Turken Gida – Chapter Thirty-nine
by JanaftyWashegari asabar muka tashi da shagalin biki. Sha ɗaya na safe a ka ɗaura aure kuma sun ce a lokacin za su tafi da amarya. Shi ya sa duk nuƙu nuƙun da a ka tsaya yi ɗaya da rabi motacin ɗaukan Amarya suka miƙa hanya. Ni mota ɗaya muka shiga da Munnira da Anty Zabba sai Marwa. Faridan Tariq tana motar Amarya a gidan gaba.
Da yake motocin sabbi ne sannan kuma masu lafiya ne a na gudu ma sai ka ji kamar ma ba a yi. Zuwa huɗu da rabi biyar saura mun sauka a gidan Amarya. Mun iske matar Jafar Nauwara, sai ƙawayen Anty Bahijja ina ga su ƴan Kaduna nan ne da wasu dangin angon su suka tarbe mu. Ma sha Allah gida ya yi kyau ƙwarai. kuma iyayenta sun kashe mata kuɗi kayan ta kaf ba na Nigeria ba ne a ƙasar waje a ka siyo su kuma ba a sauke su ko’ina ba sai Kaduna. Kuma da ya ke akwai ma’aikata maza su suka gyara komai, mu kan mu kayan kitchen ne muka zo da shi sai su cafet da labulanya sai ɗan abin da ba a rasa ba. A nan muka yi sallar la’asar muka ci abinci sannan muka kama a ka ƙarisa gyaran daƙun nan. Muna gidan har dare dangin mijin na ta zuwa a nan ne ma mu ke jin jibi jibin nan za su bi jirgin yawo zuwa Madina, mai son ganin ɗakin Amarya sai dai ya jira bayan salla kuma in sun dawo daga Hajji.
Ba a gidan Amarya muka kwana ba. Ni da Munnira da Anty Zabba har da Marwa gidan Faridan Tariq muka kwana. Ita ma Nauwaran Jafar ta diɓi wasu ƴan’uwa. Daga ƙawayenta sai kakkaninta a ka bar Amarya da su ta kwana. Kuma bayan mun kwana can muka hantse sai wajen sha ɗaya muka dawo gidan Amarya da ke anguwan malali.
Da yake abin na yan gayu ne ba wani cikowa sannan an gyara ko’ina tsab. Muna komawa ba daɗewa sai ga Naja ta zo ita da Suwaiba da Halima sai Anty Maimuna jiya ba su samu tafiya ba. Ni dai ban ga Gimbiya ba, ban kuma Tambaya ba amma Munnira sai da ta tambayi Suwaiba ita kuma ta ce Gimbiyar ce ta mata musu lokacin a na ta jiran ta daga baya ta ce su ta fi ba za ta je ba. Zuwa kai Amarya kamar wani kayan gabas ni Sadiya?
Sai da muka yi azahar muka ci abinci sannan a ka kawo mota muka ɗau Amarya da su turamen atamfa da shadda sai kayan abinci da su cincin ɗin da su Naja suka taho da shi.
Gidan Iyayen mijin muka je da ke NDA. Muka kai musu Amarya sannan da kayan da muka ta ho da shi. Amarya ta samu tarba da kuɗaɗe sosai. Da ya ke suna da kumbar susa ko su gidan iyayen na shi ma a abin kallo ne. Sai a lokacin suke faɗa mana tafiyar su Madina jibi in sha Allahu a ka yi ta fatan alheri. Muna gidan har wajen uku saura sannan muka yi shirin tafiya daman kowacce da shirin ta tun da sun faɗa mana daga nan Kano za a wuce da mu. Nan muka bar Nauwaran Jafar da Farida sai Hajiyar Tafida da Tariq ya riƙe ta wai ta jira shi zuwa gobe zai saka a mai da ita gida. Mu kan mu an ba mu turamen Atamfa kowaccen mu sannan da kuɗi cash 10k sannan a ka ɗauke mu zuwa Kano cikin motocin alfarma kamar yadda a ka ɗauko mu.
Ba mu isa gida ba sai bayan Mangariba kuma suna ijiye mu suka juya zuwa Kaduna. A gidan Anty Bahijja muka sauka tun da ita ce uwar biki ya kamata ta ga dawowar mu, amma ba domin haka ba gidana zan wuce na gaji sannan kasala duk ya rufe ni, tun da muka je ban ci wani abincin kirki ba. Na yi amai duk na galabaita barin ma yau ɗin amma ban ƙi sauka ba. A na ta yi ma na maraba da dawowa muna zaune dukkan mu a falon Anty Bahijja a na ta mai da yadda a ka yi a can Kaduna. Maman Farko na ta faɗin Sulaihait ta yi dacen surukai masu dattako sai fatan zaman lafiya sannan ga labarin kyautar ban girman da a ka yi ma na Anty Bahijja sai faman washe baki take yi. A raina na ce wato kowa na son na shi ya je ya ji daɗi. Amma ta na takura ma wasu in ta ga suna jin daɗi lalle wanzami daman a ka ce ba ya son jarfa.
Tun da muka sauka kowa na ta zuwa mana sannu da zuwa. Tun da akwai sauran jama’a a gidan har Hauwa a gidan muka same ta. Ni ban ma san Gimbiya tana gidan ba sai da na fara ganin Khalipa. Ban ga Jidda ba sai Baby ita ke faɗa mini Jidda na gidan Gwaggon su Zuwaira. > Janaftybaby: Bedroom ɗin da ke falon Anty Bahijja na shiga domin na kama ruwa na yi salla ina shiga na ga Gimbiya ta fito daga cikin tiolet ɗin cikin ɗakin ɗauke da Anwar kamar ta wanke masa kashi ne tun da na gan shi ba pampers. Ina ganinta na washe mata baki ina faɗin.
“Maman Khalipa ashe kina gidan?
Amma sai matar nan ta yi kamar ba ta ji ni ba, gani ni da ita a cikin ɗaki ban dandara ba na sake faɗin.
“Mun dawo yanzu ba daɗewa a na ta hira a falo ban gan ki ba.”
