Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Rahila ce jirgin danƙaro ita ce karshen zuwa har sai da na yi mata tsiyan tana kusa amma itace ƙarshen zuwa. Tana dariya ta ce
    ” Ni fa na ɗauka ni ce ma farkon zuwa kawai sai na ga gida ya cika.” Muna ta mata dariya ni da Ya Balki.

    Amina ta kira waya da ta ji gida cike kowa da kowa na nan kamar ta yi kuka ta ce ta yi missing. Ta so zuwa amma ba ta samu dama ba sai dai ta ce sallar layya in sha Allahu da ita za a yi.
    Ya Auwal kuma ni na kira shi a waya ya ce sun ɗan fita da laila ne da yara gidan shuru sallar duk ba daɗi sai ya ce na kunna data ya kira Video call nan ne fa suka gaisa da kowa har da Gwaggo da Alhajinmu an kai musu sun yi mgana da juna.

    Ya Hamza kuma na kira wayarsa ba ta shiga ba sai na kira na Khaleesat. Ita ke faɗin ya kwanta ashe bai jin daɗi zazzaɓi kuma ya hana a faɗa ma kowa. Muna cikin wayar ya tashi sai ta bashi wayar dukkanmu muka karɓa muka yi masa sannu da jiki ya ce ya ji sauƙi ya je asibiti maleria ne an yi masa allura kuma an bashi mganguna. Ba mu jima muna mgana da su ba tun da bai jin daɗi daga nan muka yi masa sallama da fatan samun lafiya. Datti dai za su fara jarabawa Jiya da yamma ya koma makaranta.

    Dukkan mu muna ɗakin Mama daman yawancin in dai mun zo gida mun fi zama ɗakin Mama. Gwaggo na ɗakin Alhajinmu suna ta fama da yara. Hira muke yi na can garin mu Yashe bayan sallar nan akwai bikin autar su Ya Muntari wato ɗiyar Baba Aminu kenan Yaya Aina ce ke mganar haɗa guddumuwa daman haka muke in sha’ani ya tashi sai mu haɗa kanmu kowa ta kawo abin da ta ke dashi mu haɗa mu ba ma Gwaggo ita kuma sai ta nuna ma Alhajinmu ya yi ta godiya kuma in sha’anin ya tashi ko ba dukkanmu. Yaya Murja da Yaya Balki suna zuwa ni ce ma ban cika zuwa ba sosai Rahila daman can ne tushen Mijinta tana yawan zuwa amma wannan karon tunda na ji bikin na ce sai na je Yashe na yi sati in sha Allahu tun da na daɗe ban je ba tun ina da cikin Baby da babbar ɗiyar Baba Sani ta rasu muka je gaisuwa kuma a ranar muka dawo ba mu kwana ba.

    Bikin bayan salla da sati uku ne. Yaya Aina ta ce ana jibi biki za mu tafi saboda Matar Baba Aminu magajiya mai yi ce ba ta wuce duk wani sha’anin mu ko ba ta zo ba ƙannen Yaya Muntari za su zo gaskiya tana da ƙoƙari daga ita har Baba Aminun suna da riƙo kan zumunci.
    Muna cikin hiran ne Marwa ta shigo sai dai ta ce sannanun ku gabaɗaya a ka amsa mata in da na ke zaune ta nufa tana faɗin” Umma Baby ta jiƙa kayanta da ruwa.”
    (Daman Umma ta ke ce mini kamar yadda su Jidda ke kirana.)

    Kai na jinjina kafin na ce” To ai sai ta zauna dashi. Domin ban zo mata da wasu kayan ba.”
    Da sauri ta ce” Gwaggo ta ce a cire rigar a shanya kar zazzaɓi ya kamata.”
    Kafin in yi mgana Rahila ta karɓe da cewa” To ba wasu kayan? In sanyi ya kamata fa”
    Yaya Balki ce ta yi mgana wannan karon da cewa” Sadiya ce fa da tsiyarta. Ba za a rasa wasu kayan su Baby a gidan nan ba.” > Janaftybaby: Yaya Murja na gefe ta ce” Ko ba na ta ba. Ba za a rasa kayan da za ta saka kafin na ta ya sha iska ba.”
    Muna cikin mganar Marwa ta fita sai ga Gwaggo ta leƙo ta na faɗin ita ta ce a cire mata rigar a shanya ta samu wata riga ta ba ma Marwa ta saka mata na amsa mata da to Gwaggo.
    Yaya Balki ce ke mganar ta ga Marwa ta yi mata girma ne a ido ina mirmishi na ce” Ai na kusa yin suruki in sha Allahu.”
    Yaya Balki ta amsa da Allah ya sa.

    “Aina can Marwa ta yi salla gidan Sadiya ne?

    Ya Murja ta faɗa ta na mai kallon Ya Aina wacce ta amsa da mata da cewa” E. Tun kafin ta dawo daga makaranta ta dame ni da ni Mama a gidan Umma Sadiya zan yi salla na ce to. Ta na dawowa ta gaya ma Baban shima yana dariya ya ce to yar gidan Umma Sadiya a dawo lafiya.”
    Ina mirmishin jin daɗi na ce” Ai wallahi na ji daɗin haka. Ni da za ku bar mini ita a wajena Ya Aina.”

    Yaya Balki na dariya ta ce” Topha ƴan mata ba su ishe ki ba ne Sadiya?
    “Ina fa suka ishe ni. Ban ƙi dozin ba Yaya Balki.”
    Muka saka dariya gabaɗayanmu Rahila ce ta ce” Sai Ya Aina ta baki. Ki haɗa da Jidda ki riƙe gabaɗaya.”
    Ma’u na gefe ba ta ce komai ba ta na latsa wayarta. Ya Murja na sauraran mu amma ba ta yi mgana ba Ya Aina ke faɗin Marwa za ta fara pratical a asibti kuma babanta ba zai bari ba amma don ta riƙa zuwa miki hutu lokaci bayan lokaci ba zai ce komai ba.

    na marairacewa na ce” Haba Ya Aina. In kika saka baki zai bari mana.”
    Dariya kawai ta yi ba tare da ta yi mgana ba Yaya Balki ce ke faɗin” Topha! Lalle lamarin Sadiya azimin ne.
    “Da gaske take yi.”
    In ji Rahila ni kuma na juya ina rantse musu da gaske nake yi.

