Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Gidanmu na nan a farko layin shiga anguwar Ɗorayi. Yanayin fasalin gidan babba ne sannan tun daga waje za ka fahimci tsarin gidan na tsohon ɗan boko ne.
    Domin Alhajinmu kafin ya yi Ritire(Ritaya) sai da ya riƙe mukamin babban darakta na kamfanin wuta na jihar kano(KEDCO). Bayan kasancewarsa manomi. Kuma gidanmu na da ga cikin rukunun gidajen da suka daɗe a anguwar tun da sama da shekara ashirin duk da ko mu kanmu muna da wayau lokacin da muka dawo gidan tun a wancan lokacin zamani na kwance. Sai dai yanzu lokaci bayan lokaci yana samun ƴan gyare gyare da kwaskwarima daga su Yaya Hamza.

    Ni na fara fitowa daga Motar. Yallaɓai na kuma an kira wayarsa ya tsaya a mota ya na mgana.
    Kofar gidan namu tar da hasken wuta gabaɗaya ma anguwa akwai hasken ƙwakwayen da suke kofar gidajen wasu mutane dake cikin rukunin anguwan ta Ɗorayi.

    Gidanmu na ke kallo ina tuna wasu shuɗaɗɗun al’amura da suka faru damu a cikin gidan masu daɗi da akasin su. Yallaɓai ne ya katse min tunani da cewa” Kin ga ko na manta ɗazu musabahu ya zo offishina ya bani saƙo ya ce in ji Yaya Muntari mijin Rahila.”

    Sai a lokacin na ɗago ina kallonsa ya fito daga mota ya na nuna min kullin abu a baƙar leda, yadda ya ga na taɓe baki ya sa ya san tabban nasan da saƙon.

    “Bar shi a motan kawai.”

    Bai yi musu ba sai ya koma cikin motar, ina hangensa daga waje ya buɗe akwatin motar ya jefa sannan ya fito yana ƙoƙarin rufe motar hasken wata mota da ke tunkaromu ta kashe mana ido daga ni har shi sai da muka saka hannuwammu muka kare fuskokin mu dashi.

    “Kai. Waye wannan da ba zai rage filita tunda ya shigo cikin anguwa ba.”

    Na kasa magana ne saboda mamakin ganin motar ba wucewa ta yi ba, kusa damu itama ta gyara parking, tun kafin ma na ciki su fito na shaida su waye tun daga cikin motar akwai hasken fitila.

    “Ma’u ce..”

    Haka na faɗa a cikin raina dai dai san da ta buɗe murfin mota ta fito shima mijinta ya fito daga can bangaren direba.

    “Alhaji Mustapha ne, da Ma’u ashe.”

    Yusuf ya faɗa ya na sakin mirmishi, na kalle shi wani abu ya yi mini tsaye a zuciyata. Lalle Alhajinmu wato zaman yau bayan ni da Ma’u har da gayyar mazajen mu kenan?

    Kara haɗe rai na yi, ganin Ma’u na nufoni shi kuma Yusuf ya nufi Alhaji Mustaphan shi adole ya ga ɗan’uwan mijin yayarsa. Ƙaramin tsaki na ja dai dai lokacin da Ma’u ta ƙariso kusa da ni ta na faɗin”Sadiya kema Alhajinmu ya kira ku ne ke da Injiniya?

    Ta faɗa lokaci ɗaya ta na ɗora hannunta saman kafaɗata. Sai na ji kamar ta ɗora min cuta da sauri na kauce ina yi mata wani irin kallon ke ki kiyayeni. Ita kuma ta na bi na da wannan munafukin mirmishin nata na yaudara.

    Ƙoƙarin sake matsowa kusa da ni take tana yi min mirmishinta da ba alheri a cikin sa. Tsaki na ja mai karfi na juyawa na fara tafiya zuwa ƙofar da za ta sada ni da cikin gidanmu na ji muryan Ma’u da ɗan karfi ta na faɗin”Haba Sadiya. Ke shike nan abu ba ya wucewa a wajen ki? Na yi ta ba ki haƙuri fa?

    Sai da na kai kofar gidan sai na juya ina kallonta sai na ga har su Yusuf ma sun dawo da hankalunsu kan mu, dariyan gefen ba ki na yi. Ni ai sai dai na rubuta littafi guda akan maƙircin Ma’u daman ta yi ne domin hankulansu ya dawo kan mu, shigewata cikin gida na yi ina ji Yusuf na kiran sunana na yi masa banza na yi shigewata na bar su nan ƙofar gida.

    Dogon korido ne mai ɗauke da ɗakuna uku na waje, biyu suna rufe ne sai guda ɗaya ne a buɗe. A raina na ce kila Datti ya zo gida ko kuma an yi baƙin maza daga Yashe ko Yan tumaki.
    Ban gama mamaki ba sai ga Datti ya fito daga cikin gida sai muka ci karo da juna.

    “Datti..”

    Na kira sunan shi, sai ya kalleni domin fitowarsa daman hankalinsa na kan wayar hannunsa. Daga shi sai baƙin wando da farar singileti.

    “Yaya Sadiya? A daran nan?

