng ta fito domin fitar daku kunya a ko ina. Domin ƙarin bayani kuna iya tuntuɓarta a kan wannan layi 08174821831. *** Da gaske ciwon kai ke damun Taj saboda bai iya sanya abu a rai ba. Ya so ƙwarai ya ja Abban Hamdi a jiki. Ba don neman soyayyarta ba, wannan da kansa zai yi ba ya buƙatar taimakon kowa sai Allah. Mahaifinsa yake son nunawa a rayuwa kowa da ƙaddararsa. Kuma a kowacce sana'a indai ba addini ne ya haramta ta ba, akwai mutumin banza da nagari. Don al'ada ta ƙyamaci wani abu ba shi yake nufin yinsa laifi bane. Sannan uwa uba akwai uzuri ga ƴan Adam domin ba kowa ke dawwama cikin saɓo ba. A ganinsa rashin aikin Abban Hamdi wata hanya ce ya samu da zai iya sako shi cikin tasa sana'ar. Idan Allah Ya sanya musu albarka kasuwa ta buɗe Alhaji zai iya fahimtar kowanne bawa akwai hanyar arziƙinsa. Sannan ko iyaye ba sa so indai Allah bai haramta ba sannan ɗan bai kasance mai saɓawa kowa ba, albarka za ta iya binsa duk inda yake. Ƙarar wayarsa ce ta tashe shi daga kwanciyar da ya jima yana yi. Sunan Salwa da ya gani ya sanya shi yin tsaki. Ita bata san gudunta yake yi ba? Har yau yana mamaki da bata yi tunanin kamar yadda mata ke killace kayansu na ciki haka kowanne namiji da ya san mutumcin kansa yake yiwa nasa ba. A iya saninsa ƙiwa da rashin son aikin namiji ba zai sa ya bawa ƙanwarsa shaƙiƙiya wankin ƙananan kaya ba. Ballantana kuma wadda babu wani abu da ya haɗasu. Bari ya yi kiran ya katse sannan ya kirata. "Don Allah ka buɗe min ƙofa na manta muƙullina a ciki." Falo ya fito sanye da dogon wando na sanyi ruwan toka da farar shirt. Ya buɗe mata jamlock ɗin ya juya zai koma ɗaki sai ta kira sunansa. Tun ranar da ta gyara masa ɗaki da faɗan da Ahmad ya yi mata ta rage kuzari da karsashi a komai. Fargabarta ita ce ɓacin ran da ta gani tare da Taj da kuma shawarar da Ahmad ɗin ya bata akan ta cire shi daga ranta. Da za ta iya da tun kafin ta zubar da ajinta ta cire shi ta ƙarfin tsiya tunda ta fahimci bata gabansa ta fuskar da take so. Sake kiransa tayi da bai juyo sosai ba. "Ya Taj don Allah ka yi haƙuri akan abin da ya faru rannan. Na fahimci kuskurena." "Ya wuce, kada ki damu." Fasa tafiya ya yi da ya tuna ƙanwar Ahmad ai ƙanwarsa ce shi ma. A matsayi guda duk su biyun su ke zaune a gidan. Shi yasa yaga dacewar ya bata shawara. "Ko don gaba ki kiyaye irin wannan. Ba ni ba, ko Yaya ki ka wankewa undies bana jin za ki burge shi." Kai ta sunkuyar sai ya yi murmushi "ku mata ba kwa son a taɓa koda jakarku. So just imagine ace ni nayi miki wannan karambanin. Will you realy be happy that I helped?" Kunya maganar tashi ta bata. Ta rufe ido ta shige ciki da sauri tana mayar da numfashi. Da tunanin yadda ya yi maganar a tausashe ta ƙarasa ɗaki. Sai da cire kaya za ta shiga wanka ta kuma tariyo zancen sai taji faɗuwar gaba. Shin magana ya yaɓa mata ko kuwa ya sauko ne? Domin tabbatar da matsayin maganar da sai ta tura masa SMS da yamma da ya fito falo suna hira da Ahmad. Daga kitchen ta leƙo bayan ta tura tana kallonsa ya duba saƙon, ya kuma rubuta reply. Da wani irin sauri ta koma ciki ta buɗe. Nata ta fara bi inda ta rubuta masa saƙo kamar haka. (Ya Taj nagode kuma ina mai sake baka haƙuri. If I am forgiven please give me a chance to be your friend.) Shi kuma ya rubuta wannan amsar. (Kada ki matsawa kan ki da son neman wani relationship dani bayan already akwai. Ƙanwar Yaya Ahmad ƙanwar Taj ce.) Ranar da ƙyar ta gama girki. Saƙon dake cikin amsarsa ya fito ɓaro ɓaro. A matsayin ƙanwa kaɗai ya ɗauketa. Daga yau za ta gwada cire shi daga zuciyarta. Sai dai abin da wuya domin son bai yi shawara da ita ba ya yi mata kamun kazar kuku. *** Faɗa Yaya take kamar ta ari baki a waya. Sajida da Zee su ka matsu ta gama ta basu labarin me ya faru. Sun dai fahimci Hamdi ce tayi wani laifin. Ita kuma Anti Labiba da su ke wayar banda dariya babu abin da take yi. "Abin dariya ki ka ɗauki abinnan Labiba? Wace ƴar arziƙin ce za ta guji girki kamar ba mace ba?" "Yaya ki barni da ita don Allah. Na faɗa miki ne fa kawai saboda kada ku ji shiru bata dawo ba. Zan ɗan riƙeta ne in sauke mata gammon da ta ɗauka." Cewar Labiban tana murmushi. Yaya ta gyara zama tana hararar masu matsowa jikinta don son jin me ake cewa "amma fa samun wuri ne. Bata taɓa gwada min wannan shegantakar a nan ba. Iyaka dai in tana gida girki ya faɗo kanta tayi ta cika tana batsewa kenan. Ita a dole bata son sana'ar uban da yake wahaltawa rayuwarta." Haƙuri Anti Labiba ta bata "ki barni da ita kawai Yaya. Girki kuma tunda ta iya ai magana ta ƙare." A haka su ka yi sallama bayan ta sake roƙon alfarmar kada Yaya ta yiwa Hamdi magana idan sun yi waya. Ƙarfe uku bayan yaranta biyu sun tafi islamiyya ya rage jaririyar da take goyo da yayarta mai shekara biyu da rabi. Ta fito abinta cikin shiri ta sami Hamdi a falo tana kallo. "Hamdi zan fita amma ba jimawa zan yi sosai ba. Ga kaza can na fito da ita ki yi pepper chicken kafin na dawo. Sai ki haɗa coleslaw. Na riga na dafa jallof ɗin shinkafa." Jin abin da ta ce ba shiri ta kashe TV ɗin. "Anti ni zan girka?" "Kina nufin zancen da mu ka yi jiya da gaske ki ke?" Anti Labiba ta ƙanƙance idanu. "Anti wallahi ni..." "In fasa fitar kenan komai mahimmancinta in ƙarasa girki ko?" "A'a Anti. Amma naga tattali ma yana da kyau. Tunda anci kifi da rana a bar kazar sai gobe." Ƙiris ya rage Anti Labiba ta fashe da dariya. Fuskar Hamdi na nuni da cewa da gaske take. Lallai idan ta biye mata ba za ta sami biyan buƙata ba. "Abbansu ne ya aikeni. Gashi kuma yana hanya tare da abokinsa. Na zata ke me fitar dani kunya ce..." ta sauke mayafinta "nagode da ki ka nuna min ban isa ba." Jikin Hamdi rawa ya fara. Bata son ayi fushi da ita ko kaɗan. Musamman mai kyautata mata. Da sauri ta bar falon ko kallon Antin ta ta bata kuma yi ba ta shige kitchen. Anti Labiba ta ƙunshe dariyarta ta fice. Bata zame ko ina ba sai bayan National Military Cemetary da an ɗan wuce National Stadium a nan cikin umguwarsu Karon majigi. Wurin aminiyarta Hauwa taje don nan ne take da tabbacin za ta juyawa jin kunya baya. Daga bakin ƙofa su ka rungume juna saboda sun ɗan kwana biyu basu haɗu ba. "Sannu da zumunci Labiba. Ina ta waƙar sake zuwa ganin baby amma kwanakin nan orders suna neman fin ƙarfina." Cewar Hauwa tana karɓar goyon Anti Labiba. "Mu ai haka muke so. Ɗan kasuwa baya kiran yawa. Ki dai ce kasuwa tayi albarka ki kuma godewa Allah." "Alhamdulillah ala kulli hal." Hira su ka ɗan taɓa sannan Labiba ta faɗi abin da ya kawota. "Ni kuwa kina ɗaukar ɗalibai ki koyar dasu?" "Ban fara ba amma na gama duka shirye shiryen da ya dace. Nan da ƴan kwanaki za ki ji sanarwa." Anti Labiba ta saki jiki "Masha Allah. Nayi sara akan gaɓa. Dama ƙanwata nake son kawo miki. So nake ta goge sosai a harkar snacks ɗin nan ita ma." Hauwa ta ce "akan ƙanwarki ki ke tambayar class dama? Ai kin san ko bana yi dole na koya mata." "Allah Ya ƙaro kasuwa. Nagode sosai." "Babu komai. Ai yiwa kai ne." Hirarsu su ka cigaba da yi inda Labiba take ta koɗa daɗin kayan ciye ciyen da Hauwa ta ajiye mata. Da za ta tafi ta sayi frozen samosa. * Da yake babu wani abu da zai ɗauke mata hankali, bata wani jima ba ta gama ta gyare kitchen ɗin. Tana jin an taɓa ƙofa kuwa ta soma murmushin neman shiri. Ita kuma Anti Labiba sai da ta zo bakin ƙofa ta daina fara'a. Fuska a cinkishe ta shiga gida. Hamdi ta shiga damuwa. A irin miskilancinta ɗaki za ta tafi amma ita shaida ce. Ganin ɓacin ran Anti Labiba na nufin anyi mata abin da ya ɓata mata rai sosai. "Anti zo ki gani. Na gama." "To an gode." Ta bata amsa ko kallonta bata yi ba. Fuskarta canjawa tayi kamar tayi kuka ta ce "Allah na daina Anti. Ki yi haƙuri." Ledar pack ɗin samosan ta bata ta ce ta soya. Wannan karon ko kaɗan bata nuna komai na rashin jindaɗi a fuskarta ba. Da ta gama Anti Labiba ta ce ta ci ta faɗa mata ko da daɗi. Tunda ta gutsira ta kama murmushi. "Yayi miki?" "Da daɗi sosai." Sai lokacin Anti Labiba ta saki fuska ita ma tayi murmushi. "So nake ki koma gida da sana'ar hannu. In sha Allah nan da kwana huɗu za ki fara zuwa wurin Hauwa koyon waɗannan abubuwan." Farinciki sosai ta gani a tare da Hamdi. Ta dinga dariyar yadda ta canja lokaci guda. A zahiri tana yiwa ƙannen nata uzuri idan su ka nuna ƙyamar wani abu na Abbansu. Maganar gaskiya duk kirkinsa akwai abin da fa dole ya tsayawa mutum a rai. Ƴaƴa yawanci babu ruwansu da talauci ko arziƙin iyayensu. Indai akwai jinƙai da kulawa a tsakaninsu za ka ga suna ƙaunar abinsu da zuciya ɗaya. Amma duk lokacin da kaga ƴaƴa na kunyar nuna iyayen a wasu wuraren, za ka samu nakasu ta wanni fannin. Inma dai daga ɓangaren ƴaƴan in aka samu marasa godiyar Allah, ko kuma daga iyayen idan sun shuka wani abin da zai kunyata yaransu. Ga dai shekaru sun ja. Amma har yanzu kallo ɗaya ya ishi mai idanu gane waye Abba Habibu. Irin haka ne abin da ake gudu. Kayi abu ka barshi amma tasirinsa ya gagara barin rayuwarka komai tsahon lokaci. *** Kwana biyu Kamal ya ɗauke ƙafa daga gidan Ahmad. Taj ya ƙule iya ƙulewa. Kuma ya naɗe ƙafa ba ya zuwa site ɗin aikinsu. Kamal ɗin kaɗai ke zuwa ya wuni yana monitoring komai. A rana ta uku ne ya gaji da gudun rigimar da za su yi da Taj akan zuwansa gidan Abba yaje gidan Ahmad ɗin. Bari ya yi sai gabanin azahar lokacin da ya tabbatar yayan nasu yana wajen aiki sannan yaje. Babu kowa a gidan sai Taj da Zahra dake kitchen. Fitowa tayi su ka gaisa sannan yaje ƙofar ɗakin Taj. A rufe take, ya yi sallama sannan aka buɗe. Taj bai jira shi ba ya koma ya zauna akan gado ya cigaba da aikin da yake a laptop ɗinsa. "Wai nan gaba kake dani?" Kamal ya faɗi da sanyin jiki. "Kai zan tambaya da ka daina zuwa gidan nan." Taj ya mayar masa rai a ɓace. Tausayinsa Kamal yake ji. Bayan abubuwan da yake rayuwa yana haƙuri da rashinsu, baya jin zai juri wani abu ko yaya yake ya haɗa su rigima ba. Zai fara bashi haƙuri sai aka kira Taj ɗin. Abinka da sabonsu na rashin ɓoyewa juna komai. Gaisawa kawai su ka yi da Amma ta sako zancen Anisa. Ya kunna speaker ya yafito Kamal da hannu. "Taj kana ji na kuwa?" "Ina ji yanzu Amma. Me kike cewa?" "Maganar Anisa. Kai baka ce min komai ba. Na share don ina zaton sai ka dawo za mu yi magana. To jiya Hajjo ta kira ta ce za ka wulaƙanta mata jika. Idan ba ka so ka faɗa ta samo mata wani." Hannu Kamal ya dinga juyawa yana son sanin me take nufi. "Amma da kin bari na dawo dai." "Ai ka san halinta. Yanzu sai ta juya zancen. Ba ka son Anisan ne?" Ƴar dariya ya yi daga ji bata kai zuci ba. Baya son karɓar abin da zai zame masa matsala don ko babu Hamdiyya shi bai taɓa kallonta a matsayin da ya wuce ƙanwa ba. Idan kuma ya ce baya so nan ma duk wanda ya san tarihinsa sai ya zage shi. "Wa zai ƙi mace kamarta?" "Wannan wace irin amsa ce?" Sarai ya ji ɓacin rai a cikin muryarta. Ya kalli Kamal yana neman agaji. Shi kuma sai ya raɗa masa a kunne cewa ya faɗa mata zai je Abujan su fara fahimtar juna. Haka kuwa ya faɗa mata. Nan da nan sautin muryarta ya koma daidai. Ta dinga shi masa albarka. Bata ga laifin Hajjo ba da take so wa jininta Taj. Da tana da sauran ƴa ma kafin Hajjon tayi masa tayim Anisa za ta haɗa su. Abu guda ne dai ta ajiye a ranta. Idan yaje yace baya so to fa dole a haƙura. Don sun riƙe shi bata so ayi amfani da hakan a matsayin dalilin yi masa tilas. Zai zamana ba don Allah su ka taimaka masa ba. Dariyar mugunta Kamal ya dinga yi bayan Taj ya gama faɗa masa yadda su ka yi da Hajjo. "Salwa kuma fa? Ko har yanzu ba fahimci ta mato maka ba?" "Hmmm, ai baka san me tayi min ba..." ya sake kwashe labari ya sanar dashi. Kamal dariya harda faɗowa daga kan gado. Faɗan da su ka manta dashi kenan aka koma hirar masoyan Taj. "Yanzu dai da gaske Abujan zamu je." "I'm not interested Happiness. Ina tsoron kada naje su zata na amince." "Sai mu yi mata bayani mu nemi haɗin kanta" ya ɗan kalli Taj ɗin "akwai wadda ka ke so ne?" Kamar ya faɗa sai ya tuna reaction ɗin Kamal akan Abban Hamdi kawai ya fasa. Shiryawa su ka yi su ka tafi site tare. A hanya "Na fa yi maka laifi Happy. Naje na sake lalata chance ɗin Mal. Habibu ya karɓi aiki da kai." Ana kukan targaɗe, ga karaya ta zo. Taj ya gama sauraron Kamal ya ma rasa abin da zai ce. "Kayi shiru" Kamal ya furta yana satar kallonsa. "Ka san bana ganganci da rayuwata. Ba don haka ba duka zan maka." "Sai da naje nake ganin kamar ban kyauta ba. Amma ni yadda ya ɗauki zafi da jin sunan Alhaji yafi damuna. Kana ganin ko shi ma yadda yayi maka haka yayi masa? Naji Yaya Hayatu ma yake kiransa." Da daddare Taj ya kira Hajiya ya tambayeta game da Abba Habibu. Don kada ta zargi komai sai ya ce, "Hajiya don Allah mece ce alaƙar Alhaji da Habibu ɗinnan?" "Me yasa kake son sani?" "Don na kiyaye. Kada na taɓa bari girki yasa nayi koyi da irin tasa rayuwar" Hajiya na jin haka kuwa tayi masa bayanin da yake nema. Alhaji ya so Habibu tamkar ƙaninsa na jini. A rayuwarsa kamar yadda ƴaƴansa su ke gani yana son kyautatawa duk mai mayar da hankali a harkar ilimi. To Habibu sai dai ace masa gifted. Kana faɗa yake kwashewa. Sai ka rasa wace irin ƙaddara ce ta karkata masa rayuwa ta mayar dashi ɗan daudu. Gashi a lokacin daudancin mafi akasari ba a raba shi da kawalci da sauran alfasha mai zubar da mutumci. "Da ya dawo daga Saudiyya yayi ta bibiyar Alhaji yana neman ya taimaka masa da jari ko ya ɗauke shi yaron shago. Amma waccan ƙyama da yake masa tun farkon fara daudun tasa yayi masa kora ta wulaƙanci." Jikin Taj ya yi sanyi sosai. Idanunsa su ka kaɗa su ka yi ja. "Bai taimake shi ba?" "Inaaa. Ka san shi da kafiya. Tunda ya juya masa baya bai ƙara waiwayarsa ba. Ni dai ƙarshen labarinsa da naji ance ya buɗe shago yana abincin sayarwa." Shiru taji ya yi da tana magana. Ta rage murya, "Taj ba za ka sauke naka ƙudurin kayi yadda yake so ba?" "Hajiya ba haram bane. Ki cigaba da sani a addu'a. In sha Allah ba zan taɓa yin abin da za ku yi baƙincikin zaɓina ba." *** A cikin wata guda mamallakiyar Luciousbites.ng wato Hauwa ƙawar Anti Labiba ta san tana tare da haziƙar ɗaliba. Duk snack ɗin da su ka wuni koya to in sha Allah washegari idan Hamdi tayi kuskure ba zai yi yawa ba. Ita babu ƙiwa ko ha'inci, ɗaliba kuma mai ƙoƙari. Aikin nasu yana tafiya yadda ake so. Wasu dama ta ɗan iya sai dai yanzu ta koyi hanyar da ta dace da zamani wurin inganta saninta. Sannu a hankali ta ƙware wajen yin doughnut, samosa, meatpie, springrolls, chinchin irin na ƴan gayu, gashin nama da kifi kala kala. Da kuma uwa uwa haɗaɗɗen plain youghurt, coconut infused youghurt da yogo fura. A gida irin farincikin da Anti Labiba ke gani a tare da ita har mamaki take bata. Mijinta ma sai da ya ce wai gani yake kamar an canja ta da wata. Yaran gidan kuwa tunda an yarje mata gwada abin da ta koya, sun kwashi gara ba kaɗan ba. A ci a gida kuma aje makaranta. *** Wannan wata gudan harda ƴan kwanaki a ɓangaren Taj cikin wahala su ka zo masa. Kacokan ya ajiye aikinsa bayan ya wayar nan da ya yi da Hajiya. Ya karkata akalarsa zuwa ga son lallai sai Abba yayi aiki tare da shi. Kamal da yaga ba zai iya hana shi ba sai ya bashi goyon baya. Ranar farko tun safe ya shirya yaje ƙofar gidan Abba. Bai aika a sanar da zuwansa ba. Ya yi zamansa a cikin mota har Abban ya zo fita sannan ya tare shi. Ai kuwa yana ganin shi ya sauya fuska. "Baka sami saƙona a wajen ɗan uwanka ba?" Gaishe shi Taj ya yi. Bawan Allah yana faɗan ya tsahirta ya amsa sannan ya cigaba. "Bana son rigima da mahaifinku. Ban san me ku ka ji game dani ba. Amma ko ma mene ne nufinku ni da Allah na dogara." "Don Allah ka saurareni. Da alkhairi na zo maka." Cikin gida Abba ya koma. Bai ƙara fitowa ba har la'asar. Taj ya tafi amma bai karaya ba. Washegari ma ya sake zuwa. Ranar Abba ko sauraronsa bai yi ba ya wuce ya yi tafiyarsa. A haka su ka cinye sati guda. Wasu kwanakin duk sammakonsa idan ya zo zai samu Abban ya fita kafin ya zo. A kwana na tara Taj sai ya canja tsari. Tare su ka zo da Kamal wanda ya ce zai bada haƙurin abinda ya yi kwanaki. A zatonsa ko shi yasa Abban yaƙi sauraron Taj. Yaro ya tura ya ce a faɗawa Abba su Taj sun zo kuma wallahi yunwa suke ji. Sajida ce kaɗai a gida da Yaya. Halifa da Zee suna makaranta. Sajida tana jin saƙon yaron ta figi mayafi ta fita. Yaya tana ta kiranta taƙi dawowa. Abba kuwa ƙwafa ya yi. "Bawan Allah zamu haɗaka da ƴan sanda wallahi. Bar ganin kuna da kuɗi" ta harare su duka "wallahi muna da masu tsaya mana mu kara daku a hukumance." "Ki yi haƙuri ƙanwarmu. Aiki kawai ƙanina yake son yi tare dashi. Shi ma sana'ar girki yake." "To ya ce baya so. Ai.ya faɗa mana ko ku su waye." Ta ce da tsiwa. "Ɗan tsaya mu yi magana" Taj ya ce bayan ta gama magana. Tsayuwar tayi tana karkaɗa ƙafa ita a dole ranta ya ɓaci. Tarihinsa ya bata a taƙaice. "I believe yadda nake son in dawo da ƙimata a wurin Alhaji haka Abbanku zai so mutane su yi masa uzuri su karɓi sabuwar rayuwar da ya gina." Cikin mutuwar jiki ta ce "haka ne." "Ina son yin aiki da Abba amma a setting da ya bambanta da wanda ya saba. A inda maza masu yin komai na maza su ke girki. Burina idan an kwana biyu rayuwarsa tayi daidai ta yadda masu aibata shi a bayansa za su ji kunyar abin da su ka yi." Ƙwalla ta saukowa Sajida "zai yiwu? Kana ganin wannan abubuwan na mata za su barshi?" Kamal ya sanya baki "Allah aka ce. Ba yadda za ayi ka bar kowa ka kama Shi sannan kasa rai da ganin ba daidai ba. Taj only wants to help." "Mece ce ribarsa idan ya taimaka masa?" "Mutane su fahimci akwai sana'o'in da basu keɓanta ga mata ba kawai. Sannan ƙyama ba ita ta dace da irin wanda ya yi rayuwar Abba ba. In an bi hanyoyin da su ka dace shi ma zai karɓu a cikin mutane kamar kowa" Kamal ya sake bata amsa. Abin nema ya samu Sajida ta koma gida da murnarta. Abba na ganin hawayenta ya tashi. "Me su ka yi miki?" Ta fashe da kuka "don Allah Abba ka sauraresu. In sha Allah wannan wahalar neman wurin hayar zai ƙare." Fita ya yi ya sallame su. Taj sai ya ƙi motsawa. "Zan sa a nemo min mahaifinka ya zo ya tafi da kai." "Zan tafi amma don Allah ka bani abinci. Yunwa nake ji." Abba ya kallesu. Duk sun yi laushi. "Ba ku karya bane?" Ya tausasa murya. Sai muryar tasa ta sake yin ƙasa. "Ni dai na sha tea. Happy kuma bai ci komai ba." Abba ya kalli Taj da mamaki "Happy kuma?" "Eh. Sunansa kenan" Kamal ya bashi amsa. "Yana sallah kuma?" Abba ya tambaya harda matsawa baya. Me kuwa za su yi banda dariya. Taj yana yi ya riƙe ciki. Abba ya sami kansa da yin murmushi bayan sun yi masa bayanin sunayen nasu. "Innza ku ci ko indomie ce sai na karɓo a shago Sajida ta dafa muku." "Don Allah abinci muke so. Wanda ka girka." Taj ya ce da sauri. Girgiza kai Abba yayi yana ɗan murmushi. "Ku jira nayi muku iso a ciki." Sajida ce ta leƙo ta kira su bayan ya shiga ciki. Aka yi musu shimfiɗa a tsakar gida. Yaya ta fito da lulluɓi su ka gaisa. Taj ya dinga kallon gidan yana ayyana wai fa a nan yarinyar nan da ya gani take rayuwa. Yana son tambayar ina take amma dole ya kama bakinsa. Abba ya shiga kitchen suna iya hango duka motsinsa ta tagar dake tsakar gidan. Kai kawo kawai yake yi cike da ƙwarewa. Yaya da Sajida kuma suna jansu da hira jefi jefi. Kamal ne kaɗai yake amsawa. Hankalin Taj ya yi kitchen. So yake kawai yaga yadda Abba yake aiki. Yaya ce ta lura da hakan ta yiwa Abba magana. Yaran sun burgeta saboda babu girman kai a tare dasu. "Nace ko za ka bari ya shigo ciki ya taya ka?" "A'a, nagode." Taj ya tashi "gani kawai zan yi. Ba zan saka hannu ba." Sai bayan fiye da minti ɗaya sannan Abba ya ce ya shigo amma iyakarsa ƙofa. Ai kuwa da saurinsa ya shiga. Aikin daɗewar shekaru wato experience yafi aikin iyawa. Taj yaga abin mamaki a tattare da kuzarin dattijon. Ga tsafta don ko ledar maggi babu a ƙasa. Ƙamshi mai rura wutar yunwa ya cigaba da matse masa hanji. Fried spaghetti ce yayi musu babu nama a ciki sai busasshen kifi. Ya juye a tray. Sajida ta kawo musu. Sannan ita da Yaya su ka koma falo. Samarin Alh. Hayatu su ka zauna suna zuba santi har su ka cinye. Da za su tafi ne Taj ya bashi nambar wayarsu rubuce a takarda. "Don Allah Abba kayi shawara." "Naji. Ku tafi." Faɗan nasa bai hana shi raka su har mota ba. Kuma yaƙi tafiya har su ka bar layin. Yana komawa gida ya samu Sajida tana naɗe tabarmar da su ka zauna. A ƙarƙashinta sai ga farar takarda. Ta miƙa masa ya buɗe. Roƙo da magiya ne daga Taj. Sai kuma ƙarin bayani game da restaurant ɗinsa. "...idan ka amince za ka yi aiki dani, zan kama mana wuri inda za mu yi developing recipe kafin a gama ginin. Bana son yin business ɗin da zai rushe kafin yaje ko ina. Ka taimaka min.. Happy Taj" Da Yaya su ka zauna shawara. Sai dai washegari da kwanakin da su ka biyo baya kullum sai Taj yaje cin abinci. Har su ka yi masa kwano. Tun Abba yana basarwa har dai ya karɓi tayin da yayi masa. Ba kuma komai ya janyo haka ba sai rasa wurin da zai kafa sana'arsa. Duk inda yaje sai an biyo shi da ƙabali da ba'adi wanda shi ya san gaskiyar dai ita ce ɗan daudu ne. Ba sa ma damuwa da jin ko ya daina. A gida idan yace zai yi kuma akwai iyalinsa da ba zai so mutumcinsu ya zube ba. Haka dai bayan kwanaki yana kai gauro da mari ya ce ya amince. Ya kuma duƙufa addu'ar neman taimakon Allah. A lokacin kullum Hamdi tayi waya da gida sai anyi mata zancen Taj. Yaya da ƴan uwanta sunansa a bakinsu raɗau. Ita kuwa lamarin bai burgeta ba. Wanda zai zo ya mayar da Abbanta cikin sana'ar girki ba masoyi bane. Su Taj da su ka tabbatar sun sami kan Abba sai aka fara shirin zuwa wajen Anisa. Lokacin bai fi kwana goma ya rage masa ya koma ba. A motar Kamal su ka tafi. Da yake ya san gari basu wahala ba da bin kwatance ta google map su ka isa gidan. *** Aikin snacks da Anti ta ce a tanada saboda zuwan su Taj, Hauwa aka bawa. Hajjo tuni ta fesa musu dalilin zuwan nasa. Anisa sai murna. Sai dai anyi rashin sa'a ana gobe ranar tafiya ta kama ta. A waya ta basu haƙuri ta ce amma akwai ɗalibarta da duk abubuwan da su ka zayyano za ta iya ba tare da sun ji bambancin taste ba. "Haɗani da ita" Anisa ta ce don in ba kayan Luciousbites ba, bata ganewa snacks ɗin. A waya aka gama komai. Hamdi murna da godiya ta dinga yiwa Hauwa. Ita kuma ta dinga roƙonta kada ta kunyata musu brand. Ƙoƙari kam bakin gwargwado tayi. Meatpie, doughnut da samosa su ke so. Sai coconut infused youghurt. Shi ne kaɗai Hauwan ta aiko mata da shi. Sauran kuwa babu komai a ƙasa dole sai anyi. Bayan ta gama ta kira numbar Anisan da aka bata ta sanar da ita an gama komai. "To ki bawa mai delivery. Zan turo address." Nan fa ɗaya. Bata san kowa ba. Anti Labiba ma ta dinga kiran mutanenta amma kowa sai ya ce mai delivery baya kusa. Hamdi ta kuma kiran Anisa. Lokacin ita kuma bata jima da yin waya da Taj ba. Yana ƙara neman kwatance. A yadda ta ƙiyasta bai fi minti goma zai kawo su gidan ba. Gashi babu wanda za ta iya aika. Gari an tashi da rashin mai. Duk wata motar gidansu tana layi sai guda ɗaya ta Daddy. "Hamdiyya ko za ki ɗauko bolt ki kawo min. Zan biyaki kuɗin tranport ɗin. Fitar ce babu halin yi yanzu." Hamdi ta faɗawa Anti Labiba. Su ka rasa yadda za su yi. Mijin Anti Labiba a wajen gari yake aiki. Ita kuma babu mota. Tayi shahada kawai ta samarwa Hamdi bolt ɗin. RAYUWA DA GIƁI 13 Batul Mamman💖 Kada ku manta da bibiyar shafin Hauwa a instagram _@luciousbite.ng_ ko nemeta a waya ta wannan layin domin _09078075182_ odar snacks da nau'ikan youghurt masu daɗi. *** Irin rawar jikin da Anisa da Anti suke yi da Taj tuni ya sha jinin jikinsa. Shi da ya zo don su haɗu a sirrance ya zame ashe Hajjo tayi masa handsfree da alama. Kuma a ɓangarensu zancen ya sami karɓuwa. Ɗakin Hajjo aka kaisu. Tana ganinsu ta washe baki tana tarbar Kamal. "Sai ga Haffiness ɗin Haffi a Abuja. Sannu da zuwa Kamalu." "Har kin ƙara masa wasali a sunan nasa kenan." Taj ya faɗi yana zama akan kafet. Ƙafafunsa ya miƙe da yake jin sun sage saboda zama. Kamar ba da ita yake ba.Ta cigaba da yiwa Kamal magana "Ya ka baro mutanen gida? Ya baban naku?" Kamal ya amsa ta sake sako wata tambayar. Taj ya gaisheta har sau biyu bata amsa ba. Ya dai gane fushi take dashi. Bayan kuma shi ya kamata ya nuna ɓacin ransa da tayi saurin sanya shi cikin tsaka mai wuya. Yanzu duk gidan nan za su so jin matsayarsa kan maganar Anisa. Tunda yarinya dai alamu sun nuna ta amince, ana jin zance ya sauya salo nan gaba kaɗan za a ɗora masa laifi. Share su ya yi ya kira uwayensa ɗaya bayan ɗaya ya sanar dasu sun iso lafiya. Sai kuma ya kira Abba shi ma. Su ka yi magana akan ɗan gyaran da za a ƙarasa a wurin da Taj ya kama musu kafin ya dawo. "Hajjo in kin gama gaisawa da Haffiness ɗin nima ki ɗan bani lokaci don Allah. Yau za mu koma. Bana son mu yi dare." A sukwane ta juyo rai a ɓace "banten uba! Ku iso yanzu ka ce kuma komawa za ku yi?" "To ya za ayi? Aiki ya sako ni a gaba." Dariyar Kamal a dalilin zolayarta da Taj yake sai ta gane ba tafiyar za su yi da gaske ba. Sha kunu gami da nuna masa yatsunta biyar. "Buhun ubanka Tajo." "Toohhh" Kamal ya kalleta da rashin jindaɗi. Dole taji kunya don bata ga alamun yana da idanu a tsakar ka irin na Taj ba. "Ɗan uwan naka ne bashi da kirki Haffiness. Na yi masa maganar ƙanwarsa ya amsa rimi-rimi sai kuma ya shuka ni. Yanzu ma gajiya nayi ina ta tunanin ko yarinyar ce ta ce bata so shi ne na kira uwar na tambayeta." Kai tsaye Tay ya tambayeta "Me su ka ce?" Hajjo ta danƙara masa wani irin kallo "me kuwa za su ce sama da murna. Ko kai makaho ne ya dace ace ka fahimci yadda ake ta nan nan da kai ya sha bamban da lokutan baya." Shirunsa a yanzu daidai yake da cutar kai. Idan ya kuskura ya fita daga ɗakin nan bai faɗi abin da yake ransa ba to tabbas aurensa da Anisa da wahala in ba ayi ba. Gyara zama ya yi ya ce, "To ni dai gaskiya Hajjo..." Yau da gobe tafi ƙarfin wasa. Kuma dai Kamal ya riga ya san ba so yake ba. Amma akwai kunya da kawaicin malam bahaushe. Rashin girmamawa ne idan Taj ya kalli tsabar idon Hajjo ya faɗa mata baya son jikarta. "Hajjo magana ta gaskiya yanzu Taj tsoron ɗauko zancen aure yake." "Saboda me? Yana da lalura ne?" Ta soma yi masa kallon ƙurilla. Ya girgiza kai "a'a, amma kin san matsalar da yake fuskanta daga wajen Alhaji." "Alhajin me?" Ta fara sababi "in kai ma baka da labari ka sani daga yau. Kakarku wadda ta tsuguna ta haifi Hayatu aminiyata ce ta ƙud da ƙud. Duk taurin kansa bai isa na faɗa ya faɗa ba." Kamal ya jinjina kai yana kallon Taj ko zai agaza masa. Shi kuwa shiru ya yi yana kallonsu. "Nima ba nufina zai ƙi maganar bane. Kawai dai shi Taj yafi son lokacin da zai yi aure ya kasance Alhaji ya daina fushi da shi. Baya son yadda ya kore shi daga gidan kuma ya hana ƴaƴansa shiga su ma." Hajjo ta jinjina lamarin "da gaskiyarsa kuma. To amma indai auren gida ne irin wannan ai ita Anisan ta san komai. Ga ku duka kuna ta zumuncinku. Su Haj. Gambo ma dai ko da satar hanya na san za su fito ganin jikokinsu." "Ko kin san zuwan nan har bakin mota Taj ya bishi amma su ka ja mota aka baɗe shi da ƙura? Shi ne ya yi alƙawarin ba zai yi aure ba sai Alhaji ya yafe masa." Zancen ya fara shigarta. Kamal ya zama kamar wani lauya wurin jujjuya zance. A ƙarshe dai ya samu da kanta ta hango illar auren Taj a yanayin rashin jituwa da uba. "Abin da za ayi ko Kamalu, ni zan sa a kira min Hayatun muyi magana. Na san ko babu komai idan yaji daga gareni zai girmama zancen. Ba zai wulaƙanta min jika ba." Tamkar ya sanya ihu haka yaji a wannan lokacin. Ashe duk ɓaɓatun da yake ita wani angle ɗin daban take kallo. Miƙewa Taj ya yi ya fice ya barshi yana ta kame kame. Falo ya koma inda ya yi sa'a babu kowa. Yana zama Kamal ya fito yana ta waigen baya. "This woman is too smart Happy. Kana ganin ta toshe duk wata hanyar da zan ɓullo don a kwantar da zancen nan." Murmushi Taj ya yi "kaɗan ma ka gani. Shi yasa na so faɗa mata gaskiya. Kai kuma ka hana." "Haba Happy, wani abin ai sai da siyasa. Kara wani abu ce" Kai Taj ya riƙe kawai. Kwanakin nan gajiya da damuwa suna yawan sanya masa ciwon kai. Tunda ya sami kan Abba abin ya ragu. Amma fa daga lokacin da su ka saka ranar zuwa Abujan shikenan bashi da wata walwala. "Kan ne dai?" Kamal ya yi tambayar da kulawa yana dafa shi. "Wallahi kuwa." "Ka daina damuwa. Ba a yiwa namiji auren dole fa" Kamal ɗin ya yi murmushi. "Happiness bana son takura ne. Sannan bana son ungratefulness. Ƙinta tamkar ban godewa kyautatawarsu bane." "Don ka taimaki mutum kuma bai kamata ka ɗora masa nauyin da zai takura shi ba. Ni shawarata kawai tunda Hajjon ta ɗan fahimta ka cigaba da jan ƙafa. Kuna fara magana a fito mata as unromantic as possible. Kada ka sanya mata false hope. In anyi sa'a ta gudu da kanta." Sai a lokacin Taj yaji sanyi a ransa. Ya miƙawa Kamal hannu. "Happiness nawa ni kaɗai. Yadda ka ce hakan za ayi. Thanks bro" *** Hamdi bata taɓa shiga motar haya a Abuja ba ita kaɗai. Ko yawon da su ka dinga fita da Anti Labiba farkon zuwanta, yawanci mijin Antin ke kai su. Ko kuma Anti Labiban ta kira bold ko uber. Hankalinta kwance yake tunda akwai idon garin. Yau da take ita kaɗai ne dai duniyar tayi mata zafi. Na farko dai direban motar a ƙoyasinta zai yi biyunta. Ga jiki da bai ɓuya ba. Sannan babu tantama ba bahaushe bane. Inda zasu je kuma bata sani ba. Anti Labiba dai ta ce mata zasu bi ta titin hanyar Central Mosque ɗin da su ka taɓa zuwa. To gashi an fi minti shabiyar a titi amma babu masallaci babu alamunsa. Banda hawa da sauka akan wasu gadoji da ko wuƙa aka ɗora mata ba za ta gane ko ɗaya ba, babu abin da yake yi. Ga gudu da ta lura yana yi kamar walƙiya. Hanjin cikinta su ka sami wuri su ka cure wuri guda. Zuciyarta tana harbawa kamar za ta fito waje. Sai kuma bisa rashin sa'a aka kira shi da wata wayar ba wadda take gabansa tana nuna hanya ba. Ya sanya earpiece a kunne ɗaya yana magana da yaren da bata ji. 'Passenger' da kuma 'get ready, I will be there soon' kaɗai ta iya tantancewa. Habawa, duk wani labari da ta taɓa ji game da satar mutane sai da ya dawo mata. Jikinta ya dinga rawa. A hankali ta kama shessheƙar kuka don bata so yaji. Ta fiddo wayar da Anti Labiba ta bata da za ta taho ta tura mata message. (Anti zai sayar dani a hanya ban san inda muke ba amma titin yayi kama da bayan gari) Ta rubuta a jere ko waƙafi babu tsakanin rubutun. Gashi tana zama a motar ya danna lock ta gaba. Gilasai duk an ɗagesu an sakar mata AC. Anti Labiba na kashingiɗe a falo message ɗin ya shigo. Ta tashi zaune a gigice. Ta dinga kiran Hamdi wayar taƙi shiga. Cikin matsanancin tsoro ta kira nambar Anisa da su ka yi magana ɗazu. * Abinci ta shiryo a tray ta fito dashi wayar ta shigo. Bata ɗauka ba sai da ta ajiye tray ɗin a gabansu Taj. Ta ɗauki wayar daga kan tray ɗin. "Dama yanzu nake shirin nemanki. Naga bata iso ba har yanzu." Anti Labiba ta ɗora hannu a ka "bata zo ba? Sun kusa minti arba'in da biyar da barin gida fa." Anisa da bata da saurin fushi tayi musu uzuri da cewa "maybe hold up ne. Kin san yamma tayi. An fara dawowa daga office." "Uhmm uhmm dai. Bari na turo miki message ɗin da tayi min yanzu. Zan nemi maigidan na sanar dashi." Zama Anisa tayi don ta gama kawo komai falon. Ta sha kwalliya sosai tayi kyau. Ta buɗe abincin tana tambayar Taj me za ta zuba masa wayar Anti Labiba ta sake shigowa. Tambayarta tayi taga text ɗin ta ce yanzu za ta duba. Ai tana karantawa ta kama salati. "Me ya faru?" Taj ya zare wayar a hannunta don jikinta rawa yake yi. "Anti! Anti!!" Shi ne sunan da take kira hankali a tashe. Antin ta fito da mayafi a hannu don kiran ya tsorata ta. Taj da Kamal su ma duka babu mai nutsuwa. "Wai yarinyar da na bawa aikin snacks ce ta taho tun ɗazu amma kinga bata ido ba." Anti ta ja tsaki "haba Anisa. Shi ne ki ke min wannan kiran mai firgitarwa?" Wayarta ta soma lalube Taj ya miƙa mata bayan ya gama karantawa. Ta damƙawa Antin. Itama tana karantawa su ka kira Anti Labiba. Kuka ma take a lokacin. "Wayarta ko ta shiga bata ɗauka. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." "Ki ce ta turo numbar mutumin tunda dole akwai numbarsa akan app ɗin da zai yi magana da passenger." Da gaggawa Anisa ta faɗi saƙon. Anti Labiba ta tura musu. *** Direba na tafiya ya fara jin sautin kuka na tashi kaɗan kaɗan. Gabansa ya yanke ya faɗi da ya ɗan leƙa ta madubi ya tabbata yarinyar da ya ɗauko ce take yi. Dama ana cewa fa wasu fasinjojin ba da alkhairi suke zuwa ba. Wasu ma sharri su ke ƙullawa mutane. Kaddai irinsu ya ɗauko yau? "Madam, what is wrong?" Ya kwantar da murya ya tambayeta. Ita kuma jin ya kirata sai kawai ta fashe da kuka sosai. "Please take me home." "We are almost at your destination. Did something happen?" Hamdi ta kalli titin. Babu sawun mutane sosai. Ita da zai sayar ko ya cirewa sassan jiki zai yiwa daɗin baki? "Zan sauka...drop me here." Direba ya kalli wajen sai yaji fargaba ta dirar masa. Bisa shawarar map ɗin bolt da yake bi an nuna akwai hazard akan hanyar da tafi saurin kai mutum inda zai je. Hazard ɗin kuwa yana iya zama hatsari, lalacewar mota ko goslow ɗin da ya hargitsa titi. Sai map ɗin ta zaɓar masa wata hanyar daban. Shi kuma baya son bi saboda nisanta sosai. Kuskurensa shi ne da ya ɗauke hanya bai yi mata bayani ba. Kukan da take a firgice ne ya tuna masa da hakan. Ya soma bata haƙuri da rarrashi. Amma fir Hamdi taƙi yin shiru. Ita dole ya sauketa. Shi kuma yana tsoron buɗe motar bai san me zai faru ba. Mutane ma yanzu basu fiye bincike ba. Wanda yafi rauni yana faɗin abu sai kawai a hau a zauna. Suna haka Anisa ta kira shi. Tambayarsa tayi game da fasinjar da ya ɗauko. Cike da farinciki kuwa ya faɗa mata abin da yake faruwa. "Let me talk to her." Ai ko wayar ƙin yarda tayi ta karɓa. Karshe sai speaker ya saka yadda za ta ji. "Ki kwantar da hankalinki. Ya ce hanya ce bata da kyau shi yasa ya canja wata. Amma yanzu zai kawoki." "Ni dai ki zo ki karɓi kayanki don Allah. Daga nan in ya kuma tada mota Allah ihu zan masa. Tun ɗazu fa muke yawo..." ta fashe da wani kukan. Anisa ta rasa irin bayanin da za ta yi mata. Sai kawai ta bawa Taj wayar. "Naji kamar yarinya ce, please ka ɗan kwantar mata da hankali Yaya." A tsiwace Hamdi ta ce "ni ba yarinya bace. Na yafe kuɗin. Ku zo ku ɗauka ko na bar masa a mota." Ita a wautarta in ta nuna bata tsoro ƙila a haƙura da cutar da ita. Yadda take magana sai ya bawa Taj dariya. Kai kana ji za ka san a mugun tsorace take. Wayar ya kara a kunnensa. "Big girl." Anisa da Kamal harma da Anti su ka yi dariya. Da ta amsa abinta. "Na'am." "Ni yayan Anisa ne. Yanzu zan sa direban ya turo min location ɗin ku. Sai na zo na kai ki gida. Haka ya yi?" "Eh, amma don Allah minti nawa? Kaga fitsari ya matseni." Ɗaga kai ya yi sai yaga duk sun yi alamun tausayawa gareta. "Zan yi sauri in sha Allah." Cikin mintuna kaɗan kuwa direban ya tura masa da location ta whatsapp ɗin Anisa. Su ka shiga motar Kamal su uku. Kamal ɗin ke tuƙawa. Anisa tana baya. Lokaci zuwa lokaci kuma Hamdi sai tayi flashing da wayar direban. Ta ma manta ko bashi bata yi ba. Sai ya rabu da ita tunda ta daina kukan. "Kun kusa?" "Saura kaɗan." Anisa ta kira Anti Labiba ta ce mata za su kawo Hamdi gida. "Don Allah ku yi haƙuri. Baƙuwa ce a garin." "Ban ji haushi ba. Ni tsorona ma firgitar da tayi kada ya zauna mata a rai." Cewar Anisa. Wasa wasa sun yi minti shabiyar kafin su isa. Unguwannin ne da tazara a tsakaninsu. Motar na doso su Hamdi ta kama handle za ta buɗe. Shi ma direban duk ya ƙagu. Yana ganin sun yi parking a bayansu ya cire lock. Babu takalmi haka ta jeho ƙafafunta waje ta fito. Mayafin da ta yafa akan riga da siket ɗin jikinta ya rufe rabin fuskata. Wayar Anti Labiban ma bata ɗauka ba ta fito da sauri. Mayafin da ta gyara ne ya bayyana fuskarta sosai. Taj yana fitowa su ka haɗa ido. Zuciyarsa sai da tayi wani irin abu saboda ganin abin da bai taɓa zato ba. "Hamdi?" Ya furta a can ƙasan maƙoshi shiyasa babu wanda yaji. Ita kuwa bata ma gane me ta kalla ba. Burinta dai ya cika ta fita daga motar mutumin. Kamal ya ƙarasa wurin direban ya bashi haƙuri tare da cewa ƙanwarsu ce. Shi ma ya bada haƙurin rashin yi mata bayani wanda ya janyo wannan ruɗanin. "Ga kayanta" ya ce da yaga suna shirin tafiya. Kwalaye ne madaidaita guda biyu. Ɗaya doughnut. Ɗayan kuma meatpie da samosa. Sai kuma ledar youghurt wanda Hauwa ce da kanta tayi. Anisa ce ta kula Hamdi bata da takalmi da ta zauna a baya. Za ta fita ta ɗauko mata sai Taj ya ce ta zauna. Shi ya ɗauko harda wayar yana ta mamakin wannan coincidence. Ashe tana Abuja. Shi yasa baya ganinta a gidansu. Murmushi kawai ya dinga yi har su ka soma tafiya. Hanyar gidan da ba ganewa za ta yi ba shi ma Anti Labiba ce ta turo kwatance. Anisa ta ce ta gane. Idan sun isa unguwar za ta kira sai ta kwatanta gidan. "Shhh" Hamdi ta fara yi da baki saboda fitsarin da ya gama matsarta. Tun a na farko Taj ya ji. Hankalinsa gabaɗaya yana bayan motar. "Step on it Kamal (ƙara sauri)" ya ce a hankali don kada taji kunya. Kamar a kunnen Anisa ya faɗa sai cewa tayi "eh kuwa. A matse take sosai" tana kallonta. Ko a jikin Hamdi. Burinta kawai a isa gida. Ƙafafunta sun kasa zama waje guda. Komawa gidan tayi mata nisa saboda uzurinta. Finally bayan ta gama gumi su ka shiga estate ɗin su Anti Labiba. A guje ta fita da Kamal ya tsaya. Ta sake barin takalma da wayar da dama Taj bai miƙa mata ba. Anisa ta bita cikin gidan su kuma suna waje. Anti Labiba da yara sun taso da murnarsu ta wuce su ta shige banɗaki. Bata ma kula harda maigidan ba sai da ta gama ta fito. "Washhh Allah na." Ta furta da ta dawo hayyacinta. Sai kuma ta rungume Antin tana kuka. "Mene ne na kuka kuma? Ba gashi kin dawo ba." Ta kalli maigidan da su ke kira Uncle. "Na zata ba zan sake ganinku ba." "Ke dai anyi matsoraciya." Cewar Anti Labiba tana dariya. "Ko nice fa zan tsorata. Bata san wuri ba kuma an bi hanya daban." Anisa ta kare mata. Murmushi ta yiwa Anisan gami da bata haƙurin rashin cika alƙawarin kai kaya. "Wa yake ta kaya baiwar Allah? Ai tunda dai kin dawo gida nima buƙatata ta biya." Kiran sallar magrib aka fara Anisan ta ce tare su ke da yayyenta. Uncle da kansa ya fita ya kira su cikin falo domin su yi sallah bayan an kai musu ruwa sun yi alwala a waje. Suna idarwa Anisa ta ce za su tafi. Anti Labiba dake kitchen tana haɗa zoɓo ta hana. Sai da ta haɗa komai ta kawo ta nemi Hamdi a falon ta rasa. Maigidanta ta tambaya ina take ya ce ai tun shigowar su sallah bai ganta ba. Ɗaki Anti Labiba ta bita. Ta sameta zaune a bakin gado da zumbulelen hijabinta. "Ki zo ki sake yi musu godiya za su tafi." "Anti rawar fitsari fa na dinga yi a motar. Ni dai wallahi ba za ni ba." "Harda saurin rantsuwa?" "Baki ganni bane" ta faɗi tana takaicin abin da tayi. Falon ta dawo bata san Hamdin na bayanta ba. A bayan labule ta maƙale ta ɗan leƙo da kanta. Hira Uncle yake da su Taj inda a nan su ka gane su ɗin duka ƴan Kano ne. Ya nemi su dinga zumunci domin an zama ɗaya. Ta bayan labulen ta sake haɗa ido da Taj domin yaga tsayuwarta tun farko. Baki ta buɗe don da wannan kallon ta gane shi. Zuciyarta ma bata manta ba saboda irin harbawar da tayi da sauri. Ta sanya hannu ta rufe bakinta. Za ta gudu taji muryarsa da ta gane tun a wayarsu ta ɗazu. "Kamal bani key na ɗauko mata takalma da wayarta." Anti Labiba ta waiga ta hango shatinta a labulen. "Zo ki je ki karɓo mana. Ko sai ya biyoki dasu kuma?" Sumi-sumi ta fito kai a ƙasa. Kamal ya tsaya bawa Uncle numbar wayarsa. Ita kuma Anisa santin zoɓo take tana kuma wasa da yaran gidan. Da faɗuwar gaba ta isa bakin motar. Taj ya buɗe ya ɗauko mata takalman da wayar. Maimakon ya miƙa mata sai ya jingina da motar yana kallonta. "Kin gane ni yanzu ko?" Murmushi tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. "Ashe nan ki ka gudu shi yasa ban ganki ba." Kallonsa tayi a fakaice "nema na kake yi?" "Na san inda zan same ki Hamdi. Kawai ganinki ne ban yi ba a wajen." Shi mai maganar da ita da ake yiwa duk jikinsu tamkar anyi musu duka. Zuƙatansu ke aikin wucin gadi na tsananin murnar sake haɗuwar bazata irin wannan. "Ina? Makaranta?" "A gida." Daina ɓoye fuskarta tayi. Ta kalle shi da mamaki. Muryoyin su Anisa yaji sai ya bata kayanta. "Sai mun haɗu a Kano. Take care." Motar ya shiga amma bai rufe ba har su ka iso. Hamdi ta sake yi musu godiya sannan su ka shiga mota su ka tafi. Daren ranar mutumin da bata san sunansa ba ne ya cika mata zuciya da tunani. Bata da wani aiki sai murmushin da bata san lokacin da yake zuwa ba. A ɓangaren Taj kuma suna yin sallar isha ya ce bacci zai yi. Abincin da Anisa ta dafa Kamal ne kawai ya ci. Shi kuma ya sanya snacks ɗin Hamdi a gaba. A take ya yanke shawarar sanyata a ɓangaren snacks ɗin restaurant ɗin shi wanda Kamal ya yiwa suna da HAPPY TAJ. Kuma ba shi kaɗai ba. Kowa ya ci sai yaba daɗin kayan. Wayar da su ka dinga magana ɗazu ya kira sai yaji muryar direban motar. Ba yadda ya iya. Godiya kawai ya sake yi masa ya katse kiran. Kenan ba da wayarta su ke magana ba? Yayi guntun tsaki. Babu matsala tunda samunta ba zai yi masa wahala ba. Zuciyarsa wasai ya kwanta. * Tun asuba Taj ya faɗawa Kamal cewa a yau za su koma Kano. Zai yi magana da Anisa kafin su tafi. Ba musu ya amince " gara haka don zamanmu ma zai iya sanyawa ayi tunanin wata soyayya ku ke bugawa fa." Da yake da wurwuri ta tashi ta haɗa musu breakfast. Shi ya taimaka masa wurin samun ganinta da wuri. Ta zauna a falo ta sunkuyar da kai ƙasa. Gabaɗaya sai ya dinga jin babu daɗi. Hajjo taje kawai ta sanya mata rai. "Anisa." "Na'am Yaya." "Kinji haɗin da Hajjo take son yi mana ko?" Kai ta gyaɗa da murmushinta. "Bani da abin cewa game da karamcin gidan nan naku sai godiya. Anyi min komai a lokacin da na rasa soyayyar mahaifina." Ta dube shi da tausayawa "kayi haƙuri. Komai zai daidaita in sha Allah." "Haka nake fata. Amma saboda halin da nake ciki Anisa bana son yin aure yanzu." A razane ta dube shi. Gabanta na faɗuwa kada ya ce baya sonta. A ransa hakan yake son faɗa ko don ta bawa wasu dama. Amma yana gudun me zai je ya dawo. "Ina son lokacin aurena Alhaji ya halarta ba don anyi masa dole ba. Idan na sami ƴaƴa in kai masa ya yi huɗuba yadda yake yiwa ƴaƴan ƴan uwana. Ya kuma sanyawa abin da na samu suna." Yaja numfashi "hakan ba zai samu ba yanzu saboda bai haƙura ba." "Kana nufin na nemi wani kenan?" Ta tambaye shi da sanyin jikin da ya sanya masa tausayinta. "Ina nufin mu bi komai a sannu sannan mu nemi zaɓin Allah. Bana son in yi miki alƙawarin da ba zan iya cikawa ba." Murmushi tayi ga ƙwalla ta taru a idanunta "na fahimceka, zan kuma cigaba da yi maka addu'a." "Nagode" yaji zuciyarsa maimakon ta rage nauyi ƙarawa tayi. Reaction ɗin Anisa na sauƙin kai ya kwaɓa masa lamari. Shawarar Kamal ta biyu zai bi. Ba zai yarda ya nuna mata kulawar da za ta saka rai da samunsa ba. Amma abin da kamar wuya domin Hajjo ba za ta sakar masa mara ya sha iska ba. Shi ya san da wannan. *** Sati guda ya ƙara a Kano ya tattara ya tafi. Ayyuka ne har biyu su ka taso masa na bukuwan manya wanda suka ƙi yarda su nemi wani chef ɗin duk da baya nan. Sun tsara abubuwa da dama da Abba kafin tafiyar tasa. "Ka cigaba da training ɗin yaranka kafin na dawo. Idan sun yi passing test ɗina zan yi retaining ɗinsu." Abba ya ce "shagon fa?" "Ku cigaba da girkinku kafin a ƙarasa wancan." Gidan Abba Habibu kowa ya yi farinciki da cigaban da ya samu. Wurin yanzu yafi na da komai da komai. Hamdi ce kaɗai da labari yaje mata ba kunya ta ce ko waye Taj ɗinnan bai burgeta ba. Idan taimako zai yi ai da ya samarwa Abba wata sana'ar. Kuma da yake a idanunta wani matashin ɗan daudun take gani, sai taji duk ta tsane shi tun kafin su haɗu. Haka kawai ya zo ya yi amfani da halin rashin da suke fama dashi wanda ya hanata shiga jami'a ya sake dulmiya mata uba. Har ta dawo Kano bayan wata uku da ko sau ɗaya bawan Allahn nan da ya gama da zuciyarta bai nemeta ba. Tun tana damuwa don ta sa rai za ta sake ji daga gare shi har ta haƙura. Sana'ar snacks ta kama ka'in da na'in wadda kuma Allah Ya sanyawa albarka. A ɗan tsukin wajejensu tayi suna. Biki ko suna kowa Hamdi yake kai wa aikin kayan fulawa. Kuma tana yi Abba ya sayar mata a wurinsu. Kafin wani lokaci sai ya zamana su uku suke yi. Zee ta fi ƙwarewa a yin youghurt kamar ita Luciousbites ta koyawa. Abinsu gwanin ban sha'awa. Taj yana yawan kira ya gaishe da Yaya. Wani lokacin ta wayar Sajida. Idan aka yi mata tayin gaisawa da shi sai tayi ta zillewa. Idan Yaya bata wurin kuwa wasu lokutan har tsiwarta yana ji ta wayar Sajida. Har mamakinta yake yi. Idan ance masa tana da baki haka zai ƙaryata saboda shi dai da fuskar salihai ya ganta. Su kuma ƴan uwan nata komai su ka ji game da shi ko a hira ne sai sun faɗa mata. Idan aka ce Kamal ya zo kuwa bata yarda su haɗu. Ita fa komai nasa akai kasuwa kawai. Ranar da Zee ta ce mata ya iya indiyanci babu irin shaƙiyancin da bata yi ba. Da aka kwana biyu ya kira wayar Yaya sai ta ɗauka. Amma bata saka a kunne ba. Kawai domin yaji haushi ya fita daga rayuwar gidansu tayi magana. "Yaya ga Salman Khan ɗinku ya kira." Taj ya kawar da wayar daga bakinsa ya gama dariya sannan ya maƙe murya ya kirata. "Hamdiyya." Tsigar jikinta ta tashi. Muryar bata yi irin ta mata sosai ba tunda bai saba ba. Amma dai ya kamanta don ji tayi kamar ta yar da wayar. "Aap kaise hain?" "Na'am?" Ta ce da takaici. Ƙila ma har rawa da waƙa ya iya. Ya sake maimaita tambayar wadda take nufin 'yaya kike?' Ta taɓe baki "zindagi choringe...ba dai shi ne indiyancin ba?" Ta shiga falo da sauri "Yaya ungo wayarki Taj ɗinku ne." "Zan ci mutumcinki akan yaron nan Hamdiyya. Ke da zaki ganshi sai kin raina kanki." Yaya ta faɗi ba tare da sanin Hamdin ta ɗaga kiran ba. Zee ta ƙara da cewa "ƙila ma ta ce tana son shi." "Wuce nan wallahi. Wanda nake so namijin gaske ne." "Lahhhh" Yaya ta faɗi tana jifanta da maficin hannunta "ni kike faɗawa haka ko mara kunya" Hamdi ta fice da gudu suna dariya ita da Zee. Ɗakinsu su ka koma su ka sami Sajida tana farinciki. "Me ya faru?" Rungume ƙannen nata tayi a tare "Safwan zai turo ranar asabar." Haɗuwa su ka yi su uku suna tsallen murna. Yayinda Yaya take waya da Taj wanda yake cike da nishaɗin jin muryar Hamdi. RAYUWA DA GIƁI 14 Batul Mamman💖 *** Rashin wuta da ake fama dashi ya hana Hamdi sayen naman yin meatpie da ake sayarwa a shagon Abba kullum. Har ta haƙura da cinikin ranar saboda da ta saya a daren ko ta soya zafin da ake zai iya canja mata ɗanɗanonsa idan ta haɗa. Sai Abban ya kira ya ce ko da yamma ne idan tayi Halifa ya kawo saboda ana so. Sai aka yi rashin sa'a Haiifan bai dawo daga makaranta da wuri ba. Ita kuma tana tsoron yin kwantai. "Yaya zan kai masa da kaina." Izinin tafiyar tayi mata sannan tayi mata kwatance yadda za ta gane. s Sau ɗaya ta taɓa zuwa tun dawowarta. Adaidata ta samu har can. Shagon a bakin titi yake a gefen wata plaza. Tana sauka ta matsar da kayanta gefe sosai ta kira Abba kamar yadda Yaya ta ce tayi idan ta iso. Kira huɗu, wayar tana ta ringing babu amsa. Gashi taƙi jinin a dinga kallonta. Madaidaiciyar cooler ɗin da ta sako meatpie ɗin mai hannu biyu ta kinkima ta ƙarasa. Wurin a cike yake Masha Allah. Mutane suna ta kai kawo ana ta sayen abinci. A bakin ƙofa ta kuma tsayawa ta kira Abba. Wayar ko shiga bata yi ba wani ya fito ya ganta. "Ahhh, wannan dai duk yadda aka yi ɗiyarmu ce don ga kama nan. Ƴan mata shigo daga ciki. Aunty Simagade yau ana ta fama da baƙi." Gaban Hamdi ya yanke ya faɗi. Da ganin mutumin Abba zai girme shi. Duk da dai bleaching ya caɓalɓala masa fuska fiye da ta Abban. Ya wani sha jallabiya da ɗaurin ƙirji. Kansa kuma ya yi ɗaurin ture ka ga tsiya da ɗankwali irin zanin. 'Me ya kawo ɗan daudu wajen nan?' Ta yi wa kanta tambayar cikin yanayin ƙuncin rai. Ashe kallo yana ciki. Tana sanya ƙafafunta wani irin baƙinciki ya turnuƙeta. Akwai kwastomomi da yawa a ciki. Amma fa a yau dandazon ƴan daudu sama da huɗu ne su ke ta karakaina wajen ɗaukar odarsu da kawo musu abinci. Muryoyinsu da taƙi jini sun cika ko ina. Sai shewa ake ana yiwa juna shaƙiyanci. Ita kuwa waige ta kama yi tana son hango mahaifinta. * Ubangidan Abba a birnin Jedda lokacin da yake ganiyar daudancinsa ne ya zo Kano. Ƴar Ficika ake kiransa saboda ƙanƙanta da ƙwarewa a iya shege. Duk wani mai ji da hayaƙinsa idan ya gamu da Ƴar Ficika a Saudiyya dai sai ya sauke kai. Clicks da connections na fitina babu irin wanda baya haɗawa. A lokacin da suke tare da Abba ya so ƙwarai ya sanya shi a hanyar da kowa yake bi ya yi kuɗi. Sai ya fahimci Habibu ba komai ne a gabansa ba illa girki. Shi dai a tura shi gaban murhu ya haɗa abinci. Ƙaryar mutum ya ce ya taɓa ganinsa a wani waje sama da wurin girki ko cin abinci. Ƴar Ficika sai ya tsaya masa. Ko a bayan idonsa wani ya nemi yiwa Abba wayo ya sanya shi a gurguwar turba sai ya ci mutumcin mutum. Lokacin da Baba ma yaje wurinsa, da Abba zai dawo Ƴar Ficika ne ya biya masa rabin kuɗin jirgi. Bayan dawowarsa gida babu abin da ya sake haɗa shi da kowa cikinsu. Ya tattare wannan shafin rayuwar tasa ya watsa a shara. Yaran da suke aiki a ƙarƙashinsa kaf babu ɗan daudu. Maza ne kawai masu ra'ayin girki a dalilin rashin wata sana'ar. To yau kwana uku kenan da Ƴar Ficika ya nemo Abba. A kamen takari aka watso su gida shi da wasu yaransa. Gashi girma ya kama shi amma zuciyar nema bata mutu ba. A nan gida Najeriya kuma bashi da ido da ƙafa kamar Saudiyya. Yana neman abin yi ne ya haɗu da wanda ya san inda Abba Habibu yake. Shi ne aka kawo shi har gidan abincinsa. Abba bai ɓoye masa sabuwar rayuwar da yake yi ba. Ƴar Ficika yaji ya kwaɗaitu da samun darajar da ya rasa a wajen danginsa. Shi da yaransa babu wanda baya fuskantar ƙyama daga ahalinsa. Godiya ya yiwa Abba ya ce kuma zai buɗe gidan abinci. Yana fata zai taimaka masa. "Ɗan halak baya manta alkhairi. In sha Allahu zan maka iya ƙoƙarina." "Idan babu damuwa zan so ganin yadda salon kasuwar take a nan. In zai yiwu ma kawai lokacin tafiyarka sabon restoran ɗin sai na karɓi wurin nan." Abba bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kira Taj ya sanar dashi. Shi kuma jin taƙaitaccen tarihin Ƴar Ficika da tsoron da Abba yake na kada ya komawa rayuwarsa ta gidan jiya sai ya amince. "Idan mai laifi ya so tuba yana da kyau a bashi dama. Rashin yin hakan na taimakawa wajen sake dulmiyar dasu cikin ayyuka marasa kyau." Taj ya ce "haka ne Abba. In ya rasa samun aikin da zai bashi halal zai koma ya nema daga haram ko yaya take." Da wannan shawarar Abba ya amince masa. Shi kuma saboda jindaɗi ya ce zasu dinga tayasu aiki duk lokacin da su ka sami lokaci tunda ba su da abin yi. Shi ne fa su ka zo yau. Girki harda wanda Abba ya manta. Yaji daɗi domin yau kasuwar ta buɗe fiye da kullum. Ya alaƙanta nasarar da kyakkyawar niyyarsa ta taimako. Don bai manta wulaƙancin da ya sha ba sanda ya dawo. Da wanda ya gani a dalilin neman wurin kafa sana'a da ya rasa wancan. * "Kai, kai, kai...Tabarakallah." Hamdi ta waiga baya ta haɗa ido da wani ƙarmasasshen mutum da ita kanta ta fi shi tsayi. Kanta ya yi yana murmushi kamar zai rungumeta. Kafin tayi baya Abbanta ya janyeta gefensa. Ƴar Ficika ya cigaba da murmushi yana kallonta. "Wannan ma taka ce?" Yaronsa da ta haɗu dashi a waje ne ya bada amsa. "Aiwa, baka ga kama ba? Anti Simagade an dasa kyakkyawar shuka tayi fure mai ƙamshi." Ya faɗi yana lanƙwaya hannu da juya idanu. Wani irin ɗaci ya dinga kai komo a wuyan Hamdi. Da ƙyar ta yiwa Abba biyayya ta gaishe da mutanen da ya gabatar a matsayin abokan sana'arsa a Saudiyya. "Cewa za ka yi mu iyayenta ne. An riga an zama ɗaya. Za ku yi ta ganinmu har sai mun saba." "To" ta ce da gatsali ta kuma juya ko coolar bata ajiye ba tayi waje. Tana fita hawaye ya wanke mata fuska. Wannan wace irin rayuwa ce? Ta ɗauka Abba girki da abubuwa na siffar mata kawai yake yi. Me zai sa ya mu'amalanci mutane irin waɗannan? Don sai da ta gansu ne ma ta gane me ake nufi da asalin ɗan daudu. "Hamdi" Sarai taji kiran da yake mata amma ta ƙara sauri. Kafin ta ƙarasa titi ta dire coolar a gabanta ta ɗagawa wani adaidaita sahu hannu. Kafin ya gama tsayawa ta faɗa ciki su ka yi gaba. Abba ya kalleta ya juya ya kalli Ƴar Ficika da ya biyo shi. "Ba dai ganinmu bane ya ɓata mata rai ba?" Murmushi ya ƙaƙalo "ahh haba dai. Sauri take yi." Ƴar Ficika ya murmusa "ko kai a gabana ka ƙarasa girma fa Habibu. Ta yaya zan kasa gane abin da na saba gani?" Cike da jin nauyi Abba ya faɗa masa yadda a baya bata ma son nuna shi a matsayin uba. Yana ganin babu mamaki yanzu wannan abin da tayi yana da nasaba da tunaninta na komawarsa ga ɗabi'ar baya. "To ko mu daina zuwa? In ya so lokacin da ka bar nan ɗin sai mu dawo?" Allah Ya sani kamar ya ce eh, to amma nauyi da tunanin me zai je ya dawo a rayuwar su Ƴar Ficika sai ya ce a'a. Yau kaɗai da ya haɗu dasu ya ga wani irin farinciki da annashuwa a tare dasu. Sun sake suna ta aikin abin da su ka fi ƙwarewa wato girki. Har sai da ya yi tunanin me yiwuwa tun dawowarsu babu wanda ya sami tarba mai kyau da mutuntawa sai yau. *** Hamdi tayi kuka tun daga hanya har gida. Da ƙyar ta iya labartawa Yaya abin da ta gani. Abba na dawowa kuwa Yaya ta kawo zancen ita ma nata ran a ɓace. "Yaya Habibu ka sani cewa bahaushe na cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne. Yanzu duk wanda ya ganka da mutanen nan zai yi maka kallon irinsu." Da laluma ya dubeta "Jinjin juya baya ba nawa bane ga wanda ya nemi taimakona. Duka duka yaushe muka sami wannan rayuwar bayan haɗuwa da yaron nan Taj? Ko har kin manta cin zarafin da aka dinga yi min akan neman shago? Duk unguwar da naje sai su ce kada yaransu su yi koyi dani basa so." "Naji kuma duk na fahimta. Amma hanyoyin samun lada ai suna da yawa. Shigowar mutanen nan rayuwarka a wannan lokacin da kake neman tada ƙimarka a cikin mutane gaskiya ba zai haifi ɗa mai ido ba." Ta sake faɗi cikin fushi. Duk yadda ya so ɓullo mata taƙi amincewa. Tsayuwa ya yi akan bakansa shi ma. Yau dai ɗaya zai yi abin da yake jin ya dace ko ba zai faranta ran iyalinsa ba. "A bar maganar nan. Indai Ƴar Ficika ne, ba zan kore shi ba." "To ai shikenan. Allah Ya kyauta ɓacin rana." *** Yadda Salwa ta matsawa Taj da waya da messages a duk wata kafar da zai gani, haka Anisa ma take yi. Gashi dai basu san da zaman juna ba amma kowacce ta matsa lamba. Ita Salwa banda ƙawa har Maminsu ta san irin soyayyar da take yiwa Taj. Da fari ta nuna rashin goyon baya saboda ɗan tsohon miji ne. Sai da taji ta kuma ga waye Taj a wani bidiyon girkinsa a youtube da Salwan ta nuna mata tayi mubaya'a. Matashi ne mafarkin duk wata budurwa. Burin duk wata uwa da take son ƴarta da arziƙi. Ko da wasa girkinsa bai zo ranta ba balle ya dameta. Yana da kuɗi kuma ta san asalinsa. To me ya rage? "Kada ki yarda ya manta dake. In ya tafi ki dasa kanki a cikin rayuwarsa." "Ta yaya? Ko sau ɗaya bai taɓa nemana ba da kansa." Mami tayi dariyar manya "wannan ai duk ba wata matsala bace. Ke ki dinga bibiyarsa. Gaisuwa safe, rana da dare. Ƴan abubuwan nan namu na mata ku baku iya ba. Sai a zauna sakato ana jiran namiji ya yi komai." Salwa ta sunkuyar da kai "Mami idan mace tana bin namiji fa wulaƙanta ta yake yi." Taf...taji saukar duka a kafaɗa. Rai a ɓace Mami ta ce "banda shashanci dama ai ba da soyayya za ki bishi ba. Kulawa kawai. Ko kissar ma sai na koya miki?" Ta harari ƴarta. "Na fahimta Mami." "Ko ke fa." Da haka Salwa ta kafa masa ƙahon zuƙa. Waya da saƙwanninta babu wani abu da zai bada ita har yasa Taj gudunta. Yayana sama Yayana ƙasa ne dai. Gaisuwa, bibiyar ayyukansa da yi masa fatan alkhairi. Tun yana sharewa har dai bisa shawarar Kamal ya soma amsa mata a mutumce. "Ba'a san inda rana za ta faɗi ba. Ka daina wulaƙanta duk mai nuna damuwarsa a kanka." "Kada ta sa rai ne Happiness." Dariya Kamal ya yi "kai ma kamar wani ɗan yaro in kayi wani abin. Ai yadda ta zo maka a ƙanwa haka za ka je a matsayin yaya. Tunda baka so ta bijiro da zancen soyayya sai ka toshe ƙofar." "Kamar ya?" "Ka dinga bata labarin wata a matsayin budurwarka. Wataran ka ce ma tana gaisheta." Girgiza kai Taj yayi kamar yana gaban Kamal ɗin "ba zai zama cin fuska ba kuwa?" "A ƙanwa fa tazo maka. Kuma dai kayi mata hannunka mai sanda taƙi ɗaukar haske. Ba sai ka bita ba kawai a tafi a haka. Ya dai fi akan ka dinga shareta wanda za ta fassara a matsayin wulaƙanci." A haka suke ta tafiya. Ya Taj da ƙanwarsa Salwa. A ɓangaren Anisa kuma bai san wane tudu wane kwarin aka bi ba sai ji ya yi Amma ta tado masa da zancen ko za su fara haɗa lefe kafin su koma gida. "Lefe kuma? Na wa?" Ya tambayeta kai tsaye babu mamaki a tare dashi. "Kada ka raina min wayo Taj. Ya ku ka yi da Anisa?" "Anisa kuma?" Amma ta ɗaure fuska "Allah idan na sake magana ka ce min 'kaza kuma?' Sai ranka ya ɓaci." "Yi haƙuri Ammana." Ya yi mata murmushi. Mayar masa tayi sai kuma ta sake shan kunu. "Ka san sau nawa Daddy yana yi min maganarku? Sai dai nayi ta kame kame saboda ka ƙi cewa komai." Yadda su ka yi da Anisa da Hajjo ya faɗa mata. "Ni na zata mun gama magana tunda ta fahimceni." Yanayin Amma duk babu wani kuzari ta ce "Maganar da aka fara daga sama ai a can ya dace a ƙare ta. Me yasa ba ka faɗa min ba?" Ya yi shiru. Ba zai iya ce mata yaga kamar tana so ba shi yasa ya kasa sanar da ita ba. Anti da kanta tayi mata waya tana cewa wai ta kira tayi mata murna ƴarta ta sami miji. Anisa da Taj sun daidaita. Da murna Amma amsa mata da "cewa zaki yi na cigaba da tari. Allah Yasa damu za ayi." "Amin amin" Anti ta amsa da farinciki. Da su ka yi waya da Daddy ma zancen kenan. Har yana cewa idan su ka dawo da kansa zai yiwa Alhaji magana. Ƙudurin Taj na aure bayan ya koma gida ba abin a kawo ido a zuba masa bane. Dole su za su yi nasu ƙoƙarin a yanzu da Taj ya zama successful su mayar dashi gaban mahaifinsa. Ya gama tsare tsaren hanyoyin da zai bi domin bawa Alhaji haƙuri ya janye fushinsa. Wanda hakan ya yiwa Amma daɗi sosai. Shi ne ta tayar masa zancen shi kuma ya nuna ba haka aka yi ba. "Ni yanzu ya kake so in yi Taj?" Ta ma rasa ta inda za ta ɓullowa lamarin. Idan ta nuna bata so a yanzu da maganar ta fito daga bakin kishiyarta da mijinta kowa ita zai zarga. Za a ce ita ce bata so. Sannan ga dukkan alamu ma dai gadar zare Hajjo take neman ko ma a ce ta ƙulla mata. Kuskure guda zai sa a ce tana gudun ƴar kishiya. Ko kuma a gorantawa Taj rufin asirin da aka yi masa. Ta san Hajjo sarai. Idan abu bai tafi yadda take so ba to mutum ya shiga ɗari ba ma uku ba. "Kasan me nake so da kai?" Ya girgiza kai "ko mene ne zan yi miki Amma." "Kada ka nuna musu komai ta waya yanzu. Don Allah ko da wasa kada kayi abin da Anisa za ta sami maganar da za ta kaiwa Hajjo. Idan mun koma gida sai ayi maganar a gaban kowa. Yanzu ko me zamu yi a waya babu mai fahimta." Ko da Daddy ya zo lokacin da za ayi mata send-off party na retirement basu nuna komai ba ita da Taj. Lafiya lafiya yake waya da Anisa su gaisa. Idan bata kira ba sai ayi sati biyu bai nemeta ba. Bisa shawarar Anti da Hajjo da su ka kitsa wancan zance na amincewarsa duk da Anisan bata so haka ba take yawan kiransa ko ta tura saƙo ta whatsapp. Wata gomq sun ƙare kamar ƙifta ido da buɗewa. Duk wani shiri na komawarsu gida ya kammala. Catering services ɗinsa na Happy Taj ne dai bai rufe ba. Duk lokacin da buƙata ta tashi zai iya komawa ya yi aikinsa ya dawo gida. Zuciyarsa a ranar da za su tafi tana cike da ɗokin sake ganin Hamdi. Ba tare da saninta ba, duk wasu abubuwa musamman wanda su ka shafi samari yana sani a wajen ƴan uwanta. Zee akwai surutu. Ita ke faɗa masa irin abin da Hamdi take yiwa samari idan sun zo. "Ni fa ina ganin kamar akwai wanda take so" ta taɓa faɗa masa watarana. Murmushi yayi shi kaɗai da ya ji muryar Hamdi tana cewa Zee "gulmammiya, yau kuma faifaina aka buɗewa Salman Khan? Ki gama Yaya tayi mana shari'a don ba yarda zanyi ba." Zee ta diririce, wayar da bata gama ba kenan ta tashi tana bata haƙuri. Ita kuwa kaza huce kan dami tayi. Mutumin nan na Abuja da bata san sunan shi ba ta riga ta cire shi a rai, tana kuma jin haushin yadda ya jirgata ta hanyar nuna kamar ya damu da ita. *** Dogon tsaki mai madda da gunna Ummi ta saki a lokacin da Iyaa take duba katunan bikin Sajida da Yaya ta kawo da kanta. "Allah Ya shiryeki Ummi. In Allah Ya so ba zan taɓa aibata ki da bakina ba balle ki fi haka." "Me kuma nayi? Yanzu mutum bai isa ya yi tsaki ba sai an fassara shi?" Tashi Iyaa tayi ta bar falon. Idan ta zauna tabbas za ta ƙare da dukan Ummi da duk abin da ya zo hannunta. Haka su ke ta fama tun bayan dawowarta daga makaranta. Ummi ta kangare fiye da tunaninsu. Maganar aurenta da aka sa ran yi da ta gama makaranta tabi ruwa. Mijin dama na gida ne. Duk shaiɗancinta tana masifar son sa kamar rai. Zancen duniya da baya ɓuya sai gashi mahaifiyarsa da su ke ƴan maza zar da Baba Maje sannan ƴar mace da namiji da Iyaa ta zo har gidan neman ƙarin bayani. Yayinda Ummi take ta tsula tsiyarta a makaranta bata taɓa tunanin akwai idon sani da za su iya kawo zancenta gida ba. Sai gashi a hawan hawa maganar bullying ɗinta da haura katanga tana bin samari yawo ta dawo. Maganar ayi ƙarya ko kwaskwarima ma ba za ta yiwu ba. Dole su ka faɗi gaskiya da roƙon rufin asiri. "Maganar nan ba za ta taɓa fita daga bakina ba in sha Allahu. Amma fa aure babu shi Fisabilillahi" Baba Maje ya kalli ƴar uwarsa, sai dai bai ji haushinta ba sosai. Ko shi ne zai iya yin haka. Washegari ya mayar musu da kuɗin aurensu. Kayan kuma su ka ce a barsu. A ranar babu wanda ya runtsa a gidan. Ummi kusan hauka tayi musu tuburan. Kuka da magiya harda barazanar tana son auren. "Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa. Ke ki ka haƙawa kanki wannan ramin. In kina da hankali sai ki canja tsarin rayuwarki don gujewa maimaici." Tana gunjin kuka ta ce "yanzu Baba akan ɗan daudu da ƴarsa ka gwammace rayuwata ta zama haka? Baka barni nayi jarabawa ba sannan auren ma ka kasa hana a fasa shi?" "Ɗan daudun ne kuma yake ta fafutukar ganin kin koma makaranta ba." Ya ce da faɗa "amma da yake kin daɗe kina taɓa mutumcin mutane Allah Yana yi miki talala yanzu ai kin ga ishara. Duk ƙoƙarinsa abu yaƙi ci yaƙi cinyewa. Ni kuma da hannuna ba zan sake kai ki wata makarantar ba." Gidan da su ka barta basu tsira ba. A hankali ta tsiri fita yawo. Idan ta dawo ayi faɗan, dukan da nasihar duk a bayan kunnuwanta. Shafawa idanunta toka kawai tayi tana abin da ranta yake so. Cikin watanni kaɗan ta ɗashe fata ta koma fara tas. Ga magungunan da take sha na supplement masu ƙara wasu sassan jiki. Halittarta duk ta sauya ta koma wata daban. Duk inda ta ratsa maza ke bibiyarta suna kashe mata kuɗi. Wayo da dabara irin nata yasa taƙi yarda ta bada kanta. Amma fa tana bari su fanshi wahalarsu ta hanyoyi daban daban. Hukuncin faɗa da duka ya ƙare. Sai nasiha da addua tsakaninta da iyayenta. Halin da ta shiga yana ci wa Abba da Yaya tuwo a ƙwarya. Gani su ke kamar sanadiyarsu rayuwar ƴar aminansu ta gurɓace. Yayinda su Baba Maje kuma su ke ganin dubunta ce ta cika. Halayen da take ɓoyewa su ka bayyana. Ba don abin da ta yiwa Hamdi ba da haka za ta yi ta ha'intarsu ƙila har gidan miji tana rayuwa biyu ba a sani ba. Ummi ta sake ɗaura ɗammarar watsa rayuwar Hamdi a duk lokacin da nata auren ya tashi. Kuma tsakin da tayi ba komai ya janyo ba sai takaicin lokacin ramuwarta da bai yi ba. *** Kimanin sati uku kafin bikin Sajida aka gama komai da ya dace a HAPPY TAJ. An kashe kuɗi domin ƙawata wajen yadda zai janyo mutane. Taj da Abba da kansu su ka dinga yiwa mutane gwaji idan sun zo neman aiki. Banda yaran Abba, sai da su ka ƙara mutane masu ayyuka daban daban a kitchen ɗinsu. Girki, wanke wanke, serving abinci, waiters, cashiers da masu yin fruit juice, mocktails da icecream. Gabaɗaya kitchen ɗin maza ne. Sannan ya nemi inda za su dinga sayen kayan abinci. Komai ya tafi cikin tsari. Ƙannensa Bishir da Abba su ya damƙawa ragamar tabbatar da kayan buƙatar kitchen ba za su yanke ba. Sun daidaita da masu kayan masarufi na kasuwa akan wannan. Spices kuma na recipe ɗinsh za su dinga haɗawa saboda haka raw ɗin kawai su ka nemi mai kawowa. Dankali da kayan miya kuma fresh masu kyau da tsafta daga wajen ƙawar wata sister ɗinsu Rumanatu mazauniyar Jos (08065530483) za su dinga saya. Ya zamana dai babu inda su ka bari haka nan. Masu naman tsire ko gashi su ma interview da gwaji aka yi musu. Iyawa kaɗai bata da garanti sai an duba tsaftar mutum da ingancin kayansa. Haka kuma aka yi a ɓangaren kayan fulawa. Saboda kawai Taj yana son ɗaukar Hamdi sai ya ce bakery ɗinsu mata za a saka. Application babu kama hannun yaro. Da ƙyar su ka zaɓa don babu laifi a Kano akwai masu sarrafa fulawa daban daban da kayansu suke da inganci. Wata ƙanwarsa da ta dinga zuzuta masa ƙawarta Zahra wadda aka fi sani da Donutfairy (08065156303), dole yace a nemota. Ya ɗanɗana doughnut, banana bread da youghurt ɗinta. A take ya nemi signing contract da ita tunda matar aure ce. Aka ƙayyade adadin abin da za ta dinga kawowa kullum da farashinta. Ɓangaren Kamal ma boutique ya tashi sai wanda ya gani. Garden da wurin wasan yara duka an gama zuba ma'aikata. Ranar Juma'a aka yi sauka domin kore kowanne shaiɗanci da neman albarka daga Allah. Sai kuma aka sanya sati mai zuwa a matsayin ranar buɗe restaurant ɗin. Anyi ta sanya talla ta gidajen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta. Akwai discount ga mutanen da za su zo a wannan rana. Ga kyaututtuka na yara domin za su yi gasa da wasanni. Garin Kano ya ɗauka. Ko ina ka zaga ana jiran ranar buɗe Happy Taj. * Gidan Alh. Hayatu ya hargitse da shiryawa wannan rana. In ka duna status da stories ɗin ƴaƴa da jikokin gidan ds su ka tasa, gabaɗayansu abin da su ke ɗorawa kenan. Sai kuma hoton Taj sanye da wasu fararen kaya na girki ya riƙe irin kaskon nan na zamani mai ɗan zurfi da dogon mariƙi a hannu ɗaya, sai kuma cokalin juyawa a ɗaya hannun. Harɗe hannuwansa ya yi dasu irin yanayin tsayuwar Black Panther idan sun yi alamar Wakanda Forever. Yayi matuƙar kyau da kwarjini a hoton. Ƙaryar mutum ya gan shi ya danganta shi da mace. Murmushin fuskarsa yafi komai tafiya da hankalin mai kallo. Yadda ake ta shiri da farinciki a gidan Alh. Hayatu, haka ma su Sajida su ke ta murnar wannan ɗaguwar daraja da mahaifinsu zai samu idan ya fara aiki a Happy Taj. Har anko Abba ya yiwa ƴaƴansa. Yaya kuwa nata kayan sun fi nasu tsada ma. Kowa ya yi murna banda Hajiya Hamdi. Gani take ba a rabu da Bukar bane an haifi Habu. Abbanta zai baro local ƴan daudu su Ƴar Ficika, ya koma hannun international ɗan daudu wai shi Taj. Ita dai da tana da iko da ta hana shi wallahi. Har mamakin yadda kowa na gidan yake ƙaunar Taj ɗinnan take yi. *** Komai nisan dare gari zai waye. Bayan shafe shekara guda da ƴan watanni, gobe ne ranar da za a buɗe Happy Taj. Tunda aka saka rana Hajiya, Mama, Umma da Inna duk kawaicinta su ke roƙon Alhaji da ya yi musu izinin zuwa. Amsar da ya basu ita ce ba zai hana kowa fita ba amma idan sun tafi kada su dawo. Mama da Inna har kuka su ka yi. Ya ce ai bai hana su ba. Kowacce tana da damar zuwa amma tabbas bai yarda su dawo gidansa. Hajiya ta kai ƙararsa wajen Yaya Babba sai dai dattijon ya ce ba zai ƙara yiwa rayuwar ƙanin nass katsalandan ba. Har yau yana ganin laifinsa ne korar Taj da Alhaji ya yi. Suna ji suna gani ƴan uwansu da na mijinsu da ƴaƴansu duk zasu amma ya yi musu shamaki. Walwala da farinciki sai su ka yiwa gidan kaɗan. Taj bai fasa sanar da Alhaji duk abubuwansa ba kamar yadda Amma ta koya masa. Saboda haka duk wani abu da ya danganci restaurant ɗinnan tamkar dashi ake yi. Har hotuna da bidiyo yake tura masa. Bidiyon ƙarshe da aka yi kamar film na minti ɗaya da rabi shi yafi komai ƙayatarwa. An bi ko ina a wurin daga gate har ƙurya. Ga ma'aikata da shi kan shi CEO Taj cikin farinciki suna ta aiki a wajen. Ya kwanta tun wajen tara na dare sai ya kasa bacci. Kewar ɗan nasa tayi masa wani irin kamu. Ya yi kusan awa biyu yana juyi a kwance ƙarshe ya tashi ya ɗauki muƙulli ya fice. Kowa ya yi mamakin fitarsa a wannan lokacin. Kamal zai bi shi Hajiya ta hana. "Wallahi kewar Taj yake. Ku rabu dashi. Bashi da aiki sai kallon waya. Rannan da kunnena naji muryar Taj a wannan bidiyon da yara ke yawan kunnawa. Tunda girman kai ya hana shi dawo dashi gida sai ya yi ta wahala shi ɗaya." "Hajiyarmu yau da kanki?" Abba ya faɗi da mamaki. Don ita bata da zafi kamar sauran matan. "Fita idona ni." Ta koma ɗakinta ta kwanta. Sauran matan ma duk su ka watse. Inna ce da ta shiga ɗaki ta dinga addu'ar Allah Ya daidaita lamura tsakanin uba da ɗan. To dai Alhaji bai zame ko ina ba sai Happy Taj. Shi da ya jima bai yi tuƙi ba ko a jikinsa yau. Ga dare amma haka ya fito ya tsaya a bakin gate ɗin. Ya kalli ginin da wani irin pride yana jinjina kai. Tabbas yana cikin farinciki. Taj bai lalace yadda ya zata ba. Kuma a yau ya ɗauki sama da mutum ashirin aiki da kuɗin halalinsa. "Allah Ya yi maka albarka" ya furta a zuciyarsa. Ya kai hannu ya dafa gate ɗin. Jiniya har ta fara wiii, wiii sau biyu sai ɗif ta ɗauke. Alh. Hayatu ya sake dafa gate ɗin a karo na biyu yaji shiru. Addu'a sosai ya karanta ya tofa a jiki sannan ya koma mota ya tafi. Taj dake ciki yana ƙarasa wasu cike ciken takardu ya share ƙwalla bayan tafiyar Alhajin. A gaban kwamfuta yake aikin inda take nuna masa ko ina da taimakon cctv. Yana ganin zuwan Alhajin ya ajiye aikin gabansa. Zuciyarsa ta shiga wani irin bugu mai tsanani. Ya tashi zai fita sai kuma ya fasa. Yana gudun kada zuwan nasa ya janyo wata matsalar tsakaninsu. Shi ya kashe jiniyar alarm ɗin tsaro da Alhaji ya taɓa gate ɗin. Yana ganin ya tafi ya fito ya ɗora hannunsa a inda ƙiyasinsa ya nuna mas Alhajin ya saka nashi ya sumbata. Wannan abu ya sanya shi farkawa da wani irin farinciki, jindaɗi da annashuwa washegari. * Amma da iyalin gidanta harda Hajjo a Kano su ka kwana. Da misalin ƙarfe biyu da za a buɗe gate ɗin ita da Anti da ƴaƴansu suna sahun gaba. Iman ɗinta dake Lagos ma ta zo da ƴaƴanta. Ga Anisa da Anti takanas tasa aka kira mai kwalliya ta gyare mata fuska. Ita kanta wani irin nishaɗi take ji a zuciyarta. Idan Allah Ya bata Taj, sai tafi kowa murna. Ya Ahmad ma da iyalinsa suna kan layi. Anti Zahra da su Hayat an sha ado kamar za su biki. Salwa kuwa musamman Mami ta aiko mata da sababbin kaya daga Bauchi. Light make up tayi amma ba yadda za ayi ta wuce lafiyayyen namiji ya kasa yi mata kallo na biyu. A cikin wani adaidaita sahu dake fake a wurin kuwa Hamdi ce take cika tana batsewa. Sajida da su Zee sun fito suna tsaye a bakin gate. Yaya kuwa duk yadda Abba ya kaɗa ya raya taƙi zuwa. Wai abin yara ne. Sai dai shi da ya santa yafi kowa fahimta. Har kullum bata fiye son su fita lokaci guda ba. A ganinta suna zubar da darajar ƴaƴansu ne. Uba ga yadda yake, ita kuma tun ƙuruciya har da girmanta ba a rasa yaran dake kwaikwayon tafiyarta. Sai ta zaɓi ɓoye kanta a gida don kawai ta tsira da mutumcinta. Yau Abba har fushi ya yi amma taƙi. Wurin sana'arsa da take sa ran samun ɗaga darajarsa bai dace da ita ba. Yaran nasu basu san wainar da ake toyawa ba. Da Hamdi ba za ta taɓa yarda ta fito ba. Su duka suna ƙaunar Yaya kuma basa jin kunyarta. "Ya Hamdi ki fito mana" Halifa ya dawo ya kuma kiranta don shi baya fushi. Su Zee ne su ka gaji da jiran ta sauko su ka yi tafiyarsu. Da ƙyar ya samu ta fito. Haka kawai da su ka isa gate ɗin ta fara jin yanayinta ya sauya. Ita da bata son zuwa sai farinciki ya ziyarceta har tayi murmushi bayan ta saka ƙafarta a ciki. Tunda ababen hawa basu shiga saboda cikowa, a hagunta Salwa ce take shigowa, a damanta kuma ba tare da ta kula ba Anisa ce da su ka taɓa haɗuwa a Abuja watannin baya. "Assalam alaikum wa rahmatullah" Muryar Taj ta karaɗe wurin ta speaker a daidai lokacin da su ke shiga. RAYUWA DA GIƁI 15 Batul Mamman💖 Sautin amsa sallamar cika wajen ya yi kamar zai fasa kunnuwa. Kusan a lokaci guda Hamdi, Salwa da Anisa su ka toshe kunnuwansu. Sakamakon ƙatuwar sipikar dake kusa dasu wadda ta ƙara ƙarfin sautin. La'akari su ka yi da toshe kunnen da su ka yi a lokaci guda sai su ka kama dariya. Anisa dakatawa tayi da ta kalli fuskar ƴan matan dake gabanta. Bata san Salwa ba, amma ta so ta tuna Hamdi. Ita ma Hamdin sai aka yi dace ta kalleta a lokacin. Mamaki ne ya kama ta domin kuwa babu yadda za ayi ta ce ta manta kamanni da sunan Anisa. Girarta ce ta ɗage tana mai yi mata kallon sani ta ce "Anisan Abuja?" Gaban Anisa ya yi wani mahaukacin faɗuwa. Ba wai son ganin Hamdin ne bata yi ba. Abin da ya kawota taron buɗe restaurant ɗin Taj wanda bata manta ba shi ya dinga rarrashinta a waya har su ka isa inda take a lokacin nan. Kada dai irin abin da take karantawa a social media a ce vendor tayi snatching miji ko saurayin costumer ne zai sameta? Hamdi kuwa tunda gari ya waye sai yanzu tayi dariyar da ta kai mata zuci. Fuskarta ta haskaka da farincikin da yake ranta. "Allah Sarki. Naji daɗin sake ganinki. Lokacin da mu ka haɗu bani da waya. Daga baya da nayi kuma Anti Labiba ta ce ashe bata yi saving number ɗinki ba." Da ƙyar Anisa ta haɗiyi yawu ta ƙirƙiri murmushi. Yanayinta na rashin nutsuwa duka a idon Salwa. Har ta kai ta matsu da son sanin me ya kawo wannan canji a tare da Anisan. Zuwan Sajida da Zee wajen ne ya taimakawa Anisa ta samu ta daina murmushin dolen da take ta yi. "Hamdi zo mu zauna ga seat Yaya Kamal ya ce sai an gama speech za a buɗe ko'ina a shiga." "Har Kamal kin sani?" Anisa ta ce a gigice, sai kuma tayi saurin canja zancen da taga suna kallonta da rashin fahimta "kuna da alaƙa da Kamal?" Hamdi bata da amsar bayarwa don Kamal ɗin ma bata taɓa gani ba. Sunansa kawai ta sani. Ta kalli Sajida tana jiran tayi bayani sai jin baƙuwar murya tayi tana yiwa Zee magana. "Abba Habibu ya shigo kuwa Zee? Taj ke tambayar...." Kasa ƙarasa magana yayi. Ya tsaya kallon Hamdi ba shiri da irin mamakin da ta gama na ganin Anisa. Ya kalleta, ya kalli Sajida da Zee sannan ya yi magana. "Ke ce Hamdi?" Murmushi tayi da kunyar tuna abubuwan da tayi a gabansu wannan ranar. "Ina wuni?" "Ba zan amsa ba don naga alama da gangan ki ka dinga wasan ɓuya don kada mu haɗu." Ya kalli saman stage inda Taj ya juya musu baya yana magana "bari Happy ya gama speech ya zo ya ga mai kukan bolt." Ba don hayaniya ba da sai kowa yaji sautin wucewar wani abu kamar dutse da ya tokarewa Anisa wuya tun ɗazu. Maganganun Kamal sun tsefe mata zargin da zuciya ta fara kitsa mata. Ba kunya ta saki fuska tana dariya harda cewa, "Ai kuwa na san zai yi mamaki." Kamal kuma ya dubi Sajida bayan ya gabatar musu da Salwa a matsayin ɗaya daga cikin ƙannensa. "Na jima ina son tuna inda na taɓa ganin mai kama daku na kasa. Da yake ban ma riƙe sunanta ba lokacin haɗuwarmu a Abuja shi yasa ban taɓa alaƙanta ku ba." "Ikon Allah kenan. Muma fa ta bamu labarin haɗuwar taku." Sajida ta faɗi tana kallon yadda duk wani haske na fuskar Hamdi ya ɗauke kamar an ɗauke wuta. Taɓota tayi sai tayi firgigit ta dubi Kamal ta sake kallon saman stage inda Taj yake tsaye. Dutsen da ya bar ƙirjin Anisa ashe nata ya koma. Ya haɗe mata da wani irin ɗaci na tsagwaron disappointment. Kallon mutumin da ta kasa cirewa daga ranta har rana irin ta yau a matsayin Happy Taj kawai take yi. Ubangidan Abbanta wanda take baƙincikin shigowarsa cikin rayuwarsu da ƙara ingiza mata uba ya cigaba da girki. Daina jindaɗin komai tayi a wajen sai tsananin son ta ganta ƙudundune akan katifarta a ƙuryar ɗaki. Ƙafafunta su ka koma tamkar leda don ji tayi kamar ba za su ɗauketa ba. "Hamdi lafiya kuwa?" Anisa ce tayi tambayar ganin ta dafe kai gami da runtse idanu. Ƙaryar da ta fara zuwa kanta tayi musu. "Jiri nake ji. Haka kawai kaina ya soma ciwo." Da tausayawa Kamal ya kalleta "muje in sama miki inda za ki huta ba tare da hayaniya ba." "Gida zan tafi" ta faɗi tana mai danne kukan da taji ya taso mata. Abin takaici bata ma sani ba kukan na mene ne yake barazanar kunyata ta a gaban mutane. "Yanzu wajen nan fita ma aiki ne. Ki huta ɗin dai zai fi. Maybe kema ba mai son taro da hayaniya bace kamar Happy." Kwatanta ta da Happy ɗinnan ƙara mata ciwo ya yi a zuci. Kamal ya ce su Zee su zauna zai je ya dawo. Sajida ta so bin su ya nuna gara ta zauna da ƙannenta. Zai nemi mai zama da Hamdi har taji sauƙi ta fito. Suna tafiya Salwa ta gallawa Anisa harara irin wadda ake cewa aikin banza harara a duhu domin babu wanda ya kula. Sai ta ja tsaki da ƙarfi sannan ta bar wajen. Babu abin da bata sani ba game da Anisa a cikin gidan Ahmad. Hirar su ka yi da su Taj a waya a gaban Zahra. Ita kuma saboda yadda take ganin Salwa taƙi haƙura dashi shi ne ta faɗa mata anyi masa mata a gidan Amma. Su Zahra da sauran ƴan gidansu Taj ta tafi nema. Ita ma Anisa ta tafi wajen su Anti. Zee da su Sajida ma su ka koma daga gaba inda za su ji kalmomin godiya da Taj yake yiwa duk wanda ya zo. * Ta wata ƙofar baya Kamal ya buɗewa Hamdi ainihin ginin Happy Taj. Wani ni'imtaccen sanyi da ƙamshi mai kwantar da hankali ya baƙunceta. Mantawa tayi da ciwon kai ta zuba ido tana kallon yadda aka ƙawata wajen kamar ba a Kano ba. Kodayake dama bata taɓa zuwa wajen da ya kama ƙafar wannan a kyau da tsari ba. Sama ya su ka hau. A nan taga banda jerin tebura da kujerun masu cin abinci akwai ƙofofi a rufe. Ƙofa ɗaya ya buɗe mata ya tsaya daga gefe. "Akwai ruwa da juice a fridge. Ga key sai ki rufe ta ciki. Idan kin ji ƙarfi za ki iya fitowa kawai ki ƙulle." Kujera ya nuna mata ta cushion mai irin ɗuma-ɗuman nan a can gefe da pillow na alfarma "ki kwanta a can. Ko kina so zan turo wata cikin ma'aikatanmu ta taya ki zama?" "A'a nagode" ta sake kallon wajen "ni da ka barni na tafi gida ma." "Not an option. Kina fita ƴan uwanki za su bi ki. Kinga kin shiga haƙƙinsu ko?" Murmushi yayi ita ma ta mayar masa. Bata ga alamun samun nasara a tare da shi ba. Yana tafiya ta ƙulle ƙofar ta zare muƙullin tana juya shi a yatsanta ta haye kujerar ta kwanta. A gaban kujerar akwai two seater da one seater ɗinta a gefen hagu da dama. Tsakiya teburin gilas ne wato center table akan lallausan kafet sai TV da tarkacen kallo a kan wata irin tv stand ta alfarma mai kallo ƙofa. Ɓangaren lungu ya shige ta yadda ba a ganin mene ne akan kujerar sai an zagayo gabanta. Da yake a office ɗin ba a jin hayaniya sosai shiyasa wajen ya yi mata shiru. Tunanin yadda aka yi mutumin da ta gani a makarantarsu ya zama Taj ɗin da ya karaɗe bakunan ƴan gidansu ta fara. Sai dai bai je ko'ina ba bacci ya yi awon gaba da ita saboda daɗin waje. Gajiyar jiya da yau da su ka kusa kwana yin meatpie da samosa ce ta dirar mata gadan-gadan. * Taro ya yi taro. Iyaye da yara, matasa da dattijai kowa ka gani nishaɗi da farinciki kawai yake yi in banda Salwa. Tunda ta ga Anisa taji komai ya rikice mata. Yarinyar bata da makusa ko kaɗan. Daɗinta ɗaya shine gani da tayi ta fita haske nesa ba kusa ba. Anisa black beauty ce. Idanu dara dara da hanci mai tsini. Sai ɗan bakinta madaidaici. Ita kuwa irin fararen nan ne da mazan Kano a wancan lokacin su ke fatan samu ko da mayya ce. Maminsu tana da haske bakin gwargwado. Amma mahaifinsu bafullatani ne fari tas daga garin Dambam. Ƴaƴansa duka babu baƙi. Ga kwantaccen gashi da kyawun fuska. Ɗan murmushi tayi. Babu yadda za ayi Taj ya tsallaketa ya so wata Anisa. Da wannan yaƙinin ta saki ranta aka cigaba da sha'ani cikin walwala. Kamal ɓangaren boutique ɗinsa ya nufa inda ake ta ruwan ciniki. Shi da yaran shagon babu wanda ya sami kansa balle ayi batun nutsuwa. Tuni ya manta da Hamdi da ya kai office ɗin Taj. Ana kiran la'asar mutane su ka fara gangarawa kyakkyawan masallacin dake kusa da garden ɗin wurin. Wani hafizin matashi Taj ya samu zai dinga limanci a wajen. Saboda haka ko babu niyar siyayya sawu ba zai ɗauke ba ga ƴan unguwa da su ka sami masallaci mai kyau irin wannan. Yana jin kiran sallar ya so tafiya yin alwala amma abu ya gagara. Kitchen ɗin nasu ya rikice da aiki duk da sun gama tanadin abinci kafin a fara zuwa. Ba shi ya sami kansa ba sai biyar saura. "Subhanallah" ya furta hankalinsa na tashi "Abba ku ƙarasa zan je nayi sallah." Ya ce da Abba Habibu da ya naɗa Sous Chef, wato mataimakinsa. Masallaci ya yi niyyar tafiya sai yayi tunanin mutane za su tare shi. Musamman ƴan uwansa da su ke ta son ayi hoto. Ciki ya koma. Ya hau sama da bibbiyu. Nan ma a cike yake da mutane. Ɗakunan taronsu ne kaɗai a rufe. Ƙofar office ɗinsa wanda Hamdi bata kula da label ɗinsa ba da za su shiga an rubuta EXECUTIVE CHEF. Da sauri ya buɗe office ɗin ya shige ya rufe ƙofar don kada wani ma ya ganshi. Ya faɗa toilet yayi alwala. Rigar uniform ɗinsa ta chef dake fitar da ƙamshin kitchen ya ɗan tattaro ya kara a hancinsa. Guntun tsaki ya yi ya ɓalle maɓallan da su ka ƙawata ta daga wuya har ƙasa, daidai saman cinyarsa inda yake daura apron. Wurgi ya yi da ita kan cushion chair ɗin da ta bashi baya ya nufi closet inda yake da irinsu spare har goma sha ɗaya. Kowacce set ce farar riga da farin wando. Jerin round maɓallen ne kawai baƙaƙe. Wata rigar ya ɗauko, ya zare ta daga hanger ya mayar da wandonta. Baccin Hamdi ya soma nauyi don ta fara mafarki mai daɗi taji wani abu ya faɗo a fuskarta. Ƙamshin turare mai ɗan karen daɗi ta fara shaƙa sai kuma taji na girki. A hankali ido har lokacin a rufe ta sake danna rigar a hancinta. Ta soma murmushi ita kaɗai sai kuma ƙwaƙwalwarta ta farka ta tuna a ina take. Bata san lokacin da ta ture rigar da sauri ta kuma ƙwalla salati da ƙarfi ba. A tsorace ta tashi ta kallo bayan kujerar. Taj ma saitinta ya kalla da riga a hannu. Allah Ya so shi akwai vest a jikinsa wadda ya yi tuck-in da ita a cikin wandon. "Abbanaaaaaa" Hamdi ta faɗi tana kai hannu ta ɗauki throw pillow ɗin kujerar ta jefa masa. Sakin rigar ya yi ya cafe pillon yana cigaba da ƙarasowa inda take. Kallo ɗaya ya yi mata ya ganeta. Mamakinsa dai me take yi a office ɗinsa kamar aljanna? Da hannu ya dinga yi mata alamar tayi shiru amma taƙi. "Shhhh, zan miki ihu nima." Kama bakinta tayi ta ɓame. Sannan ta lura da bashi da riga. Ba shiri ta ɗauki wadda ya wurga kan kujerar ta cilla masa. "Ya Salam!" Ya ce da sauri don ya ma manta yanayin da yake. Ya koma ya ɗauki wadda ya fiddo yanzu ya saka. Baya su ka juyawa juna daga inda su ke tsaye har ya gama ɓalle maɓallan. "Uhmm" ya yi gyaran murya "how did you get here?" Muryarsa kamar yadda ta tuna ta ba ta mata bace. Irin deep masculine voice ɗinnan wadda sautinta yake ratsa zuciyar mai saurare. Gwanar a tsiwace ta amsa. Ba don zuciyarta ta so hakan ba. Sai don kawai tana son yakice shi daga ranta. Saninsa bashi da wani amfani. A dalilinsa yau wanda bai san Abbansu ba ma ya sani. Kuma ta tabbata haka za a tafi ana cewa ɗan daudu ne. "Wani Kamal ne ya kawoni da ina jin jiri." "Subhanallah, kin ji sauƙi yanzu? Ko a je asibiti?" Taj ya ce da kulawa. "Na warke." "Alhamdulillah. Allah Ya ƙara sauƙi. Da alama kema ba kya son gatherings. Ni kaina da zan iya da zamana zan yi. Taron mutane indai ba costumers bane bana so." "Allah Sarki. Amma ni ina son taro, ciwon kan na gajiya ne" Hamdi ta yi magana tana yamutsa fuska. Taj yana lura da ita. Bai san dalilinta na yin hakan ba. Uzurin rashin lafiyar kawai ya yi mata. "Bari nayi sallah na baki wuri." "Hhhhh" ta buɗe baki tana kallon agogon office ɗin. Biyar saura minti uku. Kamar za ta yi kuka ta ce "ban yi sallar ba nima." Toilet ya nuna mata. Ta tsaya turus tana kunyar shiga banɗaki a gaban shi. Murmushi ya yi kawai ya fice. Ita kuma tayi alwala ta fito tayi sallah. A kullum idan sallah ta kama ta a waje tana yiwa Allah godiya da Yasa iyayensu tilasta musu shiga da mutumci. Idan ka gansu dole su burge ka. Ga kyau ga sanin darajar kai. * Magariba Taj ya so taro ya watse sai gashi kamar a lokacin ake tuttuɗu mutane. Shi da ma'aikatan sun gama kaiwa maƙurar gajiya. Tun suna dafawa a marmace har idan sun ga sabuwar oda sai su ji kamar su ce ba za su karɓa ba. "Don Allah ku saka CLOSE sign a ƙofar restaurant ɗin." Cewar Taj yana fiddo wayarsa daga aljihun wando. Shugabannin bakery da masu nama ya kira ya ce idan sun gama da mutanen dake gabansu su fara shirin rufewa. Yana gama wayar Abba ya ce masa da ya sani bai ce a sallami mutane ba. "Albarkar da muke nema ce ta samu kake neman ture ta?" Taj ya sadda kai "ba manufata ba kenan Abba. Naga gobe za mu fara aiki officially. Idan bamu sami isasshen hutu ba zamu iya farawa a ga gazawarmu." "Ko kusa. Dagewar yau ita za tasa ma'aikatanka su gane aiki ka ke so ba wasa ba. Maimakon a sallami mutane mu bari komai na yau ya ƙare. Babu yafi daɗi akan mun tashi." Taj yaji daɗin shawarar Abba. Shi yasa ake cewa tafiya da gwani da akwai daɗi. Sannan iyawa kaɗai ba ta tafiya daidai sai an haɗa da experience. Tsarin wasu ƙasashen ya sani akan harkar restaurant. Abba kuwa ya jima cikinta a gida Nigeria kuma garin Kano. Suna haka aka dinga kiran Abba amma yaƙi ɗauka. Aikin gabansa yake son kammalawa. Taj sai ya ƙarba. Haƙuri yaji ya bayar da alƙawarin an kusa tashi. Da ya gama ya dubi Taj yana murmushi. "Hamdi ce uwar rigima. Wai in fito mu tafi tana jin bacci." Taj sai yaji babu daɗi. Tara saura amma kamar yanzu aka fara aiki. "Shi yasa nace a tashi. Dare na ƙara yi." "Kada ka damu, muna fita za mu sami adaidaita sahu. Bana son su tafi su kaɗai ne dai tunda duhu yayi. Nayi zaton zamu iya gamawa da anyi magariba." "Bari na kira Kamal ko sun gama. Motarsa ai za ta ishe ku ko?" Abba ya yi dariyar jin ana tambayarsa ko mota za ta ishe su "Adaidaita ɗaya ma yana isar mu. Zee a sama, Halifa a kusa da direba. Mu uku a tsakiya." "A sama kuma? Saman nan dai na bayan seat?" "Eh mana." Abin ɗaure masa kai ya yi ya ce "Ninke ta za ayi ko lanƙwasawa?" Abba ya dinga dariya. Har su ka gama Taj na mamakin zancen zaman sama. Da su ka fito sai yaga har gara wurinsu. Boutique ɗin Kamal ya cika da samari da ƴan mata. Muƙullin motarsa ya karɓa ya ce masa zai kai su Abba gida. "Za ka iya dawowa kuwa?" "Me ka mayar dani ne? Zan dawo mana." Kamal ya yi dariya "a dinga haɗawa da in sha Allahu dai." Da ya fita shima Abba tambayar da ya fara yi masa ita ce ko zai gane hanyar dawowa. Ya nuna babu wata matsala sai su ka tafi. Abba na gaba, ƴaƴansa na baya. Hamdi tana ta faman kumbure kumbure don ita bata son ma a gaba ace suna cin arziƙi. Waya Abba ya gama da Yaya ya sanar da ita suna hanya. Ya duba missed calls. "Ashe kin yi ta kira bayan wadda na ɗauka Hamdi? Ban ji ba ne." "Ai Abba ƙiris ya rage ka fito kaga tana kuka. Ka san yadda bata son zuwa taro." Saurin kallon madubi Taj ya yi kamar ta sani kuwa ita ma ta kalla. Maimakon taji kunyar ƙaryar da tayi masa sai ta juya idanu ta murguɗa baki. "Kin yi kyau." Ya furta idanunsa har lokacin a kanta ta madubin. "Wa?" Abba ya faɗi yana kallonsa. Su Sajida ma duk sun zuba masa ido su na jiran amsa. "Wata mota ce ta wuce yanzun nan. Ba don motata ta kusa isowa ba da ita zan saya." A haka zancen ya mutu. Lokaci lokaci suna haɗa ido ta madubi tana harararsa. Sai bai damu ba. Zuciyarsa tana raya masa tabbas ya yi mata laifi ne. Laifin da yake ganin ba zai wuce na rashin nuna mata ya santa ba lokacin da su ka haɗu a Abuja. Ya kai su gida lafiya amma komawa ta gagara. Ƙarshe sai Abba ya kira saboda rashin dacewar neman ƴan mata sha ɗaya da rabi na dare. Da kwatancem Abban ya fita daga unguwar. Yana tafiya a hanya yana nanata 'in sha Allah ba zan kuma ɓata ba.' *** Satin farkon buɗe Happy Taj lokaci ne da Taj da Kamal ba za su taɓa mantawa dashi ba. Sun sami ciniki da yawaitar al'umma fiye da tunaninsu. Taj gani yake hakan ba ya rasa nasaba da addu'ar da Alhaji ya zo ya yi musu daren da za a buɗe wajen. Da kuma ta iyaye. Sai kuma saukar karatun da su ka yi shi da Kamal da sadaka domin neman Allah Ya sanya musu albarka. Kuma Ya tsaresu da wurin kansa daga zamewa al'umma fitina. Duk da ya yi sanarwar gama ɗaukan ma'aikata to amma fa har lokacin mutane basu fasa kawo takardun neman aiki ba. Ya rufe ido ya ƙara ɗaukar masu shara da wanke toilets. Da kuma masu wanke-wanke da shara. Irin aikinka, irin uniform ɗin da za a ɗinka maka da suna idan an ɗauke ka. Bakery ne kawai ya bar space ɗin Hamdi. Da gaske yana son yin aiki tare da ita. Ya yabawa iyawarta sannan yana kusancinsu zai taimaka masa ya sami soyayyarta. Baya son yin garajen fara nuna mata soyayya a yanayin da ake ciki. Bai san yadda Abba ma zai ɗauki maganar ba don ya kula yana da gudun rigima. Balle kuma Alhaji. Idan ya ƙyaleta haka kuma tabbas zai ji labarin wani ya yi masa shigar sauri. Da wannan shawarar ya tunkari gidan ranar wata lahadi, ana saura kwanaki huɗu kamun Sajida. Cikin gidan ya fara shiga su ka gaisa da Yaya. Bayan sun ɗan taɓa hira ya tashi ya ce ta turo masa Sajida. Kuma sarai ya san Sajidan bata nan. Tun zuwansa aka ce tana wajen gyaran jiki. Zee kuma ta tafi karɓo ɗinki. "Daddawar ɗaka ce kawai a gidan." Kamar bai san wa take nufi ba ya ce "gaskiya a ƙannena babu daddawa." "Ashe baka san Hamdi ba. Kana kallo dai tun shigowarka ta shige ɗaki. In ba kiranta nayi ba kuma da wuya ka sake ganinta har ka tafi." Daga ɗakin Hamdi ta zumɓura baki da kwance zanin da Yaya take yi mata. "Sai ki fito don na san kina jina." Yayan ta ɗaga murya. Taj bai ji ta amsa ba har ya isa zauren ya tsaya. Ya sa rai za ta jima sai gashi bai fi minti biyu ba ta fito. Bakin nan a gaba. "Kya hua Hamdiyya?" Ya zolaye ta. Shi yake yaren ita take jin kunya. "Ba na jin indiyanci." "Na ga mata suna son movies ɗinsu. A nan ku ke tsintar kalmomi. Sisters ɗina dai na san haka su ke." "To banda ni. Ba na kalla. Kuma namiji mai gani ma ba kula shi nake ba." "Allah Ya so ni kenan." Taj ya ce yana neman haɗa ido da ita amma ta ki yarda. Mamaki ya bata don bata yarda da furucinsa ba ta ce "Ba ka gani?" "Ko Salman Khan ɗin da ki ka kirani rannan ban sani ba." "Allah ban yarda ba" ta ce kai tsaye. Taj ya yi dariyar da amonta ya zauna daram a zuciyarta. Bata sani ba ko ana kiran maza cute. Ita dai da yana dariyar nema ya yi ya sauke mata bangon da take ginawa a tsakaninsu. Shammatarta da ya yi da tambayar da fito daga bakinsa ce ta yanke mata shagalar da ta so yi. "Laifin me nayi miki ne da ya zamana tsakaninmu babu kallon kirki sai harara? Ko don ban faɗa miki na san ki ba a Abuja?" Shiru tayi. Ya sake maimaita tambayar amma sai ta kawar da kanta. Bai yi fushi ba ya ajiye girma da matsayinsa ya faɗa mata abubuwan da su ka wakana tun lokacin da Firdaus ta faɗa masa sunanta da biyota gida da ya yi. "Dalilinki na zo gidan nan amma yanzu ba don ke kaɗai na nemi kusanci da Abba ba. Ina ji a jikina zamu amfani juna in sha Allah." Kasa magana tayi. Sai tunani da yawa da take fama dasu. Da yaga tayi shiru ne ya nemi jin ta bakinta. Sai ta faɗi abin da bai taɓa tsammani ba. "Da Abbanmu ya rasa wajen sana'arsa nayi murna ni dai. Na so ace wata sana'ar ya samu ba komawa girki ba." Taj yaji tamkar ta watsa masa ruwan zafi. "Kema ba kya son namiji mai girki ne? Ko kuwa wanda ya taɓa rayuwa irin ta Abba?" "Mene ne maraba? Duk namijin dake girki ba ɗan daudu sunansa ba? Har yanzu ba sunan da ake kiran Abbanmu kenan ba saboda yaƙi yin wani aikin sai na mata." "Daina magana irin haka Hamdi" Taj ya kwaɓeta "yanzu har za ki iya aibata sana'ar da mahaifinki yake yi miki komai cikinta kuma wadda Allah bai haramta ba?" Kuka ta saka masa "Baka ji muryarsa ba? Idan yana tafiya meye marabarsa da ma..." "Ya isa..." ya kaɗa kai yana mamakinta ƙwarai da gaske "indai za ki iya waɗannan maganganu akansa to waye a waje ba zai yi ba? I thought idan kowa ya ƙyamaci mahaifin mutum shi yana son abinsa." "Nima ina son sa. Amma wallahi bana son sana'arsa." Ta kalle shi ido cikin ido "kuma bana son duk wanda zai taimaka masa akan cigaba da sana'ar girki." Tunowa da Alhaji ya dinga yi da kalamanta masu ɗaci. Cikin ɓacin rai ya ce "nima ban ce ina son ki ba. So kada ki yarda ki min rashin kunya akan sana'ata. I am a Chef and I love what I do." Bata san ta ɗaga murya ba ta ce "to wa ya hanaka dama? Meye na sanya Abbana a ciki?" A ganinsa bata ma cancanci ya faɗa mata kuɗurinsa na taimakawa Abba ya rage ko bai daina duka abubuwan mata ba. So yake ya nuna masa zai iya sana'arsa cikin nutsuwa ba tare da ya yi koyi da mace ba. Shi yasa ya ɗauki riƙaƙƙun maza waɗanda ko magana su ka yi sai an san namiji ne na gaske aiki. Girki daban, daudu daban. Wannan abin yake so hausawa masu fahimta irin ta Alhaji da wannan mara kunyar yarinyar da yake jin soyayyarta har yanzu su gane. "Saboda na isa." Ya faɗi don taji haushi. "Me kake nufi? Abbana yaronka ne?" "Uba na ɗauke shi mai sawa ya hana. Wanda kuma da ni ya haifa ba zan guje shi ba." "Na ce maka ina son Abbana. Girkin ne bana so." Ya zata yi ya fahimceta? Indai Abba bai daina sana'arsa ba, gani take ba zai taɓa rabuwa da ɗabi'un da ya koyi girki cikinsu ba na daudanci. Idan mutum yana abu maras kyau a ganinta nesanta dashi, shi ne yafi alkhairi. Shi kuma Taj so yake ta gane cewa sana'ar ba ita ce ta mayar dashi haka ba. Haɗa biyun da mutane su ke yi, shi ne musabbabin da yasa mazan dake son girki da dama a ƙasar hausa su ke karkacewa su yi koyi da jinsin mata. A ganinsu kamar girki ba zai cika ba sai da waɗannan ɗabi'un. Ran kowa a ɓace su ka rabu. Don ko amsa bai iya sake bata ba ya fice abinsa. Ita kuwa tana shiga gida taji saukar lafiyayyen mari daga wajen Yaya. Huci take rai a ɓace "ki ka ce ba ki son duk mai taimakon mahaifinki akan sana'arsa Hamdi? Saboda kin tashi duk runtsi duk wuya bai taɓa ƙin kawo abin da za a ci a yi sutura ba? Ashe baki dawo daga rakiyar zuciya ta ƙyamar babanki ba?" Hannunta akan kumatu tana jin zafi har ranta ta ce "Yaya ku daina yi min irin fahimtar nan. Ina son Abba mana. Girkin ne kawai...Yaya har yanzu muryar mata gare shi fa" Sai kuka mai cin rai. Yaya ma kukan take yi. Duk cikin ƴaƴanta dama kafiya da sanya abu a rai babu wanda ya kai Hamdi. Kowa na zaton rigimarsu da Ummi ta kashe mata waccan ƙiyayya. Ashe har yanzu bata son sana'ar. To amma wacce take so ya yi? Bayan mutane suna da wuyar uzuri da ƙarɓar kuskure. A yanayi da ɗabi'unsa, duk inda ya sanya ƙafa neman taimako ko son fara sana'a sai ace ɗan daudu ne. Girkin ne kaɗai idan ya yi sai an bishi an saya. Da shi kaɗai yake tsaye a ƙafafunsa. Banda wauta da ƙuruciya me zai sa ta ƴarsa ta zauna ta faɗawa wanda ya killace mata uba daga gaban murhun da kowa yake ganinsa a da. Yanzu sai ya gama ya dawo iyakarsa kitchen. Ba a ganshi ba balle ma a aibata shi. Kuma saboda duka kitchen ɗin maza ne har ya fara ƙoƙarin gyara tafiyarsa. "Kin bani kunya wallahi." "Yaya..." "Tashi ki bani wuri." Ɗakinsu ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita. Soyayyar da take yiwa Taj ta ɗauki sabon salo. Haushinsa kawai take ji. Ba ma ta son shi. Kuma ba za ta taɓa son nashi ba. "Aikin banza. Meye abin burgewa a namiji mai girki? To da me matarsa ma za ta burge shi?" Ta ayyana a ranta duk cikin kukan. Shi a ranar kasa gane kansa aka yi a Happy Taj. Da yaga komai ƙanƙantar abu sai ya yi faɗa sai ya koma office ɗinsa kawai ya rufe ƙofa. Kan 3 seater yaje zai kwanta ya tuna Hamdi ta taɓa kwanciya a kai sai ya tashi yana tsaki. "Ashe yarinyar nan bata da kunya? Na iya haƙura ma da Alhaji ya koreni balle wata ƙaramar yarinya?" Daga inda suke kowannensu ya dage yana sauke fushinsa ta hanyar ƙara faɗawa zuciyarsa girman laifin ɗayan. Shi dai Taj baya son wadda ta kasa ganin ƙoƙarin mahaifinta a matsayin da Allah Ya ajiye shi. Ita kuma Hamdi gani take tsabar mugunta ce ma za ta sa ya cigaba da ingiza mata uba akan hanyar da babansa ya kore shi a kanta. *** An yi Kamun Sajida ranar laraba cikin farinciki da taron dangi. Hamdi tuni ta ajiye wani Taj ana ta sha'ani. Wannan karon ko ciwon kai bata ce tana yi ba saboda tsananin farinciki. Sajida ta sami wanda take so kuma yake sonta ba tare da ya taɓa goranta mata ba. Damuwar su Yaya da tsoron ƴan matansu ba za su auro ba ta kau. Komai nasu na rufin asiri sun yi domin fitar da juna kai kunya. Alhamis aka yi sisters' a wani event centre. Ranar dai har rawa Hamdi tayi tunda taron mata ne. Sai da Anti Labiba ma ta janyeta saboda ko gajiya bata yi. Ana canja kiɗa take komawa. "Wannan ko ke ce amaryar sai haka." Wata ƴar uwarsu ta kare mata "barta tayi. Ranar nata auren ai ba yi za ta yi." * Ana can ana shagalin biki wasu motoci biyu masu kyau su ka yi parking a ƙofar gidan Abba. A tsaye yake da Kamal da Taj. Kamal ne ya zo bashi tashi gudunmawar wadda ta kasance ta kayan abinci. Saɓanin ta Taj da ya bashi kuɗi. Yana ta cewa sun yi yawa da almajirai na kaiwa cikin gidan waɗannan motoci su ka tsaya. Ƴar Ficika ne ya fara fitowa daga motar gaban yana murnar ganin Abba a ƙofar gida. "Waɗannan mutanen ne su ka zo nemanka nace musu ai ka tashi daga wurin. To sai..." ya juya ya nuna wani Alhaji da ya nufosu yana takawa kamar baya so "wannan Alhajin ya nemi in kawo shi wurinka. Har za mu je restoran ɗin sai na tuna ɗazu ka ce min kana gida." Abba ya yi murmushi "ai da ka sa wani ya rako shi ma." "Yaran nawa duk basu san nan ɗin ba." Abba ya miƙawa mutumin hannu domin su gaisa sai ya ƙi ɗaga nasa. Kallon wulaƙanci kawai yake yiwa Abban. Shi da ragowar mazan da su ka firfito daga motocin har su biyar. "Kai ne Habibu Simagade?" Abba ya ɗan murmusa "a da kenan." Ya kuma miƙa hannun mutumin bai karɓa ba dai. "Ni ne uban Safwan mahaifi." Mamaki ya bayyana a fuskar Abba. Tabbas ga kama nan. To amma ba wani abu bane tunda da ana neman aure kawunnansa ne su ka zo. "Allah Sarki. Bari nasa ayi shimfiɗa a ciki." "Barshi. Zuwa nayi na faɗa maka cewa idan ka kuskura aka ɗaura aurensa da ƴarka gobe sai na ɗaure duka mutanen gidan nan." "Alhaji me ya faru?" Abba ya ce da fargaba. Taj da Kamal ma hankalinsu tashi ya yi. "Meye ma bai faru ba? Ya faɗa min yana son wata yarinya nasa aka bincika aka ce ubanta ɗan daudu ne. A ranar na soke maganar. Shi ne ya haɗa kai da wan uwarsa aka zo aka nemi aure da komai a bayan idona. Suna ta ɓoye ɓoye basu san na sani ba. Dama bari nayi sai goben in ci muku mutumci duka a wajen ɗaurin auren. Sai yayansa ya shiga maganar" ya nuna babban ɗansa "shi yasa na zo yau. In kun je an ɗaura za ku ga abin da zai faru. Zuriata tafi ƙarfin haɗa jini da irinku. Ɓata gari, lalatattun mutane" Banda Innalillahi babu abinda Abba ke faɗi. Ƴar Ficika kuwa ihu ya saka kamar mace yana ta jan jallabiyarsa sama yana tumamin wai sun shiga uku. Baban Safwan ya kalle shi cikin takaici da baƙincikin anyi asarar namiji. Haƙuri Abba ya fara bashi ya dakatar da shi. Kamal da Taj su ka saka baki ya ce babu ruwansu. Ba su yi aune ba Abba ya dire gwiwoyinsa a ƙasa zai fara roƙo mutumin ya juya abinsa bayan ya yi tsaki. "Alhaji ka yiwa Allah kada ka hana auren nan." Da sauri Taj ya kama hannunsa zai ɗaga shi amma yaƙi miƙewa. "Abba don Allah ka tashi." "Idan auren nan bai yiwu ba gabaɗaya gidana laifina za su gani. Sajida bata taɓa saurayi ba sai akan shi. Sun saka rai Taj, kowa ya saka rai. Duniya za ta zage ni. Duniya za ta min dariya.." Babu wani tunani ko hangen nesa Taj ya ce masa "Abba indai ka amince za ka bani Hamdiyya, in sha Allahu gobe za ka aurar da ƴa." "Taj?" Kamal ya kira shi gabansa na faɗuwa. "Ina son ta Abba. Saboda ita na zo gareka." Abba Habibu rasa bakin magana ya yi. Ido kawai ya zubawa Taj har motar baban Safwan ta bar layinsu bai sani ba. RAYUWA DA GIƁI 16 Batul Mamman 💖 _Ya Rabbi. Ya Zhuljalal wal Ikhram. Allah ƴaƴanmu sun koma makaranta. Ka duba mana su da dukkan abokan mu'amalarsu da sauran ƴaƴan bayinKa. Ya Allah Ka tsare su daga dukkan sharri. Ka kare su daga zamewa kowa sharri. Allah Kada a kai ƙararsu, kada su kai ƙarar wani. Ka basu ilimi mai albarka da amfani. Kasa aci moriyar abin da ake nema na boko da addini. Ya Sami'ud du'a Ka fimu sanin mawuyacin halin da ƙasarmu take ciki. Ka horewa iyaye abin da za su ciyar da iyalansu daga halali. Ka makantar damu akan haram. Duk uzurin da zai taso Ya Allahu kada Ka sa mu roƙi kowa. Ka buɗa mana. Ka albarkaci nema da samun mu. Ya Rabbi Ka kawo mana sauƙi da sassaucin rayuwa. Ka azurtamu daga taskarKa wadda bata da iyaka. Amin_ *** Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ƙauna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya miƙe tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu. "A duniya bayan iyayena da matata da kuma ƴan uwana da ba su guje ni ba da kuma ƙalilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai haɗamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata." Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da ɗanyen aikin da Taj ya ɓallo. "Abba..." Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa. "Kada ka damu Kamal. Ba zan taɓa zama butulu gareku ba. Na san duka abin da kake gudu. In sha Allahu ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai ƙara nesanta uba da ɗansa ba." Daga Taj har Kamal ba ƙaramin tausayi ya basu ba. Taj ya rufe ido ya ce, "Abba, Alhaji ya daɗe da zare hannunsa a kaina. Auren Hamdi ba zai ..." Kamal ya katse shi da hanzari "wallahi zai ƙara girman fushinsa a kanka. Haba Happy, ba ka tunanin su Inna ne?" Ya mayar da idanunsa ga Abba "ni zan auri Sajidan in sha Allahu. Laifin ba zai tattare akan Taj ba." Abba jinjina zumuncin ƴan uwan yayi. Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya faɗa musu. "Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa. Ko shaƙiƙan da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba. Amma ku tafi gida, nagode. Zan bawa Sajida haƙuri. Na san za ta yi min uzuri." "Sai dai idan ni ne baka son bawa ƴarka. Ba auren taimako zan yi ba. Allah na fi shekara ina sonta." "Har a yaushe ka santa?" Kamal ya tambaye shi don bai yarda da zancensa ba ko kaɗan. "Duka wannan bai taso ba. Ku je gida. Nagode" Abba zai shige gida Ƴar Ficika ya kamo shi da sauri. Duk sun manta dashi. Kwarwar da yake da ihu ma ba sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa. "Simagade....au Habibu ashe baka da hankali? Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi ka watsa mana ƙasa a ido. Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta ɗorawa alhakin rabata da farincikinta. Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba. Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure su duka." "A'a Balarabe. Baka san komai akan yaran nan ba. Son zuciya a yanzu ita ce ƙiyayya mafi girma da zan nuna a madadin kyautatawar da su ke min." Ƙofar gidansa ya ƙarasa da sauri don ƙirjinsa zafi yake. Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya faɗi a wurin. Ƴar Ficika aka sake samun abin yi. Ya ɗora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa. "Kada ka kuskura ka sake tara mana jama'a. Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya." "To, to" ya amsa kamar ba ɗan cikinsa bane ya yi masa tsawar. Yadda mata ke ruɗewa a irin wannan yanayin, haka nasa hankalin ya gushe. Da Kamal ya juyo bai ga Taj ba. Ya fara tunanin ko cikin gidan ya shige, don yanzu komai aka ce ya yi ba zai yi mamaki ba. Ya lura yana da taurin kai irin na Alhajinsu, sai dai kuma shi Taj ya haɗa da ɗanyen kai kamar wani ɗan ta kife. Idan ya san abu daidai ne to kawai damn the consequences. Horn ɗin mota yaji daidai ƙofar gidan. Ya leƙa Taj ya fito a lokacin. "Mu kai shi asibiti." "Ai ka bari a faɗawa Yaya ko?" Bai ma yi wannan tunanin ba. Amma da yake ya san mahimmancin yin hakan sai ya gyaɗa kai. Salatin Yaya su ka ji su ka koma cikin soron. "Damuwa ce Yaya. Kada ki ɗaga hankalinki musamman tunda da mutane a ciki. Za mu kai shi asibiti." Ɗaga shi su ka yi Kamal ya ƙarasa dashi motar. Taj kuma ya tsaya sakamakon maganar da Yaya ta fara yi. "Ƴar Ficika kuma ya ce..." Taj ya gallawa Ƴar Ficikan harara shi kuwa bawan Allah ya girgiza kai da sauri. "Wallahi ban faɗa mata komai ba." "Me ku ke ɓoye min?" Ta tambaya hankalinta a tashe. Dama bata ga abin da zai ɗaga masa hankali ya faɗi ba. Bayan bikin nan shi ne babban farinciki da cikar burinsu. Gani su ka zasu ɓata lokaci sai kawai Taj ya ce Ƴar Ficika ya faɗa mata in sun tafi. "Amma don Allah ki bar maganar a wajenki kafin ya tashi mu san abin yi. Yanzu hankalin mutane ne kawai zai tashi." "To, nagode. Idan kun je asibiti ka faɗa min. Sai na kira ƙaninsa ya taho." Kana ganin yadda take magana sai ta baka tausayi. Da gani hankalinta ya kai ƙololuwar tashi. Tana dannewa ne kawai saboda mutanen cikin gidan. * Asibitin kuɗi Kamal ya kai su amma ba wanda ƴan gidansu su kw zuwa ba. Ana buƙatar file Taj ya buɗe musu na family. Aka shiga dashi ciki aka duba shi. Jininsa ya hau sosai shi da bashi da bp. Dole aka bashi gado ana jiran jikin ya daidaita. Drip aka saka masa da allurai sannan ya sami bacci. Zaman jiran Abdulƙadir ƙaninsa Taj da Kamal su ka yi a ɗakin. Kamal ya dube shi a tsanake. "Yanzu Happy duk abubuwanbda su ka faru da kai a gida ba su isheka ba? Kai da bakinka kake cewa za ka auri Hamdi. Auren ma gobe goben nan. Less than 24hrs. Har kana yiwa Abba ƙaryar sonta kake kawai don kafi kowa iya rigima." "Allah da gaske nake ina sonta Happiness." "Kai ɗin? Ya aka yi ban sani ba?" Ya tambaya don bai gaskata shi ba. Babu wani juya zance ya ce "Saboda nayi tunanin za ka ƙaryata duk wata niyyata ta janyo Abba Happy Taj. Infact bana tunanin da ka sani ko zuwan farko ba za mu yi gidan ba in ka san waye babanta." "Lallai ka iya ganganci. Banda ɓoye min da kayi da kuma kana can tayi saurayi fa?" Taj ya yi murmushi "wallahi a next flight za ku ganni." "Da ni na ce ina sonta fa?" Kamal ya yi tambayar idanunsa cikin na ɗan uwansa. "In sha Allahu ma Allah ba zai jarabcemu da son abu ɗaya wanda mutum ɗaya ya kamata ya so ba." Ya haɗe kafaɗunsa don tsigar jikinsa tashi tayi. "Next time kada ka ɓoye min abin da ya kamata na sani." Gira Taj ya ɗaga yana ƴar dariya ganin Kamal ya ɗauki zafi da gsske. "Bros, faɗa min gaskiya. Ba ka ciki ko? Kaga matar yara ce irina." Fuska Kamal ya ɗaure amma da gani ya sauko "Ji min mutumin nan. To meye marabata da kai?" "Wata biyar mana. Kai fa kana cikin layin tuzurai." "Baka da mutumci Taj. Ni ne tuzurun? Kai kuma teenager ko?" Taj ya gyaɗa kai yana dariya. "Banda ƙuruciya, teenager kamar ka ina zai kai budurwa kamar Hamdiyya?" "Inda ake kai matan..." "Ehemm. Ughhh" Abba ya yi gyaran murya da ƙarfi don ya katse hirar tasu haka. Yaga an kusa zuwa wurin da bai kamata kunnuwan uba su ji ba. Kan sa su ka yi suna tambayarsa jiki. Da sauƙi kamar yadda idanuwansu su ke iya gani. Ya ƙara yi musu godiya sannan ya roƙesu da su bar maganar auren nan haka. Allah zai bashi yadda zai yi da iyalinsa. "Idan Alhaji ya amince za ka yarda a ɗaura goben?" Taj ya tambaye shi kafin su fita. Shi ko a fuska bai nuna damuwa ba da Abba yake ta maganar su daina zancen. Shi dai Abba ya gama gajiya da zancen. Sannan ya matsu su tafi saboda so yake ya fice ya koma gida su shawarta da Yaya. "Me zai hana? Waye zai ƙi jinin Yaya Hayatu ko ma in ce zuri'ar Alh. Sule?" Jin wannan ya kwantarwa Taj hankali. Ya san Alhaji ba shi kaɗai bane shamakinsa. Shi kan shi Abba za a sha fama da shi. *** Salati Yaya ta fara yi kafin ta fashe da kuka. Zaune su ke a cikin wani ɗan falo ƙarami na ɗakin Abba. Ita da shi da kuma Baba Maje, Inna Luba mahaifiyarta da kuma ƙaninsa Abdulƙadir. Faɗan kukan Inna Luba ta fara yi mata kafin ta koma tausarta. "Indai ku ka nunawa yarinyar nan cewa kun karaya na tabbata ciwon da za ta ji sai yafi na fasa auren." "Yaron nan ya cuce mu" cewar Abdulƙadir. "Na dai cuce mu. Rayuwar da na zaɓa ce ta zo tana bibiyar ƴaƴana" Abba ya faɗi da raunin murya. "In ka amince kuma kana jin Sajida ba za ta ƙi ba, yanzu zan kira Baballe ya zo gidan nan a rufe magana. Gobe ya auri ƙanwarsa bakin kowa alekum. Ko kuwa?" Abba ya nuna farincikinsa da godiya. "Zan so haka. Amma Maje ka tuna lallai akwai haƙƙi tsakaninmu da yaran nan. Aure ba a son yi masa shigar sauri. Yanzun nan sai ya jagwalgwala abin da ake son gyarawa." Baba Maje ya dage harda cewa "indai ba kuma rowar ƴar za ka yi min ba ka amince kawai. Ba don ni na haife shi ba amma Allah yaro ne mai biyayya. Ina sa rai in Allah Ya so ba zai bamu kunya ba." Yadda ya matsa ɗinnan sai Inna Luba ta ce a kira yaron. Ba a mayarda hannun kyauta. Kuma Allah kaɗai Ya san dalilin faruwar wannan al'amari. Cikin farinciki Baba Maje ya kira Baballe a gabansu. Allah Yasa baya nesa sosai ya ce gashi nan zuwa. Ita Iyaa da Siyama suna can wajen biki. Uwar baƙin hali kuma an tafi bikin ƙawa kamar yadda ta shirgawa Iyaa ƙarya. Kowa ya yi zugum ana jiran isowar Baballe. Baba Maje ya takura masa da waya saboda basa son ƴan biki su fara dawowa. An gargaɗe su lallai kada su wuce takwas a waje har amaryar. Baballe ya iso hankalinsa duk ya tashi. Irin wannan kira da wayar bai saba dasu daga mahaifinsa ba. Shi yasa ya dinga tunanin ko wani abu ne ya faru. Kafin ya iso sai da ya kira Iyaa yaji lafiyarta da ta Siyama. Ummi kuwa bata ɗauki wayar ba don kada a ce ta dawo gida. Sam ba ya raga mata akan halayen da ta tsiro musu da su a gidan. Tiryan tiryan haka Baba Maje ya labarta masa halin da ake ciki a gaban kowa. Wanda shi Abba ya so su keɓe. Don idan Baballe zai ƙi, ba zai ji nauyin idanuwansu ba. "Baba don Allah ko za mu koma soro mu yi magana" abin da ya ce kenan da Baban nasa ya matsa masa akan ya bada amsa. Gabansa sai da ya ɗan faɗi. Yaran yanzu ba a ci musu laya. Ya gama yabonsa shi ne yake son watsa masa ƙasa a ido. "Nan dukansu amsar da ka bani dole zan dawo musu da ita. Saboda haka gara ma kawai ka faɗa a gabansu." "Baba don Allah" ya faɗi yana cije leɓensa na ƙasa. Shiru ba zai amfane shi ba a wannan lokacin. Shi yasa yake son faɗa masa dalilin da ya sa ba zai iya auren Sajida ba. "Ka je ka saurare shi don Allah. Share ire iren waɗannan abubuwan fa don mun isa su ne su ke zama dalilan yaji ko mutuwar aure. Allah Ya kiyaye." Inna Luba ta faɗi tana nuna musu ƙofa. Ba don ya so ba ya tashi su ka fita. Ransa duk ya ɓaci don Baballe bai saba yi masa haka ba. Yaro ne shiru shiru mai sauƙin kai. Tsayinsu kusan ɗaya don ma shi shekaru sun ɗan durƙusar da shi. Fuskar Iyaa ma'abociyar fara'a ya ɗauko. Ga shi kyakkyawan matashi mai zuciyar nema. Banda aikin da ya samu ƴan watannin baya akwai shi da buga bugar neman halak. Bai san zama ko kaɗan. "Ina jin ka. Kada ka ce min budurwa gareka. Tunda ban san da ita ba, ba za ta zama silar da za ka watsa min ƙasa a ido ba." Baba Maje ya ce a kausashe. "Ba haka bane Baba" Baballe ya ce a ladabce "ƴar uwarta nake so. Na ɗan jinkirta faɗa mata ne saboda wasu dalilai. Gaskiya ba zan iya aurenta ba alhali ina yiwa ƙanwarta so na aure." Ya ƙarashe kai a ƙasa. Gumi ne ya tsatstsafowa Baba Maje. Ya dubi ƙofar cikin gidan. "Danƙari! To yanzu ya kake so nayi? Me yasa ku ke da zurfin ciki ne? Da na sani ko baka faɗa mata ba ai ba zan yi wannan karambanin ba." "Idan zai bani ƙanwar sai ka sanar da su Kawu a ayi auren goben a madadin na Sajidan. Sai a jinkirta komai tunda ban shirya ba." Baballe ya furta da hope ɗin baban zai amince. "Dama ko wace ai zan faɗa musu. Ni damuwata ma ita Hamdiyyan za ta yarda ne? Ko ka manta yadda su ka yi da Ummi a makaranta?" Da sauri Baballe ya ce "Zeenatu ce ba Hamdi ba." "Wace Zeenatu kuma?" Baba Maje ya ce don kansa ya ƙulle. Baballe ya yi murmushi "Zee. Naga bata gama makaranta ba. Niyata zuwa ƙarshen shekara idan ta gama na san lokacin na ɗan yi tari. Sai na gabatar da kaina." Kamar Baba Maje ya make shi don takaici ya ce "banza, kana can kana shiri wane zai shige tsakani sai dai kaji ana batun an kawo kuɗi." Shi dai tunda yaga kamar ya sauko sai ya kwantar da hankalinsa. Ciki su ka koma tare. Kowa ya zuba musu ido. Baba Maje ya ɗan rissina kai na jin kunyarsu ya faɗa musu yadda su ka yi da ɗansa. "Alhandulillahi ai duk gida ne." Cewar Abdulƙadir. "In kun amince dashi maimakon a fara kiran mutane ana cewa an fasa auren gobe, me zai hana a ɗaura nasu. In ya so sai ta tare bayan ta ƙare karatunta." "Hakan ma ya yi. Bari su dawo daga wajen taron sai a faɗa musu." In ji Inna Luba. * Banda gunjin kukan Zee babu abin da yake tashi a tsakar gidan. Sai da kowa ya watse sannan Inna Luba ta kira su har Halifa ɗakin Abba ta faɗa musu. Sajida ko uffan bata ce ba. Tashi tayi da mutuwar jiki ta koma ɗakinsu. Yaya za ta bita Abba ya hana. "Ki barta ta sami sararin yin kuka har taji sanyi a ranta." "Ita kaɗai?" Ta share nata hawayen. "Wata damuwar tana buƙatar kaɗaicewa kafin zuciya ta karɓe ta. Idan tana buƙatarmu da kanta za ta neme mu." Zee ya kalla da ta faɗa kan kakarta tana kuka kamar wadda za a zarewa rai. "Shikenan sai a fara yi min aure bayan ina da yayye?" Inna Luba tana shafa mata baya ta ce "Ja'ira. Ashe kukan ba na ƙin mijin bane. To ai da sauƙi. Yayyenki kuma ki sani kowacce lokacinta yana hannun Mahaliccinta kamar yadda naki yake." "Mijin ma bana so Inna." Ta ce tana ƙara sautin kukanta. "Bana son rashin hankali. Ihun da kike yi maƙota za ki tara mana ko me?" Yaya ta faɗi cikin fushi. Tana son Iyaa da Baba Maje a matsayin aminansu. Amma auren ne bata da tabbas a kai. Auren da aka yi ta soyayya ma gashi nan bai kafin ayi ya tashi. Ina ga wanda ya yi kama da cushe? Duk son su yi aure da take yi, bata so a wulaƙanta su. Hamdi ce ta riƙe Zee su ka koma ɗaki. A nan ta tarar da Sajida akan abin sallah. Kuka take yi amma babu sauti. Sai kwararar hawaye kawai. Sau tari ma'anar sunanta tana binta. Mutum ce mai yawan kai goshinta ƙasa wurin Allah. Zee daina kukan tayi ganin yayarta ta fita nutsuwa. Hamdi ta fita tayi alwala ita ma ta zo ta shimfiɗa abin sallah kusa da Sajida. Ganin haka ita ma Zee sai tabi sahu. Sun riga sun yi sallar isha tun ɗazu. Don lokacin shaɗaya ma ta kusa. Alƙur'ani kowacce ta ɗauka ta buɗe inda ya samu su ka fara karatu. Idan ka gansu abin tausayi kuma abin sha'awa. Yayinda ta ƴan uwan biyu ke nemawa kawunansu zaɓin Allah da sassaucin abin da ya tunkaro su, Hamdi su duka biyun take yiwa addu'ar zaɓin alkhairi. Tana fata kowacce ta sami aminci a ƙaddarar dake jiranta a gobe. Kuka kuwa idanuwansu ko gauta albarka. Duk wannan abu wayar Sajida vibrating take da kiran Safwan. Ita kuwa tayi alƙawarin sake haɗuwarsu ko jin muryar juna sai in sun haɗu bisa kuskure. Ba za ta ɗauka ba balle ace ta kasa haƙuri da wanda babansa ya zo har gida ya ci mutumcin nata uban. *** A ɓangaren Taj yadda abubuwa su ka kasance sai addu'a kawai. Roƙon Kamal ya yi akan ya kai shi gidan Yaya Babba ya ce babu ruwansa. "Ina son rabuwa da iyayena lafiya. Naga kai wannan is the last thing on your mind. Duk nasihar da nayi maka bata shige ka ba." "Don Allah Abba bai baka tausayi ba?" "Ya bani, amma addua ce kaɗai taimakon da zan iya yi masa. Da za ka haƙura da auren Hamdi ni kuma nayi maka alƙawarin auren Sajida." Haushin Hamdi da yake ji ya tuna, sai dai kuma wannan bai isa dalilinsa na haƙura da ita ba. Wannan tsiwar yake son ƙurewa da salon soyayyar da ya tanadar mata. Zafin kai kuwa ya yi imani da cewa bata kai shi ba. Zai gayyato ta cikin rayuwarsa su hau sama su faɗo tare. Barinta ne dai ba zai iya ba. Domin duka wannan rigimar tasu bata kama ƙafar son da yake yi mata wanda ya yi masa shigar farat ɗaya ba. Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya canja shawara. Taɓo mai adaidaita sahun ya yi. "Don Allah ka yi haƙuri. Kantin Kwari zani." "Malam lissafin kuɗinka fa zai canja." Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi. "Ko akwai ciko?" Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya. "Yallaɓai sai dai idan kuma sadaka za ka ƙara min akan wannan." Taj dake neman taimakon Allah sai ya ƙara masa dubu biyu. "Idan mun je in jira ka ne Yallaɓai? "Da ka kyauta. Inda ka đauko ni zan koma." * Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store ɗinsa mai suna Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ƙwanƙwasawa tare da sallama lokaci guda. Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance ɗa a wajen wata da su ke ƴan maza zar da ita. "Kawu dama..." "Matsa na shiga" Taj ya ce da ɗan saurayin. Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi. "Me ya kawo ka?" Ya ce da kakkausar murya. Yaron da ya nuna masa office ɗin don bai taɓa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya rufe ƙofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ƙasa. "Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne." Ya faɗi yana kallon uban. "Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?" Zuciyarsa dokawa take da ƙarfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba zai taɓa auren wadda yake so ba. "Ka fi ƙarfin komai a rayuwata." "Shi yasa ka zaɓi barina akan ka ajiye burinka?" Taj ya girgiza kai "baka bani zaɓi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena." Zuciyarsa hasala tayi. Ɗan nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya ɓata masa rai. "Rashin kunya ka zo ka yi min?" "Ban isa ba." Ya ɗaga kai daga durƙuson da ya yi "aure nake so ka yi min gobe don Allah." "Ka fara shan ƙwaya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?" "Ƴar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron ɗinki." Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu daƙiƙu sai ya buɗe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne, "Me ka ke taƙama da shi ne Taj? Kuɗin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin wannan?" Ya nuna ƙirjinsa "Ni? Ni za ka cewa kana son auren ɗiyar Habibu?" "Bana taƙama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya tsareni daga faɗawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana roƙa min." Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ƙarshe ƙarshe a gare shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo ɗa irinsa. Duk lokacin da yake son taƙwara ɗansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tanƙwara shi. "Shi yasa yanzu ma ka shirya saɓa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?" "Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni kada na saɓawa Allah akan soyayya..." "Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faɗawa waɗannan maganganun?" Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin nauyi. "Ina sonta Alhaji." Ya faɗa kai tsaye abinsa. "Ita ƴar Habibun?" "Eh." "Zo ka zauna" Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daɗe yana tunani kafin ya ce da Taj, "Ka tafi gida ka jirani." "Gidan Yayan za ka zo?" Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi. "Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani." Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai buƙatarsa ita ce ya sami damar yin auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Haƙuri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuɗi. * Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba Habibu. Kafin isha'i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ƴarsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faɗa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ƙarshe yadda ya fahimta wanda kuma da ƙamshin gaskiya a ciki, auren ragewa Habibu baƙinciki Taj yake son yi. Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaɓi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace. * Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa. "Wace tsiyar ka ƙulla?" "Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa." A harzuƙe Kamal ya ce "ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. Ƙarshenta ma harbeka zai yi." Taj ya ƙyalƙyale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj ɗin ne matsoraci. Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana. "Ɗanka ne ya ɗauko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe. Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana." Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba. "Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a ɗaura." Godiya mara adadi Taj ya yi masa. "Ba sai ka faɗawa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da kaina." Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana biyu yasa bai ji ko ɗar ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah. *** Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters' eve. Yau shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin ƴan biki babu walwala sai kowa ya sha jinin jikinsa. Banda ƴan mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar ɗaurin auren sai ƴan uwansa maza. Su duka mamaki bai hanasu haɗuwa a masallacin juma'ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tuƙosu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan ɗanyan kai na Taj. Alhaji ba zai barshi ya sha ba. Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar ɗaurin aure kamar yadda aka faɗa masa. An fara da Abubakar Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya đauki kabbara. Abba yana share ƴar ƙwallar farinciki sai yaji an taɓo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh. Hayatu. Ba ƙaramin ruɗewa ya yi ba kuwa. "Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin aurenta." Abba baki ba rawa ya ce "Yaya Hayatu..." "Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta." "Hamdiyya." Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faɗawa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka sake sanarwa. An ɗaura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu ɗari biyu. A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya ɗuka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa. "Ni ne mahaifin Sabi'u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka haƙura da abin da ya faru jiya wanda bani da masaniya. Sai ɗazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan ɗin ya yi min bayani." Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya ɗaura aure na uku. Safwan Sabi'u Mamman da Sajida Habib Umar. Allahu Akbar Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki. RAYUWA DA GIƁI 17 Batul Mamman💖 *** "Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshiia ƙasa a miƙa godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ƴan matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ƴan dugwi dugwi iyalan Baba." Ba kowa bane da wannan aiki sai Ƴar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guɗar su na yi. Yaya fitowa tayi daga ɗakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka. Anti Zinatu ce kaɗai ta san zaman me su ke a ɗakin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa kaɗai ke iya maganinsa. Hamdi na jin muryarsa ta haɗe rai bayan fitar Yaya daga ɗakin. "Wai namiji kenan. Mtsewww." Lulluɓi Yaya tayi ta fita soron. Ƴar Ficika ya wangale baki. "Sai muka ji abin arziƙi ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne." Ita ma takaicin ɗaga muryar tasa take yi. Ga zaƙin murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa na jinsu a ciki. "Da ka ɗan rage maganar saboda ƴan biki ba su san auren Zee aka ɗaura ba maimakon Sajida. Sannan kana cewa amare uku sai ayi zaton..." "Ba zato bane Jinjin. Ƴaƴan Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya aurar dasu lokaci ɗaya." Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haɗawa da wani. Sai kawai ta koma ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji. "Shirmen Ƴar Ficika ne. Shi da ko wurin ɗaurin auren basu je ba?" Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ƙarfinsa saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma'ar unguwarsu har gida. Tafiyar kimanin minti talatin. Ƙafafunsa sun yi buɗu buɗu. "Yaya! Yaya!!" Ya dinga ƙwala kira kamar makaho na neman ɗan jagoransa. "Kai Halifa lafiyarka kuwa?" Wata maƙociyarsu ta tambaye shi. "Ina Yaya?" Ya faɗi yana dariya. Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya tsallaketa ya rungume Sajida. "Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu" cewar Inna Luba. Murmushi ya yi yana duban ƴan uwansa. "Yaya an ɗaura. Duka su ukun an ɗaura musu aure." Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa. "Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?" "Ya Sajida da Yaya Safwan." Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa "Alhamdulillah." Anti Zinatu ta ce "Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku." Ya murmusa da farincikinsa "a'a, sai Ya Hamdi da Happy." Inna Luba ta ware idanu a tsorace "Hafi? Mutum ne?" Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau. "Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu." Cikin Hamdi wata irin ƙullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da haka danne shi tayi da hannu biyu. "Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?" "Wallahi ke ce Ya Hamdi. Babansa kawai muka gani ya cewa Abba yana nemawa ɗansa aurenki. Sadakinki fa dubu ɗari biyu. Cash in faɗa miki." Daga inda ya yi rantsuwar ita Hamdin ta daina jin komai sai bugun zuciyarta. Wannan wane irin mugun wasa ne Halifa yake yi mata haka? Aure? Ita ce tayi aure kamar wata kayan wasa? Kuma wai da Taj. Waye ma Taj? Kamar ta san sunan. Sama-sama taji muryar da ko gane mai ita ba yi ba tana cewa "Ku riƙeta...Sajida kama hannun. A'a rungumota kawai kada ta kai ƙasa." Luuu haka taji ƙafafunta suna narkewa su kaɗai za su kaita ƙasa. Kafin ta gama faɗuwa aka tallafota zuwa falo. Akan doguwar kujera aka kwantar da ita. Ana yi mata fifita. Daga nan ba za ta iya tuna me ya faru ba. *** Ƴan uwa da abokan arziƙi dafifi su ka yi wajen taya Abba murna a masallacin. Yadda al'amura su ka kasance maƙiyi ne kaɗai zai ce bai jidaɗi ba. Baba Maje baki har kunne shi da Baballe. Murna yake yi, ya sami damar kyautatawa amininsa bayan abin da Ummi tayi. Don tun daga lokacin shi da Iyaa su ka ja baya da iyalin Abba. Suna masu jin kunyar abin da ƴarsu tayi. Duk rashin son fita sai ya zamana Yaya ce mai ƙoƙarin zuwa. A yawan ziyarar da take kai musu ne Baballe yaga Zee ya ƙyasa. Ashe rabonsa ce bai sani ba. A ɓangaren Taj kuma inda mahaifinsa yake ya zauna tare da ƴan uwansa. Kawunnai ne na ɓangaren Alhaji shi kaɗai sai ƴan uwansa su Ahmad. Yadda ya hana Taj faɗawa su Inna tun jiya, haka ya tsallake ƴan uwansu maza da dukkanin abokansa. Mutane na ragowa ya tashi da sauri ya fita. Ƙaninsa Baba Amadu ya tare shi ganin sun nufi wurin motocinsu. "Haba Yaya Hayatu. Ba za mu tsaya mu gaisa da baban amaryar ba za mu tafi?" "Baka gane shi bane? Habibu ne fa. Meye abin gaisawa a nan?" Ya amsa a wulaƙance Daga nan gaban Taj ya faɗi. Su ka haɗa ido da Kamal kowannensu da tunanin da yake ransa. Yaya Babba kuwa haɗe rai ya yi. "Da alama akwai manufar da ta sanyaka amincewa auren nan bagatatan. Dama nayi mamaki da ka sanar dani jiya a ƙurarren lokaci. To amma saboda Taj ne shiyasa na zo don kada sai an zo ɗaurawa ka ce ka fasa don kawai ka muzanta shi." Alhaji ya yi murmushi "bani da wata manufa. Auren fitar da ubangidansa a daudanci daga kunyar al'umma yake son yi kuma nayi masa don kada ma a sami bakin zagina." Kallon tsananin mamaki Taj ya bi shi da shi. Bakinsa ya mutu. Tun ba a je ko'ina ba ya gane shigo-shigo ba zurfi Alhaji ya yi masa. "Alhaji don Allah ka tsaya" Ahmad ya roƙe shi don baya jindaɗin ganin manya su na sa'in'sa. "Kaima ban maka izini tsayuwar ba. Yanzu ku sai ku yi musabaha da mutum irin wannan?" Ya nuno Abba da yake tahowa inda suke da ƴan abokansa. Abin ban sha'awa babu ɗan daudu ko ɗaya. Dama su Ƴar Ficika ne. Shi kuma tunda a gabansa mahaifin Safwan ya ci mutumcin Abban sai ya ce shi da yaransa ba za su ɗaurin auren ba don kada a sake samun matsala. Bawan Allah bai san wainar da ake toyawa ba. Da ya iso hannu ya miƙawa Yaya Babba gami da rissinawa sosai cikin girmamawa. Har sai da Taj yaji wani iri. "Yaya barka da rana?" Fuskarsa shi ma a sake ya ce "Sannu Habibu. Shekaru da yawa. Gashi mun zama surukai." Abba ya murmusa "ina ni ina surukuta da ku Yaya? Ƴa taku ce. Sai dai ace ta bar gida ta sake komawa gida." Ragowar ƴan uwan Alhaji su ka ƙarbi musabaharsa saboda Yaya Babba ya buɗe musu hanya. Ransa fari ƙal ya sake rissinawa ya miƙa hannu ga Alhaji. "Yaya Hayatu ..." Kallon da Alhaji ya yiwa hannun yafi ƙarfin a kira shi na wulaƙanci. Sai dai a ce ƙasƙanci. Domin ba ma da duka ƙwayar idon ya kalle shi ba. Duniya bai ga abin da zai sa ya kama wannan hannun da ya gama lalacewa da bleaching ba. Knuckles ɗin (gaɓoɓin yatsu) duka baƙaƙe ƙirin. Ragowar hannun kuma fari da ɗigo ɗigon baƙi. Yawu mai ɗaci Taj ya haɗiya ganin Abba ya shanye abin da aka yi masa tamkar babu komai. Hannun kawai ya mayar ya ƙara duƙawa. "Barka da rana." "Kaga tashi don Allah. Bana son wannan ɗabi'ar taku ta gaisuwa kamar maroƙa." "Alhaji" Taj ya kira sunansa da ɗan ƙarfi ba tare da tunanin komai ba sama da son ya tunatar da shi me yake aikatawa a gaban mutane. Ko kallonsa Alhaji bai yi ba. Yaya Babba ne ma ya yi masa alama da ya yi shiru kawai. Ba tare da nuna ɓacin rai ba Abba ya miƙe yana murmushi. Zuciyar Taj ta kasa jurar ganin wannan abu. Barin wurin ya so yi. Hannun Kamal a jikin babbar rigarsa ya hana shi motsawa. Alhaji ya ce "Ina son ganinka yau bayan Isha'i. Ai ka san gidana ko?" "Gaskiya ban sani ba. Amma ko Taj sai na biyo in sha Allahu." Alhaji ya yi irin murmushin nan na ɓacin rai. Yana magana ciki ciki "na manta yanzu kai ne uban. To kada ku wuce Isha dai." Ya kalli Taj "kai kuma kada ka manta dokar gidana a kanka. Da ishan ma don ni na kiraka ne." Mota ya faɗa abinsa direba ya ja. Abba ya sake yin murmushi yana ɗagawa motar hannu tare da faɗin "Allah Ya kiyaye hanya." Hannun nasa Taj ya sauke masa ya nuna masa Baba Maje "Abba kaje ga abokinka can ina jin kai yake nema." Sai da ya tafi ƴan uwan Alhaji su ka soma bashi baki. Baki ma kasa motsawa ya yi saboda ɓacin rai. Ya dai dinga gyaɗa kai kawai. Yaya Babba ne ƙarshen yi masa magana. "Ina so ka sani cewa a musulunci iyaye suna da babbar daraja. Bana so abin da Hayatu yake yi maka ya zama sanadin da za ka mayar da martani. Domin idan kayi haka lallai kayi asara. Baka jidaɗinsa ba a duniya kuma a lahira ma ba za ka sami rangwame ba." Godiya sosai ya yiwa Yaya Babban sannan su ka tafi. Ahmad na ganin babu sauran manyan ya ce masa "mu tafi gida mu san yadda za mu yi da matan gidan. Na san dukkaninmu ba za ta yi mana kyau ba. Ace kayi aure babu wadda ta sani." Kafin yanzu da wannan tunanin Taj ya kwana. Amma ƙullin da Alhaji ya soma yi masa ya sa ya daina damuwa. "Baka ji yana yi min tuni akan kada na shigar masa gida ba?" "Ni kuma a ganina wannan shi ne lokacin da ya dace ka take wannan dokar ka shiga gidan. Rayukansu za su ɓaci. Sannan bana jin za su yarda su biyoka gidan Yaya. To a ina ka ke jin za ku haɗu har ka yi musu bayani na fahimta? Don ni ban hango sun amsa wayarka ba balle su saurareka" cewar Abba wani sarkin zuciyar. Bishir ɗan salihin cikin mazan ya ce "Ɗauko sun dai ya dace ayi su haɗu a gidan Yaya ko gidan Yaya Babba." Agogo Ahmad ya kalla. Lokaci na ƙurewa kuma ba su sami matsaya ba. "Mu je gidana ayi shawara. Zan kira su Yaya Hajiyayye dukkaninsu yanzu a hanya. Idan ya so ko mu kaɗai ne sai mu je mu yi musu bayani." Shi dai Taj bashi da ta cewa. Motar Kamal ya shiga Abba kuma ya ja motar Ahmad su ka tafi da Bishir. A hanya Ahmad ɗin duk wata yayarsu ta kusa da ta nesa ya kira ta ya sanar da ita. Bishir aka bari da kiran sauran. Duk wadda ta sami hali ta taho gidan Ahmad. Amma banda na cikin gidansu su uku. Idan aka kirasu dole a zargi wani abu. Yadda shawara ta kaya za su haɗu su je gida wuraren biyar na yamma. * Kamal na tuƙi ya ɗan kall Taj "Yanzu ka fahimci me yasa nace ka bar maganar auren nan Happy? A gaban jama'a kana ganin yadda Alhaji ya tasarma wulaƙanta Abba." Kamar bai ji shi ba sai ya yi masa tambaya. "Me yasa idan na zo da abu baya bani zaɓi Happiness? Sai dai ya bari nayi sannan ya ɗauki hukunci mai tsauri a kai." "Saboda baka tsayawa kayi hangen me zai je ya dawo. Har cewa nayi zan auri Sajida duk don ka haƙura da gaggawar nan amma ka ƙi." "Ko bana son Hamdi ba zan yarda ka auri Sajida ba. Yadda ya sallama ni haka zai yi maka. Sannan kuma ya ɗora laifin naka a kaina." Kamal ya haɗe gira "akan me zai ɗora maka?" "A dalilin kafi kowa kusanci dani mana." Taj ya bashi amsa. Tunanin bai zo masa ba a baya sai yanzu. Tabbas da ya yi auren laifin su biyu Alhaji zai rabawa. Yana ma mamakin da ya ƙyale shi ya buɗe boutique a wurin Taj. Bai zaci zai sami goyon bayansa da wuri ba. Taj ne ya yi magana bayan dogon shirun da su ka yi. "Happiness, ba fa zan bari ya wulaƙanta Abba ba. Ni ban ga dalilin da zai sa mu dinga kasa yiwa mai tsohon laifi uzuri ba. Hakan zai iya sawa su koma ga laifin." Tausayinsa Kamal yake ji. Sai dai kuma yana ganin kamar harda taurin kan Taj. Da zai sauke nasa kambun ya yiwa Alhaji biyayya da tuni an jima da wuce wannan wajen. "Na sani. Amma akwai hanyoyin samun lada da yawa sama da zaɓar wanin mahaifinka." Idanun Taj sai da su ka yi ja kafin ya bashi amsa. "Baka ji me nace bane? Happiness, Alhaji bai taɓa bani zaɓi ba. He just pushes me away and gets angry when I comply (ingiza ni yake yi kuma ya yi fushi idan nayi yadda yake so). Auren nan ina faɗa bai wani ja ba ya amince min. In baka manta ba certificate kawai naje na nunawa Yaya Babba shi kenan ya koreni. Da cewa ya yi in zaɓi girki ko zaman gidansa kaima ka san ba zan taɓa barinku ba. Ba don Amma..." Zaro idanu ya yi waje ya shiga karanto Innalillahi hankalinsa a tashe. Ya kai hannu ya damƙi hannun daman Kamal dake riƙe da sitiyari tunda yafi kusa da shi. "Kamal...ya zan yi? Amma. Ya Rabbi." Ya faɗi cikin tashin hankali. "Me ya same ta?" Kamal ɗin ma duk ya gama ruɗewa. "Ya za ta ɗauki zancen nan? Ga maganar Anisa. Kada hakan ya janyo mata matsala da Daddy." Ya kuma faɗi, damuwarsa na ƙaruwa. Har su ka ƙarasa gidan Ahmad suna jimamin yadda za su tunkari Amma da zancen nan. Kamal ya ƙara tayar masa da hankali da ya ce ya tabbata cikin kawunnansu ba za a rasa wanda zai faɗa mata ba. "Kenan ba a bakina za ta fara ji ba? Shinenan. Na gama yawo." Yadda ya marairaice Kamal dariya ya yi masa. *** Falon gidan Ahmad ya cika ya tumbatsa da ƴaƴan Alh. Hayatu. Duk wadda take cikin garin Kano ta na zaune a wurin. Yaya Zulaiha ce ƴa ta biyu a gidan. Ita ta karɓe girman daga hannun Hajiyayye don ta fi ta zafi. Ta yiwa Taj faɗa sosai. "Don kana son taimako bai dace ka dinga yin abin da zai cigaba da ɓata masa rai ba. Mahaifi ne fa." Haƙuri ya bata da alƙawarin zai yi ƙoƙari a nasa ɓangaren yaga al'amura sun daidaita. Ya ƙara da nanata musu cewa abin ne ya zo akan gaɓa. Yana son Hamdi tun farkon haɗuwarsu. Ya yi haka ne saboda sanin halin mata tunda cikinsu ya tashi. Idan ta kuskure musu, tsaf za a goranta mata wata rana. Babbar yaya Hajiyayye tana jin an kashe wancan zance sai cewa tayi, "Ya maganar lefe? Ya kamata kafin a soma zancen tariya mu haɗa wanda zai fiddo darajar gidanmu." "Kai jama'a, Ya Hajiyayye ana ga yaƙi kina ga ƙura. Wa yake ta lefe alhalin uwayen ango basu san anyi auren ba?" Wata yayar tasu ta ce. Duk sai su ka kama dariya. Hajiyayye dai ta fuske abinta ta ce a samo takarda tayi list. Tunda dai an riga an ɗaura auren sannan bata fatan ace saki ya biyo baya ai kuwa zancen lefe ya zama tilas. Ƴan son biki irinta su ka goya mata baya. Daɗi ya isheta domin ƙannen nata wani sa'in tamkar ƴaƴanta ta ɗaukesu. "Sai ka tambayar min ita size ɗin takalmi da undies. In su Mama sun bamu goyon baya da wuri kaga ba sai an yi wani jinkiri ba." "Ya Hajiyayye ki bar min sayen undies ɗin. Jibi tafiyarmu UK da Abban Farouq. Kin san na ce miki sati biyu kawai za mu yi." Wata ƙanwar tasu ta faɗi da zumuɗi. Taj ya rasa me ya kawo wannan zance a cikin mutane haka. Kunya sosai ta kama shi don bai taɓa tunanin yin irin wannan maganar da Hamdi ba. Da su ka farga da discomfort ɗinsa kuwa su ka dinga yi masa shaƙiyanci. *** Kamar kullum idan magana tana da mahimmanci a wajen Alhaji, ɗakinsa yake kiran matansa ya sanar dasu. A yanzu gidan nasa ya sha gyara mai kyau irin wanda ba a taɓa yi masa ba. Idan ka jima baka shigo ba sai ka kasa gane shi. Duk da cewa fasalin shi ne dai na da, amma an sabunta tsari da kaya yadda zai shiga sahun farko na kowanne maikuɗi. Saboda yanayi na girma, ya fitarwa kansa da wani ɓangaren ta baya inda ya yi sabon sashensa manne da babban falon ƙasan gidan. Saman ya barwa ƴan matan da basu yi aure ba da jikokinsa matasan mata dake yawan zuwa su kwana. Haka kawai Inna ta dinga jin faɗuwar gaba akan wannan kiran. Jikinta ya bata ba zai wuce akan Taj ba tunda ya zo jiya. Tana son sanya ranta yayi murnar ƙila an shirya tsakanin uban da ɗansa, amma kuma duhun fuskar Alhajin ya sare mata gwiwa. Haka su ka zazzauna har ya gama tsakurar abincinsa na rana sannan ya dube su. "Yau bayan sallar juma'a na ɗaurawa Taj aure da ƴar gidan Habibu Simagade." Isashshen lokaci ya basu zancen ya zauna musu. Cike da fargaba da tashin hankali su ke dubansa. Mama tayi ƙarfin halin tambayar ko wani laifi ya sake yi. "Da farko dai yana aiki tare da Habibu saboda ya nuna min ban isa ba. Banda haka ko masu girki nawa ne a garin nan da har sai ya nemo Habibu?" "Alhaji ina ganin ire iren matakan da kake ɗaukarwa Taj ba za su samar da biyan buƙata ba. Shi fa ɗa komai shekarunsa indai yana da iyaye to fa yana buƙatar laluma da ja a jiki." Cewar Hajiya. Cikin fushi da faɗa Alhaji ya ce "an ƙi a lallaɓa shi ɗin." Sannan ya faɗa musu abubuwan da ya binciko da dalilin auren. "Yaron da yake da hankalin son fitar da wani kunya ne zai kasa gane dacewar ya kiyaye ɓacin ran mahaifinsa?" Umma ta ce "Kayi haƙuri. In sha Allahu za mu yi masa magana." "Bakin alƙalami ya riga ya bushe tunda an ɗaura auren." Sai da kowacce ta gama rarrashin Alhaji akan ya yafewa Taj shi kuma yana botsarewa sannan Inna ta dube shi ido cikin ido. "Yanzu da ka tara mu wane hukunci ka yanke masa." Dukkaninsu sun girgiza da kalamanta da ma yanayin fitarsu. Babu wannan ladabin da kiyaye harshe da kowacce cikinsu bata isa ta ƙetare ba. "Abu? Da ni kike?" Ko gezau bata yi ba ta ce "Alhaji na gaji ne. Ina son sanin matsayarka ta uba kafin na sanar da kai tawa ta uwa." Hajiya sai ta ɗan taɓata don tayi shiru. Ita kuwa ta kafe Alhaji da ido. Mamakinta ya hana shi motsin kirki. Da yaga da gaske take ne ya iya yin magana. "Faɗa min naki hukuncin. Ai kema kin isa da shi. Wata tara ai ba kwana tara bane." Gyara zama tayi ta hakimce abinta domin a yau Alhaji ya gama kaita maƙura. "Tunda ka aurar dashi ni kuma in sha Allahu zan yi masa biki irin na ɗan da mahaifiyarsa take so kuma take alfahari da shi." "Da kyau Inna Abu." Umma ta faɗi cikin farinciki tana tafa hannuwa. Da Hajiya ta kalleta ta kaɗa kai tana dariya. Yau ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. "Biki? Yanzu ke sai ki yi bikin ɗanki ya auri ƴar ɗan daudu? Auren da baki ma san da shi ba sai yanzu?" "Aure ka ce, halattacciyar alaƙa. Kuma da kake zancen ban san dashi ba ai ba laifinsa bane. Na yarda da tarbiyar da mu ka bawa ƴaƴanmu. Yaron nan bai taɓa yin wani abu gaba gaɗi kamar mara mafaɗi ba. Tunda har kai ne ka jagoranci ɗaurin auren na tabbata ba a hanya ka tsinci zancen ba." "Haka ne" ya ce da wani irin disbelief. Wai yau Abu ce take kallon idanunsa tana faɗa masa maganganu irin waɗannan. "Na kuma jima da sanin cewa duk abin da zai yi yana turo maka saƙo ya sanar da kai." Bai yi mamakin yadda aka yi ta sani ba "Shi ya faɗa miki ko?" "A wayarka na gani." "Bincike kike min?" Ya ɗaga murya. "Ni na nuna mata" Mama ta bashi amsa ita ma yau da nata ƙwarin gwiwar. Inna ta dube shi bayan ya gama yiwa Mama nata kallon za ki gamu dani ɗin. "Abu guda nake nema daga gareka. IZINI. Duk wani abu da ya kama na bikin nan wanda zai fitar dani ko ƴan uwana..." ta nuna su Hajiya "daga gida ina roƙon ka sahale mana. Sannan ranakun taron su ma ka barmu mu je. A gidan nan kai amarya ne kaɗai uwa bata zuwa. Amma komai tare muke yi ka sani. Ko sisi ba na nema a wajenka. Alhamdulillah ina da abin hannuna na fitar da ɗana kunya." "Ɗanki? Wai yau Abu kin sha wani abu ne?" Alhaji ya ma kasa yi mata faɗa saboda ta shayar dashi mamakin da bai taɓa zato ba. "Ɗana Tajuddin ba. Wanda a kansa na fara sanin daɗin zama uwa. Yaron da tsabar taurin kai irin nasa ya laƙaba min suna Inna tun da sauran ƙuruciyata." ta faɗi cikin tuna baya da tasowar zazzafar ƙwalla "a wajen yi maka biyayya da son kyautatawa na dinga danne haƙƙinsa dake wuyana. To amma daga yau in sha Allahu an gama. Ba zan bari wata aƙida mara tushe tasa ya rayu da fushin iyaye biyu har ma rayuwar tasa ta kasa albarka ba." Tana gama magana ta tashi za ta fita don hawayen da take yi ya hanata cigaba da faɗa masa irin damuwar da ta jima tana dannewa a zuciyarta. "Zainab." Dakatawa tayi ta juyo su ka haɗa ido da Alhaji. "Ban yi miki izinin fita yin duka buƙatun da ki ka nema ba. Haka ma ku" ya kalli inda su Hajiya ke zaune suna murmushin jindaɗin wannan abu. Inna ta goge hawayenta ta kalle shi. "Samun izinin shi ne kaɗai abin da zai sa na yafe maka rabani da ɗana da kayi sama da shekara goma alhalin ba Allah Ya saɓawa ba." Ficewa tayi ko kallon inda yake bata sake yi ba. Umma da Mama su ka bi ta. Hajiya da ta ɗan jinkirta tashi kallonsa tayi. "Tura ce ta kai bango Alhaji. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan baka sassautawa Abu ba to wannan fito na fito ɗin yana nufin ta gaji da aurenka. Muma kuma ƙofa ta buɗe mana na daina shanye mulkin mallakar da kake mana. Ah to." "Wai ni Gambo anya ba sauya ku aka yi ba?" Ya faɗi da gaske. Hajiya tayi dariya "ai na faɗa maka tura ce ta kai bango. Ka bar gani na shiru shiru. Wallahi da Kamal ka yiwa abin da kake yiwa Taj da gidan nan ba zai ɗaukemu ba. Ita kanta Abu har gulmar yakana irin tata muke yi da su A'i. Akan korar Taj da kayi kuma ta cigaba da zaman gidan nan akwai yayunta biyu da su ka fita harkarta. Kafi kowa sanin tana da gata. Mace tilo cikin maza shida! Babu yadda su Alh. Lurwanu basu yi ba akan za su ɗauko Taj daga wajen Jamila taƙi. Kawai don ta faranta maka. Amma kullum sakayyar da kake yi mata ba mai daɗi bace." Ita ma ficewarta tayi ta barshi da tulin tunani da fargaba. Ba zai yaudari kansa ba. Tsoro ya mamaye shi da abin da ya faru yanzu. Idan ya matsa matansa za su iya barinsa babu waige. Idan kuma yayi sakaci gidan zai fi ƙarfinsa. Abu ɗaya ya rage. Ya dinga cizawa yana busawa. A yau dai dole ya busa don yana cizawar Abunsa za ta ɓalle. Matar da zuciya ta kasa tsufa daga yi mata soyayya tamkar yau ya aurota. RAYUWA DA GIƁI 18 Batul Mamman💖 *** Snacks lodi guda jere akan trays Zahra da Salwa su ka dinga shiga dasu falo. Komai da zafinsa saboda yanzu aka soya. Sai sassanyan zoɓo da kunun aya sun sha ƙanƙara a cikin jugs. "Zahra mun tayar dake tsaye ba notice ko? Da ba ki wahalar da kan ki ba. Yanzu mu ke shirin watsewa." Cewar Ya Zulaiha. Zahra tayi murmushi "ko yaya dai ya kamata ku ci. Abinci na so ɗorawa sai Salwa ta bani shawarar sayen frozen snacks daga Happy Taj." Zahra ta nuna Salwa ta sha mayafi "kin ganta nan tana dawowa ko zama bata yi ba ta hau suya. Da kun tafi ma sai an bi ku dashi har gida." Kowa dariya ya yi banda Ahmad da ya maka mata harara. Sai kuma Kamal da Taj da su ka kalli juna. Kamal ya yi dariyar tsokana don ya san ran Taj bai so ba. Ya Hajiyayye tana shan zoɓo ta ce "Mungode sosai. Sai ku fara shiri ku ma. Baƙon gidanku ya yi aure yau." Kallon neman ba'asi Zahra ta yiwa Ahmad. Shi kuwa Salwa da ta tsaya cak yake kallo. Rawar kanta da baya so tayi yawa. Amma duk da haka sai yaji tausayinta ya tsirgs masa kafin ya iya bawa matarsa amsa. "Taj aka ɗaurawa aure bayan sallar juma'a." Ita ma Zahran da yake ta gama harbo jirgin Salwa sai da gabanta ya faɗi. Ta waiga gefenta da sauri amma bata ga Salwan ba. Ashe Ahmad na ambaton auren Taj ta bar wajen a guje. "Me ya sami Salwa?" Wajen mutum uku su ka tambaya a tare. Zahra sai ta faɗi abin da ya fara zuwa bakinta "ai kuwa samosa ta bari akan wuta." Da sauri tabi bayanta har ɗaki. Da shigar Salwan ta banko ƙofar da sauri ta murɗa muƙulli. Kan gado ta faɗa ta riƙe ƙirji. Kukan da take tunanin yi yaƙi zuwa. Sai ajiyar zuciya kawai da wani irin zafi a ƙirji. "Ana wata ga wata" Zahra ta faɗi tana juyawa. Ahmad ta gani a bayanta. Fuskar nan tasa babu salama. Tare gabansa tayi kafin ya fara buga ƙofar. "Don Allah ka barta taji da abu ɗaya." "Wane irin rashin aji ne wannan Zahra? Ke haka kika yi?" Bayansa ta kalla "Rage muryarka don Allah kada a ji." Kamar bai ji me ta ce ba ya cigaba da faɗa. "Duk ta bi ta dami kanta akan wanda bai ma san tana yi ba. Da ta san da yadda yayi wannan auren ma sai ta godewa Allah. Na riga na faɗa mata da wuya Alhaji ya yarda ɗansa ya auri ƴar Mami." Tura shi Zahra tayi don maganganun ta tabbata za su ƙarawa Salwa zafi akan abin da take ji. Duk soyayyar da bata sami haɗin kan zuciyar da take muradi ba, abar a tausayawa ce. Lokacin da tayi ta dakon son Ahmad ta sha wuya. Allah ne Ya taimaketa ashe shima yana sonta. Ranar da ya faɗa mata sai da tayi sadaka mai kyau saboda farinciki. Ƙanana cikin matan ne su ka wanke duk abin da su ka ɓata sannan aka gyara falon kafin su tafi. Zahra ta so su bari domin dai ƴan uwan mijin nata in baka yi bani wuri ne. Kowacce tana ji da boko da gayu. Don ko kina gama secondary aka aurar dake to fa Alhaji zai yi da wajewa da mijin. Ƴarsa dole tayi karatu kamar yadda ya yi. Aiki ko kasuwanci ko zaman gida kuma zaɓin mijin ne idan ta gama. Yadda su ka zo haka su ka tattara su ka tafi gida domin ganawa da iyayensu. Taj kawai aka bari ya shige ɗakinsa ya kwanta. Addu'a kawai yake yi Allah Ya basu ikon yi masa uzuri kada laifinsa ya yi yawa. Zuwa Abuja already ya kama shi. Ya ma ƙudurce a ransa ba zai ɗauki wayar Amma ba ko ta kira. Gara su haɗu kawai ayi ta ido da ido. Abin farinciki shi ne irin tarbar da iyayen su ka yiwa zancen. "Nan da ku ka taho a ayari kun zo yi mana kwarjini ne? Alhaji ya riga ku fasa ƙwan. Har mun fara shirin biki." Umma ta faɗi tana dariya. Kamal ya ce "Tunda baku yi fushi ba mu ai Alhamdulillah." Kafin su watse Hajiyayye ta sake tado maganar lefe bayan iyayen sun tashi. "Bishir kai zan bawa aikin buɗe mana sabon group a whatsapp. Sai a sake maganar a gaban waɗanda basu zo yau ba. Kada ka sako mana Taj dai kaji ko?" Murmushi ya yi akan maganarta taƙarshe "Zan kiyaye. Yanzu mece ce shawararki yadda idan na buɗe kawai zan rubuta inda aka kwana sai kowa ya faɗi ra'ayinsa." Kowa ya yi na'am suna saurarenta. "A nawa ganin ko sisi kada Taj ya kashe da sunan lefe. Na sani cikin gidan nan babu wanda bai mori arziƙin Taj ba tun baya gari. Mu da ƴaƴanmu kullum cikin hidima yake damu. To lokaci ya yi da za a ramawa kura aniyarta. So nake ayi lefe na kece raini amma babu kuɗin ango. Ya ji da muhalli da sauran abubuwan da su ka sauwaƙa kawai." Abinka da gidan yawa. Amincewar tasu kaɗai sai da ta kawo amsa kuwwa a falon. Wai a haka ma don mata sun fi yawa. Sun tsayar da shawarar yadda Bishir zai tsara jawabin. Sai kuma a bawa kowa damar faɗin me zai kawo daidai ƙarfi. Wasu don zumuɗi tun kafin a tashi su ka fara faɗin nasu. Haɗin kansu gwanin ban sha'awa. Ɗakin Mama yafi kusa da inda suke zaune saboda haka taji duk abin da su ke cewa. A zuciyarta ta raya lallai wannan zaman lafiya da ƙullewar zumunci tsakanin matan gida da ƴaƴa shi ne mafi girman arziƙin Alhaji. Ba don haka ba da tuni gidan yafi ƙarfin duk wani zafin rai da tsare girarsa. *** Yawan mutane ƴan Allah Ya sanya alkhairi a gidan ya mantar da Abba damuwar da ya tsinci kansa ɗazu a dalilin Alhaji. Murna ake taya shi da zuciya ɗaya. Cikin hikima ta Allah ya aurar da duka ƴaƴansa ba tare da tsumi ko dabararsa ba. Amaren ne ma dai Sajida ce kawai take walwala. Zee kuka, Hamdi kuwa ba a cewa komai. Tana can ɗakin Halifa ta rufe ƙofa tana fama da ciwon kai saboda uban tunani. Dukan ne goma da ɗari ba ma ashirin ba. Ita ta sani sarai cewa haɗuwar farko ta kamu da son Taj. Irin son nan mai shigar farat ɗaya. A haɗuwarsu ta biyu lokacin ta tabbatar da gaske zuciyarta take. Sai gashi haɗuwa ta uku da ya dace su yi musayar zuƙata ya zo ba a yadda take so ba. Tarin ƙaunar da take masa take ta bi iska saboda sana'arsa. Kuma don abin haushi bai tsaya a nan ba shi ne harda sake dulmiya mata uba cikin sana'ar da tafi tsana. Me namiji zai yi da girki don Allah? Ita mace da tun ƙuruciya ake horata da ayyukan gidan miji da girki ake farawa. Komai manya za su ce game da aure da maganar ɗa'ami suke farawa ko su ƙare. Sai dai kaji ana kiran tsafta, iya kwalliya, ladabi da biyayya...sannan uwa uba girki. Shi fa girkin nan sai an ƙara masa UWA UBA saboda mahimmancinsa. Shi ne zai zo ya koya har ma ya fita iyawa. Don tayi imani girkinsa da nata zai sha bambam. Ya riga ya ƙwace abin tinƙahon da taƙamar. To ita me za ta yi? Shara da wanke-wanke? Muskutawa tayi tana sauke numfashi da ta tuna rashin kunyar da tayi masa rannan da irin abubuwan da ya ce mata shima. Ba shiri ta tashi ta zauna tana sakin murmushi. "Da kansa ma zai sakeni tunda ba sona yake ba." Ta faɗawa zuciyarta. Da wannan tunanin taji wani irin kuzari na shigarta. Tunda Sajida tayi aure ai nata ba dole bane. Salin alin za su rabu. Haka kawai ba za ta iya rayuwar uba girki, miji girki ba. Duniya ma sai tayi mata dariya. Abin da tafi gudu da ƙi ace shi ne a tare da ita muddin rai? Inaaaa! Kamar ba ita ba ta fito tsakar gida. Ana ta taron yinin Sajida. Ita da Zee taji ana cewa tunda ko kamu ba ayi musu ba, za a jira mazajensu su faɗi lokacin da su ke so su tare. A zuci tayi dariyar sai dai su kai Zee ita kaɗai. Sai ta kalli Zee ɗin. Idanunta luhu luhu sun kumbura. Tayi zuru zuru ba a buƙatar likita wurin gane bata da lafiya. Tausayin ƙanwar ya kama ta. Gashi tana ganin wannan auren mai raba shi sai Allah. Irin amincin gidajen nasu biyu da soyayyar da aka ce Baballe na yiwa Zee bata hango mata fitowa ba. Da su ka shiga ɗaki, dafa ta tayi cikin rarrashi ta ce "Allah Sarki Zee. Allah Ya sanya soyayyar Baballe a ranki. Na kula yana da mutumci da sanin darajar mutane." Zee ta sake fashewa da kuka "kema kin ga babu alamun auren nan zai rabu ko? Yaya zan yi?" "Ki kwantar da hankalinki. Bawa bai isa ya ƙetare ƙaddararsa ba. Wani ba ya auren matar wani. Yanayin yadda aka yi auren kaɗai ya ishe ki ishara." Kasaƙe Zee tayi tana sauraron nasihar Hamdi kafin tayi magana. "Ke baki da matsala kenan da auren? Kodayake me zai sa ki ƙi Taj? Nima ba don abin da Ummi ta yiwa Abba a school ɗinku ba da na haƙura." Wayarta ta miƙawa Hamdi "kin gani. Tun ɗazu yake ta turo min message." Saƙonnin har guda shida duk abu guda biyu su ke ɗauke da shi. Na farko haƙuri Baballe yake bata akan rashin sanar da ita da neman yardarta. Na biyu kuma yana jaddada mata ba auren alfarma bane tsakaninsu. Sonta yake. Kuma yana fata za ta bashi dama ya koyar da ita son shi ita ma. Murmushi sosai Hamdi tayi. Bata taɓa sanin soyayya za ta burgeta ba a zahiri sai yanzu. Da alama Baballe zai yi saurin siye zuciyar Zee ta ce a ranta. Tsarin kalaman sun taho da rarrashin da mai karatu zai ji a jikinsa. Ai dole ma ta rabu da Taj. Ko don rashin irin wannan text ɗin na Zee da wayar da Safwan ya yiwa Sajida ɗazu yana ƙara bata haƙurin abin da ya faru. "Allah Zee kada ki tada hankali da yawa. Na san irin auren nan babu daɗi. Amma ki godewa Allah da mai sonki aka haɗaki. Kuma kina ganin yadda Abba da Yaya ke ta murna. Yawan kukan zai sa su ji babu daɗi." Sajida ce ta shiga ɗakin a lokacin. Ta kalli ƙannen nata tana murmushi. "Su Hamdi malaman aure. Irin wannan huɗuba haka? Ko dai dama soyayya ku ke da Ya Taj bamu sani ba?" Idanun Hamdi hango mata Taj su ka yi a gaban tukunya sai taji tsigar jikinta na tashi. Wannan aure ba da ita ba. Ba dai za ta iya labartawa ƴan uwanta niyyarta bane saboda kada yanzun nan su kaita gaban iyayensu. "Gani nayi an riga an ɗaura. Gara mu haƙura kawai. Kukan ciwo zai sa mata." "Da gaskiyarki. Amma ni ke ce damuwata. Jiya da baki san da naki auren ba sam baki da damuwa sai tamu. Yau kuma an ɗaura naga kin yi saurin haƙura kamar ba ke ce ki ka suma ba ɗazu... Don Allah mene ne tsakaninki da shi?" Da Sajida da tayi tambayar, da Zee idanu su ka zuba mata. Tana son gilla musu ƙarya amma ta rasa wadda za ta fi dacewa. Allah ne Ya taimaketa ƴan matan danginsu su ka shigo ɗakin ana tsokanar amare. A dalilin Abba dukkaninsu basu da wasu ƙawayen kurkusa da su ke shawara dasu. Su ne dai ƙawayen juna sai cousins ɗinsu. Gabanin Magriba da baƙi su ka sarara ne Hamdi ta shige ƙuryar ɗakinta da wayar Sajida da tata a hannu. Numbar Taj ta kwafa ta gama karanto addu'o'in neman nasara ta kira shi. *** "Happy kana ganin ka kyauta kuwa? Duk fa irin yadda Yaya ya damu da mu ita ma Salwa jininsa ce." Kamal ne yake yi masa wannan tambayar a yayinda yake shiryawa zai je ɗaukan Abba su je wurin Alhaji. Yadi ne ya saka mara nauyi ruwan bula mai kyau. Rigar tasa kaɗan ya rage ta ƙarasa gwiwa. Hannunta kuma ya ɗan zarce gwiwar hannu kaɗan. Aikin wuyan da aljihu da aka yi ruwan madara ba mai yawa bane. Hula ya ɗora a kansa lokaci guda ya zama kamar ba shi ba. Ya yi kyau sosai. Sai da ya gama fesa turare sannan ya juya ya fuskanci Kamal. "Ya kake so nayi da ita? Me ma nayi mata? Banda na bi shawararka ka san Allah da ko text ɗin da take yawan yi min ba zan kula ba." "Na sani. Amma yanzu da ta shige ɗaki tun ɗazu ya dace ka kirata ka ɗan rarrasheta." Taj ya ware idanu "in yi me? So ka ke tayi zaton aurenta zan yi? Gaskiya Happiness ka rage sauƙin kai. Zai iya kai ka ya baro." "To ko Yayan ka ɗan yiwa magana mana. Sharewa kamar baka san komai ba fa ba daidai bane. Please." Kamal ya ce da damuwa. Baya son rigima irin wannan ta cikin gida. Su duka ƙannen Ahmad ne. Amma ana iya samun dalilin da zai sa Ahmad ɗin ya zaɓi ɓangare guda ya ƙuntatawa ɗayan. "Yanzu dai bani key mu je. In na dawo zan yi masa magana in sha Allah." Da murmushi Kamal ya ce "ko kai fa." Sai kuma ya sako wani zancen "Goben dai za ka tafi Abuja?" "In sha Allahu. In Amma ta tsine min tas za ta bini. Gara naje na daidaita da uwata." "Ba ka yi fushi ba dai da na ce ba zani ba ko?" Kamal ya faɗi yana sosa ƙeya. Ƙwafa Taj ya yi "Kaf ɗinku na san zaman da nake da ku. In matan suna da mazaje ai ku za ku iya zuwa. Amma har Naja da Rukky dake Abuja duk sun zame wai babu mai zuwa rakani." "Naja fa ta ce za ta turo a ɗaukoka daga airport." "Wannan ma laifi zai zama a wajen Amma. Cewa za ta yi wato har na fara neman ƴan uwana na barta." "Allah Ya fito da kai lafiya. Daga nan zan taya ka addu'a. In kaje dai ka gaishe da Anisa." Yana dariya ya yi maganar. Wata kwafar Taj yayi don ya san tsokanarsa yake. Shi ya tuƙa motar. Suna hanya yaji wayarsa tana ta ringing. Idan kiran ya katse a sake binsa da wani. Bai ɗauka ba sai da ya tsaya a danja kafin a bada hannu. Baƙuwar lamba ya gani. Kira har huɗu a jere dole ya bi. Hamdi na ganin sunansa da hasken waya ko ringing bata fara ba ta ɗauka. "Assalam alaikum wa rahmatullah" ta faɗi da ladabin da ya bawa Taj mamaki. Shi da ya sa rai da tsiwa da rashin kunya. Har ya gama tanadin yadda zai ɓullo mata. Sai gashi tana yi masa gaisuwa irin wannan. Haka kawai zuciyarsa ta hana shi soma murna. Gara yaji da me ta zo. Hamdi ce fa. Wadda ta faɗa masa ƙiri ƙiri bata son sana'arsa. Basarwa ya yi ya ce "Wa alaikum salam. Wa ke magana?" "Ya Taj ni ce. Hamdi ce. Don Allah magana nake so mu yi" Ta wani ƙara sauke murya ita a dole mutuniyar kirki. "Ina tuƙi yanzu. Idan na tsaya zan kira ki in sha Allah." Duk da idan ya so zai iya sanya earpod ɗinsa ya amsa wayar, jikinsa ya bashi dalilinta na nemansa. Shi yasa ya katse mata hanzari. "To babu komai. Nagode. Nagode. Zan jira ka don Allah." Jira ya yi ta kashe wayar kafin ya soma dariya. Ya labartawa Kamal rigimarsu ta ranar buɗe Happy Taj da kuma randa ya koma gidan. "To dai mata sai da lallaɓawa. In kana son shawo kanta sai ka ajiye taka rigimar." "Ashe ba za mu daidaita ba. Kallo ɗaya nayi mata na gane rigimammiya ce. Tana yi min zan rama don gidan abin ta zo." Da takaici Kamal ya kalle shi "Kai Happy. Matarka ce fa kuma yarinya ba abokiyar faɗa ba. Ko ina sai ka nuna hali ne?" "Take takenta kamar cewa za ta yi na saketa. Haka jikina yake bani. Ni kuma wallahi sonta nake kamar babu sauran mata a duniya." Ya ƙare magana yana kanne ido. Shi ma Kamal da shaƙiyanci ya ce "Shege...mutumin ya fola tsundum. Allah Yasa kada Alhaji ya kawo cikas dai kafin mu kwashi ƴaƴan love." "Za ka yi bayani. Bari dai hankalina ya dawo jikina in mun shirya da Amma. Ko da duka ne sai ka fađa min sunan budurwarka. In kuma babu sai muje wajen Baba Malam (yayan Inna) ayi maka ruƙiyya. In ma wata jinnu ce ta ƙyasa ayi waje da ita." "Aljana sai dai a kanka. Ni kam ƙalau nake." "To in ba tsoro ba ka faɗa min. Idan kuma kasa ka aka yi ne gara na sani. Sai na baka tips na shawo kan ƴan mata. Ka san mu masu auren nan komai mun sani." "Daga ɗaurawa? Ka rufa mana asiri dai kada ƴar mutane ta tare da ciki." "Sai kace wani namamajo" Taj ya sha kunu. "Da meye?" Da irin wannan faɗan nasu na wasa su ka isa gidan Abba. Idan ka kallesu sau ɗaya dole ka ƙara. Alhaji ya tara arziƙi a gidansa. Ba mazan ba, ba matan ba. Shi kan shi ya san wannan. Waya Taj ya yiwa Abba bayan sun fito daga motar. Ba a jima ba kuwa ya fito da shirinsa harda babbar riga. "Ko shigo ciki ku gaisa da mutan gidan mana. Dama can an zama ɗaya balle kuma yanzu. Kuma mazajen ƴan uwanta ma sun zo. Sai ku san juna ko." Ya nuna ƙofar yana murmushi. Bayansa su ka bi Taj yana sunne kai shi a dole ya shiga gidan surukai. Kamal ya faki ido ya ɗauke shi a hoto ya adana domin duk ranar da ya bashi haushi ya tura group ɗinsu na gida. * Hamdi na zaune da waya a hannu tana jiran kiran Taj a ɗakin Halifa ita kaɗai. Falonsu kuma Safwan ne da abokansa biyu. Sai kuma Baballe da iyayensa. Ga Yaya da amare Sajida da Zee. Tsakar gidan kuwa ƴan uwa ne na kurkusa su ke ta aikin kayan miya na girkin gobe saboda sun san dole a sake zuwa kafin ƴan ɗaukar Sajida su zo. Musamman waɗanda basu ji auren Hamdi da Zee da wuri ba. Abba ya shiga falon da sallama aka amsa. Taj da Kamal su ma su ka yi. Yaya jan mayafi ta ƙara yi. Bakinta har kunne. Duk yadda take son nuna kunyar surukai abu ya gagara. Allah Ya gatance mata a lokacin da bata yi zato ba. Musabaha su ka yi da duka mazan. Sannan su ka gaisa da Iyaa da Yaya. Abba ya sake gabatar musu da juna. "Safwan ai ka san Taj ko?" Safwan ya yi murmushi "sosai Abba. Tun kafin ya dawo ma ta haɗa mu. Abokina ne ko in ce ɗan uwa ma." Sajida ta sunne kai tana murmushi. Safwan ɗin dama ɗan ayi ne na gaske. "To ina jin duka dai Baballe ne baku sani ba. Sunansa Abubakar kuma ɗan amini na ne." Baballe ya taso ya sake basu hannu. "Ni ne dai ɗan autanku. Ina fata zamu yi zumunci mai ɗorewa." Iyaa taji daɗin yadda ɗan nata ya yi. Sai da ta yi dariya da Safwan da Taj su ka ce sun ɗauki girman. Aka ɗan yi raha sannan Baba Maje ya juya dama da hagu. "Ina Hamdiyya ne? Mijinta ya zo ba za ta leƙo su gaisa ba?" "Yi maza ki kirata Zee." Iyaa ta faɗi ganin Yaya ta sunkuyar da kai. A ɗakin Halifan ta sameta. Ta rasa gane zaman me take yi ita kaɗai bayan ta nuna musu ita bata da damuwar auren. "Ki zo ku gaisa da Ya Taj. Amma ki yi sauri don fita za su yi da Abba." Kafin Zee ta gama magana ta fice da ƙaton hijabin da tayi sallar magariba. Falon ta shiga da sallama. Idanunta Taj su ke nema. Shi ma kuma ƙofar yake kallo. Su ka haɗa ido ta kasa yakice nata. Tabbas Taj ne mafarkinta, amsar addu'arta kuma zaɓin zuciyarta. A wannan ɗan taƙaitaccen kallon makaman yaƙin neman sakin su ka fara saukowa ƙasa da kansu. Buɗar bakin Inna Luba da shigarta falon kenan sai cewa tayi. "Mu dai Tajo idan mun zo ɗakin amarya ba girkinta za mu ci ba. Ranar zagewa za ka yi ka girka min don ni ce da gidan ba ita ba." Dawowa daga duniyar da taso mantar da ita waye Taj tayi. Ta kuwa tura baki tana kumbure kumbure. Shi kuwa dariya ma ta so bashi. Yana ta lura da rikicikin yanayin dake bayyana a kyakkyawar fuskarta. Wani irin farinciki na shigarsa. Wannan yarinyar matarsa ce. Bai san lokacin da ya yi murmushi ba. "Ku je daga soro ku gaisa mana kafin Habibun ya fito." Baba Maje ne ya yi maganar. Hamdi bata ɓata lokacin bin umarninsa ba saboda son samun damar yiwa Taj magana. Ita ta fara zuwa soron kafin ƙamshin Taj ya yi masa iso. Ƙasa ta durƙusa da ya shigo don so take kawai a yita ta ƙare yanzu. "Ina wuni Ya Taj?" Ta furta cikin sabon salon ladabinta gare shi. "Lafiya ƙalau. Tashi mana." Ƙin motsawa tayi "dama haƙuri nake son baka akan rashin kunyar da nayi maka rannan. Don Allah ka yafe min. Wallahi ba hali na bane." 'Irin wannan ladabin na neman buƙata ne' Taj ya ayyana a ransa. A fili kuwa cewa ya yi "ya wuce. Nima ki yi haƙurin abubuwan da na ce miki." "Babu komai wallahi." Ta ce da murmushinta. "Uhmmm, dama...na ce...dama...wai ko za ka...uhmmm" ta dinga in'ina saboda kalmomin sun ƙi haɗuwa. Shi yasa ta so su yi maganar a waya. A haka duk yabi ya yi mata kwarjini. Kamal ne ya fito a lokacin. "Happy ga Abba nan. Ya ce kada lokaci ya ƙure." Taj ya dubeta. Duk tayi laushi. Fuskarta kuma tayi fayau da alama tayi kuka. "Zan kira ki in sha Allah. Kamar ƙarfe nawa ki ke kwanciya don kada na tashe ki?" "Zan jira ka. Don Allah ka kira." "Okay." Har zai fita yaji ya dace ya ɗan bata assignment ɗin da zai sa tayi tunaninsa ko bata so "aapna khayal rakhna." Ai kuwa a take ta ɗinke fuska. Taj ya kalleta ya saki murmushi. A babu yadda ta iya dole ta mayar masa tunda tana da buƙata a wajensa. Da ta koma ciki maimaita kalmar kawai take yi tana addu'ar kada Allah Ya kawo ranar da zai zage ya yi rawa da waƙa kuma. *** Kamal ne ya sanar da Alhaji zuwansu. Daga nan ya yi tafiyarsa ɗaki. A gajiye yake sosai. Ga wata yunwa da bai ma san yana jinta ba sai da ya shiga gida. Agogonsa ya kalla bayan ya cire. Ya san a ƙalla yana da minti shabiyar kafin su gama tattaunawa. Don ba zai iya baccin ba tare da sanin me zai faru da ƙaninsa ba. Ledar wasu magunguna ya ɗauko daga ƙarƙashin gadonsa. Ya ɓalli iya wanda yake buƙata ya zuba a wata ƴar roba sannan ya fita zuwa cikin gidan domin samun abin da zai ci. A waje kusa da gate inda Taj ya yi parking Alhaji ya zaɓi ganawa dasu. Gashi dare ne. Kuma lokacin zafi. Sannan wurin akwai shuke shuke. Saboda haka sauro ya far musu. Abba ya lura Taj a takure yake. "Da ka sani ka barni na taho ni kaɗai Taj. Yanzu haka ma Alhaji yana iya jin babu daɗi in ya ganmu tare." "Idan ka ɓata amaryata ba za ta yafe min ba." Salati ya kama a jejjere "Abba tuba nake. Ba da kai nake ba." "Kaji nayi magana?" Dariya su ka yi tare. "Abba ko mu koma mota ne? Sauron nan yanzu sai ya tayarwa mutum da maleriya." "Kai Taj, maleriyar ma tashi take?" Da gaskensa ya ce "ni dai tawa tashi take. Tunda na dawo bana jimawa ban yi zazzaɓin nan ba." Da damuwa Abba ya ce masa "kayi a hankali. Ba a sakaci da lafiya. Mataki za ka ɗauka don shi dai sauro bai san mutumci ba." Dariya su ka sake yi a lokacin da Alhaji ya doso inda su ke. Ya kuwa murtuke fuska saboda baƙinciki. Yaushe rabonsa da hira da Taj wadda za ta saka su dariya haka? Ya ma rasa da wanda zai yi sai Habibu. Duƙawa Abba ya so yi tunda ya fuskanci Alhaji na ƙyamar taɓa shi sai Taj ya taro shi da sauri. "Ai kun gaisa ɗazu." "Yawan gaisuwa ai yafi yawan fađa Taj." Abba ya ce sannan ya dubi Alhaji "barka da dare Yaya Hayatu." "Hmm" kawai ya ce daga maƙoshi a matsayin amsa sannan ya ce Taj ya basu wuri. Ba don ya so ba ya tafi. Zuciyarsa tana ta fama da wasiwasin kada ya barsu Alhaji ya sake yi masa abin da yafi na ɗazu. Gyaran murya ya yi bayan tafiyar Taj ya yiwa Abba duba na ƙyama. "Habibu!" "Na'am" ya sadda kai yana sauraronsa. "Ina son Tajuddin. A cikin ƴaƴana ma ban haɗa ƙaunarsa da ta kowa ba. Abin da ya shiga tsakaninmu har na kore shi bai rage min son abuna ba." Murmushin jindaɗi Abba ya yi "Alhamdulillah. Allah Ya ƙara kawo muku daidaito." "Daidaito kam ana gab da samu sai ka zo ka shiga tsakani." Hankalin Abba tashi ya yi sosai. Taj bai ɓoye masa komai game da rabuwarsa da mahaifinsa ba. Da kuma burinsa na son ya dawo gida kamar kowa. "Indai don ina aiki a gidan abincinsa ne wallahi zan ajiye...kai na ma ajiye. Ba zan so na zama sanadin sabunta ɓaraka tsakaninku ba." Wani irin murmushi Alhaji ya yi "idan ka bar aikin ma zai maye gurbinka da na wani. Bani da matsala da aikinka." Fahimta ce ta ɗarsu a zuciyar Abba. Ya dubi Alhaji a firgice. "Hamdi? Ƴata ce ba ka so tare da shi?" "Ƙwarai." Ya amsa idanunsa na kallon sararin samaniya. Auno halin da Yaya za ta shiga ya yi. Jikinsa ya soma rawa. " Ka taimaka min Yaya Hayatu. Wallahi nayi musu tarbiyya bakin gwargwadon iyawata. Duk da ni na haifeta amma na sani bata da wani aibu na halayya sai abin da ba a rasa ba na ajizancin ɗan Adam." "Ita kuwa take da aibu tunda kai ne ubanta." Ya haɗe rai "Habibu, na baka wata uku ka kashe auren nan. Cire zuri'arka daga jikina shi ne kaɗai abin da zai sa na dawo da Taj gidana. In har da gaske ka damu da shi ba za ka bari rayuwarsa ta ƙare a bin gidan ƴan uwa idan yana son ganawa da mahaifiyarsa ba." Duk dauriya sai da yaji ƙwalla na neman zubo masa. "Me yasa ka yarda aka yi auren?" "Saboda banga alamun idan naƙi zai haƙura ba. Ka riga kayi tasirin da maganarka tafi tawa a wajensa. Zai iya yin komai domin fitar da kai kunya a yadda ya zo min." Gumi sosai Abba ya dinga yi. Allah Ya sani yafi jin Yaya akan Hamdi. Wannan tsananin farincikin da ta shiga idan ya koma baƙinciki kamar ba za ta iya ɗauka ba. Mutane da yawa za su yi musu dariya. Wadda za ta fi yi mata ciwo kuwa ta ƴan uwanta da su ka haɗa uba ce da ta mahaifin nata da har yanzu yake aibata halittarta da aurenta da đan daudu. Ya sake kallon Alhaji sai dai babu wata fuska ta yin magana. Magana ɗaya Alhajin ya ƙara yi masa kafin ya koma ciki. "Ina fata za ka nuna dattako ka riƙe maganar nan tsakaninmu. Dabarar kashe auren tana hannunka. Ni dai kawai nan da wata uku magana ta ƙare." "In sha Allahu." Jikinsa rawa ya dinga yi shi yasa ya kasa komawa motar har sai da Taj ya fito. Kafin ya ƙaraso Abba ya yi composing kansa. "Yau dai na shanyaka da yawa. Muje kada dare ya ƙara yi." Kasa haƙuri yayi ya tambaye shi "Babu matsala ko Abba? Me ya ce maka?" "Ban sanka da haka ba Taj. Tattaunawa ce dai ta yaushe gamo da kuma rashin jindaɗinsa da bamu tuntuɓe shi da maganar auren ba sai a makare." Kallon rashin yarda Taj ya yi masa. Sai dai Abban ya toshe duk wata ƙofar da zai fahimci matsalar. Sun kama hanya za su koma motar Taj yaji Kamal na kiransa. Da ya juya sai yaga Inna tare da Kamal ɗin. Fuskarsa ta haskaka da wani irin annuri. Ya ce da Abba "Innata ce." Kamal juyawa ya yi bai biyota ba. Ta ƙarasa kusa da gate ɗin. Idanunta cike da ƙwalla. Taj kuwa tuni ya yi laushi don ya kwana biyu sai dai su gaisa a waya. "Baki kwanta ba?" "Ina fa. Ina ta fakon shigowar Alhaji ne idan kun gama." Sai kuma tayi murmushi "ango ka sha ƙamshi." Dariya ya yi ya rungumo kafaɗarta. Ba shiri ta ruɗe tana fama ture shi gami da waigawa don kada a gansu. "Ga Abba...surukinki." Abinka da sabo. Ƙasa ya yi zai gaisheta. "Subhanallahi. Haba don Allah. Tashi mu gaisa. Ai mun zama đaya kuma." Duk da bata so amma a mutumce su ka gaishe da juna. Yana ta bata girma. "Da farko zan fara da baka haƙuri don nayi imanin ko me Alhaji ya faɗa maka ba mai daɗi bane. Sannan don Allah kada ka wahalar da kanka wajen yiwa ƴata komai. Tunda ka iya bawa yaron nan ƴarka in sha Allahu ba zan bari ta kuka da komai ba. Nagode da karamcinka a garemu." "Ikon Allah. Hajiya ai nine da godiya da Taj bai ƙyamaci zuri'ata ba." "Wanda ya baka ƴa ai ya gama maka komai." Ta faɗi tana murmushi "idan babu damuwa ina son ya kawo mana ita cikin sati mai zuwa. Zan karɓi numbar mamanta mu yi magana kafin na zo. Ka san Alhajin naku sai da lallaɓawa." Murmushi ya yi shi ma "kada ki damu. Hamdi ƴarki ce kuma ikonki. Ina ƙara godiya." Taj ma godiyar ya yi mata. Abba ya dubi uwa da ɗan su ka bashi tausayi. Me yafi wannan ciwo ace uwa tana son ganin ɗanta amma sai dai ta saci hanya ta fito kamar mai laifi? Dole zai san yadda ya yi da Yaya da Hamdi a raba auren cikin lumana. *** Har ƙofar gida Taj ya kai Abba. Su ka yi sallama ta girmamawa. Taj yana ta sake tambayarsa ko babu matsala game da ziyarar da su ka kaiwa Alhaji. Shi kuma ya tabbatar masa babu komai. "Gobe in sha Allahu zan tafi Abuja. Idan komai ya tafi yadda nake so ba zan wuce kwana biyu ba in sha Allahu." "Kada ka damu. Happy Taj zai tafi kamar kana nan da yardar Allah." "Ba manufata ba kenan" Taj ya faɗi yana sosa ƙeya "dama akan ..." Gira Abba ya ɗage gira "matarka ko? In turo ta ku yi sallama ne?" Da sauri Taj ya koma mota yana ta dariya shi ma Abban ita yake yi. Da gangan dama ya yi tsokanar don kawai ya kawar da damuwar da yake gani a tattare da shi tun a gidansu. Hamdi na jin shigowar Abba ta leƙo yi masa sannu da zuwa. Ya kalleta ya kalli Yaya da ita ma fitowar tayi da sauri. "Suruka da matar Taj jiran me kuke yi min ne?" "Jin inda magana ta kwana mana." Cewar Yaya. Ita kuwa Hamdi wayancewa tayi ta gudu. Ɗakinsu ta koma amma akwai mutane. Sai ta zaga bayan gidan amma bata yi nisa ba. Ta zauna akan wani bulo ko tsoro bata ji ta kira Taj. Murmushi ya yi da call ɗin nata ya shigo. Ko tada motar bai yi ba don ya tsaya duba wani saƙo a waya. Ya bari sai da ta gama ringing sannan ya kirata. "Za mu iya magana yanzu?" Ta furta a hankali bayan ta kuma gaishe shi. "Yes." Raba kanta tayi da dogon tunani ta faɗi abin da ya kamata duk da ba shi bane ranta yake so. "Dama cewa nayi tunda Ya Sajida tayi aure namu ba dole bane ko? Kada ka takura kanka saboda gidanmu." Kamar bai fahimceta ba ya ce "Ban gane ba. Wani abin ne ya faru?" "Uhmmmm. Dama wai ko za ka sakeni" tayi saurin ƙarawa da "tunda ba sona kake ba. In aka ce dole ka zauna dani za a shiga haƙƙinka. Kaga kuma hakan bai dace ba. Ace mun takura maka ta wannan hanyar bayan duk irin taimakon da kake yi mana." Wannan yarinya da abin dariya take ya ayyana a zuci. Ji yadda take zuba zance kamar wadda ake karantowa. Ita kuma kasa jurewa shirun nasa tayi ta ce "Baka ce komai ba." "To me zan ce? Naga kin gama yanke hukunci ke kaɗai." Haƙuri tayi saurin bashi. Sam bata so ta ɓata masa rai kada ya yi amfani da hakan a kanta. "Wai dama tunda ba so ka ke ba..." "Ni yaushe mu ka yi maganar nan dake har nace bana so?" Gabanta ne ya faɗi. Kada fa yaƙi amincewa. "Rannan ɗin nannnn. Ka tuna? Da nayi maka rashin kunya ka ce ai ba sona kake baaa." Ta marairaice masa. "Anya kuwa nine? Ban tuna ba Hamdi." Ya danne dariyar da yake son yi. "Allah kuwa ba ƙarya nake ba." Muryarta yaji ta fara rawa. "Yanzu dai so kike a raba auren?" "Eh." "Amma bai yi wuri ba? Kada sunanki ya ɓaci a gari." "Kaga bamu zauna tare ba. Ko mun rabu babu mai cewa don nayi wani abu ne. Za ma a fahimta sosai." "Tun yaushe ki ka fara wannan tunanin?" Hamdi ta fara murnar jin muryarsa a sake. "Tun yamma. Wallahi har ciwon kai da zazzaɓi sai da su ka kamani saboda neman mafita...au...saboda nema maka mafita. Bana son mutum ya takura saboda ni." 'Zan yi maganinki' Lokaci ya duba a wayarsa. Tara da arba'in da biyu. "Yaya jikin naki? In ba a rufe muku gida ba ki ɗan fito mana." Sai kuma taji faɗuwar gaba "takardar za ka bani?" "Ina jiranki" kawai ya ce. Da sanɗa ta fito tayi sa'a ƙofar soronsu mai ƙara idan an turata a buɗe take har yanzu. Ƙofar gidan ta buɗe tana sako ƙafa su ka kusa karo da Taj. Baya tayi za ta faɗi ya yi saurin riƙo kafaɗunta. Ita da shi duka wani sabon al'amari ya baƙuncesu lokaci guda. Sai da ta daidaita tsayuwarta ya ce, "Sannu." Ta amsa da ka. Yawun bakinta ne a bushe. Tana tare da fargabar ko har ta saku. Bata yi aune ba taji hannun Taj a goshinta. "Mene ne?" "Zazzaɓin nake son ji. Da alama akwai saura. Zo mu je asibiti." "Na'am?" Ta waro masa idanunta. Wayarsa ya ɗago "bari na kira Abba na faɗa masa za mu fita." "Dani ɗin?" Ta ce a gigice. Idanunta sun soma raina fata. "Idan dare ya ƙara yi kafin mu dawo sai su rufe gidan kawai. Sai mu wuce gida mu kwana." Hanjin cikinta ya wani cure waje guda don tsoro "Wai da ni?" "Kada ki damu. Zai fahimta. Mata ta ce so babu wani abu" ya bata amsa kai tsaye. "Don Allah kayi haƙuri." "Ban yi wasa da ciwon wanda bashi da kusanci dani ba ballantana kuma naki." "Na warke tun da rana." Taj ya ƙanƙance ido "ki ka ce kuma da yamma." Da sauri ta ce "Eh, da yamman nake nufi. Kafin rana tayi sanyi." "Hamdiyya kenan. In tambayeki mana." "Ina ji." "Kina so na?" Tsareta yayi da kallo. Ta sunkuyar da kai. "Kada ki cuci kanki. Da amsarki zan yi amfani." "Ba za ka ji haushi ba?" Taj ya yi murmushi "ko kusa." "Zan fi so mu rabu." "Ban yi miki ba kenan?" Yau acting kamar daraktan kannywood ya bata training, ta marairaice masa. "A'a, ba haka nake nufi ba. Naga kamar bamu dace ba. Ka fi ƙarfin ƴar talakawa iri na." "Zan sanar da Abba duk yadda mu ka yi...." "Wane Abban? Nawa?" Ta ɗaga murya fiye da yadda ta soma magana saboda tsoro. "Kinsan ina girmama shi sosai. Ba zan yi komai ba tare da shawartarsa ba." Ganin zai ɓallo mata ruwa ba shiri ta ce "to a bar zancen nan don Allah." "Kin fasa karɓar takardar?" Ta sha kunu "na fasa." "Za mu je asibitin?" Ya kanne mata ido. Murguɗa masa baki tayi "na ma zama abar tsokana ko?" Ya rasa me yasa komai tayi yake burge shi. Wannan tsiwar ma da ba don dare ba da zai yi ta zurma ta ne tana yi masa. "Gobe zan yi tafiya. Ki min addu'a don Allah." "Allah Ya tsare hanya" ta furta kamar an matse bakin. "Baki roƙa min samun nasarar abin da zai kai ni ba." "Me zai kai ka?" "Maganar aurena da wata ƙanwata. Tunda ke ba sona kike ba gara na kawo wadda za ta so ni, nima na so ta." Yana kallon yadda fuskarta ta haɗe kamar hadari. Ya gimtse harda yi mata sai da safe ya wuce. A mota ta sami damar yin murmushi mai haɗe da dariya. Ya gama ganota. Tana so tana kaiwa kasuwa. Birkita mata lissafi kawai zai yi ta haƙura don kanta ta karɓi zuciyar da ya jima da miƙa mata. A nata ɓangaren tana shiga gida ta sauke ajiyar zuciya. Wato da ya miƙo takardar da take barazanar nema anya za ta iya karɓa kuwa? Ita kaɗai ta dinga saƙe saƙe. Sai kuma ta kama murmushi da ta tuna maganganunsu. Ko ba a faɗa ba ta san tsokana ce da shi. A ƙarshe dai ta gaji da kokawa da zuciyarta ta amince za ta bashi dama. She will give this pure feeling she has for him a chance. Ƙofar ɗakinsu ta kama za ta buɗe taji kira daga Abba. Soro ya ja hannunta su ka koma don a nan ne kawai ya san babu kunnen da zai ji su. Ya gama ninke Yaya ya nuna mata babu matsala don ta kwantar da hankalinta. Tsoron da yaji yanzu shi ne na ganin dawowar Hamdi daga wajen Taj. Idan ya bari alaƙarsu tayi nisa ƴarsa zai bari da jidali. Ya rasa abin yi sama da faɗa mata halin da ake ciki. Cikin hikima ya bata labarin Taj tun daga farko har zuwa aurensu. Taji wani irin tausayinsa da kwaɗayin ya daidaita da babansa. Hankalinta bai ƙarasa tashi ba sai da Abba ya faɗa mata tsakaninsa da Alh. Hayatu da yadda aka yi aurensu. Da kuma sharaɗin da ya gindaya masa. "Ko mahaifiyarku ban sanarwa gaskiya ba. Shi kuma Taj nayi imanin ba zai taɓa sakinki ba idan yaji daga ina umarnin ya fito. Zaɓi ɗaya ya rage min..." Kuka take a lokacin ta ce "mene ne Abba? Me za mu yi?" "Ki nuna masa na kya sonsa. Na tabbatar idan yayi tunanin da gaske kike zai sauwaƙe miki. Ni kuma zan baki goyon baya. In ta kama sai ya fita daga rayuwarmu bakiɗaya ya sami salama." "Abba kada ka saka kanka a ciki. Yanzu banda ƴan uwansa kana cikin waɗanda yake yiwa kallon uba. Ya ma faɗa min. Idan ka juya masa baya it will break his heart." "Ki yafe min Hamdiyya. Koma mene ne ni na cuceku. Rayuwa tana gaba amma kullum ana yanke muku hukunci da abin da na shuka a baya." Zuciyarta rauni tayi mara misaltuwa. Bayan shuɗewar lokaci tana gudun mahaifinta yau da kanta ta rungume shi tana kuka. Shi kaɗai yake ta haɗiyar abubuwa domin farincikinsu amma kullum ƙorafi take yi. "Abba ka yafe min nima. Ba zan ƙara faɗin aibun sana'arka ba. Kuma in sha Allahu babu mai jin zancen nan. Zan yi ƙoƙari in ga ya haƙura da auren da kansa." "Allah Ya yi miki albarka. Allah Ya bamu ikon sakawa Taj da abin da yafi buƙata a rayuwarsa wato albarkar duka iyayensa." Amin ɗin a zuci ta iya faɗinta. Ta shige ɗaki ta kwanta tana zubar da hawayen damuwar da tafi ƙarfin shekarunta RAYUWA DA GIƁI 19 Batul Mamman💖 *** Bayan sallar asuba Taj ya kira Kamal domin su yi sallama. Jiya basu sami haɗuwa a gida ba. Ya yi ta waya shiru Kamal ɗin bai ɗauka ba. Wanka ya yi ya gama shiri da sauri ya sake duba wayar. Abin mamaki Kamal bai bi kiran nasa ba. Da wahala hakan ke faruwa. Jikinsa sai ya bashi ko ba ƙalau ba. Abba ƙaninsa ya kira ko tunawa da lokaci bai yi ba. "Happiness ya fito sallar asuba kuwa?" Abba ya ɗan wartsake idanu "ya fito amma yau ya riga kowa baro masallacin. Saƙo ne?" "Ɗan leƙa min shi please." Abba baya son fita don bacci ne sosai a idonsa ya ce "Ya Taj ya dai kamata ku rage wayar asubar nan. Kai kayi aure, idan shi ma ya yi wallahi za ku dinga samun matsala da matanku." "Za ka tashi ko kuwa?" Taj ya ɗan ɗaga murya da ƙoƙarinsa na ɓoye yadda ya damu. Yana jin ƙunƙunin Abba har ya isa ƙofar ɗakin Kamal. Sallama ya haɗa da ƙwanƙwasawa. Da ƙyar Kamal ya iya buɗe jajayen idanunsa da su ka kumbura kamar wanda ya kwana yana kuka. Jikinsa gabaɗaya ciwo yake yi. Kansa kamar ana sara guduma saboda azabar ciwo. "Waye?" Muryarsa ta fito a dusashe. "Ya Taj ke nemanka." Abba ya faɗa yana saita bakinsa da ƙofar yadda za a ji da kyau "na sanar dashi. Can I go back to bed now?" "Thanks" Taj ya ce da kulawa. Wayar Kamal ya sake nema. Yadda yaji muryarsa ya tayar masa da hankali. Amma Kamal ɗin ya tabbatar masa da mura ce ta kama shi da zazzaɓi. "Allah Ya ƙara sauƙi. Ko na bar tafiyar yau muje asibiti?" Hamdi ce ta faɗo masa ya yi murmushi. "Ka tafi kafin Amma ta sauka a garin nan duk mu shiga tara." "Don Allah ka je asibiti dai. Bana so ana raina mura da zazzaɓi. Ciwukan gaske ne." "To doctor." Kamal ya zolaye shi. Suna gama wayar ya ɗauki ƴar jakarsa ta goyo (backpack) wadda ya sanya duka abubuwan buƙatarsa a ciki. Ƙananan kaya ya saka ya koma matashi sosai. Haramar tafiya ya yi sai ya tuna yadda Kamal ya damu kada Ahmad yaji babu daɗi akan halin da Salwa ke ciki. Lokaci ya duba akwai đan saura. Ya fito falo ya kira wayar Ahmad ɗin. "Yaya na shirya zan tafi." Ahmad ya miƙe da sauri. Dama bai koma bacci ba tun sallar asuba. "Bari na zo na kai ka airport." "Ka barshi. Zan sami adaidaita sahu." Fitowa Ahmad ɗin ya yi. Su ka gaisa sannan ya miƙa masa key ɗin motar Kamal. "Incase ban sami dawowa akan lokaci ba, ina sa rai jibi motata za ta iso. In bawa mutumin numbarka sai ya kawota nan ya ajiye?" "Da ina zai kai?" Cewar Ahmad yana zura muƙullin a aljihun wando. Zama Taj ya yi ya buƙaci yin magana da shi na mintuna kaɗan. "Yaya akan Salwa ne." Ahmad ya ɗan ɓata rai "ka cire lamarin yarinyar nan daga gabanka ka fuskanci matsalolinka." "A'a Yaya. Idan da kara nima ƙanwata ce. Ba kuma zan so ta shiga irin wannan yanayin akan wani ba." "Shin ka taɓa yi mata magana ko nuna mata alamun soyayya ne?" Ya kaɗa kai da sauri "a'a." "To ka gani. Rigima ce kawai irin ta ta. Tun abin nata bai yi nisa ba na bata shawara taƙi ji. Ya take so ayi mata? Ana forcing soyayya ne?" Taj dai duk nauyin yayan nasa yake ji. Sai yanzu ya gane manufar Kamal. "Duk da haka ni dai ka rarrasheta. Allah Ya bata wanda ya fini. Mafi alkhairi." "Kada ka damu. Dama a gidansu babanta ya yi mata miji. Amma kaga don fitina taƙi komawa gida. Wai tana jiran service kuma." Dariya su ka yi su biyun. Ahmad ya kwantar masa da hankali. Da ace soyayya su ke yi yanzu ya gujeta shi ne zai zama rashin kyautawa. Amma tunda hakan bata taɓa faruwa ba babu mai ɗora masa laifi. Ahmad ya sako jallabiya ya kai shi airport tunda jirgin sassafe zai bi. * Yadda Amma taga rana jiya haka taga dare. Wajajen ƙarfe biyar ta sami labarin auren Taj daga wajen matar ɗaya daga cikin ƴan uwanta. Ba don shekaru ba da tabbas ƙaryata ta za ta yi. Ta dai daure su ka gama wayar. Yaya Babba ta fara kira ya ce mata haka ne. Ji tayi tamkar an kwaɗa mata guduma. Taj ya yi aure bata sani ba. Kuma har dare bai kira ba. Haka ta ƙarasa wunin ranar cike da fargabar kada mutan gidan su ji. Da taga Allah Ya taimaketa har bayan Isha babu wanda ya ce komai shi ne Daddy na gama cin abinci ta ce masa tana son zuwa Kano gobe. Kamar Anti jira take ta shigo falon a lokacin "Hummm, Maman Ihsan kenan. Kin gaji da ɓoye ɓoyen?" Gabanta faɗuwa ya yi amma ta dake. "Ɓoyo kuma? Wani abin ne ya faru?" "Kada ki raina min hankali mana. Za ki ce ba da saninki Taj ya yi aure bane? Ko kin zata bamu sani ba?" Anti ta faɗi da matuƙar ɓacin rai. Taci burin suruka da shi saboda ya haɗa dukkan abin so. Kyau, kuɗi, suna da kuma kyawawan ɗabi'u. Idan Anisa ta sami miji irinsa ta wuce raini a wurin kowa. A dangi ma sai an dinga bata girma na musamman. "Yadda ki ka ji maganar nan nima haka na ji ta. Kuma dalilinta nake son zuwa Kanon ma kenan. Babu wanda ya neme ni. Sai aure kawai naji." "Ai in duk jikina kunne ne ni ba zan yarda ba. Yaudara ce dai an yiwa ƴata." Ran Amma ya soma ɓaci ta ce "Ita Anisan ce ta ce ya yaudare ta?" Hankali kwance Daddy ya gama cin abincinsa sannan ya tsawatar musu. "Idan kuma ban isa daku ba sai ku fita ku ƙarasa." Amma kwantar da murya tayi ta bashi haƙuri sannan tayi masa bayanin rashin sanin auren. "Idan haka ne kuwa kema bai mutuntaki ba. Kuma ya nuna bai san alkhairi ba." Wani irin kallo Amma ta yiwa Anti. Bata son cigaba da rigima a daren nan amma take taken Antin so ta a cigaba da maganar har Hajja ta ji. Daddy sallamarsu ya yi akan su bar zancen zuwa washegari. Anti na fita ta koma ɗakinta inda ta sami Anisa a zaune da waya a hannu. Zuciya ta raya mata Taj take kira ƙila yaƙi ɗauka. Ai kuwa ta tashi ta nufi ɗakin Hajja tana kuka ta karanta mata ƙarya da gaskiya. Wani abin idan ta faɗa sai Anisa ta riƙe baki don mamakin yadda uwa take yanko ƙarya bisa son zuciya. "Damuwata yanzu yadda ta saka shi a ranta." "Anti don Allah ki daina kuka. Ni wallahi na haƙura." "Ai ba ke ki ka ce kina son sa ba tun farko balle haƙuri ko rashinsa ya zama a hannunki." Hajja ta faɗi cikin fushi tana duban Anisa "har ni Jamila za ta yiwa haka? Maza kirawo min ita." Cin mutumci babu irin wanda Hajja bata yiwa Amma ba. Da Daddy ya shigar mata shi ma ta haɗa dashi ta ƙare musu tas. Yau har gorin haihuwa biyu kacal sai da aka yi mata. "Saboda shegen son kuɗi da koyi da rayuwar nasara ki ka tsayar da ƙwayayen haihuwarki. Gashi nan wanda ki ka ɗauko a dangin ya nuna miki shi ba ɗan goyo bane. Don na tabbata da sahalewar ubansa ya yi auren." Allah Yasa ita ɗin ma ba ƙyalle bace. Da maganganun su ka isheta fita tayi daga ɗakin. Hajja ta ce dama ta rainasu daga ita har mijin. Banda haka bai kamata tana yi mata magana ta fita ba. A wannan halin dai aka kwana ranar. Gidan duka babu daɗi. Anisa kanta ta sha kuka saboda ta dogara da cewa ko don alkunyar abin da gidansu su ka yiwa Taj, ba zai taɓa tsallake aurenta ba. Shi yasa da baya yi mata zancen soyayya bata wani damu ba. Aure ne dai za ayi kamar yadda Hajja ta alƙawarta mata. Da safe ma gidan babu wata walwala. Kowa kai kawo yake kamar ana tura shi. Ga tafiya Kanon da Amma ta so yi Hajja ta hana Daddy yi mata izini. * Taxi Taj ya shiga har gidan. Maigadi ya riga ya san shi saboda haka ba a tsaya sanar da mutanen ciki ba ya buɗe masa gate. Agogo ya kalla da ya isa ƙofar shiga gidan. Goma da rabi ta ɗan wuce. Sanin ba Amma bace kaɗai a ciki dole ya sanar da zuwansa don ayi masa izinin shiga. Wayarta ya kira tana gani ta taɓe baki, ɓacin ranta ya dawo sabo. Har kiran ya katse bata ɗauka ba. Ya kira yafi sau shida kafin ta daure ta amsa. "Ina jin ka." Ta ce a kausashe duk da wani ɓangare na zuciyarta yaji daɗi. Ta tabbata tana ransa tunda ya yi asubancin zuwa gareta. Ya san za a rina. Ya kwantar da kai ya faɗa mata yana bakin ƙofa. "Yau kuma gidan sirikinka ne da ba za ka shigo ba?" "A'a, dama saboda naga safiya ce..." "Bana son gulma. Shigo ina falona." "Tuba nake Amma." Ya faɗi yana buɗe ƙofar. Abin da ya guda ne ya faru. Anisa da ƙannenta duka ya samu a falon suna breakfast kowacce da kayan bacci. Ba abin ya koma ba ya riga ya sako kai. Ɗauke ido ya yi daga kallonsu ya yi musu sallama. Aka rasa mai amsawa don kishi su ke taya yayarsu, sai ita Anisan. Mai binta ta banka mata harara. Ƙaramar kuma ta ja dogon tsaki. "Aikin banza." Ko kallonsu bai yi ba ya wuce falon Amma. Uzurin ƙuruciya ya yi musu kawai. Kuma dai abin kunya ne ya biye musu. Yana ji suna ta tsaki. Ita kuma Anisa tana yi musu faɗan basu kyauta ba. Yana wucewa su ka yi rige rigen sanarwa Hajja da Anti zuwansa. A zaune ya tarar da Amma. Ita ma ko wanka bata yi ba. Komai nata a hargitse saboda rashin kwanciyar hankali. Jikinsa a sanyaye ya ajiye jakarsa a ƙasa ya zauna a gaban ƙafafunta. "Don Girman Allah Amma ki yi haƙuri. Wallahi ba da gangan nayi ba." Rai na ƙuna ta ce "Kayi ne saboda ka nuna min irin nawa matsayin a wajenka?" "Ban isa ba wallahi. A gaggauce komai ya faru." "Bayan ya faru ɗin kuma sai ka manta sunan da ka sanya min a wayarka balle ka kira ko? Haba Taj. Aure fa kayi. Nayi zaton ina sahun gaba cikin waɗanda ya kamata su sani ko da wacce irin gaggawa ya zo maka." Shi ma ya san bai kyauta ba. A daren da Alhaji ya yi masa izinin auren ya dace ya gaggauta kiranta. Sai gargaɗin Alhajin ya tsaya masa a rai. Shi ya hana shi faɗawa su Inna. Idan ya kira Amma ya tabbata sai ta faɗawa su Inna. Ita ɗin sam bata tsoron Alhaji. Akan Taj ma sai ta ƙure take yi masa magana. Gudun kada ta ɓallo masa ruwa yasa shi kama bakin nasa. Bai ƙara tunawa ba kuma sai bayan sun kama hanyar gida da Kamal. Duka wannan bayanin babu lallai ita ko wani ya đauke shi a matsayin uzuri. Kawai ya yarda bai kyauta ba, ya bata haƙuri shi ne mafi a'ala. "Don Allah ki yafe min. Ki kuma saurari bayani na ko da ba zai gamsar dake ba." "Baka da abin da za ka faɗa min Taj. Ka koma gaban iyayenka tunda dama na san burinka kenan. A nawa tunanin dai ko me zai faru ba za ka manta dani ba." Tayi maganar da ƙwalla a idanunta. "Har yanzu Alhaji bai sakko ba. Su Hajiya ma basu san da auren ba sai bayan an ɗaura. Ke kuma gani nayi bai dace ba ace ta waya na fađa miki." "Ban yi fushi ba. Ka dai koma Kanon tunda ka zama mijin aure. Allah Ya baku zaman lafiya." Ta miƙe. "Amma ki yafe min mana don Allah." "Ai nace raina bai ɓaci ba. In an tashi bikin ka daure dai ka faɗawa ƴan uwanka su Ihsan." Da yaga dai rarrashin ba zai yiwu ba sai ya marairaice mata. "Amma na baki haƙuri kin ƙi. Ina son yi miki bayanin yadda auren ya zo ma ba ki son ji. So ki ke dole ki nuna min ni ba ɗanki bane. Banda haka ai ko gudun kada auren yaƙi albarka za ki sassauta min." Hawaye yaga ta goge, ta kalle shi a raunane ya cigaba da magana "haihuwata ce fa kawai baki yi ba amma ina ji a jikina ko tsine min ki ka yi sai ta bi ni." "Tsinuwar lafiya Taj? Kada na kuma jin wannan kalmar a bakinka." Ya sake kwantar da murya "To ya kike so nayi? Fushinki ba zai barni naga hasken rayuwa ba." "Allah Ya tsareka Taj. Zauna mu yi magana" ta ce a rikice. Bata son ganinsa a yanayi irin wannan ko kaɗan. Daga bayansu su ka ji muryar Hajja da basu san tun yaushe take tsaye a bakin ƙofar ba tana cewa. "Shegen baki kamar rainon cikin gari. Na rasa me yasa ba a taɓa cin galabarka a magana." Ta nuna Amma "ke kuma da ya soma kalallameki sai ki bada kai bori ya hau. Da ɗan cikinki ne ya yi min haka wallahi ba zan masa da sauƙi ba. Ɗan riƙo dama ai ba ɗan goyo ba. Kayan aro bai taɓa rufe katara." Bayan Hajja ashe harda Anti da su Anisa. Daddy ne kaɗai basu iya zuwa kai wa rahoton zuwan Taj ba. 'Duk zan iya da ku' Taj ya faɗi a ransa. Ya je bakin ƙofar ya riƙo hannun Hajja ya zo ya zaunar da ita. "Na ɗauka ko me zai same ni a waje idan na shigo gidan nan Hajja zan sami kwanciyar hankali. A wurin ɗanki na sami baban da bai taɓa ƙyamar sana'ata ko goranta min don mahaifina ya kore ni ba." "Shi ne ka kasa yi masa alfarmar auren ƴarsa ba. Ko don ba Jamila ta haifeta ba?" Taj ya girgiza kai "kinga inda matsalar take ko? Komai nayi sai kun fassara saboda baku ɗaukeni ɗa ba. Da ace Daddy ne ya haifeni hukunci kawai za ku yi min da faɗa akan laifina na. Ba sai anyi ta zancen asalina ba." Duk fushin Hajja bata san lokacin da tayi murmushi ba "Tajo kenan. Wannan baki dai ba na ubanka bane. Shi banda haɗe rai bai iya komai." "Baki taɓa zuwa bayan magariba bane. Da har dariyar Alhajinmu sai kin ji." "Wa yaga tarangahoma. Dariyar Hayatu ai tsorata mutane za ta yi." Taj ya yi murmushi "wallahi Hajja ke kaɗai za ki taɓa min tsohona in share saboda kin isa. Kaka na ɗauke ki ba surukar Amma ba." Kwashewa tayi da dariya. Ta bar Anti da Amma da mamaki. "Ɗan duniya. To ka gama kalallame mu. Sai ka faɗa min inda maganar ƙanwarka ta kwana tunda naji ance mahaifin amaryar ɗan daudu ne." A take fuskarsa ta canja da furucin Hajja. Ta kalli Amma da mamakinta ya fi na Anti. "Kada ku ce min baku san ɗan daudu bane baban nata?" Amma ta kalli Taj tana neman ƙarin bayani a tsorace. Ɓoye ɓoye dama can ba halinsa bane. Balle kuma yanzu da ya riga ya yi aure. In ya rufe yau anjima ko gobe magana za ta fito. Saboda haka a taƙaice ya labarta musu yana aiki da Abba da kuma abin da ya faru lokacin auren Sajida har zuwa jiyan. "A taƙaice dai ba auren soyayya bane. Yarinya mai asali girɓatacce irin wannan dama sai dai auren alfarma." Cewar Anti. Hajja kuwa cewa tayi "kakarta ce kawai ta yanke saƙa. Wannan kishi da ita ma ɓata lokaci ne Anisa. Kawai ki sa a ranki ke kaɗai ce." "A'a fa Hajja" Taj ya katse musu hanzari kafin a kai matakin da zai faɗi baƙa. "A'a me?" "Ina sonta." "Taj" Amma ta kira shi don ta san hali. "Am serious Amma. Ina roƙonku don Allah kada a sake tada zancen mahaifinta ko yanayin auren. Nema nayi ba bani aka yi ba. Please" ya kallesu ɗaya bayan ɗaya. For once sai jikin Hajja ya yi sanyi. Magiya Taj yake amma irin wadda mai yinta yake fata da tsananin burin samun biyan buƙata. Tashi Hajja tayi ba tare da tayi magana ba. Ta dai ƙarewa Taj kallo sai taji babu adalci idan ta cigaba da sanya shi a kwana. "Ina ɗan uwanka Kamalu" Taj ya dubeta girarsa a cure "yana gida." "Idan ka koma ka ce ina nemansa. Shi sai ya zo su daidaita da Anisa idan bashi da wata." "Hajja!!!" Anisa, Taj da Anti su ka kirata lokaci guda. Ta taɓe baki. "Ku bar Hayatu da halinsa. Ban taɓa ganin wanda Allah Ya azurta da iyali masu kyakkyawar mu'amala da ɗabi'a kamar nasa ba. Shi yasa nake kwaɗayin haɗa zuri'a dashi ba wani abu ba." Bata jira jin me za su ce ba ta fita. Anti ma fita tayi da niyyar yiwa Daddy magana. Bata maraba da tumbling ɗin ƴarta da Hajja take yi. Ita ma Anisa bayansu ta bi. Sai dai kafin ta fita ta tsaya tayi masa magana. "Allah Ya sanya alkhairi Ya Taj." "Nagode Anisa. Kuma don Allah kada ya zama reason na lalacewar zumuncinmu." "Tun farko dama kayi min bayani. Babu wani abu. Sai mun zo ganin amarya." Da ya rage su biyu a falon Taj ya kalli Amma "that went well right?" "I think so." Ta bashi amsa da fatan hakan ne. Breakfast ta kawo musu. Bayan sun gama ya faɗa mata komai ds komai da ya danganci Abba da aurensa. "Yaron nan da a ɗan daba ka tashi sai an wahala da kai. Banda rigima ka rasa ƴar wanda za ka auro sai Simagade? Kai yanzu ka yarda Yaya Hayatu ba zai kawo matsala a gaba ba?" "Da Allah na dogara Amma. Bana son yin wannan tunanin saboda ban hango abin da zai rabani da Hamdi ba." "Sunanta ya min daɗi fa. Hamdiyya. Ɗazu da ka faɗa har zan magana na kama bakina kafin Hajja ta zageni." Cikin farincikin shiryawa da Amma ya bar gidan da yamma. Ta so ya kwana amma ya dage gara yaje hotel. Zaman nasa a ganinsa tamkar rashin kunya ne. Zai kyautu ya bawa mutanen gidan damar sake karɓarsa idan ciwon abin da su ke tunanin laifi ne ya ragu. *** A yau sha'anin biki ya ƙare. Kakan Safwan ya wakilta masu ɗauko amarya Sajida zuwa gidansa. Dama Umman Safwan ɗin bata da damuwa ko kaɗan. Babansa ne baya so. Bayan koke koken amarya da ƴan uwanta da kuma Yaya, gidan kakannin Safwan aka wuce da ita. Tsohon nan ya yi musu nasiha sosai da jan kunne. "Sai kun ji kon ƙi ji. Ku gani kuma ku ƙi gani sannan auren zai yi ƙarko. Musamman gareki jikata" Sajida ta kalle shi da jan ido "duk wanda ya sami dama a dangin nan zai faɗa miki magana son rai akan asalinki. Wannan ko ka hana wani sai ya yi. Saboda haka ki koyi kawar da kai. Inda ba za ki iya ba kuma ki kare martabar mahaifinki. Ina mai tabbatar miki da an kwana biyu zai bi jiki. Kowa zai haƙura matuƙar kun zauna lafiya. Kun bawa maraɗa kunya." Safwan ne kaɗai ya iya yi masa godiya. Sajida kuwa in banda sharar hawaye babu abin da take yi. * Ana can ana ƙarasa guntattakin gyara a gidan amarya Zee ta fice daga ɗakin da Hamdi take yiwa turaren wuta ta koma wajen gate ta kira Taj. Yamma ce liƙis. Tana ta addu'ar samunsa a wayar. Tayi sa'a kuwa bugun farko ya ɗauka. Sai kuma ya kashe ya kirata. "Zee amarya." Sake tsokanarta ya yi "to uwargida. Tun yanzu har an fara kishi kenan." "Don Allah ka bari" Yanayin muryarta ba yadda ya saba ji bane. Shi yasa bai ja wasan ba ya nemi ta sanar dashi dalilin kiran. Muryarta rawa ta fara, sai kuma ta kama kuka. A haka ta faɗa masa maganganun da taji Abba yana faɗawa Hamdi jiya ba tare da sun san ta biyo su ba. Ashe tun shigowar Hamdi cikin gidan ta taso za ta tsokaneta akan me taje yi a waje sai taga Abba ya ja ta zuwa soro. Fuskarsa da ta gani da damuwa ita tayi sanadin binsu da tayi. Tana gama jin abin da ya ce tayi saurin komawa ciki. Jijiyar kansa tashi tayi sosai. Ɓacin rai ya rufar masa. Ya rasa dalilin da yasa Alhaji yake yi masa haka. "Ya Taj don Allah ka saketa ba sai tayi maka abin da zai ɓatawa Abbs suna ba." "Yi shiru Zee. Maganar nan da wa kika yi bayan ni?" "Babu kowa." Ta ja hanci. "To don Allah ki yi min alƙawarin riƙeta a ranki kin ji." "Sakin fa?" "Hamdi ta zo kenan. Idan ku ka yi wasa ma duk sai ta riga ku haihuwa." Wayar ta cire daga kunnenta saboda kunyar kalamansa. Kamar ya sani ya ce "Oh sorry, ƙanwa ce fa ke." "Idan tayi maka laifin da zai sa ka saketa fa?" "Kada ki damu. Just focus on yourself. Ki gama karatunki ki kuma riƙe mutumcin aurenki. Ni da Hamdi in sha Allah anyi auren kenan." "Tsoro nake ji kada babanka ya yiwa Abba wani abu." "In sha Allah babu abin da zai faru. Ina son sister ɗinki. Zan kuma tsare mutumcinta da na duka family ɗinku." Ya ɗauki lokaci sosai wajen kwantar mata da hankali. Sannan ya yi mata godiya da ta tunkare shi da zancen. Wayar Kamal ya nema da su ka gama don ya faɗa masa yaji a kashe. Ya yi ɗan tsaki. Tun asuba fa Kamal ba yadda ya saba yake ba. Komai daina yi masa daɗi yake saboda yana jin tamkar wani ɓangare na jikinsa baya tare dashi. Jirgin tara na safe ya yi booking ta waya kafin ya kwanta. *** Hannuwa da ƙafafunsa ya kalla hankalinsa ya sake tashi. A kumbure suke. Fuskarsa kuwa kamar an hura balloon. Magungunan jiya ya ɗauko yayi ta dubawa ko akwai wanda ya sha ba daidai ba amma babu. Gabansa ya dinga faɗuwa da tunanin me zai faru idan yanayinsa ya cigaba a haka. Babbar matsalarsa ma ita ce yadda zai samu ya bar gidan ba tare da kowa ya gan shi ba. Daga daren jiya zuwa yanzu ya fita hayyacinsa baki ɗaya. Wayarsa ya nema ya kunna domin magana da likitarsa sai yaji ana taɓa ƙofar ɗakinsa. Hankalinsa ya sake tashi da ya kalli kansa a madubi. "Waye?" Ya furta da ɗan ƙarfi. Shiru yaji babu amsa. Sai zura muƙullai da ake tayi a ƙofar. A gwaji na biyar aka buɗe ƙofar ɗakin wanda bai taɓa zaton akwai spare key ba. Idanunsa da ƙyar su ke buɗuwa saboda hasken fitilun waje da su ka shigo. "Abba? Bishir?" Fitilar ɗakinsa aka kunna gami da rufe ƙofar ɗakin nasa. "Kamal? Shaye shaye kake yi?" A gigice ya ɗago idanunsa da suke buɗewa da ƙyar saboda kumburi ya kalli wadda ke tsaye a kansa. "Umma?"