Join our WhatsApp Group here
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚
…….Da faɗa ya faramin tare da turkeni kan saina faɗa masa dalilina na jifan Mansoor ɗin da waɗan nan kalaman. Da farko naso dojewa. Amma ganin yanda ya birkicemin a yanayin da bai taɓa ba bamma san na saki layi ba na zayyane masa komai. Tashin hankali na gani sosai a tattare da shi. Ya sake balbaleni da faɗa cikin ruɗani.
“Amma Samraah baki da hankali. Yanzu wannan abin na faruwa da ke tsahon sati biyu amma kika ja bakinki kikai shiru sai yanzune kike faɗa. Shima badan kunyi haka da Mansoor ɗin ba da bamu kamo bakin zaren ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un Samraah baki da wayo, wlhy sam baki da wayo. Dan tabbas bana raba ɗayan biyu mutumin nan ne yasa ake bibiyarki. Dolene ma ya gano kin ɗauki videon nan. Wannan abin shi nake gudu tun farko daman, shiyyasa kullum nake cikin tunanin mafita ashe nima nayi sakaci…”
“Yaya ban gane ba. Wai kana nufin wancan mutumin mai ɗaure gashi Maashi yake komi ma oho masa”.
“Idan bashi ba wanene Samraah. Tabbas dole shine zaisa a iya miki irin wannan bibiyar. Samraah kodai kinyi wani yunƙurine a kansa batare dana sani ba, dan na sanki da shegiyar wautar tsiya”.
“Wlhy Yaya ni babu abinda nayi, kaima kasan kuma bazanyi komai ba sai da saninka. Ka tambayi Mansoor ALLAH ne shaidata shima shaidatane. Daga office bana zuwa ko’ina sai gidan nan. Weekend kuwa islamiyya ce kawai ko Malam Umaru zai tabbatar maka da hakan shima. Toni wanema yunƙuri zanyi tunda kunce nabar komai a hannunku. Wlhy ko video ɗin tunda na adanashi ban sake waiwayarsa ba balle ma na kalla har wani yaji ko ya gani. Hatta da Mansoor ranar yake cemin ALLAH ya kiyaye yana rage abubuwa ya goge video ɗin nan, da ace banda shi a wayata da an samu matsala. Amma dan ALLAH na sake adanashi kada nayi sakaci tunda na sanshi shi da goge-goge a waya na tsiya.”
“Nasan baza’a samu matsala daga gareki ba Samraah. Amma dole mutumin nan yanada cctv camara ai, idan kuma mai yawan bibiyar abubuwane to tabbas anan ya gano shine yasa ake bibiyarki. Ko kuma wani ya ganki. Ina dai zuwa bari na kira Mansoor yazo ya same mu”.
Ban iya cewa da shi komai ba. Sai faɗawa duniyar tunani kawai da nayi. Harya kammala wayar bamma sani ba. Cigaba yay da kai kawonsa alamar haɗa lissafin abubuwa. Cikin abinda baifi mintuna talatin ba sai ga Mansoor yazo. Kasancewar lokacin sallar isha’i yayi suka tafi massalaci. Sai da aka idar suka dawo ina ɗakin Yaya ɗin dai har sannan. Mansoor na gaida daga haka suka shiga tattaunawa danni gaba ɗaya zuciyata bata tare da gangar jikina. Sai da Mansoor yaymin tambayar ni da waye muka je restroom ɗin a ranar? Dan tambayace da ya kamata ma ace sun min tun a waccan ranar amma basu yi ba. Saida na sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci sannan na sanar musu ɗaya daga cikin securitys ɗin da suka bada tsaro a ranar ce. Na sake maimaita musu yanda mukayi. Sun sake tambayata bayan ita ban haɗu da kowa ba? Sannan itama ɗin sanda ta tafi yin wayar bata dawo bane nemana?.
“Eh gaskiya ni dai banga ta dawo ba, kasancewar ma hankalina ya tafi akan abinda ya faru ban sake bi takanta ba. Dan haka ban san miya hanata sake komawa ba. Kuma ni gaskiya bana jin nama sake ganinta har aka tashi”.
Kallon juna Yaya da Mansoor sukai. Cikin ƙarfin hali da nuna tashin hankali Yaya Musaddiq ya ce, “Anya kuwa security ɗin nan bata koma ba a lokacin. Idan lissafina yayi dai-dai, ta koma domin su fito tare kamar yanda ta mata alƙawari, maybe bata sameta ba ta shiga nemanta, ko kuma ta sameta a lokacin da take bude-buɗen ƙofar ko ma ɗaukar video ɗin. Dan inba haka ba babu yanda za’ai tai ɓatan dabo gareta. Hasashe na biyu lokacin da take faɗa maka ko wani ya jiku. Cikin biyun nan dole ɗaya ya tabbata, kuma duk inda zancen ya fito to tabbas an samu Maash an fargar da shi komai shiyyasa yasa ake bibiyarta.”
Cikin jinjina kai Mansoor ya ce, “Tabbas hasashen ka zai iya zama gaskiya Yaya. Amma ni a wannan gaɓar ma sai hankalina yaso rabuwa biyu akan wasu dalilai. Maash bawai ƙaramin mutum bane. Kana ganin ya aikata wannan kisan ya kuma san ya aikata har wata ace ta ɗaukesa a hoto mai motsi ya sani kuma ya zauna sakaci. Duk da yanda muke tunani abinda masu hannu da shuni ɗin nan suka tsana a rayuwarsu shine su binne wani laifinsu amma ya zama yana a hannun waninsu ko waninsu ya sani. Zakaga suna gaggawa wajen ganin sun daƙile komai. Idan lissafina yayi dai-dai wata fa kusan ɗaya kenan da faruwar komai. Kana ganin zai zaman ɓata lokacine akan wani bibiyar Samraah bayan yana da hanyoyi masu yawa dama zai karɓi video ɗin a hannunta batare da wata gargada ba. Karfa ka manta har hira yazo anyi da shi kuma itace tai da shi, randa aka saki hirar kuma ƙura ta tashi sosai da kace nace ɗin mutane harda masu cewa akwai alaƙa tsakaninta da shi, nasan dai kasan komai ba sai na sake maka bayani ba. Na kawo wannan hujjojin ne saboda bana son mu shagala da yawa a kan shine wanda kuma ke son ƙulla tsiyar na gefe. Kuyi haƙuri MD kansa na cikin zargina. Dan na jima da fahimtar yana son Samraah na hauka, randa kuma ta kai musu kayan saka bikin mu ya tabbatar ma da kowa hakan. Sai ƴar uwarku Baby. Tana sona matuƙa, wasu dalilai ne suke dakufeta, naji a majiya kai ƙarfi cewar tai alƙawarin sai tabi tako wace hanya domin ganin auren nan namu bai yiwu ba, dan tana da babban plan akan haka akwai kuma mai bata ƙwarin gwiwa ta bayan fage. Saboda yima kanta alwashin indai itama bazata sameni ba sai dai su rasa su duka. Da farko na ɗauki zancen shirme kawai irin nata na ƴan shaye-shaye, sai dai wannan abin na yanzu ya fara haskomin da gaske zata iya komai fa. Dan haka musa hankalinmu jikinmu domin tabbatar da ko wanene”
“Shaye-shaye kuma? Wai babyn ce ke shaye-shaye ko wa?” na faɗa ina kafe Mansoor da idanu. Murmushi kawai ya mun da faɗin, “Hum Samraah kenan, ke dai ALLAH ya shirya mana zuri’a kawai”.
Yaya na kalla a firgice, sai naga shi babu alamar mamakin zancen akan fuskarsa. Kasa haƙuri nayi sai da na ce, “Yaya kenan kaima kasan tana Shaye-shayen?”.
Sai da ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya furta, “Na sani Samraah. Na kumayi iya yina na ganin ta daina amma hakan ya gagara. Na lurar da Abba amma ya nuna sharri nake mata. Tun daga nan na tattarasu na watsar”.
Zancen ya matuƙar girgizani gaskiya. Kamar yanda sosai maganar Mansoor tayi tasiri garemu ita game da MD da Baby da zasu iya sakawa a bibiyeni. Dan duk abinda ya faɗa gaskiya ne. Ni komai ma sai naji ya sake susuce min. Amma duk da haka Yaya yace bazamuyi sakaci da duka ɓangarorin uku ba. Zamu saka ido za kuma ku ɗauki matakin daya dace da kowanne. Dan haka zamu kai report wa yan sanda akan ana bibiyata, amma bazamuyi batun video ba fa, zamu bar ƴan sanda suyi aikinsu, idan ma Maash ɗinne da ga baya idan fito da videon ta kama sai muyi hakan. Nanma mun gamsu, kun kuma bashi goyen baya, duk da ni dai naso ace tun yanzu muka fidda video ma wa yan sanda. Amma ban san dalilinsu na son a ɓoye video ɗin nan kamar wani suna tsoronsa.
Kwana biyu dayin haka aka kawo lefena da ga gidan su Mansoor. Akwatina har goma sha biyu shaƙe da kayan alfarma na gani na faɗa. Babu wanda zaice lefen nan bai birgesa ba. Sai dai anga tsagwaron hassada daga Mom dan ta kasa haɗiye komai. Harda zage-zagenta wai ai saurayin Baby ne na kwace da asiri. Kuma ba kowa ke kawo min asirin ba sai Gwaggo Gudidi. Abu kamar wasa dai sai da aka kwashi rigima. Dan ƴaƴan Gwaggo Gudidi duk sun zo suna gidan. Rikici akai sosai na gaske. Lokacin Yaya Musaddiq shi baya gida. Yana wajen aiki, kamar dai wancan karon ya damƙa komai hannun matar ogansa aima baƙi abincin tarba da kayan maƙulashe. A wajen aikin ma ba zama yay ba shi da Mansoor suka fita police station wajen batun ƴan sanda. Sun shigar da report tare da bada lambobin mota har uku dana basu.. Suna can har aka gama rikin nan kowa ya kama gabansa dan su Gwaggo ma sun ɗauke lefen nawa daga gidan sun wuce da shi can gidanta. Acewarsu barinsa gidan Abba bazai yiwu ba su Mom zasu iya salwantarwa saboda basu da isashen mutunci. Ashe ko hasashen su Gwaggo yay dai-dai. Dan su Mom sun shirya mummunan ƙudiri kuwa akan lefen nan aka ɓata musu shiri. Wannan yasa suka huce kaina sanda na dawo. Dan bana gidan ma ni ina gidan wata ƙawata ta islamiyya. Duk yanda naso daurewa na kasa. Ranar sai da nai kuka sosai da jin kewar iyayenmu. Daga ƙarshe nai alwala nayi nafilfilina tare da miƙama UBANGIJI kukana. Wannan ɓacin ran dana kwana da shi yasa banyi aikin komaiba a gidan. Sai ma shiri da nai tunda farar safiya domin wucewa gidan su Joy ko zan rage damuwa, amma zan ɗan fara zuwa office saboda saƙon da MD ya turamin jiya da dare kusan 12 kan dan ALLAH yana son ganina a office yau idan babu damuwa. Jin yace abu mai muhimmanci ne yasa na amince zanje ɗin, kuma bana ma son yinin gidanmu a yau ɗin sam. Na fito na leƙa ɗakin Yaya sai na samu ya fita. Nayi mamakin fitar tasa ta sassafe yau. Amma sai nai wucewata akan zan kirashi awaya. Zuwa da rana sai na samesa a garejin dan ina son mu ɗan tattauna wani abu.
Napep na samu na shiga. Mun fara tafiya inata ƙoƙarin kiran numbern Yaya sai naji an kira sunana. Da mamaki na ɗago ina kallon wanda ke kusa da ni dana samu a napep ɗin, ganin babu wata alama data nuna shine yay kiran sunan nawa na kalla mai napep shima. Shima kuma babu alamar shi ɗin ne. Cikin takaici da jin haushi na sake ƙoƙarin maida kaina ina mamaki. Sai kuma aka sake faɗin, “Samraah!”. A fusace na ɗago yanzun kam. Kafin na samu damar cewa komai naji abu a fuskata. Yuuuu naji kaina ya fara mun. Cikin zabura nai yunƙurin dira daga napep ɗin sai dai na kasa hakan. Dan cikin ƙanƙanin lokaci jikina yay wani masifar nauyi na silale jikin kujera idanuna na lumshewa. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba kuma……✍️
Duk da nasan Maash ya bada kwangilar bibiyar Samraah. Amma nima zancen Mansoor ya fara sakani a cikin ruɗani. Amma bana son ku ruɗe kumuje zuwa dai, dan har yanzu fa wasan ma bai fara ba. Yaya Maash ne da wannan aika-aikar ko kuwa MD? Zai iya zama Baby ma fa. Kai Mom ma ba barinta zamuyi ba. Shin waye yay kidnapping Sam-G🤥🤔?.
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆
……Tunda suka tashi Mom taga Samraah batai aikin komai a gidan ba ta ƙara harzuƙa. Lallai yau dolene taci uban yarinyar nan dai-dai gwargwado har sai taga ubanda ya tsaya mata a gidan nan. Fuuu ta nufi ɗakin barcinsu tunda tasan yau weekend bata fita aiki. Sai dai me wayam babu Samraah. Sai auta da Bibaa dake barci. Da farko tai tunanin tana wanka. Dan haka ta koma falo tai zaman bala’i tana jira. Bayan kamar mintuna goma sai ga Bibaa ta fito tana miƙa da alama tashinta kenan.
“K koma ko kiramin yarinyar nan Samraah”.
Da ɗan mamaki Bibaa ta ce, “Ai bata ɗaki Mom.”
“K ban san iskanci ki duba toilet mana ina zata je”.
“ALLAH Mom bata toilet yanzu fa na shiga bayin na fito. Kodai tana kitchen tana aiki?”.
A ɗan ƙufule Mom ta ce, “Tunda ni makwauniya ce ko. Dalla fita nasan tana ɗakin shegen can shima munafukin na biyu. Jeki daga shi har ita ki kira min su”.
Babu musu Bibaa ta amsa da to. Sai dai babu jimawa sai gata ta dawo wai ɗakin a kulle yake. Dai-dai nan Abba ke fitowa da ga ɗakinsa. Tambayar mike faruwa yayi dan tun ɗazun yake joyo hargagin Mom da ga cikin ɗaki. Aiko a cikin tsantsar masifa take sanar masa. Ɗan jimm yay kamar ba zai ce komai ba. Sai kuma ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga neman Yaya Musaddiq. Bugu biyu kuwa ya ɗauka. Daga can ya gaida Abban cikin girmamawa. A daƙile ya amsa masa kamar yanda ya saba. Kafin ya ɗora da faɗin, “Kai kuna ina ne?”.
Da mamaki Musaddiq ya ce, “Abba ina gareji. Akwai wanda zai zo ya ɗauka motarsa ne shiyyasa na fita da wuri”.
“Uhhmyim ita Samraahn tana tare da kai kenan?”.
“Samraah kuma Abba. Ni kam mi zaisa na taho da Samraah nan. Tana nan a gida ai na barta tunda yau bazata je aiki ba”.
A harzuƙe Abba ya ce, “To bata nan”.
Sosai zuciyar Musaddiq ta wani harba. Muryarsa na nuna alamar rawa ya ce, “Abba kamar ya bata nan. Ina Samraah zata je da sassafen nan bayan bata da office yau?”.
“Sai ka tambayen tunda yawo nake da ita a bayana”. Daga haka Abba ya yanke wayarsa. Hankalin Musaddiq yay masifar tashi batare da yasan dalili ba, tunda ta saba duk inda zata ko baya gida sai ta kiransa ta sanar masa a waya. Dan haka babu arziƙi ya baro gareji da fatan ya zo ya samu Samraah ta dawo. Dan tunda Abba ya katse wayarsa ya maida akalar kiran kan Samraahn amma wayar na shiga anƙi a ɗauka. Daga baya ma aka kasheta duka baki ɗaya. Wannan kuma ba halin Kandalarsa bane ba, balle ma ace shine yay kiranta da kansa…
Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan, inda ya samu har lokacin Mum nata masifarta. Al’amarin kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai har sha biyun rana babu wani bayanin Samraah. Tun kowa na ɗaukar komai wasa har la’asar babu wani bayani. Zuwa lokacin anata buge-bugen waya wa ƴan uwa amma kowa sai yace bata je ba. Hakama ƙawayenta duk da Musaddiq yasan ita bamai yawan biye-biyen gidajen ƙawaye bace, ƴan uwan ma wace ala cika. Har gidan su Mansoor an sani zuwa sannan. Zuwa kusan biyar na yamma sai ga ɗayar wayarta an samu, wanda ya ɗaga ya tabbatar musu tsinta yayi. Harga ALLAH kuma ya yarda zai basu ne saboda yaga hoton Samraah ne a fuskar wayar. Hankali tashe Mansoor da Musaddiq sukaje inda ya kwantata yake, dan su ne dai keta faɗi tashin. Su Mom sunce basu yarda wani abune ya sameta ba sai dai idan yawon tazubar ɗin data saba tafiya ne ta tafi. Dan haka sukai burus da komai kamar basu san mima ake ba. Garama Abba yakan yi ɗan zugumm alamar tunani. Da Mom ta tsikaresa da hira kuma sai ya ware.
Mansoor da Musaddiq sun amso waya tare da mask ɗin Samraah da eyeglasses ɗinta da aka tsinta. Ya kuma kaisu inda ya tsinta ɗin mutane kuma da yawa sun bada shedar tsintar yayi da gaske. Dan abun ya faru ne a idon mutane kusan uku dake sana’a a dai-dai wajen. Kasancewar suna fitowa da safe sosai suma. Sai dai sunce sunga wata napep da mota blue sun tsaya a wajen amma basu san mi sukayi ba, sai da suka wuce ne wanda ya tsinta wayar yake ganin abinda ya tsinta ɗin. Kuma yay magana da su bai ɓoye ba. Zuwa yanzu kam hankalinsu yakai ƙololiwar tashi, dan haka take suka kai report a station mafi kusa. Dalilin Mansoor nada ɗan halinsa tun a lokacin aka shiga traicing ɗayan layin Samraah. Dan kuwa wayoyinta biyu ne, kuma duk manya ne. Ɗaya tana amfani da ita saboda aiki, ɗaya kuma abinda ya shafi family ɗinta da ƴan abubuwanta ne a ciki. To ta aikin aka ajiye aka tafi da waccan. Har dare babu wani cikakken inpometion mai gamsarwa, zuwa sannan kuma dai tashin hankalin Abba ya fito fili. Dan Gwaggo Gudidi tazo tana faman kuka da faɗin lallai a binciki su Mom sun san inda suka ɓoye Samraah. Tunda kowa yaji dama abinda Mom ɗin ke faɗa a jiya gaban kowa. Mom zata hayayyaƙo maƙwafta da suka shishshigo suma suka nuna lallai akwai ƙamshin gaskiya a batun Gwaggo Gudidin. Kamar wasa kuwa sai ga rikici ya ɓarke. Dan zuwa gab da magrib su Musaddiq suka zo anguwar da ƴan sanda. Nanfa hankalin Mom yaso ya fara tashi, sai dai tana ta ƙoƙarin dannewa ita a dole kada aga gazawarta..
Tambayoyi ƴan sanda suka musu har Auta ba’a bari ba. Mum kamar a ruɗe take amsa komai, dan haka ɗan sandan da case ɗin ke hannunsa ya dasa mata ayar tambaya. Sai dai bai ce komai ba suka wuce akan zuwa safiya zasu iya dawowa kosu nemesu a can station ɗin su.
💫 (✧✧)✨(✧✧)✨(✧✧)💫
Sannu a hankali na motsa idanuna da sukai min matuƙar nauyi da ɗaurewa. Sai kuma na shiga buɗesu sannu-sannu, a wani ɗaki mai ƙarancin haske na tsinta kaina alamar yamma tayi. Dan kiraye-kirayen sallar magrib ma naketa jiyowa. Ƙirjina ne yay wata masifar bugawa. Nai saurin ambaton ALLAH ina sake lumshe idanuna da sake buɗewa. Tabbas ta tabbata anyi kidnapping ɗina. Da ƙyar na iya tashi kasancewar duk jikin nawa babu wani ƙarfi. Ga wani irin fitsari da nake ji. Jiri-jiri dake neman kwasata yasa da ƙyar na iya dafe bango na miƙe. Lalube na shigayi ko zan samu wani haske. Cikin ikon ALLAH na samu makunar fitila. Idanuna dake lumshewa da buɗewa na sake warewa da ƙyau. Ɗakine babba sosai. Sai katifa a ƙasa ƙarama irin ta ƴan makaranta, akwai bargo da filo an kuma shimfiɗa bedsheet a kanta. Gefe kuma handbag ɗina ce sai leda mai tambarin gidan abinci har guda biyu a kusa da ita. Tare da ledar ruwa guda. Da ƙyar na iya jan ƙafata zuwa ƙofa. Na shiga ƙoƙarin murɗawa amma sai na sameta rufe gam. Inda labule yake ma sake nufa da ƙyar dan nasan bazai wuce window ba, na turesu da ƙyar. Ita ɗince kuwa, sai dai a rufe, nai ƙoƙarin na buɗe da ƙyar. Amma ƙarfen da akai adonta da shi ƙanana ne sosai ta yanda ko hannu bazai fita ba ma. Sosai zuciyata ke rawa yanzun kam. Ban haƙuraba na sake nufar ɗayar, nan ɗin ma dai irinta ce. Inda ke da kamar ɗan corridor na nufa, amma sai na samu ƙofar bayi ce a wajen. Naga hakanne sakamakon buɗewa da nai. Bamma san sanda na silale a wajen ba na saki wani irin kuka mai tsuma rai da girgiza zuciya. Na jima zaune a wajen ina kuka kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Kafin na sake miƙewa da ƙyar na shiga toilet ɗin. Fes yake babu wani datti. An kuma ajiye wadataccen sabulun wanka, omo, toothpaste brush, sosan wanka. Kai harda kayan wanke bayi. Babu dai abinda zaka nema ka rasa daya shafi hakan. Alwala na ɗaura batare da nabi takansu ba, zuba ruwan alwalar a jikina ya ƙara taimakawa naji na ɗan warware. Anan ma sai da na duba window sai dai yayi sama sosai koma ƙarami ne. Haka na fito na dawo ɗakin. A saman tabarma dake gaban katifar malale nai sallar azhar da la’asar har magrib. Sake kife kaina nai a wajen na sake buɗe sabon shafin kuka. Nama rasa ina zan kai tunani na. Kamar wadda aka zaburar na zabura inda bag ɗina take. Da sauri na buɗeta na shiga laluben wayata jikina har wani mazari yake tsabar yanda nake a ruɗe. Ganin kamar laluben ma baya min kawai na zazzage komai na cikinta burina kawai wayata ya faɗo, amma babu ita babu alamarta, sai ƴan kayan shafana dana zuba lips gloss ne kuma da fauda sai ƙaramin oil misk da face mask guda biyu da bana rabo da ita a jaka akoda yaushe. Bamma san na sake sakin wani wahallen kuka ba a wajen tare da zubewa ƙasa daga ni har bag ɗin……..✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐
…….Kusan mintuna biyu ina zabga kuka, kafin na sake jawo jakar da tarkacen ciki dana juye ƙasa duka zuwa gabana. Sake zazzagawa na koma yi kamar wadda ta zautu. Ko abinda keda alaƙa da waya babu a cikin duka wayoyina biyu. Amma na kasa yarda, sai ƙara zazzagawa nake da ɗaɗɗaga kayan dana zazzage kamar wata mai neman barimar ɗan kunne. Sai da dai zuciyata ta tursasani akan babu ɗin da gaske sannan na sake fashewa da kuka tare da yin wurgi da jakar. Haka na kasance a wannan daren babu wata nutsuwa irin ta cikakken mai hankali a tare da ni. Sai dai koda wasa ban mance ambaton UBANGIJINA ba. Gab da asubahi wani wahalallen barci yay awon gaba dani, ban tashi farkawa ba sai kusan bakwai da kwata. A firgice na miƙe na nufi toilet na ɗauro alwala. Bayan nazo na gabatar da salla koda na idar a wajen na cigaba da zama na fara karatun Alkur’ani a hankali jikina duk babu ƙarfi, dan akwai yunwa ma tare dani, jiya gaba ɗaya banci ba ban sha ba. Nafi awa ɗaya da kusan rabi a wajen naji ana ƙoƙarin buɗe ƙofa. A zabure na ɗago daga cusa kaina da nai cikin ƙafafuna dan a haka nake karatun. Kallo ɗaya mai shigowar yamun ya ɗauke kansa, yana sanye da mask baƙi kamar yanda komai na jikinsa ke baƙi, dan hatta hannunsa akwai safar hannu baƙa. Ya kuma toshe idanunsa na baƙin eyeglasses da babu abinda zan iya ganewa ko gani nashi. Irin ledar dake ajiye a ɗakin ce a hannunsa. Batare da ya tankamin ba ya ajiye ya ɗauki ta jiya dako kallonta banyi ba ya nufi hanyar fita abinsa.
Muryata na rawa nai saurin dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Wanene kai? Miyasa kuka kawoni nan? Mi kike buƙata da ga gareni? Wani laifi na muku ko kuɗin fansa kuke nema?”.
Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Ina kammala faɗa kuma bai tanka ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sake kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawaye na gangaro min da gudun tsiya. Lallai ina a tsaka mai wuya, gashi bamma san wanda zan iya zarga ba. Dan gaskiyar Mansoor ne. A wannan gaɓar hatta da Baby da MD kai har Mom da Abba kansa ni zasu iya shiga lissafina ma. To amma ni abinda ke damuna waɗan nan mutanen da duk na lissafo idan sunyi hakan gareni duk miye ribarsu? A yanzu ba kaina kawai nake tausayi ba ƴan uwana da halin da zasu shigane ke matuƙar tada min hankali fiye da komai. Ga Mansoor shima. “Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki ka kuɓutar dani da gaggawa. Kasa kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya a zukatan ƴan uwana da masoyana da ni kaina. Duk wanda bashi da laifi akan wannan al’amarin ya ALLAH ka hanashi shiga wahala. Mai hannu a ciki UBANGIJINA ka hanashi damar cutar dani koda yayi niyyar hakan a gareni”. Zamewa nai a hankali na sake kwanciya ina mai cigaba da karatun Alqur’ani na. A haka barci ɓarawo yay awan gaba dani tunda dama bai isheni ba. Ga kaina na wani kalar masifaffen ciwo.
Barci nayi sosai, dan ban tashi farkawa ba sai da naji ƙarar an buɗe ƙofa. Firgigit na miƙe kuwa ina murza ido. Mutumin ɗazu ne dai kuma kamar ɗazun fuskar tasa a rufe. Wata ledar abincin ya sake ajiye min da wata babba fara ita kuma yanzu ma ya sake ficeewarsa batare da yamun magana ba ya sake kullenin. Kwata-kwata yanzu ma hawayen nawa sun kasa fitowa. Da alama zuciyar ta fara dakewa. Salloli da nake jiyowa anatayi a masallatai yasa na miƙe a hankali. Jikina sai ciwo yake tako ina. Na tabbatar harda rashin wanka dan ni mutum ce mai son yawan wanka a rayuwa. Kuma ko yaya idan banyi ba sai na dinga jin babu daɗi. Naso na daure kada nayi, kamar yanda nake ƙoƙarin hana kaina cin komai, dan ko ruwa sai a wajen alwala nake ɗan haɗiyarsa. Amma na kasa hakan dan wani ƙyanƙyamin kaina nama fara ji, harma zuciyata na wasi-wasi akan yin salla da su. Ledar kayan na janyo na shiga fiddosu. Dogayen riguna ne har biyar duk marasa nauyi da bazasu takurani ba. Sai hijjab biyu manya. Harda su b&p shidda-shidda. Sai kayan barci har uku da man shafawa da turare. (Ko wanene wannan anyi cikakken ɗan iska ma wlhy. Wato komai anyisa akan shirine, babu kuma alamar zan bar nan ɗin a kusa tunda harda tanadin kayan sakawa). Duk a zuciya nake wannan tunanin. Cikin jin ban aminta da ɗakin ba na ɗauka doguwar riga ɗaya da b&p na shiga toilet. Wanka nayi da ruwa masu ɗumi dan akwai hitter a toilet ɗin. Sai naji jikina ya rage nauyi, hakama zuciyata. Na ɗan ji ƙarfi da nutsuwa har ƙwaƙwalwa ta na iya sarrafa tunani yanda ya kamata. Brush shima nayi na ɗauro alwala na sake fitowa. Banbi takan mai da abinci ba na koma na kwanta a katifar na lumshe idanu kawai ina mai faɗawa duniyar tunani…..