    Ya faɗa yana kallona, jiyo muryoyinsu Yusuf suna ƙokarin shigowa ya sa na raɓa ta gefensa na wuce, ina jin sa ya na tambaya ta. > Janaftybaby: “Ke kaɗai kika zo? Ina Yallaɓan da su Jidda?

    Ko juyowa ban yi na faɗa tsakar gidanmu da sallama. Gwaggo na Madafi na kuma nasan shayi ta ke dafama Alhajinmu da tun tasowarmu nasan ba ya iya barci sai ya sha wannan ruwan zafi. Ita ta amsa min sallamata tana kuma leƙowa muka ci karo da juna tsakar gidan tar yake da hasken gulop.

    “Maraba da Hajiya Dubu.”

    Sai na sa ki mirmishi ina faɗin”Kai Gwaggo ni dai wannan tsohuwar ta mutu ba ta bar mini gadon komai ba sai na sunan ta.”
    Gwaggo na dariya ta ce”Ka ji min ƴar nema. Ai ko ita ta bar miki gado tunda ta bar miki gadon suna mai daraja irin Halimatussadiya.”

    Ya na iya?. Domin in dai Gwaggo ce ta riƙa sharhin sunan kenan da kawo tarihi. Gaisheta na yi cikin girmawa ta amsa ta na faɗin”Na gan ki ke kaɗai ina shi Yusufan?
    Na rausayar da kai kafin na ce”Ga shi nan shigowa.”

    “Oh. To ina yaran suke? Ko can gida kuka baro su?

    Ban amsa mata tambayarta ba. Sai na bige da faɗin”Alhajinmu na ciki ne Gwaggo?
    Na faɗa ina kallon ƙofar falon shi da na hangi hasken wuta.

    “E. ya na ciki tun ɗazu ya dawo. Zaman jiran ku yake yi. Domin nima sai yanzu ya ke yi min taɗin kuna tafe ke da Ma’u”

    Ta na dire maganarta sai ga sallamar Ma’un ban tsaya ba ni kuma na kara sauri zuwa falon Alhajinmu.
    Da nesa kaɗan dashi ɗakin Gwaggo ne shima akwai hasken wuta daga cikin ɗakin, kusa da shi kuma ɗakin Mama ce a sakaye, daman in dai ba mu ne muka zo gida ba, ɗakin Mama yana yini a sakaye ne
    Ɗakin na kallah ta window ya yi duhu alamun an kashe hasken ɗakin gabaɗaya ƙwallah suka taho min na yi saurin shanyewa amman a fili sai da na furta” Allah ya yi miki Rahama Mama.”

    Lokaci ɗaya na cire takalmina akofar ɗakin Alhajinmu na shiga da sallama a bakina.

    Alhaji Sulaiman Abubakar Yashe(Alhajinmu) na zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu cikin jerin kujerun da suka yi ma falon kwanya. Falon da na girma sosai shi ya sa sai kujerun suka zama a can tsakiya.
    Alhajinmu ba tsoho ba ne, ko na ce yanayin jikinsa na ɓoye shekarunsa. Ya mori jiki saboda bashi da kiɓa tun zamanin samartakansa har kuma girmansa. Dattijo ne wankan tarwaɗa, mai matsaikacin faɗin fuska da furfura ta gama zagayewa. A shekarunsa zai iya haura 65 amman kuma ba zai ga za 67 ba.

    Cikin yanayin maganarsa da zafin murya irin ta Alhajinmu ya amsa min sallamata.

    “Amin wa’alaikis salam. Dubu ce tafe?

    Sai da na ƙarisa gabansa na zauna ina faɗin”Ni ce Alhajinmu barka da dare.”
    Yana yar dariyansu ta manya ya ce”Barkan mu dai. Yana ganki ne kaɗai ko Yusufan ya na waje ne?

    Ko kafin na samu zarafin magana Ma’u ta yo sallama ta shigo bayan ta kuma mijinta ne Alhaji mustapha da Yallaɓaina Injiniya Yusuf.

    Itama gaban Alhajin ta zo ta zube ta na gaishe shi, ni dai na matsa can gefe na jingina da kujera suma su Yusuf nan kasan cafet ɗin da ya malale ɗakin suka samu mazaunin zama cikin girmamawa suna gaishe da Alhajinmu ya amsa cikin sakewa da dattako, sai ya karkata kansu yana tambayan su aikinsu da sauran harkoki.

    Ni kuma kaina sai na dukar da kaina ina duba wayata ganin har tara na dare ta gota da kaɗan. Ita kuma Ma’u sai ta tankwashe kafa kamar mutuniyar kirki kanta na ƙasa ban san abin da ta ke yi ba.

    Shigowar Gwaggo ɗakin dauke da shayin Alhaji ya katse hiran ta su, ta miƙa masa a wani ƙaramin mug ya karɓa ya na faɗin”Na gode Maimuna. Allah ya yi albarka”
    Ta amsa da Amin. Sannan ta juya suna gaisawa da su Yusuf tunda da suka shigo ta ce su shiga itama ga ta nan zuwa.

    “Ma’u ya gida ya yara? Ina su Alhaji karami?