    “To ke in kina son ɗauka shi Yallaɓan na ki na so ne?

    Ya Murja ta faɗa tana kallona da sauri na ce” Haba Ya Murja na ɗauka ke mai shaidar Yallaɓai na ne. Ba Marwa ba ko wacce bai sani ba ne na kawo na ce ina so zan riƙe wallahi ba zai ce komai ba. Ballatana ma Marwa shi ya fara cewa ko za mu karɓo Marwa ne ta dawo wajen mu da zama Sadiya? Shi ya sa ma kika ji na yi mgana.”

    “Oh.”

    Kawai ta ce ba ta ƙara mgana ba. Yaya Balki ce ta karɓe mganar da cewa” Kuma fa hakane. Yallaɓan na ki ba shi da matsala gaskiya.”
    Rahila ma ta amsa da cewa” Shi da ke son yara. Allah ne dai bai bashi da yawa ba.”
    Ita dai Yaa Aina ba ta ce komai ba sai dai ta na ta mirmishi daga karshe ta kashe mganar da cewa babanta ba zai bari ba ni kuma na ce zan sako Yallaɓai a gaba mu zo tambaya Rahila na dariya ta ce” Shike nan ma an kashe boss ɗin.”

    Muna ta dariyan mu cikin nishaɗi. Daman fa ko haɗuwa aka yi waje ɗaya Ma’u da Ya Murja sun fi tsame kansu gefe ana hira sai jifa jifa suke saka baki tun ballatana ma in ina wajen. Ni kuma ban damu da su ba in suka sako ni na yi da su in ba su sako ni ba na juya na yi da waɗanda ke yi da ni. Zaitunan Yaya Abubakar tana ɗakin Gwaggo tun da ta zo sai barci kamar wata kasa Yaya Balki ta ce Allah ya sa ba ciki ne da ita ba Ma’u ta kwashe da dariya ta na faɗin” Kuma kamar kin san ta yi yaye ba.”
    Ya Aina ta ce” Kai wannan mata ta Abubakar. Allah ya sauwaƙe.”

    Ni kuma sai na kada baki na ce” Ku barta ta haihu. Iya rabon ta a duniya fa za ta haifa. “
    Sai Rahila ta ce kuma gaskiya ne. Gwaggo ce ta leƙo ta ce an kira salla ga ƴayanmu can har sun yi alwala mu ma sai mu tashi jin haka yasa muka firfito domin yin alwala ni ban samu buta ba sai na zauna ina jira Anti ta gama da na ta butan ta bani sai da ta idar da alwalan sannan ta kawo min na amsa ina faɗin” Su Anti an zama yan mata.”

    Ta na dariya ta rufe fuska kafin ta ce” Anty Sadiya ina goron sallah na.”
    Kai tsaye na ce” Gorom sallah kike so?
    Sai ta gyaɗa min kai. Ni kuma sai na rausayar da kai kafin na ce” Goron salla ai a gida ake ba da wa Anti. In kina son goron salla sai ki zo gidana ki karɓa. Yanzu ma kin makara salla ta wuce sai dai kuma ta layya in muna raye.”

    Ita Anti ba ta damu da mgana ta ba cikin dariya ta ce” Kai Anty Sadiya.” > Janaftybaby: Nima ina mata dariyan na ce” Ƙwarai Anti. Salla layya in kina son goron salla ki zo gidana da wuri ni kuma sai na cika miki jaka da kuɗi.”
    Gwaggo na bakin famfo tana alwala ta na jin mu ta dai yi mirmishi ba ta saka mana baki ba.
    “To Anty Sadiya in sha Allahu zan zo. Wannan salla a gidan Umma Ma’u na yi shi ya sa.”
    Ina mata mirmishi na ce” To ai shiken nan na ma san Ma’u ta cika miki jaka da goron sallah ba ki buƙatar tawa ko?
    Har ga Allah ni a wasa na yi mganar kawai sai gani na yi Ya Murja ta bankaɗo labule ta fito da hijabi a jikinta da alamun ta idar da salla ne kallona ta yi daga sama har ƙasa nima ko cikin mamaki na ke kallonta sai kawai ta daka ma Anti tsawa ta na faɗin ta wuce ta je ta yi sallah sai yarinyar ta wuce ɗakin Gwaggo da sauri.
    Kamar zan yi mgana sai na fasa na fara tafiya wajen famfo Gwaggo ta taso za ta shiga ɗakinta.

    “Ke Sadiya..”

    Ya Murja ta yi mini kira cikin gatsali sai na juya ina kallonta cikin mamaki. Ba ma ni kaɗai ba hadda Gwaggo.

    “Me ya faru Ya Murja?

    Na faɗa ganin kamar tana sakin huci kawai sai ta nuna ni da yatsa ta na faɗin” Daga yau in kina so ki yi min rashin kunya ki zo gare ni kai tsaye ne ba sai kin rakuɓe a jikin ƴa’ ta kina gaya min mgana ba. Ba na son rashin kunya.”
    Galala na yi da baki ina kallonta kafin na samu zarafin mgana Gwaggo ta tsawarta da cewa” Murja me kuma ya kawo wannan mganar?

    A fusace ta ce” Ba ki ji mganganun da ta ke faɗa ma Anti ba ne? Ta nuna kamar da gayya ne ban tura Anti gidanta ba na tura ta gidan maƙiyarta Ma’u ba. Duk na fahimci mganganunta.”
    Gwaggo ta yi tsaki kafin ta ce” To ni ban ji haka ba. Mganar su kawai suke yi na tsakanin uwa da ƴa.”
    Nan fa Ya Murja ta ce ita fa k a taufau da ita na ke yi. Ƙara nuna ni ta yi da yatsa kafin ta ce” Daman ba tun yau ba kin sha faɗan wai na fi son Ma’u da ke da ita kawai na ke shiri yayana ma gidanta suka sani. To yadda kika faɗan ne domin Ma’u ta fi ki ladabi da biyayya sannan ita ta ja ƴa’ƴana a jiki ke kuma da ba ƙi kaunar su ba ki ja su a jiki ba. Kin ga ko kar ki ga laifin su in ba su je in da kike ba. Gidan kuma Ma’u da ki ke jin haushin suna zuwa yanzu suka fara zuwa. Sai dai baƙin ciki ya kashe ki Sadiya”

    “Murja me ye haka don Allah.?

