Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    154 Results with the "paid" tag


    • KANWAR MATATA Thumbnail

      *🦜 _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_     _K’anwar Matata ba kirkirarren labari bane! Sai da na samu yarda da aminta sannan na soma rubuta shi. Dan haka idan yayi shige da naki irin labarin, arashi aka samu. Sannan ina gargad’i da babbar murya, ban yarda a juya min labari ta ko wani siga ba, ba tare da izini na ba ko kuma a d’aura min…

    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — A ƙaramar akwati na zuba mana duk abun da na san zamu buƙata a yinin, Baba Jummai ta goya Al'amin tana tsaye tana jiran na yafa gyale na da na ajiye a gefe. Zama na yi a gefen gado ina rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya, ta kalle ni ta ce "Ya kuma kika zauna? Tun da dai an kaiwa maƙwaftan nan abinci se ki tashi mu tafi kuma su ce zasu shigo yinin suna". "Baba ban gayawa Bilal ba" na faɗa ba tare da na kalle ta ba, "Naga abinda ya ishe ni ni Hasana, yanzu gidan ku ɗin da zaki tafi shine kike…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twelve Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — "Idan har izini na kike nema ban yarda ba, ko da yake ai kin saba yin gaban kanki. Kiyi duk yanda kika so Halima lokacin ki ne dama kika samu". Abinda Bilal ya gaya mun kenan bayan dana same shi akan maganar posting ɗina zuwa garin Bauchi. Duk yanda kuma naso da ya zauna muyi magana ta fahimta yaƙi, ƙarshe ma barin mun part ɗin yayi gaba ɗaya ya tafi can part ɗin sa da falon kaɗai muke amfani dashi ina jin sa a daren ya gyara ɗakin tun da dama da hado da komai a ciki ya dawo ya ɗauki bedsheets da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Eleven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Daƙyar na koma cikin falo na zauna ina jin kaina yana saramun. Me yasa Bilal yake haka? Kullum ace abinci ne ze ringa haɗa mu rigima? Ina nan zaune ya fito daga ɗaki yanayin shigar sa na gane nisa ze yi. Ko kallo na be yi ba ya fice sabbin hawaye suka ɓalle mu. Zuciya ta tana raya mun na barshi naga iya gudun ruwan sa amma gangar jiki na taƙi bani haɗin kai, bazan ce ga sanda na miƙe na bi bayan sa ina kiran sunan sa ba amma ko a jikin sa ya yi ficewar sa daga gidan ya bar ni a tsaye ina hawaye. Se…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa "Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga…
    • Kura a Rumbu – Chapter Nineteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Ba zan iya cewa ga ta yanda muka fita daga gidan ba ni dai kawai na san munje gidan mu; muna sauka daga Adaidaita sahu Amirah ta sake ni na dafe gini saboda jirin dake kokawar kayar dani ita kuma ta tura ƙofar get ta shiga tana rushewa da kuka tamkar wadda tazo isar da saƙon mutuwa. Daƙyar na cira ƙafata na rufa mata baya ina yi ina dakatawa saboda ciwon marar dake taso mun, na dafe ƙofar shiga falon na tsaya ina kallon mazauna ciki da suka rufu kan Amiran cikin tashin hankali suna tambayar ta ba'asin…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — *Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri* Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu…
    • Kura a Rumbu – Chapter Eighteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka shafe tsayin…
    • Kura a Rumbu – Chapter Seventeen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fourteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Afuwan kun jini shiru. Wadanda suke cikin comment section group na bayar da uzuri. A ɗarare na ƙarasa yinin cike da taraddadin yanda zamu kwashe da Bilal idan mun koma gida. Se da akayi magriba ya turo mun text a waya in fito mu tafi. Jikina ya sake yin sanyi, haka nayi sallama da Hajja da sauran yan gidan su tana ta mun godiyar abin arziƙi da tace an kawo musu daga gidan mu cikin azumi ga kuma turmin atamfa dana kai mata dama yanzu kuma na kaiwa mejegon itama Atamfa da wani lace cikin ɗinkunan biki da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Ƙaddara da kwaɗayi haɗi da son zuciya irin nasa ya janyo masa faɗawa tarkon nadama. Dukda dai tsohon halin sa ne, a baya lokacin samartaka ya kan kwatanta domin rage zafi kamar yanda hakan yake ɗabi'ar dayawan Samari a wannan zamanin. Sun ɗauki hakan a matsayin wayo ko dabara a ganin su ai basu aikata Zina a zahiri ba sai dai suna mantawa da hanin ubangiji da yace kada a kusanci Zina ba wai kada a aikatata ba Aa kwata kwata kada a kusanci duk wani abu da yake da jiɓi da ita. Da yawan su sun ɗauki…
    Note
    error: Content is protected !!