    Gwaggo ta faɗa ta na kallon Ma’u. Ita kuma sai ta ɗago ta na faɗin” Lafiyan su lau Gwaggo na baro su gida tare da Zainab”

    Gwaggo ba ta yi shuru ba sai ta kara cewa” Ya gajiyan ku? Kun sha suna. ke ce kawai daman da Sadiya ba ku biyo ta nan ba ranar sunan”
    Gum na yi da bakina saboda daman in dai Ma’u na magana ba na saka baki, can na ji ta na ce ma Gwaggo wai mun yi dare ne shi ya sa ba mu biyo ta gidan ba.

    Shi kuma Alhajinmu sai da ya yi rabin da shan shayinsa sannan ya kalli su Yusuf ya na faɗin”Ban yi muku ta yi ba, ko Maimuna ta haɗa muku shayin ne? > Janaftybaby: Alhaji Mustapha ne ya yi saurin cewa” Mun gode Alhaji.”
    Yusuf dai bai yi magana ba saboda na ji an kira wayarsa bai ɗauka ba ina jin sai ya sakata a silet.

    Ficewa Gwaggo ta yi daga Falon zuwa ɗakinta. Ta bar mu daga mu sai Alhajinmu sai da ya gama shan shayinsa sannan ya kalleni yana faɗin”Dubu kai kofin can madafi”

    Ya faɗa yana mika min mug ɗin hannun shi da ya gama shan tea, sai na miƙe da sauri na karɓa na fita zuwa tsakar gida na tura kofar madafin tun da har Gwaggo ta sakaya ban ijiye ba sai na diɓi ruwa a katon botoki mai murfin ɗin dake cikin madafin na tara a sink na wanke shi, tunda madafin gidanmu ya daɗe da komawa na zamani na kife kofin saman cabinet ɗin kitchen ɗin sannan na fito na sakaya shi kamar yadda na ga Gwaggo ta yi.

    In da na tashi nan na koma na zauna. Sai sannan Alhajimu ya gyara zama ya na sanye da jallabiya mai ruwan madara kansa ba Hula sai furfuran da suka masa kwanya daga kansa suwa gemunsa da sajensa.

    “Ma sha Allah, na ji daɗin yadda bayan na kira ku kuka amsa kirana. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya.”

    Muka amsa da Amin gabaɗayanmu. Alhajinmu ya kalleni sai ya kira sunana da sai irin haka mgana mai muhimmanci ya ke kiran sunana bayan Dubun da yan kirani.

    “Halima..”

    Sai na ɗago na kalle shi lokaci ɗaya ina mai amsawa.

    “Na’am Alhajinmu.”

    Sai ya karkata kan Ma’u itama ya kira sunanta.

    “Asma’u..”

    Itama ta amsa da na’am Alhajinmu
    Sai ya cigaba da faɗin” Kusan dalilin da ya sa na ce ina son ganin ku wannan karon tare da mazajen ku?
    Dukkanmu muka girgizanmu kanmu kafin mu haɗa baki wajen faɗin”A’a Alhajinmu.”

    Kai ya gyaɗa kai kafin ya ce”To ba saboda komai ba ne sai dalilin bayan ni kuna da wasu shugabbanin da in kuka yi ba dai dai ba, za su iya yi muku faɗa akan ku gyara kamar yadda ni zan yi muku. Mazajen ku su ne alhakin duka rayuwarku da tarbiyansu yake hannunsu bayan na aura musu ku, shi ya sa wannan karon ganin wannan rigimar da sheɗan ya ba da gudummuwa wajen gina ta a tsakaninku da ta ƙi ci ta ƙi karewa na yi tunanin saka mazajen ku a ciki, saboda ba na so na faɗi na mutu a zaman makokina ke Sadiya da ke Asma’u a ce bakwa yi ma juna mgana akan abin da bai kai ya kawo ba.”

    Sai ya dakata ya na nazarin mu, dukkanmu kan mu na ƙasa ba wacce ma ta ɗago. Sai ya karkata hankalinshi zuwa ga mazajen mu.

    “Yusufa.

    Cikin ladabi ya ce”Na’am Alhaji”

    “Mustapha.”

    Shima cikin ladabi ya amsa da Na’am Alhaji.

    Sai Alhajnmu ya gyara zama ya na faɗin”Ban sani ba ko kun taɓa sanin tsakanin matayen ku ba a ga maciji? Ma’ana ba sa haɗuwa waje ɗaya su yi rabuwan lafiya? Wataƙila za ku iya fahimtar ba sa shiri da juna amman na san ba su taɓa zama sun warware muku lamarin yadda za ku fahimta ba.

    Wannan karon Alhaji Mustapha ya fara faɗin” Haka ne Alhaji. Ban dai san me ya ke haɗa su ba amman Sadiya ba ta zuwa gidana sannan ko haɗuwa muka yi ni da ita in dai ba ni na yi mata mgana ba. Ba za ta yi mini ba, na taɓa tambayan Ma’u ko akwai wani abu a tsakaninta da Sadiya ne amman ba ta ce komai ba”

    Ya karishe faɗa yana kallona, nima ko na ɗago muka kalli juna na kauda kaina domin ba ƙarya ya faɗa ba mun sha haɗuwa da shi gidan Anty Bahijja sai na yi kamar ban gan shi ba in har bashi ya yi mini mgana ba.

    “Kai fa Yusufa? Ka taɓa fahimtar wani abu?

