Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Itama Amina sai ta samu gefen gadon da nake zaune ta zauna lokaci ɗaya tana saka hannu ta na taya ni nin ke kayan da na zube kan gado muna kuma sakawa a cikin ƙaramar akwatina.
    Allah ya sa ma sauran kayan Amina ta haɗa cikin wankin su mai wankin su ya zo ya karɓa an wanke su tas an kuma goge. Waɗanan da muke ninkewa zannuwa na sakawa a gida ne sai rigunan barci da wanduna sai unders su ne jiya da na samu sauƙin jiki na wanke su da kaina Amina ma ta yi ta yi na bari ta wanke mini na ce ta bar su zan iya yi da kaina.

    “Ina za ki je daga nan Ya Sadiya?

    Amina ta ƙara tambaya na ni kuma sai na yi mata shuru har muka gama ninke kayan gabaɗaya na ja akwatin na rufe daman sauran kayan na ciki na ja ta can gefen wardrope in da take a jingine sannan na koma in da na tashi na sake zama.

    “Na ƙi ba zan faɗa miki ba.”

    “Don Allah fa na ce.”

    Ta sake marairaicewa kamar wata ƙaramar yarinya.

    “To Yashe zan wuce.”

    Sai ta ƙwalalo ido ta na kallona kafin ta ce”Yashe fa Ya Sadiya?

    Sai na gyaɗa mata kai kafin na ce” To ina zan je in ba can ba?

    Sai Amina ta gyara zama har da matsowa kusa da ni ta na faɗin” in ba ki shawara Ya Sadiya?
    Ina kallonta sai na gyaɗa mata kai kafin na ce” Me zai hana? Ina sauraran ki.”

    Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce” Gaskiya in dai za ki ji shawarata kar ki je ko’ina. In dai ba za ki zauna anan ba sannan ba za ki je Abuja gidan Ya Auwal ba, ko gidan Ya Hamza ba to shawarata ita ce da dai ki je wani wajen gwara ki koma gida kawai Ya Sadiya.”

    Ta gama faɗa har tana ɗaga mini hannu ni kuma daman kallonta nake yi kafin na daƙuna fuska ina faɗin.
    “Wani gidan kenan?
    “Gidan auran ki mana Ya Sadiya.”

    Wata uwar harara na jefa mata kafin na yi ƙaramin tsaki ina faɗin” Ai ni da ke na faɗa miki megidan har gorin gidan ya yi mini ko?

    “To ai bai kore ki ba Ya Sadiya ɓacin rai ne.”

    “Oh kina nufin na koma duk cin kashin da ya yi mini ya tafi a banza kenan ko?

    Da sauri ta ce” Ni ban ce ki ƙyale shi ya tafi a banza ba.”

    “To me kike nufi Amina?

    Na faɗa a ƙufule.

    “Ba ki ba ni dama na gama maganata ba ne shi ya sa.”

    “In jin ki.”

    Na faɗa a tsume har ina kauda kaina domin ita kanta Aminar sai na ji ta fara ba ni haushi so ta ke yi ni ta kwaye min baya ta goyo bayan Yallaɓai?

    “Nufina yanzu duk in da za ki je Ya Sadiya wani ƙarin tonon asiri ne. Abin da ba ki taɓa yi ba kar ma ki fara. Har gwara ma ki koma gida wajen Gwaggo da ki je Yashe can fa ƙauye ne in wani ya yi shuru wallahi wani ba zai yi shuru ba. Gwara ki koma gidan ki amma shi ma Yallaɓai ki gasa mai aya a hannu yadda zai fahimci shayi ruwa ne madara ake saka masa ya yi kauri.”

    Ta gama faɗa ta na kallona ganin na ƙi mgana kuma na ƙi sakin fuska sai ta marairaice ta na sake faɗin” Ko ba haka ba? Ki duba magana ta da idon basira Ya Sadiya.”

    Yadda ta ce idon basira ne ya sa sai da na yi dariya, itama sai ta hau dariyan Kafin na jinjina kai ina fadin” Haka ne kin yi gaskiya.”

    “Yauwa Ya Sadiya ki koma ko saboda su Jidda.”

    Sai na jinjina kai a karo na biyu kafin na ce” To shi ke nan zan koma Amina.”
    Sai ta murmusa kafin ta rumgumoni tana faɗin” Ko ke fa My Ya Sadiya.”
    Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi mgana ba. Duk in da ɗan uwa ya ke daɗi gare shi ni kaina sai na ji kamar kar na tafi, sai dai kuma gaskiya ta faɗa minj duk in da zan je yanzu kamar na soka wuƙa a cinyata ne na yi kururuwa na yi kirari gwara na koma amma ni da Yallabai zaman yan marina za mu yi tsakanin ni da shi. > Janaftybaby: Falo na kuma wajen yara Amina na kitchen ta na girkin Yamma. Yasir ne da Sumayya a gidan Afra ta tafi islamiya daga baya barin su na yi a falon na shiga kitchen wajen Amina ina ta ya ta aiki jefi jefi muna hira har muka gangaro kan mganar Ma’u.

    “Wai Ma’u shuru kamar ba ta nan”

    “Ta na nan, ai tun da aka yi wannan turken ni da ita sai ta shafa mini lafiya.”

    Amina ta ƙyalƙyace da dariya ta na faɗin” Ni kaina sai mu daɗe ba mu yi waya ba, ko a group na gida ta daina mgana kamar baya.”

    “Ni kaina na ga ta yi sanyi kamar ba ita ba.”

    Na faɗa ina yanka albasa.

    “Rabon da mu yi waya tun lokacin da ta kirani ta na faɗa mini auren shema’u na ce mata ba zan samu zuwa ba.”

