Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    Ganin da na yi Yallaɓai a ruɗe yake, ni kuma jikina duk ya saki ina kwance itama jaririyan na kwance cikin ƙazanta tana ta callara kuka, tun lokacin da ta faɗo ta callara kuka na san cewa da gaske ƴa mace na sake haifa.
    Sai na kira sunan Yallaɓai ya taho wajena sai na ce ya kamani cikin rawan jiki ya kamani na tashi zaune. Sai a lokacin na fahimci jaririyar tare da uwa mahaifa ta faɗo shi ya sa na ji fitowar abu sau biyu daga ƙasana.

    Zanin da ke jikina da ya yi gefe na ce ya ɗauko jiki na rawa ya tashi ya ɗauko sannan na ce ya buɗe dirowan gadon mu ya ɗauko kit ɗin mu na magunguna akwai reza a ciki, bayan ya kawo mini na karɓa na rike jaririyan shi kuma na ce ya riƙe zanin na saka ta a cikin zanin tana hannun shi sannan na daidai ta na yanke cibiyar na ce ya matsa daga wajen tun da gabaɗaya mun yi dama dama daga ni har shi cikin kazantar haihuwa.

    “Ya zan yi mata Sadiya?

    Ya faɗa yana kallona ya na kuma riƙe da jaririyar.

    “Ka naɗe ta a cikin zanin ka kwantar da ita a kan gado ka zo ka kama ni na tashi.”

    Haka ko a ka yi bayan ya kwantar da ita sai callara kukan jarirai take yi ya zo ya kamani na tashi tsaye. Na saka shi ya buɗe karamar akwatina in da na tara kayan haihuwa na ce ya ba ni na ɗaura. Bayan na ɗaura na ce ya je ya saka min ruwa a hiter tiolet da gudu ya fita ni kuma na tattaka ina ware ƙafa domin sai ina jin kamar na ƙaru ta ƙasana na isa in da yarinyar ke kwance na ƙura mata ido ina kallonta lalle dole ta ci sunan uwata. Domin a kammanni ma ni ta ɗauko.

    Yallabai ya dawo ɗakin ya ganni tsaye ina kallon ta yana zuwa na kalle shi da mirmishi kafin na ce.

    “Alhamdulillah mace na haifa Yallaɓai. Mace Allah ya sake ba mu”

    Sai kawai ya rumgumeni bai damu da yanayin da nake ciki ba. Cikin tsananin farinciki ya ke faɗin.

    “Alhamdulillah. Allah na gode maka da ya sake nuna mini wannan ranar”

    Wai a haka don ƙarfin hali Yallaɓai sai da ya sumbaci bakina na ture shi ina faɗin” Ko minti goma ban yi da haihuwa ba Yallaɓai?
    Sai ya yi mini dariya kawai bai ce komai ba.

    Shi na saka ya kwashe kayan su Jidda dake zube akan gado ya saka musu cikin wardrope kar su ɓaci. Ba ni da tsummokarai sai kawai na ce ya kwaso doguwayen rigunan da na ɗinka na yi amfani da su lokacin ina da ciki waɗanda shi da kan shi ya saka musu suna da buhu in naɗe kazantar da su kawai a kai su bola bayan an wanke tun da sun gama amfani.

    Jaririyar kuma na goge mata jiki da dotel, tare muka goge kazantar ni da Yallaɓai ina cewa ya bar shi yana mini faɗa wai na mayar da shi mara tausayi ta ya ina cikin wannan halin zan ce ya koma ya zauna yana kallona ai sai na yi shuru. Tas muka gyara wajen duk da ba sosai ba amma mun goge kazantar haihuwar. Ita kuma uwa mahaifa na ce ya je ya haƙa rami a haraba ya rufe. Ya ɗauka cikin wani zani ya fita dashi ya je ya rufe bayan ya dawo ya sake fita da cafet tun da a kan shi na haihu na ce ma Yallaɓai kawai a wurgar da shi ya ce a’a sai an wanke in zan yi kyauta da shi ne sai na yi amma ba zai bari a wurgar da shi ba.

    A baho babba da ya ɗauko muka tara kayan da muka yi gogen-gogen na ce ya fita dashi can ta ƙotar kitchen.

    “Kar ka ce kuma za ka wanke ka bari su Ya Aina su zo don Allah.’

    Sai ya ce minI to, sai da ya dawo ne na ce ya miko mini wayata, tana falon su Jidda ya je ya ɗauko ya kawo mini jikin sa na rawa. Jaririyar na jikinsa ya nace sai da na ba shi ita.

    “Kar ta ɓata ma ka jiki. Kasan gogewa kawai na yi ba a yi mata wanka ba.’ > Janaftybaby: “To ai jikin nawa ya riga da ya ɓaci ba matsala in ta ƙara ɓatawa”
    Sai da ya yi magana na lura shima dogon wandon da ke jikinsa duk ya ɓaci da jini har farar vest ɗin jikinshi wa ya ga maza yau sun yi aiki.

    Ya Aina na kira na ce mata ta zo gida na haihu.
    “Ke Sadiya”
    “Wallahi da gaske Ya Aina. Na samu ƙaruwan mace.”
    Sai ta yi kabbara kafin ta ce min gata nan zuwa domin na ce ta yi sauri ko yarinyar ma ba a wanke ba
    Sai da na gama wayar na duba lokaci sha biyu ne da wani abu zai iya zama gab da sha biyun na haihu ko kafin ma.

    Saboda na kira Ya Aina ya sa na matsa Yallaɓai ya je ya yi wanka jikin sa ya ɓaci.

    “To ke da ita fa?

    “Za mu yi in Ya Aina ta zo.’

    “Amma za mu je asibiti a duba mini ku ko?

    Sai na yi dariya kawai ganin yadda ya kama jaririyar ya rumgume.