Na saki baki kawai ina bin ta da kallo domin zuwa ta yi ta raɓa ta gefe na ta fice daga ɗakin kamar ba ta san Allah ya yi ni a tsaye a wajen ba. Har ta na banko ƙofar a saman fuskata bam! Jikina ya yi sanyi ban san adadin sakannin da bakina ya yi a buɗe kafin na rufe shi ba. Jikina a sanyaye na shiga tiolet na yo alwala na zo na yi salla da hijabin da na samu a cikin wardrope ɗin ɗakin ina jin na Suhailait ne domin ɗakin nata ne kafin aure ya tashe ta.
Ina idarwa na fito da niyar na ce ma su Munnira ni zan ta fi gida. Sai kawai na ga Gimbiya suna mgana da Naja. Kamar zan wuce na ƙyaleta sai kuma wata zuciyar ta ce na yi mata mgana na ji ko na yi mata wani abu ne da zan yi ta mata mgana tana mini wulaƙanci.
“Anty Sadiya ba dai tafiya ba?
Naja ta faɗa ganin na taho in da suke tsaye a gefen falon suna mgaana. Tana ganina ta wani haɗe rai kamar ta ga mutuwarta.
“E yanzu na ke son tafiya ba na jin daɗin jikina ne.”
“Gaskiya sannu. “
Ta faɗa sai kuma ta juya tana ce ma Gimbiya.”Amai ta yi ta yi a can wallahi.”
Ban san ko maganar ta suɓuce mata ba ne, ko kuma daman da niyya ta faɗa ban sani ba sai ji kawai muka ji ta ja wani ubn tsaki kafin ta ce.
” Mtswww to ina ruwana ni dai mu cigaba da zencen mu. “
Ba ni kaɗai ba hatta Naja sai da ta ji wani iri ina kallonta ta na ma Gimbiyar mgana da ido. Ni ko da farkon da na zo wajen har na sauya shawara na wuce kawai ba tare da na yi mata mgana ba tun da na ga da ta ƙara ganina ta haɗe rai amma kalamanta na yanzu su suka ɓata mini rai ya sa na ce sai na yi mata mgana.
“Amma ko dai ba ruwan ki ai mgana mai daɗi ma Sadaka ne in ji Annabi(SAW)”
Na ma yar mata da martani ina kallonta sai ta wani ɗauke kanta sama jikinta na jijjiga irin ƙiris take jira ɗin.
“Don Allah ki yi haƙuri Anty Sadiya.”
Naja ta faɗa ta na kallona na so na danne zuciyata na yi haƙurin amma sai Gimbiya ta ɓata komai.
“Mi ye na wani ba ta haƙuri an yi mata wani laifi ne?
Ta faɗa tana mini yatsina. Na ga rainin hankali a lamarin Gimbiya fa ya fara yawa tun ina hakuri tana ƙure ni daman kuma tun da na samu cikin nan a wuya na ke abu kaɗan ke ɓata mini rai ina kiyaye mata sabo ni ba sa’ar yin ta ba ce wanda ya ijiye mu ni shi ne daidai da ni tun abun na mu na mu uku ta ja sai da mutane su ka far ga da abin da ke faruwa domin ni dai ba zan yi shuru ina kallonta ta na so ta ci kasuwa a kaina ba.
“Ba ko a yi mini laifi ba. Amma ina tunanin wata ƙila ni na yi miki laifi tun da tun shekaranjiya in muka haɗu a gidan nan in na yi miki magana sai ki yi kamar ba ki jini ba yau ma ban dandara ba ina ganin ki na yi miki mgana kika yi banza da ni. Ni ko Gimbiya me na yi miki da zafi haka? Me na yi miki da ya sa kike jin haushina?
Kawai sai matar nan ta fara ɗaga murya tana faɗin” A a malama ɗan dakata ba na son sharri ni yaushe kika yi mini mgana ban amsa ki ba? Ai ko sai dai in ban ji ki ba. Ni dai ki tsaya da mganar nan a nan ahto domin kar ta je gaba. Yanzu sai ki ji magana a gaba ana ƙokarin ɗora min jarkar tsaba.”
Naja na yi mata mgana amma tana mini rashin kunya har ta na wani ƙara yarfa hannu tana cigaba da faɗin” To Naja haka kurum ina cikin zaman lafiyana ta jawo mini wani masifan. Yanzu nan sai ki ji mgana ta kai kunnen Daddy shi kuma da yake ba ta laifi a wajensa ya hau ni da faɗa. To ba na so mganar ta tsaya iya nan, maganar kin yi maganar na yi banza da ke ban san an yi haka ba wataƙila lokacin da kika yi mini maganar ban ji ba ne.” > Janaftybaby: Ai sai na ma kasa mgana sabida mamaki lokacin har su Munnira sun zagaye mu suna tambayan ba’asi ita kuma Gimbiya Naja na janye ta tana ba ni haƙuri tana ce ma su Suwaiba ba wani abin faɗa ba ne na ce ne na yi ma Gimbiya mgana ta yi banza da ni sai ita kuma Gimbiyar ta ce ba ta ji ba ne. Amma ba faɗa ba ne.
“Ba faɗa ba ne ta ke faɗa minI kar na kai mganar gaba? Wato ga munafuka ko me? Kin taɓa jin wani abu ya faru Yallaɓai ya ce daga bakina ya ji? Ina ruwana da sha’aninki da za ki tsaya a gaba na balle na riƙa hirar ki da miji? Kina gidan ki ina gidana me ye haɗina da ke! Ni ma sha’anin gabana ya isheni ba ni da lokacin wannan sannan ban gane kin ce wai ni daman ba na laifi a wajen shi ba? Me kike nufi? Sannan kina nufin ni zan yi miki ƙarya ne Gimbiya? Na ci riban me? Ke ma kan ki kin san ba ki isa na yi miki ƙarya ba domin isar ki ba ta kai har haka a wajena ba”
“Sadiya me ya faru?
Maman farko da tambayeni lokacin da ta ƙariso wajen ina ƙoƙarin magana kawai sai Gimbiya ta buga shewa tana faɗin” Ahayye. Shi ya sa na ga kin yi ƙutun ƙutun kin tafi Kaduna. To ina fatan kin je kin ciwo abin da ba ki taɓa ci ba ko?
