Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Ina zaune a wajen Rahila ta ƙara kirana sai na danna mata busy. Ina mai ƙara sakin tsaki ni kaɗai ƙara miƙe kafata na yi a saman kujera mai zaman mutum biyun da nake zaune akai ina mai ƙara jin wani takaicin na ƙara cika min zuciyata. Rahila ba ta haƙura ba sai da ta ƙara kirana har wajen sau uku ina kashewa sannan daga ƙarshe sai ta turamin saƙo.

    Na ba ma Hubby saƙon ki da zai fita, zai biya gidan Bulo ya ba ma Musabahu. Zai kawo miki ko kuma in ya haɗu da Yallaban na ƙi ya bashi ya kawo miki. Ki yi haƙuri.”

    Ba saƙon ne ya ba ni dariya ba sai Hubby da na ga Rahila ta rubuto mini shi ne ya sa ni tsintsirewa da wata dariya mai sauti wanda har sai da Saude da ke kichen ta leƙo tana faɗin”Lafiya Anty?
    Ina dariya na ɗaga mata hannu ina faɗin”Bakomai Saude. Ci gaba da aikin ki.”
    Sai ta amsa min da kai ta maida ƙofar kitchen ɗin ta rufe ta bar ni nan zaune ina ta faman dariya. Wai Yaya Muntarin ne Hubby kai in na tuna da sunan ma sai na ji wata ƙarin dariya ni dai ban taɓa katarin Rahila ta kira shi da wannan sunan ba. Baban Islam na san tana kiran shi dashi ko Yaya Muktar ɗin da ta lankayamai amman yau shi ne karon farko da na taɓa jin ta kira shi da sunan Hubby.

    Ina dariya ina tuna wani zamani a can baya ina jin na kasa riƙe dariyata. Har sake karanta saƙon na yi ina dariya a fili na furta” Tab! su Rahila masu Hubby manya.”
    Saƙon Rahila shi ya tafi da kaso mafi girman ɓacin rai na, har na ji zuciyata ta yi sanyi, ban jima a falon ba na miƙe dauke da wayata ta kitchen na bi saboda daga kichen ɗin akwai ƙofar da za ta sadani da ƙofar koridin Bedrooms ɗina.

    Saude na gani a rakuɓe kamar wata bakuwa tana cin doya, a tsugunne ba ta san ma na shigo ba a saman kanta ta ɗago kawai ta ganni harara na ɓalla mata kafin na ce” Wai ban hana ki wannan ɗabi’ar ba Saude? Nan gidan baƙon ki ne? Cin abinci a tsugunne kamar an hana ki zama a in da kika ga dama?

    Da sauri ta ɗago tana faɗin” Yi hakuri Anty, daman na ga ina sauri ne shi ya sa ban zauna ba.” Ƙaramin tsaki na ja kafin na wuce ina faɗin”Ke dai kika sani, ki kuma cire hijabin nan saura na fito na ga kina aiki dashi kamar wata yar gudun hijira ki ga yadda za mu kwashe da ke a cikin a gidan nan.”

    Dariya ta yi har ina jin sautin ta kafin ta ce” To Anty.”
    Ni kuma Bedroom ɗina na koma kan Dressing ɗin mirrow ɗin da ke ɗakin na ijiye wayata na koma na kwanta har da shigewa bargo. Har ga Allah na ji ana ta kiran wayata amman ban mai da hankalina ba, na ɗauka yan gidanmu ne kan maganar ƴar gwal Ma’u shi ya sa ban ko motsa daga cikin bargon da na ke kwance ba afili ma sai da na yi ƙwafa kafin na ce”Ku ci kan ku.” Na ƙara shigar da kaina cikin bargo ina ƙara gyara kwanciyata.

    Barci ya fara ɗauka ta domin har na fara wani mafarki mai ɗan karan daɗi, kamar daga sama na ji muryan Saude ta na kirana.
    “Anty. Anty..”

    A firgice na tashi saboda a saman kaina a can cikin barci na ji kiran sunan.

    Saude na gani a cikin Bedroom ɗina daga can baƙin kofa, tana ganin na tashi zaune da sauri ta ce”Anty kin yi baƙuwa.”
    Yamutsa fuska na yi kafin na maimaita kalmar” Baƙuwa? > Janaftybaby: Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce”E. ta ce na faɗa miki Bahijja ce.”
    Shuru na yi ina tunanin wace ce kuma Bahijja, ido na ɗan waro kafin na yi saurin yaye bargon jikina na sauko daga kan gadon lokaci ɗaya ina faɗin” Tana can falo ne?
    Saude ta gyaɗa kanta kafin Ta ce” E. tana can falon farko.”
    Kai na gyaɗa kafin na ce” Je ki ce mata gani nan zuwa Saude.” Ta amsa min cikin ladabi sannan ta buɗe kofa ta fita ta barni ina sauke numfashi.

