Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    154 Results with the "paid" tag


    • KANWAR MATATA Thumbnail

      *🦜 _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_     _K’anwar Matata ba kirkirarren labari bane! Sai da na samu yarda da aminta sannan na soma rubuta shi. Dan haka idan yayi shige da naki irin labarin, arashi aka samu. Sannan ina gargad’i da babbar murya, ban yarda a juya min labari ta ko wani siga ba, ba tare da izini na ba ko kuma a d’aura min…

    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-one Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama 🙏🏽🙏🏽 A hankali na buɗe ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na buɗe idon ya saka Mama janye hannunta, ganin da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce "Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazzaɓin ya sauka". Na yunƙura na zauna ina cije baki saboda kaina daya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — HALIMA Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce, "Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-one Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Ranar Alhamis suka je jere ko ya ce ganin gida tunda dai shi yayi jere, yan buhun hunan da suka je da abinda suka kira kayan kitchen tsabar takaici kallo ɗaya ya musu ko gaisuwa mai kyau basuyi ba ya fita ya barsu da yayyensa banda Anty Amina da sukaje tarar masu jere. Bai san munafukin daya gayawa Hajja shi ya siya mata kayan ɗaki ba ai kuwa ya sha tijara wannan kuma ya sake ruguza ɗan shirin da suka farayi ta kuma ja masa kunne akan ba fa zata saɓu ba, ita da wahalar haihuwa da raino can wasu a gefe…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — HALIMA Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin daɗi nayi yaune nake ganin asalin baƙin dare. Sai da aka idar da sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi. Na tashi zaune daƙyar ina matse ido haɗi da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai faɗo saboda ciwo. Mama na tsaye ta ce "Hala kin manta abinda Abbanku ya faɗa miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara". Gabana ya yanke ya faɗi,…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Jinyar stitches ɗin Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi yakeyi, sannan ya kula da ita a ɗan taƙin lokacin kuma ya ɗan fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka ɗaura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare, maganin na…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga gare shi ko me? "Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce "Ka sameni a gidan Anty Labiba bayan Magriba" "Gidan Anty Labiba kuma?" Ya faɗa kamar a ɗan…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) — Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke mu'amala da su balle makaranta. Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa…
    Note
    error: Content is protected !!