    “Za mu je asibiti mana. Ka je ka yi wanka kafin ta zo”

    Da kyar ya ba ni jaririyar nan ya tafi ya yi wanka nima ya bar ni rumgume da ita har lokacin ina yi ma Allah kirari. Ina jin jini na zuba ta ƙasa na Allah ya sa na samu wani zani na tara a ƙasa na kafin na yi wanka. Na yi ta ma Allah kirari ina riƙe da kyautar da Ubangiji ya sake yi mini bayan na fidda rai. Ina ta hailala da kabarbari a cikin zuciyata domin Allah shi kaɗai ne wanda kum fa ya kum ne a lokacin da ya so a lokacin komai yake faruwa.

    Ina nan zaune Yallaɓai ya fito wanka, yana ma saka kaya ne Ya Aina ta kira wayata da cewa ga ta nan a bakin get shi ya sa a gurguje Yallaɓai ya shirya ya fita ya je ya buɗe mata suka taho ciki a tare yana gaba tana bin shi a baya har cikin bedroom ɗina sai ga shi ta ganni a zaune gefen gado riƙe da jaririya ai sai ta riƙe haɓa kafin ta ce.

    “Ikon Allah da gaske dai kin haihu?

    Sai kawai na yi mata dariya ba tare da na yi magana ba.

    “Wallahi Ya Aina ni kaina na yi mamakin haihuwar nan, abin da bai gaza mintina goma ba har ta haihu.”

    “Sannu Dubu. Sannu Dubu na ce barkan mu da arziƙi.”

    Ta faɗa lokaci ɗaya tana karɓan jaririyar da ke hannuna ni kuma sai na sakar mata ina faɗin” Yauwa Ya Aina.”
    Na faɗa ina mata mirmishi, gefena ta zauna a kan gadon ta na kallon jaririyar kafin ta ce” Ma sha Allah. Ga ta nan ko kamaanninki ta ɗauko Sadiya”

    “Shi ya sa na ce ta gama cin sunan Mama.”

    “In sha Allahu.”

    Yallaɓai ya ba ni amsa lokaci ɗaya yana kallona nima shi na kallah ina mai jadadda masa godiyata ta idanuwana. Ya Aina ko sai washe baki take yi cikin hamdala. Yallaɓai ne ya yi maganar tafiyar mu asibiti ya sa ta tashi ta ce bari ta saka ruwan zafi ta fara yi ma jinjirar wanka sai na ce akwai ma ruwan zafi a hiter ta tiolet
    Sai ta ce to bari ta yi amfani dashi bam damu ba sanin duk abin da ya kamata za ta yi kamar yadda ta yi mini a haihuwan Baby ita ta yi jinyata a asibiti har muka dawo gida shi ya sa nake ganin ƙimar Yaya Aina ta na yi ma zumunci kara da jikinta da aljihunta.

    Nan ta bar ni da Yallaɓai zaune mun ta sa jinjira muna kallo bakin mu ya ƙi rufuwa sai da ta ɗebo ruwan a baho sannan ta karɓe ta. Tas ta yi mata wanka bayan ta yi ta sauya ruwan Yallaɓai na faman kai da kawo, ta saba saboda in dai na haihu kaf dangina da dangin Yallaɓai sun san shi ba mai zama ba ne, da shi za a yi ta shiga da fita in na kamawa ne ya kama sai ya ga jama’a sun taru ne yake haƙura ya fice daga gidan. Na taɓa jin Anty Maimuna na yi masa tsiya a haihuwan Anwar wai yadda suka san shi da hidima a kaina in na haihu amma Gimbiya an mata aiki a asibiti ya bar gida kaca kaca bai iya gyara komai ba. A gabana ne ranar na je giden bayan an sallamota kai tsaye ya ce Sadiya kika ce, ba lalle abin da na ke yi a can na yi shi a nan ba. Sannan bai zama dole shima abin da na ke yi anan na je can na yi ba. Tana jin haka sai ta yi shuru ni ko a fili ma sai da na murmusa ban ji wani mamaki ba saboda sai da a ka yi mini kishiya na fahimci abu kaɗan ma da bai kai ya kawo ba in ba ka kai zuciyarka nesa ba sai kishi ya turniƙe ka. > Janaftybaby: Shi ya jawo mata akwatin da na haɗa kayan haihuwan ta shirya jaririyan cikin kayan sanyi masu kyau bayan ta shafe mata da man zaitun ta kuma gasa cibiyar sosai ta saka mata mgani saboda ta yi saurin faɗi, ta nannaɗeta cikin towel ta miƙa ma Yallaɓai da yake jira daman. Faɗa mini yake yi yanayin jikinta irin na Baby ne ƙatuwa ce mai kiɓa haka na haifi Baby kuma har gobe ta na nan da ɗan jikinta kuma wannan jikin na su Anty Bahijja ne ko na ce na Nene domin har yanzu da shekaru suka tura akwai jiki a tare da ita. Nan muka bar Yallaɓai Ya Aina ta iza ƙeyata tiolet ta kama mini na gasa jikina kuma sosai na ji daɗi a ciki ta bar ni ta fita zuwa kitchen ashe tea ta haɗo mini mai kauri da ƙwai sannan ta kawo min saban buredi ta bincika ta ga ma ina da garin kunu amma ba shi da yawa sai ta yi ma Yallaɓai maaganar gero sai ya ce in ya fita zai yi magana za a kawo.

    Ko da na fito shi yake faɗa mino ya yi ma ta huɗuba da suna Rukayya bayan ya lasa mata dabino a bakinta.
    “Allah ya raya mana Ruƙyyaatu Yallaɓai na.”
    “Na gode. Na gode. Na gode da wannan martabawan na ka. Ubangiji ya yi maka sakamako da wannan karan da ka yi mini.”

