Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    A hankali na riƙa buɗe idanuwana da suka yi mini wani nauyi. Da farin POP da a ka yi rufin ɗakin na fara cin karo, a hankali na juya dama da haunina amma na rasa fahimtar a in da nake, kamar dai ƙaramin ɗaki ne sai da idanuwana suka sake washewa sannan na soma fahimtar in da na tsinci kaina.

    Da ƙyar na miƙe zaune, ina sake bin ɗakin da kallo in har idanuwana sun ganin min daidai in kuma ba mafarki na ke yi ba tabbas ina asibiti kuma a gadon asibiti. Sakamakon ɓarayin hannun damana da na kalla sai na ga hannuna saƙale da abin ƙarin ruwa da na ɗaga idanuwana sama kuma sai na ga ruwa ake ƙara mini. Ɗis! Ɗis haka na ƙura ma saukan ruwa ta cikin ma zubar sa zuwa cikin jikina idanuwana jikina na bi da kallo sai na ga ba kayan da na baro gida da su ba ne jikina ba. Wata doguwar riga ce a jikina wanda in dai ban yi kuskure ba kayan Amina ne a jikina.

    “Me ya faru da ni?

    Na faɗa a sarari saboda na kasa tuna komai. Na kasa tuna lokacin da na tsinci kaina a gadon asibiti. Ɗakin ba kowa sai ni kaɗai kamar irin daƙunan ne na VIP. Kaina na dafe da hannuna na hagu jin ya ɗan saramai ina tunanin lokaci na ƙarshe kafin a hankalina ya gushe. Tabbas a gidan Amina na tuna ina cikin Toilet ɗin ta ina amai daga nan sai na ga jini. E tabbas na ga jini daga nan ne na fita hayyacina ban ƙara sanin in da kaina ya ke ba sai yanzu da na tsinci kaina a gadon asibiti.

    “Innalillahi.”

    Na faɗa Daidai lokacin da na shafa kasan marata na ji kunzugu. Da gaske ne na yi zubar jini amma me ya kawo mini zubar da jini? Damuwa ce da firgici suka kawo min zuwan period ba tare da lokacin sa ya yi ba. Haka na faɗa ma kaina a cikin zuciyata. Yanayin lokaci nake so na fahimta amma na kasa ganewa. Sakamakon ɗakin akwai wutar lantarki sannan window ɗin ɗakin ya na nesa da ni. Sai dai duk da haka na ɗan fahimci akwai haske daga waje kenan duk abin da ma ya same ni bai daɗe ba tun da har yanzu dare bai yi ba akwai sauran rana.

    Na muskuta kenan na gyara zama daidai lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin a ka shigo. Na bi wacce ta shigo da kallo Nurse ce domin fararen kaya ne a jikinta wata yar mai ƙiba da ita.

    “Sannu ya jikin na ki?

    Ta faɗa bayan ta ƙariso gaban gadon da na ke zaune.

    “Yauwa. Da sauƙi”

    Na bata amsa a hankali ita kuma sai ta saka hannu ta dauƙo wani fayel da ke saman ɗan teburin da ke gefen gadona ta buɗe ta na dubawa.

    “Don Allah wa ya kawo ni nan?

    Sai da ta kalleni kafin ta cigaba da duba fayel ɗina na ma ɗauka ba ta ji ba ne.

    “Dr Ibrahim Aliyu.”

    Sai na kalleta amma na kasa mgana saboda na kasa tuna waye na sani mai wannan sunan.

    “Jiya tare da wata mata suka kawo ki.”

    “Jiya?

    Na faɗa cikin mamaki har ina waro ido.

    Ijiye fayel ɗina ta yi lokaci ɗaya ta na cire min ƙarin ruwan da ke hannuna kafin ta cigaba da faɗin.

    “Yes. Sun kawo ba kya cikin hayyacin ki. Kin farfaɗo amma muka sake mai dake da alluran barci.”

    Kallonta kawai na ke yi na kasa magana. Tun jiya na ke asibiti ban sani ba? Me ya same ni haka?

    “Na cire miki ki ɗan huta. Zuwa an juma sai a mayar miki da shi”

    Har ta juya za ta tafi na kasa haƙuri.

    “Sister don Allah me ya same ni?

    Sai ta juyo ta na kallona kafin ta kaɗa kai ta na faɗin.

    “Miscarriage

    “Miss cra gge.”

    Na maimaita a rarrabe.

    “Yes. Kin samu ɓarin ciki ne a jiyan.” > Janaftybaby: Ta na gama faɗin haka ta juya ta na faɗin” Matar da suka kawo ki jiya ita ta kwana da ke. Ta je gida ta dawo nan ba daɗewa ba.”
    Tana gama faɗin haka ta fice lokaci ɗaya ta na jawo min ƙofar ɗakin har sai da ta ɗan ba ta sauti.

    “Ɓari? Wani irin ɓari kuma?