    Ya Aina bayan ta fito daga ɗakin Mama itama sanye da hijabi ita da Ya Balki da Rahila. Ma’u dai ba ta fito ba ni kuma tsabar mamaki ma na kasa magana.
    “Ya Murja Alhajimmu na ciki fa. Gaskiya wannan ba girman ki ba ne. Sadiya fa ba da ke ta ke mganarta ba.”
    A fusace Ya Murja ta ce” Ba za ku gane ba ne. Ni na san ga in da ta dosa. To me ye na damuwa don ƴaƴana ba su je in da ta ke ba. Marwa da kika zaɓa kina so ita ai kin gayyaceta kuma ta je suma in kika nuna kina so su je ɗin za su je.”

    Sai a lokacin na fahimci haushina ta ke ji saboda Marwa. Kai wannan mata ta ɗoramin karan tsana.
    Ba na so na yi hayaniya saboda Alhajinmu kawai sai na yi mirmishin takaici kafin na ce” Ki yi hakuri Ya Murja na ga ƙin ɗau zafi har ga Allah ba da wata munafa na faɗi mganar da na faɗa ba. Amma in ta ɓata miki rai Allah ya baki haƙuri. Mganar Anti na zuwa gidan Ma’u ban taɓa sawa a kaina ba domin da ni da Ma’u duk ɗaya ne. Ke ma kuma ina so ki gane wani abu da Anti da Marwa ɗaya suke a wajena ba Bambamci.”

    Ina gama faɗin haka na juya na wuce wajen famfo ina taran ruwa a buta. Na san dukkansu sun yi mamakin sanyina har sai da Gwaggo ta ce” Shike nan Sadiya kin gama magana. Ke kuma Babba kwabo kin ji kunya tunda har yau Sadiya ta fi ki hangen nesa.”
    Ganin ban kulata ba ya sa ta koma ɗaki fuu. Kuma kowa ita ya ba ma rashin gaskiya a wajen. Sai bayan da na ɗauro alwala na shigo cikin ɗakin ne Ma’u ta ke ce min” ki yi hakuri Sadiya ki fahimci Ya Murja don Allah itama ba da wata munafa ta yi miki mganar ba.’

    Kallonta kawai na yi ni kam wani makircin Ma’u ne ban gani ba sai kawai na ce” Bakomai. Ita za ki ƙara ba ma hakuri saboda na ga kamar ta ɗau zafi da ni.” > Janaftybaby: Ina gama faɗin haka na saka Hijabi na ta da salla. Bayan na idar sai muka ci abinci na ga dai Ya Aina ta keɓe da Ya Murja na kuma san faɗa ta ke yi mata shi ne na ga ta ɗan saki ranta a raina na ce matar nan me na yi mata wai ta tsane ni ne?
    Muna cikin cin abinci sai ga Ya Abubakar ya shigo ganin abinci kala kala muna ci ya sa ya ce”Kai. A ina aka samo abinci nau’i nau’i haka kamar an samu sabon restaurant?

    Rahila ce ta faɗa masa kowaccem mu ta dafo abinci daga gidanta sai shima ya samu waje ya zauna ya na faɗin” To shi ne ana wannan shagali aka manta da ni? Ni ne fa the head of the family”
    Ya Balki ta ce” Mun ɗauka Zaituna ta yi maka kyakyawan beta kafin ta fito gida”

    Ta faɗa ta na kallon Zaitunan da ke ta cin abincinta jin an taɓo bangarenta ya sa ta yi saurin cewa” Laa shi ya ce in taho ba sai na tsaya na yi abinci ba.”
    Rahila ta ce” Ehem daman na san za a rina.”
    Yaya Aina ke faɗin” Ke kam Zaituna ban san yaushe za ki wayau ba. Ko mu kin ga mun taho ba mu yi girki ba? Ga shaida nan tunda gashi nan kina ci in da kin dafa kafin ki fito mijin ki zai zo ya na neman abinci?
    Kanta na kasa ba ta yi mgana ba Yaya Abubakar ya wani girgiza kai kafin ya ce” Ƙyaleta Aina ta yi lokaci ne.”
    Daga haka kawai ya miƙe ya ce ya na ɗakin Alhaji a kawo masa abinci. Zaitunan Ya Aina ta tasa ta ce ta saka mai ta kai masa ta na fita Ya Murja ta ce” Mata kamar mai almatsutsai”
    Ya Aina ta ce” Lafiyan ta ƙalau iskanci ne kawai da ta samu shi Abubakar ɗin mai sanyi.”

    Ni dai ina jin su ban tanka ba ina ta cin abincina ni shinkafa da waken da Rahila ta dafa na ke ci su kuma su Ya Aina sun ci nawa sun kuma ci na Ma’u ita waina ce da Sinasir. Mganar gaskiya duk cikin mu Mijin Ma’u ya fi kuɗi kowa kuma ya san haka amma duk da haka dukkanmu ba za a ce muna cikin halin rayuwa ba dai dai gwargwado mazajen mu na da rufin asiri. Mijin Ya Murja ne ma sai a hankali domin ya samu matsala can kwanaki an kore shi daga wajen aiki ya fi shekara uku a gida amma dai an ce ya koma shi ya sa Ma’u ta samu dama tana taimakonta ita kuma kwaɗayi ya sa idanuwanta ya rufe. Ni ba na kyautar ganin ido ko ka gode min in na yi niyyar yi maka alheri na yi, in ban yi ba shike nan ba zan yi domin duniya ko kai da zan mawa ka yabeni ba ita kuma Ma’u daman halinta ne ta yi alherin da duniya za ta sani a yabe ta a kuma san tana yi ɗin da son nuna ita fa mijinta na da kuɗi domin in dai Ma’u ta san za a zo gida a haɗu ƙarshen kayanta a kyau da tsada ta ke sakawa. A fuska ba ta nuna wani abu amma ga ni da na san halinta ni na san ta na da halin son a sani.

