Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    RANAR SUNA.
    Talata.
    17,November. 2020

    A safiyar talata muka tashi da hidiman sunan Rukayyatu(Yumna). Da yake duka nan suka kwana tun asuba suka tashi da aikace aikace kafin ka ce kwabo an gama komai. Alele ne ma ƙarshen gamawa amma waina tun asuba suka fara suya tun da tun a daran jiya suka haɗa ƙullun wainar miya kuma da safen nan wuta kawai suka ta da mata tun jiya sun gama haɗa komai. Kafin azahar komai ya kammallah gida ya fes sannan duk mun yi wanka amma ba mu saka anko ba sai bayan ƙarfe biyu amma ni da yara da ba su je makaranta mun saka sabbin kaya muna walwali. Yunma ma tun safe a ka yi mata wanka a ka saka mata kyakyawan kayan jarirai masu kyau da safa da takalminta na yara mai kyau da hula cikin kayan da Yallaɓai ya ba ni kuɗi na siya mata ne.

    Da safen nan ya zo ya gan mu har Amina ta matsa masa sai da ya tsaya muka yi hoto. Shima ya sha farar shadda har da babban riga har sai da na ce masa
    ” Yallabai hala kai ma walima za ka haɗa mana?

    “A’a kawai na yi shigar fararen kaya ne domin nuna murnata a wannan ranar”

    Abin da ya faɗa mini kenan na yi shuru kawai ina kallon shi ya yi kyau sosai. Sajen sa na shafo in da tsillin furfura suka fara fito masa, Yallaɓai fa yanzu shekarunsa wajen arba’in da takwas ne yana ƙoƙarin shiga gidan hamsin Allahu akbar jiya ba yau ba, ni ina ta kallon shi a matsayin ɗan saurayin da na aura ɗan shekaru ashirin da bakwai da takwas a duniya.

    “Kallon fa Madam?

    Shi kan shi ya gaji da kallon sa da nake yi sai da ya yi mini magana sai na yi mirmishi. Na isa gare shi na rumgume shi, shima sai ya kama ƙuguna ta baya yana faɗin” Wata Sadiya ta yi kewar Yusuf ɗin ta ko?
    Ya faɗa yana sumbatar wuyana. Sai na noƙe ina ɗan mirmishi mun daɗe a haka muna shaƙan turaran juna sannan muka saki juna lokaci ɗaya muna masu kallon juna. Mun raja’a a kallon juna sai da shigowar Amina da kukan Yunma ya fargar da mu sannan muka saki juna na karɓeta na zauna gefen gado shima biyo ni ya yi shi ya zage min zip ɗin gaban riga ta na fito da nono ina ba ma Yunma. Yana zaune gefena muna hira yana faɗa mini Tariq da Kawu sun tura mai kuɗi wai ya ƙara na hidimar suna.

    “Allah ya saka musu da alheri. To sai ka ƙara mini wani abu don Allah Yallaɓai.”

    Na faɗa har langwaɓe kaina sai ya wani kalle ni kafin ya ce” Da ga jin na ce an ba ni kuɗi sai ki ce na ba ki? Ke yanzu me ya rage ba ki yi ba ko ba ki siya ba?
    “Yallaɓai ban ɗauko mai DJ da mai hoto ba fa”
    Na ƙarishe faɗa cikin shagwaɓa har ina tura masa baki.

    Yallaɓai sakin baki ya yi hakan bai ishe shi ba sai da ya riƙe haɓa yana faɗin” Kika ce me?
    “Na ce DJ da mai hoto. Domin kasan Haihuwan Yumna na dabam ne za a sha shagali.”
    “To ni ba da ni ba.”
    “Acikin gida ne fa Yallaɓai ba matsala tun da duka taron na mata ne.”
    “Ba amince ba.”
    “Yallaɓai.”
    “Sadiya na ce ban amince ba ko?

    Ya faɗa yana mai kallona a fuskarsa da maganarsa na fahimci ba wasa yake yi ba.

    “To shike nan.”

    Na so na yi fushi ne amma sai na ga bai damu ba kawai ya miƙe yana saɓa babbar rigan shi. Duƙawa ya yi ya sumbaci goshin Yunma kafin ya dago nima ya sumbaci kumatuna lokaci ɗaya yana faɗin” Na tafi. Take care a yi suna lafiya.”
    Da dai na ga zai tafin sai na ce to ya taimaka mini da kuɗin zan kira ko mai hoton ne.

    “Wani irin mai hoto kuma Sadiya? In hoto kike so ba ga wayoyi nan ba? Sai kin gaji da hotuna yau.”

    “Ni fa ba irin shi ba. Na camera nake so”

    “Lalle.”