    Domin sai na ji tunani ya tsaya cak na kasa fassaran ma’anar maganar Nurse ɗin.

    “Daman ana ɓari ba a samu ciki ba?

    Tambayar da na yi ma kaina a fili kenan kafin na samu amsar ta an sake buɗe ƙofar ɗakin an shigo. Da rinannun idanuwana da suka yi min nauyi da na ɗaga ina kallon mai shigowa.
    Amina ce a kan gaba sai megidanta biye da ita ɗauke da kwando a hannunsa ita kuma riƙe da ledoji guda biyu suka shigo ɗakin sai da na gan su ne sannan na tuna da sunan da Nurse ta faɗa min. Tabbas mijin Amina ne Dr Ibrahim Aliyu malami ne a jami’ar Kaduna. Da ya ke kuma sai da ya haura arba’in san da ya auri Amina shi ya sa duk wanda ya gan sa zai san ba yaro ƙarami ba ne.

    “Ya Sadiya kin tashi?

    Amina ta katse mini tunanina sai na kalleta ta zauna a gefen gadon ta na mai riƙo hannuna mara kanular.

    “Ya jikin na ki? Jiya kin ba ni tsaro wallahi.”

    Ta faɗa ta na yar dariya lokaci ɗaya ta na kallon mijinta.
    Kallonta kawai na ke yi na kasa mgana domin sai na ji bakina ya yi min wani irin nauyin da na kasa furta harafi ɗaya daga bakina.

    “Maman Jidda ya ƙarfin jikin na ki?

    Sai a lokacin na ji na yi magana bayan na kalle shi.

    “Da sauƙi Dr. “

    “Ma sha Allah. Allah ya ƙara lafiya.”

    Na amsa da Amin a saman leɓe na. Ita kuma Amina sai ta miƙe ta nufi kwandon da suka shigo da shi ta na tambayana me zan ci? Dr na gefe ya ce ta fara haɗa min tea ne ya warware min ciki tun da tun jiya ban ci wani abu ba.

    “Kenan da gaske ne tun jiya na ke asibtin cikin rashin hayyaci?

    Tambayar da na yi ma kaina kenan ban samu amsarta ba Amina ta haɗo min tea ta kawo min na karɓa hannuna na ɗan rawa sai Amina ta taya ni riƙewa da hannayenta ta na faɗin.

    “Har yanzu jikin na ta ba ƙarfi.”

    “Kin san daman sai a hankali.”

    Dr ya amsa mata lokaci ɗaya yana duba wayarsa da ke hannunsa.

    Ina ta taimakamin ina shan tea ɗin da cokali, Dr ba daɗe ba ya ce zai shiga cikin makaranta Amina ta sakar min kofin ganin saura kaɗan ta miƙe domin yi masa rakiya.

    “Allah ya ƙara lafiya Maman Jidda.”

    “Amin Dr. Na gode da ɗawainiya da ga zuwa baƙun ta na zo muku da hidima.”

    “Haba bakomai. Ai lalura ce Allah ya ƙara afuwa.”

    “Amin”
    .
    Na amsa a hankali, sun fice ina mai bin su da kallo kawai sai ina hakaito kaina ni da Yallaɓai. Yanzu itama Amina watan wata rana Dr zai iya nuna mata halin su na Maza ranar da ya yi aure. Wata ƙila shi kuma ba irin Yallaɓai ba ne, wataƙila shi ya san me ake kira hallaci. Duka na shanye tea ɗin domin ina jin jikina fayeu kamar takarda kuma ina jin yunwa kaɗan amma ba da yawa ba sai dai kuma ruwan zafin ya taimaka wajen farfaɗo da bushewar da cikina ya yi tare da maƙogwaro na har da saman labɓana.

    Ji na yi marata kamar ta ƙulle ina jin fitsari sai na yi ƙoƙarin miƙewa tsaye a hankali, sannan na ijiye kofin saman drewer ɗin gefen gadon da na ke kwance. Sai a lokacin na fahimci ko hijabi ma babu a jikina daga ni sai rigar nan sai ɗankwali Allah ya sa bai saɓule ba tsabar halin da na kr ci na manta da rufe jikina a gaban suruki. To su da suka kawo ni asibiti cikin rai ƙwakwa mutuwa me ye ya yi saura kuma? Da ƙyar na iya taka kafafuwana zuwa tiolet ɗin cikin ɗakin ji na yi kamar in faɗi jikina kamar fallen takarda saboda rashin ƙwarin jiki.

    Tabbas jini ke zubar min tun da ga shi a jikin pad ɗin da ke jikina. To ko dai maganar Nurse ɗin gaskiya ne na samu ɓari? Amma abin tambaya anan daman ina da ciki ne? Dawowar Amina ɗakin ne da ta ga ba ta ganni ba sai ta ƙwala min kira shi ya sa na yi tsarki na fito ina faɗin.

    “Gani nan Amina.”