    “Ni dai bayan nan mun ɗan hadu a ɗorayi “

    Na ba ma Amina amsa, an yi bikin Shema’u ko wata biyar ba a yi ba ta yi aure a gombe. Wani tsohon chairman ta aura matansa huɗu ɗaya ce ta rasu ya cike da ita dukkan mu mun je bikin amma ba mu je can Gombe ba Ma’un ce ta je su Shema an gama yawon duniya an gaji dai an yi aure can kwanaki da na je gida Gwaggo ke faɗa mini ta zo ganin gida har ta shigo gaishe su har ta ba ma Alhaji dubu biyar a raina na ce su shema an samu duniya kenan.

    Mun cigaba da hiran Ma’u ni da Amina har muka gangaro kan Anty Bahijja nan na ke ba ta labarin irin sunayen da suke kiran Gimbiya da cewa ita ce mai ƙashin arziƙi.

    “Allah na tuba Amina ai ni da arziƙina Yusuf ya aure ni. In ma tsiyar ne sai dai in shi ne ya goga mini”

    Me Amina za ta yi in ba dariya ba har ta na rike ciki na kusa buga mata ƙasan wuƙan hannuna ina faɗin” Ban son iskanci fa Amina”

    “To ke ce Ya Sadiya da wata magana.”

    “Allah kuwa. To har ni za a yi ma gorin ƙashin arziƙi.”

    Ni da ita muna ta dariya cikin annushuwa da hira muka gama girkin nan ana ta kiran sallar mangariba ni da ita muka je muka yi salla, Afra ta dawo ta isko ni daki tana mini hira akwai surutu kamar Baby ce daman kuma tsaran juna ne.

    Bayan sallar isha’i muna falo muna cin abinci Yallaɓai na ta kiran wayata bai haƙura ba.

    “Ya Sadiya ki ɗauka ki faɗa masa gobe za ki dawo”

    “Wallahi ba zan ɗauka ba.”

    Na faɗa ina hararanta sai ta sunne kai tana yar dariya. Kira uku ya yi mini bayan na ɗazu da na shiga sallar asuba na ga huɗu, ni kuma na ce wallahi ba zan taɓa daga kiran shi ba sai yau? Sai yau ne ya tuna da ni matarsa ce? Sai yau? Ai ya makara wataƙila da ya kira kafin yau ɗin da wata ƙila na saurare shi.

    Mun gama cin abinci mun dawo falo Amina ta kunna mana kallo ni ba na ma kallon hankalina na wajen Afra ina koya mata aikin makarantan da a ka ba su a english Yasir da sumyyah na ta wasannin su a tsakiyar falon

    Na ji ana kiran wayar Amina amma ban dai bi ta kai ba sai da na ji tana faɗin” Ya Hamza ke kirana.”

    Ban kawo komai a raina ba na ce” To ki ɗaga mana.”

    Na ji ta ɗauka da sallama suna gaisawa daga nan sai na ji tana faɗin” Ya Sadiya wai? E ga ta nan ina ga wayar tana ɗaki ne shi ya sa ba ta ga kiran ba.”

    Sai na dawo da hankalina kanta har ina miƙewa. A ina Ya Hamza ya san ina gidan Amina.?

    “Ga Ya Sadiyar”

    Na ji Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na ta isowa in da nake ta miƙa mini wayar na karɓa ina mata inkiya da ido a ina ya san inan nan? Sai ta rika min nuni na yi mgana Ya Hamza na jin mu.

    “Salamu Alaikum Ya Hamza.”

    “Sadiya kina lafiya?

    Ya faɗa daga bangarensa.

    “Lafiya lau. Ya su Anty Khaleesat da yara?

    “Duk suna nan lafiya.”

    Shuru na wani lokaci na kasa mgana amma gaba na ya faɗi ina tunanin a ina ya san ba na gida ina kaduna ko dai Yallaɓai ne ya kai masa ƙarana?
    Dam! Na ji ƙirjina ya amsa ban samu sararin mgana ba na ji Ya Hamza na faɗin

    “Ashe kina kaduna?

    Ina shirin na amsa masa sai kawai ya cigaba da faɗin.

    “Ke haka ake yi ehe da ga zuwa ziyara sai ki shantake a gidan ƙanwarki sama da kwana goma ba ki da ranar ƙomawa gidan mijin ki?

    Mamaki ma ya hana ni mgana. Mamakin Yallaɓai da zai tashi wasa da ni.

    “Dama daman gobe nake shirin komawa.”

    “To ya dai kamata. Shi ya kirani yanzu yana faɗa mini ba ki a gida sama da sati ya na ta kuma kiran wayarki ba ki ɗauka ba.”

    “Wayar ta na silent ne ban ji kiran na shi ba.”

    Na samu kaina da furtawa. > Janaftybaby: “To sai ki kira shi yanzu ku yi magana. Sannan gobe ki koma gidan ki Sadiya. Shi kan shi Dr sai ya ga rashin hankalin mu gandan gandan dake, ke ba suna kika zo ba sannan ba biki ba daga kun ɗan samu matsala da miji sai ki kama hanya ki tafi gidan ƙanwarki? In ma yajin za ki yi kuma tun da ba ki je ɗorayi ba me ya hana ba ki taho gidana ko gidan Auwal ba?

    “Ka yi haƙuri Ya Hamza.”

    “Ba maganar haƙuri ba ne. Ba a haka kin ji ko? Amina ƙanwarki ce bai kamata ki je gidan ta in wani abu ya faru ba. Mu ya kamata ki fara nema.”

    “To Ya Hamza.”

