Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Shirye shiryen biki Yaya Usman kawai ke kan layi yanzu saboda bikin ya rage saura kwana takwas.
    Kuma da ya ke bikin anan Gwammaja za a yi ita kuma Amarya a Kaduna gidan kakkaninta wanda ya haifi mahaifinta. Shima tsohon Soja ne mai ritaya amman ya rasu. To nan za a ɗaura aure ranar asabar amma taron biki ranar jumma’a ne asabar da an gama ɗaura aure amarya da tawaganta za su sauka a Kano sai ranar litini ango zai ɗau amaryansa da iyalansa su hau jirgi zuwa fortacol

    Kuma auran daman na yan boko ne lefe ma kuɗi kawai ya tura ma Amaryan aka ce ita ma uwargidan an ce ya ba ta kuɗi bayan ya biya mata Hajji shi da ita da Amarya bayan sallah da an fara tafiya za su ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki.
    Zuwa lokacin hatta abincin da za a dafa Yaya Usman ya saka an kawo. Biki dai za a yi na masu da shi, ba talauci a ciki ba kuma ɓarnan dukiya dai dai ruwa dai dai tsaki.

    Gimbiya ta gama Takaba tsakanin bikin Yaya Usman saura kwana goma ne. An yi walima da taro a can Rano amman ni dai ban je ba. Na ga dai su Anty Bahijja sun ta ɗora ta a status suna mata addu’an Allah ya kawo wani mijin na alheri ya kuma ƙara mata dangana. A cikin hotunan akwai wanda aka ɗauke ta a ranar da ta fita takaban ta yi kwalliya amman ta yi rama duk da dai haka a raina na ce dangana ai ta riga da ta samu ko Yallaɓai bai mini mganar ba nima ban yi masa ba. Na kuma ƙara ganin ƴan’uwan suna yi mata addu’a a group ɗin iyalan Marigayi Muhammad Inuwa 02 wanda muke ciki gabaɗayanmu har mu surukan gidan da a can Ranon gabaɗaya amman kuma suna da wani wanda ba ma ciki shi kawai na iyalan gidan ne gabaɗaya shima na sani ne saboda ina gani a wayar Yallaɓai. Kuma shi wannan da muke ciki daga baya aka saka mu, sannan ba a cika ma mgana ba sai ta kama ina ga sun fi yin ɗan sirrin su a can ne saboda ire iren mu da suke gani kamar bare.

    Yallaɓai kuma daman shi harkan chart ba wani damun shi ya yi ba. Yana yi ba wai ya yi ba ne, saboda harkokin shi da jama’a amman sai ya yi wata biyar bai saka status ba. In ma ya saka sai mutuwa ko in ya nishaɗu ranar Jumma’a ya saka salatin Annabi. Amman ni na san yana kiran Gimbiya a waya tun da ina yawan ganin sunanta a call long ɗin shi ba da kuma Niyyar bincike ba sai saboda wayarsa ba ta da shamaki a hannuna kamar yadda nima tawa ba ta da shamaki a hannunsa.

    To a irin haka ne ranar da ta yi fitar Takaban wayar na hannuna da daddare Yallaɓai ya shiga Tiolet saƙon ta ya faɗo Allah na gani ban buɗe ba amman daga sama na hango godiya zuwa ga Daddy na, na gode bi sa ɗawainiyar da ka yi ta yi da ni. Daga nan saƙon ya yanke gudun shiga hurumin da ba na wa ba sai na kauda kaina ban buɗe masa saƙo ba saboda ba ni aka tura mawa ba da ya fito kamar in faɗa masa an tura masa saƙo sai kuma na fasa na ajiye masa wayarsa a raina na ce ai zai gani. Yadda na gani ban nuna na gani ba, nima kuma bai nuna mini komai ba, sai kuma da safe kafin ya fita na ji suna waya lokacin muna dining ina haɗa masa abun kari, alƙwarin da na yi ma kaina shi ne zan zura masa ido na ga iya gudun ruwan shi daga shi Gimbiyar. Amman abin na sukan raina ganin gabaɗaya idon ta na kan mijina kamar shi kaɗai ne a dangi?
    Sai wata zuciyar ta tunasar da ni a lokacin.” Kin manta ba namijin da ta yi ma so irin mijin ki? To ko dai angulu ne ke marmarin son ta koma gidanta na tsamiya?

    **

    LARABA.”

    Yau mun wayi gari ranar laraba. Kimanin jibi Jumma’a taron bikin a can Kaduna, mu kuma nan sai ranar asabar tunda mu za mu tarbi amarya. Ita kuma Anty Zabba ta iso kano ita da ya’yanta amma a gidansu ta sauka ta ce ita a can za ta yi nata taron biki. Mijin ta kuma ya amince shi ya sa ma kowa bai damu ba. > Janaftybaby: Sai dai wanda ya ga zai iya bin ta can sai ya je, ni tun da na ji haka na ce me zai kai ka? Ai sai a ce ka je ganin gulma ne gwara mu tsaya nan Gwammaja in ta zo ma haɗu a gaisa.
    Tun safe na tashi ina aikace aikace saboda mun yi da su Hauwa a Gwammaja za mu yi ni saboda aiki. Tun asuba da na tashi ban koma ba, tun watan da ya gabata hutu ya ƙare mini Yallaɓai ya cika alkwari ya saka Saude a makaranta wata private school ce mai ɗan sauki sauki a nan kusa da anguwar Ɗorayin ta ke da kafa ma Saude ke zuwa shi ya yi mata komai har uniform da jaka da takalmi an saka ta Jss2 saboda ta yi girma a jss1.

