Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    154 Results with the "paid" tag


    • Turken Gida – Chapter Twenty-seven Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Maman Farko ce kawai ta sakar min fuska to sai Yallaɓan amma Anty Bahijja ina gaishe ta ma kamar ina faɗa mata cuta a daƙune ta amsa ni. Na zo na iske an kai Gimbiya ɗakin hutu an yi mata kuma alluran barci amma ba su fara ba da izinin a shiga a ganta ba. Muna asibitin Anty Bahijja ta kira mutane ba adadi ta na faɗa musu Gimbiya na asibiti ina ga ko suna tambayan ta cikin ne? Sai ta ɗaga murya ta na…
    • Turken Gida – Chapter Twenty-eight Cover
      by Janafty Tun dawowar Gimbiya gidana na ke ta ganin ikon Allah a wajen Yallaɓai da dangin shi, su rawan ƙafa shima rawan ƙafa, ni dai ina gefe ina ganin komai kamar al'amara kamar mafarki. A ce yau wai a gaban idanuwana Yallaɓai ke ririta wata macen ba ni ba, kuma a cikin gidana ƴan'uwansa ke zarya saboda wata ba ni ba. Rayuwa kenan abin da ya baka dariya wata rana shi zai koma ya na ba ka tsoro. Anty Bahijja ku san kullum sai ta zo gidan nan sai ka ce ni ɗin zan cutar da Gimbiyar ne. Kuma in ta zo ta riƙa…
    • Turken Gida – Chapter Twenty-nine Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* "Bahijja kina mata wani sanyi sanyi ke Sadiya har mganin asirin suke kawo miki har gida. Gimbiya ta gan ki lokacin da ƙanwar mamanki ta kawo miki su har gida ko shima za ki ƙarya ta ne? Kalaman Anty Maimuna suka buga min kai kamar an dake ni da ƙarfe sai da na ji kaina ya yi dum na ɗago ina kallonta ba bakina ba har idanuwana suna rawa ne a lokacin. "Haba Anty Maimuna me ya sa haka? Hauwa ta faɗa kamar ta…
    • Turken Gida – Chapter Twenty-three Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Yanzu Gimbiya tana cikin wata biyu ne da tarewa. Zaman su ya fara miƙawa tun ina ganin lamarin kamar wasa har dai daga karshe na saka a raina gaskiya ne sannan zan saba ɗabi'ar haka ta zame min jiki ko domin samun zaman lafiya ta. In na buɗe wardrope ɗina na ga cikin kayan Yallaɓai kashi uku babu kashi ɗaya a hankali a hankali ya na ta rage su, suna can gidan Gimbiya, bayan kaya ma hatta ma'ajiyar takalman…
    • Turken Gida – Chapter Twenty-five Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Kaina na mayar ƙasa ina wasa da gefen hijabina. Sai na sake ɗagowa ina kallon shi jin ya yi shuru sai muka haɗa ido dashi da sauri na ƙara sadda kaina ƙasa domin har ƙwalla sun cika min ƙwarmin idanuwana tuna irin cin mutumcin da Yallaɓai ya yi min. "Me ya faru? Ya sake tambayata sai na yi saurin shanye kukan da ke taso min har ina yin mirmishi wanda na aro shi na yafa a saman fuskata duk domin na kauda…
    • Turken Gida – Chapter Twenty-six Cover
      by Janafty Tun a daran alhamis Yallaɓai ya kirani a waya saboda ranar ba a gidana ya ke ba. Ce min ya yi mu shirya ni da yara za su zo shi da Gimbiya su ɗauke mu domin zuwa sallar idi na ce masa to, domin ni yanzu tsakanina da Yallaɓai to ne domin na yi ma kaina alƙwarin kome zai yi ko ya ce ba zan ƙara yi masa mgana ba, ma'ana sai dai na gani na yi kamar ban gani ba na kuma ji na yi kamar ban ji ba domin a zauna lafiya. Lokaci bayan lokaci ina tuna kalaman da ya jefe ni da su na cewa ba ni da alheri sannan…
    • Turken Gida – Chapter Thirty Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Na shiga gidan Ya Aina ko gani ba na yi saboda tashin hankali da damuwa. Tafe na ke ina jefa ƙafuwana ba tare da na san in da za su faɗa ba. Ya Aina na hanga a ɗan karamin madafinta dake tsakar gida sai ƙannen Marwa na gefen ɗakinta a kan tarbarma suna cin abinci. Ko sallama ma ban yi ba ni dai kawai na shigo kuma na dumfari ɗakin Ya Aina so na ke yi na samu waje ni kaɗai na fashe da kuka na yi kuka mai…
    • Turken Gida – Chapter Twenty-four Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Gidana duk ya yi ƙura to ba na samun zama. Shi ya sa da aka sallami Nene sai na ɗan ɗaga kafa da zuwa Gwammaja in yau na je gobe ba zan je ba. Yallaɓai shima ya samu natsuwa tun da har Kaduna ya shiga ya kwana biyu. A ranar da zai dawo daga kadunan na je can Gwammaja da ya ke Jumma'a ne tare da su Jidda na ne tunda sai da na jira suka dawo muka taho tare. Na yo ma Nene ferfesun kayan ciki saboda na son ta na…
    • Turken Gida – Chapter Thirty-two Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* *BAYAN WATANNI UKU* Watanni uku sun zo sun shuɗe kamar ƙiftawan ido. A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah da haka muke ta cinye kwanakin mu ba tare da mun farga ba. A cikin watanni ukun da suka gabata, ba ƙoƙarin da ban yi domin na manta da abin da ya faru tsakanina da Gimbiya da su Anty Bahijja ba amma na kasa. Duk lokacin da na tuna sai na ji gabaɗaya rayuwata ta yi ƙunci. Sai na ji zuciyata ta…
    • Turken Gida – Chapter Thirty-one Cover
      by Janafty *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Da yake na san Yallaɓai ba ya son cin taliya a cewarsa wai ba ta ƙosar dashi. Shi ya sa sai na dafa masa shinkafa mai karas da kabeji. Mu kuma sai muka ci sauran taliyan da ta rage ni da yara. Kayan marmarin da ya kawo rabi na ɗibar mana na wanke muka ci, rabi kuma na saka a cikin frizer. Sai da Yallaɓai ya yi wanka ya sauya kaya zuwa wasu sauƙaƙku na zaman gida sannan ya ci abinci ya na cin abincin ina…
    Note
    error: Content is protected !!