    Kafin ya yi magana Ya Aina ta dawo ɗakin tana tambaya ta omo sai na ce ta duba a dirowan kitchen duk da bai da yawa sai Yallaɓai ya ce in rubuta duk wani abu da ake bukata za a kawo anjuma.
    Ta juya da nufin fita sai na kira ta ina faɗa mata Yallaɓai ya yi mata huɗuba da sunan Mama.

    “Ma sha Allah. Allah ya raya mai sunan Mama. Allah ya sa ki biyo halin mai sunan.”

    Dukkanmh muka amsa mata da Amin Amin nan ta fice ta bar mu. Yallaɓai na riƙe da ita na shirya na saka wata doguwar rigana sai gashi ta shige ni, na ɗan ragu amma ciki na nan kamar ban haihu ba sai da Yallaɓai ya ce ko akwai twin ɗin Rukayya ne a ciki ba mu sani ba ina dariya na ce wani twin jini ne a ciki a hankali a hankali zai ta sauka amma zan ɗan riƙa ɗaure shi saboda koyarwa iyayen mu na da kenan ka riƙa ɗaure ciki a cewarsu in ka sake shi haka shi kenan zai bi jikin ka. Pamper na saka na tare ƙasana da shi sannan na zauna ina zaman ƙaryawa na biyu domin sai na ke jin kamar na shekara ne ban saka komai a cikina ba saboda yunwar da na ke ji ina tusa buredi a bakina ina kallon Yallaɓai na yi mata hoto.

    “Yallaɓai ba ka sanar da kowa haihuwan nan ba fa.”

    “Zan sanar yanzu.”

    Ya faɗa yana ƙara yi mata wani hoton har yana wani karkacewa sai da na yi dariya. Ni dai ai na sha mamakin yadda na iya ta da jug guda da tea na kuma haɗa da ƙaton saban buredi na cinye ga ƙwai manya faifai biyu lalle a gaida Haihuwa domin wani abu sai haihuwa in ba haihuwa ba da cikin jego ba ina ni ina ta da wannan uban ruwan shayin? Haka na faɗa ma Yallaɓai da na ga yana kallona sai ya yi dariya kafin ya ce.

    ” Ni wallahi hankalina baya kan ki. Ban ma lura da aikin da kika yi ba. Na ce to sannu da aiki Umma Sadiya.”

    Sai na fashe da dariya yana ta ya ni, a gurguje na shirya muka yi ma Ya Aina sallama muka fita muka barta tana ta wankin kayan haihuwa. Wayata ma a gida na bar ta, muna hanya ne, na ce ma Yallaɓai alkunyar Ruƙayya za mu riƙa kiran ta YUMNA. Ya ce abin da na ke so ai shi za a yi tun da Yallaɓai ya zama ni, nima na zama shi muna ta hiran mu har muka isa asibitin Aminu kano shashen masu awo suma sun yi mamakin haihuwanta da nake faɗa musu yadda lamarin ya faru, suka karɓi Yumna suna ta santi barin ma da suka ganni ras da ni kamar ban haihu ba. Ita dai Yumna an yi mata alluran su na jarirai ne domin rigafi aka ce ranar da ta yi kwana bakwai za mu dawo a yi wasu, ni kuma suka duba ni a tunanina ma na samu ƙari sosai sai suka ce na samu ƙari amma ba sosai ba. Amma dole ne suka rike ni sai sun yi mini ɗinki shi ya sa na kira Yallaɓai na faɗa masa sai ya ce ba damuwa sai ya jira ni daman muna zuwa sai da ya je ya yi sallar azahar da ta suɓuce masa.

    Ni ban sani ba ashe Yallaɓai ya ɗora hoton Yumna a status ya yi magana sannan ya tura a family group ɗin su na gida da cewa na sauka lafiya. > Janaftybaby: Ana ta kiran waya ta, mu kuma muna asibiti sai wajen gab da la’asar muka koma gida bayan an yi min ɗinki da dokokin na yi ta shiga ruwan ɗumi,tare da wasu magungunar da likita ya rubuta mini.
    Tun muna asibitin ruwan Nono ya fara zuwa har na ma bata ta sha, saboda tana ta rigiman alluran da a ka yi mata. Mu na mota a hanyar komawa gida sai da na ƙara ba ta, tana ta rigima ni kaina azaban nake ji daga ƙasana, saboda ɗinki kana ganina duk na jigata shi kuma Yallaɓai sai kiran shi a ke yi a waya a na masa barka yana amsawa a muryan shi cikin farinciki da Annushuwa.

    Ko da muka koma gida, jama’a cike. Rahila ta zo ita da Ma’u da Ya Murja. Ya Balki ce ba ta nan ta je suna a dangin mijinta Jigawa amma ta ce gobe za ta dawo. Nan na iske Hauwa mun dawo ba daɗewa sai ga Munnira da Mubeenan Musbahu sun iso suma, suna ta mamaki wai kamar ban haihu ba, ita kuma Munnira ta kama min masifa wai ace na haihu tun sha biyun rana amma na kasa kiran su sai dai kawai ta ga Mimisco ta poster jaririya a status ina dariya na ce ta yi haƙuri wayar a gida ma na bar ta mun tafi asibiti amma ba ta haƙura ba tana ta mita yadda suka shirya ma haihuwan nan ai kamata ya yi a ji haihuwan daga bakin su da ƙyar na samu ta haƙura amma in dai Munnira ce akwai ta da na cin magana.