= RAYUWA DA GIƁI 20 Batul Mamman💖 _Gaisuwa ta musamman ga baiwar Allah da ta tura saƙo OpenDiaries. Ina fata kin sami sauƙi. Allah Ya inganta Ya raba lafiya. Abba Habibu Simagade yace a baki haƙuri ba niyyarsa kenan ba. Shafin yau naki ne._ Ina ƙara tunatar da masu karatu posts weekdays ne kawai don Allah. Nagode sosai. SonSo *** Na ɗan taƙin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta so ƙullewa har ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba. Cikin sa'a sai ya tuno abin da ya tanadi faɗawa duk wanda ya ganshi a wannan yanayin. Murmushi ya yi mata sannan ya ɗaga hannuwa da ƙafafunsa yadda za ta gansu sosai. "Mene ne wannan Kamal? Me ya same ka kake irin wannan kumburin?" Ta ƙarasa inda yake tana tattaɓa shi. "Allergy ne Umma. A haka ma kumburin ya sauka sosai." "Subhanallahi" ta matsa hannunsa na dama "akwai zafi?" Kai ya girgiza mata. Ya zauna ya shirga mata bayanin ƙanzon kurege wai allergy gare shi kuma har yanzu likitan bai gano mene ne jikin nasa baya so ba. "Anya ya san aikinsa kuwa? Me yasa baka je wurin yayarka ba?" Gaban Kamal ya faɗi da tsoron kada Umma ta matsa masa akan zuwa wajen Yaya Kubra. Ita ce babba wajen Mama kuma sananniyar likitar ɓangaren lalurorin mata. Yana zuwa wajenta asirinsa zai tono. "Ita da take gynae? Wannan ba ɓangarenta bane." "Amma ai ba za ta kasa sanin likitan da ya dace da kai ba a asibitin Malam (AKTHA) ko? Ni dai bari nayi mata waya. Wannan kumburin ya bani tsoro. Har wani baƙi naga kayi." "Kai Umma, idonki ne." Ya wayance. Da ƙyar ya hanata kiran yayar tasu. Ya tabbatar mata likitan da yake gani ma ƙwararre ne. Harkar allergy wani zubin sai an wahala kafin a gano mene ne jiki baya so har yake reacting irin haka. Baiwar Allah sai ta yarda da zancen nasa. Ta kira masa Abba ta ce ya zo ya kai shi asibiti. "Amma me ya sa ka ɓoye mana? Jiya ina kallonka kafin ku fita wajen sirikin Taj da Innarku ka shige kitchen ka watsa magani. Kuma yau kowa ya ce bai sanyaka a ido ba. Shi ne tsoro ya kamani. Ko ƙwaya ka fara sha." Halin ciwon da yake ciki bai hana shi dariya ba. "Abin da ban yi da ƙuruciya ba Umma?" "Yo Allah na tuba shaye shaye lokaci gare shi? Kai dai kawai Allah Ya kare ku da sauran zuri'ar musulmi. Zamanin ya zo da hanyoyin ɓata tatbiyar tsofaffi balle kuma matasa masu jini a jika." Tunaninsa na yadda zai je wajen likitarsa cikin sauƙi ya sami solution. Umma ta sa Abba ya kai shi asibitin. A hanya kafin ya ƙarasa ya tura mata saƙo ta bashi amsa. Roƙonta ya yi da sirranta lalurarsa a gaban Abba. Da taimakon Abba ya iya shiga asibitin. Dauriya da ƙarfinsa sun soma ƙarewa. Wata Nos tana ganinsu ta hanzarta kiran likitar wadda dalilinsa ma ta fito don yau ranar hutunta ce. Wata kyakkyawar matashiya ce ta fito sanye da baƙar abaya da ƙaramin hijab. A fuskarta gilashi ne mai ɗan kauri dake taimakawa ganinta. Madaidaicin tsayi gareta amma kuma she is a bit chubby. Sai dai ƙibar ba mai yawa bace. Ɗakin taimakon gaggawa tasa aka shigar mata da Kamal aka kwantar akan gado. Abba ya gama tsorata da yanayinsa. Yana ganin ta farke sirinji cikin sauri ya ce "Doctor kinga jikin nasa duk ya rikice kafin mu ƙaraso. Don Allah ki gane mene ne ba ya so sai mu kiyaye." "Ɗan bamu wuri" ta ce idanunta akan Kamal. Patient ɗinta mai ɗan banzan taurin kai. Hankali a tashe Abba ya fita. Ya shiga fareti a wajen yana addu'ar a shawo kan matsalar da wuri. Yana fita Mubina ta rufe ƙofar emergency ɗin ta shiga bawa Kamal taimakon da ya kamata. Kimanin minti talatin kafin jikin nasa ya fara daidaita. Ya buɗe ido a hankali ya sauka cikin nata. Ranta a ɓace yake sosai. Kallon da tayi masa ya sanya shi murmushi. Ya đaga hannunsa guda ba wanda take yi masa ƙarin ruwa ba ya kama kunnensa. "Sorry." "Ya kake so nayi da kai? Ni a rayuwata babu abin da na tsana kamar ɓoye ɓoye." Ya ɗage gira ɗaya "a taƙaice dai kin tsaneni." Shan kunu tayi "ban ce ba." "Don Allah ki yi haƙuri." Ya tashi zaune "Zan iya tafiya?" "Jikin naka..." Sallama aka yi, kafin ta amsa Alhaji ya turo ƙofar ta buɗe gabaɗaya su ka shigo tare da Abba. Kai idan kaga fuskar shi sai ya baka tsoro. Hannuwan babbar rigarsa sun sauko amma yau ya manta da wani matsayi. Ɗansa kawai yake son gani. "Me ya same ka?" Ya kalli Dr. Mubina "Doctor me ya same shi?" Kamal bai bari tayi magana ba don ya kula ganin Alhaji ya kiɗima ta. "Allergy ne Alhaji." "Kai ne likitan?" Ya sake dubanta idanunsa na daɗa firgita ta "ina jin ki." "Allergy ne kamar yadda ya ce." "To an gano mene ne jikin nasa baya so domin a kiyaye?" "A'a, muna dai kan..." Kafaɗarsa Alhaji ya riƙe "Kai tashi. Visar ina da ina gareka yanzu da ba su ƙare ba?" Mubina taga yadda bakinsa ya kasa tattaro amsa saboda sanin kafiyar Alhajin. "Don Allah ka ɗan ƙara mana lokaci Alhaji. Lifestyle changes muke ta gwadawa. In sha Allah a hankali zamu gane trigger ɗin." "A hankali fa ki ka ce doctor. Jira zan yi har sai wani mummunan abu ya same shi?" "Kayi haƙuri. Rashin bamu dama yana daga cikin abubuwan da ke sa a dinga ganin kamar bamu san aikinmu ba." Yadda ta tare shi kai tsaye ta bashi wannan amsa sai ya sanya shi murmushi. Yana son mutane masu confidence. "Ya sunanki ne?" "Mubina...Mubina Sa'id Kibiya." Fuskar Alhaji washewa tayi. Shi ne harda dariya irin tasu ta manya. "Ikon Allah. Ke ƴar wajen Marigayi Dr. Sa'id ce?" Ta gyaɗa kai a hankali "kai masha Allah. Ƙasar nan ba ƙaramin rashi tayi ba. Arewa tayi rashin jajirtaccen likita. Allah Ya masa rahama." Idanun Mubina da ƴar ƙwalla ta ce "amin." Sakin jiki Alhaji ya yi su ka gama magana ya ce ya bata damar yiwa Kamal dukkan abin da ya dace domin samun sauƙinsa. Ya ƙara da cewa baya so ta sallame shi a yau. A kumbure gaɓoɓinsa su ke duk da a haka Abba ya ce wai ya saɓe. Fita su ka yi da Abban zai raka shi. Kamal kuma Mubina ta ce lallai ya koma ya kwanta. "Ai dole na. Idan na koma gida yau ba za mu ƙare da daɗi ba." "Gaskiya yana son ka." Ta faɗi tana murmushin yadda uban ya nuna kulawarsa akansa. "Ai baki ga komai ba. Sai ƴarsa na labour room ake gane waye Alhaji. Wallahi in dai ba baya gari ba da shi ake zaman asibiti daga lokacin da yaji an tafi haihuwar har a fito da baby." "Kun ji daɗi. Shi ne kake ɓoye masa halin da kake ciki?" "Duk tsaurinsa yana da mugun rauni akan ƴaƴa. Sanin matsalata alhalin babu abin da zai iya yi min damunsa kawai zai yi." Haƙura Mubina tayi. Ta kula da indai izinin Kamal take jira babu wani cigaba da za a samu wajen binciken sama masa waraka. Zaɓi guda ya rage mata. Za kuma tayi amfani dashi in sha Allahu. Bata tashi ƙara sanin wane irin gida ya fito ba sai da taga matan gidansu da ƴan uwansa suna ta tururuwar shigowa. Ɗakin ba ma zai ɗauki rabinsu ba domin kuwa harda jikoki. Wannan yasa ta tunani akan hanyarta ta gida. Yanzu a ce duk yawan nan nasu babu wanda jininsa da na Kamal ya zo daidai? *** Taj bai tashi sanin a asibiti Kamal ya kwana ba sai da safe. Da fari ya yi niyyar komawa gidan Amma domin su gaisa da Daddy. Sai ga wayar Naja tana sanar dashi labarin da ta samu daga gida. Ya duba wayarsa babu wanda ya kira shi. Jinjina kai ya yi ya ɗauki jakarsa ya fita. Allah Ya taimake shi bai haɗu da ɓacin rana ba. Jirgin ya tashi akan lokaci. Kai tsaye asibitin ya wuce daga airport. Ya samu ana ta rikici a bakin ƙofa tsakanin wata nos da ƴan uwansu mata. Ta tare ƙofar ta hana mutum biyar shiga. Na ciki su bakwai su ma tayi tayi sun ƙi fitowa. Ana ƙorafin sun yi yawa a ɗakin, su kuma sun ce babu wanda ya isa yasa su fita daga wajen ɗan uwansu. "Ga wani ma nan ya shigo. Shi daga wani garin ma yake." Autar gidan ta faɗi a tsiwace. "To ko ma dai waye zuwa za ku yi ku fita. Idan ba haka ba zan sanar da na gaba dani. Doka ce ba a son a wuce mutum uku a ɗakin mara lafiya." Nos ɗin ta ce da takaicin waɗannan mutane. Bakiɗayansu kamar masu kan dutse. An rasa mai lallaɓata ta haƙura ko kuma yasa baki su fita. Wata ma cewa tayi "ku sallame shi mana. Muma yayarmu likita ce. Allah na tuba don dai ƙarin ruwa da allura wanne ne ba za ta iya ba?" Ran Nos ɗinnan ya ɓaci matuƙa. Idan an zo ita za a yiwa faɗan barinsu a ɗakin. Da taga Taj ne ma ta ɗan saki rai. Ta san dai duk yadda za ayi namiji daban yake da mata. "Kai ma ɗan gidansu ne?" Caraf wata mai tsohon ciki ta ce "Baki ga kama da mara lafiyan ba?" "Don Allah ka faɗa musu su ragu. A bakin aikina nake. In kowa bai min magana ba wallahi likitarsa sai tayi. Ta ce baya buƙatar hayaniya." "Ya Taj barni da ita. So take ta nuna mana ta fi mu son ɗan uwanmu. Ba fa surutu zamu yi ba." Kamal ba jin an ambaci Taj ya yi hamdala. Shi ma sun ƙi sauraronsa. Kansa har ya fara ciwo. A tunaninsu allergy ɗin ne shi yasa su ka dage. Basu san halin da yake ciki magana ma dauriya kawai yake yi ba. "Happy. Don Allah kasa su bi dokar asibitin. Ni kaina doctor ɗin ba za ta barni ba idan ta gansu." Nos dai tana jin sunan da aka kira Taj daga waje da wanda mara lafiyan nan ya kira shi, bata san lokacin da ta ce "Happy Taj? Kai ne mai HappyTaj don Allah?" Ƴan bani na iyan gidan Alh. Hayatu ne su ka amsa mata. Harda mai cewa da ta ɗauka su ɗin local mutane ne take son wulaƙanta su. "A bakin aikina nake." Ta nanata musu. Da laluma da rarrashi Taj ya samu su ka bi tsarin asibitin. Da mutum bibbiyu aka dinga shiga ana fita. Nos ɗin tayi masa godiya bayan kowa ya tafi ta barshi ya shiga shi kaɗai. Abin mamaki yana zama ya kira sunan Kamal sai yaji shiru. Ɗaga kansa ke da wuya yaga ashe bacci ne ya ɗauke shi. Saurin bacci ba ɗabi'ar Kamal bace. Kuma bai fi minti biyar da raka ƴan uwansa waje ba don ya tabbatar sun tafi. Ya yi tsammanin zai dawo su yi hira ma tunda yaga kamar jikin da sauƙi. Hankalinsa sai bai kwanta ba. Anya allergy ne kawai? To ko kuma allurar bacci aka yi masa? Shi kaɗai ya dinga saƙe saƙe a ransa har Mubina ta shigo. Haɗuwar farko ta jinjinawa soyayyar dake tsakanin ƴan uwan biyu. Lokacin Kamal ya tashi har Taj ya bashi labarin yadda su ka yi a Abuja. Ya ɗora da mitar me yasa ya zama na ƙarshen sanin bashi da lafiya. Cacar bakinsu su ka yi aka daidaita. Sai ga Kamal kamar ba shi ba. Jikinsa ma yayi ƙwari sannan kumburin duk ya sauka. "Zan sallameka amma akwai magunguna da zan sabunta maka. Don Allah kada kayi wasa dasu." Tashi Taj ya yi ya ce "Idan akwai a pharmacy ɗinku ki bani na siyo kafin mu tafi." "A'a ka barshi kawai" in ji Kamal "Ba duka za a samu ba." Ita kuma ta ce da sauri. Murmushi Taj ya yi, amma a zuciyarsa yaji rashin yarda dasu. Zargin nasa bai sami ɗorewa ba da yaga da gaske Mubina wata kulawa ta musamman take bawa Kamal. Daɗi ya kama shi. Wannan karon da alama za a dace, Kamal zai daina gudun matan da yaga yana yi. "Bari na baku wuri ku ƙarasa maganan. Na san ba komai na patient ya kamata wasu su ji ba." "Har akwai abin da ya shafeni wanda bai kamata kaji ba?" Kamal ya faɗi yana ɗauke kai daga hararar da Mubina take masa. "In ta faɗa ka sanar dani. Bari na duba ko Bishir ya zo." Ficewa ya yi ya barsu. Mubina ta sami sakewar ƙara sanar dashi dokokin da ya kamata ya kiyaye. "Me yasa ya fita?" "Ya zata akwai wani abu tsakaninmu. Bai san ni yanzu soyayya ko sadakarta aka bani zan mayarwa mai ita ba." Murmushin zuci kawai Mubina tayi. In zai ɓoyewa kowa ita ba zai yaudareta ba. Tana da saurin karantar mutane. Tun farkon zuwan Kamal asibitin ta fahimci ya kamu da sonta. Sai dai bayan ya gama faɗa mata alamomin ciwonsa da aka yi gwaji ta sanar dashi lalurar shikenan komai nasa ya sauya. Soyayyar da take gani ƙuruƙuru ta koma yaƙin neman lafiya. Da ya gane da wuya lafiyar ta samu sai ya zama mai mugun sadaukarwa ga duk wanda yake mu'amala dasu. Musamman wannan ɗan uwan nasa Taj. A halin da ake ciki za ta cigaba da adana soyayyarta ta mayar da hankali wurin ganin ya sami lafiya. Bata son ta bari komai ya shiga tsakanin aikinta a kan samun sauƙinsa. *** Bayan kwana biyu da sallamar Kamal ya wartsake har ya koma shagonsa. Sai lokacin Taj ya sami sukuni da nutsuwa a ransa. Kullum yana tunanin Hamdi amma damuwar Kamal ta ishe shi. Daɗinsa ɗaya da ya koma gidan Ahmad Salwa ta tafi Bauchi. Hankalinsa kwance ya soma fafutukar neman gida don Inna ta faɗa masa bikinsa ba zai ɗauki lokaci ba. Yawancin fitar da Abba su ke yi ko Bishir. Bai fiye neman Kamal ɗin ba saboda yana ganin hutu ya kamace shi ba taya shi neman gida ba. A cikin kwanakin kullum yana waya da Abba. Abban ya so zuwa duba Kamal amma da ta tuna yadda su ka yi Alhaji sai ya haƙura kawai ya kira shi. Yaya har fushi tayi. Ta nuna masa rashin dacewar hakan. Shi dai haƙuri ya bata da ƴan dabarun wayo har ta daina zancen. Yau alhamis ta kama kwana shida da ɗaurin aurensa. Ya sami sabon gida a sharaɗa self-contain daidai me sabon aure. Mama ce ta bashi shawarar kada ya ce sai ƙaton gida. Gara ya mayar da hankali wajen gina filin da su ka saya shi da Kamal shekara biyu da su ka wuce. Shirye shiryen biki yana ta kankama. Iyayen basu saka rana ba sai sun ci ƙarfin shirinsu. Masu haɗa lefe su Yaya Hajiyayye kuma an taso Taj a gaba ya kawo size ɗin underwear ɗin Hamdi. Ya gama zille zillensa ta biyo shi har office a Happy Taj ta saka shi a gaba. "Kirawota a gabana ka tambaya." "Na ce miki fa zan tambaya yau ɗinnan na turo miki." "Ai na gaji da gafara sa. Kai ko irin abinnan na angwaye da an ɗaura aure su fara damun amarya da fitina da alama baka iya ba" Kunya kamar ya fice ya bar mata office ɗin. "Haba Yaya Hajiyayye. Sai kace wani ɗan is**. Kunyarki ma ta kama ni." Dariya tayi sannan ta ce "Ka kira yanzu nima jirana ake yi in faɗa." Ido ya zaro "wa da wa za ki faɗawa? Wannan ai tonon silili ne. Kowa sai ya san girmanta saboda Allah? Sirri ne fa." Ya yi kicin kicin da fuska. Yaya Hajiyayye me zata yi kuwa banda dariya. "Sirri manya. Ba dai naji ance weekend za ka kaiwa su Hajiya ita ba? Tana cire mayafi zan aunata tas da ido wallahi." "Zan fasa kawota." "Ka ma isa?" "To umarnin zan bata kada ta yarda ta cire mayafi...kai, hijab ma za ta saka." "Kayi ka gama. Telan da zai yi mata ɗinkunan biki ma ranar zai zo aunata." Ta ce tana kallon idanunsa. "Tela kuma?" Ya ambata kamar yau ya fara jin kalmar "Dama har yanzu ana wannan jahilcin Yaya? Na zata yanzu mata ke auna kansu su bawa telan idan ma namiji ne." Ganin ta same shi a hannu ta cigaba da kunna shi. "Ɗinkunan maza ai sun fi na mata kyau. Sun san duk wani lungu da saƙo da za su auna saboda shape ya fito." Abu ya yi tsamari. Taj harda gumi don takaicin yadda idanunsa ke nuna masa Hamdi a gaban wani ƙato yana gwadata. Mantawa ya yi da girman yayar tasa ya ce, "Wannan dai kafurci ne ƙaɗa'an. Kamar ba a zuwa islamiyya a garin nan?" Ta gimtse dariyarta da ƙyar "mu ne kafiran kuma yau Taj?" "Allah Ya baki haƙuri" ya ce yana kumbure kumbure. Dariyar da take dannewa sai da ta fito. Tayi mai isarta ta ce to lallai a yau ɗinnan take so ya tura mata kafin ƙanwarsu da ta tafi UK da mijinta ta dawo nan da kwana uku. Tunda ta tafi yake tunanin yadda zai tambayi Hamdi. A ganinsa mai baki amma yana da kunya. Ga amaryar tasa ita ma gwanar tsiwa. Ƙarshenta daga tambaya ta fassara shi. * A unguwar tasu ya yi Isha tare da Abba. Ya jira shi ya sanar da Yaya zuwansa sannan ya shiga su ka gaisa. "Kwana biyu mun tada kai tsaye. Naji kana ta yawon neman gida." "Yiwa kai ne Yaya." Abba ta kalla don bata daina fushin zuwa dubiya ba "Kamal bai yi fushi damu ba ko?" Shi da ya san komai a bakin Zee ya riga ya fahimci Abba tsoron zuwa yake kada su haɗu da Alhaji. Nuna mata ya yi babu komai tunda ba jimawa ya yi ba. Kwana ɗaya ne. "Allah Ya ƙara masa lafiya." Ta tashi ta ce "Me za ka ci a ɗora maka? Yau abincin ana magariba da kowa ya ci aka bayar saboda zafi. Abbanku kuma ya ce a ƙoshe yake bamu ajiye masa ba." Shi da ba wata surukuta yake yi da su ba sai cewa ya yi zai ci indomie. Abba ya miƙe saboda sabo zai tafi kitchen ɗin. "Girkin matarsa zai ci. Don Allah zo ka tafi ka watsa ruwa ka huta." "Au...haka ne fa" ya furta yana jin kamar ya faɗawa Yaya gaskiya. Baya son su fara jindaɗin kasancewa tare bayan ya san auren ba mai ɗorewa bane. Dariya su ka bawa Taj. Yaya ta ce ya jira yanzu za ta turo Hamdi. * Tana jin takun Yaya ta gyara filo ta kwanta. Dama tunda taji muryarsa ta san sai an nemeta. Ba kuma son ganinsa take yi ba. Abubuwa uku ke damunta. Haushin abin da Alhajinsa ya yiwa mahaifinta da wa'adin da ya basu, sai kuma rashin nemanta da ya yi na tsayin kwanakin nan. Na ƙarshe kuwa kewarsa ce da ta mantar da ita rashin son girkin da yake yi. Ranar da taji Kamal ne babu lafiya dai tayi masa uzuri amma sai taƙi kiransa ta kira Kamal ɗin. "Tashi kafin ranki ya ɓaci." Yaya ta kai mata duka a cinya. Ta tashi tana sosa wurin. "Kina fa da zafin hannu Yaya." "Wuce ki ɗan gyara fuskarki ki je ki dafawa Taj indomie." "Indomie kuma? Ba ya iya dafawa ba? Ya tafi gidansu mana." Ta turo baki. Hannu Yaya ta kai za ta ɗalle bakin ta gudu. "Bana son rashin ɗa'a Hamdi. Kuma saura idan kin je ki kasa gaishe shi. Mara kunya kawai." Yaya na fita tayi saurin cire kayanta ta saka riga da wando na bacci ta ɗora hijabin da ya wuce gwiwarta kaɗan. Fita ta zo yi Zee ta kama kiran Yaya. "Zo kiga a yadda za ta fita." Saurin rufe mata baki tayi "gulma dai haramun. Ina ruwanki?" "Babu ruwana amma dai a matsayina na mai jin maganar iyaye zan so ƴar uwata ma tayi hakan." Harara kawai ta gallawa Zee ɗin. Ta koma gaban ɗan madubinsu ta fesa body spray sannan ta shafa hoda da man leɓe. Dama niya tayi taje masa tana hamma ta ce bacci take ji. "To uwar iya...haka yayi ko kuwa sai na cire hijabin?" "Da yafi bada citta don wallahi har laɓe sai nayi muku." Hamdi ta tafa hannuwa "gulmawiya, shi yasa naga kin yi saving sunan Baballe da Sadiq a wayarki? Wato ɗan zuwan nan da yake yawan yi har ya kwance miki hadda. Kin manta kukan bakya so ɗin da ki ke yi." Zee taji kunya sosai. Sai ta cije don Hamdi ba za ta rabu da ita da wuri ba. "So muke mu rigaku haihuwar da Ya Taj ya ce ku za ku fara yi." "Na shiga uku. Zee zancen haihuwa yayi miki? Da wa zai haihun?" Zee ta ƙyalƙyale da dariya "Hamdiyya Habib mana" Tana faɗin haka ta fice daga ɗakin. Hamdi ta gama jimamin maganar ta fito da ƙudurin fara cika umarnin Abba. Za ta cigaba da nunawa Taj bata son girki da ma wasu abubuwan da take jin za su taimaka wurin ɓata masa rai. * Danna waya yake su na chatting da abokinsa Wakili da su ka yi karatu tare a Indiya ta shigo. Sallamar nan ciki-ciki da gaisuwar. Taj ya yi kamar bai ji ba yaƙi amsawa. Sai da ta shigo cikin falon ya ɗaga kai ya kalleta. "A dinga sallama ƴan mata." Ta juya idanu "Ai nayi." "Banji ba." Ya faɗi lokaci guda ya shagala da kallonta. A garajen fitowarta hijabi ruwan madara ta saka mara kauri. Da kaɗan ya wuce babu a jikinta. Rikita masa lissafi yaga tana neman yi ya wayance da cewa "ba za ki iya sallamar bane in tafi?" Ta turo bakin nan "to Assalam alaikum." "To wa alaikum salam." "Guda nawa kake ci?" "Me?" "Indomie ɗin mana." "Oh, ki kimanta." Ya gyara zama abinsa. Tana son tambayarsa ko me da me za ta saka a ciki amma bata son yawaita yi masa magana. Fita tayi ya ajiye wayar da dama amfaninta rage masa kallon ƙurillar da yake yi mata. Ita kaɗai ta kama tsaki da ta tuna yanzu ƙila fa duk yadda za ta dafa zai ji bata yi ba saboda sabo da girki. Yanke shawarar yinta normal kawai tayi. Ta ɗauko attaruhu da albasa za tayi grating amma bata san gejin cin yajinsa ba. Ƙarshe dai guda biyu ta saka da ƙaramar albasa. Ta raba jajjagen biyu sai taga kamar yayi yawa. Kaɗan ta saka ta dafa indomie ɗin dashi. Sai ta kuma soya wani da curry da ɗan maggi cikin mai daidai suyar ƙwai. Yana fara ƙamshi ta juye ƙwai uku da ta kaɗa a kai. Ƙamshinsa har falo. Ta kawo cucumber ta yanka rabi a zagaye ta jera a gefen plate ɗin mai ɗan zurfi kaɗan ta tsakiya. Indomie ɗin tana ƙarasawa da sauran ruwa mara yawa ta juye sannan ta rufe kanta da ƙwan. Yadda bata son ci da sanyi shi yasa tayi gaggawar kai masa. Tana ajiye tray ɗin ana ɗauke wuta. Taj ya kunna torchlight ɗin wayarsa ya hasketa tayi saurin rufe ido. "Hamdi da zuciya ɗaya kika dafa min dai ko?" "Me ka gani?" "Wuta aka ɗauke. Kin san mu a India yanzun nan sai mu fassara abu." Murmushi tayi don ta fara gano tsokanarta yake da zancen Indiyan nan. "To Shah Rukh Khan. Da me ka fassara ɗauke wutar?" Taj ya haɗiye abincin da ya kai bakinsa ya ce "Da lokacin waƙa cikin duhun dare mana. Muna bin bango muna rawa." Toshe bakinta tayi ta kama dariya. Abin nasa azimun. Wai bin bango. Ganin ya tsura mata idanu amma bai fasa cin abincin ba shi ne ta ce. "Bin bango kamar wasu ƙadangaru." "Kin ci sa'a yunwa nake ji da na tashi na gwada miki yadda ake yi." "Bana ma son sani" ta zare wayar fitila daga inda aka jona chaji ta kunna. A take haske ya wadata a falon. Ta buɗe fridge ta ɗauko ruwan sanyi ta ɗauko da kunun ayan da Yaya ta haɗa da rana. Ta kawo gabansa ta ajiye a gefen tray ɗin sannan taje ta kawo kofuna guda biyu ta dire masa. Kujerar nesa dashi taje ta zauna "Nagode" ya ce bayan ya gama. Abincin kaɗan ya rage. Hamdi ta kalle shi da wutsiyar ido "banlbu daɗi ko? Ba irin haka ka saba dafawa ba?" "Ke dai ki ce kina son in yaba miki. To nayi. Yayi min daɗi sosai." Bata yarda dashi ba "duk iya girkinka?" "Girkina daban, na matata Hamdiyya ma daban. Zan dinga taimaka miki a kitchen amma ba kullum ba. Ina son in dawo gida kamar kowane namiji in ci abincin da matar gidan ta dafa." Yana lura da yadda maganarsa tayi mata daɗi. Ba dai ta son nunawa ne. Shi kuwa indai tana da kunnuwa to ba zai fasa faɗin maganganun da za su yi tasiri a zuciyarta ba. Tashi yayi ita ma ta miƙe. "Bari na ƙarasa gida na huta kuma." Tray ɗin ta duƙa ta ɗauka ya ce "na faɗawa Yaya ranar asabar zan zo mu je gidanmu." "Gidanmu ko gidanku?" Ta ce a tsorace. "Saurin me kike yi? Gidan iyayena ba gidana ni da ke da ƴaƴanmu ba" Ya ƙare maganar yana kashe mata ido. "Sai da safe" tayi masa fuskar shanu. Hira dashi tana yi mata daɗi amma biyewa zuciya ganganci ne. "Oh, don Allah ɗauko min underwear ɗinki na sama da na ƙasa ana son ganin size." Tray ɗin hannunta ta kusa saki da taji me ya ce. Bata ankara ba taji hannuwansa sun damƙi nata. A karo na biyu su ka ji wannan yanayin da ya bambanta da in sun taɓa kowa. Zame nata hannun tayi ta bar masa tray ɗin. Taj ya ce "yauwa yi sauri. Kuma don Allah wankakku." Wata uwar harara da ta banka masa ba shiri ya ajiye tray ɗin a inda ta ɗauka. "Ai gaskiya ce. Naji an ce ƴan mata maimaici su ke na sati biyu ko ma fi kafin su wanke." Kamar za tayi kuka ta ce "Don sharri? To ba zan bayar ba. Idan ma bokanka ne yake so kace masa na hana. Ya turo aljanu su satar masa." "Dare ne dai kuma babu wuta. Ki cigaba da kiraye kirayen abubuwa. In su ka zo..." ya faɗi a hankali yadda zancen zai shigeta. Ai kuwa bayanta ta kalla da sauri ta ɗan matso kusa dashi. Tausayi ta bashi. Duk tayi wiƙi wiƙi da idanu. "Yayata ce ta ce na tambayeki fa." "Size ake tambaya ai. Ya za ka ce in baka?" Hamdi ta ce da mamakin irin nasa tunanin. "Don kada ki faɗa min ba daidai ba. Nafi son komai accurate." "To ba zan bayar ba. Ka kamanta yadda ya dace." Ta ɗora hannuwa a ƙugu. Taj ya san bata da masaniyar shigar da tayi. Da bata yi wannan tsayuwar a gabansa ba. "Don't dare me Hamdi. In ki ka yi wasa da hannuna zan kamanta." Da sauri ta koma bakin ƙofar falon har tana tuntuɓe saboda gigitar kalamansa. "Matsoraciya." "Naji." "Za ki turo size ɗin ko in sa Zee ta ɗauko min na tafi dasu?" Zai aika ta sani yanzu. Tunda ya iya faɗa mata zasu riga haihuwa ai komai ma is possible yanzu. "Zan turo." Ta ce a hankali. "Good girl. Sai jibin ko?" Kada azo tafiya ya ce su biyu kaɗai shi yasa ta ce masa da Zee za su je. Shi kuma ya ce a'a don yanzu matar aure ce. Sai ta ce to da Halifa. "Haka kawai sai in ɗauke ki da ƙato a mota?" Hamdi ta ɓata rai "Halifan ne ƙato?" "Yanzu duk duniya daga Abba sai ni sai Alhajina ne kaɗai normal maza a wajenki. Sauran kowa ƙato ne." "Kaima ƙaton ne kuwa." "Mijin ƙatuwa ba." Dariya yake yi da yayi maganar. Sai gata tana murmushi. Fushi dashi ma da alama ɓacin lokaci ne. Sai da safe ya yi mata ya tafi. Ta tattare kwanukan ta tafi kitchen tana wankewa hirarsu na dawo mata. Da ta gama gidan tsit yayi mata. Yau ko inji Halifa bai fito ya kunna ba da aka ɗauke wuta. Bata san Yaya ce ta hana ba. Wai ƙarar za ta dami Taj. Ƙaramin table ɗin da ta ɗora masa tray taje ɗaukewa sai taga wayarsa. Ta ɗaga ta juyata a hannunta. Dole masu iphone su ke jin kansu. Wayar a hannu ma daban take. Abba ta yanke shawarar bawa da safe don da alama yau sun yi baccin wuri. Kimanin rabin awa da tafiyarsa taga kira daga wani suna an sa Anti Zahra. Sai da aka kira na biyu sannan ta ɗauka. Muryarsa taji ta saki ranta. Ya ce ta ajiye wayar zai zo ya karɓa washegari. "Zan bawa Abba ya taho maka da ita." "To nagode. Goodnight." * Famfo iya famfo Mami ta yiwa Salwa. Tunda ta koma gida da ramar kwana biyu amma kamar tayi jinya hankalin Mamin ya tashi. Ta kira Ahmad ta ƙare masa tanadi. Harda kiransa wanda baya kishinta. "Aure kuma tunda tana so ko uban naku bai isa ya hana ba." "Mami kin fi so ta kai kanta inda ba a sonta? A ƙarshe ta dinga fuskantar wulaƙanci." "Rufe min baki. Matan gidanku sun gama cinye maka zuciya baka iya taɓuka komai. Arziƙin Taj kai kana da rabinsa ne?" "Kowa rabonsa yake ci Mami. Don Allah ki daina biyewa Salwa." Cikin faɗa tayi masa tsawa "Salwa za ta dawo. Ina so ka yiwa Alhajin naku maganarta don na san yana ƙaunarta. Ita wadda Taj ɗin ya aura na riga na samu bayani akanta. Bata da wani abin nunawa balle ta kara da jinina." Ta inda take shiga daban da inda take fita. Ran Ahmad ya gama ɓaci da su ka gama wayar. Yana jiran dawowarta ya nuna mata kuskuren sanya Mami tayi masa irin wannan faɗan. Bayan Mami ta gama dashi kan Salwan ta koma tana yi mata nata faɗan na rashin ɗaukar shawararta. Kissa ba ƙaramar makami bace a wajen mata. "Ki bari sai kamar shaɗayan dare ki kira shi ki gigita shi da kalamai masu daɗi." Sunkuyar da kai tayi tana murmushi. "Ki nuna masa yafi kowanne namiji ba tare da kin zubar da ajinki ba." Sai da ta gama kwasar huɗuba sannan ta shige ɗaki. Ta gama komai da wuri ta zauna jira. Shaɗaya da kwata na dare kuwa ta doka kira wayar Taj. RAYUWA DA GIƁI 21 Batul Mamman💖 This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ƙamshi babu ruwansa da gari ko ƙasa. Wuyarta ciniki ya faɗa. Za ku sami undiluted oil perfumes ɗinku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haɗa kwalabe daban daban ki gigita waɗanda ya halatta su ji ƙamshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeta a wannan layin 07065525409 . *** Da farko da taji ƙarar wayar cikin baccin da ya fara ɗaukarta tsorata tayi don ta manta da ita. Niyyarta ta barta ta gama sai ta kashe, ko waye ya kira da kansa. Ita ba mai son amsa wayar mutane bace. Wani kiran ne ya sake shigowa immediately bayan na farkon ya katse. Ta daure ta wartsake idanu ta kalli sunan mai kiran SALWA B. Wani irin tunani ne ya shiga karakaina a ƙoƙon ranta. Meye ma'anar B ɗin? Bichi, Bunkure? Ba dai brother bane tunda sunan mata ne. To ko dai baby yake nufi? Ko bestie? Haba! Zuciyarta tayi wani irin kumburi ta taso mata har wuya. Harda wani ɗaci-ɗaci kamar ta tsotsi flagyl. Mantawa tayi da maganarsu da Abba a karo na biyu yau ta amsa kiran ido rufe. Garin sauri harda _record_ ta danna a rashin sani da ta mannata a kunnenta. "Ya Taj na tasheka ko?" Salwa tayi magana da sassanyar murya da ta sha kwaskwarima domin yin tasiri a zuciyar wanda ake yiwa. "Ayya ba shi bane. Ya manta wayar ne." Hamdi ma ta mayar da zuƙaƙƙiyar murya. Ba shiri Salwa ta zabura ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi. Da ta gama shirin yadda za ta dinga mirginawa hagu da dama saboda daɗin murya da hirar da za su yi da Taj. Gabanta na faɗuwa ta ce "Wace ce ke?" Tana buɗe murya normal, Hamdi ta gane wannan wayar ba ta ƴar uwa bace. In ma ƴar uwar ce to tabbas cousin ce. "Suna na Hamdiyya." Ta ce a kunyace "manta wayar ya yi a wajena ɗazu." Tsakin Salwa taji wanda ya yi mata ciwo matuƙa kafin ta ji ta ce, "Wai ƴar gidan ɗan daudun da ya aura last week ce?" "Laahhh, ashe kin sanni." Hamdi ta amsa da sauran fara'a a muryarta kamar gaske. Bata so tayi saurin kwafsawa kuma ya kasance Salwan ƴar gidansu ce. Cikin huɗubar Mami harda kada ta ragawa yarinyar da ya aura. Tunda ance musu sakandire ta gama sun tabbatar babu wayo da wayewa a tare da ita. Tsorata ta da nuna mata ita ɗin ba komai bace zai taimaka sosai wajen samawa Salwa ƴanci idan ta shiga gidan Taj. "Da alama kina da rawar kai. To amma ba zan hana ki ba. Lokacinki ne. Ki dai sanya a zuciyarki cewa nan ba da jimawa ba wadda ta fi ki son Taj za ta shigo rayuwarsa." Hanci Hamdi ta ja kamar mai shirin kuka "Anti Salwa nayi muku laifi ne har ku ke son bashi wata daga aurenmu? Ita wadda za ku bashi ɗin bana jin ta kai ni son shi. Don dai bamu haɗu bane da kema sai kin yaba min. Tarbiyya da iya kula da miji duka ɗan daudu da miskiniyar da su ka haife ni sun koya min." Amsar Hamdi ba ƙaramin tayar mata da hankali tayi ba. Kai tsaye ta faɗa mata magana ta rama wadda tayi mata. Tana so ta ce mata ita da kanta za ta auri Taj amma gani take faɗin hakan zubar da aji ne sai ta gimtse fuska cike da takaici. "Ni ba ƴar gidansu bace." "Ikon Allah. Kuma naga ya yi saving sunanki da Sister Salwa? Cousin ɗinsa ce ke kenan?" "Sister Salwa???" Baƙinciki ya mamaye zuciyar Salwa a lokacin da take nanata kalmar "haka ya rubuta?" "Uhm, da capital letters." Tsanar Hamdi ta sake ruruwa a zuciyarta yayinda ta bata amsa. "To ko ma dai mene ne kada ki saki jiki don ba zan zauna da kishiya ba." "Lahhhhhhh, ko ke ce wadda ta suma ranar aurenmu?" Salwa ta haɗiyi yawu da ƙyar saboda jin da alama suna da yawa masoyan nasa "suma kuma? Shi ya ce miki akwai wadda ta suma a kansa?" "Ba ke bace kenan." Hamdi ta faɗi da rashin damuwa "Allah Sarki. Kada ki damu fa. Ni bani da matsala ko ya ce zai ƙara aure don na san a danginku dole a bashi wata. Tunda na samu na shiga sai dai in ce Allah Ya bawa mai rabo sa'a. Mu kwana lafiya." Katse kiran tayi ta ajiye wayar a kusa da tata tana murmushi. Za ta so ganin idanun Salwan nan. Irin yadda taji tana sauke numfashi da tana bata amsa ya kusa sanya ta dariya. Ta riga ta san mahaifinsa baya sonta. Abba kuma ya faɗa mata mahaifiyarsa tana maraba shi yasa ma ta nemi ganinta. Duk da haka ba sakin jiki zata yi ba. Dole dama ta sa rai da ganin wulaƙanci kala kala kafin ta bar musu danginsu. Ko banza dai bata bari an ƙuntata mata ba ta ce a ranta tana faɗaɗa murmushinta. Zee ta kalla tana ta sharar bacci. Ina ma idonta biyu. Yau da sun mannawa wannan cousin ɗin hauka. Don Zee dake sakandire ma ta fita sanin irin waɗannan abubuwan. Zamani na turawa, na baya suna zuwa da wayo da dabarun da waɗanda su ka gabacesu basu taɓa sani ba. Bata san lokacin da tayi bacci ba saboda yadda abin duniya ya dameta daga baya. Shin ƴan mata gare shi ko kuwa a dangi ake son aura masa daidai da shi? Zuwa gidansu jibin nan kuwa shawara me kyau ce? Da kuka Salwa ta kwana. Ba kuma na auren Taj ba wannan karon. Yadda yarinyar da ta raina ta ɓata mata rai ba tare da ta rama ba ne yake damunta. Wai bata da matsala ko zai sake aure. Kenan ma alfarma za ta yi mata ta bari a aurota. Ƙwafa tayi "sai zaman gidan Taj ya gagareki indai ni ce." *** Da Abba zai fita kamar yadda ta faɗawa Taj ta bashi wayar. Ya dubeta da kyau ganin fuskarta shar babu damuwa a tare ds ita. "Hamdi kada ki manta da maganarmu. Bana son abu ya yi nisa Alhaji yasa a ɗora miki zawarci mai ciwo. Gara ma ace ba kya son shi zai fi miki sauƙi." "In sha Allahu Abba" ta faɗi tana mai sunkuyar da kai don ta san jiya dai bata wani taɓuka abin kirki ba. "Garin yaya ya manta wayar?" "Ina jin daga aljihunsa ta fito. Sai bayan tafiyarsa na gani." "To shike nan. Ki kula dai. Sai na dawo." Tsayar da ita ya yi kafin ta koma ciki "wannan hijabin Hamdi gaskiya ko dai ki haƙura dashi ko kuma kada ki yarda wani baƙo ya ganki da shi." Da sauri ta kalli jikinta "Abba wani abin ya yi?" "Ki duba madubi." A dawo lafiya tayi masa a soron da su ke tsaye su biyu sannan ta koma ciki. Hannu ta ɗora a ka da ta ƙarewa kanta kallo. A haka fa ta fita wurin Taj jiya. Da ta tuna an ɗauke wuta ne ma ta sami nutsuwar kama aikinta na yau. Zee ce da girki idan ta dawo daga makaranta. Ita kuma wanke wanke da shara. Halifa kuma kullum shi ne da wankin banɗakuna da sharar tsakar gida zuwa soro da harabar gidan. Duk wanda ya san gidan Abba ya shaide su da tsafta. A kansu Anti Labiba ta ƙara gane cewa babu wata ƙwaƙƙwarar alaƙa tsakanin talauci da ƙazanta. Kowanne zaman kansa yake yi. * Yana cire lock ɗin wayar abin da ys fara gani shi ne (save - discard) na recording call. Ya san da wuya Hamdi ta iya yin kira da wayarsa tunda yatsansa ne mabuɗin wayar. Amma wa ya kira shi ta ɗauka har su ka kwashi waɗannan mintuna suna magana? Saving ya yi sannan ya shiga call log. Nan ya tarar da missed calls ɗin Salwa kafin wanda aka ɗauka. Da saurinsa ya nemo recording ɗin ya shige office ɗinsa ya kunna. Shi kaɗai ya dinga dariya. Hamdi bata da dama. Ta kuma burge shi. Bata cikin irin ƴan matan nan da su ke zama a taka su son rai su shiga ɗaki su yi kuka. Nishaɗi fal zuciyarsa. Salwa ce ma yaga dacewar ya taka mata burki kafin ta kai su ga ɓacin ran da wani zai ji su. Kiranta ya yi kamar tana jira ta ɗauka. Ƙin magana tayi gudun maimaicin abin da ya faru jiya. Sai da ya yi sallama ta saki rai ta amsa ta gaishe shi. "Kin kirani jiya ashe. Hope ba matsala bace?" "Eh wallahi." Ta gyara zama tana murmushi "babu wata matsala. Kira nayi kawai mu gaisa. Faɗa maka tayi na kira?" Ta ƙarashe maganar a hankali. "No, missed calls ɗinki na gani. Sai kuma naga alamun kun yi magana da Babe ɗina har na kusan five minutes. Lafiya dai ko?" Wai Babe? Siririn tsaki tayi kuma yaji. Ba don yana son a yau ya daƙile komai nata ba da ya ajiye wayar. "Na ce lafiya ko?" "Naga kwana biyu baka nema na ne." "In ce miki me Salwa? Muna gida ɗaya nayi aure ki kasa yi min fatan alkhairi." Tsayar da zuciyarta tayi wurin daina kwana-kwana a kansa. "Ohhh, wai har kana saka wannan a jerin aure Ya Taj? Ba ance babanta ɗan ..." "Yes, ɗan daudu ne a da. And one of the most wonderful people alive today. Mamanta kuma is physically challeged. Polio ya yi affecting posture ɗinta sosai." "Ta faɗa min jiya" ta ce don bata ga amfanin maimaitawar ba. Mutane irin waɗannan mene ne abin tinƙaho dasu? Idan iyayenta ne za ta yi bakin ƙoƙarinta wurin guje musu don ma kada ace ta san su. "Ina sake faɗa miki duk da na fahimci kin sani ne don ki gane cewa duka waɗannan abubuwan da wasu ke gudu ni su ne su ka sa Hamdi ta zama the most special girl alive. I love her Salwa. Bana kuma son duk wani makusancina ya dinga ganin kamar wannan abu ya isa dalilin da zai rageta a matsayin mace. She is everything I want." "Kirana kayi ka ci min mutumci saboda ina son ka? To my face ka ke faɗa min kana son wata?" Salwa tayi magana da rawar murya. "To your ears dai. Amma in kina so zan maimaita miki in mun haɗu. Ba ke kaɗai ba kuma, duk family ɗin Maitakalmi, babu wanda zan ragawa akan mutumcin matata." Iya wuya ran Salwa ya gama ɓaci. Za ta iya rantsuwa basu taɓa wata doguwar hira da Taj a waya ba idan ta kira shi kamar wannan. Saboda ƴar gwal ta kai masa gulmar wayarsu ta jiya. "Abin da Yaya Ahmad ya ce Alhaji da bakinsa ya gaya masa wata uku ya bawa babanta ya kashe auren don ka koma gida. Na san akan mace ba za ka zaɓi dawwama a haka ba" Ta faɗi kai tsaye don da alama kukan ba zai kaita ko ina ba "Ya Taj zamu yi aure kuma za ka bani haƙuri akan wulaƙanta soyayyata." Ita ta fara kashe wayar ta barshi da wani irin sanyin jiki. Bai taɓa zaton yayan nasu zai ɗauki sirrinsa ya faɗawa ƙanwarsa ba. Kowa matsayinsa daban. Maganar da ko Kamal bai samu ya faɗawa ba saboda rashin lafiyarsa. Su Innarsa da Amma da sisters ɗinsa duk basu sani ba. Shi ne zai sanar da Salwa? He felt disappointed and betrayed. Tun farko abin da ya yi ta gudu game da ita kenan. Tunda baya so dole yayan nasu ya sami ɓangare guda da zai fi tausayawa. Sai ya musgunawa ɗayan kuma? Duk da haka ya ƙudurce ajiye abin a ransa har ya gano yadda aka yi taji zancen. Bayan sun kammala wani emergency order na taro an fitar da abincin ya tafi wurin Kamal. Mutumin da kullum idan ya shiga shagon nasa har mita yake masa na rashin hutu yau a zaune ya same shi yana gyangyaɗi. Ya kan ce masa mene ne amfanin ƴan zaman shagon dake nuna kaya da waɗanda ke wurin biyan kuɗi. Shi kaɗai ya yi nan, ya yi can. Sai gashi hayaniyar kwastomas bata hana shi baccin ba. Yana zuwa hannu ya kai ya taɓa wuyansa da goshi. Abin da ya farkar da Kamal ɗin da sauri don ji ya yi kamar an ɗora masa ƙanƙara. Tsigar jikinsa har tashi tayi ya buɗe ido a firgice. "Happiness kaji jikinka kuwa? Tashi mu koma asibiti" Taj ya ce yana kai hannu gefe ya ɗauko masa wayarsa. Hamma Kamal ɗin yayi "bacci ne fa. Bari na shige ciki na kwanta" ya nuna nasa office ɗin. "Kada ka raina min hankali mana. Bacci ne yake kawo zazzaɓi? Muje don Allah." Wasa ya mayar da maganar ya ce "Sai dai in kai ka. Dama na faɗa maka yau ɗanin motarka zanyi. A adaidaita sahu ma na taho saboda son banza." "In ka bari mu ka je asibiti Allah zan yarda mu yi musanye. Saboda na san kai mayenta ne na saya." Wani irin kallo Kamal ya yi masa. Taj is just selfless akan duk abin da ya shafi Kamal. Abubuwan da ya yi masa iyayensu basu sani ba ba za su ƙirgu ba. Ciki harda bashi jarin da ya gina boutique ɗinnan. Ya rufa masa asiri a lokacin da Alhaji ya bashi miliyan goma yaja jari. Allah Ya haɗa shi da ƴan damfara su ka wanke shi. Abu kamar rufa ido. Ya shiga ƙuncin rashin sanin yadda zai tunkari Alhajin. Kawai sai Taj ya ce ya sayar da filinsa da su ka saya tun da daɗewa. Filin da Mama take jira a fara gini. Filayen biyu su ka kama miliyan shabiyar. Ko ƙwandala Taj bai karɓa ba duk yadda ya so hakan. Ya kuma so ayi rubutu idan ya samu zai biya nan ma Taj ya ce kyauta ce. Baya fatan har abada a sake tada zancen. "Tashi mana" Muryar Taj ta dawo dashi daga duniyar tunani. Miƙewa ya yi cikin dauriya ya ce masa mura ke son kama shi. Shi yasa yake zazzaɓin. "Ni kuwa sai nake ganin kamar kana ɓoye min wani abu Happiness. Kwanakin nan kamar fa baka nan. Komai ni kaɗai nake yi." "You are married Happy. Ya kamata mu fara rage wasu abubuwan. Da banyi tunanin ba sai da Abba ya ankarar dani." Taj ya taɓe baki "yanzu zancen Mal. Sule har wani abin ɗauka ne?" "Ai kuwa dai ya fi mu gaskiya. Nan gaba kaɗan sai kaji ana Malama hide my ID. Brother ɗin mijina kullum suna tare. Ko unguwa zamu sai ya kira ɗan uwansa. Bamu da wani lokaci irin na mata da miji saboda ya kankane komai. Don Allah a bani shawarar yadda zan ɓullo musu ba tare da mijin nawa yaji haushi ba." Dariya sosai Taj ya yi. "Kamal mai malaman ig. Wato har salon tura saƙon ka iya. Daɗinta dai ba Hamdi bace za ta yi wannan. Daga ji Doctor ce ta fara ƙorafi. Tell her I'll make myself scarce in kun yi aure. Ayi soyayya lafiya." Daga nan sai zolayat juna. Kamal ya dage va zai je asibiti ba wai yunwa ma yake ji. Cikin Happy Taj su ka koma. Kamal ya yi odar shinkafa da gasasshen kifi. Kamar yadda Taj ya koyo, yawancin abincim Asia duk da hannu ake ci. Masu zuwa ko sun so gayu suna fara ci sai kaga an yi yadda yake a hoto da bidiyo da suke a lungu da saƙon wajen ana ci da hannu hankali kwance. "Kawo masa kaza" Taj ya ce da waiter ɗin. "Ban gane ba. Ka dai sanni da kifi ko?" Wani article Taj ya nuna masa sannan ya tura masa a waya. A ciki anyi bayanin yawancin abincin dake kawo allergy. Akwai gyaɗa da dangoginta. Kifi, kayan da aka sarrafa daga madara, ƙwai, kantu da kayan fulawa. "Za ka daina cin duka. A hankali sai mu dinga gwada ɗaya muna gani. Wanda a kansa reaction ɗinka ya dawo kaga mun san shi ne. Nima zan daina ci don ma kada ka ce mugunta na shirya maka." Yawun bakin Kamal ɗaukewa yayi. Ya shiga damuwa amma dole ya mayar da ita dariya. Sam baya jindaɗin ɓoye ɓoyen nan. Amma yanzu da zarar sun sani ƙarshen duk wani farinciki na gidansu ya ƙare. Baya son ya zama silar daina walwalar kowa akan lafiyar da kuɗi kawai ba za su iya saya masa ba. Abincin da yake masa ɗanɗanobda magani saboda rashin jindaɗin abin da yake yi ya dinga tutturawa harma yafi Taj ci. *** Office ɗin an rubuta Dr. Kubra Hayatu a jiki. Wani private asibiti ne mai tashe na mata da yara da su ka buɗe ita da ƙawayenta biyu. Wurin yana samon mutane fiye da zato saboda ƙwarewar aikinsu musamman akan mata. Zaune take tana harhaɗa wasu takardu kafin ta fita don ta gama shift ɗinta taji bugu a bakin ƙofar. Umarnin shigowa ta bayar inda wani matashi ya shigo ya gaisheta. Ƙaramin kwali da aka yi wrapping ya miƙa mata. "Ban sayi komai ba. Bana tsammanin delivery." Ta ce masa. "Ance na wani Kamaluddeen Hayatu ne amma ke ake so ki fara gani." "Wa ya aiko ka?" Ta tashi tsaye. "Idan kin duba ciki za ki gane. A tashi lafiya" Fita ya yi kafin ta sake yin magana. Ta ɗauki kwalin taji babu nauyi sai ɗan girma. Ta jijjiga taji abu kamar magani. Buɗewa tayi da sauri sauri. Sunayen magungunan da hotunan dake jiki su ka sa ta kusa yanke jiki ta faɗi. "Kamal? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Waya ta ɗauka za ta kira Alhaji. Har ta shiga sai tayi saurin katse kiran. Duk yadda aka yi likitarsa ce ta turo saƙon. Kuma da alama hakan yana nufin tana son ganawa da ita domin tayi mata bayanin da ya dace. Kiran Alhajin ne ya biyo bayan nata. Ta ɗaga wayar a firgice. "Doctor yaya? Haihuwar Nabila (ƙanwarta mai ciki) ce ta tashi?" "A'a Alhaji. Kira nayi mu gaisa kuma sai network ya katse kiran." Kwantar da hankali ya yi su ka taɓa hira sannan ta tashi. Kao tsaye asibitin da Kamal ya kwanta ta nufa. Aka sanar da ita Dr. Mubina sai litinin za ta zo. Nambar wayarta ta nema a reception ɗin aka sanar da ita bata ƙasar ne. Ta tafi Ghana amma ranar lahadi za ta dawo. Haka nan ta tafi cike da zulumi da fatan gaggawar zuwan litinin ɗin. *** Wato ƴan gidan Alh. Hayatu gwanaye ne wajen son shagali. Duk abin da zai sa su taru a gida komai ƙanƙantarsa basa raina shi. Daga su har ƴaƴansu. To iyayen ma dai ba a barsu a baya ba. Akan maganar zuwan Hamdi sai ka rantse bikin ne ya taso. Mama ce ta kira Yaya ta nemi izini tunda har yanzu a gida take. Bayan sun gaisa ta gabatar mata da kanta. "Suna na Haj. A'i kuma Mama a gida." "Allah Sarki Hajiya. Da fatan kuna lafiya." Da jindaɗin yadda Yaya ta tarbeta Mama ta ce "Alhamdulillahi. Allah Yasa Taj ya yi muku ɗan bayanin gidan namu." "Sosai. Ya ce Hamdi surukarki ce ke da ɗayar maman tashi ta Abuja." "Ƙwarai kuwa. To muna bada haƙuri tunda mace ita ya kamata a bi. Yanayin gidan namu ne Masha Allah. Muna da yawan da in muka zo za sai ƴan unguwa sun fara tunanin ko biki ake baki gayyace su ba." Yaya ta kama dariya. Da alama barkwancinsu Taj ba a ƙasa su ka ɗauka ba. "Allah da gaske. Shi yasa mu ka ce gara ta zo. Kuma dai idan zuwan zamu yi Inna ba za ta bi mu ba. Ai kin san wacce ce Inna a cikinmu ko?" Yaya tayi murmushi "na gane." Mama ma dariyar tayi "tunda anyi auren ya dace mu san juna ko yaya ne. Ina fatan zuwan nata babu takura." "Wace irin takura kuma ku da abar ikonku? In Taj cewa yayi ta tafi kenan ai sai dai mu bita da addu'a." Da girmamawa gami da mutuntawa su ka gama magana. Taj zai ɗaukota bayan azahar. *** Abba ya yi mamakin shigowa gida ya sami Yaya ta taƙarƙare tana gogewa Hamdi jiki da ragowar dilkan Sajida. "Allah ƙadiran ala mayyasha'u. Khadijatul Kubra yau ke ce da wannan aikin? Lallai Sajida rakiya tayo a gidan nan ga ƴar so nan kin saka a gaba" ya kalli Zee dake gefe tana fifita garwashi "kema ƴar rakiyar ce ko za ayi miki?" Kunya ta kama Yaya ta tashi ta koma cikin falo. Hamdi da Zee su ka yi ta dariya. Da ƙyar Hamdi ta yarda ake yi mata. Wai cikin mutane za ta je. Bata son a rainata ta. Zee ma nata kwaɓin yana gefe. Ita kuma sai yau Baballe zai zo. Cinikin motoci ya kai shi Kwatano tun bayan auren. Yaya ta ce gara a ga ƴaƴan nata a yanayin da duk hassadar mutum sai dai ya kushe a zuci. Sai gashi Abba na sakota a gaba ta gudu. Falon ya bita "dawo ki cigaba da kankareta kada mijin ya zo a barshi jira." "Kankara kuma don Allah kamar wata faso?" Ta faɗi tana ƴar harararsa cikin wasa. Ƴaƴan da irin wannan abu ba baƙonsu bane su ka tattara su ka barsu a falon. Zee ce taƙarasa mata ita kuma ta yiwa Zee ɗin. "Wai amma gyaran jiki kamar za a kai mu yau?" Cewar Zee da su ka sanya turaren wuta cikin lulluɓin ƙaton zani kowacce ta zauna akan kujera. "Ke dai muyi kawai in ba kin shiryawa mitar Yaya ba. In taji haushi sai ta hanamu zuwa gidan Ya Sajida gobe." "Kin tambaya ma kuwa kamar yadda ta ce? Ni fa na rasa ma me zan ce. Haka kawai yanzu shige ds fice na sai in bin wani bayan a gidanmu nake" cewar Zee. "Na ma manta da tambayar. Zan dai gwada. In na kasa in rubuta a text." Shawarar ta yiwa Zee. Ita ma a text ɗin za ta rubuta. Suna idar da sallar azahar Yaya ta umarci Hamdi da yin wanka ta shirya. Jinkirin fita na ɗaya daga cikin abubuwan dake saurin kawo saɓani tsakanin ma'aurata. Ita dai nata to ne. Tana kaffa kaffa don sun gama shirya irin dabdalar da za su yi gobe da Sajida. Ga tanadin hira da neman shawara kowacce tana son ji daga babbar yaya. * Biyu da kwata Taj ya iso. Ƙememe Kamal yaƙi rako shi. Har cewa ya yi to wa zai shiga da ita gidan tunda shi a waje zai tsaya. Kamal ya ce masa in sun iso ya kira shi. Haka nan ya tafi yana mita. Sai da Hamdi ta fito ya shiga shi masa albarka. Yana zaune a falo yana zubawa Yaya santin kunun ayanta da duk sanda zai zo sai ya nema tayi sallama. Ya juya a hankali su ka yi sa'ar haɗa ido. Da ido kawai ake gani lallausar shaddar da ya saka wadda aka yiwa ɗinki irin na matasan zamani. Ruwan toka ne kamar kullum an ƙaranta adon. Very classy and elegant. Bai saka hula ba sai gyaran fuska da ya yi. Ita kuwa cikin ɗinkunansu na bikin Sajida ne ta saka guda da ya kamata su sa ranar ɗaurin aure. Riga da siket ne mai adon ja da shuɗi mara turowa ne a jiki sai baƙi. Fuskarta yau ya fara ganinta da kwalliya irin wannan. Light make up. Komai cikin tsari babu hayaniya. Tayi ɗaurinta a karkace kaɗan ta ɗora shuɗin mayafi daga rabin ɗanƙwalin. Hannuta da lallen biki ya fara tafiya ta sanyawa abin hannu a ɗaya. Ɗayan kuma agogo ne na silver. "Gara ku tashi kada yamma ta same ku ko?" Yaya ta ce da taga kallon yaƙi ƙarewa. Taj ya ma manta inda yake da alama. Ita kuma Hamdi sai juya awarwaro take. Da ya fita ta fara binsa sai taji kamar ta zura da gudu. Tsoro ya shigeta har zuciyata tana gudun famfalaƙi. Bakin wata mota da duk rashin sanin motocinta ta san wannan ta kai duk inda ake so ta kai. A idonta dai jeep ce tunda tana da tudu. Fara ƙal da tambarin BMW a jiki. Buɗe mata ya yi ta shiga sai ta daina ganin hasken rana sosai. Gilasan masu duhu ta kalla ta ƙara jin wannan tsoron. Ƙamshin daɗin da motar take fitarwa zai iya mantar da mutum a ina yake. Taj na zama a mazaunin direba ta kama kanta. Ɗan waigen ƙauyancin ya ƙare. Ya tada motar ya kunna AC sannan ya fara ribas. "Ɗan tsaya." Hamdi ta faɗi tana ɗora hannu a ƙirji. Burki ya taka da hanzari "Me ya same ki?" Idanunta har sun tara ƙwalla ta ce "Gabana ke faɗuwa wallahi." "Saboda me? Haɗuwa da ƴan gidanmu?" Ta girgiza kai da dukkan gaskiyarta ta nuna shi. Yana son honesty ɗinta. Juya kan motar yayi domin su hau titi ya ce "Kin dai san ko ina satar mutane ba zan saci jinin Abbana ba ko?" Tana jindaɗin yadda yake girmama mahaifinta sosai. Amma da yake bakin baya shiru sai cewa tayi "na sani ko ka fara yau. Ka zo da mota a rurrufe ba a gano ciki ta waje." "Ƴar ƙauye zan ce miki ko matsoraciya? Amfanin wannan tint ɗin ga irinmu shi ne yanzu misali idan naji ya kamata..." ɗauke ido ya yi daga titi su ka kalli juna. "Ya kamata me?" "Will you let me kiss you idan mun dawo? Ko yanzu in sami wurin parking?" "Ya Taj???" Idanunta su ka firfito. "Na'am. Ashe kin san suna na. Na zata Salman Khan za ki ce. Har na tanadi waƙarsa da zan miki." Ya yi maganar yana dariya. Bakin tsiwa ya mutu murus. Ya ɗan kalleta yaga hannuwanta kawai take kallo. Shi da ya tsammaci ta bashi amsa. "Hamdi? Yaya? Zazzaɓin ne yau ma?" "Uhmm" ta gyaɗa kai harda shafa wuya da goshi. "Ki ce in tanadi maganin maleriya da thypoid ranar da za ki tare kawai." "Allah da gaske nake. Jikina babu ƙwari ma." Ta ɗaga hannu ta sake shi yaraf. "Kinga mun kusa zuwa gidan. Ki rufa min asiri yanzu don za ki haɗu da ƴan jarida masu tambayar tsiya. Akwai ƴan bugun ciki ma waɗanda za ki iya faɗa musu duk hirar da muka yi yanzu ba tare da kin sani ba." A tsorace ta ce "da gaske?" "Da wasa" ya furta a hankali yana yi mata murmushi. A bakin gate ɗin wani ƙaton gida taga sun tsaya. Ya ɗaga waya ya kira Kamal ya ce masa sun iso. Tsoron nan bai barta ba ta ce "ba za ka shiga ba?" "Alhaji bai yi min izini ba." Ya amsa mata da murya mai rauni. Tausayinsa ya mamaye zuciyarta har taji kamar tayi masa kuka. "Kada ki ɓata min kwalliyar nan tun kafin na biya kuɗinta don Allah." "Ni ba don kai nayi ba" ta ce da tsiwar nan. "Mala'iku suna jin ki dai." Da sauri ta ce "Astagfirullah." Bata ankara ba ya yi abin da tun shigowarta motar yake muradin yi. Hannunta mafi kusa dashi ya kama ya sarƙe yatsun ya lanƙwashe su. "Wa ki ka yiwa kwalliyar? Suna ji dai kada ki manta." Tsuke baki tayi tana jin yadda ɗumin hannunsa ke shigarta. Ita kam ta shiga uku. Wannan aure ta son ya ɗore....Allah na tuba ta faɗi a zuci. "Hamdi?" Ya ɗan matsa hannun. "Kai na yiwa" murmushi ya soma yi ta ƙara da cewa "amma dai Yaya ce ta tilasta min nayi." "Allah Ya biya Ya mafificin alkhairi. Now can I ki..." Bata bari ya gama magana ba ta sanya hannu ta toshe masa baki. "Kaga fa Ya Kamal ya fito." Ta kalli gate ɗin a firgice. Dariya ta bashi ya cire hannun nata ya riƙe shi da ɗaya hannun. "Idan ya ƙaraso sai na ce ya tayani roƙonki. Kinga fa a waje za ki barni for God knows how long." Kamal har ya ƙaraso. Ƙwanƙwasa gilas ya yi ta ɓangaren Taj. Shi kuma ya zuge gilas ɗin ƙasa. "Happiness taƙi yi min sallama kamar bata san iyakata nan ba. In ta shiga ciki sai sanda suka ga damar sako min ita." Sunkuyar da kai tayi don har lokacin hannuwanta suna cikin nasa. Tana ja yana sake riƙewa. Kamal dariya yayi kawai "Mrs Happy haka za mu yi dake?" "Shi za ka zaɓa?" "Da me kike tunani? Ya zaɓeki a kaina?" "Naga wai ni ce ƙarama" tayi kicin kicin da fuska. A take Kamal ya canja sheƙa. "Happy buɗe mata. In ka kaita gida sai ku yi sallamar a can." "To wallahi tayi alƙawari a gabanka" Taj ya sha kunu da ya yi maganar. "Ki yi mu shiga kinji. Su Umma ke su ke jira." "Nayi." Ta faɗa don idanun ƴan uwan su biyu sun hanata sakat. Sama Taj ya yi da gilas ɗin ya kai hannunta guda bakinsa ya sumbata. Hamdi ta rasa inda za ta tsoma ranta don kunya. "Gidanmu ba irin wanda ki ka saba bane Hamdi. Duk inda ake da yawa komai is possible. Don Allah idan an ɓata miki rai ki fara faɗa min kafin su Abba. Zan baki haƙuri a madadin ko waye. Kin ji?" Murmushi tayi har zuci. Ta ɗan matsa hannunsa dake cikin nata sannan ta fita. Kamal na buɗe gate da su ka shiga ciki taji wata murya da ta so ta gane tana yi masa magana. "Ya Kamal basu iso bane?" Hamdi ta bi inda ya kalla da ido. Budurwa ta gani tayi kwalliya ta fitar hankali. Tayi kyau tamkar wata amarya. "Salwa? Saukar yaushe?" Ya ce babu wani jindaɗi a tare da tambayar. "Ɗazun nan na iso. Ina zuwa gidan kuma naga Anti Zahra za ta taho wai yau amaryar Ya Taj za ta zo gaishe da su Hajiya." "Gata ku gaisa." Ya faɗi yana kallon yadda shigarta gabaɗaya ta saɓawa sanin da ya yi mata a baya. "Sannu amarya." Ta ce tana yin gaba "bari naje na taya Ya Taj hira kafin ku fito." Kashewa Hamdi ido tayi wanda Kamal bai lura ba. Ta wuce su ta buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ta fita. Komai ya nemi tsayawa Hamdi da ta tuna yadda su ka yi a waya. Sai da Kamal ya kirata sau biyu taji ta bi bayansa tana tunanin hanyar da zata bi ta nunawa Salwa tayi kuskuren shiga gonarta. RAYUWA DA GIƁI 22 Batul Mamman💖 This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ƙamshi babu ruwansa da gari ko ƙasa. Wuyarta ciniki ya faɗa. Za ku sami undiluted oil perfumes ɗinku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haɗa kwalabe daban daban ki gigita waɗanda ya halatta su ji ƙamshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeta a wannan layin 07065525409. Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate ɗin. Kamal ya yi mamakin ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta ɗan jira shi. Ko kallon Taj ɗin bata yi ba domin ranta a ɓace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu. Kafin Kamal ya ƙarasa gate ɗin sai ga Firdaus. Ƴar wajen Yaya Hajiyayye wadda su ka gama FGC tare da Hamdi. "Anti Hamdiyya Habib Umar" ta kirata da ƙarfi cikin murna. Tana rufe baki sauran jikokin su ka firfito suna yi mata oyoyo. Abin ya bata mamaki don gaskiya idan ta ce ta sa rai da tarba mai kyau daga zuwanta tayi ƙarya. Ƙaruwa mamakin nata ya yi da Firdaus ta rungumeta. "Wai ashe matar Uncle Taj ce ke ban sani ba duk zamanmu a school. Ai da ko ruwa wallahi ba za ki ɗebo ba. Uncle Taj is my favourite." Hamdi tayi murmushi kawai tana mai jin kunya. Firdaus ta ja hannunta su ka shiga ciki. Anti Zahra ta taso da sauri. "Ke matsa min. Ƙanwata ce. Ni zan kaiwa su Hajiya ita." "To duk gidan nan dai idan aka cire Happiness kowa ya san nice ta gaban goshin Happy. So please allow me..." wata ƙanwarsu ta janyeta "sannu da zuwa Sis" "Meye haka jama'a? Ba babba babu yaro?" Umma tayi magana daga ƙofar ɗakinta. Kowa sai ya sami nutsuwa "Za ku barta ta zauna ne ko kuwa sai kun gama tsorata ta da wannan hayaniyar?" Sai a lokacin wata mai yawan murmushi ta zaunar da Hamdi akan kujera. Sai dai tana zaman ta zame jikinta ta koma ƙasa. Akayi akayi sam taƙi komawa kujerar. Ga mayafi ta sa ta rufe fiye da rabin fuskarta. A haka ta gaishesu. Umma da su Hajiya su ka fito su ma. Cike da kunya da ladabi ta gaishesu tamkar iyayenta. Aka tambayeta mutanen gida ta ce suna gaishesu. Bakin Inna kasa rufuwa yayi. Surukar tata tayi mata ta ko ina. Fargabarta ma ta ganin wata halayya da za ta nuna nakasun tarbiyya a tattare da zuri'ar Abba Habibu ta ɓace ɓat. Filin gabatarwa aka shiga inda Bishir ya nuna mata iyayensu da sunayensu. Sannan yabi ƴan uwansa ɗaya bayan ɗaya su ma. Haddacewar dai sai a hankali. A wajen ya nuna mata mata goma sha biyar. Sauran sun yi nisa. Ga jikoki gari guda. Su kaɗai sun ishi juna gayya. "Za a saka ki a family group. A hankali duk za ki gane mu." Yaya Kubra ta faɗi. Tana cikin waɗanda Hamdi ta riƙe sunansu saboda kana kallonta kaga ƴar gayu ajin ƙarshe. Gashi ance likita ce. Ta lura dai duka gidan akwai wata kamanceceniya da ko baka san su ba za ka iya danganta su da juna. Kai ta gyaɗa har lokacin ta kasa buɗe fuskarta da kyau. Hira ce ta ɓarke kowa da irin tambayar da yake yi mata. "A kawo abinci kafin ku cika mata kunne don Allah." "Hajiya ai so muke ta buɗe bakinta." "Baki zai buɗe ne babu abinci?" Mama ta fatattaki jikokin ta ce su tashi su fara ɗauko kwanuka. "Yau bamu ci komai ba muna jiran amaryarmu. Me za ki ci?" Wadda tayi maganar ta fara buɗe food flask. Akwai fried rice wadda taji kayan haɗi da hanta, tuwon shinkafa da miyar agushi, waina (masa), coleslaw, pepper chicken, farfesun kayan ciki da kuma nau'ikan lemo na kwali da ruwan roba. Abu kamar taro, kodayake taron ne tunda yawa garesu. Kai a ƙasa ta ce "Na ƙoshi." "Kada na sake jin zancen ƙoshin nan Hamdiyya. Don Allah ki saki jiki don a gida kike. Girkin yau dukkaninmu uwayenki sai da muka saka hannu." Umma tayi magana tana hararar ƴaƴan nasu "daga cewa za ki zo gaishemu duk su ka baro gidajensu saboda fitina. Ai gashi nan kun cika mata ido ta kasa sakewa." Dariya aka yi. Aka gama ajiye tarin kayan abinci kamar na biki sannan aka shiga zuzzubawa. Hamdi ta lura kusan sa'anni ake haɗawa a tray guda. Firdaus ta nace a haɗasu a tray guda amma fir aunties ɗinta su ka ƙi. Wai matar aure ba sa'arta bace. Basu san ita babu yadda za ayi ta ci abinci da kowa a zuwan farko ba. Kuma ƙila na ƙarshe. "Idan ba za ki iya ci su ba a zubo mana tare." Wani irin shiru falon ya yi na wucin gadi kowa na kallon Inna kamar ba ita tayi maganar ba. Kafin kuma su kwashe da dariya suna hailing ɗinta. Harda masu karambanin ɗauko plate za su zuba musu. Da wani irin sauri Hamdi ta matsa tray mafi kusa da ita harda gyara murya ta ce "Bismillahir Rahmanir Rahim." Waɗanda basu yi dariya da farko ba ma sai da su ka yi yanzu. Cikin ruwan sanyi Inna tayi musu maganinta. Inna ma murmushi tayi. Abinci ya yi daɗi. Ba don gidan surukai bane tabbas cin da Hamdi zata yi sai yafi wanda tayi na baƙunta. Su na ci ana kiran sallar la'asar. Ɗakin Mama aka ce a kai ta tayi sallah a can. Suna tafiya da Firdaus ne ta tambayi Salwa. Don duk abin da ake hankalinta bai bar kallon ƙofa ba. "Gidan nan kowa nada kirki Firdaus. Da ina shigowa na haɗu da wata ƴar uwar taku ma a bakin gate mu ka gaisa. Naga kamar ta tafi." "Kai anya kuwa. Kowa na nan fa." Ba don bata riƙe sunan ba ta ce "sunanta Salma ina jin." "Salwa ko?" Sai kuma ta kalli matan dake zaune ta ce "Ina Anti Salwa ne? Sai yanzu na lura bata nan." Cigiyarta aka fara yi ana kiran Anti Zahra ko ta san inda ta tafi saboda bata cewa kowa za ta fita ba. Ita dai jikinta sanyi ma ya yi. Dama tun a gida da ta rangaɗa wannan uwar kwalliyar hankalinta bai kwanta ba. "To ku kira ta mana. An duba banɗakuna? Ko bacci ya ɗauketa a wani ɗakin?" Cewar Hajiya. Hamdi ta tabbata ko ma mene ne babu hannun ƴan gidan nan, duba da yadda su ka shiga ruɗanin ina ta shiga. Firdaus ta ce musu ai Hamdi ta ce taga fitarta. "Tambayata sunan wadda su ka gaisa a waje tayi shi ne na kula ita ce bata nan." "Da shirin fita ki ka ganta?" Anti Zahra ta tambayi Hamdi. Murmushi tayi don tambayar da take jira kenan dama. "A'a, cewa tayi za ta je wajen shi..." Yaya Hajiyayye ta ce "shi wa?" "Ke kuma komai sai anyi miki gwari gwari ne? Taj take nufi ko Hamdiyya?" Yaya Zulaiha ta tambayeta. Ta sake yin murmushi kawai. Kunyar inda take ba za ta sa ta bari Salwa ta sami biyan buƙata ba. Tayi kaɗan! A yadda tazo mata da raini da isa shi yasa za ta hana ruwa gudu matsawar da igiyar Taj a kanta. Ko sun rabu Salwa ta aure shi ba za ta ce ita ce sila har taji daɗi ba. "Ku kira min ita. Ko Kamal. Ta dawo ciki" Anti Zahra ta faɗi hankalinta a tashe. Yadda tayi yasa kowa kallonta da ayar tambaya. Sai ta wayance wai taga Salwan daga tafiya ta dawo ko abinci bata ci ba su ka fito. Nan kuwa tsoronta kada taje tayi abin da zai zubar musu da mutumci. Domin duk abin da Salwa za ta yi dole a danganta ta da Ahmad. Ita kuwa bata son abin da zai taɓa mutumcin mijinta akan wata shirmen soyayyar da babu aji a ciki. Kamal ɗin aka kira ya ce sun fita da ita da Taj amma ba jimawa za su dawo. "Ya za ku fita da ita babu wanda ya sani?" Umma da ta kira wayar ta tambaye shi. "Gamu nan Umma. Mun kusa gida ba in sha Allahu." Sallah aka tafi yi. Wasu kuma suna ta aikin kwashe kwanuka. Masu aikin gidan dai za su aikatu da wanke wanke. Don ma ba da plate suke ci ba, haɗawa ake yi. Hamdi ta đauro alwala ta tada sallarta a inda aka shimfiɗa mata abin sallah. Shigarta ta kamala ta burge Mama. Taƙi jinin lokacin sallah ya yiwa mata a waje su dinga aron mayafi ko hijabi saboda nasu bai dace da tsayuwa gaban Allah ba. A ganinta rashin daraja addini ne yake sa mata fita da suturar da ba za ta musu sallah ba. Su kansu sun san hakan bai dace da tarbiyya da ma ɗa'a ga addini ba. Da ta idar sake gaishe da Mama tayi bayan ita ma ta idar. "Hamdiyya ina son mu yi magana. Matso kinji." Gaban Hamdi ya ɗan faɗi. Ko faɗa mata zata yi ta fara shirin zama bazawara? "Ina fata kin san komai game da Taj yanzu da alaƙarsa da mahaifinsa?" "Na sani" ta amsa kai a ƙasa. Mama ta numfasa ta ce "Kullum burinmu shi ne ƙila idan ya tashi aure su daidaita. Sai Allah Ya ƙaddara masa aurenki. Wannan ma ya ishi mai hankali tunani." Ta kamo hannunta ta riƙe "a halin yanzu mutumci da martabar mahaifinki da ta mijinki suna hannunki Hamdiyya. Hali da ɗabi'ar da za ki nuna mana ita za ta tabbatar da ɗorewar rigimar Alhaji ko kashe gobarar da ta tashi babu gaira babu dalili." Jin an taɓo Abbanta ne yasa ƙwalla cika mata ido. Wani ɓangare na zuciyarta yana ƙara tunatar da ita laifin mahaifinsu ne da su ke fuskantar wannan abu daga ita har shi. Yayinda wani ɓangaren kuma yake kare Abba a matsayin đan Adam ma'asumi wanda ya cancanci duniya tayi masa uzuri idan ya bayyana tubansa. Da ƙaramar murya ta ce "Me ya kamata na yi?" "Na san ke yarinya ce amma tunda na ganki naji bani ds haufi akan zaɓin da Allah Ya yiwa Taj." Mama ta faɗi tana yi mata murmushi "Alhaji yana son mutane jajirtattu. In kin kula yaran gidan nan kowa baki gare shi. To ƙuruciya su ke samun wannan ƙwarin gwiwa ta rashin gazawa daga gare shi. Saboda haka kada ki yarda ki zama sokuwa. Ko laifi aka yi miki yafi son ki gwada ƙwatarwa kanki ƴanci. Sai abin yafi ƙarfinki ya amince ki nemi wani. Abu na biyu kuma ki kasance a kodayaushe cikin nuna hali na kyakkyawar tarbiyya. Zan so ya gani kuma ya shaida cewa ƴaƴan Habibun da yake ganin ya kauce hanya ya sun cika ƴaƴa ta kowacce fuska. Na ƙarshe kuma ki so mahaifinki da mijinki. Ki nuna masa ke kina ƙaunarsu dasu da sana'ar da Allah bai haramta musu ba. Kina alfahari dasu kuma hakan bai rageki da zama ƴar da shi ko wani zai kasa ƙauna a matsayin suruka ba." A rayuwa akan ce wanin hanin daga Allah baiwa ne. Hamdi ta fahimci haka a yau. A shekaru irin nata ko ma fi wata ba za ta gane mene ne ainihin abin da Mama take so ba. Saboda duka maganar a ɗan dunƙule take fita. Amma yau da gobe saboda tashi a gaban Abba yasa ta gane. Magana da iya zuba zance a wajen cikakken ɗan daudu yana daga cikin alamomin da ake ganesu ma. Ya rage nasa ne nesa ba kusa ba da ya gane yana daga cikin abubuwan dake saurin saka a gane tsohuwar rayuwarsa. A taƙaice Mama so take ita Hamdi ta saye zuciyar Alhaji da halaye masu kyau ta yadda zai gane Habibun da ya raina bai gaza ba wurin tarbiyyar ƴaƴansa. Sannan sana'ar Taj bata cikin dalilan da mutum zai yi fushi da ɗansa. Godiya tayi mata da alƙawarin kamantawa da yardar Allah. "In kin kula gidan nan babu ƴan ubanci tsakanin ƴaƴanmu. Duk da Alhaji ne ya ɗora mu akan turbar zaman lafiya to amma fa akwai ƙoƙari matuƙa daga Hajiya. Daga cikin irin zaman ne alhakin kula da kuma tarbiyar ƴaƴa maza ta dawo hannuna. Ba don Allah Ya tsare ba da tuni a sanadiyar korar Taj komai ya rikice mana. Ni kaina ina ɗorawa kaina laifi domin kuwa ni na ƙarfafa masa gwiwar girki. Fatana da raina da lafiyata in ga lokacin da Alhaji zai shigo da Taj ya damƙawa mahaifiyarsa." Kowane gida akwai nasu kalar damuwar. Tana ganin kamar duk duniya sun fi kowa sai gashi gidan da tun shigowarta komai na jama'ar ciki yake burgeta su ma da nasu. Ɗakin Umma, Mama ta kaita. A nan ma babu kowa sai Umman ita kaɗai zaune akan abin sallah. Suna shiga Mama ta fita ta barta. Umma ta ɗaga hannuwa tana addu'a, Hamdi sai ta ɗaga ita ma har Umma ta kammala ta ce Amin. Umma ta zolayeta da cewa "Wato kin ji ina roƙa muku ƴan bibbiyu sau biyu a shekara shi ne ki ke ta cewa amin ko?" Kunya kamar ta nutse "Allah ban san ita kike yi ba." "Janye Amin ɗin za ki yi?" "Eh" Hamdi ta faɗi da sauri, kunya duk ta ishe ta. "Yanzu addu'ar tawa ce ba kya so?" Sake daburcewa tayi ta ce "A'a ban janye ba. Yi haƙuri don Allah" Umma tayi dariya sosai. "Wasa nake miki kinji Hamdiyya. Zo ki zauna." Ita ma kamar Mama da yi mata bayani akan gidansu babu ɓaraka ts fannin zamantakewa ta fara. Sai abin da ba a rasawa na zaman tare. Ko a cikin ƴaƴa tunda ba a raba siblings da ƴan rigingimunsu. Amma dai duk inda aka je aka dawo su ɗin tsintsiya ne masu maɗauri guda. "Hamdiyya don Allah ki riƙe mijinki riƙon da Allah Ya umarci bayinSa kinji. Ki bawa maraɗa kunya." "In sha Allahu Umma." "Na tambaye shi ya min rantsuwar ba taimako da rufin asiri kaɗai ya so yiwa mahaifinki ba. Auren yake so kuma ke ya zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa. Saboda haka don Allah ki ji, ki ƙi ji. Ki gani, ki ƙi gani. Babu wata rayuwar auren da take ɗari bisa ɗari. Amma indai kun riƙe juna amana za a sami nutsuwa da rahamar da Allah Ya sanya a cikin aure." Wani tunani ne ya ɗarsu a zuciyar Hamdi da Umma ta kaita ɗakin Hajiya. Shin matan gidan nan sun san shirin da mijinsu yake yi a kanta na raba aurenta da Taj ne? Amsar a bakin Hajiyan ta samo ta ba tare da ta tambaya ba. Ita ma kamar ƴan uwanta zancen da ta fara akan zaman lafiyar iyalinsu ne. Shekaru arba'in da ɗoriya suna gina ƴaƴansu akan turba mai ɓullewa. Ba za su taɓa maraba da abin da zai kawo rabuwar kai tsakaninsu ba. "Nayi imanin kin ji daga bakin mahaifinki cewa Alhaji ya bashi wata uku ya san yadda ya yi Taj ya sake ki. Haka ne?" Taurin zuciya irin na Hamdi sai ta kasa kuka. Idanunta ne kawai su ka yi jazur kamar gauta. Ta gyaɗa a hankali. Hajiya ta dafa kafaɗarta da kulawa "Inna ce kaɗai cikinmu bata sani ba sai kuma ƴan uwanku da shi Taj ɗin. Ko kin faɗa masa?" "A'a." "Da kyau. Don Allah ki bar zancen a cikinki. Abin da nake so shi ne ki ginawa kanki matsugunin da babu wanda ya isa ya rabaki da shi. Kina ganin yadda ƴan uwansa su ka karɓeki hannu bibbiyu. Innarsa da danginta kuwa ..." ta kasa ƙarasawa. Haƙiƙa wannan karon akan Taj yayyen Inna da ƙannenta da su ke duk maza sai ɓarin kuɗi suke yi. Takanas babban wan ya turo matarsa ta sanar da Hajiya cewa su za su yi komai na bikin. Kayan gida da Inna ta ce za ta yiwa Hamdi duk an ɗauke musu. Lefen da ƴan uwansa ke haɗawa kawai aka bar musu. Shi ma kuma akwai gudunmawa gagaruma daga garesu. Yadda Taj yake kyautatawa a gidansu da dangin babansa haka su ma can yake yi musu. Ita dai Hamdi zuciyarta tsinkewa ta sake yi. Bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ce "Hajiya maganar mahaifi ba abar wasa bace. Musamman shi da suke da wannan matsalar." "Hamdiyya addu'a nake so ki yi. Ki roƙi Allah ki kuma yi taki bajintar saboda muddin Taj ya fara sakin aure a tsukin lokaci irin wannan wallahi sunansa zai ɓaci. Alhaji bai san wannan hukuncin duka gidan nan zai shafa ba. Za a ce da gaske tunda ubansa ya kore shi ba mutumin arziƙi bane. Sannan ina mai tabbatar miki Innarsa ba za ta zauna ba. Don wannan karon a shirye take. Dama can wa'adin zaman ne bai ƙare ba amma da tabi ta ƴan uwanta da ta daɗe a gida." "Subhanallahi" Hamdi ta faɗi cike da tsoro. "Ƙwarai kuwa. Idan Inna ta tafi kuma Mama...Haj. A'i da ki yi sallah a ɗakinta ma tafiya za ta yi. Saboda kullum gani take laifinta ne Taj ya tashi da son girki." Ya dubi Hamdi da kyau "a yadda ki ka fuskanci gidan nan kina ganin ni da Umma za mu zauna? In kuma duka mu ka tafi yaya makomar shekarun da muka ɓata muna gina ƴaƴanmu akan soyayyar juna da zumunci?" Murya na rawa Hamdi ta ce "Hajiya aikin ya yi min nauyi." "Ke fa mace ce. Kada ki bari na kuma jin wannan kalmar ta gazawa." "Abbana...Yaya ma tana da lalura. Waye zai mutunta abin da zan yi?" "Ubangijin da Ya tayar dake a cikin zuri'arsu, Ya kuma kawoki cikin tamu, Shi zai dafa miki." "To amma ta yaya zan yi abin da aka yi shekaru ba a samu ba?" Har a lokacin zuciyarta ta kasa ganin me su ke so taƙamaimai. "Mace na juya miji Hamdiyya. Mu dai namu ina jin a kan shi aka ƙare kafiya da taurin kai" Hajiya ta faɗi tana dariya. Hamdi ma murmushi tayi. "Duk ya bi ya ɓata mana yara da halin. Sai dai kawai na wani yafi na wani. Tunda Taj ya hana shigo masa gida ba iyalin Taj ba ina ganin yau da gobe yana ganinki da kyawawan halayenki zai gane ɗansa da baban naki da yake ƙi basu ragu da komai ba akan sana'arsu. Allah Yasa kin fahimceni." "Na gane Hajiya. Amma..." "Za ki iya Hamdiyya. Wallahi ina jiye mana ranar da Abu za ta botsare a gidan nan. Mai haƙuri bai iya fushi ba. Komai na zaman lafiyarmu zai tashi a banza. Ƴaƴa ashirin da takwas idan kansu ya rabu yaya zamu yi?" Yau dai bata sani ba kuka ya kamata tayi ko dariya. Duk inda ta shiga magana ɗaya su ke yi mata. Ina ita ina ɗaukar wannan nauyin? Alhajin da ya raina mahaifinta bata jin za ta taɓa yi masa abin da zai burge shi har ya yafewa wani. Hajiya tashi tayi ta ce mata su je ɗakin Inna. Sun sameta da yawancin ƴan matan jikokin nasu. Zolayarta su ke son rai tana biye musu. "Ku zo ku fita." Hajiya ta nuna musu ƙofa. Babu wadda tayi gardama sai Hayat ɗin Ahmad da ya dage ba zai fita ba. "Ƙyale shi Hajiya" Inna ta kalli Hamdi tayi murmushi "iyayenki na san duka sun gama yi miki nasiha. Nawa kawai tuni ne akan ki riƙe maganganunsu domin su ne iyayen Taj. Sai Amma dake Abuja. Ya taɓa haɗaku kuwa?" "A'a" Hamdi ta bata amsa "Ai ta ce tana tafe jibi. Ita ma ba za ta bari su yi haɗuwar wajen biki ba tunda an riga an ɗaura." Ta nunawa Hamdi kujera "Zauna ba a rasa abin faɗa miki ba. Sai dai in kuma kara ce ba za ki yiwa Mama ba." Cewar Hajiya ga Inna. Bayan ta fita Hamdi taji kunyar da tafi ta sauran ɗakunan. Innar Taj tana da wani irin kwarjini da cika ido. "Kina da zaɓin kalar kayan ɗakin da ki ke so?" Tambayar a bazata ta zo mata. Ta ɗaga kai daga sunkuyon da tayi. "A'a." "Taso ki gani" Inna ta nuna mata waje kusa da ita akan makeken gadonta da tun shigowar Hamdi take santinsa a zuciyarta. Kasa tashi tayi sai da Inna ta maimaita maganar tare da umarnin lallai ta taso. A ɗofane ta zauna. Inna ta buɗe catalogue ta ɗora mata a cinya. "Buɗe ki zaɓi wanda ya yi miki. Sai kuma ki zaɓarwa mijinki." Yawu ta haɗiya. Jikinta har wani rawa yake tana jin sanyi sanyi na ratsa ƙasusuwanta. Wannan fa ita ta haifi Taj. Da Yaya za ta ga zaman da tayi kusa da ita irin wannan ƙarshenta sai ta ɓallata. "Hamdi" Ita kaɗai ta kirata da sunan da ake kiranta a gida. Wannan yasa taji ranta ya đan sake. Inna ta cigaba da magana "kin shiga ɗakuna uku na surukai. Nan kuma ɗakin na mamanki ne. Don Allah ki ɗaukeni a matsayinta domin hakan ne kaɗai zai bani damar yi miki riƙon ƴar cikina." Cikin rashin jindaɗi Hamdi ta ce "Ki yi haƙuri." "Ba fushi nayi ba. So nake ki ajiye komai ki saurareni da kyau." Hamdi ta miƙa mata hankalinta kacokan. Inna ta fara da yiwa Abba da Yaya addu'a da su ka haifi matar da ta auri Taj. Saboda ta jima tana tsoron kada aurensa ya tashi iyayen ƴar su fasa saboda korarsa da mahaifins ya yi. Abu na biyu kuwa fito mata tayi a mutum. So take Hamdi ta amsa sunanta na matar Taj ba tare da taji ɗar a zuciyarta ba. "Indai mijinki ne to ki manta da matsayinsa ki kama abinki a hannu. Na san komai da ƴan uwana su ke ɓoyewa game da sharaɗin da Alhaji ya bawa mahaifinki. Ni kuma in Allah Yaso Ya yarda kin shigo kenan. Allah ba zai bawa kowa damar ganin ƙarshen auren ba ballantana su cigaba da ɗora zarginsu. Hatta ƴan uwanki ina yi musu fatan samun nasarar zaman gidajensu. Abu ƙanƙani ne zai faru a ɗorawa babanku laifi. Idan kuwa ta ɓangarenki ne to da uba da miji duka a kunnuwanki za ki ji ana cin zarafinsu." Darasi mai girma Inna ta ɗora mata, saɓanin su Hajiya da aikin da su ka bata ne mai girman. Akan shekarunta taji kamar an ƙara mata ashirin saboda yadda take ganin ba za ta iya ba. Amma kuma ta sami ƙwarin gwiwa sosai. "Taj yana son ki. Ki sa ya ƙara ƙaunarki Hamdi. Ki hana zuciyarsa sakat ta yadda aurenku ba zai sami tangarɗa daga yinsa ba don Allah." Bayan ta gama ɗaukar karatun mai girma sannan Inna ta kira Firdaus ta ce su koma falo. A can aka cigaba da hira wadda ita dai amsarta bata wuce murmushi sai eh ko a'a. Tunanin da aka barta dashi yafi ƙarfinta. Abu guda ta fahimta shi ne matan gidan duka basa son auren nan ya mutu. Gashi Abbanta ya tsorata da barazanar Alhaji yana ta yi mata tuni. Cikin dabara aka sa Firdaus ta tambayeta size ɗin da taƙi turawa Taj. Da ƙyar ita ma ɗin ta sanar da ita. Sannan cikin ƙanen Taj wata ta aunata gwajin riga da siket da na doguwar riga. Sai gashi kafin magrib ta soma sakewa dasu. Naƙasun da aka samu bai wuce na rashin shigowar Kamal ko Salwa ba. Sannan ko sau ɗaya Taj bai kirata ba. Ta shaƙa tayi fam tana jiran ya tsikareta ta fashe. Ita ma Anti Zahra har fargabar zuwan Ahmad ɗaukarsu take yi. Ta san shi sarai. Laifinta zai fara gani kafin ya saukewa ƙanwar tasa kwandon masifa. *** Ikon Allah Taj da Kamal su ka gani yayinda Salwa ta soma kuka tun a bakin gate wai Taj yana wulaƙanta ta. Aka yi ta rarrashinta taƙi shiru saboda makirci. A dole Kamal ya ce ta shiga motar. Shi ne su ka tafi Happy Taj. Office ɗin Kamal dake cikin boutique ɗinsa su ka shiga. Ta sami wuri ta zauna tana goge ƙwalla. "Salwa tunda ku ke da Taj ya taɓa cewa yana son ki?" Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Taj yaji a duniya yanzu babu abin da ya tsana kamar mace ta dinga wasa da yatsunta. Tsaki ya ja ta dubi Kamal. "Kana ganin abin da yake yi min? Meye laifina don na ce ina son shi? Ba fa cewa nayi ya saki yarinyar da ya aura ba." "Ki dinga gyara kalamanki akan matata. Sannan kin fi kowa sanin cewa ba zan juyo ba. Ba yaudararki nayi ba so don't give me that crap wai in haɗaku." "Haɗamu ma bai taso ba tunda Alhaji ya ce..." "A wurin wa ki ka ji wannan maganar?" Ya tambayeta muryarsa a sama. "A wurin Yaya mana." Ta bashi amsa tana tura baki. Kallonsu Kamal ya yi don bai gane komai ba ya ce "wace magana ce Happy?" A taƙaice Taj ya yi masa bayanin da bai yi ba saboda rashin lafiyarsa. "Bana jin Yaya zai faɗa mata." Kamal ya faɗi yana kallonta "a ina ki ka ji?" Rigimar da Mami ta ce ta haddasa tsakanin Taj da duk wanda zai goyi bayan yaƙi aurenta ta tuna. Ta kuwa taɓe baki cike da raini. "Ina ruwanka? Kai dai burinka ba ya saki Hamdi ka aura ba?" Duka su biyu zabura su ka yi cikin ɓacin rai. "Salwa!" Kamal ya yi mata tsawar da a tunaninta ba zai taɓa iyawa ba saboda yafi Taj sanyin hali. "Ki kiyayeni wallahi." "Idan naƙi fa? Ya Kamal na fa san kana son yarinyar nan. Ko ba abin da ya kwantar da kai ba kenan? Me yasa baka taɓa yin wani ciwon allergy ba sai da Ya Taj ya aureta? Wallahi zan iya dafa izu sittin baka da wani allergy." "Kinga Salwa, kalleni nan" Taj ya yi mata magana yana cijewa don ta riga ta kai shi matakin da yake son taɓa lafiyarta. Wani abu da bai taɓa yi ba ko da wasa. Idanunta a bushe ta kalle shi. Bai san bata tunkari wannan rigimar ba sai da ta shirya mata daga gida. "Ina jin ka" "Zo ki tafi kafin wani cikinmu ya yi miki rauni." "Please Taj kada ka biye mata. Ka bar zancen raunin nan kada wani ma yaji." Kamal ya yi maganar da kana gani za ka gane yadda yake ƙoƙarin danne ɓacin ransa. "Za ka aureni Ya Taj. Allah kuwa..." Kawai ta sa kai ta fita. Bayan tafiyarta Kamal ya zo zai yi masa rantsuwar zancenta ƙarya ne Taj ya dakatar dashi. "Idan kana tunanin na yarda da zancenta har ina buƙatar ka wanke kanka to gaskiya akwai matsala tsakaninmu." Murmushi Kamal ya yi "Allah Ya huci zuciyarka." "Amma wane irin ciwo gareka Happiness?" Koda Kamal ya juya ya kalli Taj sai yaga babu alamun wasa a tare dashi. Allah Ya taimake shi ya fara ajiye magungunan allergy su antihistamine saboda rana irin wannan. Durowar magungunan ya buɗe ya fiddosu duka. "Ka ce baka yarda da zancenta ba." "Daga cikin addu'ar da nake yawan yi mana harda kada Allah Ya haɗamu son abu guda da mutum biyu basa tarayya a kansa. Zancen ciwo kuwa ai rantsuwa tayi. Tunda tana sa gaba gabas zancenta zai iya zama gaskiya." Ɗaya bayan ɗaya yabi magungunan ya dudduba. Pain relievers ne da wanda su ka danganci kwantar da abin da ya shafi allergy. "Allah Ya baka lafiya Happiness." "Amin." *** Tafiyar minti biyar a mota za ta kai mutum wani babban mall da ya yi shura a titin kafin a gina Happy Taj. Ƴan Kano da son sabon abu na yayi kusan kowa ka taɓa zai ce maka ya yi siyayya a Glory Mall. Wurin shaƙe yake da kaya na alfarma. Sannan akwai snacks irinsu shawarma, small chops, popcorn, ice cream da sauransu. Har event centre garesu a ciki. Wurin mallakar wani hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ya damƙawa babban ɗansa alhakin kula da shi. Kuma a shekara biyu da rabin farko uban ya yi alfahari da ɗansa. Ciniki ake yi na bugawa a jarida. Komai ya soma taɓarɓare musu cikin abin da bai fi sati guda da buɗe Happy Taj ba. Idan kaya ake so boutique ɗin Kamal yana da na kowanne jinsi manya da yara. Abin da ya shafi abinci kuwa harda wanda mutane basu sani ba akwai a ɓangaren Taj. Kamar wasa su ka dinga tunanin ko irin abin nan ne na ɗokin sabon waje. Idan an kwana biyu abu zai koma normal. Sai aka yi rashin sa'a kasuwa da gaske take damawa da su Taj cikin albarkar Allah. Haka kawai mutane su ka fara janye jiki. Ciniki ya yi wani irin ja da baya mara daɗi. Alh. Usaini ya shiga gagarumar matsala da mahaifinsa. Inda rashin tawakkali yasa uban ya taso shi a gaba da muggan kalamai da tsoratarwa. Indai ciniki bai daidaita ba to ya kwana da sanin zai karɓe mall ɗinsa ne ya bawa wani daban cikin ƴaƴansa. Wannan abu ya yi matuƙar tayar masa da hankali. Ya shiga faɗi tashin hanyar dawo da martabar mall ɗinsu amma abu yaci tura. Har an kai wasu masu kai musu kaya sun fara janye jiki. A irin wannan yanayin na neman hanya kowacce iri ce Allah Ya haɗa Alh. Usaini da Ummi. Cutar hassada tayi mata lulluɓi tun daga kai har tafin ƙafa a lokacin da taji labarin auren Hamdi da mamallakin Happy Taj. Ranar harda kuka sai da tayi. Zuciyarta a cunkushe tana fama da takaicin yadda ƴar ɗan daudu ta sami miji irin Taj. Ta taɓa zuwa wajen da wani saurayinta. Yadda taga Taj ta san wadda ta fita ma bata isa ta aure shi ba, balle kuma Hamdin da bata kama ƙafarta a gayu da rufin asiri ba. Wani abin kayan haushin kuma jan kunne da gargaɗin iyayenta da yayanta akan ƙanwar Hamdi da ya aura. Ko kallon banza ta yiwa Zee ya yi alƙawarin canja mata kamanni. Ranar da ta haɗu da Alh. Usaini, cikin jin zafin auren Hamdi ta fito ds niyyar zuwa Happy Taj ta ɓata ta a gaban Taj. Sai da ta iso kuma ta rasa me ya kawo mata tsoro ta kasa ƙarasawa. Haka kawai ƙafafunta su ka kaita Glory mall. Ta je wurin snacks ta sayi meatpie da lemo ta sami wuri tana ci. Amma hankalinta gabaɗaya yana kan ginin Happy Taj. "Ki tafi can mana idan nan bai yi miki ba." Kallonsa Ummi tayi za ta faɗi baƙar sai ta adana. Mutumin zai yi shekara arba'in da biyar. Ya sha shadda ƴar ubansu da ɗinki na alhazawan birni. Ga ƙamshi na waɗanda naira ta tsaga jikinsu ta zauna da kyau. Murmushi tayi masa "ba kallon son zuwa nake ba. Fatan abin da zai zo ya tayar da wurin gabaɗaya koda gobara ce nake yi." Ta kashe masa ido. "Ko zan san dalili?" Amsarta tasa ya sami interest akanta. "Kaji daɗin kaini gaba? Allah Ya kiyaye." Ta tashi tsaye. "Ko kusa. Nima burina kenan.." ya kashe mata ido yadda tayi masa. "Dalili?" "Sun kashe min kasuwar mall ɗina mana." Zama ta koma tayi "nan wurinka ne?" "Eh. Amma yana fuskantar barazanar rufewa saboda su." Dariyar mugunta Ummi tayi a zuci. Daga ranar su ka ƙulla ita da Alh. Usaini. Suna neman hanyar da za su nakasa Taj domin su gurgunta masa sana'a. A wannan rana ta asabar da Salwa ta fito daga Happy Taj cikin ɓacin rai, ta faɗa Glory Mall saboda akwai mai POS daga bakin gate ɗinsu. Tana jiran mutumin ya idar daga sallar la'sar a gefen ƴar container ɗinsa take waya da Mami. A ciki take zayyane mata duk fa abin da ta ce tayi ta gwada amma ƙarshe Taj yaci mutumcinta. "Ni dai Mami da kin barni naje masa a yadda nake. Na tabbata idan ina kwantar da kai zai dube ni." Zaginta Mamin tayi ta ce mata kuma ta kwantar da hankalinta. Ta sanar da mahaifinsu ya ce zai kira Alhajin su yi magana. Tana da yaƙinin yadda Alhaji yake ragawa Salwa don mutumcin babanta da yake gani nw. Duk taurin kansa ba zai ƙi tayin ƴa ba. Musamman tunda ba son wadda Taj ɗin ya aura yake yi ba. "Kin nuna musu kin san baya son auren?" "Eh, kuma ban faɗa musu cewa waya naji Yaya Ahmad yana yi da matan gidansu yana sanar dasu ba. Har wani cewa yake su yi wani abu kada a raba Taj da wadda yake so. Ni ko oho." "Ki daina yin komai. Da kansu za su nemi ki idan babanki ya yi masa magana." Wayarta duka a kunnuwan Ummi da Alh. Usaini waɗanda su ka yiwa juna wani irin kallo gami da murmushi. Tana gama wayar Ummi ta matsa kusa da ita su ka gaisa. Sai ta nuna kamar ita ma mai POS ɗin take jira. Abin ka da mata in an haɗu. Hira a taɓa nan a taɓa can sai gashi sun yi exchanging number. Bayan Salwa ta ciri kuɗin ne ta fito Kamal ya kirata. Babu ja in ja ta faɗa masa inda take. Shi ne su ka ɗauketa don darajar Ahmad kawai. A hanya harda basu haƙuri wai ranta ne ya ɓaci. Babu wanda ya kulata a cikinsu har su ka isa gidan. Taj ya yi zamansa a mota. "Happiness ka turo min ita in kaita gida kafin magrib." Salwa bata ce musu komai ba tayi wucewarta ciki. Ganin Kamal bai shigo ba ta tsaya ta goga hoda da lipgloss kafin ta shiga ciki. Hayaniyar mutan gidan taji daga ɗan korido ɗin da ake ajiye takalma kafin a shiga falon. Ta ƙara yin tsaki. Bata san za ta ƙi mutanen nan ba sai da taga yadda aka dinga kai kawo akan zuwan Hamdi. Yanzu kuma da alama hirar ma da ita suke yi. Sallama tayi ta shiga da wani irin farinciki a fuskarta. Bata sha wahalar haɗa ido da Hamdi ba don ita ma ɗin sallamar tasa ta ɗaga kai ta kalli ƙofa. Murmushin nasara ta sakar mata. Hamdi ta mayar mata. Daga ita har Taj ɗin sai ta fanshe wannan ɓacin ran da su ka sa ta wuni cikinsa. "Salwa ina ki ka je?" Ɗan firgita tayi domin kuwa Ahmad ne ya yi tambayar da kakkausar murya. "Da Ya Taj muka fita. Cewa ya yi na raka shi Happy Taj. Shi ne mu kaje harda Ya Kamal" "Bangane ba? Ya zai kawo matarsa kuma ya yi wani wajen. To da izinin wa ma ki ka fita?" Kafin ta bawa Yaya Zulaiha amsa Kamal ya shigo. Sai ta canja akalar tambayar. "Ko dai soyayya ku ke da Kamal?" Da wani irin sauri ya ce "Allah Ya kiyaye. Ina da wadda nake so." Jama'ar falon su ka kama ihun murna. Harda masu cewa ko a dakatar da bikin Taj saboda dama indai da amana tare ya kamata su yi aure. Wannan amsa ta Kamal ta ɓakanta ran Salwa. Yadda ya faɗa tamkar wata abar ƙyama. Ahmad kansa sai da yaji babu daɗi. Anti Zahra ta kallesu su biyun. Idan Salwa ta cigaba da zama dasu za a iya samun matsala tsakaninsa da ƴan uwansa. Ko me za ta yi ita ma jininsa ce. "Ku tashi mu tafi" ya ce da Anti Zahra, bana son Magariba tayi min. "Kai Ahmad, kamar kana dawa? Don Allah ka zauna." "Ai mun gaisa da ƙanwar tawa ko?" Ya yiwa Hamdi murmushi. "An kusa kira Yaya. So kake Ya Taj ya yi sallah shi kaɗai?" Bishir ya ce. Fin ƙarfi aka yiwa Ahmad. So yake kawai su shiga mota ya gamu da Salwa. A dole ya bi ƙannensa waje su ka tare cikin motar Taj abin tausayi suna hira. Aka sake tashi yin sallah. Hamdi ta koma ɗakin Mama. Salwa sai ta faki ido ta bi bayanta. Su Mama suna ɗakin Umma ana ta shirye shirye. "Washhh. Wannan zirga zirga Ya Taj duk ya tara min gajiya." Ƙin kulata Hamdi tayi. Kowa yaci tuwo da ita ai miya ya sha. Darajar inda su ke yanzu yasa ta kama kanta. Amma ramuwa kam zata yi gwargadon abin da aka yi mata! *** Gayya guda aka rako Hamdi bakin gate da sha tara ta arziƙi. Har ta dinga jin wani iri saboda bata kawo musu komai ba. Yawancin kowa a bayan mota ya ajiye kyautarsa. Banda likitar gidan. Yaya Kubra a hannu ta damƙa mata wata baƙar pepper bag da aka rubuta Scentmania a jiki. Ƙamshi a take ya cika gaban motar tun ba a buɗe ba. Ya haɗe da sanyin AC sai ya bada wani irin ni'imtaccen yanayi. "Zamu yi waya in miki bayanin turarukan kinji. Mun kuma gode da wannan ziyara." "Nima nagode sosai. Allah Ya saka muku da alkhairi." Suna ta ɗagawa juna hannu aka rabu a mutumce. Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Taga ta zubawa idanu tana kallon gilmawar ababen hawa da fitilunsu. Taj ya kalleta yafi a ƙirga ya tabbatar da gaske shi ne bata son kulawa. Murmushi ya yi. Ya taɓa wayarsa wanda Hamdi ta gani da wutsiyar ido amma ta share. "Hello, Salwa..." Iya abin da taji ya ce kenan ta juya a fusace su ka haɗa ido. Wayar a gefe ya ajiyeta. Babu kuma wani abu da zai nuna mata wayar yake yi. Dariyar kamata ya fara sai yaga babu fuska sam. Ta tsuke baki kawai ta sake juyawa. Har wani numfashi mai nauyi ya kula tana saukewa. Gabaɗaya sai yaji ya kasa sukuni. Dama ya san za ta ji haushi. Amma ya yi zaton za ta jira bayani daga gare shi. "Mrs Happy" Shiru. "Hamdi" sunan nan har tafin ƙafarta take jinsa idan ya faɗa amma ko motsi bata yi ba. "Please ki juyo.." nan ma biris tayi dashi " to kada ki ga laifina duk abin da ya biyo baya." Gyaran murya taji ya fara ta taɓe baki. Wato zai fara yi mata daɗin bakin maza da take ji ....katse mata zancen zucin ya yi. "Dil ne yeh kaha hain dil se (my heart has said this to your heart)" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Banda waƙar India don Allah. Wallahi kunya ma nake ji. Bana son namiji yana..." "Mohabbat ho gayi hai tumse (I have fallen in love with you)" "Na shiga uku" Hamdi ta sanya hannuwanta biyu ta toshe kunnuwanta "ka bari don Allah zan saurareka." "Meri jaan, mere dilbar (my life, my love)." "Ya Taj wasa nake. Ba ma fushi nayi ba..." "Mere aitbaar karlo (have faith in me)" "Happyyy" ta faɗi kamar tayi kuka wai yau ita ce miji yake yiwa waƙar india. "Jitna beqarar hoon main (how much restless I am)" Titi yake kallo abinsa yana sakin baiti. Ta rasa yadda zata yi dashi. Kawai sai ta kai hannuwanta ta cupping fuskarsa wanda ya sanya shi ɗauke wuta na wucin gadi. "Allah na haƙura." Ta fada a hankali. Gefen titi ya gangara da motar ya ɗaga handbrake tare da canja giya zuwa 'P'. Ya juyo su ka haɗa ido har lokacin bata cire hannuwanta daga fuskarsa ba. Shan kunu ya yi "Ki barni in ƙarasa. Ba ke nake yiwa ba." Ita kuma ta marairaice masa "Don Allah kayi haƙuri to sai na fita." Ƙwayar idanunta yake kallo sai ta rufe idon. "Can I have that kiss now?" Zame hannuwanta ta soma yi daga fuskarsa ya janyota gabaɗaya. Garin ya ɗorata a cinyarsa handbrake ya sauka. Motar ta ɗan yi gaba amma ba da sauri ba saboda giyar da ya canja. Rungume shi tayi ƙamƙam tana salati ta sanya fuskarta a tsakiyar ƙirjin shi. "Wayyo Allah Abbana...Yaya..." Bata san lokacin da ya sake tsayar da motar ba. Hannunsa đaya kawai taji a ƙasan haɓarta ya ɗago kanta sama. "Salwa bata da matsayi ko kaɗan a wajena kinji." Kai ta gyaɗa a hankali. "Fitar da muka yi ba abin da kike tunani bane. Happiness ne yake ƙoƙarin fahimtar da ita ta haƙura." "Ai na yarda." "Akwai waƙa da ta dace da irin wannan yanayin." Ya ɗage gira. "Kada kayi don Allah." "Ke dai???" "Bana so." Ta turo baki. "Hamdi." "Na'am." Ta ce tana mai jin nauyinsa don yaƙi sakinta balle ta koma mazauninta. "I love you." Ƙasa ta so yi da fuskarta don kunyar yanzu tafi ko yaushe. Sai dai Taj yaci alwashin yau sai ya rage wani abu a kunyar nan ya tafi dashi gida. Shammatarta ya yi kamar zai yi magana taji saukar leɓensa akan nata. He was so gentle amma ya kashe mata jiki har ta sake narkewa a jikinsa bata sani ba. Rungumeta yayi a haka kanta a gefen kafaɗarsa kamar mai bacci. Shi kuwa wani irin contentment ya samu ds nutsuwa a zuciyarsa. Basu yi aune ba su ka ji ana ƙwanƙwasa gilas ḍin motar. Mutanen dake waje suna cewa ko lalacewa tayi ko kuma mai ita wani abu ya same shi. Kamar ƙifta ido Hamdi ta koma wurinta tana raba idanu. Taj ya kalli mutanen ya ga da wuya su fahimci matarsa ce idan su ka gan shi da mace. Kawai sai ya canja giya ya yi gaba. Shi da Hamdi su ka haɗa ido su ka kama dariya. _Uwargida....I see you! SonSo Sis Juwairiyya_ RAYUWA DA GIƁI 23 Batul Mamman Har su ka ƙarasa gida idan sun kalli juna sai sun yi murmushi. Abin da ya ɗaurewa Hamdi kai shi ne yadda Taj har wani kawar da kai gefe yake irin na masu jin kunya. To ai ita ma kunyar take ji. Kuma ita ya dace ta dinga yin haka. Sai gashi kafin tayi yake yi. Gajiya tayi lokacin sun iso layinsu ta kalle shi. "Wai mene ne?" Gefe ya kaɗa kai yana wani rufe ido "Awwnnnnn, ni ki daina tambayata. Kin fi ni sanin ko mene ne." Murmushin fuskar Hamdi ɗaukewa yayi. Ta soma harararsa. "Banda waƙa kuma harda irin haka kake yi?" "Irin yaya?" Ya tambaya kamar bai gane manufarta ba. "Meye wani awwnnn don Allah?" Hannu ya kai ya shafa kumatunta "Saboda ina son ganin wannan hararar da juya idanun naki. You always look cute." Murmushi ta soma yi ya kuwa sake cewa "awwnnnn" yana dafa saitin zuciyarsa. Wannan karon dariya tayi. Irin dariyar da bai taɓa gani daga gareta ba. Zuciyarta tayi fari kamar auduga. "Kin san wani abu? Zo mu shiga ciki kafin haƙurin Abba ya ƙare." Bakin ƙofar gidansu ta kalla. Ai kuwa Abbanta ne yake ɗan leƙowa. Bai yi zaton za su yi dare ba. Kuma sun iso ɗin ma taƙi fitowa. Shi ne ya kasa sukuni. Kada fa ta biyewa Taj al'amari ya kwaɓe a gaba. "Zan kira ki idan naje gida. I hope ba da wuri ki ke bacci ba." Bata iya bashi amsa ba da ta hango inuwar Abban da gaske. Kamar an tsikareta ta fito da sauri. Tana hango shi ya koma cikin gida ta bi bayansa. Taj ya yi murmushi kawai. Ya juya baya zai yi ribas ya yi arba da ledojin da ƴan uwansa su ka ajiye mata. Parking ya gyara ya ɗebi yadda hannuwansa za su iya ɗauka ya je ƙofar gidan yana sallama. Caraf yaji Abba yana yiwa Hamdi faɗan kada ta manta da maganarsu. Shi ba zai iya ja da Alh. Hayatu ba. Jin sallamarsa yasa shi yin shiru. Hamdi kuma ta ruga ciki da sauri. "Taj baka tafi ba?" Ya fito waje. "Saƙonta ne ta manta." Ya nuna ledojin hannunsa. "Harda wahala haka?" "Ƙanwarsu su ka yiwa. Bari na shigar mata dasu." Taj ya wuce ciki kafin Abban ya ce shi zai karɓa. Hakan zai zama raini ma. A tsakar gidan ya sake sallama, Yaya ta amsa da yi masa izinin shiga falon. Akan kujera ya ajiye ledojin ya ce da saura. Ta saki baki har yaje ya dawo. Lokacin ita da Abba ne a falon. Waɗanda ya dawo dasu har sun fi na farkon yawa. "Mene ne haka Taj? Daga zuwa gaishe su kuma sai ka haɗota da wannan kayan?" "Babu ruwana Yaya. Ƴan uwanta ne su ka bata." Yaya dai bata jidaɗi ba. Ta san kwaɗayi ba halin Hamdi bane to amma za a iya fassara ta dashi ga wanda bai santa ba in yaga kayan. Da dai bata karɓa ba. Kiranta tayi ta dawo falon da sauri don kiran ta san na faɗa ne. Kaya dama ta tafi cirewa. Wata free doguwar riga ta saka da hula a kanta. "Me yasa ki ka karɓo kayan nan Hamdi? Tarbiyyar gidan nan kenan?" Durƙusawa Hamdi tayi a gaban kujerar da ya zube kayan tana ƙare musu kallo. Ita kanta bata san sun kai haka ba. "Allah Yaya ba roƙa nayi ba. Ba ma a hannuna su ka bani ba." Kusa da ita Taj ya dawo ya zauna a ƙasa ya fara sauko da kayan gabansu. "Yaya yanzu abin hannun ƴan uwana kike faɗa a kai? Kin san da roƙa tayi nima ba zan yarda mu taho dasu ba ko?" Yaya ta ce "Kada ka kare mata. Ai ta san irin abin da ya dace da wanda bai dace ba." Hamdi ta sunkuyar da kai ta ce "Ki yi haƙuri." "Ni ya kamata na bata haƙuri. Na zata mun zama ɗaya ne ko ban aureki ba shi yasa ban ɗauki karɓar kayan a matsayin laifi ba." Ya yi wani iri da fuska yadda za a tausaya masa "a zatona na kai matsayin da zan iya tambayar Halifa da yake ƙarami abu idan ina so. Na ɗauka hakan ne a wajenku ku ma. Kuskuren daga gareni ne. Ki yi haƙuri." Yaya dariya ta kama yi. Abba kuwa ya girgiza kai don dama ya san za a rina. "Anya Taj ba ɓatan kai kayi na zaɓen aiki ba? Da lauya ka dace. Yanzu Fisabilillah wannan marairaicewar duk don nayi maganar karɓar kaya ne?" Da rashin jindaɗi kamar gaske ya ce "To Yaya abin hannun ƴan gidanmu ai baya cikin wanda za a yi mata faɗa a kai ko?" "Baya ciki. Magana ma dai ta wuce." Ya kalli Abba dake yi musu dariya da Hamdi da kana ganinta ka san taji daɗin ceton da ya yi mata a hannun Yaya. "Gara dai na baki haƙuri kuma nan gaba duk mu kiyaye." "Nace magana ta wuce Taj." "Mungode. In sha Allah zan yi musu magana su ma kada su sake..." "Ya Rabbi. Taj a bar maganar nan. Ni na fara kuma na janye." Yaya ta faɗi da ta rasa yadda za tayi dashi ya yi shiru. Tashi ma tayi tace musu sai da safe. In ta biyewa Taj sai ta koma basu haƙuri tana tumami a ƙasa. Ai kuwa su ka sanya dariya harda shi uban gayyar. Yaya da Abba na miƙewa ya ɗaga hannunsa yana kallon Hamdi. Bata kula da cewa basu gama fita ba ta tafa dashi a hankali. Yaya na gani ta ƙara sauri. Abba yabi bayanta yana dariya. "Ai naga kayan amma ban ce komai ba saboda sanin halinsa. Da yanzu muna ƙofar gida yana kalallameni yadda ya yi miki." "Ka san Allah? Zuciyata fes nake jinta. Sajida da Zee duka mazansu su na son su. Hamdi kuwa nayi zaton Allah auren rufin asiri ne. Ashe da gaske yake da yace yana sonta." "Da kin tuna Yaya Hayatu sai in ce miki halinsu guda. Kaifi ɗaya ne. Kawai dai shi bashi da tsatstsauran ra'ayin uban ne." "Ita ma ja'ira anya bata son shi kuwa? Da tabi ta ƙulla masa kafin su haɗu. Ban zata za a sami kanta da wuri ba haka. Amma yanzu ko makaho ya san inda zuciyarta ta dosa." Abba jikinsa duk ya yi sanyi da irin murnar da take yi da kuma gaskata batun Hamdi na son Taj. "Uwar zamani. Kina nan kina zancen soyayyar ƴaƴanki." Tayi dariya "a uwar ɗaka ba. Da mahaifinsu." Zee ce ta tayata kwashe kayan zuwa ɗakin Abba bayan tafiyar Taj. Tafiyar ma don dai kawai dare ya soma tunda an idar da Isha'i. Ba don haka ba yadda ya soma samun kan amaryar tasa da sai abin da aka gani. * Washegari kamar yadda su ka shirya zuwa gidan Sajida, Zee da Hamdi sun kammala ayyukansu na gida da wurwuri. Tsabar ɗokin son ganin ƴar uwar tasu da aka hana su yi da wuri ko ƴar cacar bakin da su ka saba ba ayi ba. Yaya zuba musu idanu kawai tayi. Sai gasu shaɗaya da rabi sun fito cikin shiri. "Wadda ta san ta tambayi mijinta ta zo ta wuce. Wadda bata tam...." Hamdi ce ta fara cewa "Innalillahi" hannunta na sauri ta buɗe jaka ta ɗauko waya za ta kira Taj, Yaya ta ce ba za ta lamunce titsiye ba. "Tunda ku ka fara zancen nan ai saboda nauyin dake kanku yasa na hanaku wannan ziyarar ta rashin kan gado da ake yiwa amare da zarar sun tare. Amma ban faɗa muku izinin fita ya bar hannunmu ba?" Idanun Zee harda ƙwalla ta soma roƙonta "don Allah ki bari mu tambaya yanzu. Allah ni mantawa ma nake yi." "Haƙƙun, ai kuwa sai a fara shirin tariyarku tunda zaman gida ya sa kun manta darajar da Allah ya yi muku. Ƙarshenta a waje ma idan wani ya yi muku magana sauraronsa za ku yi saboda kun manta." Zamanta tayi akan kujera tana kallon ƴaƴan nata. Babu wadda bata tunawa ta kira mijinta ta nemi izinin fitar ba aƙalla sau uku. Idan tayi magana sai su hau dariya suna tsokanar juna. Jiya da daddare har za ta sake yi musu tuni Abba ya ce ta ƙyalesu. Indai basu yi da wuri ba to kira cikin dare ko da safe duk ɗaya ne. Titse ne wanda maza da yawa basa so. "Yaya don Allah." Hamdi ta sake roƙonta kamar tayi kuka. "Kun san babu abin da naƙi kamar mutum ya dinga kira min mantuwa. Maganar nan mun yi yafi sau nawa. Amma aka rasa mai aiwatarwa. Sai ku koma ɗaki ku kwanta. Hutun ma ai abin so ne." Waya Zee ta đauko ta duba. Ita dai jiya da yamma a text ta tambayi Baballe. Tunda ta tura text ɗin bata ƙara dubawa ba saboda ta san in ya gani kiranta zai yi. Wurin da ya tafi aiki a Kaduna ƙauye ne. Tana dubawa kuwa sai taga ya yi mata reply. Izinin fitar ya bata da bayanin raunin network da ya hana shi kiranta tun safiyar jiya. Ihun murna ta kama yi harda tsalle. "Yaya ya barni. Allah ni an barni. Kin gani" ta miƙa mata wayar don ma kada ta ƙaryata ta. "Sai ki zo ki tafi. Allah Ya tsare. Ana la'asar ki fito." "Don Allah ki barni in kira yanzu." Hamdi ta soma yiwa Yaya magiya. Da ƙyar ta aminci. Ta kira shi ya fi sau biyar baya ɗauka. Hawaye kawai ta soma don wani irin abu ne ya sami wuri a maƙoshinta ya zauna. Duk magiyarta kuma Yaya ta ce babu inda za ta. Duk da taji tausayinta amma ba za ta buɗe ƙofar irin haka tsakaninta da mijinta ba. Wannan kuskuren na miji bai sani ba ko ya ce kada ayi, uwa kuma ta ce sai anyi ba da ita ba. Bata buƙatar wani ya faɗa mata irin sa'ar da tayi da Allah Ya aurar mata da ƴaƴan lokaci guda. Ganin halin da ta shiga yasa Zee cewa ta fasa fita. Yaya ta ce bata isa ba. Haƙuri ta bawa Hamdi ta tafi. Ita kuma ta shige ɗaki ta sha kukanta ta more. Tun Yaya na ɗan jiyota har taji ɗif. Ta leƙa ɗakin ta sameta ta duƙunƙune jikinta tana bacci. Ga shatin hawayen da ya bushe ya fito raɗau akan hodar da ta shafa. Murmushi tayi ta kirata shagwaɓaɓɓiya a zuci. Ta tabbata daga ita har Zee ɗin daga yanzu za su bawa abubuwan da su ka shafi aurensu mahimmanci. Dama wani darasin sai uwa ta daure zuciyarta take iya koyar dashi. Shabiyu ta gota Taj ya farka daga baccin da ya ɗauke shi a dalilin ciwon kai da murar da su ka dirar masa bayan ya dawo jiya. Magani ya sha amma baccin ya gagara. Sai bayan ya yi sallar asuba sannan ya samu ya kwanta. Missed calls ɗin Hamdi da ya gani ya yi tunanin ba lafiya ba. Sai kuma yaga message tana roƙon zuwa gidan Sajida. Ya kwatanta lokacin da ta kira da sanda ya gani. Yau akwai daru da alama. Yawan kiran ya san a matse take da tafiyar. Ko abinci bai nema ba bayan ya yi wanka ya fita saboda Salwa da ta kankane falon. Yau Happy Taj yana fin kullum cika. Idan ya shiga sai an gan shi kawai. Shi yasa ya yanke shawarar fara zuwa ganin Hamdi. Zai kirata ya ce mata ya zo yayi sa'a Halifa ya dawo daga Tahfiz. Yaje ya gaishe shi sannan ya shiga ya faɗawa Yaya saboda Hamdi na banɗaki tana watsa ruwa. Yaya ta ce a faɗa masa ya shigo. Shi kuma gwanin sai da ya faɗa masa wanka take yi kafin ya faɗi saƙon Yayan. Ƙananan kaya ya saka shi yasa ya so zama a mota da farko. Tunda Yaya ta ce ya shigo babu yadda ya iya. "Ya na ganka haka yau? Ko ba ka jindaɗi ne?" Yaya ta tambaye shi ganin fuskarsa ta ɗan faɗa akan ganin da tayi masa jiya. "Mura ce ta saka min ciwon kai." "Ai kuwa gashi naji muryarka ta canja. Allah Ya ƙara sauƙi." Hamdi bata san yazo ba. Wata shirt mai gajeren hannu ta saka da zani ta fito ko ɗankwali babu. Fuskarta fayau sai idanu a kumbure saboda kukan da tayi. Babu abin da ke tashi a jikinta sai wani irin ni'imtaccen ƙamshin body oils ɗin Scentmania. Gwaji kawai tayi tunda dama tun kafin fitarsu ta so sakawa amma sanin rashin dacewar haka a addinance yasa ta fasa. Wurin ƙarfe goma na safe taga saƙon Yaya Kubra ta whatsapp. Ashe tun jiya ma ta turo. Bata yi mamakin ganin sunan ba saboda Firdaus ce ta zauna tayi ta kiranta da lambobin ƴan gidan tana mata saving. Bayanin sirrin dake tattare da ƙamshi ga matar aure ta turo mata wanda ainihin mai turarukan Scentmania ta tura mata. A ciki ta gane ƙamshi ba ƙaramin tasiri gare shi ba idan ana amfani dashi ta hanyar da ya dace. Musamman idan mace tayi katarin sani da sayen body oils ɗin da ita dai Hamdi bata taɓa jin ƙamshi irin nasu ba. Har shawara take bayarwa cewa yana da kyau mace ta samu wani ƙamshi da za ta yawaita amfani dashi wanda miji zai ganeta dashi. To ko makamancinsa yaji a waje ita zai fara tunawa ya sami nutsuwa. Gashi wai har classes tana yi. Sannan packages ɗin ba dai arha ba. Dole ma ta faɗawa su Sajida idan ta huce daga fushin yau. Don tana ta hango su ana can ana raha banda ita. (07065525409 - Scentmania by Sana) A ƙofar falon ta tsaya don kads Yaya tayi mata magana akan idonta. "Yaya me za a dafa na dare?" Tayi magana muryar nan na nuni da har yanzu ranta ba a sake yake ba. Daga ciki Yaya ta amsa mata. "Abincin daren za ki ɗora tun yanzu? Ƙarfe biyu ma bata yi ba." "Gara na gama tun yanzu." "Ai fa yau tunda na hanaki fita sai abin da hali ya yi. To shigo ki gaishe da mijinki da jiki. Baya jindaɗi." Labule ta ɗaga tana cewa "waya ku ka yi?" Sai ta ganshi a zaune ya jinginar da kansa a jikin kujera. Ciwon kan ke neman dawowa harda zazzaɓi. Da baya ta fara tafiya za ta koma. "Ina kuma za ki? Fita zan yi gidan Gwaggo Dela in duba ta." Ta gaban Hamdi ta zo ta wuce abinta. Tana fita tsakar gida ta ja kunnen Halifa akan kada ya shiga falo sai Taj ya tafi. Dariyar shaƙiyanci kawai ya yi. Tana jiyo shi ta ce "Ɗan banza." A ranta kuwa gani take in ba wajen matarsa ba yanzu ina zai je in bashi da lafiya. Uwa ce dai tafi cancanta yaje ya narke mata da shagwaɓa da rakin maza. To kuma babu dama. Sai da Yaya ta fita daga gidan sannan Hamdi ta yarda ta ƙara kallon Taj. Yana daga zaunen ya nuna mata kusa dashi da hannu amma bai yi magana ba. Ta juya ta kalli bayanta sai ta girgiza kai. "Please. Bani da lafiya fa." Taj ya faɗi yana lumshe idanu. Shahada tayi kawai ta biye masa duk da kafin yazo da ta gama fushin rashin amsa wayarta da ya yi. A hankali ta isa bakin kujerar amma taƙi zama. Ya miƙa hannu ya janyota gefensa. "Bani da ƙarfin ɗaukanki saboda wani irin weakness da nake ji. Da tun daga bakin ƙofar zan taroki." Rumgumota yayi a gefensa. Ƙamshin jikinta mai sanyi ya buge shi. Bai san lokacin da ya sanya fuskarsa a tsakanin wuyanta ba. Ta fara noƙewa taga kamar ma angiza shi take sai ta haƙura. "You smell..." ya kai hancinsa bayan kunnenta ya ja numfashi ya sauke a hankali "relaxing and sweet." Ɗumin da taji a fuskarsa dake bin wuyanta yasa ta daina mutsu-mutsu har ta tabbatar ba normal ɗumin jikin mutum bane. "Zazzaɓi kake yi haka?" Ta faɗi tana janye jikinta don su fuskanci juna. "Uhmm." Ya amsa da rashin kuzari "harda kaina." Juyawa tayi ta taɓa goshinsa. Ya ɗora hannunsa akan nata. Cike da kasala ya ce, "Ba don bana jindaɗi ba da na nuna miki yadda shigar nan taki tayi min kyau." Hannunsa dake tracing ƙaramin hannun rigarta ta riƙe tana mamakin yadda yake tunanin wani abu daban da zazzaɓin jikinsa. Sake janyota yayi ya mayar da kansa kafaɗarta yana ƙara rungumeta. "Ina zuwa." Fita tayi ta barshi. Ya runtse ido don kan nasa ba da wasa yake ciwo ba. Duk yadda aka yi zirga zirga da rashin hutun kwanakin nan ke tambayarsa. Abinci tayi niyyar kawo masa sai tayi tunanin babu lallai ya iya ci. Ta ɗauko gasara ta dama masa kunu da tsamiya kaɗan saboda yaji daɗin bakin. Da ta koma falon idonsa a rufe ta same shi. Ta zuba kunun a kofi ta zauna a gefensa. "Ya Taj?" A hankali ya buɗe idonsa. Ta nuna masa kofin. Ya buɗe bakinsa. Ƙofa ta kalla "Yaya fa za ta iya dawowa." "Ba kya tausayina? Allah I am sick. Amma dai kawo. Zan rama idan na warke." Yana shanyewa ko magana bai yi mata ba ya miƙa mata wayarsa bayan ya buɗeta. "Kira min Happiness. Kaina..." Hankalinta a tashe ta kira. * Tun dare bayan gidan nasu ya watse, ƴan uwa duk sun tafi Kamal ya soma jin jikinsa yana neman dawowa. Ya sha magungunansa ya shige ɗaki ya rufe ƙofa. Rashin kuzarin dake tattare da ciwon gami da ciwon jiki da wahalar numfashi ya soma ji. Ya dinga juye juye akan gado har Allah Ya kawo masa bacci. Da gari ya waye ya ɗan ji sauƙi amma ba sosai ba. Ya lallaɓa ya tafi boutique ɗinsa ya shige office ya kwanta. Idan yana gida damunsa za ayi da tambayar ko lafiya. Nan kuwa yaransa ba za su neme shi ba sai ya zama dole indai ba da kansa ya fito ba. Yana kwance cikin ciwon nan ne Hamdi ta kira shi. Ya sani sarai ciwon wasa ba zai sa Taj nemansa ba. Haka ya tashi ya lalubi muƙullin motarsa. Kafin ya kai ƙofa amai ya taso masa. A cikin office ɗin ya fara da ƙyar ya ƙarasa toilet. Tun yana yi a tsaye sai da ya yi zaman dirshan a ƙasa. Kusan minti sha biyar kafin yaji dama-dama ya tashi yasa tissue ya goge duk inda ya ɓata a office ɗin sannan ya fita. Wayar Taj ya kira domin yaji jikin tare da bashi haƙuri akan rashin fitowa da wuri. "Ya naji muryarka a shaƙe? Allergy ɗin ne? Me ka ci?" Taj ya manta da ciwonsa ya tashi zaune da kyau. "Ƙwarewa nayi. Baka ganni ba harda amai saboda tari." Komawa Taj ya yi ya sake kwantar da kansa "ai kaƙi jin magana akan shan abu kana surutu." "Ba za ka yi min sannu ba to?" "Sannu ba don halinka ba." Kowannensu ya yi maganar cikin dauriyar ciwo. Su ka yi sallama Kamal ya cigaba da tuƙi. Yana son faɗawa Taj lalurarsa amma mene ne amfanin sanya shi cikin damuwa? Da nasa ciwon ya ƙarasa gidan Abba ya ɗauke shi. A soro ya yi sallama da Hamdi don ya ce turarenta hijab ɗin da ta ɗora ma bai hana shi mara lafiya ji ba. "Allah Ya baka lafiya." "Amin." "Za ka kirani idan kun gama da asibitin?" Tayi magana tana kallon ƙasa. "Dole na. Ko don na baki haƙuri." "Haƙurin me?" "Wanka da shirin tarbar maigidan da ki ka yi mana. Ni kuma nazo na haɗaki da jinya. Maimakon na yaba miki da kyau tunda babu kowa a gidan. Mtswww, Allah ban jidaɗi ba." "Allah Ya shiryeka." Ta tura shi. "Ya shiryemu dai Hamdi. Ni dake idanunmu iri ɗaya ne." "Wane iri?" Ta tambaya don bata gane ba. "Zan miki bayani a gaba." Motar Kamal ya shiga su ka tafi asibiti aka yi masa allura da bashi magani. Bai ga komai a tattare da Kamal ba domin ya daure sosai yana danne nasa ciwon saboda yadda yaga Taj. *** Da wuri Yaya Kubra tayi clearing schedule ɗinta ranar litinin. Ta tabbatar bata da sauran aiki na gaggawa a asibitinsu sannan ta fita domin ganawa da Dr. Mubina. Hankalinta a ƴan kwanakin da su ka gabata sam ba a kwance yake ba. Tana dai daurewa ne kawai saboda kada kowa ya gane. Ta dai sakawa Kamal ido fiye da koyaushe. Duk wani motsinsa tana bi. Zuwanta biyu Happy Taj ma tana siyayyar dole duk don ta sami ganinsa. Bata son kiransa ta ɗora masa wahalar zuwa gidanta ko asibiti. A reception ta bada katinta ta ce don Allah a miƙawa Dr. Mubina idan tana nan. Matar ta karɓa ta duba. "Tun ɗazu ta ce idan kin zo a nuna miki inda take. Bismillah." Babu mamaki ko kaɗan a tare da Mubina da zuwan Yaya Kubra. Wannan yasa da ta shiga office ɗin ta ce , "Allah Yasa ban ɓata miki lokaci ba. Naga kamar jirana kike." "Na san yanayin aikin. Ina da niyyar jira har zuwa dare ko za ki zo." Ita ce amsar da bata sannan su ka gaisa. Yaya Kubra ta ɗora ledar kwalin maganin akan tebur tana fuskantarta. "Na sami saƙonki. Amma mene ne dalilinki na breaking doctor-patient confidentiality? Laifi ne babba kin sani." Murmushi Mubina tayi "domin mu ceci Kamal kamar yadda ki ke tunani. Sannan ban karya doka ba. Magungunan ba a same su a nan ba shi ne nayi masa order daga India. Da su ka iso ni bana nan ina wajen conference a Ghana. Za ki iya duba date ɗin. Na kira shi bana samu. Kuma ban san numbar kowa nasa ba, sai sunanki da na asibitinki. Shi yasa na tura." "Kema kin san dai ba zan yarda da wannan zancen ba." Mubina ta dage taƙi bari fuskarta ta nuna ta san bata kyauta ba. Dags ƙarshe dai ta ce, "Tura miki kawai nayi. Ban san za ki buɗe ba." Dariya Yaya Kubra tayi. Da alama babu yadda za ayi ta kama wannan matashiyar likitar da laifi. "Ki yi min bayanin ciwon Kamal baki da baki ba abin da nake zargi daga magani ba." "Ƙoda ce. Duka biyun. Idan ciwon ya sake tashi sai dai mu fara dialysis. Shekara guda kenan yana fama. Kusan duk wani magani da na sani mun gwada. Amma they are barely functioning." Mubina ta faɗi da rawar murya. Jikinta har yafi na Mubina rawa Yaya Kubra ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Doctor kun taɓa shawarta yi masa transplant?" "A nan matsalar take. Ya ce min shi kaɗai ne mai rhesus negative blood group a gidan. Dalilin da yasa yaƙi sanar da kowa kenan." "Wannan ai ba dalili bane. Ya ma aka yi shi kaɗai yake da negative? Wane blood group ne?" Yaya Kubra tayi maganar cikin hawayen da bata san ya sauko ba. Ita da ta zo da niyyar jin ko kidney stone ko wani infection. Bata zata abin ya kai haka ba. Kamal, Happiness ɗinsu da ciwon ƙoda wadda take gab da daina aiki gabaɗaya. Kukan da ita Mubina tayi a lokacin da ta hanga taga kamar mafita ta ƙarewa masoyinta, shi yayarsa take yi. Abin da yake faruwa babba ne. Ƙoda ba abar sayarwa bace. Sannan ko a cikin gidan su mutum ba fa kowa ne zai iya yarda a cire tasa a bawa wani ba. Duk da tana da yaƙinin da wuya aje da maganar gida ba a sami kaso fiye da saba'in a shirye da su bayar ba. A ina za su sami ƙoda? A dangi?...abin da kamar wuya. Sannan zancen cigiya ma bai taso ba. Hukumomin tsaro da na lafiya basu yarda wani ya saka kuɗi ya sayi wani ɓangare na jiki ba. Faruwar haka zai sa mutane su dinga sayar da organs ɗinsu da zarar sun shiga matsala da ma abubuwa daban daban marasa daɗi da za su iya biyo baya. "Ki kwantar da hankalinki mu yi magana doctor." A gigice Yaya Kubra ta ce "ta ina hankalina zai kwanta? Iyayenmu duka na tabbata jininsu positive ne. A ina ya sami negative don Allah?" Bayanin wannan ruɗani Mubina tayi mata kamar ba likita ba don hankalinta na neman gushewa. Da gaske likitoci kamar kowa in lalura ta waji nasu ce su ma ba sa ji, basa gani. Group ɗin jini daban kamar yadda ta sani guda huɗu. A, B, AB da O. Sannan yana ɗauke da wani sinadari da ake kira rhesus. Idan akwai sai wannan blood group ɗin ya zama positive (+), idan kuma babu sai ace negative (-). Abin mamakin shi ne da group ɗin jinin da rhesus ɗin duka a wajen iyaye ake gada. Uwa za ta iya zama A+, uba kuma O-, sai su haifi ɗa O+. Ya gaji group a wajen uba, rhesus a wajen uwa. Wannan shi ne normal. To a case ɗin Kamal an wayi gari shi kaɗai ne yake ɗauke da jini rhesus negative. Wannan yana nufin ɗaya daga cikin iyayensa yana ɗauke da alamun rhesus negative ɗin a ɓoye. Tunda kowanne abu na jikin ɗan Adam ana samu daga uwa da uba a tare, wanda yafi ƙarfi ya nuna kansa (domimant gene). Ɗayan kuma ya zama a ɓoye (recessive gene). To wannan ɓoyayyen zai iya bayyana a jikin ƴaƴan da za su haifa a matsayin mai ƙarfi. A taƙaice dai ɗaya daga cikin iyayen Alhaji ko Hajiya suna ɗauke da rhesus negative gene. (Batul ba likita bace. Wannan bayani na samu shi ne bisa bincike da nayi. Idan yaci ƙaro da ƙa'idar likitanci don Allah ayi min uzuri. Littafin fiction ne dama.) "Allah Sarki Kamal. Nagode Doctor. In sha Allah zan yi cigiya a family ɗin Hajiya. Don da ace daga ɓangaren Alhaji ne tabbas Kamal ba zai kasance shi kaɗai ne mai wannan blood group ɗin ba." "Cigiya kuma? Doctor Kubra please ki duba abin a matsayin likita. Anya ya kamata ki fara bin dangi kina neman mai bashi ƙoda?" "Zuba ido zan yi ciwo ya cinye shi? Me yasa ki ka faɗa min in ba don haka ba?" "Saboda mu nemi mafita amma ba da garaje ba. Cigiya zata iya zama laifi a shari'ance. Musamman idan mai bayarwar ya nemi a biya shi." Duk ta inda Yaya Kubra ta ɓullo sai Mubina tayi mata nuni da illar hakan. Iyayensa ya kamata su sani. Shi kuma Kamal yaƙi amincewa saboda a ganinsa tayar musu da hankali zai yi. Ga ciwo, ga kuɗi amma babu mai iya taimakawa. Damuwar da za su shiga sai ta ninka ciwon nasa. "Da na sani Taj na faɗawa." Mubina ta ce da taga Yaya Kubra ta manta da dokokin aikin nasu. Yadda zai sami lafiya kawai take nema. "Rufa mana asiri. Gara kowa yaji akan Taj. Ina miki rantsuwa da sai yafi Kamal jinya. Those two are like one soul in two bodies." Da ƙyar Mubina ta sami kan Yaya Kubra. Sun tsayar da magana akan cewa za ta zo ranar next appointnent ɗinsa. Daga nan sai su san abin yi kuma. *** Yadda Mami ta so ko ana muzuru ana shaho haka Alh. Mukhtar maigidanta kuma uba ga Salwa yake yi. Ta zauna ta kalallame shi da ƙarya da gaskiya aka son da Salwa take yiwa Taj. "Mu ne da alhakin sama mata farincikinta. Idan ba haka ba Allah muna gab da rasata." "Ni uban mace ki ke so in kira tsohon mijinki in roƙi ya sa ɗansa auren ƴata? Da hankalina fa." Ɗaure fuska tayi "to sai ka barta ciwon so ya kasheta ai." "Ki gaggauta kiranta ta dawo gida kafin ranta ya ɓaci wallahi." Har wani haki yake don ɓacin rai. Rainin hankalin Mami ya yi yawa. Juyawa ya yi zai fita tayi saurin jefa layarta ta biyan buƙata a baki ta tauna. Kamar an tsayar da ƙafafunsa ya tsaya cak. "Nace ka kira Alh. Hayatu ka san yadda za ka yi dashi ya amince a aurawa ɗansa Taj Salwa." Ta faɗi da izza. "To. Yanzu ko yaushe?" "Zauna ka kira yanzu." Zaman ya yi ya ɗauko waya. Ta miƙa masa wayarta mai ɗauke da numbar Alh. Hayatu ya kwafa ya yi dialing. "Assalamu alaikum" Ta jiyo muryar tsohon masoyinta abin begenta har yau. Sake tauna layar tayi ta zarewa Alh. Mukhtar idanu. Jiki na rawa ya amsa sallamar tare da gabatar da kansa. RAYUWA DA GIƁI 24 Batul Mamman💖 Lallai Alh. Mukhtar ɗinnan ya gamu da sharrin Mami shi ne abin da Alhaji ya fara rayawa a ransa bayan sun gama waya. Yadda ya dinga koro bayani akan irin son da ƴarsa take yiwa Taj da fatan amincewar Alhajin don ayi aurensu kai ka san kan ba ƙalau ba. Shi dai yana son ƴaƴansa, amma fa yana ganin babu ƴar da ta isa ta saka shi zubar da mutumci haka a gaban tsohon mijin matarsa. Irin waɗannan abubuwan ya fara gani da burinta na fin kowacce mace matsayi ta kowacce hanya yasa shi sakinta. Yana da labarin yadda matan Alh. Mukhtar biyu su ka fita bayan an aurota. Kuma duk wadda ya ƙaro bata jimawa za ta yi waje ita ma. Zama ya gyara da ya tuna yadda ya ce masa ya amince kai tsaye. Fakewa zai yi da guzuma ya harbi karsana. Ya san a taurin kai irin na Taj akan ya auri Salwa ya faranta masa gara ya saki Hamdi. Ana yin sakin da kansa zai ce masa ya janye batun auren. Duk da a iya saninsa Salwa yarinya ce mai saukin hali. Babu mamaki sirrin zuciyarta ta sanar da Mamin ita kuma tayi amfani da raunin ƴar ta ɗorata akan hanya mara ɓullewa irin wannan. Tsigar jikinsa har wanu tashi tayi da ya yi addu'ar Allah Ya tsare shi surukuta da Mami da lusarin mijinta kamar yadda ya laƙaba masa suna. Bai ga alamun Habibu Simagade zai iya wani kataɓus wurin raba yaran ba. Yanzu da ya sami dama shine zai yi amfani da ita. Ɗansa yake muradi ya dawo gida. Amma ba tare da iri ko jinin ɗan daudu a tare dashi ba. Saboda rashin son ganin Hamdi ranar da aka ce za ta zo gidan zamansa ya yi a kasuwa har ƙarfe tara. Shi ba abin ya ce kada ta zo ba matan gidan su soma tijara. Ya fahimci yanzu kamar ma jira suke ya ce kule su ce masa cass. Ahmad ya nema da yazo gida yana son ganinsa da daddare. Bayan ya taso daga office kai tsaye can ya wuce. Alhaji ya keɓe dashi yana tambayarsa alaƙar Taj da Salwa tunda duka a gidansa su ke. Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ahmad. "Alhaji wata maganar ka ji?" "Ya zan yi maka tambaya ka amsa min da tambaya?" Da sauri ya bashi haƙuri tare da amsa tambayar da ya yi masa. "Babu komai a tsakaninsu amma kuma ba faɗa su ke yi ba. Shi Taj ma bai fiye zaman gida ba ai saboda kullum su ke buɗewa." "Babanta, Alh. Mukhtar sunansa ko?" Alhaji ya faɗi da irin rashin damuwar nan. Ahmad baya jindaɗin yadda ake magana akan Salwa yanzu. Rannan ƴan uwansa ne su ka yi ana ta dariya. Yau kuma Alhaji ke tambayar sunan babanta kamar wani abin gudu. "Sunansa kenan." "Ya kirani yana roƙon na amince Taj ya aureta." Maganar ta dake shi sosai "Roƙo kuma Alhaji?" "Roƙo mana. Ya tabbatar min ita take son sa. Kaima yanzu ka ce babu komai tsakaninsu. To me zai sa ita babar taku ta amince harma mijinta ya kirani?" "Zan yi mata magana Alhaji." Ya girgiza kai "Gobe in sha Allah zan mayar da ita Bauchin. Idan ma mijin ne su sama mata a can." Tashi ya yi zai tafi. Alhaji ya ce ya dawo. "Babu daɗi mutum ya nemeka akan wata alfarma ka nuna masa baka so. Saboda haka na faɗa masa na amince. Saƙon da nake son baka shi ne ka sanar dasu cewa bana so komai ya wuce wata ɗaya indai da gaske su ke." Yana magana ne yana kallon yanayin Ahmad. A ransa kuma yana addu'ar Allah Yasa ɗan nasa ya yafe masa. Da gangan yake maganar a haka saboda yana so idan Ahmad ya tashi kai saƙon ya nuna musu shi fa bai ɗauki maganar da mahimmanci ba. Sannan baya ɗokin haɗa zuri'a da ƴarsu. Ya sami wannan canjin ra'ayin ne bayan wani nazari da ya yi. A matsayinsa na uba sai hankalinsa bai kwanta da ya yi amfani da ƴar wani domin biyan buƙatarsa ba. Idan komai ya tafi yadda yake so ya dawo ya ce da Taj kada ya auri Salwa me kenan ya yi? Shi mai ƴaƴa da jikoki mata ya dace ya tozarta ƴar wani haka? Gashi saboda sanin halin babarta ya tabbatar idan ya yi sake ta auri Taj sai sun mayar masa ɗa abin wasan yara. Ba a raba hanta da jini. Hakan da yake yi ya san duka Ahmad zai faɗawa Mami. Kuma tunda yaro ne hankali zai yi ƙoƙarin nusar da ita illar bari a yiwa ƴarta irin wannan auren. Da bakinsa ne dai akwai nauyi bayan ya aminci ɗazu ya dawo ya ce ya fasa. Abin zai zama cin fuska sosai. Fatansa yanzu dai Allah Yasa iyayen suna da hankalin gane manufarsa. Da wannan damuwar Anti Zahra ta tarbi Ahmad. Juyin duniya tayi ta tambayarsa amma yaƙi faɗa mata abin da yake faruwa. Abinci ma kasa ci ya yi saboda baƙincikin yadda Salwa take zubar da darajarta ta ƴa mace. Gashi yanzu ta sa iyayenta biye mata. Don ma su Hajiya akwai kawaici. Babu mai zancen Mami a gidan ko a aibata ta. Amma yanzu da sun ji maganar auren nan babu abin da zai hanasu fitowa ƙiriƙiri su ƙi. Salwan ya kira tana ɗaki tana chatting da Ummi. Cikin sigar wayon da Alh. Usaini ya koya mata take ta jan Salwa tana dukan cikinta. Rai bai so ba ta katse hirar ta fita wajen Ahmad. Ɗakinsa ya kirata ba ma falo ba. "Kun yi maganar Taj ne da Mami?" "Eh" ta amsa masa babu wannan girmamawar da ya santa da ita. Yadda su ka yi da Alhaji ya faɗa mata. Babu kunya ta kama murmushi. Baki har kunne. "Da ni ne ke Salwa da na haƙura da mutumin da bai damu dani ba. Wane irin aure za ku yi yanzu? Shi baya so kuma na tabbata da wahala ƴan gidanmu su so." "Ai ba da su zan zauna ba." Ta ce da tsiwar da bai santa da ita ba. Wai duk so ne ya canjata ko kuwa dama can halinta ne da bai sani ba? "Shikenan. Zan kira Mami na faɗa mata. Duk abin da ya biyo baya kada ki ce ban yi warning ɗin ki ba." Da ƙunƙuni ta tashi tana cewa "alkhairi zan gani." Daina bashi mamaki tayi. Ya ce mata ta haɗa kayanta gobe za ta koma gida. Ƙarfe tara za su kama hanya. Tana fita ya kira Mami ta rangaɗa uwar shewa. Mantawa tayi da wa take magana ta ce, "In ya san wata ai bai san wata ba. Har ni zai wulaƙantawa ƴa saboda yaci sa'a tana son shi?" "Mami ana dole ne? Aurensa duka-duka sati ne fa da ƴan kwanaki. Ni dai da za ku ɗauki shawarata da kin ce mata ta haƙura." Da faɗa Mami ta ce "to mai halin ubansa. Wanda baya kishina da na ƴaƴana. Idan ta haƙura kai za ka aureta?" "Allah Ya baki haƙuri." Kawai ya ce. "Amin. Kuma ka tanadi abin da za ka bani don a wata guda ko babanta ba zai iya haɗa abin da ya dace ba." Allah Ya sani bashi da irin kuɗin da ya san idan ya bata ba za ta raina ba a yanzu. Sabon wata ne kuma farkon term an koma makaranta. Ɗa ɗaya amma ɗawainiyar karatu sai dai kawai a dinga yiwa iyaye addu'a. A bisa tsarin gidansu kuma tunda su ka soma kawo ƙarfi sun ɗaukewa Alhaji abubuwa da dama. Ba kuma don bashi da kuɗin ba. Ko a danginsa babu kamar shi har yanzu. Suna yi ne don neman albarka. Kayan abinci, kayan buƙata na gida irin su sabulu da kuɗin kashewa ga iyayensu. Duk masu aiki da masu kasuwanci suna contributing. A matsayinsa na babban namiji duk da cikin matan akwai waɗanda samunsu yafi nashi, amma yana ƙoƙarin ganin ya yi bajinta. A haka kuma yake bawa Mamin dubu talatin duk wata. "Kai, Ahmad. Baka ce komai ba." Ya ma manta waya yake. "Allah Ya hore. Sai da safe." Ko minti goma basu yi da gama wayar ba ta sake kira. Ya san zancen ba zai wuce na kada ya dawo da Salwa ba. Shi yasa yaƙi ɗauka. Zai kaita gida gobe in sha Allahu. Ƙarfe bakwai da rabi Anti Zahra ta same shi a ɗaki wai Salwa ta fita. "Bangane ba. Ina ta tafi?" "Ina ta tambayarta tana kuka. Da alama bata son tafiyar. Da ka ƙyaleta." A harzuƙe ya tashi yana ta faɗa. Sai a lokacin Anti Zahra taji me yake faruwa. Ta ma kasa comprehending wannan al'amari. "Don Allah kayi shiru kada Taj ya ji. Kwanansa biyu yana fama da zazzaɓin nan mai zafi. Sannan ko babu komai ka haɗa uwa da ita. Mutumcinta abin karewa ne a wajenka komai rashin daɗin da abin ya yi maka." "Gidan wa zata da safiyar nan? Idan tana tunanin zan bita ne wallahi tayi kuskure." "Naji. Ka san ba za ta wuce gidan ƙanwar babanta ba ta Sheka. In ba nan ba kuma ƙila ta wuce Bauchin." "Ita ta sani." Sai dare ya ɗauki wayar Mami. Ta ƙare masa tanadi kuwa. Shi kuma ya tsaya akan bakansa na cewa indai Salwa ta dawo gidansa to Bauchi zai maidota. Ba zai zauna da mara kunyar da bai isa ya faɗa mata taji ba. Mami da taga yaƙi tanƙwaruwa ta haƙura. "Shegen yaro mai halin ubansa." *** A kwana biyun nan kullum Hamdi sai ta kira Taj. Zazzaɓi ne irin wanda ya kan zo gama gari mai shiga gida gida. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da ciwon nasa da kuma rashin ganinsa. Da Zee ta tsegumtawa Sajida halin da take ciki haɗuwa su ka yi suna tsokanarta. Zee ta ce "Salman Khan ya sallame zuciyar Hamdi." Ita kuma Sajida tana dariya ta tuna mata tsohon ƙudurinta. "Ta dai gama cika bakin bata son namiji mai girki. Yanzu gashi nan mai gidan abinci ya hanata sukuni." Da yake a wayar Zee ake ta bidirin, gajiya tayi da kare kanta ta tsuke bakin nan. "Aljannar mace dai tana ƙarƙashin ƙafar mijinta. In kuma kuna baƙincikin kada na samu ne sai in ji." Sajida da Zee me za su yi kuwa banda dariya. Ashe rana irin wannan za ta zo musu a kurkusa haka basu sani ba. Ƙyalesu tayi ta koma kitchen wajen girkinta. Tana aiki tana tunaninsa. Yau ce rana ta uku tun zuwan da ya yi ta kira masa Kamal. Wayar ma idan sun yi ba wani jimawa su ke ba. Gaisuwa ce da jin yaya jikin nasa. Ɗan wasan nan duk ya daina. "Ke!" A firgice ta kalli Yaya. Bata san tun yaushe take tsaye tana yi mata magana ba. "Jikin nasa ne har yanzu?" Wayancewa tayi kamar bata gane ba "wa?" "Garinku in kin san shi. Wa ma za ki ce min?" Ƙasa ta kalla a kunyace. Fuskarta babu walwala. Yaya ta fahimci har yanzu a kwance yake. "Jiya dama Abbanku yake zancen zuwa a dubo shi. Zan sake yi masa magana yanzu in sha Allah a waya." Fuska mai tona asirin zuciya. A take fuskar Hamdi ta washe. Yaya ta kama baki tana salati. "Anya dama ba shirya maganar auren nan ku ka yi da Taj ba? Cikin ƴan kwanaki kin zurma haka?" "Ni ban zurma ba Yaya" "Tsiwar ma ai naga ta ragu. Allah Ya yiwa aure albarka. Amma ki rage murna don ba dake zai je ba. Halifa zai ɗauka." "Kai Yaya, ni yaushe na ce zan je?" Dariya tayi "nima wasa nake miki. Ai na san ko tayi aka yi miki za ki ce a'a." Bata ƙara magana ba tunda ta gane Yayan ma tsokanarta take yi. To ita har me tayi da ake mata wannan fassara? * A ɓangaren Taj abin da ya zata zazzaɓin gajiya ne ashe combo ne na typhoid da maleriya. Ciwon da ya manta rabonsa da yi. Shi ne ya yi masa rubdugu irin wannan. Kuma da yake zafi ake yi sai ya haɗu goma da ashirin. Dalilin zazzaɓin ne ma su Mama su ka tsahirta da sanya lokacin biki. Shirye shirye dai sai abin da ba a rasa ba. So su ke amarya ta shiga ɗakinta nan da sati uku ko wata guda. A nasu shirin idan ta tare da wuri za su ɓata shirin Alhaji. A ganinsu dama wata ukun nan da ya bayar ya yi ne saboda sanin cewa da wahala ace Abba Habibu yana da abin da zai yi bikin wata ƴar nan kusa. Sosai Ahmad yake bashi kulawa. Musamman bayan tafiyar Salwa. Fushin da ya fara akan yadda aka yi mata dole ya kau da ya gaskata ita ce ta janyowa kanta. Kamal ne dai tun ranar da ya kai shi asibiti ya ƙirƙiri tafiya washegari. Ciwo ke neman kayar dashi kuma baya son kowa ya sani. Haka ya tattara ya tafi asibiti. Mubina ta kwantar dashi. Magunguna tana iya bakin ƙoƙarinta. Bata so su fara dialysis domin ana kaiwa wannan matakin, transplant (dashe) shi ne best option ɗin da zai rage. Ranar da ta kwantar dashi bayan ya zama stable ta kira Yaya Kubra. Dama kullum jiran wayarta take yi. Tana gani kuwa ta bar ayyukan gabanta ta tafi asibitin. "Akwai shirin da ki ka fara yi ne Doctor saboda in san next course of action?" Yaya Kubra ta gyaɗa kai "na fara bincike ta bayan gida. Wata questionnaire na ƙirƙira a google form nace ta research ɗina ce. Ita na tura a groups na family ake ta cike min. Harda families ɗin duka matan gidan mu. Kuma da yake da suna so far na sami mutum huɗu that are rhesus negative." Idanun Mubina harda ƙwalla ta ce "Masha Allah. Amma dangin kusa ne?" "Surprisingly daga dangin Hajiya na sami uku. Ɗaya ne a dangin Umma. Ai jinsi baya hana bayarwa ko? Duka huɗun mata ne." Mubina ta ce gender baya hanawa. "Amma fa Kamal A negative ne. Indai ba irin nasa ba kinsan sai dai O ko AB negative ko?" "Dukkaninsu O negative ne. Yanzu su Alhaji ya rage su sani sai a tuntuɓe su." "Muje ki ganshi. Akwai Nephrologist da na fara magana dashi daga Port Harcourt. Idan an sami nasarar samun mai bayarwa sai naji yaushe zai iya zuwa." Godiya Yaya Kubra tayi mata har ta rasa kalmar faɗa. Mubina ta shige gaba zuwa ɗakin da Kamal yake. A hanya tayi ta nanata mata don Allah ta daure zuciyarta idan ta ganshi. Wannan yasa zuciyar Yaya Kubra ga tsinke tun kafin su shiga. Mubina ce ta fara shiga da sallama. Yana kwance gaɓoɓi da fuskarsa sun kumburo sosai. Shi kaɗai ya san irin azabar ciwon da yake ji. Amsa sallamar ya fara da muryarsa can ƙasa kawai sai ya yi tozali da Yaya Kubra. Ya yunƙura ya tashi zaune kafin ta ƙaraso. Hannu ta ɗora akan bakinta don kada tayi kuka mai haɗe da ihu da taga yadda ya koma. "Kamal?" Ta kira shi da rawar murya. Ya miƙa mata hannu, kwarmin idanunsa yana ziraro hawaye ta riƙe. A gefen gadon ta zauna su ka rungume juna. For the first time tun bayan ciwon nan ya same shi ya fashe da kuka mai ban tausayi. Duk wani ciwo, ƙunci da damuwa da yake ɓoyewa ya bari ya nuna kansa a wannan lokacin. Shi ɗan dangi yana ta fama da damuwa shi kaɗai. Abin da gidansu basu saba ba. Yaya Kubra tana kuka tana shafa bayansa da lallashi. Mubina kuwa ficewa tayi don bata son karyar masa da zuciya fiye da halin da yake ciki. Mara lafiya baya son ganin rauni a tattare da likitansa. Tsahon minti goma zuwa shabiyar kafin yaji sanyi a ransa ya daina kukan. "Kiranki tayi ko?" Ya tambayeta yana nufin Mubina. Faɗa ta soma yi masa "Me yasa ka zaɓi wannan rayuwar Kamal? Bamu da mahimmanci a wurinka? Ko kana ganin ba za mu damu da lalurarka ba?" "Irin wannan kallon kamar kina yi min sallama shi ne bana son gani. Wannan kukan zamu dinga yi kullum har lokaci..." "In sha Allahu za a dace. Ina nan ina bincike." "Bata faɗa miki cewa ko dialysis ba zai iya riƙeni na tsayin lokaci ba?" "Na sani Kamal. You need a new kidney. And we'll find one in sha Allah" ta share masa hawaye da hannunta. Alƙawarin riƙe masa sirri ya roƙeta har zuwa lokacin da za ayi bikin Taj. Sannan ƙanwarsu mai shirin haihuwa ko yau ko gobe ita ma ta sauke. "Me yasa? Wallahi ka san ba za ka burge Taj ba. Infact ni ba zan so ganin ranar da zai sani ba. Za ku yi faɗa Kamal. Za ku yi faɗa sosai. Ko jiya da naje duba shi sai da yayi ta zancen wai ina duba maka magungunan allergy kuwa." Jingina ya yi da pillow don ya gaji da zaman. Ya yi ajiyar zuciya. "Na sani. Amma Happy zai tsayar da duka uzurin rayuwarsa ne. Zuwa yanzu kin san mutum ne mai sanya abu a rai. Amma kina gani saboda mu ya mayar da komai ba komai ba tsakaninsa da Alhaji. Kuma hakan fa ba ƙaramin ciwo yake yi masa ba." "Tsakanin uba da ɗa ne wannan. Ina maganar Happy da Happiness. Sai ka shiryawa duk abin da zai biyo baya." "In ya ganni a haka kina tunanin zai iya yi min mita? Kuka kawai za mu zauna mu sha abinmu." Yadda yake maganar kai ka san akwai tsantsar tawakkali. Yaya Kubra a nan ta wuni har tara na dare sannan ta tafi. Ta amince za ta yi shiru amma ba don Kamal ba. So take ta samu cikin dangin wanda idan ta bijiro da buƙatar ba zai ƙi ba. Maganar neman donor ta hanyar gwamnati ba zai yiwu ba. Waɗanda su ke kan list sun yi yawa sosai. Tsakanin Kamal da Taj a waya sai ta whtsapp. Kamal ya cire simcard da sunan baya ƙasar. Wai ya tafi China odar takalma. Taj harda mitar me yasa bai faɗa masa shirin tafiyar ba. Ya ce wanda ya bawa sautu ne ya sami matsala. Gashi kuma komai ya kammala. Ana buƙatar mai kaya. Abinka da rashin sabo da yi. Taj bai kawo komai ba ya yarda. Iyaka dai in suna waya ya dinga kiran wash wash kenan don kawai yaji Kamal yana sannu kamar ya ari baki. Bai san ciwon Kamal ɗin ya ninka nashi ba. *** Kamar yadda Anti Zahra tayi hasashe, Salwa gidan ƙanwar babanta ta tafi. Gidan da tun farkon karatunta baban ya so taje amma saboda Mami ta raina arziƙinsu ta rufe ido ta ce bata san zance ba. Wannan tafiya da tayi sai ta sami lasisin fita yadda take so tana haɗuwa da Ummi. Gwaggonta kuma bata iya yi mata magana saboda tsoron jarabar Mami. Bayan bugun cikin da Ummi tayi mata sai ta nuna mata cewa tana jajanta mata rashin samun soyayyar Taj. Ta kuma yi mata alƙawarin za ta taimaka mata ta sami biyan buƙata indai tana so. "Mamina ma ta gama komai har an fara maganar aurenmu" ta faɗawa Ummi da farinciki. Taɓe baki Ummin tayi "in an ɗaura muku auren kina tunanin kin yi nasara ko me? Mutumin da baya sonki kuma igiyar auren tana hannunsa." A tsorace Salwa ta ce "kuma fa haka ne. Amma ba sona bane baya yi. Haɗuwarsa da matar da aka aura masa ƴar ɗan daudu duk shi ya lalata komai. Da muna waya normal." A zuci Ummi tayi tsaki. Wannan Salwan irin matan nan ne da sakarci ya rinjayi tunaninsu. Gashi dai ta san cewa ta girmeta amma irin shirmen da take yi da sunan soyayya ita ko da wasa ba za ta yi ba. "Ni naga sharrin ƴar ɗan daudu. Akanta aka koreni daga makaranta sannan aka fasa bikina. Gidanmu kowa ya tsaneni akansu. Wallahi da zan haɗu da Hamdiyya Habib sai na rama abin da tayi min ko yaya ne." Idanu Salwa ta zaro tana kallonta "Hamdiyya? Ai kuwa ita ma sunanta kenan. Babanta yana aiki a Happy Taj." "Ni ban san a ina yake ba. Amma dai shi ma sana'ar girki yake yi. Kin ganta. A yadda suke matsiyata bana jin ko iskar da mai Happy Taj yake shaƙa ita ma za ta shaƙa wataran." Hoton Hamdi ta nuna mata wanda ta samu ta ɗauka daga wayar Siyama na ranar aurensu. Salwa ta dinga sallallami gami da rantsuwar ita ce. Ita ma Ummi ta nuna nata mamakin ƙwarai. "Indai Hamdi ce nayi miki alƙawarin zan bada nawa taimakon na raba su da masoyinki." "Nagode. Ni kam alkhairi ne ashe ya kai ni Glory mall rannan." Ummi sai dariyar yaƙe kawai take yi. Ita kanta duk fitinarta abin da Alh. Usaini ya tanadarwa Taj ya yi mata hatsabibanci da yawa. Ta riga ta nuna masa tana tare dashi bata da hanyar guduwa. Haka kawai take tsoron mutane irinsa waɗanda za su iya yin komai domin biyan buƙatarsu. Rashin kunyarta bata kai nan ba. Domin kuwa duk iya shegenta akwai abubuwan da take tsoron yi don kada su koma kunnen iyayenta. Tunda Allah Ya kawo Salwa sai ta bashi shawarar amfani da ita don ya cimma burinsa. *** Jinyar sati guda Taj ya yi kafin ya farfaɗo sosai. Har ya faɗa kuwa. Abba yaje duba shi har gidan Ahmad. Kuma ya sami tarba ta mutumci daga gare shi. Wannan ya sake daɗaɗa ransa akan halin ƴaƴan Yaya Hayatu. Da zai tafi ne Taj ya yi masa maganar Hamdi. "Abba don Allah ina neman alfarma a gareka." "Indai zan iya in sha Allahu zan maka." "Maganar rabani da Hamdi. Don Allah ka cire komai a ranka ka bimu da addu'a." "Innalillahi..." Abba ya riƙe kai "faɗa maka tayi? Ban san Hamdi da surutu ba wallahi." Taj ya yi murmushi "ba ita ta faɗa min ba." Ya tuna maganar da Salwa tayi ya ce "Yaya Ahmad ne ya faɗa. Amma ya ce kada na damu in sha Allah su Inna ba za su bari ba." "Lamari na iyaye..." "Allah bai bawa iyayenmu damar kashe mana aure ba. Musamman idan raba auren cutarwa ne ba hanyar samun maslaha ba." "Ina jiye maka yawan saɓanin da kuke samu dashi. Hakan ba zai haifar da alkairi ba." "Abba ina ƙoƙarin tsayuwa akan iyakar addini kan abin da ya shafi Alhaji. Duka abubuwan da yake fushu dani a kai shi yake nuna amincewarsa sannan ya zargeni da rashin kyautawa." Shi dai Abba gani ya yi zai shiga tsaka mai wuya. Ya yi ta nunawa Taj illar dake tattare da zama cikin fushin iyaye. "Don Allah ka nemi sulhu dashi kafin lokaci ya ƙure." Muryar Taj a raunane ya ce "na jima ina wannan amma yaƙi bani dama. Zan cigaba da ƙoƙari amma Abba kada ka kuma sako aurena a ciki don Allah." Tausayi ya bawa Abban "na daina. Allah Ya kiyaye mana ɓacin rana." "A sunnar Annabi SAW? Inaaa, Abba ai sai dai lada." Nauyi Abba ya fara ji tun kafin Taj ɗin ya je inda bai dace ba ya ce "naga ka fara jin sauƙi. Bari na tashi." Taj ya dinga dariya kamar ba shi ne yake kwance kafin zuwan Abban ba. *** Inna tana falonta ana yi mata kitso aka yi mata waya. Baƙuwar lamba ta gani. Ta ɗauka da sallama su ka gaisa da matar da ta kira. "Na san ba ki gane ni ba tunda bamu zauna tare ba. Mahaifiyar Ahmad ce. Ahmad babban ɗa namiji wajen Alh. Hayatu nake nufi." Murmushi Inna tayi. Wannan ƙalau take kuwa? A take ta cire wayar daga kunnenta ta karanto Ayatul Kursiyyu. Ɗabi'arta ce haka. Duk abin da bata gamsu dashi ba koda bata aka yi sai ta tofe shi da Ayatul Kursiyyu kafin tayi amfani dashi. Yadda Mami ta gabatar da kanta sam bai yi mata ba. Sai da ta gama sannan su ka gaisa da ita. "Dama naji shiru ne ina ta sa rai da wayarki amma baki kira ba. Nace bari ni na neme ki naji me ake ciki." "Wace magana kenan?" Tashi tayi daga wurin kitson ta koma ɗaki. "Auren Taj da Salwa. Alhaji ya ce baya son a wuce wata guda. Naga har an cinye sati." Azkar ɗin tunkarar shugaban da kake tsoron cutarwa daga gare shi Inna ta karanto wannan karon kafin tayi magana. (Allahummak finihin bima shi'ta) "Wane Taj ɗin wai? Nawa dai sati biyu kenan da aurensa. Bani kuma da labarin zai ƙara wani." Mami tayi kwafa a hankali tana raya duk za su zo hannu ne. Da ta san haka za ta yi mata tun farko ma da ta karɓo laya. "To ki tambayi maigidan naki. Sai mu yi magana daga nan." Inna ce ta fara kashe wayar. Ta dinga karanto addu'o'i. Me yasa duk wata rigimar gidan akan Taj take kunno kai? Istigfari tayi da sauri sannan ta fita ta tafi ɓangaren Alhajin. Dama yana gida. Girkin Umma ne. Inna tayi sallama ta shiga falon bayan Umma ta amsa ta iske shi yana cin abinci. "Alhaji me nake ji daga bakin tsohuwar matarka?" Karo na biyu kenan da Inna tayi masa magana babu kyautata kafazi. Yana namiji sai da yaji wanibabu a ransa. Maganar Hajiya na neman tabbata da ta ce masa kada ya ƙure haƙurin Abu don mai haƙuri bai iya fushi ba. "Wani abin ne ya faru?" Ya tambayeta kamar bai sani ba. "Ka fini sani Alhaji. To amma ina so ka sani ka gama yi min hawan karkatacciyar kuka. Wannan juya min yaro da kake yi ya isa haka." "Haba Inna. In ranki ya ɓaci kada ki bari hankalinki ya gushe mana. Da mijinki fa kike magana." Umma ta ankarar da ita don muryarta tashi take sosai. "Me ya rage min? Yau ko agola ne Tajuddin ai iyakar abin da mijin uwa da baya sonsa zai yi masa kenan. Wai ni matar nan za ta kira ta ce ya maganar auren Taj da Salwa?" "Me?" Umma ma ta ɗaga murya ba tare da tunani ba. "Ah to, kema kya faɗa. Wai da Alhaji su ka yi magana." Ya fa manta da maganar nan. Duk a zatonsa idan Ahmad ya faɗa mata yadda su ka yi za taji haushi ta ce basa so. Daga ranar da su ka yi maganar ko tunawa bai sake yi ba saboda rashin mahimmancin zancen a wajensa. Umma ta dube shi "Alhaji wai haka?" "Eh. Mun yi magana da mijinta ya bawa Taj Salwa. Sharaɗina kenan idan ba zai saki ƴar gidan Habibu ba. In ba haka ba kuwa..." "Kana son ya saketa kafin auren ya wuce wata uku ko? Ahmad, ɗan halak ya faɗa mana" Inna ta ƙarashe masa. "Tunda kun sani sai ku sa ya zaɓi ɗaya. Na gama magana." "Ahaf. Ai babban kuskurenka da ka bari aka yi auren nan Alhaji. Shi ne mai wuyar. Ko yanzu ba abin mamaki bane ace Hamdi tana da juna biyu." Ba Alhaji da ya kusa ƙwarewa da ruwan da yake sha ba, Inna ma zaro idanu tayi. "Kai Umma?" "Auren yanzu da ake yiwa yara bayan duk sun ƙosa. Ko mu nan nawa ne ƴaƴanmu su ka haihu wata tara ko goma da aure? Indai an bada sadaki ai magana ta ƙare. Don ma ba lafiya gare shi ba." "Ai kuwa sati mai zuwa za ta tare." Inna ta faɗi sannan ta dubi Alhaji "ka faɗawa tsohuwar matarka ta nemarwa ƴarta miji tun wuri." Inna na fita Alhaji ya tsare Umma da tambaya. Shi fa daina gane komai ya yi daga inda ta ce bashi da lafiya. "Ciwo ne da Taj ɗin?" "Typhoid yake da maleriya. Satinsa guda ko aiki baya zuwa." Ransa a ɓace ya ce "Kuma shi ne aka rasa wanda zai faɗa min?" "Taj ne fa. Ka damu da ciwonsa ne dama?" "Me kike nufi?" "Wai abin da ido ya gani baki ke faɗa." Ta jima da fita daga ɗakin ta bar Alhaji da tunani. Me yasa sai akan Taj iyalinsa su ke yi masa irin wannan? Sai kuma maganar Salwa. Bai san har yanzu Mami bata da cikakken hankali ba. Ai da maimakon hannunka mai sanda sai ya fito musu a mutum kawai. Yana wannan lissafin tuni Mami ta garzaya wajen toshe ɓarakar da take hangowa. Magana ta yiwa Alh. Mukhtar. Ya kuma aiwatar duk da baya so. Alhaji sai waya kawai yaji. Ganin sunan mai kiran ya hanzarta ɗauka domin ya kashe maganar Salwa. Sai dai kafin ya ce komai Alh. Mukhtar ya yi masa dabaibayi. "Akwai wasu ƴan uwana mazauna Kano da muka yi magana mutum biyar. Ɗaya ma ƙanin mahaifina ne uwa ɗaya uba ɗaya." "Wani abu ne ya same su?" Alhaji ya ƙosa yaji ƙarshen zancen ko ya sami damar yin nasa. "Lafiya ƙalau. Dama don a sama muku sauƙi ba sai kun taho har nan ba. Shi Baffan namu na sanar dashi za ku zo neman aure da biyan sadaki. In kun saka rana sai ka sanar dani. Na tura musu lambarka ma dai." Alh. Hayatu mai baki sai yaji yawun bakinsa ya ƙafe. Ta ina zai fara cewa ya fasa? Abin da kamar wuya. Girmansa zubewa zai yi. Idan matansa su ka san halin da yake ciki ya tabbata dariya za su yi masa. "Idan na saka ranar zan sanar da kai." "Yauwa to nagode." Ya đan numfasa "don Allah kada a ja lokacin. Nima na gama shiri." "To" Alhaji ya gyaɗa kai. Kuma har zuciyarsa sai yaji yana tausayin Alh. Mukhtar ɗin. Shi da zai iya dafa littafi mai tsarki ya yi rantsuwar matansa basa biye biyen tsibbu ashe a aljanna yake. Gudun faɗuwar girma ya janyo ya kasa kyautata musu akan abu guda da su ke buƙata daga gare shi. * Inna na dawowa daga ɓangarensa taci karo da wasu rantsattsun akwatuna manya manya guda huɗu a tsakiyar falo. Ƴan gidan an haɗu ana ta murnar yaushe gamo da Amma. Rabonta da shigowa gidan yayan nata an jima. "Takwara oyoyo" Umma ta ce daga bayan Inna da ta kasa magana. "Yauwa Takwara" Amma ta ce, ita da su Mama su ka bi Inna da kallo. Murmushin dole tayi musu gami da yiwa Amma sannu da zuwa sai ta shige ɗaki. Ta manta da mai kitson sai da ta ganta zaune tana jiranta. Kuɗin kitson ta bata sannan ta ce ta tafi za ta nemeta daga baya. Matar bata matsa ba don ta lura Inna bata cikin nutsuwa. Uwar ɗaka ma ta shige ta rufo ƙofa. Wayarta ta ɗauka ta kira babban wanta. Tana jin muryarsa ta fashe da kuka. "Me yake son ya mayar da rayuwar yaron nan? Shi ba fasiƙi ba, ba ɓarawo ko ɗan fashi ba. Amma ace duk wani abu dake nuni da ba a son mutum akansa yake ƙarewa?" Rarrashinta ya yi sannan cikin kuka ta labarta masa abin da ya tunkaro su kuma. "Ina jin lokaci ya yi da zan nunawa Hayatu bai fi ni zafin kai ba. Turo min lambar baban ita matar Taj ɗin. Sati na sama in sha Allahu za ta tare. Idan ya kuma barazanar rabasu kuma ni da kaina zan ɗauki mataki." "Yaya ita kuma tsohuwar matar tasa fa?" Dariya ya yi ta manyan dattijai "kinsan Allah, barazana ce kawai. Hayatu da wuya yake yar da abu ya waiwaye shi. Abin da ya raba shi da Habibu kenan tun farko. A yanzu kuwa ban hango zai taɓa yarda babar Ahmad ta zama surukarsa ba. Rabuwarsu ba ta daɗi bace." Nutsuwa ta samu da wannan wayar. Ta fito falonta don zuwa wajen Amma ta gansu duka zaune. Umma ta faɗa musu abin da ya faru. Su ka haɗu suna bata baki. Tun bata son nuna ai ɗan cikinta Alhaji yake yiwa haka har ya kai ta fito tana faɗa da bakinta. Su ka haɗu da Amma su ka bata baki. Auren ƴar Mami kuma ko Taj ne ya kwaso da kansa ba za su yarda ba. Suna wannan tattaunawar Alhaji ya shigo ɓangaren nasu. Ganin babu kowa ya tambayi ina su ke. Aka ce su na ɗakin Inna. Juyawa ya yi bakinsa alekum ya fice, musamman da yaji cewa Amma ta zo. Sake hargitsasu za ta yi ta zuge su tas. Ƙarshenta in bai yi da gaske ba sai anyi sa'in'sa a gaban mutane idan ya ce zai nemasu yanzu. *** Sai washegari Taj ya sami ƙwarin fita sosai. Jiya da su ka yi waya da Hamdi ya ce zai je Happy Taj ta ce ya bari ya ƙara hutawa. "Kin isa matar Happy. Dama tunda Happiness ya yi tafiya na san ba wani daɗin wajen zan ji ba sosai. Da ni ɗan gata ne dai sai ki zo ki tayani zama." Yayi maganar a hankali. "Naƙi wayon. So ka ke Abba ya tsireni? Yana wajen sai na zo na wuce." Marairaicewa ya yi "A misali da ba zai yi faɗa ba za ki zo? Uhmm? Allah naji jiki fa. Ga rama." "Kullum fa ina kiranka." "Kira daban, gani da ido daban. Kin san fa babu jinya mai daɗi kamar kayi a gaban matarka." Hamdi tayi dariya. Da alama Taj kallon yarinya yake yi mata. Shi ne zai yi mata wayo. "Allah ko? Saboda me?" "Ana yi ana petting ɗin mutum. Ga pecks here and there. Sai ka manta ma da ciwon." Ya bata amsa yana jin dama so samu ne. Baƙuwar kalmar da taji ta tambaye shi. "Meye kuma pecks?" Taj na jin haka ya tashi zaune yana ƴar dariya. Ashe ma wayon da take ta zillewa zai yiwu. "Peck ɗin ne baki sani ba? Ko dai kin faɗa ne?" "Allah ban san shi ba. Pecks naji ka ce." Da fatan kada ta ɗago shi ya ce "Da yawa ne pecks. Gashi akwai nauyi da na ɗauko miki." "Idan da rabo sai na gani watarana." Duk a zatonta wani abu ne da ido zai iya gani kuma hannu zai ɗauka. Dama ce ta zo wa Taj bayan sun gama wayar da yamma. Mama ta kira Yaya ta sanar da ita za su zo washegari ita da su Amma. Wasu daliliai sun janyo suna son ayi biki sati mai zuwa. To dama su ma suna ta ɗan shirinsu don ba a zauna haka ba. Yaya sai ta kira Hamdi ta ce ta tambayi Taj ko gidan Sajida ne gobe ta tafi. "Idan baki je yanzu ba aka fara biki za ku kwana biyu baku haɗu ba." Daɗi ya kama Hamdi. Tana ta murna ta kira shi. Sai ya ce ta shirya shi zai zo ya kaita. Shi ne fa yau ya shirya yau cikin nishaɗi. Happy Taj ya fara zuwa. Akan idon Alh. Usaini ya wuce. Nan da nan ya kira Ummi ya ce aikinsu zai iya yiwuwa yau. Da alama Taj ya dawo aiki. Tunda suna ta kula da shige da ficensa tun bayan sun gama shirinsu. Sai dai bai ƙara zuwa ba sai yau ɗin. Kai tsaye Salwa Ummi ta kira. Don dama Alh. Usaini bai yarda Salwan ta san shi ba. Ko ta kwaɓe sai dai su ƙare tsakaninsu da Ummi. Tana zuwa Ummin ta bata turarukan da Alh. Usaini ya bayar. Guda biyu ne masu wani irin ɗan karen ƙamshi. Ɗaya a yadda Ummin ta faɗa mata zai haddasa faɗa tsakanin Hamdi da Taj. Ɗayan kuma zai haɗa ƙaƙƙarfar soyayya tsakaninta da shi. "Amma me yasa ki ke taimaka min Ummi?" Salwa ta tambayeta bayan ta karɓi turarukan. "Saboda ba zan taɓa sanya ido Hamdi ta zauna a gidan miji alhali ni ta hana ni aure ba." Da farinciki Salwa ta ce "Allah Ya bani ikon taimaka miki nima a duk lokacin da kike buƙata." "Amin" Bayanin yadda zata saka turaren Ummi tayi mata. Ta fito za ta tsallaka ta shiga Happy Taj sai taga motar Taj ɗin yana fitowa. Hankalinta ya tashi. Ummi ta ce kada ta damu. Su jira zuwa la'asar domin indai ya shigo ko ya fita da wahala a rufe wurin baya nan. Jin haka sai ta sami wuri ta zauna su ka cigaba da ƙulla yadda za ayi bikin Salwa da Taj bayan sun yi nasara. *** Zee ce ta yiwa Hamdi light make up sannan ta shirya. Doguwar rigar atampa ta saka wadda take fitted daga sama. Sai kuma aka buɗeta daga ciki har ƙasa. Turarukanta na scentmania tabi ta shafe jikinta dasu. "Don Allah Ya Hamdi a dinga ragawa Salman Khan." "Wallahi zan miki rashin mutunci akan kiransa Salman Khan." Zee ta dinga dariya. Suna gama ɗaurin ɗankwali ya kirata. Yaya tana son yi mata ɗan gargaɗin manya amma kuma ta rasa me ya dace ta ce. Miji da mata wane gargaɗi kuma za ayi musu wanda ba zai shiga hurumin shari'a ba? Ƙarshe dai sai cewa tayi, "A kula da kai dai. Banda yin abin da bai dace ba." Tunda ta fito ya kasa ɗauke ido daga kanta. Yana mamakin yadda ya mallaki wannan yarinyar da ya taɓa gani tana practicing speech. Ganin farko ta kanainaye masa zuciya. Ita ce first true love ɗinsa. Ya kuma yi sa'ar zama mijinta. Daga ciki ya buɗe mata ƙofa. Sai da ta zo shiga ta fara jin faɗuwar gaba. Ta kasa gane ta murnar ganinsa ce ko ta tsoron fitinarsa, ko kuwa ta wani abin daban da bata sani ba? Zama tayi ta rufe ƙofar sannan ta gaishe shi. Tana yi tana kawar da kai daga kallon fuskarsa. Ta san yanzu yana ganin kwalliyarta zai ce kama tsokanarta. "Mrs Happy yau kuma ƴar ɓoye fuska ce? Irin yanayin nan da Indians..." A gaggauce ta ɗaga fuska su ka haɗa ido. "Kada ka ƙarasa. Ka bar Indiyawa su sarara don Allah." Lumshe ido ya yi ya buɗesu akan fuskarta. "Na barsu. Yau ko su basu da kalaman da zan yabawa Hamdina." Yatsa ɗaya ya ɗaga a gaban fuskarsa "In ce awwnnn sau ɗaya don Allah?" Riga shi tayi harda fari da idanu "awwnnnnn" Taj ya sanya hannayensa duka a saitin zuciyarsa "yarinyar nan za ki kashe ni. That was just too cute." "Tunda kaga ba kai kaɗai ka iya ba don Allah ka daina." "Ban yi alƙawari ba. Atleast zan cigaba kafin na samu wani abin tsokanar taki." Tuƙi ya fara a hankali suna tafiya Hamdi ta sake yi masa sannu da jiki. "Ka rame da gaske fa." "Sauron garin nan wasa ne? Jiya na kira mai kula da gidanmu na ce su duba duk wata ƙofa ko window a saka net." Don jin me za ta ce ya ƙara da cewa "ko mu je ki gani?" "Allah Ya baka haƙuri. So kake Yaya ta ce a biyoni da kayana kada na dawo gida yau?" "To ba shikenan ba. Kowa ya huta." Cewa tayi bata yarda ba. Ya ce sai ya kaita. Dama ya kamata su gaisa da Amma. Tunda tana can da su Umma kafin su je wajen Yaya sai su haɗu. Hamdi ta rikice sosai don ya đauke hanya daga inda ta kwatanta masa gidan Sajida. Ya gama janta sannan ya ce Happy Taj za su fara zuwa. Narke masa fuska tayi "so dai kake dole yau nayi laifi ko?" "Ba zama zamuyi ba. I just realllyyy need to show you that peck." Zazzaro masa idanu tayi "da ka bari ma kawai..." Taj ya kama dariya "yau wata za ta yiwa Abba bayani. Ki ka ce min baki sani ba." "Muna gama waya na duba a google." Ta bashi amsa da ƙaramar murya. "Wannan fassarar google ce. Ni dai sai na nuna miki." "Don..." "Shhhhh. Ba a faɗa miki babu kyau roƙo ba?" Wanda baya jin magiya biye masa kawai ake yi. Daina zancen tayi ta karkata zamanta ta zuba masa idanu yana tuƙi. "Mene ne?" "Jira nake muje ka nuna min peck ɗin nan." "Haaa, shi yasa nace kalarmu ɗaya. Ni dake duk fitinannu ne. Allah dai Ya shiryemu." Juyo da abin kanta ya yi ya dinga tsokanarta har su ka isa akan idon Salwa don ta riga Ummi ganin motar tasa. Nan gabanta ya cigaba da faɗuwa kada su haɗu da Abba. Taj ya buɗe mata wata ƙofa ta baya wadda directly office ɗinsa za ta kai mutum. "Emergency exit ce for naughty people like us." "Banda ni." "Kin ganki fa." Ya janyota ya rungumeta a jikinsa gabaɗayanta "ke da aka ce ki tafi gidan yayarki kin biyo miji office." "Laifin wa don Allah?" "Naki mana" ya soma magana a hankali. Ƙamshin jikinta ya tayar masa da kewar sati guda "I miss you so much." Idanunta sun soma raina fata don akwaita da tsoro ta ce "ka zo mu tafi." "Uhm uhmm" peck ɗin da ta ce bata sani ba ya soma sauke mata a fuska. "Happy" ta daure ta kira shi. Tsoro ne fal a zuciyarta. Na zuwa wajen da kuma na shi kan shi mijin nata. "Mrs Happy" Daidai lokacin su ka ji an ƙwanƙwasa ƙofar. Hamdi ta ƙwace daga hannunsa a firgice. Shikenan, idan Abba ne ta gama yawo a wurin Yaya ba shi ba. Muryar wani yaronsa yake ji yana rantsuwar baya nan. Sai kuma ta mace da ya tabbatar Salwa ce tana cewa taga shigowarsa. A buɗe mata ta jira shi. To da yake yaron ya santa sai ya ce ta bari ya ɗauko spare key. Ita Hamdi ko maganganun bata ji da kyau. Ƙofar kawai da taji an riƙe yasa ta neman toilet. "Stay with me please. Ba Abba bane." Ta girgiza kai ta gudu. Idan ba Abba bane ai dai zai iya samun labari. Tana shigewa Taj ya buɗe ƙofar. Salwa ya gani a tsaye yau ita ce da mayafi a kafaɗa ɗaya ɗan mitsitsi haka? "Ya Taj" ta kira sunan shi tana murmushi. Baya ya yi don ta samu ta shigo saboda kada ta faɗi abin da zai kunyata shi. Tana sanya ƙafarta a ciki ta rufe ƙofar. "Salwa me ya kawo..." Faɗo masa tayi a jiki kafin ya gama tambayarta. Hannunta hagu da dama kowanne da turaren da Ummi ta bata. Wuyansa ta riƙe da hannayen saboda ance lallai ta taɓa fatarsa da turaren ba kaya ba. Ya sanya hannuwansa zai cire nata sai dai kuma duka hannuwan ta shafesu suma. Saboda haka yana taɓawa abin ya sake shigarsa. "Sake ni Salwa" ya ce yana jin wani irin abu na shigarsa. "My Taj..." ta sake yunƙurin rungumarsa. Fincikota taji anyi ta baya don bata ji lokacin da aka buɗe ƙofar banɗakin ba. Ta juya za ta yi magana Hamdi ta tsinketa da mari. "Ke! Ni za ki..." Rai a matuƙar ɓace Hamdi ta sake marinta sannan ta saka hannu ta rabata da Taj. "Fita." "Nace ki fita ko na tara miki mutane. Banza kwartuwa." "Ya Taj warn this girl." Salwa ta ce tana ƴar dariya "ko na kashe maka jiki ne?" Shi fa jiri ne ma yake ɗaukarsa. Amma idanun Hamdi sun rufe da ganin da tayi musu. Me zai sa ya bari Salwa ta rungume shi na tsayin lokaci har ta fito. Ƙofar office ɗin Hamdi ta buɗe ta kamo hannun Salwa ta janyota. Inda ta sami ƙarfin hali da na jiki ma bata sani ba. Ita kuwa dariya ma take yi ta ce "Baki ga komai ba ƴar ɗan daudu. Sai na zo har gida." Ta yi murmushi ta fita. Idanu a birkice Hamdi ta juyo ta kalli Taj. Kan da yake riƙewa ma a wajenta ba komai bane illa pretense. "Abin da ka kawoni ka nuna min kenan?" Tayi magana tana hawaye masu zafi. "Hamdi ba haka bane." "Dama ku maza munafukai ne." "Ni ne munafukin? Ni?" Zuciyarsa ta harzuƙo da wani irin ɓacin rai. "To ko ɗayan zan kira ka? Wanda ya dace da mazan dake neman matan da ba nasu ba?" Ta faɗa kai tsaye. Rufe bakinta ke da wuya kuwa ya ɗaga hannu zai mareta. "Bismillah. In baka mareni ba baka haifu cikin uwa da uba ba." Tassss. Shi da yayi marin da ita da ya mara su ka kama zubar da hawaye lokaci guda. Komai na jikinsu da zuƙata yana nuna musu illar kalamansu ga juna da abin da su ke yi. Amma kuma wani abu daga gefe yana ingiza su da jin haushin juna na ban mamaki. RAYUWA DA GIƁI 25 Batul Mamman💖 Taurin zuciya ya hana Hamdi kukan da sauti. Sai hawaye kawai da ajiyar zuciya. Ji take kamar ta buɗe ido ta ganta a gaban Yaya. Auren za ta ce ta fasa da gaske. Gashi dai zuciyarta tana ƙaunarsa. Ƙauna da son da har yanzu bata taɓa faɗa masa ba saboda kunya da jan aji na mata. Sai dai tayi abin da zai gane shi ɗin mai matsayi ne babba. Tana tanadin kalmominta masu tsada zuwa lokacin da za su kasance a muhalli guda. Abin da ya gagareta fahimta bai wuce yadda ta rufe ido ta iya kiran shi munafuki ba. Haƙiƙa duk wanda ya santa zai yi mata shaidar tsiwa. Amma rashin kunya irin wannan kuma ga mijin aure, abu ne da ita kanta bata taɓa kawowa zata yi ba. Kuma har yanzu yadda take jin son nasa haka kuma wani irin haushinsa yake cin zuciyarta. So take kawai ya sake yin wani abin ita kuma ta cigaba da faɗa masa abin da zai ji haushi. Shi kuwa Taj ya ma rasa me yake yi masa daɗi a duniya. Juya mata baya ya yi ya runtse idanunsa. Sai ya yi yunƙurin juyawa yaga halin da take ciki, sai yaji zuciyarsa tana tuna masa kalamanta a gare shi. Ransa ya ƙara ɓaci har wani tafasa zuciyarsa take yi. Muddin za ta cigaba da yi masa rashin kunya yana kyautata zaton zai iya yi mata dukan da sai an ɗagata....Duka??? Ai ko ƙannensa mata ba za su yi masa wannan shaidar ba yayi saurin kwaɓar kansa. Me ya kai shi marinta? A hankali ya juya su ka fuskanci juna. Kumatunta ya yi shatin yatsunsa raɗau. Gabansa ya faɗi da ganin aika aikar da ya yi a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Wayarsa ya ɗauko ya kira Sajida don tabbas ba zai iya kai Hamdi gidan a haka ba. Hamdi na cikin yanayin ɓacin ran nan taji yana cewa ba zai sami damar kaita ba. Da haka ta gane da wa yake wayar. Bata san me Sajidan ta ce ba ya bata wannan amsar. "Lafiyarta ƙalau, kawai dai tana cikin yanayin da bai kamata taje ko ina ba. So please ki min alfarma kada ki faɗa a gida cewa bata zo ba." Kallon mamaki Hamdi ta fara yi masa. Kafin kuma cikin fushi ta fara neman karɓe wayar. Za ta soma ɗaga murya ya danne wayar da kafaɗarsa ita kuma ya sanya hannu guda ya rufe mata baki. Ɗayan kuma matseta ya yi a jikinsa da shi. Ya yi ɗan murmushi da Sajidan ta soma cewa ta gane duk da muryarta ta bada ita. "Ba fa abin da kike tunani bane wallahi. Fitowar ce dai kawai ba zan iya ba." "Ko dai bata da lafiya ne?" "She is fine. Bari tayi miki magana." Kallon gargaɗi ya yi mata kafin ya cire hannunsa daga bakinta a hankali ya kara mata wayar a kunne. Ta ɗaga jajayen idanuwanta ta dube shi. Kalmar 'please' ta karanta a laɓɓansa. Ranta sosai yake ƙuna. "Ya Sajida." "Alhamdulillah" hankali kwance tunda taji muryarta ta ƙara da cewa "asha soyayya lafiya." Da sauri Hamdi ta yanke shawarar fađa mata me ya faru. "Mar..." Bai bari ta ƙarasa ba ya cire wayar. Ta buɗe baki za ta yi magana da ƙarfi yadda zata ji ya zauna tare da ita a jikinsa ya turata ƙuryar kujera yana girgiza kai. Dolenta tayi shiru kawai sai harare harare bayan ta tattare ƙafafunta ta cure jiki waje guda. Sam ba zai yarda a ganta da shatin nan har a fara tambayoyi ba. Muryarsa ya gyara ya ce "Don Allah Sajida. I realy need this favour from you. Kin san dai ba zan cutar da ita ba. Duk da tana ta rigimar sai na kawota." "Subhanallahi. Ya Taj me ya kawo wannan maganar? In sha Allah babu mai ji. Ita kuma kada ma ka biye mata." "To nagode." Akan centre table ɗin wurin cushion chairs ɗin mai kyau na gilas ya ajiye wayar ya fuskanceta. Zuciyarsa tana ta kai komo wurin faɗa masa ƙarya da gaskiya. Ya rasa tudun dafawa guda ɗaya. Hannunsa ya kai kumatunta zai taɓa tayi saurin karewa da nata,tana mai sadda kai ƙasa. Bai kulata ba ya riƙe hannun nata ya kai ya taɓa inda ya yi marin. Baya jin za ta kai shi jin ciwon wannan abu. "Am sorry" ya ce muryarsa a shaƙe. Ai kamar ya kunna famfo. Sabbin hawaye su ka sauko mata. Muryarta har ta soma dashewa ta ce, "Mari na fa kayi." "You hurt me with your words Hamdi. Munafuki, kuma ki ce ban haifu ba?" Cikin kuka tana ajiyar zuciya ta bashi amsa "Allah maganar da kanta ta fito. Ban yi niyya ba." Muryarta ta sake karyar masa da zuciya. "Duka ba halina bane. Ki yi haƙuri." Da ka ta amsa. Ya sanya hannayensa duka ya rungumota. A lokaci guda kuma zuƙatansu su ka dinga harbawa da faɗuwar gaba. Kamar hakan laifi ne gagarumi. Kusan a tare su ka saki juna. "Mu yi sallah sai na samo miki abinci. Me za ki ci?" Zumɓura masa baki tayi "ni bana cin girkin maza." Ya ɗage gira yana ɗan murmushi "da gaske?" Ta san manufarsa shi yasa ta ce "sai na Abbana kaɗai." "Za ki ci nawa nima." Ya ɗauko copy ɗin menu ɗinsu daga kan table ɗinsa ya bata. Ko buɗewa bata yi ba ta ce " abin da babu a nan zan ci." "No problem." Sallar azahar su ka yi. Ya ce ta jira shi zai iya kaiwa awa ɗaya kafin ya dawo. Tana ji ya rufeta da muƙulli ta waje. Ta koma kan kujerar da ta taɓa yin bacci ta kwanta ta rufe ido. Ƙamshin turaren Salwa da ya kama office ɗin yana cigaba da shigarta a hankali. Shi ma kuma da ya shiga kitchen ɗin, ƙamshin da ya rage a wuyansa tunda ya wanke hannayen a wajen alwala ne ya dinga bugarsa. Yaransa suna son zuwa ganin sabon girkin da babu a menu ɗinsu amma a karon farko ubangidan nasu bai bada wannan fuskar ba. Ya gama dafa Afghani pulao ɗinsa yana kaucewa haɗuwa da Abba. Saboda gani yake suna ganin juna zau gane me ya yiwa ƴarsa. *** Ummi da Salwa rungume juna su ka yi cikin farinciki bayan ta koma. Alh. Usaini yana daga cikin mota yana kallonsu. Murmushi ya saki na samun nasara. Malamin tsibbun da ya bashi turarukan ya tabbatar masa da cewa babu abin da zai hana shi samun biyan ɓukata. Duk abin da zasu yi basu isa su kara dashi ba. Turaren farko na raba Taj da matarsa wanda shi ba abu bane dake gabansa, ya dai karɓa ne saboda Ummi da Salwa da za ta yi musu aikin. Sanin halin mata na barbaɗa da surutu, idan Ummi taji shiru tunda ta san inda yake za ta iya tona masa asiri. Ba dai tsoronta yake ji ba. Wani ƙuduri ya ɗora akanta wanda baya son a sami tangarɗa a gaba. Babban aikin yana ga turare na biyu wanda Taj da Hamdi basu ma ji ƙamshinsa ba. Shi ne mai muguwar tsadar wanda a sannu zai kassara Happy Taj sai dai a dinga faɗinsa kawai a labari. "Baki ga idonta ba da ta ganni a jikinsa." Cewar Salwa tana ƴar dariya. Magana ta gaskiya ita ce yau tayi abin da bata taɓa ba. Shigarta da rungumar Taj babu guda da ta saba dashi bisa tarbiyar mahaifinta da Ahmad. Son zuciya da rashin haƙuri yasa ta tsallaka titin da Mami taso tayi amfani da kyanta taje gareshi tuntuni. Ummi ta bata hannu su ka tafa "Muna nan dake za ki ji anyi saki nan da ƴan kwanaki" "Banda rashin kamun kai ma ba ayi bikinsu ba amma take binsa har office? Me kike tunanin zai faru da ban je ba? Kuma fa babanta a wajen yake." "Ɗan daudu har wani uba ne? Ƙila ma shi zai kitsa mata ya ce ta dinga zuwa. Kin san fa su sana'arsu tambaɗewa tayi yawa. Da ba ƴarsa ya aura ba ma zai iya kawo masa wata." Salwa ta jinjina kai "ai kuwa dole ma su rabu. Ba zan ma yi zaman kishi da ƙazamai irinsu ba." "Turaren nan ƙarshe ne. Kuma ko asiri tayi ta same shi to wanda ya bani wannan ya ce min babu wanda ya kaishi iya sihiri." "Idan anyi aurenmu za ki kaini wajen Ummi. Ko don gudun matsala a gaba. A bani shi a hannu in dinga juyawa." Wata uwar shewa su ka sake yi. Ummi tana ta son Salwa tayi ta tafi amma taƙi motsi. Ita kuwa ba don ta matsu ayi aikin ba da ba za ta fito ba. Ɗan jarabar gidansu Baballe yana hanya. Idan Iyaa ta faɗa masa yawonta da ya ƙaru a kwanakin nan bata san me zai yi mata ba. Wata zuciyar har tana raya mata ko su ma ƴan gidan ta samu a rufe musu baki. Kuma a kautar da idanunsu daga kanta. *** Irin mutumci da karamcin da Yaya take gani a wajen bayin Allahn nan dake gabanta sai hamdala. Mata huɗu ne. Ɗaya ance mata ƙanwar Alhaji ce Amma. Sunan ba baƙonta bane a wurin Taj. Matar ta haɗu iya haɗuwa amma she is so down to earth in ji bature. Girman kai da nuna isa duka babu su a tare da ita. Mata ukun kuma Hajiya ce da Mama da Umma. Su kam ko cikinsu ɗaya iyakar abin da ido zai gani kenan. Allah Yasa ita ma bata yi ƙasa a gwiwa ba. Ta kira Iyaa da kuma su Anti Zinatu saboda bata san me za su tattauna ba. An dai ce mata akan maganar biki ne. "Ranar Asabar in Allah Ya yarda maza za su kawo lefe. Sati mai zuwa muke son ayi biki ta tare." Hajiya ce take wannan bayani. Amma kuma ta ce "ayi mana haƙuri mun zo da maganar a taƙaitaccen lokaci. Mun ga babu amfanin ayi aure kuma duka ba wani uzuri ne a gabansu ba ace tana gida har yanzu" Anti Zinatu ta nuna musu hakan ba zai yiwu ba "Wannan gaskiya ne. To amma Hajiya kun san shiri irin namu yana buƙatar lokaci. Ina laifin wata guda ko biyu? Mai ƴaƴa mata baya rasa ɗan tanadinsa. To amma ba zai isa ace mun rufeta mun kai ɗakin miji ba gaskiya." Jin haka Amma ta ce mata "Hajiya Zinatu mu ba baƙin juna bane. Wuri guda muka tashi. Babu zancen ɓoye ɓoye. Na tabbata kun san akan girki Yaya Hayatu ya kori ɗansa daga gida. Haka nan ba za mu manta yadda ya juyawa kyakkyawar zumuntarsa da Yaya Habibu baya akan ƙaddarar da ta same shi ba." "Haka ne." "Babu wanda ya taɓa kawowa zai amince da auren nan amma gashi anyi. Mu duka nan muna tsoron kada jinkiri yasa ya ɓullo da wani abin. Tunda ko me Taj ya yi baya burge shi. Don Allah ku barmu mu bawa duk maraɗa da mahassada kunya." Ita dai Yaya jikinta ya soma sanyi. Anya ba wani abin su ka ji ba wanda yasa su ke so a gaggauta bikin nan? Kada fa azo a mayar mata da ƴa ƙaramar bazawara idan Alhaji ya canja ra'ayi. Bata yi nauyin baki ba kuwa ta faɗa musu. "Ni dai idan kun san da matsala don Allah ku faɗa mana sai a yiwa tufkar hanci tun wuri." "Ko ɗaya. In sha Allahu alkhairi zamu ƙulla. Mu dai fatanmu ku bamu haɗin kai. Zancen shiri kuma wallahi Innar Taj da ƴan uwanta sun ce ko tsinke kada ku damu da saye. Komai na biki su za su yi." Cewar Umma don ta kwantar musu da hankali. "Ayi haka?" Amma ta ce "An ma yi. Ba don abubuwan da su ka gabata ba ina da yaƙinin da Yaya Hayatu ne zai aurar da ƴaƴan gidan nan. Haka nan Allah Ya haɗa jininsu wanda a yanzu idan ina kallon Taj da Kamal su suke tuna min. Bambancin shekaru bai hana su ƙulla kyakkyawar mu'amala ba." Yaya da Anti Zinatu sun yi ta ja amma babu yadda su ka iya da waɗannan gogaggun matan. Ƙarshe Yaya ta ce bari ta sansanar da Abba. Ɗaki ta koma ta kira shi a waya. Ya tuna yadda su ka yi da Taj yace ta amince. Zai san yadda ya yi tunda anyi aure Hamdi ba ikonsu bace. Idan su ka cigaba da ja'inja ba zai amfanesu ba. Yau ko ƙofa Taj ya ƙwanƙwasa yace a bashi matarsa basu da hurumin hanawa a shari'a. Balle kuma bidi'o'in biki da ko babu su aure ya ɗauro. Sun nuna jindaɗinsu da amsar da ta kawo. Cikin farinciki Mama ta zayyane musu yadda su ka yi nasu tsarin bikin. Idan akwai abin da su Yaya su ke so sai su faɗa. Alhamis mai kamawa za ayi kamu. Ranar Juma'a kuma dinner. Asabar ana la'asar za su zo su ɗauki amarya. A kaita gidan Alh. Hayatu. Daga nan Taj zai ɗauketa (wannan shirin Amma ne. Tayi rantsuwar Taj ba zai fara rayuwar aure ba sai ya taka gidan mahaifinsa. Kuma da izinin uban.) Iyaa ta ce hakan ya yi musu. Ranar asabar za su yi yininsu a gida. Kuma tana roƙon a barsu su ɗauki nauyin abinsu. Dariya ta bawa su Hajiya. Kowa ya yi na'am da yadda zaman ya kasance. Aka rabu cikin mutumci. Bayan an cika musu ciki da daddaɗan abinci. *** "Ba za ka ci ba?" Hamdi ta tambayi Taj bayan ya ajiye mata wani faffaɗan plate mai kyau da haɗaɗɗiyar shinkafar da sabo yasa bai jima ba ya gama dafawa. Asalinta girkin mutanen Afghanistan ne amma ya ta sami karɓuwa a wasu sassa na ƙasashen Asia. Afghani Pulao dafaffiyar shinkafar basmati ce wadda cikin kayan ƙamshin dafata harda sinadarin cumin da cardamom. Sai kuma naman ƙaramar dabba wanda ake marinating ɗinsa da kayan ƙamshi kafin a dafa shi ya yi laushi luguf. Ita kuma shinkafar ana haɗata da caras da aka yayyanka sirara kuma ƙanana. A haɗa shi da raisin (bushasshen inibi) wanda ake soyawa sama sama da sugar sannan a haɗa da nuts. Kansa da ya soma juyawa tun baysn ya sake arba da ita yake matsawa da hannu ɗaya. "Ki ci kawai. Bana jin yunwa." Ba shiri ta ture plate ɗin. "Meye haka?" Ya ɓata rai. Zuciyar tana kuma ciwo shi. Ita ma baki ba linzami yau ta turo shi "na san me ka zuba tunda na shiga tsakaninka da Salawaitu." Dariyar dole ta sa Taj "Salwa ce ta koma Salawaitu?" "Gaskiya dai na faɗa. Gashi nan ranka ya ɓaci don na canja mata suna." "Ke za ki ji daɗi a ɓata naki?" Ya tambaya yana ƙarewa yadda take murguɗe murguɗen baki kallo. "Mutum ya daɗe bai ɓata ba. Kuma na faɗa ɗin. Salawaitu, Salwanatu, Sal..." Hannunsa da yake jin kamar ƙwaƙwalwar kansa gareshi, yana marmarin sake dukanta ya damƙe a da ɗan uwansa ta baya. Dukanta yake so ya ƙara yi. Rashin kunyarta da a mizanin masu tunani ma wani ko kallonta ba zai yi ba idan tana yi shi ne yake jin kamar ya kama ta da duka. "Ki ci abincin nan kafin na dawo." Ya kama ƙofa zai fita yana ji tayi siririn tsaki. Innalillahi...har tafin ƙafarsa yake jin ɓacin rai. Garam haka ya buga ƙofa ya sake rufeta a ciki. Ta zauna tana ta faman girgiza ƙafa. Bata so ya fita ba tare da rigimar ta girmi haka ba. Ya saketa kawai ta huta. Ta kalli abincin ta janyo plate ɗin a fusace. "Idan ban ci ba ma waccan Salonin zai bawa." Ta faɗawa kanta domin ta sami nutsuwar ci. * Mota Taj ya koma. Idanunsa jawur kawai don yaƙi biyewa zuciyarsa. Shi ya tabbatar da zai taɓa lafiyarta tabbas zai ji dama a ransa. Kamal ya kira ta whtsapp. Bawan Allah sauƙi ya samu tunda aka fara sabon treatment. Kusan babu sauran kumburi. Sai duhu da yayi wanda a da ya ɗara Taj haske. Fari ne sosai kamar duka ƴaƴan Hajiya. "Happiness" Ya kira shi da wata irin murya mai rauni. Abin da yake faruwa tsakaninsa da Hamdi a ƙasa da awa biyu is not normal. Ta yaya zai dinga jin son dukanta kamar ba matar aurensa ba? Yarinyar da ɗazun nan yake jin zai iya keta bille ya aikata kowacce irin rashin kunya yau ɗinnan akanta. Da tsokana ya ce "Happy nawa na gargajiya. Ka kai Mrs Happy gidan Sajidan ko kuwa naka gidan?" Taj ya ɗan yi murmushi "I'm in trouble Happiness. Yaushe za ka dawo?" Salati Kamal ya yi kafin ya hau shi da faɗa "wane irin rashin haƙuri ne da kai ne Happy? Kwana nawa ya rage ta tare? Yanzu tana ina? Allah Yasa ba hotel ka kai musu ƴa ba." "Ba shi bane. Kai ma ka san ɗazu wasa nake maka..wata matsalar ce daban." Hankalin Kamal kwanciya ya yi. Da safe da su ka yi waya ne Taj yace masa zai je kai Hamdi gidan Sajida. Amma fa har gidan da za su zauna sai sun je. Kamal ya dinga yi masa magiyar kada ya kunyata su amma ya dage sai sun je saboda kawai jindaɗin tsokanar ɗan uwan nasa. "Ina jin ka to. Me ya faru? Ba dai sakin ta kayi ba?" Kamar zai yi kuka ya ce "Marinta nayi Kamal. I slapped Hamdi har hannuna ya fito a kumatunta." Tashi tsaye Kamal ya yi. Ya koma ya zauna sannan ya kuma tashi. "Mari? Hamdin? Me tayi?" Yadda ta kasance daga shigowar Salwa har fitarta Taj ya faɗa masa. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil." "Sai rashin kunya take min. Ni kuma ina jin kamar na shaƙeta na huta." "Daina faɗa Happy. In sha Allah zan yi booking next flight na taho." "Ana haka dama? Kana son mutum kuma kaji kana son inflicting pain a jikinsa? Happiness indai haka ake aure wallahi kada kayi. It hurts...so much." "Kuka kake yi? Happy?" Shiru bai amsa ba "Tajuddin?" Katse wayar Taj yayi. Ya shafa idonsa yaji shi a jiƙe. "What is wrong with me?" Ɗazu ma sun kallon juna da Hamdi ya yi hawayen nan. Shi yasa ya juya mata baya kafin ta gani. Bai yarda ya sake komawa saman ba sai da su ka yi jam'in la'asar yaga fitar Abba. Ya koma ya sameta tayi sallah ita ma. Kanta a ƙasa tana ta avoiding kallonsa. Hakan ya fiye masa komai. "Zo mu tafi." Kamar jira take ta miƙe. Ta hanyar da su ka zo su ka koma. Salwa baƙin naci sai da taga fitar motarsa sannan ta tashi ta tafi gida. Yau yadda zuciyarta take wasai har girkin dare ta yiwa Gwaggonta. *** Abu ya ƙara taɓarɓarewa tsakanin Hamdi da Taj amma babu wanda ya sani. Yanzu ko a waya su ke magana sai anyi faɗa. A kwana na uku wanda ranar ne Kamal ya dawo ya sanya Taj a gaba ya kira Hamdi. Irin faɗan da suke yi ya tayar masa da hankali sosai. "Ni wannan abu ya ishe ni. Kaje ka auri Salwa. Ka cinyeta. Ka haɗiyeta ma duka. Amma don Allah ka rabu dani. Bana sonka. Bana son auren." Guntun tsaki ya yi "matsalata dake bakinki baya shiru. Just keep quite for once. Maybe zamu iya komawa daidai idan kina kama bakinki." "Anƙi ɗin." "Kin san zan iya zuwa har gidan in hukunta ki ko?" Ya gargaɗeta. Kafin ya kira kuma kamar ana azalzalar zuciyarsa. Kewarta kawai ke damunsa. "Kuma aka ce maka iyayena za su zuba ido kayi yadda kake so?" Tana wani irin cije baki ta ce " Bar ganin Abbana yana yi maka aiki. Wallahi kana kuma taɓani idan na sanar dashi zai rama min." "Me ya kawo zancen iyaye kuma?" "Naga ƴaƴan masu kuɗi sun raina iyayen irinmu ne." "Allah ki kiyayeni." Ya soma magana Kamal ya karɓe wayar. Sallama ya yi wadda Hamdi tana ji nutsuwarta ta dawo harda gaishe shi. "Me yake faruwa Hamdiyya?" Kuka ta saka masa. Duk tambayar duniya ta kasa bashi amsa sai "shi ne" kawai da take ta faɗi. Da ƙyar ya rarrasheta sannan ya yi mata tambaya. "Kina son sa?" "Shi ma ba sona yake ba." Ta amsa da kuka. Kamal ya kwantar da murya "wa yake ta tashi? Ƙanwata nake tambaya. Kina son Taj?" Hamdi ta kalli ɗakinsu da babu kowa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ce sannan tayi magana. "A da ba." "Yanzu fa?" "Nima ban sani ba. Salawaitu yake so. Ni kuma sai in yi ta son shi? Haka ake yi?" Murmushi ya yi. Ya sami amsarsa koda ba kai tsaye bane. "A'a gaskiya. Abin da nake so dake dai don Allah ki bar abubuwan nan tsakaninmu. In ki ka bari wani yaji har aka raba auren ina mai tabbatar miki Salawaitun zai aura." Wawan duka Taj ya kai masa a baya. Baya ƙaunar zancen Salwa tuntuni balle yanzu da yake cikin damuwa shi da amaryarsa. Ajiyar zuciya tayi "Ba zan faɗa ba" A ransa yake auno yadda zai tsokanesu duk su biyun idan komai ya daidaita. Yana gama wayar ya koma kan Taj. "Happy ina ganin wannan maganar fa ba tamu bace mu biyu." "Me kake nufi? In faɗawa wani? In aka ce na sake ta fa?" Ya soma magana cikin tashin hankali. Nutsuwa Kamal ya yi wanda yasa Taj ya gyara zama. "Me ka ke tunani?" "Ka faɗawa Inna." "Inna kuma? Me za tayi?" "Duk matsalar duniya Happy uwa ce ƙarshenta. Ko bata magance ba in sha Allahu za ta faɗa maka yadda za ka yi. Sannan ga addu'arta da bata da shamaki. Abin naku kamar asiri." Kallonsa Taj ya yi "kai duka matsalolinka kake faɗawa Hajiya?" "Wanda ya dace lallai ta sani ba." Kallon tuhuma Taj ya yi masa "Me yasa ka ɓoye mata ciwonka bayan ka san idan tayi addu'a za ta karɓu?" Gaban Kamal faɗuwa yayi. Cikin sarƙewar harshe ya ce "ai...dama. hhhh. Saboda gudun tashin hankalinsu ne." "I see" kawai Taj ya ce. Kamal duk ya ruɗe "Kayi haƙuri don Allah. Ban ɓoye da wata manufa ba." A nutse Taj ya karance shi. Inda ya dosa daban da inda yake tunanin Kamal ya dosa. Kenan akwai abin da Happiness yake ɓoyewa wanda bai sani ba? Shi ne mai dogon bakin faɗa masa komai wato. "Akwai abin da ka ke ɓoye mana ne banda allergy da asirinka ya tonu?" Wani gwauron numfashi da Kamal yaja sai da Taj yaji hantar cikinsa ta kaɗa. Babu shakka akwai sirrin da bai sani ba. Zai kuma sani ne don Kamal bai isa ya ninke shi baibai ba tunda ya gano da matsala. "Shi ne. Allergy ɗin ne. A China ma ya tashi. Ba ka ga har wani duhu nayi ba?" "Na gani. Yanzu nake shirin cewa ko man bleaching ɗin naka ne ya ƙare a can?" Kamal ya taso ya yi kansa. Su ka gama zolayar juna sannan Taj ya koma cikin Happy Taj. *** Shiru shiru Salwa tana jiran wayar Taj amma ko flashing babu. Hankalinta ya soma tashi. Kwanakin da aka ɗiba domin aurensu sun kusa. Ta kira Mami tana ta kuka. Mamin ta ce mata ta taho gida. "Idan na ƙara nesa dashi ai babu lallai ya tuna dani ma." "Ki taho nace miki. Zan sake shiri." Ta samu Salwan ta amince za ta dawo. Sai dai bata san ta ina za ta fara ba. Alh. Mukhtar ya sake kiran Alhaji akan maganar ranar da za su je wajen kawunsa amma ƙememe yaƙi ɗauka. Baya son yi masa ƙarya sannan kuma baya son faɗa masa gaskiya. Idan ya faɗi gaskiyar girmansa da kullum yake tattali ne zai zube. Daga baya ne ya tausaya masa da yawan wayar ya ɗauka ya ce ya ƙara wata guda. Saboda wasu uzurirrika da su ka taso masa. Alh. Mukhtar dai tunda ya sami amsar bawa Mami hankalinsa ya kwanta. "Nufinsa sai waccan yarinyar ta tare sannan zai auri Salwa?" "Ina laifi?" "Ai kuwa akwai shi tunda nima ban zauna da kishiya ba. Ƴata ma daga ita sai miji." *** Girki ya faɗo kan Inna ranar Juma'a. Da ta haɗa abincin Alhaji Bishir na shigowa ta ce ya kai masa. Kuma bata leƙa ɓangaren ba kamar yadda su ka saba. Mai girki za ta je ta zuba masa abinci su yi hira. Idan ya gama ta aikawa sauran matan cewa ya dawo. Duk za su zo a ɗan taɓa hira sannan su tashi. Abinci ya yi kusan awa guda Alhaji yana kallonsa. Ga yunwa ga gajiya amma yaƙi zubawa. So yake yaga iya gudun ruwan Zainabu Abu. To dai tun bayan masallaci har la'asar bata shigo ba. Da ya dawo daga masallaci cikin gidan ya shiga ya wuce ɗakinta. Jallabiya ce a jikinsa yana danna counter mai fasalin carbi ta sama. Babu kowa a falo. Ya shige uwar ɗakin. Yana sanya ƙafa ita kuma tana ɗora waya a kunne. Don ya san da wa take magana ta kira Taj da sabon suna. "Angon Hamdi" A tunanin Alhaji ko da gangan ta ɗauki wayar. Hannu yasa ya karɓe. Ganin sunan Taj da gaske sai ya miƙa mata. Ita kuwa ta saka speaker yadda ta saba idan ita kaɗai ce a ɗakin saboda wayarsu bata ƙarewa da wuri. "Inna kina ji na kuwa?" "Me ka ce?" Bai san yadda za ta ɗauki maganar ba amma dole ya đauki shawarar Kamal yau. Faɗan da su ka yi da Hamdi a motarsa Allah ne kawai ya bashi ikon mallakar kansa ya buɗe mata ƙofa ya ce ta fita. Daga zuwa kai mata kati cibi ya zama ƙari. Saboda yau ta iya bakinta bata ce komai ba shi ne ya ce ba a yi mata tarbiyar godiya ba. Ai kamar jira take. Tunda ta buɗe baki ta fara surfa rashin kunya sai da yaji inama bai je gidan ba. Gyaran murya ya yi "na ce ko za a fasa bikin?" Alhaji da ya kama hanyar fita sai gashi ya dawo. Inna tayi sauri za ta mayar da wayar iya kunnenta ya harɗe fuska. Taɓe baki tayi a ranta ta ce ana so ana kaiwa kasuwa. Dama taji yadda ya rikice da yaji bashi da lafiya. "Kai da ka san baka son biki ne yasa ka bari mu ka zazzage asusunmu? Haƙuri za ka yi kawai." "Uhmmm, Inna ba bikin ba. Auren nake nufi." Bata san lokacin da ta gyara zama ba. "Ka fara shaye shaye ne? Auren? Saki fa kenan." Baya son yawan tada maganar don ransa ƙara ɓaci yake. Amma dolensa ya faɗa mata gaskiya. "Matsaloli muke ta samu. Kullum sai mun yi faɗa." "Wannan shaiɗan ne kawai. Ku dage da addu'a." Ta ce, hankalinta ya soma kwanciya. "Inna har marinta nayi." Shiru ya yi yana jiran yaji me za ta ce. Ta kalli Alhaji shi ma ya kalleta. "Taj ka sameni a gidan Yaya Malam (yayanta na biyu.)" Ta miƙe ta dubi Alhaji da ya yi tsaye kamar an dasa shi. "Ka yi min izinin fita?" "Jeki." Hijabi kawai ta ɗauka ta fita ta shiga ɗakunan su Hajiya ta ce musu ga inda za ta je. Duk su ka bata saƙon gaisuwa ga iyalin gidan. Direba ta kira su ka tafi. Aka bar Alhaji da tunani. Yadda hankalinsa ya tashi sai da yaji kamar ya ce Taj din yazo gida. Abin da mamaki ace wai shi ne da marin mace. Wace irin tarbiyya Habibu ya yiwa ƴaƴansa? * Ƙasa da awa guda uwa da ɗa su ka keɓe a falon maigidan. Taj ya zayyane mata abubuwan da su ka faru. Bata ko tambaye shi me ya kai shi tafiya da Hamdi wurin sana'arsa ba. "Idan na fahimta da kyau tun daga zuwan Salwa ku ka fara faɗan?" "Haka ne. Na so yi mata bayanin babu komai a tsakaninmu amma ta rufe ido tana gaya min maganganu." Inna tayi salati sannan ta ce "ya maganar azkar? Kana yi?" Kai ya sunkuyar "ina yi." "Ni da kai ne Taj. Ka faɗa min gaskiya." "Allah ina ƙoƙartawa Inna." Ya kuma faɗa don ta yarda da shi. Aikin gama ya riga ya gama. Ko yana yi dama ba zai hana ƙaddara da ikon Allah faruwa ba. Sai dai ya sauƙaƙa. Gargaɗinsa tayi akan kada ya yarda su sake haɗuwa. Wayar ma ko ita ta kira kada ya ɗauka. Sannan mafi mahimmanci ya tabbatar kalmar saki bata shiga tsakaninsu ba. "Ka tashi ka tafi. Za ka ji ni in sha Allah idan mun gama magana da Yaya Malam. In ma sihiri ne to in sha Allah zai koma ya ci mai shi. Addu'a, sadaka, qiyamul laili da hanyoyin neman kusanci da Allah nake so ka runguma kaji ko?" Ya gyaɗa mata kai kamar yaro. "Ki yi haƙuri na tayar miki da hankali. Alhaji ya kamata na nema..." Wani irin tausayinsa ne ya kama ta. Ta dafa kansa tayi masa addu'o'in neman tsari wanda Ayatul Kursiyyu ke kan gaba. Sai da ya tafi ta fashe da kuka. Duk ya wani rame. Kana ganinsa ka san hankalinsa ne ba a kwance ba. A gidan ta zauna har yayan nata ya dawo ta faɗa masa. Ya kwantar mata da hankali. "Kada ki ƙulla sharri akan wanda ki ke zargi. Shi zargi dama bashi da kyau a addini. Zan kira shi ya zo gobe in sha Allah." "Yaya har zasu yi lafiya kafin bikin?" Ta tambaye shi da damuwa. "Ke ta biki ma kike wato?" "A'a, tsorona kada ta tare yadda yake cewa yana jin kamar yayi ta dukanta yaje ya lahanta ƴar mutane." Kwantar mata da hankali ya yi. "Allah zamu roƙa ba mutum ba. Shi kuma ba ayi maSa gaggawa. Tunda ya ce idan mun roƙa zai bamu to ki saka ranki a inuwa. Ko daga ina matsalar take bata wuce Qulhuwallahu, Falaqi da Nasi ba." Da ƙwarin gwiwarta ta fita daga gidan. A ranar yadda ta hana idonta bacci haka ta tada Taj. Shi kuma ya sami kansa da turawa Hamdi saƙo. (Idan Allah Yasa kin gani kafin safiya ki tashi ki yi sallah da addu'a. Idan akwai alkhairi cikin aurenmu Allah Ya warware mana matsala.) Sai uku da rabi ta gani da ta tashi fitsari. Ta ɗauro alwala ta zauna tana ta kuka. Zee na jinta amma ta ƙyale. Yaya ce ta bata aikin sanya mata ido saboda kwanakin nan kowa ya san ta canja. A ɓangaren Alh. Hayatu kuwa, yana ganin shigowar Inna ya kira Yaya Malam. "Ka biyo sahun ɗanka ne?" Malam ya faɗi kai tsaye domin duka gidansu dai haushinsa su ke ji. Murje ido ya yi tunda in ba a nan ba babu wanda zai tambaya kuma "A gabana ta fara wayar shi yasa. Da gaske ya mari matarsa?" "Ƙwarai kuwa." "Kaga abin da nake faɗa ai. Namiji mai irin sana'arsa fa ji yake kamar shi ma mace ne. Shi yasa yake daidaita tunaninsa da nata. Cikakken namiji ba zai fara kai hannu daga aure ko wata ba ayi ba." Yaya Malam dai dariya kawai ya yi. Ya shaida duk wata rigima da yake yi bata yi tasirin hana shi son ɗansa ba. Abin da yaji ya faɗa masa. Ya yi godiya su ka yi sallama. Washegari ya san da zancen kai lefe da maza za su yi. An kira shi ya gani bayan an kammala komai. Harda akwatuna huɗun da Amma ta taho dasu waɗanda kayan ciki su ka amsa sunan kayan ƴar gata. Tunda ba dashi za a yi ba babu wanda ya sa masa ido da ya yi sammakon fita. Ko matansa bai faɗa musu inda za shi ba. Ya dai yi musu sallama ya fice. Yana zama a mota ya ce da direbansa Bauchi za su je. "Bauchi Alhaji?" "Ba ka san hanya bane?" Da sauri ya hau bada haƙuri "na sani. Allah Ya kai mu lafiya." "Amin" Zuciyarsa a baka take da ɓacin rai. Bai runtsa ba jiya tunda ya yi waya da Yaya Malam. Arziƙin rabon Ahmad dake tsakaninsa da Mami yasa ba zai haɗata da hukuma ba. Amma tabbas sai tayi nadamar kai ɗansa gaban ƴan iskan bokayenta. Bai san bata da masaniyar abin da Salwa tayi ba. *** Tun dare Ƴar Ficika da yaransa su ke aikin kayan kwalamar da za a tarbi masu kawo lefe dasu. Shi ya ce da Abba lallai ko ruwa kada ya siya. Za su kawo komai. "Abin zai yi yawa. Don Allah kada ka wahalar da kan ka. Kada ka manta girma fa ya cimmana." Yar Ficika ya karya kai yana riƙe da ƙasan jallabiyarsa. "Haba Simagade, ina aikin yake a nan? Ai idan daɗin miya bai karya ludayi ba, wahala ba za ta karya guga ba. Ka ganni nan..." ya bubbuga ƙafa a ƙasa "digirgir nake a tsaye. Abin da zan yi in daɗaɗa maka ba zai taɓa zame min wahala ba." Abba ya yi masa godiya. Ƴar Ficika ya koma cikin kitchen ɗinsu inda ake ta yanka naman kaza. Guda cikin yaran ya samu yana gyara wutar gashi. "Tasalluwa me za ayi da wannan uban garwashi?" "Ba gasa naman za ayi ba?" Duka Ƴar Ficika ya kai masa a ƙeya "sai shegen rawar kai yawa akwalan keke. Abin da ya kamata ba shi kake yi ba. A zafin nan za a gasa nama tun yanzu a ajiye? Ba sai ya buga ba?" Tasalluwa ya ɓata rai "daga abin arziƙi?" "Idan aka basu naman yana hamami ai raini za ka jawowa ɗiyar tamu. Ko baka san ɗan Alh. Hayatu Maitakalmi take aure ba?" Tasalluwa ya tafa hannuwa "eyyee, ashe abin babba ne, wai an kashe kwarkwata da taɓarya. Aikin na bajinta zamu yi." Wani dake kusa yana jin hirar tasu ya ce "ai ke dai Allah Ya kawo kuɗi talauci yaji kunya. Nan da lokacin da za ta haihu kaji hamsin za mu babbake ba ashirin ba." "Ahayyeeee" Su ka dinga tafawa ana tsara irin girkin da za ayi idan Hamdi ta haihu. A cewarsu aikin yau ba ayi yadda ya kamata ba saboda tsadar rayuwar da ake fama. A haka kuma ba ƙaramin ƙaƙari Ƴar Ficika ya yi ba. Kaji ashirin za su yiwa gashin tukuba, meatpie, donut da cake duka guda ɗari ɗari yaran da su ka ƙware a nan fannin su ke yi. Sai abincin gargajiya. Tuwon shinkafa da miyar gyaɗa da kabewa wadda taji naman rago da alayyahu, waina, funkaso da alkubus kuma da farfesun kai da ƙafar rago. Sai lemon ginger da zoɓo da su ka ƙware wajen yi ana zubawa a sababbin robobi masu tambarin sunan gidan abincin nasu. Shi dai ya haƙura ya san ya makara, da wuya ya haifa. To amma fa wanda Simagade ya haifo musu sai inda ƙarfi ya ƙare. RAYUWA DA GIƁI 26 Batul Mamman💖 *** Shirin fita zuwa wani katafaren wurin gyaran jiki da Amma ta biya kuma ta ce za ta turo direba ya ɗauki Hamdi kafin ƴan kawo lefe su iso take yi. Zee da ƙanwar Anti Labiba mai suna Fadila ne ƴan rakiya. Komai cikin mutuwar jiki take yinsa musamman da jiya bata sami isashshen bacci ba. Tayi ibada kuma tayi kuka sosai. Yawanci akan ce asiri birkita tunanin mutum yake yi har ya kasa gane taƙamaimai me yake damunsa. Halin da take ciki kenan yanzu. Tana son Taj, sannan kuma tana gudun kasancewa inuwa guda da shi. A daren jiya ne da tana addu'a ta fara mamakin wannan sabon al'amari da ya tunkaro su. Alaƙarta da Taj ba irin wadda ake shan wahalar farata bace. Lokaci guda su ka yi clicking kamar hagu da daman mayen ƙarfe. Irin wannan rashin sakewar kafin a saba duk basu fuskanta ba. Lokaci guda su ka karbi juna a sabon matsayin da Allah Ya ajiyesu. "HAMDIYYA!" Firgigit ta dawo hayyacinta da jin kiran Yaya da ƙarfi. "Tunanin me kike yi haka?" "Babu komai" ta miƙe tsaye tana neman mayafinta. "Me ki ke nema?" Yaya ta tambayeta. "Mayafina." "Wanda ki ka yafa kuma fa" Kallon jikinta tayi ta ce "au..." "Zauna Hamdi. Magana za mu yi." Bata kawo komai ba tunda a tunaninta ta ɓoye yanayinta sosai ta zauna. Yaya ta tsareta da tambayar me yake damunta kwana biyu. Ta fara rantse rantse Yaya ta ce bata san zance ba. "Idan ba wata uwar gareki a waje wadda ta dace da sanin damuwarki ba ina son sanin me ya sanyaki kwana kina sallah da kuka." Gaban Hamdi faɗuwa ya yi. Ba za ta iya faɗawa kowa Taj ya mareta ba. Haka kawai take ganin kamar za su yi rabuwa ta har abada idan aka sani. "Yaya babu komai." "Kina ganin saboda lalurata da yanayin Abbanku bamu isa mu share miki hawaye idan kina da damuwa ba ko?" Ɓacin ran uwa abin gudu. Nan da nan hankalinta ya tashi ta soma bata haƙuri. "Ki daina faɗin haka. Wa nake da shi bayan ku?" Da wata irin murya mai ban tausayi Yaya ta ce "Ba yau ki ka fara ba. Tun ƙuruciyarki na san kin tashi da ganin kamar bamu cika iyaye ba." Kuka sosai Hamdi tayi. Wannan banzan tunanin tun yaushe ta ajiye shi. Ummi ta ankarar da ita girman mahaifinta a lokacin da take ganiyar gudun a alaƙantasu. Yaya ce dama tun farko bata taɓa rainawa ba. Tana son abarta a yadda take. Wannan furucin da tayi ne dai ya sake karyar mata da zuciya tayi ta kuka tana bata haƙuri. Bayan wani ɗan lokaci da Yayan ta ce ta haƙura shi ne ta faɗa mata rabin gaskiyar zancen. Akwai mai son Taj, ta dawo da wayar da su ka taɓa yi ta ce ai matar har kiranta tayi ta tsorata ta. "Wai idan na yarda na tare sai ta illata rayuwata." Dariya taga Yaya tayi kafin kuma ta ce, "Shi ne kike kuka? Kodayake Allah ki ke gayawa. Ya isar miki akan komai. Duk da haka cewa Yayi ka tashi In taimakeka. Kada ki yarda wata mace ta zama silar hawayenki a gidan miji." "Ko da yafi sonta?" Hamdi ta tambayeta tana kuka. Da yake Yaya bata saba ganin ƴar tata ta nuna rauni irin haka ba sai take ganin son da take yiwa Taj ne kawai bata son abin da zai shiga tsakaninsu. Kalaman da za su kwantar mata da hankali ta zaɓo. A cikin ranta kuma tana ƙudurta yi mata addu'a da sauran ƴan uwanta akan kada Allah Ya haɗa mazajensu da matan banza. "Yafi son nata ya aureki? Ko kin manta ba tayinki aka yi masa ba?" "Haka ne." "Ki cigaba da addu'a sannan ki dage ki ƙwaci kanki a gidan aure. Mu bamu san boka da malami ba. Kuma bamu san makirci da sharri ba. Indai kin tsaya a tarbiyar musulunci ta zaman aure da kuma riƙo da dabarun zaman duniya za ki ga baki da yawan damuwa." Kai tsaye ta ce "Yaya kin koya mana dabarun zaman duniyar ne?" Yaya tayi dariya "Hamdi kenan. Da gaske ki ke son kare martabar aurenki. Hakan ya yi kyau. Lusarar mace bata taba burge miji dama." Ta gyara zama "su dabarun zaman duniya yau ce take koya maka. Sai kuma amfani da dama idan ta zo da kuma zurfafa tunani da hangen nesa. Sauri ko gaggawa a komai ɓata lamura suke. Saboda haka don wata ta kira ki tana surutu kada ki yarda ya zama dalilin da za ki ce kin gama aure ko kin bar mata miji. Ki ƙoƙarta. Sai idan kin yi naki kin ga mijin ƙwallon mangwaro ne sannan za ki jefar dashi ki huta." Ji tayi kamar an sauke mata dutse daga zuciyarta. Ta faɗa jikin Yaya tana dariya mai haɗe da jin kunya. Yaya ta rungume abarta tana shi mata albarka. Da Zee ta leƙo domin ta faɗa musu zuwan direban da zai ka su tayi mamakin yadda ta gansu. "Wallahi nima sai anyi dani." Ta daka tsalle dama idan shirmenta ya motsa sai addu'a, ta faɗa kansu. Sai washhh ɗin Yaya kawai kake ji tana cewa su tashi za su ɓalla ƙashin da bashi da ƙwari. *** Cikin ginin wani kamfanin robobi wanda a halin yanzu shi ne dukiyar taƙamar Alh. Mukhtar da iyalinsa direban Alhaji ya shiga. Akwai mota a gabansu ta wasu manyan ƴan kasuwa guda biyu wanda su ma direba ne ya kawo su. Su ne su ka yi musu jagora har wurin. Da su ka firfito da girmamawa su ka zo wajen motar Alh. Hayatu su ka sske tarbarsa tunda dama a hanya su ka haɗu da farko. "Alhaji ni fa ka sanya ni a duhu da ka ce mu faɗawa Alh. Mukhtar lallai ya tafi kamfani yau duk da asabar ce kana son ganinsa. Allah Yasa lafiya dai." Cewar guda daga cikinsu. Fuskar Alh. Hayatu babu fara'a ko ɗigo ya ce masa "lafiyar kenan. Yana da kyau mutum ya dinga zaga dukiyarsa ne saboda halin rayuwa." "Shakka babu uban Kantin Kwari da kewaye." Ɗayan ya ɗaga hannu yana jinjina masa "Ka san na faɗa muku akwai wata alaƙa tsakanina da shi." "Ƙwarai kuwa. Saboda ka ce kuna da dangantaka. Lokacin kuma mu duka bamu shirya barin kasuwa mu zauna a nan ba mu ka bashi. Yanzu gashi cikin ikon Allah ya mallaki kaso ashirin da takwas cikin ɗari. Kasuwa tayi albarka, shi yasa mu ka bari ya zama partner ɗinmu." Na farkon ya yi bayani a taƙaice. Alhaji ya gyaɗa kai yana tuno wasu ƴan shekaru a baya. Lokacin Ahmad bai yi aure ba amma idan ka ganshi tamkar mai mata huɗu da ƴaƴa goma. Ya fige tamkar kazar mayu. Kullum yana rama ga zafin nema kai ka ce wani yake ciyarwa. Matan gidansu su ka shiga damuwa. Alhaji ya tsananta bincike domin a lokacin Ahmad ƙin faɗa masa gaskiya yayi. Ashe karayar arziƙi ce ta sami Alh. Mukhtar. Mami ta taso shi a gaba. Ashana wannan idan suna buƙata sai ta kira Ahmad. Ita bata yarda tayi rayuwa daidai da samun mijinta ba a lokacin. Ta ƙuntatawa yaron iyakar ƙuntata. Duk wata kadara da Alhaji ya mallaka masa ya sayar ya bata kuɗin. Idan babu yawa tayi ta bala'i da kiran za ta tsine masa. Ranar da Alhaji ya san gaskiya sai da ya yiwa ɗansa hawaye saboda tsabar tausayinsa da yaji. Gashi kuma ya san cewa ba huruminsa bane raba ɗa da uwa. Shi yasa bai taɓa hana Inna mu'amala da Taj ba. Gidansa kawai ya hana shi shiga. To dama ya san da maganar buɗe kamfanin robobin. A wurinsa ma su ka ranci kuɗin. Shi ne ya basu shawarar ɗauko wanda ya yi boko sosai wato Alh. Mukhtar aka yi masa MD. Yana fara samu Mami ta sakarwa Ahmad mara. Babu wanda ya san maganar nan har yau. "Ku kaini ofishinsa. Ina son magana dashi." Da rawar jiki su ka yi gaba. Har yanzu akwai wajen kaso talatin da biyar na kuɗin da ya ranta musu da basu gama biya ba. Hankalinsu in ya yi dubu to a tashe yake. Sun isa ofishin MD inda Alh. Mukhtar na ganinsu shi ma ya tashi da rawar jikin ganin iyayen gidansa. Aka gaisa su ka zauna. Ya miƙowa Alh. Hayatu hannu yaga babu fuska ko alamar zai karɓa. Ba shiri ya ja da baya. "Wurinka Alhaji ya zo. Ka gane shi ko?" "A'a" Alh. Mukhtar ya faɗi da gaskiyarsa "sai dai fuskar kamar na san mai irinta." Muryar nan ta Alhaji a dake ta fito ya ce "Ɗana Ahmad Hayatu Sule Maitakalmi ko?" Idanu Alh. Mukhtar ya zaro "Alh. Hayatu? Kai ne? Ikon Allah." Ɗaya daga cikin Alhazan da su ka zo tare Alhaji ya cewa ya yi bayanin matsayinsa a garesu. Tiryan tiryan kuwa ya yi duk da sun cika da mamaki. Bayan ya gama kana ganin Alh. Mukhtar ka san ya gama rikicewa don gumin da yake ko ruwan sama albarka. Alhaji ya ce waɗancan biyun su ɗan basu wuri. Su na fita ya soma faɗa. "A lokacin matarka ta so sabauta rayuwar ɗana. Shi yasa na ajiyeka a nan domin in kare Ahmad. To yau kuma an wayi gari taje tayi abin da ta saba tana neman shiga tsakanin wani ɗan nawa da matarsa." Ya yi maganar cikin ɗaga murya. "Alhaji ban sani ba wallahi..." "Ta yaya za ayi ka sani bayan kaima juyaka take yi?" "Kada kasa su koreni. Ina da ƴaƴa wallahi." Ya ce hankalinsa na neman gushewa. "Ka ce ni Hayatu na ce ta karya asirin. Ita ko wani nata sun yi kaɗan su tarwatsa rayuwar zuri'ata. Taj ba ɗanta bane. Idan na ƙyaleta akan Ahmad saboda haƙƙin uwa ne. Amma muddin ta sake shiga rayuwar wani nawa wallahi sai ta ɗanɗani kuɗarta. Ni da kake gani kaza ne akan ƴaƴana. Ina iya taka abuna idan sun min ba daidai ba domin su gyara. Amma idan wani ya kamanta zai sha tsatstsaga har sai anga jini. Ina fata ka fahimceni." Jikin Alh. Mukhtar babu inda baya rawa. Bai taba ganin mutum mai ban tsoro da kwarjini kamar Alh. Hayatu ba. "Na gane. Don Allah ka yi haƙuri." Alh. Hayatu ya tashi "ina son ganin canji a tattare da Taj kafin sati mai zuwa. Ta karya koma me tayi don ta sanni farin sani. Akwai irin abin da bana yafewa. Taɓa min ƴaƴa yana sahun gaba. Sannan ka tashi tsaye kamar kowanne magidanci ka nemi tsari daga sihirice sihircen marasa tsoron Allah." Ko kallon Alh. Mukhtar bai sake yi ba ya fita. A waje ya yi sallama da alhazawan nan ya kama hanyar Kano ko ruwan garin bai sha ba. Sallah kawai su ka yi su ka tafi. *** Abu na maza, babu wanda ya yi tunanin raini ko surutu akan gidan Abba Habibu. Irin abin da mata za su yi ta gutsiri tsoma ana cewa me ya kai shi auren wadda bata kama ƙafar arziƙinsa da na iyayensa ba. Ahmad da Kamal sun zo. Sai ƙanin Inna da kuma ƙannen Alhaji guda biyu. Irin tarbar arziƙin da Abba ya yi musu ba ƙaramin daɗi su ka ji ba. Sun riga sun san ko waye, ba a ɓoyewa kowa ba. Ga amininsa Baba Maje, sai ƙaninsa Abdulƙadir da wasu ƴan uwansu maza da su ka lallabo su ka dawo rayuwarsa bayan ganin luɗufin da yake samu. Abinci ne na gani da fađa su Ƴar Ficika su ka yi. Kuma kamar yadda ya yi alƙawari tuntuni ko hanyar gidan basu zo ba shi da yaransa. Baba Maje ya yi rawar gani ya kawo dubu ashirin a bayar tukwici. Abdulƙadir ma ya kawo sha biyar. Abba ya cike ya zama hamsin. Ƴan kawo lefe kuma su ka ƙi karɓa. Sai da Abba ya ce rainawa su ka yi saboda sun gan shi a haka. Ba shiri su ka karɓa aka rabu a mutumce. Ko rabin awa basu yi da tafiya ba gidan ya soma cika da ƴan kallon kaya. Gashi Zee bata nan. Sajida ce kaɗai take ta fama. Sai ga Iyaa ta zo da Siyama da Ummi. Ta kuma umarcesu da taimakawa Sajida wajen saka ido akan kayan da kuma aikin buɗewa mutane. Ƙiris ya rage Ummi ta haɗiyi zuciya ta bar duniya. Dama Baballe ne ya taho dasu a motarsa. Dolenta ta taho. Yawan akwatunan da irin kayan da ta gani ya birkita mata lissafi. Zuwa yanzu ma dai sakin aure ya kamata su ji anyi. Maimakon haka sai wannan uban kaya kamar za a buɗe shago. Dole ma ta kira Salwa idan sun koma gida. Abin baƙinciki yadda Iyaa ta ɗora mata aikin kula da wata ƙaramar jaka da aka shaƙare da sarƙoƙin gwal, awarwaraye, zobba da kuma sarƙoƙi na fashion masu matuƙar tsada. Sai da Iyaa ta ƙirga komai harda sanya Siyama ɗauka a hoto sannan ta miƙa mata. "Ko kwali ne ya ɓata to ku ɓata tare. Ki kula dasu sosai. A nunawa mutane arziƙin Hamdi amma a kula da masu ɗan hali da mahassada." Ummi za ta iya rantsuwar maganar mahaifiyarta da harshen damo ta fito. Bata sani ba ko tsagwaron baƙincikin da take ji a zuciyarta Iyaa ta gani. Haka nan ta karɓi jakar ba don tana so ba. Irin baƙincikin da take ji ba wai so take ta mallaki kayan ko ta sace ba. Ita da ace za su ɓace ko su ƙone ƙurmus Hamdi ta rasa da ko miliyan biyar aka damƙa mata ba za ta yi farinciki kamar haka ba. * Bayan tafiyar Alh. Hayatu, karatun ta nutsu Alh. Mukhtar ya yiwa kansa. Ya dinga haɗa ɗaya da biyu yana lissafin yadda yake aikata abubuwa da yawa bisa umarnin Mami kuma ba a son ransa ba. Ya yarda hannunka mai sanda Alhaji ya yi masa da zancensa na ƙarshe. Ji dai maganar Taj ɗin da ta ce dole ya auri Salwa. Gashi takanas akan yaron mahaifinsa ya zo ya yanka masa gargaɗi mai kyau. Rasa tudun dafawa yayi ya kira babbar ƴarsa da wani tunsni ya zo masa. A gidan take shekara talatin da huɗu duk wanda ya zo da maganar aure da kansa yake gudu. Ita da duka sauran ƴan matan gidan su huɗu da samari biyu babu uwayensu mata biyu da yake aure kafin zuwan Mami sun fita ta ƙarfin tsiya. Ƴaƴan Mami a gidan huɗu ne. Salwa da ƙannenta maza biyu. "Bushra ki ce da Mami wai na kira ban sameta ba. Kowa ya fita daga gidan zan turo mai feshin maganin sauro. Ke kuma ki zauna ki jirani. Idan akwai aikin yi ko share share bayan an gama sai ki yi." Saƙon nasa ta faɗawa Mamin da umarninsa na ta zauna tayi aiki. Mami ta saki murmushi. Yadda ta farraƙa shi da ƴaƴan yana burgeta. Gashi yau ko tishin tauna layar bata yi ba amma ya aikata da kansa. Salwa ta kira su ka fita. Samarin dama basa nan. Ita kuma Bushra ta sanar da ƴan uwanta duk su ka tafi maƙota. Ba a jima ba Alh. Mukhtar ya dawo. "Faɗa min gaskiya Bushra, Mami tana da kayan asiri a gidan nan?" Rawa jikinta ya fara. Idanunta su ka ƙara girma don tsoro da firgici. A ƙagauce ya ce "Ba mu da lokaci. Ki faɗa min idan akwai." Kai ta gyaɗa. Ya ce idan ta san inda su ke maza ta nuna masa. "Ban sani ba. Sai dai mu duba." Babbar rigarsa ya ajiye a kan kujera ya ce ta saki jiki su yi aiki da sauri. Ai kuwa yaga zafin nama. Duk gidan sun gaji da rayuwar da Mami ta ƙaƙaba musu. Ɗakin Mamin suka fara zuwa. Yana karanto surorin neman tsari ya watso duka kayan cikin wardrobe ɗinta da kowacce durowa. Sun tsinci ƙulle ƙulle da wasu ƙwarya da tarkace guda biyar. Aka koma ƙasan gado nan ma akwai. Daga nan sai ɗakinsa. Abu ya ƙazanta. Kansa har ciwo ya dinga yi saboda tashin hankali. A ɗakin ƴaran gidan ne dai ba a sami komai ba. Kitchen ma Bushra ta nuna wani ruwa da ta kan ga Mami ta tsiyaya musu a girki. Ya ɗauka ya tuttular. Kit ɗinta inda take ajiye abubuwa masu mahimmanci ya ɗauka ya muƙa da ƙasa sai gashi ya buɗe. A nan ya tsinci laya mai sunansa da ake taunawa. Sai kuma masu sunan duka ƴaƴansa banda nata. Da kuma sababbi a leda ɗaya Taj, ɗaya Zainab (Inna). "Wallahi Baba wannan take sakawa a baki ta ce kayi mana abu kuma sai kayi. Ko ranar da ka ce in na kuma fita zance za ka tsine min da ita tayi magana." Haƙuri ya bawa ƴar tasa. Ya rasa matakin ɗauka na gaba. Ita ta bashi shawarar su ƙona komai. Ya ce kada ta taɓa. Da tsintsiya da abin kwasar shara ya tattara komai ya tara a tsakar gida. Ya kawo fetur ya zuba sannan ya kira Mami ya ce su dawo. "Har maganin ya fita?" "An fasa, sai gobe." Masifa ta yi masa na katse mata baccin yamma sannan su ka taho gida. Ana buɗe musu gate ta hango shi daga shi sai ƴar shara a jikinsa ya sanya wasu tarkace a gaba. Su ka fito daga mota ta taho inda yake. Jikinta ne ya saki lokaci guda da ta gane mene ne a gabansa. "Alllll....hhhhajjii? Mmmmene nee wannnnan?" Haɗe rai ya yi sosai ya tura mata ashana da ƙafarsa. "Ɗauki ki cinna musu wuta." Jikinta rawa ya kama yi sosai. Tana ta gumi ta rasa abin yi. "Ɗauki mana!" Ya daka mata tsawa. Ta kasa motsi sai ƙullewar ciki. Salwa da taga halin da babarta ta shiga ita ma tsorata tayi. Tunda bata san kayan mene ne ba durƙusawa tayi ta ɗauki ashanar. "Baba ni bari na ƙona." Kafin Mami ta iya tare ta har ta ƙyasta ashana. Tana cillawa kuwa kayan nan su ka yi wata mahaukaciyar ƙara tamkar tashin gurneti. Mami tayi zaman daɓaro a ƙasa tana ihu. "Kin kashe ni. Salwa kin kashe gidan nan." Da faɗa Alh. Mukhtar ya ce "ta dai kashe ki ke kaɗai banda gidana." "Mami kayan meye?" Salwa ta tambayeta ganin kuka take haiƙan. Bata sami amsa ba sai daga bakin babanta. "Nagodewa Allah da Ya turo Alh. Hayatu gareni ya farkar dani mugun baccin da nake yi. Sai yau na gane ashe zaman waɗannan abubuwan muke yi ba aure ba." Mami kuka kawai take yi da gurnani. Hankalinta ya kai ƙarshen tashi. Idan ya saketa bata da tudun dafawa. A zaune ta ja jiki zuwa inda yake za ta kama ƙafarsa ya janye da sauri. "Ka rufa min asiri." "Ki rufawa kan ki dai" ya dubesu ita da Salwa dake tayata kuka "yauwa, Alh. Hayatu ya ce in faɗa miki ki warware abin da ki ka yiwa ɗansa har su ke rigima da matarsa. Idan ba haka ba kuma ki jira martani daga gare shi." Ya wuce ciki. Mami ta zauna tana tumami da kuka kafin ta tashi ta bishi ciki da sauri. "Wane ɗan? Taj? Wallahi ban yi masa komai ba." "Ki daina saurin kama sunan Allah tunda baki san shi ba. Da idona naga laya da sunansa." Mami ta kwantar da murya "Ayyaaa Alhaji, bamu yi amfani da ita ba. Dama na ajiye ne sai sun yi aure da Salwa. Ai ban baki ba ko...." Ta juya babu Salwa babu dalilinta. "Salwa? Alhaji ina Salwa?" Tayi maganar kamar wata zararriya. Tsoro take ji kada ƙona kayan nan ya janyowa ƴarta wani abu. Don dai tabbas malaminta ya sha yi mata kashedi akan kada ma wani ya gani balle a taɓa. Ɗakunan gidan ta duba bata ganta ba. Tayi wajen gate tana faman kiranta ko kallon titi bata yi. Bata yi aune ba mota ta ɗebe ta tayi sama ta dawo. Maigadin Alh. Mukhtar da ya biyota yana son faɗa mata Salwan ta fita ne ya koma ya sanar dashi abin da ya faru. Ya fito su ka wuce asibiti tare da mai motar da ya bugeta. Salwa kuwa tunda taji saƙon babanta hankalinta ya tashi. Indai Alhajinsu Taj ne ya yi waccan maganar kenan asirin ya kama su. Matsalar kawai tunda ake zargin Mami a hankali zsi gano ita ce. In haka ta faru kuma zai hana Taj aurenta idan su ka fara soyayya. Tasha ta wuce tunda da atm a jikinta ta ciri kuɗi sai Kano. Wurin Ummi za ta je ta taimaka mata da wanda za a rufe bakin Alhaji. Motarsu ko fita gari bata yi ba Alh. Mukhtar ya kirata ya faɗa mata abin da ya sami Mami. Don baƙinciki sai da tayi kuka. Haka ta sauka daga motar ta tafi asibiti. *** Mai shawara aka ce aikinsa ba ya ɓaci. Duka abubuwan da Inna ta sa Taj yi ya rungumesu hannu bibbiyu. Ƙuncin zuciyarsa ya ragu sosai. Duk da ya kan ji haushin Hamdi yana taso masa lokaci zuwa lokaci tunda fitar asiri sai a hankali, amma a zuciyarsa ya sani cewa ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba kamar yadda ya dinga ji a kwanakin baya. Banda yawan addu'a, Inna ta sa yanzu ya ware plate goma na abinci kullum sai sun bayar sadaka. Ba wai ragowar na mutane ba. Mai kyau da an gama dafawa ake packaging. Ranar farko ma na mutum ɗari biyu su ka yi aka kai asibitin gwamnati. Kusan zai rantse ma daga ranar ya fara jin canji sosai. Ciyar da mabuƙata ba ƙaramin abu bane. Duka wani jere da gyaran gidan amarya an gama shi a farkon sati. Duk wanda ya shiga kamar kada ya fito. Hatta kayan da za su saka Kamal ya kai wa Hamdi nata ana jibi fara biki. Bayan ta shiga gida ta gwaggwada ta dawo ta same shi. Ta faɗa masa babu wanda yake buƙatar gyara. Sai kuma tayi godiya sosai. "Yanzu yaya kike ji game da ɗan uwana?" Kai ta sunkuyar tana murmushi. Da ya sake yin tambayar ta ce "Alhamdulillah." "Kina ganin faɗa ya ƙare? Za ku iya zama babu tashin hankali?" "Ban sani ba ko daga wurin shi." Ita ce amsar da ta bayar da ƙaramar murya. "Nayi magana da shi. Ke nake tambaya kuma." Kunya ce ta isheta ya ce gara ma ta daina domin tunda ta shigo danginsu ta sani cewa bayan shi yanzu ta sami ƙarin ƴan uwa. Kuma kowa zai tsaya mata idan Taj ya yi nufin cutar da ita. "Zan iya in sha Allah." "Alhamdulillah. Kamar yadda na faɗa masa ku bi komai a sannu. Kada ku ce dole a yau ko gobe ku ke son ganin alaƙarku ta dawo kamar da. Wannan zai janyo muku too much expectation, wanda kuma rashin samunsa zai sa ku zama disappointed." "In sha Allah zan kiyaye." "Hamdiyya" Mrs Happy ya saba kiranta. Shi yasa Hamdiyyar ya faɗar mata da gaba. "Na'am Ya Kamal." "Don Allah ki riƙe min Taj amana. Abubuwa da yawa sun same shi. Yana buƙatar inda zai sami kwanciyar hankali." Ɗan murmuhi tayi "ai kana nan Ya Kamal sai mu dinga shawara. Ka fini sanin abin da ya dace da shi." Murmushin da Kamal ya mayar mata mai matuƙar rauni ne. Da ace idanunsa ma take kallo za ta ga sun kaɗa. "Yanzu ke ce mafi kusa dashi." "Ba zan shiga tsakaninku ba in sha Allah" ta faɗi da sauri. "Rayuwa da yau da gobe za su iya shiga. Ni dai na baki amanar Happy. Please Hamdiyya, give him the happiness he deserves." Har ya tafi tana juyayin maganganunsa masu kama da sallama. Anya lafiya kuwa? *** Idan ka ji yara na waƙar gobe Juma'a, kuturu dariya yake ko zai sami ɗan kwabo to lallai ranar ta kama Alhamis. Ta wannan satin ita ce ranar Kamun amarya Hamdi wadda iyayen ango Taj su ka yi rawar gani wurin tsara taro na burgewa. Biki ne na ƴan kasuwa kuma ƴan boko. In baka yi bani wuri. Sun tsara abinsu na yau ma mata kawai. Mazan gidansu ko mutum ɗaya ba a yarje masa zuwa ba. Daga DJ ɗinsu kuwa har mai hoto da MC duka mata ne. Daga cikin wani katari da Alh. Hayatu ya sake yi a rayuwa harda dacewa da kyakkyawar tarbiyar ƴaƴansa akan sunnar Fiyayyen halitta SAW. Ba dai a rasa nono a ruga, wani dole sai ya bauɗe. To amma dai majority a gidan sun ginu da wannan tarbiyar ta iyayensu mata. Wannan yana daga cikin dalilan da su ka sa Alhaji ya kan kasa yiwa wanda ya kuskure uzuri. Shi fa kusan komai Allah Ya bashi. Bai san wani nau'i bane na gwajin rayuwa. Idan ya ƙanƙantar da kai ya yarda rahama ce daga cikin taskar Ubangijinsa sai Allah Ya ƙara masa da lada mai gwaɓi. Idan kuwa girman kai da jin cewa isarsa da iyawarsa ne su ka bashi kamar yadda ya tsinci kansa yanzu, to dama Allah barin mutum yake da iyawar tasa. Ƙarfe ɗayan rana mai kwalliya ta zo ta fara rangaɗawa Hamdi bayan tayi sallar azahar. Jiki ya sha gyara na gaske saboda haka in ka ganta sai ka ƙara kallo. Ga ƙamshi wanda da kanta ta ce a bar turara mata jiki haka nan saboda kada ta fara ɗaukar zunubi a cikin mutane. Tana idar da sallar la'asar ta saka kaya aka ɗaura mata ashoke. Da ta fito daga ɗaki Yaya tashi tayi ta bar wajen. Bata son kowa yaga ƙwallar da ta cika mata idanu. Yau ita ce Allah Ya nufi ƴarta da auren gata irin wannan. Da bikin Sajida abin bai yi armashi sosai ba saboda tangal tangal da auren ya soma yi tun kafin a ɗaura shi. Leshi ne haɗaɗɗe mai laushi aka yi mata ɗinkin gargajiya wato buba da zani. Ado da kyan leshin kaɗai sun wadata ba sai an ɓata ɗinkin da tarkace ba. Ruwan toka ne da adon ja kaɗan a jikin zare sai navy blue ɗin fulawoyi. Ta riƙo jar ƙaramar jaka ta amare tana kuma sanye da jan takalmi mai tsini da maɗauri. Ashokenta na ka da na kafaɗa navy blue da silver. Sai wata danƙareriyar sarƙa mai duwatsu navy blue su ma da ja. Make up ɗinta na hankali bata koma aljana a kwaba ba. A tsakar gidan aka tsaya ana ta ɗauke ɗauken hotuna da ƴan uwa. Bata sani ba ashe Taj ya kirata ya kai sau shida. Amma ce ta turo shi ɗauko musu amarya. Fitowar