    Da sauri ta zo ta kamani ganin ina faman da fa bango ta maida ni har saman gado na zauna sannan ta koma gefe na kamar ɗazu ta zauna.

    “Ya Sadiya jiya kin ba ni tsoro”

    “Me ya faru? Na kasa tuna komai”

    Na faɗa ina kallon ta. > Janaftybaby: “Suma fa kika yi a cikin tiolet ga shi kina ta zubar da jini. Na ƙwalla ƙara ina ta ihu ba mai jina. Ƙwatsam sai ga shi Allah ya aiko min da Baban Yunma shi ya taimaka min muka kawo ki asibitin nan, ko da muka zo kin fita hayyacin ki tun jiya sai yau kika farfaɗo “

    Ina kallonta amma na kasa mgana, sai ta cigaba da faɗin” Jiyan kin farfaɗo da daddare amma sai kika koma bayan sun yi miki alluran barci.”

    “Da gaske ne tun jiya na ke kwance a nan?

    Amina ta ɗaga min kai kafin ta ce” E nan kika kwana tare da ni da safen nan ne na koma gida na yo abin karyawa sannan na taho miki da wasu kaya.”

    Ta mike ta na nuna min kayan sawan ta da ta zo min da shi ganin pant da pad a cikin kayan ya sa na gasgata zargina.

    “Me ya same ni? Me ya sa na ke zubar da jini?

    Sai ta dawo kusa da ni again ta sake zama ta na faɗin” Ya Sadiya ɓari kika yi fa?
    Ƙura mata ido na yi ba tare da na yi mgana ba sai ta riƙe hannuna guda ɗaya ta na faɗin.

    ” Wallahi Ya Sadiya. Na ce ashe ciki gare ki ban sani ba?

    “Nima ban san da shi ba Amina.”

    Na faɗa wasu hawaye masu zafin da ban da taruwan su ba suka kece mini. Hawayen baƙin ciki. Hawayen takaici, hawayen nadama da dana sanin da na biye ma Yallaɓai ya yi sanadiyar na rasa wani abu mai muhimmaci da na daɗe ina neman tsawon shekaru goma na cikin rayuwar da ubangiji ya ba ni.

    “Wallahi Ya Sadiya kin zubar da jini shi ya sa likitan ya ce ki riƙa shan ko cin a baben ƙarin jini.”

    “Wata nawa ne cikin?

    Na faɗa ina kallonta cikin kuka. Sai a lokacin ita ta farga ma kuka na ke yi da sauri ta dafa kafaɗata lokaci ɗaya ta na faɗin.

    “Ƙarami ne likitan ya ce sati huɗu bai ma gama cika ba ƙila shi ya sa ma ba ki san da shi ba “

    Wasu hawayen ne suka ƙara ke ce min ban sani ba. Ban taɓa kawo ma kaina ciki gare ni ba, ko da period ɗina ya tsallake min wata ban yi tunanin haka ba, sanin daman ya na yi min haka sai dai ban saka lissafin da cewa tun da na sha mganin lokacin al’ada ya gyaru ba kawai sai na yi tunanin ya dawo da yi min wasan da ya fara min a baya ne. Ashe ashe ciki ne Allah ya ba ni bayan na fidda rai da yaƙinin zan sake haihuwa. Ban san ina kuka har da shessheƙa ba sai da na ji Amina na bubbuga bayana ta na mai faɗin.

    “Ki daina kuka Ya Sadiya. In sha Allahu Allah zai kawo wani da gaggawa. Allah kuma ma ya taimaka cikin ya fita duka ba su yi miki ma wankin ciki ba.”

    Amina na kallah itama ni ta ke kallo kawai sai na fashe da kuka mai sauti na kwantar da kaina a saman cinyarta ina kuka ina ma tana lallashina amma har muryanta ta fara rawa.

    “Ni kaina Ya Sadiya sai da na yi ƙwalla da aka ce ciki ne da ke amma kin samu ɓari. Na ce Allah sarki Ya Sadiya abin da ta daɗe ta na nema ga shi ta samu amma Ubangiji ya yi ikon shi. Ki yi haƙuri za ki samu wani da ikon Allah.”

    Ba wani Ubangiji da ya yi ikon shi. Yallabai ne ya yi sanadiyar da na rasa ɗana gudun jinina. Domin shi ne ya saka ni cikin cikin baƙin cikin da har ya yi sanadiyar ɓarin cikina. Cikin da na shafe tsawon shekaru goma ina fafutukan samun sa sai ga shi ya samu ɗin amma tun kafin na ma san da wanzuwar shi ya bi rariya. Kuka na ke yi da ƙarfi da dukkan zuciya ta. Kukan rasa gudan jinina. Kukan baƙin ciki da wani kullutun abu da ya tokre min a ƙirji na jin wani irin haushin Yallaɓai da ban taɓa jin irin shi ba sai yau.