    Tun da ta fara zuwa makaranta shikenan aikin gidana ya dawo kaina saboda ba ta samun lokaci sai biyu suke ta shi in kuma ta dawo da la’asar ta na zuwa islamiya. Sai alhamis da jumma take zuwamin in ta dawo daga makaranta tun da ba islamiya weekend kuma sai ta je Allo ta dawo.
    Aiki duk ya yi min yawa rabo na da barcin safe har na manta da su Jidda sun tafi makaranta zan fara gyaran gida ina gamawa na je na tada Yallaɓai ya yi wanka ya zo mu karya to sai ya fita ne nake samun daman kwanciya na huta bayan azahar irin uku saura na miƙe na shiga kitchen na ɗora girki saboda yan makaranta.
    Kibar da na fara yi saboda hutu duk ta zazzage ga shi daman ni ba gwanar aiki ba. Ina yi ina jin na gaji kai har gobe ba zan kaunaci aiki ba. Ga shi yanzu Yallaɓai ya lalace ba iya taya ni da komai ko da ya na gida ne sai dai ma ya yi ta mini dariya in ya ganni na yi shigar aiki na tsuke cikin Boom short da ƙaramar riga sai ya hau tsokanata.

    “Sadiya ƴar laushi barka da aiki.”

    Ranar haka ya ke shan harara ba na ma tanka shi domin na biye masa sai ya ɓata mini lokaci shi kuma bai tayani ba, ballatana ya rage min wani aikin Ahalin na san ba abin da bai iya ba shima kuma ya san na san ya iya komai.

    Yau dai aiki ya kacame mini ga wanke wanke jiya ban yi da yamma ba. Jidda ta so ta yi lokacin an kusan mangariba sai na ce ta barshi sannan ga shara na gama sai na yi mopping tunda na ɗan kwana biyu ban yi ba sannan na saka turaren wuta a burner gidan ya ɗau kamshi. Na riga na wanke tiolet ɗin su Jidda saura na mu shi na shiga na wanke ban gyara Bedroom ɗin mu ba Yallabai na kwance ya na barci har da minshari.

    Falon yara na koma na zauna ina maida numfashi. Na huta kafin na tashi na yi wanke wanke. Amman na so Yallaɓai ya ta shi ya yi wanka ya karya sai na haɗa komai na wanke domin da na fara shara na fara jin jiri tuni na je na karya cikina ya cika to ina zan zauna shi ya na can kwance ni kuma ina aiki yunwa ta far min a ciki na faɗi a sume tuni na nema ma kaina mafita na karya na barshi.
    Na yi hutun sama da minti talatin domin kallo ma ne ya ɗau hankalina wani film ɗin hausa da suke haskawa tashar Arewa24 na ga ya fara mini kyau sai na zauna ina kallo tuna ina hutun jaki da kaya a saman kaina ne ya sa na miƙe. Har na fara wanke wanke kuma sai na tsame hannuna a cikin ruwan omo na wanke da ruwa na fita zuwa cikin bedroom ɗinmu.

    Tsaye na yi kawai a gaban gado ina kallon Yallaɓai ina sanye da wando baki plazo rigar jikina vest ce ta lame min jiki kaina ɗankwalin doguwar riga ne na yi gammo da shi a saman kaina.
    Zuwa na yi kusa dashi, na fara jan bargon ina kiran sunan shi amman sai ya juya ya na jan bargon ina ja, alamun dai ba zai iya ta shi ba.

    “Yallaɓai..”

    Na faɗa ina dai dai ta saitin kunnuwan shi. A hankali ya buɗe idanuwansa da suka shige ciki saboda barci.

    “Mene ne kuma?

    Ya faɗa da muryan barci har ya na wani yamutsa fusaka ina ganin haka na saka hannuna na shafa kumatunsa sai ya ji sanyi da sauri ya ware ido yana kallona ni kuma sai na koma na riƙe kugu ina kallonshi rabi harara harara.

    Ɗan tashi ya yi kaɗan ya na jingina da jikin gado kafin ya kalleni daga sama har ƙasa sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce” Me kuma na yi! ?
    Baki buɗe na ce” Me ka yi fa ka ke tambayata Yallaɓai? > Janaftybaby: Ya na kallona ya ce” To ba dole na tambaya ba, kin ta da ni kamar yaƙi. Ga shi ke kuma kin riƙe kugu kamar mai shirin dambe.”
    Yana cewa mai shirin dambe na dunkule hannu na ware kafa ina masa gusha gusha sai na kai masa hannu kamar zan naushe shi. Dariya ya ke ta yi kafin ya ce”Oh yau tekwando rana za mu yi kenan! To ai na iya irin wannan ba ri ki gani”
    Kawai sai na ga ya sauko ƙafafunsa ƙasa ya janye bargon sanin halin shi ya sa na yi saurin dawowa dai dai na riƙe masa hannu ya koma ya zauna na zauna a gefen shi na mararaice ina faɗin” Yallaɓai na.”