    Cikin girmamawa ya ce”E. Na fahimci ba shiri tsakaninsu. Amman na ɗauka faɗa ne kawai na ƴan’uwa ba mai tsananin da zai haifar da matsala ba ne Alhaji.”

    Alhajinmu sai ya sauke numfashi kafin ya ce”Kowa ma haka ya ɗauka daga farko farko. Amman suna ƙara girma lamarin na su na ci gaba, tun suna yara har suka girma na aurar da su gare ku, suka hayayyafa suka zama iyaye sun tashi daga yara sun koma uwaye waɗanda ba zan ce ba su san ciwon kansu ba. Sun sa ni tunda Tarbiya ne ma a ƙarƙashin ikon su, daga lokacin ne na fara fahimtar lamarin ya wuce tunanin zai tsaya anan ina tsoron kada su mutu su bar ƴaƴansu cikin muguwar gaban da sheɗan ya kulla a tsakanin su.” > Janaftybaby: Dalon sai ya yi shuru, Alhajinmu kuma bayan ya yi shuru na wani lokaci kafin ya cigaba da faɗin”Ba yau ne na saba sulhu tsakanin Halima da Asma’u ba, tun yan’uwansu na yi musu ban sani ba har ya fi karfinsu suka dangana da ni, na yi nasihan da ban baki sai sun ce sun bari amman ba a daɗewa sai an zo an faɗa mini sun haɗu kuma sun yi faɗa. Wannan zaman saboda dalilin faɗan ne da suka haɗu shekaranjiya a gidan sunan ƴar Rahila. Murja ta zo har gida nan ta na faɗa mini a gaban mutane ke Halima kika yi ta ma yar uwanki ɗiban albarka, ita kuma an ce Asma’u haƙuri take ba ma Sadiya amman dai sun sanar dani faɗan dalilin ita ƙawar Asma’un ce da ta je sunan ƴar Rahilan”

    Yusuf ya ce”Subhanallah”
    Shi kuma Alhaji Mustpha ya kaɗa kai kafin ya ce”Asha. Abu bai yi daɗi ba.”

    Ni ko kaina na ƙasa a raina ina mamakin Yaya Murja, ko miye riban ta na zuwa ta karantama Alhaji komai?

    “Wannan dalilin ya sa na ce zan saka ku a ciki. Gani ga ku zan tambayesu ɗaya bayan ɗaya menene haƙikanin matsalansu da ko da yaushe suka haɗu sai sun yi faɗa? Ko sun manta su ƴan uwan juna ne dangi ɗaya? Ko ke Sadiya kin manta matsayin Asma’u a gare ki ne? Ko ke Asma’u kin manta matsayin Sadiya a gare ki ne?

    Ya ƙarishe faɗa ya na bin mu da kallo, kowaccen mu ta kasa ɗagowa saboda nauyin idanuwan Alhaji a kan mu.

    “Ke Sadiya ke ce Babba da ke zan fara. Ɗago ki kalle ni”

    Ba ni da mafita illa ɗago kaina ina kallon Alhajinmu cikin muryansa a kaushashe da ɓacin rai ya ce”Halima na san halin ki, kina da tsiwa da mgana sannan ke ce daman ko faɗa aka yi dake ko an yi sulhu ba kya hakura ki yi ta gaba saboda daman gaba ba ta yi miki wahala. Ki faɗa mini gani ga Asma’u da mijinki wani irin abu ne Ma’u take yi da ba ki so? Ki faɗa mana sai ta ji ta ba ƙi hakuri ta kuma ɗauki alkwarin za ta daina yi miki saboda ku samu zaman lafiya”

    Shuru na yi na wani lokaci kafin na ce”Alhajinmu ba fa ni kaɗai na tsani Ma’u ba. Itama ta tsane ni tun zuwanta gidan nan ba ta sona nima ba zan maka ƙarya ba ba na sonta Alhaji. In kuma ana son a samu zaman lafiya to Ma’u ta daina bin hanyata ni daman ba ta gabana domin na fi ƙarfinta Alhajinmu ka raba tsakanina da Ma’u don girman Allah.”

    Na karishe faɗa har ina haɗa hannu alamun roƙo, gabaɗaya ni suke kallo har Ma’u sai kawai na ga ta fashe da kuka, ban ko razana ba domin kaɗan daga cikin makircin Ma’u kenan.

    Yusuf kuma ni ya ke kallona, saboda ya san halina ina da taurin kai, in na kuma ce na tsani abu to da gaske na ke yi ba na son shi.

    “Innalillahi ni ko Sadiya me na taɓa miki a rayuwa da kika tsane ni haka?

    Kai tsaye na ce” Ban sani ba. Ke za a tambaya abin da na yi miki kika bi kika addabi rayuwata kina yi mino bita da kulli a wajen iyayena da ƴan’uwana wannan bai isheki ba kin fara yi min ta bangaren dangina mijina wannan bai isheki ba sai kin je kina yamaɗiɗi da ni cewa planning na yi shi yasa har yanzu na ke neman haihuwa ido rufe ban samu ba, har wannan matsiyaciyar ƙawar na ki ta kalli tsabar ido na tana gaya mini mgana.”

    Na ƙarishe faɗa cikin tsawa domin nima raina ya ɓaci. Tuna abin da ya faru da a gidan Rahila kaɗai kan haifar mini da ƙuncin zuciya.