    Na yi kuka sosai kukan rasa gudan jinina. Lallashin Amina bai sa zuciya ta ta yi sanyi, sai da na yi kuka sannan na ɗan ji sanyi sanyi amma wannan taɓon da Yallabai ya saka min ba na jin zan iya mantawa. Idanuwana sun yi jajir sun tasa saboda kuka Amina faɗi ta ke yi Allah zai ba ni wani na daina kuka jin ta kawai na ke yo. Ko na samu wani ba shi zai goge taɓon na samu kafin shi kuma ya zuɓe ba, kuma ba shi zai taɓa goge taɓon sanadiyar baƙin ciki Yallabai na rasa abu mafi soyuwa gare ni a karon farko ba.

    Da ƙyar Amina ta lallasheni na ci abinci fanten doya da hanta na ci na ɗora da maltina sai na ji na fara samun ƙarfin jiki na komawa na yi na kwanta ina kukan zucci sai ga Likita ya shigo duba ni ya yi min tambayoyi na amsa masa cikin raunin zuciya. > Janaftybaby: Ledan ruwa ya sake rubutamin sannan ya umarci Nurse ɗin da suke tare ta mai da ruwan da ya rage da aka cire da safe ya ida sa shiga jikina.

    “Madam kin samu misscarrge so za mu riƙe ki a nan kwana uku saboda jikin ki ya samu karfi. Hop za ki bamu haɗin kai ki riƙa cin abinci saboda kina bukatar jini sosai.”

    Sai na gyaɗa masa kai, sai ya jinjina min kai shima kafin ya ce. “Good. Allah ya ƙara lafiya.”
    Daga nan ya fice tare da zugan Nurse ɗin da ke bayan shi takardan da ya rubuta Amina ta karɓa itama ta bi bayan su da cewa bari ta je ta siyo. Ba daɗewa ga shi ta dawo da kwali a hannunta a jikin kwalin ne na ga sunan asibitin GARKUWA HOSPITAL.
    Amina ta daɗe a tare da ni sannan ta ce min za ta koma gida ta yi girki sannan ta taho min da ruwan zafin da zan yi wanka.

    “To.”

    Na amsa mata da farko sannan na ce” Ina su Yumna?
    “Suna makaranta. Jiya da babansu suka kwana da safe ma shi ya yi musu shirin makaranta.”
    Sai na yi mirmishi ban yi mgana ba.
    Ta haɗa kayan da za ta koma da su sannan ta yi min sallama ta ce sai anjuma za ta dawo.

    “To sai an juma ɗin.”

    Ta faɗa ta na rike hannuna mara ƙanula.

    “Sai anjuma.”

    Na faɗa a hankali ina jin kamar barci na son ɗauka ta.

    Har ta kama hanyar fita sai ta dawo da sauri ta na faɗin.
    “Laa kin ga na manta ga wayarki “
    Ta faɗa lokaci ɗaya ta na fiddo wayata daga jakarta ta miƙa min na saka hannuna mai lafiya na karɓa ina juyata cikin mamaki sannan ina kallon Amina.

    “A cikin jakar ki na gani shi ne na saka miki ita chaji. In kina bukatar wani abu ki kirani shi ya sa na taho miki da ita. Ko in za ki kira Baban su Jidda ki faɗa mai halin da ake ciki.”

    “Ba zan faɗa masa ba.”

    Na bata amsa da sauri sai ta tsaya ta na kallona cikin nazari.

    “Ba shi ba, har can mutanen gidan kar ki sake ki faɗa ma kowa ko da sun kira ki.”

    “To me ya sa?

    “Haka nan kawai ai na ji sauƙi ba buƙatar a tashi hankali kowa.”

    Na faɗa ina kallonta.

    “To ko Yallaɓai ba za ki kira ba?

    Wannan karon kai na girgiza mata alamun a’a sai ta zakuɗa kafaɗa kafin ta ce shikenan kayan hannunta ta duka ta ɗauka sannan ta yi min sallama ta fice daga ɗakin na bi ta da kallo sai da ta ficen sannan na danna gefen wayar haske ta kawo. 12:30pm na rana ne agogon wayar ya nuna ita Amina ta ɗauka rashin chaji ne ya sa wayar ta mutu ba ta san ni na kashe ta da kaina ba tun jiya ɗin nan ba wanda ya kirani.
    Wanda na ke tunanin ya kiran kuma ni na san ba zai kira din ba kamar zan sake kashe wayar sai kuma na fasa na bar ta a kunne bayan na tura ta ƙasan filon da na ke kwance.
    Kamar a jikin ƙarin ruwan an yi min allura barci ban daɗe ba barci ya tafi da ni mai nauyi sosai wanda har ina jin nauyin sa a yadda jikina ya saki gabaɗaya ko ɗan ya tsana na kasa ɗagawa saboda nauyin barcin da ya kwasheni.