    A gaban madubi na tsaya ina kallon fuskarta sai da na tabbatar da ba ni da wani abu da za ta kalla ta yi ƙorafi sannan na gayyato mirmishi da fara’a a saman fuskata sannan na zura takalmina mai taushi na zirga zirgan cikin gida, na zo zan gota ta jikin madubin sai da na ƙara tsayawa na kurama kaina ido ta cikin madubin ina jin gabbaina suna yin wani irin sanyi ƙalau, yanayin jikina na bi da kallo tabbas ina da son gayu da gyara ni macece da kana ganina kafin ma a faɗa maka wani abu akaina za ka sha shaida ina da son gyara, tun da ga kan gyaran fata na gashi da gyaran ƙasa na mace duka ba na wasa dasu bangaren gyaran fata kayan AISHA LAME +234 703 666 2633 na ke amfani da su, in kuma bangaren kayan ƙawa na gayu ne tun da ga kan atamfofi da abayoyi da takalma a wajen DIJA COLLECTION na kan yi siyayyata da ga ni har su Jidda shi ya sa kayana tare da na ƴaƴana muka fita dabam a cikin Dangi.

    Numfashi na ja sannan na ƙara fesarwa, wayata na ɗauka sannan na fice daga ɗakin ba ta kitchen na bi ba sai ta bi ta korido tunda falon farko zan je, ina tafe ne ina latsa wayata na ji na tsorata lokacin da na ga cikin waɗanda suka kirani har da Anty Bahijja, lalle yau Allah ne kaɗai ya isa ya cece ni daga ƙorafi da ƙananun mganganu sai wanda kunnena suka iya ji, ina tura ƙofar falon lokaci ɗaya tare da sallamata da kuma tahowa da fara’a a saman fuskata.
    +234 903 661 7473

    Ta na hakimce kan kujera mai zaman mutum ɗaya, sanye da dogon hijabi mai ruwan kuka har da liƙabinta, kenan daga makaranta take, ta biyo ta nan ina nufarta ina washe baki lokaci ɗaya ina faɗin”Maraba da Anty Bahijja.”
    Sai a lokacin ta ɗago kanta daga duba wayarta da take yi, sai da na kariso gabanta na zauna saman kujera mai zaman mutum ukun da take gefenta ina faɗin” Ina kwana Anty Bahijja.”
    Sai a lokacin ta iya ɗaga likaɓin ta sama fuskarta ta bayyana.
    Cikin yanayin maganarta ta kalleni daga sama har ƙasa ni kuma ina ta faman yi mata mirmishi.

    “Barka dai ta tashi gimbiya ko na ce Sadiya yar laushi ba”

    Wani abu mai ɗaci ya taho daga cikina ya tokare a saman ƙirjina. Shi ya sa har abada ba zan taɓa ƙaunar Ma’u ba, kuma ni da ita ba za mu taɓa zama a inuwa ɗaya ba. Amman ban nuna mata ba sai ma na ɓige da yin wani kayattacen mirmishi kafin na ce”Kai Anty Bahijja, ki yi haƙuri kin kirani ban ji ba. Na ɗan kwanta ne.”
    Baki ta taɓe kafin ta ce”Ai fa aikin kenan barci, kina ciki kin kwanta yar aiki na yi miki aikace aikace”
    Kai tsaye nima na ce” Saude ai tana zuwa tana taimaka mini ne, kinsan aikin gida da yawa Anty Bahijja.”

    “Ina wani yawa a aikin gidan nan Sadiya? Kawai daman kin saba da hutu shi ya sa kike kallon shi a matsayin aiki.”

    Ni ko sai na yi mata mirmishi duk da maganar ta na sukan zuciyata amman sai na ɓoye hakan a saman fuskata. Kai na kaɗa kafin na ce”Hutun ne ya zo Anty Bahijja amman karki manta a baya nima na yi aikin.”
    Ta san magana na gaya mata shi ya sa ta yi mini wani kallo, ban bari ta samu damar magana ba na cigaba da faɗin” Kuma Anty Bahijja laifi ne in mace ta samu hutu ta huta a gidan mijinta? Kema fa kina da yar aikin nan sannan ki na fatan nan gaba in su Sulaihat suka yi aure suma su samu gidan da za su huta ko ba haka ba ne? Ba fa wanda ba ya son jin daɗin nan fa.”