“Ke Gimbiya me ye haka?
Anty Maimuna ta faɗa tana shiga tsakanin mu.
“Ba dai rashin kunya za ki yi ma Sadiyar ba ko?
Anty Zabba ta faɗa. Hauwa ko rike ni ta yi tana cewa kar na ce komai Munnira ko faɗi take yi” Jaruba wallahi kika ce za ki yi ma Sadiya rashin za ki daku a falon nan wallahi.”
Wata shewar ta buga kafin ta ce” Ko ita ba zan da kun mata ba. Ballatana ku yan koren ta.”
“Haba Saudatu”
Maman Farko ta faɗa kamar ranta ya ƙara ɓaci Anty Bahijja ba ta wajen daga baya a ka kirata ta zo dai dai lokacin da Munnira ke sa’in sa da Gimbiya.
“Ni kaina ba kai isar da zan yi sa’in sa dake ba. Ballanata Sadiya ta fi ƙarfin ki. Kuma Kaduna ta je ke ma ya sa ba ki je ba? Kin ga kenan isar ki ce ba ta kai ba ita kuma da na ta isar ya kai miji ya sahale mata ta je duk shi ne haushin na ki? Sorry ki yarinya mijin wata kika aura dole ki zamo ta baya ko kina so ko bakya so. Kuma na san duk wannan kumfar bakin da kike yi ba a kan tafiyar mu Kaduna ba ce, haushi ne baƙin ciki kin ji labarin Sadiya na da ciki sannan Tafida na ririta ta shike nan sai hassadarki ta motsa wato kin so ne ke da kika zo kika aure mata miji sannan kuma ki zama ke ce ke ta haihuwa ita kuma ko oho ko? Sai ga shi ba ke kaɗai ke da Allah ba. Ubangiji na kowa da kowa ne. Ta samu ciki kin kasa ɓoye hassdarki shi ya sa kika zo za ki yi ma mutane rashin kunya. To ba sa’an ki anan kuma duk tsiya dai a baya kika zo sai da aura ta rage sannan kika samu.”
“Ke Munnira”
In ji Anty Bahijja. Maman Farko ba ta yi magana ba Anty Maimuna ce ta ce” Munnira ke ba za ki ba da haƙuri ba sai hura wuta! Wallahi kar na ƙara jin bakin ki”
“Ta yi magana dole fa a mayar mata da martani domin rashin kunya ce za ta yi ma mutane.”
Munnira ta faɗa a fusace. Anty Zabba sai ta yi aikin hankali ta kama hannuna tana faɗin” Ta ho mu je Sadiya kin ga ba ke kaɗai ba ne. Ɓaçin rai kaɗan zai iya shafar abin da ke cikin ki. Munnira ai ta gama mgana taho mu je.”
Har na bi ta, saboda raina ya ɓaci har wani duhu duhu na ke gani amma tabbas Munnira ta faɗa masu zafi shi ya sa ta kasa magana amma Gimbiya ba ta so mganar ta tsaya nan ba sai ta fara masifa har tana fizge hannunta a cikin na Naja da ke riƙe ta, tana faɗin kar ta tanka mgana ta mutu har Maman Farko sai da ta roƙe ta da kar ta ce komai a bar mganan hakanan
“Ahayye. Nanaye baƙin cikin me zan yi niSaudatu! Ai duk haihuwan da za a sake yi ma Daddy sai dai ta biyo bayan haihuwar da na yi masa. Biyu ne amma kamar da goma ne. Irin kuma haihuwar da ba a taɓa masa ba sai da ya auro ni sannan na haifa masa.'”
“Ke Saudatu me ya sa ke b a ki jin mgana ne?
Maman Farko ta faɗa a fusace tana cigaba da faɗin” A na cewa a bar mganar kina ƙara magana?
“Kyaleta Mama ba riba za ta ci ba domin kowa a nan wajen ya san ba ta da gaskiya.”
In ji Suwaiba saboda kowa ran shi ya ɓaci da mganganun Gimbiya. Har na ci burki da zan juya na bata amsa Munnira ta ƙara fansana > Janaftybaby: “Wallahi ƙarya kike yi. Ai am gama yi ma Tafida farar haihuwa tun haihuwan Jidda. Kin san soyayyar a haifa ma ɗa kana tashen samartaka! Kin san girman soyayya auran saurayi da budurwa? Wallahi ko goma za ki ta haifa maza sai dai ki biyo baya amma ba dai ki zo a gaba ba. Kuma in Sadiya ta haihu ki rubuta ki ijiye sai kin gane cewa ke dai kin yi irin na ki haihuwan amma ba dai ki yi irin na Sadiya ba.”
Na so na yi shuru amma sai na kasa saboda na biyu kenan ta na faɗin ta yi haihuwan da ba a taɓa yi ma Tafida ba saboda ta haifi maza ni kuma ban iya haihuwan namiji ba shi ne ban iya farar haihuwa ba.
kawai sai na juya na fizge hannuna daga na Anty Zabba na isa gaban Gimbiya ina kallonta kafin na ce.
” Sau biyu kenan ina jin kina nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. Ban yi miki magana a farko ba amma yau na kasa haƙuri sai na tanka. Gimbiya ni fa Yusuf kaɗai na aura kuma soyayyace ta sa na yarda da shi har ma iyayena suka aminta da shi muka zama a ƙarƙashin inuwar aure. Yau ko mata dubu zan haifa da ɗigon jinin Yusuf wallahi ni Allah ya gama mini komai Gimbiya. Ya tsamoni cikin duba ya yi mini ni’imar da ba kowa ya yi ma wa ba. Haihuwan namiji ko mace ni ban ɗauke shi a wani abu ba. Ɗaya na ɗauke shi. Mata suna da matuƙar tasiri a rayuwar mu da addininmu. Kin manta cewa mace ce ta fara karɓan addinin musulunci a mata? Kin manta da tarihin matar Firauna? Hasiya da irin gwagwarmayan da ta yi domin addinin Allah. Ko kina da labarin Allah ya gina mata gida a Aljannah? To kamar yadda Maza suke da tarihi a cikin addininmu haka ma Mata ke da wannan tarihin. Saboda haka ni in mata Allah zai ba ni ina so in ta haihuwarsu ina roƙon Allah ya shirya mini su. Ya kuma sa su yi ma addininsu hidima. Ke kuma da kike son Mazan saboda tunanin su ne ke da gidan Allah ya yi ta baki ko dubu za ki haifa wallahi tallahi ba zai tsole mini gefen ganina ba Gimbiya. Gargaɗin da zan yi miki shi ne ki daina ƙoƙarin mayar da ƴa’ƴana a baya. Suma ƴa’ƴa ne dai-dai da irin haihuwan da kike tunanin kin yi a kan su Khalipa.”