    Daga Alhajinmu har su Yusuf shuru kawai suka yi suna kallon mu. Ma’u ta na kuka ƙaryan da ta saba na yaudaran mutane ta fara rantsuwa ta na faɗin” Wallahi tallahi in kin yarda dani Sadiya ban san a ina Shema’u ta ji wannan labarin kuma, a gabanki na yi mata mganar ban ji daɗin abin da ta yi ba, saboda haka ya sa ko yau ta zo gida ta na faman bani haƙuri ban saurareta ba. Har a waya tana ta kirana ban ɗauka ba domin na faɗa mata ba ke ta tozarta ba ni ta tozarta domin abin da ya yi ki shi ya yi ni Sadiya da ni da ke bamu da bambamci”

    Ta ƙarishe faɗa tana shesshekan kuka sai kuma ta kalli Alhaji tana cigaba da faɗin”Alhaji wallahi Allah ɗaya kenan ba ni da wani mugun nufi kan Sadiya. Ina son ta kamar yadda na ke kaunar yar uwata Zainab, ina son ta ƙwatankwacin yadda nake son su Rahila. > Janaftybaby: Amman ban san me ya sa Sadiya ta kasa fahimtata ba, Alhajinmu ko rashin fahimtar da ta faru a baya ta maganar aurena da Yaya Hamza tabbas raina ya ɓaci kuma na ji haushin Sadiya amman har ga Allah daga baya na cire abin a raina ban taɓa kallon Sadiya dashi ba. Ni ko me ya sa zan yi haka? Alhaji Sadiya ce ba ta sona ban kuma san me na yi mata ta tsane ni ba tana hulɗa da kowa Alhaji ban da ni in dai abu ya shafe ni Sadiya tsame hannunta ta ke yi a ciki ba ta zuwa gidana ni in na je wallahi ko bare Sadiya ba ta yi masu abin da ta ke yi mini, in muka haɗu a gida ko gidajen ƴan’uwa Alhaji ko na yi ma Sadiya magana ba ta yi mini ta yi ta gaba da ni. Na zauna ta yi ta tunanin abin da na yi ma Sadiya ta tsane ni amman na kasa ganewa, daga baya sai na fara tunanin ƙila saboda Alhaji ka ɗauke ni ka sanyani cikin Iyalanka ne, ita kuma Sadiya ba ta so wani daga waje ya raɓe ta, sai kuma daga baya na kwaɓi kaina da cewa ai ni ba bare ba ce Alhajinmu ni ma ƴarka ce kamar Sadiya”

    Ta faɗa har ta na riƙe kafar Alhaji, tana kuka, gabaɗaya na san ta gama cika zuciyar Alhaji da tausasa kalamanta.
    Ni ko a raina ban ji na yi nadama ba, kallonta na ke yi ina mamakinta har ta manta mganganun da ta gaya mini a lokacin da aka fasa auranta da Yaya Hamza? Har ta manta?

    “Tashi. Tashi Asma’u. Ke kam ba bare ba ce ke ƴa ce kamar Sadiya. Ta shi daina kuka kin ji bari kuka nan”

    Ya faɗa cikin sigan lallashi, Alhaji Mustapha har da mika mata wani farin hanky, ya na faɗin”Ki share hawayen ki Ma’u”
    Ba wanda ya fi baƙanta min rai irin Yusuf har da shi a masu ba ma Ma’u hakuri daman halinta ne ta shirya makirci a raja’a a kanta.

    Tsaki na ja mai ƙara kafin na ce” Ke dai Ma’u wallahi an yi baƙar munafuka kuma makira, ke wai kina kuka saboda ki zama abin yarda ni kuma na zama victim kamar ko yaushe ko? Har kin manta? Har kin manta maganar da kika faɗa mini lokacin da aka rushe maganar auran ki da Yaya Hamza? Na ce kin manta? To wallahi kamar yadda baki ƙaunata nima abada ba..’

    “HALIMA…”

    Alhajinmu ya katseni tare da kiran sunana a tsawa ce, ban kalle shi ba na cigaba da faɗin”Alhajinmu cewa ta yi fa sai ta rama abin na yi mata sai ta kun samini kwatankwacin baƙin cikin da na kunsa mata kuma..”

    “Na ce ya isa ko Halima? Ko so kike yi na saɓa miki?

    Alhaji ya faɗa ransa ɓace, sai na yi sansarai rai, ganin ya koma ya ba ma Ma’u haƙuri tana shessheƙan kuka.
    Baƙin ciki da ya tokare mini zuciya ya ta so mini ba kasafai na ke kuka kan abu ba amman daman Ma’u ta saba cin nasara a kaina akan kowa ko da yaushe ni ce victim ita kuma mai gaskiya.

    Ban san nima na fashe da kuka ba, sai kawai na miƙe zan fita daga falon ina faɗin” Shike nan ai daman ita mai gaskiya ce ita ce ba ta laifi ni ce fitananniya. Alhajinmu ni fa ƴar ka ce Ma’u fa? Bai kai kamar ni da ka haifa da gudan jinin ka ba.”

    “Ke ke Sadiya ina za ki je?

    Alhajinmu ya fada saboda na juya ina kuka zan fita ne.

    “Wallahi zan saɓa miki in kika fita Halima.”