    Na faɗa ina kallonta saboda na ga kuma wata magana za ta ƙara faɗa mini, sai na ga ta juyar da kai ta na faɗin”Ba irin na ki ba Sadiya.”
    Ban yi magana na nima sai na kauda kaina ina ɗan mirmishi, na rasa wani hutu suke hangomin a cikin wannan gidan? Sun manta a baya komai na gidana da mijina da ƴaƴana ni nake yi ma kaina? Saude ba ta fara zuwa mini aiki ba sai bayan mun tare a wannan sabon gidan amman gabaɗaya ƴan’uwan Yusuf gani suke > Janaftybaby: yi da kuɗin ɗan’uwansu na ke walwali ina haskawa sannan na samu duniya ina ta jin daɗina.

    Ban ƙara ce mata ƙala ba, amman ita sai faman kalle kallen falon take yi tana wani taɓe baƙi, ba yarinya ba ce tunda Yayar Yallaɓai ce, daga ita sai shi tana da manyan ƴaƴa amman ba taba aurarwa ba suna karatu ne.
    Can ta ga ji da zaman mulkinta ta kalleni ta na faɗin” Su Jidda suna makaranta ko?
    Sai na gyaɗa mata kai, kafin na yi magana ta rigani da cewa” Kuma sai satin nan ba ki kai su gidan Yaya Maimuna ba? Me ya sa ?

    Daman na san rashin zuwan su gidan Anty Maimuna sai ya zame min abin magana, zama na gyara kafin na fara faɗin” Ba su samu zuwa ba. Amman weekend ɗin nan in sha Allahu za su je.”
    Anty Bahijja ta ƙara faɗin” Me ya sa na ke tambaya?
    Kai tsaye na ce”Gidanmu muka yini ranar asabar, lahadi kuma na ce su tsaya saboda shiryen shiryem makaranta, su goge uniform da homework lokaci ya ƙure shi ya sa sai na ce bari su bari wannan satin da sun dawo makaranta ranar jumma’a zan tsa yar mai mashin ɗin su, sai ya kai su in sha Allahu.”

    Miƙewa ta yi, lokaci ɗaya ta na rayata jakarta, kafin ta kalleni tana faɗin”Kina da ƙulafucin ƴa’ƴan Sadiya. To ki yi zuciya ki sake haihuwa mana. Amman ace kamar gidan Yusuf shi da ke son yara a ce ƴaƴa biyu kaɗai gare shi kamar ba shi da wani zaɓi, yanzu in muka ce ya ƙara aure sai ki ji haushin mu ko?
    Ƙuramin ido ta yi saboda tana so ta ga yadda zan yi, sai ni kuma na nuna mata har yanzu ba ta gama sanin wacece Sadiya ba.

    Dariya na saki har ta na fidda sauti kafin na ce” Jin haushi kuma Anty Bahijja? Ai aure umarnin Allah ne shi ya ba su damar ƙarawa, wallahi tallahi na sha faɗa ma Yallaɓai in zai ƙara aure ya ƙara domin ni ba ni da matsala da ƙarin auransa tun da ba akaina za ta zauna ba, kuma ko ta zo sai dai ta zo a ta biyu kin ga kenan ko ya ya dai na ke na amsa sunan Turken gida. Haihuwa kuma ta Allah ce, in ya tsara min ƴa’ya biyu zan haifa shike nan, kuma ni ba zan yi ma Yallaɓaina baƙin cikin ya ƙara aure ya sake haihuwa ba, duk wani abu da ya fito daga tsatson Yusuf abin so ne a wajena.”

    Kamar ba ta yarda da magana ta ba, domin sai ta ƙara kallona take yi, tana mirmishi, kallonta na yi domin har ta mirmishinta irin na Yallaɓaina ne. Ganin ta kama hanyar barin falon ya sa na miƙe na bi bayanta dai dai lokacin da na ji ta na faɗin”Ke fa kika tsaida haihuwan da kanki Sadiya kin ga ko, ko auran Yusuf ya ƙara bai yi miki rashin adalci ba.”
    Ina bin bayanta na yi mirmishi amman ban yi magana ba.

    Ni ce har haraban gida na rakata, ina ce mata”Ba ki zo da mota ba ne Anty Bahijja?
    Kai tsaye ta ce” Tana waje.”
    Sai na gyaɗa kaina fulawowin gidan ta bi da kallo kafin ta ce” Fulawowin nan sun ƙara ma gidan nan kyau fa.”
    Na biye mata ina cewa” Sosai ni ko ma da farko ban so Yallaɓai ya saka su ba sai bayan sun fara girma sai na ga sun yi ma wajen aiki.”