    Yanzu ma muna cin abincin ta na ba da labarin Alhaji Mustapha ya ce zai ba ta jari na miliyan biyar ta fara kasuwanci shi ne take neman shawarammu wata sana’a za ta fara. kowacce na faɗin albarkacin bakinta nima sai na tofa nawa na ce ta saro dogayen riguna da takalma da mayafai na mata ta fara saidawa mu gani ko za su tafi. Sai Ya Aina ta ce yauwa ta ƙara har da atamfofi da kayan yara ni kuma sai na ce kayan yara ta jinkirta tukunna zuwa gaba ta fara da waɗanan dai ta gani yadda kasuwan za ta kaya.

    Cikin mirmishi ta ce” Haka ma Shema ta ce. Da ya ke mun yi mganar da ita ta waya. Ya ce dai na tsaida shawara visa na fitowa Egypt za mu je a can zan yo sarin kayan nawa in sha Allahu.”
    Ya Murja ta washe baki tana faɗin” Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ƙanwata.”
    Ta amsa mata da Amin Amin. Ita kuma Ya Balki ta ce ” Sai ki faɗa ma Gwaggo da Alhaji su suka albarka.”
    Sai ta ce za ta faɗa musu sai mata fatan alheri suke yi nima na yi mata ta re da fatan Allah ya sa a fara a sa’a ta amsa lokaci ɗaya ta na kallona kafin ta ce” Amin Sadiya. Amma fa kema ya kamata ki zo ki fara wata sana’ar zama haka ba daɗi.”

    Wani abu ya tsaya mini a maƙogawaro. Ma’u ta bala’in raina min wayau. Kuma kawai sai su Ya Balki suka amsa da wallahi kuwa Sadiya. Rahila ce ke faɗin” Ita fa Sadiya Shagon saloon da gyaran jiki take son buɗewa” > Janaftybaby: Ya Balki ta ce” To wannan ai lissafi ne me yawa. Ta dai yi tunanin fara wani abun kafin ta yi ƙarfin da za ta buɗe saloon ɗin.”
    Duk yadda na so na yi mgana sai kuma na kasa. Da na so na mayar mata da martanin mganarta ne sai kuma na yi tunanin ina yi magana za a ce ni ce fitinanniya Ma’u ta yi min mganar arziƙi na maida shi ta tsiya

    Sai kawai na kalli Ma’u nima sai na mayar mata da martanin mirmishinta kafin na ce” Kar ki damu ki maida hankali kan naki. Nima soon in sha Allahu Suprise zan ba ku.”
    Sai ta ce Allah ya yarda ta na min wannan dariyan na ta na mugunta. Ya Aina ko sai faman mgana take yi ta na cewa sana’a ita ce mace ko da mijinki na maka komai to ka yi dogaro da kan ka ko domin wata rana.
    Ya Balki ta ce” Har da ma rayuwa Ya Aina.”
    Rahila ma na ji tana fadin itama za ta fara awo a cikin gida Ya Aina ta ce kasuwanci mai kyau. ita Ya Aina tana saida kayan miya da kayan nau’in ɗanɗanon girki ita kuma Ya Balki tana saida gwanjuna. Ni ce daman ban saida komai sai Rahila Ma’u kuma daman tana nuna mijinta na mata komai sai yanzu ne ta zo da labarin za ta fara na ta kasuwamcin.

    “Albishirin ku”

    Na faɗa ina musu mirmishi. Na gama cin abinci tuni har na sha ruwa na yi gatsa.

    “Goro fari ƙal.”
    In ji Rahila da Ya Balki har suna haɗa baki.

    “Nan da kwana uku za mu cika shekara sha biyar da aure ni da Yallaɓai na. Haka ma Rahila da Ya Muntari.”

    Na faɗa ina musu mirmishi.
    Ya Balki ta fara cewa” Ma sha Allah. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Kai ashe kun daɗe kamar jiya ne na ke ganin bikin ku fa ke da Rahila?
    Rahila na dariya ta ce” Sadiya ta na lissafi ni fa mancewa na ke yi. Ko da muka yi shekara goma sai da na ga sun yi walima ne na ce ma Ya Muktar yau auran mu shekaru goma Cif.”
    Ya Aina ta ce” Shekarun suna gudu ba wuya. Allah ya ƙaro muku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya raya muku zuru’a.”
    Muka amsa da Amin Ya Murja ma ta yi addu’a muka amsa mata. Sai Ma’u da ta gyara zama tana fadin” Ma sha Allah. Allah ya ƙara ɗankon kauna Mrs Yallaɓai da Mrs Ya Muktar.”
    Ni ce na amsa mata Rahila ta na jin kunya Zaituna ce ta yi karaf ta na faɗin” Sadiya akwai walima ne?
    Ina mata dariya na ce” Akwai amma ta iya ni da Yallaɓai ce da yara.”

    Ma’u ta ce” Allah? Ban damu kenan? Ina mata fari na ce” Ai kun gama na ku tunda kun yi addu”a.
    Ya Aina ta ce” Shi ne ko babban mgana.”
    Zaituna na kallah ina faɗin” Tambayi Rahilan Hubby ƙila za su haɗa mana walima.”
    Duka ta ɗaka min a cinya ta na faɗin” Sadiya ban son wulaƙanci.”
    Kamar zan yi kuka na ce” Wai don na ce Rahilan Hubby shi ne har da duka? Rahila sai kawai ta balla min harara kunya duk ya kamata mu kuma gabaɗayanmu muka fashe mata da dariya.
    Sai ta ji kunya ta tashi ta fita, ta na fita Ya Balki ta ce” Daga Rahilan har Muntari masu kunya ne.”
    Ya Aina ta ce” Wallahi ba su da hayaniya. Alhajinmu ya sha cewa tabbas an ijiye kwarya a gurɓinta.”