    Na furta ina ƙokarin mai da ƙwalla da suka cika mini ƙwarmin idanuwana.

    “Ki yi haƙuri ki koma giden ki ki rumgumi mijin ki da ƴaƴanki. Ya faɗa mini da kan shi ranshi ne ya ɓaci ya ɗan faɗa miki wasu mganganu ma su zafi sai kika ji haushi kika ce za ki taho kaduna. Ya ce ya bar ki taho ne saboda ke da shi ku samu zukatan ku su huta sai kuma ya ga kin shantake kin ƙi dawowa yana ta kiran wayarki kuma ba ki ɗauka ba.”

    Shuru na yi domin kalaman bakina sun gama ƙarewa. Yallaɓai ya shirya wasan ƙwaikwayon shi ya nemi yan wasa kuma har an yi wasa an tashi karshe dai shi ke da nasara akaina bayan tarin tozarcin da ya yi mini

    “Ki yi haƙuri kin ji ko? Haba Sadiya da girman ki ai yaji bai kamace ki ba, ki yi hakuri ki koma gidan ki, ke yanzu uwa ce sai dai ma ki yi ma wasu faɗa.”

    “To Ya Hamza in sha Allahu gobe da safe zan koma.”

    “Yauwa. To mu kwana lafiya amma ki kira shi yanzu.”

    Da haka muka yi sallama da shi muna gama wayar Amina ta zauna gefena tana faɗin” Wai me Babansu Jidda ya kira Ya Hamza ya faɗa ma sa? Na ji ya na miki faɗa ne?

    Sai na kalleta, lokaci ɗaya hawayen da na ke ta riƙewa suka kece mini amma sai na yi saurin saka hannu na goge hawayen ina faɗin.

    “Ya kira shi ya faɗa mai mun ɗan samu sabani ranshi ya ɓaci ya ɗan faɗa mini mganganu ni kuma sai na ji haushi na ce zan taho Kaduna a cewarsa ya bar ni na taho saboda ni da shi mu samu zuciyarmu ta yi sanyi amma sai ya ga na daɗe ban dawo ba kuma yana ta kirana a waya ban ɗauka ba”

    “Lalle ne ma. “

    Amina ta faɗa ta na riƙe haba kafin ta cigaba da faɗin” Yallaɓan nan na ki ya Saduiya sai ke”
    Ta faɗa tana dariya na kalleta amma ban yi mgana ba.

    Na fahimci manufarsa ya yi saurin kiran Ya Hamza ne ya faɗa masa saboda ni ya rigani wanda ko daga baya na faɗi wata mgana ba za a goya mink baya. Yallabai ya san ni sarai kamar yadda na san shi ciki da bai. Ya san ba zan taɓa zuwa na kai ƙaran shi ba ya kuma san ba zan taɓa fasa mganar faɗan mu ba amma ya san ina da kafiya zan iya ƙin dawowa a lokacin da ya so ya kuma san in ba Ya Hamza ko Ya Auwal ba, ba wanda zai matsa mini na koma shi ya sa sai ya yi saurin kiran Ya Hamza. Ya san da gangam na ƙi ɗaga wayarsa ya kuma sha jinin jikinsa ko kunya ne zencen ban sanin masa ba. Sai yanzu ne ya tuna da ina da amfani a rayuwarsa? Wallahi tallahi sai ya raina kansa kuma bashin gorin da ya yi mini na gida da na haihuwa watan tara na zai biya su. Sannan ya yi sanadiyar na rasa gudan jinina bana jin ko da na yafe masa laifinsa to ba na jin zan iya yafe masa wannan kasadar da ya ja mini na rasa wani abu mai muhimmaci a rayuwata.

    Zan koma ba domin Ya Hamza ya yi min mgana ba sai domin ina da niyyar komawar. Amma kuma kiɗa ya sauya dole rawa shima ya sauya. Na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitan da zan nema ma kaina in na koma gida.
    Na yi tunanin zan koma makaranta na yi masters ɗina sannan zan inganta sana’ata ta hijabai har ma da ƙarin wani sana’o’in na daina dogara da Yallaɓai na kuma daina dogara da duk abin da ya ke takaman ya mallaka. Daga ni sai ƴaƴana domin nan duniya su ne kaɗai na aminta da ɗari bisa ɗari ba za su taɓa juya min baya ba.

    Da safiyar talata na yi shirin komawa Kano. Tare muka fita da Amina za ta je saloon ita da Yasir ne Afra da Sumaiyya na makaranta Amina sai sha’awata take ba ni ta iya driving ba in da ba ta zuwa a garin Kaduna da yar motar ta da Dr ya siya mata. Ni ma a raina na kudiri niyyar zan dukufa da sana’a har nima na mallaki mota ta kaina da gumina. Ita ta kai ni tasha na samu mota sannan muka yi sallama sai da motar ta tashi na bar ta a tasha. > Janaftybaby: Kuma har kuɗin motar ita ta biya mini da cewa Dr ne ya ce ta ba ni na ƙara riƙewa a hannuna. Mun rabu ina ɗaga mata hanmu tana ɗaga mini nima.

    Motar mu ta tashi goma saura ba mu isa Kano ba sai biyu na rana. Daga tasha na hau adaidaita zuwa gidana. Ba kowa a gidan sai da na saka makulli na buɗe gidan na shiga ko’ina ya yi ƙura. Na shiga cikin bedroom ɗina na ijiye akwatin hannuna da jaka sannan na zare mayafi na shiga tiolet na kama ruwa na yo alwala na taho na yi salla ina idarwa na tashi na shiga kitchen, shima dai duk ya yi ƙura amma dai ba a yi amfani da komai ba.