    Na faɗa har ina masa fari, ina zan yarda ya yi wasan chinese da ni. Lokacin ina amarya sai ya ce mu yi daga karshe dai na gane ni ce ke shan wuya ya fi ni karfi awasa duk ya naushe ni in na yi shagwaɓa na ce da zafi sai ya ce wai saboda kashina ya yi ƙwari kuma nan gaba ya koya min faɗan kare kai. Daga baya na ce ni wallahi ba na so shi ya sa muka daina amman ina amarya ba wasannin da ba mu sha yi ba. Ko dawowarmu nan gida in ya na da lokaci muna yar gudu ni da shi da yara ranar weekend muna da kayan jugging. Daga baya na daina fita saboda na gaji ban iyawa shi kuma ya ce wai na tara kitse ne shi ya sa. Sai dai ranar da ya so ya na fita tare da jidda da Baby ya na kuma gaya musu motsa jiki na ƙara lafiya a jikin ɗan adam.

    Yadda na yi masa farin ne da yanayin maganata ya sa ya san akwai abinda na ke so.
    Cikin mirmishi ya ce” Me kike so ne Sadiya? Domin in za ki cuce ni haka kike yi.”
    Hannuwansa na riƙe cikin nawa na marairaice ina faɗin” Haba Yallaɓai na wani rin cuta kuma? In miji ya taimaki matarsa sai a kira shi cuta?

    “Kamar wani taimako kenan?

    Ya faɗa ya na mai tsare ni da ido da sauri na marairaice kafin na ce” Yallaɓai na yi shara na yi mopping na wanke Tiolets baya na duk ya kage to kuma ga wanke wanke can ba a yi ba.”

    “To shi me? Wai na je na yi wanke wanken?

    Ya faɗa yana kallona da sauri na ce” Ni ban ce ba.”
    Sai kuma na saki hannun shi na miƙe ina tafiya daƙyar kafin na ce” Ka tausaya mini Yallaɓai Allah bayana ke ciwo.”

    “Kina da ciwon baya ne ban sani ba?

    Ban juyo ba na ce” To ni dai ina tunanin tun lokacin haihuwan jidda na goce. Kasan kuma sai a hankali a hankali ya ke tashi.”
    Da iya gaskiya na faɗa domin wani lokacin in na yi aiki bayana sai ya rike amman sai Yallaɓai ya ce” Ba shakka. To sannu.”

    Yanayin mganar na shi ya sa na san bai yarda ba sai na juya ina faɗin” Fisabillahi Yallabai yanzu ka lalace sam ba ka son aiki.”
    Me Yallaɓai zai yi ba dariya ba, ni ko sai na tsaya ina kallon shi da gaske fa haushi ya ke ba ni, ya na gida ace ba zan more shi ba.
    Sai kawai na tura baki kafin na ce” Ko a da ka fi tausayina ne! Yanzu kuma ka daina tausayina ko?

    Ganin yana kallona yana dariya yasa na fara matsan kwallar karya ina faɗin” Ko dai ka daina sona ne Yallabai?
    Na tsare shi da ido har lokacin fa bai daina dariya ba. Sai kawai na fashe da kukan da ba hawaye ina faɗin” Na shiga uku Yallaɓai na ya daina so na”
    Ya na dariyan ya ƙariso ya rumgumeni yana faɗin” Mamaki na ke yi da har yanzu ba ki san aikin da nake yi mai muhimmanci a cikin gidan nan ba?
    Sai na ɗago ina kallon shi kafin na ce” Wani aiki ne? Barci ko?

    Sai kawai ya kai hannun shi saman ƙirjina ya na shafawa ina kallon shi na ga ya dage min gira ai da sauri na kwace jikina ina faɗin” Ai daman anan kafi auki ba za ka zo ka tayani aiki ka motsa jikin ka ba.”

    Na faɗa ina tura masa baki. Yana dariya ya ce” Ai abin da nake yi shi ne babban misalin motsa jiki.”
    Sai kawai na jinjina kai kafin na ce” Kuma kana taimakon kanka ba.”
    Sai ya daga hannu saama kafin ya ce” In ji wa? Taimakon kai da kai dai ko?
    Balla masa harara na yi na kama hanyar fita ina faɗin” Kai dai ka sani.”
    Ina jin sa ya biyo bayana yana faɗin” Ciwon bayan ya warke ne?
    Sai na tuna da sauri na riƙe kugu na sauya tafiya ina cije baki. Yallaɓai dariya har tana sauti na yi masa banza na fice ina faɗin ai sai ya yi ta kwanciya. > Janaftybaby: Har na dawo zan cigaba da wanke wanke ya leƙo ya ce na zo na bashi abin karyawa. Dole na koma falo na haɗa masa tea na zuba masa ɗumamen tuwon da na yi jiya da daddare miyan allayu zama na yi sai da ya gama ci muna yi muna hira bayan ya gama na tattara komai zuwa kitchen sai ya biyo ni ya na faɗin” Je ki huta bari na yi “
    Ina jin haka na daka tsalle na rumgume shi na bashi sumba a baki kafin na ce” Yaron kirki Yallaɓan Sadiya.”
    Kaina ya dankwanfar ya na faɗin” Sai na fasa.”
    Da sauri na ce” Na tuba ranka ya daɗe ka yi mini rai.”
    Yana dariya ina dariya ban kuma iya zuwa na huta ba saman cabinet ɗin kitchen ɗin na haye na zauna yana wankewa ina karba ina jera su a muhallinsu.