    Wani kallo ta yi min ta cikin likabinta da ta saki kafin ta ce”To gidan ki ne? Da sai kin zaɓi abin da zai saka ma gidan shi? Dariya na yi kafin na ce” Gidana ne mana Anty Bahijja, ko kwatance za a yi gidan Sadiya za a ce ko Maman su Jidda, kamar yadda kema a ke kwatancen gidan mijin ki da gidan Malama Bahijja.”
    Kallona ta yi ido cikin ido ni ko sai na waske ina dariya.

    Sai ta bige da yin mirmishi kafin ta ce”kin samu dai kan Yallaɓai ta bakin ki kina yadda kika ga dama, to tunda ya yi miki gida saura mota ko?
    Ina riƙe baki na ce”Ni Sadiya? Ai ko kuɗin ya samu kuka ji zai siya mino mota hana shi za ku yi Anty Bahijja”
    Kai tsaye Ta ce”Tabbas. Gwara ya yi aure shima ya tara zura’a kar ki manta a gidasu mata huɗu cif ne da kimanin ƴaƴa 21 ban da waɗanda suka rasu.”
    Ni ko da gayya na ce”Allah ya bashi kuɗin da zai wadatamu. Sannan sai ya yo auran miye a ciki?

    Anty Bahijja ta san halina ko Hajiya Maimuna ba na raga mawa, in suka faɗa min cuta zan faɗa musu mutuwa, duk da suna yayyen mijina, saboda suna da ƙananun maganganu sannan sun sakama rayuwata ido, a wasa ne za su yi ta faɗa minI magana > Janaftybaby: Nima ko a wasa na ke maida musu martani. Anty Zuwaira ce kaɗai ba haka a tsakanin mu saboda ita tana kama girmanta, da yake yar boko ce ga isa da gadara ba ta da ma lokacin tsayawa ƙananun maganganu. Har makaranta private nata na kanta gare ta, sannan ita ma ta kai matsayin Principal a wata makaranta ƴan mata ta cikin gari, sannan uwa uba mijinta a Mininsty of education reshen jihar kano ya ke aiki.

    Ban bar jikin get ba sai da Anty Bahijja ta shiga motar ta ta tafi, ina ɗaga mata hannu bayan na ce ta gaida su Suhailat, sannan na rufe get ɗin na koma cikin gida a falon da muka zauna na koma na sake zama.
    Duk a cikin maganganun Anty Bahijja magana ɗaya ta fi tsayamin a rai.
    Wai da ta ce ni na tsaida haihuwa da kaina, tuni na ji kaina ya fara sarawa abin nan mai ɗaci ya tokaremin a cikin kirjina ya kasa wucewa, wani tuƙiƙi kawai na ke ji kamar zan shiɗe.
    Har yau na kasa aminta da ba Yusuf ba ne ya je ya kwance min zani a kasuwa a gaban ƴan’uwan shi ba, tunda ya na da wani hali na faɗi ba a tambayeka ba, sai sai Ma’u ita ce abin zargina na biyu saboda tana auran yaron mai bi ma Mijin Anty Bahijja ma’ana suna aure a dangi ɗaya duk wasu maganganu da suke samu a kaina ta bakin Anty Bahijja ne, ko sunan Sadiya yar laushi da ke bakinta ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba daga baƙin Ma’u ne.

    Wannan yarinyar tun zuwanta gidanmu na san annoba ya zo cikin zuru’armu, idanuwan kowa ya rufe sun kasa gane tsabar makircin Ma’u da ta yi gadon shi wajen uwarta Baaba Asiya ta tsotsa a nono, ban san ina hawaye ba sai da na ji danshin saman kumatuna. Baƙin ciki ya cika min zuciya, me ya sa mutane suke kasa gane wani abu. Mace da Namiji waɗanda ke zaune ƙarkashin inuwa ɗaya ta ma’aurata tsakaninsu sai Allah, ba za ka ji bangare ɗaya ka yankema bangare ɗaya hukunci ba saboda Ubangiji ne kaɗai ya san mai ya ke faruwa tsakaninsu. Ƴan’uwan Yusuf suna ganin kamar komai na ke da shi sanadin ɗan’uwansu na samu Allah na tuba ba kyau tone tone in har da abin da nake dashi ya zauna a hannuna da yanzu na wuce matsayin da nake a yanzu, sun manta a yadda na auri ɗan’uwansu bashi da komai sai kwalin Degree da Masters sun manta gwagwarmayan da muka shafe shekaru sama da goma muna yi tare dashi rana tsaka saboda ya ɗan samu rufin asiri har ana tunanin ya ba ni duniya ina kwance a gida ina hutawa.