    Shi ya sa na fasa fita amman sai na coge a tsaye ina sharan kwalla. Ran Alhaji ya ɓaci ya ɗaga murya ya na kiran sunan Gwaggo.

    Sai gata ta shigo da sauri ta na sanye da Hijabi a jikinta. Gani na tsaye ina goge idanuwana sannan ga Ma’u na ta shesshekan kuka Alhajinmu na faman ba ta haƙuri.

    Cikin mamaki da damuwa a saman fuskarta har kuma ya bayanna a muryanta ta ce”Subhanallah. Alhaji lafiya? Me ya faru ne?
    Duk da ta san dalilin zaman amman shi dailin koken koken namu ne ba ta sani ba.

    Yusuf ne ya tashi daga in da ya ke zai iso in da na ke tsaye amman Alhajinmu sai ya dakatar dashi.

    “Dawo ka yi zaman ka Yusufa ƙyaleni da ita.”

    Sai ya koma ya zauna a inda ya tashi amman gabaɗaya hankalinsa na kaina kamar yadda hankalin Alhaji Mustapha ke kan matarsa.

    “Taho min da Halima nan gaba na Maimuna.”

    Umarnin da Alhajinmu ya ba ma Gwaggo kenan sai ta riƙo ni lokaci ɗaya ta na faɗin” Mu je Sadiya. Mu je Alhaji na kiran ki.”

    Ban isa na yi musu ba sai na bita har gaban Alhaji ta kuma zaunar da ni a gabansa a kuma in da na tashi, jan majina na ke yi ina ƙokarin shanye takaicina. > Janaftybaby: Gwaggo ta kalli Alhajinmu kafin ta ce”Daga sulhun ne suka fara koke koke kuma Alhaji?

    Bai amsa mata tambayarta ba, sai ma kallonta da ya yi kafin ya ce” Samu waje ki zama, saboda abin da zan faɗa ina so kema ki zama shaida.”

    Sai Gwaggo ta koma ta zauna a kujeran mai zaman mutum biyu dai dai lokacin da ta ke kallon Ma’u wacce ke ta faman tsane hawayenta da hanky ɗin da ke hannunta. Sannan lokaci ɗaya ta na cigaba da shessheƙan kukanta.

    “Ke ma Ma’u ki bar kukan ya isa haka nan.”

    Ta fada cikin wani yanayi, a cikin ranta tana tunanin komai Alhaji zai yi ba za a taɓa samun daidaito ta bangaran Ma’u da Sadiya ba.

    “Halima..”

    Kamar daga sama na ji Alhajinmu ya kira sunana a kausashe kuma da karfi jikina da zuciyata suna rawa na ɗaga kai ina kallonsa cikin ɓacin ran da ya bayyana har a saman fuskarsa na ga ya nuna ni da yatsar sa manuniya da ya hana ni ma iya amsa masa kiran sunana da ya yi.

    “Yau ce rana ta farko kuma ta karshe da zan ji ƙin ƙara kiran Ma’u da bare, yau ce rana ta ƙarshe da za ki ƙara yi mata kallon wata ba ƴar uwanki ba. Na san halin ki saboda ni na haifeki da gaske ki na da fitina da rashin haƙuri sannan ba ki da yafiya da barin abu ya wuce, sannan kina da nacin faɗa, kowa sai ya manta amman ke zuciyarki ba ta iya mantuwa. “

    Ya ƙarishe faɗa da karfi, kamar zai kai mini duka daman Alhajinmu akwai faɗa in ran shi ya ɓaci. Kuma ka da ka ba ri faɗan shi ya faɗo ta kanka domin ba za ka taba jin daɗi ba.

    Shi ya sa na ji zuciyata ta karye na fara kuka, kenan har a yau ma Ma’u ce za ta sake yin nasara a kaina?

    “Kar na kuskura na kara jin kin danganta Ma’u da bare, ita ba bare ba ce. Jinin ki ce domin in aka tsaga jininta za a ga na ki jinin haka itama in aka tsaka na ta jinin za a ga naki, bari na tunasar da ke abin da nasan ba ki manta ba, ni na saki nono mahaifiyar Asma’u ta kama Asiya ƙanwata ce uwa ɗaya uba ɗaya. Me ya sa kike da tunanin banza ne? Me ta yi miki? Tana bin ki amman kina ƙara nuna mata tsana? Ina ce har hakuri Murja ta ce ta yi ta ba ki kika tafi kina ta cin mutumci? Ke sheɗan ce da ba ki jin bari Halima ko so kike ki zama sheɗaniya a cikin mutane?

    Kuka kawai na ke yi, wannan karon kukan da na ke yi ya fi na wanda Ma’u ta yi fidda amon sauti, falon ya yi tsit sai tashin faɗan Alhaji kawai ake ji har Gwaggo tana zaune ne amman ba ta iya dakatar da Alhaji ba.

    Ma’u ce ta ɗago kanta tana kallon Alhaji kafin ta ce” Alhajinmu har a waya na kira ta bata ɗauka ba sai na yi mata saƙon murya ta WhatApps bari ma ka ji.”
    Nan da nan ta ɗauko wayarta ta shiga ta duba sai ga shi ta kunna muryanta tarwai ta na fadin”Ki yi hakuri Sadiya da abin da Shema’u ta yi miki. Har ga Allah ban san a ina ji maganar ba. Na nuna mata ban ji daɗi ba na kuma ce sai ta ba ki hakuri saboda haka zan tura mata lambarki sai ta kira ki ta baki hakuri.”