    Nan na bar musu jaririyan Ya Murja ta saka mini ruwan ɗumi na shiga na gasa ƙasa na sannan na sake yin wanka ina fitowa suka kawo abinci mai rai da lafiya shinkafa da miya da nama suka ce cefane a ka kawo bayan fitan mu na san Yallaɓai ne ya tura kuɗi a ka kawo mana cefane, sai da na natsa sannan na ɗau wayata na ga tarin kira ba adadi. Har Gwaggo ta kira ni sai da na sake dubawa ne sannan na ga har Alhajin mu ya kira ni. Ya Auwal da Ya Hamza dukkansu tare da matayen su sun kira wayata. Sameena ma ta kirani ita da Nafeesa, ina ga lokacin da suka ji labarin haihuwan ne suka yi ta kirana sai dai na riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya ina kiran su muna gaisawa da ƙarfin gwiwata na ke faɗin sunan Mamana ta ci Rukayya amma za mu yi mata alkunya da Yumna. Sameena ta ce ai sun sa ni Yallaɓai ya saka a status ɗin shi lamarin ya ba ni mamaki na san ya kan saka hoto wani lokacin amma bai cika yin rubutu a ƙasa ba. Ban da Haihuwan Jidda lokacin a na cikin samartaka wannan ya ɗora ta ya yi ta ma Allah godiya amma Haihuwan Baby bai saka hoto ba ya dai yi rubutun ya samu ƙaruwa. Haka ma na su Anwar da Khalipa amma ita Yumna ta zo a sa a tun da har ya ɗora ta ya yi rubutu nan da nan na buɗe data na shiga na gani. Ta yi kyau ƙwarai a hoton wato wanda ya ɗauke ta ina zaune ne a ɗazu ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton shi ne.

    “Alhamdulillah. Allah na gode maka. Ubangiji ya sake azurtani da samun ƙaruwa daga Sadiyata. Na yi ta jira ban fidda rai ba, na yi ta ji a jikina Ubangiji bai yanke mini samun zuru’a daga tsatson Sadiya ba. Na yi haƙurin jira. Na shekara ɗaya,biyu, uku har zuwa shekaru goma ban cire tsammani ba. Kwatsam sai ga Ruƙayyatu(Yumna) kyautar da Ubangiji ya yi mana ita da misalin ƙarfe 12pm na rana. Ku yi mata addu’ar Allah ya raya mana ita tare da sauran ƴan’uwanta.”

    Ni kaɗai ina ta faman mirmishi, hoton na ɗauka nima na ɗora a status ɗina.
    “It’s Baby girl. Name Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna)”
    Nan na ga ruwan comments ana ta Allah ya raya.
    Har Hauwa Jamilu sai da ta buga ihu ta yo mini VN tana ce mini ikon Allah ba ta taɓa tunanin zan ƙara haihuwa ba.
    Maijidda Bala yar anguwan mu kuwa ta ce mini ita ko in sha Allahu sai ta zo suna sai na ji daɗi na ce mata ina gayyatar duka yan set ɗin mu in sha Allahu gagarumin suna zan haɗa saboda murnan samun Rukayyatu da na yi a lokacin da na fidda tsammani. Nan ta ke Maijidda ta tura mganar haihuwan tawa a cikin group ɗin mu na makaranta sai tagging ɗina a ke yi ana mini barka wanda bai gane ni ba ma su Hauwa na ta yi masu kwatance, a zuciyata sai na ji wani iri lokaci ya yi da zan gyara mu’amalata da ƙawayena ana yi da kai ai ya fi a ce ba a yi da kai. > Janaftybaby: Ranar yini na yi amsa waya da zirga zirgan mutane. Da yamma su Jidda suka dawo daga makaranta ai sai buga ihun murna da suka ganni da jaririya na haihu, Baby ta haye gadon ta ɗauke ta ta ƙamƙame tana faɗin na bar mata ina ta mata dariya Hauwa ta ce ta ɗauka ai daman na ta ne. Jidda kuma ni take kallo kafin ta ce” Wai da gaske kin haihu ne Umma?
    Ina hararanta na ce” A a ban haihu ba jaririyar roba ce.”
    Munnira da Hauwa na ta mata dariya sai ta ji kunya ta kauda kanta. Baiwar Allah sai ta matso kusa da ni a hankali ta na ce min” Umma amma ba abin da ya same ki ko?
    Sai na dafa kafaɗanta ina faɗin.

    “Ba abin da ya same ni Hauwa’u. Na gode da kulawa Allah ya yi miki albarka.”

    Sai ta yi mirmishi ta amsa da Amin a hankali. Da ƙyar Baby ta bari ta ɗauki jaririyar nan sai da Munnira ta zare mata ido tana faɗin” Ke ba fa taki ce ke kaɗai ba.” Sai Baby ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka Hauwa ta rumgumeta tana lallashinta ni dai ina gefe ina mirmishi su da iyayen su. .Su Rahila da Ma’u da su Ya Aina suna can tare da su Mubeena suna aiki Tuwo suke yi Ya Murja kuma ta koma gida sai da safe za ta dawo da yamma nan sai ga Zabba’un Ya Abubakar fakam fakam da cewa daga gidan Gwaggo take ita ke faɗa mata na haihu sai a lokacin na tuna ban kira su ita da Alhajin mu ba sai na bari sai da a ka idar da sallar mangariba sannan na fara kiran Gwaggo. Ita ce bayan ta min barka na faɗa mata sunan Mama jaririyar ta ci.

    “Haka Aina’u ta ce. Allah ya raya mana ita cikin addinin musulunci”

    Na amsa mata da Amin Amin sai ta miƙa ma Alhajin wayar ni na fara gaishe shi cikin girmamawa.

    “Lafiya lau Dubu an buɗe ido lafiya! Na amsa masa da lafiya lau.

    “Kin tabbatar da ba abin da ke damun ki?

    Ina mirmishin jin daɗi na amsa masa da cewa ba na jin komai alhamdulillah.

    “To Allah ya ba ki lafiya. Gwaggon ku ta faɗa mini sunan jmRukayya kika ma yar ko?
    Na ce E Alhajin mu nan take ya fara kwarara mata addu’o’i.

