Search
You have no alerts.

    Wahalar So na Sa’adatu Bello

    Wahalar So na Sa’adatu Bello

    πŸ…ΏοΈ 1

    ……………Da sauri na hango wani saurayi matashi yana saukowa daga matattakalar bene dake cikin wani k`aton gida wanda zai tabbatar maku cewa naira ta kwanta acikin gida.

    Wata dattijuwa naga tana kallon saukowarsa tana murmushi mai k`ayatarwa da alama shekarunta zasu kai sitting(60) Amma fa duk da tsufanta bai hana bayyana kyawunta fitowa ba ga kuma kamaninta nan da wannan matashin saurayin.

    Daga ganinsa dai kaga d`an gata bazai wuce shekara talatin da biyar ba(35yrs) Kai da ka gannsu kasan suna cikin farin ciki.

    Ni kam abunda ya bani mamaki na tsaya na saki baki da hanci ina kallon yanda parlon gidan ya had`u kamar ba’a cikin birnin katsina gidan yake ba.ban gama jin-jina kyawun parlon ba naji muryar saurayin nan ta doki dodon kunne na!

    “Granny me yasa baki tasheni a barci ba?” Ja mashi dogon hancinsa tayi.

    “Kaga Ahmed naga ka kwaso gajiya ne shiyasa na barka ka huta awa nawa kayi a jirgi?” Ya mutsa fuska yayi tare da hugging dinta, Itama sumbatarsa tayi a goshi.

    “Gaskiya ne Granny Spain akwai tafiya.”

    “To yanzu dai muje kayi breakfast wannan shirin dakayi nasan na fita ne.”

    “Yes Granny zan leKa company ne amma ba dadewa zanyi ba. Wai Mami bata fito bane ba?” Ya karashe magana yana kallon part din Mami. Jim! tayi kadan.

    “Damuwar Ahmed kenan yar uwarsa baya son abunda zai taba mashi ita shiyasa har yanzu ya ki yin Aure.bata gama magana a zuciyarta ba taji muryarsa.

    ” Granny ko bata da lafiya ne?”

    “A’a Ahmed kawai tashiga ne tayi wanka don itama nasan zata lek`a office ne.”

    Ajiyar zuciya ya sauke tare da jan kujerar daining ya zauna.gaskiya kowa ya bar gida- gida ya barshi. Kunun gyada ya zuba da kosai wanda kamshinsa ya cika wurin cup din ya daga yakai bakinsa tare da gutsurar kosai din lumshe idanuwansa yayi tare da furta.

    “I really missing u my sweet Mami wannan hidimar nasan don ni kikayi ta.”

    Murmushin jin dadi Granny tayi na jin dadin yanda jikokin nata ke k`aunar junansu.

    (Ahmed Ibrahim Galadima) Shine cikakken sunansa.

    Wayar daya daga ne yasa yayi saurin mikewa yana cewa ” kujirani nan da 20mins zan iso insha Allahu.”kwashe keys d`in motarsa yayi ya kalli part din Mami again.tsaki yayi “mtssss ya furta a hankali ” ban ganta ba zan fita.”

    Granny data maida hankalinta a TV ya kalla, Granny kice ma Mami zan sameta Office an kirani a company zan gana da wasu bak`ine daga pakistan.”

    “To ba komi zan sanar mata adawo lafiya.”

    “Thank u my Granny.”

    Da sauri ya fita ya nufi parking lot ya dauki wata katuwar Mazda wadda 2022 ta fito ni kaina kallon motar na tsayayi kai!masu kud`i na sha’aninsu rivos yayi mai gadi ya wangale masa get ya sulala kan motarsa.

    Dai-dai inda danja ta tsaida su jikake kwatsam!!an bugi bayan motarsa wanda har saida danjar motar ta tsage amma kadan wani mai mashin ne dauke da wata yarinya wadda shekarunta basa wuce 18-19 daga gani mai mashin din dan acab`a ne gaba daya wurin kallon sai ya koma ga wanda zai fito daga motar don ganin wane sakarai ne zai buga mashi mota haka.

    Ganin mace ce bisa mashin din yasa yaji ranshi yayi mummunan baci kowa kallon yanda yayi kan mai mashin din yayi kamar wani zaki suna jiran ganin mai zaiyi masa? Yana isa fisgo yarinyar yayi a bayan mai mashin din………..
    WAHALA SO

    πŸ’πŸ’πŸ’
    πŸ’”πŸ’”
    πŸ’š

    πŸ…ΏοΈ 2

    …………..A fusace ya juya zai wanke mai mashin din da mari, da sauri yarinya ta rike masa hannu itama afusace ta fara magana.