    Hawayena na share ina jan ƙaramin tsaki, ni ba domin Yallaɓai ya hana ni aiki ba da tuni ba su ganni ina zaman gidan ba, amman in har ya biyani kuɗina da nake bin shi ina nan da tunanin buɗe shagon Saloon kamar yadda na ke buri. Suna alfahari da wannan gidan su a tunanim kamar ya gama mini komai tunda ya gina min wannan gidan sun manta tsawon shekarun da na kwashe ina zaman haya. Maganar auran sa ba ta gaba na ta lafiyata na ke, na riga na shafa faɗama Yallaɓai cewa ba zan taɓa baƙin ciki domin zai ƙara aure ba amman ya sani kafin ya yi tunanin ƙara aure ya yi tunanin mu ya wadatamu da komai na rayuwa da ni da ƴaƴansa ba kuma mu ba mu wadatatu ba, ya je ya ɗauko mata ta zo ita a wahale mu a wahale.

    Jikina ya yi sanyin da na ƙasa tashi daga kan kujeran da nake zaune. Yallaɓai na kira domin na tuna masa maganar da muka yi na komawata ganin Gynea Asibitin ABU SHIKA.
    Ya sake kiran Uncle Abba mu ji yadda suka yi da wani abokin shi da ya ce zai kira a can Zaria zai taimaka mini.
    Amman ban same shi ba daman wani lokacin wajajen office ɗin sa ba Network a yi ta neman wayarsa ba a samu.
    A shekarun baya wani babban asibitin kuɗi ma’ana private Hospital na yi ta wahala da jelangen zuwa ba wani cigaba sai cin uban kuɗi sai aka bani shawara na koma babban asibiti ko Aminu kano ko ABU Shika da ke Zariya. Yallaɓai ya so na zaɓi Aminu kano, ban san me ya sa tunani na ya fi karkata da gwara na fara ganin likita a Asibitin Shika ba. Shi kuma daman Yallaɓai ya na girmama ra’ayina da buƙatuna shi ya sa bai hana ni ba. > Janaftybaby: Daga nan sai na sake buɗe data Group ɗin mu na BUK ya fara ɗaukan Hankalina saboda na ga ana ta massages da yawa kuma ni dai nasan tun da muka gama makaranta ba wani mgana ake yi sosai ba. In magana ta yi yawa to ɗayan biyu ne ko rasuwa ko an samu ƙaruwan aure ko na haihuwa.

    Ina shiga ko sai na ga Hauwa Jamilu ce ta haihu ƴ’a mace, ƙawarta Samira Aliyu ne ma ta tura hoton Baby da sanarwan haihuwan, na ƙurama hoton Baby ido mai kyau da ita. Ina son haihuwa ina son na ƙara haihuwa har a cikin raina, ko a ina naga an yi haihuwa sai na ji dama ni ce ko da ace daga shi in na yi ba zan ƙara haihuwan ba.

    Tagging na yi sai na yi mata barka a ƙasa kuma nace zan kira wayar ita Hauwan, duk da ban da wata ƙawa sanda muka yi BUK amman kuma ina gaisawa da mutane. Daga baya ma bayan mun gama makaranta na fi zumunci tun da in aka yi rashi ko ƙaruwa ko ban je na kan kira waya in kuma za a haɗa gudummuwa na kan tura nawa. Ina yin maganar Samira na Online ta yi min Reply.

    “Amin Amin. S Yashe ku kam dai kun gama ko?

    Sai na ba ta amsa da cewa” Mun gama me Samira Aliyu?
    “Haihuwan mana, kin daɗe fa ba ki ƙara haihuwa ba ina jin”
    Emojin mirmishi na tura mata ban yi magana ba. Ina gani Maijidda Bala, ta yi tagging ɗin maganar Samira da cewa” Ƴan boko ne matar Injiniya guda ko matar Yallaɓai zan ce?
    Sai da na yi dariyan Sarari saboda ko username ɗina Sadiyar Yallaɓai ce a rubuce.
    Kuma Maijidda Bala anguwanmu ɗaya, ta san gidanmu na san na su , duk halina na rashin son sakewa da mutane amman Maijidda na zuwa gidanmu saboda Rahila, to daman duk wanda ya zo gidanmu saboda Rahila ce ko Ma’u su ne masu jama’a. Ba zan taɓa mantawa da maganar Mama tun muna ƴan mata ta sha ce mini” Ke kam Sadiya da wuya ki ta shi aure ki ga jama’a. A yi mutum ba shi da son shiga jama’ a kwata kwata.”
    A lokacin dariya na kan yi kafin na ce”Shike nan sai ke da Gwaggo ku ci min ƙawayen amarya.”