Ina gama faɗin haka na wuce. Maman farko ta jinjina kai tana na faɗin” Shi kenan Sadiya kin gama mgana.”
Kowa sai ya yi shuru ya yi sanyi ita ko Gimbiya sai ta fashe da kuka jin yadda har Hajiya iya da ba ta san farkon faɗan ba ta na salla sai da ta ce Gimbiya ce ba ta da gaskiya.
“Ko ba ta girme ki ba ai tana gaba da ke a aure.”
“Balle ma wallahi Sadiya ta girme ta. Sai dai ta yi sa’ar ƙanwar ta Amina.”
In ji Munnira, Suwaiba ta karɓe da cewa” Tsaya tsaya ma ko da ma a ce ba ta girme ta a shekaru ba a gidan aure ita ce babba. Kuma bai kamata ta girmama ta ba? Ai kowa ya ji wannan abin da ya faru a san ba ki ta ki gaskiya ba Gimbiyan”
Ni dai ban tsaya ba na ce zan tafi gida. Yau ma tun safe rabon da mu yi waya da Yallaɓai. Anty Maimuna ta ba ni mamaki har da ita a masu ba ni haƙuri Anty Bahijja kuma ta rufe Gimbiya ta faɗa tana kukan munafunci. Tare da Marwa da Munnira muka fita Hauwa ta ce Muttaƙa zai zo ya ɗauke ta. Anty Zabba kuma gidan su ta ce za ta je ta kwana. Amaryan ta ma tun da suka sauka daman gidansu ta sauka bikin ma daga can ta zo.
Muna cikin adaidaita Munnira sai jaraba take yi tana ce mini wai ina yi ma Gimbiya sanyi sanyi shi ya sa ta raina ni.
“Wallahi ta ba ni mamaki ko kunya ba ta ji ba.”
Marwa ta faɗa cikin mamaki. Munnira ta ce”To daman tana da kunyar ne! Wallah ba ta da kunya ta daɗe tana neman da man da za ta ci kasuwa a kan Sadiya.”
“Sai me? Don Allah ku bar mganar ni wallahi raina ma ƙara ɓaci yake yi “
Na faɗa ni a ƙokarina su bar mganar amma Munnira ba ta bar ta ba sai masifa take yi tana cewa na faɗa ma Yallaɓai domin ya dauƙi mataki.
“Ni ba ruwana ba ki ji ta ce kar na kai ta gaba ba.”
“Ki kaita ɗin domin ta san kin isa.”
Shuru na yi ban yi magana ba. Saboda ni ba halina ba ne wannan surutun, abubuwa da dama sai dai ya ji su can a bakin ƴan gidan su. Ni bar ni da mgana in na ga za a cuce ni ko magana kan lamarin da ya shafe ni amma ba ruwana da mganar kishiya. > Janaftybaby: Ko kafin ma ya yi aure ko hatsiyar mu da yayyen shi ban taɓa faɗa masa sai dai in ya ji labari ya zo ya tambaye ni amma ba dai ni na kwashi jiki na je ina ce masa an yi kaza an yi kaza ba. Shi ya sa yau ɗin ma na yi shuru amma har a ƙasan raina ba zan faɗa masa ko da kuma ba zai ji labari ba amma dai ina da yaƙinin tabbas zai iya sani.
Mu mai adaidaita ya fara saukewa sannan ya wuce da Munnira. Allah ya so ni ga Marwa ina komawa gida na kwanta sai zazzaɓi ita ce na samu ta dama min kuni na sha ya zauna a cikina. Ni saboda bacin rai ko Baby ban nema ba da zamu taho. Sai kawai na ce gobe sai su dawo tare da Jidda. Haka Yallaɓai ya zo ya same ni a kwance ya yi ta faɗan sai da ya ce ba ya son na je Anty Zuwaaira ta matsa sai an je da ni gashi nan na dawo ba ni da lafiya sai da na ce masa ba fa komai ba ne aman da na yi a can sai ɗan zazzaɓi kuma ya san ina yin zazzaɓi haka daddare sannan ya ɗan sarara da faɗan da ya fara
Paracetamol ya ba ni na sha na yi sallah na kwanta sai na ji daɗin jiki na zuwa safe kuma sai na ji ya sake ni. Marwa ta gyara minI gida ta yi mana abin kari itama da safen ta wuce Ɗorayi za ta gai da su Gwaggo. Daga can ta wuce gidan su ta kwana da safe ta wuce Rano. Iya kwanakin da Kawu ya ba ta kenan. Ni kaɗai a gida domin Yallaɓai da hantsi shima ya fita, sai can bayan la’asar dai ga shi an kawo su Jidda. Ita na samu ta yi girki ni kuma na ce ta dama mini kuni domin wanda Marwa ta dama min tas na shanye shi kuma shi kaɗai na ke samu ya na zama a cikina sai ganye haka irin su Kabeji, latas da allayahu. In a ka sanya su a cikin abinci ina samu na ci sosai. Amma wani kifi wani nama ko warin shi ba na so balle su ƙwai da sauran nau’ikan abincin da ba na so ma na ji warin su in ana dafawa. Ni warin ma maggi mai star ne kwata kwata ba na so shi ya sa na daina ma giftawa ta Kitchen ɗin na bar ma Jidda ne ban san yadda yake ciki ba, domin na daɗe ban shiga cikin sa ba.
Har a ka kwarari kwana huɗu da dawowata gida ban ji Yallaɓai ya yi mini wata mgana ba. Sai ranar jumma’a ranar ma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne.
