Turken Gida – Chapter Twenty-eight
by JanaftyTun dawowar Gimbiya gidana na ke ta ganin ikon Allah a wajen Yallaɓai da dangin shi, su rawan ƙafa shima rawan ƙafa, ni dai ina gefe ina ganin komai kamar al'amara kamar mafarki. A ce yau wai a gaban idanuwana Yallaɓai ke ririta wata macen ba ni ba, kuma a cikin gidana ƴan'uwansa ke zarya saboda wata ba ni ba. Rayuwa kenan abin da ya baka dariya wata rana shi zai koma ya na ba ka tsoro.
Anty Bahijja ku san kullum sai ta zo gidan nan sai ka ce ni ɗin zan cutar da Gimbiyar. . .