✨💞✨💞✨💞✨
Zuwa safiya labari ya fara karaɗe gari da social media. Abinka da sananniya musamman ma a watanni biyun nan da sunanta yay amsa kuwwa a lungu da saƙo sakamakon abinda ya faru a wajen taron buɗe Companyn Maash da kuma hirar da tai da shi. Ta wani ɓangaren kuma wanda basa harkar yanar gizo sun santa ne a dalilin shirin da take gabatarwa ta hanyar rediyo. Duk wani wanda ke a office ɗinsu hankalinsa a tashe yake. Musamman ma MD da ƴan sanda suka gano shine mutum na ƙarshe daya tura mata text message akan yana son ganinta. Dan haka a ranar Monday ɗin ƴan sandan suka gayyacesa office ɗin su. Gefe kuma gasu Mom suma an tattare zuwa station saboda abinda sukaita faɗa a randa aka kawo lefen Samraah, ga kuma rikicin da suka sake yi a daren bayan mutane sun watse maƙwafta da suka ji komai sun faɗa da sake tabbatar da anyi hakan. ALLAH sarki Mansoor da Musaddiq sai su baka tausayi. Dan kwana ɗaya kacal duk sun fita hayyacinsu. Hafizzullah ma a ranar Monday ɗin ya tsallako karatunsa ya nufo Kano..
Shigar mahaifin Mansoor a zancen ya saka ƴan sanda sake ɗaukarsa da girma. Dan a yanzu D.c.o ɗin ne ma da kansa yake gudanar da binciken. A yau har Attahir ma Yayan Mansoor ba’a bari a baya ba, dan shima dai yana a station ɗin anata ɗan kai kawo dai akan batun…
Al’amari kamar wasa akan ɓatan Samraah ƙaramar magana na neman zama babba. Dan ƴan sanda sun matuƙar takurama MD da Baby da Mansoor ya tabbatar da yana zargi. Sannan wani mai shago a anguwarsu ya tabbatar da yaga sanda Samraah ta tare napep ta shiga, dan har gaida shi ma tayi kamar yanda ta saba. Ya kuma tabbatar da zai iya gane napep ɗin dan har number ɗinta da tambarin dake jikinta ya riƙe saboda mai napep ɗin ya jima tsaye a ɗan nesa da shagonsa shi yama yi zaton ko wani yake jira a wajen. Sai can ya maida hankali ga sallamar mutane sai ga Samraah. Lokacin da take gaishesa tabbas ya ɗago ya kalleta yaga tana ƙoƙarin tsaida Napep. Sai dai bai ga mai shirin ɗaukar tata ba har sai da ta shiga ciki. Mai napep ɗin ma yaja sun fara tafiya, ya ɗan zabure da nufin tsaidasu dan hankalinsa yaji bai kwanta ba amma har sun wuce. Sai kawai ya bisu da addu’a tunda bawai yasan gaibu bane, kuma yaga bayan ita akwai wani kamar ma a ciki.
Bayanin mai shagon nan yayi matuƙar yima ƴan sanda da duk wani masoyin Samraah daɗi. Dan koba komai an fara kama bakin zaren. Sakamakon kamar yanda mai shagon nan ya faɗi tambarin dake jikin napep ɗin nan haka mutanen da aka ajiye wayarta a inda suke suma suka maimaita dan tambari bai kamata a manta da shi ba. Wannan yasa duk wani masoyinta buɗe idonsa tarwai akan lura da shigi da ficin masu napep duk da kuwa kamar banza suke a Kano dan yawa. A ta gefen jami’an tsaro kuwa kai tsaye ofishin shugaban masu kula da ƴan napep suka je. Inda suka bada report akan napep ɗin da mai tuƙata. A take kuma babu ɓata lokaci aka shiga bincikenta. Abinka da komai a tsare a yinin ranar sai da aka gane wanda ke tuƙa napep ɗin. Tuni ƴan sanda suka saka aka cikuykuyosa shi da napep ɗin tasa. Inda wanda suka gani suka tabbatar da ita ɗin ce kuwa. Sai dai basu da tabbacin shine a ciki ko ba shine ba. Amma tabbas dai napep itace.
Kasancewar dare yayi ba’a wani tuhumi mai napep ba a ranar sai washe gari da Samraah ke cika kwanaki uku kenan. Sai dai me, a yayin tuhumar mai napep yayi rantsuwa ya ƙara kan shi bai san komai ba. Hasalima a ranar napep ɗin ba’a wajensa ma ta kwana ba. Ya bama wani abokinsa da yamma akan zai yi aiki ya ɗan samu nashi har zuwa dare sai ya dawo masa da ita. To bai dawo masan da ita ba sai washe gari kusan takwas dan har sukai faɗa ma saboda ya karya masa alƙawari, ga shi shi kuma yana fita aikin wurine amma ranar yasa ya makara……..✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
……D.c.o ya tura yaransa neman abokin mai napep, sai dai an samu wai baya nan yayi tafiya. Wannan dalilin yasa sukace zasu cigaba da riƙesa har sai an kamo abokin nasa. Hankalin ƴan uwansa ya tashi kamar yanda shima nashi ke a tashe. Amma dai d.c.o yaƙi saurarensu. Dan ya tabbatar musu da yana akan aikinsa ne. Babu yanda zasuyi dole suka haƙura suka tafi. A ɓangaren ƴan media suna nan suna cigaba da tattauna batun ɓatan Samraah. Yayinda hotunanta ke yawo lungu da saƙo kowa na faɗin abinda fahimtarsa ta bashi. Dan wasu har suna danganta komai da cewar ita ta jama kanta. Dama taya zata taɓa irinsu Maash tace zata zauna lafiya. Ai gashi nan ya mata lunbu-lunbu da ga ƙarshe ya ruftata dan mawuyacine ace bashine ya saka aka kwamusheta ba. Musamman in akai dubi da yanda ta samu damar tattaunawa da shi ta yanda manyan ƴan jarida suka daɗe suna fatan haka amma basu samu ba. Wasu ko na ganin wani ne ya saceta dan kawai a ƙullama Maash sharri. Wasu na ganin ko dai MD ɗin nasu ne musamman yanda zancen son da yake mata ya karaɗe ko’ina, ga shi kuma an saka mata ranar aure da ya rage saura sati uku kacal. Wasu dai kuma zarginsu na akan Maash ɗinne dai da tunanin son da yake mata ne ya sashi aikata hakan ganin an saka mata ranar aure da waninsa. Hakama wasu zarginsu bai bar kan Baby ba itama jin TAKUN SAƘAR dake tsakaninta da Samraah ɗin akan Mansoor ba, hakama mahaifiyarta da tun fil azal ba son su Samraah ɗin take ba. Ga kuma abinda tayi a randa aka kai lefe. Kai hatta da abokan huɗɗar Mansoor ɗin wasu a ciki sun shigo zargin jama’a. Tawani fannin kuma akance maƙiyane kawai ko kidnappers ne kawai saboda yanda sunan Samraah ɗin ya samu ɗaukaka cikin ƙanƙanin lokaci game da shirin da take akan matasa da yanda take nuna illar lalacewar matasa a cikin al’umma. Kaso marasa ƙarfi kuwa na ganin adai bunciki sauran samarin Samraah suma dan zasu iya aikata komai ganin Mansoor na shirin wuff da ita, ko kuma shi ƴammatan Mansoor ɗin. Kai zance ne dai gashi nan kala da iri harda wanda ma bashi da ma’ana. Kamar wasa a haka sati ɗaya ta shuɗe ana fakon abokin mai napep. Ba’a samu damar damƙosa ba kuwa sai a randa take cika kwanaki tara ciff.
★ “Kidnapping kuma? Ni wlhy yallaɓai bani bane. Mizai sa nai kidnapping mutum? Idan na ɗauketa ma ina zan kaita?”.
Cikin tsawa yaron d.c.o dake tuhumar tasa ya ce, “Kai karka raina mana hankali. In ba kai bane ba to waye bayan abokinka ya tabbatar da kai ya bama key ɗin napep ɗin tasa? Kuma da ita aka ɗauketa daga nan ba’a sake jin labarinta ba har yanzu”.
“Tabbas ni ya bamawa yallaɓai. Kuma ba ranar muka fara yin haka da shi ba. Saboda nima lokacin da nake da napep ɗin nakan bashi. Hasalima nine na koya masa tuƙinta, da taimakona kuma aka bashi napep ɗin ma a office ɗin mu. Amma wlhy ni banyi kidnapping kowa ba”.
“Ƙarya kake yi kai ne. Tunda har ka iya barin gari sai yau kake dawowa a tunaninka komai ya lafa ko”.
“Ranka ya daɗe ni ban bar gari dan komai ba wlhy. Ƙauyenmu naje da yake ina noma duk shekara. Shine na je nakai taki gonata. Can ɗin babu network shiyyasa wlhy bamma san mike faruwa ba. Sai yanzu da nake ji ma a bakinka. Amma na tuna wani abu, idan ban manta ba da safe abokinmu da shima mukanyi irin haka da shi yazo yace na ara masa key ɗin keken Salisu zai amso saƙo a tasha, tasa na gareji sai azhar zai amso.”
Da sauri ɗan sandan ya ce, “Ka tabbata?”.
“Tabbas anyi haka ranka ya daɗe. Dan ƙanina ma na ɗakin a gabansa akai komai. Yaje kusan awa biyu sai gashi ya dawo ya kawomin yay godiya. Har ma naji haushi saboda ya saɓa lokacin daya dace ace na maidawa Salisu kasancewar yana fitar sassafe shi”.
“Yanzu ina zamu samesa?”.
“Anguwarmu ɗaya da shi, sai dai ta bayan layinmu gidansu yake. Shima kuma yana harkar adaidaitan, nasan yanzu baza’a iya samunsa a gida ba sai irin takwas haka ko bayan magriba gaskiya”.
“Karka damu zamu samoshi”.
Ɗan sandan ya faɗa yana miƙewa. Kai tsaye office ɗin d.c.o ya nufa. Bayanin da yaron ya masa duk ya maimaita masa. Goyon baya d.c.o ya bashi akan su tabbatar sun samo wancan yaron kafin zuwa safiya. Ya tabbatar masa da in sha ALLAHU za’ai hakan kafin ya bashi damar fita. Cikin girmamawa yay salute ɗinsa sannan ya fice. Shiru kawai d.c.o yay yana mamakin wannan irin juya-juya. Dan case ɗin gaba ɗaya ya ɗauki zafi saboda yanda mutane keta ka-ce-na-ce akan batun yarinyar, shi kansa yanda yaga an ɗauki al’amarin nata da muhimmanci ya sashi bibiyar shirye-shiryenta na baya a daren jiya, tare da shafukanta na sada zumunta dake ɗauke da fallowers masu yawan gaske, sai yaji ta shiga ransa. Gata dai ƴar yarinya amma akwai kaifin basira da nuna kwazo akan aikinta. Ga mahaifin Mansoor da Mansoor ɗin sun addabama rayuwarsu. Kowane motsinsu yanzu yana a station ɗinsu ne. Azalzalar su kawai suke faman yi akan a gano musu inda Samraah ɗinsu take su dai. Hakama Yaya Musaddiq idan ka kallesa sai ya baka tausayi, rashin dauriya kawai Mansoor ya fisa. Shiko Hafizzullah sai dai kuka. Yayinda jikin Abba ya fara sanyi, sai dai yaƙi yarda ya nuna hakan ga mutane saboda shakkar Mom..
⭐❤️⭐❤️⭐❤️⭐❤️⭐
Faɗa muku yanayin da nake ciki a kwanaki tara ɗin nan da suka gabata sam bazai yiwu ba. Dan koda da kwatance nace zanyi hakan bai zama lallai ku iya fahimtata yanda ya kamata ba. Abinda kawai nake so ku fahimta al’amarin sam bashi da sauƙi. Nayi kuka matuƙa Bily. Irin wanda ni kaina sai da na tabbatar da nayi sa. Sai dai ku sani badan kaina nake yinsa ba. Domin ƴan uwana biyu ne da nasan zasu fi kowa shiga tashin hankali ne. Sai kuma masoyina da ya rage saura kwanaki goma sha uku kacal ya amsa sunan mijina. Dai-dai da daƙiƙa ɗaya ban gaza wajen miƙama UBANGIJI kukana akan ya kuɓutar dani daga wannan ƙangi, ya sa ina da rabon komawa ga dangina. Bani da wani ƙarfin nuna yunƙurina saboda halin rashin lafiya da nake ciki. Ciwon kai da zazzaɓi sun kasa barina. Na kuma gagara faɗama wanda ke zaryar ajiyemin abincina da har yanzu bai taɓa min magana ba, ban kuma taɓa ganin fuskarsa ba. Sai a yau da safe kusan goma da rabi sai gashi ya shigo. Nayi mamakin shigowar tasa saboda ba lokacin kawo min abinci bane, kuma baya shigowa dama sai zai kawo abincin. Amma ganin waya a kunnesa yasa na zuba masa manyan idanuna. Har gabana ya ƙaraso, batare da yamun magana ba ya tsaya ƙiƙam a kaina kamar wani mai gadin gidan kallon kwallo. Wayar dake a kunnensa ya sauke. Batare da yamun magana ba ya ajiyeta a ƙasa gabana. Na ɗago da nufin kallonsa maganar da akai cikin wayar ta katseni. Da sauri na maida kallona akan wayar, wata dattijuwar murya ce da nake ji kamar na taɓa saninta, cikin nuna ƙarfin iko da tabbatar da rashin wasa aka furta.
“Nasan zuwa yanzu kin fahimci inda kike ba wajen wasan yara bane ba. Ba kuma filin ɗaukar rahoto bane ko dandalin sada zumunta. Baƙya buƙatar wani bayani kam dogo yanzu ƴammata. Sanin wanene ni? Miye dalili? Mi kika aikata duk bana buƙatar ji. Video recording ɗin hannunki kawai nake buƙata, mi zanyi da shi, ko minene alaƙata da shi ba damuwarki bane. Na duba a duk wayoyinki babu kin ciresa a ciki, ya rage naki faɗar inda yake ko wajen wanda yake a bani ke kuma ki kama gabanki. Idan kuma kikace zaki zama mai taurin kai tabbas zaki dawwama a wannan ɗakin tamkar kabarinki, dan ko mutuwa kikai a ciki zamu gina miki kabari mu bizne ki batare da wani mahaluki ya taɓa sanin hakan ba har abada. Kuma zan mallaki video ɗin sannan na ɓatar da duk wani ahalinki daga doron ƙasa. Zaɓi ya rage naki lokaci na tafiya miki dan nasan kina shirin zama amarya”.
Ni kaina ban san sanda murmushi ya suɓuce min ba. A karan farko na wani ja numfashi mai nauyi tare da sakin wata siririyar dariyar ƙarfin hali. Kaina tsaye na nima na furta,……..✍️
Shin wa kuke tunani ne? Gashi dai Sam-G tace muryar Dattijo, kai nafa ruɗe nima. Amma mu haɗu a comment section ko wani zai canko mana🤔😞
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓
……..“Oh oh wannan irin dogon zance haka Baba, bakinka ko gajiya bayayi. Kayi haƙuri ina jin girman tsufarka a cikin raina duk da ba ganinka nake ba. Sai dai ga saƙo zan baka. Ka faɗama shi wanda ta aikokan shin tsoron Samraah Abdul-wahab Gwarzo yake ne? Ko kuwa shi bai cika namiji bane daya laɓe a bayan tsufarka a yimin barazana? To idan yana kusa da kai ya buɗe kunnuwansa da ƙyau ya saurareni, idan kuma baya kusa ka masa recording. Ni Samraah Abdul-wahab Gwarzo ban yi video ɗin dan aimun barazana na bada ba. Idan buƙatarsa yake mu haɗu gaban hukuma. Idan kuma yana da ƙarfi yazo muyi gaba-da-gabq kwanta. Sai dai ya sani ko dungurin wani da ga cikin ahalina yayi bazai sauke hannunsa ba video ɗin zai baza duniya. Dan haka zaɓi ya rage nashi, ku farka daga wannan nannauyan barcin na barku lafiya”. Da ga haka na yanke wayar tun kafin shi ya yanke. A fusace wanda ya kawo min wayar yake hararata. Amma nai biris da shi na ɗauke kaina. Kiran wayar aka sake yi, da sauri ya ɗauka ya kai kunne. Ban san mi aka faɗa masa ba na ga dai ya sake hararata ya juya ya fita. Nima da harar na raka nasa bayan ina taɓe baki. Da ga haka na zame na kwanta zuciyata na wata irin tafasa. Sai dai a wani gefen ina jin daɗi dan koba komai na samu bakin zaren wanda yasa aka kawoni nan. Zargin mutane da yawa ya fitamun a dai zuwa yanzun, musamman ma jama’ar gidanmu.
Barcina na sha yau da rana sosai, dan yanzu bani da wani aiki sai inci in kwanta ɗin, sai idan naji na gaji ne da zaman waje ɗayan sosai nakan ta zagaye ɗakin wani lokacin ma na ɗan motsa jikina dai, saboda na fahimci na fara ƴar ƙiba ba kamar sanda aka kawoni da bana cin abinci ba sai yawan kuka. Ganin zan halaka kaina a banza nama masoyana asara yasa na fara cin abincin tunda nasan ban isa canja abinda yazo a littafin ƘADDARA ba ai. A yanayin ɗan ƙarfin jiki dana tashi da shi ya sani jin zan iya tunkaresa koda zai ƙarar da numfashi na, sai dai zan fara da wannan mai kawo min abincin a yau ɗin nan. Amma sai zuciyata ke gargaɗina da hakan kai tsaye, dan haka na shiryama raina wata sabuwar dabara ina kuma addu’ar cin nasarar hakan amma sai na gwada plan ɗin farko baiyi ba tukunna dai.
Kamar ko yaushe cikin ƙarfin hali na tashi nai wanka da ruwan ɗumi. Kaya na saka na sake dawowa na kwanta a katifar dan jiri nake ji na neman ɗibata. Ina nan kwance tamkar mai barci naji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Luff na sake kwantawa har aka shigo aka sake maida ƙofar aka kulle. Sai da ya shigo tsakkiyar ɗakin sannan ya tsaya cak. Idanu na ɗan ƙara buɗewa ta can ƙasa yanda zan gansa da ƙyau. Ƙofar bayi yake kallo, nasan kuma dalilin yin hakan, dan kan shower ɗin na ɓalle nabar ruwa nata zuba. Ka ɗan naga ya duƙa yana kai yatsansa biyu ƙasa ya dangwala, sai kuma naga yay saurin ajiye ledar abincin hannunsa ya nufi toilet ɗin da alama ruwan ne ya fara fitowa.
“Lafiya miya faru?”.
Na faɗa a hankali. Bai tanka min ba, bai kuma tsaya ba. Na saki murmushi ina tashi zaune. Bayansa na bi. Duƙe na samesa yana ƙoƙarin buɗe hanyar da ruwa ke fita gaba ɗaya da ɗayan hannunsa. Ɗayan kuma ya danne pipe ɗin shower ɗin ya cusa babban yatsarsa a ciki ya tsayar da ruwan. Sai dai duk da haka yana ɗan fita sii. Da wannan damar nai amfani nima na shigo ina faɗin, “Tun ɗazu nake kiranka dan ka duba amma baka amsamin ba.”
Kaɗan ya juyo ya kalleni sai kuma ya sake maida kansa ga abinda yake yi. Ni ko na duƙa kamar zan janye masa boket dana jiƙa kaya ciki na samu nasarar zare wayarsa. Da sauri na tusata cikin rigata. Na janye bokatin na fita abina. Sake komawa nai cikin katifar nai kwanciyata. Sai dai zuciyata sai faman gudu take a ƙirjina. ALLAH ALLAH nake ya zo ya fita kafin ya farga babu wayar tasa. Amma bai fiton ba sai kusan bayan minti goma. Batare daya kallan ba ya nufi hanyar fita. Cikin rawar jiki ina jin ya kulleni ta baya alamar ya tafi kenan. Na ciro wayar. Naji daɗin ganin babu password jiki, cikin rawar jiki data hannau na saka number Yaya Musaddiq na danna masa kira. Harta katse bai ɗauka ba. Hankalina ya sake tashi jikina har kakkarwa yake. Sake ƙoƙarin kira nake ina kallon ƙofar. Nan ma ta shiga amma har tana neman yankewa babu alamar za’a ɗauka. Nama gama sadaƙarwa dan idanuna har sun cika da hawaye sai ya ɗaga. A yanda yay sallama cikin wani yanayi na mutum mai damuwa yasa idanuna sun ciko da ƙwalla. Cikin rawar muryar alamar son sakin kuka na ce, “Yaya Musaddiq nice. Nice kandalarka. Dan ALLAH kuzo ku fiddani anan karna mutu. Yaya banda lafiya ciwo zai kasheni. Sun kawoni nan sun ɓoye kullum sai dai suyita bani abinci kawa…..”
Fittt naji an ƙwace wayar daga hannuna. Hannu ya ɗaga zai ɗauke fuskata da mari sai kuma miya tuna oho masa ya tsaya cak. Niko tsoron da naji na kar ya kai ƙaton hannunsa kaina ya sani dunƙilewa waje ɗaya na rumtse ido. Jin shiru banji saukar marin ba na buɗe idona. Dai-dai nan yake ƙoƙarin fita a ɗakin. Na taso kuwa da uban gudu na nufi ƙofar nima, ina gab da ƙarasawa ya datse da sauri. Zubewa nai a wajen na saki wani kalar kuka mai ban tausayi da cin zuciyar mai sauraro.. Ina a wajen ko cikakken minti biyu baiyi da fita ba sai gashi ya dawo cikin sassarfa. Jin saukar handkerchief kawai nai a saman face ɗina. Kamar waccan ranar nayi niyyar yunƙurin tashi amma abinda suka shaƙa min yaci ƙarfina. Kamar ƙyaftawar ido na sulale ƙasa, daga haka ban sake sanin abinda ke faruwa ba kuma..
✨●●)(●●)(●●)(●●✨
Gaba ɗaya yanda Yaya Musaddiq da Mansoor suka rikice bama su fahimci wayar ya yanke ba. Dan suna tare ne a mota sanda Samraah ta kira wayar. Da farko hankalin Mansoor ba’a kan Musaddiq yake ba. Sai da yaga yayi wata shegiyar zabura yana ƙwala kiran sunan Samraah jikinsa har wani gab-gab yake na rawa sannan. Wayar shima ya fisga jikinsa na rawa yake faman kiran ta. Sake ƙarɓewa shima Yaya Musaddiq ɗin yayi. Duk sun rikice sun ruɗe, jin dai ɗif ɗin yayi yawa suka ɗan fara dawowa hankalinsu. Sai sannan suka fahimci wayarma ta yanke. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga rige-rigen sakkoma Yaya Musaddiq. Dan harga ALLAH yana matuƙar ƙaunar ƙanwarsa. Mansoor ma dai idonsa cike yake da ƙwalla, cikin ƙarfin hali ya buɗe motar ya fita. A ɗan zabure Musaddiq ya figi wayarsa dai-dai sanda Mansoor ke fita a motar, dan tunawa da ya dace ma su kira d.c.o fa. Kiran nasa kuwa yayi, sai dai ba’a ɗagaba. Cikin tashi hankali ya cigaba da kira. Har 3 miscall, fita yay da sauri a mota. A jikin motar ya samu Mansoor jingine idonsa a lumshe. Cikin sauri-sauri yake faɗin, “Na kira d.c.o amma bai ɗagaba. Inaga ya kamata mu ƙarasa police station ɗin mu sanar masa”. Shima ɗan zaburar Mansoor yay, cikin alamar gamsuwa da zaburowa ya nufi motar yana faɗin, “Hakane yaya, wlhy ni kaina ma ya tushe na rasa mizan yi, amma bara na kira Yaya Attahir ya nemesa tunda abokinsa ne”.
Musaddiq ya gamsu da hakan, cikin ƙanƙanin lokaci Mansoor ya sanarma yayansa halin da ake ciki, kafin suma su ɗauki hanyar zuwa police station ɗin. Sosai Mansoor ke gudu, hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka iso station ɗin. Sun samu d.c.o baya nan ya fita sai dai Yaya Attahir ya kira Mansoor ya sanar masa yay magana da d.c.o ɗin ta waya, gashi nan zuwa ma su jirashi. Dole sukai zaman jiran dawowarsa duk a ƙage. Sai bayan kusan mintina sha biyar kuwa sai gashi ya dawo. Ganin yanda suke hankali a tashe ya buƙaci fara ganinsu. Suna gaya masa kamar yanda Attahir ya sanar masa tun a waya, shiyyasa ma ya katse abinda yake acan ya taho, ya amshi wayar Musaddiq tare da kiran yaronsa yace ya kwashe number ɗin yanzun nan ai masa tracing. Amsa yaron nasa yay ya kwashe number ɗin ya fita da hanzarinsa………✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆
……A matuƙar hanzarce cikin tashin hankali yake bin umarnin ogan nasa. Ita daya shaƙama abu ya fara kinkima ya kai mota. Ya sake dawowa ya tattara duk abinda ya shafeta ya fita da su suma. Hatta kayan data jiƙa domin wankewa bai bari ba. Bedsheet da komai ya tattare katifa kawai ya bari a ɗakin. Cikin abinda bai wuce minti goma ba ya bar gidan da ita da komai nata. Cikin uban gudu ya nufi hanyar inda ogan nasa ya sashi maidata. Yayi nisa a tafiyarsa saƙo ya shigo masa. Sanin wayar da mutum ɗaya take da alaƙa ya sashi taka birki da sauri ya ɗan gangara gefen hanya. Titine da bai cika yawan kai kawon motoci ba saboda sabuwar anguwace sosai kuma a gefen gari ne ma. Idanu ya waro matuƙa sakamakon ganin saƙon da ogan nasa ya turo masa, tare da sauri ɓalle murfin wayar kasancewar ƙarama ce dama ya cire batteryn shima ya zare layin. Karyashi yay huɗu yay cilli da shi yana mai kwanciya akan steering ɗin da sauke nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yayi kusa minti biyu a haka sannan ya ɗago. Samraah dake kwance a baya tamkar gunkiya ya kalla, cikin cije baki ya ɗauke kansa. Motar yay ƙoƙarin sake tadawa akai knocking glass. Da wani irin bala’in sauri ya kalla gefen nasa, dan motar tinted glass ne da ita shiyyasa. Yasan wanda yake ta wajen bai ganinsa, amma shi yana ganinsa. Ganin kamar babu wani alamun kasancewar sa jami’in tsaro ya sashi sauke gilashin a hankali. Matashin saurayi da bai wuce sa’ansa ba ya ɗan sake duƙowa da faɗin, “Barka oga. Badai wata matsala bace ba ko?”.
Murmushi yay shima cikin sauri ya ce, “Barkanmu. A’a babu komai na ɗan tsaya amsa kiran waya ne kawai. Nama gama yanzu zan wuce”.
“A to masha ALLAH, dama ina tunanin ko akwai matsala ne. ALLAH ya tsare hanya”.
Godiya ya masa yana ƙoƙarin maida gilashin kawai yaga an buɗe murfin gefensa an shigo. Da sauri ya juyo nan ɗin. Mutum ne garjejen gaske gashi cikin baƙaƙen kaya kamar shi. Sai dai wannan yasan ko’a mafarki sukai wasan kokawa ɗagashi zai dingayi yana nanawa da ƙasa. Amma cikin dauriya ya ce, “Malam lafiya kuwa?”.
“Itace ta kawo haka”.
Mutumin ya faɗa a gadarance. Sai kuma ya sa hannu ya zare key ɗin motar yana faɗin, “Fita ka koma baya”.
“Na koma baya kamar ya? Ni da motata ka shigo min babu wani neman excuse kace kuma na fita na koma baya. To kai a wa kuma?”.
Uffan mutumin baice da shi ba. Sai ma ɗora masa bindigar daya zaro a jikinsa yay a saman cikinsa. Da sauri saurayin ya kalla bindigar, cikin son ɓoye tashin hankalinsa amma yana ta son bayyana kansa ya ce, “Malam miye kuma na bindiga anan?”.
Shi dai bai tanka masa ba. Sai ma ƙoƙarin saƙala yatsarsa yake akan kunamar bindiga ɗin, shima sai kawai ya buɗe motar ya fita zuciyarsa na wata irin bugawa da sauri. Turus yayi jikinsa na tsuma ganin zuƙa-zuƙan motoci har biyu baƙaƙe wulik, ga Samraah ana ƙoƙarin sakawa a ɗaya. Sai garadan maza har uku irin wanda ya titsiyesa a mota tsaitsaye da bindigu suma. Yana ji yana gani haka ya shiga bayan motar dan dolensa, saboda babu makami ko ɗaya a tare da shi. Kodama akwai ai sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Sannan waɗan nan kam sunfi ƙarfinsa, dan yama riga ya sadaƙar kawai jami’an tsaro ne su ɗin.
Shima abu suka shaƙa masa, a take ya sulale sai barci. Daga haka bai sake sanin a wace duniya yake ba sai farkawa yay ya gansa a inda bai taɓa sani ba. Dan ɗaki guda shima aka ajiyesa shi kaɗai. A yanzu kam hankalinsa ya fara tashi ƙololuwa. Dan ya fahimci ba ƴan sanda bane ba. To ko ogan nasa ne yasa akai masa haka? Amma mizaisa yay hakan kuma?. (Ka nema ɓata masa aiki mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya ayyana masa. Kansa ya dafe da ƙyar, dan gaba ɗaya jikinsa yay masa nauyi. Jin kamar jiri na ɗibarsa ya ɗan zame ya sake kwanciya yana mai lumshe idanunsa…
(✿(✿(✿)(✿)✿)✿)
A ɓangaren su Yaya Musaddiq kam anyi traicing number da Samraah tai kiransa an kuma gano inda suke. A take babu ɓata lokaci d.c.o ya shirya mutanensa. Duk yanda yaso su Mansoor su zauna sun dage da roƙon son binsu, ya fahimci koda ya hanasu zasu iya binsu a baya, hakan kuma akwai haɗari dan haka ya haƙura aka fita har dasu. Sunyi tafiya baifi ta mintuna uku ba layin ya yanke. Da sauri yaron d.c.o ya sanar masa.