    Ranar yini muka yi ana ta hira a yi daɗi a yi tsiya bayan mangariba Gwaggo ta ce Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shiri ta koma gidanta yinin ya isa haka. Jin haka yasa muka fara shiri saboda tun da Alhaji ya yi mgana to dole fa kowa ta kama hanya. Ni dai Yallaɓai na kira sai ya ce bari a yi sallar isha’i sai ya zo mu tafi gida. Ma’u ta fara tafiya Alhajinta ya zo ɗaukansu ita da yara haka ya yi mana yayyafim kuɗi goron salla damu da ya’yanmu ban sam kuma nawa ya ijiye ma Alhaji da Gwaggo ba. Su suka tafi da Zaituna da ƴaƴanta za su sauke su a gida daga can na ji Ma’u na faɗa ma Gwaggo za ta biya gidan su Shema’u.
    Kafin ya zo daman Ma’u ta sanar da Alhajimmu da Gwaggo mganar jarin da ya ce zai ba ta su ka yi ta masa godiya da saka albarka.
    Nima da Yallaɓai ya zo mun je gaban Alhaji na faɗa masa nan da kwana kaɗan auran mu zai cika shekara goma sha biyar da ni da Rahila.

    Alhajinmu ya yi mirmishi kafin ya ce” Ma sha Allah. Shekaru goma sha biyar masu albarka da tarin albarka zuru’a. Allah ya ƙara haɗa kawunanku. Haƙiƙa Yusufa da Muntari sun cika ƴaƴa tunda duk tsawon wannan shekarun ba su taɓa kawo min ƙaran ku da sunan kun yi musu wani abu ba hakan ma abin alfaharina ne. Allah ya yi muku albarka ya bar ku tare har jikokin ki.” > Janaftybaby: Kan mu na ƙasa ni da Yallaɓai muna ta amsawa da Amin Amin.
    Gwaggo na gefe ta na ta saka albarka kafin ta ce” Jiya ba yau ba. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Na tuna da Mama itama shekarunta a ƙasa kenan Allah ya jiƙanta ita da Hajiya gabaɗaya.”
    Muka amsa mata da Amin Amin da za mu tafi shima Yallaɓai ya ba ma yaran su Ya Murja goron sallah Marwa dai ta ce za ta bi Ya Aina zuwa gida amma jibi za ta dawo. Yallaɓai ya ba ma Alhajimmu kuɗi da Gwaggo amma ban sam ko nawa ba ne. Daga nan muka yi musu sallama ya ɗauke mu zuwa gida.

    Sai da muka koma gida har mun yi shirin kwanciya muna rumgume da juna Yallaɓai na shafa gashin kaina ya ce.

    “Sadiya ta.”

    “Yallaɓai na”

    Na amsa masa cikin so da ƙauna. Sai kawai ya ce” Gani na ke yi kamar jiya jiya muka yi aure sai ga shi wai mun kusa cimma shekaru goma sha biyar da aure cikin yan kwanaki ƙalilan masu zuwa.”
    “Nima haka na ke ji a zuciyata.” Haka na faɗa masa na ke jin kamar jiya muka yi auran ashe shekarun sun tafi.
    Ƙara kamkameni ya yi kafin ya ce” Har yanzu ba ki sauya daga Sadiyar da na fara sani yar shekara sha tara ba.”
    Nima ina mirmishi na ce” Kai ma har gobe baka sauya min a wannan gwarzon matashin da na aura a shekaru ashirin da bakwai ba.”
    Sai kuma muka kalli juna ta cikin duhun ɗakin da ɗan hasken da ya kan shigo ta window ɗin cikin bedroom ɗin kafin ya sumbaci goshina ni ma sai na maida masa martani na sumbaci kumatunsa kafin mu koma mu kwanta yama ƙamƙame dani kamar za mu koma abu ɗaya.

    **

    Wed.13 JULY 2015.

    Rana ta ƙara zagayowa ranar da a irinta ne aka ɗaura mana aure ni da Yallaɓai a irin kuma ranar ne muka zama miji da mata. Jiya Yallaɓai ya dawo domin tun washegarin ranar da muka dawo daga Ɗorayi ya je kaduna sai jiya da daddare ya dawo. Kuma yau tun safe ya fita saboda Nene ta kira shi a waya tana son ganin shi. Bai ko tsaya a gida ya ƙarya ba ya fita wanka kawai ya yi. Su Jidda sun koma makaranta tun jiya sun tafi gidan ba kowa sai ni kaɗai Marwa ba ta dawo ba amma na kira Saude na ce ta zo ta ta ya ni mu gyara gidan.

    Na ba da a yi mana cake babba sannan a gida na ce zan yi mana zoɓo muna da sauran naman sallah na ce kawai sai mu yi amfani dashi bayan haka na yi dambun nama da yawa ya na nan. Kawai dai yar walima ce daga ni sai mijina sai ƴa’yana.

    Saude ta zo da wuri tare muka gyara gidan ko’ina muka turare shi da turaren kamshi. Saude na saka ta dafa farar shinkafa tunda ina da miya da na yi a frigde sai na koma ɗaki na ɗau wayata na kira telanmu domin na ɗinka wani material mai kyau saboda wannan ranar na tuna masa yau zan yi amfani da shi sai ya ce zai aiko min da shi anjuma kaɗan. Sauran kazar da na siya wajen Surayya Halin yau na ce Saude ta ɗumama ta kai mini falon yara ni kuma sai na kunna data na shiga ina ganin saƙonni.

    Na ga group ɗin gidanmu ana ta tagging ɗina ina shiga sai na ga Ma’u ce ta sanar da Anniversery ɗin mu ana ta yi mana fatan alheri ni da Rahila da Ya Muntari.
    “Mrs Injinya Allah ya ƙara dankon ƙauna.”
    In ji Yaya Auwal shi kuma Ya Hamza tagging ɗina ya yi kafin ya ce” Yallaɓiya an gangara a bautar ubangiji.. Allah ya zaunar da ku lafiya.”
    Haka suka yi ta ma Ya Muntari shaƙiyanci wai ɗankwali ya ja hula.
    Nima na shiga ina amsawa cikin farimciki.
    Na je na yi status amma ban saka hoto ba na dai saka Alhamdulillah!
    Sannan sai na rubuta”

    “Shekaru goma sha biyar cikin farinciki Alhamdulillah.”