tasa ma sai da tayi da gaske. Anti Zahra tun safe ta bar gidan. Su na can gidan Alh. Lurwanu yayan Inna don a nan za ayi Kamun. Saboda ƙurewar lokaci basu iya samun event centre ba. A waya ta faɗa masa cewa ana la'asar yaje ya ɗauko Hamdi. Hankalinsa a take ya tashi. Wato ƴan kwanakin nan da ya soma dawowa daidai babu abin da yake gudu kamar haɗuwa da amaryar tasa. Da wane baki zai bata haƙuri akan marin da ya yi mata? Inna bata ce masa komai akan asiri ba tunda Yaya Malam ya gargaɗeta da zargi. Gani yake girmansa ya gama zubewa a idanunta. Namiji mai dukan mata bashi da wata daraja a idonsa. "Bari na faɗawa Happiness ya shirya mu tafi da wuri." "Kai Happino. Nace happino" Amma tayi magana a fusace "ɗauko matar auren naka ma sai da shi? Ince ko daren farkon ma tare za ku." Da mamaki ya ce "Amma me ya yi zafi? Kamal nake nufi fa." "Shi ɗin fa! Ku yanzu sam baku iya lissafi da zurfin tunani. Dama me yasa ake haɗa angwaye da ƴan rakiya? Ai saboda gudun fitinar zamani ne. Ku kuwa tunda an riga an ɗaura aure me za ka yi da ɗan rakiya?" Dariya sosai ta bashi ya ce "to Allah Ya baki haƙuri. In kina so ma sai na ɗaukota na kai muku ita har kujerar da za ta zauna." "Ɗan banza mai bakin tsiya. In baka yi wasa ba wallahi har wurin zaman sai in ce ka kawota mu ga ƙarshen rashin kunya." "Cewa dai za ayi tarbiyarki ce." Ya ce da tsokana. Ita ma da ta san hali bata san me ya sa ta biye masa ba. Rabuwa tayi da shi bayan ta tuna masa ƙarfe biyar daidai su ke son farawa. Da ya faɗawa Kamal yadda su ka yi a wayar dariya su ka dinga yi son ransu. Kamal na cewa Happy ya girma shi kuma yana baya so. "Ni wallahi kunyar haɗuwarmu ma nake ji." "Hamdi fa bata da matsala. Kawai ka bata haƙuri a wuce wajen." "Kaga last faɗanmu kuwa da na kai mata kati? Tana faɗa ina yi kamar wasu kaji. I am seriously ashamed og myself." Ya rufe fuska da tafukan hannayensa. "Dalla kada ka bada maza. Kawai ka sabunta mata karatu yau yau ɗinnan. Su fa mata kana rarrashinsu ka gama dasu." Taj ya gyaɗa kai "Allah bari in samu a kai min rigimammiyar nan gida. Zan yiwa su Mama famfo akanka sosai. Dr. Mubina will be Mrs Happiness." Kamal murmushin yaƙe kawai ya yi. Taj ya yi wanka ya saka shirt da wando abinsa ya zo zai fita. "Wani sabon salon wulaƙanci ne wannan ko me? Ina kayan da Abba ya karɓo daga wajen tela?" "Direba fa zan yi. Amma ta ce ba zan shiga ba. Kuma kawai sai na saka sababbin kayana su yamutse?" "Kaina ciwo yake Happy. Bani da ƙarfin yi maka surutu. Kayi abin da ya dace ka fita." Kamar ya yi musu sai dai yaga babu alamun wasa tattare da Kamal ɗin. Dama kuma tsokana ce tasa shi saka waɗancan. Ya canja da wasu sababbi cikin na bikin. Sai gashi yayi kyau sosai. Ya tambaye Kamal ko zai sha magani ya ce a'a. Gajiya ce. Taj na fita ya kira Mubina ya faɗa mata jikinsa fa babu daɗi. Tana hanyar zuwa wurin kamun ita da ƙanwarta don har gida Yaya Kubra ta aika mata katunan bikin duka. Dole ta juya ta koma asibiti. A hanya ta sauke ƙanwar ta ta tace mata patient gareta. Ruwa ta saka masa da wasu magunguna masu ƙarfi har ya dawo daidai. "Ban faɗawa Dr. Kubra ba saboda bana son raba mata hankali. Ciwon nan mun barshi tsakaninmu zuwa lokacin da za a gama bikin ɗan uwanka kamar yadda ka buƙata. Idan bata faɗa ba ni zan je har wajen Alhajinku wallahi." Ranta a ɓace yake. Kamal ya yi mata murmushi. "Wannan faɗan duk don na hanaki zuwa cin shinkafar biki ne ko?" Harara ya samu "Wasa ma ka mayar da abin?" "Sorry Doc." Ya ɗauko wayarsa dake gefen gadon "zo mu yi hoto." Yadda ya yi maganar ya taɓa mata zuciya. Tayi murmushi duk da tana ƙoƙarin nuna masa fushinta. Ya gyara zama ta koma gefensa ta zauna tayi musu selfie. Tana tashi ya ɗauketa wasu. Bai taɓa ganinta da kwalliya irin ta yau ba. Kasa haƙuri ya yi ya ce da ita, "A misali da zan warke za ki iya aurena Mubina?" Abin control ɗin gudun ruwan da take ƙara masa take dubawa da ya yi tambayar. Yasa ta kusa ture ƙarfen gabaɗaya saboda yadda zancen ya taɓa ta. Allah Yasa bayanta yake kallo da yaga halin da ya jefa zuciyarta. Tattaro nutsuwa tayi "A'a." "Ni? Ni?" Ya nuna kansa kamar yato ya sanyata dariya "nayi tsammanin za ki bani amsar da zan ji daɗi." "Baka cancanci hakan ba Kamal. You are very stubborn. Rantsuwar dake kare alaƙar likita da patient ce kawai ta hanani yi maka handsfree." "Na nawa kuma? Ba kin faɗawa Yaya Kubra ba?" "Da kai da ita akwai wanda zai rantse cewa na faɗa? Magani ta gani ta zo tayi tambaya." Kallonta kawai yake yi yana jin inama ƙalau yake. Da ita ma tana wajen Kamu ana kama masa ita. "To da ace ni ɗin patient ne mai bada haɗin kai irin yadda kike so, za ki iya aurena idan na warke?" Sai da ta kalli idanunsa sannan ta bashi amsa "Da gudu" sai kuma ta soma hawaye "please let us help you Kamal. Akwai dama indai mu ka sami donor. Kada ka ɗora min zawarci tun kafin nayi aure don Allah." Tana gama faɗin haka ta fice saboda kukan da take shirin yi a gabansa. Shi ma hawaye ya goge bayan ta fita. Yana tsoron sanya rai da rayuwa bayan samun lafiyarsa ba abu bane mai sauƙi. Shi yasa yake ta kaucewa sanar da mutane. Amma zai bi shawararta. Idan an gama bikin Taj da kamar sati ɗaya da kan shi zai faɗawa iyayensa. * Mota Sajida da Fadila su ka rako Hamdi bayan an rufa mata wani net ja wanda dama an faɗa musu da shi za ta fara shiga. Sai an yi kamun za a cire mata. Haka aka rufe motar gabanta yana matsanancin faɗuwa. A hankali yake tuƙi cikin nutsuwa. Ƙamshin da take yi ya kwance duk wani notin arziƙi na kansa. Yana son yi mata maganar abin da ya faru amma yana jin nauyin hakan. Kamal ya ce ya bata haƙuri. Amma idan kuma ya bata ta sake yi masa maganar da wancan yanayin zai dawo fa? Tsoron da yake ji bai kai nata ba. In ka cire gaisuwar da tayi masa a gaban su Sajida bata sake ko da ɗaga kanta ba. Kwata kwata bata yarda da bakinta ba. Yanzu dai lafiya ƙalau su ke tafiya. Idan kuma tayi magana irin kalaman nan dake fita da kansu su ka bar harshenta fa? Kowa kama bakinsa ya yi. Da Salwa za ta ga yadda aikinta ya yi tasiri a wajen nan da ta daka tsallen ƴan bori ta dire don murna. Shirun damunsa ya yi ya kunna musu rediyo. Tashar farko da ya samu ya bari. Aka yi dace ko rashinsa domin kuwa a daidai lokacin mai tallan maganin gargajiya ce take ta kwararo bayanin maganin basir. (Wato shi fa basir idan yaci jikin magidanci sai kaga ko kukan jarirai an daina yi a gidansa. Cikinsa kullum a ƙulle tamau kamar yarinya tana koyon ɗaurin zani. Da shi da matarsa babu maraba. A jaraba maganin nan domin kawo ƙarshensa. Akwai mai tsiro, da mai jini.) Cikin kujera Hamdi ta shige saboda tsabar kunya. Mai magani ta cigaba da ɓaro zance mai nauyi. Aka barta da satar kallon Taj. Ɗan duniya da ya fahimci kunya take ji sai ya ƙara volume. Can sai cewa yayi "Nagode Allah ni dai ƙalau nake. Masu fama kuma Allah Ya yaye musu." Shiru tayi tana ƙifta idanu. Gara yayi mata waƙoƙinsa akan wannan magana. Kallonta ya yi ya saki murmushi. Wani irin jindaɗi da nutsuwa yake ji a ransa. "Ko kina da shi in saya miki..." "Innalillahi..." ta kalle shi babu shiri ta yaye lulluɓin. Numfashi ya ja da ƙarfi da su ka haɗa ido. Tayi masa kyau ba kaɗan ba. "Ni lafiyata ƙalau wallahi." A daidai lokacin mai maganin ta zaɓi ɗora zancenta da dawowa kan mata. (Na dawo gareku matan gida. Ina da magunguna sahihai waɗanda mu ka gada tun kakanni. Maganin sanyi da magungunan mata masu gigita maigida.) Hannu ta kai za ta kashe rediyon ya damƙe shi yana murzawa a hankali. "Don Allah ka canja." "Shhh...an zo wajen naku. Bari mu ji." "A ji me?" Ta tambaye shi looking horrified. (Mace sai ta bari sanyi ya gama cinye mata jiki. Sai miji ya mayar da ita bora sannan za ta fara neman magani. Ina mai fama da ƙaiƙayin...) Hamdi ta dube shi kamar tayi kuka. "Allah idan baka kashe ba zan iya yin kuka." "Allah Ya baki haƙuri. Daga taimako?" "Ba na so." Ta turo baki. Soyayyarta da ta kwanta wucin gadi ta dawo masa sabuwa fil. Ba ƙaramin kewar wannan Hamdin yayi ba. Yana son faɗa mata amma sun riga sun iso gidan Alh. Lurwanu. Inda zai ajiyeta Amma ta faɗa masa bayan ya shiga ciki da motar. Yana hango masu rakata wurin zamanta su Zee da su Firdaus. "Wanne zan saya miki? Kin dai ji ance mace bora take zama idan bata sha ba." Tsuke bakinta tayi. Sai da ya buɗe lock za ta fita ta yi magana a hankali yadda babu mai ji cikin ƴan rakiyarta. "Nafi ƙarfin zama borar gida." "Za ki maimaita wannan maganar nan da saturday." "Allah Ya kaimu" ta faɗi sannan ta ƙifta masa ido don tsokana. A tunaninta za ta samu guduwa ne a lokacin. Sai gashi su Firdaus sun dage sai sun yi musu hoto kafin a shiga da ita ciki. Fitowa yayi daga motar ya tsaya a gefenta. "Kai Uncle Taj. Irin wannan hoton tun zamanin su Mama. Ku ɗan ƙara matsowa mana." Hamdi bata ankara ba taji ya janyota kusa dashi. Hannunsa ɗaya a tsakiyar bayanta. Jin kamar za ta faɗi sai ta ɗora nata hannuwan a kafaɗunsa. "In miki waƙa?" Ya ce a saitin kunnenta. Hakan ya bada style na hoton masoyan da su ka yi nisa da ƙaunar juna. Ta san tsokanarta yake yi shi yasa tayi dariya. A haka aka ɗauki hoton. Ya yi kyau sosai. Bayan an gama taro mai ban sha'awa da Firdaus ta koma gida ta dinga ɗora hotunan kamu a status. Kuma wannan hoto shi ne na farkon da Salwa ta fara cin karo dashi. Zuciyarta a take ta ɗauki zafi. Ta juya ta kalli Mami dake kwance tana bacci ga yawu yana dalala ta gefen bakinta. Dole taje Kano ko ta wane hali. Wayarta ta ɗauko ta kira Ahmad ta faɗa masa hatsarin da Mami tayi da roƙonsa akan ya dawo dasu Aminu Kano Teaching Hospital saboda a nan Bauchi babanta yaƙi sakin kuɗi a dubata yadda ya dace (a ƙaryarta). Duk da baban nata ya gargaɗesu da ƴan uwanta da su yi shiru har sai ta farfaɗo saboda bai san me zai cewa Ahmad ɗin ba. Yana kunyar yaron kuma yana tsoron sake ɓatawa Alh. Hayatu rai. "Me ya sa zai ce kada a faɗa min? Kwananku nawa a asibitin? Shi ne kullum idan na kira ki ke min ƙaryar ƙauye ta tafi" Ahmad ya ce cikin tashin hankali. "Sharri aka yi mata wai tayi masa asiri." "Zan kira shi mu yi magana. Ku shirya, idan na zo gobe in sha Allah sai mu taho tare." RAYUWA DA GIƁI 27 Batul Mamman💖 _For Maryam Yusra because you deserve it! Allah Ya baki lafiya._ (Don Allah duk waɗanda su ka biya kuɗin talla na cikin labari kada su ƙosa. Saboda kun fi son wanda zai fito cikin labarin dole sai an zo gaɓar da zai dace. Ina fatan jinkirin ba zai sa muku damuwa ba. Har kullum ina godiya. SonSo) *** A mafarki ko ido biyu, Alhaji bai taɓa tunanin zuwan wannan rana ba sai da ta zo ɗin. Yau dai zahiri ba zance ba shi ne yake zaune a cikin falonsa babu kowa sai masu gadi da direbansa dake bakin gate su na hira da daddare. Gabaɗaya gidan ana idar da sallar magariba su ka daɗe. Duk an tafi wajen dinner ɗin Taj da Hamdi. Hatta masu aikin gidan babu wanda aka bari. Kasa zaman falon nasa ya yi ya shiga ɓangaren matan gidan. Nan kam sai da zuciyarsa ta motsa da tausayin kansa. Shiru ne mai ratsa ɓargo. Sai kayayyyakin ƴaƴansa da jikoki da ba a gama tattarewa ba. Wasu ma a ƙasa su ka bar nasu. "Ganɗoki" ya yi murmushi yana mai duƙawa ya ɗauke kwalbar turaren da aka bari a ƙasa. Samun kansa ya yi da tsince duk wani abu dake ƙasa wanda bai kamata ba. Yana yi ransa na tunatar dashi cewa duka mutanen da su ka shirya a wajen nan da ɗakunan matansa fa nasa ne. Zuri'arsa ce. Shi kaɗai a shekarunsa sittin da takwas ya tara jikoki sama da arba'in. Ga ƴaƴa ga tarin dukiyar da ko yau ya ajiye kasuwanci ba za su buƙaci komai ba a shekara goma masu zuwa. Ya auro mata masu mabambantan tushe amma waɗanda su ka yi tarayya wajen taya shi gina gida irin wannan. Tabbas shi ma ya sani cewa arziƙinsa ba a naira da kwabo yake ba. Iyalinsa sune arziƙinsa. Banda dai abubuwan yau da gobe da ba a rasawa amma ya tabbatar cikin ƴaƴansa babu fasiƙi. Allah Ya yi masa gamdakatar Ya shirya masa zuri'a. Kuma komai ya ce ya zauna daram kenan a gidan. Duka ya ɗauka ƙarfin ikonsa da tsare gida ne wanda cikakken namiji kaɗai ke iyawa. Sai gashi an wayi gari sun haɗa kai suna neman juya masa baya. Jiya sun tafi wajen kamu ƙwai da kwarkwata. Bayan saboda girman gidansa ƴaƴan dangi ma suna cin arziƙin ayi bikinsu a nan. Shi su ka tafi gidan Alh. Lurwanu don su nunawa duniya gazawarsa. Yau kuma Hajiya ta ce masa event centre za su je kuma sai an gansu. Abin tambaya a wajensa yanzu shi ne wai me yasa su duka su ke ganin aibun hukuncinnda ya yankewa Taj? Anya sun san yadda illar dake tattare da daudanci? Habibunsa fa daga son girki ya fara kamar wasa. Idan a baya Taj bai yi ɗabi'un mata ba yanzu zai iya. Surukuta ta shiga tsakaninsu da ɗan daudu kuma ga aiki suna yi tare. Ya numfasa a yayinda ya zauna ya kula cewa gyara sosai ya yiwa falon. Dole ne ya raba Taj da Hamdi. Barazanar da ya yi a Bauchi bata nufin ya karɓi wannan aure. Salwa ce ba zai taɓa bari ta kusanci danginsa ba. Duk lalacewar ɗan daudu yafi mushriki a wurinsa. *** Ƙememe Yaya taƙi shiryawa,wai ba za ta je wajen bikin ba. Duk ga ƴan uwa za su wakilceta. Za ta zauna a gida da Innarta Luba da ta zo jiya. Aka kaɗa aka raya taƙi chanja shawara. Gashi ƴan matan nata duka ukun basa nan. Yanayin gidansu bai basu damar yin ƙawaye ba. Shi yasa duk wani abu da za ayi da ƙawa tare su ke yi. Tun azahar Safwan ya kwashesu zuwa event centre ɗin inda a saman wurin ne za a rangaɗa musu kwalliya. Kowacce mijinta ne ya biya mata. Ita Hamdi lalle aka fara yi mata. Ɗaya daga cikin yayyen Taj tana da saloon da wurin lallen amare da na matan ƙwalisa. Wadda tafi iyawa ta tura ta yiwa Hamdi baƙi da ja. Tun kafin a gama ake santin kyawun da yayi. Ana gamawa aka koma kwalliya bayan tayi sallar la'asar. An fito da ita fita ta girma. Sai wanda ya sani ne kawai zai iya gane ita ɗin Hamdiyya ce ɗiyar Habibu Simagade. A haka kuwa za ka yi zaton ƴar wani ƙusa ce. Ana kammala kwalliyar tayi sallar magariba sannan ta saka kaya. Anti Labiba ce ta kira Sajida ta faɗa mata rigimar da ake yi da Yaya akan ta shirya. Sajida tana ji ta san babu wani kunya ko kawaici da yasa mahaifiyar tasu son zaman gida. A nata tunanin rashin zuwan zai taimaka ya ɗago darajar ƴaƴanta a idon mutane. Bata son yin abin da zai janyo mata ido harma ayi ta ambaton ita ce maman amarya, daga nan wanda bai sani ba a bashi labarin cewa babansu ma tsohon ɗan daudu ne. "Don Allah ba ta wayar Anti." Harara kala kala Yaya ta gama yiwa Anti Labiba kafin ta karɓa. "Yaya me yasa ba za ki je ba?" Caraf a kunnen Hamdi. Ta karɓi wayar ana yi mata ɗauri da wani yadi haɗe da net mai santsi. "Yaya ba za ki ba?" Shiru tayi saboda taji yadda muryar Hamdin ta canja. "Yaya?" "Ina jin ki. Ga iyayenku nan. Kowa zai je. Me zan je yi ni kuma?" Zee da Sajida kusa da Hamdi su ka dawo su ka kara kunnuwansu. Kowacce tana iya gane zancen na Yaya akwai damuwa a ciki. Hamdi sai cewa tayi, "Wallahi Yaya idan baki je ba nima daga nan gida zan taho." Su Zee jinjina mata su ka yi da thumbs up da ta faɗi haka. "Ke ba na son rashin kunya." "Allah Yaya. Zan zauna a saman nan har sai kin zo." Sajida ta miƙawa wayarta ta koma aka cigaba da ɗauri. Sai dai ana yi ƙwalla na sauko mata. Mai kwalliya tabi ta tada hankali. Idan kwalliyar ta caɓe ko amarya bata sauka da wuri ba za a sami matsala. "Za fa ta zo tunda taji kin yi rantsuwar nan." Cewar Sajida. "Ke ma ai bata je naki ba." Zee ta tunatar da ita. Ita dai me kwalliya haƙuri ta soma bawa Hamdi ganin wankin hula yana neman kai su dare. Sai da ya rage pins kawai za a saka a jikin mayafi da head ɗin sannan kukan nata ya ƙaru. Daga can ƙasan zuciyarta take yinsa. Ta ƙara jinjinawa uwa a duk inda take. Babu yadda za ayi ace Yaya bata son ganin ƴaƴanta a wajen bikinsu suna walwala kamar kowacce uwa. Amma kawai don kada a aibata mata su saboda yanayin tafiyarta shi ne ta zaɓi zaman gida. Da bikin Sajida duk sun ɗauka kawaicin uwa ne. Musamman da basu ga mahaifiyar Safwan a wajen event ɗin nasu ba (baban Safwan ya hanata zuwa). Yanzu kuwa jiya komai da iyayen Taj aka yi. Yau ma su ne ƙirjin biki. Sai ace babu mahaifiyarta? Saboda miskiniya ce. "Ya Hamdi meye haka ne? Ji idonki har ya soma caɓewa fa." Cewar Zee ta ƙara miƙawa mai kwalliyar tissue domin a gyara idon. Sajida wayarta ta shiga dannawa tana cewa "bar ni da ita." Sai ji su ka yi tana gaishe da Taj. Ta kuma faɗa masa kukan da Hamdi take yi da dalilinsa. "Saka mata wayar a kunne." Da canjin numfashin da yaji ya gane ta saka mata ɗin. Da rarrashi ya yi mata magana. "Zan kawo miki Yaya in sha Allahu. Ki daina kuka idan ba haka ba kuma yau sai mun yi kuch kuch hota hai a gaban mutane. Mu yi ta rangwaɗa kai kamar ƙadangaru." Dariya ce ta kama Hamdi. Sajida, Zee da maikwalliya su ka saki baki suna kallon ikon Allah. "Waƙar bata da hayaniya sai na taya ka." "Haka ki ka ce?" Ya tambayeta yana murmushi "Wayarki na kusa?" "Eh" "To ki dubo waƙar I am a disco dancer a youtube. Ni kuma idan baki daina wannan kukan shagwaɓar ba in baki mamaki a gaban mutane. Ita zan yi. Kin kuma san zan iya. 80s aka yi ta ba ta zamaninku bace." "To Baba Happy. Na ma share hawayen" ta goge idonta da kanta don barazanar Taj ba abin da za ta share bane. "Wannan ladabin ba na gaske bane. Sai na tambayi Sajida naji ko kin ƙara yin kuka." "Allah na daina." "Hamdiyya" ya kirata a tausashe. Kasa buɗe baki ta amsa tayi saboda kiran nasa na daban ne. "Uhmm" "I'll see you later." "Bye" ta miƙawa Sajida wayar. "Iiiiiikon Allah" Sajida ta faɗi baki buɗe "me zan gani ni Sajida ƴar Habibu? Hamdi? Dama rashin jin muryar mijinki ne yasa ki kuka? Shi ne ki ka ɗorawa baiwar Allah Yaya. Ai kuwa bari nace mata tayi zamanta." Da sauri Hamdi ta miƙe tana kici kicin karɓe wayar "ɗaukota fa zai je ya yi. Shi yasa ki ka ga nayi dariya." Zee tayi dariya "anya kuwa? Naji fa kina zancen wata waƙa wai bata da hayaniya." "Ke, kira Ya Baballe ku gaisa kema ki ji daɗi." "Baballen lafiya? Sunansa Sadiq" ta faɗa tana kallon yayyen nata. A tare su ka bushe da dariya sannan Hamdi ta koma ta zauna aka gyare fuskarta kamar bata yi kuka ba. Ana gamawa ta koma gefe ta buɗe youtube. Hannunta yana ƙaiƙayin ganin waƙar da Taj yake cewa zai yi. Da ta kunna ɗaya tayi kama da ta 80s ɗin daga ɗaukan ma. Ɗayar kuwa ɗaukan zamani ne. Bata ma ɓata lokacin kallon ta zamanin ba wadda ta kasance remake ɗin tsohuwar. Danna tsohuwar tayi inda kunya ta kusa sumar da ita da rawar da Mithun yake yi. Saboda raye raye nan taƙi jinin waƙe-waƙe. Idan Taj ya yi wannan girgizar da karya jikin tabbas a wurin dinar za ta tafi ta barshi. Su Zee dai kallonta kawai suke yi. Tana duban waya da ido ɗaya tana kawar da kai. "Ta fa ci kai wannan." Sajida ta faɗi su ka yi dariya ko kula su bata yi ba duk da taji. * Da Taj ya gama wayar, ji ya yi an ture shi. Sai lokacin ya ankara ashe a jikin Kamal ya jingina da shauƙi na ɗibarsa. Ya rasa me yasa shi da Hamdi basa iya yiwa juna baƙunta. Kamar ba jiya jiyan nan da sauran ƴar rigimarsu ba. Yau kam komai ya wuce! Ɗaure fuska Kamal ya yi "Na ma rasa abin da zan ce maka Happy? Wato haka ake soyayyar ni ka barni ina fama da instagram da daddare?" Taj ya kama dariya "ba dai ka tsaya wasa ba? So kake sai Dr. Mubina ta kawo maka katin aurenta ka zo ka ce min zuciyarka za ta fashe ko?" "Allah ma Ya kiyaye. In sha Allah ba zan ga aurenta ba." Cewar Kamal yana mantawa da wa yake magana. Wata irin juyowa Taj ya yi yana kallonsa "saboda kai za ka aureta ko kuwa ƙasar za ka bari idan ta tashi auren wani a dalilin nauyin bakinka?" Wayancewa Kamal ya yi "likitoci na auren ƴan kasuwa ne? Idan rabon wani ce sai in tafi China odar kaya kafin a gama bikin." Tsaki Taj ya yi "ta nan kuma ka ɓullo? Hmmm, kai ka san yanayin aurena da matsalar Alhaji ne su ka shige min gaba. Ba don haka ba da yanzu kai ma kana kwanciya kamar gasara a ruwa idan kuna waya." "Wannan karin magana ne ko me?" Kamal yana dariya ya tambaye shi. "A bakin Ƴar Ficikar nan naji." Dariya su ka yi sannan Kamal ya ce zai fita waje ya tada mota kafin Taj ya fito sai su ɗauko Yaya. Ɓata lokacinsu faɗan iyaye zai jawo musu. Yana fita Taj ya bishi da ido. Jikinsa yana bashi tabbas akwai abin da ɗan uwan nasa yake ɓoyewa. Kwana biyu ma tunda ya dawo ya gan shi a rame. Yanzu ne ma ya ɗan ciko. Zuciyarsa ta bashi ko ma mene ne ya shafi Dr. Mubina. Kuma yafi tunanin ƙila soyayyar Happiness ce bata karɓa ba. Da an gama bikin nan zai je ya sameta har asibiti ko ya nemi gidansu. Indai ba wani aka bawa ita ba zai nuna mata cewa rashin karɓar Kamal asararta ce. Happiness is a rare gem. Ko shi da ya same shi a matsayin ɗan uwa ba ƙaramin dace ya yi ba. Ƙarasa shirinsa ya yi su ka fice daga gidan. A daidai bakin layin su ka ga motar Ahmad wanda dawowarsa kenan daga Bauchi. Horn su ka yiwa juna. Basu kula da Salwa a gaban motar da kuma Mami dake kwance a baya ba. Kiran wayarsa Kamal ya yi yana sanar dashi kayansa wanda duka ƴan mazan gidan zasu saka banda ango suna ɗakinsa. Sun bawa Anti Zahra ta ajiye masa kafin ta tafi. "Zan ɗan makara amma. A gajiye nake." "Wai ina ka je ne? Ance tun safe ka fita." Ahmad ya kalli bayan motarsa ya sauke numfashi. "Sai mun haɗu dai." Da taimakon Salwa su ka shigar da Mami cikin gidan. Gabaɗaya ta rikirkice saboda ƙamshin turaren Taj da hancinta yake iya bambancewa duk inda ta ji shi. Ɗakin da take zama Ahmad ya ce su shiga da Mami. "Bari nayi wanka naje wajen dinner ɗinnan. Ba zan jima ba in sha Allah. Gobe da safe sai mu tafi asibitin." Da azama ta miƙe ita ma bayan ta kwantar da Mami "Nima bari na shirya kafin ka fito." Haɗe fuska Ahmad ya yi "Salwa." "Na'am." Sai kuma tayi murmushi "wallahi sauri zan yi Yaya." "Ba ki da hankali ashe." Ya nuna kansa yana juya ɗan manunin yatsansa cikin ɓacin rai "wa za ki barwa Mamin da kike zancen zuwa dinner?" Murmushi tayi "lahh, Ya Ahmad ai kai ma ka san ba zan tafi haka kawai ba. Tun a hanya nayi magana da Anti Zabba'u (ƙanwar Mami). Tana hanya ma don na faɗa mata mun shigo gari." "Yaushe ku ka yi maganar ban sani ba?" Ahmad ya tuhume ta. "Tun jiya ne bayan mun yi waya da kai." Zama ya yi a gefen gadon yana matse gaban goshinsa kafin ya ɗaga kai ya kalleta da takaici. "Dama shirinki kenan shi yasa ki ka yi min ƙaryar Alhajinku ba ya kula da lafiyarta?" "Wallahi Yaya..." A harzuƙe ya tashi kamar zai kifa mata mari "Shut up Salwa. You are very stupid." "Don na ce zan je bikin ƙaninka kake zagina Ya Ahmad?" "Ba za ki ba! Ko ƙalau Mami take babu inda zaki. Haba! Yarinya kin bi kin haukace kuma kina neman haukata kowa. Taj baya son ki, kuma ko yana so ina cikin masu hana shi aurenki saboda baki san bambancin so da obcession ba." Kuka ta fashe masa dashi. Tana jin saukar maganganunsa tamkar sukar mashi. Sai ta mallaki Taj a matsayin miji kuma akan idonsa ta ƙudurta a ranta. Mami tana daga kwance tana ɗaga lafiyayyen hannunta akan su yi shiru. Kallonta Ahmad ya yi ya fice kawai domin dai ba a canjawa tuwo suna. Alh. Mukhtar ya faɗa masa komai da yaje ɗaukarta. Ya kuma sanar dashi cewa ya saketa sannan idan sun tafi to ta tafi kenan daga rayuwarsa. Har abada baya son sake ganinta. Ƙannen Salwa mazan suna wajensa. Ita kuma ya ce idan sun gama zaman asibiti ya dawo masa da ita domin aurar da ita zai yi. Sun gama magana da wanda zai aureta ma. Wannan ne dalilin da yasa ya taho da ita. Ba wai ƙaryar da tayi masa ba. Don tabbas komai na buƙata Ahmad yaje ya samu suna dashi. Kawai mijin nata ne dai ya fita harkarta. "Zan jira Anti Zabba'u ta iso kafin na tafi." Ta ce da Mami. "Uhmm uhmm Salwa" Mami ta ce da ƙyar. "Mami zani fa. Na san da lafiyarki ƙalau za ki bani goyon baya." Banɗaki ta shiga ta sillo wanka. Ta fito tana cikin shiri Anti Zabba'u tayi mata waya cewa tana bakin gate. Garin saurin ta buɗe mata abu ya faɗo daga jikinta bata sani ba. Yunƙurawa Mami tayi ta leƙa abin. Sai da jikinta ya kama rawa. Sabuwar laya ce don zaren fari ne tas irin wadda take taunawa idan za ta yiwa Alh. Mukhtar magana. Zarginta akan Salwa ya tabbata. A asibiti Salwan tayi zaton bacci take ta ɗauki wayarta ta kwafi lamba. Kuma taji buƙatar da ta faɗa...tana son mallake wani. Sai yanzu ta gane malamin tsibbunta ne Salwan ta ɗauki lambarsa. Kenan duk abin da take yi ƴar na lura? Bata son inda tabi har rayuwa tayi mata wannan atishawar ƴan tsakin ita ma Salwa ta bi. Da ƙalau take duk inda ake takawa zata je domin farincikin ƴarta, amma bata so ƴaƴan su yi wannan rayuwar. Bakin Salwa kasa rufuwa ya yi da ta buɗe ƙaramar ƙofar gate su Anti Zabba'u su ka shigo. Don ma babu motar Ahmad ta san ya tafi. Gayya guda har su shida. Ita da ƴan matan ƴaƴanta guda uku. Sai babbar bazawara da goyo. Kowacce ta bawa shabiyar baya. Ita ma Anti Zabba'un ta gaji da aure aure ta haƙura. Dama kuma ta jima tana roƙon Mami ta tilasta Ahmad auren guda cikin ƴaƴan nata amma taƙi yarda saboda kar ta san kar ne. Sai gashi Salwa ta faɗa mata halin da Mamin take ciki. Da murna ta kwaso jiki. Ko Ahmad yana so ko baya so sai ya auri ɗaya kuma ya saki wannan mai dara daran idanuwan. Ita dai Salwa bata san Mami taga layarta ba. Ɗaukewa tayi ta tura a jaka. Ta gama shirinta tsaf ta haɗa da turaren wajen su Ummi ta fita. A rashin sani turaren aikin Alh. Usaini ta ɗauka tunda shi ne aka ce mata zai kawo soyayya tsakaninsu. A daidaita sahu ta samu har event centre ɗin. Motoci ko ta ina. Ta zo bakin gate tayi turus don babu kati! *** Shafawa ido toka Taj ya yi da ya shiga ciki ya ce da Abba ya roƙi da Yaya ta fito su tafi saboda abin da Hamdi ta ce. Yayan da Inna Luba suna zaune a wajen. "Ayi haka Taj? Muna da gefe bai fi ba?" "To nima dai idan bata fito ba tabbas babu inda zani tunda amaryar tayi rantsuwar ba za ta fito ba." "Barni da ita. Yanzu zan kira in yi mata faɗa." Cewar Abba yana ƙara kaurara murya don ya ƙara mata kwarjini. Taj ya ce "Abba me ɓoyon zai ƙara ko ya rage? Waye bai san ƴarka nake aure ba? Wa kuma kuke son ɓoyewa kanku? Kuna jin gata ne kuke yi musu? Mushirikai da fasiƙan iyaye ake gudun nunawa. Amma idan kuna yin haka nan gaba sai sun fi ku jin kunyar a ganku tare. Kunga sai ayi ta rubuta musu zunubin rashin kyautatawa iyaye." "Kai Tajo, me yayi zafi?" Inna Luba ta ce a tsorace "ke tashi ki shirya ku tafi." "Ke fa Inna?" Taj ya ɗaga mata gira "nawa kakannin babu. Ki zo ki wakilci kowa." "Ja'iri, to bari nasa kaya. Dama wannan ƴar ce ta hana ni zuwa amma na so bin su wallahi" ta miƙe da murnarta. Murmushi Abba ya yi. Yaya da Inna Luba su ka shiga ɗaki. Basu daɗe ba kowacce ta fito cikin shiga mai kyau. Yaya lace ɗin da Mama ta aiko ta ce mata ankon manya ne ta saka. Kai kana ganinta banda lalurar ƙafa da ba ƙaramar mace za ayi ba. Fuska dai kam Masha Allah. Akwai kyau irin na Katsinawa wanda ƴaƴanta su ka haɗa da na Simagade su ka fito gwanin ban sha'awa. *** Ƙarfe bakwai da minti arba'in da biyar daidai Amma ta kira Taj ya ce mata suna wajen parking. "Bari a sauko da amaryar sai ku shigo." "Amma tare muke da Yaya." "Tun ɗazu nake lalubenta cikin baƙi. Gani nan fitowa." Da kanta taje wajen motar ta riƙo Yaya su ka shigo. Mama na hangota daga wajen zaman iyaye ta tada Umma su ka ƙarasa. Hajiya ma ta ce da Inna lallai ta tashi. Tunda aka ce Taj ne ya kawota ta san tana tattare da jin nauyin shiga jama'a ne. Mutane sun fara kallon Yaya ana ƙusƙus da faɗin uwar amarya ce sai aka ga matan Alh. Hayatu Sule masu aji sun je inda take suna yi mata maraba. Kayansu ita da matan da Amma iri ɗaya. Sannan su duka har ƙasa su ka gaishe da Inna Luba. Wannan abu yasa duk mai abin faɗa ta haɗiye kayanta. Dukkan alamu sun nuna su ɗin suna cikin farinciki da son juna. Gutsiri tsomar ƴan gayya bata da tasiri. A ɓangaren amarya kuma ƴaƴan Amma wato Ihsan da Amira da kuma Anisa sun haɗu da masu ƙananun shekaru cikin ƴan gidansu Taj da Anti Zahra sai kuma Sajida da Zee wajen rako amarya. Gabaɗaya matan doguwar riga su ka saka ta wani yadi sky blue da ɗigon fari da pale yellow wadda aka yiwa wani irin ɗinkin bubu mai kyau. Umarnin Hajiya Gambo kenan. Duk wata jininsu da tayi ɗinki mai fitar da shape a gida zata ci bikinta. Babu head sai rolling da su ka yi da pale yellow ɗin yadi mai santsi. Babu yadda za ayi ka gansu basu burgeka ba. Modesty and elegance at its peak! Amarya Hamdiyya kuwa gown ɗinta fara mai dogon hannu kuma wadatacciya. Bata bi jikinta ta tona sirrin wanda ya bada sadaki a gaban kowa da kowa ba. A kanta anyi mata ɗauri da net silver wanda aka ɗorawa wani abin ado mai duwatsu sky blue na gashi ya kwanta ta ɓari ɗaya. Daga tsakiyar ɗaurin inda gashinta yake a suturce aka ɗora farin net dogo har ƙasa. Wuyanta sarƙar farin gwal ce. Sai clutch bag ɗinta da takalmi mai tsini sky blue. Tayi kyau har ta gaji. Ƙasa suka sauko sannan aka zo bakin ƙofa aka jera yadda za a shigo. Kallo ɗaya Anisa ta yiwa Hamdi tunda sai yau su ka iso ta ganeta. "Mai kukan uber?" Ta faɗa ba tare da wani tunani ba. Hamdi ta ɗago su ka haɗa ido. Ta saki murmushi mai ban sha'awa. Haka kawai sai Anisa taji ƙuncin zuciyarta ya kau. Ta matsa kusa da ita tayi musu selfie sannan aka ce su tsaya kamar yadda aka tsara musu. Matan layi layi suka yi hagu da dama har layi shida. Sai Hamdi a tsaye. A bayanta kuma Bishir da Abba. Sai kuma Kamal da Ahmad a bayansu. Sanye su ke da yadi pale yellow da aka yiwa ɗinki ma hannu da ya wuce gwiwar hannu da kaɗan. Daga hula har zuwa takalmi komai nasu iri ɗaya in banda agogo. Hamdi tayi zaton tafiya za su fara yi don hankalinta a tashe yake tun a nan ga hasken flash ana ta ɗaukar hoto. Ƙofar hall ɗin aka buɗe ta soma jin sanyi da ƙamshin wajen na buso ta sai ji tayi hannuwa sun kama nata da gentle riƙo. Tsigar jikinta tashi tayi da tsoro da kuma gane hannun waye. Tsayuwarsa kaɗai a kusa da ita ta sanya sanyin nan ya ragu don kansa. Ta ɗaga kai su ka haɗa ido. Kayan jikinsa sky blue ne harda babbar riga irin wadda ake yi ta zamani ba burum-burum ɗinnan ba. Shi ma hannun rigarsa ta ciki ƙarami ne kamar na ƴan uwansa. Ya sanya hula da takalmi cover shoe navy blue mai duhu sosai. Gashin baki da gemunsa da basu cika yawa ba sun sha gyara. "Ya Rabbi, har na fara tsoron ko ni kaɗai zan shiga" Hamdi ta faɗi a hankali tana kawar da kai don kallon nasa babu rissina a ciki. "Ina tare dake kowanne taku. Ki daina jin tsoro." Ya bata amsa a kunnenta. Hannunta zai saki yaji ta kuma damƙe nasa. "Don Allah ka riƙeni har mu zauna. Zan iya faɗuwa da takalmin nan." Ta marairaice masa idanu har lokacin tana magana a hankali don kada na gabansu ko baya su ji. "Awwwnnnn, zuciyata" Taj ya dafe ƙirji kuma da gaske yadda tayi ɗin ya shige shi ne sosai. Fari tayi da ido tana harararsa "A nan ɗin ma sai kayi?" "Kin gama dani ne Mrs Ha..." Wani abu su ka ji kamar harbin bindiga da ya katse masa magana. Sai kuma muryar MC yana sanar da shigowar ango da amarya da umarnin kada kowa ya bar wurin zamansa da sunan ɗaukar hoto. Wani irin kiɗan taushi ne yake tashi babu waƙa a yayinda suke shigowa wajen cikin nutsuwa. Matan dake gaba basu mai rawa sai ɗan kwanon hannunsu mai fulawoyi masu kyau da su ke ta watsawa sama. Da su ka iso gaba Yaya ta ƙyallara idanu ta hango ƴan matanta, bata san lokacin da idanunta su ka tara ƙwalla ba. Ta dinga hamdala a zuciyarta. Ashe Inna Luba ma hakan take a wajenta. Sai dai ita bata iya ɓoye nata hawayen ba. Jikokin kenan sai Halifa cikon na huɗu. Sai kuwa na yayarta abar alfaharinta har kullum. Amma dai jininta da take da cikakken iko dasu waɗannan ne. Da kanta ta dinga bin ƴan uwan Yaya wato ƴqƴan abokiyar zamanta mazansu da matansu a samu mai zuwa bikin nan amma yadda su ka ƙi zuwa na Sajida wannan ma ƙi su ka yi. Ta roƙi maigidanta ko sau ɗaya ne ya yi musu magana ko ya zo ƴarsa taji daɗi ya ce ba zai taɓa murna don ƴaƴan ɗan daudu sun yi aure ba. Su je can su ƙarata. Godiya kawai take ga Allah domin bai haɗa mata zuri'a da lalatattun mutane ba. Dukiyar bata tsole mata ido ba. Girmamawar daga surukan ƴaƴan shi ne komai a wajenta. A teburin gefensu Iyaa ce da su Ummi, sai kuma surukar Sajida da ƙannen Safwan. Shi da Baballe suna can ɓangaren maza. Amarya da ango sun sami waje sun zauna sannan ƴan rakiyar su ka koma nasu waje. Aka shiga cikin taro ka'in da na'in. An fara da addu'a daga bakin babbar baƙuwa Malama Maimuna. Bayan ta gama aka ce ta faɗi kalmomi biyu zuwa uku na shawara ga ango da amarya. "Tajuddin da Hamdiyya. Abu ɗaya zan faɗa muku. Duk abin da za ku yi ku tuna cewa kowa cikinku mai kiwo ne kuma abin tambaya akan kiwon da Allah Ya bashi. Duk wanda ya tozarta amanar Allah sai Ya tanadi amsar bayarwa." MC ya karɓi mike ya ce "wannan fa damu duka take. In kin san satar fita kika yi ki ka zo nan babu ruwanmu. Kai kuma mai shirin samun sabuwar budurwa a nan domin ka ci zarafin ta gida ta hanyar kwaye mata baya kana tona mata asiri to kai ma dai ahir ɗinka." Dariya aka yi sannan ya ce ina Hajiya Amina aminiyar Inna. Tasowa tayi ita ma ya buƙaci kalmar shawararta. "Kada ku yarda soyayya ta sanyaku saɓawa Mahalicci. A komai na rayuwa ba a yiwa umarnin da ya saɓawa Allah biyayya ga kowa." Godiya aka yi musu sannan MC ya ɗora. Agendarsu ta gaba ita ce gasar da aka shiryawa team ɗin ango da amarya. Tambayoyi ne da za su amsa game da juna. Aka sanya kujeru biyu suna kallon juna su ka zauna. A team ɗin ango akwai Sajida, Zee da Halifa. Team ɗin amarya kuma Yaya Hajiyayye da ta ce ta fi kowa sanin duka ƙannenta, Kamal da Ihsan ɗin Amma. "Ba zan tambayeku birthday ɗin juna ba." Ya raba musu takardu guda goma. Kowa a takardarsa zai rubuta amsa da taimakon team members ɗinsa. Wanda ya yi na ɗaya zai sa wanda ya faɗi yin duk abin da yake so. Ƴan biki aka kasa zaune aka kasa tsaye da ganin wannan sabon salon. Kowa ya zata rawa za a sha yadda aka saba ana liƙi a gaban DJ. MC ya ce "a rubuta min cikakken kwanan watan ranar da ku ka fara haɗuwa a cikin sakan talatin." (12/08/2021) Kusan tare su ka ɗaga takardunsu kafin lokaci ya cika. Kemara ta ɗauka aka haska a manya manyan talabijin dake manne a jikin bangon hall ɗin ta kowacce kusurwa. Daga nan ya dinga yi musu tambayoyi akan juna. Kamal, Yaya Hajiyayye da Ihsan da ta rayu da Taj kafin tayi aure a US sun taimakawa Hamdi sosai. Kazalika su Sajida. Aka gama tambayoyi suna kunnen doki. "Dole a sami na ɗaya da na biyu fa. Team members ku koma ku zauna a barsu su kara su kaɗai." "Banda ke Hamdiyya, wa Taj yafi so? Kai ma banda kai wa tafi so?" Suna gama rubutun su ka ɗago kai. "Happy Taj wa ka fi so?" "Alh. Hayatu Sule Maitakalmi" ya faɗi da murya mai ban tausayi. Inna sunkuyar da kai tayi ta bar su Amma dasu Mama su da share ƙwalla. "Amarya wa ki ka rubuta?" Takardar ta ɗaga masa (Alhaji) ta rubuta. Ƴan uwan Taj su ka dinga tafa mata suna murna. "Wa ki ka fi so amaryar Happy Taj?" MC ya tambayeta. Da murmushi ta ce "Mamana, Yaya" tana mai kallon inda Yaya take a zaune. Baiwar Allah ita ma ƙwallar ta kama yi. "Taj wa ka rubuta?" (Duka iyayenta) MC ya nuna Hamdi ya ce "a tafawa amarya Hamdiyya." Wurin ya kaure da hayaniya da murnar mutane. Wurin amsa tambayoyin nan ba ƙaramin kiɗima jama'a suka yi ba tun ma suna tare da masu taimaka musu. Taj ya fitittike ya ce bai yarda ba. "Ni fa da gangan na faɗi saboda nayi zaton ba za ta iya amsa nawa ba tunda ban taɓa faɗa mata ba." MC ya ce "Kaga rigimammen ango" aka bushe da dariya "abin da za ta saka ka kake gudu?" "Eh wallahi. Na san me wahala za ta saka ni." Ya sha kunu da wasa. "Wai haka?" "A'a" ta amsa mischieviously. Kai kana ganin farincikinta ka san amsar bata kai zuci ba. "To ke mu ke sauraro" Hamdi ta zaro ido "wai a nan zan faɗa?" "Eh mana" cewar MC "Iyayenmu fa duk suna nan" ta kalli saitin teburin iyayen nasu a kunyace. "Ga takarda ki rubuta masa ba sai mun ji ba." (Don Allah ka daina yi min waƙar India) Tana bashi ya saka loudspeaker a bakinsa ya karantawa kowa. Aka fara dariya da ya ce a bashi fili. "Waƙar ƙarshe zan yi irin wadda ake mirginawa a ƙasa ana kuka a gidan boss." Hamdi duka hannuwa tasa ta rufe fuskarta. "Na fasa kada tayi mana kuka." Taj ya faɗi yana murmushi. Mutane suna ta dariya. MC ya ce Taj ya faɗi wani abu kafin su koma mazauninsu. "Nagode Allah da Ya bani Hamdiyya Habib Umar. Allah Ya bamu zaman lafiya." MC ya turawa Hamdi speaker saitinta "ke kuma me za ki ce?" Ta kalli Taj ta rufe fuska da gefen mayafi "Amin....au mungode zan ce." "Awwnnnnnnn" ɗin mutane kamar ta fasa dodon kunne. Aka dinga tafa musu har su ka zauna. Mutane sun nishaɗantu matuƙa. Daga nan aka fara rabon abinci wanda a yau ma'aikatan Happy Taj su ka baje kolin basira wajen yin wanda yafi na kullum daɗi. Nau'in girki na gaske kala kala aka yi. Luciousbites da kanta ba saƙo ba kuma ita tayi snacks da kuma daddaɗan youghurt da furarta wanda ake sha ana santi. Juice kuwa sai wanda mutum ya zaɓa. Babu mutum ɗaya da zai ce ya tafi gida da yunwa. Kowa yaci ya ƙoshi. Bayan an gama ne DJ ya soma nasa aikin. Anti Zahra tana bawa Hayat ruwa ta hango Ahmad yana yi mata signal. Wayarta yace ta duba. Tana ɗauka call ɗin Salwa na shigowa. Kira yafi arba'in. A zatonta abin da zai ce ta duba kenan shi yasa ta ɗauka. Salwa ta saki wata wawiyar ajiyar zuciya "Anti ina ta kira..." "Banji ba ne Salwa. Ya gida?" A gadarance ta ce "ina waje tun ɗazu. Kin taho da katina?" Anti Zahra ta kalli Ahmad da har yanzu alamar duba waya yake yi mata da hannu tace "wane katin?" "Ba a aiko min ba?" "Ke da kike Bauchi ai ban san za ki zo ba." Tashi tayi ta bar yaran a wajen ƴan uwanta da suke seat guda ta ƙarasa wajen Ahmad. Waje su ka fita saboda hayaniya. "Ya zance ki duba waya ki tsaya amsa kira kuma?" "Sorry, na zata kiran Salwa kake nufin na duba." Ta nuna masa missed calls. "Ƙyaleta. Nayi miki text nace na taho da Mami bata da lafiya. Gobe zan kai ta asibiti in sha Allah." "Subhanallah. Shi ne muke nan? Bari na ɗauko su Aisha mu tafi." "Kada ki damu. Salwa na gidan. Bana so mu koma ne kiga baƙi. A can ma ya dace na sanar dake to kuma ban sami nutsuwa ba." Murmushi tayi masa "babu komai. Amma Salwa fa ta ce min tana waje." "Waje kuma?" "Eh, kati take so in..." "Koma ciki." Yayi maganar yana sauko matattakalar da za ta sada shi da hanyar fita. A waje ya ganta tsaye can gefe ta rakuɓe kamar wata almajira. Duk sauron wajen nan ya tabbata ya gama cinyeta. Ta ɗan bashi tausayi amma bai nuna mata ba. "Taho mu je." Masu gadin suna ganin shi su ka bata hanya ta wuce. Magana ta so yi masa amma babu fuska. Da sauri sauri ya ding tafiya sai da su ka shiga hall ɗin sannan ya nuna mata inda ango da amarya suke. Taj da Hamdi ke tsaye a filin rawa taƙi motsi. Ya riƙe hannayenta yana magana tana dariya. Ce mata yake ko dai ta saki jikinta ko ya kama break dance yanzun nan. "Kin gani Salwa? Ke ya fara sani kafin Hamdiyya. Da yana sonki da kece a tsaye a can. Don Allah ki samawa kanki lafiya ki jira naki mijin." "Na haƙura Yaya. Tafiya ma zan yi." Ta ce kamar gaske. "Jirani a nan in faɗawa Zahra. Nan da kamar 15 minutes sai mu tafi." Yana barin wajen tayi gaba. Ido rufe ta nufi inda su Taj su ke. Sun bar rawar sai hotuna da ake ta ɗauka. Tun kafin ta ƙarasa inda suke Hamdi ta hangota. Gabanta ya kama faɗuwa sai ta soma karanta Ayatul kursiyyu. Salwa na zuwa ta shige tsakaninsu ko sallama babu. "Ya Taj ayi mana hoto." Yadda kafaɗarta take gugar tasa ko Hamdi da suke tsaye tun dazu bata yi wannan tsayuwar dashi ba. Matsawa yayi da sauri yana a'ziyya a zuci sai ji yayi ta riƙe masa hannu. Wani maiƙo maiƙo da danshin da ya yi zaton na gumi ne daga hannun nata duk ta shafa masa. Idanun Hamdi a take su ka rikiɗe sai dai ganin idon mutane sai ta daure zuciyarta. Taj na jan hannunsa ya fara jin ciwon kai Salwa sai ta sake ƙarfin riƙon. Basu san daga ina ba kawai sai wani hannun su ka ji ya kama hannayensu dake haɗe ya raba. "Zan ci mutumcinki Salwa akan yarona kin ji ko." A matuƙar tsorace Salwa ta dubi Inna. Hanjin cikinta su ka kaɗa. Layar da take shirin sakawa a baki ta tauna sannan ta umarce shi da ya biyota ta saɓule ba tare da ta sani ba. Barin wurin tayi da wani irin sauri. Tana tafiya Inna ta duƙa da sunan Allah a bakinta ta ɗauki layar. Sunan ɗanta ta gani ɓaro ɓaro a jiki. Ta haɗa ido da Hamdi da taga komai ta matsa kusa da ita. "Kama shi ku zauna. Zan faɗawa Amma a rufe taron haka." Kai Hamdi ta gyaɗa. Ta riƙo Taj da idanunsa su ka birkice. Bayan sun zauna tana ta tofa masa addu'a a fakaice ya dawo daidai. Ya ce ta tashi ya kaita gida. "Su Yaya fa?" "Bishir zai kai su. I need alone time with you." "Na'am?" "Nace muje na kama mana hotel." "Wallahi ba haka ka ce ba." Ta faɗa a tsorace. Dariya ya yi mata "Ki ka ce baki ji ba." "Da wasa nake." "Matsoraciya." Addu'ar rufe taro aka yi. Kowa ya tashi cikin murna da jindaɗin wannan biki mai ban sha'awa. Baballe ya ɗauki Zee, Safwan ya ɗauki Sajida sannan Taj ya tafi da Hamdi. Ahmad da Anti Zahra kuwa mamakin duniya ne ya kama su da su ka shiga gida su ka tarar ana bushashar cin shinkafa dafaduka da farfesun kifi wanda ɗaya daga cikin ƴaƴan Anti Zabba'u ta dafa. RAYUWA DA GIƁI 28 Batul Mamman💖 This page is sponsored by SAFFADEMPORIUM the world of amazing scents. Kun san da wuya na tallata abin da ban sani ba. To jama'a akan saffademporium ni ɗin jiyau ce kuma ganau. Ido ya gani, hanci ya shaida! Safiyya Ummu Abdoul our one and only Chairlady ta Fikra Writers Association ita ce mamallakiyarsa. Komai na Fikra kuwa daban yake. Akwai Raudha turaren carpet da kujeru, Naeema airfreshner, oils zafafa guda biyar, turaren kaya na maza da mata. Khumra masu tsayawa a rai da kuma turaren wuta. Za ku iya samunta a manhajar instagram @saffademporium ko wannan layin 07010137848. Sayen nagari...mayar da ƙamshi gida! ~~~~~~~~ Kun kira Kun turo saƙo Kun zo dubiya har asibiti Ni kuwa me zan ce da masoyan SonSo idan ba kyakkyawar addu'a da fatan alkhairi ba? A yayinda da nake post babu abin da yake yi min daɗi sama da kyawawan addu'o'in biyan buƙata da ku ke yi min. Wannan addu'ar ita ce babban abin dake ƙarfafa min gwiwar typing ko da jikina baya min daɗi domin bawa bai san alkhairin bakin mutane ba. A yau ina mai ƙara godiya ga Allah da ku bakiɗaya. Na sauka lafiya na kuma sami lafiyar jiki bayan aikin da aka yi min. Ahmad Amir dani da duka ahalinmu muna godiya da karamcinku. Nayi kewarku da sharhinku mai sanya ni nishaɗi. In sha Allah zan cigaba da posting sai dai ba zai zama kullum ba. Sai kun ƙara haƙuri saboda yanayi ya ƙara canjawa. Ga ƙaramin goyo, yara, ɗawainiyar gida da aiki. Duk da haka kada ku sare da tunanin jira zai dinga tsaho. In Allah Ya yarda labarin zai cigaba cikin amincin Allah. SonSo *** Idan kaga yadda ake shiga gidan Alh. Hayatu sai mutum ya rantse gayyar mutane ce masu zuwa biki. Nan kuwa kaf ɗinsu ahalin gidan ne. Babu bare ko ɗaya sai masu aiki. Ƴaƴansa ne da jikoki. Kuma a haka wasu ba a nan za su kwana ba. Falon kamar ba zai ɗaukesu ba saboda yawa. Da yake an gama gajiya, rabon wajen kwana kawai aka tsaya yi. "Duk wanda ya san ya fita ya bar kaya a falo ko cikin ɗakuna tun wuri aje a kwashe. Ba za ku dame mu da cigiya ba gobe." Cewar Ummukulsum ga jikokin. Ita ce babbar ƴar Yaya Hajiyayye kuma jika ta farko a gidan ta girmi Firdaus ƴar ajin su Hamdi. "Ni dai ban ga kayana da na ajiye a nan ba..." Cigiyar da take gudu tunda ta san komai wajenta ƙannen za su zo nema mazansu da matansu aka fara yi daga rufe bakinta. Kula su ka yi falon a gyare yake. Aka tambayi masu aiki kowacce ta ce ba ita tayi ba kafin su tafi. Abin da mamaki dai. "To ko dai Alhaji ne? Naga motarsa..." Hamɓare bakin mai maganar Yaya Samira tayi kafin ta kai ƙarshe. "Baban namu ne zai yi muku gyaran falo don rainin wayo?" "Gani Mugenbo shugaban marasa kirkin duniya ko?" Muryarsa su ka ji kafin su gan shi yana fitowa daga ƙofar ɓangarensa dake cikin falon. A gurguje masu ƙuruciyar ciki su ka yi kansa saboda sabon da su ka yi dashi. Ƴan matasan kuwa su ka shiga sunne kai. Manyan kuma dariya su ka yi. Su sun fi sanin baban nasu akan ƴan baya baya da su ka taso lokacin da ya fara fushi da Taj. Tsaurin ra'ayinsa bai hana shi kamanta mu'amalantar iyalinsa yanda addini ya tsara bakin gwargwado a lokacin ba. Dalilin da yasa ma ya sami damar iya tafiyar dasu akan ra'ayinsa kenan koda zuƙatansu basa son abu. Ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sa iyalinsa su butulce masa. Cikin jikokin wani ɗan shekara biyar zuwa ya yi jikinsa ya tsaya yana fuskantar wadda ta ce ko Alhaji ne ya kwashe kayan. "Alhaji ba ya yin aikin mata. Shi ba ɗan daudu bane." Tsit falon yayi. Kunya ta kama su aka rasa mai kwaɓarsa. Alhaji ya jinjina maganar musamman da ya karanci yadda kowa ya sha jinin jikinsa. Duk sai yaji babu daɗi. Murmushi ya yi na jin kunyarsu ya dafa yaron "kwashe kaya da ninkewa ai ba aikin mata bane kaɗai Amir. Duk wanda zai iya saka kaya ya kamata ace zai iya ninke su." "Laahhh, Uncle Taj ma ba ɗan daudu bane kenan ko?" "Me yasa ka ce haka?" Alhaji ya tambayi yaron da sakakkiyar fuska don ya bashi amsa. "Saboda duk wanda ya iya cin abinci shi ma ya kamata ya iya dafawa." Mahaifiyar Amir kasa tsayuwa tayi saboda tsoron me Alhaji zai yi bayan jin amsarsa. Ta kalli yayyenta su Yaya Kubra tana neman ceto. Matan gidan ne ƙarshen shigowa dama. Saboda haka daga baki bakin ƙofa suke tsaye. Hajiya tana kallon idon Alhaji ta yiwa Amir tambaya. "Kai ka san waye ɗan daudu?" "Eh mana" ya amsa da karsashi na yaron da aka yiwa tambaya mai sauƙi "sune masu yin haka..." ya ɗaga hannuwa ya tafa da iska "ahayyyeee cass, rass... ko?" Hannuwansa Bishir ya yi saurin riƙewa ya ce "dare ya yi, ayi shirin bacci a kwanta haka nan." Da sauri sauri su ka dinga watsewa aka bar Alhaji a tsaye cikin tunani da wata irin kunya. Yau kuma yaro ɗan shekara biyar ne ya shiga sahun masu faɗa masa gaskiya? Kuma wannan karon a gaban mutanen da yake jin ya isa dasu ta kowacce fuska! "Alhaji na ce Allah Ya bamu alkhairi." Da muryar Umma tunanin da ya fara ya kau ya dawo da hankalinsa ga matansa. Hajiya ma sai da safen tayi masa ta shige yayinda Mama tayi masa tambayar ko ya gama da kwanukan abincin dare da ta ajiye masa domin ta kwaso. Amsa ya bata sannan ya mayar da dubansa ga neman Inna don tunda su ka shigo ko tari bai ji tayi ba. Jiran ta ce masa sai da safe kamar ƴan uwanta yake sai yaga bata wajen. 'Fushi take? Me kuma nayi? Ba na bada izinin yin bikin ba? Sai da safen ma yau ban isa ace min ba?' Ya ayyana a zuciyarsa. "Ba tare ku ka shigo da Abu bane?" Ya tambayi Mama. Yanayinta yaga ya sauya sannan ta ce masa ya shiga ɗakin Innar ya sameta. Hankalinsa tashi ya yi don ko bata faɗa ba yaji a jikinsa babu lafiya. Tabbas Hajiya da Umma ma basa cikin walwalar da yayi tsammanin za su dawo da ita. Ɗakin ya shiga kai tsaye ya tarar da ɓangarenta da ƴan kwana. Wuce na falon ya yi ya shiga ainihin ɗakin baccinta inda nan ma wasu ke ciki. Sai dai suna ganinsu su ka fita. Zai yi magana ta riga shi ta hanyar miƙa masa wannan layar. Ya miƙa hannu zai karɓa kenan sai Inna taga ya yi baya da hannunsa da sauri yana zaro idanu. "A'uzubillahi..." "Ka san ko mene ne kenan?" Ta ajiye layar a wajen madubi jikinta a sanyaye. "A ina ki ka samo ta?" Ya tambaya cikin matsanancin tashin hankali fiye da wanda tayi tsammani. "Sal..." Kafin ta kai ƙarshen sunan ya gane wa za ta ce. Ya ɗaga layar yaga sunan Taj. Ransa kuwa ya yi mummunan ɓaci. "Ɗana? Me matar nan ta taka da har take tunanin zan zuba ido ta mayar min da ɗa mutum mutumi?" Inna na jin haka nata hankalin ya sake tashi. "Mugun tsafi ne ko? Innalillahi. Tun a wajen naga ya fara runtse idanu." Maganarta sake tunzura zuciyar Alhaji tayi. Sirrin da ya sakayawa Mami albarkacin Ahmad ya dawo masa tar cikin ransa. Haƙiƙa kamar sauran matansa ita ma so ya saka shi aurenta. Ta zo da fitina da neman rigima. Kullum cikin takalar Hajiya da Mama faɗa dake gidan a lokacin take. Aka mayar masa da gida filin kai ƙara. Wani abin idan tayi shi kan shi sai ya yi mamakin mene ne abin tashin hankali a ciki da har za ta nemi faɗa. Abin mamakin ma shi ne kasancewar shi ɗin jajirtaccen namiji ne amma ko zai ari baki wajen yi mata faɗa da nasiha anjima ko gobe ma sai ta ƙara. Sannu a hankali ya shiga karantarta inda ya fahimci ashe asiri take yi masa, kuma yawan rigimarta tana yi ne domin aunawa taga ko sihirin ya ci. Bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da yaga wannan layar da yaji da kunnuwansa ranar da Zabba'u ta kawo mata tana cewa sunanta Raƙumi da akala. Har tana yi mata rantsuwar idan ta tauna ko me ta umarce shi zai aikata. Burinta a lokacin tunda ta haifi Ahmad yana ƙarami ta fitar da su Hajiya. Ƙin nuna musu ya gani ya yi. Ya kuma bari tayi amfani da ita. Ranar ta yiwa Hajiya ɗiban albarka ajin ƙarshe duk yana jinsu daga ɗaki. Zuciyarsa kamar ta fito ta baki amma ya kasa fitowa saboda a kan idonsa ta saka a bakin ba tare da ta san yana gani ba. Ta tauna ta umarce shi da ya zauna a ɗaki kada ya fito ko me zai faru. Haka kuwa aka yi. Rigima ta kaure amma duk yadda yaso haka ya zauna a ɗaki. Don baƙinciki har hawaye sai da ya yi. Sai kuma ya shiga karanto addu'o'in tsari tunda ya gama gano illar layar. Lallai idan ya zauna da ita rayuwarsa za ta zama mara amfani. Shigowa Mami tayi da aka gama faɗan tana kumbure kumbure. "So nake ka saki Haj. Gambo yanzu yanzun nan." Ko ɗaga kai ya kalleta bai yi ba ta sake maimaita umarnin amma shiru. Dama layar na hannunta sai ta ɗaga ta juya masa baya za ta mayar cikin bakin. Bata yi aune ba taji ya damƙe hannun ya zare layar. "Ki je gida na sake ki saki uku." Farat ɗaya ya faɗi maganar don kada a sami matsala. Ta kuwa dafe ƙirji a gigice. "Haj. Gambo nace..." Ƙarfin gwiwarsa ya dawo gare shi ya ce "ni kuma ke nace." "Wallahi baka isa ba...wayyo Allah. Na shiga uku. Alhaji ina zani? Ina kake so nayi da Ahmad bayan ka san ni marainiya ce?" Gabaɗaya kamanninta sauyawa suka yi a take. Tana wannan hargagin ya kira Mama ya ce ta ɗauko Ahmad duk inda yake a gidan ta goya shi. "Idan ba ni ba kada ki bawa kowa har uwar da ta haife shi." Mafarin da goyon Ahmad ya koma hannun Mama kenan. Ba a raba ɗa da uwa amma bai san sunan da za a kira shi ba idan ya bari jininsa ya tashi a gidan shirka. Haka ya nunawa iyalinsa cewa faɗan da ta takali Hajiya ne yasa shi sallamarta. Ya kuma yi ne don kyautata ƙimar ɗansa a gidan. Daga lokacin bai sake shiga harkarta ba sai da ta fara ɗorawa Ahmad ɗin buƙatun da su ka fi ƙarfinsa yaje ya samawa mijinta aiki. Baya son haɗa inuwa da mushiriki kuma wanda yake tu'ammali da tsibbu. Shi yasa ya nesanta kansa daga gareta. Baya bari komai ya haɗasu. To amma yau dai tura ta kai bango. Idan tana cin ƙasa lallai ta kiyayi ta shuri. Ƴarta ko ita ce autar mata kuma masoyiya ga Taj ba zai taɓa sahale masa aurenta ba. Wayarsa ya ɗaga da sauri ya kira Taj...abin da rabonsa da yi har ya manta. *** Ƙirjin Anti Zahra dukan tara tara ya kama yi da ganin wannan rashin hankali da ake yi mata a gida. Inda su ka sami ƙarfin halin iya shigar mata kitchen su ka yi binciken kayan abinci da girki shi ne babban abin mamaki. Gashi an zuzzubar da shinkafa akan kafet. Yaran babbar ƴar Anti Zabba'u sun tattake wata a wurin. Ƙarnin kifi kuwa ba a magana. Maiƙon duk an shafe a kujeru da centre table don ƙeta. Wata ma remote ne a hannunta na daman. A hagu kuma tana riƙe da kofin da aka keɓe domin maigidan ta cika shi da juice. Shi kuwa Ahmad Anti Zabba'u da Salwa yake kallo yana neman wadda za ta yi masa bayani. Saboda yadda ransa ya ɓaci kuwa Adam's apple ɗinsa hawa da sauka kawai yake yi ya kasa magana. Gani yake duk kalmar da za ta fito bata da ƙarfin nuna yadda yake ji a zuciyarsa. Anti Zabba'u ko a jikinta domin da shirinta ta fito. Ta saki rai tayi musu maraba kuma bata damu ba da basu amsa ba. Sai ma kaɗa baki da tayi ta ƙwalawa ƴarta da ta tafi kitchen ƙaro musu juice tayi. Ita ce ake so Ahmad ya aura yanzu. "Habitti (Habibty take kiranta saboda tafi ƴan uwanta kyau, sunan sai ya bita) fito ga yayan naki ya dawo." Ta kalle shi "tun ɗazu take damunmu da mitar ka ƙi dawowa." Daga cikin kitchen ɗin aka ƙwala ihu duk wai na murna sannan wata ƴar tsumburburar budurwa ta fito da sassarfa cikin farinciki. Sanye take da matsatsen wando skin tight wanda daga gani a can ƙasan dilar gwanjo aka samo shi. Ta ɗora masa wata yarbatsulan riga mai rawa a jiki da wasu irin igiyoyi. Sai da ta tabbatar ta haɗa ido da Anti Zahra sannan ta buɗe hannuwa. "Yaya Ahmet oyoyo." Saurin shiga tsakaninsu Anti Zahra tayi don ta kula Ahmad bashi da niyar kaucewa. "A gabana? Baki da hankali da alama." Cewar Anti Zahra cikin fushi "nayi miki kama da matan da za su ɗauki wannan ɗabi'ar ta wasan banza tsakanin cousins?" Da wani salon shagwaɓa Habitti ta ce "Ya Ahmet kana jin matarka ko?" Ko kallonta bai yi ba balle tasa ran yaji ƙorafinta. Hankalinsa ya tattara ya dubi matarsa. "Me yasa ki ka shiga tsakaninmu Zahra? Da kin barta ta ƙarasa abin da tayi niyya." Anti Zahra taji wani abu ya soki zuciyarta. Ita kuwa Anti Zabba'u har ta fara murmushin ƙeta sai taji ya cigaba da magana. "...ni kuma sai na nuna mata idan tana taƙama ta sha nonon hauka to nima na tsotsa tunda duk tushenmu ɗaya." Siɗe hannu Anti Zabba'u tayi da sauri ta miƙe tana taro zanin da ta kwance domin taji daɗin yin lodi. "Ahmad ni ce mahaukaciya?" "Kin ji na ambaci sunanki?!" Yayi magana muryarsa a sama. Yau da yarinya ce tayi masa haka da wahala idan bai zane ta ba. Ita da ƴan matan duka jikinsa sanyi ya yi don ba haka su ka zata ba. "Rashin kunya za ka yi min don na zo gidanka jinyar mahaifiyarka?" "Jinya ki ka zo? Wa ya kira ki?" Ya buɗe mata wuta. Anti Zahra sai da taji babu daɗi ta ɗan taɓa hannunsa "ƙanwar Mami ce fa. Ka sassauta harshenka a kanta." "Kin fini saninta ne?" Ta girgiza kai da sauri don bata taɓa ganin fushinsa irin wannan ba. Anti Zabba'un ya sake kallo "cikin wađannan ƴaƴan naki babu wadda za ki je gidan aurenta ki yi wannan abin ba tare da mijinta ya yi muku kallon rashin nutsuwa ba. Kin kuma sani amma shi ne ni ki ka yi min saboda ga karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ko?" Hankalinta sake tashi ya yi don yau tv ta sayar daga lokacin da Salwa ta kirata ta haɗa kuɗin aikin da aka yiwa Habitti. "Saboda uwarka tana kwance shi ne za ka ci min mutumci?" "Idan da ƙalau take ba ki isa ki shigo gidan nan ba wallahi. Yau nayi aure? Ƴaƴana biyu fa! amma ko sau ɗaya babu ke babu waɗannan abubuwan..." ya nuna matan da jikinsu ya gama laƙwas sama da ƙasa. Babbar ce ma Hansatu ta ɗan taɓuka abin kirki ta tashi tsaye "idan ka cigaba da faɗawa mamanmu magana fa ba za mu yarda ba." Da wutsiyar ido ya kalleta sai gata tayi tsit ita ma. Ya juya ga Salwa da ko tari bata yi ba tun shigowarsu. Babu shiri tayi ƙasa da kanta ta kama hanyar ɗaki za ta wuce sumsum. "Idan kin wuce ciki wane mahaukacin ne zai yi min bayanin me yake faruwa da gidana? Ban soke batun zuwan nasu kafin na fita ba?" "Yaya..." "Ina raga miki ne kawai saboda ke mace ce, ba don haka ba da tuni na sauke miki abin da yake damun ƙwaƙwalwarki. Shashasha wadda bata san ciwon kanta ba." Rasa da me za ta ji tayi. Da ɓacin ran Ahmad wanda bata saba gani ba, ko kuwa da ganin da Innar Taj tayi mata dumu-dumu a wajen dinner akan abin da take shirin yi? Haƙuri ta buɗe baki za ta bashi ya ɗaga hannu ya dakatar da ita. "Ku haɗu ke da su ku kwana a ɗakin da ki ke. Gobe da safe..." ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye akan centre table yana kallon su Anti Zabba'u "ku ɗauki wannan ku yi kuɗin mota kuma a gyara min gida kafin a fita." Ita kuma Salwa ya ce "ke kuma zan kira babanki ya turo mai ɗaukarki ki koma gida. Kuma wallahi kin ji na rantse idan ki ka fita daga gidan nan kafin lokacin tafiyarki sai na baki mamaki." Yana gama magana ya shige ɗakin Salwan ya ɗauko Mami kamar jinjira don duk ta zuge. Kai tsaye ɗakin Zahra ya wuce da ita kowa yana ganin hawaye shaɓe shaɓe da su ka jiƙa fuskarta. Duk abin da aka yi tana ji. Tafi kowa sanin dole ƙanwarta ta zo da wata manufa. Takaicinta da ko magana bata iyawa sosai yanzu sai dalalar yawu. Da ko zama a gidan Zabba'u bata isa tayi ba. Sai kuma murnar Ahmad ya nunawa duniya ya haifu. Wannan sauƙin kan nasa da take ganin za a iya cutarsa yasa ƙafa ya ture. Ya nuna mata shi ɗin jinin Alh. Hayatu ne babu ƙarya. Sai da ya kwantar da ita sannan ya ce da Anti Zahra ta ɗauko duk abin buƙatarta da na yaran su koma ɗakinsa. "Idan tana buƙatar wani abu fa?" "Zan dinga leƙawa." Bai amince ta kwana ba don ya sani akwai cin zali ma idan yace sai ta kula da Mamin da ta ɗora mata karan tsana tun kafin aurensu. * Mummunar shaƙa Salwa taji a wuyanta. Gashi bata san ko wace ce ba domin ta bada baya tana shirin cire kaya. "Sakar min wuya" ta ce da riƙon ya yi ƙarfi ta tabbatar ba na wasa bane. "Mu za ki yiwa shigo-shigo ba zurfi ki sa a ci mana mutumci?" Da mamakin muryar ta ce "Anti ni za ki shaƙewa wuya?" "Haifarki nayi da ba zan shaƙe ki ba?" Da zafin nama Salwa ta juyo ta doke hannun nata. Ganin ta buɗe baki tana shirin yi mata magana yasa ta ce "tunda baki haife ni ba nima ba zan kasa doke miki hannu ba." "Wato na kula shiri ku ka yi da Ahmet ki ka taso mu don ku wulaƙanta mu." Cewar Habitti tana hura hanci. Ba su san ran Salwa yafi nasu ɓaci ba saboda disappointments ɗin da ta kwasa. Shi yasa bata ji nauyin ramawa ba. "Kwaɗayi dai ya kawo ku tunda uwarku na kira ba ku ba..." Kiffff, taji saukar marin da yafi kama da gwaɓe baki don sai da laɓɓanta su ka amsa. A take kuma idanunta su ka kaɗa da ƙwallar azaba. A makance ta kai hannu domin ramawa akan Hansatu da tayi marin sai hannun ya sauka a kuncin Anti Zabba'u. Ita kanta Salwa sai da gabanta ya faɗi da taga wa ta mara, sai dai kafin ta gama sanin me za ta yi ƴaƴan gwaggon tasu su ka yi mata rubdugu. Kowa na kai hannu aka lillisa mata jiki. Ihun ma da za ta yi don Ahmad yaji ya kawo mata ɗauki an toshe bakin. Sai da su ka tabbatar tayi laushi su ka barta da ta daina ƙoƙarin kare kanta. Abinka da waɗanda su ka saba da damben gidan haya. Kukan da take fitarwa a hankali ga jini yana ta zuba daga hancinta ne ya sanya Anti Zabba'u cewa "Yanzu idan Ahmad ya ganta ya zamu yi?" "Ba ma zai ganta ba. Kafin su tashi zamu kama gabanmu. Banda dare ai da babu abin da zai sa mu kwana" Habitti ta faɗi tana sake dungure mata kai. *** Shiru motar ba ka jin komai sai hawa da saukar numfashin Hamdi dake baccin gajiya. Musu su ke da Taj yana tsokanarta da cewa yau shi ya haskata tana cewa ita ta haska shi. Can sai ji ya yi ta koma uhm da uhm-uhm idan yayi magana. Yana juyawa yaga ɗaurinta ya karkace saboda yadda ta kwantar da kai a jikin kujera. Mamaki da haushin ta rusa masa plans ɗinsa su ka kama shi. "Lallai ma yarinyar nan. Bacci ma kike yi a irin wannan lokacin?" Kafaɗarta ya girgiza a hankali ta ɗan buɗe ido ta kuma rufewa. "Ko ki tashi ko in wuce gidanmu dake" ya faɗi yana karantar fuskarta. Ko gezau bata yi ba wanda yasa shi tunanin tabbas bacci take yi. Don da ido biyu take ba za ta yi shiru ba. Ƙwafa ya yi ya kaɗa kai. "Allah Ya kaimu gobe nima sai na rama. Idan an kawo ki a kwance ina bacci za a ganni akan gadon amarya." Nauyin baccin da ya rufeta bai hanata jin abin da ya ce ba. Murmushi tayi a ɓoye ta gyara kwanciyarta. Baccin kwanakin nan da bata samu ne ya yi mata kamun kazar kuku. Taj cigaba ya yi da tuƙin yana yi yana kallonta. A baccin ma tayi masa kyau. Sai da ya kusa shiga unguwarsu ciwon kan da ya soma ji bayan Salwa ta taɓa shi ya dawo masa da ƙarfi. Abu kamar wasa sai gashi yana gumi. Da ƙyar ya iya ƙarasawa ya tsayar da motar amma bai kashe ba. Sai da ciwon ya lafa ya fita ya zagaya gefenta ya buɗe sannan ya ranƙwafa yana kallonta sosai. Ƙamshin turarensa da numfashin da yake yi daf da ita ne yasa tsigar jikinta tashi tun kafin ta buɗe ido. Yunƙurawar da za ta yi yayi daidai da sake matsowar Taj. Kawunansu su ka haɗu da ƙarfi. "Ya Salam" Taj ya dafa kansa da hannu ɗaya, ya kuma ɗora ɗayan a goshinta inda yake tunanin ta nan su ka buge. "Fasa min kai za ka...." Hamdi ta fara cewa sai ta kula idanunsa sun yi ja da taimakon fitilar waje ta gidansu. "Kuka kake yi? Kan nawa da zafi ne?" Ta tambaye shi ganin yana runtse ido. Bata san fami ta yiwa ciwon kan nasa ba. Yadda tayi tambayar sai da yasa shi yin murmushi. "Abu kamar auduga ina zafi a nan?" "Awwnnnn" ta ce tana yi masa murmushi da fari da idanu "wai irin abin nan ace tsabar soyayya ka buge ma baka ji zafi ba." Taj kasa jira ta gama magana ya yi. Tunda ta rangwaɗa kai ta ce awwnnn ɗinnan ya daina gane komai. Ɗan yatsansa ya ɗora akan bakinta yana zana leɓen wanda ya sanyata shirun dole. Sannan ya zame hannun a hankali ya kawo kansa daidai fuskarta. " I realy tried to be a gentleman tonight Mrs Happy amma kin hana." "Me kuma nayi?" Hamdi tayi tambayar cikin faɗuwar gaba don ta fara tsorata. So take ta ganta a cikin gida kawai. "Baki yi komai ba sai taɓa zuciyar Tajuddin." Wayancewa tayi saboda take takensa da take gani ta ce "Wai ka san ma'anar sunanka kuwa?" Shi ma da gatse ya bata amsa "Ta yaya zan sani baki faɗa min ba?" "Taj yana nufin crown, kaga Tajuddin yana nufin..." ta fara cewa ya katseta. "Ina son ki Hamdiyya Habib Umar" Sannan ya turo kanta ta hanyar turo kanta gaba da hannunsa da ya sanya a bayan kan. Sauran maganganun da su ke bakunansu basu sami damar shiga kunne ba saboda sabon al'amarin da Taj ya kawo musu. Tun hankalin Hamdi na kan ƙofar gidansu har ta manta a ina take. Sunan Taj ne kaɗai yake tafiya tare da bugun zuciyarta. Kamar ba za su rabu ba. Taj ne ya yi ta maza ya ɗaga kai yana kallonta da murmushi. "It seems like zama dani ya fara shafarki fa yarinyar nan. Haka ake so. Wani abin ma sai gobe ko?" "Kai da ka ce bacci za ka yi kafin mu ci kaz..." kasa ƙarasawa tayi ta kama laɓɓanta ta ɓame da ta ankara da katoɓarar da take shirin yi. Ba za ta so ya fassarata da rashin kunya ba. Ta sunkuyar da kai tana faman matsa hannuwa kamar mai tausar gajiya. Sai dai ta makaro! Haɓarta Taj ya ɗago a hankali ta kawar da kai gefe ido a rufe. Yana murmushi ya ce, "Kalle ni nan." Ya ɗage gira "Ni fa ba haka nake nufi ba." Hamdi ta ce kamar tayi kuka don wani kallon kya yi kya gama Taj yake yi mata. "Me ki ka ji na ce?" Cikin shagwaɓa Hamdi ta ce "to ka daina yi min irin wannan kallon." Amsar da ya tanada don ya cigaba da tsokanarta ya fasa faɗi da yaji kamar an kwaɗa masa guduma a ka. Haka kawai lokaci ɗaya abin ya ta'azzara. Numfashi ya ja da ƙarfi sannan ya ce "Kira min Abba don Allah." "Ƙara ta za ka kai?" Jikinsa nauyi ya yiwa ƙafafunsa sai gashi ya yo kanta gabaɗaya. Da fari ta zaci wasa ne sai da taji ya sakar mata nauyi yana jan hailala a hankali. Ruɗewa ajin ƙarshe Hamdi tayi. Ta tattaɓa shi tana kiransa bata ji ya amsa ba. Kansa ta ɗago ta sanya hannunta ɗaya ta dafa kumatunsa. "Don Girman Allah ka tashi. Wannan ba wasa bane wallahi." Nan ma shiru sai numfashinsa da yake fita da sauri sauri. Da ƙyar ta yunƙura ta ɗauko jakarta ta zaro waya. Abba ta kira ya fito da gaggawa da yaji yanayin muryarta. Da farko da ya hango ƙafafun Taj ta ƙofar gaba inda take zaune har zai koma. Kunya ta kama shi sai yaji Hamdi na kiransa da ƙarfi. "Abba zo ka gani." Ko da ya ƙarasa bai san lokacin da ya kai hannu ya ɗago Taj ɗin daga jikinta ba. Yadda duka gaɓɓanta su ke karkarwa haka nasa su ka fara. Da rawar baki Hamdi ta iya faɗa masa iya abin da ta san ya faru. Ido Taj ɗin ya buɗe a hankali da yaji an ɗaga shi. Hamdi ta buɗe bayan motar Abba ya taimaka masa ya shiga. "Bari na duba waye yake gida tsakanin yaran Mal. Baƙo da Halliru sai mu kai shi asibiti." Da sauri ya yi gaba zuwa gidan maƙotansa da su ka iya tuƙin mota. Tafiyarsa ke da wuya kiran Alhaji ya shigo wayar Taj. Da kansa ya zaro ta daga aljihu ya miƙawa Hamdi. Cike da dauriya da cije baki ya ce mata idan Kamal ne kada ta sanar dashi don baya son tayar masa da hankali. In sun je asibiti sai a faɗa masa. Screen ɗin ta kalla lokacin kiran farko ya katse ta ɗaga kai domin faɗa masa sunan da ta gani sai kawai ya kwantar da nasa kan a cinyarta ya rufe idon. "Ɗauki ko ki kashe. Ƙarar tana damuna." Ruɗanin ciwon nasa da wata fargaba da ta shigeta saboda tsoron mai kiran ne su ka sa ta kiransa da sunan da taga Taj ya yi saving numbar. "Alhajina ina wuni?" Alhaji ya cire wayar daga kunnensa ya duba sunan don ya fara kokonton wa ya kira. "Alhajinki kuma?" "Au...lahhh...Alhajinsa nake nufi" Hamdi ta sake gigicewa da ƙarfin amon muryarsa. "Shi wa?" Ya tambayeta yana yafito Inna da hannu. Wayarta ya karɓa zai kira Taj ɗin. A zatonsa ko ya daina amfani da wannan layin da ya sani. Aunawa tayi taga idan ta ce masa Taj kai tsaye zai ce bata da kunya. Kuma ita ma dai nauyin sunan take ji. "Shi ɗin dai" ta ce da ƙaramar murya. Ta ƙara da ɗan bayani a fakaice "uhmm...Hamdiyya ce" Kai tsaye kuwa ya ganeta ya ce "Hamdiyya ina Taj? Bashi wayar." Ɗan taɓa shi tayi ta ce masa Alhaji ne sai ya nuna mata kansa. Rabonsa da ganin sunan mahaifinsa a allon wayarsa ace ya kira shi ba zai iya tunawa ba. Sai dai kuma yau ya kira a yanayin da ba zai iya magana ba. "Ba ya iya magana saboda ciwon kai." Katse ta ya yi kafin ta ƙarasa "bashi da lafiya ko? Me ku ke yi baku kai shi asibiti ba? Ba shi wayar na ce!" Muryarsa da take tattare da tashin hankali ta fito mata da sauti na umarni kuma cikin faɗa. Sai ta share ta sanar dashi cewa ba zai iya tuƙi ba. Amma Abbanta ya tafi neman wanda zai ja motar a maƙota. "Shi me yake yi da ba zai tuƙa motar ba? In bashi da ita ya ja ta Taj ɗin mana." Da ƙaramar murya ta amsa masa "bai iya tuƙi ba." Fargabar ɓata lokaci da halin da Taj zai iya shiga ne su ka saka shi juyawa ga Inna ya yi magana wadda ta shiga raɗau kunnuwan Hamdi "kinga illar daudanci ko? A shekarun Habibu ace bai iya tuƙi ba kamar ba namiji ba." Wannan magana ta sanya Hamdi jin nauyi da wani irin zafi a zuciyarta. Idanunta kuwa su ka soma zafi tunda dama kukan a kusa yake a dalilin ciwon Taj. Da hawayen ya zubo sai idon yayi kamar an baɗa barkono saboda tsananin ƙuncin da take ji. Abban nata yake faɗawa waɗannan maganganun? Ta tuna dama ya so a kashe auren. Babu mamaki sai da ya faɗa masa abin da yafi wannan ciwo a gaban idonsa. Kasa daurewa tayi tana ganin kamar in tayi shiru ta yarda mahaifinta bashi da daraja. Sai da ta kalli fuskar Taj taji kunya, amma duk da haka bata ji a ranta za ta fasa faɗa masar abin da yazo bakinta ba. Numfashinta har canjawa yayi saboda ɓacin rai. Ta buɗe baki za ta yi magana Taj ya tashi zaune ya karɓe wayar. Jiran abin da zai ce tayi sai taga ya miƙawa Abba da ya dawo yana tsaye a baƙin ƙofa wayar. "Alhaji ne" kawai ya ce ya damƙa masa wayar. Magana su ka yi akan asibitin da za su haɗu su jira isowar Alhajin. Ita dai Hamdi ta bi Taj da kallon da har zuciyarsa bai yi masa daɗi ba har Halliru ya tada motar su ka hau titi. Duka wayar yana iya jiyo abin da Alhajin yake faɗi. A daidai lokacin da take shirin bada amsa ya daure ya karɓi wayar saboda a ganinsa idan ta yiwa Alhaji rashin kunyar da ya tabbatar tana gab da yi, to babu makawa gazawar Abba zai cigaba da gani. Har ma ya ce ya kasa yiwa ƴaƴansa tarbiyya. Hannunta ya riƙe ya ɗan matse ta zare abinta ko kallonsa bata yi. Ya dinga ƙoƙarin su haɗa ido nan ma ta fuske. Ba don an fara tafiya ba kuma ga dare da tabbas sauka za ta yi. Fahimta ɗaya ta yiwa abin da ya yi. Ya shigarwa mahaifinsa kamar kowanne ɗan halak, amma ita ya hanata tsayawa nata uban. Wata zuciyar ma tayi mata nuni da cewa ƙarshenta shi ma bai ɗauke shi cikakken namiji ba. Abin da take ji na baƙinciki yaƙi sauka. Har su ka isa banda sharar ƙwalla babu abin da take yi. * Da Bishir yana parking Alhaji bai yi mamakin ganin motar Kamal a wajen ba. Shi kaɗai ma ya lura sai bai faɗawa ƴaƴan nasa ba saboda a tunaninsa dama dole Kamal ya sami labarin halin da ɗan uwansa yake ciki. Suna fitowa daga mota su Hamdi su ka iso. Bishir da Abba su ka ƙarasa bakin motar su ka taimakawa Taj ya fito. "Ya kuke kama ni ne kamar wani gurgu. I can walk on my own" ya zame hannayensu daga kafaɗunsa. Hannun wanda bai taɓa zato bane ya maye gurbin nasu. Inda Alhaji ya janyo shi jikinsa ya kuma tallafe shi ta hanyar riƙe kafadar damansa da hannunsa na hagu. Sai ya zamana Taj na manne da jikin mahaifinsa. Bishir da Abba kallon juna su ka yi cikin mamaki da jindaɗi. Shi kuwa Taj neman ciwon kan ya yi ya rasa. Komai ya tattara ya koma zuciyarsa. Inda ta cika fam da wani irin farinciki mara misaltuwa. "Mu je ciki a duba ka." Alhaji ya faɗa yana mai soma takawa a hankali don kada ya wahalar dashi. Taj ya juya ya haɗa ido da Hamdi zai ce ta taho su shiga sai kawai yaga ta ɗauke kai. Abba da Halliru ta fuskanta. "Abba ku taho mu tafi kada mu rasa abin hawa." "Ki bari mu ji abin da yake damunsa mana." Fuskarta a cunkushe ta ɗaga kai daga kallon wayarta ta kuma cewa "Shabiyu ta kusa fa kuma ba abin hawa garemu ba." "Hamdi ki kwantar da hankalinki na kira Bawalle (mai adaidaita sahu maƙocinsu) zai zo ya ɗaukemu." Abba Habibu ya faɗi yana duban Alhaji da yanayi na ban haƙuri game da kalaman ƴarsa. Kada ace bata damu da mijinta ba. "Ba sai ka kira kowa ba. Zan kai ku da kaina ma" Cewar Bishir. "Ka bar shi mun gode. Adaidaitan ma ya ishemu." Ita ce amsar da Hamdi ta bashi kai tsaye. Kallon nutsuwa Alhaji ya yi mata sai tayi saurin kawar da kanta gefe amma bai kasa gane tana cikin ɓacin rai ba. Bata so tayi kuka a gaban mutane. Cigaba da tsayuwarta a nan kuwa tana ganin yadda Abbanta yake takatsantsan hatta wajen yin motsi sai taji duk ta tsargu. Auren ya zo mata wuya har tana tunanin makomarsa. A haka ma bata da labarin alaƙarsu da juna kafin a haifeta. Ba a son ranta su ka shiga ciki har likita ya zo ya buƙaci ya shiga office ɗinsa. Ko da Alhaji ya tayar dashi za su shiga wajen likitan can jerin kujerun baya inda ta zauna ya kalla yana sake nazartarta. A take kuma wata irin kunya ta saukar masa. Hamdiyya bata ce komai ba amma yanayin komai nata a yanzu yana yi masa nuni da cewa anyi mata abin da bata ji daɗi ba. Ba tare da tsawaita tunani ba ya san waye da wannan aikin. 'Lallai Habibu ya haihu' ya faɗa a ransa. Yayinda duniya take ƙyamar irinsu har ta kasa karɓar uzurinsu in sun tuba, ƴarsa ta ture girma da yawan arziƙin gidan aurenta tana mai nuna ba za ta lamuncewa taka darajarsa ba. Abin da bai taɓa zato bane yaji a ransa. Hamdiyya ƴar Habibu ta burge shi har wani sashe na zuciyarsa yana kamanta wannan hali nata da abin da yake tsammata daga jininsa. RAYUWA DA GIƁI 29 Batul Mamman💖 *** Wata doguwar allura Mubina ta zare daga tsakiyar cikin Kamal ta ajiyeta akan kwanon tasa daidai girmanta. Ta koma gefe ta haɗa yatsunta na hagu da dama ta sarƙesu, sannan cikin dabara ta cire gloves ɗinta. Duk abin da take yi kwata-kwata taƙi yarda ta haɗa ido dashi. Umarni kawai take bawa Nos ɗin da ya taya ta aikin akan abin da zai yi. Shi kuwa yana ta kallonta har ta gama bai ce uffan ba. Canjawar yanayinta ya sanya zuciyarsa tsirgawa don ya san bashi da nasaba da kasancewarsa babu riga a wajen. Baya ta bashi yana daga kwance ta harɗe hannuwanta a ƙirji. "Sauƙin da za ka samu yanzu ba mai ɗorewa bane. Daga shi sai dialysis wanda shi ma tasirinsa ba ya wuce lokacin da za a sami ƙodar da za a dasa." Numfashi kawai yaja da ƙarfi yana mai rufe idanuwansa. Zuciya da jikin nasa duka sun gaji. A ƙoƙarinsa na ganin bai ɗagawa kowa hankali ba yayi exhausting ɗin kansa. Duk wata lakar jikinsa mutuwa tayi sakamakon jin abin da tace. Tashi ma sai ya gagare shi. Ji yake kamar lokaci zai cimmasa yanzu yanzu. He badly needed a shoulder to cry on. A ɗan rarrashe shi a bashi baki. Sai yanzu yake nadamar ƙauron bakinsa. Sunan Happy yake kira a zuci domin shi ne zai iya bashi shawarar yadda za su fasa ƙwan a gida. Shirun da ya yi ya sanya Mubina yin gyaran murya. "Bari na baka wuri ka shirya." Da sanyin jiki ya yi mata magana kafin ta fita. "Kada ki tafi Mubina. Bana son zama ni ɗaya don Allah. Not when you just told me I don't have much time left." Tsayuwa tayi amma bata ce komai ba har ya mayar da rigarsa ya sanar da ita. Ta juya a hankali ta dube shi. Idanunsa sun kaɗa sun yi ja sosai. Sai wata ƙwalla da take barazanar wanke masa fuska. Koma mata ɗan yaro ya yi mai jiran rarrashin uwa. Komai nata da ya danganci juriya a take ya ƙwace. Jikinta ya kama rawa a yayinda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai. "Yaya za ka yi da haƙƙina da ka ɗauka Kamal?" Idanunsa ko buɗewa da kyau basa yi ya ɗaga kai ya kalleta. "Me nayi miki kuma?" "Ka san baka da burin rayuwar duniya me yasa ka bari na kamu da son ka? Me yasa kake azabtar dani ta hanyar nuna min kanka a yanayin ciwo amma ka ƙi bani haɗin kan nema maka magani?" "Ashe kina sona..." Kamal ya tattaro ƙarfin hali yayi murmushi gami da komawa ya kwanta "kinga har naji ƙarfi a jikina. Bari na huta sai na tafi." Wani irin kallo Mubina tayi masa "ka san ƙarfe nawa kuwa? Ko ka manta za a sake allurar ƙarfe shida na asuba?" "Kada ki damu zan dawo in sha Allahu." Mamaki ya bata. Ta zata gaskiyar da ta faɗa masa mai ban tsoro za ta sa ya soma tunani da yin abin da ya dace. Rai a ɓace ta ce "You are simply unbelievable! Me za ka je yi a gidan bayan dare ya raba? Kai da ka zo a sume ne kake zancen zuwa gida." Ya za ayi ya manta? Dama dauriya ya dinga yi a wajen dinner ɗin. Taj na fita da Hamdi ya kirata. Lokacin ta kusa gida ma tunda ita ma taje dinar. A asibiti su ka haɗu sai dai kafin ta iso ya suma a mota. Wurin parking ta dinga dubawa har ta gano motarsa tasa aka ɗauko shi. "Zan fa dawo da gaske. So nake in sanar da Alhaji lalurata. Ko ba haka kike so ba?" "Kada ma ka faɗa mana. Ni ina ruwana? Na daina damuwa." Kamal ya yi murmushi "to wallahi ki canja taku don soyayya babu nunawa juna damuwa bata da armashi. It won't even last." Ƙwalla ta goge da ƙasan mayafinta ta harare shi "kai ɗin lasting zaka yi balle soyayyarka?" "Ahhhh, abu na Allah...ki ka san ta inda sauƙi zai zo min? In warke muyi aure. Duk shekara na raka ki labour room ɗin can naku na sama." Ba lokacin wasa bane amma sai da Happiness ya sanyata murmushi sannan su ka fito daga ɗakin. * Alhaji bai yi mamaki ba da bincike ya nuna banda jinin Taj da ya hau babu wani abu da likitan ya iya gani da zai zama silar ciwon kai mai tsanani irin wanda yake fama dashi. Ya duba ido da kunne har ma haƙoransa domin ciwonsu kan jawo ciwon kai amma duk ƙalau suke. Kuma ya ce yana bacci. "To ko stress ɗin biki ne?" Likitan ya tambaya da damuwa. Miƙewa tsaye Alhaji yayi "kada ka damu doctor. Kawai ka rubuta masa pain reliever mu tafi." Idan sihiri ne ba a asibiti za a gani ba. Rubutawar ya yi su ka fito. Taj yana mai ƙara jin mamakin mahaifin nasa. Yadda yake abubuwa kai ka ce babu abin da ya taɓa faruwa a tsakaninsu. Kowa tasowa yayi da ganinsu banda Hamdi. Da farko tana ganin ƙofar ta buɗe ta tashi da sauri. Tana haɗa ido da Alhaji sai ta koma ta zauna ta kama kallon gefe. Kama kanta tayi don kada ya faɗi abin da zai sake damunta. Taj ɗin ma ƙin kallonsa tayi wanda Alhaji ya karanci yadda hakan ya dame shi. Da alama kasancewarsa a wajen ce kawai ta hana shi ƙarasawa gareta. Ita ma kuma dauriya ce da taimakon fushin da tayi tun a hanya ya hanata ko da satar kallonsa. Murmushi Alhaji ya yi ba tare da ya sani ba. Wannan yarinya anyi rigimammiya. Wato ita nan maganarsa ce har yanzu ba ta haƙura ba. 'To ai shikenan. Na san maganinku daga ke har Taj ɗin.' "Abba zo ka kaisu gida sai ka taho da motar Taj ɗin." Zumbur ta miƙe tayi gaba. Taj ya auna yaga idan ya bari ta fita fa akwai matsala a gaba. Kai ya ɗan sunkuyar yaƙi kallon Alhaji da Abba ya ce, "Ina zuwa Alhaji." "Ina za ka je?" Hamdi da ta kusa ƙofa kuma taji maganganun da suke yi sai ta tsaya cak. Kuka kawai take son yi. Wato umarnin kada ya bita aka bashi yanzu kuma. Bata juya ba ta sake ɗaga ƙafa ita ma Alhajin ya tsayar da ita. "Kema ina za ki je a daren nan kike ƙoƙarin fita ke kaɗai?" "Tafiya za mu yi Alhaji. Dare ya raba sosai." Abba Habibu ne ya bashi amsa. "Ai na san daren ya yi shi yasa nace Abba ya kai ku gida kai da wanda ya tuƙo motar." Ba shiri Hamdi ta juyo. Taj ma dai Alhajin yake kallo. "Ku kuma ku wuce mu tafi gida." "Mu su wa?" Taj ya yi tambayar a gaggauce. "Kai da matarka mana. Ko kana tunanin a daren nan zan bari ka tafi gidan Ahmad ka tashe su?" A zahiri kuwa baya son yaje ne ya sake haɗuwa da Salwa ta ƙulla wani abin. Bai ga abin da zai sa ya bar Taj ya kwana nesa da gida ba yau ɗinnan. Furucinsa Halliru mai tuƙo mota ne kaɗai bai bawa mamaki ba tunda bai san komai ba. Fuskokinsu su duka abin dariya don dai ma Alhajin yana gudun raini a gaba da ya dara. Idanun Hamdi ƙara girma suka yi. Na Abbanta kuwa da Taj sun yi micimici kamar ya ce zai yanka wani. Taj baya son saka rai a banza sai cewa ya yi "ban taho da muƙullan gidan ba." "Naku gidan ba da gayyar mata ku ke shigarsa ba?" Alhaji ya ce yana tafiya har ya wuce Hamdi ya fita. Bata iya tafiya ba sai da Taj ya ƙarasa inda take ya riƙo hannunta. Suna zuwa bakin ƙofa ta ƙwace hannun ta fito. Abba Habibu dai ya shiga duhu dole ya nemi ƙarin haske. "Alhaji ina za su je ne?" "Gidana." Ya amsa kai tsaye. Hankalin Hamdi sai yanzu ya yi asalin tashi. Ta dubi Abbanta tana girgiza kai kamar zata cire shi. "Bishir muƙullin motar yana wajenka ko?" Nuna masa muƙullin ya yi shi kuma kai tsaye ya yi gaba ko jiran wani ya yi magana bai tsaya yi ba. Ya sakar musu bomb ya barsu da hayaƙi. "Abba don Allah ba za ni ba" cewar Hamdi harda hawaye. Taj kuwa kai ya girgiza masa cike da murna "Abba ku tafi sai da safe." "A yi haka?" "Abba kana ji fa Alhaji da kansa ya ce in zo gida na kwana ba roƙa nayi ba." Ya kalli Hamdi, kallo na girmamawa "albarkacinki naci. Wallahi albarkacin aurenki ne. Nagode Hamdi." Shi ma Abba sai lokacin ya fahimta sosai. Ya riƙe hannuwan Taj su ka yiwa juna murmushi na farinciki. "In sha Allah daga yau waccan magana sai dai a tarihi kuma. Allah Ya cigaba da toshe dukkan ɓaraka." "Amin Abba. Nagode. Nagode" Ya amsa da murmushi. "Ni fa ba zan..." "Bi mijinki ku tafi Hamdi. Sai da safe." Abba ya katseta da sauri. Yana gama magana yabi bayan su Halliru. Aka barta da Taj. Hannunta ya kamo kada su yiwa Alhaji laifin barinsa jira. Suna zuwa su ka samu ya shiga gaba. Su biyun su ka zauna a baya. Motar tayi tsit. Alhaji ne kaɗai yake jin wani irin farinciki na kasancewa tare da Taj a wannan yanayin. Ribas Bishir ya yi idanun Alhaji su ka sake sauka akan motar Kamal. Da sauri ya ce da Bishir ya tsaya. Bai yi musu magana ba ya fita ya koma cikin asibitin. Shaf ya manta yaga motar lokacin shigarsu. To me yake yi a ciki basu gan shi a reception ba sannan bai neme su ba? Mota kuma tasa ce babu tantama. Yana shiga ciki ya nufi wajen Receptionist ɗin sai ga Kamal da Mubina suna fitowa daga koridon inda Emergency room yake. "Kamal?" Hantar cikin Kamal sai da ta kaɗa da ya tabbatar Alhaji yake gani. Ya yiwa Mubina kallon tuhuma sai tayi saurin girgiza kai. "Baka da lafiya ne?" Alhaji ya tambaye shi. "A'a. Dawo da ita nayi daga wajen dinner." A tsanake Alhaji ya kallesu sannan ya ce "Me ka zauna yi to? Naga motarka tun zuwanmu kusan awa guda da ta wuce." Kamal ya rasa ƙaryar da zai gilla sai Mubina ce ta ƙwato shi saboda yadda taga ya gama ruɗewa. "Emergency case na samu Baba. Sai yanzu na fito." "Allah Ya bada lafiya. Amma duk da haka da shi sai ya tafi gida tunda dare ya yi." Haƙuri Kamal ya bashi. Yana shirin tambayar waye babu lafiya Alhaji ya sake yi masa tambaya. "Me ma ya zaunar da kai? Ko akwai alaƙa a tsakaninku da ban sani ba?" Kaɗan daga aikin Alhaji kenan. Faɗin magana kai tsaye ba tare da ɓoye ɓoye ba. Mubina ji tayi kamar ƙasa ta buɗeta shige ciki. Kamal kuma da yake neman mafaka tuni ya cafke wannan damar ya nuna hakan ne. Tsaf Alhaji ya haɗe rai kuwa. "To ni bana son irin haka? Idan kana neman mace sanar dani ya kamata ka fara yi saboda nayi magana da manyan ta. Amma haka kawai ka ɗauko ƴar mutane ka zauna a wajen aikinta da talatainin dare irin wannan ai bai yi ba." "Ayi haƙuri Alhaji." "Kema da ki ka biyo shi baki kyautawa kanki ba. Na yarda da tarbiyar Kamal a matsayin uba amma ku ƴaƴan zamani ba a ci muki laya. Allah dai ya kiyaye kawai." Ita ma haƙurin ta shiga bayarwa ba ji ba gani. Da dai Kamal yaga tarkonsa ya kama sai ya cigaba a haka. Ya karɓi laifin da bai yi ba ya cigaba da bada haƙuri. Sai da komai ya lafa ya tambayi waye babu lafiya. Da yaji Taj ne ai sai ya ture nasa ciwon ya fita. Mubina ma sallama tayi masa ta koma ciki. "Alhaji mu je mana" ya dawo da ya ankara shi kaɗai ya fita. "Jeka. Likitan da ya duba shi zan tambaya game da wani bayani da ya yi min." Da sauri Kamal ya wuce. Alhaji ya bi shi da kallo har ya fita sannan ya koma reception jiki babu ƙwari. Gabaɗaya Kamal ɗin ya sauya sosai. Tun rashin lafiyar kwanaki da aka ce allergy ne ya lura yaron nasa ba yadda ya saba yake ba. Ya dai haƙura da yawan tambayarsa ya jiki ne da yaga yana harkokinsa na yau da gobe babu fashi. "Doctor ɗinnan da muka gama magana gobe ƙarfe nawa za ta tashi? Akwai patient da nake son ta duba min na manta ban faɗa mata ba." Wani ɗan littafi mutumin ya duba ya ce "yau bata da night (call), sai 3 na yamma kuma za ta shigo goben. Yanzu ma na san alfarma kawai ta yi masa tunda ya saba zuwa amma she is off." "Shi wa kenan?" Alhaji ya ɓoye matsanancin tashin hankalin da ya kama shi. "Wanda ka gansu tare." "To nagode" Wani irin sanyi mai farawa daga cikin ƙashi ne ya dirarwa Alh. Hayatu. Kamal bashi da lafiya kuma yana ɓoye masa. Fargabar da ya dawo mota da ita ce ta hana shi sakar musu fuska yadda ya yi niyya. "Alhaji ko su dawo motata?" Kamal ya tambaye shi bayan ya zauna mazauninsa. Ba tare da ya kalli inda Kamal ɗin yake tsaye da Taj ba ya ce "Tunda cinyesu zanyi ko?" "Tuba nake." Kamal ya faɗi yana dariya "Happy mu haɗu a gidal" Motarsu Alhajin ya koma shi kuma Kamal ya ja tasa shi kaɗai. Yana murna da Alhaji ya hana su biyo shi domin da sun ƙara lokaci a tsaye Taj zai cigaba da yi masa tambayar ƙure. A motar ma duk da ba hira suke ba amma Alhaji sai da ya tambayi Taj ko Kamal ya faɗa masa me yake yi a asibiti cikin dare. Amsar bata sauya daga irin wadda ya bashi ba da kansa ba. Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Kowa ya yi shiru har aka isa gidan. Da su ka isa tsayuwa su ka yi a bakin motar don basu san ina za su nufa ba kuma. Alhaji da ya san jiransa suke yi sai lokacin ya ɗan saki fuska bayan isowar Kamal. Wayar Inna ya kira kuma bai yi mamakin da bata yi bacci ba ta ɗauka. Ya ce mata ta fito akwai baƙuwa. Inna ta taso da hijabinta don dama sallah kawai take yi tana addu'o'i. Da ta buɗe ƙofar sakin baki tayi kafin kuma ta fito waje sosai inda suke ta rungumo Hamdi. "Alhaji lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau. Kawai dai naga bai dace ta koma gida a daren nan ba tunda matar aure ce." "Haka ne" Inna ta gyaɗa kawai cike da mamakin da yaƙi ƙarewa "shi kuma wannan gidan Ahmad za a kai shi ko?" "A'a" Alhaji ya amsa mata da wani irin murmushi a fuskarsa. Haka kawai yake jin son kyautata mata ko don yadda hankalinta ya tashi ɗazu "a gidan nan zai kwana." Wani irin farinciki mara misali ya sake mamaye Taj. Kamal kam rungume shi ya yi yana faɗin "mun gode Alhaji. Allah Ya ƙara girma. Ya ja kwana. Mun gode" Ya dafa kafaɗar Taj ɗin "Happy zo mu je ka kwanta." Sake basu mamaki ya yi da cewa "Kada ku takura, ya kwana a ɗakin ƙasa na ɓangare na." Wai kuma sai ya juya zai shige ciki. Inna har lokacin tana riƙe da hannun Hamdi ta juya ita ma da sauri tana mai danne kukan da take shirin yi. Taj kawai ta kalla taga yadda furucin mahaifinsa na ƙarshe ya kawo wani irin hasken annuri ya shifiɗe masa a fuska. Sai hamdala da take ta karanta daga laɓɓansa. Abin da ake jira kuma ake ganin kamar ba zai yiwu ba ne ya faru a lokacin da ba a zato. "Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min. Ina roƙon Allah Ya kawo maka ɗauki ta inda ba ka zato akan duk masifa ko rashin kwanciyar hankalin da zai tunkaroka. Na gode Yaya Hayatu." Yau ake kira farar rana. Rabon da Zainabu Abu ta kira Alhaji da sunan da ta saba kiransa a matsayinsa na ɗan uwanta ya manta. Yana son ya juyo ya bata amsa daidai da addu'ar da tayi masa amma ga ƴaƴa da suruka a wajen. Don kada ya bada kansa sai ya gyaɗa kai kawai. Hamdi ta ajiye fushinta a gefe domin wannan abu maƙiyi ne kaɗai ba zai taya Taj murna ba. Ita da bata cika son magana ba sai take jin ya kamata ta ƙara nunawa Alhaji cewa mahaifinta ya horar dasu da kyakkyawar tarbiyya. Da wannan tunanin a duƙa har ƙasa a gefen Inna. Muryarta a hankali cikin nutsuwa ta ce, "Allah Ya saka da alkhairi Alhaji. Allah Ya bamu ikon faranta maka fiye da yadda kayi mana. Mun gode." Sai yanzu ya yi magana "babu komai. Ku shige ku kwanta." Inna dama jira take ta sami damar yin kukan farinciki. Da sauri ta wuce ciki. Tana riƙe da hannun Hamdi har ɗakinta. Ƴan kwanan kowa ya kwanta banda mutum biyu Badi'a da Sadiya da su ka san Taj babu lafiya. Basu tashi matan gidan ba su ka zauna jiran su Alhaji. Suna ganinta da Hamdi ta yi musu bayani kafin ma su tambaya. "Aikin babanku ne ya taho da ita daga asibiti wai dare yayi." Badi'a ta ce "to ina Taj ɗin?" Da wata irin murna ta wanda yake cikin zaƙuwar bada labari ta sake cewa "Alhaji ya dawo dashi gida" Sai kuma ta faɗi cikin sujjada tana yiwa Allah kirari. Hanyar fita Sadiya tabi za ta fita ta fesawa ƴan uwanta Inna ta dakatar da ita. Ta nuna mata dare yayi ga gajiyar da aka kwaso. Da ƙyar Sadiya ta haɗiye zancen ta haƙura sai asuba. "Hamdi akwai ruwa a heater. Ki ɗan watsa ruwa don jikinki yayi daɗi sai ki kwanta." Babu musu ta tashi za ta shiga banɗakin da Inna ta nuna mata. Jikinta tayi tsamin gajiya sosai. Innar ta bata wata doguwar riga da ƴar hula ta shige dasu. Kafin baɗakin akwai wani ɗan wuri da aka saka shoe rack da wani ɗan tabur inda aka ajiye mai da turaren jiki irin oils ɗinnan na Scentmania irin nata. Nan ne wurin shafa mai sannan mutum ya shiga ɗaki ya ƙarasa shafe shafensa. Wanka tayi ta ɗauro alwala. Tana fitowa ta samu su Sadiya sun kwanta. Sai Inna dake sallah. Dama tana kunyar yadda za ta kwanta ɗaki ɗaya da mahaifiyar Taj. Da taga tana sallah kawai sai ta zauna. Ita kuma Inna da ta idar ta tambayeta me ya hanata kwanciya. "Nima sallar zan yi Inna." Wani murmushin farinciki da Inna tayi ya nuna tsantsar jindaɗinta. Ta bata hijab su ka yi raka'a shida sannan Hamdi ta soma hamma. Sai tayi kamar ta idar. Ai kuwa akan abin sallar Hamdi tayi bacci. Wannan qiyamul laili da tayi tare da Inna kuwa ta saya mata wajen da babu wata mace da za ta taɓa auren Taj ta mallaki wannan gurbi. Kaɗan daga sirrin Tahajjud! A ɓangaren Alhaji kuma Kamal, Bishir da Abba da ya dawo daga baya duk ɗaki guda su ka kwana da Taj. Alhaji yana jiyo hayaniyar murnarsu kamar ba dare ba. Sai ya tuna ƙuruciyarsu da kuma samartakarsu da ya katse na tsayin shekaru. Rashin jindaɗin abin da yayi gami da tunanin wane ciwo ke damun Kamal sai su ka hana shi baccin kirki. Wuraren huɗu da rabi yaji alamun an buɗe ƙofar ɓangaren nasa. Dama baccin babu nauyi. Da sauri ya leƙa domin ya gani ko jikin Taj ne ya tashi. Fitowarsa tayi daidai da fitar Kamal. Nan jikinsa ya sake mutuwa. Ya koma bakin gado ya zauna. Baccin da bai koma ba kenan sai kawai ya ta da nafila. Yana ji aka soma kiraye kirayen assalatu. A zuciyarsa ya ƙudurta sauka ya tashi su Taj nan da minti talatin sai su yi alwala su tafi masallaci. Ko minti goma ba ayi ba yaji ana buɗe gate a hankali. Ya sake tashi ya leƙa sai ya hango motar Kamal ce ta fita. Bai yi wata wata ba ya sauka ƙasa da muƙullin wata sabuwar motarsa. Da kansa ya ja hankalinsa a matuƙar tashe. Rabonsa da tuƙi ya ma manta. Cikin sa'a da yabi hanyar asibitin sai ya hangi motar Kamal tunda titi fayau yake dai motoci jifa jifa. Haka ya bishi har asibitin ba tare da ya sani ba. Yana parking bayan shigar Kamal ciki sai ga Mubina. Da sauri ta shiga asibitin tana magana a waya. Bayanta Alh. Hayatu yabi da sauri. Tana shiga cikin asibitin tayi hanyar emergency inda ya ga fitowarsu ɗazu ya kirata da kakkausar murya. "Dr. Mubina" Cikinta ya ba da wani mahaukacin sauti domin ta riga ta gane muryarsa. Ta juyo kamar mara laka a tsorace. "Kai ni wajen yarona." Gaba tayi ya bita a baya har ɗakin. Ta buɗe da sallama. Nos ɗin da ya taya ta aiki da daddare yana tsaye akan Kamal dake kwance babu riga. Juyawar nan da Kamal ya yi da yaji motsinta sai idanuwansa su ka sauka a cikin na Alh. Hayatu Sule Maitakalmi. RAYUWA DA GIƁI 30 Batul Mamman💖 Kuna neman reliable data ba cuta va cutarwa? Ku saya a baku na kowane layi cikin aminci da rahusa? Look no further. Contact MKdataservices for your data, airtime, tv subscription and nepa bills. 08038258489 https://www.mkdatasarvices.com.ng Sayen nagari....mayar da data gida! ~~~~~ Ya yunƙura zai tashi ba shiri don ya san yau ɗin abin da zai fuskanta sai ya gwammace kiɗa da karatu. Alhaji ya yi masa alama da ya koma. Ya sake yunƙurawa dai sai Alhajin ya kalle shi yana mai buɗe masa idanu. Dolensa ya koma ya tada kai da filo. Mubina dake tsaye da tasar allura tayi wiƙi-wiƙi da idanu ya duba "Ƙarasa ki duba min shi mana." Tayi sauri ta isa gaban gadon. Ido Kamal ya rufe don allurar akwai zafi. Alhaji yaji wani irin tausayinsa ya tsirga masa. Kujerar gaban gadon yaje ya zauna. Ya kama hannun Kamal na dama ya riƙe. Irin riƙon ƙarfafa gwiwa da rarrashi. Dama yaya lafiyar kura? Duk wani emotion na rauni da Kamal yake adanawa tun farkon rashin lafiyar a lokaci guda ya fashe. Ya ƙara ƙarfin riƙon hannun mahaifinsa yana kuka mara sauti. Tsananin tausayinsa yasa Mubina taya shi. Nos ɗin ma kawar da kai gefe yayi. Shi kuwa Alhaji dakewa ya yi duk irin yadda hankalinsa ya tashi. "Kuka a gaban mace Kamal kamar wani mace? Ni fa ka san ba shiri nake da rago ba." Hawayen ƙaruwa su ka yi. Ya dawo da kansa saitin Alhaji kawai ya cigaba da abinsa. Alhaji yayi murmushi "matana basu taɓa ganin hawayena ba duk shekarun nan. Kai kuwa ka saka mace a gaba kana abin kunya. Ko batun alaƙar taku shi ma ƙarya ku ka yi min?" Girgiza kai Kamal ya yi. Alhaji ya dubi Mubina da allura a hannu tana kallon ƙasa. Allurar ya ce tayi tunda da alama akan lokaci ake buƙatarta. Ba don haka ba ya san Kamal ba zai fito da asuba ba. Bayan anyi allurar wadda yadda yaga an soka ta ciki ya ƙara kiɗima shi sai ya tambayi Nos ɗinnan abin sallah. Gari har ya soma haske basu yi asuba ba. Daga kan gadon Kamal ya bi shi sallar. Bayan sun idar suna zaune su biyu, Alhaji yana zaune akan abin sallah ya tambaye shi game da ciwon. "Lalurar dake damunka a hanyar fasiƙanci ka same ta ne?" "A'a Alhaji" ita ce amsarsa. Muryar Alhaji ta karye domin a tsorace yake Allah Ya sani. Kamar kada ya idar da sallah ya yi tambayar tun farko. "To me yasa? Mene ne dalilin ɓoyewar?" "Saboda maganin ba mai samuwa bane Alhaji. Ƙoda nake buƙata kuma ..." Yana son yin faɗa amma ya san cewa abin da zai sa Kamal yi masa ɓoyon ciwo ba ƙaramin abu bane. "Gani, ga ƴan uwanka mutum ashirin da bakwai amma ka kasa faɗa? Bayan na san karamcin da Allah Ya yi min a gidana. Yau ko babu ni babu mahaifiyarka ina da yaƙinin cewa sauran uwayenka za su tsaya maka ka samu a jikin ƴan uwanka ko da kuwa ƴaƴan cikinsu ne." Nan dai Kamal ya yi masa bayani akan matsalar da aka samu. Bai gamsu ba sai da Mubina tayi masa fashin baƙi. Amma duk da haka zuciyarsa fafur taƙi amincewa. Ana bayanin yana jin zufa a duka jikinsa. Gabansa kuwa faɗuwa kawai yake yi. Yayi salati yafi a ƙirga. Kamal ya yi mamaki domin faɗa yasa rai zai yi masa. "Alhaji baka yi min faɗa ba." "Wane irin faɗa kuma Kamal? Ta yaya ma za ka yi tunanin zan maka faɗa? Halin da zuciyarka take ciki na firgicin ciwon ma da ina da iko wallahi zan raba ka dashi. Da ace akwai yadda zanyi cikin ku babu mai yin atishawar da zai ji a jikinsa. Baka ganin dalilin ciwo na dawo da ɗan uwanka? Ta yaya kai kuma zan yi fushi da kai?" "Kayi haƙuri." Tare su ka fito bayan allurar ta saki Kamal. Alhaji ya dage sai dai ya bishi a motarsa. Zai turo a ɗaukar masa tasa. "Kawo muƙullin to.." ya miƙa hannu zai karɓa. Alhaji ya hana. "Da ƴaƴana da jikoki kake tunanin zan yarda kana rabin mutum ka ja ni?" Suka yi dariya sannan su ka shiga Alhaji ya ja su. Jifa jifa su kalli juna su yi murmushi don su kwantarwa juna hankali. "Alhaji don Allah maganar nan.." Kamal ya fara roƙonsa da su ka isa gida. "Shiga ciki Kamaluddeen" Alhaji ya katse magiyar da ya so yi masa akan ya yi shiru da maganar. Bayan Kamal ɗin yabi ya same shi yana yiwa su Taj ƙaryar abin da ya fitar da shi da asuba. Murmushi yayi musu bayan ya amsa gaisuwarsu. Su huɗu yau su ka kwana a ɗaki guda kamar wasu yara ƙanana. "Yaya kan naka?" Abba ya wani turo Taj gaba "taɓa shi kaji Alhaji. Jikin da sauƙi. Ai jiya bamu yi bacci ba saboda yi maka gadinsa." "Nagode Sulaiman. Yau ni ne abin tsokana ko? Ko da yake girmanka ne baban Hayatu." Aka saka dariya sannan ya haye sama ya kira Ahmad. Taj ne kawai ba ya sakin jiki ya yi dariyar saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa gaskata wai shi ne a gida. *** Rabon da Abba Habibu yaga rigimar Yaya irin wadda ya gani tun bayan dawowarsa a daren jiya ya manta. Ta nuna masa rashin jindaɗinta sosai. Da mitar ta kwana ta tashi. "Amma dai kin san ba dawa taje ta kwana ba." "To mene ne maraba? Gidan surukan da bata riga ta tare ba saboda Allah. Salon a sami abin goranta mata nan gaba." Kwanciya Abba ya gyara don bacci sam bai ishe shi ba. Ya yi dare a waje sannan rikici ya hanasu bacci sosai. Yaya ta haɗe rai "kwanciya ma za ka yi?" "Da fa? So ki ke muyi ta ɗaga murya a sami abin goranta mata da yawa?" Saukowa tayi don kanta da taji me yace "amma ka san damuwata. Ina gudun kada ace bamu saya mata mutumci ba." "Akwai mutumcin da ya wuce auren da aka ɗaura mata? Kuma na nanata miki cewa ba Taj bane ya ce ta zo su tafi. Yaya Hayatu ne ya ce ta bi mijinta." "Zancen nawa dai ya fito. Ya ce ta bi shi saboda yana ganin ya isa. Ni bana son wani ya rainaka ne." Ta faɗi da ƙanƙanuwar murya. "Nayi zaton kin yi min sanin hagu da dama ashe ba haka bane? Wallahi kuɗi ko muƙami ba zai sa na wulaƙanta ƴata ba. An riga an ɗaura aure. Bai kamata na nuna mata bijerewa umarnin mahaifin mijinta garesu daidai bane. Ko har kin manta matsayin da muka haɗu da Taj tsakaninsa da babansa?" Jikinta sai ya sake yin la'asar. Ta kama bakinta bayan ta bashi haƙuri. Bawan Allah dama ba riƙo gare shi ba. Nan da nan ya kashe wancan zancen ya sako maganar kai amarya tunda ya san dole za a dawo da Hamdi daga gidan Alh. Hayatu. Sai da su ka gama tsara komai ya koma ya kwanta ita kuma ta fito falo. A firgice ta sami Zee tana kai kawo. Zee ɗin na ganinta tayi maza ta rufe ƙofar falon kada kowa ya ji. "Yaya kada ki tada hankali idan ki ka ji me zan faɗa." "Allah Yasa dai lafiya Zee." "Jiya Hamdi bata dawo gidan nan ba." Da gangan Yaya ta ce "kai haba?" Zee ta sake kwantar da murya "Wallahi kuwa. Nayi ta kiran wayarta bata ɗauka. Sai da asuba tayi min message wai tana gidan su Ya Taj." "Indai haka ne ai babu damuwa." Zee kasa ɓoye mamakinta tayi. Da tsammanin faɗa ta zo sai ta samu ba haka ba. Yaya ta gama tsokanarta sannan ta taimaka tayi mata bayanin me yake faruwa. Su ka gama dariya da tunanin me za su ce da mutanen da suka kwana idan aka fara cigiyar amarya. *** Hajiya, Umma da Mama sai da safe Inna ta sanar dasu duka abubuwan da su ka faru a gidan da daddare, har ma da baƙuwarsu. Murna a wurinsu ba a cewa komai. Dawowar Taj abin farinciki ne da shi kaɗai ya cancanci ayi ƙwarya ƙwaryar walima saboda farinciki. "Amma banda abin Alhaji me zai sa ya taho da Hamdiyya bayan tare da mahaifinta su ke?" Umma ta faɗi bayan sun ɗan nutsu da murnar. "Kema dai Jamila kamar baki san halin mijin naki ba. Ƙarshenta gani ya yi kamar Taj ya damu shi ne zai taho masa da ita don ya kwantar masa da hankali. Son ƴaƴa kuma a wajen mutumin nan ai ba a magana." In ji Mama. Wata uwar guɗa su ka ji daga falo. Dama suna ɗakin Mama ne. Inna ta sallami kowa ta bar Hamdi saboda baccin da ya sake ɗauketa bayan tayi sallar asuba. Fitowa su ka yi iyaye, ƴaƴa da jikoki. Ashe Amma ce tayi fitowar sassafe ko wanka bata yi ba. Hijabi kawai ta ɗora akan rigar baccinta ta fito. Tana ganin matan gidan, musamman Inna sai ta kama kuka. "In da na san aure ne zai dawo da Taj gida ai da ko kwana guda ba zai yi a matsayin ɗan da uba ya kora ba. Kai, Allah mun gode maKa." Waɗanda basu sani ba duk sun ji a lokacin. Murna da farinciki kamar me. A wajen Taj ta sami labari tun daren. Nan falon nasu su ka kira Kamal ya shigo da Taj. Sai abu ya koma kamar ranar kowa ya ƙara ganinsa tun tafiyarsa ta farko. Waɗanda basu kwana a gidan ba ma duk an kira su. Kafin bakwai sun cika gidan. Taj murmushi kawai yake yi. Yana cikin farinciki fiye da kowa. Ciwon kan ma ya tafi gabaɗaya ya tafi. Zuciyarsa kamar yau aka dasa masa ita. Babu damuwar komai a ciki. A gaban ƙafafun Amma ya zauna akan kafet tare da ƴan uwansa. Baka jin komai sai hamdala da ake yawaita yi. "Kai ku duba min Hamdiyya ko ta tashi." Hajiya ce tayi maganar tana mai duban ƙofar ɗakin Inna. A take mutum uku ƴan mata da wasu biyar cikin jikoki su ka miƙe a guje kowacce tana cewa ita za ta duba. "Mijinta na zaune wa ya aike ku?" Mama tayi musu tsawa. Sai kuma ta kalli Taj "tashi kaje mana." "Ina?" Ya tambaya don bai san kan gidan ba yanzu. "Tana ɗakin Inna" cewar Firdaus. Tashi ya yi kafin yana waige "wanne ne?" Yayinda wasu ke nuna masa, masu hankali wannan tambayar fami tayi musu. Inna mai yawan kawaici sai gata ta duƙar da kai tana share hawaye. Ace ɗan halak bai san ɗakin mahaifiyarsa ba a gidan ubansa! Tabbas wannan abu akwai ciwo. Yana ganin halin da su ka shiga ya yi saurin barin wajen domin baya son ayi ɗa kwance uwa kwance. Murnar kowa za ta koma kuka. Abin da ba zai so ba. Tafiyarsa kuwa tsokanar ƴan uwansa ta janyo masa. Aka yi ta masa dariyar shaƙiyanci. Hakan sai ya hana koke koken da iyayensu su ka fara. * Hamdi ta fi minti goma sha biyar tana son fitowa amma tana kunyar mutan gidan. Na farko bata san lokacin da kowa ya fita ba saboda bacci.....'bacci a đakin uwar miji don abin kunya' shi ne abin da ta fara faɗawa kanta da ta farka. A saman kayanta na jiya kuma taga an ajiye sabuwar doguwar riga an cireta daga leda amma da tag. Da ta ɗaga wani irin ƙamshi ne mai daɗaɗa ruhi yake tashi a jikinta. Babu makawa turara ta aka yi. Ga wata ƙaramar ledar an saka sabon brush. Ta san ita aka ajiyewa. Banɗaki ta shiga tayi wanka a gurguje ta fito. Bata son kowa ya shigo ya ganta. Musamman Inna. Gaban dressing mirror ta zo ta tsaya ta shafa man da Innar ta nuna mata jiya. Daga nan bata sake taɓa komai ba ta saka rigarta mai kyau ta yafa ƙaramin mayafin ta fita falon ɗakin. Nan ma babu kowa shi ne ta dinga zuwa ƙofar fita tana dawowa. Buɗe ƙofar taji anyi tayi saurin gyara zama a zatonta Inna ce. Sallamar da ya yi ce ta sake tada mata hankali. Idan wani ya shigo ya gan su a ɗakin fa? Idan Inna.... "Baki amsa min sallama ba kin tsaya kina yaba Salman Khan daga sama har ƙasa." Taj ya faɗa yana zama a kan kujerar da take. Da sauri ta tashi tsaye tana kallon ƙofa ta ce "Ni ba kai nake kallo ba" da ƴar tsiwarta saboda ba wai ta manta abin da ya yi bane jiya. "As if..." sai kuma ya koma kallon falon yana inhaling ƙamshinsa kafin ya miƙe tsaye "Wanne ne ɗakin baccin Inna?" Da hannu Hamdi ta nuna masa. Yadda ya dinga tafiya ne ya taɓa mata zuciya. Ta bi bayansa har ciki. Nan kam har lumshe idanu ya dinga yi saboda yadda ƙamshin ɗakin yake nutsar masa da zuciya. Irin ƙamshin da ya dace da Innarsa. Mai sanyi, daɗi da kuma kama waje ya zauna a ran wanda ya shaƙe shi. Juyawa tayi za ta fita ta bashi wuri sai kawai taji ya janyota ya rungume ta baya. Duƙar da kansa ya yi daidai kunnenta. Wani nau'in ƙamshin ya shaƙa mai daɗi. A ransa ya ƙudurta neman sunan mai sayarwa a wajen Inna don ba za a bar matarsa da gidansa a baya ba. " Yau ma arziƙinki na ci aka ce na shigo ɗakin Inna kamar yadda Alhaji ya barni na shigo gidan nan domin ki. I owe yoy big time Hamdi. Thank you." Tausayinsa taji kamar daren jiya ta ce "Na taya ka murna Happy." "Kin dai taya mu." Ya juyo da ita suna fuskantar juna. "A'a fa. Ni dama tun farkon zuwana Alhaji bai koreni ba." "Sai ni uban ƴan taurin kai ko?" "Ni dai ban faɗa ba" tayi murmushi. "Kin ayyana a ranki na sani." Ya kama hannuwanta yana murmushi. "Ka dai tsargu kawai saboda baka da gaskiya" Janta ya yi wajen gadon "Zo mu ɗana gadon Inna." "Ni kaza?" Hamdi ta ce a firgice "kada ka janyo min abin faɗa har jikoki mana." Zillewa tayi ta fita daga ɗakin ya bita falo kafin ta fita. Haƙuri ya bata akan maganganum Alhaji ga Abba jiya. "Abin da nayi jiya har yasa ki fushi was for you Hamdi. Na san baki ji daɗi ba amma ina so muyi clearing issue ɗin kafin anjima." Da ya san amsar da za ta fito daga bakinta da bai tayar da wannan maganar ba. Kallonsa tayi. Kallo mai tarin ma'anoni. A wajenta kuwa da manufa ɗaya tayi shi...