    *

    Kwana huɗu na yi a asibiti sannan a ka sallame ni. Kuma duka abin da a ka kashe na asibitin nan Dr ya biya ga shi asibitin na kuɗi ne amma haka suka yi ta ɗawainiya da ni.
    Na ji sauƙi kuma na samu ƙarfin jiki amma dai na ɗan yi rama, sannan likita ya yi ta jadaddamin na riƙa cin abincin da zai ƙara min jini, sannan na riƙa cin abinci da ganye da wake sannan na yi ta shan maltina da madara. Sannan suka rubutamin mugungunar da zan rika sha na wanke mara ko da sauran wani jini ko datti sannan na ɗan yi complain ɗin ciwon mara shima sun rubuta min mgani. Kuma a nan asibitin muka siya mganin kafin mu koma gida.

    Gidan Amina na sake komawa ina ta jin nauyin ma Dr cikin ikon Allah kwana biyu da sallamoni daga asibiti ya tafi Seminar lagos sai na ɗan samu sakewa duk da ni ina ɗakin Amina ne tare da Yunma ita kuma ta na ɗakin Megidan tare da Sumayya da Yasir.
    Tafiyar Dr ya sa sai na ɗan saki jikina har ina fitowa falo. Sati ɗaya jini ya ɗauke min na yi wankan tsarki na fara ibada ta, kuma duk wannan tsawon lokaci Yallaɓai bai neme ni ba nima kuma ban neme sa ba sannan da gayya na bar waya ta a kunne domin na fahimci zurfin yadda na zama mara amfani a rayuwar Yusuf gabaɗaya sai ga shi na gani. Sama da kwana takwas na bar gida bai taɓa kirana dai-dai da rana ɗaya ya ji ya lafiyata ba. > Janaftybaby: Har Musbahu ya kirani domin Mubeena ya tura gidana ta dawo ta ce ba na nan sai da ya kirani ne na ce masa ina kaduna, kai tsaye ya ce ba su maganar da Tafida ba a raina na ce daman ai ba zai yi ba.

    Ina da kwana goma a Kaduna Munnira ta kira wayata da yamma ta ce ga ta a kofar gidana ta na bugawa kamar ba kowa.

    “Ina Kaduna Munnira.”

    Ina jin yadda ta maimaita kadunan cikin mamaki kafin ta ce.

    “Topha. Me ya faru? Aminar ba ta da lafiya ne?

    “Lafiyanta ƙalau na zo ganinta ne kawai.”

    “Ki ce zumumcin ganin Amina ya motsa. To yara fa? Ko suna Gwamnaja?

    “Ban sani ba. Gida na bar su tare da babansu.”

    “Wata ƙila suna gidan Gimbiya.”

    Da haka muka bar mganar hira muka ɗan yi sama sama kafin mu yi sallama sai da ta ce yaushe zan dawo?

    “Ban saka rana ba.”

    “Eyye. Kin ji ki tsaya ki ɗan huta”

    Ina mata dariya daga nan muka yi sallama. Ita ta faɗa ma Hauwa ina kaduna sai gashi ta kirani, su har sun damu da ni amma wanda ya ijiye ni na koma ni da banza duk ɗaya a wajensa. Ban taɓa tunanin zan kai tsawon kwanakin ba tare da Yallaɓai ya neme ba amma ganin har na kwarari sati biyu bai kirani ba sai na daina mamakinsa na kuma ɗauka da gasken na gama yi ma Yusuf amfani a rayuwarsa. Duk na yi waya da su Ya Aina amma ban nuna musu ba na gida ba har Ya Balki mun yi magana wasu maƙotan ta na son Hijabai na ce na hannuna sun ƙare sai an sake kawowa.

    Ban faɗa ma Amina komai ba, itama ba ta dame ni da mgana ba. Amma tabbas a raina na san cewa ta yi shuru ita kanta ta san lafiya lafiya ba zan zo gidan ta na shantake ba. Ashe ma duk ta na lura da motsi na ban sani ba sai ranar da na ke da sati biyu muna zaune a falo ni da su Yunma in na kallon su tuna wa na ke yi da nawa yaran da suka yi min nisa ina cikin kewarsu sai na yi kamar in kira Yallaɓai ba sabo da shi ba sai saboda yarana amma sai na ji na kasa domin wani irin haushin shi na ke ji haushin da ban taɓa ji ba shi ya sa na ke danne komai amma Allah kaɗai ya san damuwar da na ke ciki. Duk dare sai na yi kukan ɓarin cikina kuma sai na ji na ƙara jin haushin Yallabai daga ƙasan zuciyata.

    “Ya Sadiya”

    Amina ta kirani sai na bar kallon yaran da ke wasa a tsakar falon na koma ina kallonta. Tsaye ta ke a gefen kujeran da na ke zaune daman muna tare ne muna hira sai ta tashi ta shiga ciki.

    “Mu je ɗaki na mu yi mgana.”

    Ban kawo cewa mganar Yusuf ba ne da ba zan yi saurin tashi na bi ta ciki ba

    Gefen gadonta muka zauna gabaɗaya.

    “Me ya faru?

    Na faɗa ina kallonta ganin ta yi shuru ta ƙi mgana.

    “Ya Sadiya kun samu matsala da Baban su Jidda ne ko?

    Sai na kalleta kafin na ce” Me kika gani?

    “Abubuwa da yawa. Ba ya kiran ki ke ma haka. Infact ma ni ban taɓa ganin ya kiran ki ba tun dawowar mu daga asibiti.”

    Sai na yi shuru na kasa mgana saboda ba ni da amsarta a lokacin

    “Ko bai san kin taho nan ba ne?

    “Ya sani”

    Na amsa mata da sauri ina ƙokarin mai da kwallar da suka cika min ƙwarmin idanuwana.

    “Ya sani fa kika ce?

    “Ya sani Amina.”

    Wannan karon na faɗa cikin kwarin gwiwa. Sai kuma hawaye suka ke ce min wasu na korar wasu sai ta ruɗe ta riƙo hannayena ta na faɗin.

    “Na shiga uku ba dai sakin ki ya yi ba ko?

    “Bai sake ni ba.”

    Na amsa mata ina kallonta ina ganinta ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta ce” Alhamdulillah da sauƙi.”
    Sai kuma ta koma ta na kallona kafin ta ce” Me ya faru?
    Na kasa mgana kawai sai kuka ya kece min, na riƙe hannayena Amina a saman fuskata ina kuka har da shessheƙa.

    “Amina wai ni Yallaɓai ya kalli idanuwana ya ce ina yi ma baƙin ciki da Matarsa da ƴaƴansa saboda ban ƙara haihuwa ba.”

    Amina ta ƙwalalo idanuwana ta na kallona. Hannayenta na jinƙe cikin nawa ina jin kamar za ta iya cire min ƙuncin da ke zuciyata in na faɗa mata halin da na ke ciki.

    “Amina bai tsaya anan ba sai da ya yi min gorin haihuwa. Ya ce ina baƙin ciki da yayansa kuma sai dai na mutu. Sannan ya ce gida gidan shi ba gidan ubana ba ne.”

    “Shi Yallaɓan ya ce miki haka? > Janaftybaby: Amina ta katse ni cikin mamaki da alja’abi na gyaɗa mata ina kuka ina ba ta labarin duk abin da ya faru daga farko har ƙarshe na ƙarishe da faɗin” Amina na taho gidan ki cikin damuwa da kuka. Tsawon kwanaki nan Yallaɓai bai nemi ba? Me ya ke nufi? Hakan da ya yi ba ya nuni da abin da ya faɗa har zuciyarsa ba ne? Amina yau Yallaɓai ya nuna min ba ni da sauran amfani a wajensa Gimbiya ce matar arziƙi uwar yaya maza ita ce mai amfani yanzu a wajen shi da ƴan’uwan shi.”

    Na faɗa ina kuka. Kukan baƙin ciki kukan kishi da kukan nadaman yadda na yarda da Yallaɓai daga ƙarshe ya tozartani na baro gidanshi na zo gidan ƙanwata ina zaune. Me ya fi wannan tozarci da cin zarafi?
    Amina ma kamar ta yi kuka mamaki ma ya hana ta mgana.

    “Shi Yallaɓai nan duk ya aika miki haka Ya Sadiya?

    “Ya wuce wai Amina. Ni yanzu na rasa ya zan yi? In na kashe aurena ina za ni Amina? Shekara sha takwas da aurena jidda ta isa minzali amma ban wuce tozarcin Namiji ba.”

    Sai a yanzu na ke jin sauƙi sauƙi da na ke fada ma Amina damuwata. Amma a kasan raina danƙare ya ke da nadama. Nadamar yadda na yarda da duka kalaman Yusuf Inuwa tun a ranar farko na da fara ganin shi da ace ban bari ya ruɗe ni da kalamansa ba da wata ƙila wannan ranar ba ta zo ba.

    “Gaskiya ya ba ni mamaki. Ƙiri ƙiri ya yi miki rashin adalci ki yi mgana kuma ya nemi tozarki? Tsskani ga Allah ya dace ya ce da yaro zaku riƙa kwana? Ba ya tunanin in kina buƙatar sa fa?

    “Shi ba ya buƙatata domin ina tunanin rabo na da Yallaɓai na ƙarshe ranar da na samu cikin da ya zube ne Amina. Sai ya zo gida na har ya koma can wani abu ba ya shiga tsakanina da shi.”

    Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso min.

    “Bai kyauta ba. Kuma wallahi zai gane kuren shi.”

    Kai kawai na girgiza na kasa mgana saboda in na zauna ina faɗin wani abun ma sai a ce na yi masa sharri ne.