    Duk da ban yi caption ba sai aka fara mini mgana ta private ana mana addu’a yawanci duk yan makarantar mu ne da muka yi BUK tare waɗanda na ke da lambarsu.

    Sai Adnan ɗin su Yallaɓai da ya gani ya ce min” Ma sha Allah Happy Wedding Anniversery Mrs Yusuf Muhammad Tafida.”
    Musabahu ma haka ya ce mini” Ma sha Allah Allah ya ƙaro danƙon kauna ta Yallaɓai”
    Duk na amsa su. Sauran dai su Anty Bahijja ban ga sun gani ba. Zuwa na yi na zaƙulo hoton Rahila a waya na ranar sunan ɗiyarta da aka ɗauka na saka a status ɗina na c > Janaftybaby: ” Happy 15 years Wedding Annivesary Mrs Muntari Amini yashe(Hubby)”
    Sai na ƙara da emojin rawa da murna da dariya. Ina ta dariya saboda na san in ta gani sai ta yi mgana Ya Hamza ya fara gani kawai sai ya yi tagging ɗin status ɗin da cewa.

    “Ina na ki hoton?

    Ina dariya na ce ni ban da hoto ya ce ban isa ba. Kowa sai ya ce wai ina hotona da na Yallaɓai tunda na saka na Rahila. Ganin sun dameni ya sa dauko hoton da ranar idi ne ma Marwa ta ɗauke mu da wayata ni da Yallaɓai yana tsaye ni kuma na jinginar da kafaɗata a saman kafaɗarsa. Shi waya ma ya ke yi bai san ana hoton ba ni kuma ina mirmishi. Hoton ya yi kyau sosai yana sanye da farar shadda mai babban riga sai dai ya cire babban rigan. Ni kuma na saka leshi mai ruwan haske akwai zanen marun a jikin leshin sai ya haskani gabaɗaya.
    Ina mirmishi shi kuma Yallaɓai ya ɗan sunkuya yana kallona aka ɗau hoton shi na saka a kasan hoton sai na saka.

    “Barka da shekaru goma sha biyar cikin Aminci, soyayya, sadaukarwa a gare ka ya amintattace na. MRS HALIMATUSADIYA YUSUF MUHAMMAD (YALLAƁAI NA)”
    Na ƙara da gayyar emoji kafin ka ce kwabo duk yan gidanmu sun ce na tura musu a group ɗin gida na tura hotunan tuni har sun sakamu a status daga ni har Rahila ni a bayan wannan sai na saka hoton Jidda da Baby shima da wannan sallan aka yi musu na yi mgana a ƙasa da cewa.

    ” A shekaru 15 da auren mu ga albarka da Ubangiji ya yi mana nan. Allah ya raya ku HAUWA’U YUSUF MUHAMMAD(Jidda) DA MAIMUNATU YUSUF MUHAMMAD(Baby).”

    Kowa sai addu’a ya ke yi. Har ta Ma’u sai da ta ce na tura mata itama ta saka ta yi mana addu’a na amsa mata ko da bai kai zucci ba.

    Na duba Yallaɓai ba ya online na kuma kira layin shi ba ta shiga. Sai kawai na tura masa test massages.

    “Happy Wedding Anniversy Yallaɓai na”

    Na jira na jira amman bai turomin amsa ba sai na yi tunanin ƙila Network ya sa bai shiga ba. Da ya tafin na kira shi na ji ko Jikin Nenen ne ya tashi sai ya ce mini yanzu ya iso gidan lafiyanta ƙalau sai hankalina ya kwanta.

    Na yini cikin farincikina ina ta amsa wayoyin yan’ uwa da abokan arzuƙa har mutanen fatakol Anty Zabba ta kirani ta na min fatan alheri Haka Munnira Hauwa dai wayar ta ya lalace ba ta sani ba.
    Amma har Nafisa Muhammad Sani mun yi mgana da ita, sauran yan gidansu Yallaɓai duk waɗanda suka ga status ɗina mun yi mgana hatta da Halima Autar su Yallaɓai amma ban ga Anty Bahijja ko Anty Maimuna sun gani ba Mimisco dai tana online amma ba ta duba ba.

    Ban damu ba, na cigaba da harkokina. Saude sai wajen uku ta tafi gida ni kuma salla kawai ke ta da ni a inda na ke Yallaɓai har lokacin bai dawo ba na kuma kira shi ta shiga bai ɗauka ba na ƙara kira shuru sai can ya turamin saƙon zai kirani ya je wani waje ne ni kuma sanin sabgoginshi sai ban damu ba.
    Na cinye sauran kazar hadin uwargida duka na sha gumba sannan na sha kayan marmari ranar ko abinci ban ci ba har Jidda suka dawo makaranta daman na gaya musu in Yallaɓai ya dawo da daddare za mu yi walima Jidda ta ce” Umma waliman mene?
    Ina mirmishi na ce” Na cikar mu shekaru sha biyar da aure ni da Abbanku.”

    Da ya ke ta na da wayau sai ta ce” Umma Allah ya bar ku tare.” Na amsa da Amin Baby kuma sai tsallen murna ta ke yi, ko kafin mangariba har ɗinkina an kawo min daman kunshin sallar da na yi bai fita kitso kuma daman bai dameni ba ƙara gyara kaina kawai na yi, na saka Jidda ta ƙara gyara gidan ta kunna turaren wuta. Ina da bloons na ma Baby ne jidda ta kama min muka hura su na ɗaura su a falon mu wajen guda ashirin kala kala. Sai falon ya yi kyau sai bayan mun yi sallar mangariba sannan mai cake ta aiko mini dashi da kwatance sai gashi a gidana ta online na siya ƙanwar wata mate ɗina ce da muka yi Buk ce ke yi.
    Sannan na siya ma Yallaɓai gift wani agogo mai kyau 25k shima a wajen wacce muka yi BUK na siya daman kayan maza take saidawa na saba siyayya a wajenta in dai zan siyam Yallaɓai wani abu na gift wajenta na ke siya. > Janaftybaby: Bayan mun idar da salla mangariba muka ƙara kawata falon a center table na ijiye cake ɗin sai muka zagaye shi da voul na nama da dambun nama cake, da donut sai lemuka da ruwa. wajen ya yi kyau muna gamawa na ce Jidda ta kashe hasken falon in an ji motar Yallaɓai yana shigowa sai a kunna daga nan na ce su je ta yi wanka ta yi ma Baby na ce su saka dogayen rigunan da na siya musu yan kati ita na Jidda riga da wando ne. Baby kuma doguwar riga ce kala ɗaya na siya musu mai kalan baƙi da fari.