    “Allah ya albarkaci rayuwarta Allah ya raya ta. Allah ya tsare ta daga sharrin zamani. Allah ya ba ku ikon yi mata tarbiya. Allah ya yi musu albarka ita da sauran yan’uwanta gabaɗaya. Shi kuma mahaifin su Allah ya yalwata masa arziƙinsa yadda ba zai gajiya ba wajen hidimar ku gabaɗaya.”

    Na yi ta amsa da Amin Amin ni dai sai da na kashe wayata ina jin tahowar ƙwalla a cikin ƙwarmin idanuwana. Allah sarki iyaye ma su daɗi a fili sai da na ce” Allah ya jiƙan ki Mama “
    Na faɗa ina mai kallon jaririyar da ta ci sunan ta, ta na kwance tana sharan barcin ta, duk ba su tafi ba sai bayan isha’i bayan har wanka Ya Aina ta sake yi ma Yumna ni ma na sake yi na shiga ruwan ɗumi sannan na take cikina da tuwo miyar agushi da kuni dukkansu sun tafi da cewa sai gobe za su dawo suka bar sai ni kaɗai sai yara can zuwa ƙarfe tara sai ga Yallaɓai ya dawo gidan ya taho mini da fura da kayan marmari da yawa na ce Jidda ta karɓa ta ɗaurayo ma na sauran kuma bayan sun ɗiba ta saka shi cikin frizer.

    Yallaɓai na gidan Mimisco ta kira ni ta yi minI barka bayan ita sai Anty Bahijja ita Anty Maimuna daman tun ɗazu ta kira ni, abin mamaki Gimbiya ba ta kira ni ba sannan ta ga status ɗina amma ba ta mini magana ba. Na so na yi ma Yallaɓai magana sai ban yi ba yana gidan har wajen sha ɗaya saura na dare nan ya ci tuwo ya zauna riƙe da Yumna muna ta hira da ni da shi da yara. Amma Gimbiya da ta kafa kira sai da ya yi mana sallama ya tafi, yau girkinta ne a fargabanta kar ya kwana a wajena tun da na haihu. Dama muna mganar abubuwan da babu ne na ce masa akwai komai sai dai kayan abinci in zai ƙaro sai omo da sabulun wanka da na wanki sai geron da Ya Aina ta yi masa mgana sai ya ce mini na rubuta na aika masa da shi gobe da safe Musbahu zai kawo min. Haka ko a kayi kafin na kwanta na rubuta na tura masa, tare da yara muka kwana Yumna ta tashi da kukan dare bayan na ba ta nono na sakar ma Jidda ita tana lallashinta ban ma san yauahe suka kwanta ba ni dai kamar ƴar maye haka na kwanta ina barci. > Janaftybaby: Washegari tun safe Ya Murja ta fara dira ko da ta zo ma har Jidda sun yi wanka ta gama ɗumama sauran tuwon jiya. Baby ce har da rigiman ita ba za ta je makaranta ba na ce lalle ta na da aiki ni masifa na fara mata za ta fara mini kuka na ce zan mata bugun tsiya ƙarshen ta dai Ya Murja ta lallaɓata sannan ta amince suka tafi. Yau Ya Murja ta yi ma Yumna wanka nima ta taimaka mini na gasa jikina bayan na shiga ruwan ɗumi saboda ɗinkin dake jikina. Sannan ta fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Gwaggo ita da Balaraba Maman Saude sun zo mini barka kamar haɗin baki sai ga Nene da Hajiya Iya sai Maman farko Adnan ya kawo su sai da na faɗa musu Yunma ta zama mai sa’a kishiyoyinta na ta kara kaina a kanta suna ta dariya. Sun ji daɗin ganin mu tas lafiya lau kamar ban haihu ba. Ba su wani jima ba suka tafi amma Balaraba sai ta tsaya tana kama ma Ya Murja aiki. Bayan fitan su ba daɗewa sai ga jama’ar Gandun albasa ni da kaina na kira Inna Mariya na sanar da ita na haihu, tare ta ke da matan su Kawu Tasi’u dukkansu dai suka yi mini barka ba daɗewa suka tafi.
    Da safen Musbahu ya kawo buhun gero sai rabin buhun siga sai kwalin omo guda biyu, tissue sai kayan tea da yawa saboda daman na ce masa sun kusa ƙarewa. Kayan abinci kuma ya ce sai anjuma za a kawo daga kasuwa.

    Ranar ma kamar jiya ne, yini gidan ya yi a cike da yan barka Amina ta kira ni a waya tana faɗin tun ana jibi suna za ta taho na ce daman ban ɗauke ma kowa ba har su Ya Hamza na faɗa musu in su na yafe musu to ban yafe ma matan su ba. Tun da na haihu kullun gidana Munnira da Hauwa suke yini da Mubeena , Su Ya Aina ma kullum sai sun leƙo Ma’u da Rahila suma kullun sai sun taho kamar haihuwar farko. Yadda na daɗe ban haihu ba , ba shakka na faɗa ma Yallaɓai taro zan yi ba ni da taro ba domin na yo gayya. Har Tariq da ya kira ni ya yi mini barka sai da na ce ban ɗauke ma Farida ba. Haka ma Kawu da ya kawo Marwa shi da ita na ce to ya sani tun ana gobe suna domin suna zan shirya sunan da ban taɓa yi ba yana dariya ya ce ya amince mini domin ya cancanci na yi taro na gani da za a ba da labari.