    Gas na kunna na dafa ruwan zafi na sha tea, sai ƙwai da na soya guda uku bayan na gama na koma ɗaki na ɗauko wayata kamar in kira shi sai na fasa. Domin ban bi umarnin Ya Hamza, jiya ban neme shi ba shima bai sake nema ba ina da tabbacin wata ƙila ya sake kiran Ya Hamzan ne shi kuma ya faɗa masa na ce yau zan koma gida.

    Ganin ba zan iya kiran shi ba sai kawai na tura masa saƙo.

    “Na dawo gida.”

    Ina gama tura masa sai na kira wayar Salisu direba bayan mun gaisa na ce masa yau in ya dauko su Jidda ya kawo mini su gida na dawo. Yana ta min sannu da zuwa na gama waya dashi kenan Balaraba ta kira ni ta na faɗa mini Saude ta sauka duk sai na ji ɓacin raina ya tafi ina mata barka ta samu megida tun da namiji ta haifa. A Lokacin na kira wayar sai mijinta ya ɗauka ya ce ta na wankan da yake ba a asibiti ta haihu ba a gida ne amma sun kira anguwan zoma. Mun rabu a kan cewa in ta fito zai faɗa mata za ta kirani. Sai ko gashi ta na fitowa ta kira ni muka yi magana abin hamdalar shi ne ta haihu lafiya ba wata matsala na yi mata mganar za ta dawo gida ne ko anan za ta zauna sai ta ce min ita ba ta sani ba, ni ko kai tsaye na ce mata gwara dai ta dawo gida a kula da ita ko bayan suna ne sai ta ce mini za ta yi magana da megidanta na ce ya kamata.

    Na ɗan kwanta sai la’asar sannan na tashi na yi salla sannan na fara gyaran gidan na share ko’ina na goge na saka turaren wuta gidan ya fara ƙamshi duk da na gaji ban zauna ba na fara tunanin abin da zan dafa na duba friza na sai na ci karo da miyar da na yi ana gobe tafiyata tana nan ba ta yi komai ba kuma ina da sauran kayan miya da kayan lambu sai dai duk sun bushe sai na kwashe su kawai na zubar har da ma su kankana suma duk ƙanƙara ya sa sun yi wani nakwa nakwa saboda daɗewa sai kawai duk na kwashe na zubar a bola na goge firizan. Miyan na sake gyarawa na dafa mana farar shinkafa na gama shidda saura na yamma na goge kitchen ɗin sannan na je na yi wanka na fito kenan ina saka kaya na ji ana buga get a raina na ce to yan makaranta sun dawo.

    Wani riga da wando na saka pakistan ne rigar ja ne da baƙi ba ta da hannu sai daga kasa an ɗan zoɓa ta, sai wando sakakke ne bai kama min jiki ba sai na saka hula baƙa mai kwalliya ta sama, kaina akwai kitso a can Kaduna Amina ta yi min shi duk da ba ta wani iya kitson ba amma na gaji da kan ya tsufa sai na tsife na ce ta yi min ko kalaba ne shi ne ta zarga min shi haka, kuma gashi ba ta kama shi da kyau ba duk ya fara sukurkucewa har kunya na ke ji na buɗe kan a gaban mutane.

    Silafas ɗin cikin gida na saka sannan na saka mayafi na fita zuwa haraban gidan na buɗe ma yara ƙofa suna ganina har Jidda sai da suka faɗa jikina suna min oyoyo na tarbe su cikin farinciki. Da gaske na yi kewar su sosai musamman ma surutun Baby. Salisu bai tafi ba daman in ya kawo su sai ya tabbatar da an buɗe gida sun shiga ya ke tafiya mun gaisa da shi ya yi min barka da dawowa ni kuma na ce ya gaida iyalan na shi, na rufe gida muka dawo cikin gida ni da ƴaƴana.

    “Baby ciwo kika yi? Na ga kin rame ne?

    Na faɗa ina tattaɓa wuyan ta lokacin da muka dawo cikin gida.

    “Ta yi zazzaɓi na kwana biyu a gidan Anty Gimbiya.”

    Jidda ta ba ni amsa sai na zauna saman kujera na jawo Baby ta zauna saman cinyata ina shafa fuskarta na ke faɗin.

    “Ayya sorry My princess Umma ta tafi ta bar ki ko? > Janaftybaby: Sai Baby ta fara tura baki tana faɗin” Umma ni dai kar ki ƙara tafiya ba ki tafi da ni ba ina ta kuka Abba sai ya yi ta cewa za ki dawo ba ki dawo ba sai da aka daɗe.”
    Dariya na yi ina mai rumgumeta kafin na ce” Ba zan ƙara tafiya na bar My princess ba in sha Allahu “
    Jin haka ya sa ta fara tsallen murna ita dai Jidda na zaune ta na mirmishi. Ranar ni na ta ya Baby cire kayan makaranta ta saka na gida Jidda ma ta sauya ta fito na zubo mana abinci a filet muka ci tare. Na sha labarai wajen Baby duk abin da ya faru da ba na nan sai da ta faɗa mini Jidda na gefe ta na cin abincinta tak ba ta ce ba, ashe ranar da na tafi ranar daga makaranta ya ce salisu ya kai su sharaɗa ba su ma kwana a gidan ba kenan.

    Bayan mun gama Jidda ta tattara komai ta kai kitchen ta kuma share in da muka ɓata. An kira mangariba muka yi alwala muka yi salla a falo, muka yi azkar sannan na ce mun dade ba mu yi karatun Qur’ani su ɗauko mu yi karatu. Ba mu muka tsagaita da karatun ba sai da a ka kira sallar isha’i sannan muka dakata muka yi salla, muna idarwa na ce su yi aikin makaranta ni kuma sai na shiga ciki na ɗauki wayata ina dubawa sai na ga Yallaɓai ya yi min saƙo.