(na san abin da nake yi). "Uba uba ne Ya Taj. Nagode da baka barni na yiwa Alhaji rashin kunya ba da yanzu ina nadama don ba tarbiyar gidanmu bace. Amma ina so ka sani cewa WALLAHI ba zan taɓa sakin jiki a gidanka ba sai Alhaji ya ɗauki Abbana da darajar da Allah Ya bashi." "Me kike nufi?" Taj ya tambayeta da yaji komai nasa ya fara kwancewa. "Aurena kayi ba sadaka aka baka ba. Allah Ya sani ba zan iya ɗauke kai ina gani ana yiwa mutum mafi girman daraja a wurina irin haka ba. Sai in ga kamar nima na yarda bai kai a girmama shi ba." "Amma ni wane irin girma ne bana bashi?" Abin da bata son farawa don kar ta kasa dainawa ne ya zubo. Hawaye. Hankalin Taj ya sake tashi. Ya matso ta matsa baya. "Ba da kai nake ba. Ba kuma faɗa nake da Alhaji ba. Amma kai ma ka san irin matsayin da ya bashi daga maganarsa ta jiya. Kana gani ko zuwana nan ba shawartarsa ya yi ba duk da dai an ɗaura aure. Ko don ya taɓa yin daudanci ne?" A lokacin ya gane Hamdi bata da labarin ainihin abin da yake tsakanin iyayensu maza. Bata san sanayyarsu ta wuce ta zaman unguwa ɗaya ba. Akwai sauran rina a kaba kenan. Amma da ta buɗe ƙofa ce ta kawo ƙarshen zancen. Sam bata nuna musu taji maganganunsu na baya bayan nan kuma ta fahimci inda suka dosa ba. Faɗan hana Hamdin fitowa tayi masa. "Abinci za ta ci a mayar da ita gida." *** Wayar Alhaji ce ta tayar da Ahmad daga baccin da ya koma. Kamar yadda dalilai daban daban su ka hana yawancin mutan gidansu bacci, shi ma haka Salwa tayi sanadin wargaza nasa zaman lafiyar da ta gayyato Anti Zabba'u gidansa. Ana kiran assalatu da ya tafi masallaci su ka tattara za su bar gidan ko tsinke basu gyara ba daga ɓarna da almubazzarancin da su ka yi da daddare. Suka taɓa ƙofa su ka ji a garƙame. Ya sanya kwaɗo ta waje da zai fita. Anti Zabba'u ta dinga ruwan ashariya tana cewa tafi ƙarfin Ahmad ya wulaƙanta ta. "Mu gyara gidan nan kawai kafin ya dawo. Ni bana son rigima." Wata a cikin ƴan matan ta ce. Rai a ɓace Anti Zabba'u ta ce "An faɗa miki saboda shara ya rufemu? Nuna isa ne kawai da cin mutumci irin na uwarsa." "Duk da haka gara mu gyara. Zan fi son mu fita salin alin kafin ya fahimci halin da waccan mara kunyar take ciki." Da wannan maganar su ka duƙufa. Gyaran dai sai a hankali amma dai yafi babu. Duk abin da su ke yi kuwa Anti Zahra tana jinsu tayi zamanta a ɗaki. Mami ma taji komai tana cike da takaicin ba za ta iya ɗaukar mataki ba. Da ya dawo don kansa ya ce su bar aikin saboda yadda su ka tasarma damalmala gidan. Ruwan mopping wannan klin aka zuba masa kuma ba a bari ya narke ba aka matse mop ɗin sama sama aka soma yaɓawa a ƙasa. "Ga gidanka nan za mu fita amma wallahi Ahmad bashi kaci. Wannan wulaƙancin sai kayi nadamarsa." "Boka ne fa ki ke taƙama dashi. Ni kuma da wanda ya busawa bokayen rai na dogara. Ki ajiye makaman kawai ayi zumunci Fisabilillahi." Ƙwafa tayi. Ranta yana tafarfasa. Mutumin da ta bawa kuɗinta kuma aiki bai ci sai ya yi nadama shi ma. Sun zo fita Ahmad ya ce "ina Salwa?" Kamar jira suke kuwa yana magana su ka fice gabaɗaya a gurguje. Bai tsaya tambayarsu ko lafiya ba ya shiga ɗakin ya ganta a zaune a kan kafet da kumburarriyar fuska tana kuka. "Tunda bugun fanke kaɗai su ka yi miki ki taso ki gyara gidan nan yanzu yanzu." "Yaya baka ganin fuskata ne?" Ta sauke mayafinta yadda zai gani da kyau. "Allah Ya ƙara. Maza ki fito ki gyara gidan. Amma ki fara duba ko Mami tana buƙatar wani abu." Kwanciyarsa kenan Alhaji ya kira. Dama ya tsorata saboda yayi wuri mutum ya amsa waya. Hankalinsa sai ya nemi barinsa bayan ya faɗa masa me Salwa tayi da kuma babban abin wato ciwon Kamal. Muryarsa kuma rawa take yi sosai. "Ban faɗawa kowa ba sai kai. Ina buƙatar ka zo mu yi shawara Ahmad. Zan iya rasa Kamal a kowacce daƙiƙa." "Kayi haƙuri. In sha Allahu zamu sami mafita. Gani nan zuwa." "Ka taho da Salwa." RAYUWA DA GIƁI 31 BATUL MAMMAN💖 YA HAKIMU gwanin Sarkin *** "Salwa kuma Alhaji? Wani abu tayi?" Ahmad ya yi tambayar ne saboda a tunaninsa ciwon Kamal kaɗai ya isa ya gigita Alhaji. Me zai sa ya tuna da Salwa har ya nemi a taho da ita a lokaci mai mahimmanci irin wannan? Gwiwa a sage ya tambaye shi "Laifi tayi ko?" "Kai dai ka taho min da ita." Yana bashi wannan amsar ya gane ko ma mene ne ba abin wasa bane tunda lalura mai girma kamar ciwon ƙodar Kamal bai hana shi nemanta ba. A kitchen ya same ta da himilin kwanuka kamar a gidan ake taron biki. Ko tausayi bata bashi ba don taurin kai da kafiya gami da son zuciyarta ne ya jawo mata. Abu guda ne dai. Ya sanyawa ransa sai ya bi kadin dukan da aka yi mata a cikin gidansa. Su Habitti ba a ci bulus ba. Muƙullin mota ya ɗauka ya ce da Zahra kiransa ake yi a gida game da bikin Taj ya fice. Da ya kira Salwa su tafi ba ƙaramin rawar jiki ta dinga yi ba. Bata san ina za su je ba amma hankalinta duk ya tashi. Tayi zaton ya canja shawara ne zai kai ta tasha ta koma gida. Ta dinga bashi haƙuri da magiya. Bata san damuwarsa ta ninka duk wani abu da ya shafeta ba. Ciwon Kamal ya ɗaga masa hankali sosai. Haƙurin da take bayarwa kamar ba shigarsa yake ba. Shi ne ta koma barazana "Yaya Ahmad kada ka ɓata kuɗinka. Ba zan tafi ba domin na tabbata Taj zai zo gareni da ƙafafunsa. Ko mun je Bauchi zan shigo wata motar na dawo." Ko ci kanki bai ce mata ba. Bashi da wannan lokacin. Ita kuwa bata sam ta shiga one chance ba sai da ta gane hanyar ina su ke bi. Ta zaro idanu da su ka ƙanƙance cikin kumburarriyar fuskarta. Ta kama ƙofa a tsorace tana kokawar buɗewa a titi. "Me za ka kaini ayi min? Yaya Ahmad buɗe min na fita." A haukace take dukan gilas tana neman yi masa ɓarna. Ya juyo ransa yana suya ya daka matsa tsawar da ta gigita ta. Saboda tsorata da tayi a lokacin da za a tambayeta sunanta da wuya ta faɗa farat ɗaya. "Salwa!!!" Laƙwas tayi a kan kujera har su ka isa. Su ka shiga falon tare ya sami gidan a cike fam. Zuciyarsa a take ta faɗo ƙasa daga ƙirjinsa saboda mummunan tunanin da ya zo masa. Allah Ya taimake shi su na ganinsa aka soma bashi labarin abin farincikin da aka wayi gari dashi a gidan. Idanunsa su ka sauka akan Kamal zaune a tsakiya. Wata irin ajiyar zuciya yayi mai ƙarfi sannan ya sami damar sakin ransa ya shiga cikinsu. Ko gaisawa basu gama yi ba Alhaji ya buɗe ƙofar ɓangarensa ya kira shi. "Ahmad kai fa nake jira." Da saurinsa ya tashi har yana tuntuɓe. Kamal ya sha jinin jikinsa. Ƴar hira da dauriyar da yake yi ya kasa jurewa. Ɗakinsa zai koma kawai kafin Alhaji ya neme shi. A hanyar fita ya yi kiciɓus da Salwa. Da yake bashi da masaniyar me yake faruwa sai bai canja mata ba. "Salwa? Ashe tare kuke ki ka tsaya a nan?" Ya kalli fuskarta "me ya same ki haka a fuska?" Yuuuu idanu su ka dawo kanta. Jiki a mace kamar magen da aka tsamo daga lamba two ta ƙarasa ciki tana raɓe raɓe. Ƴaƴan gidan dai babu sauyin fuska amma iyayensu ko kallonta basu yi. "Zamewa nayi." "Allah Ya sauwake" ya ce ya fita. Ita kuma ta ƙaraso aka gama yi mata sannu sannan ta matsa gaishe da su Inna. "Hajiya ina kwana?" Ta durƙusa a gabanta. "Lafiya" ita ce taƙaitaciyar amsar da ta samu ba tare da sakin fuska ba. A ranta tayi tsaki. Ai dai ba ita ce ta haifi Taj ba take wani sha mata kunu. Ko ita Innar bata fi ƙarfin a kai sunanta gaban malam ya ƙulle mata baki ba. Nan gaba ma wajen malamin Ummi za ta je domin da alama zai fi na Mami iya aiki. Muskutawa tayi ta ƙara matsowa ciki. "Mama..." Mama bata jira ta gama gaisuwar ba ta tashi abinta tana duban Amma. "Uhmmm, Jamila duba ki ga me Taj da Hamdiyya suke yi a ɗakin nan har yanzu shiru." Jin furucinta yasa gaban Salwa ya faɗi, ya sake faɗuwa. Baki ya kama rawa kamar mazari ya ji kiɗa. Dama ga fuska a kumbure. Sai tayi wani irin yanayi mara kyau duk suna gani. Umma tayi dariya "kema dai Mama da rigima kike. Ba kya ko tsoron me za a buɗe a tarar? Sabon aure basa son sa ido fa. In ba haka ba kuwa sai aji kunya." Inna tashi tayi zumbur ta bar musu wajen. Su ka dinga dariya banda Amma da bata gane manufarsu ba. "Takwara me ki ka mayar min da ɗa ne? Ki ka sani ko bacci ya samu tana yi?" "Sai ya zauna korar mata sauro ko?" In ji Hajiya. Umma da Mama sai shewa harda tafawa. Ƴaƴan na gani amma su ma basu san me ake yi ba. Ita dai Amma tashi tayi ta barsu suna kallon suman zaunen Salwa a fakaice. Ta zubawa ƙofar ɗakin Inna da Amma ta nufa ido tana jiran ganin da gaske Hamdi za ta fito daga ciki ko yaya? In tana ciki me ya kawota gidan da sassafe? Ko dai ita ma murnar ta zo taya shi? Ai kuwa da an kira iyayenta marasa kamun kai. Me zai hana su jira ido na ganin ido? Don baƙin naci an biyo shi har gida a lokaci irin wannan da yake buƙatar ahalinsa. * Duk da ba komai Amma ta ji ba amma iya maganganun da su ka shiga kunnuwanta sun fahimtar da ita me yake faruwa. Akwai wani abu da Alhaji ya yiwa mahaifin Hamdi. Jikinta kuwa ya yi sanyi sai dai wayewa da sanin yau da gobe yasa ta je musu da fuskar rashin sani. Bayan ta gama ɗorawa Taj laifin hana Hamdi zuwa cin abinci, sai ta shiga ta riƙo hannunta. "Sai da na shigo nake jin ashe jiya rigimar babanku ta haɗa dake." Hamdi ta sunkuyar da kai kawai tana murmushi "Zo ki ci abinci in kai ki gida in kuma bada haƙuri kada ace ba za a bamu ke anjima ba." Sake yin ƙasa Hamdi tayi da kanta cike da kunya. Balle da Taj ya ce shi zai kai ta. Ya ce da Amma "Akwai maganar da za mu yi da ita." "Fita idona Taj." Ta harare shi. "Please mana Ammata." "Don ƙaniyarka ka san irin bikin da ake ta yiwa Hamdi a falo?" "Ni kuma?" Hamdi ta fito da idanu. Amma kuwa sai dariya ta sami damar tsokanarta domin a yanayin fuskokinsu ba za ta so su fita ba. Gidan akwai manya da masu experience da yawa. Yanzun nan za a harbo jirginsu a gane da matsala. "Harda masu cewa ko a biyo ku da abincin nan idan ya so sai muje mu karɓo miki kayanki a gida." "Ya Rabbi, to ya zan yi? Ko kada na fita?" Kai da ganin idanunta da jin muryarta ka san hankalinta ya nausa da nisa. Kunya, tsoro da jin nauyi sun cika mata ciki. Da Taj ya dubeta sai da yaji kamar ya kamota a gaban Amma ya ɓoyeta cikin jikinsa. She looked so cute and innocent kamar ba bakinta bane ya gama zaro masa zantuka ɗazu. "Wasa take yi miki. Ko Amma?" Ya rage murya shi ma ɗin ba son jin wata magana babba yake yi a bakin ƴan gidan nasu ba. Dariya Amma tayi musu. Tana yi musu fatan alkhairi a zamansu. Sun dace sosai da juna. Sweet young Hamdiyya and Charming Happy Taj. Za ta cigaba da sanya musu ido a fakaice ta gani ko za su shirya ba tare da tsoma bakin manya ba tunda ta kula basa so a sani. Idan basu daidaita ba sai ta shiga tsakani kafin ƙaramar magana ta zama babba. Hamdi ce ƙarshen fitowa daga ɗakin bayan Amma da Taj. Salwa ta kasa ɓoye baƙinciki da kishinta a fili. Wata irin zabura ma tayi daga zaune. Numfashinta ya nemi yankewa. A zatonta turaren jiya sake janyo ɓaraka zai yi tsakaninsu. Me Hamdi take a gidan? Wata zuciyar ta kwaɓeta da sauri. Ko dai har an sami matsalar? Maybe shi ne aka turo su gida sulhu. Munafukar dariya tayi a zuci. Ta miƙe tsaye domin ta nunawa kowa matsayinta a wajen Taj. Kashe murya tayi tana kwarkwasa. "Ya Taj" Ai fa ta zo gidan yawa. Idanu sun fi goma a kanta. Hamdi wani malolon abu taji ya mata karan tsaye a wuya. Faɗi take tana nanatawa In sha Allahu ba za ta sake kiransa da Ya Taj ba. Sunan ko daɗi babu ashe, bata sani ba sai yau. Taj kuwa Hamdi kawai ya kalla tayi kamar bata jinsu. Murmushi ma take yi abinta da ƴan uwansa suke ta nuna mamakinsu akan kwanan da tayi basu sani ba. Aka dinga yiwa ƴan kwanan ɗakin Inna surutu. Su ka ce ita ta sanya su yin shiru saboda kada su tashi Hamdin da hayaniyarsu. Shi da ya san akan tsini yake ba zai yi kuskuren sake ɓata mata rai ba. Kawar da kansa ya yi kamar bai ji ba. Yana gudun me zai faru idan ya amsa. Ta sake shaƙa har wuya. Abinci ƴan uwansa su ka kawo wa Hamsi shi ne ya samu ya fita wajen Kamal. Amma ta karanci duk motsinsu. Me yake faruwa ne wanda bata sani ba? Zama bai ganta ba. Ɗakin Mama ta shige inda Inna ta shiga ta zauna jin abubuwan da bata san da su ba. Mamaki mabayyani ta nuna akan wannan sabon al'amari. "Ashe yarinyar nan bata da wayo ban sani ba? Ana soyayya dole ne?" "Gabaɗaya ta ɓata rawarta da tsalle. Halin da uwarta ta so nuna mana a gidan nan shi ne ita ma take son gwadawa." Umma kallon Mama tayi da mamaki "kada ki ce min asiri ne ya koreta, don na tabbata ko ita ce autar mata akan ƴan biye biye tsaf Alhaji zai nuna mata ƙofar gida." Hajiya ta murmusa "ai har yau bai san mun san ainihin me ya dinga faruwa ba. Bayan wani asirin ma a gabanmu take yi kawai don ta san ta ɗaure mana baki. Ai ke dai anyi abu fa a gidan nan. Allah kada Ya maimaita mana kawai." "Amin. Don dai kam ko Taj ya rasa mace in sha Allahu babu shi babu wannan yarinyar." Cewar Mama. Hirar shekarun baya su ka koma yi. Inna ta sake kaɗuwa da jin wace ce Mami. Ashe zama bai ganta ba kuwa. Dole ta dage ta nesanta Taj da Hamdi daga Salwa. * "Yaya haka Ahmad? Ni da na kira ka mu san abin yi sai ka kama kuka?" Ahmad bai san cewa duk bayanin da yaji a waya bai kama ƙafar wanda ya ji yanzu ba. Ƙodar duka biyu Kamal ya rasa kuma wai cikin su ashirin da bakwai babu wanda tasa za ta yi. Idan babu mai taimakon Kamal a cikinsu daidai yake da babu Kamal ɗin. "Alhaji bayaninka fa yana nufin duk yawanmu ba za mu amfane shi ba tunda babu jinin wanda ya dace dashi." "Haka su ka yi min bayani da likitan." "Anya ba ya faɗa bane kawai saboda baya son takura kowa?" Ahmad ya yi tambayar da basu san amsarta ba. Alhaji sai ya shiga tunani. Tabbas kowa a gidansa ya yi fice akan wata halayya. Indai ana batun sadaukarwa to Kamaluddin ɗinsa shi ne na farko. Wuyarta ka nema zai baka ko shi ne abu na ƙarshe a tare dashi. Ba abin mamaki bane in ya zamo yaƙi yarda a cire ƙodar kowa a dasa masa. Wannan tunanin kaɗai ya haskaka zuciyar Alhaji. Zai nemi Kubra ta haɗa shi da likitan da ya dace a Aminu Kano Teaching Hospital. All hope is not yet lost. Sun tattauna yadda za su yi idan aka yi rashin sa'a da gaske babu wanda jinin nasa ya yi daidai. Alhaji ya sanyawa ransa daga yau zuwa sati in ba a dace ba za su bar ƙasar. Ɗan lokacin ma ya bari ne saboda su sami damar yin booking ɗin asibitoci a ƙasashen waje. Duk wanda aka sami appointment da wuri, shi za su je. Baya son su fara tafiya a can ma ace ƙodar ake buƙata dole kuma babu mai bayarwa. Da su ka gama ne Ahmad ya ce "maganar Salwa..." "Yauwa..." ya tashi "mu je ƙasan. Wani rami nake son toshewa kafin ya zama ƙofa." Gaban Ahmad faɗuwa ya yi "Alhaji ka sami labarin tana son Taj ne? Nayi mata faɗa. Ko a hanyarmu..." "Bana fatan abin da zai sa na ci zarafin jininka Ahmad. Amma tabbas idan Salwa ta cigaba a turbar da ta ɗauka to lallai za ta fuskanci fushina." Hankalinsa ƙara tashi ya yi. Me kuma tayi? Bai sami amsarsa ba sai da su ka shiga mota ya matsa mata da tambaya saboda abin da Alhajin ya yi ya bawa kowa mamaki. Hamdi ya nema suna saukowa. Amma ta ce masa ya yi sa'a kuwa domin yanzun nan suke shirin fita ita da Hajiya da Na'ima wadda ke bin Hajiyayye za su kai ta gida. "Da kun koma kun ɗaukota kuwa" cewar Alhaji yana shafa kan ƙananun jikokinsa "ni na kawota. Idan ba a jira na mayar da ita ba sai a nemi izini na kafin a kaita gida." "Mun kusa yin laifi ashe. To Allah Ya bada haƙuri" in ji Umma. Gabansa Amma ta kawo Hamdi. Ta durƙusa ta gaishe shi kai a sunkuye. Yadda ya amsa mata da sakin fuska har Inna sai da ta jinjina lamarin. "Ni dai ba zan bar magana a cikina ba." Amma tayi maganar da ta janyo hankalin kowa gareta "da mun san aurenki ne zai dawo da Taj gidan nan Hamdiyya ai da ranar da ya fita zai dawo. Sannunki Hamdiyya tauraruwar Tajuddin." Dariya aka kama yi. Ita kuwa ta cigaba da cewa "Allah kuwa da gaske nake. Ji fa irin fara'ar da kake yi mata Yaya Hayatu. Irin ka yi na'am ɗinnan da auren hands down." Hararar ƙanwar tasa ya yi ya ce "A'a hands up." Yaran kuwa me zasu yi banda dariya. Da kowa ya nutsu ne Alhaji ya ce ina Salwa. Tana daga gefe ta kawo wuya da abubuwan da ake yi a falon. Tasowa tayi kamar ƙwai ya fashe mata a ciki. Tayi zaton magana zai yi mata a gabansu sai ya ƙara gaba ta bishi. Kowa na gani amma ba a san me yake cewa ba. "Kin ga matar Taj ko?" Shiru tayi da farko. Ya nanata tambayar da wata irin murya mai cikar kwarjini. "Kin ga Hamdiyya matar Taj ko?" "Eh" ta gyaɗa kai da sauri. "Kin kuma fahimci me yasa na nuna miki ita ko?" Nan ma eh ta ce ba tare da jiran ya kuma tambaya ba. "To kada na ji, kada na gani Salwa." Ya juya mata baya "ki je Ahmad ya mayar dake gida." * "Yarinyar nan ya nuna min" ita ce amsar Salwa ga Ahmad da ya kusan kai mata duka akan ƙin amsa masa tambayar me Alhaji ya ce mata da farko. "Wace yarinya?" Ciki-ciki ta ce "matar Ya Taj." "You are the least of my problems Salwa so ko ki buɗe baki ki bani amsa ko ki riƙe abinki duk ke ta shafa." Ahmad ya faɗi da faɗa-faɗa. Yadda su ka yi ta faɗa masa. Ya kalleta yana mai taɓe baki. "Kina gab da yin nadama mara amfani idan baki dawo daga rakiyar zuciya ba. Duk wanda ya bari tasa ta mulki tunaninsa da wuya yake cin riba. Dubi yadda gabaɗaya ki ka sauya akan wannan obsession ɗin naki. Kin zubar da mutumcinki ana ta takawa a banza." Ci kanka bata ce masa ba. Yana magana ma Ummi take turawa text tana neman inda za su haɗu yau. Ta riga tayi nisa bata jin kira. Burinta kawai Taj ya so ta ko iyayensa basa so kuwa sai sun yi aure. *** GIDAN TAJ DA HAMDI (Sponsored by annurifoods, nafsbedding and meensincense) Jeren gidan amarya ba mai yawa bane ta ɓangaren gidan Abba Habibu. Inna tayi rawar gani da nunawa fiye da tunaninsu. Ta cika gidan da komai na buƙatar amarya da ango. Sai dai kuma duk da haka Abba da Yaya basu fasa yin nasu ba. Makusantansu ma sun nuna bajinta ba kaɗan ba. Kayan zaƙi na gara irinsu dubulan, alkaki, nakiya, gireba, bakilawa da cincin Ƴar Ficika da muƙarrabansa ne su ka yi. Abin ka da tsofaffin takari, nasu ya sha bamban sosai da wanda aka saba. Iyaa kuwa gidan ƙanwarta taje a hotoro aka rakata wajen wata ƙwararriya a harkar kayan kaɗi da abubuwan abincin gargajiya. Samira Muhammad kenan, mai Annurfoods. Mace mai faram faram da iya mu'amala. Tun abin da ya haɗa Ummi da Hamdi a makaranta Iyaa take neman hanyoyin daɗa wanke iyalinta duk da su Yaya basu canja musu fuska ba. Bayan gudunmawar kuɗi da su ka bayar shi ne ta haɗo wannan. Da ta kawo kayan Yaya kasa rufe baki tayi. Wanda ta haɗawa amarya dole ta ajiye domin babu yadda za a kai Hamdi ba tare da kayan annurfoods ba. Garin kuka da kuɓewa masu kyau a madaidaitan bokiti. Sai daddawa wadda ana haɗa kayan Anti Labiba ta ce ita dai ayi haƙuri sai ta ɗiba saboda daɗin ƙamshinta. Babu warin nan mai hawa kai mutum ya rasa inda zai yi da ransa. Sai nau'in yaji daban daban. Jan yaji mai tafarnuwa da wanda babu, na daddawa da kuma na ƙuliƙuli. Niƙaƙƙiya da kuma markaɗaɗɗiyar gyaɗa (gari da paste), garin ɗanwake, garin kunu wanda yaji duka kayan haɗi da kuma soyayyen man shanu mai daɗin ƙamshi. (Samira Muhammad 08039183880, instagram @annurfoods.ng) "Altine wannan kaya basu yi yawa ba?" Faɗin Yaya tana jin kamar tayi kuka saboda karamcin da ake ta nuna musu. "Ina abin yake Jinjin?" "Haba dai, wannan yafi ƙarfin a bi shi da kalmar ina abin yake. Ke dai Allah Ya biyaki da mafificin alkhairi." Iyaa ta ce "amin Ya Allah." Sajida aka damƙawa kayan a hannunta da umarnin idan sun je gidan tunda da wuri za su fita kafin a kai amarya ta saka komai a inda ya dace. Ana haka su Amma su ka yi sallama. Allah Yasa sauran safiya ce. Babu baƙin fuska a gidan. Aka sauke su a falo. Hajiya ta fara da bawa Yaya haƙurin tafiya da Hamdi da Alhaji ya yi. Don ta rufa masa asiri ma ta ƙara da cewa yayi haka ne kawai don ya kula suna cikin damuwar ciwon Taj. Yaya tayi murmushi. Gashi dai an shigo gidan amma hannun Hamdi yana cikin na Amma a gefen Hajiya tayi mata riƙo na ƴar da ake ji da ita. "Wallahi babu komai. Da nan da can duk ɗaya ne." "Kin sami labarin Alhaji ya yiwa Taj izinin komawa gida?" Amma ta yi tambayar saboda ita fa a yanzu wannan yafi bikin ma a wajenta. "Ƙwarai kuwa..." sannan Yaya ta taya su murna. Cikin mutumci aka gama komai. Za su fita Amma da bata iya shiru ta ce da Yaya don Allah wane irin turare ne aka saka a ɗakin yake fitar da ƙamshin da su ke ji tun shigowarsu? Hajiya girgiza kai ta kama tana murmushi. Amma bata iya baƙunta ba. Sai dai idan bata ga fuska ba. Ta gode mata dai saboda ita ɗin ma surukuta ce ta hanata tambaya tun shigowarsu. Daɗin ƙamshin ba daga nan ba. Bayan kujera Yaya ta nuna musu. Inda aka ajiye turarukan wuta a cikin bokitai an rurrufe bakunansu da salatif. "Ko kunnawa ba'ayi ba. Na gidan ƴarku ne." Tashi Hamdi tayi ta bar falon. Yaya ta ƙwalawa Zee kira. Tana shigowa ta ce ta ɗauko a buɗe musu su gani. "Haba Maman Hamdi? Don Allah kada a buɗe. Ƙamshin ne ya yi min daɗi na kasa barwa cikina" Amma ta faɗi da sauri. "Ni dai ban ga komai a ciki ba. Nan kuke ta cewa an zama ɗaya" cewar Yaya tana kama guda ɗaya "in sun je gidan yanzu ma buɗewa zasu yi su zuzzuba a rufe sauran." Da ƙyar su Hajiya su ka hanata buɗe musu. Bayan tafiyarsu ta sanya a ranta lallai za ta sayi wani ta aika musu. Zuciyarta kuwa fari ƙal don daɗi. Duk da ana ta yaba ƙamshin a gidan tayi zaton na ganin ido ne kawai. Sai yanzu da waɗanda basu san dashi ba su ka yi magana ta kuma gaskatawa. Matar Halliru maƙobcinsu Hairat ce ta dinga zuzuta kyau da ingancin turarukan wata ƴar garinsu Bauchi. Da farko Yaya har cewa tayi duk turarukan Kano ace sai ta nemi na wani gari? Matar Halliru taƙi haƙura domin ta san me za su rasa idan ba a saya ba kamar na lokacin bikin Sajida. Na wajenta da basu da yawa ta kawo. Zee ta kunna da yamma. Sai da kowa ya fito tsakar gida ranar. Washe gari Yaya ta karɓi numbar Amina (08036387204, instagram @meens_incense). Ta kira su ka yi ciniki akan farashin da idan ka karɓi turaren ma sai ka ce sadaka kawai aka baka. Da turarukan su ka iso kasa rufe baki tayi don murna. Ta dai ɓoyesu kafin Hamdi ta dawo gida ranar saboda ko za ayi mata faɗa sai ta kunna. Soyayyarta da ƙamshi ta daban ce. Ga dai turaruka kala kala, kwalaccam ɗinta kuwa abar duƙan ƙirji ce (I mean it, the scent simply calms the heart), sai kuma humra irin wađanda sai hancin da yaci karo dasu ne kawai zai gane. Haka aka tattara komai aka zuba a mota domin kammala gyare gyare kafin zuwan amarya. *** Banɗaki Ummi ta shiga da waya ta turawa Alh. Usaini saƙo cewa jiya ma Salwa ta sake shafawa Taj turaren nan. Kuma da alama anyi nasara domin ta sami labari a daren aka kai shi asibiti. Daga maganar da taji Baba Maje da Iyaa suna yi bayan wayarsa da Abba Habibu da safen ta fahimci ba rashin lafiya bace kawai ta kama shi. Salwa kuma ta tabbatar mata a text. Ita Iyaa da wuri ta tafi gidan bikin. Ta barsu in sun gama girki da gyaran gida sai su biyota kafin dai a fita da amarya. Yana karantawa ya kirata. Da ta ɗauka tsoro ya bata da taji ya fashe da wata irin dariya mara daɗin ji. Da jindaɗi ya ce "Ƙarshen wannan ɗan daudun ya zo." "A'a fa, ba ɗan daudu bane" Ummi taji ba za ta iya shiru ba. Ko makaho ya shafa Taj ba zai kira shi ɗan daudu ba, balle mai ido. Idon ma irin nata mai son abu mai kyau. "Ummi kenan. Wai me ya hanaki cewa ayi aikin da za ki sami soyayyarsa maimakon wannan sakaryar Salwan?" "Bana ra'ayin namijin da kowa ke rububi." Tana ji Alh. Usaini ya yi dariyar rashin yarda. Tunanin Taj ya so ta bai zo kanta ba saboda tayi nata binciken akan waye shi. Labarin mahaifinsa kaɗai ya isheta dalilin mayar da kwaɗayinta. Sannan ta san cewa ko ana muzuru ana shaho a yadda Baba Maje yake ganin darajar Abban Hamdi, da wuya ta gaske a barta ta aure shi. Ita kuwa abin da take ji a kansa ba na irin mu'amalarta da banzayen samarinta bane. Ya girmi hakan. Shi yasa kawai taga babu mafita sama da rusa shi. Ita da Hamdi kowa zero. Mafi munin hassada kenan. "Ki tabbatar kin je kai amarya kuma kin bibiyi me suke ciki na ƴan kwanakin nan. Kin san na faɗa miki aikinsa a hankali yake ci." "Bana son yin abin da zai sa a zargeni. Ba wani shiri muke da Hamdi ba kuma kowa ya sani." "Sai ki san yadda za ki yi." Ya ɗaga mata murya kamar wata ƴarsa. Bai san bashi da wani kwarjini a idonta ba. Yana shiru ta ce "Ban gane ba? Wannan abu fa duk kai ne da riba. Idan ka damu ka sa malamin da ya yi maka aiki akan Taj ɗin ya tura aljanu su binciko maka mana. Mtseww" Wayarta ta kashe ta sake buga tsaki. "Aikin banza. Ni za ka ɗagawa mur..." Haɗiye maganar tayi cikin tashin hankali saboda haɗa ido da tayi da Siyama. Ita kuma cikin sauri da ta karanci fuskar Ummin sai ta kama ɗaɗɗaga ƙafa. "Fitsari, fito don Allah." Fitowar Ummi tayi tana wasiwasin Siyama taji wayar da tayi ko kuwa. Gaba na faɗuwa Siyama ta dakata a bakin ƙofa ta nemi mafita don kaɗan daga aikin Ummi tayi mata wani abu idan ta san ta ji. "Naji kina ta gunaguni da tsaki, ba dai flushing ki ka yi yaƙi tafiya ba? Kada na shiga nayi gamo." Ba kunya Ummi ta saki fuska harda ƴar dariya "shiga ki ganewa kanki" ta turata ciki. Siyama na nuna kamar bata son shiga ta bari Ummin tafi ƙarfinta. Fitsarin da ya kawota da gaske ta daina ji. Tabbas akwai manaƙisar da Ummi take shiryawa Hamdi da Taj tunda taji sunayensu. Hankalinta ya tashi. Har su ka tafi gidan bikin tana faman satar kallon Ummi. Da zuwansu babu daɗewa ta nemi keɓewa da Iyaa. Ummi kamar an tsikareta ta tashi tayi musu laɓe. Da taimakon Allah ta sami basirar lauya zancen. Wata maganar daban ta ɗauko har Iyaa za ta fara yi mata faɗan me yasa ta janyota akan shirme, sai ta ƙifta mata ido. Ganin haka sai ta kalli bakin Siyama da ta faɗi sunan Ummi iya leɓe. Wannan yasa ta fahimta. "Iyaa za ki barni zuwa kai amarya har ango yazo? Ni fa ban taɓa zuwa ba." "To naji sai ki biyo yayanku don na san zai je ko don ɗauko Zee." Murna ta kama yi harda rungume Iyaa. Da wannan ta samu Ummi ta daina saka mata ido har ta sami damar sanar da Iyaa wayar da taji. "Ban ji ance komai ba amma ko da wani abu zai biyo baya to da hannunta wallahi." Sallamarta Iyaa tayi ta jingina da bango domin gabaɗaya jikinta ya mutu. Nauyi taji jikin yayi mata ta sulale a wajen kawai ta zauna. Babu abin da take yi sai kiran sunan Allah da neman agajinSa. Haƙiƙa kowane ɗa da halinsa yake zuwa. Tarbiya bakin gwargwado sun bawa ƴaƴansu. Amma tun ƙananun shekaru tanƙwara Ummi ke wahalar dasu. Bata da bakin ɗorawa ƙawaye alhakin ɓata mata ƴa domin kuwa duk inda Ummi ta zauna ita ke shugabantar waɗanda take mu'amala dasu. Ita ce boss mai sawa da hanawa. Ko dai kawo ƙara da wasu iyayen ke buri da alfaharin gara a kawo musu ƙarar ƴaƴansu akan su kai na wasu da tayi ke bibiyarta? Duk inda Ummi ta zauna sai tayi faɗa kuma ana bincike ita ce mara gaskiya. Kuskurenta a lokacin da suke cikin yaran yarbawa a tsakiyar Agege shi ne na jindaɗi da Ummi bata taɓuwa. Babu mai yi mata kwarjini ko ya bata tsoro. Kana cewa kule take ce maka asss. Wata maƙociyarta bahaushiya a lokacin ta kan ce "Iyaan Baballe ki daina murna. Duk da cewa ba ma son a zalinci yaranmu to amma fa idan sun fita ya dace ki dinga addu'ar kada su taɓa ɗan kowa. Babban abin alfaharin rayuwa shi ne kayi dace kai ko wani naka bai zama silar ƙunci ko zubar hawaye ko jinin wani ba. Sannan kaima kada ɗan kowa ya yiwa naka. Ko babu komai akwai baki da ido kuma su ɗin gaskiya ne. Allah Ya kyauta." Amsarta a lokacin ita ce tunda suna zaune a waje irin wannan ba za ta so yaranta su zama lusarai ba. Wannan mata kuwa ta nuna mata cewa duk runtsi ai gara idan an je gaban Allah ka zama mai kai ƙara da a kai ƙararka. Za ta koyawa yaranta su ƙwaci kansu amma kada su zama silar rigima kuma banda zalunci da wuce gona da iri. Manzon Tsira SAW cewa yayi kada mu cutar kuma kada mu bari a cucemu. Hawaye ya zubowa Iyaa. Ta ɗauki laifin ta ɗorawa kanta. Cin zalin da Ummin da dinga yiwa Siyama ne yasa ta canja tsarin tarbiyar lokacin. To amma ɗan wannan guntun sakacin da kuma halayyar fiɗrar da aka haifeta sun riga sun yi tasiri. "Allah na tuba. Allah Ka duba min." Wata walwala da jindaɗinta duk sai su ka kau a lokacin. Ciwon kai ta ɗorawa laifin hakan da Yaya ta tambayeta game da sauyin da ta gani a tare da ita. * "Kai Happiness me ya same ka haka ka kumbura?" A madadin sallama abin da Taj ya fara cewa kenan da ya shiga ɗakin Kamal. Son faɗawa Happy gaskiya yayi sai dai kuma a ganinsa faɗa a yau ba ƙaramin rashin adalci bane. Babu yadda za ayi Taj ya san gaskiya kuma ya tare a gidansa a yau. In ya yi haka kuwa ya cutar da Hamdi. "Wai ashe kifi ne jikina baya so yanzu ni ban sani ba? Jiya da ka kula tun a wajen dinner bani da kuzari. Kifi na ci last kafin mu tafi." "Subhanallahi. Kuma Alhamdulillah tunda an gano. We'll just avoid it don a zauna lafiya." "We? Kai kuma me zai sa ka daina ci?" Kamal ya tambaye shi. "Ai ka sanni da kirki. Ba zan so na dinga ci a gabanka ba." Da dabara Kamal ya sauya zancen da dai yaga Taj ya yarda. "Wai ni ya na ganka haka kamar ba wanda ya kwana gida ɗaya da Hamdi ba?" "Akwai ƙura fa Happiness. Alhaji ya ɓallo min ruwa jiya." Ya faɗa masa abin da ya faru. "Tabɗijam ake cewa ko cabɗijan...yanzu kana nufin ni da kai yau duk pillow za mu runguma?" Bugu Taj ya kai masa ya goce "ta Allah ba taka ba. In sha Allahu gadona da naka yau sai an sami bambanci." "Salman Khan na Hamdiyya wato ana yi maka kallon salihi ashe ashe ba haka bane." Kamal ya faɗi yana yi masa dariya. "Aure dai nayi...idan mutum yaji haushi wata asabar ɗin mu kai shi ɗakin doctor" "Maimakon ka zo mu zanta yadda za ayi a shawo kanta tun kafin ƴan kai amarya su watse ka zauna tsokana." "On a serious note kana ganin abin da take so zai samu yanzu? Alhaji fa take so ya canja yadda yake yiwa Abba. Bata san na fita son hakan ba ta ɗauki fushi dani." Shawarwari Kamal ya soma bashi sai dai a yau ko kusa zancen ba shigarsa yake ba. Ya riga ya san da me zai kama Hamdi a hannu. Damuwarsa yanzu canjin da ya gani tattare da Kamal mai yawa tsakanin jiya da yau. Happiness is hiding something. Yana ji har cikin ɓargonsa. Ko maganganun da suke yanzu yana hango pain ɗin da ɗan uwansa yake ƙoƙarin ɓoye masa. Dole zai yi wani abu a kai. Kamal bai fi shi wayo ba. * Wannan asabar ta kafa tarihi mai girma a gidan Alh. Hayatu. Yinin bikin Taj da aka shirya yi a gidan wan Inna sai ya dawo gidan mahaifinsa. Ƴan uwa na kurkusa da su ka san me ya wakana tsakanin uba da ɗa sun taho harda maza irinsu dattijon arziƙi Yaya Babba su ka yi fatan alkhairi su ka tafi tare da Alhaji. Aka dinga kiran ƴan biki cewa venue ya canja last minute. Ƴaƴa, surukai da jokokin Marigayi Alh. Sule Maitakalmi sun gwangwaje cikin farinciki. Inna da ƴan uwanta su Hajiya anko su ka yi da Amma uwar goyon Taj. Ango ya fito tsakiyar dangi babu shayi ko tararrabi gwanin ban sha'awa. Wai aka ce taɓa kiɗi taɓa karatu. Da yake a gida suke matashin ɗan Yaya Kubra ne yayi musu DJ. Ba kunya ita da kanta ta ce masa ya kunna musu waƙar da ta faɗa masa tun a gida. Ta sanya autar Alhaji Surayya tayi coordinating komai. Layi aka yi a jere tun daga Yaya Hajiyayye har ita Surayyan. Dukkaninsu sanye da anko iri ɗaya na shadda light brown. Ɗinkin mata irin ɗaya, haka ma na mazan. Daga kan Yaya Hajiyayye kuma ta jere Inna, Umma, Mama da Hajiya a gefe da gefen juna. DJ ya saki waƙa su ka dinga bi. Hurry hurry come carry your baby go Come and see my mother ahh.... Kowa sai ya bar abin da yake yi ana kallon zugar gidan Alh. Hayatu. Babu wanda bai yi rawa ba idan an zo kansa, har Ahmad da tun safe yake cikin ƙunci. Sai yanzu da yaga Kamal yana walwala har yafi Taj rawar ma ya sake. Bayan sun gama matsawa su suka koma gefe suna nuna uwayensu ana ta dariya. Wani abin burgewa shi ne da Taj ya taka har gaban Amma yana nunata da hannuwansa biyu yana faɗin come and see my mother. Bata san lokacin da ƙwala ta zubo mata ba. Ya rungumeta a wurin yana ɗan dukan bayanta. A wurin kowa har angon wannan wunin is the best event. Kowa yaji daɗi. Ana la'asar Mama ta ce ayi haramar ɗauko amarya a kaita gidanta. * Ƙarfe biyar da rabi motocin kai amarya su ka cika layin gidan Abba Habibu. Motoci na alfarma da kece raini. Taj bashi da wasu abokai na a zo a gani sai cikin ƴan uwansa. Su ne kuma su ka cika wurin ƙwai da kwarkwata. Kowa ya zo ɗaukar amaryar Taj. Su ma biki suka yi sosai. Gidan Abba Habibu babu masaka tsinke. Abinci da abin sha sai mutum ya ture. Ƙarfe uku aka shige ciki da amarya. Kayan gyaran jikin da Amina Meens_insense take yi Hairat matar Halliru ta saya domin yau. Ba don nisa ba da ita da kanta za ta sake yiwa Hamdi gyaran nan kafin a kaita. Sake scrubbing jikin tayi ta turarata sosai. Bayan an gama ta sanyata ta tashe jikinta da kwalacca ɗin meens ɗin. Sannan tabi gaɓoɓi da oil ɗin scentmania. Ita kanta Hamdi duk kukan rabuwa da gida da ta fara sai da ta dakata ta shaƙi ƙamshin sosai. "Hamdi kada ki yi wasa da ƙamshi. A jikinki da gidanki. Rahama ne shi babba kuma abokin yaƙi da nasarar kamo zuciyar maigida. Mace mai wayo bata bari mijinta yaji wari a jikinta." "Ba za ki amsa ba uwar miskilanci? Ana baki darasi kin wani haɗe rai." Cewar Sajida tana harararta da gefen ido. "Idan na amsa ace bani da kunya. Nayi shirun kuma ban tsira ba. Me ya hanaki yi min kara ki ce to?" Hamdi ta rama hararar. "Ba laifinki bane. Gidan miji za ki kwana yau, dole ki min rashin kunya." Sajida ta faɗa da rawar murya. "Kinga kin saka ta kuka ko?" Zee ta matsa jikin Sajida ganin har ta soma zubar da hawaye. Jiki a sanyaye Hamdi ta matsa kusa dasu "ni me na ce don Allah. In ranki ya ɓaci ki faɗa min mana. Meye na kuka?" Ita ma sai ƙwalla. "To ni wa zan rarrasa cikin ku?" Zee ma ta kama kuka. Rungume juna su ka yi suka kama kuka haiƙan. Ta tabbata yau su uku kowa makwancinta daban. Aure abin so kuma abin alkhairi ya rabasu. Hairat fita tayi ta basu wuri. Ana ganinta a waje aka fara tambayar ko Hamdi ta gama shiri. "Yaya leƙa ɗakin." Ta ce da Yaya. "Ga iyayensu nan..." Yaya ta faɗi cikin kunya. Hairat kuwa ta ce ita ya dace taje. Ƴan uwan nasu ma su ka goyi baya. Tana shiga ta samesu su uku suna sharɓar hawaye. Da su ka ganta wajenta su ka ƙarasa kowacce kukanta ya ƙaru. Ta fara yi musu nasiha sai gashi tabi sahu. Sai da aka ji shiru aka biyo bayansu. Inna Luba da kanta da sanya Hamdi a gaba ta saka kaya. Riga da zani na leshi mai ɗan karen laushi. Fuskarta babu makeup sai hoda da kwalli da ɗan pink lipstick sama sama. A haka ma tayi kyau sosai. "Har a fita ban yarda ki sake sanya min ƴa kuka ba. Ki daure ki riƙe hawayenki don Allah." "Haba Inna? Ba ma ta ni kike yi ba sai Yaya?" Hamdi ta kyaɓe fuska. "So so ne Hamdiyya..." cewar Inna Luba tana dariyar tsokanar jikar tata. "Amma son kai yafi ko? Naji da ana cewa wai mutane sun fi son jikokinsu akan ƴaƴa." Inna Luba ta kaɗa baki ta ce "Duk ƙarya ne." "Ai kuwa sai na faɗawa Yaya ta daina jin babu daɗi idan kina shareta." "Zo nan don ƙaniyarki" Inna Luba ta yafito ta ta gudu. Matar Kawu Abduƙadir ƙanin Abba Habibu ce ta zauna da Hamdi bayan ta gama shirin ta bata kayan gyara ba mata da sati guda kenan ana bata ta shanye. "Ki kula da abincin da kike ci da tsafta. Wannan sinadari ne. Kada ki dinga yi musu shan ƙoshi don Allah. Komai saisa-saisa yafi" Sunkuyar da kai tayi har ta gama yi mata bayani ta tashi. Daga nan gida ya kaure da guɗar shigowar dangin Taj. Cikin Hamdi ya yamutsa da wata irin fargaba. Kukansu ita da su Zee ya dawo sabo fil. Aka fita da ita ko Abbanta da taci burin gani bata sanya a ido ba. Yadda ya bar gidan ranar kai Sajida ita ma haka yayi mata. Ba zai iya ganin fitarsu ba. A motar Kamal aka sanya amarya. Mummy matar Yaya Babba da uwargidan Alh. Lurwanu wan Inna su ka saka ta a tsakiya. A gaba kuma wata Anti Zinatu ce. Rantsuwa kala kala Kamal ya yiwa Yaya Kubra akan lafiyarsa kafin ta bari ya fito. Tana barazanar za ta tona masa asiri yayi dariya. "Ni za ki lallaɓa kafin na tona naki asirin. Alhaji da Yaya Ahmad sun san da ciwon. Na rufa miki asiri ne dai kawai..." "Alhaji ya sani? Kamal ka kyauta kenan? Idan ya san nima na ɓoye ka san me zai min?" Ta katse shi a tsorace. "Shi yasa nace ki barni na fita kada na janyo miki" dariya ya yi mata ta bashi hanya da zai fita ya ce "ba maganarki ce bana ji ba, sai dai ina so ki min haƙuri don ban sani ba ko wannan ne abu na ƙarshe da zan yiwa Taj." Haka ya fita ya barta tana share hawaye. Ta gama ƙarar da duk basirarta da waɗanda za ta nema amma ba a dace ba. *** Gidan amarya ko yaya yake sai kaji ana son barka. Balle kuma gidan Tajuddin da Hamdiyya. Duk wanda ya shiga da santin gidan yake fita. Kayan ƙawa da ƙyale ƙyale an saka amma masu aji wanda basu cika waje sannan basu fiye ƙyalƙyali ba. Harkar girma da girma kawai. Inna da masoyanta waɗanda su ka goya mata baya sun yi rawar gani sosai. Haka zalika Abba Habibu da Yaya. Basu kwanta anyi musu komai ko don gudun raini da wulaƙanci. Da sunan Allah a baki da zuci iyaye su ka kai Hamdi ɗakin aurenta. Aka kuma umarci ƴan uwanta da su bar kuka haka nan saboda ta sami nutsuwa. A gidan aka yi sallar magariba sannan aka soma tafiya. Yan matan dangin amarya da ango kowa da irin salon nasiha da shaƙiyancin da yake yiwa amarya a kunne. Da aka watse ya rage Sajida da Zee sai Siyama da sa'aninsu daga ƴaƴan ƴan uwan Abba Habibu. Sun zage sun sake gyare komai kafin shigowar angwaye. Iyaa bata bari Ummi ta bi su ba. * Taj ya haɗuwa da Alhaji kafin su fita. So yayi su gana su kaɗai ya ƙara yi masa godiyar dawo dashi cikin ahalinsa da yayi. Sannan yana so ya faɗa masa yanayin Kamal da baya yi masa daɗi. A ƙarshe ya roƙe shi ya matsawa Kamal ɗin ya sanar dashi damuwarsa. Tunda ya san ba zai kalli idon Alhaji ya yi masa ƙarya ba. Da Ahmad su ka shiga wajensu Hajiya. Kowanne ɗaki idan yaje sai anyi masa addu'a. Sisters ɗinsa su ka kama koke koke. Ahmad ya haɗasu manya da yara ya dinga faɗa. "Auren ku ke yiwa kuka?" "Kwanansa ɗaya a gida fa zai sake tafiya." "Sai ka koma basu gaji da ganinka ba" cewar Ahmad yana haɗe rai don baya son ɓata lokacin da ake yi. Taj ya kanne ido ɗaya ya kawar da kai gefe "ni dai Hamdi" "Lahhhh" Suna tsokamarsa wai bashi da kunya da ya faɗi haka a gaban iyaye ya ce su ma basu da ita da su ka kawo zancen ya sake kwana. Aka gama wasa da dariya su ka fito. A hanya ya fara faɗawa Ahmad damuwarsa akan Kamal. "Gabana har faɗuwa yake yi idan ya faɗo min a rai. Gani nake kamar ba wani ciwon allery." Ahmad yayi ta maza sosai da ya iya daurewa ya cije yadda Taj ba zai gane ba. "Ka tambaye shi?" "Ina ɗauko maganar yake neman hanyar canjata." "Kada ka sa komai a ranka. Zan binciko maka." Ajiyar zuciya Taj yayi "nagode Yaya." Shiru su ka ɗanyi kafin Ahmad ya ɗauko zancen Salwa. "Naji duk abin da tayi. Kayi haƙuri. Yau na so ta koma Bauchi amma ban sami zama ba." Katse shi yayi "Yaya Ahmad don Allah mu bar zancen. Ƙanwarka ce. Nima kuma ƙaninka ne. Na san babu sani ko goyon bayanka saboda haka kada ka ja zancen nan ko ka bani haƙuri. Ita ce ma zan bawa saboda ƙin karɓar tayinta da nayi." Samun gidan yawa irin na Alh. Hayatu mai tattare da haɗin kan iyali ba abu ne mai wahala ba. Na farko mutum ya zaɓo mata nagari sannan ya tafiyar da mu'amalar gidansa a bisa tsarin shari'ar musulunci. Na ƙarshe kuma ya dage da addua. Saɓani a yau da kullum dole ne. Amma a ƙalla wasu abubuwan da dama sai dai kaji ana faɗi ba dai a gidanka ba. A farfajiyar gidan su ka haɗu da sauran ƴan uwansu da tsiraran abokai. Sai Safwan da Baballe. Ahmad ya ce ba zai shiga ba a matsayinsa na wan ango. Su Kamal ne su ka raka shi ciki. "Ya Taj ina ledar kazar amarya? Ko tana mota?" Abba ne ya yi tambayar kafin su bar bakin motocin. Taj ya tsaya turus, wallahi ya manta ana wannan siyayyar. Bai taɓa raka ango ba amma Kamal ya faɗa masa. "Subhanallahi...zo ka siyo min." Ya zira hannu a aljihu. "Gashi na siyo" Kamal ya ɗago ledoji biyu daga gaban motarsa. Rungume shi Taj yaje ya yi. "What will I ever do without you?" "Sake ni dalla kada ka sani kuka" Kamal ya ture shi. Taj yaƙi saki. Bishir da wani cousin ɗinsu harda ƴar ƙwalla. "Ya aka yi ka san ban saya ba?" "Wallahi jiki na ne kawai ya bani." Murmushi suka yi sannan Taj ma ya karanto addu'a kafin ya shiga gidansa karo na farko a matsayin mijin aure. A falo su ka sami ƴan matan amarya da amaryarsu a tsakiya an lulluɓeta da laffayar jikinta. Tana ji ana gaishe gaishe an barta da faɗuwar gaba. Ta kama hannun Sajida tayi masa kyakkyawan riƙo kamar za ta tsinke mata shi. Addu'a da fatan alkhairi aka yi musu a mutumce. Babu wannan rashin kunyar rungume rungumen sabbin aure da ake a gaban mutane. Ko kuma maganganu na rashin ɗa'a tsakanin angwaye da amare. Da aka gama Safwan ya ce ya kamata su tashi haka nan. Waɗanda za a kai gida su fito a kai su. "Ni dai ina da abin cewa guda ɗaya kacal. Happy..." Taj ya kalli Kamal. "Mrs Happy..." Hamdi ma ta ɗaga kai a hankali amma bata buɗe fuska ba. "Duk abin da za ku yi, ku ji tsoron Allah. Ku yiwa juna uzuri kuma ku kyautatawa juna zato." Yanzu dai bata yi kuka sosai ba da zasu tafi sai hawaye. Taj ya fita ya raka su sannan ya rufo ƙofa ya dawo. Hamdi tana nan bata motsa ba. Ya yi murmushi ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Gabanta ya kama dukan tara tara. Yau da anyi an gama. Inda take yanzu gidansu ne ita da Taj. Magana take jira ya yi ko wani motsi duk taji shiru. Ba zato taji saukar abu a gefenta. Ta ɗaga kai da sauri, kafin ta buɗe fuskar Taj yasa hannu ya haɗe gaban laffar ta saitin fuskarta. "Ni zan buɗe. Kada ki ɓata min tafiyar tarihin wannan daren." Komawa tayi jiki babu kuzari ta zauna da ta gane babbar rigarsa ce ya ajiye a kusa da ita. Rage tsayi yayi a gabanta ya ce "Zan taɓaki Hamdi. Kin bani dama?" "Na'am?" Hamdi taji wata baƙuwar murya ta fito daga bakinta ma'abociyar tsoro. "Na fahimci a tsorace kike ne shi yasa na faɗa miki." Kafin ta sake yin magana taji hannuwansa a duka kafaɗunta ya tayar da ita. Sannan ya kama laffayar ya soma warwareta har ta ƙare. Ya kalleta daga sama har ƙasa ya godewa Allah a ransa. Babu zato daga gareta kawai taji ya janyota jikinsa ya sanya hannuwanta a gefe da gefen cikinsa sannan ya rungumeta. Sun ɗauki lokaci a haka kowa yana fama da yanayin da ya shiga kafin ya ɗago haɓarta yana kallon idanunta. "Mun shirya Hamdi? Kin daina fushin?" "Ba fushi nake ba." "Har akan maganar ɗazu?" "Ɗazu gaskiyata na faɗa maka ai" ta ɗan kawar da kai. "Kina nufin yau ni da gwaurayen da su ka fita daga gidan nan bamu da bambanci?" So tayi ta haɗe fuska don ya san mahimmancin abin da ta faɗa amma wannan maganar sai da tasa ta yin murmushi. Sannan ta ce "Haka ne." Hannunta ya riƙe su ka zauna "su rungumi pillow nima na runguma kenan fa?" "Uhmm" ta amsa kunya na kamata. Taj ya kalleta da kyau ya ɓata rai "ke Allah kuwa da sake. Sadaki fa na biya." Da dabara ta ɗora hannu a kan bakinta don kada yaga dariyar da take neman yi. "Aka biya maka dai." maganar ta fito kamar ba daga bakinta ba. Ƙayataccen murmushi ya yi "Lallai, kin ce wani abu. Zan tuna miki a lokacin da baki zato." Ledojin da Kamal ya ajiye akan centre table ya buɗe "zo mu ci abinci. Kuma kada ki ce kin ƙoshi." "Ƙoshi kuma? Yunwa fa nake ji." Ƙasa ta zamo abinta ta zauna. Taj ya shagala da kallonta ta nuna masa ledojin da ido. "Ba za ki taimaka min ba?" "Amarya nake. Yau ɗaya ina zaune kayi min komai." "Burina ma kullum na taimaka miki." Ya wuce kitchen ya samo tray da kofuna. Tana zaune ya buɗe ledojin ya ajiye tray ɗin a tsakiyarsu. Akwai youghurt da juice, sai snacks irin su doughnut, croissant da pizza. Ga kwali madaidaici a ciki akwai cake da aka rubuta beautiful beginning Happy and Mrs Happy. "Allah Sarki Happiness mai sona da gaskiya." Taj ya yi magana yana kallon Hamdi a kaikaice. Ta gane da biyu yayi magana shi yasa ta ce "Wallahi kuwa, Allah dai ya ƙaro aminci." Taj ya yi ƙwafa kawai ya buɗe ledar gasashshiyar kaza da gurasa. "Wanne za ki ci?" "Mene ne wannan?" Ta nuna croissant ɗin. "Abincin maza ne." Ya tsokaneta. Yana rufe baki ta ɗauka ta gutsira harda lumshe ido ta ce da daɗi. "Na ce miki na maza ne." "Nima ai ta mazan ce" Hamdi is just too cute. Yadda take maganar kaɗai ya gama hargitsa masa tunani. "Har mu nawa?" "Ga Abbana, ga Halifa sannan..." Ya zuba mata idanu. Dole taji kunya ta saki murmushi. "Sannan kuma ga Happy nawa." "Happy naki." Ya maimaita da murmushin jindaɗin. Ture tray ɗin ya yi ya dawo kusa da ita kamar zai mayar da ita jikinsa ya ce "saboda Allah da gaske kike to akan maganar nan?" "Da gaske nake." "Amma in banda ke wa yake kama wani da laifin da ba nasa ba?" Ya marairaice mata. Yadda komai tayi yake taɓa masa zuciya bai san ita ma haka yake a wajenta ba. Haɓarta ta ɗora akan tafin hannunta ɗaya tana kallonsa ta ce "Yanzu ya kake so ayi?" Kalmomi neman ɓace masa suka yi saboda har cikin zuciyarsa yake jinta. "Stop acting all coy..." "Meye coy?" Tambayar ma a yangance tayi ta. Ba kuma wani abu bane yasa take yi masa haka sai don kada ya ɗauki zafi akan shawarar da ta yankewa zamansu. Soyayyarsa tana jinta kamar da ita ta rayu. Ɓata masa rai is the last thing on her mind. To amma me zai faru idan zama yayi zama sai kawai Alhaji ya yiwa Abbanta abin da zata ji haƙurinta ya ƙare? Idan wataran ta kasa riƙe bakinta ta rama fa? Da wane ido za su kalli juna ita da Taj? "Acting all lovey dovey,.. and shy...and bold, and...." "This?" Hamdi ta saƙala hannuwanta a wuyansa. Gabaɗaya su ka tafi. Sai da ya kaita kan kafet ɗin. Fuskokinsu na kallon juna. Numfashinsu na gauraya sannan zuƙatansu na bugawa lokaci guda. "Hamdiyya" "Taaajjj" sunansa ya fito da wani irin shauƙi kwatankwacin yadda ya kirata. "Duk abin da za ki yi, ki ji tsoron Allah kada ki ɗauki alhakina." Murmushi mai kama da dariya tayi "Ba zan ɗauka ba." Tausayi ya bata ta danno wuyansa ya ƙara yin ƙasa. Ta ɗago kanta a hankali su ka haɗu. Bata sani ba ko don yau a gidansu suke babu fargabar da yake barinta da ita ta tunanin wani zai gansu. Sakin jiki tayi ta bari yana kissing ɗinta kamar ranar ya fara. Sai da zancen ya fara fin ƙarfinta ta shiga neman ƙwatar kanta. "Yunwa...yunwa nake ji Allah." Ƙarfin hali ya yi ya sake turo mata tray ɗin da su ka ture da ƙafa. Kallon duk motsinta yake yi ta rufe ido. "Ni gaskiya kunyarka nake ji. Ka daina kallona." "Ji min gulma. Ki gama tumurmu..." Hannu tasa ta toshe masa baki "ba ni bace." Taj ya kama dariya "haka ne. Mrs Happy ce." Ƙin kallonsa tayi. Saboda kunyar da ta rufar mata bata san ta loda abinci da yawa a gabanta ba. "Ni fa ba ci zanyi ba." Ya yi maganar yana bin gefen kunnenta da wuya da bakinsa. "Nima na ƙoshi." Ta matsar da tray ɗin. Abin da yake mata ya toshe duka senses ɗinta. "Cikinki duk ya cushe ko? Tashi kawai muje mu kwanta." Ya tayar da ita jikinsa. Harararsa tayi tana magana da shagwaɓa "Amma dai a tarihin angwaye kai ne ka fara hana matarka cin abinci ranar da aka kawota. Duk labarin da nake ji tura musu abinci ake yi ko basa so." "Cewa za ki yi duk na fi sauran son matata. Ba zan takuraki ba but I promise you komai dare ki ka ji yunwa ki tada ni. Zan kawo miki abinci." Da gaske...ba a taɓa cinye Taj da magana. Hankali kwance ya lauya zancen ya fitar da kansa. Abincin da ba a ci ba kenan. Ɗakinta ya rakata wanda yake da ƴar tazara da nashi ta shiga wanka shi kuma ya koma falo. Yana kwashe abincin nasu yana rausaya. A fridge ya ajiye komai inda ba za su lalace ba. Ya ɗauki robar youghurt ɗaya ya kai ɗakin Hamdi da kofi sannan ya tafi nasa ɗakin. Youghurt ɗin ta fara sha tana mamakin yadda aka yi yunwar da take ji ta ɓace. Ta gama shirinta tsaf yadda aka yi mata huɗuba a gida. Sassanyan ƙamshi yana tashi koina a jikinta. Ta kawo hijabinta har ƙasa ta ɗora akan rigar baccin da ta saka mai santsi wadda ta tsaya mata a gwiwa. Taj ma nutsuwa ya yi ya gama shirin bacci sannan ya taho ɗakinta. Wani abu ne ya bashi mamaki da yana shiryawar har ya kashe masa dukkan karsashi da ɗokinsa. Da ya saka kaya ya fesa turaruka da body spray sosai amma sam bai ji ƙamshin ko guda ba. Ya ɗauki turaren ya kara a hancinsa amma har lokacin babu. Ya koma toilet ya đaga sabulunsa wanda yanzu da yana wanka yake sake yaba ƙamshinsa sai yaji yanzu baya jin komai. Zuciyarsa wani irin harbawa tayi. Yaje ya buɗe fridge nan ma babu komai. Hankalinsa a tashe ya ɗauki kwalin juice ya kafa kai don yana son jin sanyi a zuciyarsa. Sai dai me??? Harshensa kwata-kwata babu ɗanɗano. Afuwan 🙏🙏🙏 Its late, I know. RAYUWA DA GIƁI 32 Batul Mamman💖 This page is sponsored by NAFS-BEDDINGS (Nafisa Tofa 08034581454). A trusted and reliable plug for bedsheets and duvets. A trial is all it takes to get conviced. Ƴar uwa a yar da ɗan yagwalgwalin zanin gadon nan da ya gama tashi daga wanki ɗaya a sayi garanti! * Rashin walwala da kuzarin Taj har su ka idar da sallah yasa Hamdi wasu irin tunani marasa daɗi. Me tayi masa? Ko wani abu ne ya same shi? Ko kuwa wani abu yaji wanda bai yi masa daɗi ba? Idan sun haɗa ido sai ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki. Cikin idanunsa fargaba take gani. Tayi zaton mata ko ace amare ne kaɗai su ke shiga yanayin tsoro a irin wannan dare. Ashe harda maza. Kai, amma bata zaton haka a wajen Taj. Anya kuwa irin abin da yasa zuciyarta tseren da take yi tun ɗazu shi ne a ransa? Suna zaune kowa akan abin sallarsa ta zuba masa idanu. Abu ne da bata taɓa samun damar yi ba a baya. Indai suna tare shi ne da kallon. Ko satar kallonsa ta so yi da wuya ta sami cikakken minti guda kafin ya sake juyowa. Amma abin mamaki yau da ake zaton wuta a maƙera sai aka sameta a masaƙa. Tafi minti goma tana nazartarsa bai sani ba. Daga zaune ta ja jiki ta matso kusa dashi tunda dama babu nisa tsakaninsu. Muryarta a tausashe ta ce "Wani abu ne ya faru?" "Me ki ka gani?" Taj ya faɗi yana miƙe ƙafafunsa. Sannan ya sanya hannunsa a kafaɗarta ya dawo da ita jikinsa. "Babu komai tunda baka son faɗa min." "Am fine Hamdi. Gajiya ce kawai." "Allah Ya warware. Ka kwanta kayi bacci zuwa safiya za ka ji sauƙi in sha Allah." Bata yarda ba. Kuma ta san cewa shi ma da ya faɗa ya san bata yarda ba ɗin. Neman abin cewa yake yi wanda zai kwantar mata da hankali sai wata ƙaƙƙarfar atishawa ta zo masa. Sau biyar yayi ta a jere. Kowacce ta fito sai ya ce Alhamdulillah. Ita kuma ta bi masa da YarhamukAllah. Tabbas a cikin ambaton Allah akwai rangwame ga bayi. Tun a ta uku Taj ya soma jin ƙamshin ɗakin da na jikin Hamdi sun cika ƙofifin hancinsa. To dama sihirin ba ayi shi don ya kama shi da wuri ba. Musamman Alh. Usaini ya nemi wanda zai shiga sannu a hankali saboda Taj ya zata cuta ce. Idan haka ta faru asarar dukiya kawai zai yi ta yi wajen neman magani. Babu lallai in shi ko wani nasa ba masu yarda da harkar sihiri da bokanci su yi tunanin neman karya aikin da Ayar Allah. Shi dai tunda yaji wannan ƙamshin ya tashi da ƙarfinsa ya sungumi Hamdi yana faɗin Alhamdulillah. "Wai don Allah me ya faru?" Hancinsa ya ɗora akan nata tana cikin hannuwansa ya ce "its nothing" ya kama juyi da ita. Daga nan ya manta da komai ya kuma mantar da ita. Daren ya zama tarihin Tajuddin da Hamdiyya su kaɗai. *** Wai bahaushe ya ce kayi da kanka kafin ayi da kai. Tunda Kamal ya faɗawa Yaya Kubra cewa Alhaji da Ahmad sun san da ciwonsa ta kasa samun kwanciyar hankali. Gani take kowane lokaci Alhaji zai iya kiranta. Abin da zai biyo baya kuwa sai Allah. Ilai kuwa wajajen goma na dare sai ga text ɗinsa. Bangajiyar biki ya fara yi mata sannan ya rubuta (Ki nemi izinin mijinki. Ina son ganinki gobe da safe.) Bacci ɓarawo da tarin gajiya ne su ka yi awon gaba da ita ba don ta so ba. Maigidan nata ta faɗawa komai a hali na tashin hankali. "Wallahi ba ya son ɓoye ɓoye. Goben nan ban san me zai yi min ba." "Baki kyauta masa bane kema kin sani. Ba don ya neme ki ba da nima zan nuna miki kuskurenki na biyewa Kamal. A wautarsa gata yayi muku na yin shiru. Amma a zahiri cutar kansa ya yi. Ance a problem shared is a problem solved. Bamu san ta inda za a dace ba da ya faɗa da wuri." Wannan magana ƙara dagula mata lissafi tayi. Washegari a daddafe ta jira ƙarfe bakwai da rabi tayi ta kama hanya ta tafi gida. Waya ta ɗauka ta kira Alhaji. Yayi mamakin sammakonta. "Idan kina da aikin safe ne ki wuce Kubra sai na same ki a office idan na shirya." "A'a Alhaji. Na san akan abin da kake nemana. Babu aikin da zan iya idan baka fahimceni ba." Katseta yayi da ya gane me take nufi. "Jira ni a ɗakin Kamal." "To Alhaji. Kayi haƙuri don Allah." Ta faɗi da rawar murya. Ko amsata bai yi ba ya kashe wayarsa. Yaƙi jinin ƙumbiya ƙumbiya. Shi yasa yake jan su a jiki tun basu da wayo. Ko fensir wannan bai yarda wani ya zo ya ce wane na buƙata ba. Ya fi son ka je da kanka ka faɗa. "Ban faɗa masa komai ba." Kamal ya tabbatar mata da ta shiga ɗakin. "Nafi tunanin gaya min zai yi. Gara da na faɗa masa gaskiya a waya don ban san yadda zanyi na fidda kaina a gabansa ba." Sai bayan kimanin minti sha biyar Alhaji ya shigo tare da Bishir da Abba. Kana ganinsu ka san basu san me yake faruwa ba. Sun dai kama bakinsu tunda sun san koma mene ne yanza za su ji. Ita dai Yaya Kubra tana haɗa ido da Alhaji ta sunkuyar da kai. Daga daren shekaranjiya zuwa yau ya faɗa. Dakakkiyar shadda ce a jikin shi ruwan toka. Babbar rigar a ninke Abba ya rataya a hannunsa. Kwarjini iya kwarjini sai Alh. Hayatu. Da kakkausar murya ya ce mata "Kin kyauta." "Alhaji don Allah..." ta fara cewa tana zamowa daga kan gado. "Ya isa." Ya zauna a inda ta tashi. Yaran nasa su ka zagaye shi a ƙasa banda Kamal da ya hana motsawa daga kan kujera. "Wace gudunmawa shirunki ya sama min?" Iya bincikenta na ƴan uwansu na kurkusa (gidansu Alhaji da Hajiya) ta sanar dashi. Abin al'ajabi cikinsu babu mai blood group AB(-). Ana bikin Taj ta tura musu survey link na google form inda ta buƙaci su cike da cewar research (bincike) ne take yi da ya shafi aikinta. A ciki tayi tambayar da mutum sai ya saka sunan dangin da ya fito. Ta haka ta rarrabe kowa. "An sami masu rhesus negative mutum huɗu." Alhaji ranƙwafowa yayi kamar da haka ne zai ji me za ta ce sosai. "Biyu ba za su iya yi masa amfani ba domin ɗaya A ne, ɗayar kuma B." "Ina jin ki Kubra." "Masu O negative biyu da za su iya taimaka masa, ɗaya ɗiyar ƙanwar Hajiya ce." "Mata suna iya bayarwa ne?" Alhaji ya tambayeta hankalinsa a tashe. Bishir da Abba su ka sake shiga duhu. "Eh, amma...amma da wuya a samu nata. Widad ce. Yaranta biyu tana da cikin na uku" Yaya Kubra ta faɗi, ita ma kanta tana cikin jin ciwon hakan. Kamal ya dube su. Irin wannan abin yake gudu. "Alhaji don Allah..." "Ka rufe bakinka Kamal" ya tsawatar masa. Ya juya ga Yaya Kubra "Sai wa kuma?" "Ɗan Widad ɗin na farko mai shekara biyar. Yayi ƙanƙanta." "Wai me ake buƙata ne Yaya Kubra?" Abba ya gaji da jin maganar da bai fahimta ba kuma yana ganin masu yinta cikin rashin nutsuwa. "Ƙoda ce Abba. Duka ƙodojin Kamal ciwo ya cinye su." Alhaji ya bashi amsa da kansa. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Abba da Bishir kuka su ka fashe dashi. Alhaji ko hanasu bai yi ba. Kowanne yana cewa a cire tashi. Da su ka ji ba da ka za a ɗauka ba nan ma sun sake shiga tashin hankali. Kamal mai ciwon shi ya koma rarrashinsu. "Amma fa ni ban gane ba. Me yasa masu A da B ba za su iya bashi ba, bayan kuma su ma ɗin negative ne? Jiya fa nayi ta bincike Kubra. A da B duka donors ne." Cewar Alhaji da sanyin jiki. "Haka ne Alhaji. Mai B ɗin sickler ce." Alhaji ya ce "Ita ma mace? Bana ma son a kai ga ɗaukar na mace. A ɗin fa?" "Ɗan Kawu Sayyadi ne (ƙanin Hajiya). Shi kaɗai ne bayan mu nan wanda ya san da ciwon Kamal. Naje na same shi. Ban ko roƙa ba ya ce a shirye yake da aje a cire tasa. Shekaranjiya kafin naje wajen bikin test muka fara zuwa aka yi masa." Ta ja numfashi sannan ta ce "yana da Hepatitis." "A taƙaice dai ...Ya Rabbi....Allah na" Alhaji ya danne ƙirjinsa da ya kama wani irin ciwo. Duka su ka rufar masa. Yaya Kubra ta tashi zata koma mota don motar likita ba ta rabuwa da kayan bada kulawar gaggawa. "Dawo ki zauna." Alhaji ya tashi ya dafa kafaɗar Kamal "akwai Allah kaji ko." Ya dubi Abba "ka haɗa muku kaya kai da Kamal akwai jirgi gobe. Yanzu zan sa Ahmad ya sayi ticket ku tafi Saudiyya." "Alhaji ni fa? Me zan yi?" Bishir ya tashi tsaye da zafin nama yana goge ƙwalla. "Tare zamu bisu jibi da Ahmad. Bana son iyayenku su gane komai. Kawai zan ce musu Umra zamu ni da yarana maza." "A nan za ku barni Alhaji?" Yaya Kubra ta soma sabon kuka. "Kina da visa ne?" Da sauri da amsa cewa akwai "ki tattaro komai na asibitinsa a wajen Dr. Mubina jibin sai mu tafi. Ki san me za ki faɗawa iyayenki tunda kin ƙware a rufa-rufa." Kai ta sunkuyar. "Me zan faɗawa Taj?" Kamal ya yi tambayar ga Alhaji. "Zai yi zargin baka haƙura ba shi yasa baka haɗa da shi ba." Inji Bishir. Alhaji wayarsa ya ɗauko daga aljihun gaban rigarsa ya dubi lokaci. Yayi wuri ya kira mai sabon aure. Sai ya ce da Kamal, "Ka faɗa masa zamu je Umra amma ba da shi ba. Yaje ya yiwa matarsa passport a nemi visa a sanar dani sai su tafi daga baya." Da ya fita ya kulle musu ƙofar ɗakin sai ya sami damar barin zazzafar ƙwallar da ya danne a gaban ƴaƴansa saukowa. Sau ɗaya ya haɗa ido da Kamal yaga yayi masa murmushi na wanda ya karɓi ƙaddararsa hannu biyu. "Ya Allah ban isa ba. Ba iyawata bace ta bani ƴaƴan nan. Allah nagodewa ni'imominKa gareni. Da rauni da gazawata na zo gareKa cikin ƙanƙantar da kai. Ka ceci rayuwar ɗana Ya Ubangijina." Bayan shekaru masu ɗimbin yawa ya sami kansa da fashewa da kuka mai ciwo da cin zuciya. Yana ƙaunar ƴaƴansa kamar rai. Waɗanda ya rasa a ɓari da biyu da su ka tafi da ƙananun shekaru har yau yana jin abin a ransa. Tsayuwarsa ya yi a wajen yana neman nutsuwa amma idan ya tuna haƙuri irin na Kamal sai yaji zuciyarsa tana zafi. Duk gidan shi ne yafi kowa damunsa akan maganar Taj. A dalilinsa ya haƙura ya bar iyalinsa suna mu'amala da Taj ɗin. Domin da fari niyarsa ya yanke shi daga jikinsa gabaɗaya. Ƙofar ɗakin Yaya Kubra ta zo da shirin fita taji sautin da mahaifinta yake dannewa. Bata san lokacin da ta koma da baya ta ɗora kukan ba. Abba da Bishir su ka kara kunnuwa su ka ji. Kowa ya koma ya zauna da kuka. Shi kuma ya koma ciki ya shige ɗaki ya rufe ƙofa. "Magana ake ta Kamal yana da rai har yanzu. To me hwaru?" Kamal ya faɗi yana dariya. "Ni ban taɓa tsanar wannan kalmar ba sai kamar yau." Abba ya sha kunu. Yaya Kubra tayi murmushi "dole ka sako wasa kafin Taj yaji wannan maganar." "Don Allah ki bar tayar min da hankali. Da me kike so in ji? Ciwon ko tararrabin abin da zai zo yayi?" *** "Siyama kin tabbatar duk abin da Iyaa ta faɗa min gaskiya ne?" Yadda Baba Maje ya ɗauki zafi sai da gaban Siyama ya faɗi. Ta dai san cewa ba gulma ta kawo ba tunda cutar da mutum taji za ayi take son hanawa da ikon da Allah Ya bata. "Da gaske ne Baba." "Kirawo min Ummin" Tashin muryar iyayen nata ne ya fito da ita daga ɗaki inda taji Baba Maje na rantsuwar sai ya karya Ummi. Iyaa kuma tana tare shi. Da ƙyar ta samu ya nutsu shi ne ta ce masa, "Taurin kai gareta ka sani. Idan baka bi komai a hankali ba wallahi ko me zai faru ba faɗin gaskiya zata yi ba." Bai daina faɗan ba sai dai ya haƙura da zancen zuwa ya tasheta da duka. Hankalin Siyama sai ya tashi shi ne ta fito yake tambayarta. "Ita hayaniyar nan bata tasheta ba?" Ya faɗi yana girgiza ƙafa da kallon ƙofa. "Yanzu zan taso maka ita. Amma don Allah ka bi komai a sannu." Ɗakin nasu Iyaa ta shiga ta taso Ummi. Har ta fara kiran bacci bai isheta ba Iyaa ta daka mata tsawa. Haka ta biyota tana zumɓura baki. A zatonta aiki ne za a saka ta. Sai gata tayi ido huɗu da Baba da su ka sauko ƙasa. "Ke Siyama hau sama ki ɗauko min wayar Ummi." Firgigit duk wani baccin iya shege da hammar ƙarya su ka gudu. "Wayata Baba? Ke tsaya Siyama." Siyama ta dakata. Baba ya zaro mata idanu ta kama bin bene ba shiri. "Baba me nayi? Don Allah kada ka duba min waya." Ummi ta juya za ta hau benen. "Ki ka kuskura ki ka hau benen nan sai nasa Baballe ya karyaki." Cak ta tsaya "Baba me nayi?" Bai kulata ba don bata cancanci hakan ba har Siyama ta sauko ta bashi wayar. "Ɗakinku ɗaya. Ki faɗa min gaskiya, akwai wata ko babu?" Mugun kallo Ummi ta watsawa Siyama. Ita kuma jikinta ya ɗan yi sanyi. Iyaa ta ce "Baki ji me aka ce miki bane?" "Akwai" "Ɗauko min." "Baba don Allah..." Ummi ta zube a ƙasa tana magiya. Abubuwan dake cikin wayar dake ɗakin sun fi ƙarfin me wayar. Dukkan wata mu'amalarta ta waje da fitintinunta suna ciki. Ba jimawa Siyama ta sauko saboda a ƙasan filo Ummi ta ajiyeta da ta raba dare tana dannata jiya. "Zan saurari Habibu don nayi imanin indai wani abu ya faru gidan ƴaƴansa ba zai ɓoye min ba. Idan abin da Siyama taji kina ƙullawa ya tabbata to ki kuka da kanki. Sannan in ki ka saka ƙafa a ƙofar gida to kada ki dawo na yafeki." Ya kalli Iyaa da Siyama "duk wanda ya bata aron waya ba da yawuna ba." Wayoyin ya kashe a gabanta ya tashi ya shige nasa ɗakin. Ummi ta rasa gane kuka ya kamace ta ko me. Abin da yake taso mata yafi ƙarfin hawaye ko kalaman da take jin tana son zazzagawa Siyama. *** Ahmad ya so ƙwarai ya kira baban Salwa akan ya turo a ɗauketa. Da wannan niyar ya shiga ɗakinta inda ya mayar da Mami bayan tafiyarsu Anti Zabba'u ya shiga da ya gama wayar. Ɗakin wari yake yi mai ɗauke numfashi. Ya yi mata kallo ɗaya ya juya. Nan ya barta tana so tayi kuka amma bakin ma ya karkace sai dai hawaye kawai. Kallon da yayi mata na takaici ne da baƙincikin halin da ta saka kanta kuma su ma ta jefa su. Mami bata da kowa sai ƴan uwa waɗanda ta jima da barranta kanta daga garesu saboda abin duniya. Bata zuwa sabgar kowa sai dangin dangiro da abokan arziƙi masu kuɗi. Jininta dai ta datse zumunci da rashin mutumci saboda ita tana gidan mai kuɗi. Yau ga ranar ƴan uwa amma babu wanda zai nema ya taimaka masa da kula da ita. In ya ɗorawa Zahra wankin kashi da fitsarinta ba ƙaramin rashin adalci hakan zai zama ba. Yau da gobe sai Allah. Gashi Mamin a baya bata nuna mata ƙauna saboda akwai wadda ta so ya aura. Wannan tunanin yasa shi fasa neman Salwa ta tafi. Ita ce mace kuma dolen Mami. Zai saka mata ido kafin ya sami wadda zai dinga biya. Shawarar da ya yanke ya faɗawa Zahra. Ta bashi goyon baya da alƙawarin za ta dinga taimakawa ita ma. "Ni ban san me yasa ka damu da komawarta ba tun farko. In don Taj ne ina ganin yanzu ai ta haƙura." "Ke dai ayi shiru kawai. Allah Yasa ta haƙura ɗin. Ni dai duk ranar da ta fita daga gidan nan idan bana nan ki kirani." "In sha Allah" Taɓe baki Salwa tayi. Zancen ba a bayan idonta ake yi ba. Tana kitchen kuma suma sun san tana jinsu. Ba za ta nuna ɓacin rai don an barta zaman jinyar Mami ba. Za ta kwantar da kai ta bi Ahmad sau da ƙafa domin zamanta a gidan shi ne babban hujjarta da rufin asiri a Kano. Kafin nan dai da lokacin aurenta da Taj dole tana buƙatar gidan zama. Idan yaso in tayi aure sai taga wanda Ahmad zai ɗorawa aikin Mami idan ba Zahran ba. Wayar Ummi ta sake kira bata samu ba. Ta doka tsaki ta ajiye wayar ta cigaba da wanke wanke. *** Tsaye tayi a ƙofar banɗakinta dake cikin ɗaki tana kallon sauyin da gadon ya samu. Taj ya canja bedsheet ya gyare gadon. Halin da take ciki na ciwo da zazzaɓi bai hanata yaba kyawun setin american bedsheet da duvet ɗin da ya shimfiɗa ba. Navy blue da red flowers ne a jiki wanda kalar farkon ta dace da ta labulen ɗakin nata. Ita kam me za ta ce da Inna? Duk wani abu da uwa za ta yiwa ƴa ita ma anyi mata na gata. Akan sayen zannuwan gadon Inna da kanta ta kira Yaya ta faɗa mata sun saya a wadace. Indai ba akwai wanda ta tanada ba tuntuni to kada ta sayawa Hamdin wasu. Bayan wannan wayar sai ta turo aka kawo guda shida. Duvets biyu, normal bedsheets huɗu ta ce a rabawa Sajida da Zee. Sajida ta dinga murna kuwa da taga sunan dake jikin ledar. "Ni fa a instagram nake following ɗinta (@nafs_beddings). Ashe zan ga kayanta zahiri." "Kyau garesu ko me?" Cewar Zee da bata san murnar me take yi ba. "Kyau ma ai faɗar ɓata baki ne. Ki je shafinta ki gani. Ina maganar quality ne. Ki taɓa ki san kin haɗu da kayan ƙwarai ba jabu ba. Yadin sam ba ya tashi ki ga yayi kurajen nan kamar pimples a fuskar budurwa." Hamdi bata manta yadda su ka dinga dariya ba. Sai yanzu ta gane ashe dai da gaske ne maganar Sajida. Zama tayi tana shafa laushin duvet ɗin tana jindaɗin mallakarsa. (Kamar kullum ni ɗin ganau ce don har baby Ahmad na sayawa baby set a wajenta. Kayanta speak for themselves. Don Allah ku nemi Nafisa Tofa 08034581454 ku rabu da jabon zannuwan gado.) Kwanciya tayi ta rufe jikinta. Bata ji motsin Taj ba. Ta dai yi tunanin ƙila yana nasa ɗakin. Gara ya yi zamansa a can. Bata son abin da zai sake janyowa su haɗa ido. Tashinta da yayi da asuba ma don babu yadda za ta yi ne. Zancen zuci ta cigaba da yi wanda gabaɗaya ya ƙare akan baƙuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki jiya. Taj ya nuna mata so da ƙauna kamar ya haɗiyeta. Wata zuciyar ta ce mata ya kuma saka ki kuka kamar zai ƙarar miki da hawaye ba. Tunaninta na kaiwa daidai nan ya buɗe ƙofar da sallama ya shigo. Da sauri kuwa ta sake yin ƙasa da kanta ta rufe ko ina. Taj murmushi ya yi ya je bakin gadon ya soma buɗe lulluɓin da tayi. Bata bari ya gama ba ta kama duvet ɗin da nata ƙarfin. Sai ya saki, ya hau gadon daga gefenta ya turata ciki ta hanyar matsawa yana rufa shima. "Matsa min, matsa min" ya dinga faɗi har su ka koma tsakiyar gadon sannan ya daina turata. "Me ya hana ki bacci? Ko jirana kike yi?" Ya yi maganar yana rungumota gabaɗaya a ɓangaren damansa. Hamdi ga tsoro ga tsiwa, ta haɗa biyun ta ce, "In jira ka kayi min me?" Da rawar murya. Taj ya yi dariya "Hamdiyya matar Malam Tajo. Maida wuƙar ni ba wani abu nake nufi ba." "Waye kuma Tajo? Ɗan uwanku ne?" Ta harare shi. "Ni ne shi, shi ne ni." Ya nuna kansa. Hamdi ta yamutsa fuska "A'a gaskiya." "To ke ce shi, shi ne ke?" "A'a fa." Ta ƙara da tura baki. Abin ya burge shi ya kwanta a jikinta "To ya abin yake?" Murmushi tayi na kunya "Ni ce kai, kai ne ni...shi kuma Tajo bamu san shi ba." "Taj ɗin ma in kin ce baki san shi ba sai a siyo rago a saka min sabo." Ya faɗi maganar da wani shauƙi dake kwasarsa saboda shagwaɓar Hamdi "duk yadda kike so haka za a yi Mrs Happy." Wani sabon shafin ya so a buɗe ta ce sam bata san zance ba indai ba sumar da ita zai kuma yi ba. Ya dinga yi mata dariya. Su na ƴar hirarsu har bacci ya sake kwashe su. Ba su su ka farka ba sai da aka kira Taj. Ƙanwarsa ce wadda a jerin haihuwarsu bayan Kamal sai shi sai kuma ita Rawda. Abincin amarya da ango na sati guda ta ɗauki nauyi saboda gidanta yafi na kowa yin kusa da na Taj. Kullum safe, rana da dare take turo yaron gidanta ya kawo a babur. Amarya da ango su ka sake samun lokacin shaƙuwa da sabo da juna. Taj ya bar Happy Taj a hannun yaransa. Sai Abba Habibu dake zuwa amma ba kullum ba. Taj yayi yayi ya ɗauki hutu amma yaƙi. Wata irin soyayya Taj da Hamdi suke yiwa juna wadda bata da shamaki ko basaja. Sak su ka fitowa juna tun farko, shiyasa alaƙar tasu tayi saurin ƙulluwa. Jin junansu suke yi tamkar tare da soyayyar juna su ka tashi. Ga Taj gwanin zolaya wadda a sati gudan nan Hamdi ta koya. Duk baƙon da ya shigo gidan sai ya fita da murmushi saboda nishaɗin da zai samu daga masoyan. Abu biyu ne su ka so damun Taj amma dalilai sun sa basu yi tasiri ba. Na farko tafiyar su Kamal Umra bagatatan ko haɗuwa basu yi ba. Yayi mita kuwa kamar ya ari baki. A ranar da su ka tafi wadda ta kasance kwana biyu da tarewar Hamdi, da yamma ya tafi gida bayan wayar sallamar da Kamal ya yi masa daga cikin jirgi. Cikin farinciki su ka gaisa da su Umma kafin ya hau sama da aka yi masa iso wajen Alhaji. Gaishe shi ya duƙa yayi Alhaji ya miƙa masa hannu yana girgiza kai. "Kai ka san ba haka nake gaisawa da ƴaƴana ba." Da sauri Taj ya tashi ya ƙarasa gaban Alhaji ya miƙa masa hannu. Alhaji yayi murmushi sannan su ka zauna. "Ina matar taka?" Kai a ƙasa yana susar ƙeya Taj ya ce "tana gida. Ta ce na gaishe ku." "Ina amsawa idan da gaske kake." Rantsuwa Taj ya fara sai yaga Alhaji yana murmushi. Da alama dai yayi furucinsa da zolaya ne. Sannan babu shakka yana sane da abin da ya yiwa Abba Habibu ya ɓata ran Hamdi. Ba dai zai ɗauko zancen ba saboda ba shi ya kawo shi ba. Yana da mahimmancin da shi ma zuwa da zama na musamman ya dace da shi. "Alhaji maganar Kamal ce ta kawo ni." "Kayi aure Taj. Bai kamata ka zauna kana ƙunƙuni don ya tafi ba tare da kai ba. Ya dace ka fara sanin ragamar rayuwarka da ta ƴar mutane ce a wuyanka yanzu. Ba dole bane Kamal ya daidaita tafiya da kai ba." "Ba haka nake nufi ba" cewar Taj Tausayi ya bawa Alhaji yadda ya yi maganar. Shi kuma ya katse shi ne kawai saboda baya son hankalin Taj ɗin ya kai ga abin da ake ɓoye masa. "To ina jinka." Shiru Taj yayi. Alhaji ya sami kansa da yin murmushi. Yayi matuƙar kewar Taj da halayansa. Idan kayi masa faɗa alhali bai yi laifi ba, haka zai yi ta marairaicewa sai ka koma rarrashinsa ko babu niyya. "Ashe baka canja hali ba har yau? Mijin aure fa kake." "To ai ba maganar tafiyar nazo yi ba. Duk da dai naji haushi. Ko ba a je dani ba da sai a faɗa min. Ɗan Adam ba ya rasa buƙatu a wajen Allah." "To ka roƙa mana a inda kake. Allah Yana ko'ina." "Amma dai ba kamar idan ana shafa Ka'aba ana ambaton suna na da buƙatuna ba ko Alhaji." Sake faɗaɗa murmushi Alhaji ya yi. Ya dubi Taj ya ce "welcome home." Tsabar daɗin da Taj yaji bai san lokacin da koma kusa da Alhaji ya rungume shi ba. Alhaji ya gama basarwa amma a ransa daɗi yake ji. Da ya nutsu ne ya faɗa masa ainihin abin da yake tunani. Yana magana Alhaji shiru kawai yayi. Daga dawowa gida, bayan kwana biyu da tarewar matarsa ya zai yi idan yaji ciwon da yake damun ɗan uwa mafi soyuwa a gare shi? "Baka yarda da ilimin Dr. Mubina ɗin bane har kake tunanin wani ciwon ne yake damunsa?" "Ba haka bane Alhaji. Ban sani ba ko idanuna ne amma har wani kumburi naga yayi rannan. Yanayin bai yi kama da ƙiba ba." Shi da baya son ɓoye abu bai san dalilinsa na son bawa Taj ɗan lokacin samun farincikin aurensa ba kafin ƙwai ya fashe. "Yanzu mece ce shawararka?" "Idan kun tafi don Allah ka tilasta masa zuwa asibiti. Idan da kai ne dole zai je ayi masa thorough check up." Alhaji ya yi murmushi don ya ɓoye halin da yake ciki. "In sha Allahu zamu je." "Nagode." Ya dinga faɗi har ya fita. A zuciyarsa yana mai fatan Allah Yasa babu komai. To tafiyarsu Alhajin ne kuma sau biyu ya sake samun kansa a yanayi na ɗaukewar jin ƙamshi da ɗanɗano. A na biyun da ƙyar ya iya ɓoyewa Hamdi ya shiga ɗaki yayi ta bulbula turare kafin daga baya abin ya daidaita. Ranar da ya tasar masa na ukun kuwa ana gobe za su yi sati ne. Saboda tsabar tashin hankali, yadda yaga rana haka yaga dare. Cikin tsananin kiɗima ya zame jiki daga wajen Hamdi ya koma falo ya kira Kamal a waya. RAYUWA DA GIƁI 33 Batul Mamman💖 This page is sponsored by spicesbyMrsghaleetk....yep, MRS GHALEE TK. Nace ba, wai kina cikin masu cewa girki da spices baya daɗi? Ko kuwa kin saba saya kina bari ya siƙe a kitchen saboda baki gane ɗanɗanon da yake bayarwa ba? Albishirinki, Mrs Ghalee TK dai za ta yi Ramadan promo. Dama ce ta samu gareki wajen sayen ingantattun kayan girki masu tallafawa cefane musamman a wannan marra ta tsadar kayan abinci. Ke dai ƴar uwa, harma da ɗan uwan da ya saba taimakawa iyayensa ko matarsa, ko kuma mai son burge iyali, ku yi tanadi don Mrs Ghalee TK ta zo da rangwame domin gyara tukwanenku. Ku sai ku garzaya ku nemeta akan wannan layin ta manhajar whatsapp ko kiran waya 08032834178. Taku ce Batul Mamman, ganau akan kayayyakin da nake tallata muku. *** A cikin yanayin ciwo da gajiyar jiki Kamal ya buɗe idanu ya miƙa hannu zai ɗauki wayarsa. A gadon asibiti yake inda yake samun kulawa ta musamman. Da yake dokar asibitin ba a zaman jinya, shi kaɗai ne a ɗakin. Alhaji da su Ahmad suna hotel kusa da asibitin. Tafiyar just ƙafa ke kawo su. Tare dashi su ke wuni sai takwas na dare idan an buƙaci duka baƙi da masu ziyara su fita sannan su ke tafiya. Kwanaki goma aka bashi ya gama shan magani da allurai kafin a fara dialysis. "Happy lafiya dai ko?" Ya ce cikin bacci da firgici domin kuwa ukun dare harda kwata lokacin. Kamar an tsunkuli Taj ya ɗaga kai ya kalli kyakkyawan agogon bangon falon. Baki ya buɗe gami da girgiza kai. "Don Allah Happiness kayi haƙuri. Kasan Allah ban duba time ba. Ashe past one. A nan uku ta wuce ko?" Kamal ya gyara zama ya ce "Eh...mene ne ya faru? Haka kawai ba za ka manta lokaci ba." "Gobe sai muyi magana in sha Allah. Am very sorry." Taj ya ce har zuciyarsa. "Taj" Kamal ya kira shi da ɗan ƙarfi "me ya faru?" Roƙonsa Taj ya fara yi akan ya jira safiya don har ya katse kiran amma ya sake kiransa. Su ka ɗan yi ja'inja ɗinsu sannan Taj ya faɗa masa abin da yake faruwa dashi game da ɗaukewar ɗanɗano da jin ƙamshi ko wari wasu lokutan. "Zuciyata tana bani Covid ce. Nayi browsing naga ɗaukewar sense of smell da taste suna cikin symptoms ɗinta. Ni bana mura amma bayan magrib ina ƙirgawa sau bakwai Hamdi tayi atishawa." Kamal yayi ƴar dariya "sannu Doctor." Taj ya ɓata rai "Happiness its not funny." "Na sani. Shi yasa nake mamaki da kana zaune a gida ka yankewa kanka cutar dake damunka." Murmushi ne ya kama shi. Tabbas asibiti ya kamata yaje amma fargaba ta hana. Ba kuma kansa yake jiyewa tsoro ba. Idan ta tabbata yana da corona shikenan Hamdi ma ta samu. Daga tarewa ya haɗata da ciwo. "Gobe zan je in sha Allah. Thank you and sorry." Sai da safe suka yiwa juna. Kamal ya ce yana jiran jin sakamakon idan ya dawo daga asibitin. Da ya koma ɗakin a dunƙule waje guda ya sami Hamdi. Ta dawo tsakiyar gadon tana baccinta hankali kwance. Sama ya kalla ya sake yin addu'ar da ya wuni yana yi. Allah Yasa ba covid bace. Idan kuma ita ce yana fatan Hamdi bata samu ba. Sai dai abin da kamar wuya. Yadda su ke manne da juna ana amarci ai taimakon Allah ne kawai zai hanata kamuwa. Kwanciya yayi a can gefe. Ko minti biyu bai yi ba yaji Hamdi a jikinsa ta ɗora rabin kanta a ƙirjinsa. Wani ɗan murmushi yayi ya sake shige mata har yayi bacci. *** Yawan kallon wayar da Kamal yake yi ne yasa Alhaji tambayarsa kira ko saƙon wa yake jira. Shi kuwa ya faɗa masa yadda suka yi da Taj a waya. "Result ɗin nake dubawa ko ya turo." Shiru Alhaji yayi na wani lokaci yana tunani kafin daga bisani yace idan ya faɗa masa yana son ji shi ma. Zuwa la'asar kuwa bayan Taj ya turo ya faɗawa Alhajin cewa ba corona bace. "To Alhamdulillah. Ince dai bai hanaka faɗawa kowa ba? Zan kira shi nayi masa ya jiki." Da jindaɗi Kamal ya ce Taj bai hana ba. Alhaji bai tashi kiran Taj ba sai bayan sun koma masaukinsu ya shiga ɗakinsa. Bayanin yadda yake ji ya buƙaci ya yi masa. "An baka magani?" "Eh Alhaji. Sun ce stress ne kawai" "To Allah Ya ƙara lafiya. Ciwon da ya shafi harshe da hanci a wajenka ba abin ɗauka da wasa bane duba da irin sana'arka. Ka mayar da hankali wajen shan magani." Taj ya yi godiya yana cike da murnar wannan kulawa ta Alhaji. * Wando ne tight ruwan zuma a jikin Hamdi. Jikinsa yana da wani irin laushi ga rashin nauyi. Ta ɗora shirt ɗin Taj baƙa mai maɓallai a gaba da dogon hannu. Maɓallan gaban guda huɗu ne kaɗai a ɓalle ta bar na farkon. Hannuwan kuwa tsayawa tayi naɗe su har dantsen hannu. Ga gashinta da bata taje ba ta tattara tayi packing bai shige sosai ba. Fuskarta ko ɗigon kwalliya babu. Sai ƙamshi kamar a ɗauketa a gudu don daɗinsa. Duka wannan saurin shirin saboda sun gama sati yau za ta fara shiga kitchen ne. Ta kwana tana tsara me za ta dafa saboda baƙin da zasu yi daga gidansu Taj. Shi kuma kawai yana tashi ya ce ta faɗa masa me take son dafawa. "Ki kwanta ki huta in dafa." "Ka dafa?" Ta juya tana kallonsa "ni ce fa amaryar." "Ni kuma angon amarya ba." "Girkin nawa ne baka son ci ko baka yarda dashi ba?" "Taimako ne fa kawai. Besides na gaji da zaman nan. I miss my kitchen." Wata uwar harara ya samu wadda ta sanya shi tuntsirewa da dariya. "Me kuma nayi? To ki bar min aikin duka idan rabawa ne ba kya so mu yi." "Yanzu don Allah baka san kowacce amarya jiran wannan ranar take yi ba? Ranar da za ta fara yiwa mijinta girki. Sai kawai kace in bar maka kayi?" "Nayi zaton murna za ki yi fa. Ki ce yau ga ranar auren Taj" ya ɗage gira. "Ni kuma to da me zan burgeka? Girki a wajen mace ni dai a wajena abin alfahari ne." Hamdi ta ce idanunta a kan shi. Hannunta ya kama su ka shiga kitchen ɗin. "Ke ce sarauniya a nan. Ni kuma bafade mai neman suna a wajen uwarɗakinsa." Murmushi Hamdi tayi. Ta buɗe store Taj yana kallonta shi ma yana murmushi. Juyawa tayi ta kalle shi "kada in yi shinkafa da miya ko? Its too common." "Dafa shinkafar ki bar min miyar. Sai in yi chicken curry maimakon stew da potato salad." Abin da take ta gudu da alama dai shi zai faru a gidan nan nasu. Girke girken ƙwalisar da ta koyo a wajen Abbanta ƙarshenta duk ba za su burge shi ba. "Na fasa ma. Kullum shinkafa ake ci. Naga akwai macaroni shape daban daban..." Don tsokana kawai Taj ya ce "ni yanzu ba abin in ce miki pasta ake cewa ba ki ji haushi. Macaroni is just a type of pasta." Hamdi ta sha kunu shi kuwa ya ɓoye dariyarsa. "Ka gama faɗa ai, wato ko fashewa zan yi babu ruwanka?" Laɓɓansa ya ɓame gami da alamar yiwa bakinsa zip. Ita kuma da yake tana son yin shawara dashi don kada tayi gaban kanta sai ta sake yi masa tambaya. "In dafa ita pasta đin?" Allah Ya sani ya ma manta, bai san lokacin da ya ce "Ki zauna in yi musu creamy chicken pasta kawai." "Na fasa." Rarrashinta ya kama yi "dafa abin ki, ba zan saka miki hannu ba." "Naƙi wayon. Ban ma iya ba." Fushin nata da ture turen baki dariya su ke bashi. Ya dai bata haƙuri ya ce kuma ba zai kuma magana ba. "Tuwon shinkafa ma zan yi." Ta faɗi da murna don tana tunanin baya cikin abin da ya ƙware. Store ɗin ta shiga da wuƙarta a hannu za ta buɗe buhun shinkafar tuwo. Shiru Taj bai ce komai ba har ta soma farke buhun sai ta ɗaga kai ta kalle shi. "Don Allah baka iya tuwo ba ai ko?" "Uhmm" ya faɗi yana rufe baki. Ga mamakinsa kawai sai Hamdi ta ajiye wuƙar a kan buhun ta fito ta zauna akan wata kujerar kitchen a gefen sink mai ɗan tsayi ta kama kukan shagwaɓa. "Ban iya tuwo ba. Don Allah ki yi shiru. Da gaske ban iya ba." Taj ya ce a rikice. Da dai ta san ta kunna shi da kukan sai taƙi dainawa. Yana lallaɓata tana mita. "To ni da me zan burgeka? Me yasa ka iya komai? Mene ne baka iya ba?" "Ban iya ɗan wake ba" ya faɗi da sauri don ta daina kukan. "Ahaaa...ashe ka iya tuwon" tayi maganar tana jinjina kai. Sai lokacin ya fahimci me tayi. Dole ace mata daban suke. Ƴar ƙaramar yarinya tayi masa wayo. "Ai ba sosai na iya ba. Ɗaki ma zan tafi har ki gama." Ya saketa zai fita. Hannunsa ta kamo ya tsaya suna kallon juna. "Allah so nake na dafa maka abin da baka iya ba. Wanda in kaci za ka yaba min da zuciya ɗaya." "Come on Love, ko me ki ka dafa kin san zan yaba." Ya rungumeta yana shafa mata kai. "Honest review nake so. Ka yaba har zuciyarka ba don naji daɗi ba kawai." "To shikenan. Maganar gaskiya na iya tuwo amma ban fiye yi ba." "Da gaske don Allah." "Da gaske." Da murnarta ta nuna masa ƙofa "To ka tafi falo ko ɗaki ka huta." "Ranki ya daɗe duba fridge ɗinki dai ki tabbatar babu abin da ki ke buƙata." Da wani rangaji duk na jindaɗin cewa bai iya tuwo ba sosai ta tafi ta buɗe freezer. Nama kala-kala akwai. Ga kayan miya da aka wanke aka ɗaɗɗaura a ledoji. Ɗaurayewa kawai zata yi tayi blending. "To idan babu takura don Allah ina da saƙo." "Yes Ma. Me kike so?" Ya tashi yana sauraronta. Ganyen ugu da alayyahu ta buƙata daidai yadda take jin zai isheta yiwa mutum biyar da za su zo da kuma su na gidan abinci. Bayan fitar Taj a bincikenta na store taga kwali na kayan annurfoods. Ta buɗe ta ɗauko garin tsaftatacciyar niƙaƙƙiyar farar shinkafa. Ta fito ta ɗora ruwan tuwo sannan a wata tukunyar ta ɗora nama. A ruwan tafasar bayan ta saka maggi da gishiri, sai ta sanya paste ɗin citta da tafarnuwa. Ta kawo mixed spices, da garin lawashi duka na Mrs Ghalee TK ta zuba. Ya kusa dahuwa ta zuba yankakkiyar ganda ƙanana da aka zuzzuba a zip lock aka ajiye mata. Sannan ta kawo albasa ta yanka da girma ta zuba. A gefe kuma ta tafasa kifi sama-sama a wata tukunyar ta ciccire ƙayar ba tare da ta fasa tsokar sosai ba. Tana yi tana azkar cikin kwanciyar hankali. Tana tuƙin tuwo Taj ya dawo. Tayi masa sannu da zuwa ya sami wuri ya zauna. "Kada ki koreni please." "To kada ka taɓa komai." "No problem." "Kuma kada kayi magana" Alamar yiwa baki zip yayi. Ya zauna yana kallon yadda take komai cikin ƙwarewa da kazar kazar. Duk motsinta burge shi kawai yake yi. Ta dami kanta akan iya girkinsa da tsoron kada ta gaza ta wannan fannin a idonsa. Bata san shi kuma cikar buri yake gani ba a tare da ita. Samun matar da ko bata iya girki ba za ta ƙoƙarta tayi masa a matsayinsa na mijinta ba ƙwararren mai sana'ar girki ba. Shi ma yaji shi isasshen namiji a cikin gidansa. A flask mai kyau ta jera tuwon da ta ƙulle a farar leda. Taj ya ɗaga hannu tamkar a aji. Hamdi ta yi murmushi. Dama ta san ba shirun zai yi ba. "Ina jin ka." "Tuwon mene ne wannan don Allah?" Ta faɗa masa. Yace bai san ana yi ba. Sai ya kuma wata tambayar. Yana so ta faɗa masa miyar me za ta yi. "Miyar ganye." Bai ƙara magana ba sai da yaga ta gama yanka ganyen daban daban ta wankesu da kyau sannan kowanne ta ɗora a tukunya daban da ruwa kaɗan. Za ta kunna wutar taga alamun zai yi magana sai ta dawo gabansa ta tsaya ta duƙar da kanta. Yayi zaton magana za ta yi. Sai ta shammace shi tayi kissing ɗinsa. "Na rufe maka bakin nan. Don Allah kayi shiru. I want to surprise you." "Surprise ya wuce wannan?" Ya taɓa bakinsa "ai kawai ki kashe wutar ki zo in baki tukwici." Guje guje su ka gama har falo tana zille masa. Da ta gaji ta jingina da bango ta dafe ƙirji tana mayar da numfashi. "Don Allah ka barni haka." "Kin san me?" Ya faɗi yana zama "wallahi na fi ki gajiya." Dariya suka yi sannan ya barta ta koma bakin aikinta. Kowanne ganye ta kunna shi ya soma tafasa kaɗan sai ta kashe ta tsane ruwansa tas. Ta haka ne miyar ba za ta yi ruwa ba yadda take so. Sannan kalar za ta fi kyau. Manja ta zuba a tukunya ta kawo garin daddawarta na annurfoods ta zuba a ciki. Ta zuba tumatir, albasa da attaruhu da tayi blending sama-sama. Ya fara suyowa ta ƙara da wata albasar da ta yayyanka mai ɗan dama. Ita ma tana yi mata daidai ta juye ruwan naman nan a kai ta ɗanɗana. Abin da bai ji ba ta ƙara ta bari ya haɗe jikinsa sannan ta fara zuba ganyen ugu da shuwaka ƴar kaɗan wadda Yaya da kanta ta wanke masu a gida ta busar. Jiķata kawai tayi da ruwan zafi ta taso. Ƙamshin girkin har falo. Ta zuba alayyahun da ugun yayi yadda take so sannan ta ƙara da kifin da ta riga ta gyara. Ta zuba garin crayfish ta rufe tukunya. Bayan minti biyar ta kashe ta saɓa murfin tukunyar. "Zuba min nawa yanzu." Firgigit ta juya don bata ji shigowarsa ba. "Ka bari su iso mana tunda sun ce a nan za su yi azahar." "Ko ki bani ta laluma ko in miki ɓarna a tukunya." Hannunsa ta ja har bakin tukunyar ta ce ya ɗanɗana miyar. Ya zuba a plate ya ɗeɓi zallar miyar da bata yi ruwa ba ga kyau a ido ya ci. "Mrs Happy..." "Yes" Hamdi ta amsa da ɗoki. "Kin sami 100/100" Mamaki ta kuma bashi da ta kama rawa tana juya ƙugu. Ya kuwa dangwarar da plate ɗin ya kwasheta. Abincin da basu ci ba kenan sai da baƙinsu su ka zo. Suma kuwa su ka yi ta santin girkin amarya. *** Jiki na rawa Yaya ta kira Inna Luba a waya tana kuka. Innarta ta tada hankali tana ta tambayarta me ya faru. "Ke kaɗai Allah Ya bani Jinjin. Idan kika ɓoye min damuwarki waye zai faɗa min tasa? Ko ba kya son addu'ata?" Mijinta da kishiyarta suna tsakar gidan take wannan wayar. Su ka tsayar da hirar da suke wadda har yau basu sakata a sabgarsu suna sauraronta. "Hmmm, ƙarshenta ɗan daudun mijinta ko ƴaƴanta ne wani ya kwaso abin kunya." Cewar kishiyar Inna Sarai. "Ko kuma ta cangala ƙafarta a inda bai kamata ba" Malam ya faɗi yana zungura baki irin shi dai babu ruwansa ɗinnan. Inna Luba ko ta kansu bata bi ba ta cigaba da cewa Yaya ta faɗa mata me ya faru. To dama Abba Habibu yana gefe yana dariya. Da yaji kukanta yaƙi yankewa bayan ta kira wayar shi ne ya karɓe wayar. "Inna kada ta tayar miki da hankali. Makka za ta je shi ne take kukan murna." "Allahu Akbar kabiran" Inna Luba ta faɗi da dariyarta "Habibu wa ya biya mata?" "Ni ne Inna" Abba ya bata amsa yana murmushi. Yaya sai ta karɓe wayar "Inna ashe yana ta tarin kuɗi ban sani ba. Yaje domin ya biya mana kuɗin sun ƙaru akan yadds ya sani. Shi ne ya ce shi ya taɓa yi ni na tafi. Inna tarinsa na tsayin lokaci amma ya zaɓi ya tura miskiniyar matarsa akan yaje" ta sake fashewa da kuka. Inna Luba ma sai da tayi kuka. Ta dinga yiwa yayarta da mijinta Mal. Umaru addu'a. Sun ƙaunaceta, sun ƙaunaci gudan jininta. Yau gashi da ranta da lafiyarta take jin Jinjin za ta keta hazo taje ƙasa mai tsarki. Da ta gama wayar Malam dawowa yayi gabanta ya tsaya. "Naji kina zancen zuwa Saudiyya. Waye zai je?" "Yarinyar nan ce mijinta ya biya mata." Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye. "Wai Jinjin ɗin ko guda cikin ƴaƴanta?" Malam ya kasa ɓoye son abin duniyar da ya taso masa haiƙan. Idan ƴar cikinsa taje Makka tabbas ya sami abin cika baki da fankama cikin abokansa a ƙauyen. Bugu da ƙari yadda bata da rowa yasa rai da jallabiya, ɗan madina da tashi-ka-fiye-naci. Ƴar bagaruwan nan a gaban su Mal. Ya'u zai dinga ɓantara yana korawa da zamzam. Zuciyarsa ta luluƙa birnin tunani da yaji ita ce dai mai zuwa, Inna Sarai ta katse masa daddaɗan mafarkinsa. "Daga ji an fara biye biye kenan. Dama naji labarin auren jari aka yiwa yaran nata. Shi ne za ku fara kai mazajen ana mallakesu. To dai a dinga jin tsoron Allah." Inna Luba ta dubeta da kallon baki ishe ni kallo ba ta kawar da kai. "An faɗa miki kowa irinku ne? Da mallakar namiji tana gabana ke kin isa Malam ya kalle ki? Ku da malaman tsibbu ku ka dogara. Ni kuwa kin san gidan Qur'ani da hadisi na fito. Har yanzu akwai irin ɗaliban babana da ko ƙwandala ba zan bayar ba za su ban mijin naki a tafin hannu." "Ai wallahi ƙaryarki. Malam nan gani nan bari daga ke har musakar ƴarki." Lokaci guda ga mamakin matan nasa ya daka tsawa. "Ba na son sakarci Sarai. Duk abin da za ku yi na kishi a daina haɗawa da ƴata." "Jinjin ɗin? Mai shan inna" cewar Inna Sarai don tana ganin kamar bai gane ba. "Shan inna kika ce ai ko? Kowa ya san lalura ce ba ita ta ɗorawa kanta ba." Wannan furucin nasa ya sanya duka matan kallonsa da mamakin da yafi na farko. Shin mafarki suke yi ko gaske ne. Inna Sarai haɓa ta riƙe daga baya ta koma tafa hannuwa. Inna Luba kuwa ƙare masa kallo tayi ta kama hanya ta wuce ɗaki. Tana jiyo shewar Inna Sarai tana kiran Malam mai kwaɗayi. *** Kamar kullum Ahmad yau ma da ya kira Zahra sai da ya nemi Salwa. Baya kiran wayarta saboda ya san yanzu yi masa ƙaryar taja gida ba zai bata wahala ba. Ta gaishe shi da ladabin kura ta saurari jawabinsa. Wai ya samo asibiti sun gama komai za a kwantar da Mami. "Ke za ki zauna da ita. Akwai wani yaron office ɗinmu da nayi making arrangement dashi akan kawo muku abinci idan Zahra ta gama" "To Yaya. Allah Ya dawo daku lafiya." Babu wata ƙofa da Salwa ta bari a buɗe wadda Ahmad zai yi zargin wani abu. Zahra ma da su ke gida ɗaya bata ga komai ba. Duka su biyun har suna addu'ar Allah Yasa shiriya ce ta zo. Ta dawo hayyacinta. Salwan da su ka sani ce a gabansu. Ashe kwantan ɓauna tayi musu. A ranar da yamma su ka koma asibiti ita da Mami. Bayan tafiyar Zahra rufe ƙofa tayi tayi juyin murna son rai. A nan dai Ahmad bai isa ya ce ta bawa Mami su yi magana don ya tabbatar tana asibiti. Dama ce ta samu da za ta bi kadin aikin da tayi don ayi a wuce wajen. Bari tayi sai wuraren shabiyun rana washegari ta silla wanka ta ci ado tamkar a gidan biki take ba asibiti ba. Tayi nan tayi can tana ta shiri, Mami na aikin binta da ido. Sarai Salwa ta san tuhuma ce take mata da irin kallon da take binta dashi. Ita kuwa yanzu wannan kallon ya bar yi mata kwarjini. Mamin kanta ta jima da rasa martabarta ta uwa daga ranar da ta buɗewa Salwa sirrinta na biye biyen malaman tsibbu. Gajiya tayi da kallon da ake mata ta dubi Mamin tana mai taɓe baki. "Naga kina ta kallona. Unguwa zanje. Ga nurses nan za su kula dake kafin na dawo." Mami ta girgiza kai. Tana takaicin yadda ta koma babu magana kuma babu damar yi da gaɓɓai. Da ƙyar ta iya girgiza kai ta kafe Salwa da ido da kallon gargaɗi. Ita kuwa tayi mirsisi tamkar bata san me Mamin take nufi ba. Su kansu ma'aikatan asibitin sun yi mamaki sosai da ta fito zata tafi. Wata mai shara ta kasa ɓoyewa har sai da ta magantu da Salwan ta ce su dinga leƙa daƙin kafin ta dawo. "Baiwar Allah wace irin unguwa ce wannan da ba za ki iya jiran wani a ƴan uwa ya canjeki ba sai ki tafi?" "Au..." Salwa ta faɗi cikin murmushi sannan ta buɗe jakarta ta fito da wallet. Dubu biyar ta miƙawa ta kusa da wadda tayi maganar "gashi ku raba da duk wadda ta tayaki dubata. Ba wani jimawa zan yi ba." Suna ji suna gani ta fita abinta. Wadda aka bawa kuɗin kamar ta karɓi wuta sai sannan tunaninta ya dawo. Zubar da kuɗin tayi ba shiri domin ta san dokar asibitinsu. Zuwa duba mara lafiya indai ba shara ce ta kaisu ba ba huruminsu ba. Sauran ma kowacce neman zillewa tayi. Sai a ƙarshe su ka yanke shawarar kai kuɗin wurin wata babbar metiron kafin ya janyo musu matsala. Ai kuwa tayi ta fađa da su ka je. "Mahaifiya babu lafiya ai ko jarabawa ce da ita ta haƙura tunda babu kowa." Su dai sub-staff ɗin babu wadda ta sake magana. Suna kallo ta tashi da kuɗin a hannu ta tafi ofishin daraktan asibitin. Shi tashi yayi yaje yaga halin da Mami take ciki. Tayi fitsari har ya gangaro kan kafet. Idanun jajir tasha kukan baƙinciki. Ƴar cikinta ce ta banzatar da ita saboda nata muradin kamar yadda ta dinga yiwa nata ƴan uwan. Barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Ko ma mene ne laifinta ne! Darakta ya bincika yaji likitan da yake kula da case ɗinta wanda aka haɗa da Ahmad ta waya har su ka yi magana kafin a kwantar dasu. A matsayin wurin na asibiti, fitsarin ba shi bane damuwarsu kamar fitar Salwa wadda ita ya dace ta neme su idan wani abu ya faru. Bai ɓata lokaci ba kuwa ya kira numbar Ahmad ta Saudiyya wadda su ke magana. "Laifi ne babba wani daga waje ya biya ma'aikatanmu su yi masa personal aiki kuma a cikin asibitin. In asibitin ne bai yi muku ba kuna iya ɗauke patient ɗin. Amma ba za mu yarda da negligence daga gareku ba tunda patient ɗinku mai buƙatar kulawa ce 24/7 sannan daga baya azo ana kuka damu." Ran Ahmad yayi matuƙar ɓaci. Ya bawa likitan haƙuri da alƙawarin za a gyara. Wayar Salwa ya shiga nema ba ji ba gani. Lokacin bata jima da sauka daga adaidaita sahu a bakin gate ɗin gidan Taj ba. Ta fiddo wayar taga sunan mai kiran sai kawai ta mayar cikin jaka ta buga gate ɗin. Zuciyarta wani irin zillo tayi da maigadi ya buɗe mata ta shiga bayan ta tabbatar masa da cewa ita ƙanwar maigidan ce. "Allah Sarki. Gaskiya kuna da yawa Masha Allah. Jiya wasu sun zo. Yau ma kinga mota can..." ya nuna mata motar gidan Yaya Hajiyayye "ta ƴan uwanku da su ka riga ki isowa." Wani abu Salwa taji a ranta. Kamar ta juya ta koma. Sai ta tuna da aikin da aka tabbatar mata da zai kama shi. Ta saki murmushi. A gaban ƴan uwansa shi ne wuri mafi dacewa da ya kamata ya nuna soyayyarsa gareta. Da wannan tunanin ta shiga gidan gaba gaɗi. RAYUWA DA GIƁI 34 Batul Mamman💖 * Saɓanin baƙin jiya da bata gama sabawa dasu ba, yau da yake Yaya Hajiyye da Firdaus ta zo sai Hamdi tayi saurin sakewa. Ga albishir ɗin tafiyar Yaya da ya sake faranta mata rai. Kitchen su ka shige da Firdaus suna ƙusƙus. A falo kuma Taj ne da Yaya Hajiyayye su ke tasu hirar. "Wai ka san Kubra tare su ka tafi da Alhaji? Ko ni kaɗai ce ban san da tafiyar ba?" "Bana son jin kowa na faɗin bai sani ba. Sai nayi ta wasu irin tunani." Taj ya faɗa da damuwa a tare da shi "kamar wani abu ake ɓoyewa." "Kai ka san Alhaji bashi da wannan. To ma me zai ɓoye? Kawai maybe taji maganar ne ta ce ita ma zata sai ya barta." "Amma ta kasa faɗa a Home group?" Waya Yaya Hajiyayye ta ɗauko ta dubi Taj "zan yi sanarwa yanzu. Duk mai ƴan matsabbai da lokaci da kuma niyya ta shirya sayen ticket mu bi su." "Ayi min alfarma. Jiya na kai Hamdi anyi passport. A jira ya fito a sami visa." "Gaskiya za a iya jimawa. Mu tafi za ku taho?" Ta ce don akwaita da wutar ciki. Bata son ɓata lokaci idan aka ce za ayi abu. Taj ya bata amsa da cewa "Alfarma na nema" yana sa ran komai zai samu da wuri in sha Allahu. Basu gama hirar ba Salwa ta ƙwanƙwasa ƙofa. Taj ya tashi zai buɗe sai ga Firdaus ta fito daga kitchen. Maimakon ya koma wajen zamansa sai yayi kitchen. Ita kuwa Firdaus hannun ƙofar ta kama da murnarta tana cewa "Ko ƴan gidanmu ne?" Wani irin kallo na rashin fahimta ta yiwa Salwa da ta gani a tsaye taci kwalliya irin wadda bata taɓa ganinta da ita ba. "Anti Salwa ke kaɗai? Ina Anti Zahra da su Hayat?" "Ni kaɗai ce. Ya Taj yana nan?" "Eh, shigo ciki." Ƙamshin turarukan da Salwa ta yiwa fesawar Allah tsine saboda yawa ya doki hancin Yaya Hajiyayye da Taj. Ta dinga taku ta shigo ciki da kwarkwasa. Ta kuma rasa inda za ta zauna sai kusa da Taj dake zaune akam two-sitter. Shi da yayarsa tsayuwa ganin ikon Allah da tana nufo shi suka yi. Shi yasa babu wanda ya iya dakatar da ita. "Ya Taj ina wuni?" Tayi magana da wata zuƙaƙƙiyar murya. "Lafiya ƙalau." "Ka ganni sai yau ko?" Tashi ya yi tsaye da yaji me ta ce ya ce "mun yi dake za ki zo ne?" Ko a jikinta ta sake kashe murya ta ce "Noooo, I thought you want to see me. Miss me?" "Ba sai kin canja harshe ba Salwa, gidanmu babu wanda bai yi karatu ba." Yaya Hajiyayye ta ce tana jifan Taj da wata muguwar harara "akwai wani abu a tsakaninku ne?" Duk da ya gane tambayar domin abin da Salwa take yi da kalamanta kowa zai harbo jirginta da wuri. "Me ki ka gani?" "Me ta zo yi gidanka a haka?" Yaya Hajiyayye ta nuna ta sama da ƙasa. Danne ɓacin ranta tayi ta ɗauke kai ta dubi Taj. "Ya Taj a ina za mu yi magana?" Gajiya da sauraronsu Hamdi tayi ta baro ƙofar kitchen ɗin inda take tsaye ita da Firdaus tun bayan ta faɗa mata baƙuwar da aka yi. "Ga hanyar ɗakinsa can ku je can ku yi." "Ba laifi, gara na san yadda yake tun yanzu kafin na dawo cikinsa." Ko shakka bata ji ba ta bada wannan amsar tana murmushin cin nasara. Zuciyar Hamdi kamar ta fashe ta juya za ta bar wajen Taj ya damƙo hannunta. Ta ja za ta fizge ya janyota gabaɗaya jikinsa yayi mata wata irin kyakkyawar runguma a gabansu. Ta kuwa fashe da kukan da Anti Labiba ta faɗa mata a gida ana yiwa miji. Da gatanki da tarin soyayya a zuciyarsa ake yinsa don kawai an isa. Kissa adon mata! Da aka faɗa tayi zaton shegantaka ce za ta sa mace kuka babu duka ba zagi daga miji. Ashe ba haka bane. Shi ma kukan yana sanin lokacin zuwansa yayi. Tayi nasara fiye da tunani. Taj ya shiga tashin hankali sosai. Bayanta kawai yake shafawa yana faɗa mata kalaman kwantar da hankali. Wannan abu ya tayar da hankalin Salwa fiye da ƙima. Me yake faruwa ne? Ya dace zuwa yanzu hankalin Taj ya koma gareta. Ko zuwan nan, tayi ne don son ganin rigimar da take sa ran sun fara. "Ya Taj..." shiru bai waigo ba, yadda ka san Hamdi ce kaɗai a duniya. Ƙirjinta ya kama hawa da sauka cikin kiɗima ta ce "magana nake fa." "Kana ji tana kiranka. Ni gidanmu zani. Da na sani ban..." Hamdi ta soma faɗi cikin kuka. Yaya Hajiyayye ta hanata ƙarasawa da cewa "Hamdiyya ki yi haƙuri kinji ko. Taj ya ci albarkacina kada ki yarda ki ɗaga masa hankali akan Salwa. Ƴa na ɗauke ki ba matar ƙani ba. In har na isa to don Allah ki barni da ita." Hamdi ta ɗaga kai ta ture Taj da ta farga da yadda su ke ta ce "Kin isa Yaya. Wallahi kin isa." "Salwa baki da lafiya ne ko me? Haka kike dama ko kuwa wani abu ne ya same ki?" Yaya Hajiyayye tayi tambayar tana kallon ta. Kasa magana tayi. Idanunta na bin Hamdi da kallon tsana. At the same time tana jifan Taj da nasa salon kallon na bege. Ta kasa gane ya aka haihu a ragaya. Yardar da tayi da aikin yasa bata kawo haka zai iya faruwa ba. A karo na uku dai ta sake gwada sa'arta ta gani ko akwai dama. "Ka bani minti biyar mu yi magana Ya Taj. Wurinka na zo don Allah." Haɓa Yaya Hajiyayye ta kama tsabar mamakin wannan ƙarfin hali. Muryarta a kausashe kuwa ta ce, "Wuce ciki da matarka yanzun nan." Ta dubi Firdaus "koma kitchen ki kula da girkin." Sannan ta dawo da dubanta ga Salwa "ke kuma kama gabanki yanzun nan kafin in gwada miki ni wace ce." "Allah na tuba sani kuma na nawa zan yi miki Yaya Hajiyayye? Kishiya ta hanaki zama a gidanki na farko. Alhajinku ya ƙaƙaba wa yaronsa ke aka haifi waɗannan" Salwa ta nuna Firdaus tana yatsina fuska. Wani kukan kura Firdaus tayi, tayi kan Salwa. Kafin ta kai mata duka Hamdi ta riƙeta da iya ƙarfinta. Firdaus na ƙoƙarin ƙwacewa Taj ya ɗaga hannu zai kai mata mari shi ma Yaya Hajiyayye ta riƙe nasa hannun. "Jinin Alh. Hayatu da dukan mace? Allah Ya kiyaye." Maganarta ta farko yaji ta jan hannun Hamdi domin su bar falon. Zamansa tabbas zai janyowa gidansu abin faɗa. Da Firdaus ya haɗa su ka shiga ɗakin Hamdi ya ce su zauna shi kuma ya sake fitowa. Daidai lokacin Yaya Hajiyayye tana yiwa Salwa magana. "Ki tafi gida Salwa. Wannan abin da kike yi ba zai taɓa baki abin da ki ke nema a mutumce ba." Taj gaban Salwa ya ƙarasa ya tsaya fuskarsa a murtuke "Salwa na taɓa cewa ina son ki?" Shiru tayi. Zuciyarta cike taf da uwar kunya sai dai son zuciya ya riga yaci ƙarfinta. Sunanta kawai da ya kira sau da ya saukar mata da kasala da ƙarin son sa. "Tunda baki da amsa to ina roƙonki this should realy be the last time. Ina raga miki ne kawai saboda Yaya Ahmad." 