Yau Mubeenan Musbahu ta zo ta yinin mini ita ta yi girki da gyaran gida. Tun da ya ga ba ni da lafiya yana yawan turo ta gidana kuma ina jin daɗin haka. Sai dare Musbahu ya zo ya ɗauke ta shi ya sa na koma ɗaki na kwanta saboda na ji na fara jin sanyi sanyi. Ina cikin bargo ina shafa kasan marata cikina ya shiga wata na huɗu kuma har ya fara turowa. Ina jin ƙaunar abin da ke cikina sosai wata ƙila don irin wahalan laulayin da na ke sha ne na tuna kafin bikin Suhailat maganar da muka yi da Yallaɓai.
“Yallaɓai in na mace na haifa sunan Mama za mu saka mata.”
“In kuma Namiji ne to sunan Alhajin Ɗorayi za mu saka masa ko?
Ya ƙarishe mini yana dariya. Nima dariyan na yi kafin na ce” Ka yi gaskiya. Tabbas haka ne a raina.”
A lokacin jawo ni jikinsa ya yi yana faɗin” Kar ki damu fata na ki sauka lafiya duk sunan da kike so shi za mu sanya kin ji ko?
Sai na ji daɗi har ina ba shi sumba.
Vibration ɗin waya ta ne ya dawo da ni daga tunanin da na faɗa. Ta na gefen in da na ke kwance ne na saka hannu na ɗauko ta sai na ga Yallaɓai ke kirana. Ban kawo komai a raina a tunanina sallama zai yi mini kamar yadda ya ke yi in bai samu zuwa ba.
“Zan taho da Daughter yanzu ina so mu yi mgana gabaɗaya.”
Abin da ya ce minI kenan bayan mun gaisa. Sai na ce masa sai sun taho. Har muka gama wayar tunanina bai hasaso mini kan abin da ya faru ba ne sai daga baya na fara tunanin wataƙila kan haka ne amma kuma a ina ya ji? Ko wa ya faɗa masa? Watsar da tunanin na yi saboda ba ni da mai ba ni amsar su.
Sai da suka zo gidan sannan na fito daga ɗakin na saka hijabi amma duk wanda ya gani ya san ina fama da azaban laulayi duk na yi fari na lashe na kuma rame. kullum ina fama da bushewar baki da maƙogwaro. Ina ganin Gimbiya sai na tuna da faɗan da ya shiga tsakanin mu da ita shi ya sa na yi kamar ban gan ta ba kamar yadda itama na ga ta yi, sai wani cin magani take yi tana wani hura hanci. > Janaftybaby: Shima gogan ransa a ɓace na gan shi da ga gani sun yi ta ne kafin su ƙariso. Jidda ya haɗa da yaran gabaɗaya da cewa su koma falon su za mu yi mganam ita ta tattara su suka bar mana falon. Shi yana saman kujera mai zaman mutun uku ni kuma ina zaune a mai zaman mutum biyu a gefen sa ita kuma sai ta zauna kan mai zaman mutum ɗaya muna fuskatan juna ni da ita. Ai ni tun da ta yi mini wannan wulakancin na yi alƙwarin duk in da za mu haɗu in ba ta ce sannu ba ba zan tanka ta ba. Da mutumcina ba zan zauna wacce ba ta isa ta zubar mini da ƙima ba.
“Ba ku gaisa ba?
Ya faɗa bayan ya kore shurun namu gabaɗaya.
“Tsakanin ni da ita wa ya zo ya samu wani?
Na tambaye shi ina mai kallon shi da idananuwa da suka ƙanƙance.
“Ita ce “
Ya faɗa yana kaɗa kai, ni ban yi magana ba sai shi ne ya kalleta kafin ya ce” Ki gaishe ta mana.”
Ta yi shuru taƙi mgana ni dai kaina na ƙasa ina wasa da gefeb hijabina da ya sani bai ɗauko mini ita ba. Ta zo har falo na tana yi mini Taƙama.
“Ba da ke nake mgana ba.”
Na ji ya da ka mata tsawa.
“Ina yini.”
Ta faɗa kamar dole. Ko da ya ke ai dolen ce ya saka ta.
“Ke kuma ki amsa tun da ta gaishe ki.”
Ya faɗa muryansa a sama daga gani yau an taɓo zuciyar ƴan maza.
“Lafiya lau.”
Nima na faɗa a tsume saboda ni ba gan amfanin wannan zaman ba tun da wacce ta yi laifin ba ta ji a karan kanta ta yi nadamar abin da ta yi ba.
“Hakan da kuka nuna shi ne ya ƙara tabbatar mini akwai wani abu da ya faru a tsakanin ku wanda kuka rufe ni ba ku gaya mini ba. Ban sani ba ba domin Kawu Abba ya kirani ya faɗa mini ba, sannan Maman Farko ma ta kira ni ta ce na tara ku kun samu yar hatsaniya ranar a gidan Bahijja amma cikin ku a ka rasa me faɗa mini wani abu ya faru? Me ya sa haka?
Dukkan mu muka yi shuru. Ni sai da ya faɗa sannan na gano in da ya fara samun labari. Wato Marwa ce ta sanar ma da mijinta shi kuma ya kira Yallaɓai ya faɗa masa. Sai Maman farko da ta yi masa mgana ashe ita ma mara kunyar ba ta faɗa masa ba.
“Daku fa na ke mgana?
“Me ya sa ba ku faɗa mini ba?
Ya faɗa yana ɗan sausaauta fushinsa saboda ya yi ƙasa da muryan sa.
“Kasan daman ni ba halina ba ne na tare ka da mganar an yi kaza an yi kaza. Ballatana matarka daman ta ce ni ce ke kai ta gaba a wajen ka.”
“Wannan ba Hujja ba ne. Ke ce babba bai kamata ki same ni ki faɗa mini wani abu ya faru ba?
Ba na so mganar ta yi tsayi ya sa na ce” Ka yi haƙuri na yi kuskure.”
“Gaskiya ban ji daɗi ba. A ce sama da kwanaki ban san wani abu ya faru da matana ba sai wasu ne za su kirani suna faɗa mini ? Kun yi mini adalci kenan?
“Ka yi haƙuri.”
Na sake faɗa ita hajiyar tana zaune tana karkaɗa kafa ba ta yi mgana ba.