    “Amina ki yi fatan ki mutu tare da mijinki da ƴaƴan ku. In kuma ƙarin aure na cikin kaddaran shi ki yi ta fatan Allah ya ba ki haƙuri da juriya sannan ya ba ki wuyan ɗauka. Domin kishi na da zafi sannan masifa ne kuma bala’i ne”

    Amina sai ta yi shuru ta kasa mgana. Ni kuma ina share hawayena na cigaba da faɗin” Domin duk zaman lafiyan da ke tsakanin ki da mijin ki in ya auro ta sai ta shiga tsakanin wannan zaman lafiya. Sannan duk amincin da ke tsakanin ki da shi sai ta zo ta raba shi haka ma duk yardan da ke tsakanin ku wata rana sai ya ce ke ba abin amincewa ba ce. Duk faɗan da za ku yi da mijin ki ke kaɗai ba zai kai girman faɗan da za ku yi in ya karo aure ba ki sani duk haƙurin ki da kawaicin ki wara rana sai an ƙure ki. Ki sani kishiya ƙalubale mai zaman kanta a gidan aure wanda ba a yi mawa ba ko za a bashi labari ba zai taɓa ganewa ba sai wanda ya tsinci kan shi a yanayin kaɗai zai iya sanin raɗaɗi tare da ƙalubalen.”

    “To in haka ne Allah ya raba mu da kishiya.”

    “In ta alherin ce fa ?

    “Ko ta alherin ce Allah ya yi mana tsari da ita.”

    Sai Amina ta ba ni dariya sai da na murmusa. Ita manaki ta ke yi a tunanin Yallaɓai ba zai taɓa juya min baya ba na manta namiji mai manta alheri wasu mazan da yawa batulai ne, an yi musu alheri su manta su nemi saka ma mutumin da ya yi musu alheri da sharri. Amina ta ce ita ma ta na goyon baya kar na sake na neme shi har mahadi ko ya bayyana tun da bai san mutumci ba.

    Maganar da muka yi da Amina sai ya fama min da mikin da ke cikin zuciyata. Ranar sukuku na yini sannan na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitar da zan nema ma kaina ba zan zauna takaicin wani namiji ya kashe ni ba, in ma bai kashe ni ba ya saka min zuciyan da zan rayuwa sunan mattaciya. Ya zama dole na koyi jajircewa na kuma koyi tsayuwa da ƙafafuwana. Na yi tunanin ba zan cigaba da fakewa a gidan Amina ba in mijin ta ya dawo lamarin zai zama wani iri. Ba kuma zan koma Kano ba saboda duk da in da na je ba za a fars duba masalahata ba. Ni kuma a yanzu na shirya ma Yallaɓai da duk abin da ya ke takama da shi. In koma gida Alhajinmu ba zai zauna ina zauna a gida kuma ya yi shuru ba. > Janaftybaby: Gwara kawai daga nan na wuce Yashe wajen Baaba Aminu na fashe masa da kuka ya na tausayi na tabbata zai fara duba masalahata kafin wani abu ya biyo baya.

    Haka na tsai da shawara da ni da zuciyata ko Amina ba ta sani ba. Washegarin da muka yi maganar da ita Gwaggo ta kira waya ta har gabana ya faɗi na ɗauka ma ko maganar ba na gida ta je musu ne amma sai na ji ta ce kwana biyu ta ji ni shuru ne ya sa ta kira ni. Ga ma Alhajinmu nan ya na ta cigiya har ta ba ni Alhajin mu ka gaisa ya na min zolayan shi da ya saba na Hajiya Dubu kwana biyu. Sai na yi ƙaryan ba na ɗan jin daɗi ne shi ya sa har muka gama waya ina ɗari dari saboda ba na so su ji wani abu yanzu na fi so komai mai zai faru ya zama na tsakanina da Yallaɓai ne kamar yadda aka saba. A ranar har Marwa ma mun yi waya da ita amma itama ban faɗa mata ba saboda da ta ji Kawu Abba ya ji shi kuma in ya ji zai yi shuru ba faruwan haka sai Yallaɓai ya dauka shi ɗin ya isa ne shi ya sa na kai ƙaran shi wajen abokinsa kuma ɗan’uwan shim shi ya sa ban bari ma ta fahimci wani abu ba.

    Ranar da na ke da kwana ashirin a gidan Amina da daddare Gimbiya ta kira wayata. Har sau biyu ban ɗauka ba saboda ban san me ya haɗa ni da ita da za ta kirani ba sai da na ga kiran ya ƙi ƙarewa sannan na ɗaga kiran amma maimakon na ji muryanta sai na ji muryan Jidda.

    “Jidda.”

    Na faɗa ina mai tashi zaune saboda mamakin jin muryan ta ban za ta ba.

    “Na’am Umma mun yi kewar ki yaushe za ki dawo?

    Ta faɗa cikin sanyin ta a koda yaushe.

    ” Ina nan dawowa Jidda. Kuna lafiya? Ina Baby?