    Nima na shiga bedroom ɗina na tuɓe na faɗa Tiolet na yi wanka amma a ƙasan raina ina tunanin ina Yallaɓai ya je? Ko kaduna ya je? Ya ce zai kirani amma shuru har na fito wanka ina wasi wasi. Daman na yo alwalata ana kiran isha’i na kabbarta salla bayan na idar ne na zo na zauna gaban madubi na tsantsara kwallya mai ƙayatarwa.
    Na gyara gashina na sake shi baya na yi ɗauri mai kyau ɗinki riga ds sikat ne sun kamani sun yi mini cif a jikina haka na yi ma kaina barin turaren humra ko’ina na gifta ina tashin kamshi na saka wani takalmina baƙi mai ɗan tsini kaɗan ina tafiya ya na ɗan ba da sauti kaɗan ƙwas! Ƙwas

    Falon yara na shiga na gansu sun yi kyau suma. Jidda ma ta ce” Umma kin yi kyau” na ce na gode sai na ja su muka yi ta ɗaukan hotuna sun ɗan yi ma duhu saboda dare tare muka zauna sun kunna cartoon ni kuma waya ce a hannuna ina ta kiran Yallaɓai wayarsa a kashe tun ina duba agogo ina saran dawowar Yallaɓai har na sare Baby ta gaji har ta fara barci ita kanta Jiddam ma barci ta ke ji.

    “Umma Abba bai dawo ba?

    “Yana kan hanya in sha Allahu.”

    Na faɗa mata cikin karfin hali. Tashi na yi na fara zagayen falon ina yi ina duba agogon wayata. Tara da rabi ta yi shuru sai hankalina ya tashi na fara tunanin ba lafiya goma na yi na ce bari na kira Nene na ji ko yana can ai kuma ya san da ina gida ina jiran shi.
    Na latso lambar Nene kenan zan kira sai kira ya shigo mini na ɗauka Yallaɓai ne jikina na rawa na koma na zauna sai dai kuma sunan wacce ke kira ne ya sa sai da gabana ya faɗi Ras! Haka kurum na ji kamar ba alheri ba ne ya sa ta yi min wannan kiran karfe goma na dare.

    “Ma’u ce.’

    Jikina sai ya kama rawa har ta katse ban ɗauka ba. A ƙoƙarina na kira Nene amma ba ta bari ba kawai sai ga wani kiranta ya ƙara shigowa cikin dauriya da shahada na ɗaga kiran

    “Ma’u.”

    Na faɗa kafin ma na yi mata sallama. Sai ta amsa mini cikin yanayin muryanta amma cikin farinciki.

    “Na’am Sadiyar Yallaɓai.”

    Yadda ta faɗi sunan ne sai na ji ban yarda da ita ba.
    Kafin na samu zarafin mgana ta cigaba da faɗin” Na san za ki ce kira cikin daren nan ko? .
    Da sauri na ce” E ina fatan lafiya.”
    Sai da ta yi wata irin dariya kafin ta ce” Lafiya sumul. Murna cika shekaru sha biyar da aure na kira na yi miki sannan tare da ba ki wani kyakyawan albishir.”

    Sai kawai na ji zuciyata ta tsinke amma sai na ɗaure cikin karfi hali na ce” Na gode. Ina jin ki wani albishir ne wannan da ba za ki iya jiran safe ba ki ka kira cikin daren nan?

    Tana dariyan nan na ta na mugunta ta ce” Ba na so wani ya rigani ne. Na fi so ki fara jin wannan albishir ɗin daga bakina.”
    Juyawa na yi sai na ga Jidda har ta fara barci daga kan kujera sai kawai na miƙe na buɗe kofar falon Yallaɓai na shiga na maida ƙofar na rufe a cikin duhun nan na lalubi kujeran dining na ja na zauna ina faɗin” Uhm ina jin ki Ma’u.”

    “Zan kashe wayata yanzu. amma ki kunna data ki hau whatspp na tura miki saƙo.”

    Ko kafin na ce wani abu ta kashe wayarta. Ni fa na gama sakankancewa daman ba alheri Ma’u za ta nuna min ba. Amman ban taɓa tunanin ganin abin da na gani ba. Jikina na rawa na buɗe data saƙonni na shigowa amma ba ta su na ke ba Ma’u na ke nema ina ko ganin ta tura mini abu kamar hoto na faɗa hannuna na rawa na danna sama yana buɗewa.
    Wallahi tallahi yana buɗewa ne amma kamar yana buɗewa da gudun numfashina ne. > Janaftybaby: Yana gama buɗewa na ji kirjina ya amsa. Kaina ya sara, hannunawana sun fara ƙarkawa saboda jikina da zuciyata suna rawa ne a lokaci ɗaya a lokacin idanuwana sun firfito ba domin na ji mamakin abin da na gani ba ne. Sai domin ban taɓa tsammacin shi a lokaci kusa haka ba. Ina wannan rawan jikin da na zuciyan kiran Ma’u ya sake shigowa ban ɗauka zan samu kuzarin ɗaukan wayarta ba amma sai gashi na ja na ɗauka na kuma ƙarata a kunnina duk da yadda zuciyata ke gudu da sauri da sauri.

    “Ina fatan kin ga irin kyakyawan albishirin ɗin da na ke so na gaya miki ko Sadiya?