    Amma Yallaɓai na neman ya kawo minI yawa wai shi ba shi da kuɗi ya faɗa mini an gama ginin kamfamin shi yanzu oder kayan amfani ke gaban shi zuwa farkon shekaran 2021 yake son su fara aiki. A takaice dai yana faɗa mini ba shi da kuɗi na ce na ji ya ba ni iya abin da ya yi niyya.
    100k ya tura mini na shgalin suna, 100k kuma ya ce na siya kayan fitar suna ni da yara. Daman ni bai san ina da kala uku a ɗinke ba cikin kuɗin da ya ba ni na hidimar haihuwa na siya ma kaina. Da kuɗin da ya ba ni sai na siya mana wani swiss lece mai kyau blue ni da yara daman suma na yi musu kala ɗaya na Atamfa super kowaccen su na yi mata riga da zani. Nima na ɗinka super wax ɗin amma kalata na dabam ne. Sannan su Munnira sun fitar da ankon suna wata vatik mai kyau da yarari, suka kuma ce ba su ɗauke ma kowa ba. Kaf yayyena sun siya tun da Munnira ce ta saro ankon haka Farida ta ce a ɗaukan mata in kai mata ɗinki ita da Amina Marwa ma an nan kano a ka kai mata ɗinki har Saude da ke dutse ta siya itama za ta zo matan su Ya Hamza a mota a ka sanya musu na su a cewar su ba su yarda a ɗinka musu a nan ba. A dangin Yallaɓai daga Sameena sai Jamila da Suwaiba suka yi, Mimiaco ba ta yi ba amma ta yi ma yaranta ƙananun Mubeena daman yar gidana ce, Munnira duk ta nuna ma su Anty Bahijja amma take faɗa mini Anty Maimuna sai da ta ce wai na cika tsirfa haihuwa ta ukun ne sai na fidda anko ita kuma ta ce su suka fidda. Ba dai wacce ta yi mu ma ba mu damu da su yi ɗin ba domin ba saboda da su muka fidda ba. Na tura su Hauwa Jamilu da su samira duk sun siya an akai musu har gida sun yi mini alƙwarin zuwa mini suna.

    Gimbiya ma ba ta siya ba ni da sai da na kwana biyu da haihuwa sannan ta zo mini barka da borin kunya wai ba ta samun zama ne ga aiki ga shago ni dai tak ban ce mata ba. Da Munnira ta nuna mata ankon sai ta ce ba a nuna mata da wuri ba ba lalle ta samu ɗinki ba har tana cewa ai irin wannan in an san za a yi sai a fiddo shi tun kafin in haihun. > Janaftybaby: Munnira na ba ni labarin amsar da ta ba ta sai da na yi dariya wai su yanzu suka ga damar fiddawa kuma ba dole a ka ce sai ta yi ba daman fita haƙƙi ne. Na yi dariya sanin halin Munnira da ba ta barin ta kwana. Har Naja tana ta ya ƙawarta kishi ba ta yi ankon nan ba, ba domin ya gagare ta ba Anty Zabba ba za ta samu zuwa ba amma ta ce mini zan ga saƙo in sha Allahu. Su a tunanin su sunan da zan yi duk na salon na saka ɗan’uwan su kashe kuɗi ne domin Anty Bahijja ma ta furta a can gidan Nene a na jibi suna Suwaiba da ta zo ta ke faɗa mini, ni ko na ce ya ba ni kuɗi da kayan abinci amma sauran hidima tawa ce ba hannun Yallaɓai a cikin shi. Ni Halima ce ma ta ke ƙara ba ni mamaki sau ɗaya ta zo mini barka shima ba ta wani daɗe bs ta yi tafiyarta. Na tuna lokacin da nake zuwa gidanta na ci uwar aiki amma yau ni ce banza a idanuwanta Gimbiya ce gwana. Na yi kyafci a cikin zuciyata domin na saka ma raina akwai ranar da in ta mu ta haɗo mu sai na yi mata wankan tsarki da za ta gane ba ta da wayau.

    Tun ranar litini da ya kama ana goben sunan Yumna gidana ya ɗinke da baƙi. Daman tun da na haihu na ce Yallaɓai ya koma wajen Gimbiya ya ce bai ga dama ba sai jiya ne ya tafi can amma ban sanin masa ko zai dawo bayan suna ba amma ni dai na ce masa ya koma gidanta har sai na yi arba’in ya ce ban isa ba. Amina tun safe suka sauka ita da Farida tare suka haɗa tafiyar Marwa ma da azahar ta iso. Rahila da Ma’u da kayan su suka taho tare da yaransu daman na faɗa musu in suka zo sai an gama suna can kuma sai ga Sameena sai da muka rumgume ga shi dai ƙanwar Gimbiya ce amma tana ƙaunata saboda da Allah. Daga Rano ta ke sannan ta sauka a gidana. Su Munnira daman ai suna nan sai suna ya tashi. A ranar mai ƙunshi ta zo ta yi mini saloon kuma tun safe na je shagon Amesty ta yi mini. Har su Munnira sun ce za su yi ƙunshin. Can sai ga Saude ta iso itama sai na ji daɗi su Khaleesat ne sai gobe amma Laila Ya Auwal ya ce mini ta na hanya.

