Search
You have no alerts.

    154 Results with the "paid" tag


    • KANWAR MATATA Thumbnail

      *🦜 _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_     _K’anwar Matata ba kirkirarren labari bane! Sai da na samu yarda da aminta sannan na soma rubuta shi. Dan haka idan yayi shige da naki irin labarin, arashi aka samu. Sannan ina gargad’i da babbar murya, ban yarda a juya min labari ta ko wani siga ba, ba tare da izini na ba ko kuma a d’aura min…

    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Jinyar stitches ɗin Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi yakeyi, sannan ya kula da ita a ɗan taƙin lokacin kuma ya ɗan fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka ɗaura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare, maganin na…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga gare shi ko me? "Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce "Ka sameni a gidan Anty Labiba bayan Magriba" "Gidan Anty Labiba kuma?" Ya faɗa kamar a ɗan…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke mu'amala da su balle makaranta. Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Kafin mu gana gane me ya faru Mu'azzam ya shigo ɗakin babu kuma ɓata lokaci ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukan Bilal yanda ka san Allah ya aiko shi. Gefe na ja da sauri cikin tashin hankali na ɗora hannu biyu a ka na fasa ihu ina kiran sunan Mu'azzam ɗin, abin takaici Nasir da yake namiji daya kamata ko murɗe Mu'azzam ɗin yayi ya ƙwace bulalar idan ma yana tsoron kaiwa Bilal ɗin agaji ya haɗa da shi wai sai ya tsaya daga gefe yana ce masa ya bari. Bilal kuwa kamar mace haka ya shiga birgima…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Madallah da mutane masu karamci. Nagode ƙwarai dagaske, ina lafiya wani aiki ne ya ɗauke ni tsayin kwanaki amma Alhamdulillah mun kammala na kuma gode ƙwarai da haƙurinku ina fatan har mu kammala babu wani uzuri da zai sake gifta mana 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 *KURA A RUMBU littafin kuɗi ne 800, yake mai jira nayi posting ki fitar kiji tsoron Allah dakw da wacce take jira ki turo ta karanta a bati ku guji haƙƙin komai ƙanƙantarsa. Duk wacce ta shirya sauke nauyi ta tura mun kuɗi na a asususun…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Ashe baka da mutunchi kai mutumin banza ne ban sani ba? Ban taɓa zaton haka kake ba, ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan idon mu kana can kana zubar mana da mutunchi kana tozarta kanka; matan banza kake bi Bilal?" Ya dafe in da ta mare shi ba tareda ya bari sun haɗa ido ba ya ce "Ni wlh ba wasu mata da nake bi Hajja sharri kawai suka mun". Wani marin ta sake kai masa ya goce ta ce "Yanzu kake da bakin kare kanka kenan? Ni zaka kalla ka ce sharri ake maka saboda ka raina ni mai ya sa a gabansa baka…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) BILAL Yana kwance a gida Hajja ta kirashi wai ya kawo musu kayan miyan da za'ayi tuwon ɗaurin auren Fadila da za'a ɗaura a gobe Juma'a. Da yake a tsini suke yayi mata laifi shiyasa bai musa ba ya tashi ya tafi kasuwar Yankaba ya yiwo musu cefanen ya tafi ya kai. Zagayewa yayi yaje ya samu Kawu Ɗayyabu, Yayan Hajja ne da suke uba ɗaya da yake mutum ne mara ɗaukar raini shiyasa duk rashin mutunchin Hajjan take shakkarsa ko da wasa kuma bata bari wani abu ya gilma a tsakaninsu shi Bilal ɗin yaje ya samu…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Lallai su Bilal anyi Amarya, toh Allah ya zaunar lafiya" amsar da Hansa'u ta bani kenan duk kuma yanda na so da naji ƙarin bayani bata sake cewa komai ba, Da na isheta da tambaya ma balbaleni tayi da faɗa tana cewa "Wai menene haɗin ki da matarsa ne Halima? Mutum ya rabu dake tuni ma shi ya manta ya taɓa rayuwa da wata Halima har yana shirin fara rayuwa da wata amma ke ashe kina nan kina dakon wahala sai anyi magana ki fara rantsuwar kin cireshi a ranki gashi kina bibiyarsa". Tilas na bar maganar…
    Note
    error: Content is protected !!