    “Ya yi kyau.”

    Abin da ya ce kenan a saƙon na shi ƙaramin tsaki na ja na danna delete saƙon ya goge daga wayata. Data na kunna ina ganin saƙonni nata shigo mini ma su tambaya hijabai ne daga yan makarantar mu ta BUK daman suna siya tun da duk na yi musu tallah. Na amsa na yi ta ba su da cewa cikin satin nan za a kawo tun da ina Kaduna ma mun yi mgana da mai ɗinkin Hijaban lissafi kawai za mu yi na tura masa kuɗin shi, sannan na fara tunanin yadda zan in ganta kasuwancina shi ya sa a I.G na yi ta following ɗin masu ƙananun kasuwanci domin na ga yadda suke marketing ɗin kayan su sai na fahimci ina bukatar suna da ledan da zan rika saka ma kowa hijabin shi in ya siya shima duk inganta kasuwanci ne, sannan ina bukatar ɗinka hijaban in diffirent styles ma’ana kowani yanayin ɗinki ya kasance ana samu bambamci sosai da ganin abu unique a hijaban da na ke siyarwa sannan akwai bukatar na ƙara da wani abu. Ni kaɗai na zauna ina ta tunanin da me zan kara? Na fi son abin da ni kaɗai na ke siyarwa ba ko ba ma ni kaɗai ba to ya kasance bai yi yawa ba. Lamarin ya kai har littafi da biro na ɗauko na fara rubutu har takalma na saka da atamfofi amma sai na ji hankalina bai kwanta da su ba sai kawai na saka under wears irin su pant, bra, sikat gajerun wanduna da dogaye tare da sleeping drees sai na ji na fi karkata anan sai na fara tunanin sunan da zan saka a jikin logon kasuwancina daga jarshe da na ga na matsa ma kaina da yawa sai na ijiye zuwa da safe amma waya na hannuna ina ta shige-shige ina ganin sunayen da mata ke sanya ma kasuwancin su very interesting.

    Ina cikin shige- shige na sai ga kiran Surayya Dee Bojuwa herbel, da na ga kiran ta sai da na ji kunya na daɗe ban nema ta ba daman ina shirin neman ta ne muka samu matsala da Yallaɓai. Ta ce kwana biyu ba ta ji motsina ba shi ya sa ta kira ta ji ko lafiya
    Ina dariya na ce” Lafiya ƙalau wallahi kwanaki can ne na kwanta asibiti da yake na samu ɓari.”
    “Subhanallahi Sannu. Allah ya kawo wani mai albarka.”
    Na amsa mata da Amin sai ta fara min mganar tun da na yi ɓari ai ya kamata na yi gyara sai na ce mata zan yi in sha Allahu amma ba ni da kuɗi a hannu in na samu zan yi mata mgana.

    “Haba Matar injiniya. Ni dake ai ba haka tsakanin mu kawai ki yi lissafin abin da kike so mai delivery da safe sai ya kawo miki”
    Sai na kasa ce mata komai tabbas mun saba ko ba ni da kuɗi a hannu ta na ba ni kaya in na samu sai na tura mata. In na ce zan yi mata wani bayani ba za ta taɓa ganewa ba sai kawai na ce zan tura mata whatsApp abubuwan da nake so da haka muka yi sallama.
    Sai na yi zuru ina tunani to gyaran me zan yi? Na gyara ma wanda ya gaji da ni! Ko na ce na fara tsufa na rage daɗi shi ya sa yanzu Yallaɓai ya daina marmarina. > Janaftybaby: Na so na sha kayan lambu ne su kankana da rake da za su ɗan ta da min ni’ima saboda amfanin kaina ba domin shi ba, amma ban yi niyyar siyan wani mgani na sha ba shi ya sa ma na share Surayya kawai ban tura mata ba, na dai kira Aisha lame na ce ta aiko min da lotion sai shower gel saboda na wajena saura kaɗan ya ƙare mun rabu da ita kan cewa da safe zan san ya mata kuɗin.

    Hankalina ya yi kan wayata shi ya sa ko shigowar motar Yallaɓai ban ji ba sannan ban ji maganar yaran ba, ina kwance ruf da ciki a saman gado ya shigo ɗakin ba domin ban san shigowarsa gidan da ba da a ce na sani da ba zan taɓa ɗaga idanuwana na kalle shi ba amma tun da cikin rashin sani ne ina ɗagowa muka haɗa ido huɗu da shi, da sauri na mai da kaina kan wayata. Saboda sai da na gan shi sai na ji wani irin ƙunci na mamaye min zuciya. Na so na daure ma zuciyata ko sannu da zuwa na yi masa amma na kasa shi ya sa na yi kamar ban san da shigowarsa ɗakin ba shima ina ga ya na jiran ne na fara yi masa mgana shi ya sa har ya ijiye ƙaramar jakar hannunsa saman side drower ɗin gadon tare da agogon fatan da ya cire daga hannun shi ya fita bai ce min sannu ba nima ban ce masa ba ina kwance in da nake ya dawo ya tuɓe kayan jikinsa daga shi sai gajerun wando ya koma tiolet duk ina kallon shi ta wutsiyar ido sannan na raka shi da hararan da bai san ina yi ba har kuma ya yi wankan shi ya fto ban ta shi ba, ya shafa mai sannan ya saka saukaƙkun kayan zaman gida ya fita can wajen su Jidda. Ni kuma na daɗe kan wayata sai wajen goma da rabi na kashe data nima na miƙe na faɗa tiolet na kama ruwa, sannan na zo na saka kayan barci na shafa ma wuyana da hannuna humra sannan na kwanta har ina kashe wutar bedroom ɗin kuma cikin ikon Allah barci ya ɗauke ni ban ta shi ba sai huɗu da rabi na asuba, na je na kama ruwa na yo alwala na zo na shimfiɗa sallaya na ta da salla, ina kan darduman Yallaɓai ya tashi lokacin an fara kiran sallar farko ni kuma na gama nafilfiluna ina ta jan casbaha ko kallo bai isheni ba kamar yadda shima bai nuna ma ya san ina gidan ba.

