Turken Gida – Chapter Twenty-six
by JanaftyTun a daran alhamis Yallaɓai ya kirani a waya saboda ranar ba a gidana ya ke ba. Ce min ya yi mu shirya ni da yara za su zo shi da Gimbiya su ɗauke mu domin zuwa sallar idi na ce masa to, domin ni yanzu tsakanina da Yallaɓai to ne domin na yi ma kaina alƙwarin kome zai yi ko ya ce ba zan ƙara yi masa mgana ba, ma'ana sai dai na gani na yi kamar ban gani ba na kuma ji na yi kamar ban ji ba domin a zauna lafiya.
Lokaci bayan. . .