    “Ta na can falo ita da Abba da Anty Gimbiya.”

    Wani abu ya tsaya min a ƙasan maƙoshi da ƙyar na ce” Wa ya ba ki waya?
    “Ɗauka na yi Umma ba ta sani ba. Ina ta tambayan Abba yaushe za ki dawo ya ce kin je Kaduna gidan Umma Amina.”

    Ashe dai bai manta da in da na je ba. Lallashin Jidda na yi da cewa zan dawo kwanan nan, na ce ta gaishe min da Baby ina nan dawowa muna magana wayar sai na fara hawaye a ƙasan zuciyata ina ta tsine ma Yallaɓai domin shi ne ya yi sanadiyar da na yi nesa da ƴaƴana. A ƙasan raina ina jin daɗi in na tuna yau ni na samu ciki duk da ya zube amma dai na samu sassaucin cewa wataƙila mahaifata za ta iya ɗaukan ciki ba shike nan ba kamar yadda na ke tunani a baya. Ke nan gidan Gimbiya ya tarkata yaran ya kai mata? Oh itama ta ji in da daɗi godiyar ta ma ɗaya daga Jidda har Baby ba yara ba ne ban da girki ba ɗawainiyar da za ta yi musu girkin ma Jidda ta iya makaranta ne kaɗai cikas ɗin ta.

    Da safe na tashi fuska a kumbure. Sai kuma Amina ta ke faɗa min Dr gobe zai dawo sai hankalina ya tashi.

    “Amina zan zo na tafi ba zan bari Dr ya dawo ya same ni ba.”

    “Me ya sa?

    “Da kunya Amina. To zaman me na ke yi a gidan sama da sati biyu?

    Itama sai ta yi shuru domin ta hasaso abin da ni na na hasaso.

    “Abin kunya ne fa Amina. Ke ƙanwata ba yayata ba.”

    “To Ya Sadiya ba sai na faɗa masa matsala kuka samu da Baban Jidda ba?

    Hararanta na yi kafin na ce” Ban saka ki ba. Ba ki da hankali yarinyar nan.”
    Ina tunanin wucewa Yashe ya kamani gwara na fara shiri yau na wuce.

    “To ina za ki je? Ko gida za ki koma?

    “Ba zan koma ba Amina. Zan dai nemi wani wajen na je kawai”

    “Ina to za ki je?

    Sai na kalleta amma ban yi mgana ba na wuce cikin ɗaki sai ta biyo bayana ta na na cin sai na fada mata in da zan je.

    ” Ke ki ƙyale ni “

    Na faɗa ina jawo akwatina sai ta riƙe ta na faɗin” Don Allah ya Sadiya ki zauna Allah ba na son ki tafi.”
    Ta faɗa cikin shagwaɓa sai ta warce shi daga hannunta ina faɗin.
    ” Na ki wasa ne yarinya”

    “Abuja za ki je?

    Sai na kalleta shuru ina wani nazari ni ban kawo gidan Ya Auwal a raina ba saboda in dai na je sai ya ji ba a si ba kuma zai kira Yallaɓai. Dama dai Ya Hamza ne shi ne ɗan goya min baya amma shima ba zan je gidan shi ba saboda shima zai iya kiran Yallaɓai ni kuma ba na so ya ji a ran shi na damu da shi ne shi ya sa na je na kai karan shi yadda ya zaɓa nima haka na zaɓar ma kaina.

    “A’a ba zan je can ba.”

    Amina sai ta kasa mgana, ni kuma na fara haɗa kayana kenan wayata da ke gefen gado ta fara kuka alamun ana kira Amina ta fi kusa da wayar ba tare da na kalleta ba na ce. > Janaftybaby: “Wa ye ke kira hala?

    “Yallaɓai na.”

    Amina ta faɗa a hankali da sauri na kalleta cikin mamaki a kallo nawa ganin haka yasa sai ta miƙa min wayar na karɓa cikin san yin jiki.
    A hannuna wayar ta yanke kuma ba daɗewa ya sake kira. Sai da ya yi min kira biyae bi da bi ban ɗauka ba sannab shuɗewar mintina huɗu tsakani saƙon shi ya shigo.

    “Yaushe za ki dawo ne? Yara sun damu da tambarki.”

    Yara ne suka damu ba shi ba, to tun da shi da ya ijiye ni bai dami ba shike nan yara kuma shi ne uban su tsaki na yi na dankwar da wayar gefe na cigaba da haɗa kayana Amina ta ɗau wayar ta na dubawa kafin ta ce.

    “Ka ji wani kutumar uba wai yara sun damu? Shi ne fa ya damu ya rasa abin da zai ce shi ne ya fake da yara.”

    “Mtsewww.!”

    Muka ja wani dogon tsaki a tare ni da ita sannan muka kalli juna muka yi dariya.

    *Janafty* > Janaftybaby:

    Note
    error: Content is protected !!