    Runtse ido na yi zuciya na fat fat! Amma sai wata zuciyar ta ce Sadiya kar ki bari a ga gazawarki daman shi Ma’u take jira kamar an dake ni na dawo hayyacina sai na saki wani mirmishi wanda ya fi yin kuka daɗi na ce” Haba ai kin makaro Ma’u domin Yallaɓai ya riga ki yi mini wannan albishir ɗin’

    Shuru ta yi domin ni na san ta yi mamakin jin kalamaina. Ban bari ta ƙara mgana ba na ce” kin yi gaggawa Ma’u da kin jira da ni da kaina zan kira ki na faɗa miki Yallaɓai YA ƘARA AURE”

    Ban ƙara ba ta wata damar mgana ba na cigaba da faɗin” Walimar da na shiryama ma a gida saboda Anniversary ɗin mu ne da kuma taya shi Murnan ƙaruwan da ya samu na aure.”

    Ina gama faɗin haka kit na kashe wayar saboda sai na ji kamar santsi na ja na ina shirin na sumulmiyo daga kan kujeran da na ke zaune. Sai na kama jikin kujeran da hannuna ɗaya na ƙanƙame jikina ba inda ba ya rawa. Zuciya ta da tunanina sun tsaya waje ɗaya cak na kasa yin ma wani tunani. Ji na ke yi kamar ina zaune ne amma jiri na ke gani shi ya sa na ƙamƙame kujeran da na ke zaune amma ban san lokacin da na ji na sulmiyo ƙasa ba. Sai ga ni zaune a kan mazaunaina a ƙasan tayel ina kokawa da numfashina wayata ta yi zaman dirshan a kan jikina na saka hannunawa da suke rawa na ɗauka na buɗe na koma whatpps na shiga kan sunan Ma’u ina kallon hoton da ta tura mini sai a lokacin na lura da in da Ma’u ta ga hoton.

    Sunan Anty Bahijja ne a saman sreenshoot ɗin da ta yi, sannan hoton na GIMBIYA CE(SAUDATU) tsohon hotona kamar ma a gidanta na Abuja ne kafin mijinta ya rasu. Tana tsaye a falon gidanta a lokacin ta na mirmishi ta saka wata doguwar riga ne a hoton. Abin da ya fi ɗaukan hankalina shi ne kalaman da aka yi amfani dashi a ƙasan hoton.

    “Allahu Akbar alƙawarin Allah ya tabbata. Congratulation Mrs Yusuf Muhammad(Tafida).”

    An ce wai ka yi ma hawaye rahama ne. Sai yanzu na amince da wannan mganar, na kasa jin kuka ya taho mini ma idanuwana sun ƙeƙashe.
    Shi kenan ta faru ta ƙare an yi ma mai dami ɗaya sata. Daman shi ne suprise da Yallaɓai ya ke ta faɗin zai ba ni? Lalle ko na karɓi kyakyawan suprise.
    Ban san lokacin da ya shigo gidan ba domin ban ji ƙaran buɗe get da shigowar motar sa ba ba. Sai da na ji lokacin da ya ke saka ɗan makulli yana ƙoƙarin buɗe kofar falon kamar an jani an mikar dani tsaye sai ga ni a tsaye a kan kafafuna. Wayata kuma tana jimƙe a hannuna. Ya buɗe kofar kenan ya shigo ni kuma sai na fara takawa ƙwas ƙwas ina ji jikina na rawa amma na daure na isa ga makunnin wuta na kunna dai dai yana ƙoƙarin ciro wayarsa daga aljihu domin haska fitila.

    Haske ya gauraye falon. Ya bi ko’ina da kallo dai dai lokacin kuma wasu daga cikin bloons ɗin da na saka afalon suka fashe ji ka ke yi tus! Tus! Sai da ya ɗan waiga sannan ya juyo yana sauke kallon shi a kaina dai dai ni kuma ina tsaye a gaban shi na harɗe hannayena a bayana.
    Na ƙasa takawa zuwa gare shi, saboda sai na ga kamar ba Yallaɓaina bane kamar wani ne wanda ban saba dashi ba, sai na ke jin kamar wannan Yallaɓan yanzu akwai wata tazara da ya shimfiɗa a tsakanimu daga yau.

    Kafafuna sun yi sanyi kamar gara ya kama su in na ce zan cire ƙafa zan iya zubewa saboda firgici.
    Shi ma sai na ga ya tsaya yana kallona amma kuma bai tsawaita ba da sauri ya kauda kanshi. Mirmishi ya ke gayyato ma fuskarshi sai dai ban bari ya gayyato ma kanshi ba ni na fara gayyato ma kaina mirmishi lokaci ɗaya ina faɗin.

    “HAPPY 15 YEARS WEDDING ANNIVERSARY YUSUF MUHAMMAD TAFIDA.” > Janaftybaby: Na faɗa ina kallon ƙwayar idanuwanshi. Yadda ban je gare shi domin na rumgume shi ba. Shima bai yi saurin takowa gare ni ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana mai ijiye ledojin da ya shigo da su a hannun shi a ƙasa wanda ban san abin da ke ciki ba.
    Kafin ya ɗago kansa cikin ƙwayar idanuwanshi na ga rauni. Kasala tsoro da wani abu da na kasa ganewa. A kuma yanayin ya kira sunana cikin wata irin muryan da ban taɓa sanin Yallaɓai na da ita ba.

    “HALIMA.”

    Zan iya kirga sau nawa Yallaɓai ya taɓa kirana da sunana Halima, a da in ya kirani ina jin kaina ya yi girma. Amma ban da yau domin sai na ji kamar ya kwarara min ruwan zafin a cikin jikina. Har ina jin tururunshi da hucin shi daga fatar jikina. Sai na ji kamar komai yana sauyawa kamar duk wata kyakyawan alaqan da muka gina ta tare da Yallaɓai tana zangayewa tana komawa ruwa. Kamar kuma ruwan ya fara zuba a ƙasa ya na kwarara da ƙarfin gaske wanda daga ni har shi ba za mu iya tare shi ba.

    *Ƙarshen littafi na Ɗaya*

    Note
    error: Content is protected !!