    Allah Sarki Mama Allah ya sa kina aljannah. Ban biye ma mangaganunsu ba na sauka saboda kar na manta nan take na kira Hauwa na yi mata barka, har tana mini tsiyan ni na gama na ji daɗi na. Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba. Saboda ko me zan ce ba za ta gane ba sai da na ji tana faɗin”Nima daga wannan na faɗa ma Baban Afnan na gama wallahi. Allura zan je a yi min na shekara biyar.”
    Da sauri na ce”Kul ɗin ki Hauwa. Karki yi wannan gangancin, in kika tsaida haihuwa na shekara biyar to za ki yi ta nadama har na shekaru ashirin ba ki daina ba. Saboda lokacin da kike son ki ƙara haihuwan ba za ki samu wannan damar ba.”

    Na faɗa ina jin raɗadin abin a cikin raina Hauwa ko cewa ta yi” Ko Sadiya? Sai kawai na rausayar dakai kamar tana ganina kafin na ce” Ku yi na gargajiya ko na musulunci Hauwa. Saboda haka ina gargaɗin ki in ba so kike yi ki ƙare a zuwa gaban Gynea ba.”
    Hauwa na jin haka sai ta ce to shike nan za ta yi magana da Daddyn Afnan duk yadda ta so na yi mata wata mgana ban yi ba saboda ba close na ke da ita ba, rayuwa ai darasi ne amman da zan buɗe mata cikina sai ta ji tunanin da ke cikin ranta ya fita ba domin komai ba sai tsira daga faɗawa irin halin da ni na faɗa.

    Ina nan zaune ina ɗan duba wayata amman ban shiga group ɗin gidanmu ba sannan ban shiga na ɗaiɗaikun su da suka yi min magana ta private ba saboda nasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Fita na yi zuwa Instergram ina kallon kwalliya domin ni Allah ya yi da son abu fashion. Domin har certificate gare ni akam koyon kwalliya ba ma ɗaya ba sannan ina da na koyon saloon da gyaran jiki, shi ya sa wayata cike suke da ire iren su. Ban san na ɗau lokaci haka ba sai da Saude ta zo ta ce mini ta gama da ciki za ta gyara falo sannan na ba ta waje, bayan na ce in ta gama ta ɗora min ruwa a gas ta dafa taliya fara tunda ina da miya a firiza.

    Bedroom na koma na yi zama ma ina ta kallon Videos ɗin yadda ake kwalliya da na ɗaurin ɗan kwalli a istergram daman ni can na fi auki, kiran sallar azahar ya tada ni na ijiye wayar na je na yi sallah lokacin har Saude ta tsane taliyan da na ce ta dafa guda biyu, ni na karɓe ta na ce ta shiga ɗakin su Jidda ta yi sallah ni kuma sai na fito da miyar na > Janaftybaby: ɗumama.
    Na saka ma kaina sauran kuma na bar shi a cooler. Ƙaramin falo na koma na kunna kallo sai na sauya tasha zuwa Mb2 na iske a wani film mai kyau sai na barshi, filet ɗin abincin na kan jikina ni kuma na miƙe kafata saman cafet ina cin abinci ina kallo har Saude ta fito sai na ce ta ɗauko kofin ta tsiyayo mini ruwa a Dispenser.

    Sai ta kawo mini sannan na kalle ta ina faɗin” Ki ɗiba abinci ki ci sai ki zo ki wuce gida kin san kina da makaranta.”
    Da toh ta amsa min ta wuce kitchen ta diɓo taliyan ta zo ta zauna a kasa ta na ci, ba hira muke yi ba sai ni ce ma ke mata tambayoyi.

    “Babanku ya dawo?

    Sai ta ce min a’a sai na girgiza kai kawai, lagos ya ke zuwa kwadago in ya tafi sai ya yi rabin shekara bai dawo ba ya bar iyalansa da wahala.
    Ni na riga ta tashi, na tafi da filet ɗin hannuna da kofi zuwa kitchen na saka a sink ɗin wanke wanke.
    Leda na samu na buɗe drower ɗin cabinet ɗin kitchen ɗin na auna mata shinkafa tiya biyu sai taliya da maracaroni da na diɓar mata tunda nima abincin nawa ya yi ƙasa.