    “Me yayi maka?da zaka sanya hannu ka dake shi?ai abunda ya faru ba da gangan bane ba, asalima kai kayi kok`arin haye mu amma saboda kai wani ne shiyasa zaka ci zarafinsa?”

    Kallon karamar yarinyar yakeyi da mamaki fal aransa shi yaushe ma ya taba tsayawa mace tana gaya mashi magana data minti biyar ba arayuwarsa? Bare wata k`aramar yarinya.”

    Ganin ya tsaya kallonta ne yasa ta fisge hannunta daga rikon dayayi mata takardun dake hannuwanta ta kara gyarawa kamar daga sama yaji muryar yarinyar tana fad`in.

    “Mr” kabamu wuri tunda naga anjaye motar taka daga wurin kuma ga danja ta bada hannu nasan dai baka da tausayin dazaka ba mai mashin din nan kud`in gyara tunda kake niyyar kwashe shi da mari.”

    “Stop!! That nonsens my frnd!!”

    Jikinta ne yakama rawa saboda tsabar tsoro kamar zata saki fitsari a wando dama fa maganar data keyi kawai k`arfin hali ne domin dai daga gani wannan wani ne agarin amma saboda tsabar kasada irin ta ta takeyi masa rashin kunya.kamar a mafarki ta sake jin muryasa yana tambayar.

    “Nawa ne kud`in gyaran mashin din?”

    Amsa ta bashi batare data san menene ya fito bakin ta ba saboda a kidime take ta kosa ya barsu su wuce kada fitsari ya kubce mata.

    “Dubu goma.”

    Dariya taso bashi don ya lura yarinyar ba cikin hayyacinta take ba. Amma fa bata da kunya daga ganinta.kara daure fuska yayi kafin ya juya wurin da driver ya kawo masa wata motar ya janye wannan dama tun kafin ya fito motarsa yayi ma mutumin text da kuma dai-dai inda yake yana zuwa ya ajiye masa wannan sannan kuma ya janye wadda aka buga da mashin d`in.

    Bude motar yayi ya dauko wata jaka ya bude ya zaro rapas na 50k ya dawo wurin da take tsaye ya jefa mata su a fuska!

    “Poor girl kije keda kazamin mai acabarki ku raba tunda naga alama kema neman kud`in kika fito.”

    Gaba daya mutane dake kallon drama da sukeyi suka saki baki ganin wulakancin da yakeyi mata.

    Ita kam gyalenta tasanya ta tare kudin.binshi tayi da kallo yanda ya juya ko ajikinsa ya nufi motarsa ya shiga batare da ya K`ara ko waiwayensu ba.

    Mai mashin din ne ya matso kusa da ita sai lokacin yasamu damar magana.

    “Amma Hajiya kidaina yin wannan kasadar haka, kinga halin masu kudin nan bashi da kyau badon ke ba da bansan irin wulakantar da
    zanyi ba.”

    “Karka damu da alama wannan baisan darajar mutane ba zai samu dai-dai dashi muje ina makara ga kudin gyara mashin dinka.”

    “To shikenan nagode da taimakonki.”

    “Bakomi ka godema Allah.”

    Haka suka karasa har company data ce masa zataje interview anan ya sauketa dama itama naira dari biyu ne kacal gareta zuwa da dawowa da kyar ma ta samesu wurin Auntyn ta. 20k ta mika ma mai mashin din tace yaje yayi gyara sauran kuma Allah ya bashi.

    Godiya yayi mata sosai kafin tasanya sauran a jaka ta sanya kai cikin company wanda gabansa ke dauke da tambarin sunan (A .I .GALADIMA DISTRBUSHIN COMPANY.). Ta karamar kofar get din tashiga tana ta kalle -kalle irin haduwar company wai duk na mutum dayane.Allah ma ya taimaketa da sauran lokaci ba’a fara ba.tambaya tayi aka nuna mata wurin dazata shiga.

    Daga sama wurin da zai gana da bakinsa akan benen ya hangota zata shiga kofar da zata sadaka da office din da akeyin interview din da mamaki yake kara tsayawa yana kallonta tabbas ita ce!! Wani irin murmushi!! yayi na mugunta da sauri ya juya ya dawo kasa har yana sarsarfa akan mattakalar benen……
    WAHALAR SO

    πŸ’πŸ’πŸ’
    πŸ’”πŸ’”
    πŸ’š

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!