“Ya wuce. Amma kar a ƙara irin haka ba na so. Duk abin da zai faru da ya wuce ku biyu wasu suka sani to nima ya kamata na sani ɗin”
“In sha Allahu.”
Na faɗa ina muskutawa domin na gaji da zama duk na takura.
“Me ya faru ne a tsakanin ku da a ka ce kun yi sa’in sa a gaban mutane? Yaushe kuka fara sa’in sa a tsakanin ku ni ban sani ba?
Tambayar gabaɗayan mu ya yi mana. Amma ni ban ce komai ba ita kuma sai ta fara faɗin” Ai na ɗauka ka san duk abin da ya faru.”
“Na sani zan zo in tara ku ina tambayar ku?
Ya faɗa a ɗan fusace ganin ya harzuƙa ya sa ta fara mgana a ƙoƙarinta na ta juya mganar tun da ta fara faɗin wai na ce na yi mata mgana ta yi banza da ita. Ita ba ta ji ba ne amma shi kenan na fara faɗa ina faɗin ta ji da gangan ne.
“Sadiya”
Ya katseta da kiran sunana sai na ɗago kaina ina amsawa.
“Na’am”
“Ki yi mini bayanin abin da ya faru daga farko.”
Na buɗe baki zan yi mgana ta tare ni da cewa” Ni ba ka yarda da ni ba sai ita kenan?
“E. Ai ita na fara sanin kafin ke. Saboda haka ita zan fara ba ma Amincina kafin na baki “
Sai ta yi shuru bayan ta koma ta haɗe rai tana faɗin.
“To ai shike nan.”
Ni dai ban bi ta kanta ba na yi masa bayanin duk abin da ya faru tun daga farko. Ban ɓoye masa komai ba har mganganun da na gaya mata da wanda su Munnira suka faɗa mata duka na faɗa masa na ƙarishe da cewa” Na yi ƙoƙarin na danne zuciyata amma na kasa. Saboda na ga ta na ta nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. > Janaftybaby: In su ta ce farar haihuwa ne su kuma su Jidda ɓakar haihuwa take son ta kira su? Ta fada mganar nan ba sau ɗaya ba kuma sau biyu ba. Shi ya sa na tanka mata har ta kai mu ga sa’in sa”
Sai ta taso mini tana faɗin” Ni yaushe na ce su baƙar haihuwan? Ni fa ba haka nake nufi ba. Munnira ce ta ce wai ina bakin ciki da kin samu ciki ni ko na ce me zai dame ni,? Ni da na yi farar haihuwa..”
“Shutup.”
Ya katse ta bayan ya da ka mata tsawa. Sai ta yi shuru ta na wani nuƙufarci.
“Har kina sake maimaitawa?
“To ai na ga ba.”
“Ki rufe mini baki na ce ko?
Ya sake mata tsawa har ya na miƙewa kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin” Ni shikenan ba za a bar ni na yi mgana ba. To da yake ita kake so ai ka bar ta ta yi mgana ni kuma da a ka tsana ina mgana kana mini tsawa.”
“An hana ki ɗin. Kuma ba a son ki ɗin, an tsane ki, ki yi abin da za ki yi wawuya kawai “
Kamar famfio sai ta ƙara ma kukanta volume.
“Ki yi mini shuru na ce ko?
Ya sake faɗa a fusace dole ta kama bakinta ta koma tana haɗiyan zuciya.
Shima sai ya koma ya zauna yana sauke numfashi kafin ya kalleni yana faɗin” kin yi mini laifi Sadiya. Me ya sa da kika yi ta mata mgana tana miki wulaƙanci ba ki faɗa mini ba! Da tun lokacin zan faɗa mata ko ni da nake aurrn ki ba ki taɓa mini mgana na yi miki haka ba ballatana ita ? Sannan mganar tun da kika samu ciki ba kya laifi a wajena sai ki faɗa mata tun kafin ki samu ciki ke ɗin daman ba kya laifina a wajena ko za ta ɗau mataki ne? Wallahi da kin faɗa mini da na ci mata mutumci da ba ta isa ta tare ki da wata mgana ba.”
“Ka yi hakuri.”
“Kar ƙi kara ganinta ki ce za ki yi mata mgana. Umarni ne daga ni na ce duk in da kuka haɗu ita ce za ta fara gaishe ki “
“Tabɗijam”
“Ko ba za ki bi Umarnina ba ne?
Ya katse ta a fusace kamar zai kai mata duka.
“Na ji.”
“Wallahi tallahi kika kuskura na sake jin kin yi sa’in sa da Sadiya sai na nuna miki kalata. Haba. Ke ba ki jin lallashi ne? Wani irin haƙuri ne ban baki ba ? In Sadiya ce wallahi umarni ɗaya nake ba ta ta bishi amma ke sai yanzu za ki fiddomin sabbin hallaya? Haka kike daman? Ko zuga ki a ke yi! To in ma zugi ne ba ki isa ki ce ni za ki juya ni ba. Ni ba batulu ba ne kafin na same ki da Sadiya kika ganni. Kin san faɗin tashin da muka sha tare kafin mu kawo a lokacin da kika aure ni? Kin san gwagwarmayan da muka faro ta da ni da ita kafin zuwan ki? Ni ban raina ta ba sai ke? Ki raina mini mata sannan ki na neman ɓata mini ƴa’ƴana? Har kina dukan ƙirji da kin yi mini farar haihuwa? Na taɓa faɗa miki na bambamce tsakanin su Khalipa da su Jidda ne? Ban da ba ki da tunanin ba su Jidda na fara samu kafin su Khalipan ba? Dukkansu ƴa’ƴana ne kuma ina son su amma mace ko namiji ba wanda ya fi wani a wajena. Na rantse da wanda raina ke hannun shi Saudatu in na ƙara samun labarin kin ce ke farar haihuwa kika yi sai na saɓa miki. Saɓawa mafi munin da ba ki taɓa sanin haka nake ba “
Ya dakata ya na sauke numfashi ita kuma tana ta kuka.
“Ki bata haƙuri. Kuma wallahi in kuka ƙara haɗuwa ko kallon banza kika yi mata in na ji labari ni da ke ne.”