    Ina idar da sallar asuba na tafi ɗakin su Jidda muka yi azkar da karatu bayan mun gama muka shiga kitchen ni da Jidda muka yi abin karyawa. Kuni na ji ina son sha tun jiya daman na jika geron sai na wanke na niƙa shi a blander Jidda kuma wanke wake shima na niƙa shi a blander, ni na dama kunin da tsamiya Jidda kuma ta fara tuyan ƙosan daga baya na karɓa na ce ta je ta shirya kar ta makara. Ni da ƴaƴana muka karya lokaci na yi Salisu ya zo ɗaukan su suka wuce ni ko daman na ci na ƙoshi sai na kishigiɗa a kan kujeran falon su Jidda tibin a kunne sai na ɗauki remot na sauya tasha zuwa arewa24 suna maimacin shirin daɗin kowa. Ina nan zaune ina kallo sai na ji motsin fitowar Yallaɓai ta wutsiyar ido na kalle shi, ya fito daga shi sai dogon wando da farar singlet Yallaɓai har wani kiba ya narka to in ba idona ƙarya ya yi min ba har da timbi ya fara ijiyewa ya samu duniya. Yau ɗin ma na so na daure na gaishe shi amma sai na ka sa ma na ƙara sautin talabijin ɗin a zuwan ko ya yi mini magana ma ba zan ji sa ba.

    Ina zaune nan ya zo ya wuce ni zuwa kitchen ai ban gama mamaki ba sai ga shi ya fito da Mug cike da kunu sai filet shaƙe da ƙosai, daman ni ban shirya masa na sa a saman dining ba, a kitchen na bar komai shi ne ya shiga ya gani ya nema ma kansa mafita. Baki na saki ina kallon shi ya zo ya zauna saman kujeran dake fuskanta ta, har ya na haɗe kafafunwabaa ya kuma jawo center table ɗin da ke tsakiyar falon zuwa gaban shi ya ijiye mug ɗin kunun da filet ɗin da ya shaƙo kosan a ciki.
    Remot na gefe na ya ta so ya zo ya ɗauka, ya sauya ta sha zuwa MbcAction. Ina ga ya so na yi magana ne sai kuma ya ga na mike tsam na wuce ciki na bar sa anan. Ban san yadda ya ƙare ba ina shiga ciki na kwanta sai barci tashi kawai na yi na ga bashi a gidan ya fita a raina na ce ɗan renin wayau ranar da yamma Salisu ya kawo min cefane shi na ba ma kuɗi ya je ya siyo mini kayan marmari na yi fruit salat na sha sannan na faɗa masa da safe direba zai kira shi za a kawo min hijabai daga Zariya zai karɓo daman tun da Musbahu ya yi aure sai na koma > Janaftybaby: Salisu ke karɓan kayan a tasha.

    Haka muka yi ta zaman doya da manja tsakanina da Yallaɓai in ya na gidana. In kuma ya na gidan Gimbiya ya kan zo duba mu da daddare. Har kuma ya gama zaman shi ya tafi ko ma ya ganni ba ma mgana. Ya san halina sarai na iya gaba shi kuma ina ga jirana yake na je na bashi haƙuri tun da ni na yi masa ba dai-dai ba ni kuma a raina na ce wallahi ya yi kaɗan ina yin abinci na ijiye masa na shi saman dining kuma ba kunya yake zama ya narka ma cikin sa. Na san har Jidda ta fahimci tsakanina da Abban na su ba zaman lafiya domin tun tasowarta ba haka ta ga muna gudanar da rayuwar mu ba, shi ya sa ta tsiri in ya shigo gidan ta biyo ni ɗaki ta na faɗa mini ga Abba ni kuma sai na ce ta je ga ni nan zuwa kuma haka zan yi ƙeme ƙeme na ƙi fita sai dai su in yana son wani abu ya ce su yi masa tun yarinyar bata fahimta ba har na fara fahimtar ba jituwa a tsakaninmu yanzu. Ranar da yana gidan Gimbiya ya zo mana sallama da daddare ina ɗaki ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ba su ba ni kuɗi ta shigo tana faɗa mini ga Abba ya zo ya na falo.

    Sai da na yi mata wani kallo sannan na ce” Ke in kika ƙara zuwa min ikina wani iyayin ga Abba ya zo sai na yi fata fata dake wallahi.”
    Sai Jidda ta kasa mgana ta tsaya ta na kallona kafin ta ce” Amma Umm.”
    “Fita ki ba ni waje. Shi bai san in da nake ba ne? Ko sai kin zo kina damuna? Ki sake dawo ki gani in ban yi miki bugun tsiya ba.”
    Ai Jidda da sauri ta fice tana mai rufomin ƙofa na bi ta da ƙwafa ina faɗin” Ka ji min munasiran yarinya.”
    Sai da yi kyafci sannan na cigaba da rubutuna amma a kasan raina ina jin zafi shi ai ya san in da nake, tun da bai neme ni ba ni kuma me ya sa zan nuna na san da zuwan shi?
    Jira ya ke yi har yanzu na zo ina bashi haƙuri lalle ko bai san taurin kaina ba ne shi ya sa. Wallahi ba zan ba shi haƙuri ba, domin ni ban ga laifin da na yi masa ba. Sai ma shi ne ya yi min laifi da yake buƙatar ya ba ni haƙuri amma ya yi fuska yana jiran ne na fara ba shi haƙuri ai ko sai da ya bushe.