    Gida ya kacame da ayuuka. Da yake za su yi waina sai sinasir da aikatau muka kai sannam za su yi alale da shinkafa jalop mai kaza. tun da akwai naman miya da Yallaɓai ya aiko da shi. Raguna kuma uku Yallaɓai zai yan ka ma Rukayy suma ragunan su Suwaiba na faɗa mini su Anty Bahijja suna ta surutu ni a bakin ta ma nake jin raguna biyu Ya Usman ya siya masa ɗayan kuma Mimisco ce kuma ya ce tun da da sunan Rukayya a ka ba da su to duka za a yanka mata su. Sannan nima na ba da a yi mini tsire sannan na saka mai yin ledojin kayana na hijabai ya buga mini na suna da jakar nan mai ɗauke da sunan Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna) name on 17 November 2020
    Cut-ceey: Hauwa’u Yusuf Muhammad(Jidda) and Maimunatu Yusuf Muhammad(Baby)
    Lemuka da ruwan roba katan katan Yallaɓai ya saka a ka sauke mini sanman ni kuma za mu yi zoɓo da kunin aya duk za mu saka a robobin ma su ɗauke da sunan Rukayyatu.
    Wanda a ledan za a saka mutum da jalof ɗin shinkafa mai kaza sai tsire da zoɓo wannan na in zai tafi gida ne. Da yamma kwandon tumatir da solon tattasai da attarugu mai yawa Musbahu ya zo da shi tare da gyararrun kaji guda ashirin a buhu, lokacin su Anty Bahijja da su Gimbiya duk suna gidan ba aikin da suke yi sun kame a gefe suna tsegumi tare da taɓe baki ni ko kallo ba su ishe ni ba, da suka ga an kawo wannan kayan nan kamar su mutu sun ɗauka Yallaɓai ne ke ta kashe mini kuɗi tun da nima yar matsiyata ne ba ni da kuɗi. Ya Hamza da Ya Auwal sai suka suka haɗa mini 150k na kuɗi saboda na ce musu zan yi suna kuma Yallaɓai ba shi da kuɗi, abin da ya ba ni ba za su ishe ni ba, Shi ya sa suka tura mini kuɗi har Datti sai da ya tura mini 30k ya ce na ƙara. Kawu Abba 50k ya tura mini bayan Marwa ta zo mini da atamfofi masu tsada guda uuku da kayan jarirai. Amina ma turamen ta kawo mini da kayan jarirai Farida ita ma turminta huɗu da kayan jarirai sama da guda biyar, tun kafin goben ta yi gefen gadona ya fara cika da kaya sannan wasu ma hidiman su Munnira ke yi ba sa faɗa mini. Suma ita da Hauwa turame uku suka yi min da su pampers da kayan sanyi sannan sun ba da an yi mini yajin jego mai yawa mai daddawa. > Janaftybaby: Ina can cikin ɗaki ban sani ba Hauwa ta zo tana faɗa mini wai ashe sai da Anty Bahijja ta kira Musbahu tana tambayan shi ko Tafida ne ya ba da saƙo ya kawo? Shi kuma ya ce ni na tura masa kuɗi ba Yallaɓai ba ni tana faɗa minibsai da na bushe da dariya. Matar nan ba za ta bar ni na huta ba na yi alƙwarin in ta sake magana a gabana sai na mayar mata da martani ana cikin gida a na aiki su kuma suna zaunes sai ji da jiyarwa.

    Bayan mangariba mai ɗinkin mu ya kawo mini sauran nawa da na yara sai na Farida da Amina. Ni na fita har haraban gida na karɓa muka yi maganar ƙarishen kuɗin ɗinki na dawo kenan falon Baby ta tare ni tana faɗin wai Anty Gimbiya ba ta zo da su Khalipa ba. Kayan ɗinkin da ke hannuna na miƙa ma Amina da ta zo ta tare ni da mgana na ce ta bari in zo.
    Ina sanye da doguwar riga tsaraban makka ne cikin tsaraban Yallaɓai., rigar ba takai mini har ƙasa sosai ba tana da mayafinta shi ne ma jiki na, na yi kyau ɓulɓul da ni domin ga ruwan zafi daman sannan kuma na saka Aisha lame ta kawo mini mai da shower gel, kuma ina kula da jikina ina cin mai kyau ina shan mai kyau ni kaina na san na yi kyau da haihuwan Yumna sannan cikina ya fara komawa jikina ya yi cif sai na zama wata yar dumduma gwanin sha’awa kowa ya zo ya ganni sai ya ce mini na ƙara kyau da na haihu mene ne sirrin? Na ce Yallaɓai ne sirrina muna ta dariya.

    A tsakiyar falon Yallaɓai na tsaya tun da nan suke zaune har da su Halima. Anty Maimuna ba ta zo ba itama Anty Bahijja gulma ne ya kawo ta. Yau ga shi Anty Bahijja na zaune amma bayan gaisuwa ba abin da ya ƙara haɗa su da Ma’u duniya juyi juyi. Gimbiya ta ƙura mini ido tana kallona ita kuma Naja da gayya take ce mini” Ka ga uwar gida a gidan Uncle Tafida”
    Na yi mata fari ina faɗin” Faɗi ki ƙara Uwargida mai babban muƙami a wajen megida “

    Sai ta yi shuru ai ba zan bari ta saƙa mini magana ba Gimbiya na kalla ina faɗin” Baby ta kawo min ƙaran ki.”
    Sai ta yi wani luu da ido kafin ta ce” Ni fa? Me ta ce miki na yi?
    “Ta ce ba ki zo da Khalipa ba”
    Anwar ma da za ta zo da shi ya na wajen Halima.
    “Ayya ai Khalipa na Rano Anty Marliya da ta zo ya saka rigima sai ya bita sai kawai na ce su ta fi dashi.”
    Sai na jinjina kai kafin na ce” Amma ai da kin ce su zo da shi saboda suna ko?
    Kawai karaf Halima ta saka bakinta.

    “Don dai suna me ya sa zai dawo? Suna dai ba biki ba fisabilillahi.”

    “To nima shi na gani.”

    In ji Naja.

    Anty Bahijja dai ba ta yi mgana ba, ni ko sai na juya ina kallon Halima kafin na ce” Aa. fa ba suna kawai ba wannan sunan ya sha bambam da sunan da kika saba zuwa ko gani Halima. Suna ne garurumin da baki taɓa ganin irin shi ba.”

    “Allah ko?