Ba ta da yadda ta iya ne ya sa ta ba ni haƙuri tana kuka.
“In ba ɗan adam da manta alheri ba wani wahala da kara ne Sadiya ba ta yi miki lokacin da kike da cikin Khalipa ba? Har kin manta yanzu ba ki da abin ciwa mutumci sai ita? To bari ki ji ki sani in kika tozarta Sadiya kamar ni kika tozarta. Tozartani kuma da-dai yake da kin tozarta auran ki. Ita da zuciya ɗaya take zaune da ke amma ke ki zo ki auran mata miji kuma ki hana ta zaman lafiya? To ba ki isa ba ki shiga taitayin ki da ni wallahi in ba haka ba ki kasa gane kaina”
Sai kuka take yi ta kasa mgana ina ga ba ta yi tunanin lamarin zai ɓare da ita kamar haka ɗin ba. Yallaɓai ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba har sai da ta koma tana ba ni tausayi.
“Ka yi haƙuri ma na Yallaɓai.”
Na faɗa ina so ya bar mganar amma bai bari ba sai da ya gaji don kan shi sannan ya koma yana sauke numfashi.
“Itama ta yi haƙuri kan mganganun da ta ce Munnira ta faɗa mata.”
“Ai ba mganar haƙuri duk mganar da ta faɗa gaskiya ta faɗa mata. Saboda haka ba wani mganar a bata ma haƙuri.” > Janaftybaby: “A’a ka saka ta ba ni haƙuri nima ba laifin in na ba ta haƙuri.”
Sai ya yi shuru ni kuma sai na juya ina kallonta kafin na ce” Ki yi haƙuri kan mganganun da na faɗa miki har da wanda ma su Munnira suka yi. Hakan ba za ta ƙara faruwa ba.”
Ba ta yi mgana ba sai jan zuciya kawai take yi. Yallabai ya yi mgana ta ƙarshe shi ne kar ya sake jin labari makamcin wannan ya sake faruwa in hakan ya sake faruwa kowacce cikin mu ke da laifi zai haɗa mu ne gabaɗaya ya hukuntamu.
“In sha Allahu hakan ba zai ƙara faruwa ba. Ka yi haƙuri.”
“Na gode Sadiya ta.”
Haka ya ɗauke ta suka koma. Ni na san za su kwana ba zaman lafiya domin a fusace ta fita haraba yaran ma shi ya tsaya ya taho da su. Ni dai a raina na ce ku ƙarata faɗan da ba ruwan ai daɗin kallo ne da shi. Sannan daman in har ka rike gaskiya a je dai a dawo wata rana kai ke da nasara.
Tun da ya yi mana wannan sulhun ban ƙara bi ta kanta ba har aka zo a yi sallar babbar salla ba mu ƙara haɗuwa ba sai a Gwammaja a falon Nene da ya ke ba a sallar idi saboda corona yadda ta gaisheni ba fara’a nima haka na amsa mata cikin yanayin da ta gaisheni. Nene ta ji labari ta sake kiran mu har cikin ɗakin ta ni da Gimbiyar ta sake yi mana faɗa, ni dai na ce mata na yi mata alƙwarin hakan ba zai ƙara faruwa ba. Itama ta ce ta bari ba za ta ƙara ba.
Amma har muka bar gidan nan ba mu ƙara ma zama a inuwa ɗaya ba. Kowa na harkan gaban shi, Munnira ta dame ni sai da na faɗa musu tara mu da Yallaɓai ya yi amma ban faɗa musu masifan da ya yi ta mata ba amma dai na sanar da su ya ce in muka ƙara haduwa ita ce za ta riƙa gaishe ni.
“Da kyau. Tafida daman ai Namiji ne.”
Ni dai ban ce komai ba. Saboda namiji ne mai canza launi baƙin cikin sa kuma amarya da uwargida duk sun kurɓe sa. Shi ya sa don ya yi wannan faɗan zuwa Gimbiya bai saka na ji daɗin haka ba wata rana ni kaina zai iya yi mini haka kuma a gabanta. Abu ɗaya na ji daɗin shi yadda ya nuna mata shi a wajen shi daga mace har namiji duk ɗaya suke kuma ya nuna mata ina da daraja ta nan kawai ya burgeni.
*
Haka lokaci ya ci gaba da tafiya tun ina sa ran za a buɗe gari har na fidda raina. To ko an buɗe gari ina mganar komawa makaranta ina fama da kaina. Jdda ma nake ji itama daga farko ne ta damu daga karshe sai ta saki jikinta kawai zaman gida dole. Ko Tahfiz ɗin su babu duk wata makaranta an daina yin ta in dai za ta haifar da cunkosun jama’a. Ni kuma gefe ɗaya ina cigaba da renon cikina da ya shiga watani shidda har na fara zuwa awo a nan asibitin Aminu Kano AKTH.
Cikina ya fito daga gani cikin zai yi girma wannan karon. Allah ya taimake ni lokacin da ya shiga watani biyar sai na dawo da cin abinci kamar gara shi ya sa cikin wata ɗaya na mai da jikina har na fara haɗa wata kiɓa. Kumatuna sun yi luhu luhu wuyana har ya na neman haɗewa saboda kiba. Abincin na ke ci kamar hauka a rana sama da sau huɗu har cikin dare, yanzu tea na saka ma ƙahon zuƙa madara ba ta sati ta ƙare har Yallabai sai da ya ce wato abincin da ban ci ba ne a baya na ke famshewa. Kowa ya ganni sai ya ce Sadiya cikin nan ya buɗa ki? Shi ya sa hancina da bakina suka yi girma saboda yadda fuskata ta ciko sosai.
***
Lahadi.
August, 2020
Lahadin ƙarshe mako ne Yallaɓai a gidana yake tun ranar jumma’a ya je Abuja sao jiya da daddare ya dawo. Can ma aiki ya samu na gina ma’aikatan sarrafa leda ba ya samun hutu sai a yi ƙarshen mako sama da biyar bai kwanta a gida ya huta ba. Jiya ma ya dawo da daddare mun daɗe muna hira saboda ni tun da cikina ya shiga wattanin sa na shidda na daina barcin dare sosai amma ina yi na rana hani’an.