    Da safe Amina ta kirani bayan mun gaisa tana mini tambayar banza wai na faɗa ma Yallaɓai na yi ɓari kuwa?
    Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce” Ban faɗa masa ba. Wani abu ne?
    “Kai Ya Sadiya ai kamata ya sani ko?
    “To ke sai ki faɗa masa tun da ya kamata ya sani ɗin”
    Sai ta fara dariya ƙasa ƙasa ta na faɗin Allah ya ba ni haƙuri sai na fara masifa ina faɗin.
    “Ai bai nemi ya sani ba, tun da na dawo ba ya mini mgana bai ma san ina rayuwa ba sai ni ce zan bishi ina faɗa masa na yi ɓari? A she ma yana gaba na kenan”

    Sai Amina ta kashe wayarta ta bar ni ina ta masifa ni kaɗai. Haushin kowa na ke ji yanzu ina shiri zan je Ɗorayi, saboda Balaraba ta kirani kan zuwa Jigawa gobe sunan Saude daman na ce zan je, da safen ba a gidana ya kwana ba saƙo na tura masa kuma har na gama shirina na fita bai dawo mini da amsa ba. Sai da na fara biyawa gida na gaida Gwaggo Alhaji ba ya nan ya tafi Yashe duba gonakinsa. An kusa fara noma damina ta fara mana sallama na ɗan jima a gidan sannan na shiga gidan su Saude. Ma su zuwa sunan ƙannenta ne guda biyu sai ƙannen Saude da maƙota haka gobe za mu tafi sai jibi mu dawo tare da Sauden gabaɗaya tun da mijin ya amince ta dawo gida ta yi jegon ta. Sai azahar na baro ɗorayi bayan na yi salla a gida shagon Amesty na biya na yi tsifa sannan na yi Saloon yau ma sai da ta yi mini mganar ya mganar buɗe shagona na ce mata ya na nan soon in sha Allahu.

    Ban ji a raina zan haƙura da burina ba so kawai nake yi na tsaya da kafafuna amma sai na cika burina na buɗe shagon saloon in sha Allahu. Daga nan na dawo gida sai ma da na dawo gida ne na duba wayata na ga saƙon Yallaɓai na adawo lafiya a raina na ce aikin ɓur in ji tusa, na fara shirin tafiya jigawa suna. Daman tuni na siya Atamfa wajen Dija collection da pampers tare da rigan yaro sai na haɗa mata da setin mayukan jarirai, ina da ƴan kuɗaɗena da su na yi amfani da daddare daman Yallaɓai zai dawo gidana shi ya sa sai da na bari ya shigo gidan yana falo tare da su Jidda sai na fito na kira Jidda ta na zuwa na ce ta je ta faɗa ma Babanta gobe zan je Jigawa Saude ta haihu. > Janaftybaby: Na ga ta tsaya ta na kallona amma yadda na haɗe rai ne ya sa ba ta samu damar mgana ba ta wuce ta koma falon ni kuma na koma bedroom na zauna ina jiran ta.

    Can ba daɗewa sai ga shi ta dawo da kuɗi a hannunta sabbi yan dubu ta miƙa mini tana na faɗin” Abba ya ce Allah ya kiyaye hanya.”
    Ban karɓa ba na bi kuɗin da kallo kafin na ce” Wannan kuɗin fa?
    “Shi ya ce na ba ki.”
    Karɓa na yi na kirga 10k ne cif kamar wata almajira ai ko siyayyan da na yi ma Saude ta fi karfin 10k ballanta a zo maganar kuɗin mota.

    Mai da ma Jidda kuɗin na yi sai ta ƙi karɓa ta tsaya tana kallona.
    “Ki mayar masa. Na gode.”
    Kuma yarinya sai ta ƙi karɓa wani kallo na yi mata kafin na ce” Ki karɓa mana.”
    Sai ta noƙe hannu tana faɗin” Umma kar ki yi haka”
    Bai kamata Abba ya ba ki kuɗi kuma ki ce ba za ki karɓa ba.”
    Baki na saki kawai ina kallon Jidda. Wai ta na faɗa mini abin da ya kamace ni.

    “Kuma Umma ni dai ba zan iya mayar masa ba sai dai ki mayar masa da kan ki”

    Kafin ta rufe baki na watsa mata kuɗin a fusace na miƙe ina faɗin” Ke da kuɗin kar ki bari na buɗe idanuwana na gan ku a ɗakin nan. Ki kwashe su salim alim ki fice ki ba ni waje Jidda.”
    Amma sai ta tsaya za ta mini mgana ai ko na da ka mata tsawa ina faɗin.
    “Ki fita na ce ko?
    Sai ta duka ta tattara kudin ta fice cikin san yi jiki na dafe kaina ina tsaki, Jidda ma laifina ta ke gani, uban ta na yi min wulakanci tana ƙoƙarin kare masa saboda ba ta da tunani sakarya ce. Ni kaɗai a ɗaki ina ta masifa sai ma na tattara kayana da duk abin da zan buƙata na kai ɗayan ɗakin na can na kwana da asuba ma kuma mun haɗu na fito daga cikin ɗakin shi kuma ya fito daga tiolet muka kusa cin karo, ya yi baya nima na yi baya. Ya kuma kalleni ni ma na kalle shi amma kowannen mu sai ya kauda kan shi, ya shiga ɗakin barcin mu ni kuma na shiga tiolet.