    Ta faɗa cikin mamaki ni kuma sai na gyaɗa mata kai, muna cikin haka ne sai ga su baby da murna da akwati Laaila ta iso mutanen Abuja. Muka rumgume juna ina yi mata maraba ta gaggaisa da su Anty Bahijja. Yara wajen ɗaukan wata leda suka yagata kayan ciki ya zube kayan fulawa ne ta yo mini cincin da donot sai cake, ina ta faɗa sai ta ce ai namu ne ta zo mini da shi saboda gobe. Ta ce mini ma ta saka ƙanwarta ta yi mini meatpie gobe za ta kawo. Su Amina duk sun taho falon da suka ji tahowar Laila.

    Munnira ta daddage ta rangaɗa guɗa Amina na ta ya ta. Ina ta dariyan farinciki na ce”Na gode Anty Laila.”
    “Ba komai an zama ɗaya. Kin ga yadda yayanki ya ruɗe. Ki yi ki gama aikin nan ki tafi kayan fulawan nan ma duk tare da shi muka shiga kasuwa muka siyo komai ina cewa ya bari na siya da kuɗina ya hana shi dai faɗi yake Sadiya ce ta haihu ta yi ma Mama takwara saboda haka muma za mu yi ma wannan haihuwan na ta kara.”

    A gaban su Anty Bahijja ta fiddo mini kayan suna. Atamfa biyu leshi ɗaya sai kayan jaririya guda bakwai bayan su pampers da mayuka da rigunan sanyi. Har su Aina sun ƙariso suna ta ɗaga kaya suna gani da farinciki. Amina ta ranguɗa guɗa tana faɗin” wannan yarinya ta ga gata. Ta shaida ita ɗin yar dangi ce gaba da baya.”

    “Tabbas yar dangi ce. Ya Hamza ya nuna bajintarsa ga Ya Auwal ma ya nuna na shi Ubangiji Allah ya bar zumumci.” > Janaftybaby: Aka amsa da Amin gabaɗaya da gayya ba na ce” Kuma duk sun tura mini kuɗi duk da su na yi wasu hidiman.”
    Mu mun man ta da su Gimbiya a falon ma ballanta su ce da gayya mu ke yi sai da daga baya ne da muka haɗa ido da Gimbiyar sannan na ce bari nima na ɗan ɗana.

    “Na daɗe da sanin ni yar dangi ce amma na ƙara ganin kara a haihuwan Rukayyatu. Na ga karamci a wajen ku yan uwana na gode. Alhajin mu ma buhun shinkafa cir shanshera ya ba ni saboda Rukayya”
    Su Rahila har da kabbara
    Ni kuma na cigaba da faɗin “Mijina ya yi mini dukkan gata na gode masa. Sannan ƙawayena da ku dangina gabaɗaya kun rufa mini asiri kuma ina mai gode maku uUbangiji ya ruɓanya muku.”

    Munnira da Amina sun fi kowa zaƙin murya wajen amsawa da Amin
    Munnira har ta na faɗin wani abun ma sai gobe. Ta ba ni hannu muka tafa ni da ita. Gabaɗaya su Gimbiya sun gama muzanta Anty Bahijja ma ba san tafiyarta ba na ji daɗin haka saboda ta fahimci ba Yallaɓai kaɗai ya yi mini hidima ba, Gimbiyar ma sai wajen tara na dare suka fita tare da Naja da Halima sai bayan tafiyar su ne da muka zauna da Sameena nake jin wasu manganganu. Ni da ita ba mu taɓa zama mun yi maganar zama na da Gimbiya ba sai ranar. Kusan raba dare muka yi muna hira na faɗa mata wasu rigingimun da suka faru tsakanina da Gimbiya. Itama tana ba ni wasu labaran da ban san da su ba.

    Ashe Gimbiya kishi take yi da ni da tana da iko da tuni ta koreni. A bakin Sameena nake jin ko maganar haihuwan ta ce Tafida sai rawam jiki yake yi a kaina kuɗin shi duk a kaina da yayana ya ke ƙarewa to daɗin abin ma dai ban yi irin haihuwanta ba mace na haifa. Haka ƙannenta suke ta faɗa da masu goya mata baya. Kuma wai a haihuwan nan da na yi sai da ta nemi ya ranta mata kuɗi ta biya kuɗin shipping, amma ya ce mata ba shi da kuɗi aamma ni ga shi nan ya ba ni kuɗi ina ta wadaƙa har suna na shirya mai kama da biki. Har cewa ta yi yadda Yallaɓai ke jin maganata ko Nene albarka.

    Na yi dariya kafin na ce ma Sameena.” Duk maganganun su Anty Bahijja a kaina ne itama ta ɗauka. Ni gaskiya na riƙe kuma shi ke riƙe da ni har gobe. Maganar hidimar suna kuma wallahi kayan abinci da kayan sawa kawai Yallaɓai ya yi mini. Sai sauran abin da ba a raasa ba. Maganar gaskiya nima na yi hidima da kuɗina sannan ku ma da muke tare kun yi mini amma ba kuɗin Yallaɓai ba ne balle hankalinsu ya tashi kar na karar da kuɗin ɗan’uwan su.”

    Sameena ta ce wallahi ita ta sani ita ko magana ta ji a kaina ba ta yarda. Lamarin Gimbiya ya daina ba ni mamaki tun da kishin take so a yi to za a yi. Sannan suna kuma za a yi sai dai ta mutu.

    Ni Allah ya ji ƙaina da ban yi haƙuri a lokaci haihuwar Gimbiya ba, da tuni an buga mini tambari amma yau da na yi haƙuri ga shi komai ya wuce abin da Yallaɓai ya yi mata ko rabin shi bai yi mini a haihuwan Rukayya ba amma Na tsaya mata a ƙahon zuciya saboda kishi da baƙin ciki.

    *Janafty* > Janaftybaby:

    Note
    error: Content is protected !!