    Anan ne ma ya ke ce mini yanzu ya girma iyalai sun fara taruwa ba girman shi ba ne a ka ga yana aiki
    Ni ko sai na buɗe baki na ce” To mi ye a ciki? Ko ƴayan ka sun gan kana aiki ba abin kunya ka yi ba ka na koyi da sunnar ma’aikin mu ne kuma daman da shi muke koyi “

    “Uhm daɗin baki ko?

    Ya faɗa ya na kallona da sauri na ce” Haba Yallabai ai tsakanimu ba daɗin baki sai dai gaskiya da gaskiya.”
    Na faɗa ina masa yar dariya sai kawai ya kalleni ya girgiza kai kafin ya ce” To ke ina wani aikin da kike ta zuzutawa? Tun auran mu tare muke aikin nan ban daɗe da daina yi miki girki kina kwance ba.”

    Sai na buɗe baki ina kallon shi, ban rufe ba ya cigaba da faɗin” Kuma hatta renon su Jidda tare muka yi shi to ina aikin da kike ta kira?
    Sai na rufe bakina na kasa mgana sai da ya yarfa min ruwan wanke wanken da ke hannun shi yana faɗin” kin kasa mgana ne?
    Sai na kauda kai ina faɗin” To na ga abin ya koma gori ne gwara a bar mganar.”
    Dariya ya yi yana ƙokarin sake mgana na yi saurin cewa” Yallabai yau ba za ka fita ba ne?

    “Zan fita mana. Zan je office akan mganar aikin nan na kaduna ki yi min addu’an Allah ya sa ta faɗa za mu samu alheri in sha Allahu.'”

    Da sauri na ce” In alheri ne Allah ya tabbatar in babu Allah ya kawo na alherin.”

    “Amin Amin Abar ƙauna ta.”
    Ya faɗa ya na min wani kallo sai nima na tsume ina masa kallon soyayya. Sai kawai Yallaɓai ya ce a hankali” Ko mu je mu yi ɓarnan ruwa ne mu dawo?
    Da sauri na ce” A’a. Fita fa za ka yi nima zan je Gwammaja.”

    “To mu haɗa wankan mana ba shikenan ba.”

    “Ba ko shiken nan ba.’

    Na faɗa ina haran shi, dariya ya fara yi min kafin ya ce” Me ke damun ki ne? Allah kin fara zama raguwa.”

    Ko magana ban yi masa duk irin ƙokarin da nake yi wai na fara zama raguwa.

    “Na ƙosa ki sami ciki irin na Baby. Ko banza ki yi ta nema na ni kuma da sunan taimako ina shan Shagalina.”

    Kafaɗansa na kaima duka ina faɗin” Ba Amin ba.”
    Shi kuma ya na min dariya har ya na maƙale murya yana tsokanata.

    “Yallaɓai na. Uhm
    Uhm..”

    Kunya ta kamani na saka tafukan hannuna ina rufe fuska shi kuma ya na mini dariya. In na tuna lokacin har kunyar kaina na ke ji abu kamar cin tuwo na maida shi, ba na gajiya ni dai kawai a yi kuma da an gama sai na ji a lokacin nake son abin gaskiya ba zan so na samu ciki irin na Baby ba.

    Haka dai Yallaɓai ya gama wanke wanke sai na ce ya cika ladanshi ya wanke wajen ya goge mini kitchen ɗin harara ta ya yi ya ce” Shi wannan ɗin ba ni da lada ne ko ba ki gode ba ne? Da sauri na ce” Na gode. Allah ya ƙara girma mai girma Tafidan Rano.”
    Kaina ya shafa ya na faɗin” Rayuwarki ta yi albarka ɗiyar ga.”

    Ni da shi muka saka dariya gabaɗaya. Haka nan ya haƙura ya tayani muka gyara kitchen ɗin muka goge sannan muka koma ɗaki Yallabai dai sai da ya aikata abin da ya ce wato mu ka haɗa wanka Musbahu na ta kiran shi baƙi sun iso amman shi ya na gida yana shagali.

    Tare muka fita bayan mun shirya na rufe gida bayan na ɗaukan ma Baby dogon wando kawai suna da kayan sawa a gidan Nene domin wani lokacin in sun je sun kwana ba duka kayansu suke dawowa da shi ba, ni kuma ba na damuwa saboda irin haka suna wucewa daga makaranta ba ni da haufin kayan da za su sauya. > Janaftybaby: Yallaɓai na sauke ni a Gwammaja ko shiga bai yi ba ya wuce office ya ce mini sai ya dawo
    A can na samu Hauwa Munnira ce ba ta kariso ba. Gida cike da dangin Maman Farko sannan a bangaren ƴaƴa kuma su Anty Zulaihat da Nasara sune kan gaba su da su Anty Bahijja. Anty Zuwaira kuma da ya ke yar sabga ce ba ta zo ba ƙila sai yamma. Suwaiba, Jamila da Hindatu duk suna nan Safiya ma haka Hafsat ce tana Abuja ba ta ƙariso ba matar Muhammad Sani an ce sai Jumma’a za su taho tare da mijin nata.
    Ummu Salma ma da ke aure a Bauchi da wuri ta zo, na zo ba daɗewa Jawahir ta dawo daga makaranta sun samu hutun sati biyu.