    Tun safe na shirya takwas da wani na safe aka kirani an samu mota ana jirana. Kuma ga Yallaɓai bai fita ba. Ba domin yana falon shi ba da ba abin da bai hana ni tafiyata ban yi masa sallama ba. Amma ganin shi a falo ya sa da na fito na yi masa sallama na ce na tafi amma mutumin nan ya na ta duba abu a system ɗin shi bai ko ɗago ba ya ce min Allah ya kiyaye hanya. Kamar zan ce masa zan yi kwana ɗaya amma yadda ya nuna mini halin ko in kula, ya sa na yi tafiya ta ba tare da na yi masa wata mgana ba amma har na kai ɗorayi raina na ƙuna.

    Na fara shiga gida na gai da Gwaggo na iske ƴaƴan Ya Abubakar wai zaituna ta tafi Funtua biki, na ce sai su ɗebe miki kewan Alhaji Gwaggo. Ƙarfe tara da rabi muka kama hanya a golf da aka yo mana tasha. Balaraba 5k na ba ta sannan na nuna mata abin da na siya ma Saude ta yi ta mini godiya. Ni ko na ce haba ai Saude ƙanwata ce ballantana ta yi min alheri ƙwarai kuma sakamakon alheri to ya zama alheri ne. Mun isa da azahar lafiya mun iske ana ta suna dangin miji da makota sun cika gida Saude ta ji daɗin ganina sosai ta nuna murnan ta mun sha suna Rahila ta kirani ta ce ta zo gida Gwaggo ta ce ina Jigawa na je suna. Na ce mata wallahi ga shi sai ma gobe zan dawo mun daɗe muna waya da ita kafin mu yi sallama.

    Da daddare mu muka gyara gidan da aka ɓata sannan muka shirya ma Saude kayan ta na tafiya. Ta samu kayan suna ba laifi, sai godiya shima mijin na ta ya iya bakin ƙoƙarin shi, bayan duk mun gama ayyukan ina kwance a kan kafitar da aka shimfiɗa mana ni da kanwar maman su Saude Yallabai ya kira waya ta sai na fita falo ina duba agogon bangon da ke ɗaki goma har ta gota amma abin mamaki me ya sa ya ke kirana?

    “Assalamu alaikum”

    “Kina ina ne?

    Ko amsa sallama ta bai yi ba ya tare ni da mganar ko ina ina ne ?

    “Ina gidan Saude a jigawa.”

    “Can za ki kwana ne?

    Sai na haɗiye wani abu a maƙoshina saboda na ji kamar a zafafa ya ke mgana.

    “E sai gobe za mu dawo tare da ita.”

    “Da izinin wa za ki kwana? Kin faɗa min kwana za ki yi Sadiya?

    Sai na kasa magana tun da dai ba ni da gaskiya.

    “Sadiya don kina gaba da ni ba shi zai hana tasirin ni mijin ki ba ne ya yi aiki a kan ki ba. Ki na yin abubuwa gaban kan ki ina ta kauda kai amma wallahi kin fara ƙure ni kar ki bari na faɗo kan ki” > Janaftybaby: Ban yi mamaki ba. To daman ni da ya ke ji ra bai samu dama ba sai yanzu.

    “Kin aiko min Jidda da cewa za ki je suna na ce sai kin dawo na aika miki da kuɗi kin dawo min da su Sadiya me kike nufi
    da ni? A she ba zan ci albarkacin Jidda ki karɓi kuɗin nan ba? Dole sai kin nuna mata ni da ke babu jituwa ko! To kin kyauta kuma ya yi miki kyau.”

    Ashe dai ya ji haushin dawo masa da kuɗin da na yi. Na ko ji daɗi a cikin zuciyata da ya ji shima haushin da na daɗe ina ji.

    “Allah ya kai mu goben ki dawo. Za mu zauna sai ki faɗa min duk abin da na yi miki da zafi da ya sa kika maidani ni da banza duk ɗaya Sadiya.”

    “Ka yi haƙuri.”

    Na faɗa saboda ina so ya ƙyale ni barci nake ji na gaji.

    ” Bakomai kawai ban ji daɗin da ba ki faɗa mini zaki kwana ba ne.”

    Baki na buɗe na sake rufewa ya wani sassauta murya jin na bashi haƙuri sai ma abin na shi ya ba ni dariya sai da na murmusa shima ina jin sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce.

    “Na yi kewar mirmishin ki Sadiya ta. “

    “Uhm!”

    Na faɗa a ƙasan maƙoshi.

    “Sai kin dawo goben a matsayina na Babba zan ba ki haƙuri a duka laifukan da kike tunanin na yi miki su Sadiya.”

    Ban yi magana ba amma na yi shuru ina jin sa. Ban yi mamaki ba daman na san ya na neman hanyar da za mu shirya ne.

    “Na gaji. Na gaji da wannan horon da muka yi ma juna. Ki dawo mu zauna mu warware komai a tsakanin mu kin ji ko?

    Ya faɗa cikin sanyin murya sai na gyaɗa kai kamar ya na ganina kafin na ce.

    ” Sai da safe.'”

    “Sai da safe Madam.”

    Daga haka na katse wayata. Na daɗe zaune ina tunani daman ai yanzu duk zai ce na yi haƙuri shi ba da gayya ya faɗin duk mganar da ya faɗa ba. In ma na haƙura amma ba shi zai saka na manta da abin da ya yi mini ba.

    *Janafty*.

    Note
    error: Content is protected !!