    Alhajinmu ya girgiza kai kafin ya kalleni ya na faɗin”Ta yi ta ba ki hakuri akan laifin da ba ita ta yi miki ba amman kin kasa hakura. Tabbas na fahimce ke ce sheɗaniya sannan ke ce ke hassada duk abun da ke faruwa.”

    Ina rawan muryan kuka na kwashi rantsuwa ina faɗin”Wallahi Alhajinmu…”

    “Rufe min ba ki, ki kuma tsaya dakyau ki saurareni. Ga uwarki nan ta zama shaida ga mijin ki nan ya zama shaida, daga yau ina mai ba ki umarni a matsayina na mahaifinki, ki ijiye duk abin da ke cikin ranki game da Asma’u ki rumgumi ƴar uwarki. Sannan ki yi zumunci da ita ki je gidanta in abin farinciki ya same ta ki taya ta murna. Sannan ki je a lokacin jaje domin ki ta ya ta jimami. Sannan in ku ka haɗu ke za ki fara yi mata magana, ki bi ta a inda ta ke ku gaisa cikin zumunci da ƙaunar juna. Gargaɗi na ƙarshe a gareki shine ki bi umarnina ya zama wannan shi ne zama na ƙarshe da zan yi a kan wannan mganar, na ƙara faɗa miki ki yarda makaman yaƙin ki ki bi Asma’u sannan ki yi zumunci da ita, in kika saɓa ma ko ɗaya daga cikin umarnina zan yi fushi da ke fushi mai tsananin da ba ki taɓa tsammani ba Halima. Saboda haka in kina so ki rabauta har a ranar gobe ƙiyama ki yi gaggawan bin umarnin da na ba ki.” > Janaftybaby: Alhajinmu na mgana ina jin kamar zuciyata za ta faso ƙirjina ta fito tsabar baƙin ciki tuni kukana ya ɗauke. Saboda ban ga amfanin ina zauna ina kuka saboda Ma’u. Na yarda ta yi nasara a kaina kamar ko yaushe.

    Muryanta na rawa na ce”Na ji Alhaji in sha Allahu zan zama mai bin Umarnin ka.”
    Na faɗa ina sauke numfashi saboda na ji kamar numfashina na shirin kwacewa.

    Alhajinmu ya gyaɗa kai kafin ya ce” Kin yi kyan kai. Ki sani ko da rana ɗaya na ji labarin kin bambanta Asma’u da Rahila ki sani kin ɓata mini sannan zan daɗe ban iya kallon ki ba, zan daɗe ina miki kallon wacce ta gagare ni.”

    Da sauri Gwaggo ta ce” Haka ma ba zai faru ba. Sadiya kara ba ma Alhaji haƙuri.”

    Kaina na ƙasa na ƙara faɗin” Allah ya huci zuciyarka Alhaji. In sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba.”
    Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso mini daga ƙasan zuciyata.

    Sai ya saussauta fushin sa jin har Yusuf ya rankwafa ya na neman min afuwa har da Ma’un da mijinta sai Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce” Bakomai. Na tsorata ne sabo da halin rayuwa. Ka da na faɗi na mutu na bar baraka daga zuru’a ta, na ji daɗin da kika hangi kuskuranki kika kuma yi aniyar gyarawa. Ki yi ma Asma’u sallama ta amsa miki tare da musabaha yanzu a gabana Dubu.”

    Ban yi musu ba na juya ina miƙa ma Ma’u hannu lokaci ɗaya ina yi mata sallama. Ta miƙo min hannunta ta na yi min wani irin mirmishin da ni kaɗai nasan ma’anarshi lokaci ɗaya tana amsa sallamata tare da sarƙe hannun juna. Ni ma sai na yi mata mirmishi kwatankwancin mirmishin da ta yi mini, ai ba Ma’u kaɗai ita iya bariki ba nima na iya tunda na fahimci ta na cin nasara a kaina ne ta hanyar amfanin da makirci.

    “Ki yi hakuri Ma’u. Ki yafe mini sharrin sheɗan ne.”

    Haka na faɗa ina mai gayyato mirmishi da rahama a saman fuskata, ko ta yi mamaki ba ta nuna ba sai ta waske, kafin ta ce”Bakomai. Na ji daɗin haka Yar’uwata.”

    Daga zaunen na matsa na rumgumeta, sai da ta yi wani sansarairai kafin ta rumgume bayana ta na ɗan mirmishi nima mirmishin na ke yi sannna muka saki juna bayan mun kalli juna kowaccenmu ta yi mirmishin da bai kai zuuci ba.

    Gwaggo ta yi hamdala Alhajinmu ma haka ya ɗora da cewa” Na ji daɗin haka. Allah na gode maka da korar min sheɗanin da ya shigo cikin zuru’ata. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya, ku kuma na ƙara ɗora muku nauyi ku yi musu gyara in sun yi ba dai dai ba. Sannan kuma ku gaya musu su sada zumunci a tsakaninsu saboda samun falala wajen ubangiji irin ta masu sada zumunci.”