Faɗa mini yake ba shi da kuɗi ya kwashe ya saka a ginin ma’aikatan shi, ga wannan aikin sai da ya ɗan ci bashi daɗin sa ma sun ce za su ba da rabin aiki rabi kuma sai an gama. Ga na Dutse bai kamallah ba amma an kusa sai ya raba yaran na shi uku. Biyu ya kai su Abuja. Kaɗan kuma suka zauna a Dutse suna ƙarisawa. Wasu kuma suna na ma’aikatan shi duk sauran aikin kaɗan ne. Kofofi ne suka rage sai fanti da sauran ɗan abin da ba a rasa ba a gama. > Janaftybaby: Shi damuwar shi in an gama aiki furnitures ɗin da za a sanya a a wajen ne tunanin shi ya so ya yi oder ɗin ko da rabi ne amma bai samu ba sai na bashi shawaran ya bi komai a hankali in an gama aikin Dutse an gama biya sai ya yi oder ɗin ko rabi ne Allah bar shi daga ya siya saura. A yadda ya faɗa mini yana so a farkon shekaran 2021 kamfanin shi ya fara aiki a sabon gini. Ni na yi ta kwantar masa da hamkali har wajen biyu na dare sannan muka kwanta da asuba kuma bayan mun idar da salla ya ce sai ya yi barnan ruwa. Ni dai ina tura baki aka yi a ka gama maganar gaskiya cikin nan ba ya son ɓarnan ruwan nan shi ya sa ya ce bai ji daɗin da ba irin cikin Baby na ƙara samu ba ina hararan shi na ce wato ya so ne ya ƙara samun damar da zai ta shagalin sa ya ce kamar na sani. Tun da ya kwanta ya ke barci har azahar.
Ganin azahar ta yi ya sa na tashe shi wajen ɗaya da rabi. Da ƙyar ya tashi ya yi sallah ya so ya koma barci na ce masa don Allah ya bari ya yi wanka ya karya. Wanka ma ni na taya shi na gaggasamai jiki saboda ya ce ko’ina ciwo suke yi masa.
‘”Wai ni hala ƙankare nan kake ɗauka a saman kai ne?
“Ba na ɗauka amma in ta kama ina ɗauka. Kamar yadda suke yini a tsaye suna aiki nima a matsayina na Injiniya mai kula da aikin kamar haka ne a tsayen na ke yini.”
Cikin tausayawa na ce” Sannu. Allah ya tsare mana kai mijin mu.”
Na faɗa ina danna masa kafaɗunsa lokacin ina sha masa vesiline ne.
Ya amsa da Amin yana dariya.
“Ko in shafa ma ka man zafi ne?
“Yauwa shafa mini Allah ya yi miki albarka.”
Dirowan gado na jawo na ɗauko na fara sha fa masa kafaɗunsa zuwa bayansa ya na tambayana in da na samu man zafi na ce Gwaggo ta ba ni ta ce na riƙa shafawa a kafafuna da suke kumbura.
“Ba kumburi ba ne tsabar cin abinci ne ko?
Ya faɗa yana dariya sai na lakato na shafa masa a fuska ya ji zafinn yajin ya sa ya kare fuskarsa yana faɗin” Makanta ni kike son yi Sadiya?
Ni kuma ina ta dariya ina faɗin” Ka kara cewa ina da cin abinci. Wai ba ɗanka ba ne ke saka ni cin ba?
“Shi ne.”
Ya faɗa yana danne dariyan shi. Haka na gama shafa masa muna hira nima har sha fa mini ya yi a ƙafafun nawa sannan ya saka kaya. Yau a bedroon na kawo masa abin ƙarin bayan ya gama na kwashe na mai da kitchen su Jidda ma sai da suka biyo sa suka gaishe shi a ciki.
Nan na bar shi na je falo muna duba hijabai ni da Jidda. Jiya suka iso na ce ta ɗauko list mu cire ma waɗanda suka saka oder. Can na ɓata lokaci ko da na koma ɗaki na ɗauka zan gan shi ya na barci amma sai na iske shi zaune yana waya ina shigowa ma ya gama wayar.
“Yallaɓai ba ka kwanta ba?
“Yanzu waya ta tashe ni.”
Sai na zauna kusa da shi ina matsa masa kafaɗanshi.
“Sun daina ciwo?
“Sun yi sauƙi.”
Ya faɗa yana kallona. Sai na sake shi ina faɗin” Yallaɓai ni fa ina son ka fara koya mini mota.”
Daga maganar arziƙi sai kawai na ga Yallaɓai ya kalleni ya wani kwashe dariya.
“Mota? A hakan ne za ki koyi mota?
Ya faɗa ya na kallon cikina. Sai na fusata a kuma fusacen na ce” E a hakan ko ba za ka koya mini ba ne?
Na fada ina haɗe fuskata ganin yana ta mini dariya sai ka ce na faɗin abin dariya.
“Ko ba za ka koya mini ba ne. Na je wajen da ake biya na koya?
“E to gaskiya domin ni ina na ga lokacin koya miki mota fisabilillahi Sadiya? Wai ma to ke kina da motar ne da kike son koya?
“Ba ni da shi amma ina da niyar siya ne”
“Da wani kuɗin?
Yallaɓai ya faɗa har yana tagumi.
“Da kuɗina mana”
“Kina da kuɗi ne da man?
Tambayoyinsa sun fara ƙular da ni ya sa a ɗan tsume na ce.
“Ai ba zaman banza nake yi ba kasan ina da sana’ata.”
“Wai da riban hijaban ne za ki siya mota da man?
Sai kawai na kalle shi na kasa mgana. Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba har ya na duƙawa rike da ciki.
“Ke yanzu daman kin san riba ake samu haka tsagwa gwa shi ne ba ki faɗa mini na saka hannun jarina ba? To wai kamar nawa yanzu kika tara na siyan motan?
“Ban sani ba.”
Na faɗa a fusace ina mikewa da cikina gaba. Har na bar ɗakin Yallaɓai na tintsira mini dariya abin ya yi mini ciwo. Kuma wallahi zan bashi mamaki da ni yake zencen.
*Janafty* > Janaftybaby: