WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)
Chapter One
Sai da ƙarfe ɗaya muka shiga kaduna,
kayan kwalliyata na ciro na kuma gyara fuskata,
Na goggoga turaruka a jikina.
Ina nuna ma direba hanya muka isa har gidan,
Horn direba yayi,ina niyyar sanar ma shi ba maigadi ya saurara,
aka wangale get ɗin,
wani wanda ban taɓa gani ba sai a yau,
shi ya buɗe,
ya kuma iso wurin yana tanbayar wurin wa muka zo.
Ni na yi mishi bayani,
haƙuri ya shiga bani kafin ya soma gaishe ni.
Motar ta kunna kai cikin gidan,
Maigadin ya biyo mu da sauri,
na fito ina kallon yanda aka ƙara gyara gidan,
taɓe baki nayi
ƙila sanda zai yi amarya ya yi gyaran.
Direba ya shiga fito min da kayana,
maigadi ya kira Garba me wanki wanda shi na bari kafin tafiyata Lagos.
Kuɗi na ciro babansu laila ya bani
da naje yi mishi sallama,
ya ce ba lallai ina da kudin nan ba, in riƙe za su yi min amfani.
Nayi ma direba alheri na sallame shi,
Maigadi da Garba suka biyo ni da kayana,
Knocking nayi a ƙofar main falon, daga ciki aka bada izinin shigowa,
Takun ƙwas ƙwas da takalmina ke yi
yasa mazauna falon maido hankalinsu inda nake,
Zaune suke a kujerin da suka yi wa falon ƙawanya dukkansu har megidan.
Maigadi da ke bayana
ya tanbayi inda za a ajiye min kayan,
Ƙofar ɗakina na nuna masa,
Zama nayi ɗaya daga cikin kujerun,
kowace da irin kallon da take min,
kafin suka soma min sannu da zuwa,
nayi mamakin canzawar su,
mun gaisa na gaida megidan,
suka bi ni da kallon ita ɗin ce koko wata aka canzo bayan na miƙe zuwa ɗakina.
Key na fiddo cikin hand bag ɗina,
na buɗe dakin
ina cusa kai mamaki ya rufe ni dan ko ina a gyare yake tsaf yana tashin ƙamshi,
Ba alamar an daɗe ba a yi amfani da shi ba.
Jakata na ajiye na cire takalmi,
na koma kofar daki na shigo da jakunkuna na
Basma ce ta shigo abinci ta miƙo min,
na ƙarba tare da godiya cikin wani bala’in mamaki da ya kara rufe ni game da matan na Tahir,
Na dai ajiye nayi alwala nayi sallah,
da na idar na ji cikina yana bukatar abinci,
amma zuciyata bata nutsu in ci wanda aka kawo min ba
dan ni dai ina ta mamakin canjin nasu.
Wani danbun nama da laila ta sanyo min cikin kayana na ci sai na sha ruwa,
canza rigar jikina nayi zuwa wasu riga da wando masu santsi
na koma bisa kujera na miƙe ina latsa wayata.
Tahir ya shigo,
Zaune na tashi ina ƙara gaishe shi ban samu amsawar shi ba illa faɗan da ya lullube ni da shi,
Mutum shi da iyalin sa an nuna masa iyakar shi,
ana ma shi iko da matarsa.
Shiru nayi ina sauraren shi,
zuciya na kawo min wuya,
kamar in ba shi amsa sai na kasa,har ya ƙare
wai kuma sai yana faɗa min ni zan yi girki yau,
komawa nayi na kwanta
Na ce “Gaskiya a gajiye nake ka bar me girki ta kare girkinta in ya zagayo kaina sai in yi”.
Wani kallon mamaki ya kafe ni da shi,
“Saboda me?
“Saboda ba yau zan tare da kai ba”
ba tare da na dube shi ba
na ba shi amsar
wata iska ya furzar me bayyanar da takaici sai ya mike ya nufi hanyar fita,
“Ki tabbatar kin shiga ɗakina kin gyara girkin ba dole bane,
zan zo da take away”.
Daga haka ya fice,
ban ko bi shi da kallo ba dan wani ƙullutun bakin ciki da ya tokare ni,
wannan ita ce marabar da ta dace in samu a wurin mijina, bayan shafe tsawon watanni biyu bana nan.
Na miƙe zan shiga bed room kiran Aunty Kulu ya shigo amaryar kawun Tahir ce wanda ya riƙe shi,
na ɗauka da murmushin karfin hali a fuskata,
ta ce “Mutanen waccan kasar,tun jiya nake neman layin yaki shiga”.
na ce “Ban canza sim ɗin ba Aunty”.
na soma gaisheta,
tayi min fatan Allah yasa an yi karbabbiya.
Na ce “Aunty na ga akwatunana,
an kuma gyara min ɗakina, ƙamshin da naji yana yi na tabbatar da hannunki a gyaran”.
ƴar dariya tayi
“Na zo Kaduna,
ganin Sodangi yana kadunan saboda karatun shi yasa na taho maki da kayanki, gyara kuma ni na ce idan akwai key ya bayar a gyara maki ɗakin,
sai na sa masu aikin gidan malam na nan suka taya ni muka yi gyaran.
“Na kuwa gode Aunty, Allah ya ƙara girma”.
ta ce “Da zan tafi bamu haɗu da Sodangi ba, sai idan Malam zai zo zan ba shi key ya zo maki da shi”.
na ce “To Aunty”
Mun jima muna fira hakan ya mantar da ni damuwar da na shiga daga dawowata.
Ina ɗakina ban fito ba,
sai bayan an yi sallar isha’i sai ga shi ya shigo,
Wai ba zan fito in ci abinci ba?
na ce”Zan fito”
Kowace da ledar ta a gabanta, soyayyar taliya ce da kaza, gamawata sai na miƙe, da niyyar in koma ɗaki,
dakatar da ni ya yi ya ce
“In zauna a yi fira”
suna firarsu ina nazarin maganganunsu, ina kuma ta tambayar kaina ko bayan yin amaryar matan suka samu hadin kai haka, ban dai yarda na sanya masu baki ba.
Goma dai dai nayi masu sai da safe na wuce abuna,key na sanya ma ƙofata, nayi shirin kwanciya na kwanta.
Tunda ta bar wurin hankalinsa ya koma kanta, sai dai ganin idon sauran matan na shi yasa ya ci gaba da zama yana aikin shi a system ɗinshi, duk da ba wani gane aikin yake ba, dan kacokan hankalin sa ya koma kanta.
Basma ta soma tashi,
Halima ce ƙarshe,
ganin shigewar su shima ya miƙe,
har ya ƙare shirin kwanciya ba ummulkhairi ba alamar ta,
wayarshi ya dauko ya lalubi lambarta a rufe ya ji ta, ya yi wurgi da wayar bisa gado,
ya kwanta dafe da goshinsa yana tunanin mafita,
dan zuciyarsa na ba shi shawarar ya share ta kawai ya shiga barcinsa,
Sai dai wata kuma na zuga shi da kwaɗaita masa matar tasa da kewarta da ya yi.
Ya daɗe yana juyi amma barci ya kasa nasarar sace shi zuciyar shi ke azalzalar a samo mata abinda take muradi.
Ganin ba shi da zabi yasa ya mike ,
silifas ya zura
sai ya sauko ƙasa inda ɗakunan matanshi suke,
a hankali yake takawa dan gani yake kamar cikin matan nashi wata za ta fito ta gan shi,
sanin ba wacce yake bi sai dai ki kawo kanki,
amman kuma ya makara dan Basma da Halima mutanen da kishin kwanan da zai yi da ummulkhairi ya hana su barci, musamman ganin yanda ta canza ta waye ta goge kamar wacce ta shekara ƙasar Turai.
A hankali yake ranƙwashin ƙofarta,
gaba dayansu kowace ta leƙo Halima da ke da window ta inda za ta riƙa hango shi ta ɗaga labulan,
Basma kuma ƙofarta ta buɗe kaɗan ta fito.
Tun yana yi a hankali har ya zage yana bugawa,
amma ba alamun za a bude,
cikin matuƙar bacin rai ya juya dan komawa wurinshi,
A sittin Basma ta faɗa dakinta ta rufo ,
sai Halima da ta sha gabansa,
duk da rashin wadataccen haske bai hana shi gane ta ba,
Sun aika ma juna wani bahagon kallo,
dan yasan tsayuwarta nan baya nufin alheri,
yayinda ita kuma wani bakin kishi ya tokare mata kirji.
Zai ratse ta ya wuce ta sha gabansa ta ce
“Lallai wasu matan rako wasu suka yi, ta yamutsa baki.
“Adalci kenan? wace macen ka taba bi dakinta, koko sai ita da yake nata abin na gwal ne”
Murmushin takaici ya yi
“Duk a maganganunki babu karya, wata ko da kanta ta kawo maka sai dai kayi kan dole”.
daga haka ya ture ta daga bake baken da tayi masa a hanya ya wuce.
Wani uban ihu haɗe da kuka ta fasa,
duk wanda ke wurin ya ji sai dai me nauyin barci,
Basma da ke lekensu ta saki labulen tana tsaki,
da itama tayi gigin tunkararsa tare zai gasa masu maganar da za ta hana ta runtsawa,
gara ma Halimar ita kaɗai yake daure wa tsiyar ta,
In ita ce bata san iya abinda zai mata ba.
wata shegiyar kwafa tayi ta sulale bisa gadonta.
Tahir yana wuce Halima saman shi ya hau ya rufe ƙofar, dan yasan wannan bakar maganar da ya yaɓa wa mata bata barinta,
zama kawai yayi ya rasa wane ma irin tunani zai yi.
Ina kwance naji fasa kukan Halima, nasan labarin gizo bai wuce ƙoƙi,sanin zafin kishinta.
Maida kaina kawai nayi na kwantar,
na rufe idona da ƙarfi a fatan da nake barci ya ɗauke ni.
Ina idar da Sallar asuba duk da gajiyar da nake ciki kitchen na shiga,
gudun ƙara wa kaina laifi,
dan abinda na wa Tahir
a daren jiya ban san hukuncin da zai yanke min ba,
ina cikin aikin me masu aiki ta shigo ba Ade bace wata baƙuwar fuska ce a gare ni.
Ita ta kama min bayan ta gaishe ni da girmamawa,
sai da na shirya komai kan dinning,
kafin na wuce ɗakina,
wanka nayi me kyau
na zauna na gyara jikina,
turaruka na musamman da mahaifiyar su laila ta saya mana nayi amfani da su wanda na san Tahir na shaƙa sai ya sukurkuce.
Saƙon ƙamshin da na aika masu yasa su juyowa,
zaune suke matan biyu kan dinning,
sai dai ban san me ya hana su fara ci ba,
kowaccensu kamar dole ta amsa gaisuwar da na haɗesu nayi masu, kamar yadda na yi hasashen zaman nasu ma kamar dolen ce ta sasu yin shi,
Basma na latsa wayarta,
Halima tayi tagumi kawai
fuskarta kamar hadari.
Takun saukowar megidan yasa kowaccen mu gyara zamanta,
kallo ɗaya nayi masa na maida kaina ƙasa na sunkuyar,
dan yadda na ga ya haɗa fuska kamar gobara.
Maimakon ya zauna wurin karyawar,
hanyar fita ya nufa
ban san na shagala
wurin bin bayan shi da kallo ba cike da alhinin wannan cin fuska da ya yi min a gaban kishiyoyi,
sai da naji tashin shewar matan biyu,
wa’anda abinda aka yi min ya yi matukar kayatar da su.
A fakaice na dube su
kafin na maida idona kan kayan abincin zubawa nayi na soma ci kamar bani da wata mas’ala,
alhali ji nake kamar zuciyata za ta fashe,
Basma ta zuba itama ta fara ci,
kammalawa ta sai na miƙe zuwa ɗaki inda nayi ta zubar da hawaye tare da ƙudiri kala kala na yanda zan rama abinda Tahir ya yi min.
Cikin kunci na wuni wanda na lura su kuma ɗanyan ganye suke abinda ban san basma da shi ba dan girman kanta ba ya barinta sakin jiki da kowa.
Megidan dai bai kuma shigowa ba har sai da aka yi sallar isha’i,
Ina ji matan nashi na tanbayar inda ya shiga,
ni kam kokowa nake tayi da zuciyata me cewa in share shi saboda wulaƙancin da ya yi min,
sai kuma me rarrashina da cewa auren kenan
cike yake da ƙalubale,
hakuri shi ne kawai.
Da haka na samu ta rinjayi me min zugar in share shi.
Na fito na karɓi jakar da ya shigo da ita ,
na ratsa saman shi na ajiye ma shi,
sai da na haɗa ma shi ruwan wanka sai na sauko,
ban tsaya inda suke ba
ɗakina na wuce kamar inyi wanka sai dai na miƙe bisa sopa dan wata kasala da naji ta rufe ni.
Hannuna na sa na dafe goshina idanuwana suna lumshe,
Muryar Halima naji a kaina tana shaida min in fito in basu abinci,
da to na amsa mata na tashi zaune ina bin bayanta da kallo,tare da jinjina girman tseguminta,
miƙewa nayi bakina ɗauke da addu’a,
dan faɗuwar gaban da ta
sanyo ni gaba
dan nayi imani ba tsakani da Allah Halima ta shigo ɗakina tana neman in zo in basu abinci sai dan sha’awar ganin wane irin tozarci Tahir zai min yanzu kuma.
Na fito jikina a mace
sun hallara sai megidan ne babu,
wanda kafin in kai ga zama ya soma takowa step ɗin benen,
cikin jallabiya yake me guntun hannu
ƙamshin turarenshi ya cika wurin,
ya zauna na zuba ma shi
sosai ya ci ya dora da jus ɗin da na haɗa masa
wanda na san sosai yake san shi.
Gaban system ɗinshi ya koma ya umurce ni in ɗauko masa phone ɗin sa a daki,
ko da na kawo zama kawai nayi ina danna wayata,
gyaran murya yayi wanda yasa kowaccen mu ƙara shiga nutsuwarta,
“Idan Allah ya kaimu gobe amaryata za ta tare”
Ko da ban sani ba
a tare gabanmu ya faɗi,
dan kallon da kowaccen mu tayi saurin aika masa,
Ba kuma wacce ta furta komai illa Halima da ta yi saurin miƙewa ta wuce zuwa ɗakinta,
Basma ma bata ɓata lokaci ba ta bi bayanta ni nayi saura a wurin,
goma na bugawa kamar jiya na miƙe sai na nufi ɗakina.