“Oga akwai matsala fa. Da alama sun farga damu dan layin ya daina aiki. Hakan na nufin an ciresa a wayane, dan da yana kan wayar ko kasheta sukai zamu same su”.
Shima hankalin d.c.o ya tashi, amma sai ya dake shi cikin bada umarni ya ce, “Ku ƙarasa har inda layin ya dakata da aiki”.
“Okay sir”.
Ya faɗa yana yanke wayar. Su Mansoor basu san halin da ake ciki ba. Dan suna a ɗayar motar ne. Gashi kuma an cigaba da tafiya kamar yanda aka faro. Cikin abinda bai gaza mintuna talatin da biyu ba suka iso dai-dai wajen, dan gefen gari ne sosai. Sun sami mota kaɗai, amma babu alamar mutum. A take duk suka fito, sauran da basu san mike faruwa ba duk sun zagaye mota da bindiga. Wanda dai yake kamar ogan tafiyar ne ya sake kiran d.c.o ya sanar masa cewar gafa mota sun samu, sai dai basu sani ba koda mutum a ciki ko babu. Nan ma umarnin bincikawa ya basu, dan haka suka fara aikinsu, sai dai an hana Mansoor da Musaddiq zuwa kusa da motar duk da yanda suke a zalame.
Cikin kulawa da ƙwarewar aiki aka buɗe motar, sai dai me babu kowa a ciki sai kayan Samraah harda jiƙaƙƙun nan na botiki, sun cigaba da bincike motar tako ina, har suka samu nasarar ganin layin wayar a gefen titin an karyasa. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga kwaranyoma Musaddiq, hakama Mansoor ya duƙar da kansa jikin motar ƴan sandan kawai da alama shima dai kukan yake yi. Dan ba sai an faɗa musu ba komai ya tabbatar musu da mutanen nan sun sake samun nasarar tserewa da Samraah kuma.
Komai an tattara har motar aka wuce da su station. Wasu a cikin ƴan sandan kuma suka watsu a wajen ta cikin jejin har ma da cikin ƙauye dake ata wajen bisa umarnin d.c.o. Dan yana zargin wanda suka ɗauke tan ko dai sun shiga jejin, ko kuma sun shiga cikin ƙauyen domin tsira tunda har aka samu motarsu anan. Sauran ƴan sandan da suka wuce station nata ƙoƙarin kwantarma da su Musaddiq hankali. Dan a take sun nema bayanai daga companyn layin wayar da Samraah tai kiran Musaddiq. Za’a binciki dukan abinda akai da layin a kwanakin da suka gabata. Kai tunma daga randa aka sayesa. D.c.o ya tabbatar musu da in sha ALLAHU za’a dace tanan. Badan dai sun gamsu ba suka haƙura suka tafi, dan bayanan sai zuwa gobe za’a samesu…
(✿(✿(✿)✿)✿)
Tunda na farka daga nannauyan barcin dana kasa tuna lokacin farawarsa rufin ɗakin da nake kwance kawai nake iya kallo. Rufine dake tabbatar da ba’a ƙaramin gida nake ba. Dan yanayinsa da fentin bangon ɗakin kawai ya isa ya tabbatar da haka. Na jima a hakan kafin na motsa da ƙyar. Saman gado nake, tabbas hakan ne, na ayyana a raina cikin tabbatarwa da kaina. Komawa nai na sake kwantawa batare dana ƙarasa tashin ba. A take komai ya shiga dawo min dalla-dalla. Na zare wayar wanda ke gadina na kira Yaya Musaddiq, bayan ya ƙwace ya shaƙa min abu, daga haka ban sake sanin komai ba. Kenan dai ɗakkoni yay daga can gidan ya maidoni nan saboda gudun tonan asirinsa. Hakan na nufin babu rana balle watan komawa ga zuri’ata. A hankali wasu hawaye suka shiga silalo min masu zafi. Yau saura kwanaki takwas aurena, na tabbata duk hankalin wani masoyina ba’a kwance yake ba zuwa yanzu. Musamman Yaya Musaddiq, Mansoor, Hafizzullah… Wani murɗawa da marata tai ya katse min dukan tunani na. Faɗuwa gabana yay, Dan kuwa lallai lokacin prioud ɗina ne. Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un. Aiko akwai matsala, idan na kasance a wannan halin anan waye zai kula dani? Dan ba ƙaramar wahala nake sha ba har sai an mun allura, wani lokacin ma ai allurar taƙi sauka. Shiyyasa har shan magani nake a ɓoye dan kar jinin yazo. Abinka daba uwa ba balle ta gani ta kwaɓa, sai babu wanda yasan ina hakan har yanzu, kuma na jima inayin hakan, dan ko yanzu kusan watana na biyar kenan banyi ba saboda bana wasa da maganin a duk sanda nasan kwanakin period ɗina sun gabato, yanzu ma da ace akwai shan kawai zanyi shike nan bazai zo ɗin ba. Jin yaɗan lafa min na sake buɗe idanuna tare da yunƙurawa da ƙyar na tashi zaune. Ɗakine babba, sai dai babu komai a cikinsa sai iya katifar da nake kai, ashe ba gado bane, irin ƙatuwar katifar nan ce irin wadda ba’a sakawa a gado. A hankali na miƙe da ƙyar, windows ɗin ɗakin nabi na lalleƙa, sai dai bana iya gane komai sai dai ina iya jiyo magana mutane ƙasa-ƙasa. Hakan yasa na nufi inda nake ƙyautata zaton ƙoface. Bugawa na shigayi babu ji babu gani ina kuka. Sosai nake ma ƙofar bugun hauka da nasan dolene ya damesu. Amma ƴan iskan nan kamar kurame, ga wani irin murɗi da marata kemun na azaba, tun ina ƙarfin hali har na sulale ƙasa jikin ƙofar na zube. Tuni nayi sharkaf da zufa na azaba, ga jikina dake rawa, sai kuma uban kuka da nake ina kiran sunan ALLAH da fatan Yaya Musaddiq ya zo ya ɗaukan………✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙
…….Dukkanin bayanan da d.c.o ya buƙata an kawo daga companyn layin wayar mutumin. Dan haka yay zaman dubawa daki-daki. Sabon layi ne, an kuma buɗesa wata ɗaya daya gabata. Sai dai ba’a taɓa waya da kowa da shi ba sai number Yaya Musaddiq da Samraah ta kira. Sai kuma number ɗaya jal da sakwanni kawai aka dinga tura masa da ita. Dukannin sakwanin kuma a gajarce ne. Babu kuma wata ma’anar da za’a fahimcesu sai su da suka yi abinsu. A yanda kuma sakwannin suke kamar babu sanayya tsakanin wanda ke amfani da layin da mai tura saƙon da alamu suka tabbatar shine ya saka akai kidnapping Samraah ɗin. Abin ya tsayama d.c.o a zuciya. Amma dai ya sake bada number da ake tura saƙon itama a basu bayani a kanta. Nan ma sunce sai washe gari. Hakan yasa d.c.o sakawa ai masa traicing number ɗin kafin su kawo bayananta. Sai dai me sam layin babu shi akan network kwata-kwata ma. Hakan na nufin shima mai shi ya karya shi ɗin kenan ko ya yarda ko ya sauke. Wani irin dukan ɓacin rai d.c.o ya kaima desk ɗinsa. Dan ya fahimci wannan al’amari gaba ɗaya akwai rainin wayo a cikinsa. Duk kuma wanda ya shirya ɗauke yarinyar nan yana da basira ƙwarai da gaske. Dan bai ɗauketan ba sai da ya gama tsara dukkan hanyoyin ɓullewarsa daki-daki ta yanda gano wanene shi zai yi matuƙar wahala. Amma babu komai, ai dole ne ko yaya yayi kuskure. Da kuma wannan ɗan ƙaramin kuskuren kaɗai zasu iya kama shi in sha ALLAH..
Ranar da kansa ya zo gidan Abba ba yaransa ba. Lokacin kuma anyi sa’a duk suna gida. Hatta Nabil yazo weekend bai koma ba dan shi a hostel yake zama. Hafizzullah dai ya koma bisa tirsasawar Yaya Musaddiq. Da farko kicin-kicin Mum tai da fuska. Dan ita fa magana ta gaskiya zancen Samraah ɗin nan ya fara isarta. Zirga-zirgan da ƴan sanda ke musu kullum a gida yanzu ta fara cimata rai. D.c.o dake ta binta da kallo cikin dakewa ya ce, “Ina ganin muna gab da ganin Samraah in sha ALLAHU”.
Mum data gama cika taf cikin ɓacin rai ta ce, “Yo dama kune ke wahalar da kanku, duk ma inda take ai itace takai kanta. Dan ni nasan abokan iskancinta tabi wani garin kawai suke zaman shashancinsu a wani wajen. Amma yallaɓai duk kunbi kun tadama kanku hankali muma kun gagara barinmu mu huta. Haba, Samraah dai Samraah dai kamar wata allura ko sarƙar gwal ko diamond”.
“To amma Hajiya duk kin san da haka miyyasa baki sanar mana ba tun farko?”.
“Ni! Rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mata ba. Taya zan sanar muku kuwa yallaɓai. Ace kuma na laƙa mata sheri. Kadai san ɗan riƙo komi zaka masa ba tsira kake ba. Amma tun yaushe wannan yarinyar ke bin maza suna barin gari. Wane hotel ne bata san da zamansa a garin nan da wajen garin ba. Ai ni bana raba ɗayan biyu wannan yarinyar ta zubar da ciki sama da sau bakwai kuwa. Tunda nan zata dinga mana ihu da murƙususu wai mararta na ciwo, haka zakaga jini na binta, in ba zubda ciki ba kuwa mi tayi?”.
Kai kawai d.c.o ke faman jinjina wa. Yayinda Abba keta hararar Mum da mata alamar tai shiru amma matar nan sai da takai aya ta haɗiyi yawu bakinta kamar an ɓarka zani. Kallon Abba d.c.o yayi bayan ya gama ɗan rubuce-rubucen sa. “Amma Alhaji matsayinka na uba duk kasan da hakan baka taɓa ɗaukar wani mataki ba?”
Kafin Abba yay magana caraf Mum ta sake amshewa. “Matakin mi zai iya ɗauka a kanta yallaɓai. Bayan duk gidan nan babu wanda take shakka ko tsoro tafi ƙarfinmu. Sannan ɗan uwanta duk da saninsa take komai tunda shine kawalinta…..”
“Amma Hajiya ina magana da mijinki ne. Shi kuma nake son ya amsa min wannan tambayar.” kai Mum ta ɗauke gefe tana laɓe baki. D.c.o ya sake maida hankalinsa ga Abba da yanayinsa ya nuna sam baya jin daɗin abinda Mum ɗin keyi, amma ya gagara tsawatar mata. “Kai nake saurare Alhaji”.
“To yallaɓai ni mizance. Al’amarin ne gaba ɗaya akwai ruɗarwa. Amma ina yin iya bakin ƙoƙarina, sai dai kasan mu maza koda yaushe kana waje ba zaman gidan kake ba, shiyyasa ita ta fini sanin abubuwan”.
Shiru kawai d.c.o yay tare da zubama Abba dake ta ƴan kame-kame ido. Yaya Musaddiq da idanunsa suka cika da ƙwalla cikin sarƙewar murya ya ce, “Ranka ya daɗe Samraah bata taɓa aikata fasiƙanci ba. Sannan inba akan aikin nan nata ba zan iya rantse maka bata taɓa shiga hotel ba. Sannan ciwo da takeyi tana yinsa ne duk wata sakamakon al’adarsu ta mata. Amma inaga abar maganar nan, duk kuma inda take in sha ALLAHU addu’armu na biye da ita. ALLAH ya bayyanata, ya kuma bata kariya daga sharrin duk wani mai sharri”.
Maganganun Yaya Musaddiq sun sake saka Abba shiga wani yanayi, dan sai zufa yake kamar wanda ya haɗiyi kunama. Yayinda Mum keta ƙunƙuni ƙasa-ƙasa tana jin kamar ta rufe Musaddiq da duka. Sai dai babu damar hakan kodan d.c.o dake zaune. D.c.o ya gamsu da zancen Musaddiq, dan haka bai sake cewa komai ba ya miƙe. Miƙewar shima Musaddiq ɗin yayi batare da ya sake kallon inda su Abba suke ba ma, dan bai taɓa jin ɓacin rai mai tsanani akan abinda suke musu ba irin yau. Wani irin zafi yake ji a zuciyarsa game da su matuƙa….
★💫★💫★💫★💫★💫
Ciwo ne sosai yaci ƙarfina. Harma nake ganin ya ninka wanda nakeyi a baya. Ko hakan nada nasaba da yanda nasha magani wata na biyar kenan ma banyi ba. Sama-sama nake jin ana buɗe ƙofar. Daga haka ma nai ɗiff alamar hankalina ya gushe daga gangar jikina.
Da sauri wanda ya shigo ɗin ya koma baya ganin Samraah ta suma. Cikin tashin hakanli yake sanarma sauran ƴan uwansa, “Kai yarinyar nan fa kamar ta mutu”.
“Mutuwa fa?”.
Suka faɗa a tare suma cikin zaburowa. Komawa yay da gudu yana faɗin, “Kuzo to ku gani wlhy”. Duk binsa sukai cikin sassarfa suma. Wanda ke da ɗan yanayin hausawa a cikinsu ne ya ce, “Kamar suma tayi dai, Ayo ka kira oga Please, kasan dai irin gargaɗi da sharuɗɗan daya gindaya mana. Kar muce zamuyi shiru mu samu matsa”.
“Exertly maganarka gaskiya ne.” ya faɗa yana ƙoƙarin danna waya. Duk cikin harshen nasara suke maganar. Baifi mintuna biyu ba sai gashi ya dawo. Ya sanar musu oga yace duk su fita a ɗakin za’azo da doctor yanzu. Hakan kuwa akai duk suka fita, Ayo ya kulle ɗakin kamar yanda aka umarcesa. Bako a cika minti talatin cif ba sai ga driver ya kawo doctor. Ita kaɗai ta shiga ɗakin bayan Ayo ya buɗe mata. Sai da ta ƙarema fuskar Samraah kallo kafin ta kira Ayo ya taimaka mata suka maidata saman katifar. Duk taimakon daya dace tai ƙoƙarin bata, cikin ko ƙanƙanin lokaci ta farfaɗo. Sai dai tana buɗe ido ta dafe mararta da hannu bibbiyu tana kuka da murƙususu sosai. Da ƙyar ma take iya amsa tambayoyin doctor ɗin. Kasancewar likitar ƙwararriya ba’a wani ja da nisa ba ta fahimci matsalar Samraah. A take tai kiran wanda ya sakata aikin. Ta sanar masa zata turo sunayen magungunan da alluran da take buƙata yanzun nan a sayo a kawo mata. Yace okay ba damuwa ta tura. Rubutawa tai ta tura, sannan ta cigaba da bama Samraah taimakon daya dace kafin a kawo. Ba’a ɗauki lokaci ba Ayo yay knocking, izinin shigowa ta bashi. Ya shigo ɗauke da leda yace an kawone a bata. Amsa tai da godiya, shi kuma ya juya ya fita.
Duk zafin ciwo baya hanani shiga ruɗani a duk sanda za’amin allura. Yanzun ma hakane. Dan tunda na fahimci abinda take shirin mun na birkice mata. Duk yanda taso tankwarani kuwa ta kasa. Dan da gasken gaske na tsani allura harma da magani. Dole tai kiran wani wai yazo ya riƙeni. Nako tubure akan wlhy babu shegen gardin da zai taɓani. Ta ɗauka azabar ciwoce kawai ta sakani faɗin hakan. Sai da mutumin data kira ya shigo yana kawo hannu sukaga na rarumi handbag ɗinta zan kai masa duka sannan. Shiko yay baya da sauri yana yare da ɗaga hannaye sama. Ina kallonta tai murmushi da bashi umarnin fita. Ita kuma ta ɗauki waya, sai da ta daddana sannan takai kunne. Ina jinta sama-sama tana sanarma wanda ta kira cewar ina tsoron allura, na kuma ƙi yarda a riƙeni. Ban san mi aka gaya mata daga can ba na dai jita tana cewa okay. Daga haka ma ciwo yaci ƙarfina har tai allurar bamma sani ba saboda yanda marata kemin azaba har ina shiɗewa. Sai gani nai kawai ta haɗa kayan tafiya. Babu jimawa barci ya ɗaukeni, dama haka allurar kemin duk sanda akayita.
In dai aka min irin allurar nan cikin amincin ALLAH da nayi barci na farka shike nan. Amma abin mamaki yau saɓanin haka. Dan cikin dare na farka amma da sabon ciwon mara da yafi na farko ma. Ciwo sosai harna suma sau kusan biyu. Bamma san yaya akai ba naga doctor ɗin ɗazun a kaina. Tare da wata fuska dana taɓa sani sai dai na mance a ina nasan fuskar dan ciwo ya sakani galabaita dishi-dishi nake ɗan ganinsu, amma tabbas nasan fuskar wannan mutumin, kuma ya kamata na tuna ina ne na sanshi…….✍️
🥱Ya kamata ki tuno dai kam, koma fita a ruɗani muma Samraatu🚴.
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏
…….Yanzun ma dai barci ne mai nauyi sosai ya sake yin awon gaba dani batare dana gama tantance fuskar mutumin ba. Ban kuma farka ba sai washe gari da rana gatse-gatse. A yanzun ma dai ba farkawar daɗin rai bace ba. Dan still dai ciwon ne ya farkar dani ta yanda har sai da doctor ta sake dawowa. Yanzun kam naga alamun ruɗanin yanayin nawa a fuskarta itama. Dan bayan ta ɗan duddubani fita tayi tana danna waya, da alama magana take son yi da wani…
Bata wani jima sosai ba ta sake dawowa. Allurar dai ta sake fakar idona tamun, sai dai da alama tamafi ta jiya ƙarfi. Dan ko minti biyu cikakku banyi ba na sake komawa barci, daga haka ban san wainar da ake toyawa ba kuma…
A ɓangaren Doctor bayan tama Samraah allurar barci ya ɗauketa babu jimawa wanda tai kira a waya ya iso. Kamar yanda ta shawarcesa da kai Samraah asibiti ya amince. Sai dai da kansa ya nuna zai kaisu asibitin data tabbatar masa akwai dukkan tsaron da suke buƙata. Dan ya sanar mata alaƙarsu da yarinyar ta yanda hankalinta zai ɗauka bawai ainahin gaskiyar sato ta ko kwatota ne ma oho musu ba. Ita kuma jin wanda ya saka aikin yasa bata wani damu ko ɗarsa zargi a ranta ba take bata duk wannan kulawar. Dan tun jiya da tasan yana a garin Abujar nan take jin wani farin ciki, tasan kuma a dalilin aikin yarinyar nan zata iya haɗuwa da shi, duk da dai yanayin ciwon yarinyar yana buƙatar aje da ita asibitin da gasken..
Sun isa asibiti batare da wata matsala ba. An kuma yima Samraah dukkan binciken daya dace. Dan har dare suna a asibitin, sai kusan goma suka gano matsalarta. A take suka haɗo duk abinda zai taimaka mata a matakin farko kafin ai mata abinda ya dace. Gidan suka sake maidota aka saka mata drip kamar yanda ya buƙata, daga haka suka fice aka barta da masu tsaronta.
Tunda suka shigo katafaren ginannen gidan take jin jina kai da sakin kurmushi. Duk da tasan wannan ba komai bane daga mamallakin gidan. Amma dai tayi mamakin yanda yaron nasa ya bata labarin an ginashi cikin ƙanƙanin lokaci tare da wani ma a Kano. Duk da kuwa tasan yana da gidaje sosai a Abujar nan da basu da adadi ma musamman ga ita da ba kowanne ta sani ba, amma tasan wannan ɗin na musamman ne gaskiya. Har kusan ƙofar falon ya kai kafin yay parking, cikin murmushi yay mata nuni da suje ciki. Babu musu ta ɓalle murfin motar ta fita, sai wani taku take cikin yauƙi da yanga. Tun a takun farko na shigowa falon wani sanyi da ƙamshi mai sauke gajiya suka ratsata. Ta wani shaƙi iska da dogon hancinta ta fesar a slowly. Ko makaho yasan falon ya haɗu tamkar mai shi. A hankali ta ɗan kai dubanta ta gefen damarta da take jin ƙamshinsa yafi yawaita a tanan. Shine kuwa zaune cikin kujera 1sitter da laptop a saman ƙafafunsa daya miƙe saman Centre table. Yanda keyboard ɗin laptop ɗin ke bada sautin ƙara zai tabbatar maka da typing abu yake. Da alama kuma mai matuƙar muhimmanci ne. Dan gaba ɗaya hankalinsa na kan screen ɗin, kuma yana dannawa ne da ɗan yanayin sauri na ƙwarewar sabo da hakan. Ƙananun kaya ne a jikinsa kamar ko yaushe. Dan sune suturar da yafi sakawa sai ko suit kamar dangin yahudu. Sai dai kasancewar wandon nasa kaɗan ya zarta gwiwa ya bama ƙafafunsa damar bayyana samɓal. Har suka kai zaune bai kallesu ba balle ya nuna yasan da shigowarsu. Sai da ya ɓata kusan mintuna shida curr sannan yay magana batare da ya kallesun ba yanzu ma.
“Any problems?”.
Ya faɗa a daƙile cikin silent voice ɗinsa. Hayatu ne ya jin jina kai yana mai sake sakama kansa nutsu da gyara tsaiwarsa cikin nuna girmamawa sosai. “Eh to Sir dama dai akan batun yarinyar can ne. Kasan tun jiya na sanar maka abinda ke faruwa na rashin lafiyar da take ciki, har kace Dr Rumaisa tazo ta dubata. To tun dai jiyan tayi duk abinda ya dace amma ba’a dace ba. Ɗazun dai dole tasa mukaje da ita asibiti domin a bincika matsalar ta shine dama muka zo sanar maka dan yan zun ne muke dawo wa…”
Shiru kamar bazai tanka ba, sai da ya mula dan kasa ya furta, “Uhum ina sauraren ku”.
Da sauri Doctor Rumaisa tai tsigil ta ce, “Ranka ya daɗe Good evening”.
Bai amsa mata ba, illa ɗan jinjina kansa da yay kawai alamar amsawar kenan batare da ya kalleta ba kuma. Taji ba daɗi, dan ba haka taso ba. Amma sai ta daure ko za’a dace ta cigaba da faɗin, “Gaskiya yarinyar akwai babbar matsala a tare da ita. Da alama tun kafin yanzu tana fama da pain a duk sanda zatayi prioud, kuma yana mata tsanani. Maybe hakan ne ya jata ta dinga shan maganin hana zuwan prioud ɗin a duk sanda lokacinsa yayi, shine ya haifar da matsalar wannan karon ɗin. Dan sai wahala kawai take sha amma jinin yaƙi ya fita, yanzu dai in sha ALLAHU na mata dukkan abinda ya dace akoda yaushe zai iya fita ɗin, sai kuma ta kiyaye cigaba da shan wancan magungunan inba haka ba zatama kanta illa. Dan a yanzu hakan ma sai an ɗorata akan magunguna masu ƙarfi sosai da zai dai-daita mata komai, sai dai sunada wahalar samu maganin dan sunada tsada gaskiya, ba kowanne pharmacy zaka iya ganinsu anan ba ma”.
A yanzu ɗin ma dai babu alamar zai amsa dan kamar ma bashi takema bayanin ba. Hakan yasa Hayatu bata amsar dan yasan Maash bazai sake magana ba kuma. “Sir zan ƙarasa komai in sha ALLAH. Dama dai na kawota ne kawai ta maka bayani yanda zakafi fahimta.” daga haka yayma Dr Rumaisa nunin ta miƙe shima yana tashi. Sam ba haka taso ba, dan fuskarta ma ta nuna. Ta kafe Maash da kallo tana mai fatan ya sake cewa wani abu koda bazai ɗago ɗin ya kalleta ba, dan dama ita ta matsama Hayatu akan ya kawota ta masa bayani da kanta. Amma sai bai ko kallonsu ba aikinsa ma ya cigaba dayi kamar yanda suka shigo suka samesa. Sai ka ɗauka ma ya manta da su a falon ne tsabar halin yarfin mutumin nan.
Suna fita ta kalli Hayatu rai ɓace. “Amma ba haka mukai da kai ba Hayatu?”.
“To yaya kike so nayi doctor. Kin san dai halin Boss ba sai na sake tisa miki ba. Ba yau ne kika fara masa aiki ba kuma. Shiyyasa naso ma ki bari muyi komai mu gama iya mu kaɗai tunda ba gagara zai yi ba. Tunda kuma shine yasa kizo zai buƙaci ku haɗu kafin mubar garin. Yanzu dai kiyi haƙuri a madadinsa. Kiyi kuma magana da pharmacy ɗin da kikace zasu turo maganungunan nata. Sannan ki bada account number da za’a saka kuɗin.”
Gaba ɗaya fuskarta ta sauya da tsantsar damuwa da ɓacin rai. Duk da dai tasan zata shaƙi kuɗi a aikin nan, dan ko Hayatu hannunsa a buɗe yake tamkar boss ɗin nashi a wajen ƙyautatawa. Kamar zatayi magana sai kuma dai ta shanye da ƙyar, gaba tai idanunta na cika da hawaye ta buɗe motar da suka zo ta shiga. Murmushi Hayatu dake binta da kallo yayi, acan ƙasan ransa kuma yana jin tausayinta. Dan yasan tamkar ta ɗebo ruwan dafa kanta ne dakon soyayyar wanda soyayyar uwa kawai da familynsa ya sani sama data wata ɗiya mace a wannan rayuwar. Shi kansa har mamaki yake anya ogan nasa nada lafiya kuwa, dan shi dai zai iya rantsewa, bayan abokan huɗɗa dana aiki be taɓa ganin wata mace a gefen ogansa ba da sunan yana mata kallon mace mahaɗin rayuwa ko wani ɓangaren jin daɗin duniya. Shi dai kawai neman kuɗi, ina zaka business ina ka fito business. Abinda kawai ke birgesa da shi neman kuɗi bai taɓa shagaltar da shi bautan ALLAH ba. Ga shi dai nan da zubin tsagerun mutane, amma batun ibada babu wasa.. Motar ya shiga shima, yay mata key suka fice a gidan bayan securitys dake gate ɗin sun buɗe masa. Lallashi da daɗaɗan kalamai ya dinga gayama Doctor Rumaisa, acewarsa ta cigaba da addu’a, idan ALLAH ya ƙaddara Maash mijinta ne sai ya aureta. A hankali ta saki murmushi kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta, shi ko ya girgiza kansa dan shima ya san dai gangan yake faɗa, dan ga wata can ma a Lagos data fita wayewa da komai ana tirƙa-tirƙa bayan na bayan fage da iyayensu suke faman masa tallarsu wasu ko sune da kansu suke masa tallar kansun. Shifa yasha ganin ballagazayen wasu matan na kuka akan Maash ko kwanciya yay dasu idana bazai aurensu ba, amma ko kallonsu bayayi ma balle su samu karɓuwa. Gaskiya kuɗi a mafi yawan lokuta fitinarsu tafi alkairinsu yawa. Shi shaida ne. Dan shi kansa ma da bashi ke da dukiyar ba yana cin azaba balle shi Maash ɗin da kansa. Aure ma da ƙyar akai masa a shekarar data wuce, yanzu haka matar nada ciki, amma kullum cikin faɗa suke akan rashin lokacinsa. inaga kuma matar mai gayya mai aiki da ake fatan ta shigo, ai duk wadda zata zauna da shi a matsayin aure kam sai ta jajirce, ko dai ta dinga binsa duk inda zai je itama taji a jikinta dan yawon ma ba hutu bane, ko kuma ta cigaba da hakuri da abinda ta gani kawai…….✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕
……Har gidansu dake anan Abujar Hayatu ya maida doctor. Koda ya dawo a inda suka barsa nan ya sake samunsa. Yanda yaga fuskarsa tai kicin-kicin sosai ya sashi sake nutsuwa, kamar yaron da yayma mamarsa laifi kafin ya tafi makaranta. Sun kai tsahon minti uku a hakan yana satar kallonsa, shiko yana aikinsa kamar bai san da shigowar tasa ba. Sai can a bazata cikin daƙilalliyar muryar nan tasa dake fita silent ya furta, “Bani black tea”.
Da sauri Hayatu ya amsa da, “Okay Sir” yana nufar hanyar kitchen. Bai wani jima sosai ba sai gashi da abinda yace masan. Lokacin da yake amsa ya ɗan kallesa, hakan yasa Hayatu saurin rissinar da idanunsa, dan ko motsi ogan nasa yayi yasan abinda yake nufi. Shayinsa ya kai baki ya ɗan kurɓa sau biyu sannan ya sake kallon Hayatun. “Minace maka akan yarinyar nan?”.