    Suka amsa ma Alhaji da In sha Allahu. Ganin har sha ɗaya ta yi na dare sai ya ce mu ta shi mu ta fi gida mun bar yara su kaɗai a gida.

    Dukkanmu a tare muka yi ma Alhajinmu da Gwaggo sallama muka fita, muna gaba ni da Ma’u su kuma mazajen namu suna bin bayan mu.

    Ni ce na fara kallon Ma’u dai dai mun fito kofar gida, ƙasa ƙass na ce”Kin iya acting kyan shi ki faɗa harkan film za ki ci kuɗi sosai”
    Dariya ta yi kafin ta ce”Ko Sadiya? Ke ma ashe kin san na iya acting sosai.”
    Sai na gimtse fuska kafin na ce”Kin sha yin nasara a kaina Ma’u kamar baya yau ma kin ci nasara. Amman ina mai ba ki tabbacin daga yau ba za ki ƙara samun nasara a kaina ba har abada.”

    Cikin reni ta ce”Kai don Allah? Da gaske?
    Ban tsaya sauraranta ba na ƙarisa jikin motar Yusuf,ganin sun kariso suma ya sa na ɗaga murya ina faɗin” Sai da safe Ma’u. Alhajin Ma’u mu kwana lafiya a gaida yaran.”

    Shi ya amsa min cikin sakewa, ita kuma Ma’u sai ta bige da mirmishi kafin ta ce” A gaida min da yarana Sadiya.” Kai na jinjina mata a saman leɓena na amsa.
    Mu muka fara yin gaba sannan su, a juctiion muka rabu mu muka ɗau hanyar Lodge road, su kuma suka ɗauki hanyar Rijiyar zaki in da gidan Alhaji mustapha ya ke.

    Tun da muka ɗau hanya ban yi magana ba. Hawaye na ke yi a ɓoye ina sharewa da gefen jijabina jikina. Yusuf sau ɗaya ya yi min magana na ce ya rabu da ni, sai ya maida hankalinsa kan tuƙi amman rabi da kwatan hankalinshi na kaina ganin yadda hawaye ke kwaramyamin wani na korar wani, ba wanda zai iya fahimtar yanayin baƙin cikin da na ke ciki, Ma’u ta daɗe ta na gigita duniyata ba tare da an sani ba amman komai > Janaftybaby: ya zo ƙarshe. Na fahimci ni nake ba ma Ma’u daman da ta ke cin galaba a kaina to in haka ne zan dakile wannan damar zan toshe mata duk wata hanyar da za ta ƙara kuntatamin.

    Sanda muka isa gida ko jiran Yusuf ban yi ba, na yi shigewata cikin ɗaki na barsa yana leƙa ɗakin yara. Bedroom ɗin mu na shiga na faɗa kan gado na saki kukan da na ke ta riƙewa tun dazu har da fitar da sauti.

    Ina ji Yusuf ya shigo ganin ina kuka ya sa ya nufeni da sauri ya na faɗin”Haba Sadiyata, ina raye kike kuka? Ko za ki yi kuka ba za ki yi kuka a saman kafaɗata saboda na ji daɗin lallashin ki ba?

    Ya faɗa ya na mai hawa gadon ya tarairayoni jikinsa, sai na faɗa masa muka durkushe saman gadon ina wani irin gunjin kuka shi kuma yana ta ɗan tapping ɗin bayana alamun lallashi bai hana ni kuka ba sai da na yi ya isheni sannan ya ɗago fuskata ya saka hannuwansa ya na share min hawaye lokaci ɗaya yana faɗin.

    “Ya isa. Ki daina kuka ka da kanki ya fara ciwo. Shii.. is ok kin ji ko?

    Haka ya ke faɗa, cikin sanyin murya, buɗe idanuwana da suke rufe ina kallonsa da jajayen idanuwana kafin na ce” Ka yarda da cewa Ma’u makira ce? Ka ga fa ta haɗa ni da mahaifina a gabana na kasa wani abu Yusuf, ta haɗa ni da kowa nawa.’
    Sai na ƙara fashewa da kuka ina faɗin” Na rasa me na yi mata ta ke yi min haka? In saboda fasa auranta da Yaya Hamza ne ban yi nadama ba, saboda in da na bari da tuni ta haɗa mana yaƙi a gidanmu. “

    Shi dai yana ta faman ba ni, ba ki ya na cewa na yi hakuri na daina kuka tunda Alhaji ya yi min faɗa na bi umarninsa.

    Ƙura masa ido na yi kafin na ce”Haka ne zan bi umarninsa. Bakomai.”
    Daga haka na tashi daga saman jikinsa na sauka daga kan gadon lokaci ɗaya ina cire Hijabin jikina.
    Fita na yi zuwa toilet ina wani tunani a cikin raina. Ba haka zan zauna Ma’u ta cigaba da cin galaba a kaina ba, tunda har ta riga ta samu magoya baya, ni kuma daman ba ki na yasa ko ina da gaskiya na ke zama mara gaskiya gwara na yi amfani da fatar bakin nawa domin ka da Alhaji ya sake yin fushi da ni gwara na cigaba da tafiyar da Ma’u kamar yadda nima ta ke tafiyar da ni.

    KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
    07045308523.

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*

    Note
    error: Content is protected !!