Turken Gida – Chapter Nineteen
by JanaftyKamar a zahiri kallonsa na ke yi amma a baɗini ba shi na ke kallo ba. Hankalina da tunani ya yi nisan kiwo. Jikina gabaɗaya ya saki sai na ke jin kamar ba zan iya ba, kamar za'a ga gazawata in tafiya ta yi nisa.
"Kin yi shuru ba ki ce komai ba Sadiya."
Shi ya katse min tunani da ya sa na dawo hayyacina. Ajiyar zuciya na sauke kafin na maida hankalina zuwa ga kallon ƙasan cafet ɗin da ke gefen gadon. Ina so na yi magana amma sai na ji kamar an ɗaure min baki. . .