    A ɗakin Nene na sauka. Tunda nan ne ɗakin Uwar mijina. Ana mganar abincin da za a yi su Anty Bahijja suka ce a yi tuwo da shinkafa sai alale sannan za a yi zoɓo duk da akwai lemuka da ruwa da aka sauke sai Nama da aka ce za a kawo naman sa da na rago za a gyara a soya domin a yi amfani da shi ga baƙi masu zuwa. Sai can bayan azahar sai ga Muninira Halima ma sai bayan la’asar ta zo. Mu surukan gidan muka gyara wake tunda an farke shi ya fara ƙwari bayan mun gama an kawo kayan miya da yawa ni dai daman yar laushi ce su Hauwa na bari da gyaran kayan miya ni dai na gyara albasa Munira na yi min tsiya gyaran albasa kaɗai ne aiki a wajen? Na ce shi ne na ga zan iya. Hauwa dai an yi dama dama cikin gyaran kayan miya ina zan iya. Ba zan yi ba ada dai kam na yi amman ban da yanzu.

    Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya zo muka koma gida washegari ma Alhamis mun koma ranar nama aka gyara aka soya sai kum an tafasa kayan miyan da aka nuƙo. A ranar baƙin Rano suka iso har da Gimbiya a ciki ban ɗauka ma za ta zo bikin ba amman sai na ji ana mganar har da cuku cukun transfer ɗinta ya kawo ta bikin.
    Sai can da mangariba ne ma muka haɗu muka gaisa. Baby dai ta kawo mini chaculate ta ce Anty Gimbiya ta ba ta, ba tun yau ba tana son su Jidda ba kyauttukan da ba ta yi musu tun tana gida ko bayan auranta da suka je honeymoon da mijinta Paris ta siyo musu kaya masu kyau da yarari.

    Can da dare ma tare na ganta da su Jidda da yaran Naja’atu. Sai ranar jumma’a Ango ya iso gida. Sai ihun ango ƴan uwa ke yi masa yana kamewa kusan Soja da tsare gida a ranar ma Tariq ya zo shi da Faridarsa. Muhammad Sani da Nafisa tun da safe suka iso shi Jafar ma da matar shi Nauwara ma sun iso ranar duk da Kaduna za a ɗaura auran amma dai ya zo gida shima.
    zuwa kuma yamma komai an kammale shi.
    Za a yi waina amma an ba da ne a yi sai dai Tuwon da miyan anan gidan za a yi shi kuma Alalen Anty Bahijja ta ce namu ne mu surukai mu za mu yi tsakani ga Allah ta na son ɗora mana wahala. Hauwa da Muniira na bar ma jagoracin su da ya ke a nan gidan suka kwana ni kuma gidana na koma na kwana na ce musu in sun ga ban zo da wuri ba kar su jira ni su fara aikin daman sun san halina ba da wurin zan zo ba. Jidda nan ta kwana tare da yara sa’aninta ita kuma baby ta na tare da Gimbiya Yallaɓai ke faɗa mini ta kira shi a waya ta faɗa masa ta tafi da Baby gidan Naja acan za ta kwana.

    Da safe sai da na sha barcina na gajiya. Yallaɓai ma a gida ya barni na dai shirya shi cikin wata dakakkiyar shadda mai ruwan ƙasa har da babban riga hula da takalminsa bakaƙe haka ma agogon fatan dake hannun shi na fesa masa turare na bishi da Allah ya kiyaye ba da motarsa ya je ba shi. Da shi da Tariq motar Uncle Abba za su bi zuwa Kaduna.
    Motar shi kuma Muttaƙƙa zai tukata zuwa Kadunan shima ɗaurin aure 11 ne na safe tun takwas suka ɗau hanya.

    Ni ina gida ma sai wajen goma da rabi na fita. Rahila ta kira ni ta ce za ta zo na ce sai ta zo domin ni ban gayyaci kowa ba Yaya Balki ma da ta yi mini mganar muna da biki ba gayya na ce ni ban yi gayya ba.
    Sai dai in sun zo domin Allah Gwaggo daman ta ce sai bayan biki za ta je Allah ya sanya alheri.
    Ma’u daman na san za ta zo balle Uwar ɗakin nata ne yan gaba gaba. Ko da na je su Hauwa sun gama alale Munnira na ta harara ta na ce su yi haƙuri na tsaya shirya Yallaɓai ne. > Janaftybaby: “Au to me Yallaɓai? Mu ma ai muna da mazajen da za mu shirya amman ba mu je ba sai ke mai Yallaɓai a ‘a yallaɓiya”
    Munira ta faɗa ta na mai ƙara ɓalla minibharara.
    Ina dariya na ce” To ai ban hanaku ba. Da kun tafi kuma”