    Bedroom na koma na ɗauko mata 2k daga cikin jakata sannan na dawo falon lokacin ta gama cin abincin sai na ce ta wanke hannu ta zo.
    Ina zaune ta zo ta zauna gabana ta na faɗin” Ga ni Anty”
    Ledan na tura mata gabanta lokaci ɗaya ina mika mata kuɗin hannuna ina faɗin”Ki kaima mamanku kin ji ko?
    Ta karɓa tana faɗin”An gode Allah ya saka da alheri.” Na amsa da Amin ina faɗin”Ki yi sauri ki hau mashin ne biyu ta kusa.”
    Sai ta amsa minI, tare muka fita saboda zan rufe gida tana fita na maida gidan na rufe na dawo falo ina kallo, film ɗin horror ne ya ɗauki hankalina sai da aka gama shi amman za a yi part 2 ɗin shi.
    Uku na rana na koma ɗaki na kwanta sai barci ban ta shi ba sai huɗu da rabi, sai na yi alwala na yi sallah na ga tunda huɗu ta wuce sai kawai na ce bari na yi azkar ɗina.

    Ni kaɗai a gida kamar mayya na matsu su Jidda su dawo sai shidda suka dawo saboda biyar da rabi ake tashin su kafin ya je ya ɗauko su shidda ta yi tunda makaranta boko da isalamiya ne. Dawowarsu ne ya sa na fito falo suna bani labaran makaranta suna cin abincin, Baby ce mai surutun Jidda irin Babanta ne tana da sanyi sosai ba kamar Baby ba.
    Suna gama cin abinci suka sauya kaya zuwa na gida. Unform ɗin Jidda ta ce za ta wanke na ce yamma ta yi, tunda suna da guda biyu ta bari zan wanke musu gobe da safe

    Tare muka yi sallar mangariba, muna idarwa a ƙaramin falo muka fara karatu. Jidda na suratul maryam ne Babby kuma tana ƙasa ƙasa sai da suka biya na jiya na ƙara musu sannan muka yi azkar tare. Muna gamawa sai muka miƙe muka yi isha’i tunda an kira. Muna idarwa na bar su a falo suna kallo ni kuma na shiga kitchen na dafa ma Yallaɓai tea daman na dafa masa farar shinkafa tunda shi taliya ba ta dame shi ba, ina gamawa na shiga wanka ina wankan ma na ji shigowar motar Yallaɓai.

    A gurguje na shirya cikin riga da wando, wandon plazo ne mai buɗewa ta kasa. Rigar kuma Top ce mai wuya ta kama jikina sai na gyara gashin kaina na tufke a tsakiya na saka wata hula mai love a saman kaina kalan pick . Tsakiya babu komai, kwalliya na yi kamar yadda na saba na saka jan baki na kamar yadda na saba.
    Na ji ƙaran bude ƙofa ganin bai shigo ba ya sa na san ya shiga tiolet ne.
    Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ina zaune a gefen gado ina bin shi da mirmishi bayan na amsa sallamarsa.

    Hannuwana ya buɗe minI na tashi da sauri na faɗa masa ya rumgumeni. Nima sai na ƙamƙamesa ina fadin”Barka da dawowa Yallaɓai na.”
    Ya na shinshina ƙamshin humran dake jikina ƙasa ƙasa ya ce” Uhm. I like it.”
    Ɗagowa na yi muna kallon juna kafin na ce’Me? Yana mini wani kallo ya ce”ƙamshin ki mana.”
    Far na yi masa da ido kafin na ce”All is yours”
    Kumatuna ya shafa kafin ya ce” Allah ya yi miki albarka.” Na amsa da Amin.
    Ruwan wanka na ce zan haɗa masa ya yi wanka sai ya ci abinci.
    Shi kuma sai ya ce”E. sai mu ta fi wajen kiran Alhaji ba” > Janaftybaby: Gyaɗa masa kai na yi ba tare da na yi mgana ba. Sanda ya shiga wanka ni kuma na je haɗa masa abinci bayan ya fito ya sauya kaya zuwa wani yadi riga da wando ɗinkin zamani. Falon farko mu ka je saman dining ya ci abinci su Jidda kuma suna ƙaramin falo
    Bayan mun gama ba mu tsaya ɓata lokaci ba ya ce na saho hijabi mu ta fi, daman na fito da Hijabin jalbab mai ruwan ƙasa har ƙasa sai na saka takalmina iri ɗaya da wanda Yallaɓai ya saka daman tare ya siya mana.