'Ko dai shafa masa turaren zan yi in kuma yi masa magana a lokacin?' Salwa ta raya a ranta. Wanda yake hannunta da ta shafa a bakin ƙofar falon ta duba ta hanyar mitstsika yatsunta. Tana ɗaga hannuwa ita kuma Yaya Hajiyayye tayi tunanin rungumarsa za ta yi shi yasa tayi saurin shiga tsakani ta tsinketa da mari tasss. Kunnuwan Salwa sai da su ka ɗauke wuta na wucin gadi. "Ke jakar ina ce kike ƙoƙarin rungumar baligin namiji mai aure?" Caraf maganar a kunnuwan Hamdi. Ta yunƙura za ta tashi Firdaus ta ce ko ta fita kada ta saka baki. "Ki barta da Mama. Wallahi yau ko me take ji dashi ta tara ta samu." Hannuwa duka biyu riƙe da kumatu su ka sameta. Taj ya kasa kallonta. Zama kawai yayi ya dafe kansa. "Bata da lafiya Yaya Hajiyayye. Wannan ba abin da mai lafiyayyar ƙwaƙwalwa zai yi bane." "Babu wani hauka a tare da ita. A nono ta zuƙa kuma in sha Allahu gidanmu nan gani nan bari." Tana rufe bakinta ta dannawa Ahmad kira. "Yaya please zan kira ki anjima kaɗan..." rashin samun Salwa a waya ne ya kiɗima shi. Ya rasa wa zai kira ya tafi asibitin. Mami da danginta amma tamkar wadda ta faɗo ita kaɗai saboda baƙin halinta ya kori kowa. "Ai koma mene ne uzurin indai ba sallah bace to ka saurare ni. Batun wannan yarinyar ne Salwa..." Katse ta yayi da saurin sa "gidan ki ta zo?" "Ina fa. Gata a gidan Taj." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yaya Hajiyayye tun ɗazu nake kiranta ina nemanta." Ya ce a sanyaye gwanin ban tausayi. "Ta ina za ta ɗauka bayan ta fito yawon zubar da mutumci?" A tsiwace Salwa ta ce "ni da aure nake son shi ba..." "Rufe bakin ki" Yaya Hajiyayye ta daka mata tsawar da Hamdi ma sai da zuciyarta ta kaɗa. Firdaus kuwa ta san halin mahaifiyarta dama. Akwai ban dariya da iya zolaya amma kada ka shiga huruminta. Yanzun nan za ta birkice. "Kana ji na Ahmad? Albarkacin ka zan sassauta mata. Amma lallai ka ja mata kunne. Idan ma hauka ne to tayi a wani wajen." Bai ji daɗi ba amma kuma bai ji haushin yayar tasa ba saboda ya san gaskiya ce take faɗa. Kuma Salwa ce ta jawo wa kanta "Ƙalau take wallahi. Tsabar son zuciya ne da rashin tawakkali. Idan tana da zuciya ko aurenta ya ce zai yi ai ta ce bata so a yanzu. Saka ni a speaker" Yaya Hajiyayye ta saka. Ahmad ya kalli inda Kamal yake kwance ya ƙara jin nauyi a zuciyarsa. Ga damuwar gaske amma haka kawai Salwa tana tayar masa da hankali. "Idan kin fita ki koma asibiti ko ki wuce gidan ubanki kin ji ko. Na gaji. Ba ni na haife ki ba saboda haka ba za ki saka min hawan jini ba. Duk abin da ki ka zaɓarwa kan ki daga yau ya rage naki. Kada ki yarda ki koma gidana." Bai jira jin ta bakin kowa ba ya katse call ɗin. Salwa ta bi su da kallo ɗaiɗai. Ta muzanta ajin ƙarshe. Haka ta miƙe ta yi ƙwafa da ƙarfi ta fita. "Ƴar banzar yarinya. A dalilin ki yau har rungume rungumen ango da amarya sai da na gani." Yaya Hajiyayye ta cigaba da mita. Taj ya kama dariya. Hamdi kuwa hanyar ɗaki ta nufa, Firdaus na yi mata dariya. A lokaci guda falon ya mamaye da ƙaurin girkin da ya rasa kulawar waɗanda su ka ɗora shi. Su huɗun dake falo a tare su ka yi hanyar kitchen ɗin. *** Tsinuwa da zagi da mummunar addu'a babu irin wanda Salwa bata yiwa Ummi ba da ta fito. Ta tari adaidaita sahu amma ta rasa ina za ta ce ya kaita. Sai da ya yi shirin tafiya tayi saurin faɗin sunan unguwar da za ta. Suna tafe a hanya tayi mamaki ƙwarai da ta gane gidan. Sau ɗaya ta taɓa biyo Ummi a baya bayan sun tashi daga wata haɗuwa da su ka yi kafin bikin su Hamdi. Zuciya tana ta ingiza ta. Baƙinciki da ɓacin ran da take ciki ya yi yawa. Da ta ƙwanƙwasa ƙofa Siyama ce ta buɗe. "Ummi nake nema." "Wa zan ce mata?" Siyama ta tambaya a tsorace. Fuskar Salwa abin tsoro. Kana ganinta ka san ba da alkhairi ta zo ba. Daga tambayar Salwa ta gane Ummi tana ciki. Bata ɓata lokaci ba ta hankaɗe Siyama gefe ta faɗa cikin gidan tana ƙwala kira. "Ummi. Ummi. Ummi..." A firgice Ummi ta fito daga ɗakin Iyaa inda aka saka ta gyaran wardrobe. Gabanta ya faɗi da ta tabbatar Salwa ce ba muryar ke mata gizo ba. "Me ya kawo ki gidan mu? Wa ma ya nuna miki?" Ummi ta ja hannunta su ka koma ƙofar gida. Iyaa da Baba Maje fitowa su ka yi daga ɗakinsa da Baballe inda su ke tattaunawa akan ginin gidansa inda Zee za ta tare. Wajen su ka je amma Ummi da Salwa basu ankare da su ba. Salwa ta cakumi wuyan Ummi "Ni za ki ha'inta? Turaren da ku ka bani dama ba wanda zai sa Ya Taj ya saki wannan ƴar ɗan daudun bane ya aure ni?" Tsohuwar bully an saba dambe. Ummi mantawa tayi da inda take ta doke hannun Salwa ita ma ta riƙe mata wuyan riga. "Banza a banza...duk soyayyar da za a siya da asiri wallahi na raina ta. Turare kuma ba na kashe aure bane." Don baƙin ciki Salwa harda kuka ta ce "Na mene ne? Me ku ka sa nayi?" "Ummi..." Iyaa ta fara kiranta horrified da jin abin da su ke cewa. Sai dai da wuri Baba Maje ya yi mata nuni da tayi shiru. Abin kunya har mutane sun fara taruwa. "Ki jira ki gani amma tabbas soyayyarsa ba ta ciki." "Wani aikin ku ka saka ni?" "Alh. Usaini dai ya saka ki. Ni mene ne nawa a ciki?" Cikin karaji Salwa ta ce "Waye Alh. Usaini? Me nayi Ummi? Turaren mene ne?" "Turaren kassara sana'ar mijin Hamdi." Ta amsa mata da yanayin tsokana. Ai tana rufe baki Salwa ta daddage ta kai mata wawura. Kan kace meye wannan dambe ya kacame a tsakaninsu. Duka harda yaga riguna a gaban mutane. Iyaa hawaye kawai take zubarwa. Baba Maje kuwa cikin gida ya koma yana mai jin kunyar abin da ƴarsa tayi na zubar musu da mutumci. Baballe duk zafinsa akan Ummi shi ma komawa yayi yana mai jan hannun Siyama. Ƴan unguwa su ka yi ƙoƙarin rabasu abu yaci tura. Wani kawai sai ya kira ƴan sanda. Daga cikin gidan su ka ji jiniyar motar. Baba Maje ya ce kada wanda ya fita. Aka tattara su sai Police station. Nambar Baba Maje Ummi ta bayar. Da aka kira shi akan case ɗin ya ce zai zo. Suna gama magana ya kashe wayarsa gabaɗaya. Ya kuma ce da su iyalinsa kada wanda ya amsa kiran baƙuwar namba. Ummi ta zauna ta koyi hankali. Salwa ta fi Ummi tsurewa. Kwana a nan abu ne da ba za ta iya ba. Gashi ita ɗin mai laifi ce. Ta kasa bada numbar Zahra saboda gudun tashin hankalin da za su yi da Ahmad. Garin Kano cike yake da dangin Mami, yau ga ranarsu amma babu wanda za ta iya kira kai tsaye saboda ba ayi mu'amalar arziƙi ba. Ƙarshe nambar babanta ta bayar. Aka kira shi sau biyar baya kusa bai ɗauka ba. "Tunda baku da kowa mu bamu rasa masaukin baƙi. A wuce dasu su shiga su huta." Cewar DPO ya na barin inda su ke. Hankali a tashe Salwa ta ce "Don Allah ka sa a sake kiran Babana. Ni wallahi ba zan iya kwana a nan ba." Ummi kuwa ko gezau. Bata shaida ta shiga one chance ba sai da aka haɗa su cell ɗaya da wasu yan daban mata. Ashe damben su da Salwa wasa ne. Irin dukan da aka yi musu a cell đin ya ƙazanta. Babu wadda jikinta bai amsa ba. Kafin wani lokaci kowacce fa kama kukan gaske. *** Saboda yawan kiran waya sai da kunnen Ahmad ya yi zafi. Duk wasu ƴan uwa Mami na kusa da na nesa ya dinga kira yana neman taimakonsu akan kula da itaa asibiti. Duk wanda ya kira suna yabon yadda ya kiyaye zumunci amma kowa da irin labarin cin kashin da Mami tayi masa a baya. Bottom line dai babu mai zuwa. Ya shiga damuwa sosai. Kamar ya faɗawa Alhaji sai dai yana tsoron me zai faru. Daɗin daɗawa ga Kamal a kwance sai na'u'rori. Kansa ya ƙulle. Lokaci guda wata shawara ta zo masa. Ya kira likitan Mami ya ce a bashi Nos guda da za ta zauna da Mami tsahon sati ɗaya kafin ya dawo. Zai biya ko nawa ne. Aka tsadance ya tura kuɗin a take su kuma su ka tura wadda za ta iya ɗakin. Sai lokacin ya sami nutsuwa ya kira Baban Salwa ya tambayi ko ta koma. "Bata dawo ba amma zan kira ta. Ina so ka zare hannunka a kanta. Zan yi maganin abin da kaina." *** Kwanaki huɗu bayan nan Taj ya shirya zai koma Happy Taj. Hamdi ta dasa masa rigima kala kala. Rarrashi iri daban daban yayi mata. Ƙarshe ba shi ya fita ba sai ƙarfe goma da minti kusan arba'in. Ya fara kaita gida saboda suna sa ran tafiyar Yaya ta samu nan da kwana biyar. Yana zuwa yaran kitchen ɗinsa su ka ce yau gwaji za su yi masa su tabbatar aure bai mantar dashi girki ba. "Kada daɗin abincin amarya yasa ka manta naka." Kowa yayi dariya kuwa. Shi kuma ya ƙarɓi ragamar dafa chicken kabsa. A lokacin ne kuma aikin su Alh. Usaini ya yi tasirin gaske. Ya haɗa spices ɗinsa tunda abin da zai dafa dama spices ne sinadarin sa. Komai ya ajiye a gefe yayi marinating kazar. Bai ḍanɗana ba tunda hannu ya gama sabawa. Cikin ƙwarewarsa ya gama hađa komai saura jiran dahuwar abinci. Yana duba list ɗin abubuwan da aka ƙaro da baya nan yaga wasu cikin ma'aikatansa sun shigo kitchen ɗin a guje. "Sir baka ji ƙauri ba?" Wani ya tambaye shi da ya ce me ya faru. Ya juya ya buḍe tukunyar. Ƙauri ya sake cika kitchen ɗin. Kowa na tari banda shi. Shinkfar tayi ɓaki ta ƙone babu abin mora a ciki. Abin ya ɗaure masa kai. Ya faki idonsu ya da dangwali gishiri ya lasa. Ko ɗigo bai ji ɗanɗanon sa ba. Ya sake ɗora wata shinkafar ita kuma da ya gama aka yi serving ga masu saye babu wanda yaci rabi. Haka aka dinga dawo da plates ɗin cike da abinci. Bakinsa still babu taste. Yasa yaran kitchen ɗin ɗanɗawa. Kowa ya kai baki sai ya gumtse abinsa ya dangana bakin shara ya tofar. Akwai wanda ya soma amai a gabansa ma. "Me kuke ji?" Yayi tambayar calmly. "Gishiri da garlic sun yi yawa sosai. Yawan daido duk dauriya mutum ba zai iya rufe ya ci ba." Hankalinsa sayiwani irin tashi yayi. Bai yiwa kowa sallama ba ya fita. Yana zuwa gida ya buɗe fridge ya ɗauki mixed fruit juice ɗin da ya haɗa da hannunsa jiya. Nan ma shiru baki da hanci bai ji komai ba. *** Abba Habibu da iyalinsa suna tattaunawa game da waɗanda Yaya za ta bi saboda ta sami muharrami. "Abba dama dai ka jira ka samu wasu kuɗin kun tafi tare." Cewar Zee "Yanzu Allah Ya kirata. Ku dai ku yi mata addu'a. Banda abin ku mijin Labiba ai ya zama ɗan gida. Yan uwan nasa da zai yi tafiyar dasu jiya har kirana su ka yi mu ka gaisa." "To kun gani ko..." Abba ya ce da murna. Suna wannan hirar Halifa ya buɗe passport ɗin Yaya yana gani. "Laah Yaya wane irin blood group ne wannan O minus?" Hamdi ta karɓe ta kalla " ya kamata in ɗan yi studying bambancin blood group ɗinnan. Nima anyi min test ɗinsa amma ban duba ba da shi da geno type." "Da aka yi min sai da mutumin ya ce min wai jinina na musamman ne don yana wahala." Zee da Halifa sai cewa su ka yi su ma ɗin za su je ayi musu. Daga wannan hirar Abba ya ce, "Hamdi ki bamu numbar Kamal ta can, idan ta isa sai ta kira shi su gaisa." "Idan bamu da nisa in je dai mu gaisa zai fi." Yaya ta faɗi tana murmushi. RAYUWA DA GIƁI 35 Batul Mamman💖 *** Kwana biyu a ƙirgen Hamdi tana lura da duk wani motsin Taj. Ta riga taji a jikinta tun randa ya koma Happy Taj bai dawo gidan da irin jovial spirit ɗin da ya fita dashi ba. Aura ɗinsa gabaɗaya is down amma a zahiri babu wata alama ta ciwo. Ta tambaye shi me ya faru tun a lokacin ya nuna babu komai. Da dare kafin su kwanta ta sake maimaita tambayar sai ya shashantar da zancen. Jiya ma haka aka yi, domin da ya dawo bai sake fita daga ɗaki ba. Ya ce mata mura yake ji tana neman kama shi. Tayi iya yinta ta rabu dashi. Haka su ka kwana kowa ya juyawa ɗan uwansa baya. Sai da asuba da farka ne ta ganta tayi matashi da ƙirjinsa ya rungumeta sosai. Shi kenan aka cigaba da ranar lafiya ƙalau kafin ya fita. Da ya dawo Yau dai yana fita ta kira Abba Habibu. Kunya ta so hanata tambaya. Tana ta juya zancen a zuci. Kamar ya sani sai ya ɗauko maganar komawar Taj ɗin aiki. "Ance maigidan naki ya soma fita ko?" "Eh, ashe ba ku haɗu ba." Ta amsa da sauri. "Satin nan ban fita ba. Kin san yana ta matsa min da na ajiye aikin. Ni kuma ban saba zaman haka kawai ba. Na fahimci saboda yana aurenki kamar zai takura idan ina ƙarƙashinsa...duk da tun a baya bai taɓa ci min fuska ba. Na rasa shawarar yankewa Hamdi." Hamdi tayi murmushi "Abba indai ka san wani aikin za ka nema idan ka bar Happy Taj ɗin gara kayi zamanka." "Ba za ki ji komai ba?" Numfasawa tayi da rawar murya "ba zan ji ba. Wanda nayi a baya ma don Allah ka yafe min Abba." Kafin ta karyar masa da zuciya har ya kai ga kasa ɓoye rauninsa ya ce "ba ki min komai ba. Har abada babu riƙo tsakani na daku in sha Allah. Allah Ya yi muku albarka." "Amin Abbana" tayi maganar cikin farinciki. Hira ce ta kankama tsakaninsu wadda duk akan tafiyar Yaya ce. Kafin su yi sallama ne ta daure tayi masa tambayar duk da gudun kada yaga rashin kunyarta. "Abba wani abu yana faruwa a Happy Taj ne?" "Me ki ka gani? Me ya faru?" Ya tambayeta da sauri kuma cikin tashin hankali. Ba komai ya janyo hakan ba sai lura da yayi yanzu kullum Baba Maje sai ya yi masa tambayar da ta shafi Happy Taj da kuma lafiyar Hamdi da Taj ɗin. Amsar tasa ta ishe ta samun gamsuwa "Kullum idan ya dawo yanayinsa babu daɗi. Na fahimci kamar daga can ne matsalar." Wayancewa Abba Habibu yayi tunda bai san mene ne manufar tambayoyin Baba Maje ba. Shi yasa bai sanar da ita ba. "Anya kuwa? Da wani abu ya faru zan ji. Amma ki bari zan tambaya." Taƙaita zancen yayi cikin sauri da su ka gama wayar ya kira ɗaya daga cikin ma'aikatan kitchen ɗin Happy Taj. Babu wani ɓoye ɓoye ya ce ya fađa masa abin da yake son ji. Yaron bai musu ba. Don ya ce dama sun yi niyar kiransa da kansu ma. Labarin da yaji bai yi masa daɗi ba. Kwana uku a jere girkin Taj ba ya ciwuwa. Duk abin da zai ɗora sai an sami matsala. Haka nan indai ya taimaka musu da nasu aikin su ma ba ya tafiya daidai. "Yau bai saka mana hannu a girki ba. Da za ayi serving wasu baƙi sake yin taro a ƙaramin conference room wallahi Abba Habibu baka ga ɓarin da yayi ba. Trolley (food trolley) ɗin gabaɗaya ya kifar a gabansu." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yanzu yana ina?" "Ya ce kwastoman ƙarshe na fita mu tashi. Idan akwai sauran abinci a bayar." Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ce "Nagode." Allah Ya taimake shi Yaya bata nan. Ita da bata da son fita yau ta nemi Zee ta rakata unguwa...gidan Baba Maje ta tafi yi musu bangajiya na musamman duk da an riga anyi a waya. Ta sayi atamfa da shadda masu kyau da tsada za ta basu na kyautatawa. *** "Wai ni ina Ummi ne? Ba za ta fito mu gaisa ba?" Cewar Yaya bayan an sami kimanin awa gida suna hira da Iyaa. A ƙofar gidan daga cikin adaidaita su ka rabu da Zee don ta ce ba za ta shiga ba. Cikin gari gidan ƙanwar kakansu ta gudu. Idan Yayan ta gama za ta dawo su tafi. Iyaa ta numfasa "tun ɗazu nake ta addu'ar kada ki yi cigiyarta." "Allah Yasa lafiya. Indai ƙalau take ba sai kin yi min bayani ba." Yaya ta faɗi tana murmushi. "Jinjin kenan. Kina da kawaici sosai. Yanzu idan naƙi faɗa miki ba za ki ji haushi ba?" "Banda abin ki ai ba ayi ciki domin tuwo ba kaɗai. Kuma idan bamu zama murfin sirrin ƴaƴanmu na farko ba to wa zai zama? Kada ki ji komai. Allah Ya dafa mana akan yaran nan kawai." Daga bayansu su ka muryar Baba Maje "sirrin Ummi ba zai rufu ba saboda lokacin bankaɗo shi ya yi." Kallonsa Iyaa tayi tana girgiza kai. Duk lalacewar Ummi ba za ta so hakan ba. Ba kuma don tana goyon bayan abin da tayi ba. Ko kusa! Duk duniya ko Baba Maje bai kai ta son shiryuwar Ummi ba. Kuma ta yarda da Yaya ɗari bisa ɗari amma dole tayi kwaɗayin sakayawa indai ba ya zama dole ba. "Sakaya kan ki Habibu zai shigo." Jin haka Yaya ta juya ba shiri ta kalle shi. Murmushi ya yi kawai mai tarin ma'anoni ya fita. Me zai kawo Abba a wannan lokacin? Wannan ita ce tambayar da ta yiwa kanta kafin su shigo tare da Baba Maje. Babu zancen gaishe gaishe. Kai tsaye Baba Maje ya soma magana. "A waya kayi min tambayar me yasa kwanakin nan kullum sai na tuntuɓeka game da lafiyar Hamdi da mijinta." "Shi ne kuma za ka ce in zo gida na same ka?" Abba ya tambaye shi domin shi ma ɗin ya shiga duhu. "Inda zamu je yafi kusa da nan shi yasa. Kafin mu tafi amma zan so sanin me ya ankarar da kai har kayi min tambayar. Na san don ina yawan tambayar lafiyarsu ba zai zama abin tuhuma ba." "Ƙwarai kuwa. Sai dai keɓe Hamdi ba tare da yawan bibiyar lafiyar su Sajida ba shi ne yasa da naji wata magana game da Taj na neme ka. Amma ka sani ban yi da wata mamufa ba sai son jin ko kana ɓoye min wani abu ne don kada na shiga damuwa." Hankalin Iyaa sai yafi na Baba Maje tashi. So kawai take taji me yake faruwa da Taj ɗin. Abba Habibu ya faɗa musu abin da yaji daga Hamdi da ma'aikacin Happy Taj. Da yake Yaya akwai dauriya idan ka kalli fuskarta ba za ka fahimci yadda wannan zance ya kaɗa ta ba. Iyaa kuwa kukan baƙinciki take yi. Wannan abin da yake faruwa akwai hannun Ummi. Wace uwa ce za ta yi alfahari da haka? Baba Maje ya labarta musu rigimar da ta faru tsakanin Ummi da Salwa. "Tun ranar babu wanda yaje a cikinmu. Rayuwar da ta zaɓa ce take yi mata horo tun yanzu. Gara a barta da duniya ta koya mata hankali." "Kada ka ce haka. Babu ɗan da aka taba barwa duniya aka ga daidai. Kuma ita ma yanzu da ka ƙyaleta idan ta haɗu da waɗanda su ka fita fitina fa?" "Ummi ce fa! Babu wanda ya lalata ta sama da biyewa ruɗin zuciyarta. Indai bata ɓata ɗan wani ba, to kuwa babu wanda zai ɓata ta. Da kanta ta mayar da halayenta irin wanda mutane ke gudun yaransu su yi abota da ita." Su huɗu su ka rankaya police station ɗin da aka rufe su Ummi. Wani tsamurmurin Kofur ya fara yi musu surutu akan rashin zuwa tun ranar da aka kawo su. Baba Maje ya ce barinta yayi a ladabtar da ita. Kuma ko yanzu ba beli ya zo yi ba. "Ɗakin da muke tsaron nasu fa a cunkushe yake. Tunda rigima ce kawai ta mata za a iya baku su." Ɗauke kai daga gare shi Baba Maje yayi. Ya ce yana son ganin wanda ya dace domin a fito da Ummi su yi magana. Aka dangana su da ofishin DPO inda a nan ne aka fito musu da Ummi. Kwanaki uku kacal! Ummi ta zuge ta fita hayyacinta. Babu wanka babu wanki. Kayan jikinta kamar tsummokara. Kumatunta sun yi shatin hawaye dabbara dabbara. Gabaɗayanta babu kyawun gani. Haka ta ƙaraso gabansu tana ɗingishi. Wanđanda su ka tarar a cell ɗinsu sun yi musu duka ita da Salwa. Kamar haɗin baki. Babu wanda ya nuna damuwa akan ciwukanta. A gaban DPO ɗin dai Baba Maje ya ɗauko zancen Taj. "Ki faɗa min gaskiya Ummi. Me ki ka yiwa mijin Hamdi har ya fara fuskantar irin waɗannan matsaloli daga komawa aiki?" Allah Ya sani ta gaji da wajen nan don haka ba za ta wahalar da kanta wurin ɓoye ɓoye ba. Abin gudun ya riga ya faru. Kwana uku babu baccin kirki, ta fannin abinci ma sai addu'a. Wurin zagayawa kuwa tun tana amai har ta daina. Gashi don bala'i cikinta ya rasa lokacin lalacewa sai a nan. Bugu da ƙari ƴan cell ɗin nasu sun ɗora mata karan tsana. Daga ita har Salwa sun daku amma nata yafi yawa saboda ita ce mai ramawa da farko. "Salwa ce ba ni ba." "Wace ce Salwa?" Kofur ɗin ɗazu ya ce "ita ce aka kawo su nan tare. Ace ƴar mutum tana sakaye amma bai san ma ita da waye ba sannan babu waiwaye." Fuska a haɗe DPO ya kalle shi ya ce "Kofur Ɗanliti yaya haka ne? Me ma kake yi a nan?" "Yallaɓai wasu iyayen ne sam ba sa gane illar barin ƴaƴansu mata a station." "Kai dai naka ƴaƴan suna gida ko?" DPO ya ce a harzuƙe. "La shakka." "To jeka ka kawo Salwa ɗin ka kama gabanka." Wani sassanyan murmushi Kofur Ɗanliti ya yiwa Ummi da zai fita. Harda cewa ta kwantar da hankalinta. Yanzu gaskiya za ta yi halinta. Ƙila ma a yau ta sami damar tafiya. Tsawar da DPO ya daka masa ce tasa shi gaggawar fita yana ƙananun surutai akan ƙulle mutane ba bisa haƙƙi ba. Ita kuwa Ummi wata muguwar harara ta galla masa da ya juya. Tun zuwansu yake ta rawar ƙafa a kanta. Matan da suka yi mata duka ma ya so basu horo irin yadda ake yiwa masu laifi saidai yana ganin shugabarsu ya fita yana Allah Ya isa. Matar regular ce kuma tantiriya. A tsaye ta fishi nesa ba kusa ba. Ba a jima ba su ka shigo da Salwa. Ta tsaya musu ƙerere tana harararsu. Ta gane iyayen Hamdi ta kuma gane iyayen Ummi daga kamanninsu. "Durƙusa" Kofur Ɗanladi ya ce da tsawa saboda haushinta da yake ji. DPO kai ya girgiza kawai don ya ɗago shi ya ce Ummi ta maimaita abin da ta ce. Nan kuwa ta nuna sam bata san komai akan Taj ba. Salwa ke son shi kuma ita ce tayi masa asiri. "Lallai ma. To a ina na samo turaren? Ba ke bace ki ka bani?" Salwa ta kalli DPO "Wallahi cewa tayi idan na shafa masa zai saki Hamdi ya aure ni." "To yanzu me ya haɗa ku faɗa?" Salwa ta ce tayi amfani da turaren yadda aka ce amma Taj wulaƙanta ta ma yayi fiye da yadda yake yi a baya. "Ummi har kin san bin bokaye kuma?" Iyaa ta fashe da kuka. "Nima bani aka yi Iyaa. Don Allah ku tafi dani gida." Ba a wani sha wahala ba ta faɗi cewa Alh. Usaini ne ya bata. Kuma a zahiri ga abin da ya ce mata zai faru da Taj saɓanin yadda su ka faɗawa Salwa. "Aikin ku nayi muku kenan? Kin san mutanen da na rabu dasu saboda tunanin zan sami Taj?" Salwa tayi kan Ummi cikin ɓacin rai. Kofur Ɗanliti yayi saurin anjige ta kafin ta cakumi Ummi ta faɗi a ƙasa. Abba Habibu da Yaya sun ga ikon Allah. Bayan Ummi ta kwatanta inda za a sami Alh. Usaini. Ta tabbatar musu da cewa akwai chats ɗinsu harma da recording ɗin wayoyinsu a wayarta. "Damma kin shiryawa rana irin wannan ne?" "A'a, na dai kula idan muka gama chatting yana bin duka abin da ya turo ya goge. Shi yasa na soma yin screenshot saboda kada a gaba wani abu ya faru ya zame ya barni." "Allah ma Ya sa kina da wayonki. Irinsu haka su ke amfani da marasa wayo su cuce su." Ayyanawa Ummi tayi a ranta cewa indai Kofur Ɗanliti yayi gigin cewa yana sonta, za ta nuna masa rashin mutumcin da zai jima yana yi masa ciwo. Idan ba karambani ba ai shi ma daga gani ya san su ba sa'annin juna ba. Duka duka bai fi rabinta ba a faɗi. Tsayi kuwa ba zai wuceta ba. Gida Abba Habibu ya buƙaci Yaya ta koma tunda kawo Alh. Usaini zai ɗauki lokaci. Babu musu ta tashi. Jikinta yayi matuƙar sanyi. Ka haifi đa ya zama silar zubar mutumcin mutum babu ruwansa da gazawar tarbiyya. Wani duk ƙoƙarin iyayensa sai ya janyo musu magana hankalinsa yake kwanciya. Baba Maje ma ya ce Iyaa ta tafi ta nuna zama za ta yi. So take taji ƙarshen wannan abu da Ummi ta zama sakarya wajen jagosarsa. Minti ashirin bayan tafiyar Yaya sannan aka zo da Alh. Usaini. Tun a waje yake ta bala'i da zage zage. Da yaga Ummi sai ya taɓe baki. "Kina da shaidar nunawa kice da hannuna?" Ya kalli Salwa "ke kin sanni ne?" "Kaga ka ajiye wannan surutun zai amfane ka a kotu."in ji DPO "Kotu??" Salwa da Ummi su ka maimaita cikin tashin hankali. "Ƙwarai kuwa. Kafin lokacin muna buƙatar shi Taj ɗin a nan." Ranar har dare suna station dai. Taj da Hamdi su ka zo aka maimaita komai. Ya dubi Alh. Usaini ya ce masa da shi da su Salwa duk ya yafe musu ya juya ya fita. Fitarsu ke da wuya mahaifin Alh. Usaini ya je. Bayan ya gama zagi da ci masa mutumci a gaban mutane yace ba zai bashi shugabancin komai cikin kadarorinsa ba. Gado ma ba don Allah ne Yayi da Kansa ba tabbas da ya ce ba zai gaje shi ba. A ƙarshe ya fice. Su Baba Maje ma su ka kama gabansu. Abba Habibu ne ya karɓi Ummi albarkacin iyayenta. Salwa ma an saketa amma ko da ta fito ta rasa inda za ta tafi. *** Da Hamdi ta shiga ɗaki a kwance ta sami Taj amma ya juya mata baya. A hankali ta lallaɓa ta hau gadon ta kwanta a bayansa. Hannunta ɗaya ta zura ta ƙarƙashin jikinsa, ɗayan kuma ta gaba ta haɗe su ta rungume shi. "Kuka kake yi ne?" "Tsokana ta ma kike yi?" Ya yi maganar ba tare da ya juyo ba. "Ƙorafi dai na zo yi. Ta yaya zan aureka kuma ace safe, rana da dare duk ni ce a kitchen. Gaskiya da sake." Tashin da bai yi niyya ba yayi. "Kin manta halin da nake ciki ko kuwa da gaske tsokanar ce?" Hamdi ta ce "Ka faɗa min damuwarka ne? Ba da kaina na nemo amsar ba?" "Da ki ka nemo ba ki ji tausayina ba?" "Girkin ne ba za ka tayani ba kake tada zancen?" Ta kyaɓe fuska. Taj ya riƙe baki da yaga da gaske idanunta suna neman zubo da ƙwalla "Abu ya same ni amma saboda ƙarfin hali ke ce da ɓata rai da shirin kuka?" "Na fi ka shiga tashin hankali. Ka da aka mana aure hancin ka da baki duk suna aiki. Yanzu da haka ta faru sai anyi min cikon sadaki." Tayi kicin kicin da fuska. Taj bai san lokacin da ya soma dariya ba "cikon sadaki fa kika ce?" Ta goge ƙwallar ƙarya "Eh mana. Na baka tausayi ko?" "Haƙƙun." "Zan iya yafewa in za ka yarda ka fito daga ɗakin nan mu shiga kitchen." "Hamdi..." "I'll be your nose" ta tsaya akan gwiyoyinta akan gadon ta goga hancinta da nasa "and your tongue." Ta rataya hannuwanta a wuyansa ta sumbace shi "I'll be you har ka sami lafiya." Ƙanƙameta Taj yayi. Ta dage ta ƙi barin raunin zuciyarta ya bayyana balle tayi kukan da take ta dannewa. "I love you." "Me too" ta faɗi har lokacin wuyanta na kafaɗarsa. A ranar bata yarda sun sake komawa wannan zancen ba. Sai ma mitar da take yi wai ta rasa sunan da za ta dinga kiransa. Ya Taj ɗin da take jindaɗin faɗa shi taji Salwa na kiransa dashi. Yana dariya ya ce "Ki kirani Malam kawai?" Ita ma dariyar tayi ta ce "Happy ya ishe ni. " *** Washegari Taj yaje gida ya faɗawa su Inna abin da ya faru. Da Salwa ta san illar baki da bata janyowa kanta abin da zai sa ta shiga bakin mutane ba. Hajiya bata yi ƙasa a gwiwa ba ta kira Alhaji ta faɗa masa. Hankalinsa ya sake tashi fiye da baya. Bayan sun gama jajantawa juna ya kira sauran matansa. Sun jima suna magana da Inna yana kwantar mata da hankali. Ya ce su dage da yin addu'a. Shi kuma zai san yadda yayi da Alh. Usaini. Yadda su ka ƙulla abin su za su kwance in sha Allah. "Kun sa ranar dawowa ne?" "A'a. Za mu yi magana daga baya." Ajiye wayar yayi yana ta juyayin abubuwa. Case ɗin Taj da Kamal ba ɗaya bane amma a ƙalla mahaifiyar Taj ta san abin da ya shafi ɗanta. Addu'arta tana kai masa. Hajiya fa? Ta ina zai fara? Duk da haka dole ta sani zuciyarsa ta faɗa masa. Kamar haɗin baki a daren ranar Yaya Hajiyayye ta kira shi tana tambayar saura kwana nawa su dawo. "Mene ne?" "Alfarma zan roƙa ku ƙara lokaci. Nan da kwana shida zamu taho in sha Allah." "Ba na ce Taj ya bari Hamdiyya ta sami visa ba?" Yaya Hajiyayye tayi dariya "ai ta samu. Surprise mu ka so yi muku. Yanzun nan nayi tunanin kada fa garin surprise mu yi saɓani." Farincikinsa ya nuna. Ya ajiye wayar sai yaji sanyi yana ratsa shi. Yaya zsi yi da matansa? Dama yana kusa ne da sauƙi. Haka nan ya yi ta maza ya kira Hajiya. Tunda taji ya ce ta keɓe za su yi magana gabanta ya faɗi. Ya fara da wa'azi ds tunatarwa akan sharuɗan imani. "Na yarda da ƙaddara. Ka faɗa min kawai me na rasa." Ta ce da rawar murya. "Baki rasa ba amma duk wani hope yana neman ƙare min." Jikinta taji yayi nauyi ta sami waje ta zauna. Duk yadda Alhaji ya so rage mata raɗaɗin da za ta ji ta hanyar amfani da kalmomi masu kwantar da hankali abu ya faskara. Kamal yana dab da rasa rayuwarsa saboda rashin dacen mai bashi ƙoda. Yayi zaton za ta yi kuka sai yaji shiru. Can ta numfasa. "Yaushe ne akwai jirgi kurkusa?" "Zan bincika..." "Ka duba ka biya mana. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Sai ta katse kiran. Alhaji ya yi ta kiranta taƙi ɗauka. Mama ya nema yace su haɗu da su Inna yana da magana. Su ukun nan kuka suke yi babu mai rarrashin wani. Su ka shiga ɗakin Hajiya su ka sameta tana haɗa kaya. "Ku ma ku gaggauta haɗawa domin ko gobe aka sami jirgi zamu tafi tare ko?" Cikin kuka Umma ta ce "dolenmu Hajiya." Inna da Mama kuwa ko bakin magana babu. Basu bari yaran sun sani ba. A kwana uku aka gama yi musu komai. Yaran nasu suna ta mitar me yasa basu jira su tafi tare ba. Mama tayi ƙarfin halin cewa mijinsu ke nemansu. Aka mayar da abin shaƙiyanci ana dariya. * Tafiyarsu da kwana biyu shi ne lokacin tafiyar Yaya. A airport su ka haɗu da abokan tafiyarta. Su Hamdi su ka yi mata rakiya da mazajensu. Abin da ya bawa Taj mamaki da kuma tayar masa da hankali bai wuce ganin Dr. Mubina tana fitowa daga wajen check in ba. Ta rame sosai kamar wadda ta jima tana ciwo. Duk wasu alamun rashin kwanciyar hankali sun bayyana gareta. Da ta gan shi da farko gabanta ya faɗi kuma ya gani. Ta basar shi ma ya nuna bai gane komai ba. Hamdi ya kira su ka gaisa ya ce "Ku fara ƙawance don da alama ita ce Mrs Happiness." Hamdi sai murna ta zolayeta "Umra za ki ko Ya Kamal za ki bi?" Dr. Mubina tayi murmushi kawai. Taj ya nuna mata Yaya ya ce ga ƙarin abokan tafiya ta samu tunda yaga kamar ita kaɗai ce. "Na gode kuwa." Da aka kira su Hamdi da Taj na kallo Dr. Mubina ta haɗa akwatin ta da na Yaya tana ja. Sun ji daɗin hakan kuwa. A ƙofar jirgi inda ake nuna boarding pass Yaya za ta ɗauko nata ta haɗa da ƴar takardar da su Hamdi su ka gani wadda aka saka cikin passport ɗinta. Ita ce mai ɗauke da bayanin lalurarta da su blood group ko da wani abu na emergency zai sameta. Bata san ta yar ba tayi gaba. Mubina ce ta ɗauko mata. Tana shirin bata ta kula da bayanin da yake jiki. Zuciyarta sai da ta girgiza. Ta miƙa mata da rawar hannu. RAYUWA DA GIƁI 36 Batul Mamman💖 *** A dalilin ba lokaci ɗaya aka saya musu ticket ba, wurin zaman Yaya da na abokan tafiyarta daban daban ne. Ɗan saurayin cikinsu Yaya tayi niyar bawa boarding pass ɗinta domin ya duba mata wurin zamanta, haka Abba Habibu ya sanar da ita tayi. Ya ceba inda mutum yake so zai je ya zauna ba. Ta ɗaga hannu za ta bashi Mubina ta riga karɓa. Ta kaita har wurin kujerar ta taimaka mata da ɗora hand luggage a sama sannan ta ɗaura mata belt. Ko ba a faɗa ba ta riga ta gane Yaya bata raɓa shiga jirgi ba. Yaya tayi ta godiya da sanya mata albarka. Ita kuwa Allah Ya sani da biyu take yi. Kafin jirgi ya tashi bayan kowa ya zauna ta zo ta roƙi wadda take kusa da Yaya da cewa mamanta ce su ka yi musanyen seat. Wannan abu yasa Yaya jindaɗi matuƙa. Ta saki jiki da Mubina suna ta hira. Da jirgin zai tashi duk wani tsoronta Mubina ce ta dinga kwantar mata da hankali. Har aman da ta dinga ji Mubina leda ta bata sannan ta dinga shafa mata baya tana cewa ta hura iskar bakinta a ledar. A haka har su ka daidaita a iska. "Allah Ya yi miki albarka Ya raya miki zuri'a. Ya jiƙan mahaifa." "Amin Mama." "Yaya yaran su ke kirana. Kema in babu damuwa ki dinga kirana da hakan." Da murmushi Mubina ta ce "to Yaya." Lokacin da aka kawo abinci Yaya bacci take yi. Mubina ta tasheta ta ci sannan da dabara ta sako zancen da ta zauna dominsa. "Takardar nan ta passport ɗin ki naga jininki O- ne ko?" "Ban dai riƙe ba amma tun a gida yara ke cewa O. Wani abin ne?" Da sauri Mubina ta girgiza kai tana mai son ɓoye zallar farincikinta sai dai Yaya ta fi ta wayo. "Babu wata matsala. Jinin naki mai kyau ne domin babu wata lalurar da za a buƙaci wani abu na sassan jiki da ba za ki iya taimakawa ba." "Ikon Allah. Ki ce idan na koma in nemi ƙarin sadaki a wajen Abban su Hamdi." Dariya Mubina tayi kawai sannan ta kuma tambayarta ƴaƴanta nawa. "Huɗu ne." "Kin taɓa yin ɓari?" "Wai, sosai kuwa. Biyu nayi kafin babbar. A tsakaninsu kuma yaran na ƙara uku. Wani lokacin sai na sa rai da cikin sai ya zube." Mubina bayani gamsashshe tayi wa Yaya game da rhesus da irin rawar da yake takawa idan aka sami saɓaninsa a tsakanin mata da miji wurin haihuwa. "Ilimi kogi. Dole ake cewa tafiya mabuɗin ilimi. Kinga zaman abin da bai kai wuni ba amma na ƙaru." Da yake ita ɗin akwai zurfafa tunani sai ta tambayi Mubina me yaja hankalinta har take ganin farinciki a tattare da ita game da jinin. Kunya ta kama Mubina. "Allah ni likita ce. Yana ƙayatar da mu ganin masu abin da wasu su ke buƙata ido rufe." Tayi dariya "kada ki ce yau kin gamu da mayya." Yaya ma dariya tayi. Sai dai kuma daga lokacin ta dinga karantar Mubina. Akwai abin da take ganin ta ɓoye mata. Kai gani ma take tana son faɗa mata amma kamar tana jin tsoro. A zuciyarta ta ce 'Allah Yasa alkhairi ne'. *** Yau sun tashi jikin na Kamal kwata kwata babu daɗi. Anyi alluran, an saka ruwa amma duk da haka ciwo yaƙi sauka. Su Umma ke kuka Hajiya na rarrashinsu. Tun zuwansu ko sau ɗaya bata zubar da hawaye ba. Halin da ta riski Kamal a kullum gani take ba zai shiga wata sa'ar ba. Sai dare take zuwa asibitin. Kullum tana hanya daga Jeddah inda asibitin yake zuwa Makka ta wuni a Harami tana ibada. Ta zabge sosai kamar ba ita ba. Masu rarrashin nata kuma sun fita nuna rauni. Suna tausayin Kamal suna tausayinta. "Yanzu Alhaji ace Kamal yana cikin wannan yanayi amma Taj bai sani ba? Anya kun yi musu adalci kuwa? Ka yiwa sauran ƴan uwansa adalci? Yau ko addu'a su ke yi masa ai zai sami rangwamen ciwo." Cewar Mama tana zubar da hawaye. "Kin fi kowa sanin cewa dukkaninsu sai sun taho. Ina gudun su zo a yanzu su haɗu wajen kashe masa ƙarfin gwiwarsa da koke kokensu." "Ka yi haƙuri amma wannan magana fa ba hujja bace. Yaron da ya tashi a gidan gandu irin namu ace yana jinya da jama'ar da ko rabin gidan basu kai ba ai zai ji babu daɗi." "Hajiyayye bata faɗa muku za su taho ba?" "Ta faɗa. Kayi haƙuri. Na rasa me ya dace ayi ne." Ta cigaba da kukanta "ko sake auna jinin nasa za ayi a tabbatar? Ko kuma..." "Mama ki yi haƙuri" Kamal ne ya yi maganar yana mai runtse idanuwansa. Komai a jikinsa ciwo yake yi. Magana ma da ƙyar yake cijewa ya yi. Muryarsa da su ka ji ce tasa su duka matsowa kusa da gadon nasa suna yi masa sannu. A lokacin Bishir ya shigo da waya a hannu yana kallon Alhaji. "Ya Taj ne wai yake ta neman Ya Kamal. Ya tayar da hankalinsa wai tun jiya basu yi magana ba. Me zan ..." "Kira min shi." Inna ta hana "Kamal yanzu ba lokacin da za ka biye masa kuna hira bane." "Bai sani ba Inna. Ki ka sani ma ko bamu da rabon sake ga.." Umma bata bari ya gama magana ba ta ce "Ya isa. Kira masa shi Bishir." Kiran yayi amma Kamal ba zai iya karɓa ba sai Bishir ne ya kara masa a kunne. "In ka fara neman mutum kamar tsohuwar bazawara ta fito neman miji." Kamal ya faɗi yana murmushi da ƙyar. Taj ya yi murmushi "Ba zan ji haushi ba balle buƙata ta taƙi biya." "Me ka ke so?" "Tambaya zan yi maka. Please ka matsa daga inda su Alhaji su ke." "Na matsa. Mene ne?" "Me Alhaji yake ɓoye mana ne Happiness? Tun tafiyarku hankalina ya kasa kwanciya. Amarcin ma na kasa sakin jiki nayi abuna yadda ya dace." "In na yarda da kai in tafi a tsaye. Akwai damuwar da zata sa ka kasa amarci?" Yana maganar ne ido a rufe don baya son haɗa ido da iyayensa. Ai kuwa hatta Alhaji sai da duka su ka yi dariya. Kamal ya nuna wa Taj lallai komai lafiya ƙalau. Ba yadda ya iya dole ya yarda. "Mun haɗu da Mubina a airport da mu ka raka Yaya. Anya ibada ku ka je yi kuwa?" Nan ma Kamal dariya yayi. Shi da Alhaji sun san da zuwanta. An kuma faɗawa su Hajiya. Ta ce duba shi za ta zo yi amma kowa ya san zuwan nata na sallama ne. Bakunan su ne dai ba za su iya faɗin abin da yake zuci ba. Sun cire hope. "Happiness amana..." "Me?" Kamal ya dawo daga tunani. Bai ji me Taj yace ba. Taj ya sake maimaita cewa zai bashi amana. Ya sanar dashi lalurar da ta same shi da abin da su Salwa su ka yi. Shi ya so fara faɗawa amma ya gagara samunsa a waya. Hankalin Kamal ya tashi sosai. "Ka yi min addua kafin na zo. Idan ban warke ba to ka shirya. Ni yara 12 za a haifa min kuma cin mu da sha duka wuyanka zai dawo." "Har wasa kake yi da abu mai mahimmanci irin wannan?" "Ina da kai Happiness mene ne zai dame ni? Amma nayi tunanin za ku j8 zancen a wajen su Alhaji fa. Sai naga da kai da su Bishir shiru. Ya Ahmad kuma kunyar nemansa nake yi." "Da gaskiyarka. Amma na san ba zai riƙe ka a rai ba. Yana masallaci." Suna gama wayar, Hamdi dake zaune kusa da shi tana shirya akwatin tafiyarta ya fuskanta. "Kin san Allah, akwai abin da yake faruwa mai girma da su Alhaji. Yau kwana nawa a ce babu wanda ya faɗawa su Happiness abin da ya faru?" "Maybe don kada su tashi hankalinsu tunda ibada su ka je" ta faɗa domin kwantar masa da hankali. "Allah Ya kai mu gobe. Idan ma akwai wani abu zan gani." "Me yasa ba za ka yi tunanin komai lafiya ba?" Hamdi ta sake faɗi. "Saboda jikina yana bani cewa akwai problem. Kin tuna abin da ya faru daga ciwon kan da nayi a wurin dinner? Saboda damuwa gida Alhaji ya mayar dani. Sai yanzu da na faɗa musu hancina da harshe sun zama useless ne su ke nuna min rashin damuwar da nayi tsammanin gani." Zungure shi Hamdi tayi tana murmushi "wannan dai rigima ce kawai da shagwaɓa. To taho in jajanta maka. Ni ai ba na kira komai naka useless ba." Taj ya saki fuska yana murmushi. "Allah ko Mrs Happy?" "Kana musu ne?" Ta kashe masa iso. Aikin da take yi ya nemi rabata da shi taki yarda tana yi masa dariya. Yanayin damuwar da ya shiga ya kau. Ya koma tsakaninsu sai tsokanar juna. "Wannan akwatin kin haɗa shi ya kai sau goma." "Ba fa zan damu ba idan ka tsoka ne ni akan wannan tafiyar. Kuma baka ga komai ba. Rawar kai sai na saka harami." Ta tashi tana buɗa kafaɗa "kai dai Allah Ya kai mu." "Amin." *** Daga airport ya kamata su raba tafiya da Mubina. Su Yaya Madina za su fara tafiya ita kuma cikin Jeddah za ta ƙarasa asibitin da Kamal yake mai suna King Abdul Aziz Medical City. Yadda ta dinga bin Yaya tana taimaka mata da abubuwa duk da cewa abokan tafiyarta ma suna ƙoƙari duk sai ya dami Yaya. Jikinta ya bata akwai wata a ƙasa. Kafin tayi tambayar ne Mubina ta ce za ta shiga banɗaki. Yaya sai ta nemi su jira domin su yi sallama. Zuciya cike da tunani da fargaba Mubina ta shiga banɗaki. Ta shige guda ta rufe kanta kawai ta fashe da kuka. Duk yadda take son Kamal ta sani cewa idan Yaya mahaifiyarta ce ba za ta yi na'am kai tsaye ta bada ƙodarta ba. Uwa fa aka ce. Ina adalci da sanin ya kamata idanta ingiza wadda bata sani ba tayi abu saboda nata son zuciyar? "Allah Ka yafe ni" ta faɗa tana sake goge hawaye. Tana buɗe ƙofar tayi ido huɗu da Yaya. "Lafiya dai ko Mubina? Na ji ki shiru." Murmushi ta kama yi na dole "abu ne ya shigar min ido. Kin gan shi yayi ja ko? Mu je na ɗauki kayana kada na sa ku yi dare a hanya." "To" Yaya ta ce ba don ta yarda ba. Da su ka fito taxi Mubina ta shiga. Yaya na kallo motar kawai taji wani abu ya tsungule ta. Jakarta ta hannu ce kawai a jikinta ta dubi matan tawagar tasu ta ce musu tana zuwa. "Maman Sajida ina za ki?" "Ku wuce Madinan don Allah. Zan same ku da yardar Allah." Suna ta tsayar da ita amma ina. Da irin nata saurin ta shiga tasin gabanta ta nuna masa wadda Mubina ke ciki tana shirin barin harabar airport ɗin. "Haza sayyara" ta nuna motar, shi kuwa ya gane ya gyaɗa kai "to yalla-yalla, ta'al-ta'al. Kuḍi, uhmmm, riyalai haqibatun" ta jijjiga masa jakarta. Bawan Allah damuwar da ya gani a tare da ita ta ishe shi. Kuma duk daƙiƙancin mutum dole ya gane me ta faɗa. Zama ya ce tayi ya kwashi mota su ka bi su Mubina. Tafiya kamar ba za ta ƙare ba. Wajen minti talatin sannan motar ta tsaya a bakin asibitin. Yaya ta bari sai da Mubina ta shige ta wajen wata ƙofar gilas da wani yaro mai fuskar Taj yake tsaye yana jiranta sannan ta bi bayansu. Haka kawai ta dinga jin faɗuwar gaba. Tana tafiya basu ganta ba har su ka shiga lift. Nan fa ake yinta. Na farko bata taɓa shiga ba kuma bata san inda za su je ba. Ita a tunaninta ma ƙofar ɗaki ce. Ta tsaya a jiki ta fara ƙwanƙwasawa sai ga wani mutum. Ya tsayar da lift ɗin taga ƙofa ta buɗe amma basa ciki. "Ya Hayyu Ya Qayyumu. Ina su ka ɓace kuma?" Kamar daga sama sai taji kuka a bayanta. Juyawar nan da za ta yi taga Hajiya ce a birkice. Babu ɓata lokaci sai ta shiga tunda Hajiyar ma ya shiga kuma san bata lura da ita ba. Addu'a take yi tana wani irin kuka. Alhaji da kansa ya yi kiranta ya ce ta dawo jikin Kamal babu daɗi. "Allah na gatan bawa. Ya Rabbi ga Kamal. Ubangijina ka ƙara rufa min asiri akan ƙaddarar rayuwa. Allah kada in yi saɓo. Ka taimakeni Ya Rabbi. Wayyo Allah. Allah Ka dubi Kamal." Yaya ta gama sarewa da lamarin nan. Me ya sami Kamal wanda su Taj basu sani ba? Tayi imanin babu abin da zai zaunar da Taj yana raha a gida bayan lalurar da same shi da ya san ɗan uwansa yana wani hali. Da sassarfa Hajiya ta fita daga lift ita ma Yaya tabi bayanta. Don ma tana ɗan jiri saboda rashin sabo. Ƙofar ɗakin a buɗe take. Tana hango Kamal a kwance da likitoci a kansa. Fuskarsa ɓoye cikin abin shaƙar iska. Don dai taji Hajiya ta ambace shi ne ta gane shi. A ƙofar ɗakin Yaya Kubra ce ta rungume Alhaji tana kuka. Inna, Umma da Mama kowacce fuska jiƙe da hawaye. Mubina kuwa gefen bango ta samu tana wani irin kuka a hankali. Bata yi tunanin ƙarasawa garesu ba. Ta tuna kalaman Mubina ne kawai. Wani likita na fitowa daga ɗakin Yaya ta bishi da sauri. Hankalinsa a tashe kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tausaya mata. Saurin da take yi da ƙafarta a haka ya san akwai wahala. Yaya ta nuna ɗakin ta sake haɗo larabcinta na islamiyya a karo na biyu. "Haka gurfa..." ya gyaɗa kai "to ma haza Kamal?" Likitan ya kalleta yana son yi mata bayani amma sauri yake yi. Juyawa yayi sai ta kuma kiransa. Da ya juyo zai nuna mata inda za ta je reception idan taimako take nema sai ta miƙa masa takardar nan da aka rubuta jininta. "O netif (negative)" ta nuna ƙirjinta "Kamal ahali (ɗan uwanta ne)." "Alhamdulillah" ya fara cewa zai koma ɗakin ta girgiza kai. "Hausa...a nemo mai yi min Hausa." "Hausa? Nigeria? Kano?" "Nace maka ahali ai su ɗin" ta kuma nuno ɗakin. Ya gyaɗa kai kuwa ya ce ta biyo shi. Suna tafe yana buge bugen waya. Bata san cigiyar mai jin hausa yake yi ba. Ba a wahala ba ya samu. Mai shara ne amma ya tadi gida. Ba shi da nisa dai. Wuri mai kyau aka bata ta zauna har mutumin ya zo. Ɗan Katsina ne yake aiki a nan. Shi likitan ya faɗawa ya tambayeta alaƙarsu. Sun yi mamakin wai wan mijin ƴarta ne Nan da nan ta faɗa. Sai ya sanar da shi ciwon Kamal da abin da yake buƙata. Yaya ta dafe ƙirji da fari. Sai kuma kawai ta fashe da kuka tana faɗin, "Allah Hakimu. Allah Hakimu." Daga ƙarshe ta ɗauko wayarta ta nuna nambar Abba Habibu ta ce a kira shi. Likitan da kansa ya kira. Yana ganin baƙuwar namba ta Saudiyya ya ɗauka. A kiɗime yake sosai. Abokan tafiyar sun kira gida sun ce a faɗa masa abin da ya faru. Bai riga ya sanar da su Sajida ba amma ya gama gigicewa. "Ina kika je? Kin jefa ni a wani irin tashin hankali." "Allah Ya huci zuciyarka Yayana Habibu. Tuba nake Abban Sajida." Murmushi ya yi "yanzu kina ina?" "Asibiti." "Baki da lafiya ne?" Ya sake tashin hankalinsa "A'a, alfarma nake nema domin babu lokaci." "Kin fara tsorata ni. Me ya faru?" "Yaya Habibu mijin Jinjin miskiniyar Allah. Da uwata da ubana Allah Ya gatance rayuta da iyayenka. Kirari nake maka mijina a duniya da ƙiyama. Ƙanin Zeenatu uban Zeenatu ɗawisun zuciyata. Domin isa da alfarmar Mai Duka kayi min lamuni in share hawayen wata uwa kamar yadda Allah Ya share mana ranar auren yaran nan" "Me kike so?" Ya ce da tsinkakkiyar zuciya. "Ceton rai zan yi!" "Kiyi min magana yadda zan gane." "Wallahi ba zan iya ba. Amma ina so ka sani cewa ikon Allah ne ya kawoni ba tanadinmu ba. Komai da yake faruwa damu daga tsarin Mai Kowa da Komai ne." "Jikina rawa yake yi. Idan na hanaki za ki haƙura?" "Sosai kuwa. Amma ina da yaƙinin cewa kai ɗin kafi kowa kyawun zuciya a duka mutanen da na sani. Duk abin da za kayi domin ka taimaki wani kana yi. Shi yasa Allah ba Ya barin kowa yaga bayan ka." "Khadija." Ya kirata da sunanta na gaskiya. "Yayana." Ta amsa da dakakkiyar murya don bata son komai ya karyar mata da zuciya. "Ki kira ni idan kin gama. Tsoro mai girma ya shiga zuciyata. Amma naji ba zan iya hanaki ko mene ne ba. Allah Ya baki ikon yin taimakon ba tare da kin wahala ba." "Amin." Sallama su ka yi ta ce ta shirya. Likitan ya kira hukumar asibiti ya sanar. Komai cikin gaggawa ake yi saboda Kamal ya kai wata gaɓa mai sammatsi. Aka gama cike ciken takardu sannan aka bata form ta cike da taimakon mai sharar nan da yake karanta mata ya fassara. Daga nan lab aka je aka yiwa Yaya dukkan wani gwaji na dacewa. Sakamakon da aka samu sai shukura. Likitan ya ce su je wajen su Alhaji ta ce a'a. Kawai a zo ayi. Ɗaki VIP aka bata ta zauna kafin a shiryo Kamal. Tana zama ta dubi mai sharar nan. Ɗan dattijo ne kamar Abba Habibu. "Yaya sunan ka ne Malam?" "Salisu." "To Mal. Salisu recoder nake so ka kunno min a waya zan yi magana. Idan an fito daga aikin ka kunnawa su Alh. Hayatu." A wayarsa ya kunna ya bata. Ta kara a bakinta ta soma magana. Kalaman da take yi sun shige shi fiye da tunani har ta kai yana zubar da ƙwalla. * A ƙofar ɗakin su ka dinga zubewa suna sujjadar godiya ga Allah. Likita ya ce an sami donor amma ba a bari sun san waye ba. Mubina sai da ta tuno Yaya. Sai tayi murmushi tana godiya ga Allah da bata yi mata magana ba. Kamal bai san a inda yake ba har aka gama komai aka shiga tiyata. Kamar wasa sai da su ka kwashi awa huɗu ana abu ɗaya sannan aka kammala. Addu'a kam da shi da Yaya duk sun sha ta sosai. * ICU aka gangara su su biyun domin kulawa ta musamman sannan wanda ya jagoranci aikin ya zo ya sami su Alhaji. Fuskokinsu duka babu nutsuwa. Yana tsayuwa su ka taso gabansa. "Alhamdulillah, it was a success." Kowa sai hamdala da ajiyar zuciya suna rungume junansu. "What about the donor?" Alhaji ya yi tambayar dake gabansa. "He" likitan ya nuna Mal. Salisu yana murmushi "will explain." Kallon rashin sani su ka yi masa. Ya murmusa ya ce dama basu san shi ba. Shi kuma bashi da wata alaƙa da donor ɗin. Amma ga saƙon da ta ce a kunna musu idan an fito. Daga gyaran muryar Mubina ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba da ta gane Yaya ce. (Assalamu alaikum wa rahmatullah. Suna na Khadija Yusuf wadda aka fi sani da Jinjin matar Habibu.) "Wannan ba muryar Yayan Hamdiyya bace?" Umma ta soma magana da wata irin kaɗuwa. "Ku saurara" Alhaji ya karɓi wayar don ji yayi duk wani gashi na jikinsa ya miƙe tsaye. (Na bawa Kamal ƙoda ba bisa tilastawa ko cinikayya ba. Cikin Hikimar Allah maigidana ya biya min kuɗin Umara da tanadin shekaru. Sai gashi ina zuwa Allah Ya yi sanadin da naga Kamal a yanayin da nayi imanin ƴan uwansa na gida basu sani ba. Kuma ni kaɗai ce Allah Ya ni'imta da damar taimaka masa a kusa. Lallai Girman Ubangijina ba abin wasa bane. Ya tsara komai daki daki ni wace ce da zan fahimci hakan kuma na juya baya? Na aminta saboda Kamal na zo a wannan rana. Allah Yasa lafiyar ta samu. Ina fata mahaifinka ba zai ƙyamaci rayuwarka da ƙodar miskiniya ba. Abu na biyu kuma idan ban tashi ba don Allah ku faɗawa Abban su Sajida ba a bina bashi kuma ni ma bana bi. Na sallami kowa kafin na taho. Akwai banki a ƙasan gadona. Na tanadin auren Halifana ne. Sajida, Hamdi da Zeenatu don Allah ku haɗa kai ku zama sirrin juna da ƙaninku. Ina yi muku fatan Allah Ya albarka ce ku a duk inda kuke. Allah Ya tsayar da ku duka akan ƙafafuwanku ta yadda babu wanda zai zamewa wani nauyi a gaba balle har ya ƙosa a sami tawayar zumunci. Ku bawa Abbanku goyon baya ya sake aure. Yaya Habibu Allah Ya gatance maka kamar yadda kayi min. -Cikin kuka ta cigaba da magana- bakina ba zai taɓa daina yabonka ba har numfashin ƙarshe. A wajen wasu ka gaza, a wajena kuwa a wannan zamani babu mai martaba da daraja kamar ka. Allah Yasa Habibu ne mijina a lokacin da Allah Ya sabunta min halitta da miƙaƙen jiki a aljanna. A ƙarshe don Allah ku roƙa min gafarar iyayena. Ku cewa Baba ina gaishe shi. Ku bawa Innata haƙuri.) Sai ta ɗan ja hanci (umara na zo ashe bani da rabon ganin ɗakin Allah da ziyarar masoyina. Amma Alhamdulillah. Kamal da zuciya ɗaya zan taimaka maka. Allah Ya bamu alkhairi. Nagode.) Audio ɗin a nan ya ƙare. Mal. Salisu ya faɗa musu yadda ta sanar dashi zuwanta asibitin. Mubina ta biyo ba tare da ta sani ba. "Wallahi ban sani ba. Kuma ni bamu yi zancen da ita ba." Mubina ta faɗi a ruɗe. "Hikimar Allah aka ce Dr. Mubina. Magana ta ƙare." Inna ta faɗi tana ɗan bubbuga mata baya. Alh. Hayatu kuwa juyawa yayi zai bar wajen. Ahmad ya bi shi da sauri. Su Hajiya ma tambayarsa au ke yi ina zai je a wannan yanayin. "Ashe duk baku ji lokacin da ta ce Umra ta zo ba?" "Mun sani dama. Taj ya so mu jinkirta tahowarmu tunda ita kaɗai ce mu ka ƙi. Ashe saurin da muke yi ita ce maganin komai." "Ahmad samo min mota na koma hotel na sako harami na." "Alhaji..." Inna ta soma magana. "Idan bata tashi ba fa? Umrar zan yi mata. Ai ya halatta ka yiwa wanda bashi da dama ko?" Yayi tambayar ga Mal. Salisu. "Ana yi." "Nima zan yi mata" Hajiya ta share hawaye ta miƙe tsaye. "Nima" "Nima" "Nima" Sai da ya rage Bishir kaɗai sannan Alhaji ya ce ya haƙura kada a bar asibitin babu kowa. Ahmad ma zama ya yi saboda Alhaji ya bashi aikin neman visa da ticket ko nawa za a kashe domin kawo Abba Habibu. Da su ka fita a mota abin mamaki ga iyalinsa dake baya bai wuce yadda yake ta goge idanunsa da bayan hannu ba. Yau Alh. Hayatu ne yake kuka akan wani ba jininsa ba. Tun yana yi a zuci har ta kasance suna jin shessheƙarsa. Wannan yasa babu wadda bata bayyana nata kukan ba. Direban tasi ɗin yana son tambayarsu amma kasa. Sai haƙuri kawai yake basu. Jiransu su ka buƙaci yayi su ka shiga hotel ɗin su ka yi haramar Umra kamar yadda yake a tsare cewa mai shiga Makka daga Jeddah nan ne Miqatinsa. Mutum biyar su ka fito a tare. Alh. Hayatu, Haj. Gambo, Mama A'i, Umma Jamila, Inna Abu da Sulaiman Hayatu Sule (Abba) da niyyar yiwa Jinjin ɗin Abba Habibu Umra a ƙasa Mai Tsarki. _In sha Allah last post ba zai kai Lahadi ba._ [4/2, 11:37 PM] +234 803 761 4669: RAYUWA DA GIƁI 37 Batul Mamman💖 ALLAH YA SANYAYA MUKU ZUƘATA GWARGWADON HAƘURINKU. INA SO KU SANI CEWA BA DA GANGAN BANE. *** Salati a jere a jere Amma ta dinga yi a yayinda Alh Babba yake sanar da ita abin da yake faruwa. Tana yi muryarta na rawa bata ma san cewa ta fara kuka ba sai da taji yana rarrashinta. "Yaya Babba dashen ƙoda fa ka ce..." muryarta ta sarƙe a tsakiyar zancen. "Godiya ya kamata mu yi wa Allah ba kuka ba. Banda haka da yanzu wani zancen ake ba wannan ba." Da ta tuna hakan sai taji wani irin tsoron Allah Ya sske shigarta. Barin ma da ya ɗan labarta mata yadda aka yi Yaya ta je asibitin. Bayan hankali ya ɗan kwanta tayi masa zancen yaushe za su tafi. "Mu bari zuwa nan da kwana biyu tukunna. Sannan don Allah ki kama bakin ki kiyi shiru. Su Taj basu san komai ba. Haka ma shi Habibu da yaransa. Ke kaɗai da sauran ƴan uwa na faɗa wa domin Hayatu yana cikin ruɗani. Lallai yana buƙatar tausasawa daga wajen ƴan uwansa." *** Tashin hankali mara misali ne ya kama Abba Habibu bayan sun gama waya da Yaya. Awanni shida sun wuce amma ya rasa inda zai tsoma ransa. Ya sake kiran layin da ta bada numbarsa su ka yi magana yafi a ƙirga ba a ɗauka. Lokacin likitan yana cikin tiyata ana transplant surgery ɗin. Da ya fito kuma wasu abubuwan su ka ɗauke masa hankali. Can bayan isha ya dawo daga masallaci sai ga wayar Ahmad. Shi dai tunda yaga baƙuwar lambar Saudiyya kawai ya ɗauka da sauri. Sallama ya yi yana jiran ta amsa sai yaji muryar namiji. Zuciyarsa bata ƙara tsinkewa ba sai da Ahmad ɗin ya gabatar da kansa. "Ahmad ne, yayan Taj." "Ahmad kana da labarin halin da iyalina take ciki ne?" Ya tambaya da sanyin jiki. Zuciyarsa ta bashi dalilin kiran kenan. "Alhamdulillah." Ahmad ya kasa ɗorawa daga nan. "Hamdala ai wajibin musulmi ce ko a bakin kura yake. Ina nufin labarin da zan iya bawa ƴaƴanta. Kuma tana da uwa da uba a raye. Su ma ina neman abin faɗa musu." Ya ce da wani irin yanayi mai raunana zuciyar mai sauraro. "Haka ne" Ahmad ya yi jim kaɗan sannan ya cigaba da magana "akwai abokina da zai zo nan gidan ka yanzu. Na faɗa masa sunan unguwar. Idan ya zo zai kira ka." Allah kaɗai Yake riƙe da Abba Habibu. Maganganun Ahmad sun sake dulmiya shi cikin fargaba. "Abokin ka? A gida na? Me zai kawo shi?" A gurguje Ahmad ya ce ticket za a saya masa inji Alh. Hayatu. Idan anyi sa'a yana da visa to a gobe zai sami damar tahowa sai dai ba jirgin su Hamdi ba. "Ni ɗin Musulmi ne Ahmad. Kullum ina adduar kada Allah Ya ɗora min ƙaddarar da tafi ƙarfin imani na. In sha Allah idan ka faɗa min gaskiya ba zan kasa ɗauka ba." Cike da jin nauyi Ahmad ya ce "Don Allah kada ka tambayeni. Ba zan iya faɗa maka ba. Na dai san tana nan lafiya." "Hakan ma amsa ce. Da ranta kenan." Sai ya ƙara da cewa "ina Alhajin?" "Nauyin ka ba zai bari ya iya yi maka magana a waya ba. Ya tafi yiwa Maman Hamdiyya Umra amma ka kwantar da hankalinka da ranta. Wannan shi kaɗai ne abin zan iya faɗa maka." "Nagode." Da ya ajiye wayar sai hawaye ya sauko masa. Ya sharce su da sauri. Yawan kuka yana daga cikin abubuwan da yake gudu saboda kada a danganta shi da mata. "Me kika yi Jinjin? Wane irin taimako ne?" Abokin Ahmad ya kira shi. Ya bada passport ya koma cikin gida. Zee da Halifa basu san wainar da ake toyawa ba. A wannan yanayin na zulumi ya kwana bai runtsa ba. Ƙarfe tara da rabi na safe abokin Ahmad ya kira shi ya ce su haɗu a airport nan da uku na rana. Jirgin da zai bi takwas zai tashi na dare. Kaɗuwa iya kaɗuwa Abba Habibu ya gama yi. A haka ya dinga ɓoyewa Zee da Halifa saboda rashin sanin amsar da ta dace idan sun nemi ƙarin bayani. Kaya kala uku ya iya haɗawa a wata ƙaramar jaka. Suma ɗin don ya san dole ne dai ya canja ba don haka ba da a haka zai tafi. Agogon bangon ɗakin ya kalla. Goma ma bata yi ba. Gani yake kamar ya jawo lokaci ya ganshi tare da Yaya ko a wane hali take kuwa. "Abba in yi tuwon shinkafa da rana?" Muryar Zee a ƙofar ɗakin yaji. Sannan ya tuna ai bashi da damar tafiya ya barsu su kaɗai a gida. Dole wani ya san me yake faruwa. Shiru ba zai kai shi ko'ina ba. "Abba?" Zee ta sake yin magana a hankali don ta fara tunanin ko bacci ya koma. Tasowa yayi ya buɗe ƙofar ta matsa masa ya fito. "Kada ki ɗora komai yanzu sai iya wanda za ku ci. Shi ma ɗin kaɗan. Zan ɗan fita unguwa na dawo." Yanayinsa ya bawa Zee tsoro. Ta kalle shi a tsanake. "Abba baka da lafiya ne?" "Me ki ka gani?" Ya ƙirƙiro murmushi. "Wallahi duk kayi wani iri." Ta faɗi da sanyin jiki. A zuciyarta kuwa tunani take ba zai wuce kewar Yaya yake yi ba. "Bacci ne bai isheni ba. Matata ta tafi ta barni." Zee ƙumshe baki tayi tana dariyar shaƙiyanci. Da haka Abba Habibu ya samu ya fita ba tare da ta tsananta bincike ba. * Anti Zinatu da sauran yan uwan Abba Habibu sun shiga mummunan tashin hankali bayan ya gama faɗa musu halin da ake ciki. A gidan Anti Zinatun suka haɗu domin ya kikkira su kafin ya iso gidan. Cikin sa'a kuma duka babu mai uzurin da ya hana shi fitowa akan lokaci. "Wai ba da dangin mijin Labiba ta tafi ba? Ya aka yi cikinsu babu wanda ya bi bayanta?" Wadda tayi tambayar tana rufe baki Abdulƙadir ya yi musu alama da hannayensa akan yana so su saurare shi. Sai da yaga sun dawo da hankali gareshi ya dubi Abba Habibu cikin yanayi na jin nauyi. "Gaskiya ina tsammanin abin da nake ji yana faruwa a Iyafot ɗin ƙasa mai Tsarki fa gaske ne." "Me kaji?" Suka haɗa baki wajen tambayarsa. Sai da ya ɗan jajantawa kansa girman maganar kafin ya fitar da ita. "Yaya Habibu kayi haƙuri da furucina amma magana ta gaskiya ita ce yanzu an tsananta kame da binciken masu nakasa." Da sauri Abba Habibu ya canja zama "me? Me ka ke nufi?" "Naga ya faru a unguwarmu. A'ilo Gurguwa ko ƙasar bata shiga ba aka aunota gida. Kuma kusan kowa ya sani cewa bara ta tafi yi." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Salam. Subhanallahi..." Abba Habibu yake ta faɗi shi kaɗai. Sauran ƴan uwansu kuwa sai sallallami. Abdulƙadir ya dubi Abba Habibu "bani da tabbas amma ina zargin haka ɗin ne. Idan ba haka ba me zai sa a kama ta?" "Ni fa ban ce an kama ta ba" Abba Habibu yaci gyaransa da wuri "iyalin Yaya Hayatu sun san halin da take ciki. Faɗa ne ba za su yi ba a waya." "Ba da nufin tozarci nake yi maka zancen nan ba. Na faɗi abin da na sani ne saboda ka tafi da shirinka wajen kareta." "Maganganunka tsorata ni suke yi Abdulƙadir. A bar zancen nan kawai." Anti Zinatu tana zubar hawaye ta ce "Habibu ko mun ƙi ko mun so fa da ƙamshin gaskiya cikin zancen nan. Kamar yadda yace ne ka tafi da shiri a zuciyarka kada gaskiya ta baka mamaki. Zuciyata sam bata son wannan tunanin to amma shi kaɗai ne muke iya hasashe." Abba Habibu gani yayi bashi da wata hanyar kashe maganar. Sun riga sun ƙarfafa zarginsu. Shi kuwa tunanin kaɗai ma ya ishe shi fargaba. A Saudiyya, Sijin (prison) suke kai kusan duk mai laifi irin wannan su ajiye. Idan na korowa gida ne daga can ake kai su airport. Masu hukuncin kisa....inaaa. Zumbur ya miƙe ya zura takalmansa. "Bari na ƙarasa gidan na sanar dasu su shirya su taho. Wannan magana kuma don Allah ayi shiru sai naje na ganewa idanuna." Zaman bai ƙara masa komai ba sai tashin hankali. Ya yi imanin basu faɗi komai domin cusguna masa ba. Iya gaskiyar da suke iya hangowa ce aka faɗa masa. A hanya yayi ta tufka da warwara akan abin da zai faɗawa su Zee. Da fari tunanin ya ce musu Inna Luba ce babu lafiya. Da sauri ya girgiza kai da ya hango saurin gano shi da za ayi. Idan basu bishi ba tabbas zasu kirata a waya domin jin yanayin jikin nata. Daga nan ita kuma nata hankalin ya tashi. Ƙarshe dai gaskiyar da yake gudu dole ya faɗeta domin duk inda yace musu zai tafi dole za su kira waya. * Abba Habibu ya kasa hakuri ganin ya gama bayani amma Halifa da Zee ko motsi basu yi ba. Zuciyarsa tana cike da fargabar kada su matsanta masa da tambaya akan kwaskwarimar da ya yiwa zancen. Nuna musu yayi cewa Alh. Hayatu da kansa ya kira shi yace bai dace Yaya ta tafi ita kadai ba. Shine yasa aka yi masa komai cikin gaggawa don ya tafi da wuri. Kamar ba za su yi magana ba sai kuma Zee ta fashe da kuka. Tana jan hanci tana magana. "Wallahi Abba tun zancen tafiyar tunanin da nake ta yi kenan nima. Kasan ko taimako take nema ba lallai ta sanar da abokan tafiyarta ba. Gashi Allah Ya kawo mata sauƙi da wurwuri." Murmushi Abba Habibu yayi da jin zancenta. "Hamdala ya kamata kiyi ba kuka ba." Halifa kuwa cewa yayi "To yanzu dai gidan wa zamu je mu zauna don wallahi tsoron gidan nan zan ji idan mu biyu ne kacal" Zee ta ce "Abba mu tafi gidan Anti Zinatu ko?" Da tsokana Halifa ya ce "Malaminmu dai ya ce mata masu aure su dinga yin komai da izinin miji." A fusace Zee ta tashi. Halifa ya fita da gudu ta bishi. Abba Habibu kuwa ya jinjina taimakon Allah mara yankewa. Ya gama tayar da hankalinsa sai gashi cikin sauki ya sami mafita. * Da ɗokin tafiyar nan Hamdi ta wuni jiya. Amma zuwa dare gabaɗaya jikinta ya mutu. Zee da Sajida da su ka yi waya ma babu ƴar zolayar nan da suke yi mata na ba saban ba za ta shiga jirgi. Hirar tafiyar Abban nasu ma sama-sama ta saka musu baki. Halifa kuwa dama list ya ce zai tura mata kamar yadda ya bawa Yaya. Harda cewa kada ta damu tunda Abba zai tafi zai rage wasu kayan. Yanayinta ya dami Taj sosai amma kuma bashi da kuzarin yawaita magana. Ya rasa mene ne yake ci masa rai ya hana shi walwala. Haka su ka kwana a gidan kowa da abin da yake kai komo a ƙirjinsa. Da safe su ka haɗu ƙarfe tara a harabar gidan Alh. Hayatu. Wata luxury bus ɗin gidan mai ɗaukan mutum talatin suka shiga direba ya kai su airport. Jirgin Abba Habibu sai uku. Su zasu shiga Qatar Airways, shi kuma zai shiga Ethiopia. * Saɓanin abin da ƴan uwan Taj suka yi zato na cewa zai dage sai Hamdi ta zauna kusa dashi kamar yadda tsarin boarding pass ɗinsu ya nuna, sai suka ga akasi. Daga zolaya a ka ce ta zauna seat ɗaya da ƙannensa sai suka ga ta tafi ko a jikinta. Zama tayi ta rufe idanunta tun kafin jirgin ya fara motsi. Taj kuma bai yi cigiyarta ba. Da Yaya Hajiyayye ta kula ne ta zo da kanta ta kamo hannunta. "Ina yi miki kallon wayayyiya za ki wani bari ƴan uwan miji su shigar miki hanci? Zaman me zaki yi a cikinsu bayan ga mijinki?" "Nan ɗin ma duk ɗaya ne." Hamdi ta amsa da sanyin murya. "Duk biyu dai." Cewar Yaya Hajiyayye. Ta kaita inda Taj yake. Ƙanwarsu dake zaune a wajen ta harara ba shiri ta tashi tana dariya. "Mu fa rigima muka so haɗawa. Muce sai ya biya zata dawo nan. Amma sun manna mana hauka ko magana babu wanda yayi." Ta faɗi tana dariya. "Sun san me suka taka ne. Gashi nan babbar yaya ta shigar musu. To mu dai duk da haka sai an biya mu. Abaya za ka saya mana dukkanin mu." Sai a lokacin Taj ya magantu bayan Hamdi ta zauna. "Dama ku biyun nan akan ku Alhaji ya fitar da zakka. Ƴan 419 kawai. Yahoo girls." Ai kuwa me zasu yi banda dariya. Har Hamdi sai da tayi. Da aka yi sanarwar kowa ya zauna Taj ya saka mata seat belt sannan ya kama hannunta ya sarƙe da nasa. A lokacin taji komai ya kwance mata. Raunin zuciyarta ya ninku sosai. Ƙwalla ta taru ta cika idanun fal. "Happy" ta kira Taj da murya a shaƙe. Ya gyara zama "Uhmm." "Me yasa na daina ɗokin tafiyar nan?" Bata jira yayi magana ba ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. "Shhhh. Please...." ya ɗago haɓarta. Abin da ya gani bai yi masa daɗi ba. She looked so confused. Ya buɗe hannuwansa ya yi mata kyakkyawar runguma. Tayi kukan mai isarta amma bata ji sauƙi ba. Suna wannan yanayin har jirgin ya gama taxi ya tashi. Riƙon da tayi masa ne kawai ya ƙara ƙarfi amma bata yarda da ɗago kanta ba. Jim kaɗan bayan jirgin ya daidaita a iska Taj yaji riƙon yayi sako-sako. Ya ɗan girgizata bata motsa ba, sai ma kwanciya da ta gyara a jikinsa tana bacci. Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasul ya karanta ya tofa mata sannan ya ranƙwafa ya kwantar mata da kujerarta. Baccin mai nauyi ne ya kama ta. Yaji daɗi domin jiya shi da ita marathon ɗin juye juye kawai suka dinga yi. Ba ita ta farka ba sai da ya rage bai fi minti talatin su sauka a Doha ba. Za su yi transit na awa biyu sannan su kama hanyar Saudiyya. Kowa watsewa yayi an tafi window shopping. Masu ra'ayi kuma idan sun ga abin da suke sha'awa za su saya. Hamdi da Taj kaɗai aka bari. Suna zaune gadin kaya sannan ba hira suke yi ba. Yaya Hajiyayye tana ankare dasu. Bata jima ba ta dawo ta sanya su a gaba. "Wai har kun fara faɗa ne daga aure?" "Tuf, tuf, tufff" Taj ya kama tofi da baki. Kama ƙugu tayi ta harare shi "Ni kake tofewa Tajo?" "Kece ana zaman lafiya zaki kawo abin da babu." "Ai naga sai wani basarwa kuke yi. Ko laulayi kika fara ne Hamdiyya?" Yadda ta sako maganar kai tsaye sai da Hamdi ta zabura ta hau rantse-rantsen ita bata da komai. Shi kuma Taj sai cewa yayi "ki ka sani ko akwai?" Wata uwar harara Hamdi ta watsa masa ba shiri. "Ni wallahi ƙalau nake." Yaya Hajiyayye ta kallesu tayi dariya. Kunya duk ta kama Hamdi. Taj ya tashi yace ta taso su zaga su ma. "Indai da matsala Hamdi ki faɗa min. Ko baki yi karatu da Firdaus ba kinsan dai na haifeki. Taj ɗin ma..." Da sauri Taj ya katse Yaya Hajiyayye kafin ta gama bayar dashi a gaban matarsa. "Haba, haba Yaya Hajiyayye. A lissafin waɗanda kika haifa ai kinsan dai babu ni. Sai da na zama mutum fa aka yi miki aure." "Wai ka zama mutum. Taj kaji tsoron Allah. Lokacin da kuke zuwa gidana fa ko tsar..." Da wani irin sauri Taj ya tashi yana dan dukan laɓɓansa a gabanta don tayi shiru. Tuni ta gano ashe ta ɗauko hanyar bada maza. Ita da Hamdi suka ƙyalƙyale da dariya. Ya harari Hamdi "Ke kuma meye abin dariya?" "Ba dariya nake ba ciwon kumatu ne ya kamani." Ta bashi amsa tana gimtse wata dariyar. A haka Yaya Hajiyayye tayi amfani da hikimar manya ta mantar dasu damuwarsu. Su ka rankaya da ita wajen ƴan uwansu ana ta raha har lokacin boarding ɗinsu yayi. A gefe guda ta tsaya tana kallon ƙannenta lokacin da suke ta hayaniya ta saki murmushin da ya tsaya a fatar bakinta kaɗai. Jikinta a mace yake da nauyin tunani kala-kala. Zuwa yanzu ta riga ta tabbatar ko me zasu tarar idan sun haɗu da ƴan uwansu ba mai daɗi bane. Fatanta kawai Allah Yasa yazo da sauƙi. *** JEDDAH A cikin ƴaƴan Alh. Hayatu ashirin da takwas, mutum biyar ne basu sami damar zuwa Umrar da aka fake musu da ita ba. Daga mai haihuwa ko yau ko gobe sai uku a ƙasashen ƙetare, ɗayar kuma an saka mata ranar defence na Masters a Sokoto. Da suka sauka daga jirgi sun yi zaton Umra zasu fara yi. Dama Abba ya yiwa Taj kwatancen inda zasu same shi idan sun fito. Basu wahala ba kuwa suka hango shi a jikin wata farar bus mai girma. Direbanta yana ciki a zaune. Da murnarsu suka nufi motar sai dai Abba sam babu wani kuzarin kirki a tare dashi sai yaƙe. Tambayar da Taj ya fara yi masa da ya miƙa masa hannu ita ce "Ina Happiness?" "Suna hotel. Motar zata yi kaɗan idan dukkanmu muka taho." "Ka san kuwa ni bana ƙaunar takura." Kowa ya yiwa kanwarsu da tayi maganar dariya saboda ƙibarta sannan suka fara tafiya. Taj da Hamdi wuri ɗaya suka zauna. Tana jikin taga shi kuma yana gefenta. Duk motsinsa tana karanta yadda walwalarsa ta sake ɗaukewa. "Kamar kana cikin damuwa." Ɗan guntun tsaki ya fara yi na frustration. "Kin san irin abin nan da mutum yake gane akwai matsala amma ya kasa pin pointing ɗinta?" Hamdi ta gyaɗa kai. "To haka nake ji." "In sha Allahu ma babu komai." Suka sarƙe hannuwansu waje guda har zuwa lokacin da motar ta fara slow. Nan fa hankalin kowa yayi mugun tashi. Sunan asibiti suke gani ɓaro-ɓaro. Daga jerin kujerun baya mafi kusa da direba Yaya Hajiyayye ta zura hannu ta kaiwa Abba duka a kafaɗa. Jikinta yana wata irin rawa. "Abba waye a asibiti? WAYE?" Da muryar kuka ta ƙara da cewa "Dama jikina ya bani wallahi" "Yaya ki bari mu shiga don Allah." Abba ya bata amsa da sanyin jiki. Motar kuwa ta ruɗe da hayaniyar fargabar ƴan uwan. Direban na tsayawa suka dinga fita da sauri. Taj ne kaɗai bai fita ba kuma ya hana Hamdi tashi sai da kowa ya fita. "Ka tashi mu fita don Allah." Ita kanta a gigice take. "Happiness ne fa bashi da lafiya. Ina jin ma babu shi gabaɗaya." Tafin hannu Hamdi tasa ta rufe masa baki. Sai ga hawaye ya sauko daga idanunsa. Hamdi ta rungume shi ita ma ta soma nata kukan. Tayar da ita yayi suka fita gaba na faɗuwa. Suna sauka daga motar suka ga Ahmad da Mubina. "Hamdi ban so maganata ta tabbata ba. Kinga Dr. Mubina" ya nuno mata su "dalilin Kamal ta zo na tabbata." Jikinta ya sake yin sanyi ƙalau har suka isa inda suke. Ahmad ya ɗan bugawa Taj kafaɗa. Mubina kuma ta rungumo Hamdi jikinta suka shiga lift kamar tana so ta rarrasheta. Mamakin hakan ya kama Hamdi. Ba wai bata damu da Kamal ba, amma a ganinta akwai waɗanda suka fita buƙatar rarrashi akan sa ko me ya same shi. Tamkar wanda bashi da laka Taj ya dinga tafiya da ƙofar lift ɗin ta buɗe. Suna yin kwanar farko ya hango zugar gidansu harda iyayen a corridor ana ta koke-koke. Taj ya kalli sama inda aka rubuta 'Room 7' sai yaji hankalinsa ya sake tashi. Wani zafi ya mamaye jikinsa. Bai san yadda aka yi ya isa gaban Alh. Hayatu ya tsaya ba. "Alhaji me ya same shi?" "Kidney transplant aka yi masa." Ya bashi amsa amma hankalinsa yana kan Hamdi. Wani irin nauyinta yake ji. Taj yayi gaba da sauri zai shiga ɗakin idanunsa sun yi wani irin ja mara misali. Bishir ya riƙe shi da ƙarfi ya janye shi daga wajen. Umarnin likitocin Kamal ne suka ce kada a shiga ɗakin duk da ya farfaɗo. Yana buƙatar hutu sosai. Ita Hamdi bata kula da abin da ya faru ba. Hankalinta yana kan su Inna. Ta rasa me zata yi saboda kowa hankalinsa a tashe yake. Kawai sai ta duƙa da nufin gaishesu. Umma tayi saurin tareta a jikinta. "Tashi Hamdi. Zo mu ƙarasa can ki zauna." Ta girgiza kai. "A'a zan zauna a nan nima." Ga mamakinta da na sauran Alhaji da kansa yace ta bi Umma. "Ku je Hamdi." Bata da zaɓi sama da bin Umman. Kallo duka sai ya dawo kanta. Haka ta bisu cike da tsarguwa. Me yasa za a ce ita kaɗai ta tafi? Ko sirri zasu yi? Ko dai Kamal ɗin ya... "Hamdiyya" Muryar Hajiya ce ta fito da yanayi mai ban tausayi. Hamdi ta juya ta ganta a tsaye. Hajiyan ta da ta sani da wannan dake gabanta da bambanci. Ramar da alamun rashin kwanciyar hankali sun yi yawa sosai. "Hajiya yaya mai jikin?" Hannuwanta Hajiya ta kama ta rufe da nata yatsun. Hamdi ta ɗaga kai taga Inna, Mama da Umma duka suna kallonta da wani irin yanayi na tausayi. Idanuwansu sun nuna alamun an sha kuka. A take jikinta ya soma rawa. A take taji gwiwoyinta sun saki ba za su iya ɗaukar nauyinta ba. Bata san jikinta ƙasa yake yi yana neman wajen zubewa ba sai da Hajiya ta rungumeta a jikinta. Da kuka Hajiya tayi mata magana suna wannan yanayin. "Hamdiyya na rasa me zan fara ce miki. Godiya zanyi ko haƙuri zan baki?" "Hajiya ku faɗa min abin da yake faruwa. Wallahi ji nake kamar zuciyata za ta buga don fargaba." Jin haka sai Hajiya ta ja hannunta har gaban Inna ta haɗa hannuwansu. "Kai ta." Gaba na matsananciyar faɗuwa Inna ta riƙe Hamdi har ICU ɗin mata. Ta jikin gilas ɗin ƙofa Inna ta nuna mata gadon da Yaya take kwance. "Wwwwaaaa..yyyyeee?" Ta matse hannuwan Inna ba tare da ta sani ba tana kuka. Jikinta kuwa tamkar mazari yana ta rawa. "Rage sautin muryarki kada ace mu bar wajen." "Na rage. Nayi shiru...." Hamdi ta soma faɗi sai ta kasa ƙarasawa. Wani abu ta lura dashi daga yanayin kwanciyar mara lafiyan duk da bata ganin fuskar. Ta saki hannun Inna ta sanya duka hannuwanta ta dafa gilas ɗin ta sake kara fuskarta da kyau. Realization hit her kamar an jefeta da dutse. "Yaya?" Ta juya da sauri "Inna, Yaya ce a kwance?" Sai hawaye kamar famfo. Inna ta gyaɗa kai, itama wani sabon hawayen yana zubo mata. Kokawa Hamdi ta fara yi da ƙofar ɗakin sai dai ko gezau taƙi motsi. Inna tayi saurin riƙe mata hannuwa tana turjewa. "Yaya ce Inna. Ku barni na shiga." "Ba za su bari ba Hamdi. Zo mu je nayi miki bayani." Hamdi taƙi tashi sai kuka kawai da take yi tana roƙonsu da su faɗa mata gaskiyar halin da Yaya take ciki. Mubina ce ta tafi da niyyar kiran Taj suka haɗu a hanya. Muryar Hamdi ya jiyo shi ne ya taho da sauri. "Me ya same ta? Me aka yi mata take wannan kukan?" Mubina ta haɗiyi yawu. Ganin bata da niyyar faɗa masa sai ya ƙara sauri ya zagaya ta inda suke. Inna na ganinsa ta fara cewa "Taj kama min ita mu bar wurin nan kafin..." Riƙe hannunta yayi zai janyeta duk da cewa hankalinsa yayi masifar tashi sai yaji ta turje. Maimakon ta bishi sai ta janyo shi jikin ƙofar ta nuna masa Yaya ta gilas ɗin da ake hangota. Da sanyin murya mai tsinka zuciya Hamdi tayi masa magana. "Yaya ce. ICU aka rubuta kuma Yaya tana ciki. Ji nake duniyar ta tsaya min. Ka taimakeni..." ta juya tana kallon su Inna "ku taimaka min. Ku taimaka mata." Ta sulale a ƙasa a hankali tana ajiyar zuciya. Kukan ma ya ɗauke mata. Taj kasa taɓata yayi saboda maganganunta tamkar almara yaji su. A kiɗime ya koma jikin gilas ɗin ya sake kallon wadda take kwance. Ya dawo ya riƙo hannayen Inna jikinsa yana tsuma "Inna da gaske Yaya ce?" Hannunsa da na Hamdi ta kama ta nufi hanyar lift. Su biyun a take suka nuna ba zasu fita ba. "Zaman ku babu abin da zai ƙara musu. Addu'a suke buƙata. Ku zo muje mu samu wuri nayi muku bayani." Tana rufe bakinta Mal. Salisu mai shara ya iso wajen. Idanuwansa akan Hamdi suka tsaya. Inna ta lura da haka. Sai ta ce, "Ƴarta ce." Mal. Salisu ya jinjina kai "wannan ne mijin nata ɗan uwan Kamal?" Inna ta gyaɗa kai. "To ku zo muje. Alhaji yayi magana da Dr. Hadifi ya sama muku inda zaku keɓe ku yi magana." A baya su ka bi Mal. Salisu har zuwa bakin wata ƙofa ta wani ƙaramin ɗakin taro. A nan suka tarar da Alhaji, su Hajiya da Yaya Hajiyayye, Yaya Kubra da Dr. Mubina. Hamdi bata san da yaya ta ƙarasa shiga ciki ba. Ta dai ganta zaune a kusa da kujerar Alhaji. Kwantar da kai da murya yayi sosai babu isa da ɗagawa wajen yi mata bayani. "Dashen ƙoda aka yiwa Kamal. Ciwo yayi masa tsanani..." Hamdi bata tuna da wata surukuta ba ta katse masa hanzari a firgice tana kallonsa da dara-daran idanunta. "Ta Yaya aka dasa masa?" "Ki yi haƙuri Hamdi." Mama ta ce cikin kuka. Tashin hankalin da ya sake bayyana a fuskar Hamdi har yafi na farko. Tana so tayi ihu, kuka ko ƙorafi amma duka ta kasa. Zuciyarta ce kawai take harbawa fiye da ƙa'ida. Taj duƙar da kai yayi ƙasa don bai ma san me yake ji ba a lokacin. Sai shiru ya mamaye wajen na ƴan daƙiƙu sannan Hamdi ta iya samun damar yin magana da dashashiyar murya. "Da izininta aka ɗauka?" Umma tayi gaggawar amsawa "Sosai. Mu bamu ma san ita ce donor ɗin ba sai da aka yi." A hankali Hamdi ta ɗaga kai ta kalli Alhaji. Yayi mata kwarjini amma dole tayi masa tambayar dake ranta. "Alhaji don Allah ba tursasata aka yi ba?" Raunin muryar Hamdi a yayin da take kwaɗayin samun amsar da zata sassauta raɗaɗin zuciyarta ya shiga jikin kowa. Taj kam gabansa faɗuwa yayi. Idan amsar bata yi daɗi ba me zai ce da Hamdi? "Baiwar Allah ni nafi cancanta ki yiwa wannan tambayar." Kowa ya kalli Mal. Salisu. Cikin tausasan kalamai ya sanar dasu yadda komai ya kasance har aka yi aikin. Abu na ƙarshe kuwa shi ne kunna musu audio ɗin Yaya. Kuka kuwa har su Inna da ba yanzu su ka fara ji ba. Ita dai Hamdi zuciyarta kusan tsayuwa tayi ma. Kukan kuma ya ƙi zuwa balle ta sami salama. "Idan kuna son sake tabbatarwa zan iya kai ku a nuna muku CCTV. Jiya sai da muka kalla tare da Dr. Hadifi wanda ya jagoranci aikin." Ya ƙarƙare da cewa " Malama Khadija ita ta kawo kanta asibitin nan da ikon Allah." "Ya Allah. Ya Allah Ka basu lafiya. Allah Yasa anyi aikin a sa'a." Hamdi ta shiga furtawa. Mamaki ya turnuƙe Alhaji da sauran mutanen. Ji wani irin tawakkali a tattare da ƙaramar yarinya. Domin ta ɗan sami sauƙi ya sanar da ita tahowar Abba Habibu wanda bata da masaniya. Ko a lokacin da ya faɗawa su Zee hanasu sanar da ita yayi. Ya san halinta. Bagarar da ita akan kada ta tsawaita tambaya zai fi wahalar da shi fiye da ƴan uwanta. Abin da kawai ta ce shi ne "Allah Ya kawo shi lafiya. Mungode." Daga nan bata ƙara magana ba kuma bata yarda ta haɗa ido da kowa ba. Bata so ainihin damuwarta ta bayyana. Cike take da fargabar me zai faru da Yaya. Me ya hanata farfaɗowa? Idan gudan ƙodar ta sami matsala yaya zata yi? Hanyar banɗaki ta tambayi Yaya Kubra ta nuna mata. Taj yayi saurin tashi zai bita sai Ahmad ya sha gabansa har ta fara nisa. "Kuka zata je ta kuma yi" ya faɗi yana ƙoƙarin kaucewa Ahmad ɗin dake tare duk hanyar da ya bi. Tausayi Taj ya bashi sai dai a ganinsa Hamdi tana buƙatar ɗan lokaci ita kaɗai a wannan yanayin tunda babu kowa daga gidansu a kusa. A tausashe ya yi masa magana. "Allow her Taj. Let her cry." Taj ya girgiza kai "she needs me. Don Allah ka bari na bita." "Ɗan uwanka aka sakawa ƙodar mahaifiyarta fa Taj. Kamal ya farfaɗo amma ita tunda aka fito bata buɗe ido ba. So kake tayi ta murmushin ɗan uwanka zai tashi ko kuwa tayi kukan mamanta a gabanka? Give her that space ko na minti goma ne to sort her feelings please." "Amma.." ya soma cewa cikin damuwa. Alhaji ya ɗora hannu a kafaɗarsa sai yayi shiru ya juya yana kallonsa "ka bi umarnin yayanka." Haƙura yayi ba don ya so ba. *** A cikin banɗakin, Hamdi ƙulle kanta tayi ta fashe da kuka mai matuƙar ban tausayi. Tana yi jikinta yana rawa. Idan Yaya bata tashi ba ina zata saka kanta? Me ta taɓa yiwa iyayenta na kyautatawa da zata iya dogara dashi taji salama a bayan su? Wai ma wace magana suka yi ƙarshe? Wane hali Abbansu zai shiga? Tambayoyi birjik a ƙoƙon kanta. Tayi kuka sosai har sai da taji kamar hawayen ya daina fitowa sannan ta buɗe ƙofar ta fito. A inda take tsaye daga bayanta ƙofofi ne na toilet guda takwas. Gabanta kuwa dogon sink ne da kawonan famfo da madubi. A gaban madubin ne taga wata mata wadda da alamu balarabiya ce sai dai bata iya ganin komai illa idanunta. Sanye ta da abaya da niqab harda safar hannu. Hamdi ta kasa ƙarasawa gaban sink ɗin saboda kunya da taji tunda ta san dole matar ta gama jin kukan da tayi. Ga mamakinta matar sai ta ɗage niqab ɗinta. Ba yarinya bace. A ƙalla tayi hamsin a ƙiyasinta. Matar kawai buɗe hannuwanta tayi ta matso ta rungume Hamdi. Kamar tana jira ta ƙanƙame wannan complete stranger ɗin ta sabunta kukanta. Tana yi matar tana bubbuga mata baya har tayi mai isarta ta ɗago kai a kunyace. "Am sorry" Da turancinta irin na larabawa matar ta tambayeta "You lost someone?" (Rashi kika yi?) "No, my mother is in the ICU" (Mamana tana icu) Matar ta ce mata ta duba Husnul Muslim akwai addu'a sahihiya daga Manzon Allah SAW da ya ce musulmi su dinga karantawa a yayinda su ke cikin damuwa ko tashin hankali. (La'ilaha illallahul Azimul Halim La'ilaha illallahu Rabbul arshil Azim La'ilaha illallahu Rabbus samawati wa Rabbul ardi wa Rabbul Arshil Karim.) Da murmushi matar ta ƙara da cewa "Na rasa kalmomin da zan nuna miki alkhairi da albarkar dake cikin yi wa Allah kirari da wannan addu'ar. Ki yita da yarda, aminci da imani. In sha Allah za ki faɗawa wani a gaba. Allah Ya yaye miki damuwa." Ba tare da musayar suna ko wani information game da juna ba suka rabu. Hamdi taji wani irin ƙwarin gwiwa tamkar Yaya ta tashi ta gama. Ta yabi Allah, tayi Masa godiyar haɗata da wannan mata sannan ta buɗe wayarta ta duba Husnul Muslim ta buɗe addu'ar ta fara yi. Da yake kuma ta ssnyawa zuciyarta cikakken yaƙini, nan da nan taji salama a ranta. In an cire jajaye kuma kumburarrun idanunta, za a iya cewa tafi kowa dauriya da ta koma cikin su Yaya Hajiyayye. Ko zama bata samu tayi ba Ahmad yace su tashi domin shirin tafiya Umra. Wasu cikin ƙannensa suka so kawo turjiya wai sai Kamal ya tashi zasu tafi. A fusace Umma ta daka musu tsawa ganin an kiransu ɗaya bayan ɗaya suna noƙewa kamar ƙananan yara. "Kai dalla can ku tashi. Na zata kuna da hankalin sanin cewa nacewa ibada ake yi idan ana da buƙata a wajen Allah SWT." Babu shiri suka fara tashi. Ta harare su "in kuma zaman ku ka fi so sai a bada himma amma ba a nan ba. Yanzu ma alfarma suka yi mana aka bamu wajen zama." Shi dai Alhaji yana kallonsu har suka fice bai ce uffan ba. Zuciyarsa gabaɗaya ta shiga tunanin da fuskar da zai kalli Abba Habibu idan ya iso. Ya ɓoyewa iyalinsa yadda suka yi da likitoci akan rashin farkawar Yaya da wuri. Amsar guda ce. Ta zubar da jini sosai a lokacin aikin. Duk da an saka mata wani, amma jikinta bai daidaita ba har yanzu. "Ya Allah, Ya Allah Ka rufa min asiri Ka bawa wannan baiwa taka lafiya" ya faɗi a hankali iya laɓɓansa. *** "Kin san Allah Yaya Zahra yau zan tafi gida. Na gaji! Ba zan iya ba." Zahra ta kalli ƙanwarta Ilham dake tsaye ta sanya hannu ta riƙe ƙugu tana faman yin ƙwafa da motsa kai hagu da dama cikin ɓacin rai. "Ki gaishe da su Mama" Zahra kawai ta iya cewa da sanyin murya ta sami waje ta zauna akan kujera a falo. Alamun gajiya ta kowacce fuska sun bayyana a tare da ita. Da gani bata cikin nutsuwa. Ilham sai taji kunyar abin da tayi. Cikin jin nauyi ta zauna a kusa da yayarta ta ɗan dafa ta. "Ki yi haƙuri. Kawai gani nayi kina ta wahala da matar da ba wani mutumci ne da ita ba." Da sauri Zahra ta kalli hanyar ɗakin Salwa inda Mami take kwance yanzu. Ilham ta gane tana tsoron kada Mamin taji ne. Sai dai ita ko a jikinta. Mami ta sirewa kowa a gidansu saboda ire-iren rashin mutumcin da ta dinga yiwa Zahra. A haka ma don ba gari ɗaya suke ba. "Na rasa me yasa Mama tace ki cigaba da kula da matar nan bayan ƴar cikinta ma ta gudu. Shima kuma Daddyn Hayat yayi tafiyarsa ya barki." Ta taɓe baki "kada ki ji haushina amma Allah na tuba wace Umra zai tafi alhalin ya bar mahaifiyarsa a wannan halin?" Zahra ta girgiza kai "Ilham indai kin gaji ki tafi kawai." Ilham ta sami waje ta zauna a kusa da yayarta. Jikinta yana bata akwai wata gagarumar matsalar a gefe wadda tasa dole Ahmad yayi nisa da gida a yanayin da ake ciki. "Yaya Zahra me yake faruwa ne don Allah? Ban kai matsayin da za ki faɗa min damuwarki ba?" Sai da Ilham ta zubar da hawaye kamar yadda Zahra take yi bayan ta sami amsar tambayarta. Cikin kuka ta sanar da ita abin da yake faruwa a gidan surukinta. Tayi mata bayanin tsaka mai wuya da Ahmad yake ciki wanda indai bata tausaya masa ba, bai kamata ta ƙara masa damuwa ba. Ga Maminsa a wannan yanayi. Ta sami labarin an saki su Salwa a wajen Ahmad amma har yau bata dawo ba. A gefe guda kuma ga Kamal a kwance, sun samu da ƙyar jiya anyi masa transplant amma daga nan ba za ta ɗorar da komai ba. "Amma Yaya Zahra su da suke da yawa don dai shi kaɗai ya dawo saboda mahaifiyarsa ai bai kamata ya zama laifi ba." "Alhaji ko sunan Mami baya son ji. Kuma kinga abubuwan da Salwa ta janyo musu. I know he feels responsible shiyasa na tabbata nauyin faɗa masa yake ji. Sannan komai na gidansu shi yake sakawa a matsayinsa na babban ɗansa namiji. Wannan ma zai iya contributing." Cewar Zahra a sanyaye. Ilham ta jinjina kai a hankali sai kuma ta kama dariya tana cewa "lallai aure ibada ne. Duk takurar da kike ciki amma kina auna komai ta fuska daban daban da yadda zai yi affecting mijinki." Ta murmusa "na ɗauki wani gagarumin darasi. Na san dole yana alfahari dake" Zahra tayi murmushi "za ki cigaba da tayani zama?" Ilham ta zumɓura baki ta koma ta kwanta akan kujera alamun dai ta fasa tafiyar. Zahra kuwa ta daddage ta kai mata duka a ƙafa sai da tayi ihu. "Me nayi miki kuma?" Ta tambaya tana murza ƙafar. "Tayar min da hankali mana. Wai ni kike yiwa barazanar komawa gida ƴar rainin hankali." Ilham ta tuntsire da dariya "sai ga Yaya Zahra an kwantar da kai ana marairaice murya." Wani dukan Zahra ta kai mata ta miƙe babu shiri ta gudu. A cikin ɗaki, Mami ke kukan zuci ita kaɗai. Ga ƴan uwa, ga ƴaƴa amma babu kowa a kusa da ita! *** A wulaƙance Alh. Usaini yake duban Salwa. Tana durƙushe a gabansa ta fita kamaninta saboda tsabar naci. Shi ko ganinta baya son yi saboda yadda yake jin haushinta. Makauniyar soyayyarta ta janyo tonuwar asirinsa da lalacewar aikinsu gami da korar da mahaifinsa yayi masa. Da azal ta hau shi kuma ranar da aka sako su a titi ya ganta tana tafe tana jan ƙafa. Ya tsaya rage mata hanya da manufa guda...ci mata mutumci akan asarar da ta janyo masa. Sai aka yi rashin sa'a ashe ƙarfen ƙafa ya kwaso. Wani hotel ya tafi da ita yana ayyana azabar da zai gana mata. Ashe ita za ta gana masa. Salwa ta nace lallai sai ya kaita wajen malaminsa. Tana da tabbacin za ta sami kan Taj tunda ta shaida da idanunta yadda wancan maganin ya birkita masa lissafi. Ba don iyaye sun shigo ciki ba da yanzu ƙarshenta an fara shirye shiryen rufe Happy Taj. "Zan yi maka biyayya Alh. Usaini. Duk abin da kake so zan baka banda mutumcina." Murmushi ƙayatacce ta saki sannan ta ɗora da cewa "Taj nake tanadarwa kaina." Wani kallon banza yayi mata yana ɗage hanci kamar tsohuwa zata tsallake lambatu "Wai ke wawiyar ina ce? Ana so dole ne? Banda masifa irin taki waye ma yake ta soyayya yanzu? Life is all about money, money and more money." "Ba za ka gane ba. Wallahi ni Taj ne rayuwata. Idan ban aure shi ba zan iya rasa raina." "Ƙaryar banza. Me ya hana ki mutuwa tuntuni?" Ya ɗan sassauta murya "kinga ki zo ki tafi gidanku don Allah. Hotel ɗinnan sun hana ni fita saboda ke. Naje checking out ance sai mun fito tare don kada na bar musu liability." "Ka taimaka ka haɗamu. Nayi maka alƙawarin ba za ka ƙara jin ko da suna na ba." Wani baƙinciki ya tokare masa wuya. Ya tashi kamar zai kai mata duka sai ya fasa. Baya son janyowa kansa wata sabuwar rigimar. "Wayyo Allah na. Salwa ki tafi kada na illata lafiyarki." "Zan jure. Wallahi ko me zaka yi min zan jure. Ka taimaka min." A hasale ya zauna. Magana da mahaukaci ɓata lokaci ne. Ba don Allah Yasa mata basa gabansa ba da tuni sunan Salwa sorry. Ita ko tsoro bata ji ba take zaune da shi a hotel a ɗaki guda. Safe, rana da dare duka zancen ɗaya ne. Idan yana so tayi shiru sai dai in yana waya. To gashi ta ƙare masa. Duk wani wanda zai roƙar masa mahaifinsa ya yafe masa ya zare hannu a kansa. A halin yanzu bashi da tudun dafawa. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka kashe masa gwiwar yi mata wani abu. Tunani da damuwarsa sun shallake ƙaramar lalurar Salwa ta son maso wani. Abin da bai sani ba shi ne akwai wata ƙanwar kakarsa ta wajen uwa da ta saka baki akan maganarsa. Ga tsufa ga lalurar ƙafa amma a haka tasa aka kaita gaban mahaifinsa har gida ta bashi haƙuri a madadinsa. Ganin girmanta yasa shi yafe masa. Bayan ta tafi ya saka aka binciko masa inda ɗan nasa yake. Bayan nan aka tabbatar masa da cewa tunda ya shiga hotel ɗin bai fita ba. Abin ka da ɗa da mahaifi. Sai ya tashi da kansa yace ƙanin Usainin ya kai shi. [4/2, 11:37 PM] +234 803 761 4669: RAYUWA DA GIƁI 38 Batul Mamman💖 Nagode da karamcin ku. SonSo *** Addu'a kam babu irin wadda bakunan ƴaƴan Alh. Hayatu ba su yiwa Yaya ba ta samun lafiya cikin ibadarsu. Hamdi ta zauna ta dinga yi wa Allah SWT kirari tana faɗin buƙatarta. Da ƙyar ta iya baro masallacin saboda shauƙin kasancewa a waje mafi tsarki kuma inda take da tabbacin karɓuwar addu'arta. Sai bayan isha su ka koma Jedda. Ana yi musu tayin tafiya masauki amma kowa ya ce sai sun ga isowar Abba Habibu. Ahmad da yake tracking tafiyarsu ya sami bayanin tsaiko da aka samu da su ka tsaya transit a Egypt sakamakon hazo da ya lulluɓe garin. Haka su ka kasance jugum-jugum ana ta tasbihi a zuci da fatar baki. A can Bauchi kuma mahaifin Salwa bai san me yake faruwa ba sai da Ahmad ya kira shi a waya. Keɓewa ya yi daga ƴan uwansa ya sami wuri ya kira shi. Abban nata bai ɓoye masa rashin jindaɗinsa ba kuwa. "Haba Ahmad. Kai da nake yabon hankalinka, ta yaya za ka bari har a kwashi waɗannan kwanaki kafin ka sanar dani?" Ahmad bai yi mamaki ba. Dole ko wane ne yaji babu daɗi. Shi yasa ya zauna yayi masa bayanin dukkan abin da yake faruwa da gidansu. Baban Salwa ya jajanta masa ya kuma yi masa uzuri. Musamman da yace ya dakata ne daman yana jiran ganin ko zata dawo, kada yayi saurin tayar masa da hankali. "Babu komai. Zan nemeta a waya. Idan ban samu ba ma akwai wani ɗan ƙanwata da zai iya yi min tracing ɗin layinta." "Allah Yasa a dace. Nima zan cigaba da kiranta." Suna tsakar sallama Baban Salwa ya dakatar da Ahmad ya yi masa nasiha mai ratsa zuciya. "Ana canja abokin zama amma kaga iyaye? Iyayen ma musamman uwa, sai dai haƙuri kawai. Na san kana ƙoƙari kuma kana haƙurin amma ka ƙara domin neman albarka ba don ita Mamin taku ba." Ɗacin abubuwan da Mami ta aikata waɗanda suka kawo su wannan lokaci ya dawo masa amma basu bari ya ƙi amsar shawarar ba. "In sha Allahu. Nagode" Da haka suka yi sallama. Ahmad ya koma cikin ƴan uwansa a inda suka taru suna jiran isowar Abba Habibu. *** Daga lokacin da Abba Habibu ya sauka daga jirgi zuwa yanzu da yake fitowa da ƴar jakarsa a hannu, gabansa ya faɗi sau ba adadi. Tunani iya tunani yayi amma ya kasa samun abu guda da zai iya cewa shi ne yake jin ya sami Yaya. Haka ya fito da sassarfa yana jan addu'o'i daban daban. Yana sako ƙafarsa waje ya ɗaga kai yana waige-waige. Abokin Ahmad ya sanar da shi cewa Alh. Hayatu zai turo a ɗauke shi. Shi yasa yake baza idanu ko zai hango guda cikin yaran nasa. Sai dai abin mamaki maimakon ƴaƴan, Alh. Hayatu ya gani da kansa yana tunkaro shi. Wani irin abu mai zafi yaji ya tsirga masa daga tsakiyar kai har tafin ƙafa. Ƙafar ta zaɓi wannan lokacin taƙi motsawa kwata-kwata ma. Yana gani Alh. Hayatu ya cigaba da nufo shi amma ya kasa ɗaga ko da ɗan yatsa har ya iso gaban shi ya tsaya. Da rawar murya Abba Habibu ya ce "Tun a waya na ce da Ahmad ya faɗa min gaskiya yace min da ranta." Alh. Hayatu ya gyaɗa kai da sauri "da ranta Habibu. Iyalin ka tana nan da rai." "To me ya same ta? Ni na san gagarumar matsala ce kaɗai za ta sa ka zo tarba ta a nan." Abba Habibu ya furta helplessly. Alh. Hayatu kasa magana ya yi, sai wata uwar kunya da ta mamaye shi. Abba Habibu bai yi ƙarya ba. Haka nan me zai kawo shi tarbarsa? Mutumin da yake ƙyama yau a dalilin matarsa yana yi masa kallon mafi girman daraja a cikin mutanen da yake tare da su. Kafaɗar Abba Habibu ya dafa ya nuno masa motar dake jiran su "Zo mu tafi Habibu." "Kayya da dai ka faɗa min me zan tarar da nafi samun nutsuwa." Ya kalli Alh. Hayatu da yanayi da yasa dole ya ƙara jin tausayinsa. "Ganin ka a nan da tausasa kalaman ka a gareni sun fi faɗar min da gaba fiye da wayar da Ahmad yayi min jiya. Don Allah ina zamu je? Ko dai da gaske ne an kama ta cikin masu nakasar dake taho wa bara?" Ba a nan Alh. Hayatu ya so sanar da shi ba. A wannan yanayin na tsananin firgici da yake gani a wajen Abba Habibu bai dace ya tsorata shi ba. Gudun tarwatsa labarin a bakin yara shi ne musabbabin tahowarsa. Sai dai kuma har ƙasan zuciyarsa shi ya san babu wani lokaci da ya dace ayi breaking mummunan labari ga makusancin wanda abu ya shafa. Ana faɗa ne kawai idan dama ta samu tare da addu'ar haƙuri da tawakkali. Ba tare da jan rai ko kwaskwarima ba ya sanar da shi gaskiya. "Ƙoda ta bawa Kamal. Tana kwance a asibiti yanzu haka muna jiran farfaɗowarta." Ko cikakken sakan Abba Habibu bai ɗauka ba wajen fahimtar kalaman Alh. Hayatu. Sun yi masa dirar aradu mai ƙarfi. Ga wasu irin tambayoyi suna tsaruwa a kansa cikin karo da juna wurin son fara fitowa. Amma duk da haka sai ya kasa furta ko ɗaya a dalilin tunawa da wayar da Yaya tayi masa tana neman izini. "Yaya jikin Kamal ɗin?" Mamakin wannan tambaya Alh. Hayatu ya yi kafin ya iya cewa da sauƙi a hankali. "To mu je" Abba Habibu ya ɗaga ƙafa yana mai danne tsananin tsoron da ya taso masa. Sai da suka shiga mota Alh. Hayatu ya kasa daurewa ya ce "Ba ka tambaye ni lafiyarta ba?" "Ka manta ka ce min ana jiran farfaɗowarta?" "Haka ne." Ya faɗi yana jinjina kai "to amma ba ka tambayeni komai ba?" "Za ta bani amsa da kanta idan ta tashi in sha Allahu." Abba Habibu ya jingina bayansa da kujera cikin yaƙini. A yayin da wani ɗaci ɗaci ya dinga taso masa na tsoro sai ya dinga faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal Wakeel". Ba su ƙara magana ba har su ka isa asibitin. Abba Habibu yana tafiya ne tamkar a mafarki. Yadda aka yi ya iso ƙofar ICU ɗin abu ne da ko an saka masa wuƙa ba zai iya faɗa ba. Bai ma san lokacin da Hamdi ta iso ba sai ji ya yi ta faɗa jikinsa tana kuka. Iyalin Alh. Hayatu kuwa gaishe shi su ke ta yi ya dinga amsawa da sakin fuska. Za ka rantse baya cikin mummunan tashin hankali mara misaltuwa. Sun yi mamakin hakan ƙwarai da gaske. Mafi ƙarancin abin da su ka yi zato shi ne yi blaming ɗin Alhajinsu ya ce laifinsa ne matarsa take kwance a wannan yanayi. Shi dai Abba Habibu bai ma yi la'akari da kallon kallo da su ke yi ba. A lokacin Dr. Hadifi ya iso, Alhaji ya matsa kusa da shi domin nemawa Abba Habibu izinin shiga wajen Yaya. Suna magana a gefe Abba Habibu ya ɗago Hamdi daga jikinsa ya kalleta a cikin ido ya girgiza kai. Bai yi mata magana ba a lokacin sai ya ja ta gefe ɗan nesa da sauran. "A gabansu ki ke wannan kukan Hamdi? So ki ke su yi zaton kina baƙincikin sadaukarwar mahaifiyarki ga ɗan uwansu?" "A'a" ta girgiza kai da sauri. "Haka za su yi zato idan ba ki yi shiru ba mana." Hannuwansa riƙe da nata ya rarrashe ta " Don Allah kada ki sa su ji a ransu kamar sun yi wa kowa laifi. Wallahi da izini na ta bayar." "Abba da izinin ka?" A gurguje ya faɗa mata wayar da su ka yi sannan ya cigaba da cewa "farinciki da nutsuwar zuciyar da zamu nuna musu shi ne zai yi nuni da cewa mun girmama wannan kyakkyawan aiki da tayi." Duk wannan bayanin da Abba Habibu yake yiwa Hamdi ashe a kunnuwan Alh. Hayatu, Hajiya da Taj yayi. Sun biyo bayan su ne a zaton su faɗa zai yiwa Hamdin. Hamdi ta sanya ƙasan hijabinta ta goge idanunta. Cikin muryar kuka ta ce "Abba ina tausayinta ne kawai. Ga yanayinta ga ciwo. Gani nake kamar shi yasa ita bata tashi ba." A wannan halin ya ƙirƙiri ƴar raha domin kwantarwa ƴarsa da hankali. "Kada ki raina min mata mana Hamdi. Ta haife ku ku huɗu rigis sannan ki dinga tunanin wannan zai bata wahala? Ko an faɗa miki kowa ma rago ne irin ku?" "Kai Abba..." ta faɗi tayi murmushi akan kumburarriyar fuskarta dake jiƙe da hawaye. Hajiya bata san lokacin da tsananin tausayi da girmansu yasa ta sake fashewa da kuka ba. Hakan ya bayyana musu cewa ba su kaɗai bane. Ta rungume Hamdi tana rarrashinta amma kuma ita ma ɗin kukan take yi sosai. Alh. Hayatu ya kira Abba Habibu ya kai shi gaban Dr. Hadifi. Nan da nan aka shiga ciki da shi. Aka bashi riga da dukkanin kayan kariya ga mara lafiya domin kada a shiga da baƙuwar cuta. Sai da ya shirya tsaf aka bashi damar ƙarasawa gaban Yaya. Sannan Alh. Hayatu ya matsa gefe yana kallon what it truly means to be a great person. Kuɗi, mulki, lafiya, mazantaka da suna do not make a man. Habibu Umar Simagade ya nuna masa haka daga airport zuwa yanzu. Kuma duka abubuwan da yake taƙama dasu a yau ba su hana shi jin nauyi da kunyar wanda ya raina a baya ba. Zuciyarsa ta karaya matuƙa da ya tuna wani shuɗaɗɗen lokaci da Abba Habibu ya zo neman taimako wajen sa a kasuwa. Akan ce idan maye ya manta, uwar ɗa ba za ta manta ba. To shi dai da kansa mayen bai manta ba. *** SHEKARUN BAYA Abba Habibu ne yake tafiya a cikin kwanonin tsakiyar Kantin Kwari da gammo a kansa wanda ya ɗorawa madaidaiciyar cooler. Kayan jikinsa jamfa ce da wando kuma gwargwadon iyawarsa yana ta kamanta taku irin na maza, sai dai ko kusa baya iyawa. Tafiyar tasa tafi kama da rangwaɗa irin ta ƴan matan dake ji da kansu. Nauyin kayan da ya ɗauko ko kaɗan bai ɓoye yanayinsa na ɗan daudu ba. Da kwatance saboda daɗewa da sababbin gine-gine a kasuwar ya gano jerin shagunan Alh. Hayatu. Cikin farinciki ya shiga da sallama daidai lokacin da yaran shagon su ke ganiyar ciniki da wasu kwastomomi. Alh. Hayatu kuma yana magana a gefe guda da ƴan mazan ƴaƴansa su uku. Dukkaninsu sanye su ke da shadda wagambari tana ɗaukar ido. Ahmad, Kamal da Taj. Kamar kowacce Juma'a, Alhaji ya tura an ɗauko masa su daga gida bayan sun dawo daga makaranta domin zuwa masallaci. Alhaji na ganin Abba Habibu yaji tamkar an ɗauke masa wutar jikinsa. Sam baya son abin da zai haɗa su waje guda saboda yadda yake ƙyamarsa. Idan ya tuna Habibun da ya sani, ya kalli wannan sai yaji wani irin takaici. Da ƙyar ya amsa sallamar da yayi. Kuma gabaɗaya ya tsargu da kallon su da mutanen cikin shagon su ka kama yi. Yana ji a jikinsa yau shi zai zama jigon gulmar cikin kasuwar. Fuska cike da fara'a da jindaɗi Abba Habibu ya miƙa hannu zai dafa kan Ahmad yana cewa "girman ɗan mutum ba wuya. Yaya Hayatu haka Ahmad ya girma?" Ya kalli su Taj "waɗannan ƙannensa ne?" Kafin hannunsa ya taɓa Ahmad tuni Alh. Hayatu ya janye ɗansa gefe ya kuma bi shi da kallon me-ya-kawo-ka? Abba Habibu ya ɗan rissina gami da miƙa masa hannu sai dai haka ya koma da abinsa da bai mayar da musabahar ba. Still with a smiling face ya gaishe shi ya kuma tambaye shi lafiyar iyali. "Ƙalau! Aiko ka aka yi ne?" Alh. Hayatu ya tambaya a ƙagauce. "Dama magana na ke so mu yi" Abba Habibu ya bashi amsa da sanyin jiki. Attitude ɗin da yake yi masa yasa shi shan jinin jikinsa. Shi ɗin ba baƙon da ake maraba da zuwansa bane. Wata kusurwa a cikin shagon Alh. Hayatu ya ja shi maimakon su keɓe a office. Yadda mutane suke yanzun nan zai iya jin an yi masa muguwar fassara. Cikin jin nauyi Abba Habibu ya keta billensa ya roƙe shi akan ya taimakawa rayuwarsa. "Wallahi ban iya komai ba sai girki. Na fara koyon ɗinki amma saboda zama sai naji ba zan iya ba tunda na saba da kai komo. Ni kuma ba karatu na gama ba balle na nemi aiki." "Me ka ke so?" "Ba na son zama cima zaune. Idan da hali ko yaron shago ka ɗauk..." Ko direwa bai yi ba Alh. Hayatu ya hau shi da faɗa. "A'a...kada ma ka yaudari kan ka. Ta yaya zan bari mutumcina ya zube a wajen sana'ata saboda kai? Ban gaya maka zaka yi nadamar wannan hanyar da ka ɗauka ba?" "Ka faɗa Yaya Hayatu. Ba kai ba ma. Kowa ya faɗa kuma na gani." Idanuwansa su ka ciko da ƙwalla. Hakan ya sake ɓatawa Alh. Hayatu rai. Namiji har namiji amma mai saurin kuka. Tirrr da daudanci wallahi ya ayyana a ransa. "Habibu ka san ban iya munafurci ba ko? To ba za ka zauna min a shago ba. Ana girmama ni a wajen nan." Abba Habibu ya yi murmushi "nima kaina ina ƙyamar yadda rayuwa ta kasance min amma wallahi girki kaɗai nayi a cikinta. Duk sauran shiriritar da kake tunani ban taɓa yi ba. Kuskurena biyu ne. Na farko da nayi tunanin dole sai na koma mace zan sami damar yin girkin da nake so. Na biyu kuma da na bari son girkin ya rinjayi zuciyata zuwa ga saɓon Allah." Ya haɗa hannuwansa biyu "na tuba ga Ubangijina Yaya Hayatu. Ko zan mutu ina yawo a titi ba zan ƙara daudu ba. Tafiya, magana da wannan karya jikin ma don dai na rasa yadda zanyi na daina ne. Don Allah Ka taimaka min ko da jari ne." Zuciyar Alh. Hayatu ta fara karaya da zantukan Abba Habibu a wannan lokaci. Yanayin tamke fuskarsa ma ya sassauta. A lokaci guda yaji makamansa sun fara ƙarewa. Ya ja gwauron numfashi ya sauke. "Ba zan iya zama da kai a kasuwa ba Habibu amma in sha Allahu zan taimaka maka." Ya sami kujera ya zauna sannan ya dube shi "Yanzu idan na baka jari wace sana'a za ka yi?" Murna, nutsuwar zuciya, ɗoki da girmamawa ga Alh. Hayatu su ka taru su ka mamaye zuciyar Abba Habibu. Bakinsa har yana rawa don tsabar farinciki. "Girki!" Alh. Hayatu yaji wani irin haushi da takaici sun lulluɓe shi. Girkin dai zai koma wa? "Sana'ar abinci zan cigaba da yi domin a nan nake da ido. Kada na dulmiya kuɗin a inda zai salwata saboda rashin sabo. Ko yaya ka gani?" Ɗaga murya ya yi "Baka shirya gyara rayuwarka ba Habibu. Ka zo ka fita. Fita na ce!!!" Ka nuna masa waje. Abba Habibu ya waiga hagu da dama a rikice don bai san me ya sake tunzura Alh. Hayatu ba. "Yaya Hayatu..." ya soma kiran shi da sigar magiya. A yadda Alh. Hayatu yake ɗaga murya yanzu da yaran shagon nasa, kwastomomi da mutanen dake haraba kowa ya dawo da hankali garesu. "Girkin ba shi ya kawo ka wannan mummunan matsayin na ɗan daudu ba? Shi ne za ka kalli tsabar idona ka ce min idan na baka jari shi za ka cigaba da yi. Anya Habibu kana da hankali kuwa?" "Shi ne kaɗai nake ganin zan yi ba tare da mutane sun guji mu'amala dani ba. Yanzun nan fa kace min ba za ka iya zaman shago dani ba. Kana ganin akwai sana'ar da zan yi a saya a wannan zamanin namu da ake ƙyanƙyamin masu rayuwa irin tawa? Abincin mu ne kawai na san ba a gudu." "Habibu ka fita na ce. Kuma ko a hanya ka ganni kada ka kuskura kayi gangancin nuna ka taɓa sani na. Aikin banza." Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ya juya zai fita. Idanuwan dake kallonsa sun fi ashirin. Nan take zuciyarsa ta sake raunana. Ƙwalla ta cika masa idanu taf sai dai bai bari ta sauko ba. A wulaƙance Alh. Hayatu ya kalli cooler ɗin da ya shigo da ita. Ya sa ƙafa ya zungureta. "Dawo ka yi mantuwa." Murmushin yaƙe Abba Habibu ya yi "dama kawo maka nayi a bawa yara." "A bawa yara? Me?" Ya sake tambaya yana taɓe fuska. "Zabi ne aka soya" Katse shi yayi da sauri "Allah Ya kiyaye jini na su ci girkin ɗan daudu wallahi. Ba ma tare da yunwa Habibu. Ka kwashe kazantarka." Abba Habibu ya kalli kular ya koma ya kalli mutane suna ta ƙananun maganganu a gefensa. Jikinsa yaji duk ya mutu kamar anyi masa duka. Wannan kular ya tabbatar a yadda yake jin kansa ba iya ɗauka zai yi ba. Ƙwaƙƙwaran motsi idan yayi zai iya yin hawayen da Alh. Hayatu zai sake aibata shi a kansu. Rago zai kira shi. "Don Allah ko a nan ne ka bayar." "Ai ba ni ba, wanda ya raɓe ni ma yafi ƙarfin cin abin hannunka." Ya kalli biyu cikin yaransa "ku ɗauka a kaiwa karnuka tunda ba ya so." Jin haka Abba Hayatu ya koma ya ɗauki kular kafin su taɓa. Mahaifiyarsa ce ta dafa sai dai baya jin Alh. Hayatu yana buƙatar dogon bayani irin wannan. Da ya fita bai sake waigowa ba. * In ya tuna, shi da Abba Habibu basu sake haɗuwa ba sai da maganar auren Taj da Hamdi ta taso sai yaji a ransa tamkar Abba Habibu yayi nasara a kansa har sau biyu. Na farko izzarsa ta kife a ƙasa a yayinda ɗansa mafi soyuwa a gare shi ya zaɓi girkin da ya tsani gani a wajen ɗa namiji a matsayin sana'a. It was as if karma came knocking and laughing at him lokaci guda. Na biyu kuma shi ne yadda ƙaddara ta sake haɗa ɗan nasa da yar Habibu. Abu kamar almara. Idan ya ce bai yi tunanin ko asirice masa ɗa Abba Habibu yayi ba tabbas yayi ƙarya. A karon farko zazzafar ƙwalla ta dinga kwaranya daga idanun Alh. Hayatu. After all these years, abar ikon Abba Habibu ce ta zama silar warakar gudan jininsa. Yau idan Kamal ya cigaba da rayuwa, Allah ne Ya yi ikonSa amma matar Habibu ce sila. Habibun da yake ganin bai cika mutum ba. Wasu cikin kalamansa gare shi masu zafi su ka dinga dawo masa da wata irin amsa kuwwa. Shi ya faɗe su amma yau yafi Abba Habibu jin zafinsu. Nadama da tulin dana-sani su ka sarƙafi zuciyarsa. Tabbas tun a jiya zuciyarsa ta shiga alhini da jin nauyin abubuwan da ya yi a baya. Amma a wannan sa'ar, da Habibu ya zo gabansa amma ko kusa fuskarsa bata nuna alamun zuciyarsa na ɓoyon baƙincikin sadaukarwar matarsa ba. Hasalima tuhumar kukan ƴarsa yake yi har yana shawartar ta da kada tayi abin da su da aka yiwa alfarma za su ji babu daɗi. Sai ya ji komai ya kwance masa. Babu sauran jin kai da ƙafafa. Shi Hayatu ya yarda ƙaddara bata fi ƙarfin kowa ba. Zaɓin yadda ɗan Adam zai tafiyar da halin da ya tsinci kansa shi ne ma'aunin dacewa. "Alhaji lafiya? Me ya faru kuma?" Firgigit Alh. Hayatu ya dubi su Hajiya dake tsaye da wasu cikin ƴaƴansa suna kallon shi. Kawar da kansa ya yi gefe bai cewa kowa uffan ba. Kallo guda Inna ta yiwa yaran nasu su ka fahimceta. Kafin wani lokaci dukkaninsu sun bar wajen. Masaukinsu Ahmad ya ce su zo su tafi saboda asibitin ba a jinya. Kamal kuma yana buƙatar hutu sosai tunda ko magana bai fara yi ba. Ya dai dawo hayyacinsa amma yana cikin magagin ciwo. "Mubina tare za mu tafi ki samu ki ɗan yi bacci ko yaya ne." Ya dubi Taj "ka zauna da Hamdi sai ku taho tare da su Alhaji." *** Tsaye a bakin gadon Yaya, Abba Habibu ne da wata nurse. Sharuɗɗan shiga ICU ɗin ta bashi wanda a ciki ta nanata masa banda ɗaga sauti cikin magana ko kuka. Ya tambayi ko zai iya taɓa ta tayi masa izini amma shi ma ba riƙo mai ƙarfi ba. Komawa tayi table ɗinta a can tsakiyar ɗakin ta barshi gefen da aka keɓewa Yaya. Abba Habibu ya daure sosai ya hana kansa kuka ko da a zuci. Gani yake da zarar ya karaya wani abu zai iya samunta. Hannunsa ya ɗora akan nata ya riƙe kamar zasu yi musabaha. "Ashe waliyya nake aure ban sani ba? Gaskiya ki tashi haka nan in kwashi tubarraki." Kamar daga sama yaji muryar Yaya tana magana a hankali sosai. Salati ne take yi da sauri-sauri cikin kiɗima. Abba Habibu ya ranƙwafo kansa su ka haɗa ido. Ai da ya tabbatar ta tashi da saurinsa ya juya zai fita domin ya kira nurse. Ita kuwa Yaya ta sake damƙar hannun tana mai jin tsoron kada ya fita ya barta. "Sannu. Nurse zan kira a zo a duba ki." A hankali ta rufe ido ta buɗe cikin nutsuwa. Sai a lokacin ta dawo hayyacinta. "Yaushe ka zo?" Kafin ya amsa ta kaɗa kai "kai ne ɗin dai ba gizo idanuna suke ba ko?" "Ni ne Jinjin. Yau na zo. Yaya kike ji a jikin naki? Ki bari na kira Nurse." Cikin ƙanƙanin lokaci likitoci biyu da nurse su ka tsaya akanta. Aka duba lafiyarta sosai su ka tabbatar cewa babu sauran matsala. In sha Allahu bata cikin haɗari. Sannan aka bata awa guda ta sake hutawa kafin a mayar da ita ɗaki. Wannan abu ya farantawa Abba Habibu rai sosai. Bayan fitar likitocin waɗanda su ka jima suna yabonta kafin su tafi, Yaya ta dubi Abba Habibu. Bayani ta so yi masa yace sam bai yarda tayi magana ba. "Ki bari sauƙi ya samu shine babban burina. Ina so dai ki saka a ranki cewa kin yi jihadi kuma ko kaɗan baki ɓata min rai ba." Lokaci na cika ko minti biyar ba a ƙara ba aka gangaro Yaya zuwa ɗakin da hukumar asibiti ta tanadar mata na musamman domin karramawa. VIP wing aka nufa da ita wanda sai an shiga lift an sake ƙara hawa uku akan inda su ke. Tun a ƙofar ICU ɗin Hamdi ta kama mata hannu tana biye dasu. Idanunta jazur duk ta fita hayyacinta amma a haka take ta murmushi saboda kada ta karyar mata da zuciya. Taj tsayawa yayi tare da Alhaji. Yana kallo su Hajiya su ka bi su a baya. "Ka bi su mana" cewar Alhaji gare shi. "Abin da ya hana ka bin su nima shi ya hana ni Alhaji." Ya kalli Alhajin da ɗan murmushi a fuskarsa "na san ba surukuta ce ta hana ka bin su ba." Alhaji ya numfasa yana bin hanyar da aka gangara gadon Yaya da kallo. Ya jinjina kai sannan ya zauna a kan kujerar. Taj ma kusa dashi ya zauna su ka kasance gefe da gefen juna sun jingina baya da bango. "Ɗan Adam ba ya gane cewa ba a bakin komai yake ba sai ya ga ikon Allah a inda yake tunanin wayo ko dabararsa sun ishe shi." Kallonsa Taj yayi yana sauraronsa da kunnuwan basira amma bai ce komai ba. Alhaji ya cigaba da magana. "Idan wani ya ce min ɗan cikina mace ma ba namiji ba zata ci abinci da sana'ar abinci wallahi zan ƙaryata Taj. I was so confident cewa Allah Ya lamunce min rayuwata akan tsarin da nake so. Ina da kuɗi kuma nayi muku tarbiyya daidai gwargwado. Fitintinun zamani da ake kuka dasu babu ko ɗaya a cikin gidana. Ƴaƴana duk inda su ka shiga ana alfahari dasu. Na zata..." muryarsa ta kama rawa "Taj na zata gobe na kamar yau zata cigaba da kasancewa muddin rai. Hmmm" Ya sauke ajiyar zuciya da ƙarfi. "Tajuddeen Hayatu sai ka zaɓi kitchen. Sana'ar da bayan ƙiyayyar da nake yi mata ban taɓa hango wani nawa cikinta ba. Kuma kamar da gayya sai ga ka da auren ƴar Habibu. Wato Taj da ace zan iya fito da zuciyata ka ga tsanar da na yiwa auren ku a dalilin Habibu, da ko da wasa ba za ka tunkare ni da maganar Hamdiyya ba." Taj ya yi kasaƙe yana jin furucin mahaifinsa dalla-dalla. "Subhanallah! Komai yana tafiya cikin tsari da ƙudurin Al-Hakimu. Ba don auren ku ba da babu abin da zai kawo mahaifiyar Hamdi inda muke ko da a asibitin nan take aiki. It's like everything happened for this day Taj. Allah Ya rubuta da ƙodar matar Habibu kuma surukarka Kamal zai cigaba da jan numfashi a duniya. Kuma duk tarin shekaruna sai a yanzu na gane wannan izinar." "Tsarki ya tabbata ga Sarkin da gyangyaɗi da bacci ba sa cikin siffofinSa." Taj ya faɗi cikin shauƙin alawar imani wadda zaƙinta yakan tashi a lokutan da bawa ya yaba wa sarautar Ubangijinsa, gatansa, majiɓincin lamuransa. Alhaji ya gyaɗa kai sai da raunin murya ya ce "Zuciyata ta cika da kokonton karɓuwar dukkan alkhairi na na baya." Wani irin kallo Taj ya yi masa ya ce "Alhaji me ya sa za ka yi wannan tunanin? Don Allah ka kyautatawa Allah zato." A gurguje Alhaji ya bawa Taj labarin abin da ya gama tunawa ɗazu akan zuwan Abba Habibu neman taimako wajensa a shekarun baya. "Ka san Annabi SAW ya gargaɗe mu da gujewa girman kai da illarsa akan ayyukan ladan mu." "Haka ne." Cewar Taj da sauri yana jiran yaji sauran abin da Alhaji zai ce. "Dole na daina yaudarar kaina idan ina son ganin daidai. Tabbas tuntuni na jima da ji a raina cewa Habibu ya tuba. A zuciyata ina muradin janyo shi jikina in inganta masa rayuwa. Amma a gefe guda ina tunanin makomar mutumcina a idon duniya. Ina ƙyamar a ce ina mu'amala da mutum irinsa." Muryarsa ta koma abin tausayi a yayinda yake cewa "kaga gabaɗaya fushin nawa ya zama ba don Allah ba. Girman kai ne kawai ya hana ni yin abin da ya dace ba wai don ban san ya dace ɗin ba. Tun girma da arziƙi ban nemi shiri da shi ba gashi yanzu dole in ƙanƙantar da kai a gaban sa tunda girman da arziƙin nasa ne. Kowa yaƙi sharar masallaci..." "Yaya Hayatu dai ba zai yi ta kasuwa ba!" Tare su ka juya da jin muryar Abba Habibu a gefen su. Abba Habibu ne tsaye shi da Hamdi. Ganin su ya sa su miƙewa su ma. Tun shigar su ɗaki, Yaya ta ce Hamdi ta koma su dawo tare da Taj. Ta hango shi yana ja da baya. Mama ta ce musu tana tunanin yana jin nauyin fuskantarta ne bayan ta gamu da lalura a dalilin ɗan uwansa. "Ai kuwa ba zan yarda da wannan tsirfar ba. Maza bi shi ki ce ina nemansa." Da ta fito sai ta manta a hawa na nawa su ka baro su. Ta koma tambaya shi ne Abba Habibu ya hana Umma da tayi yunƙurin rakota biyota. Ashe rabon za su ji maganganun su Alhaji ne. "Habibu..." Alhaji ya fara cewa da wata ƙaramar murya kamar ba shi ba. Sai dai Abba Habibu bai jira ya gama magana ba ya girgiza masa kai. "Ko me za ka ce don Allah ka bari indai ina da sauran mutumci ko yaya a idon ka. Ya wuce. Komai ya wuce in sha Allahu." "Ba za ka bari na baka haƙuri ba?" Lura yayi Taj ya yiwa Hamdi alama suna shirin barin wajen ya koma gare su "kada ku tafi." Abba Habibu ya tsaya tare da yaran nasu suna kallon Alhaji. "Ƙaddarar auren ku ita ta kawo mu wannan ranar saboda haka ina so ku shaida kuma ku taya ni bawa Habibu haƙurin dukkan wani abu na rashi daɗi komai girma ko ƙanƙanta da na taɓa yi masa." Da rashin jindaɗi Abba Habibu ya ce "Amma na ce ya wuce. Ban riƙe ka ba wallahi." "Kayya dai Habibu. Zuciya tana son mai kyautata mata ne. Abubuwan da nayi ko bakin ka bai faɗa ba na san dole rai ya sosu." Murmushi kawai Abba Habibu ya yi ya ƙara maimaita cewa komai ya wuce. Su ka koma ɗakin Yaya tare. Alhaji gabaɗaya ya kasa sakewa duk yadda Abba Habibu da Yaya su ka yi ta ƙoƙarin nuna babu komai. Hakan yasa su Hajiya tsangwamar kansu su ma. Tun abin yana burge Taj har dai ya ƙosa su bari haka nan. Alhaji yana ta maimaita ban haƙuri. Abba Habibu yana ƙoƙarin nuna komai ya wuce. Iyayen su mata kuma suna taya mazan su. "Alhaji da dai kun bar abin nan haka kun fara tunanin gaba. Misali kaga kai sai kayi fama da su Daddy (Yaya Babba) kafin su karɓi uzurinka na ƙin faɗa musu ciwon Happiness da wuri. " Ya juya ya kalli Abba Habibu "su Zee za su iya saurin fahimta idan ka kira su amma Inna Luba dai ban sani ba ko za ta yarda ba sayar da ƙodar Yaya kayi ba." Ya mayar da duban sa ga su Hajiya yana sosa tsakiyar kai "yau dai ya kamata ku kikkira naku ƴan uwan ku ma ko kuwa?" Ɗakin ya yi tsit. Taj ya harba bomb ya barsu da jiran tashin sa. Wayar da basu yi tunanin kira ba a tsukin kwanakin baya sai yanzu su ke tsoron abin da zai biyo baya. Tabbas ƴan uwan kowannen su za su ji babu daɗin ɓoye musu zancen nan ba. Da ya kula attention ɗin su ya samu don irin su Inna har an ɗauko waya sai cewa ya yi "amma dai kada ku kira yau domin tunda magriba ta wuce a gida dare ya riga ya yi. Zancen zai iya hana wasu bacci. Ga masu BP da ƴan rikicin tsufa." Mama dai hannu ta ɗaga za ta kai masa duka ya zille da sauri yana dariya. Su ma ɗin su na son yin dariyar amma babu hali. Zungurin da ya yi musu akan wayoyi masu mahimmanci da ya kamata su yi duk ya ɗaga musu hankula. "Zo mu tafi Hamdi. Its late and I am tired." "Haƙƙun! Sannu mai mata. Wato ta zo ku tafi ko? Kai babu ruwan ka tunda mu tayar mana da namu BP ɗin kuma za ka hana mu bacci ba." Umma ce tayi maganar tana harararsa sama da ƙasa. Dole kowa ya dara kuwa har Yaya akan gadon ta. Daga dai su ka yi sallama domin su ƙara raguwa. Abba Habibu kaɗai za a bari. Su Alhaji gabaɗayan su kuma su ka fito tare. Agogo ya nuna ƙarfe uku da kwata na dare. A muhalli uku bayin Allah suna kan abin sallah cikin ganawa da Ubangiji SWT. Abba Habibu na zaune hannuwa a sama bayan ya idar da nafila yana mai ƙasƙantar da kai cikin neman yardar Allah. Fatansa Yaya da Kamal su koma gida da ƙafafun su. Sai kuma ya miƙa dukkan al'amuransa, na iyalinsa da na dukkan wanda mu'amala ta haɗa su komai ƙanƙanta ga Allah SWT. A cikin ɗakin Alhaji ma shi kuka yake yi sosai yana roƙon gafarar Sarkin Sarakuna SWT. Hakan kuma take tsakanin Taj da Hamdi. Gajiyar da su ka kwaso bata hana su raya daren da sallah ba domin kyakkyawan fata akan gobe. A ɗakin Kamal, idanu ya buɗe tar cikin hayyacinsa. Tashin farko ya kai hannunsa ciki ya tabbatar akwai yanka alamun an yi masa aiki. Bai san lokacin da ya runtse idanunsa ba yana faɗin "Allahu Akbar. Allahu Akbar. Allahu Akbar" *** RAYUWA DA GIƁI 39 Batul Mamman💖 Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN Saƙon ta'aziyya ga ƴar uwa kuma shugabar mu ta WOMEN OF WORDS wato Hassana (Sanah) Sulaiman Ismail Matazu bisa rashin mahafinta da tayi. Allah Ya jiƙan shi. Ya gafarta masa. Allah Ya sa ya huta. Ya baku dangana. Amin Idanun Salma tsilli-tsilli kamar an kasa gurjiya a faranti. Irin yanayin nan da akan samu a wajen munafukin da ƙaryarsa ta ƙare. Sam ta rasa gane me ma ya kamata tayi tun bayan mahaifinta ya sanar da ita baƙin labarin da a wajenta gara mutuwa sau dubu a kan shi. Wai an ɗaura aurenta da Alh. Usaini. "Kaiiiii. Wallahi ba zan yarda ba. Ni ba zan zauna da shi ba ko sama da ƙasa za ta haɗe. Taj nake so kuma shi zan..." Kaf taji saukar duka akan laɓɓanta. Dukan ya shige ta kuwa domin babu arziƙi tayi shiru sai zugi a bakin. "Wallahi Salwa idan na ƙara jin sunan Taj a bakin ki zan iya tsine miki. Shashashar banza wadda bata san ciwon kanta ba." Baki za ta buɗe ya juya bayan hannunsa a fusace zai kai mata mangara dole ta fasa yin maganar. "Ko mata sun ƙare kina tunanin Taj zai aure ki? Ke ko yana son ki ina mai tabbatar miki Alh. Hayatu ba mahaukaci bane. Ba zai taɓa amsar ki a matsayin suruka ba." "Na ji amma don Allah ka kashe auren nan. Ba zan iya zama da mushiriki ba" "Har kura za ta ce da kare maye? Ba ki ji kin bawa kan ki dariya ba Salwa?" Ya faɗi yana yi mata kallo irin na wadda ta rainawa kanta hankali. Tashi ya yi ya kalli ɗakin hotel ɗin yaji wani abu ya sake turnuƙe masa zuciya. Wato dai da gaske da bahaushe ya ce son zuciya, ɓacinta. Ko a tatsuniya shi bai taɓa jin an ɗaura aure a ɗakin hotel ba sai da shi da kansa ya karɓi sadakin ƴarsa. Yadda abin ya kasance ya fi kama da almara. * Ɗazu da azahar mahaifin Alh. Usaini ya je hotel ɗin da su ke shi da Salwa. He got the shock of his life lokacin da ƙanin Usaini ya ƙwanƙwasa ƙofar su ka ji muryarsa yana cewa. "Ƙar ki taɓa ƙofar nan. Kada ki buɗe." Ransa kuwa ya sosu fiye da tunani. Dama can barazana yayi a reception har aka rako su ɗakin. Saboda haka sai ya yi wa ma'aikacin hotel ɗin inkiya da hannu ya yi magana. "Yallaɓai baƙo ne da kai a ƙasa." Da sauri Alh. Usaini ya ce "kada ka bari ya hawo gani nan saukowa. Ƙanina ne. Dama mun yi waya na faɗa masa ya same ni a nan ɗin." Ya ɗaga yatsa ya gargaɗi Salwa "zan fita kuma na rantse da Allah idan ki ka min halin jakancin nan naki ki ka fito sai na ɓaɓɓalla ki. Wawiya kawai. Dalla can gafara in wuce." Ta murguɗa baki tana yatsine fuska "jaka tana can gidan jaki mai furfura." 'Yau kuma jakuna mu ka koma' Baban Alh. Usaini ya jinjina kai yana zancen zuci. Ran Alh. Usaini ya ƙara ɓaci sosai ya ɗaga hannu ya zabga mata mari. "Iyayena ki ke zagi Salwa? Iyayena?" Kumatu ta fara riƙewa ta ce "Ni ka mara?" Sai kuma ta cakumu wuyansa "wallahi ba ka doki banza ba. Yadda kake jin kana da gata nima ina da shi." "To gatan naki ya zo yanzu don uban mutum." Daga nan sai sautin duka da kukan Salwa da kuma maganganun Alh. Usaini. Baban ya nuna wa ma'aikacin hotel ɗin lallai ya buɗe kafin ayi kisan kai. Da yake tsoron afkuwar ɓarnar tafi yawa akan privacy ɗin costumer, dolensa ya buɗe. Su ka yi mummunan gamo. Tsananin fushi da ɓacin rai ya sa Alh. Usaini yiwa Salwa dukan biredi. Ita ma kuma ta samu nasarar jifansa da abubuwa don har goshi ta kumbura masa. Sandarewa ya yi a lokacin da idanun sa su ka sauka cikin na mahaifinsa da aka buɗe ƙofar ɗakin. Ya saki Salwa a gigice kamar wanda ya ɗauki garwashi ya kama rantse-rantse. "Wallahi biyo ni tayi Baba. Duk abin da ka ke zato ba haka bane. Sam ni ba na harkar mata." Ya sassauta murya sosai "Salwa faɗa masa gaskiya. Ai babu komai tsakanin mu ko?" Maimakon ta faɗi gaskiya sai ta zaɓi amfani da wannan damar. Zubewa tayi a ƙasa ta kama kuka. "Mene ne tsakanin ku?" Baban ya fara tambayarta sai ya fasa ya dubi wanda ya rako su "kwanan su nawa a nan?" "Kwana uku ne." "Shike nan. Kana iya tafiya." Bayan ya fita Baban Alh. Usaini ya buƙaci Salwa ta bashi numbar wani nata su yi magana. Tana jin haka idanunta su ka raina fata, ta kasa motsawa. Sai ya kalli ɗansa. Yana iya ganin tsananin tashin hankali a tare da shi. "Ka karɓar min numbar wanda zai zo ya karɓeta ta koma gida." Jikinsa na rawa ya tashi ya buɗe handbag ɗinta ya ciro wayarta. Wayar ma a kashe sai da ya kunna sannan ya bata don ta buɗe wayar. Jikinta ya yi la'asar don ta kula tsoron babansa yake yi shi ne ta ce "Ka bani abin da nake buƙata in tafi da kaina." "Ai baki isa ba. Wallahi gara a zo a ɗauke ki in san na rabu da ƙaya." Tsawa taji daga sama kafin ma ta sake yin gardama daga babansa "Ke! Bani number na ce yanzun nan. Ki tabbatar wadda za ki bani mai shiga ce." Da ka ta karanto masa numbar Babanta saboda Ahmad dai baya nan sannan bata ga alamun za su wanye lafiya ba idan tayi ƙarya. Waje ya fita da ya yi dialing numbar. Salwa ta matsa kusa da Alh. Usaini kafin ya dawo. "Kaga ka bani abin da nake nema na tafi tun kafin ya dawo. Ban san me yake shirin yi ba kuma ba na burin sani." "Hummm...kin makaro. Ƙaryar da ki ka yi masa da alama ke za ki kwana a ciki don na san dole ya kira baban ki a zo a ɗauke ki." Wajen rabin awa ya share yana wayar kafin ya dawo. Umarni ɗaya ya basu kafin ya fita. "Zan dawo gobe in sha Allah. Ina fata idan na zo na same ku tare. Idan ka bari ta tafi Usaini to ka tabbatar babu ni, babu kai wallahi." Yana gama magana su ka fice. Alh. Usaini ya ƙulle ƙofar ya dinga naushin bango kamar mahaukaci. Salwa jiki na ta tsuma ta ɗora hannuwanta akan kunnuwanta tana hawaye. Gabaɗaya a tsorace take kuma tayi imani motsin kirki idan tayi sai ya sake jibgarta. * Ko awa guda ƙwaƙƙwara Abban Salwa bai iya sake yi ba ya biyo hanyar Kano tare da ƙannenta. Saboda munin labarin da ya samu sai ya kasance ko murnar ganinta da aka yi bai yi ba. Mutumin da ya kira shi ya faɗa masa cewa ya same su da ɗansa su na rigima harda doke-doke. Shin yaushe lalacewarta ta kai haka ba tare da ya sani ba? Yanzu ya ƙara yarda duk wanda ya sayi rariya dole ya ga zubar ruwa. Cikin dalilai huɗu da Manzon Allah SAW ya hori musulmi da aure, guda ɗaya tal ya duba lokacin auren Mami wato kyau. Ƙwarai ta haifa masa kyawawan yara abin nunawa ta wannan fannin. Amma a halin yanzu hatta mazan ba wai ya sami yadda yake so bane daga gare su. Kawai dai ana cikin yanayin da babu gara ba daɗi. Takwas da arbain na dare a Kano tayi musu. Ko masauki bai nema ba ya kira Baban Alh. Usaini. Nan ya faɗa masa sunan hotel ɗin ya ce ya jira shi zai taho shi ma yanzu. Da su ka haɗu sun jima su na tattaunawa game da halin ɗan yau da abin da son zuciya ke kawowa. Baban Alh. Usaini shi ne ya kawo shawarar lallai a ɗaura musu aure. Wannan ne zai sa har ƴan baya ma su shiga taitayinsu. Matsanancin tsoron da ya kama Salwa da Alh. Usaini a yayinda iyayensu da ƴan uwan su su ka shigo ɗakin da su ke ba zai faɗu ba. Banda ƙannen Salwa biyu akwai wasu biyun na Alh. Usaini da Babansa ya taho tare da su. * "Aure???" Salwa da Alh. Usaini su ka yi tambayar da sun riga sun san amsarta ga iyayensu a lokaci guda. Kamar ba da mutane su ke ba. Babu wanda ya tanka musu. Sai ma Limamin Masallacin Khamsa Salawatin kusa da hotel ɗin da aka yi wa iso ya shigo ya zauna. Kafin wani lokaci ɗakin ya kasance babu masaka tsinke a dalilin mutanen da su ka shigo ganin ƙwaf. Labari ya bazu tun daga reception za a ɗaura aure. Sai ga mutane su na buɗe ɗakunan su suna tahowa kallo. Video kuwa harda masu yin live a social media handles ɗin su. Salwa sai wani ɗakin aka shigar da ita. Abu kamar almara. Aka ɗaura aure bisa sadaki naira dubu hamsin lakadan tsakanin Salwa hauka mai son ma so wani ƙoshin wahala da Alh. Usaini shugaban ƴan hassada da baƙinciki. Aure ne wanda iyaye su ka yi alƙawarin yin baki ga ƴaƴan nasu idan su ka kuskura su ka rabu. Bayan an watse ne Abban Salwa ya miƙa mata sadakinta a hannu. Shi ne take ta roƙo da magiyar ya yi haƙuri ya sa a sauwaƙe mata. "Aure an yi kenan in sha Allah. Daga nan in kun fita ku yanki daji ku fara bokanci ko bori tunda silar haɗuwar ku kenan." Kalaman sa sun yi mata zafi. Yanzu kuma bokanci yake kira mata kamar ba ƴar cikinsa ba? "Daddy ni ce kuma zan yi bokanci?^" "Meye a ciki? Boka mushiriki, mai zuwa wajen boka ma mushiriki abu na Ɗanjuma da Ɗanjummai." Su na ji su na gani iyayen su ka tattara su ka watse abin su bayan dogon gargaɗi akan dole su zauna tare. Su ka tafi tare inda Baban Alh. Usaini ya ce yau a gidansa za su kwana. Sannan gobe zai kira duk wanda ya dace ya san da auren domin su gabatar da junansu a gaban shaidu. Salwa kuka kamar ranta zai fita, Alh Usaini ko kallonta bai tsaya yi ba. Ya riga ya yi wa kansa alƙawarin zama da ita amma fa sai ta ɗanɗana kuɗarta. Son da yake yiwa kuɗin babansa bai kama ƙafar tsanar da ya yi mata ba. Ita ta ja masa komai. Ta saurari hukunci. *** Gaba na faɗuwa Taj ya kama ƙofar ɗakin Kamal. Hannun nasa har wani sanyi ya yi kamar ba a jikinsa ba saboda tararrabi. Bayan asuba su ka taho asibitin saboda kira da su ka samu akan tashinsa babu sauran magagin allura. Kowa ya kama shiri sai Alhaji ya ce su yi haƙuri a dinga tafiya in batches. "Kun gan mu unguwa guda idan mu ka cika musu wuri irin na jiya ba za su ji daɗi ba. Idan wasu su ka dawo sai wasu su tafi." Ba dai haka su ka so ba amma sun san tsarin nasa shi ne daidai. Nan ba a jinya ba kamar tamu ƙasar ba. Sannan babu damar zama idan ba layin ganin likita ba. Maimakon su yi ta zama a mota ana jiran juna gara kowa ya kintsa a cikin nutsuwa. Taj da Hamdi da iyayensu mata ne su ka fara tafiya tare da Alhaji. Idan sun gama sai Ahmad ya taho da wasu. A hanya aka dinga mayar da zancen yadda ƴan uwa da abokan arziƙi su ka ƙarbi zancen abin da ya faru da aka kikkira su a waya. Don tausayi, sosai an tausaya kuma an jajanta. Amma fa hatta waɗanda su ke matsayin ƙanne a garesu babu wanda bai nuna ɓacin rai akan shirun da aka yi ba. Alhaji Babba ma cewa yayi zai zo amma ba don su ba sai don Kamal da kuma Yaya da tayi musu halacci. "Duk wannan bai isa ba Taj sai da ka san yadda kayi ka juya magana a wajen Jamila (Amma) ka sa ta kira ni tana yi min rashin kunya. Ƴaƴan arziƙi da rufin asiri aka san su." Taj ya kyaɓe fuska har sai da Hamdi tayi murmushi. Kunya ta kama ta da ta kula ashe Mama na kallonta lokacin da take kallonsa ita ma. "Yanzu Alhaji ni ba ɗan arziƙi bane? Kuma dai maganar gaskiya ku ne fa ku ka hana mu yin ƙarya." Alhaji ya bashi amsa da cewa "Eh, amma kuma duk mai hankali ya san akwai lokutan da ake yi wa gaskiya kwaskwarima don a sami zaman lafiya." "Mix ɗin ƙarya da gaskiya fa kenan Alhaji." "Dama duk tsayin shekarun nan bakin ka bai mutu ba Tajuddeen?" Me za su yi kuwa banda dariya. Tun farkon sanin ciwon Kamal sai yau ne aka samu sukunin yin farinciki daga zuci ba iya fatar baki ba kaɗai. Sai da su Alhaji su ka fito daga wajen Kamal sannan Taj ya taho zai shiga. Hamdi dama tun shigowarsu ta tafi wajen Yaya. Idan ƴan uwan sun sami nutsuwa za ta je su gaisa. "Rufe ƙofar" Kamal ya umarci Taj bayan ya amsa masa sallama. Wani babbasarwa Taj ɗin ya kama yi kamar bai ji shi ba. Kamal ya yi murmushi. "Da dai ka rufe kada kukan garada ya cika wa mutane kunne." "Kuka za mu yi kenan? Abin babba ne" Taj ya rufe yana juyowa don duk a zatonsa Kamal wasa yake yi sai kawai yaga ya fashe da kuka. Kuka ba na wasa ba. It was coming from the dept of his heart. Kukan tsoro, ciwo da farinciki. Taj ya ja kujera ya zauna a gabansa. Bai ce masa komai ba sai da ya kula cewa ya fara jin sauƙin damuwarsa. "Was it that hard?" Ya tambaye shi a yayinda yake miƙa masa tissue. Nannauyan numfashi Kamal ya sauke sannan ya ce "it was. Taj I was so scared. Na zata zuwa yanzu na zama tarihi. Kai kuma ka shigo kana wani ɓata rai. Ni da cuta kai da shan kunu." Abin da yake ransa ya amayar duk da ya yi matuƙar ƙoƙarin danne ɓacin rai a fuskarsa "Kamal kayi min adalci? Ni ne fa. Haba!" "Don Allah kada ka tuhume ni akan shirun da nayi. It was extremely difficult for me. Bana son ganin kuna yi min kallon tausayi ko a dinga koke-koke." "Ka ga sharrin kallon movies ko? Wannan wane irin banzan tunani ne? Da kuma ka tafi fa? Happiness da ace ba ka sami kidney ba fa? Sai dai na zo na tarar da mummunan labari? So kayi ka tafi ka barni da tunanin irin halin da ka shiga yana haunting ɗina?" A raunane Kamal ya ce "ba haka bane." "To yaya ne?" Bai san ya fara hawaye ba "I was happy Kamal. Ina dariya ina nishaɗi saboda na auri wadda nake so kuma na samu Alhaji ya yafe min. How could I be happy. I shouldn't..." Kamal ya marairaice masa "Da ka zauna mun yi kukan nan kawai mun share. Wannan mitar bata da amfani. Laifi ne na riga nayi kuma na karɓa. Haba Happy na Happiness." Ya kama murmushin ganin ya soma samun kansa "nace kai ma ka na kallon finafinai kenan ko? Na ga sai wani blaming kanka kake yi irin abin nan na masu ɗan uwa." Cije leɓe Taj yayi yana harararsa. Daga ƙarshe ya yi kwafa gami da jinjina kai. "Za mu haɗu." Daga nan hirar ta koma kan tambayar jikin Kamal da yadda yake ji a yanzu. Motsi kaɗan zai yi Taj ya dinga tambayarsa me yake so. Shi kuwa tambayar da su Alhaji su ka yi ta kakkaucewa amsa masa ya samu ya yi. "Happy wa ya bani ƙoda?" Alamun alhini Kamal ya fara gani a tattare da Taj shi yasa ko da ya wayance da cewa "Ban fahimce ka ba? Masu alhakin faɗa maka ɗin shiru su ka yi don su jiƙa min aiki?" Ya tashi zai fita "bari na kirawo maka Alhaji." "Ka ajiye maganar wasa don Allah. I need...I must know." Allah Ya sani bai so haka ba amma kuma rashin amsawar ba komai zai janyo ba sai tashin hankali ga mara lafiya, wanda kuma ko kusa ba a son haka. "Kamal, Yaya ce tayi donating. Yaya mahaifiyar Hamdi." Da wani irin yanayi Kamal ya zabura sai da Taj ya danne masa kafaɗa. "Yaya fa ka ce. Let me go." Ya doke hannun Taj "ka sake ni mana. Taj ba fa wasa nake ba. Ka ƙyaleni na tashi." "Ina za ka idan ka tashi? Wai ma so kake aikin ya buɗe ka mayar da hannun agogo baya?" Kawai sai Kamal ya sanya tafukan hannunsa ya rufe fuska ya fashe da kuka. This time around fassara kukan nasa ma abin wahala ne. "She is fine fa Happiness. Wallahi jikinta da sauƙi sosai." "Me ya faru? Na kasa fahimtar komai." Taj took his time ya labarta masa abin da Mubina ta sanar da shi da Hamdi jiyan bayan komawarsu masauki. Guilt ke damunta har lokacin shi ne ta zaɓi sanar dasu yadda aka yi Yaya ta fara tunanin binta daga hirarsu a jirgi. Hatta recording ɗin saƙon da ta bari ya fayyace masa. "Na kasa murna Happy. I feel...Subhanallah" idanun Kamal cike fal da hawaye ya rirriƙe Taj "ka kai ni wajenta don Allah ko na tafi da kaina." *** Ɗakin yayi shiru sai sautin kuka da yake fitowa daga wayar Ahmad ta speaker. Whatsapp call ya kira ta wayar Sajida. Ita da Zee da Halifa babu wanda ba ya kuka. Hamdi ma kukan take taya su. Yayinda Abba Habibu da Yaya murmushi su ke yi kawai wanda babu komai cikinsa illa dauriya. An ɗaga mata gadon ta yadda bayanta yana jingine da filo. Muryar Halifa ce ta fito daga wayar yana shessheƙa "don Allah a mayar da kiran nan bidiyo mu ganta." "Yanzun nan kuwa" Ahmad ya saita wayar akan Yaya bayan ya juya call ɗin. Yaya tayi saurin gyara yanayin fuskarta gami da faɗaɗa murmushinta. "Kun ganni fa. Wallahi naji sauƙi sosai. Ku kwantar da hankalinku." Hamdi ta ƙara musu da cewa "Da a ce da matsala kun san ba zan ɓoye muku ba." "Wai me ya kai ki gidan mutane da sassafe Sajida? Nan yanzu ba na jin bakwai ta yi." Abba Habibu ya yi maganar yana duban agogon wayarsa. Awa biyu ne tsakaninsu da Nigeria. Tara saura ƴan mintuna yana nufin a can bakwai ne saura. Sai lokacin Anti Zinatu da take ta aikin matsar ƙwalla tayi magana. Tun dare da Abba Habibu ya sanar da ita halin da ake ciki ta karɓi lambar Safwan da dabara a wajen Zee. Ta sanar da shi komai sannan ta buƙaci ya kawo Sajidan wajenta a lokacin da za a sanar da su. To ashe shi ɗin ma mutum ne mai saurin ruɗewa. Daga wayar nan bai sake yin wani abin kirki ba, ko bacci ɓarawo da ƙyar ya sace shi. Ai kuwa ana sallame asuba ya ce ta shirya su taho. "Ni dai yanzu alfarmar da zan roƙe ku don Allah kada wanda ya tayarwa Innata hankali. Ku bar zancen nan har sai na dawo in sha Allahu. In lafiya ta samu yadda ake so ma ba sai ta sani ba." Shawarar Yaya rabi ce ta sami karɓuwa a wajen Alhaji. Batun a rufe maganar kuma ya ce ba zai yiwu ba. "Sadaukar da ƙoda babban abu ne wanda a halin da muke ciki yanzu da wuya maganar ta ɓuya. Idan wani bai fađa ba, wani zai iya faɗa. Saboda haka za mu jira ki sami sauƙi sai mu auna mu gani shirun da faɗar gaskiyar wanne ne yafi ko kuwa Habibu?" Tattaunawa su ka cigaba da yi cikin lumana da girmamawa na ɗan lokaci. Hamdi ta ji duk ta takura. Zantukan nasu sun shafe su amma bai kamata ta tsaya musu a wajen ba. Tunanin dabarar ficewa ta fara yi sai ga kiran Bishir ta wayar Hajiya. Ya faɗa mata yana ƙasa tare da Mubina. Wai tana son tafiya Madina ne yau shi ne ta zo tayi musu sallama. "Amma don ragon azanci ta kasa faɗa mana mu taho tare?" Dariya taji ya soma yi yayi magana da zolaya "Hajiyarmu ta gargajiya kenan. Yanzu duk ɓarin hawayen da ta gama yi a asibitin nan baki gane komai ba?" "Me aka yi?" Kafin ya bata amsa ta soma murmushi "kai Bishir ka tabbata?" "Kin gano kenan" ya kama dariya sosai. Mubina dake gefensa ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin ɓoye murmushin dake neman kufce mata. Ta ji abin da yake cewa ta kuma gane me hakan yake nufi. Hajiya cewa tayi su hawo da sauri sannan ta zaga bayan Mama ta faɗa mata yadda su ka yi da Bishir. Baki ya kasa rufuwa da Mama ta fesawa kowa zancen. Yaya ma daga kwance ta taya su murna. Sannan ko kusa bata yi mamaki ba. A ganinta dama soyayya ce kaɗai za ta sanya Mubina biyo bayan patient har wata ƙasar. Alhaji da Abba Habibu ma sun nuna farinciki ƙwarai. Hamdi sai ta sake amfani da wannan damar za ta sulale ta gudu kafin su farga. Kamar haɗin baki ta na buɗewa Taj ya turo Kamal akan wheelchair. Hirar iyayen a take ta yanke sai tambayar me yake faruwa. "Wajen Yaya na zo." Kamal ya ba su amsa da kansa. Murmushi Yaya ta yi masa da su ka haɗa ido "ai bai kamata ka fito a wannan yanayin ba. Taj da ba ka kawo shi ba." "Nayi ƙoƙarin hana shi Yaya amma wallahi ya ƙi. Dole na kira wani Nurse shi ne ya ɗora shi a nan" ya nuna wheelchair ɗin. A daidai lokacin kuma Bishir da Mubina su ka shigo ɗakin. Hankalin Kamal ya yi gaba bai kula da su ba da farko. Ya ce Taj ya matsar da shi daf da gadon Yaya. Ya tura shi kuwa jikin gadon sosai. Kamal ya miƙa hannunsa na dama dake ɗauke da canula saboda ƙarin ruwa da ake yi masa ya riƙe nata hannun sannan ya kalli Abba Habibu. "Abba na riga na zama ɗan Yaya shi ya sa ban nemi izinin taɓa hannunta ba." Abba Habibu ya gyaɗa kai yana murmushin nan nasa. Ragowar kuwa duka aka yi shiru ana sauraron Kamal. "Duk wahalar dake tattare da ɗaukar ciki da haihuwa a wurin mata a ƙarshe tana da riba Yaya. Za a kalli mace a kira ta UWA ko da ɗan ba a gabanta yake rayuwa ba. Su kan su mata abinda ya sa su ke jurar wannan wahalar komai tsananinta bai wuce domin samun wannan matsayin ba. Mace za ta zama mai cikakken iko akan wani bawan Allah da yake rayuwa da jinin jikinta." Ya ja numfashi "Allah Yana biyan wahalhalun da ta sha akan ƴaƴanta da mafi ƙololuwar daraja. Ya bata martabar da babu mai kamo ta a wajen wannan bawa har ƙarshen rayuwarsu su biyun." Ya yi murmushi idanunsa fal hawaye. Ko da ya ɗaga kai ya kalli Yaya sai hawayen ya zubo. Nata ma ya zubo...idan ka cire Alhaji, Abba Habibu, Ahmad da Taj, duka waɗanda su ke ɗakin sai da su ka zubar da ƙwalla. "Yaya wace daraja ki ke tunanin Allah Ya tanadarwa matar da ta bawa ɗan da bata da alaƙa da shi ta jini wani ɓangare na jikinta don ya rayu? Bayan kin san cewa wahala, azabar ciwo da fargabar me zai je ya dawo a dalilin sadaukar da ƙodarki ba zai mayar dani ɗan ki ba. Taki juriyar naƙasu ce a jikinki da lafiyarki. Babu wata riba ta kurkusa ko ta nesa don ban ga abin da za a biya ki da zai maye gurbin ɓangaren jikin ki da ki ka bani ba Yaya." "Kamal ka yi shiru don Allah. Jikin ka babu ƙwari." Yaya ta faɗi cikin kuka. "Yadda ɗa baya yin godiya ga iyayensa akan haihuwarsa da su ka yi, haka ni ma ba zan yi miki godiya akan kyautar da ki ka yi min ba. Alfarma kawai na zo sake roƙa domin Allah." "Ina jin ka Kamal. Don Allah ka daina kukan nan." "Yaya idan kina lissafin ƴaƴanki ki dinga farawa daga Kamaluddeen Hayatu don Allah." Kuka sosai yake yi a wannan gaɓar. "Idan kina da sirri irin na uwa da ɗa don Allah ki yi dani." Yaya ta gyaɗa kai. "Damuwa ko wacce iri ce irin ta uwa da ɗa kada ki tsallake ni." Nan ma ta sake nuna amincewarta. "Buƙata ko wacce iri ce ta uwa da ɗa ki fara faɗa min tunda kin ga Halifa ƙarami ne. Su Hamdi kuma mata ne ma su rauni." "To Kamal" Yaya ta amsa cikin kuka. "Idan su Sajida sun yi miki laifi don Allah kada ki ɓoye min. Ki rufa musu asiri a wajen Abba amma ki sanar dani. Zan yi mu su faɗa tamkar cikin mu ɗaya." "Na sani Kamal, ko babu wannan abu ai kai me tsaya mu su ne." Kamal ya girgiza kai "a da sai dai nayi kara, yanzu kuwa duk abin da ya shafe ki Yaya ya zama dolena." Ku san sai a lokacin ya lura da tsayuwar Mubina a ɗakin. Sai ya yafito ta da hannu. Ta so cogewa amma Mama da kanta ta kaita kusa da Kamal ɗin. "Kin amince da zaɓina Yaya? Idan na auri Mubina ƴar mu ta farko in sha Allahu sunan ku ɗaya. Sunan ta..." ya kalli Hamdi yana jiran ta ba shi amsa. "Khadija." "In sha Allahu sunanta Khadija." Yaya ta rasa abin cewa. Tana gudun zaƙalƙalewa a gaban iyayensa. Gashi kuma ya tsare ta da idanu yana kallonta with so much adoration. Alhaji ne ya yi stepping in da ya ga ta kasa magana. "Ba ki ce komai ba game da zaɓin ɗan naki Yaya?" Yaya ta ɗaga kai a rikice ta kalli Abba Habibu tana neman agajin sa. Ita fa komai bambarakwai take jin sa tun shigowar Alhaji ɗakin nata. Ba ta son yin abin da zai sake janyo wa mijinta abin magana. Cikin nutsuwa Hajiya ta matso ta kama ɗayan hannun Yaya a yayinda ɗayan har lokacin ya na cikin na Kamal. "Ko ba ki karɓi tayin da Kamal ya yi miki bane na zama uwa a gare shi?" Ta haɗa hannuwanta biyu tana magiya "Don Allah ka da ki kasa yi masa wannan alfarmar. Kamar yadda ya faɗa babu zancen biya ta kowacce fuska tsakanin mu. Hakan raini ne ma akan girman abin da ki ka yi mana. Ƙara shi cikin zuri'arki ne kaɗai abin da za mu iya duk da cewa mu ne dai da sake samun riba." "Don Allah ku daina magana irin haka. Domin Allah nayi." Ta zame hannunta dake cikin na Kamal ta nuna ƙirjinta "Karamcin Ubangina a gare ni mai girma ne. Shi Ya nufe ni da zuwa a lokacin da Kamal yake tsananin buƙatar hakan ba tare da sani ko shirin wanin mu ba. Kuma Ya azurta ni da dakewar zuciya na cika umarnin ƙaddara. Ni da har yau nake tsoron allura sai gashi na kawo kaina inda za a yanka min ciki. Na fi ku riba wallahi. Allah Ya bani ikon ceton rai sannan Ya ƙara faɗaɗa ƴaƴana." Ta sanya hannu ta shafa kumatun Kamal. Shi kuwa ya ɗora hannunsa akan nata ya lumshe idanunsa cikin farinciki. Maimakon kuka kuma sai farinciki ya mamaye ɗakin. Mubina ta kasa daurewa ta bawa Yaya haƙuri domin tana ganin cewa ita ce ta jawo mata zuwa nan ɗin. "Kada ki sake magana irin wannan Dokta. Mu duka mu na yin komai ne cikin tsarin Ubangijinmu. Ba ki yi min laifi ba amaryar ɗana." Kunya ta kama Mubina. Ta koma kusa da Hamdi ta sunkuyar da kanta. Da jindaɗi Alhaji ya ce "Tunda abin ya zo da haka ku ba ni dama na yi mu ku karambani akan Baban Khadija da Maman Khadija mana." "Innalillahi..." Mubina ta faɗi a kiɗime da jin furucin Alhaji tana mai ƙanƙame hannun Hamdi. Ita ma dai babu halin zolaya kunyar ce ta kama ta. "Abban Kamal ka yi shiru." "To Alhaji mun ba ka dama." Abba Habibu shi ma dai yana cikin jin nauyin wannan sabon lamari. Shi kuwa Alhaji dama da gayya ya yi. Yana so ne ya canja takun mu'amala a tsakanin su tun wuri saboda a sake sabon lale tun kafin su koma gida. Waya ya ɗaga a gaban su ya kira kawun Dr. Mubina, yayan mahaifinta. Ita kanta ba ta san inda ya samo numbar ba tunda bai tambayeta ba. Maganar su ta ƙarshe ita da shi sosai dai tun kwanciyar Kamal a asibiti ne inda su ka fara haɗuwa har ya ce ya san Marigayi mahaifinta. Ya fara da gabatar da kansa wanda da alamu hakan bai yi wa kawun nata wahalar ganewa ba. Daga nan ga mamakin dukkanin su ya ɗauko maganar su da Kamal. Ya soma yi masa bayanin rashin lafiyar sa sai kawun ya ce ya gane shi. Bai dai san cewa ɗan Alhajin ne patient ɗin da ta dinga roƙonsa har ya barta tahowa duba shi da yin Umra ba. "Tunda dai har an dace ya sami ƙodar, ina ganin kawai ta zauna ta ƙarasa ladanta. Ina fata ka fahimce ni." A take Alhaji ya danna speaker yana murmushi sosai. Komai ya zo masa da sauƙi fiye da yadda ya yi tsammani. "Ƙwarai kuwa. Na saka ka a speaker a gaban iyalina, Kamal da ita Mubina. Zan so ka maimaita abin da ka ce domin nima dalilin kiran kenan. Ina son a san da zaman mu zuwa lokacin da Allah zai sa ya sami lafiya ya dawo gida." Kawu ya maimaita "Ka fi ƙarfin haka Alh. Hayatu. Me yiwu wa ba za ka iya tunawa ba amma ni abin yana raina sosai. Mun taɓa zuwa wajen ka nema wa yaran wasu ƙauyuka kuɗin jarabawar SSCE har su ɗari da sittin da bakwai. Bayan ka biya ka ɗauki ukun farko ka biya musu kuɗin jami'a in full sannan ka sa mu ka yi alƙawarin ba za su taɓa sanin kai ne ba. Shi ya sa wasu lokutan taimako yake zuwa ga bayin Allah ta inda ba sa zato. Sadaka babban jari ce." Alhaji ya yi ɗan murmushi kawai. Ɗan Adam ba ma'asomi ba. Kullum mu na cikin iyo tsakanin dai-dai da kura-kurai. Yawan tuba, ƙoƙarin fifita aikata ayyukan alkhairi da uwa uwa kyautatawa Allah SWT zato shi ne babbar maslahar rayuwa. Zai iya cewa a tsukin lokacin nan ya ƙara fahimtar rayuwa ta fuskoki mabambanta. Da fari ya yi karo da tsohon kuskurensa sannan yanzu ya gamu da tsohon alkhairi. FABI AYYI AALA'I RABBIKUMA TUKAZZIBAN Kawu kuma ya ɗora maganar sa. "Mubina ki zauna ki ƙarasa ladan ki har a sallame shi ." Mamaki tayi sosai "Kawu aikina fa? Kuma ..." ta saci kallon su Ahmad "ba ya buƙatar zama na." "Ai kuwa ki shirya domin kowa zai tafi ya bar ki da shi. Haɗa ni da Alh. Hayatun." Jikin Mubina ya yi sanyi ƙalau har ta kasa motsin kirki. Zuciyarta kawai ke harbawa da daidai da fitar kalmomin godiya daga bakin Alhaji domin ya cire wayar daga handsfree. Bayan ɗan lokaci ya miƙa mata wayar. "Je ki waje ki amsa" Da sauri ta fita har lokacin tana riƙe da hannun Hamdi. Ita kuma ganin haka sai ta nemi zare hannunta. Mubina ta dube ta da raunin murya. "Raka ni don Allah." * Shiru Mubina tayi tana sauraron Kawunta. "Alh. Hayatu ya ce zai sake kira na anjima kaɗan mu ƙarƙare magana. Idan komai ya tafi daidai in sha Allahu yau zan sauke amanar ɗan uwana, zan aurar dake ga mutumin da na tabbatar ki na so sannan ga dangin da nake fatan ba za su taɓa wulaƙanta ki ba." "Amma Kawu..." "Na san ban shiga haƙƙin ki ba da na yanke wannan shawarar. Soyayya ta Fisabilillahi ce kaɗai ta saka ki kusan zaucewa akan yaron nan kafin ki tafi. Yanayin ki ya bani tsoro shi ya sa ban hana ki tafiya ba da ki ka buƙaci zuwa Umra ke kaɗai saɓanin yadda mu ka yi shirin tafiyar gida cikin ƴan uwa." Kuka ta fashe da shi. "Ki bar kuka Mubina. Ina son amincewar ki ne domin yanzu zan tafi wajen Umman ki. Ki amince?" Da ka ta fara amsawa sai ta tuna ba ya ganin ta shi ne ta ce "Uhm" a hankali. "Allah Ya yi miki albarka." Rungume Hamdi tayi bayan ta gama wayar. Hamdi ta dinga bubbuga mata baya saboda kuka ne take yi sosai. Bata taɓa zato ko da wasa akwai ranar da burinta zai cika akan Kamal ba. Ta fi karkata da tunanin cewa zuwa yanzu ya ma bar duniyar. "Ki daina kukan nan haka Matar Yaya. Ni ce ke sujjada zan yi domin wannan babbar falala ce daga Allah SWT." Hamdi ta rarrasheta. "Nagode Hamdi. Abin ne duk wani iri. Kin ga ana shirin aurar dani babu kowa nawa." "Gani." Ta sakar mata murmushi "Don Allah ko da wasa kada ki taɓa yi min kallon matar ƙanin miji. Ƴan gidansu sun yi min tarbar ƴa kuma ƴar uwa ba suruka ba. Ina ganin rashin adalci ne zai sa mu kuma mu ɗauki kan mu da wani matsayi daban da na ƴan uwan taka." * A cikin ɗakin kuma bayan fitar su Mubina, Kamal ya ce Taj ya mayar da shi ɗaki. A hankali ya juya wheelchair ɗin yana mai kulawa da dukkan motsin da zai iya janyo wa Kamal jin zafi. Sallama Kamal ya yi wa kowa. Da ya zo kan Alhaji sai cewa ya yi da Taj ya tsaya. "Na ji kana ta magana a hankali ga Alhajin ka tambaye shi da kan ka?" Taj ya yi turus domin gabaɗaya bai gane me Kamal yake nufi ba. Ya kuma san cewa tunda ya yi haka to akwai abin da yake ransa. Lokacin wana shi ya samu. Sai ya rama ɓoye-ɓoyen da aka yi masa. "Me ka ke son tambaya?" Alhaji ya zuba mu su ido don ya gano wayon Kamal. "A bar maganar Alhaji. Zan dawo idan na kai shi ɗaki." Taj ya ɗan tura Kamal sai yaji kujerar ta turje. Kamal ya saki burkin tayar don kada su tafi. Ya yi kalar tausayi. "Ai gara ka tambaya yanzu saboda ni bana so ka tafi ka barni ni kaɗai." Abba Habibu murmushi ya yi. It is obvious Kamal a matse yake da son jin manufar maganganun Alhaji a waya. Ahmad kam dariya yake yi sosai. Alhaji ya yi ƴar dariya shi ma "Kamal ina jin ka. Me Taj ya ke son sani?" "Cewa ya yi wai ya ji kamar ana maganar aure na." Taj bai san lokacin da ya ce "Ni? Kamal yaushe?" Don bai yi tunanin tambayar da Kamal ɗin zai yi kenan ba. Inna ta shigar wa Kamal "Ai tunda ya ce ka yi kawai ka yarda cewa ka yi ɗin don a zauna lafiya." Da gangan Taj ya ce "Shikenan to." Ya kalli Alhaji "na ji kamar ka na maganar aure na." Ya yi nasarar tunzura Kamal kuwa don bai san lokacin da ya gyara masa ba. "Aurenka kuma? Yaushe ka yi aure da har ka ke tunanin ƙari?" "Ƙarin aure kuma Allah na tuba ai ba abu bane mai wahala." "To wai nufin ka Hamdi za ka yi wa kishiya? Happy akan su fa ni babu ruwana da dangantaka. Hamdi comes first yanzu. Da kai da mazajen su Sajida duk ɗaya ne a wajena. Kai suruki ne, ni kuwa ɗa ne ko Yaya?" Shi ma ya rama zolayar da Taj ya yi masa. Sai ga Taj da riƙe haɓa. Aiki ya biyo ta kan ma su gida. "Lallai ma! Happiness kada mu ɓata daga farfaɗowarka fa. Har za ka faɗa min kusanci da Yaya?" "Wannan ko shakka babu." Kamal ya ce kai tsaye "kai ƴa kawai ta baka. Ni kuwa ƙoda ta bani. Akwai jinin jikinta a tare da ni. Tsakanin mu ma babu haɗi. Mayar da rigimar tasu aka yi abin dariya a ɗakin. Taj ya nemi taimakon Abba Habibu da Yaya ta gyaɗa kai tana supporting ɗin Kamal. "Abba ka na jin sa fa." "Ƙyale su Taj kai fa ɗan maigida ne. Shi kuwa Kamal agolan gida ne, ka san su akwai rawar kai. Gida na hannunka. Duk yadda ka dama dole a sha ko ba a so." Dariya aka sake yi inda Kamal da Yaya su ka ce basu yarda da wannan muƙami da Abba Habibu ya bawa Taj ba. A wannan halin Hamdi da Mubina su ka dawo. Taj ya ja Kamal su ka koma nasa ɗakin. Ahmad kuma ya mayar da Mubina da Hamdi hotel. Yayinda Alh. Hayatu ya cigaba da nasa shirin daga nan. Ƴan uwansa maza ya kira ya sanar da su shawarar da ya yanke. Su ka yi na'am da farinciki. Yaya Babba ya shiga gaba su ka haɗu da ƴan uwan Hajiya, wani abokin Alh. Hayatu da ƴan uwa shaƙiƙan sauran matan mutum ɗaiɗai sai gidan Kawun Mubina. Shi ma kafin zuwan nasu ya riga ya faɗawa duk wanda ya kamata. Ana idar da sallar la'asar wanda ya yi daidai da magrib a birnin Jeddah aka ɗaura auren a masallacin unguwa. Asibitin gabaɗaya ya kaure da murna. Ma'aikatansu waɗanda su ka san Kamal da Yaya su ma duka sun taya su murna sosai. RAYUWA DA GIƁI 40 ƘARSHE Batul Mamman💖 Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN A can hotel Mubina ba ƙaramar takura ta shiga ba. Aure dai an ɗaura amma kamar yadda ta ce babu kowa nata sai dangin miji. Duk sai ta koma abar tausayi. Yaya Kubra ta lura da haka sai su ka yi magana da Yaya Hajiyayye, aka kama mata ɗaki daban domin kwana biyun da su ka yi ɗakunan da su ka kama na group ne masu gado hurhuɗu. "Hamdiyya ki koma wajenta ki tayata zama. Idan kuna buƙatar wani abu ki mana magana. Na san ba za ta sake da mu ba yanzu kuma sai a hankali." Hamdi tayi murmushi harda rufe fuska da tafukan hannu "nima dama kunyar taku nake ji har yanzu." Yaya Kubra ta harareta da wasa "Ehhh lallai, wallahi ki ka sake cewa kina jin kunyarmu sai na yi mi ki handsfree a gaban Alhaji." "Tsegumta min mana likita. Me ki ka gani? Tajo ya yi ajiya ko? Oh ni uwar babana. Aure ko wata biyu ba a yi ba. Dama na san za a rina. Taj ko kaɗan bai yi kama da salihai ba. Hararar da take yiwa Hamdi komawa tayi kan Yaya Hajiyayye. "Ke fa daɗina da ke sakin zance wallahi. Don Allah kina yi kina tauna magana kafin ki furzar. Me ya kawo batun salihanci tsakanin mata da miji banda abin ki?" "Raini ya jima da shiga tsakaninmu dama Kubra. Gara ki kwaye min baya a gaban...." ta waiga babu Hamdi babu dalilinta. Can ta hangota ta kusa ƙure korido tana ta zuba sauri kamar ta kifa. Ita da Kubra su ka haɗa ido su ka kwashe da dariya. Faɗan da ba su ƙarasa ba kenan. * Ƙarfe tara da rabi Umma ta shiga ɗakin su Mubina. Hamdi kaɗai ta samu ta kashingiɗe akan abin sallah. Umman na shiga ta tashi zaune. Umma tayi murmushi "ƙanwar Ango ina amaryar yayanki?" "Tana banɗaki" ta amsa mata ita ma tana murmushin. "Ai gara tayi wank..." Caraf Mubina ta katse Umma daga cikin toilet ɗin da rawar murya. Tsoro muraran ya bayyana a tare da ita. "Ba wanka nake yi ba. Alwala zan yi na fito." "Ai ba laifi ki ka yi ba Mubina. Ki yi wankan ki shirya a nutse Alhaji ya ce ni da Hajiyayye mu raka ki asibitin." "Na'am? Asibiti kuma" Ta buɗe ƙofar ta fito a firgice. Idanunta zuru-zuru sai ɓare-ɓare take yi. Mubina akwai ruɗewa sai a lokacin hakan ya bayyana. Hamdi ta kalli Mubina sai taji wani tausayinta ya tsirga mata. Shi fa aure kwarjini gare shi na daban. Gashi dai da ƙafarta ta taho ƙasar amma yau ɗaya duk ta sauya saboda alhini. Umma zama tayi akan gado ta yafito Mubina da hannu. "Mene ne amfanin aure idan mace bata kasance tare da mijinta ba Mubina? Asibitin da kansu su ka ce sun yarje miki zama tare da shi tunda ke likita ce sannan sabon aure." "Umma ni dai don Allah" sai kawai ta fashe da kuka. Umma ta tashi tsam ta rungume ta. "Kamal ɗin ne ba kya so?" Mubina ta girgiza kai. "Aure a irin wannan yanayin ko? Ba haka aka saba ba na sani, amma faruwarsa a hakan ya sa naku ya zama special." Ba kunya Mubina ta ɓare baki "ni dai Mamana, Umma don Allah wajen Mamana zan tafi." Ɗago kanta Umma tayi ta ce "Tamɓali! Mubina? Shekararki nawa ne?" Mubina ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana kuka tana murmushi lokaci guda. "Na fahimce ki" Umma ta sake yin murmushi "ƙarasa abin da ki ke yi ki kwanta" Ta juya za ta fita Mubina ta kira ta kai a ƙasa saboda nauyinta da take ji. "Umma ba za ku yi fushi ba?" "Haba dai. Mubina ba na jin Kamal zai taɓa samun soyayya irin wadda ki ke yi masa. Kin haɗu da shi a halin ciwo kin so shi. Sannan a lokacin da dukkan wata ƙofa ta ƙulle sai Allah Ya yi amfani da ƙudurinki na biyo shi domin..." muryarta ta karye "ku yi sallama sai Ya kawo mafita. Hamdiyya kina ganin akwai..." ta juya ko sama ko ƙasa babu Hamdi sai kawai ta kama dariya "wannan ƙanwar taki ta san yakamata sosai Mubina. A duk lokacin da take jin ana buƙatar keɓewa cikin magana sai ki ga ta bar wajen da dabara." "Nima na kula Umma." "Idan ku ka rayu tamkar ƴan uwa tare da sauran yaran namu da matar Ahmad haƙiƙa kun gama yi mana komai." "In sha Allahu." "To amarya sai da safe." Umma ta fita fuskarta babu komai sai annashuwa. Mubina kuwa wata ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi ta faɗa kan gado. Yanzu da Umma ba mai fahimta bace kawai sai a wuce da ita asibiti tinƙis-tinƙis. Gobe kuma a dinga zuwa dubiya ana ganinta a ɗakin Kamal. Ai da kunya! 'Kamal' ta maimaita sunan a zuciyarta. Yanzu fa wai ya zama mijinta. Wani juyi tayi na farinciki tana ƙara yiwa Allah godiya. * Hamdi na fita ɗakinsu da Taj ta wuce da niyyar ta ɗauko kayan baccinta ta dawo wajen Mubina. She was just smiling idan ta tuna yadda ta baro Mubinan. Tana ji a jikinta Umma ba za ta matsanta mata ba. Nata key ɗin ta saka ta buɗe ɗakin. Tana shiga taji anyi sama da ita. Ta buɗe baki za ta yi ihu Taj ya sauketa ya jingina bayanta da ƙofar ɗakin. Ya tare mata hanyar wucewa. "Kina yi su Alhaji za su zo kinga sai mu taru mu yi musu bayanin me ya firgita mu." Ta harare shi "abin da ya firgita ni dai." "Da na sani ma a toilet na ɓuya sai kin fi tsorata." Hango irin tsoron da za ta ji tayi ta yi murmushi "da kuwa mai raba ka da yayana sai Allah." "Kinga ki kiyaye ni da zancen yayanki ɗan kalen dangi. Yana can gadon asibiti me zai iya? Taj will do what Taj wants." Ya ƙare magana girarsa ɗaya a sama. Kai ta girgiza "Gobe idan mun je ka maimaita abin da ka ce yanzu in koma gefe in sha kallo." "You are looking for my trouble fa, and I will give it to you har sai kin ce ya isa." Dariya ya bata ta kama ƙugu da hannu guda. "Bring it on." Janyota ya yi su ka nufi 3 sitter ɗin ɗakin su ka zauna. Ta ɗora kanta a ƙirjinsa shi kuma ya sake rungumeta. "Ƴar caras matar Tajuddeen." Ya kira ta affectionately. "Uhmmm." Ta amsa muryarta can ƙasa-ƙasa. Kasancewarsu tare ya saukar mata da nutsuwa fiye da kullum a yau. Jikin Yaya yana ta ƙara kyau. Sai yanzu ta sami damar appreciating zuwa ƙasa mai tsarki a dalilinsa. "Yau ban ce miki ina son ki ba Hamdi na. I love you." "Ni ɗin kake so ko ƴar caras?" Ta tambaye shi bayan ta zauna su na fuskantar juna. "Why do you ask?" Baki ta tura kafin ta ce "Tun ina yarinya ake cewa jiki zan yi idan nayi aure. Wai ƙirar mu ɗaya da ƴaƴan Anti Zinatu." "Ƙira kuma sai ka ce wata mota?" "To dai ance zan yi ƙiba. Kai kuma har wani ƴar caras kake cewa. Kada na fashe nan gaba na daina burge ka." Damuwa sosai yake iya gani tare da ita. Ya yi dariya ya kuma zolayarta. "Ki fashe kamar wata kwalba?" "Happy manaaaa" ta buga ƙafa a ƙasa. He hugged her tightly sannan ya yi magana a hankali. "Ko me za a ce mi ki, ko me ki ka zama a gaba Hamdiyya ki sani cewa Taj is your home. You can be anything as long as Hamdin Abba Habibu ce ina son abata. Hamdi ƴar tsinke" ya fara ƙirge da yatsansa "Hamdi ƴar doguwa, Hamdi ƴar gajera, Hamdi ƴar lukuta, Hamdi mai tumbi, Hamdi shafi mulera..." Yana kaiwa nan wata wawuyar cakuma yaji ta kai masa tana rigima ya kwashe da dariya. "Wai ina faɗa ne don ki san cewa ke nake so ba jikinki ba." Daga nan ya lallaɓa abarsa su ka kwanta. Sai shabiyu saura Hamdi ta farka firgigit kamar an tsunkule ta. "Mubina tana jira na mu kwana tare. Ya Subhanallah." Ta tashi tana neman hijabi. Sai da ta saka tukunna Taj ya ce "to amara ƙirjin biki dawo ki kwanta. Amarya tana wajen Angonta." "Anya kuwa? Ban ga alamun za ta tafi ba." Ta faɗa masa iya abin da ta gani da Umma taje ɗakin. Taj ya soma dariyar mugunta. Hamdi tun tana mamaki har ta koma kusa da shi tana jiran ya faɗa mata me ya kawo dariyar. "Kaza gashin Najeriya" ya ce da ƙyar dariya na cin sa. "Ban gane ba fa." "Yayanki..." dariyar harda ƙwalla. Hamdi ta kama baki "yau ina ganin ikon Allah." Da ƙyar ya saisaita kansa "ana cewa an ɗaura auren nan yayanki ɗan kalen dangi ya sa ni fita neman kaza. Wai bai dace amarya ta zo babu wani abu da zai tuna mata al'adar gida ba." Yana kallonta ya cigaba da cewa "kin dai sanni da faɗin gaskiya ko Hamdi na...to haka na aje kunya a gefe na nuna masa rashin fa'idar nemo kazar nan saboda kada amarya ta fassara shi yana kwance magashiyan." Ya sake yin dariya. "Ba ka da kirki fa" ita ma ta soma dariya don ta hango inda zancen zai dire. "Rawar kai irin ta ango sabon shiga ya ce bai yarda ba. Babe, tun la'asar nake neman kaza don ya ce dole na nemo gashin Najeriya mai ɗan ƙuli-ƙuli da yaji. Kuma bai yarda na tambayi su Bishir ba duk da sun fi ni sanin gari wai kada a raina shi. To cut the story short naji a jikina. Wurin ana layi haka nayi ta zama har na samo." "Shi ne kake yi masa dariya?" Ita ma fa dariyar take yi. "Sai da yasa na dawo na ɗauko masa aron kayana. Ga ciwo ga wahala amma haka ya dage na saka masa shadda harda hula. A table ɗin gefen gadon na jera masa kazar amarci, juice, youghurt da biryani. Kaiiiii, wa zai cirewa Happiness kayan nan? Ko dai in kira shi ne? Ba za su yi daɗin bacci ba." Hamdi dariya, Taj dariya. Sai sun yi kamar sun gama da sun haɗa ido sai a sake daga farko. "Harda turaren angwanci yasa na nemo masa mai mugun tsada ya feshe jikinsa." Hamdi ta goge ƙwallar dariya da yatsa "Ni damuwata akwai fridge a ɗakin?" "Fridge kuma? Akwai." "Yauwa dama don kada kazar ta buga." Su ka sake tuntsirewa da wata dariyar that was just contagious. Da mutum zai shigo ɗakin dole ya taya su. After 1am Taj ya raka Hamdi ƙofar ɗakin Mubina. Ta shiga ta sameta tana sallah. They just smiled at each other sannan Hamdi ta ɗauro alwala ta zo ta tayar a kusa da ita. *** Yau dukkanninsu su ka tafi asibitin domin daga nan za su wuce su shiga jirgin ƙasa zuwa birnin Madina. Hajiya dai ta ce da Abba Habibu babu inda za ta har sai Yaya ta fara tashi da kanta. Anyi-anyi da ita ta tafi saboda akwai kulawa sosai a asibitin amma ta rufe ido ta ce su ƙyaleta. Alhaji ya goya mata baya tunda shi ma ba tafiya zai yi ba. Kamal kuma za a bar masa Abba da amaryarsa. Duk wannan zancen kafin su fito aka gama yinsa. Alhaji ya ce da Mubina idan tafi son fara yin Umrarta a nutse cikin ƴan uwa babu damuwa. Sai kawai ta duƙar da kai. Mama ta fassara masa da cewa ta amince da zaman ne. Kuma hakan yake a zuciyarta. Tun asuba mahaifiyarta ta kira ta su ka yi magana akan yin abin da ya kamata. Wasu lokutan mutum ya kan ajiye kunya da tsammanin al'ada ya yi abin da ya dace da halin da yake ciki. Daga ɗakin Yaya su ka rankaya ɗakin Kamal. Ango ya dinga cika yana batsewa. Taj ne kaɗai ya san dawan garin. Ya yi ƙoƙari sosai bai yi dariya ya tona masa asiri ba. Sun fara yi masa sallama a zaton sa harda Mubina a tafiyar sai ya kaɗa baki ya ce, "Mubina matso mu yi sallama, sannan ga kazar ki nan ki tafi da ita." "Innalillahiiii...." ta tattaro numfashi kafin ta dire "wa inna ilaihi raji'un." Ji tayi kamar ya tsomata a cikin ruwan sanyi saboda kunya. Ɗaki ya yi tsit kamar ruwa ya cinye su na wucin gadi. "Ku fita mu tafi. Kamal, Allah Ya ƙara sauƙi." Ahmad ya yi ta maza ya kawo ƙarshen kallon-kallon da ake yi. Ai kamar jira su ke yi su ka fita a layi ko waige babu. Mubina ko motsi ta kasa yi. "Da alama anaesthesia bata sake shi ba har yanzu doctor. Lamarin Happiness sai kin haɗa da haƙuri. " cewar Taj. Kowa ya watse. Babu mutum guda da ya kalli Mubina ko ya yi murmushi ko da ƙasa-ƙasa ne kuwa. Ba su isa ba ne. Duk barkwancin yayyensu sun san Yaya Kubra ko Yaya Hajiyayye ce ba za ta ɗaga mata ƙafa ba. Sun san wasan da ya kamata su shiga da wanda bai dace ba. "Ashe haka ka ke Kamal?" Ta faɗi baki buɗe don har yanzu tana mamakin wannan magana. Ya juya mata ƙeya "Me na yi?" "Babu komai." Ta rage murya tana magana a hankali amma yadda zai ji "dama Taj ya ce na lallaɓa ka da sauran allura a jikin ka." Ta sami wuri ta zauna akan kujera ta juya masa baya ita ma. Ɗakin ya koma shiru. Da ya ga babu Sarki sai Allah sai ya sauko. Yana magana abin tausayi. "Jiya ba ki kyauta min ba. I waited." "Shi ne yasa ka bani kunya a gaban ƴan uwanka?" Briefly ya labarta mata yadda jiya ta kasance a wajensa. Mubina ta dinga girgiza kai ita a dole ya bata tausayi. Ya gane sarai abin nata harda tsokana. "Kar ki yi min dariya." That was it! Magiyarsa tamkar zuga ta koma a gareta. Dariya ta kufce mata ta kare baki ta yi. Kamal samun kansa ya yi da zuba mata idanu kamar haɗuwar farko. She looked so cute tana wannan dariyar. Ya ji zuciyarsa tana neman cika masa ƙirji saboda farincikin da ya samu daga abin da take yi yanzu. Da ta gama dariyar tashi tayi ta dudduba ɗakin bata ga alamun nama ba. "Ka saka min rai kuma ni ban ga kazar ba." "Laifin naki kenan." "Me kuma ya na yi?" "Na zama abin tsokana dai da alama. To ki kwantar da hankalin ki domin kema kin shiga one chance yadda na shiga jiya." Ƴar dariyar da take yi ta daina babu shiri ta dawo kujerar gefen gadon ta zauna. Kamal ya sosa ƙeya. "Ba na faɗa miki sai da na sa Happy ya canja min kaya ba?" "Yesss" "Kaya dai har sai da su Alhaji su ka shigo yi min sai da safe su ka ganni da su, na kasa cirewa. Shi da Abba Habibu ne su ka cire min. It took more than 10 minutes saboda su na tsoron fama min ɗinki." "Ya Rahman" Mubina kanta sai da taji kunya. "Da su ka gama ne Alhaji ya ce sai na biya ladan wahalar da jikin girma. A gabana su ka cinye naman nan. Harda cewa ranar da za ki tare zai biya mu." Ya ɗan cije baki "Saboda Allah me zai sa ya yi min zancen tariya? Don na ɗan yi kwalliya shikenan sai a fassara ni? Ko ni na kawo fitina duniya ai dole in jira nayi healing ko?" "Ni dai na shiga uku." "Wallahi kin shiga. Kazar amarci surukan ki maza sun cinye. An barwa ƴaƴa tarihi." Kamar za ta yi kuka ta ce "to ni yanzu yaya zan yi?" Kamal ya ware hannuwansa yana kallon cikin idanunta. "You can start by giving me that first halal hug." Bata san abin da zai ce ba kenan da ba za ta zauna a kurkusa yadda kunyarsa za ta kama ta da yawa haka ba. "Idan ka warke kayi da kan ka." Ta faɗa a ciki-ciki. "Mubina" ya tsare ta da ido. "Na'am." "Now please." Magiya ce ko umarni? Ita dai bata gane ba. Abin da ta fahimta kawai shi ne zuciyarta tana muradin yin abin da mamallakinta yake so. She gave him the warmest hug. Zuciya da gangan jiki su ka sami kyakkyawar nutsuwa. A lokacin da Kamal yake tunanin Mubina ta gama biyansa da alkhairi, she brushed his lips lightly da nata. Tsokana ta so yi, reshe sai ya juye da mujiya. Happiness got his happiness and he wasn't willing to let go easily. Kamal da Mubina Allah Ya ƙara lafiya da zaman lafiya! *** Wani irin kuka Inna Luba ta fasa daga ɗaki mai firgitarwa. Malam da yake ririta ta tun jin Yaya ta tafi Saudiyya ya fito daga banɗaki da zariyar wando a hannu. "Luba me ya faru? Mutuwa aka yi?" Inna Luba kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa. Amarya duk jarabarta jikinta ya ɗan yi sanyi. Shi yasa bata faɗi magana mara daɗi ba da ta fito. Banda haka da tuni ta fara domin tsufa bai rage mata komai ba. Da ƙyar Malam ya samu cikin kuka Inna Luba ta faɗa masa wayar da aka kira ta daga Kano. "Surukar Abdulƙadir ce ta kira yanzu wai za ta yi min jaje." "Waye kuma Abdulƙadir?" "Ƙanin Habibu mana." "To, sata aka yi ko gobara wani cikinsu ya yi?" Amarya ta tambaya tana jin haushin tsurkun da ta fito kuma da alama labarin ba zai ƙayatar da ita ba. "Yarinyar nan ce..." Malam ya dafa bango jiki na rawa. Sai ka rantse bai taɓa nunawa Yaya ƙyama ba. Ya marairaice sosai gwanin ban tausayi. "Lubabatu bar zancen nan haka. Zuciyata ba za ta iya ɗaukar zancen mara daɗi akan gudan jini na ba." "Wannan kam dole sai ka ji. Wai anyi mata aiki an cire mata ƙoda guda ɗaya an dasawa wani yaro." Da wani irin zafin nama Malam ya zabura kamar ba tsohon da yake taku da ƙyar ba saboda ciwon ƙafa. "Me???" Yadda taji ta maimaita. Dama su kan gaisa a waya da ita a matsayin surukai. Ashe duk gargaɗin ds Abdulƙadir ya yiwa matar tasa akan ɓoye zancen sai da ta sanarwa ƴan gidansu kaf. Ita kuwa Mamansu da bata san ɓoye zancen ake yi ba ta kira Inna Luba domin ta jajanta mata. Jinjin ta bayar da ƙoda an dasawa wani ɗan balarabe a Makka. "Jar uba! Kin ga kira Ɗandaudun nan ki haɗa mu kawai. " Baba Malam ya nuna kansa yana jijjiga jiki "Ni za a ha'inta? Ɗiyar tawa za a feɗe daga zuwa ibada? Dama can ban yarda yana da kuɗin kai Jinjin Saudiyya ba. Matsiyaci mai tafiyar mata. Ina yi masa kallon wanda ko ƙuda ba zai iya kashewa ba ashe ja'irin ƙodar ɗiyata zai sayar. Allah Ya isa Habibu!" To Inna Luba dai babu bakin kare Abba Habibu domin kuwa bata san gaskiyar me yake faruwa ba. Ana haka gida ya kaure da tsine-tsine da zagin bawan Allah Abba Habibu sai ga wani ɗan saurayi cikin jikokin Amarya. Inna Luba ta miƙa masa wayarta ko zama bai yi ba. "Ya'u maza lalubo min lambar Sajida ka kira." Ya'u ya yi abin da ta ce ba tare da tambayar komai ba duk da mamakin da ya cika masa zuciya. Kiran na shiga ya miƙa mata wayar sai dai kafin ta ankara Malam ya karɓe ya manna a kunne yana masifa. "Maza-maza ki yiwa ubaki waya ki ce ya kira ni yanzun nan." "Baba Malam me a ka faɗa muku?" Sajida ta fahimci ba lafiya ba "don Allah ka tsaya nayi maka bayani." "Ƴal ƙwal uba har ki na da bayanin da za ki mani? Me ya hana ki neman mu kafin yanzu tunda da alama kin san komi" ya yi ƙwafa "wato kun haɗa kai da baban ku za a kawo muku kuɗin jini ku wanki biyar ku tsoma biyar, ni da na san zafin haihuwarta kuma a barni da kukan rashin ɗiyata. To wallahi ba ku isa ba. Nemo shi ki ce masa lallai a mayar mata da ƙodarta." Sajida ta sake kwantar da murya "Baba Malam ka yi haƙuri. Ba abin da ka ke tunani bane. Yaya taimako tayi da ceton rai." "Da ƙodarta? Ke Sajada, kada ki raina min wayau mana don kawai kin ga ina rayuwa a ƙauye. Tun Kaka da Kakanni ban taɓa jin an cire sassan jikin wani an dasawa wani ba. Zancen nan bai yi kama da wanda hankali zai ɗauka ba." Haƙurin ta sake bashi ya ji haushi ya surfa mata zagi daidai wa daida. Ya ce kuma ta saka a ranta cewa Yaya na dawowa zai maka Abba Habibu a kotu a raba auren su. Jin haka Inna Luba ta karɓe wayarta ta ce da Sajida tayi maza ta nemi Abbansu. "Idan bai kira ni ba to nima zan bi shawarar Malam." Ta katse kiran. Hankalin Sajida ya tashi sosai. Ranar kwanan su Taj biyu da tafiya Madina ta kira ta sanar da Abba Habibu yadda su ka yi da su Baba Malam. Murnar sauƙin da su Yaya ke samu sai ta koma ciki domin kuwa nasa hankalin ba ƙaramin tashi yayi ba. Alh. Hayatu ya yi Allah wadai da halin surutun wasu mutanen. "Wani lokacin sai ka yi tunanin akwai masu ɗokin zama ƴan yaɗa labari mara daɗi. Suna rawar jikin zama farkon waɗanda za a ji mummunan labari daga bakinsu. Banda haka wane irin rashin nazari ne zai sa a kira tsohuwa a tayar mata da hankali irin haka?" "Yanzu ta ina zan fara? Ta yaya zan yi musu bayanin da za su fahimta?" Abba Habibu cikin damuwa, Yaya kuma tana ta kuka. Tausayinsu ya kama Hajiya, musamman da ta tuna rayuwar ɗanta ce ta janyo mu su. Jikin kowa yayi sanyi. Sun kira su Inna Luba amma ko kusa Baba Malam bai bata wayar ba. Shi kaɗai ya dinga faɗa kai ka rantse tunda Yaya ta taso bai taɓa juya mata baya ba. Maganganunsa duka ana ji domin faɗa yake yi iya ƙarfinsa. Har cewa Yaya ya yi ta tabbatar ta karɓi takardarta kafin su dawo. Hajiya dai sai da tayi kuka mai isarta. Yanayin ɗakin ya koma wani abu daban a tsukin lokacin. Ana haka sai ga kiran tawagar Madina. Dama kullum sai sun kira an gaisa. Hajiya na karɓa ta ce a bawa Yaya Kubra wayar. Sai da ta fara gargaɗinta akan kada maganar da za su yi ta fita musamman zuwa kunnen Hamdi sannan ta tambayeta shawara. "Ke ce likita Kubra. Me ya kamata mu yi? Ta ina za mu ɓullo mu su ta yadda za su fahimci girman taimakon da Yaya tayi har ma su yaba mata?" "Hajiya turo min numbar da zan same su." "Bari na karɓa sai na turo miki. Amma don Allah ki kiyaye." Kallo su ka bita da shi har ta tura numbar sannan tace musu su duka babu mai ilimin da zai iya yin bayanin da su Inna ba za su ɗauka son zuciya ba. "Mu bata dama tunda ɓangaren aikinta ne. Na san Kubra, za ta yi abin da ya dace." * Gidan Baba Malam fa babu lafiya. Inna Luba kwanciya tayi zazzaɓi ya rufe ta yayinda maƙota su ke ta zaraf-zaraftu a ƙofar gidan ana ta zuwa jaje da ganin ƙwaf. Amarya ce ta fice fit ta fesawa waɗanda ta san za su tayata yaɗawa. Kafin wani lokaci gari ya ɗauka. Abin ne da mamaki ace mutum ya bayar da ƙoda sukutum kuma yana nan da rai. Waya na ringing Inna Luba ta tashi da sauri ta ɗauka. Yaya Kubra ta gaishe ta a ladabce sannan ta buƙaci Innar ta haɗa ta da matashi ko matashiya idan akwai a kusa. "Yarinya ko me za ki ce ki faɗa min kawai." "Don Allah ki yi min wannan alfarmar Inna. Ki taimaka." Ba don ta so ba ta fito tsakar gidan. Cikin sa'a tayi kiciɓis da Ya'u. Har yanzu bai koma gidansu ba tunda ya san me yake faruwa. Rigimar kakarsa Amarya da Inna Luba ba sabgarsa bace. Yana ɗasawa da kowa a gidan. "Inna kina buƙatar wani abu ne?" Ya matso kusa da ita da sauri. "Gashi" ta bashi wayar ta koma cikin ɗakinta. Ya'u ya saka waya a kunne ya ce "hyalo?" Kai tsaye Yaya Kubra ta bijiro masa da buƙatarta bayan ta gabatar da kanta kuma taji daga ɓangarensa. Yadda take magana kaɗai ya yi masa kwarjini don jikinsa har rawa yake wajen amsa mata. "Aiki ka ke yi ko karatu?" "Aiki ne. Ina koyarwa a wata pravet a nan kusa da mu." "Masha Allah. Mal. Ya'u nawa ne albashin ka tsakani da Allah?" "Et fife (8,500) ne." Ya amsa mata cikin basarwa. Ba ya so tayi tunanin shi ɗin cima zaune ne. "To zan baka dubu ashirin a yau in sha Allah idan buƙata ta ta biya." Gigicewa yayi sosai yana ta doka murmushi ba ji ba gani. Ta gama da shi da tunaninsa kaf. "Me ki ke so nayi?" "So nake ka samo min waya mai yin bidiyo call na whatsapp." "Shike nan?" Ya tambayeta da mamaki. "Ƙwarai kuwa. Idan an samo ka bani lambar in saka data domin wayar za ta iya ɗaukar lokaci." Ya'u baki har kunne don farinciki ya ce "wayata tana yi sai dai bani da data sannan wassof ɗin ma ya yi ispiya." "Wannan layin?" "Eh." Cikin minti biyar Ya'u yaga 25G. Gani yayi abin kamar wani mafarki da zai iya tashi kodayaushe. Shi da ya saba saka datar naira ɗari zuwa ɗari biyu sa'i da lokaci ina zai kai wannan? Ya yi updating komai da sauri sannan da kansa ya kira. Dr. Kubra Hayatu tayi masa wani irin kwarjini. Ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta sannan ya kaiwa Inna Luba wayar. Kafin a fara jawabi Baba Malam da Amarya suma sun hallara. Ya'u yana gefe Yaya Kubra ta zauna tayi mu su gwari-gwari game da ciwon Kamal, zuwan Yaya asibitin, bayar da ƙodar da ma zuwan Abba Habibu. Inna Luba tayi kuka babu adadi ba. Muryarta duk ta dashe. "Yanzu ƴar nan kina da tabbacin rayuwar yarinyar nan ba za ta tawaya ba?" "In sha Allahu babu abin da zai biyo baya sai tarin alkhairi. Addu'a da kulawa kawai take buƙata." Baba Malam kuwa cewa ya yi "Idan gudan ƙodar ta sami matsala fa?" Yaya Kubra ta jinjina tambayar don ta san da wuya a rasa mai yi. "Komai na Allah ne Baba. Addu'a da kulawa kaɗai za ku iya yiwa Yaya. Sanin gobe kuma sai Allah maɗaukakin Sarki. Abu guda nayi imani da shi, Allah ba Ya taɓa barin wanda Ya fawwala Masa al'amuransa ya taɓe. Mu kyautatawa Allah zato, in sha Allahu babu nadama a cikin sadaukarwar Yaya." "Allah Ya sa ƴar nan. Allah Ya dawo mana da ita lafiya." Yaya Kubra ta tausayawa Inna Luba matuƙa. "Inna na san Yaya a ƙalla za ta yi wata a ƙasar nan kafin ta sami sahalewar shiga jirgi daga hukumar lafiya. Saboda haka ki fara haɗa jaka. Zan yi magana da ƙannena ma za mu ji yadda za ayi a samar mi ki passport da visa." "Allahu Akbar. Ni ɗin?" Ta kalli Baba Malam "wai Saudiyya zan tafi. Ikon Allah. Allah Buwayi gagara misali. Ni dai Lubabatun ko wata ƴar nan?" Yaya Kubra ta sha dariya kafin su gama waya. Tana kuma ankare da fuskar Baba Malam. Yaƙe kawai yake yi. Alhaji ta kira ta tura masa lambar Ya'u ta ce ya kira ya haɗa su Yaya da Innarta. Haka kuwa aka yi. Sun ji daɗin ganin juna. An dai sha koke-koke da addu'o'i. Har Kamal sai da su ka gaisa da shi. Ya yi musu godiya sosai da alƙawarin zuwa har gida idan ya dawo in sha Allah. *** Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah SWT. Yau kimanin sati uku kenan da yiwa Kamal dashen ƙoda. Sauƙi ya samu sosai domin duka an sallamo su daga asibiti. Likitoci dai sun hana su barin ƙasar domin suna buƙatar kulawa sosai har na tsahon wata biyu zuwa uku. "Ina ganin gara na kama mana gida kawai. Zaman hotel ba zai yiwu ba" Alh. Ya ce da matansa suna zaune duka su huɗun tare da shi a ɗakin hotel. Inna ta ce "Hakan ma shawara ce, amma kafin nan ya kamata a san masu zama don a kama ɗan daidai. Sauran yaran nan su zo su koma gida haka nan." "Kamar kin shiga zuciyata akan raguwar nan. Mata sun baro mazajensu sun tare a asibiti ayi ta hayaniya kullum" cewar Mama. "Kamawa fa tayi." Umma mai ɗan sauƙin ta ce tana murmushi. "Tunda dai suna samun lafiya mu kanmu sai mu ragu. Ko kuwa Alhaji?" "Wannan shawarar ku ce. Ni dai ƙafata-ƙafar Habibu da iyalinsa." Ya gyara zama yana sauraron su. Hajiya aka bawa dama. Ta zauna ta gama lissafinta ƴan uwanta su ka yi na'am. Umma za a bari tare da Bishir. Sai kuma Taj da Hamdi saboda zamanta kusa da Yaya yana da mahimmanci. Mubina ma babu inda za ta je. Sauran kuwa Alhaji ya ce da kansa zai faɗa musu su shirya nan da kwana uku su za su tafi. Sannan akwai wanda zai nema a samar mu su gida. "Dr. Hadifi ya ce yana son ganin mu ni da Habibu. Idan mun dawo zan yi magana da su." * Bakin Abba Habibu ya kasa rufuwa bayan fitar Dr. Hadifi daga ofishinsa inda ya barsu su yi shawara kafin a bashi amsar batun da ya zo da shi. "Habibu ba ce wani abu mana." Abba Habibu ya girgiza kai "wallahi bani da abin cewa. Ni dai abin ya yi min girma. Anya zan karɓa kuwa?" Alh. Hayatu ya ce "me zai hana? Roƙa kayi?" Ya yi gyaran murya "ba ka ganin kamar wata dama ce daga Allah SWT?" "Har na isa a bani abu makamancin wannan?" "Kada ka yi saɓo mana. Kowane bawa da arziƙinsa Allah Ya ke halittarsa. Kuma rabon mutum baya taɓa wuce shi. Ko dai ka je da ƙafarka ko ya biyo ka har inda kake." "Haka ne. Allah Ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi." "Amin amma don Allah ka yi shawara mai kyau." Abba Habibu ya yi murmushi "Zan yi istihara in Allah Ya yarda." * Zuwa yamma kowa yaji abin alkhairin da ya sami Abba Habibu. Dr. Hadifi ya yi masa kyautar gidan abinci sukutum a nan cikin birnin Jeddah. Tsohon ginin na Kawunsa ne ya saya ashe zai yi masa amfani. Abinnda Yaya tayi ya burge shi matuƙa, sai kuma ya tuna a hirarsu Abba Habibu ya ce ya taɓa sana'ar abinci a nan. A hoto ya nuna musu gidan. Kusan komai na kayan aiki akwai, gyaran da za a yi kaɗan ne sai kayan abinci da za a tanada. Yayi masa alƙawarin yi musu igama shi da Yaya da duka ƴaƴansu. Sannan zai yi masa gyare gyare da kuma zubin kayan abinci na farko kafin ciniki ya kankama. "Ku buɗe Nigerian restaurant wanda yake serving abincin ku na gargajiya." Ita ce shawarar da ya bashi. Kamar haɗin baki duka shawararzu guda. Ya karɓa. To dai ya karɓa ɗin ranar da ragowar masu tafiya za su wuce. Ba su tafi ba sai da su ka je aka ga waje aka sanya albarka. A gida ma ƴan uwa da su Zee anata murna da rawar jiki. "Ki bar tunanin tafiya dai kina da aure. A daure a koyi larabci saboda idan na dawo zai yiwu na daina jin Hausa." "To nima ai ba yanzu za ayi biki ba sai na kai level 4." Daga cikin ɗaki Anti Zinatu ta ɗago murya "to uwar iya. Ke da yanzu ki ke jarabawar gama sakandire kike kiran level 4 saboda sallamamme ne ya aure ki? To bari iyayen naki su dawo naji ko da yawunsu ki ke wannan saɓon mai girma. In baki yi wasa ba wallahi ranar asabar zan ce da Baballen ya zo ku tafi." Hankalin Zee tashi yayi tana neman yin kuka. Halifa kuwa dariya harda ƙyaƙyatawa. *** Godiya da kyautatawar da Ahmad ya yi wa Zahra ba a cewa komai. He truly appreciated kulawar da ta bawa Mami duk da irin zaman da su ka yi a baya. Da ya fito daga wajen Mamin ne ya yi mata zancen Salwa. "Babanta ne ya damu wai naje naga gidanta." "Hakan ne ya kamata dama. Ba fa a canjawa tuwo suna." "Ina ki ka baro amala da fufu? Ko duk ba ƴan uwan juna bane?" Tayi dariya "ba zan yi musu da kai ba. Don Allah ka ɗauki matsayinka na babba ka wakilce kowa ka je ka ganta. Babu mamaki ma kaga ta sauya. Aure ai ba wasan yara bane." "Allah ko? Shekararki nawa ne a ciki tuna min." "Lokaci ɗaya mu ka yi da kai." Ta zolaye shi. * Da yamma Ahmad ya kira Salwa ba don ya so ba. Ita kuwa da azama ta ɗauka don ta fidda ran sake ji daga gare shi. Gashi tana jin kunyar zuwa gidansa. Alh. Usaini har gorin dangi yayi mata. Bata yi shawara da kowa ba ta kira Anti Zabba'u. Ai kuwa ranar taga tashin hankali. Irin haukan da su ka yi a gidan Ahmad su ka kwatanta a nan. Alh. Usaini ya zo ya gani ya ci musu mutumci la'ada waje daga su har ita. Banda Mami ta jawo musu ai da yanzu dangi sai sum ture na uwa da uba. Kai ba don abin da tayi ba hatta iyalin Alh. Hayatu sai sun fitar da ita kunya. Purewater ta ɗauko guda ɗaya ta sako akan plate ta zo ta ajiye a gaban Ahmad. Ya bi ta da kallo ita da ruwan ya watsar. "Ɗauke abin ki ba ruwa na zo sha ba." Kunyar taji ta ce "Ko na fita na siyo maka mai sanyi? Ko zoɓo?" "Zauna." Zaman tayi tana godiya ga Allah da bai nemi hakan ba don ko sisi bata ajiye ba. Sadakinta ma ta nema ta rasa a cikin gidan. Ta san wanda ya ɗauka amma a yanzu tsoron tada maganar take yi. Ahmad ya sami damar ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. Abin tsoro. Auren da bai fi wata guda ba duk ta ƙare tayi baƙi sai idanu a cikin loko kamar mujiya da haƙora gayau. Falon da ta ajiye shi babba ne irin wanda kowacce amarya za ta yi farinciki da mallakarsa. Fitilu na alfarma, POP ceiling da dukkan wani abu da zai sa ace gida ya haɗu akwai shi. Abin da babu shi ne funiture da electronics. Kuma da alama har cikin ɗakuna da kitchen haka abin yake. Shima a yanzu akan tabarma yake zaune. Ɗakin kwananta ma tabarmar ce. A cikin ɗakin Alh. Usaini kuma katifar maigadi ya ɗauko bayan mahaifinsa ya kira maigadin ya ce ya bar aikin gidan. "Salwa wannan rayuwar ce ashe take jiranki shi yasa ki ka kasa kwantar da hankalinki akan rashin samun biyan buƙatar zuciyarki ko?" Ta ina za ta fara faɗa masa tayi nadama amma a lokaci irin wannan da bata da amfani? Yanzu ta gane cewa idan so cuta ne da gaske haƙuri magani ne. Da ta haƙura da Taj da tuni Mami ma bata gamu da hatsarin nan ba. Everything would have been fine. Rayuwar gidan Alh. Usaini babu daɗi ko kaɗan. Har yanzu bata gabansa, hakan bai dame ta ba kamar yadda ta zame masa wajen huce haushi idan ya fita bai samo komai ba. Mahaifinsa bai barshi da komai ba sai gidan nan albarkacin auren da ya yi. Duk inda yake ajiya a banki ya sa an rufe masa da dogon gargaɗi akan kada ya kuskura ya tada maganar. "Na san irin wadaƙar da kayi min da dukiyata. Idan zan bi kayana na tabbata baka da kuɗin biyana saboda haka magana ta mutu a tsakaninmu. Duk ranar da ka dawo mutum ni kuma nayi maka alƙawarin dawo maka da komai naka. Idan ba haka ba kuwa sai dai ka jira gado in na riga ka." Yanzu rayuwarsa ta koma bibiyar abokai da tsofaffin yaransa yana maula. Wataran a dace wataran kuma a wulaƙanta shi. Da ya gaji ne ma ya goranta mata rashin gara da kayan ɗaki. Ita kuma saboda ɗanyen kai ta kira Anti Zabba'u. Ranar anyi sa'a ƙanwarsa ta zaga ta bayan idon iyayensu ta aiko masa da kaji da jallof ɗin shinkafa ta gaske. Kafin ya dawo daga wajen abokinsa sun cinye tas. Ita kanta Salwa bata ko ɗanɗana ba. Tana ta magiyar kar su taɓa aka rasa mai sauraronta ma. Ɗan uwa aka ce rabin jiki. Ahmad ya tausaya mata sosai. Kayan ɗaki da electronics babu abin da bai tanadar mata ba amma ta watsa masa ƙasa a ido. Suna zaune ya danne fushinsa yana ta yi mata nasiha tana ta kuks sai ga Alh. Usaini. Takalman namiji kawai ya gani ya yi jifa da ledar hannunsa ya zare belt ya afka musu. Salwa na ganin shi ta tashi ta tsaya a gaban Ahmad ta bubbuɗe hannuwa da ƙafafu ta kare shi. Ai kuwa belt ta sauka a jikinta ta gantsare don azaba. Ya sake ɗagawa karo na biyu Ahmad ya miƙe. Kwarjini da cikar mutumtakarsa su ka sanya Alh. Usaini yin laƙwas kamar dafaffen alayyahu. Ahmad ya riƙe belt ɗin tare da hannunsa ya nuna masa Salwa. "Duk abin da za ka yi, musamman wanda ya shafi mu'amala da mutane kaji tsoron Allah. Da kai da ita da gurɓatacciyar rayuwarku ku ka haɗu amma hakan ba yana nufin da ita za ku ƙare har ƙarshen rayuwa ba in kun so." Ficewa yayi ko waige babu. A waje yaci karo da ledar da Alh. Usaini ya yar. Taliya ce leda ɗaya sau mai, maggi da kayan miya na naira ɗari biyu. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Yanzu Salwa ake ciyarwa a haka? Lallai kowa yaƙi sharar masallaci zai yi ta kasuwa. Ya koma gida cike da damuwa. Ya kira Abban Salwa akan maganar kayan ɗaki ya ce ya rabu da ita. Darasi yake so ta koya a cikin auren nan. Hujjojin da ya bashi duka ya gamsu da su. Duk da haka washegari ya tura ƴar ƙurƙura gidan shaƙare da kayan abinci. "Idan da kuɗi a wayarka don Allah ka bani aro na kira Yaya Ahmad nayi masa godiya." Tsaki ya banka mata ya tashi ya fita da sauri ya bi bayan mai ƙurƙurar nan da gudu. Sai da ya kusa ƙarshen layi ya tsaya. Yana faman haki ya ce ya taimaka masa da numbar wayar wanda ya aiko shi. Mutumin ya karanto masa ya kwafa. Da numfashinsa ya daidaita ya kira shi. "Dama godiya na kira nayi maka." "Ku dai ku ji tsoron Allah daga kai har Salwa. Rayuwar da kuke ciki Allah Ya azurta masoyanku da fin ƙarfinta. Cikin minti guda za a iya canja komai ma rayuwarku amma Allah bai bayar da iko ba. Hakan kaɗai ya isa ya zame muku izina. Allah Ya kyauta." Tunawa yayi da wani kalamin da yaji daga bakin Abban Salwa wanda shi kuma Baban Alh. Usaini ne ya faɗa masa a lokacin da ya nemi shawararsa game da makomar rayuwar yaran nasu. "Yunwa, ƙishi da rashin kayan more rayuwa zai sa su yi laushi harma ka ga nadama nan ba da jimawa ba a tare da su. Biyewa wannan ba ƙaramin ganganci bane. Yunwa ta ishi kowane shege darasi. Yanzun nan za ka ga mutum ya shiga taitayinsa. To amma fa ƙoshi shi kuma yana fito da ɗan iska cikin mutane. Da zarar tumbi ya ɗauka sai kowane rashin daraja ya biyo baya indai mutum ba nagari bane. Shin Alhaji ba ka ganin yadda almajirai su ke rashin mutumci a unguwa idan abinci ya wadace su? Wani fa a ƙofar gidanka zai zubar da abinci ya ce ka bashi gaya ko babu nama." Abban Salwa ya gyaɗa kai "wannan gaskiya ne." "Ina son Usaini amma nafi son gyaruwarsa. Idan mu ka yi saurin karaya akan su to ka sani komawarsu gidan jiya abu ne mai sauƙi. Irinsu bayan addu'a da nasiha dole a bari su gane cewa kyautatawa ce daga Allah privileges ɗin da su ke samu ba wai dolensu bane don sun isa. Suna buƙatar duniya tayi musu atishawar ƴan tsaki!" Abu ne mai wuya iyaye su iya ɗauke kai idan ƴaƴansu su ka shiga irin wannan yanayin to amma fa wani lokacin dole a tauna tsakuwa don aya taji tsoro. *** "Zancen Port Harcout naji tana yi a waya wallahi. Don Allah kayi wani abu kafin ta ƙarasa shiga duniya mu shiga uku." Iyaa ke wannan maganar da Baba Maje tana kuka sosai. Sababbin tsare-tsare Baba Maje ya kawo cikin gidan bayan fitowar Ummi daga police station. An karɓe babbar wayarta sannan ba a barinta ta fita ko ƙofar gida. Ƙawayenta tun daga soro ake sallamarsu. Dangi kuma aka sami abin so. Kowa ya buɗe baki a gidan biki ko suna zancenta ake yi ana aibata halinta. Isassu ma har gidasu ke zuwa su faɗi maganganu son ran su. Yarinya a cikin gidansu ta zama mujiya. Tsangwama ta ko'ina fuskantarta take yi. Watarana Iyaa ta fita sai tayi mantuwa. Ta dawo za ta wuce ɗakinta sai taji Ummin tana waya tana faɗawa wanda su ke magana ya saya mata ticket ɗin luxurious bus za ta fito nan da kwana huɗu. Iyaa ta sulale ta fice bata bari ta san da zuwanta ba. Sai dare ta sami Baba Maje ta faɗa masa. "Ummi tamkar ba jinin mu ba. Yarinya sai azabar taurin kai da son zuciya. Duk abin da yake faruwa bata saduda ba" Tana kuka tayi maganar. "Kada ki yi furucin da zai kai ki ga nadama akan Ummi. Ni dai na fahimci hanyoyin da muka ɓullo ba za su haifi ɗa mai ido ba. Ina kuma tsoron ace jini na ta shiga duniya." "To yanzu meye abin yi?" "Aure zan yi mata." "Da wa? A dangin mu wa za ka tursasa ya bari ɗansa ya aureta?" "Kofur Ɗanliti zai auri Ummi" Baba Maje ya faɗi da wani sense of relief. Iyaa tayi shiru kafin daga bisani ta ce "haka ne." "Ko kina da wata shawarar? Irin wannan auren ba shi mu ke yi mata sha'awa ba tsakani da Allah." Magana su ke yi ƙasa-ƙasa cikin alhini gwanin ban tausayi. Iyaa ta numfasa "yanzu za ayi ta aibata auren ana yamaɗiɗi da mu a cikin dangi da unguwa idan aka ga mijin da ta aura. Wasu ma su ce Allah Ya ƙara pi." "Sai mu toshe kunnuwanmu tunda ba a canjawa tuwo suna. Mune dai iyayen Ummi duk inda za a je a dawo." "Amma kana ganin za ta zauna? Mutum irin Kofur ɗinnan yana da abin riƙe mata sama da guda?" Shima kansa Baba Maje ba wai son zaɓin nasa yake yi ɗari bisa ɗari ba. Da babu ne dai gara babu daɗi. "Haka za mu haƙura don sau dubu gara ace abinci ne bata da shi a gidan miji da dai ta shiga duniya. Indai da rai da lafiya ba zan bari yunwa ta kama ta ba alfarmar Annabi SAW." "Wahala za ta ƙaru a kan ka. Ba gara mu nemi wata dabarar ba?" "Ummi bata jin magana kema kin sani. Kuma wannan shawarar da na yanke ba rashin so bane ya janyo. Ban san yaya lahira take ba amma a iya abin da Allah Ya hore min in ji a duniya game da iyalina, sai nake ganin ko aljanna na samu ba zan ji daɗinta ba idan wani cikinku bai riskeni ba a can. Ina tausayin makomar ƴata idan ba ta yiwa kanta karatun ta nutsu ba." Kawai sai ya soma hawaye. Kusa da shi Iyaa ta koma su ka riƙe hannu suna kuka mai ratsa zuciya. "Bawa baya sanin matsayin ibadarsa sai ya koma ga Allah. Kuma muna yi ne cikin kyautata zato da cikar yaƙini to amma bamu san baɗini ba. Yaya kike ji za ta kasance ace duka gidana babu wanda ya dace balle ya ceci sauran? Ai ance ana bawa salihan bayi ceto ko? Shi yasa na damu sosai." "Kafin ma a kai ga lahira ba ka ganin kamar iyalin Habibu sun ja baya da mu? Ka duba fa hatta aikin da aka yiwa Jinjin sai Baballe ne ya ji a wajen Zinatu." "Kai anya kuwa? Kada mu ɗauki haƙƙinsu." Baba Maje ya faɗi duk da yafi yarda da zancenta. A sanyaye ta ce "nima bani da tabbas, hasashe ne kawai duba da abubuwan da su ka faru. Ka san Allah da Siyama ce ta auri yaron da ya fito daga irin gidan nan namu sai na sa an sako min ita. Zan ji tsoron kada Ummi ta cutar da ita." "Kamar kin shiga zuciyata. Ina ta tunanin ko dai in sa ya sauwaƙe mata. Ƙila sun kasa faɗa mana ne saboda kawaici." "Allah Yasa bai taɓa musu ƴa ba. Ka san yaran yanzu da mugun rashin haƙuri." "Zan tuntuɓe shi. Tunda auren dama ba na soyayya bane. Zumunci mu ka so ƙullawa kuma da alama ba zai yiwu ba." Wani abu Ummi taji ya wuce mata mai ɗaci. Ta juya a hankali ta koma ɗakinsu. Ɗazu ta ga fitar Iyaa sai ta zargi ko ta ji wayar ds tayi. Shi ne ta biyo ta da Babansu ya dawo. Jikinta ɓari ya dinga yi har ta isa ta faɗa kan gado. Da yake zuciyar ta jima babu tunanin komai sama da son kai, hassada da sharholiyar duniya, sai ta kasa kuka. Ta kuma rasa addu'ar da ya dace tayi. Haushin kanta kawai take ji da takaicin jin wayarta da Iyaa tayi. * Kofur Ɗanliti har gida ya zo neman auren Ummi bayan fitowarta da kwana ɗaya. Ta zauna ta sille shi da rashin albarka iri-iri. Baba Maje sai ya bashi haƙuri ba don komai ba kuwa shi ne yadda yake gudun me zai je ya dawo. Ummi idanunta a buɗe suke. Kada tayi wa Ɗanliti abin da auren zai zo ya mutu da wuri. To amma da alama zai iya riƙonta duk botsarewarta. Haka dai yake gani amma bashi da tabbas. Saboda haka bayan shawararsu da Iyaa, sai ya kira shi su ka yi magana. "Me yasa kake son auren Ummi duk da ka san wani abu cikin halayenta?" Ɗanliti ya yi murmushi da confidence "ina sonta ne Baba." "Me yasa kake son mace irinta?" "Haɗi daga Allah. Kuma da naji laifinta sai na tuna da tawa samartakar." Gyara zama ya yi domin jindaɗin abin da zai faɗa. "Baba ni fa tsohon ɗan daba ne." Kallon Baba Maje yayi yana jiran ganin tsoro ko firgici sai yaga babu ko ɗaya. Neman ƙarin bayani kaɗai yake iya gani. Ɗanliti sai ya yi masa tun kafin ya tambaya. "Nayi dabanci da shaye-shaye sannan na taɓa tsibbu." Baba Maje yaji hankalinsa ya tashi amma kuma a yanzu dai bashi da wani zaɓi. "Abubuwa ne da na san za ka sami labarinsu idan ka tashi bincike a kaina shi yasa nake faɗa maka. Na riga na tuba tuntuni ina aiki kamar yadda ka sani." Wata zuciyar tana ƙwanƙwasarsa akan ya fasa yayinda wata take tuna masa da me zai iya faruwa idan Ummi ta shiga uwa duniya. "Na baka amanarta. Don Allah idan ka ga abin yafi ƙarfinka ka dawo da ita gida. Bana son a kai ƙadamin da za ta gudu domin yanzu ma iƙirarin da take kenan." Yanayinsa ya nuna tsantsar damuwarsa "ba na son zama abin nuni da kwantace ace ƴata ta shiga duniya." "Ba za ta shiga ba da yardar Allah. In Allah Ya so sai kayi alfahari da bani ita." Da daddare a ranar ya faɗa mata shirinsa a kanta bata ce komai ba. Abin ya bashi mamaki sosai. Haka dai yana ta tsoron kada a wayi gari ta gudu kafin auren amma yaji shiru. A fuska da baɗini bata son auren amma ta rasa gane me yasa ta kasa kataɓus. Auren tubabben ɗan tsubba zata yi bata sani ba. Surkulle da siddabaru babu wanda bai iya ba, kuma babu wanda bai shirya yi ba a kanta domin ya samu ta zauna dashi. Ko bayan zuwansa na farko ba wai haƙura ya yi ba, shiri ya tafi sakewa. Ƴan uwan Baba Maje da ya neme su akan bikin sun yi murna ƙwarai. Ashe kowa na tsoron kada ya roƙi alfarmar haɗata da nasa ɗan saboda mugun halinta. A ranar da ya kamata ta gudu, a ranar aka shafa fatiha tsakaninta da Kofur Ɗanliti. *** BAYAN WATA UKU Taj da Kamal sun duƙufa aikin gyara ko ace jeren sabon gidan Abba Habibu da Yaya. Hawa na uku kuma na ƙarshe a ginin gidan abincin da aka bashi ya mayar gida. Ko sisi basu bari ya kashe cikin kuɗin da Dr. Hadifi ya ba shi ba. Iyalin Alh. Hayatu musamman Kamal su ne suka yi komai. An sallamo su daga asibiti jiki ya yi kyau sosai. Duk da haka Taj ya hana shi ayyukan ƙarfi. Shi da Abba su ke ta kai komo. Abba Habibu da Alh. Hayatu kuma sun fita ana ƙarasa cike-ciken takardun shaidar mallaka da sanya hannun hukumomin da su ka dace. A can gidan da Alh. Hayatu ya kama kuma Inna Luba da Baba Malam (Alhaji ne ya biya masa) sun iso kwana biyu da su ka wuce. Su Amma da Yaya Babba ma duk sun zo amma sun wuce Madina. Sai an gama gyare-gyaren gida da restaurant gabaɗaya za su rankaya dukkaninsu su tafi gida. Su Abba Habibu za su koma su kimtsa a tsanake sannan su koma a fara sana'a. Hamdi da Mubina sun biyo su amma sun fita saya musu abinci. Da su ka dawo da ledoji niƙi-niƙi masu sauke kaya duk sun tafi tare da Abba. Babu kowa sai mazajensu. Ɓata fuska Hamdi tayi suna shiga falon ta zube ledojin hannunta. "Happiness kaga rigima ko? Don Allah ban ce su zauna in siyo abincin ba? Yanzu gashi nan ta dawo tana wani ɓata rai." Kamal ya tashi cikin nutsuwa don har yanzu baya yarda ya saki jiki kamar da. "Angel me ya sami ƙanwata ne?" Mubina ta kalle shi ta mayar da dubanta ga Hamdi wadda abin mamaki ta fashe musu da kuka. "Kun gama da ɗakunan?" Mubina ta tambayi Kamal. "Eh amma me ya same ta?" Shi da Taj duk sun shiga damuwa. Taj ya koma kusa da ita yana son ɗago mata kai taƙi yarda. Mubina ta nuna hanyar ɗakunan da ido, Kamal ya fahimta sai ya tashi ya bi bayanta. Suna shigewa ciki Hamdi ta faɗa kan Taj ta sake dasa kukanta daga farko. "Don Allah ki yi min bayani mana. Me na yi miki?" Cikin kuka ta labarta masa "naje sayan ice cream wai sai da aka zo kaina mutumin ya ce babu chocolate." Mamaki ya kama Taj "shi ne kike kuka? Yaushe ma ki ka fara son chocolate flavour ɗin?" "Yau shi nake so." Tashi ya yi "bari na fita na nemo miki I am sure ba za a rasa. "Ba zai zama irin nasu ba. Ni shi nake so." Taj yaga abin na gaske ne sai ya koma lallaɓata. "Ko in yi miki? Mine will taste even better." "Na su nake so" ta tura baki. "Ahhh to gaskiya Mubina ta zo ta duba min ke. Alamu sun nuna rigimar nan ba nan kusa za ki daina ta ba." Ya rungumeta yana dariya. Ture shi tayi "ni lafiyata ƙalau kawai ka samo min chocolate ice cream." "In ki ka ce nima na zama cream ɗin ai zama zan yi maman babyn Taj." Ya dinga kashe mata ido. Kunya taji ta rufe ido tana dariya. "Auuuu. Kin ma sani kenan. Tun yaushe?" Leɓenta ta taune tana murmushi "a hanya Mubina ta sa mu ka tsaya a clinic." Rungume juna su ka yi Hamdi tana tunanu. Yanzu haihuwa za ta yi ta zama maman wani? Kuma idan an ɗaga baby a ce na Taj ɗinta ne. Lallai Allah ne mai juya al'amura yadda ya so. Katse mata tunani ya yi "zo mu ci abinci." Ta zauna ya ce "mun kusa komawa gida na sami ƴancin dafa miki abin da ranki yake so." "A baki za ka bani." "An gama." A cinyarsa ya ɗorata. Rabi cin abinci rabi rarrashi da kalamai masu daɗi. * Murnar ƙaruwar da za su samu su ka gama yi sannan Kamal ya langaɓe kai ya ce "Doctor zo ki gani ban warke ba har yanzu?" Tayi dariya "Sai nan da wata uku." "Come on Angel. Kada fa ki fara ɗaukin haƙƙina. Ni dai gaskiya so nake ki tare." "Yanzu ba tare muke ba?" "Tariyar gaske nake nufi. Ni ma so nake ki fara rigimar ice cream." "Sai dai hot cream." "Wasa ma ki ka mayar da maganar ko? Do you even love me Angel?" Mubina ta koma gabansa ta durƙusa a gabansa ta kwantar da kanta a cinyarsa sannan ta sanya hannuwanta ta zagaye shi. "Har ka fara kokonton son da nake maka?" "I ....I am sorry." Ya shafa fuskarta "na fiye rashin haƙuri ko?" "No, ni ce dai na fiye tsoro. I just don't want to take any chances." "Ke ce likitan, dole nayi biyayya. Allah Ya kai damo ga harawa dai kawai." Dariya tayi "In ce amin kuwa? Wannan addu'a kamar ana yi min tanadin cin zali." "Meye wani cin zali? Ai kawai ki ce addu'ar mugunta nayi miki." "Ni dai ban ce ba" "Ni na ce" Sun ɗauki lokaci suna zolayar juna da nunawa juna soyayya kafin yunwa ta hana su sukuni. Ya tashi zai je falo ɗauko mu su nasu abincin Mubina ta ce ya yi haƙuri domin kuwa bai kamata ya je inda ƙannensa su ke ba a wannan lokacin. "Kema dai kin fiye assumptions. Ina gidan ai babu abin da zai faru." Mubina ta ce "do you want to bet?" "Happy fa ba kunya gare shi ba. Na haƙura." Ya koma ya zauna yana yamutsa fuska. Sai da Mubina ta gama yi masa dariya sannan ta tuna masa da za su iya kiran su a waya. Taj ɗan duniya sai cewa yayi wai Kamal ya so yiwa Mubina horon yunwa ne, if not me ya hana shi fitowa? "Mu da har muna tunanin rufo muku ƙofa on our way out." "Ni ne fa Happy, na san ka farin sani. Mayar da maganar kaina kake son yi?" Mubina da Hamdi dariya su ka dinga yi musu kawai. *** Sati biyu ya rage bikin Zee wanda aka sanya wata shida bayan komawar su Abba Habibu Saudiyya. Sajida a lokacin watanta guda da haihuwar Ihsan mai sunan surukarta. Gidan Abba Habibu ya sha gyara amma ba mai yawa ba tunda yanzu babu mai zama. A zuwan su na farko Abba Habibu ya nunawa Baba Maje rashin jindaɗinsa da ya tayar da maganar raba auren nasu. Aka tambayi Zee ko tana son rabuwar ta ce a'a. Su Yaya sun nuna musu cewa zumunci yanzu aka fara in sha Allahu. Har gidan Ummi ma sun je. Babu alamun yunwa a tare da ita amma fa ba sai an faɗa ba fuskarta ta nuna bata jindaɗin rayuwar auren. Duk masifarta dole ta sanyawa zuciyarta haƙuri domin kishiyoyinta sun dama ta sun shanye. Uwargidan ma ƴar sara suka ce kafin aure. Ta biyun kuwa ƴar damfara ce ta buga misali. Da su ka shigo hannun Kofur Ɗanliti zance ya sha bamban. To ga Ummi ma ta zo hannu. Jiki magayi! Da za su koma da Zee da Halifa aka tafi. Abba Habibu ya gayyato Ƴar Ficika da wasu cikin yaransa masu igama su ka koma tare. Nan fa sana'a ta kankama babu kama hannun yaro. Ta ƙarfin cin tuwo su ka canja akalar rayuwarsu daga ƴan daudu abin ƙyama zuwa maza masu sana'ar abinci. Sai ga Ƴar ficika ya sami mata, wata ƴar dattijuwar takari. Mata ta zage ana ta sana'a da ita maimakon yawon unguwa unguwa neman abin yi. Cikin watanni kacal rayuwarsu ta sauya gabaɗaya. Duka kuma albarkacin sadaukarwar da Yaya tayi wadda bata taɓa tunanin wani mahaluƙi zai saka mata a kai ba. * Dinner ta ƴan boko, ƴan gayu kuma masu kuɗi Kamal ya shiryawa Zee. Bai yarda ko sulai biyar wani ya saka masa ba. Taj ya ce zai ɗauki nauyin abinci amma yaƙi. Zama ya yi aka yi lissafi ya cake wa Happy Taj kuɗinsu. Ango Sadiq wato Baballe kuma ya sha gargaɗi da jan kunne akan ya riƙe amanar ƙanwarsa. Abin na Kamal dai harda ƴar barazana. Yaya saka shi tayi a gaba saboda ɓarin kuɗin yayi yawa. "Kamal don Allah ka saurarawa kanka haka nan. Wallahi domin Allah na baka ƙodar nan. Kana saka ni jin nauyinka da na su Hajiya. Ɗawainiya da kashe kuɗin ya yi yawa." "Yaya da ke ki ka haifeni za ki ce kyautatawar da nake muku da ƙannena ta yi yawa?" Yaya tayi shiru. "Yaya da kin san yadda ɗan Adam yake ji idan ya hango ƙarshen rayuwarsa kuma babu hanyar gudu da baki ga wauta ta ba. Ga ciwo ga tashin hankalin sanin bani da wata mafita." Idanunsa su ka yi jawur amma bai bari ƙwalla ta zubo ba "ga kuɗi, ga dangi amma babu mai ceto. Yaya, a wannan lokacin ban dinga tuna komai ba sai ranar da kowa zai juyawa masoyinsa baya saboda tsananin tashin hankali. Duk wanda Allah bai taimaka ba a lokacin to dole ya cire rai da samun kowane irin taimako." muryarsa ta soma rawa "na hangowa kaina rayuwar barzahu da tashin hankalin da mara rabo zai riski kansa... bani da tabbacin tsallakewa. Komai ya zo gab sai Allah Ya kawo ki. Yaya babu tunanin taki makomar da ta iyalinki ki ka kwanta aka cire taki ƙodar domin na sake shan iskar duniya. Domin iyayena su share hawayensu..." ya miƙe tsaye "ban isa na biya ki ba amma kuma ba zan taɓa gajiya da yi miki hidima ba in sha Allahu. Kin isa, kin cancanta. Don Allah kada ki sake nuna rashin jindaɗin ki idan nayi wani abu." Ƙwallarta ta goge tayi masa murmushi "idan da ni na haifeka zan karɓi duk abin da ka kawo min cikin farinciki amma duk da haka zan ce maka ka dinga yi saisa-saisa saboda kaima ka kusa zama baban wasu. Haihuwa ba a yi mata tanadin gobe ko jibi sai ta baka mamaki. Sayen pampas kaɗai ya ishe ka ka gane ba ka da wayo" ta ƙare maganar tana dariya. "Ki yi min addu'a kawai, Allah Ya ƙara buɗa min. Tanadi kuma in sha Allahu zan kiyaye shawararki." "Allah Ya yi maka albarka Kamal banban ɗan Jinjin" "Abu Khadija za ki ce." Ya sunkuyar da kai yana susar ƙeya. Tare su ka yi dariya sai ga Abba Hayatu nan. "Agolan gidana me ka ke yi a nan ka zo ka saka min mata kuka?" "Sirrin uwa da ɗa ne Abba." "Nima yanzu mu ka gama namu sirrin da Taj babban ɗana." Kamal ya ce "Sirikinka dai. Mijin ƙanwata." Yaya da Abba Habibu dariya su ka yi. Kamal ya fita ya shiga mota su ka tafi gida da Taj da yake gidajensu babu nisa da juna. Mubina tana gida laulayi ya make ta amma ta gama shiri Hamdi kuma ciki ya tsufa sosai. Haihuwa ko yau ko gobe. * Kukan Hamdi na huɗu kenan yau saboda Taj ya ce ba za ta je dinner ba. Da ya shigo kallon juna su ka yi kowa ya ɗauke kai. Yana fitowa daga wanka da gangan ya leƙo falo. "Taso ki fito min da kaya." "Suna kan gado." "Turare fa? Wanne zan saka?" Ta sake kawar da kai "Na fesa a jikin kayan" "Body spray fa?" "Akwai akan dressing mirror." Ta san jan magana ne kawai tunda abubuwa ne da yake yiwa kansa. Ya koma ya shirya cikin ankon su na shadda shi da su Kamal. A gabanta ya tsaya ya cika mata hanci da ƙamshi mai daɗi. "Menene ne kuma?" Ta ce da muryar kuka. "My goodbye kiss." Da kumburarrun idanunta ta harare shi "na ajiye a ƙofar gida." "Wannan kuma ba ki isa ba. Ki min kawai na tafi." "You are looking for my trouble." Ta tura baki tana jan hanci. "Yep." "Wai me nayi maka ne?" "Kin kasa kallona saboda kina fushi ki ce nayi kyau." Satar kallonsa tayi ta ce "kayi kyau." "Ko ke fa. To tashi ki shirya mu tafi." Maganar a bazata ta shiga kunnuwanta. Ta tashi da ƙarfinta ta rungumo shi tana dariya. "Da gaske kake?" "Idan naƙuda ta taho ki tabbatar kin riƙeta tunda rigima ta sa ba ki son zama a gida." Da dariya Hamdi ta ce "ni fa ba bikin ne ya dame ni ba. Ƴan matan da za su ji ka burgesu nake son na hana samun dama. Ka sanni da kishi." Taj ya tuntsire da dariya. Ya zauna ya ce mata nan da minti shabiyar idan bata fito ba zai tafi. Da sauri ta dinga komai. Ta fito a minti ashirin da biyu. Taj yana zaune yana waya. Hannunta ya riƙe su ka fita daga gidan tare. * Biki yayi biki domin ya sami halartar mutane da dama cikin ƴan uwa da abokan arziƙi. Ƴan uwan Yaya da ƴaƴansu sun zo daga Batsari tare da Inna Luba. Ya'u ya zama na hannun daman Yaya Kubra domin har ta mayar da shi makaranta. Amma da su Anisa harda Hajjo su ma sun zo. Ƴar ficika da matarsa ba a barsu a baya ba. Haka dangin Alh. Hayatu da na matansa na kurkusa duk sun zo. Ahmad ya taho da Zahra sannan ya ce Salwa lallai sai ta zo saboda shi bai ga amfanin ƙauracewa mutane ba. Idan ana haɗuwa ko yaya yau da gobe za a iya yafe mata. To ashe Ummi ma da kishiyoyinta harda maigidan Kofar Ɗanliti su ma sun taho. Hamdi ta tako da ƙyar take ɗaga ƙafa taji kamar da mutane a gefenta. Ta juya hagu ta haɗa ido da Salwa gayauna. A ɓangaren dama kuma Ummi yangaura. Kowacce ta lalace ta fita hayyacinta. Su ukun suna yiwa juna kallon kallo su ka tsinkayi muryar Taj daga bakin ƙofar hall ɗin. "Ke da na ce ki jira ni a mota in fara sama miki wurin zama? Na zo na ɗauke ki?" Salwa da Ummi su ka bi shi da kallo. Ya fi Taj ɗin da su ka sani cika, kyau da ɗaukar ido. Aure ya karɓe shi kamar yadda ya karɓi matarsa. Ko me su ka ji a ransu ba su furta ba. "Ka zo ka tayani tafiya dai." Taho wa ya yi Hamdi ta saƙale hannu a waist ɗinsa saboda support su ka dinga takawa tare har su ka ɓacewa ganinsu. Sai su ka sake kallon juna, kowacce ta buga tsaki. Za su fara cacar baki sai Ummi ta kula Alh. Usaini yana tahowa. Yadda Salwa ta fige shi har ya fi ta. Wata muguwar dariya ce ta suɓuce mata bata sani ba. Kamar daga sama taji muryar Kofur. "Ummi ban hana ki dariya irin wannan ba?" A gefensa hagu da dama kishiyoyinta ne. "Wai, sannu fa." Salwa ta ce sannan ta rama dariyar da tayi mata. * A falon gidan Abba Habibu, shi ne da Alh. Hayatu su ke hira irin tasu ta manya. Hirar yawanci ta iyalansu ce da abubuwan da su ka shafi rayuwar yau da gobe. Can dai Alh. Hayatu ya ce "ni kuwa Habibu akwai abin da nake sha'awar ci amma na kasa faɗawa iyalina tunda ban saba ba." "To ya aka yi ka san kana so tunda baka ci?" "Ka san jikoki akwai kyauta. A baki aka zo aka bani rannan da aka yi. Si ka tayar min da kwaɗayi amma ban isa na nemi ƙari ba kada na zama abin surutu a gidan." Abba Habibu ya miƙe yana dariya "ban yi ritaya ba har yanzu. Ya sunan sa in dafa maka?" "Wainar fulawa" Alh. Hayatu ya faɗa yana wani basarwa don kada Abba Habibu yayi masa dariya. Bai tsira ba kuwa don sai da ya yi masa dariyar sannan ya shiga kitchen. Bayan minti talatin Alh. Hayatu ya ɗora babbar rigarsa a saman kujera wai kada ta ɓaci da manja. Ya zauna a kan kafet yana cin wainar fulawa yana jindaɗi sai ga wayar Kamal sun wai wuce asibiti da Hamdi shi da Mubina da Taj. Iyayensu sun biyo bayansu. Ya kalli plate ɗin ko rabi bai ci ba kamar kada ya tashi don wannan tafi wadda aka yi a gidansa daɗi. Sai da ya ƙara loma guda sannan ya tashi su ka tafi asibitin. Suna shiga Mubina na fito musu da jariri. Abba Habibu ya ce a miƙawa Alh. Hayatu. Yana karɓa sai cewa ya yi "wainar" Abba Habibu ya yi saurin cewa "Wai ina wa?" "Wai ina maigidan nata?" Alh. Ya wayance. "Gamu nan fa Alhaji." Ya juya ashe sun wuce kowa a wurin bai sani ba. Farin kaya mai tonon silili Inna ce ta fara cewa "Mene ne wannan a gaban rigarka Alhaji?" "Ina babbar rigarsa za ki ce" in ji Mama. Hajiya ta ce "Ƙamshin manja nake ji kamar wainar fulawa." Alh. Hayatu da Abba Habibu su ka soma kame kame duka wajen ya kaure da dariya. Basu bar asibitin ba sai da aka fito da Hamdi kowa ya ganta lafiya. Alh. Hayatu ya miƙa mata jaririn da amarya Zee ta ƙanƙame bayan iyaye sun gama saka masa albarka. Ya miƙawa Hamdi bayan ta zauna akan gado. " Hamdi ga Habib Tajuddeen Hayatu. Allah Ya raya shi bisa sunnar Ma'aiki SAW. Allah Ya sa ya yi koyi da kyawawan halayen mai sunansa." "AMIN" kowa ya amsa da farinciki. Abba Habibu da bai taɓa zaton wannan karamcin ba ya rasa me zai ce sai kawai ya dinga murmushi yana godiya ga Allah da Ya nufe shi da ganin wannan rana. Alhamdulillah bata gushe daga bakinsa ba har ya kwanta yana tunanin rayuwar duniya mara tabbas. Ace har ya yi ƙimar da za a yi masa takwara? "Allah na gode Maka. Ya Rabbi Ka ƙara shiriya da albarka ga iyalanmu da mu kan mu. Ka raba mu da bin hanyar taɓewa. Ka dawo da ɓatattun cikin mu hanya madaidaiciya. Amin" HAMDAN KATHIRAN ƊAYYIBAN MUBARAKAN FIHI. Ya Allah Ka yafe min kurakuran da su ke ciki. Ka sa mu amfana da darrusan. AMIN