    Hauwa ta ce” Mu tafi Anty Bahijja ta tsire mu ko? Daman da ba ki zo ba ta ce Munirra ta ɗau girman tun da ke ba ki daraja girman da Allah ya ba ki.”
    Ina dariya na ce” Ran Munirra ya daɗe. Zan zama mai yi miki biyayya.”
    Kafaɗata ta daka tana dariya. Hauwa ke faɗa mini Nafisa ba ta da lafiya ta na ta amai ba ta yin komai ba na ce yanzu haka ciki gare ta. Nauwara kuwa gidansu ta gudu har na zo ba ta dawo ba.
    Shashen Marigayi Hajiya Karima muka gyara muka zauna tunda sauran duk ya na cike da jama’a Shashen Nene duk mutanen Rano ne Hajiyar Tafida ma da safe ta iso. Ni daman na yi wanka na a gida Jidda na nema na bata kayan da za ta saka da takalmi da mayafi saura na Baby ne an ce ba su dawo ba. Faridan Tariq kuma suna da ƴan uwa acikin gari can ta je ta kwana bayan ta dawo itama muna tare. Sameena ma sai a ranar ta so ashe ba ta nan ta je can Niger wajen dangin mijinta duk muna tare da su anan ɗakin.

    Karfe sha ɗaya da mintina goma Nasir ya kira Munnira ya ce an ɗaura aure acan ma cikin gida an kira su Anty Bahijja sai suka fara guɗa suna ta iface ifacen murna. Sai wajen sha biyu muka sake wanka muka saka ankom mu. Ni na yi kitso amman ban yi ƙunshi ba saboda wacce ke yi min kunshi ta yi tafiya kuma wacce ta yi ma su Hauwa na ga kunshinta bai yi min ba sai ban yi ba.
    Mu aka bari da wahalan raba abinci shi dai na yi saboda Mimisco ce ta kirani da kanta ta yi mini mgana shi ya sa na yi abin da ta ce.

    Kafin bayan azahar kowa ka gani ya ci kwalliya sannan wasu sun ci sun sha ko na ce ana kan cin da sha ɗin. Sai a lokacin su Baby suka dawo an saka mata wani leshi mai duwatsu dogowar riga sai da na natsu na fahinci anko ne irin shi ne a jikin Gimbiya da Naja’atu da ƴayanta sun kuma saka musu ƙananun hijabi a saman kansu har takalmin su baki mai igiya iri ɗaya ne. Baby na ta murna ta nuna mini na ce kaya sun yi kyau na kuma yi ma Gimbiyar godiya ta na mirmishi ta ce mini bakomai.
    A she ban sani ba har da Jidda sai can wajajen La’aaar na ga Jidda ta sauya atamfa ta saka kayan itama tana murna ta ce mini Anty Gimbiya ta yi mata na ce ta gode.

    Rahila da Yaya Balki ne suka zo min biki domin ba zan saka Ma’u da ƙawarta a lissafina ba. Ni fa ban ma san ta zo ba sai da Yaya Balki ta ce kafin su fito sun yi waya ta ce musu ta na gidan tun ɗazu na ce ni kam ban san ta zo ba sai da suka ci abinci na raka su ɗakin Maman Farko suka yi mata Allah ya sanya alheri daganan muka shiga ɗakin Nene nan na ga abin mamaki Ma’u da ƙawarta shema’u filet ɗin abincin su cike da kaji da nama sannan suna tare da su Gimbiya da Anty Bahijja ana ta hira ana shewa.
    Tana ganin mu ta tsargu ni ko da gangan na kalleta kafin na ce” Su Ma’u manya maso bare kiƙi dangi. Kin zo amman ba ki iya nema na ba?
    Sai ta fara kame kamen ta nemi ni ba ta ganni ba sai tana taɓe baki kafin na ce” Muna shashen su Jawahir tare da su Hauwa.”
    Nan dai muka gaisa ni dai na kai su ciki su ka gaida Nene da Hajiyar Tafida bayan mun fito na ga sun tsaya suna mgana da Ma’u da shirina na yi tafiya ta. Allah ya so mu ma Mimisco ta ce mu ɗiba komai saboda namu baƙin kuma daman ina nemanta saboda ba a diɓar mana na mazajen mu ba, mun yi waya da Yallaɓai duk da sun yi reception a can akwai bukatar mu ijiye musu abinci.

    Anty Maimuna na tare da baƙin ta dangin mijinta. Sulaihat na gani na ce ina Mimisco sai ta ce mini tana bangaren Hajiya iya sai na kalli Anty Bahijja ina faɗin.

    ” Anty Bahijja muna bukatar nama sannan da waina.”

    Kai tsaye ta ce” Duk wanda aka ba ku fa?
    Nima kai tsayen na ce” To na mutane ne wannan, shi wannan da na ke magana na mazajen mu ne da suka tafi ɗaurin aure ne na yi ma Mimisco ma mgana.” > Janaftybaby: Sai gabaɗaya suka kalleni har da Gimbiya.
    Sai Anty Bahijja ta riƙe baki tana faɗin” To ma su miji. Mu namu mazajen da suka tafi fa? Ba su da rai ne ?
    Ina dariya na ce” Kowa na shi ya sani Anty Bahijja. Ba zan hanaki ki ijiye ma Baban Sulaihat ba. Amma ni kam sai na ijiye ma Yallaɓai duk abin da na ci.”