    Na ce musu Jidda su kula da gida za mu je gidansu Gwaggo mu dawo. Baby taa saka rigiman sai ta je Babanta ya tsaya yana lallashinta da zai siyo mata ice cream sannan ta yarda na ce in za su kwanta su kashe komai za mu fita da key da toh Jidda ta amsa da yi mana a dawo lafiya.
    Sai da muka fita da motar sannan Yusuf ya koma ya rufe get ɗin
    Sannan ya dawo muka kama hanya mun ɗauki hanya kenan na kalle shi kafin na ce” Na gwada kiran ka yau ban same ka ba.”

    Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce”Nima na kira ki ban same ki ba.”
    Sai ya kalleni kafin ya ce”Me ya faru?
    Kai tsaye na ce”Kan mganar komawata Abu shika ne, Uncle Abba bai ƙara kiran ka ba?
    Sai a lokacin ya tuna ya ce”Kash! Ya kirani amman shaf na manta ba mu yi mganar ba. Amman bari yanzu zan kira shi.”

    Ni ya miƙa ma wayar ya ce na kira shi, Kawu Abba daman ya saka masa da na kira sai na saka a speaker har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

    “Kawu barka da dare.”

    Shuru bai yi mgana ba.

    “Uncle Abba barka da dare”

    Wata murya a dakushe ya ce”Yusuf in ma bashi kake nema na kuɗi ba ni dashi wallahi. Wanda ma nake binka EFCC ne za su ƙwatar mini haƙƙina.”

    Daga ni har Yusuf sai da muka kyalƙyace da dariya.
    Ni ce na ce”Haba Uncle Abba ba amana yanzu sai ka kai mini Yallaɓai EFCC?
    Jin muryata ya sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce” Sadiya? daman kina kusa? Na amsa masa da e, sannan muka gaisa dashi.
    Shi kuma sai ya bige da faɗin”Yallaɓan nan naki ya ci bashina kamar gadon ubansa yaƙi biyana. Gwara babbar hukuma ta shiga ciki, in na je gaban manya sai a saka sanayya a ciki gwara a kame shi ko amansu ne sai ya yi.”

    Yusuf na dariya ya ce” Na ci fa halas, abin da ya yi Nene shi ya yi ka fa Kawu Abba.” Kai tsye ya ce”Ko? To ai ko ita Nenen ta ci kuɗina sai ta biyani ballatana kai.”

    Ni dai ina ta dariya ganin sun sarƙe da gaddama shi Yusuf ya na faɗin ya ci halas kawu na fadin shi ba ƙanin Uban shi ba ne na uwarsa ne bashi da gadonsa. Zungurin kafar Yallaɓai na yi sannan ya yi gyaran murya yana fadin”Sadiya ta ce a yi maka tuni ka yi mganar da Dr Fadil ɗin?
    Kawu Abba dagacan bangaren ya ce”Kash na manta. Amman bari na kira shi na ji yadda muka yi zan kira ka.”

    Sai ya kashe wayar, dai dai Yusuf na faɗin” Kina ganin komawarki can da ganin likitan ba damuwa?
    Sai na gyaɗa mai kai ina fadin”E, ba matsala can ma ƙwararru ne. Tunda na yi ta nan ban dace shi ne aka ban shawara na gwada can ɗin.”
    Sai ya jinjina kai, bai yi magana ba sai ni ce na cigaba da faɗin”In ina da appoitment na ganin likita tun ana gobe zan je zariya na sauka gidan Ya Hamza bayan na gama ganin likitan sai na dawo.”

    Kai tsaye ya ce”E hakan ma ya yi. Allah ya sa a dace.”
    Na amsa masa da Amin.
    Mun shiga anguwan ɗorayi kawu Abba ya sake kira ya ce sun yi mgana da abokin nashi Dr Fadil shi likita ne a bangaren zuciya amman ya ce ya yi ma wata Dr Nayami mgana musulma ce amman ba bahaushiya ba ce, ya ɗan yi mata brief na matsalata ta ce zuwa sati mai zuwa za ta iya bani appiotment in har ya tabbata zai kira Kawun ya sanar dashi.

    Jin haka ya sa sai na ji daɗi kamar na je ta shaida mini zan iya sake samun wani cikin haka na riƙa ji. Daidai lokacin Yallaɓai na gyara parking a kofar gidanmu da ke anguwan Ɗorayi.

    KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
    07045308523.

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*

    Note
    error: Content is protected !!