Turken Gida – Chapter Thirty-four
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Sama da mintina goma da fitar Yallaɓai amma na kasa ko da motsa ɗan yatsa na saboda da al'ajabi daga mgana sai cibi ya zama ƙari.? Har ya na min wani gorin ya na kirana Abar ƙaunarsa ni na saka shi? Ban da ma gulma yaushe ne ya fara kirana da wannan sunan? Ba sai da ya yo min kishiya ba ne ya fara min sanaben kirana da sunaye kala kala. Sannan in zai kirani da wannan sunan sai in zai min. . .