    Naja’atu ta buga guɗa kafin ta ce” Kin burgeni Anty Sadiya. Shi ya sa Kawu dai ya fara ajiyan tumbi.”
    Ina mata dariya na ce” Ai na iya kiwo ne.”
    Ta ce kwarai kam. Sai aka maida mganar dariya Anty Bahijja ta miƙe ta na faɗin.

    “Muje mai Yallabai.”

    Ta faɗa tana riƙo hannuna sai aka kara saka dariya ni ko sai na rike ta muka fita daga falon muna tafe tana ce mini wai shi Yallaɓan nan ba zai ci abinci acan ba ne? Na marairai ce na ce zai ci amman akwai tafiya kar ya dawo ya na jin yunwa.

    A can shashen Hajiya iya muka je ta diɓar min waina da naman na je na kawo kula ta saka mini tana ta min tsiya Mimisco ta kare min da cewa abin da na yi mai kyau ne mata da dama in ana sha’ani sai su manta da mazajen su.
    Ni dai na wuce na barsu ina zuwa na ce su Hauwa sun ci sun ƙoshi suna sakin tusa sun manta da mazajensu to ni na yunƙura na samo ma mazajen namu abinci sai suka fara min dariya nace su gode minibko na fasa ba su Munnira ne wajen gaba gaban gode mini. Su Rahila da wuri suka tafi kafin mangariba Ma’u kam tana gidan tawagan masu ɗaurin aure da amarya suka dawo. A shashen Hajiya Iya aka safki amarya da tawaganta. Ana yin mamgariba na kira Yallaɓai na tambaye shi ko yana ina? Ya ce min suna cikin gida a ɗakin Musbahu da kaina na yi lulluɓi na kai masa abinci da ruwa da lemu na san daman shi da Tariq da Uncle Abba ne nama daman da yawa na diɓar musu sauran na bar ma su Munirra domin na ga su ba su damu da cikin mazajen su ba.

    Yallaɓai sai da ya rumgumeni ya ba ni sumbata a baki kafin ya ce” Allah ga baiwarr ka nan Halima Allah ka jiɓanci lamuranta kamar yadda take jiblɓanta nawa.”

    Daman sun ce yunwa suke ji. Suna ma shirin tashi su fita su je su ci abinci a cikin gari ne sai ga ni, Tariq dai ba baka sai kunni ya fara cin nama Uncle Abba kuma sai ya kalleni kafin ya ce” Sadiya na ce wai ba ki da yar ƙanwa ne a gida?
    Gabaɗaya suka saka masa dariya nima sai da na dara kafin na ce” Babu Uncle Abba kana so ne sai a duba maka a dangi?

    Sai ya ɗau naman kaza ya saka a baki yana tauna kafin ya ce” Ina tunanin haka na gaji da wulaƙancin da yaran nan suke yi mini. Yusuf a gabana bai ji kunyar kama mace ba ina kawun sa.”
    Yallaɓai na cin waina ya ce” Ba fa Mace ba. Matata na kama. Kawu kuma ai ban hana shi aure ba ko?. In ka ji haushi gobe a ɗaura ko Tariq?
    Ya faɗa ya na kallonshi Tariq ya gyaɗa kai sannan ya ɗaga hannu Abba ya zungure shi da ƙafa yana faɗin” Shege sarkin cin abinci.”

    Ni dai gajiya na yi na fita na bar su domin ba za su fasa ba sai dai idan ba su haɗu ba.
    Farida dai na faɗa mata ba ta damuwa Tariq na tare da Yallaɓai. Su kuma su Hauwa suka ce wai na yi musu wayau na kwashe tsokoki na bar ma mazajensu kashi ina dariya na ce” To wai na hana ku diɓar musu ne da farko? Bana son son zuciya fa. Ku dai cigaba da zama.”

    Ranar ma ban kwana ba gida na koma amman tare da Farida da Sameena su Munnira ma gida za ta koma ta kwanta Hauwa ce na ga tana shirin ƙara kwana na ce ta je gida ta kula da mijinta tun da ban ga abin da za ta yi ba in ta kwanan
    Uncle Abba da Tariq Rano suka koma suka kwana Yallaɓai kan gida ya dawo su Farida a ɗakin su Jidda na sauke su da safe bayan mun karya mun yi wanka muka koma Gwammaja.
    Sai a ranar muka shiga muka ga Amarya. Doguwa ce baka mai jiki. A shashen da muka zauna ajiya yau ma nan muka zauna da farko ba mu yi niyyar zuwa gidan su Anty Zabba ba sai da ta kira Munnira ta ce tun da mun zama yan amarya ta yafe mu shi ne yasa muka shirya bayan azahar muka tafi can anguwarsu ta Rijiyar zaƙi.

    Da muka ce ga in da zamu a gidan kafin mu tafi, sai da Anty Bahijja ta yi ƙorafin ne zai kai mu? Ita da Anty Zulaihat wai ai da gangan ta ki sauka anan a yi biki gabaɗaya Mimisco ta kashe bakin su da cewa” Ku bar su je yana da kyau haka a matsayin su na surukan gidan nan” > Janaftybaby: Dole suka yi shuru. Mun je ma Anty Zabba biki da muka je har tana cewa ta yi fushi nima ta ce ko waya ban kira ba na bata hakuri.
    Anty Zabba har ta ɗan rame amman kuma ta yi gayunta tsab da ita itama ta yi taro gidansu cike da mutane yaran nata sai a ranar da za mu taho suka biyo mu zuwa gidan kakaninsu a daran kuma aka zagaya da amarya duka ɗakunan gida mu ma aka tara mu aka yi mata bayanimmu ɗaya bayan ɗaya.