“Sir wlhy ba laifina bane. Kasan tanada shegen naci, nunawa tai ma idan ban kawota inda kake ba a jiya da ciwon yarinyar ya motsa bazata taɓata ba”.
“Sai akace ita kaɗaice likita kuma?”.
“Am sorry Sir. Anyi kuskure amma za’a kiyaye in sha ALLAHU”.
Shiru kamar bazai sake tanka masa ba. Har sai da ya gama shan shayin ya ajiye kofin yana miƙewa sannan ya furta, “A dawo da yarinyar nan gidan”.
Wani mugun waro idanu Hayatu yayi yana binsa da kallo. Sai dai shi bai ko waiwayo ba har ya gama haye stairs ɗin da zai kaika inda bedroom ɗin sa ya ke. Jagwab Hayatu ya zube a kujera tare da faɗin, “Boss rigimarka tafi ta sojojin yaƙin basasa wlhy. Kai komai idan zuciyarka ta raya maka sai kace ayi baka tuna abinda zai iya zuwa ya dawo. Yarinyar da ake nema ruwa a jallo kawota gidan nan ai haɗari ne, mun ɗakkota da ga Kano jiya ALLAH ya somu mun fito lafiya, yau kuma kace a kawota nan. Mu kuma da muka zo jiya zamu iya wucewa akoda yaushe ya za’ai da ita a gidan nan da ko ƴan aiki duk maza ne?” ya zabga tagumi bayan ya gama sambatunsa babu mai bashi amsa. Sai dai yasan ko giyar wake ya sha bai isa ƙin bin umarnin nan ba kuma. Dole ya miƙe ya tattare kayan daya baza falon ya koma tsaf. Shima ficewar yayi domin duba ɗakin daya dace a saka yarinyar idan sun ɗakkota…..
💞💥💞💥💞💥💞
A hankali nake buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi. Hakama jikina jinsa nake tamkar ba nawa ba dan yayi min jingim. Ga laima ina jina kwance a ciki kamar wadda tai fitsarin kwance. Hannuna na ɗaga da ƙyar nakai inda nake jin laimar na taɓo, da ƙyar na ƙara ɗago hannun domin ganin minene. Duk da dama shi ɗin nai zaton gani sai da gabana ya faɗi, nai wani kalar rumtse ido da ƙarfin gaske ina cije lips ɗina shima da ƙarfi kamar zan huda su. A dai-dai nan naji ana taɓa ƙofar, sake faɗuwa gabana yay, nai ƙoƙarin yunƙurawa dan na tashi zaune amma har an riga an buɗe. Rashin ƙarfin jiki yasa na kasa jawo blanket ɗin dake a gefe, duk da ma wani sashe na zuciyata mamakin ganin kuma a inda nake ya kamani. Dan nan ɗakine mai ɗauke da kayan gado complete, sannan yafi wancan ƙyau fiye da zaton mai zato ma gashi ƙato sosai.
Mutumin nan da sukai min allura tare da doctor a daren jiya ne ya fara shigowa. Sangamemen ƙato biye da shi da da ledoji a hannu. Muna haɗa ido da shi na kauda kaina. Shima nasa kan ya kauda, batare da ya sake kallona ba ya furta, “Waɗan nan naki ne zaki iya amfani da su. Bayan su duk ma abinda zaki iya buƙata akwaisa a ɗakin. Likitarki ta gama aikinta, har magungunanki gasu anan ta kawo”. Daga haka ya juya ya fita. Da kallo na bisa zuciyata na wani irin kai-kawo. Kenan dai da gaske mutanen nan ne sukai kidnapping ɗina. Sune kuma suka saka ake bibiyata? Hakan na nufin sun san na ɗauki wannan video recording ɗin dai kamar yanda nai tunani?. (Ya ALLAH ta yaya hakan ta kasance?) Na faɗa a zuciyata, a zahiri kam ina mai runtse idanuna dake cike da nauyi har yanzu. Na kai tsahon mintuna goma ina faman tunani kafin na yunƙura na tashi da ƙyar, dan dama yanayin da jikina ke ciki yasa bance da shi komai ba da ya shigo. Yanda na jiƙa wajen da jini ya bani tsoro sosai, kamar wadda tai ɓarin ciki jama’a, haka dai na daure na sakko, sai dai ganin an saka min abune a inda na kwanta ɗin ba ainahin gadon na ɓata ba na ɗan saki ajiyar zuciya. Abin mai kama da leda-leda katifa-katifa na tattare na ɗauke. Cikin ɗingisa ƙafata dake ciwo na nufi hanyar da nake ƙyautata zaton toilet ne. Shi ɗinne kuwa, sai dai ya tsaru matuƙa, dan da za’a bani zaɓin wajen kwanciya maybe na kawo katifata nan na shimfiɗa, bawai dan yafi ko ina ƙyau ba, kawai dai ya birgeni ne shima. Duk da rashin ƙarfin da nake ji haka nai ƙarfin halin gyara jikina yanda ya kamata, nai wanka da ruwa mai zafi sosai. Sai a lokacin kuma hankalina ke neman tashi tuna bani da pant balle azo ga batun bad, sai dai tuna abinda yace yasa na fito. Ledojin da suka ajiye na shiga buɗewa, ta farko abinci ne, ta biyu kuwa kayan ciye-ciye ne. Sai ta ƙarshe ce ke ɗauke da kayan sawa, a ciki na samu pants da bad ɗin. Duk da naji wani iri da ganin hakan banda damar ƙorafi, ɗauka nai kawai na koma ciki na kimtsa jikina na dawo ɗakin. Kayan na sake buɗewa na ɗauki doguwar riga na saka batare da na damu da sanin sauran abinda ke ciki ba. Bana jin yunwa, dan in har ina a wannan yanayin ban cika son cin abinci ba, sai masifaffen kwaɗayi kamar sabuwar mayya. Dan hankalina duk yana akan naman can dana gani, ko naso basarwa kuma bazan iya hakan ba, garama naci bai nak yanda zan samu ƙarfin sauke musu abinda ke kaina. Zama nai kuwa nacisa sosai har saida naji na ƙoshi, na fiddo magungunan dana gani na duba duk yanda aka tsara shansu suma nasha.
A yanzu bana buƙatar zaman yin dogon tunani, tunda na fahimci a hannun waɗanda nake saɓanin kwanakin da suka gabata da nake canki canka da rashin tabbas. Yanzu babbar damuwata ahalina. Na tabbata duk inda Yaya Musaddiq da Mansoor suke hankalinsu a matuƙar tashe yake kodan kiran da nai a waya. Amma ina fatan askine yazo gaban goshi, dan nayi alwashin komi mutanen nan zasumin bazan taɓa basu video ɗin nan ba ko faɗa musu a inda zasu samesa, iyaka dai suce nima zasu halaka ni, ban damu ba, dan hakan da zasu yi shine mafi girman kuskure da zai tona asirinsu insha ALLAHU.
Shan maganin ya ƙara saka min jin daɗin jikina. Sai dai damuwa data kasa ɓoyuwa a kan fuskata. Sai gajiyar zama waje ɗaya daban saba ba. Nida nake yini tsaye kan ƙafafuna ina faman bautar aiki, garama idan office naje akan ɗan samu sassauci tunda shi kusan daga zaune ne. Motsin sake buɗe ƙofa da naji ya sakani tashi daga kwancen da nake cikin kujerar ɗakin, ɗan kwalin abayar naja na rufe kaina zuwa ƙirjina da ƙyau. Dai-dai nan aka ƙarasa shigowa. Mutumin ɗazu ɗinne dai, daga bakin ƙofa ya tsaya yayinda ni kuma nake kallonsa a tsiwace. Dan sai yanzu ne komai ke dawo min game da sanin da nai masa. Tabbas shine yaron mutumin nan mai kama da ƴan daudu ko nace ɗan daba ma ko sara suka oho duk ya cancanta, shine kuma ya kira da PA ɗinsa a ranar wancan taron. Nai saurin kauda kaina ina ƙoƙarin dai-daita fuskata da jikina. Tsahon mintuna kusan biyu ɗakin shiru, kafin cikin son nuna jarumta na furta,
“Dama kune kukai kidnapping ɗina?”.
Maimakon bani amsar dana buƙata sai jinai cikin bada umarni ya ce, “Zaku iya shigowa”. Baima ko gama rufe baki ba kuwa garadan samari biyu suka shigo. Ko namiji yaga wannan samudawan dole ya ji tsoro balle ni, amma dai nayi ƙoƙarin dake zuciyata ban bari tsorona ya fito a saman fuska ba. Sai dai faman haɗiyar yawu nake da ƙyar zuciyata na faman kai da kawo a cikin ƙirjina. Umarnin tashi suka bani, bani da ikon yin musu ko dan bindugun dake a hannunsa, ɗaya daga cikinsu ne ya koma ta bayana ya ɗauro ƙyalle a saman idona, zanyi magana ya ce, “Shiii!! Young Lady, inba hakaba harsashi ya rufe miki baki”.
Yawu na sake haɗiyewa mai kauri, daga haka ban sake magana ba har suka bani umarnin tafiya bayan sun saka min wani abu a hannu na riƙe. Tafiya kawai naji munayi batare dana san ina muke nufa ba, amma dai baka jin hayaniyar komai ko’ina tsitt sai kukan tsuntsaye daga ɗan nesa damu kaɗan. Da ace hannuna babu handcuffs wlhy sai na cire abinda aka rufen fuskar komai ma za’ayi ayi. A haka naji mun shigo wani waje mai shegen sanyi da ƙamshi na musamman. Nanma mun ɗan yi tafiya kafin naji mun tsaya cak a inda ƙafata ta taka wani lallausan abu………✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆
……Kamar yanda d.c.o ya nema washe gari an sake kawo masa bayani akan ɗayan daya buƙata. Sai dai abin baƙin ciki shima layin na taƙaitaccen lokaci ne kamar wancan, ba kuma a taɓa kiran wani da shi ba. Nasara ɗaya da suka samu itace na shi wanda yay register ɗin layukan duk mutum ɗaya ne. Kuma a lokaci ɗaya yayisa. Sun saka a nemo musu shi a duk inda yake. Hakama abokin masu napep an samu nasarar cafkosa a safiyar yau. Bayan kamar awa biyu da kawosa police station ɗin aka kaisa office ɗin d.c.o kamar yanda ya buƙata. Sai da ya gama masa kallon tsaf daga sama har ƙasa kafin ya tura masa hoton Samraah dake gabansa.
“Kasan wannan?”.
Ya faɗa kansa tsaye idanunsa ƙyam akan saurayin. Hoton saurayin ya ɗauka ya kalla na kusan sakan talatin, ɗagowa yay ya kalla d.c.o sai kuma ya rissinar da kansa yana ɗan jinjina kai. “Nasanta ranka ya daɗe. Sam-G ake kiranta, tana gabatar da shirin matasa kuma ina ɗaya daga cikin fans nata da shirin baya wuceni ta redio ko shafukanta na sada zumunta musamman YouTube da ake ɗora shirin, nakan je na kalla videos ɗinta”.
Kai d.c.o ya jinjina masa da faɗin, “Masha ALLAH. Minene sana’ar ka?”.
“Direban napep ne yallaɓai”.
“Kozan iya sanin ranar goma ga watan nan kana ina? Da ga shida na safe har zuwa ƙarfe takwas?”.
Jimm yay irin na mai son tunano abu. Har kusan minti ɗaya sai kuma ya ɗago yana girgiza kansa. “Na manta yallaɓai. Saboda kwanakin sun ja da yawa”.
“Uhhm yayi ƙyau” d.c.o ya faɗa yana kallon yaronsa. “Azo da yaran nan su duka”.
Kai yaron nasa ya jinjina cikin girmamawa. Fita yay babu jimawa sai gashi ya dawo tare da samarin farko da aka fara kamawa. Yanda suke kallon saurayin haka yake kallonsu. Duk da babu duka ko zagi da akai musu zaman waje ɗaya da ɗan karan Dauda yasa duk sunyi wujiga-wujiga dasu….
“Kasan waɗan nan?”.
“Eh yallaɓai na sansu, su duka abokaina ne. Tare ma muke harkar napep ɗin ma.”
“Kace ka manta mi kayi ranar goma ga watan nan da safe ko?”.
“Eh yallaɓai a gafarceni”.
D.c.o baice dashi komai ba. Sai abokinsa ya kalla ya ce, “Kai tuna masa”.
Kai tsaye abokin nasa ya ce, “Kazo ɗakinmu ni da ƙanina bayan sallar asuba dan gari ma bai gama haske ba. Kace na baka makulin mashin ɗin Imran zakaje amso saƙo tasha kai taka tayar na gareji dan naka babur ɗin ya samu matsala tun jiya sai barinsa ma kayi ya kwana a gareji kan yau zaka kai musu tayoyi da zasu canja maka. A gaban ƙanina Isa akai komai kuma”.
Da sauri ya dafe kansa ya ce, “Tabbas anyi haka Salisu. Tabbas abinda ya faɗa gaskiyane yallaɓai, amma a gafarceni inada yawan mantuwa ne wlhy. Na amshi mashin ɗin, abinda nace kuma zanyi naje nayi da shi”.
“Masha ALLAH haka muke son ji ai dama. Ina ka kai yarinya to? Sannan waye ya sakaka kidnapping ɗinta? Ko raɗin kanka ne kawai?”.
“Ya salam kidnapping kuma? Ni banyi kidnapping kowaba ranka ya daɗe. Duk wanda ke tare dani kuma yasan wannan ba aikina bane ba inada sana’a. Taya ma kuma na rasa wanda zan ɗauka sai Sam-G”.
“Ƙarya kake yi, a waccan ranar ba gareji kaje da napep ɗin abokinka ba Yakasai kaje layin gidan su Samraah. Kai zaman jiranta na kusan mintuna talatin da huɗu. Zata iya yiwuwa kasan dama zata fito a lokacin ne. Dan haka tana fitowa da shirin tsaida abin hawa kazo ka ɗauketa. Ka tsaya a dai-dai fita anguwar ta titin bayansu gaba ɗaya. Ka cire wayarta da facemask da eyeglasses ɗinta ka ajiye saboda maybe kana tunanin za’a iya ganeka ko kuma wanda ya saka ka aikinne ya baka umarnin yin hakan. Ɗan saurayi ban kawoka nan dan ka raina min hankalina ba. Amma kana da zaɓi guda biyu. Fitomin da komai a yanda yake dan ka samu sassauci ko cigaba da raina min hankali na saka ka faɗa ta dole wanne ka zaɓa?”.
Ɗan jimm yay na wasu sakanni, sai kuma ya sauke numfashi da faɗin, “Zan faɗa maka gaskiya yallaɓai…….
🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟
Cikin fisgar zaren da suka ɗaure min ido naji sun warwaresa. Har sai da na ɗan ciza lips saboda yanda naji zafi, amma dai na dake ina mai buɗe idanun nawa a hankali, dan zan gama da ogansu ne sannan na dawo kansu shegu masu suffar bakaken aljanun kan kuka. Sosai gabana yay masifar faɗuwa dan kai tsaye idanuna akan mutumin dake zaune cikin kujera yay crossing ƙafafunsa idanunsa a tab.. dake a hannunsa suka sauka. Ga wani daddaɗan ƙamshinsa da ya cika min hanci da gauraye falon gaba ɗaya. Fuskarsa ciɗin-ciɗin kamar bai taɓa sanin abinda ake kira dariya ba ko saƙon wani bala’i ya riskesa a yanzu. yauma akwai kitso a kansa guda biyu rak da suka zanu tamkar an zana a takarda dan zaka rantse ba hannu ya kitsasu ba, sai farin sirrin gilashi da ya zauna masa ɗaram a fuska tamkar an haliccesa da shi ne. Yatsunsa biyu ya ɗan juya, da sauri sangama-sangaman samarin nan da suka rakoni da bindiga duk suka fice aka bar abokin cin mushen nasa kawai. Sai lokacin ya ɗago ya zuba min cat eyes ɗinsa. Kallon ido cikin ido mukaima juna. A take naji ciwon marata na neman dawowa sabo fil, ba shiri nai saurin duƙar da kaina ƙasa zuciyata na wani kalar masifaffen bugu kamar zata faso ƙirjina ta fita. Amma cikin ƙarfin hali na murguɗa masa baki bayan na saukar da idanun.
Shima janye nasa yay cikin yanayin isa da ƙasaita. “Sit!” ya faɗa a daƙile yana maida kansa ga tab ɗin tasa. Duk da na gane dani yake banyi abinda yace ɗin ba har sai da yaronsa ya sake maimaita min a ɗan tsawace. Ta ƙasan ido na hararesu su duka, kafin na kai zaune saman lallausar kujerar falon, amma sai yaron nasa ya daka min tsawa da mun nuni da wai na zauna ƙasa. (Munafuki ɗan baƙin ciki) na faɗa a raina, a zahiri kam hararsa na sake yi sannan nayi yanda yace na zauna ƙasan carpet ɗin da ko makaho ya laluba yasan ya haɗu. Jikina na ɗan takure a waje ɗaya, na tallafo ƙafafuna duka da hannayena biyu idanuna na kallon carpet ɗin. Sai da kusan mintuna uku suka sake shuɗewa babu alamar zai sake magana, sai kuma a cikin daƙilalliyar muryar nan tasa ya ce, “Wa kike ma aiki a kaina?”.
Sosai tambayar tai matuƙar bani mamaki, har takai na ɗago na ɗan kallesa. Amma a mamakina bama ni yake kalloba, wasu files ne a hannunsa yan rubutu a ciki ya ajiye tab ɗin yanzu. A hankali na maida kaina na duƙar, nima sai da na kwashe wasu sakanni kafin cikin siririyar muryata da yanayin gafara na bashi amsa, “Ni nafi ƙarfin yima kowa aiki ai, dan ni ma ɗin gayyace”. Shiru baice komai ba, dan haka na cigaba da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa batare da tunanin zasu ji ni ba. (Ni ai nafi ƙarfin aiken wani, sai dai zuwan kai da kai. Dan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ai. Idan kuma baka san haka ba kaje kayi bincike. Ashe ma matsoraci ne, tunda har baka iya fito na fito sai ta YAƘIN SUNƘURU…)
Harara yaron nasa ya zuba min. Kafin cikin kakkausar murya ya furta, “Hattara dai ƴammata. Dan ba’a ado da furuci wani lokacin takobin yanka wuyan mai shi yake zama. Nan ba gidan jarida bane, fadar SARKI ce mai cikakken iko kike.”
Murtanin harar nima na maida masa ƙasa-ƙasa. Sai dai na gagara iya cewa komai saboda yanda ogan nasa ya tsareni da shegun kaifafan idanunsa na maguna. Tsahon lokaci falon shiru, yayinda tuni ya janye idanun ya maida ga abinda yake yi. Sai zuwa can a wani irin daƙile ya furta, “A duk sanda wani ya nema shiga min hanci nakan ji farin ciki da mazantakar fyatosa. Shiyyasa abinda yafi birgeni a duniya sune mutane irinki masu taya business ɗin da bai shafesu ba. Well ba tabbatar miki da ni waye yasa nasa a kawoki nan ba, dan inada tarin ayyuka na kai da kai matuƙa. WAYE YA AIKO KI WAJENA?”.
Takaicin maganganunsa yasa bamma san sanda na furta, “Umarnin kaina nake bi ni, na kuma faɗa ai”.
A harzuƙe yaronsa ya katseni da faɗin, “Be careful ƴammata. Walƙiya ba tana nufin ado ne kawai ga sararin samaniya ba. Takan zama gargaɗi ga ma’abota shagala ne. Jirgin ƙasa duk ƙawatuwarsa a hanyarsa kawai yake iya tafiya, saɓanin hakan faɗuwar baƙar tasa zaiyi ta yanda ko kufansa bazai moru ba balle ma’abota shiga cikinsa. Ki dinga bambance tsakanin sama da ƙasa a duk lokacin da kikai tunanin hawa tsani da tunanin taɓa rana ko farin wata. Dan batun wanda zashi sama ya taka leda zance ne kawai irin na masu iya magana.”
Baki na laɓe tare da watsa masa harara ta ƙasan ido. Cigaba yay da faɗin, “Kina da zaɓi biyu, bada abinda ke hannunki ki koma ki cigaba da rayuwarki cikin salama, ki kuma sakama ranki baki taɓa ganin komai ba a wacan ranar, ko nuna taurin kai ki dawwama anan har ƙarshen numfashinki, kin buƙaci 500m an baki rabinsu, amma ke kin kasa cika naki alƙawarin duk da an tabbatar miki idan kin bada za’a baki sauran 250m ɗin. Ke kin san kuwa dawa kike tare ana?”.
Yanzu kam sosai na ɗago a razane matuƙa, tare da wurga masa hararesa dan naga yama fi ogan nasa zaƙewa. A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?……..✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚
…….A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?. Aikin naku ya wuce kisan kai da kidnapping harda sharri kuma. Lallai tatsuniyar gizo da ƙoƙi kenan young man, kasan kuwa gaibu ce dan hikimace kawai irin ta masu iya zance da rubuta hikayoyi. Idan har ka yarda ba’a mutuwa a dawo, to ka ɗauka abinda duk yake a hannun Samraah Gwarzo mallakinta ne ita kaɗai, ko a mafarki bazan taɓa cinikayyarsa da wani ba. An gaya maka nima faƙiriyace bana neman na kaina ne da zan zauna neman a bani fansar kuɗin jinin mutane akan video?. ALLAH ya sawwaƙe, Banyi lalacewar baƙar tasa ba ai, banga kuma wata dukiya da wani zai tara taja hankalina ba dan nima dai kasuwancin nan inayinsa. Ɗan jarin nan na dubu ashirin da ake rainawa na tara wataran sune zasu koma miliyan dubu ashirin ɗin. Dan haka kuma nema wanda ya amsa kuɗinku tun wuri amma ba ɗiyar Abdul-wahab ba. Idan kuma kaine ke yawo da hankalinsa ka faɗa masa gaskiya inma dan kaga baya jin Hausa ne, oho can dai muku matsalarku ce ma wannan dai. Dannni idan har Yaya Musaddiq da Mansoor na numfashi a duniya na maka alwashin nan da kwana takwas iyanzu ina can a tsakkiyar dangina suna shagalin taron bikin aurena tare da ni, yayinda ku kuma zaku kasance a police station kuna amsa tambayoyi”.
“Yaro bai san wuta ba sai ga taka”. Yaron nasa ya faɗa
“Babba bai san yaro ba sai ya latsa”.
Na bashi amsa nima a kausashe ina sake balla masa harara kamar manyan idanuna da ke nuna yanayin bana jin daɗi zasu zubo ƙasa. Juyawa nai shima ogan nasa zan hararesa sai naga ya zuba min ido kamar wanda yay zurfi a tunani. Ban fasa hararar tasa ba, dan haka na maka masa kawai na ɗauke kai ina ƙunƙuni ƙasa-ƙasa (Garama ku sakan tunkan kuja a saka sunanku cikin jerin manyan ƴan ta’addan duniya dan wlhy tona muku asiri zanyi ni babu ruwana).
Tsawa yaron nasa ya daka min alamar ya jini, duk da na tsorata amma mai kicin-kicin da fuska naƙi nunawa. Kuma bakina bai bar motsin ƙunƙuni ba. Wani shegen murmushi ogan nasa da tun maganar farko da yayi bai sake nuna yama san da zaman mu a falon ba ya saki. Tare da lumshe idanunsa cike da salo luuuu ya kuma buɗesu a slowly warrr. Batare da ya sake furta komai ba ya miƙe abinsa ya nufi wata hanyar gilashi data mamaye kusan bango guda na falon har kana iya hango ƙyawawan korayen ciyayin dake ta waje da ga nan, fita yay abinsa cikin wani irin takun mazantaka da nuna ƙarfin iko…..
Wata ƴar siririyar dariyar da yaronsa ya saki ta sakani kallonsa. Ya rumtse hannunsa tare da nuna babban yatsar hannunsa kasa👎 yana wani ɗaure fuska ya furta, “Lallai na tayaki jaje ƴammata. Dan kin taro babban match da baki da defenders balle ƴan kallo. Tunda har kika bari boss ɗina ya taya wannan wasan sai kinyi dana sanin da sai tafi biliyan a cikin koguna biliyoyi. Dan shi giwa ne baya WAIWAYE. Sannan zaki ne ba’a gaba da gaba da shi. Ki jira TAKUN FARKO na wasan kawai, tun anan zaki raina kanki.”
Baki na laɓe nima, tare da watsa masa harara. Cike da tsiwar ƙarfin hali na ce, “Shi kaɗai ka sani da dukkan salonsa. Abinda kuma ni zan iya sirrina ne, kaga kenan tsakanin ni da shi ba’asan maci tuwo ba sai miya ta ƙare a wasan. Dan haka ina baka shawara tunda kaine abokin sharrin nasa. Ka gaya masa da gaggawa ya maidani inda kuka saka aka ɗakkoni, idan ba haka ba, wlhy sai kunyi dana sanin shiga sabgata. Dan zan ajiye muku tarihin da bazaku sake gwada cutar da wani ba bayan ni. Koda kuwa kasheni kukayi fatalwata bazata barku ku zauna lafiya ba. Dan nasan abinda kuka iya kenan kashe mutane kuyi tsafi da jininsu ko”.
Dariyar kularwa ya saki da faɗin, “Irinku dama boss yafi buƙata a wasa. Kema shaida ce tunda a gabanki ga faɗa da bakinsa. Tunda kin shirya game ɗin ga fili ga mai doki, ni dama nawa shawara ce. Kuzo ku maidata inda kuka ɗakkota”. Ya ƙare maganar ƙarshe cikin ɗaga murya. Baima gama rufe baki ba sai ga garadan ɗazun sun shigo kuwa..
(Tofa, Samraah miya faru kuma bayan hakan?).
Humm Bily komai ma ya faru, dan zan iya ce miki a wannan gaɓar ma ne labarin ya ɗauki dai-dai saitin inda kowa ya kamata ya fahimci raunin daya taɓani da kuma nasarorin dana samu. Dan komai da kika ji a baya dai-dai yake da sharar fage. Konace shimfiɗar labarin. Amma kundinsa wannan gaɓar itace SHAFIN FARKO. An maidani ɗakin da aka fiddoni kamar yanda yaronsa ya bada umarni. Da ga haka ban sake ganin kowannensu ba. Sai dai ana kawo min abinci sau uku a kowanne rana. Kamar yanda na kasance a kulle a wancan gidan nan ɗin ma hakanne. Sai dai akwai masu tsarona anan, kuma na nan sun ma fi nacan firgitarwa. A ƙuntace nake matuƙar ƙunci, ga ciwon jiki dana zuciya. Ga kewar ahalina data masoyi. A kowane cikar minti ɗaya na agogo sai na lissafa sauran daƙiƙun da suka rage na cikar ranar aurena. Hakan yasa a duk sanda tunani ya nema fasan zuciya zaki sameni ina karatun Alkur’ani ne. Ina jin sauƙi sosai a raina, bayan na koma yin salla ma Alhamdullah na sake rungumar ibada ta. Dan akoda yaushe cikin kaima UBANGIJINA kukana nake. Ina kuma jin yaƙinin zai karɓa min.. Zakisha mamaki idan nace dake maganar da yaronsa yay na cewar na buƙaci su bani 500m kuma sun bada 250 a cewarsu ban wani sakata a raina ba. Danni a nawa wautar kawai sun faɗane bisa raɗin kansu da son min barazana ne dan na basu abinda suke son, dan haka na cigaba da harkar gabana kawai na manta da duk wani gargaɗinsu balle zuciyata ta fara min wani hasashe mai muhimmanci daya kamata ace nayi, ban san rashin yin shine zai zame min babban kuskure ba kuwa. Dan da’ace nayin maybe da abubuwa basu kasance a wani matsayi daban taɓa tsarama kaina ba bisa ƙaddarar rayuwa. Karna cikaki da zance muje zuwa dai…..
💞☞💞☞💞☞💞
“Ranka ya daɗe zan faɗi gaskiyar abinda ma sani. Sai dai yanda ka fahimci al’amarin sam ba haka yake ba. Wlhy wlhy duk abinda zan faɗa maka shine gaskiyar abinda ya faru. Tsoro ya hanani faɗar gaskiya tun ma a farkon fara case ɗin. Amma na gwada yin hakan tun sanda naji zancen ɓatar Sam-G da kuma kama Salis da akai. Ni bani na saceta ba, hasalima ban san ita za’a ɗauka ba. Wanda kuma ya ɗauketan wlhy ban san kidnapping ɗinta zaiyi ba. Kamar yanda na sanar ma abokina Isa da gaske na amashi mashin ɗin Salis ne a hannunsa domin zanje amsar sako tasha da aka turoma Mamana daga Maiduguri, da kuma tayoyi da za’a sakamin a nawa daya samu matsala. Na fito titin anguwarmu kaɗan wani bawan ALLAH ya tsaidani, banyi niyyar tsayawarba, saboda ina da uziri, ban fitoba kuma domin yin aiki ba. Gashi kuma safiya ce sosai dan ko haske gari bai gama yi ba. Sai dai ganin dattijo ne mutumin yasa naji tausayinsa. Dan harma na gotashi na dai dawo, tambayarsa nai inda zaije, dan naji ko yayi dai-dai da inda na nufa. Amma sai da ya shigo ya zauna yake gaya min. Ga abinda yace min da yasa na ɗaukesa tilas badan naso ba. (Yaro dan ALLAH ka taimaka min, Yakasai zanje, yarinyatace take da lalurar aljanu, jiya da dare muka nemeta muka rasa, sai ɗazun nan da asuba ƙanina yay kirana tana gidansa ta kwana acan Yakasai ɗin. To munsan zata iya barin nan ɗin akoda yaushe, kuma idan suka kaɗata bamu san ina zataje ba. Yanzu ma ko gidan bazamu ƙarasa ba zamu ɗan tsaya ne a kan layi data fito mu mata wayo, zan kira ɗan uwanta da zarar mun ɗauketa sai yazo ya ɗaukemu dan in kai tsaye ne bazata yarda ta shiga motarsa ba, amma idan na shaƙa mata maganinta zamu samu nasarar yin hakan). Yanda dattijon ke magana yasa na amince da shi, dan sam baiyi kama da wanda zai yi ƙarya ba, gashi kuma a cikin kamala. Lalura kawai daya kira yasa nai tunanin taimaka masa, dan nima ƙanwata nada irin makamancin lalurar, na kuma san irin tashin hankalin da muke shiga. Cikin nuna damuwa nai mata addu’ar samun lafiya, sannan na sanar masa gaskiyar ba aiki na fito ba, amma idan bazamu jimaba zan taimakesa, sai dai idan ta jima bata fito ba zan sakashi a wata napep ɗin ni na tafi uzirina dan abokina na jiran napep ɗin sa. Babu musu ya yarda da hakan har yana jeramin addu’oi ga hawaye yana faman yi. Ni dai na bashi haƙuri muka ɗauki hanya. Mun isa Yakasai, shine kuma ya nuna min inda zan tsaya, shi kuma ya fita ya maƙale a ɗan nesa dani. Nayi zaman kusan mintuna ashirin duk naji na ƙosa dan babu abinda nake sai faman tsaki, ina ma niyyar barin wajen ne sai gashi da saurinsa yake sanar min gatanan zuwa, dan ALLAH na taimaka kada na bari ta shiga ko wane mashin sai nawa. Yanda naga yana rawar jiki ga hawaye yana sharewa da gefen rigarsa yasa naji tausayinsa, duk kuma yanda ya tsara haka nayi. Mun fito a wajen mai saida lemo da aka tsinta wayarta daka faɗa yace na tsaya ga ƴaƴanta a mota………✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆
…..Hakan kuwa akai na tsaya dai-dai motar dake a fake, wanda akace Yayanta ya fito cikin nuna alhini yana min godiya, su biyu suka kamata suka saka a motar, ni sai lokacin ma na lura sun shaƙa mata maganin da yace, amma sai ban kawo komai a raina ba tunda dai dama yace zai saka mata magani. Yayan nata ne ya bani kuɗi masu yawa, nace masa bazan amsa ba ni dan ALLAH nayi, kuma ma ai kuɗin daya bani sun wuce na hakkin aikina. Murmushi kawai yamun ya ajiye kuɗin ya faɗa mota. Daga haka suka wuce suka barni ina kallon kuɗin, wlhy ban san sun yadda wayarta da facemask harda eyeglasses ba. Kuma suma ina ƙyautata zaton basu san sun faɗi ba kuskure kawai aka samu maybe. Suna wucewa nima na wuce, ban kuma san mike faruwa ba sai da yamma nake jin labari, abinda ya tada min hankali shine yanda ake misalta al’amarin yayi dai-dai da abinda ya faru da safe ni da dattijo, washe gari kuma sai naji batun kama Salis dangane da napep ɗinsa. Wlhy iya abinda nasani kenan, amma banda alaƙa da ɗaukar tata nima sai da naji daga baya hankalina ya tashi wlhy. Dan da nasan abinda zasuyi kenan babu yanda zan taimakesu, idan ma naga sunfi ƙarfina zan kira ƴan sanda. Dan ka tambaya kaji munsha irin wannan taimakon, adalilin haka har karyani an taɓayi abokaina gasu nan shaida ne”.
Shiru d.c.o yay na wasu mintuna kamar mai nazari, sai kuma ya sake kallonsa ya ce, “Zaka iya gane mutumin da saurayi yanzu idan ka gansu?”.
“Tabbas zan iya ganesu musamman ma dattijon duk da ya saka hirami a kansa ranka ya daɗe”.
Kai kawai d.c.o ya jinjina batare da ya sake cewa komai ba ya bama yaransa umarnin a maidasu cell. Hakan kayi, bayan an maidasu ya zauna da yaronsa dake kan case ɗin.
“Ɗan Bakori mika fahimta a zancen yaron nan?”.
“Ranka ya daɗe al’amarin ne akwai wuyar sha’ani, amma dai kamar akwai ƙamshin gaskiya a zancen nasa. Wani abu dana fahimta shine amfani kawai akai da shi, kuma tabbas in har da gaske bashi da hannu duk waɗanda sukai abun to sun sanshi dan dole sunada kusanci koda ta zaman anguwa ne. Shiyyasa sukai masa wayo da batun iska tunda sun san ƙanwarsa na fuskantar irin matsalar zai fi saurin afkawa. Zancen daya faɗa ya taɓa samun karaya akan taimakon wata yarinya kuwa gaskiya ne. Dan na samu wannan labarin a binciken da nayi tun a farko. Mutanen na shegune suna da wayo, kuma sun shirya komai yanda suke so kafin su tunkaresa. Abu na ƙarshe bana raba ɗayan biyu duk wanda yay aikin nan na jikinta ne, ta sanshi ya santa sosai, dan inba haka ba tayaya suka san zata fito a lokacin tunda ba ranar aiki bace ba?”.
“Tabbas zancenka na akan hanya ɗan Bakori. A wannan gaɓar dole aikinmu ya ɗan sake komawa baya kaɗan. Wayarta da aka tsinta daga biyar na yammacin ana gobe abin zai faru har washe gari a duba dawa tai waya? Waye yay kiranta? Koya turama saƙo koya turo mata.”
“Okay Sir, amma naji kamar Yayanta yace da waya biyu take amfani, kuma sun wuce da ɗayar”.
“Wannan ba damuwa bane, duk da dai ta wani fanin kasancewar wayoyin duka biyu zai fi mana. Amma ɗayar ma zata taimaka mana. Dan kamar yanda yaron nan ta faɗa sam basu san sanda ita wannan wayar ta faɗi ba kuskure aka samu. Itama in sha ALLAHU zamu samu abinda zai taimaka mana ku bincika”.
Cike da gamsuwa ɗan Bakori ya miƙe tare da yin salute ɗin sa sannan ya fita da sauri….
💥💫💥💫💥💫💥
Ɗan taku yake cikin kai-kawo babu alamar rikicewa ko shiga wani yanayi a tare da fuskarsa a bayyane. Sai dai a can ƙasan zuciyarsa auna komai daya fita daga bakin Samraah yake kalma bayan kalma. Tare da ajiye kowanne word a mizanin hankali. A wannan yanayin Hayatu ya samesa. Ganin a yanayin da ogan nasa yake sai ransa ya ƙara ɓaci shima, dan haka a harzuƙe ya ce, “Sir yarinyar nan fa nada ɗan banzan wayo, ga bakinta kamar reza baya mutuwa. Ƙarya take tasan komai tana pretending ne kawai. Ba gashi yaron nan da aka amsheta a wajensa yace itace ta sakashi yay kidnapping ɗinta Dan ta bada ƙafa……”
Wani irin murmushi Maash daya kafa masa ido ya saki a karo na farko, sai kuma ya girgiza kansa kawai tare da janye idanun ya maida kan ƙyawawan firannin fulawoyi da aka ƙawata wajen da su, baka jin komai sai daddaɗar iskar da suke badawa da ƙamshinsu a wajen. Shiru bashi da niyyar cema Hayatun komai har shi Hayatun ya ƙosa da shirun nasa duk da ba sabon abu bane a wajensa. Dan inma bai gadama ba zai iya sharesa yaƙi cewa komai kuma shikenan amsar tabi ruwa.
Sun kai tsahon mintuna uku a haka kafin cikin silent voice ɗinsa a can ƙasan maƙoshi a daƙile ya furta, “Hayat be a man mana. Kullum ina sanar maka ka dinga lissafi akan abubuwa. Amma na fahimci brain naka harkar business kawai take iya ganewa. Mizai hana a duk sanda baka fahimci miya dace akan abu ba ka dinga bashi lokacinsa dan ka fahimta. Ina matuƙar tsoron kada maƙiyan dake bayana suyi amfani da wannan ruɗanin naka da rashin hange wataran su ci nasara akan ka. Yarinyar tanada tsiwa da raini. Sannan harshenta nada kaifi. Zan mata hukunci dai-dai da wautarta. Kuɗina kuma nasan inda suke, zakuma su dawo nan bada jimawa ba batare da rasa ko naira ba a cikinsu. Video kuma dake hannunta muna farautarsa ne mu da su a hannunta, sai dai basu san MAASH ba shashasha bane irinsu. Zan tabbatar musu kuma da hakan, dan a matakin wasan farko da su zan fara buga game ɗin kafin na dawo kanta. Ka siyama Sani ticket a yau ɗin nan ya biyo jirgi zuwa Abuja. Hakama Abubakar ina son ganinsa yau da dare”.
Daga haka ya juya ciki batare da ko waiwayen Hayatu ba. Da kallo Hayatu ya bisa galala kamar idanunsa zasu zubo. A zuciyarsa ya shiga faɗin, (Idan nace mutumin nan Aljani ne ace ba haka ba. Yanzu dan ALLAH duk wannan zaƙewar da nake dama ni yakema kallon wawa? To wai tsaya ma. Shi abinda ban gane ba anan. Kuɗi dai ni aka saka na turasu a account no.. da mutumin ya turo. Kuma ni da shi mun tabbatar da sabon account ne aka buɗe muna saka kuɗin kuma aka ciresu tare da blocking account ɗin ma gaba ɗaya. To shi tayaya ya bibiya ya gano komai? Mutumin da kullum damuwarsa maida naira ta zama dala. Kai nikam fa na fara tsoron boss ɗina. Ko yanzu ma ji nake zazzaɓi na nemam rufeni, dole ne sai naje asibiti naga likita). Ya ƙare zancen zucin nasa da kai hannu ya taɓa goshinsa da wuyansa kamar wani ƙaramin yaro.
(HAYATU na buƙatar ganin dacta. Likitocin gidan nan ku fito ku bashi agaji🤣😂🙏)
💞✨💞✨💞✨💞
A lokacin da ƴan sanda keta nasu ƙoƙarin, a ɓangaren Yaya Musaddiq shima yana can tare da su Kawu Musa da sukazo da ga Gwarzo. Ba wannan ne zuwansu na farko ba. Sun dai sake dawowa ne suji yaya ake ciki duk da suna waya da Musaddiq ɗin akai akai game da al’amarin. Da ƙyar Mum ta yarda ta basu abinci, dan saida ma Abba ya nuna mazantaka yau. Bayan sun gama cin abincinne suka zauna tattauna abinda ya kawosu. Kawu Lurwani ne ya fara magana alamar shi suka wakilta yayi. Sai da ya kalla Abba da Musaddiq sannan ya fara faɗin. “Wato Imamu magana ce mai muhimmanci ta kawomu nan tare da sake jajantama juna akan batun yarinyar nan. Al’amarin nata akwai mamaki da ban tsoro ƙwarai matuƙa. Dan zuwa yanzu dai duk mai hankali ya kamata ya fahimci ba waɗan nan mutanen bane masu cewa a basu kuɗi idan sun kama mutum. Dan da ace hakanne da tuni sunyi maganar kuɗin. Amma gashi yau har kwanaki goma sha uku da rasata babu wani bayani. Hakan na nufin aikin magautane tunda yarinya ce mai farin jinin mutane sakamakon aikinta. Yanzu mu kai tsaye bazamu ce ga wanda yay wannan aika-aikar gareta ba damu ma kammu da ke a cikin tashin hankali. Bamu ce kuma ƴan sanda sun gaza ba, dan suna iya ƙoƙarin su suma. Amma magana ta gaskiya bai kamata muma mu rungume hannu muna jiransu ba…..”
“To Lurwanu yaya zamuyi idan ba hakan ba. Aikinsu ne ai, sune kawai suke da dabarun bincike, dan a yanzu haka since wanda ya ɗauke ta a napep yana hannunsu ma, sai dai yaƙi amsa laifinsa”. Abbane yay maganar cikin katse Kawu Lurwanu. Kai Kawu Lurwanu ya girgiza, “To ai ban kai ƙarshe ba nima ka katseni Imamu, abinda nake so nace bafa zama zamuyi mu rungume hannaye muna jiransu su kaɗai ba. Kamata yay muma mu saka roƙon ALLAH tako ina. Sai dai kasan mu ɗin ba masu ƙarfi bane, kuma al’amarin yana buƙatar sadaka. Dan haka muka yanke hukuncin dawo da waɗan nan kuɗi na aurenta da aka karɓa, dan dubu ashirin kawai mukaci a ciki aka ajiye tamanin akan idan lokaci yayi zamu ƙara da wasu a rage maka hidima. Kaga kaima saika kawo wani abu daga cikin wanda ke hannunka a haɗa a sai abinci da wasu abubuwa aita sadaka ana addu’a sai kaga anci nasara ALLAH ya bayyanata cikin sauƙi. Dan yarinyar nan kullum kwanakin bikinta sake matsowa sukeyi, dan ma yaron kirki ta samu, kuma danginsa basu da fitina, amma wlhy da wasu ne da yanzu sun fara zame-zame akan al’amarin nan. Amma kaga yaron nan da shi aketa faman faɗi tashi na son ganin an samota har ma da iyayen nasa. Amma yaya ka gani shawara ce?”.
A ɗan fusace Abba ya ce, “Ni gaskiya babu kuɗin nan yanzu a hannuna. Sai dai idan shi Musaddiq nada su ya aramin idan na samu zan bashi”.
Kaf falon babu wanda bai ƙwalalo idanu waje dan mamaki ba…….✍️
Ai ni kaina idanun nawa a waje. Abba al’amarin ka ya fara ban tsoro da mamaki. Ya rabbi kasa mu rayu da ƴaƴanmu, maraici da banne wlhy a rayuwa😭.
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐
…….. Musaddiq ne kawai yay murmushi yana mai girgiza kansa. Ganin Kawu Musa na neman fusata dan dama shi akwai zuciyar tsiya yay saurin faɗin, “Uhm Kawu inaga babu damuwa ai. Kuma na wajenku ku barsu. In sha ALLAHU babu abinda zai gagara na sadakar. Ko daga gobe in ALLAH ya kaimu ake son fara duk abinda ya dace ni a shirye nake.”
Sosai suke kallonsa zukatansu na ƙara rauni. Yaron jarumine na gaske da kowaɗanne irin iyaye zasu yi alfahari da shi. Gaba ɗaya halin Musaddiq irin na mahaifinsa ne. Ga sanyin hali ga haƙuri ga kirki da jarunta. Sun nuna masa zadai su bashi kuɗin amma ya dage kan bazai amsa ko sisi ba. Dole suka haƙura suka barsa. Ƙyawawan halayen yaron na sake saka musu jin kunyar wofamtar dasu da sukayi a lokacin da suke matuƙar buƙatar tallafinsu, amma kuma bakin alƙalami ya riga ya bushe yanzu kam sai dai haƙuri, dan ta wani ɓangaren suma ba laifinsu bane. Ƙanin mahaifiyarsu ne ya nuna musu shi ɗan boko ne kawai sjiyyasa sukai zuciya suka bar masa su.
Kaf abinda ya faru a zaman sai da Mum ta tsare Abba ya sanar mata. Aiko ta sake zugesa akan babu wata addu’a sun zo ne kawai su yaudaresa su amshi kuɗin. In ba hakaba wace addu’a ce za’a wani ce sai da kuɗi. Daga ƙarshe ta sake ingizashi kan ya binciki Musaddiq duk yanda akai yaron kuɗine da shi, in ba hakaba taya komai ya taso sai yace zai yi. Daram kuwa ya hau ya zauna ko kunyar ALLAH babu washe gari yay kiran Musaddiq yay masa tujara. Ya kuma ce yana buƙatar 1mil a wajensa da za’aima Samraah kayan ɗaki, sannan ya bada kuɗin kayan kitchen suma Mum zatayi masa list ɗin komai. Sai da ya gama sauraren Abba kaf sannan yay murmushin sa mai sanyi. Cikin nuna rashin wata damuwa a fuska ya ce, “Ba damuwa Abba ka saurareni zan samo in sha ALLAHU”.
Sallamarsa Abba yay yana ƙara jaddada masa. Yana fita Mum tai wuff ta fito alamar dama laɓe tai musu. Zama tai kusa da Abba tana faɗin, “Bana gaya maka ba Abban Abbas. Yanzu ka yarda ko? To ALLAH kaɗai yasan mi yaron nan ya tara yake raina mana wayo ya barmu da nauyin hidimar rawuwarsu. Ana gama hidimar bikin nan ya kamata ka sashi ya bama Abbas jari yabar wannan gantalin rashin aikin, sannan itama Baby ta fito da miji dan nagaji da yawon nan nata haka nan”.
Babu wani dogon nazari ko tunani a wannan magana Abba ya amsa Mum tare da bata goyon baya ɗari bisa ɗari. Daga haka suka cigaba da hirarsu cike da soyayya.
A ɓangaren Musaddiq kam shi al’amarin su Abba kam ya fara bashi tsoro. Dan ya wuce abin mamaki ko al’ajabi. Amma dai a wannan karon zai ari halin Samraah ko kaɗanne ya gani ko zasu fahimci shi ɗin bawai sakarai bane. Yana binsu ne kawai da halayensu saboda wasu dalilai. Yanzu banda rashin adalci bama damuwarsu ɓatar ƴar uwarsa ba kusan sati biyu kenan, shi dama gani yake Mum da Baby kamar farin ciki suke da rashin Samraah a gidan. Ko mi tai musu haka da zafi oho ya kasa fahimta. Yasan Samraah fitinanniya ce, to amma duk abinta saika shiga sabgarta ne, kuma mafi yawan lokaci sune ke fara takalarta ita kuma ta maida murtani.
Washe gari kamar yanda suka tsara aka fara gudanar da addu’oi. A masallatai da islamiyoyi, aka kuma dafa abinci aka dinga rabawa mutane musamman ƙananun yara da almajirai. Dan har tsangayoyi aka kai abincin ma. Acan gwarzo ma su Kawu Musa abinda sukai ƙoƙarin yi kenan da kuɗin da Musaddiq ya basu. Dan Mansoor ya taimaka musu sosai da yaji shirin nasu. Dan ko abincin nan ma da aka dafa anan shine ya bada aka dafosa da taimakon Mamynsa.
Kwana uku anata addu’oi da raba dafaffen abinci. Ga kwanakin biki nata sake matsowa daf. Gefe Musaddiq nata wasan ɓuya tsakaninsa da Abba da Mum. Yayinda su kuma suke zaman jiran a kawo musu kuɗi…..
✨★✨★✨★✨
Tabbas duk wanda ya miƙa al’amarinsa ga UBANGIJI babu shi babu taɓewa Bily, naga fa’idar hakan ƙwarai da gaske a wannan gaɓar. Domin kuwa duƙufar da nai wajen gayama UBANGIJI damuwata ya saka min ƙwarin zuciya da jin sabon ƙarfi na dawo Samraah ta tada. A daren da nake lissafin kwanakin aurena da Mansoor saura biyar kacal a bazata naji ana ƙoƙarin buɗe ɗakin da nake. Hakan ya bani matuƙar mamaki dan ba lokaci bane da ake kawo min abinci, kusan ƙarfe goma da wasu mintuna ake yanzu na dare. Hijjabina daya kasance ɗaya jal da nake salla da shi na ɗauka da sauri na saka. Bamma kai ga ƙarasa sakawarba har an riga an shigo. Baki na buɗe cikin ɓacin rai zanyi magana kawai ya jefamin wata muguwar harara. Ba kowa bane face yaronsa ɗin nan mai dogayen kunnuwa uwa na zomaye. Nima hararsa nai da mare baki, a fili na furta, “Daka daina burga dan baka da banbanci da damisar takarda. Kullum kana bayan wani kamar mai gadi”.
A take fuskarsa ta rine zuwa ɓacin rai, ya ɗaga hannu kamar zai ƙwaɗan mari sai kuma miya tuna oho masa ya fasa. Ya dunƙule hannun yana ɗan kaima iska naushi a cikin takaici. Ni dariya ma ya bani, amma sai na dake banyi ba. A cikin zafin rai ya furta “Shigo ki mata”. Ban gama hahimtar mi yake nufi ba likitar ranar data dubani akan matsalar ciwon mara ta shigo. Matar ƴar gayuce sosai. Da gani kuma kasan itama ƴar masu kuɗice. Murmushi tai min cikin tsokana tace ashe dai patient ɗina ta miƙe?”. Watsar da ita nai kamar banji mita faɗa ba, dan haka kawai bata mun ba, nama ɗauke kaina gaba ɗaya. Magana tai yunƙurin sake yi mai kunnen zomaye ya dakatar da ita cikin magana zafi-zafi ya ce, “Doctor kimata kawai”.
Itama amsa masa tai da to tana zaro syringe. Kambu idona idon allura na zabura zan miƙe, sai dai mi jinai kawai an damƙomin hannu an riƙe, kafin na farga ta saka min handcuffs. Ido rufe na buɗe baki zan balbaleta da masifa ta shamaceni kawai sai shigar allura naji a hannuna. Kafin wani dogon motsi ta zareta tana sauke ajiyar zuciya kamar daga jikinta take cirowar. Kaina ne ya fara juyawa na koma ganin ɗakin da su kansu bibbiyu, da ƙyar na iya ɗaga hannu ina nunasu amma na kasa magana. Dan idanuna lumshewa suke kaina na ƙara nauyi, a cikin abinda bai wuce minti ɗaya da wasu sakanni ba komai ya koma min ɗiff. Sai buɗe idanuna nai na ganni a inda banyi zato ko tsammani ba….
💫💥💫💥💫💥💫
Duk da tasowar hadari mai ƙarfi na farkon damuna bai hana Musaddiq tashi ba jin an ƙwalla kiran sallar asubahi. Ya fara alwala aka fara yaf-yaf na yayyafi. A gagauce ya ƙarasa ya wuce massalaci. Kamar jira ruwan nan yake a idar da salla ya fara sauka da ƙarfinsa. Kusan duk wanda ke a massalacin da gudu-gudu ya fita domin shiga gida. Hakance ta kasance tsakanin Yaya Musaddiq da Abba. Kusan a tare suka ja wani bahagon birki a ƙofar gidan sakamakon cin karo da abinda basuyi tunani ba ko zaton gani haka. (Tabbas Samraah ce ba gizo bane, ba kuma mafarkin daya sabayi bane ba). Musaddiq ya ayyana a zuciyarsa dake faman gudu da uban sauri a cikin ƙirjinsa. Da sassarfa ya ƙarasa inda take. Dai-dai nan ta fara motsa jikinta sakamakon ruwan sama dake sauka da ƙarfi. Kuka Musaddiq ya saki tare da durƙushewa a gabanta. Gaba ɗayanta ya wawuso ya rungume a jikinsa. Hakkane ya saka Abba dawowa hayyacinsa shima ya nufesu. Cikin rawar murya data jiki ya furta, “Musaddiq da gaske Samraah ɗin ce?”. Bai jira amsarsa ba shima ya kai durƙushe gabansu. Duk wanda yazo gittawa ya gansu sai ya tsaya. Kafin kace mi maƙwaftansu sun ɗan taru a wajen. Duk mazane da aka dawo daga massalaci. Maƙwafcinsu da suke katanga ɗaya ne ya bada shawarar a shiga da ita cikin gida. Wannan shawara tasa ta saka Musaddiq miƙewa ɗauke da Samraah. Ta farfaɗo amma bata iya banbance komai kamar wadda ke a buge cikin maye. Wannan yanayi nata yasa da yawan wanda suka taru a wajen ransu ya ɗarsu da abinda bashine ba.
Abba ne ya shiga kwala kiran sunan Mum. Sai gata a firgice. Da alama ma ita sai yanzu take tashi sallar. Su Baby ma ihun Abban ne ya tashesu a nasu barcin suma duk suka fito. Kowa yaci karo da Samraah sai yay wani irin ja da baya yana zaro idanu. Musaddiq ne kawai keta ƙoƙarin ganin ta buɗe idanunta da take lumshewa da buɗewa da ƙyar tamkar me maye. Kusan mintuna biyar kafin ta buɗe idanun da ƙyar sosai ta kallesa. Cikin siririyar muryarta data surka da mayen barci ta ce, “Yay..a Mu…sad…diq”.
Jikinsa har rawa yake wajen amsa mata da, “Na’am Samraah! Kandalata nine. Buɗe idonki da ƙyau ki sake ganina. Alhamdullah ya rabbi Alhamdullah.” yanda yake sambatun yana hawaye ga dariya sai ka ɗauka ya zautu ne. Su dai su Mum na tsatstsaye ciko-ciko kawai suna kallonsu. Musaddiq da duk ya gama rikicewa ya zaro wayarsa da sauri. Mansoor ya fara kira, dan abokin kuka shi ake fara gayawa mutuwa, wani ihun farin ciki da Mansoor ɗin ya saki sai da ya janye wayar dan jin zai fasa masa dodon kunne. Daga nan yay kiran d.c.o shima dan ya sani. Shima yanda yake ta jera Alhmdllh zai tabbatar maka yaji farin cikin. Suma yan gwarzo yay kiransu ya sanar musu. Ai kafin kace mi anata shigowa gidan, dan Mansoor ma cikin ruwan nan ya taho duk da gari bai gama washewa ba, sai daga baya jama’ar gidansu suka biyosa. Sanda suka taho an wuce da Samraah asibiti domin duba lafiyarta kamar yanda d.c.o ya bada umarni. Dan sam Samraah bata cikin hayyacinta saboda allurar da sukai mata…….✍️
Hummm dangin Samraah sai a barmu mu hyaƙata, ga ƴarku nan mun sakar muku. Su o’e duk an addabemu dama🚴🚴😞.
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
…….Lokacin da goma tayi gidajen rediyo dana tv da yawa sun sanar da ganin Samraah. Gidan tvn su ne ya fara fitar da batun, dan danan sai ga ƴan jarida. Sai dai an hanasu kowace irin dama ta ganin Samraah, dan har lokacin barci ma takeyi ita. Ƴan gidansu ma da ƴan gidan su Mansoor duk suna daga waje ne. Sai wajen sha ɗaya ƴan Gwarzo suka iso suma. Nan fa asibitin ya ƙara cika. Dole doctor ya roƙa su ragu. Dan ana buƙatar sanda zata farko ta farka a cikin hayyacinta. Gamsuwa da hakan yasa aka ragu, Mansoor da Yaya Musaddiq da Abba sai Kawu Musa kawai aka bari, sauran duk suka wuce gida.
Ƙarfe ɗaya da wasu mintuna Samraah ta farka. A lokacin babu kowa a ɗakin dan wanda aka bari asibitin duk sun wuce massalaci salla. Sai Nurse da aka bari ta kula da ita dan zata iya farkawa a koda yaushe. Hakance kuwa ta faru. Sai dai tana buɗe idanunta bakinta da addu’a Nurse ɗin nan ta miƙe. Sannu ta mata da farko, sai kuma ta ɗan fita kamar zatayi kiran Doctor ne. Babu jimawa sai gata ta dawo. A lokacin Samraah ta ɗan daddafa ta tashi dan wani irin fitsari take ji. Matsowa Nurse ɗin tayi gaban gadon tana mai cire wayar dake a kunnenta tai ɗan danne-danne da bai wuce sakan biyar ba ta nuna wayar akan fuskar Samraah dake kallonta. Dan ta rufe fuskarta ruff da face mask idanunta kawai ake iya gani. Baki Samraah ta buɗe zatayi magana da ƙyar dan ganin Nurse ɗin ta saka mata waya a gaban fuska. Amma saita mata nuni da wayar alamar nan zata kalla. Babu musu ta juya kanta a hankali tare da buɗe manyan idanunta da suka kumburo sosai sukayi ɗan ja a jikin fatar amma cikinsu tar-tar ta sauke su akan fuskar wayar. Numfashi ta nema janyo wa da sauri, amma hakan ya gagara sakamakon cin karo da fuskar wanda batai zato ko tsammanin gani ba shima ya zuba mata idanun nan nasa tamkar zai cinyeta ɗanya da su. Zaune yake ƙafa ɗaya kan ɗaya da salon zaman ƙasaitar nan tasa. A yanayin location ɗin da yake zai tabbatar maka da ba’a Nigeria yake ba ma. Duk da ta cikin wayane jinai kallonsa na neman yamutsa min kaina. Amma na dake a zahirance, sai ma wani irin mummunan kallo da nima nake jifansa da shi batare da nasan ina yi ba. Ƙara tsatstsareni yay da idanun cikin yanayin irin ke baki da kunya ko. Niko na yamutse fuska irin eh banda kunyar sai yaya.
Hannunsa ya kai ya shafo gashin dake a haɓarsa, cikin salon ƙara tamke fuskarsa cike da gizago shi a dole bai san raini murya a kausashe ya fara magana da ƙyar dan yanda lips ɗin ma ke motsawa kaɗan-kaɗan sai ka ɗauka bazaka iya jin abinda yake faɗa ba. Amma kuma sai na dinga jin muryar tasa raɗam a kunnena kamar ba’a waya yake ba.
“Ganinki cikin zur’arki bashi ke nufin wasan ya ƙare ba. Sai dai kina da zaɓi biyu. Bakin ki ya kasance shiru ki cigaba da rayuwa da waɗan nan mutane biyun”. Hoton Hafizzullah da Yaya Musaddiq ya bayyana. Bamma san sanda na waro idanuna waje sosai ba ina ɗan zabura. Shiko hankali kwance ya ciga da faɗin, “Ko ki buɗe sa da zance a kaina ni kuma na rufe miki shi ta yanda ko mai irin harafin farkon sunana kika ji sai kin firgita. Na barki lafiya”.
Da sauri nima cikin jin wani ƙarfi na ce, “Yaƙin sunƙuru ai na mai tsoro ne. Idan ka cika namiji kabar laɓe-laɓe a bayan ƙarfin dukiya kazo muyi gaba da gaba sai a banbance waye jarumin tsakanin ni da kai. Ita Sam-G a ko ina Samraah ɗinta take, bana ado da wasu domin kare suna ko ƙarfin iko na. Sannan garkuwa da wasu domin cimma buri ai tsohon salo ne. Video ne dai bazan bayarba, kuma har abada bazaka taɓa sanin inda yake ba, kai ni kaina bazaka sake gani na ba”.
Wani jahilin murmushi ya saki da sai da ƙirjina ya harba dan wani kalar mugun ƙyawunsa ne ya sake bayyana. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kaina cikin yanayin kallon ƙasa-ƙasa, bamma san na murguɗa masa baki da janye nawa ba. Ya ɗan taɓe baki cike da basarwa. Tare da motsa lips ɗinsa a daƙile ya ce, “Ina matuƙar son wasa da mutum irinki mai taurin kai da kaifin baki. Dan haka kar kiyi gaggawa, in dai yaƙin gaba da gaba ne yana tunkaro ki, dan haka jekiyi shiri na musamman, dan yaƙi da Awwab Maash dai-dai yake da tunkarar mayaƙan duniya. Bye sai mun haɗu a filin daga”. Ya ƙare magana da salon kashe ido ɗaya ya ɗaga min yatsu biyu. Ai bamma san na zabura baya ba ina waro idanuna gaba ɗaya waje dan al’ajabi, ka jimin kwarto zai iskantani, dan wannan abun da yay ai na ƴan iska ne. Baki na buɗe zanyi magana. Ɓat ya ɓace tamkar bai taɓa bayyana a fuskar wayar ba. A hargitse na kalla Nurse ɗin da ke ƙoƙarin amshe wayarta. Itama ni take kallo. Cikin tsumar jiki na ce, “Malama sake kiransa!”.
Baki taɗan taɓe, a gadarance ta ce, “Ai shi Boss GIWA ne baya WAIWAYE.”
Cikin ɓacin rai na ce, “Wacece ke?”.
“Sanin wacece ni bazai amfaneki da komai ba. Kare rayuwar ƴan uwanki biyu shine mafi muhimmanci gareki da yin shirin yaƙin dake tunkaroki kamar yanda ya faɗa a yanzu, dan shi baya magana biyu, kada ki sakankance da yawa, in har yace zaiyi, to lallai ya gama shirya yin ne. Idan yace bazai yi ba, babu mai sakasa yin. Zan sake baki shawara akan abinda boss ya faɗa miki. Idan kin kiyaye tabbas kin tsira, domin shi tamkar ifiritin ALJANI yake. A duk inda kika saka ƙafarki yanzu ki ɗauka yana biye dake ne taku bayan taku. Rayuwar ƴan uwanki tana da matukar muhimmanci a gareki, kece kuma zaki tabbatar ma da duniya hakan ta hanyar sakawa a ranki kamar baki taɓa ji ko ganin komai ba akan Boss. Zaɓi ya rage naki, nima na barki lafiya”.
Da sauri na yunƙura da nufin cafkota, sai dai wani irin jiri ya nema kwasata dole na koma saman gadon jagwaf ina mai dafe kaina dake juya mun. Dai-dai nan Doctor ya shigo tare da Nurse. A kaina suka rufu suna jera min sannu. Niko gaba ɗaya ma bawai ina jinsu bane ba da ƙyau. Dan hatta ɗakin jinake yana amsa amon muryarsa tamkar a yanzun ne yake jera min gargaɗin ko barazana zan jirashi ma ban sani ba. Sama-sama nake jiyo doctor na faɗin, “Barcin nan bai gama sakinta ba. Sister Fadila gyara mata kwanciya”. Daga haka ban sake jin su ba.
★★Sai yamma lis na sake farkawa. Yanzu kam Alhamdullah dan duk wanda ya kalleni yasan ina a hayyacina. Dukan ƴan uwana kuma an basu damar shigowa dubani. Ina zaune a gadon na jingina da filo Gwaggo Gudidi na bani shayi. Gaba ɗaya idona ya kasa barin kan Yaya Musaddiq, kaɗan-kaɗan kuma nakan ce masa ya kira Hafizzullah ya ji yana lafiya. Yanda nake ɗin sai kowa ke ganin kamar ban gama saki bane shiyyasa. Niko ni kaɗai nasan a halin da nake ciki. Wani furuci da Mum ta furta lokacin da ƴan gidan su Mansoor suka zo ya saka ɗakin yin tsit duk aka zuba min ido har ina jin jinina na yamutsawa.
A gatsine bayan ta kallan da ga sama har ƙasa lokacin da Gwaggo ke lallaɓani na ƙarasa shan shayi ta furta, “Ai waɗan nan kidnappers ɗin ma dai masu mutunci ne da wayewar kai. Yanda duk wanda aka kama ke dawowa wujiga-wujiga amma ita Samraah gata nan fes da ita. Sai ma uban haske data sake ga fata sai ƙyallin jin daɗi take yi kamar mai yaron ciki. Koda yake ance idan sukaga masu ƙyau musamman ƴammata sukan maida su kamar matansu ne suyita musu gata kuma. Maza ne dai ke shan baƙar wahala da duka. Da alama kema dai sa’ar kika ciwo kansu ɗiyata, mudai in ma wani bai aureki a cikinsu ko ya lalata miki rayuwa ba ai Alhamdullah, duk da kema ɗin ba abin yabo bace tunda dama ko ina yawonki kike yi tumma kan faruwar hakan”.
Gwaggo Gudidi ce ta katse shirun ɗakin idonta akan Yaya Musaddiq daya wani dunƙule hannu. Gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun gama fitowa alamar yau ɓacin ran maza ya fito fili. Ya ɗan motsa da alamar zai yunƙuro Gwaggo ta katse hakan ta hanyar duban Mum da ƙyau. Murmushi ta sakar mata itama, sannan ta furta,……..✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓
…….“To banda abinki Jalilah ai kidinafa ɗin dama kala-kala ne. Duk wanda ya fahimci wanda suka ɗauki Samraah kuma ai yasan ba masu neman kuɗi bane. Akwai wata manufa da ake son cimmawa. Ba kuma na raba ɗayan biyu akan rahamar da UBANGIJI yay mata ta samun miji kawai ake son aga an tarwatsa. Sai kuma ALLAH da yake shi maji roƙon bayinsa ne sai gashi ya rusa duk wani makircin masu makirci ƙarfin addu’a yayi tasiri dan gashi UBANGIJI ya dawo da ita gida a lokacin da magauta wannan aure basu so ba. Kuma in sha ALLAHU babu fashi ranar juma’a iyanzu tana nan da igiyoyi uku a kanta”.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Mansoor ya sauke yana mai lumshe idanunsa. Yayinda Mamyn sa tai ɗan murmushi kawai. Hakama Dad ɗinsa da su Kawu Lurwanu duk murmushin sukayi. Attahir kuwa mintsinin Mansoor yayi yana kashe masa ido ɗaya cike da tsokana. Hakama ƙannensa Islam da Sakeena dake zaune kusa da Samraah duk murmushin sukayi. Aiko Mum kamar zata haɗiyi zuciya, amma dai ta danne tana murmushin yaƙen itama kamar kowa. Abba ma baice komai ba, da ga ƙarshe ya wayance da an kirasa a waya ya fita yana amsawa. Yaya Musaddiq ma a hankali ya dinga sakin ajiyar zuciya jijiyoyin kan nasa na saki sannu-sannu, dan koba komai amsar da Gwaggo ta bama Mum ta fanshi duk wani ɗaci da fushin daya yunƙuro masa. Ni dai kaina a ƙasa ina satar kallon Yaya Musaddiq, zancen Gwaggo ya sakani jin kunyar kowa dake ɗakin musamman ma family ɗin Mansoor. Dan dama tunda suka shigo ban sake yarda na kalli kowa ba. Ko magana da ƙannensa ke mun ƙasa-ƙasa ɗan murmushi kawai nake musu. Lokacin sallar magrib kowa ya watse. Iyayen Mansoor da ƙannensa suka wuce. Hakama Mum da su Kawu Lurwanu Yaya Musaddiq ya tafi kaisu masauki. Shi dama Abba tun wayar nan daya fita bai sake dawowa ba. Su Baby kam har yanzu ban gansu a asibitin ba. Dan ko Abbas dake matsayin babbansu bana jin yama zo dubani, koma basu san na dawo bane oho, koda yake da wuya ace hakan ta kasance gaskiya.
Daga ni sai Gwaggo Gudidi aka bari, sai bayan sallar isha’i ne Yaya Musaddiq da Mansoor suka dawo. Babu jimawa da shigowar tasu sai ga d.c.o da yaransa guda biyu. Sun nuna jin daɗinsu na ganina garau yanzun, dan doctor ma yace zai sallaman da safe tunda banda wata matsala a tare dani, sai rashin ƙarfin jiki na allurar da suka min, tun ma a daren yay niyyar sallamata Mansoor ya ce a barni sai washe gari dai na sake jin ƙarfi da kuzari. Mun gaisa da su suka jajanta min kan abinda ya faru. Kafin d.c.o ya tabbatar min dana kwantar da hankalina na kuma basu haɗin kai mutanen nan ko su waye su sai sun kamasu an hukuntasu.
Amsa masa nai kawai da kaina dan nasan abinda yake faɗar bamai yiwuwa bane ba. Wani ma idan nace ga wanda yay kidnapping ɗina cazai ƙarya nake yi. Su kuwa koda ma sun san gaskiya babu abinda zasu iya yi ɗin kamar yanda yake faɗa. To shi hatsabibin aljanin ma zai basu wata ƙafane da zasu gane shine, dan magana ta ALLAH al’amarin mutumin nan ya fara sakani a firgici, dan bana jin na taɓa cin karo da makirin mutum, hatsabibin gaske da ko tsoro bazaka taɓa karanta a yanayinsa ba irin wannan mutumin. Ga shi yayta wani shan ƙamshi cikin gadara da karfin iko kai kace shike mulkar ƙasar. Ta wani ɓangaren kuma ina buƙatar rayuwar ƴan uwana. Dan wannan mutumin babu shakka zai iya aikata abinda ya faɗa koma fiye da shi tunda na gani da idona sanda yake zare wuƙa a jikin wani. Ga kuma abinda Nurse ɗin nan tace, a duk inda muke yana biye damu ƙafa da ƙafa. Zan kare rayuwar ƴan uwana kamar yanda yay min barazana, sai dai fa idan yasan wata baisan wata ba. Nayi alƙawarin saina ƙullama rayuwarsa tarkon da bazai taɓa iya kuɓutar da kansa ba. Dan saina tabbatar masa da TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE da ƴar Abdul-wahab Gwarzo yake magana. Nashi kuma wasa ne, bai san mi ake kira kaidin mata ba sai na tabbatar masa…..
Taɓanin da Yaya Musaddiq yay ya sani dawowa hayyacina firgigit. Cike da kulawa ya furta, “Tunanin mi kike anata magana Samraah?”.
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, sai kuma cikin sanyin murya na ce, “Ba komai Yaya. Kuyi haƙuri”.
Baki ya buɗe zai sake magana naga ɗan sandan ya masa alamar ya barni. Shirun kuwa yayi, suma sai sukai mana sallama akan zasu wuce. Amma an ajiye ƴan sanda biyu domin tsarona gudun abinda zaije ya dawo. Godiya Mansoor da Yaya Musaddiq da Gwaggo suketa jera musu, ni dai bance komai ba face zamewa na kwanta kawai. Dan a ganina bani ke buƙatar ƴan sanda ba Yaya Musaddiq da Hafizzullah ne. Tunda idan sake niyyar saceni yay nikam nasan abune mai sauƙi a garesa. Nama fara zargin bayan Nurse likitan ma nasa ne. Kai kowama dake asibitin kallon yana da alaƙa da shi nake yanzu. Sai dai ban san ta yanda zan fito na faɗi hakan ba kuma a fahimta a kuma gaskata ni…..
💢💢💢💢💢💢💢
Agogon dake bangon ɗakin ta sake kallo a karo na barkatai, sai kuma ta ja sirrin tsaki. Ɗagowa mijin nata yay ya kalleta. Ganin yanda ta ɗauke kai gefe ya sashi faɗin, “Lafiya kuwa kike Safina?”.
Kanta ta ɗan girgiza, cikin nuna damuwa ta ce, “Ba komai. Yaron nan ne dai al’amarinsa ya fara bani tsoro. Kalla agogo maganar ɗaya ake na dare amma har yanzu bai shigo gidan nan ba. Hakan na nufin a asibitin zai kwana ko mi?”.
Agogon ya kalla shima, sai kuma ya ɗauka wayarsa batare da yace mata komai ba. Kunnensa ya kai alamar kira yake bayan yay ƴan danne-danne. Ana ɗagawa kuwa bayan amsa sallama ya ce, “Ɗan uwanka bai dawo gidan nan bane har yanzu Attahiru?”. Ɗan jimm yay alamar saurare. Sai kuma ya janye wayar batare da ya sake cewa komai ba. Kallonsa Mamy tayi cikin ƙagara ta ce, “Bai dawo ba ko?”. Kansa ya jinjina mata alamar eh. Zai cigaba da aikinsa a computer ta dakatar da shi. “Ya kuma zaka cigaba da aiki ka dadynsu? Ka kirashi ɗan ALLAH mana muji yana ina”. Kafeta yay da ido na tsawon sakanni. Sai kuma ya girgiza kansa da faɗin, “Mansoor yaro ne ƙarami Safina. Karki manta shirin ɗaura masa aure fa ake nan da kwanaki huɗu. Kinga ko ai yasan abinda yake ko”.
“Nifa gaskiya Daddynsu bana wani jin batun auren nan a raina yanzu. Kuma dama can kaima kasan dan ya nace ne akan yarinyar nan yasa ka zuba ido da kuma dagewa da nayi nima saboda yarinyar ta shiga raina da farko. Amma magana ta gaskiya maganar matar kawunta ta ɗazun ta shigeni matuƙa. Shiyyasa tunda na dawo gidan nan naketa auna abubuwa. Dan zancen abin a duba ne fa, musamman idan muka tsaida hankalinmu muka nazarci komai a yanda yake”.
Idanu kawai ya zuba mata kamar zai cinyeta da su. Itako ta ɗauke kai tana wani kum-kum da fuska tabbacin zancen nata fa tun daga zuciya ne.
“Safina kin san kuwa mi kike faɗa? Kin san fa yanda ɗanki ke matuƙar son yarinyar nan. Idan har a baya na kasa hanashi dake kanki a yanzu mi kike tunanin zan iya? Naga kece kika zaƙe da faɗar ƙyawawan halayyar yarinyar a baya duk da ni na nuna batai min ba. Ina baki shawarar kawai ki bisu da addu’a kamar yanda kika saba tun farko. Maganar matar kawunta kuma ai ba lallai ne ya zama gaskiya ba. Tunda ba’a san wani kalar kidnappers ne suka kamata ba…..”
“Oh amma yallaɓai su Kidnappers ɗin har suna da wani banbanci da juna ne?. Ai duk wanda akace kidnapper to Kidnapper ɗinne kawai babu wani ba rabe a ciki. Na kula yanzu ba gane maganata kake ba, bayan kuma ada ba son yarinyar kake ba, ban san miya canjaka a yanzu ba kuma. Amma dai ka zauna kayi nazari kaima. Wlhy sam babu alamar wahala a tattare da yarinyar nan. Sai ma uban haske da ƙyau data ƙara duk da kuwa sau biyu na taɓa ganinta ido da ido. Amma ai biye nake da program ɗinta duk sati a gidan tvn su.”
Shi kam dai Dad ɗin su Mansoor yama kasa magana. Dan mamaki ma da al’ajabi matar tasa ke bashi yau kam. Sai yake ganin kamar ma ba ita ba. Irin wannan kafiya haka har ina kuma. Anya kuwa ba wani ne ya zugata ba?. Bashi da mai bashi amsa. Dan haka ya girgiza kansa kawai yana ƙoƙarin manyan abubuwan dake ransa tare da haɗiyesu a zuciyarsa da ga shi sai UBANGIJINSA. Gudun damuwarta saboda tanada hawan jini ya sashi sassauta nasa yanayin, cike da kulawa ya ce, “Tom naji zanyi nazari kamar yanda kika ce in sha ALLAH. Kuma zan yi bincike. Shima ɗan naki bari na taɓasa a waya. Ki kwanta ki huta kema”. Kafin ma tace wani abu ya ɗauka wayarsa ya fara ƙoƙarin kiran Mansoor……..✍️
Tofa wata sabuwa masu karatu🥱
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆
……Yana kai wayar kunnensa dai-dai nan ma yake jin horn ɗin motar Mansoor ɗin da ƙarar buɗe gate. Wayar ya sauke tare da ajiyar zuciya ya ce, “To Alhamdullah gashi can ma ya dawo ai. Sai ki kwantar da hankalinki
Ajiyar zuciya Mamy ta sauke kuwa. Ta yunƙura zata miƙe Dad ɗin ya zuba mata ido. “Ina kuma zaki?”. “Zanje na duba shi ne mana. Kofa abincin dare baici ba. Kasanshi kuma da abinci, inba tsaresa akai ba ba wani son ci yake ba”.
Kai Dad ɗin ya girgiza. Sai kuma ya ce, “Uhm kinga Safina zauna Please”. Babu musu ta koma ta zauna. Sake cemata yay “Kwanta sai da safe. Tunda dai Mansoor ba jariri bane balle kice baki gama rainonsa ba.” tasan halin mijin nata dan haka bata sake magana ba kuma. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya tana akan son sanin a wane hali ɗan nata yake ciki. Amma tunda yace bazata je ba to bata isa fitarba kuwa. Shima dai hankalinsa ya sake maidawa ga aikinsa bai sake bi takanta ba kuma. Ga shi ya haɗe fuska dan bama ya son tace zata roƙesa ko ta takura masa da batun auren Mansoor ɗin kuma…..
💞🌟💞🌟💞🌟💞
Washe gari kamar yanda doctor ya faɗa aka sallameni. Gwaggo Gudidi taso wucewa da ni can Dawanau gidanta amma Yaya Musaddiq ya roƙeta kan ta barni na koma can gidan ɗin. Tunda har Mansoor yayi magana kan baya son a ɗaga bikin nan a yanda yake koda na kwana ɗaya ne kawai ayi a wuce wajen. Ya kamata kuma muje can gidan Abba a ƙarasa komai daya kamata kada halin Mum ya dameta. Badan Gwaggo taso hakan ba ta yarda.
Tarba muka samu babu yabo babu fallasa da ga Mum. Hakama su Baby na zaune a falo amma babu wanda yay min sannu ko nuna farin cikin dawowata garesu. Sai auta ne ya tsillo da gudu ya ruƙunƙumeni. Duk da miskilancin yaron sai da ya furta, “Adda nayi kewarki. Adda Bibaa tace kin mutu bayan sake ganinki ba ashe ƙarya take min”.
Murmushi kawai na masa tare da shafa fuskarsa. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “Ta mutu kuma? To in ALLAH ya yarda ba yanzu ba, mu bazamuga mutuwa ba sai alkairi nan da kwana huɗu. Ke kuma baƙin halin naki sak na uwarki dai ashe, da wani shegen goshinki kamar jirgin tsallake ruwan bagwai”. Ta ƙare maganar tana nuna Bibaa data tura baki gaba zomomo. Na zata Mum zatayi magana. Sai naji shiru ta dai sake tsuke fuska. Ni dai sai ma na yunƙura na nufi bedroom ɗinmu dan so nake na ɗan watsa ruwa ko zanji daɗin jikina. Yanda na tadda ɗakin kaca-kaca sai da ƙirjina ya buga. Abu sai kace turken dabbobi. Wai ni yaushe Bibaa zatayi hankali ni Samraah. Na jima tsaye zuciyata cike da takaici ga ƙyanƙyami dan bazan iya zama a ɗakin ba. Dole na juya na fita cikin ƙarfin hali da son ƙarfafa kaina. Har yanzu duk suna a falon, Gwaggo Gudidi tai saurin faɗin, “Ya kuma kika fito Samraatu lafiya dai ko?”.
Kaina na jinjina mata a yanayin rashin ƙarfi jiki, cikin yamutse fuska na ce, “Gwaggo zan ɗakko kayan shara ne ɗakin yayi datti ina jin ƙyanƙyami”.
Dukansu sai da suka ɗago suka kalleni. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “To kaji kuma wani sheɗancin kuma, yanzu duk waɗan nan zagada-zagadan ƴan matan uwa wa ƴan matan amarya a gida ashe hotiho suke. Yo ni dama tunda na shigo naga gidan yamun wani harmutsai a ido nasan ana ƙwaɓa hauka dan har bashi-bashi da tsami-tsamin dauɗa nake shaƙowa ma. Yanzu ke Julaila kike ko mima oho miki bayan koyama ƴaƴanki rashin kunya abinda zai taimaki rayuwar tasu ma kin tauyesu basu iya ba. Komai kun tattara akan marainiyar ALLAH. To wlhy ba mugunta kikai mata ba idan ma ke haka kike tunani, su waɗan nan da kike gani ƴan hutu a gabanki su kika kashewa rayuwa, dan su zasu gurji kan ubansu nan gaba kaɗan. Zaku ma ki tabbatar da hakan ke da su ranar da tusa ta ƙarewa bodari, ɗiya mace bata iya komai ba ai bata cika mace ba wlhy, babu kuma namijin da zai juri zama da ita, idan ma ya haƙura ya jure dan yanada kuɗin biyan wasu suyi to bazata taɓa daraja a idonsa ba dan wataran ko shine ƙaruna akan kuɗi zai so matarsa ta masa hidima. Kai ai wlhy baki birgeba kuwa. Ashe ma fuggukar taki da ɗaga hanci kamar ƙofar gora na wofine” ta ƙare faɗa a fusace. Bibaa ta nuna da Baby “Ku dan ubanku Imamu ku tashi ku ɗakko kayan shara, ke kuma zoki zauna anan wazai barki kiyi wani aiki kina fama da kanki. Zakiyya ma na hanya gyaran jiki zata fara miki yau ɗin nan dan duk da gaki nan fes da ke ga kuma ƙarancin lokaci bazai hana nasa a kwaskware min ke ba dan kowa ya sake tabbatar da amarya ƴar gata zan kai”.
Sosai Bibaa da Baby ke kallonta ransu a ɓace, sai kuma su kalla Mum da taƙi cewa komai. Tsawa ta daka musu, babu shiri suka miƙe a zabure kuwa. Nayi mamakin shirun Mum dan nasan yanda suke ƴar tsama da Gwaggo Gudidi, rashin jituwar tasu ma ce tasa Gwaggon daina zuwa gidan gaba ɗaya. Amma dai dole a wannan shirun nata akwai ayar tambaya.
Su Baby naji na gani Gwaggo ta turkesu sukai gyaran ɗakin, sau biyu tana maidasu su maimaita wai bai mata ba. Bayan sun kammala sunata zungure-zunguren baki tasa Bibaa ta tattara kayanta ta maida ɗakin Baby. Shima auta aka haɗa masa nasa aka sanda shi ɗakin Mum. Acewar Gwaggo nan sune zasu zauna har sai biki ya tashi. Ni dai dariya ma abin ke ban. Dan Gwaggo Gudidi fitinanniya ce sai dai idan bataso ba zaka ga ta watsar da kai kamar mai shiru-shiru. Halin namu dai na kamanceceniya sosai, ƙila dai ita na gado ma (🤣). Fuu Mum ta tashi batare da tace mana komai ba ta bar falon, mu duka da kallo muka bita, sai dai babu wanda yace komai.
“Mum na shiga ɗaki waya ta ɗauka, sai faman huci take da jan numfashi, kai daka ganta kasan dama danne komai take da ƙyar kawai. Ko sallama balle gaisuwa batayi ga wanda ta kira ɗin ba ta fara magana a hasale. “Mama magana ta gaskiya bazan iya haƙurin da kikace da wannan tsohuwar ba. Kinga daga dawowarsu yanzu tabi ta addabar min yara. Nidai bazan iya ɗauka ba. Wannan plan ɗin naki na fara jin kamar bazan iya juresa ba. Ina dalili yara tun suna ƙanana sun tare min komai yanzu kuma an saka min ƴaƴa a gaba duk da kwacen saurayi da akaima Baby”.
Siririyar dariya akayi mai sauti daga can. Sai kuma dattijuwar murya ta fara faɗin, “Jalila wani lokacin idan kina wani shashancin sai nake ganin kamar bani ce na haifeki ba. Ke matsalarki baki iya ɓoye abu aranki. Shiyyasa tun farko ko riƙon yaran nan nace ki yi na siyasa ta yanda koshi mijin naki bazai fahimci baki ƙaunarsu ko son zama daku ba. Amma ina kin kasa. Yanzu kina ganin matsala ta taso kaso biyu bisa uku na mutane har yanzu ke suke zargi da satar yarinyar nan har da ƴaƴanki. Ko ƴan sandan nan idonsu kema na’a kanki. Amma kin kasa fahimta. Ko shi mijin naki badan mun danne masa kai ba tuni kina ganin bake zai zarga ba ne? Shin wai rayuwa babu siyasa ta yiyu haka ne?”.
“Wai Mama sai kice siyasa, siyasa. Dan kawai ina son na birge wani sai na dinga nunawa wanda bana so so. Nidai a bar wannan maganar, kawai ki faɗa min abinda zanyi na gaba dan na fara ƙosawa da halin tsohuwarnan, zan karta mata rashin mutunci wlhy bazata zo cikin gidana ta hanani rawar gaban hantsi ba”.
“A’a ban aikeki ba nikam. Ki bari anjima kaɗan zan zo gidan. Dama ga ƴar uwarki nan tazo itama babu jimawa. Kuma ni abinda nasa a raina kofa auren nan akai sai munyi duk yanda zamuyi basu zauna lafiya ba. Dan yanda ta rabashi da takwarata itama bazata taɓa jin daɗin ba. Na fara ji kuma a raina wannan tsohuwar duk itace ke ƙulla komai, maybe ma itace ta amaso asirin da aka juya kan yaron nan. Shiyyasa sam ban sonta tun aurenki da Imam. Amma idan sun san wata su basu san wata ba ai. Daga su har ita zasu ci ubansu ne da ni suke zancen. Yanzu dai ki cigaba da kwantar da hankalinki bana son jin wata fitina. Bari na ƙarasa aiki mu fito”.
“To Mama dan ALLAH kuyi sauri”.
Suna ajiye wayar zama tai jagwab a bakin gado, ita kaɗai tasan irin ƙunar da take ji a ranta game da auren nan. Ji take kamar ta sakama yarinyar nan shinkafar ɓera a abinci ta mutu kowa ya huta, dan tafi sauran ƴan uwanta tsaya mata a rai, shegiya ga ƙyawu kamar wadda ta tashi a rayuwar hutu, duk baƙar izayar da take mata kullum zaka ganta fes-fes ga shegen Musaddiq ɗin can kullum cikin saya mata suturu yake. Tanada plans daban-daban da zata iya bi ta wargaza auren nan dama rayuwar yarinyar nan duka, amma Mamanta na hanata. Amma yau kam tana ji in har Mama bata iya tayi komai ba itafa zatabi ɗaya daga cikin plans ɗinta ne. Dan bazata taɓa yarda a ƙwacema ƴarta da tafi so abinda ke nata ba. Sai dai ko duk su rasa, ko kuma ƴarta ta samu ita…….✍️
Humm Mom to bari muga yaya wasan zai kaya 🚴.
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙
…….Bayan nayi wanka nayi sallar Azhar da tayi ina zaune ina ɗan tsakurar abinci zuciyata fal tunani. Zantukan mutumin nan kawai ke min kai-kawo a rai. Dan tun jiya nake son fassarasu amma na gagara hakan. Ina son na sanar ma Mansoor da Yaya Musaddiq gaskiya amma ina jin shakkun abinda zai je ya dawo. In har zai iya saceni harna tsahon kwanaki goma sha bakwai, kuma ya dawo dani gida batare da wani ya gani ko yaji ko gano shine ba har jami’an tsaro wane makami kuke tunanin zan iya ɗauka domin kare kaina?. Bily ina da taurin kai da kafiya. A wasu lokutan harda tsiwa ma. Amma fa babban weakness ɗina a rayuwa sune ƴan uwana guda biyu. Zan iya bada rayuwata a wajen karesu kamar yanda nasan suma zasu iya hakan. Dan su ɗin garkuwa ta ne. In dai hakane kenan ya kamata na kwantar da hankalina na nutsu waje guda har a gama bikin nan na koma ƙarƙashin ikon Mansoor. Na tabbata zai taimaka min da duk irin gudunmawar da nake buƙata game da bama ƴan uwana garkuwa batare da hatsabibin ya farga ba. Na kuma tona asirin sa ta hanyar da bai zato ba. Tunda yanada wayo shima ya kamata a tabbatar masa da TSUNTSU mai WAYO ta baki ake kamasa. Hakan kuma bazai yiwu ba har sai na nutsar da hankalina waje ɗaya na shirya nima tsaf ta yanda zan zame masa tamkar kifin tarwaɗa da baza’a taɓa iya kamashi da santsin kalkashi a hannu ba. Dan a yanzu ni kaɗai nasan inda video ɗin yake. Dan abinda Mansoor bai sani ba ni da kaina na goge na wayarsa, badan kuma ban yarda da shi nai hakan ba. A’a ina tsoron a masa barazana dani ne a amsa wataran. Shiko Yaya Musaddiq dama bai tura ba kwata-kwata. Dan haka na ciresa daga tawa wayar nima na maidashi a flash drive dana sayo na adanashi inda daga UBANGIJINA sai ni muka san inda yake…..
“Oh Amarsu irin wannan zurfin tunani haka?”.
Aunty Zakiyyar Gwaggo da bamma san lokacin data shigo ba ta faɗa cikin katseni ta hanyar taɓani na kawo nannauyan numfashi. “Har kin fara tunanin rabuwa da gidan ne raguwa? Sai bakin tsiya kuma”. Ta sake faɗa cike da tsokana. Murmushi na sakar mata ina duƙar da kaina. Na ce, “Kai aunty yaushe kika shigo bamma sani ba”.
“A taya zaki sani kin lula duniyar tunani. Yaya jikin naki dai to?”.
“Alhamdullah Aunty, dama babu inda ke min ciwo, allurar da suka min ce kawai ta sakani wannan dogon barcin”.
“ALLAH sarki to Alhamdullah ai haka akeso. ALLAH kuma ya kiyaye gaba. Ya tona asirin duk wanda keda hannu a kan hakan. Damma dai Alhamdullah addu’a tayi tasiri ƙwarai da gaske. Kuma da alama duk ma wanda suka kamakin ba mugaye bane. Dan masu amsar kuɗin nan sunfi haɗari. Amma waɗan nan da alama suna da tasu manufar ne a kanki gaskiya. Na kuma fi ƙyautata zaton akan auren nan ne kamar yanda kowa ke zargi, musamman akan wannan maman taku da Baby. Kowa yafi dangantasu da al’amarin nan wlhy, dan zuciyarsu babu ƙyau komai zasu iya aikatawa tunda sun gagara ɓoye hassadarsu”.
“In sha ALLAHU Aunty bazasu ci nasara ba kuma. Tunda gashi ma ALLAH ya kuɓutar dani cikin sauƙi, dan tabbas addu’ar ce tai tasiri a kansu suka sakeni batare da sun shirya ba, amma kuma ni bana danganta al’amarin da su Mum da dalalin auren nan kamar yanda kowa ke kallo, dan in dan auren ne ai kinga babu yanda za’ai su sakeni haka da sauƙi da sai lokacin bikin ya wuce ko”.
“Tabbas hakanne kam Samraah kema kinzo da batun dubawa. Amma dai ai zaki iya ganesu? Dan naga angon nan naki da gaske ya shirya ɗaukar mataki, a yanzu haka suna ƙofar gida da ƴan sanda da Musaddiq da Yaya Imam.”
Idanu na zuba mata kawai, sai kuma na nisa a hankali na ce, “Aunty bazan iya gane su ba. Saboda abinci kawai suke kawo min sau uku a rana. Kuma komai nasu a rufe hatta da hannayensu ma. Kuma basa mun magana sai dai su ajiye kawai su juya su fita. Ko’a ranar dana samu damar kiran Yaya Musaddiq ma kwato nayi, sai kuma suka kamani bayan sun amshe wayar suka shaƙamin abu suka ɗaukeni da ga gidan sai farkawa nai na ganni a wani sabon waje. Hakama yanzu sai da suka min allura sannan suka kawo ni ƙofar gidan nan.”
Aunty Zakiyya na shirin yin magana dai-dai nan Yaya Musaddiq yay sallama. A tare muka amsa masa. Batare da ya shigo ba yace nazo. Miƙewa nai na ɗauki hujjab ɗina na saka sannan na fita. A falon baƙi na samesu shi da d.c.o da Mansoor sai Gwaggo Gudidi da Abba. Daga can gefe Baby ce ta masifar zubama Mansoor ido kamar zata cinyesa. Shiko sai wani cin magani yake tamkar an aiko masa saƙon mutuwa. Sai da muka haɗa ido ya ɗan sauke numfashi tare da sakar min murmushi. Murtani na mayar masa nima ina duƙar da kaina ƙasa. Gaisar da d.c.o nayi cikin girmamawa, shima ya amsa min da kulawa tare da tambayata ya jikina. Kaina a ƙasan na ce, “Alhamdullah bana jin ciwon komai Sir”.
“Masha ALLAH, Alhamdullah haka muke son ji ai dama. Samraah wannan zuwan naki ne. Muna fatan zamu samu haɗin kai domin son sanin komai daya faru dake tun daga fitarki a gida a waccan ranar har zuwa yau da ALLAH ya maido mana ke bisa ƙarfin ikonsa”.
Babu musu na jinjina masa kaina tare da faɗin, “In sha ALLAHU ranka ya daɗe zan faɗi abinda na sani”.
Zamansa ya gayara sosai yana fuskantata. Kafin ya furta, “Yauwa Ina jinki”. Bayani na fara masa tiryan-tiryan tun daga shirin fitata. Kiran dana samu daga MD har zuwa fita cikin layi da tare napep. Jefamin handkerchief da wanda na samu a napep ɗin yayi bayan ya kira sunana tabbacin ya sanni ko yana son tabbatar da ni ɗin ce, har zuwa buɗe ido na ganni a wani waje daban. Yanda na rayu a gidan farko har zuwa kiran wayar Yaya Musaddiq da nayi da wayar ɗaya daga cikin mutanen da kuma canja min gida da sukayi. Sai dai na samu kaina da kasa faɗar wanda ya saka akai kidnapping ɗin nawa kamar yanda ya nuna min kansa da buƙatar na bashi abinda ke a hannuna da yayi, hakama dalilin ɗaukar tawa duk ban faɗa ba. Maidoni gida da sukayi da kuma kiran da yayma Nurse a asibiti ta bani. Kawai dai na sanar musu kamar yanda na sanarma Aunty Zakiyya ne. Sosai falon yay tsitt suna saurarena. Yayinda d.c.o ya kafeni da idanu ko ƙyaftawa bayayi. Jinai duk na tsargu, amma na dake abina kun dai san mutuniyar taku ai. Dan kansa ya gaji ya janye idanunsa a kaina. Cikin sauke numfashi ya furta, “Kin tabbata iya abinda ta faru kenan Samraah? Dan bana son ki ɓoye mana komai, kar kiji tsoron barazana ma idan sun miki babu abinda zai faru”.
“Iyakarsa kenan yallaɓai. In har na ba mance wani abu to bashi da muhimmanci ne”.
Kansa ya jinjina cikin nuna gamsuwa, kafin ya kalla yaronsa dake rubuta duk abinda nake faɗa, sai kuma ya maida idonsa kansu Yaya Musaddiq. “Inaga fa dole ne mu sake gayyatar MD ɗin nan nasu, dan komai idan aka tattara ya ta’allaka ne akansa. Amma bawai ina tabbatar da shi ɗin ne ba. Dan ita shiri’a saɓanin hankali. Kuma tunda har ta dawo gida cikin ƙoshin lafiya Alhmdllh, koma minene zai zo mana da sauƙi. Yanzu dai inaga sai a kiyaye gaskiya. Fita anyhow dole ta jingine ta. Mukuma duk inda ta saka ƙafa idan ma har ta fitan zata kasance a ƙarƙashin kulawarmu ne.”
“In sha ALLAHU babu damuwa ranka ya daɗe. Dan ko batun zuwa aiki ma dama zata ɗan dakata, in ma zata cigaban ne sai bayan bikinta idan mijinta ya amince sai taje ɗin”.
“Wannan ma dabara ce kam mai ƙyau sosai. Amma taron bikin nan fa dole ayisa da kulawa. Koda yake zamu haɗata da jami’ar mu mace domin ta kasance da ita ama duk inda take like handbag ɗinsu na mata. Hakan zai sauƙaƙa mana aikin mu insha ALLAHU.”
Kowa a falon yaji daɗin zancen nasa kuwa. Dan har fuskokinsu sun gagara ɓoyewa. Ni dai kaina a ƙasa kawai abubuwa da yawa nata min kai kawo a zuciya. D.c.o ya ɗan ƙara tattaunawa da su Yaya Musaddiq kafin suyi mana sallama su wuce. Tare da jaddada min duk sanda suka buƙaci gani na zan iya ganinsu a gidan, ko kuma su aiko a ɗaukan zuwa office ɗinsu. Da to kawai na amsa musu ni dai. Gwaggo Gudidi sai jera musu godiya take. Mansoor da Yaya Musaddiq kuma suka tafi musu rakkiya waje. Muma miƙewa mukai muka koma cikin gidan. Dan Aunty Zakiyya ta tabbatar min da yau babu fashi zata fara min gyaran jiki. Ban musa ba, dan nima ina son zuwa fadar masoyina fes tamkar wata ɗan daren sha biyar………✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏
……..Tun daga shigowar ƴan sanda har fitarsu a gidan Mum ta sani, amma batako leƙo ba. Sun tafi ma babu jimawa sai ga Mamanta da ƙanwarta dake aure a Bauchi. Acewarta tazo ne bikin Samraah domin yima Mom Kara. Bata bari sun zauna a falo ba ta shige dasu bedroom ɗinta. Da kanta kuma ta fito ta haɗa musu abinci takai musu. Ko kunya babu yanda ƙanwarta ta cire mayafi ta fara lodar abinci haka itama Maman tayi. Kai bakace a gidan suruki take ba. Bayani ta sake ma ƙanwar tata akan duk yanda aka samo Samraah, dan ita Mamansu tasan komai. Ƴar uwar tata kai ta jinjina. Sai kuma tai ɗan jimm alamar tunani, kafin ta sake ɗagowa tana kallonsu bayan ta gama ƙulla abinda take ganin zai fanshi yarinyar nan tsakaninta da ALLAH. Dan magana ta gaskiya ita su Samraah sun jima suna bata tausayi, sai dai bazata iya fitowa ta faɗa ba dan tana shakkar Yayar tata da Mamansu saboda masifaffu ne na bugawa a jarida. Amma tana ji a ranta a wannan gaɓar bazata bari a cutama marainiyar ALLAH ba. Sai dai dole tai komai cikin siyasa. “Niko inada shawara”. Ta faɗa kanta tsaye.duk sake maida hankali sukai a kanta. Cike da zumuɗi Mum tace, “Miye shawarar Ikili, dan ALLAH faɗi muji”.
Numfashi Ikilima ta sauke tare da ajiye cokalin hannunta ta sake fuskantarsu. “Ban sani ba shawarar ko zata gamsar daku, amma dai a yanayin da nake gani kamar guri ya ƙure mana a yanzu zata iya zama mafita. Mizai hana mubar yarinyar nan tai aurenta kawai. Bayan bikin mu duƙufa samowa Baby mijin aure na garari da yafi shi wannan yaron. Bayan itama ansha nata bikin mun nunama musu koda goma ta lalace tafi biyar albarka, sannan mu fara shiri akan komai ma da muke ganin ya dace akan auren nata. Dalilina na kawo wannan shawarar shine idan fa muka hana auren nan kamar mun gogama gidan nan wani baƙin fenti ne. Kun san dai halin mutane ai, hakan kuma na nufin kammu muka cutar tunda namu yaran ne dai basuyi aure ba a bayanta, dan ita wani zai iya jin tausayinta yazo ya aureta, sannan mu za’aita zagi da zargin mun hana ko muna mata baƙin ciki. Amma idan muka bari akayi hankali kwance babu mai aibanta mu balle idan mutanen kirki sun zo neman auren su Bibaa wani shege ya sokemu. Kunga mun samu nasara biyu kenan, mun kuɓutar da yaranmu, sannan mun sama musu abinda muke fata. Yo har miye wani Mansoor yake ma komi ALLAH na tuba. Shi da dukiyar ba tasa bace ta babansa ce. Mu ɗan gaske zamu samo mai dukiyar kansa da kansa. Dama ba akwai mutumin nan daya haukace akan baby na anguwarmu ba amma tanata masa wulaƙanci ita bazata zauna da kishiya ba. To wlhy yanzu yazo nan Kano yayi wani mahaukacin gida a hotoro g.r.a ina gaya muku kuma aure yake son yi ruwa a jallo ya saka matar anan, su kuma waɗan can zasu cigaba da zamansu can Bauchin saboda ya musu tayi sunce su bazasu iya barin mahaifarsu da ƴan uwansu ba. Amma yaya kuka gani?”.
Cike da zumuɗi Maman ta ce, “Ni dai wannan shawara tamun wlhy Ikilima, amma ke Jalilah yaya kika gani?”.
Shiru Mun tai kamar bazatace komai ba, sai kuma ta sauke numfashi mai nauyi da faɗin, “Nima shawarar ta ɗan mun, sai dai ina tsoron tsutsun Baby wlhy, Dan nasan yanda ta tsani kishiya…”
“Yo biye mata zamuyi, tuni zamu shiga mu fita a dasa mata sonshi a zuciya sanda ma zata soshin fawa tai shawara. Mufa muka haifeta ba itace ta haifemu ba. Kishiyoyi kuwa ai dasu da babu duk ɗaya ne tunda ba’a waje guda zasu zauna ba”.
“Yo Mama ko waje guna ne Baby bata da matsala. Dan matansa wlhy a hakan ma kowa rayuwarsa yake babu wadda ta damu da wata tunda kowa da gidanta kuma kowacce kuɗi take juyawa na hauka. Yi kishin ma fa dama matan malam shehune sukafi zaman yin na haukannan aita damben tsiya da hayaniya. Amma mata masu aji da kuɗin nan zakiga kishin ma na ƴan boko akeyi, itama kuma dai tanada iliminta babu abinda za’a nuna mata. Kuma tana shiga zai bata maƙudan kuɗi ta fara kasuwanci kamar sauran dan haka yake yi”
“Hakane wlhy Ikilima. Ni kubar komai a hannuna kawai zanyi maganinta, yanzun kam hidimar biki duk mu ware aitayinta damu. Ai kwantan mage zamu musu a yayin kama ɓera, tuni sai suzo hannunmu batare da sun farga ba”….
(😂ALLAH ya rabamu da son zuciya to).
💦🌟💦🌟💦🌟💦
Zaune yake a office yana ƴan ayyukansa sakatariyarsa ta shigo ta sanar masa d.c.o yazo yana son ganinsa. Karo na farko da MD yaji ransa ya fara ɓaci da bibbinin da d.c.o ɗin ke masa. Idan yace da yana da dalili yanzu kam shi baiga dalilin ba. Samraah dai ce ta kuma dawo sai me kuma, shi ma yaje dubata tare da staffs nasu har asibiti. To minene kuma na zuwa masa office yau. Rashin amsa ya sashi jan sirrin tsaki, tare da bama sakatariya umarnin ta barsa ya shigo.
Fitarta bai fi da mintuna uku ba ko sai ga d.c.o ɗin ya shigo, sun gaisa cike da girmama juna. Kafin MD ya ce, “Yallaɓai akwai wata matsala ne?”.
“No babu matsalar komai MD. Waccan dai matsalar ce akan staff ɗinku Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Dan kasan koda ta bayyana ya kamata mu cigaba da bibiyar case ɗin domin gano da kama wanda sukai kidnapping ɗinta kodan musan dalilinsu”.
“Hakan nada ƙyau yallaɓai. Domin muma zamu so ace an kama sun. Sai dai muna ƙarama ALLAH godiya da kuɓutar tata cikin ƙoshin lafiya. Yanzu mike tafe da kai?”.
“Uhm kamar dai yanda aka saba zamu sake gayyatarka office ɗin mu idan babu damuwa. Kana kuma da damar muje ka samemu a can, ko mu tafi tare”.
Murmushi MD yayi mai ƙayatarwa. Sai kuma cikin rashin damuwa ya ce, “Babu matsala muje ɗin kawai, dan bawani aiki nake da shi ba sosai yanzun. Zuwa anjima kuma aikin zai iya shamin kai, kaga kuma bai ƙyautu ace ban amsa gayyatar ba”
“To Masha ALLAH, hakane kam mun gode sosai”.
Murmushi kawai MD ya sake masa yana miƙewa. A jere suka fice suna ƴar hirarsu tamkar wasu abokai. Dan haka sauran staffs basu fahimci komai ba face tunanin akan dai case ɗin Samraah ɗin ne. Kuma babu wani damuwa a cikin ganin MD da ƴan sandan dake bincike akan case ɗin tunda ba yau ne mafari ba. Suma kansu dai duk sai da suka sha tambayoyi a kwanakin baya….
💢🌟💢🌟💢🌟💢
Kwanaki na biyu kenan da dawowa gida. Kwanaki biyu kuma kacal ya rage ɗaurin aurena. Dan zuwa yau har baƙin kusa sun fara isowa musamman dangi na jiki sosai. Ga Aunty Zakiyya ta duƙufa min gyaran jiki da ɗuramin abubuwa. Niko dana faki idonta sai na zubar dan bana sha sosai. Abinda zai baku mamaki duk da haramin biki da gida ya fara ɗauka ga masu gidan babu wani alamar motsi irin na biki a tattare da su. Dan hatta da abinci da aka girkama baƙin dake a gidan yau Yaya Musaddiq ne ya kawosa. Suko su Gwaggo suka girka batare da sun bi takan Mum daketa faman ɗacin rai ba. Shi dai Abba saboda su Gwaggo Gudidi yana ɗan nuna alamar damuwa da shirye-shirye. Sai dai fa bana aljihu ba na gayyatar mutanensa kawai, sai kuma takurama Yaya Musaddiq da yake ta bayan fage akan kuɗin kayan ɗakina da wanda za’ai hidimar abincin biki. Shiko Yaya Musaddiq nata masa zame-zame. Sai a yau ya fito fili ya shaida masa karya damu shi ya riga da ya kammala komai. Dan hatta da kayan kitchen ɗina ma a tanade suke tuni. Hakama kayan gado kafintan ya jima da kammalasu duk da Mansoor yace kar ayi shi baibi ta nasa ba. Wannan zance ya ƙona zuciyar Abba matuƙa. Amma ya gagara magana kodan mutane dake cike a gidan, yasan fitowar zancen babban abin kunya ne a garesa musamman a wajen danginsu dana ɓangaren mahaifinmu.
Ban gayyaci wasu ƙawaye ba dan banda su, amma a ranar da yamma sai ga su Ruƙayya ƴan Office dinmu da gayyar ƴan ajinmu na islamiyya. Naji daɗin ganinsu sosai, dan ko kusa banyi zato ba. A bakinsu na fara jin ƙananun maganganu akan rashin kawo kayan da zanyi amfani dasu na biki da Mansoor ya ce sai daga baya dan ba’a saka ɗinkakken kaya ko ɗaya a lefen ba, kuma kowa na saka ran yau ne za’a kawo ɗin saboda kamu da ake shirin yi gashi babu kayan dazan saka. Amma har yamma shiru kake ji. Gashi yanzu banda waya a hannuna ko ɗaya. Rabona da Mansoor kuma tun jiya da dare. Koda yake nice nace yau kar yazo, kai daga jiya ma bazan sake yarda mu haɗu ba sai a gidansa. Shiko ya yarda da hakan acewarsa zai gwada yaga ko zai iya. Nayi tunanin kiranshi amma zuciyata ya ƙwaɓeni game da hakan, dan haka bance da su komai ba na haɗiye zancen a raina har sai bayan sallar isha’i da nasan Yaya Musaddiq ya dawo gida sannan na lallaɓa ɗakinsa na samesa, a wajen kamu kuwa Aunty Zakiyya ta samo kayan dana saka kawai……..✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕
……..Kai tsaye ɗakin Yaya Musaddiq na nufa. Bayan na gaishesa ya ɗan tsokaneni nai masa zancen da naji ana tsogumi ɗazun a kai. Murmushi yay min da faɗin, “Kandala ƙyale batun mutane da halinsu. Dan su basu iya komai ba daman sai gulma kawai. Yanzun nan babu jimawa muka rabu da Mansoor ɗin ma, dan munje can gidan nasa ne da kafintan da yay kayanki saboda zasu kaisu da sassafe gobe in sha ALLAHU. Ya kuma min batun kayan sai gobe in sha ALLAHU zasu kawo wata ƙanwar Mamynsu ce da zatazo da ga Dubai a yau da dare ake jira dan akwai wasu kaya a hannunta, amma shima yana cikin damuwar rashin kawo su shiyyasa ma ya kasa neman ko Hafizzullah a waya ya haɗaku dan kunyarki yake ji”.
Ajiyar zuciya na sauke a hankali. Dan nama san ƙanwar Mamyn tasu, yasha bani ita muyi waya. Murmushi yay min yana kai ma kaina rankwashi da faɗin, “Sam yanzu Kandala baki da kunya. Yanzu ni kike zuwa tambayar batun kayan aurenki ma”. Hannu na saka na rufe fuskata ina dariya. Shima dariyar yake yi. A dai-dai nan Hafizzullah ya shigo ɗakin da sallama. Dan tun washe garin da aka ganni yazo gida dama. Ledar hannunsa na warce ina faɗin, “Zaga gari mi kuma ka samo anan?”.
Ƙoƙarin warce ledar shima yake a hannuna yana hararata. Ban yarda masa ba har sai da na buɗe. Ganin awara yasa na taɓe baki ina miƙa masa. “Oh oh kwantar da hankalinka ashema naman talaka ce”.
“Oho dai, kema naga ci kike”.
“Ai ni in naci ba komai bane. Amma kamarka dai saurayi mai hurama ƴammata hanci abin kunya ne. ALLAH yau da ina da waya saina ɗauki hotonka nasa a status ƴan matanka sun gani”.
Dariya ya sanya da yimin gwalo, ya ce, “Ai sai ki samama kanki lafiya tunda baki da. Kuma sai na zuga Yaya Mansoor kar ya saya miki waya har sai kin shekara a gidansa”.
“ALLAH sarki jiki duk baƙin ciki su Hafizu. Aiko zakasha mamaki, kafin rana ita yau kasa a ranka na mallaki waya”. Na ƙare maganar ina kai masa rsankwashi a kansa.
💥💫💥💫💥💫
Kamar yanda Mansoor ya faɗa hakance ta kasance. Dan washe gari misalin sha biyu na rana ƴan kawo kayan nan suka iso gidanmu su uku. Zuwa lokacin baƙi sun ƙaru. Dan wasu matan ma a cikin ƴan Gwarzo ma sun iso. Tuni Aunty Zakiyya ta shiga maƙwafta tai kiransu dan Mum taki aikawa a kira kowa aiki. Sai ma yi take kamar wadda ta ruɗe. Dan ma ƙanwarta na tare da ita tana saitota. Baby kam ban san ina ta tafi ba dan tun jiya da yamma ban sake ganinta a gidan ba kuma. Waɗan nan kaya sun matuƙar girgiza sukata. Dan da gasken gaske Mansoor da ahalinsa sun nuna bajinta. Duk da ba fariyya akayi ba komai na nan dai-dai misali amma kuma na bajinta da zai tabbatar maka an kashe kuɗaɗe sosai. Dan komai acan-acan ko maƙiyi yasan kaya sunyi ga kuma kayan lefe da dama sun riga sun kawo.
Har aka gama karɓar kayan ni dai ban ko leƙo ba sam. Sai da dangin Mansoor suka wuce sannan aka maido kayan nan ɗakin da muke da su Gwaggo Gudidi sannan su Asiya suka tsareni sai na gani harda Aunty Zakiyya. Na ɗan kalla sama-sama na rufe akwatin ni dai. Har raina ina sake jin kima da girman Mansoor matuƙa dama ahalinsa gaba ɗaya….
💦💦💦💦💦💦💦
“Aunty dan ALLAH ki kwantar da hankalinki ni banga aibun yarinyar nanba sam wlhy. Ga danginta mutanen kirki. Karfa kiga irin tarbar da akai mana ta girmamawa wlhy.”
“Humm Anesa ni fa bance tanada aibu ba. Amma ya kamata ku fahimci abinda nake nuna muku. Yanzu dan ALLAH da kikaga yarinyar tayi kama da wadda akai kidnapping na tsawon sati biyu da wasu kwanaki? Nafa fiku son yarinyar nan, kuma har yanzu ina jin sonta a raina”.
“Aunty wlhy ni ban ganta ba.”
“Humm to ai naso ki ganta da kin tabbatar. Amma al’amarin da mamaki ace ai kidnapping yarinya budurwa ƙyaƙykyawa kamar wannan wai ta tsallake tarkon namiji. Sannan kuma basu nema kuɗin fansa ba saboda sun sami abinda yafi kuɗin kenan. Ya kamata kowa ya gane maganar matar kawunta da abar a duba ce fa. Dan dolene ɗayan biyu a samu ɗaya. Kodai da ƙafarta tabi wanda suka sacetan nan zuwa wani hotel ko guest house. Ko kuma wanda sukai kidnapping ɗin nata sun samu abinda yafi kuɗi a jikinta. Wai Kinga kuwa yanda ta ƙara wani fresh na haske da laushin fata tamkar wadda ke rayuwa a ac. Ai bana jin ko kafin a sacetan jikinta yay wannan luf-luf ɗin. Amma da yake yaron nan ya makance da shirme shi ko sau ɗaya bai zauna yayi tunanin komai ba. Na rasa mike damun kan Mansoor ne. Ga ubansa shima yama ƙi ya sauraran balle ya gane abinda nake nufi. Kema kuma gashi kina nuna bazaki fahimceni ɗin ba”.
“A’a Aunty, ba fahimtarki ne bazanyiba nikam. Abinda kawai nake son ki duba bakin alƙalami fa ya riga ta bushe. Tunda gashi yau har sauran kayan lefe mun damƙa musu. Sannan Mansoor ya sanar min sun kai kayansu can gidansa wasuma a dangin nata na jerensu yanzu haka. Sannan Aunty gobe ne fa ɗaurin aure. Kuma kin ce Abban Attahir ma yaƙi fahimtarki balle ma shi Mansoor ɗin da kin gagara tunkararsa da batun, to tayaya kike tunanin zamu iya wani abu a ƙurarren lokacin nan?”.
“Zamu iya kuwa Aneesa. Dan anma zauna a filin ɗaurin aure ya watse ballema wannan da sai gobe. Mansoor da kike gani sam bashi da wani isashen wayo. Wlhy koda yasan yarinyar nan bata ƙwarai bace zai iya shanyewa saboda son da yake mata na masifa da ni sai a yanzu ma zuciyata kemin wasuwasin bana lafiya bane. Dan abun yayi yawa wlhy. Wace soyayyar haukace haka kamar wani labaran littafin hausa. Ku shaida ne nima naso yarinyar nan a baya, dan ina gaba-gaba wajen shawo kan Abban Attahir harya amince da auren nan duk da fama da aka sha sosai saboda dagewar da yay akan sai Attahir ya fara aure sannan Mansoor ɗin yayi. Amma magana ta gaskiya zancen matar kawunta na jiya ya dawo dani a hankalina. Sannan ganin yarinyar a cikin hayyacinta fes saima ƙyau data ƙara shima ya tsaya mun a rai. Dan haka shekaran jiya nace Mansoor ya kamata ya nema likita yasa a mata gwajin ciki amma yaron nan sai ya koma min wani kalar tausayi kamar zai yi kuka, yana faman roƙona nabar wannan maganar dan ALLAH kada wani yaji, shi yasan wacece Samraah. Da ace wata matsala ta faru da ita acan sai ta faɗa masa bazata munafuncesa ba. Kajimin yaro fa dan ALLAH”.
“Humm Aunty kar kiga laifinsa. Dan dama abin da kamar wuya ace ya fahimta kai tsaye. Amma dai kam al’amarin akwai ɗaure kai”.
“Bana wasa ba ma. Inda shi wani ne dan ALLAH basai ya haƙuraba, idan ma ya matsune yay auren dole a goben basai a ɗaura da Waleeda ba. Nasan dai Daddynta bazai ce komai ba wlhy”.
Idanu sosai ƙanwar tata ta waro waje. Sai kuma ta ɗan murmusa da faɗin, “Kai Aunty wannan ai babbar magana ce. Ni dai abinda nake gani anan kawai addu’a ce tafi dacewa. Sannan kisa a ranki in sha ALLAHU abinda zuciyarki ke ayyana miki bazai zama hakan ba.”
Baki kawai Mamy ta taɓe batare data sake cewa komai ba…..
💢💫💢💫💢💫💢💫💢
RANA BATA ƘARYA BILYN ABDULL. MASU IYA MAGANA SUN CE SAI DAI WAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA. Na yarda da batun masu hikimar zance. Domin kuwa nima da kaina na yarda wannan rana tawace kam. Sannan in har Mum na amsa sunan uwa a gareni to taji kunyar kuwa. Dan halayyar da take nunawa yasa dangin mahaifinmu suka gagara haƙuri sai da suka yayyaɓa mata magana. Dan har Kawu Lurwanu na iƙirarin mata dukan tsiya. Yaya Musaddiq ɗin da take gani aba komai ba a gareta ne yayta basu haƙuri da kareta har aka samu ƙurar ta lafa. Gida ya gama cika danƙam da mutane. Dangi na kusa dana nesa sun nuna halacci. Ga abinci kala-kala anyo daga Gwarzo batare da an zaman jiran sauraren na nan gidan Abba da kunya ta sakashi kawo buhun shinkafa a jiya da dare ba, sai wasu ƴan kayan miya cakwat da nama a baƙar leda abin zakkunya dai.
Kafin goma na fito shar dani a amaryata. Ga ƙunshin da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya ta rangaɗa min a daren jiya ja da baƙi yay masifar fitowa kamar kaci. Duk da gyaran ƴan kwanaki akai mun na fito fes dani kamar fure a tsakkiyar lu’u-lu’u. Wani cotton lass ne a jikina lemon green ɗaya daga cikin kayan da suka kawo jiya aunty Zakiyya ta ciro min. Dan duk kayan da zanyi hidimar biki dama sai da Mansoor ya ɗaukan mukaje tela ya gwadani tun kusan wata biyu da ya shige. Aiko ɗinkin yay masifar zaunamin a jiki. Sai wata stones sarƙa mai ƙyalƙyali da walwali tamkar diamond na gaskiya. Awarwaraye zobba da komai sunji a hannayena. Ta sama gashina da a daren jiya shima yasha wanki daga ƙanwar mijin Aunty Zakiyyar dai dan aikinta kenan shima sai ƙyalli da ɗaukar idanu yake. Bayan ta gama tsaramin kwalliyar da naita zame-zame a farko aka naɗa min ɗauri na azo a gani. Nan take hasken camara na waya ya shiga kai-kawo a kaina. Nanfa wasu sukace sai sun turama ango fa. Ciki harda Hafizzullah. Ban tanka musu ba face murmushi kawai da nake yi……..✍️
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆
……Daga can tsakar gida kam taro yay taro gida ya kacame da hayaniya irin ta biki, anan ɗakin ƙawayena na zagaye dani. Wasu na hotuna wasu na kwalliya, wasu na hirarsu akan batun dinner da za’ayi bayan an kai amarya. Dan can gidan su Mansoor ɗinne suka shirya. Kiran da Yaya Musaddiq yazo yamin ne ya sakani saka gyale na rufe har fuskata. Shine ya kama hannuna har falon baƙi. Tunda muka fito kuwa gidan ya sake ruɗewa da buɗe-buɗe. Ni dai kaina na ƙasa a cikin gyale dan haka kawai sai naji ina jin kunya kowa.
Ban ida daburcewa ba sai da muka isa falon baƙi. Dan ganin kaf kawunaina na ɓangaren uwa da uba harda Abba. Sai gwagganni da innoni suma dai duk suna nan na kusa sosai. A tsakkiyarsu Yaya Musaddiq ya kaini ya zaunar ƙasan carpet. Shima sai ya nema waje ya zauna.
Kawu Musa ne ya fara min da nasiha mai ratsa jiki. Kafin sauran ma su dinga karɓa ɗaya bayan ɗaya. Daga baya suka koma faɗa da gargaɗi, yayinda ni kuma nike sharɓan kuka ta cikin gyale. Dan babu abinda ya tadamin hankali sai jin muryar Yaya Musaddiq na rawa alamar karaya sanda yake min addu’ar zaman lafiya a gidan aurena. Abba ma dai yamun tasa a taƙaice, daga baya kiran wayarsa da akai ya nema excuse ya fita, da alama kuma kiran da akai masan nada matuƙar muhimmanci ne. Dan naga sai da ya fara magana da Kawu Musa suka miƙe tare suka fita. Fitar tasu bai hana iyayena cigaba da mun nasiha ba, sai da suka gamsu sun min yanda suke buƙata kafin suka sallaman Inna Hauwa ta kamani ta maidani ciki, dan mazan zasu wuce massalaci ne daga can kuma za’a ɗauro aure. Dole sai da aka sake min kwalliya bayan nayi sallar azhar saboda na ɓata fuskar dan kukan da nasha. Kaya na canja zuwa wata shadda da taci uban aiki da stones sai walwali take yi. Ga ƙamshi irin na amare ƴan ƙwalisa ina zubawa. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar nan. Lokacin da ƙarfe biyu ke cika maza suka fara dawowa alamar an ɗauro auren gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri. Wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da jijiya har ina jin wani kalar sanyi-sanyi duk da kuwa uban zafi ake zugawa a gari kasancewar watan azumin Ramadan na kawo jiki. Ƙawayena sun shiga min shaƙiyanci da buɗa a saman kai, sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba. Shin murna da farin cikin mallakar matashin saurayi ƙyaƙyƙyawa ɗan ƙwalisa mai cikar kamala da dattako irin Mansoor ne, ko kuwa fargabar rabuwa da ƴan uwana biyu ne da ke a cikin tarkon wancan terror ɗin. Bily a lokacin sam na kasa ganewa. Na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa. Sai ma wani sabon bugun zuciyar da na sake ji sakamakon shigowar aunty Zakiyya kamar a firgice tana kiran Gwaggo Gudidi data shigo tana miƙamin fura a kofi da aka dama wai na sha. Koda Gwaggo ta tambayeta lafiya, sai tace mata su Kawune ke kiranta kuma sunce tai sauri dan kamar dai akwai wata matsala. Da saurin kuwa ta fita alamar itama tana a cikin ruɗanin ne..
Na cigaba da zama kamar butun butumi a tsakkiyar ƙawayena daketa hotuna abinsu batare da su sun fahimci kamar akwai abinda ke faruwa ba. Muna nan dai shiru hayaniyar gidan na sake ƙaruwa alamar mutane na sake cika gidan ƙananun magana suka ɗan fara fitowa. Sai dai anƙi a fito da komai a fili ana ta son basar da mutane dai. Abinda ya ɗan fara tsayamun a rai shine rashin zuwan Mansoor gidan. Dan a burikanmu akwai zuwa hotuna bayan ɗaura aure da yace zasuyi shi da abokansa da kuma ni da ƙawayena da ƴan uwana. Amma dai zuciyata nata tausata akan masa uziri, dan maybe mutane sun masan yawan da hakan bazai yiwu ba ya cika wannan alƙawarin. Wannan tunanin yasa na danne zuciyata na ajiye wannan batun a gefe.
Isowar masu kiɗan ƙwarya bayan sallar la’asar yasa Inna Hussaina zuwa ta fita dani a ɗakin ni da ƙawayena. Sosai gidan ya cika da mutane har sai da naji ƙwalla ta cika min ido. Dan ban san munada taron dangi har kamar haka ba da zasu iya nuna wannan soyayyar garemu a irin wannan ranar. Ko a wajen kiɗan ƙwaryar ma duk da ba rawa nake ba tsaye kawai nake tsakiya ƙawaye na da ƴan uwana masu rawar zagaye da ni sai da dinga shigowa ana min liƙi, wasu kuma sukanyi hoto dani a waya harda masu video. Kusan ƙarfe biyar sai ga Gwaggo Magajiya riƙe da hannun Yaya Musaddiq da Hafizzullah wai sai sun min liƙi. Kallo ɗaya na musu su duka biyun na fahimci sunyi kuka. Dan idanun Yaya Musaddiq jajur suke. Na Hafizzullah kuwa har sun kumburo saboda shima fari ne kamar ni, dan mu biyun munfi Yaya Musaddiq haske. Hankalina ne ya tashi a take nima idanuna suka ciko da ƙwalla ina binsu da kallo. Amma sai suka ƙi yarda mu haɗa ido sai liƙi da sukemin kawai ana ihu kawunansu a ƙasa suna murmushin da ni kaɗai na fahimci na yaƙe ne. Duk yanda naso riƙe kukan nawa hakan ya gagara, bamma san sanda na riƙo hannayensu su duka ba cikin nawa. Dole suka kalleni a tare. Kukan na sakar musu kawai na faɗa jikin Yaya Musaddiq. Shima sai Hafizzullah ya ya rungumemu mu duka biyun ya saki nasa kukan. A take wajen yay tsitt, wasu na ganin mun birgesu da fassara abin namu da tsananin shaƙuwa ne da soyayyar juna. Wasu ko da suka san wani abu dake ɓoye sai suke jin tsananin tausayinmu da jin karaya suma. Nan take aka ringa tuno alkairan iyayenmu da musu addu’a. Dole dai Yaya Musaddiq ya jamu muka fita daga filin. Nan Gwaggo Gudidi ta jamu zuwa ɗakinsa ta dinga lallashinmu da mana nasiha. Haka kawai maganganun nata sai suke ta min kai da kawo dan na gagara fahimta da fassara wasu nikam. Kiran Yaya Musaddiq da akai a waya ne ya sashi miƙewa ya fita. Babu jimawa ya dawo yay kiran Hafizzullah. Anan ne Gwaggo ke tambayarsa lafiya? Sai yake sanar mata zasu maida kayan can gidan ne dan an gama kwashesu. Cikin nuna gamsuwa tace, “Oh to hakan yayi, bari na tattara su Zakiyya su sameku acan yanda aikin zaiyi sauri. In sha ALLAHU ai yanzu zakaga an kammala”.
Da to ya amsa mata yana ficewa. Hafizzullah ya canja riga suka fice. Babu abinda na gane a zancen nasu, amma na gagara haƙuri sai da nace, “Gwaggo kodai akwai abinda ke faruwa ne? Naga sai magana kuketa yi kamar a ƙudundune?”.
Kai tsaye tace min, “A’a babu komai ƴar nan. Kinga tashi mu koma ciki dan da anyi magriba zaki yi wanka a wanke wannan fentin da aka cika miki a fuska. Koda masu ɗaukar amarya dai sun zo ɗin sai dai mu yazam mune muka jirasu basu zasu jiramu ba”.
Banda tacewa face bin umarninta. Tunda dama nasan dai ya kamata a kainin da wuri kodan dinner da su Mansoor suka shirya. Amma kwalliya kona wanketa dole a sake wata basai munje can gidan ba kuma aita dibi-dibi nasan Mansoor da ƙosawa akan abu, sam baya son jira. Acan ƙasan zuciyata kam ina jin babu daɗi saboda rashin ganin duk jama’ar gidan a cikin sha’anin bikin nawa. Dan yaran duka babu wanda na gani har Auta da su Yaya Abbas da Nabel da shi banama zaton yazo gidan yana makaranta. Gara ma ita Mum ɗin bayan ɗaura aure sanda Yaya Musaddiq yazo ya fita dani ɗin nan zuwa falon baƙi na ganta ita da wasu ƙawayenta a tsaye sunata faman dariya da alama akwai abinda suke tattaunawa a tsakaninsu.
★★Bayan nayi sallar magrib kamar yanda Gwaggo ta faɗa aka haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito da taimakon Gwaggo na kimtsa jikina. Ta kuma tsareni sai da naci abinci da wani nama na musamman mai romo a cikin kula. Naman yayi daɗi dan haka na saki jiki naci sosai, koda tace sai na cinyesa ma ban musaba na dage na cinye nasha romon. Hakan yasa cin abincin bai armashi ba garan sosai. Tun ina kallon agogo harna daina. Sai dai a raina inata mamaki, dan tara dai-dai ya kamata ace muna a wajen dinner. Amma gashi anan har taran yama wuce ba’a kaini gidan su Mansoor ba balle ai batun zuwa dinner. Bily kar kiga kamar na cika zumuɗi ne fa. Kawai dai bana son naga an saɓama Mansoor alƙawari ne, to amma yaya zanyi, sai sanda aka kaini. Matsalata kawai da babu waya a hannuna.
Muna nan zaune Gwaggo na ƙaramin nasiha kusan goma saura akace su Yaya Musaddiq sun dawo sai a fito da amarya ga motoci sun zo. Sai a lokacin kuma naji duk na rikice. Nanfa na saki musu kuka. Duk yanda akaso na miƙe naƙi nai hakan har sai da Kawu Musa da kansa ya shigo yana faɗa sannan. Kuka nake sosai har numfashina na shiɗewa. Amma babu wanda ya saurareni, sai ma gaban Mum da aka kaini na roƙi yafiyarta. Cikin taɓe baki tana wani fisge-fisge ta ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya sai aje aita haƙuri, dama ita rayuwa ai haka take babu tabbas…” ganin tana neman sakin layi Gwaggo ta kamani muka fito. Abba ma an sake kaini na masa sallama. Yaya Musaddiq kam ya rufe kansa a ɗaki yaƙi yarda. Nasan kuka yake, dan haka nima na ƙara ƙarfin nawa kukan ina tutturjewa, amma babu wanda ya saurareni sai dai wasu nata bani haƙuri wasu na tayani matsalar ƙwallar aka fita dani. A rikicen da nake yasa bamma san kala ko adadin motocin da suka zo ɗaukata ba. Ni dai kawai an sakani a motar da ƙamshin da take yaso sakamin razani a zuciya, sai dai kuma rashin ƙarfinsa sosai da ruɗanin da nake a ciki na rabuwa da ƴan uwana ya hanani bama abin muhimmanci. Gwaggo Gudidi da Inna Magajiya ne tare da ni, sai gaba Ruƙayya ce ta office ɗin mu data zame min kamar babbar ƙawa ita da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya……..✍️
🤭Uhummm inji mai ciwon haƙori.
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚
…….Har muka iso kuka nake sosai, haka dai aka fita dani kaina a lulluɓe. Ina jin mutane nata yaba gidan. Hakan baisa naji wani abu daban ba saboda nasan gidan Mansoor kam tabbas yayi ƙyau da tsari. Sannan babu laifi babbane. Da addu’a na shiga kamar yadda Gwaggo ta bani umarni. Dan motar da aka ɗakkoni ce kawai dama ta shigo har cikin gidan. Sauran duk a waje suka tsaya. A falo aka ajiyeni kamar yanda Inna Magajiya tace. Mutane suka ɗan shishshiga kitchen da inda ba’a rasa ba. Bedrooms dai a rufe suke duka biyu dake a gidan kamar yanda naji suna faɗa. A karan farko na ɗan ji mamaki, dan nasan bedrooms huɗu ne a gidan Mansoor. Amma dai banda tacewa, bayan mutane sun gama zazzagawa suka fita dan dare ya farayi za’a maidasu gida. Sai da kowa ya fita sannan Gwaggo ta kama hannuna ta kaini bedroom da naji tana faɗa bayan ta buɗe da makulli, anan ne na gane ashe keys ɗin na hannunta sune dai suka hana mutane shiga wai dan kar a ɓata tunda dare yayi babu damar zama a gyara min. A bakin gado ta zaunar dani, tana sake jaddada min kalmar haƙuri, haƙuri dai da duk abinda zan gani, dan shi aure ibada ne bawai wasan yara ko nanaye kamar yanda mu yaran yanzu muke tunani ba. Ni dai kuka kawai nake zabga mata. Tadai samu ta zame jikinta ta gudu ta barni. Kuka na sake fashewa da shi irin mai cin rai da zuciya ɗin nan, harna zame na kwanta a gadon batare dana sani ba na cigaba da kukana.
Tun ina darzar kuka da tunanin Mansoor zai iya shigowa har al’amarin ya fara bani tsoro. Dan gari yay wani irin shiru sai kukan karnuna amma babu Mansoor babu labarinsa. Kai komai ya fara canja min daga yanda nake tunani da hasashensa. Dan daga jiya zuwa yau komai da nake gani ba irin tsare-tsaren Mansoor ɗina bane. Komai yana zuwa min a banbancin abinda muka tsara. Mi hakan ke nufi, Mansoor ne ya canja komai a yanda na sanshi ko yaya al’amarin yake ne?. Banda mai bani amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyi na. Dan haka na cigaba da kwanciya a wajen ga ciwon kai mai tsanani na ratsani, kafin ma wani dogon lokaci na fara rawar sanyi. Ina jin yanda wata iskar hadari ke tasowa da ƙarfin tsiya amma na kasa ko motsi. Haka na cigaba da kasancewa a wajen na tsawon lokacin da ban san adadi ba har barci yay awon gaba dani batare dana farga ba….
Hasken rana irin mai kashe idon nan ne ya addabi fuskata. Dole na buɗe idanuna da sukai min wani masifar nauyi saboda kukan da nasha. Ganin a inda nake nada banbanci da inda na saba ya tuna min da mike faruwa. Zumbur na miƙe zaune ƙirjina na luguden daka. Ɗakin na shiga bi da kallo, madaidaici ne ba wani ƙato ba can. Sai dai kayan sun masa ƙyau cas. Abu na farko dana fara lura da shi sam ba irin fentin gidan Mansoor bane ba, kuma bedroom da Mansoor ya nunan a matsayin nawa randa mukazo ƙatone sosai. Ƙirjina yay wata irin girgiza. Sai dai tunawa da banyi sallar asuba ba yasa na tattare komai zuwa gefe na miƙe. Ƙofar da na gani da nakema zaton bayi ne na nufa. Nan ma dai ba irin toilet ɗin gidan Mansoor bane. Kai ƙwalwar kaina fa na neman juyewa. Amma dai na sake ƙoƙarin dakewa nayi alwala na fito. Akwatin dana gani saman bed side drawer na buɗe, na samu hijjab kamar yanda nai fata, dan haka na nutsu domin gabatar da salla..
Ina idar da sallar na miƙe kamar zararriya, dan kaina gaba ɗaya a juye yake da komai. Fitowa nai gaba ɗaya daga bedroom ɗin. Ganin wani dake a kusa da shi yasa na buɗe na shiga nan. Gabana ya faɗi. Dan babu komai a ciki sai ƙatuwar katifa irin wadda ba’a sanyawa a gadon nan. Sai wani ɗan ƙaramin akwati mai shegen ƙyau. sai takalma haif cover suma dai masu ƙyau sosai, a saman katifar da agogo da waya kusa da shi, sai can gefe kaya ne da aka cire shadda honey color data ciza sosai. Ga wani ƙamshi na musamman dake tashi har ina jin kamar nasan ƙamshin, amma dai na hana zuciyata hasasowa. Fitowa nai ƙwaƙwalwata na sake birkicewa. Falo ne dake tsaka tsaki, shima dai yayi ƙyau da kayan da aka jera masa, saukar idanuna akan wanda ke zaune daga can cikin ɗaya a kujerun dining ya saka zuciyata wata irin girgizar da ya rage kaɗan ta biyo ta bakina ta fito. Karkarwa jikina ya shiga yi, irin wadda bamma san na cigaba da tafiya ba cikin matuƙar sassarfa. Har na iso gaban dining ɗin bai ɗago ba. Yanata danne-dannesa a laptop hankali kwance. Ga mug dake ta turiri alamar shayi ko coffee a ciki.
“Wanene kai? Miya kawoka nan? Ina ka kaimin mijina?”.
Tambayoyi uku a jere suka fito a bakina dake rawa. Kamar baima jini ba, ko nace bai san da zuwana wajen ba. Dan ko motsi baiyi ba balle ya ɗago ya kallan, aikinsa kawai yake hankali kwance cike da ƙwarewa.
A matuƙar harzuƙe hawaye masu zafi na rige-rigen sakko mini cikin daka tsawa na ce, “Da kai nake magana malam!!”.
Cak ya tsaya daga danna keyboard ɗin laptop ɗin da yake yi. Nasan kuma yanda nai tsawar ne da matuƙar ƙarfi ga jikina na girgizar tashin hankali da ɓacin rai. Na sake zabura zan masa wata tsawar ganin nan ma bai amsa min ba yay wata irin juyowar da ta saka ni yin tsalle a lokaci guda da zuciyata saboda tsabar kiɗima. Sai gani rijif a ƙasa wanwar.
“Ba’a min tsawa”.
Ya faɗa a dakensa cikin silent voice ɗin nan nasa na gadara babu alamar damuwa da halin da yaga na shiga kuma. Sai ma ɗauke kansa da yay ya sake maidawa ga screen ɗin laptop ɗin. Yaraf kake jina na ƙarasa zubewa ƙasa gaba ɗaya. A hankali sai kaina ya fara juyawa, yayinda lips ɗina ke wata masifaffen rawa ina nunasa da yatsana da shima ke rawar. Tun ma ina banbance tsakanin haske da duhu har hakan ya fara neman gagarata. Tuni na tafi luuu ƙasa gaba ɗaya alamar ina neman suma. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba sai farkawa nai na sake gani na a inda na faɗin yashe. Da ƙyar na iya miƙewa hannuna dafe da kaina dake faman juya min. Kai tsaye inda nasan yana zaune na kai idona. Wayam babu kowa daga shi har laptop ɗin nasa. Sai mug ɗin nan na shayi kawai ajiye. Falon na juya ina sake ƙarema kallo. Yanzu kam ni kaɗaice a cikinsa da alama, sai zuciyata ke ayyana min kodai mafarki ma nake yi ne? A gaskiya sai dai mafarkin kuwa, dan wanda idona ya ganarmin a gidan nan nafi fatan ya kasance a mafarkin ne. Kasa daurewa nai, cikin layin juyewar kai tamkar wata ƴar maye na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton hanyar fita ce. Da ƙyar na iya lalubar handle ɗinta na buɗe, cikin yanayin dishi-dishi na dinga bin harabar gidan da kallo, ba wata babba bace dan bata wuce ɗaukar motoci uku ba suma a ɗan takure. Motar da nake ƙyautata zaton an ɗakkoni a ciki jiya kawai ce a ajiye. Saukar idanuna akan buzun dake zaune a gate yana fifita wuta alamar shayi yake dafawa yasa ni jin ƙarin gwiwar nufar can. Sai dai ina kai rabin harabar wani mahaukacin farin kare mai kama da tumakin turawa a gashi ko nace zaki a ƙarfi da girma ya wani irin zaburowa kaina daga inda yake kwance a saman motar yana haushi na hauka ga harshensa waje. Daburcewa nai na rikice dan na tsani kare. Balle irin wannan mara ƙyan gani da suffa, sauƙinsa ɗaya daya kasance fari. Ganin yana gab da iskoni na ƙwalla ƙara ina durƙushewa a wajen na ƙanƙame jikina dake rawar mazari.
“Laalah!”.
Aka faɗa a ɗan tsawace, sai dai hakan bai hana fitar muryar tasa acan ƙasan maƙoshi ba. Sannan karen ya tsaya cak bai ƙaraso inda nake ba. Sai kallonsa da yay yayi haushi sau biyu yana kallona kamar mai son masa ishara dani. Da alama ya fahimci mi karen ke nufi, dan a daƙile ya sake faɗi, “leave here”.
Abin mamaki tinƙas-tinƙas karen nan yabar inda nake ya koma saman motar daya taso yay kwanciyarsa kamar bashi ba. Sai lokacin na samu damar sake fashewa da kuma. Ganin ya juya abinsa zai koma inda ya fito na miƙe a zabure nima. Kusan atare muka shigo falon. Batare dama nasan mi nakeyi ba a tsawace na furta, “Ina ka kaimin mijina? Mi kayima Mansoor ɗina? Miya kawoka gidan aurena? Yanzun ma kidnapping ɗina kayi?”.
Bai ko kallan ba ya cigaba da tafiyarsa zuwa bedroom ɗin nan mai katifa. Ai bamma san lokacin dana daka wani uban tsalle ba nabi bayansa nima. Dan amsoshin tambayoyina kawai nake buƙata. Dole kuma ya bani, inba haka ba kuwa zaiga tsagwaron tashin hankali, kuma a wannan karon saina tabbatar masa da kaidin mace, dan ko dare bazan sake kaiwa a gidan nan ba. Ina isa ƙofar ɗakin yana rufota bamm, handle ɗin na kama da rawar jiki na fara murɗawa da jijjiga ƙofar amma ko motsi batai ba alamar ya kulle ta ciki. Wani irin kuka mai tsuma zuciya na sake fashewa da shi ina cigaba da jijjiga ƙofar da bugata a haukace amma mutumin nan ko tari baiyi ba. Galabaita ta sakani silalewa jikin ƙofar zuwa ƙasa wasu zafafan hawaye na rige-rigen sakkomin da masifar gudu. Cikin jin karaya da sarewa na shiga furta, “Awwab why? Why Maash? Why zakamun haka a ranar da tafi kowacce rana muhimmanci a garemu. Mike shirin faruwa? Ina mijina Mansoor?!! Miyyasa ka sake satoni zuwa nan a ranar auren…” kuka ya sarƙeni na kasa cigaba da maganar✍️
🤔🤔🤔😞
Alhamdullah 🙏. Anan zamu dakata a book one na wannan littafi mai suna TSUTSAR NAMA. sai kuma ALLAH yasa muna da rabon kaiwa bayan salla.
★Tofa masu karatu yaya take ne?.
★Mike shirin faruwa?.
★Ina Mansoor ango?.
★Miya kawo Maash a madadinsa?
★Kidnapping Sam-G ya sake yi kamar yanda take tunani itama kokuwa yaya al’amarin yake?
★Waye yay kidnapping Sam-G a farko tunda Maash ya tabbatar mana bashi bane?.
★Waye Maash ya kashe ma wai?
★Wake amfani da sunan Samraah wajen amsar kuɗi maƙudai haka a wajen Maash? Tunda tace ba ita bace.
★Maash zai samu nasarar amsar videon a wajen Sam-G kuwa?
★Magana fa ake ta an kawo amarya gidan mijinta amma ango ya rikiɗa zuwa wani daban.
★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa. Hhhhumm ba’a magana, dan bama mu fara komai ba sai a book 2 da zai zo bayan salla, kuma komai da kuke buƙata yana a cikinsa ne.
★Dan shi kansa Maash fa akwai wani ƙunsashen al’amari a tashi duniyar dako fara taɓota bamuyi ba.
★Kai kar dai na cikaku da surutu, ku shirya kawai tsaff zuwa bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya domin samun duka wannan amsoshin a TSUTSAR NAMA BOOK 2 har ma da wanda baku sani ba.
★Ya rabbi ka karɓi ibadunmu, ka gafarta mana ka yafe mana kurakuran mu. Ƴar uwa! Ɗan uwa! Duk wanda naima ba dai-daiba ya gafarceni. Nima na yafema kowa. Kada ka bari ko ki bari ku zama cikin jerin mutanen da zan iya kaima UBANGIJINA kuka a kansu a acikin wannan watan mai tunkaromu. Wannan shawara ce. Dan nima bazanyi fatan nazama cikin wanda kuma zaku kai ƙarata wajen UBANGIJINA ba. Fatana kumin addu’ar fatan alkairi nima na muku tare da iyayenmu baki ɗaya.
Taku har kullum👎
BILKISU IBRAHIM MUSA
(Bilyn Abdull 💞)
(C)2024.
Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.
karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!
MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
Aslm alaikum Dan uwa Dan Allah ataimaka afada Mana wane ranaku ne da kuma time din da ake yin post awannan wuri mai albarka? Allah ya qara lpy mun gode
muna yin post duk sati sau 5 banda asabar da lahadi
Please idan mutum yanason yasamu complete book3 nawa zaibiya
muna da subscription na 500 kawai duk wata idan kika biya farkon wata bazaki kara biya ba sai karshen wata
Inso inbiya yazanyi
Allah yakara basira
Slm Dan Allah inaso asani a group Na what’s app
to bani number ka
ko ka danna wannan link din
https://chat.whatsapp.com/Gbut9ibvwWM8JPk0qoMEiZ
Tsutsar nama thirty eight
kullum munayi insha allah
Aslm brk dawarhaks
Alhamdulillah
Masha allah Allah Kara basira
I like this novel
https://chat.whatsapp.com/Gbut9ibvwWM8JPk0qoMEiZ
whatsapp group
O⁹
Dan Allah ya za ayi in samu book 3
Document din kike so
Nima inason docoment
ai bata gama book 3 ba sai dai book 2 shima yana nan akan wannan website din
Okay
ya zaayi inkanason book3
downlaod zaki yi ki dannan wannan link din https://novels.ng/tsutsar-nama-by-bilyn-abdul-book-3/ sai ki dauko
I want the complete book 3 of tsusar nama
bata gama ba amma munayin update akai akai
dan allah book 3 page 1