    Washegari litini da wuri Ango ya ɗau amaryansa da Rakiyan ƙannensa mata su Anty Nasara suka raka su gidan su Anty Zabba suka haɗa su suka yi musu nasiha daga nan sai filin jirgi suka ɗaga sai garin fatacol sai fatan Allah ya ba su zaman lafiya ya kaɗe fitina.
    Shikenan gida ya watse baƙi da nesa da na kusa zuwa talata duk sun koma gidajensu Gimbiya dai ta na nan amman na ji Hauwa na faɗin daga nan Abuja za ta wuce an kira su kan mganar rabon gado. Mganar aikin ta kuma Yallaɓai ya faɗa mini an dawo da ita nan office ɗin NGO da ke reshen Jihar kano. Amman sai ta dawo daga Abuja za ta fara zuwa aikin.
    A lokacin da ya ke gaya minibsai da na tambaye shi.
    “A wajen Nene za ta zauna kenan?
    Sai ya gyaɗa min kai har yana ce min” Nene ma ta karɓe ta. Ta ce sai kuma aure zai raba su.”

    “Uhm!

    Kawai na ce a lokacin amman ban iya sake mgana ba.

    Sai bayan bikin Yaya Usman na samu damar yi ma Yallaɓai tuni kan Anniversery ɗin mu ya ce wallahi ya manta gwara da na tuna mishi. To shima zai ba ni kyakyawan surpise a lokacin in sha Allahu ina ta murna ina cewa ko Hajji za ka biya mini? Ya ce Allah ya sa haka.

    **

    Bayan wata ɗaya da bikin Yaya Usman. Kuma a yanzu dai muna cikin watan ramadan ne har mun yi azumi takwas. Da azumi ya gabato Yallaɓai bashi da kuɗi a hannu ya samu kwangilan aikin nan na kaduna akwai kuɗin shi da ya saka a ciki, to kuma ya saba duk shekara ana yi masa kunin sadaka Maman Saude sannan yana rabama yaran dake ƙarkashin sa kuɗi ko kayan abinci.
    Wannan karon ma da bai da kuɗi kayan abinci mu a ciki ya ce. A ɗibar ma Mutakka da gidan su Saude. Yaran shi na Office kuma kuɗi ya ba su, sannan gidanmu kuma 30k ya ba ni na kai musu da ƙwai da yawa da dankalin turawa wanda Uncle Abba ya kawo mana an cire ƙwai a gidan gonan shi Dankalin ma shi ya kawo mana buhu a ciki na dibar ma gidanmu da Muttaƙa.
    Nene ma Uncle Abba ya kawo mata kwai da kayan gona muma ma mun shaida su kwaiba da mangaro har muna kyauta. Muttaƙa ma Hauwa ta ce ya samu alheri tunda shi kaɗai ne bai kai su karfi ba. Geron da Mijin Mimisco ya raba ma su Yallabai a ciki ya ce na diɓar ma su Gwaggo sauran kuma a ka kaima Balaraba na kunun Sadaka. Duk da daman a gidanmu ba mu da matsala komai akwai Yaya Hamza da Yaya Auwalu da suke da ƙarfi sun wadata su da komai, sai dai ihsani da kyauttawa namu amatsayin su na iyayenmu.

    Mijin Amina ma ya aiko da kuɗi sauran alherin da aka samu ta bangaren su Yaya Balki an tura shi can Yashe wajen su Baba Sani. Ko Mijin Ma’u mota guda ya kawo na kayan abinci Baaba ai tana cikin alheri shi ya sa Yaya Aina ta ce a can kura Baaba ce yar gaban goshi to tana da ƴa tana auren mai kuɗi kuma ana aika musu da alheri. Ni Rahila ke faɗa,mini har dangin Babanta da azumin nan ta kai musu alheri.

    Gimbiya ta dawo wajen Nene da zama saboda aikinta. Sun je Abuja tare da ƙanin mahaifinta Tafidan Rano an raba gadon dukiya ta samu gida biyi anan Abuja da kuɗi masu yawa na tumanin takaba dukkansu huɗun rabon su kenan. Su gwara su da ƴaya ita bayan tumin takaba ba ta samu komai ba. Yallabai na ji suna waya kan tana son a saida gida guda ɗaya a siya mata a fili anan kano kuɗin ta kuma Mota ta ke son siya. Da ya ke komai sai ta yi shawara da shi abin da ya ce kar a yi ta bar shi kenan wanda ya ce a yi kuma shi take yi. Ta ɗan yi facaka da ƙudin bayan Mota ta siya manyan suturu da gwala gwalai, har su Jidda ta siya ma Takalma da dogayen riguna daga Dubai oder ma ta yi, sai yan uwa suka yi mata faɗa suka ce ta fara tunanin kasuwancin da za ta fara tunda kuɗin gado kamar ruwa su ke za su ƙare ba tare da ta yi komai da su ba.

    Note
    error: Content is protected !!