    Yallaɓai ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin” Ni ba ni da kuɗi kin cika tsarabe tsarabe Sadiya. Suna ba dai a ci a sha ba ne? Kuma na tanadi abinci miye wani hoto? Hoton ma da a ka ce haramun ne?

    Ni dai ai sai na kasa mgana ina ji ina gani Yallaɓai ya fice ya bar ni zaune bai ba ni ko sisi ba, to ya za a yi ya ba ni shi da ya ce hoto ma haramun ne. Dj dai tun da ya hana amma mai hoto kam zai zo daman mun yi magana da Samira class mate ɗina ita ce na taɓa zuwa sunan yaronta na ga an kira shi sai ta ce mini ƙanin mijinta ne. > Janaftybaby: Na ɗauka zan samu wani abu a wajen Yallaɓai ne sai na ƙara tun da ban samu ba sai na ɗauka cikin kuɗina na tura mata rabi, anjuma da yamma zai zo, na samu kuɗi sosai ko Anty Zabba 20k ta tura mini ta ce ba yawa ni ko na ce mai yawan kenan, ina ta mata godiya. Har mai makeup na samu ita kuma ƙawar Anty Khaleesat ce tare suka yi makaranta ta yi mata mgana itama anjuma za ta zo ta yi mini kafin baƙi su fara suwa.

    Kaf yan uwan Mama na gandun albasa sun taho mini suna. Kuma na ji daɗi sai na sauke su a ɗakin su Jidda. Falon Yallaɓai kuma na ce a bar ma dangin Yallaɓai saboda ba na son ƙananun mganganun falon su Jidda kuma yan gidanmu da sauran mutane ciki kuma ga bedroom ɗina na zauna ni da ƙawayena da mutanen arziƙi. An kawo sinasir da tsiren sannan tun jiya a ka haɗa da kunin aya suka ɗuɗɗura a gorinan suka saka sticker a fridge ma suka kwana ina ganin haka sai na kira su Ya Aina na ce su raba komai kashi uku, ɗaya namu ne da ƴan’uwan mu ɗaya kuma na yan uwan Yallaɓai ɗaya kuma ni da ƙawayena da yara tun da Baby ta ce mini yan ajin su za su zo Jidda dai na san hali ba gayya za ta yi ba.

    Bayan na saka an diɓar ma su Gwaggo na ba da a ka kai musu sannan na saka Hauwa ta ɗibar ma Gwammaja suma suka aika da shi can wajen su Nene. Na saka suka ɗibar ma Yallaɓai na ce zam kira shi in yana office ne zan kira Musbahu da Adnan matan kuma na ce su ɗibar ma yaran su da mazajen su a yi komai cikin tsari. Na bangaren mu ragamar na hannun Amina na bangaren su Yallaɓai kuma Munnira ce ni dai na gama jan kunnenta kar ta yi faɗa da kowa a yi suna a tashi lafiya. Ta ce mini ba za ta yi ba amma ni na san sai ta yi mgana ni da na san halin Munnira.

    Karfe biyu na rana mai kwalliya ta iso kusan ma lokaci ɗaya suka iso tare da Khaleesat wai mota ta lalace musu a hanya. Itama ta kawo mini turamin atamfa da riga tare da kayan sanyi na karɓa ina ta godiya. Swiss lece na saka cikin wanda na siya na ɗinka sannan a ka tsantsara min kyakyawan kwalliya wanda tun kafin a gama kowa ya shigo sai ya yi santin kyan da na yi kyau ma sai da a ka gama ta yi mini wani irin ɗauri mai kyau da na duba madubi na ɗauka jidda ce tsabar yadda na dawo kamar budurwa. Na yi amfani da takalmi baki mai tudu kaɗan da mayafi baƙi da jaka, Na saka ɗan kunnaye na masu kyau da tsada, ba ni da zinare ko na zobe sai da na yi hawayen takaici na tuna wanda a ka siya mini da Sadaki na, Yallaɓai ya saka na siyar da shi muka cinye kuɗin, da cewa in ya samu zai siya mini wani har yau lokacin bai yi ba ina jin ma ya manta da abin da ya faru. Ni kaina na san na yi wani irin kyau duk kuma in da na gifta Ƙamshi ke tashi, oil ne mai bala’in, wajen wata mai siyar da turaruka a faceebook na san ta Maryam kitty. Tun da na fara siyan turarenta ban taɓa saka shi ba a yi santin kamshin ba Yallaɓai ya daɗe da sanar da ni yana son ƙamshina. Har na ce in na samu kuɗi zan ce ta haɗa masa na maza daga baya da ya ɓata mini rai na fasa.

    Yumna ma an sauya mata kaya ta yi kyau daman ta sha kunshi a hannu da kafa da Ya Murja ta sake kun sa mata yau da safe yau ma mun so komawa asibiti amma sai Yallaɓai ya ce mu bari gobe da safe kar mu je a yi mata allura ta dawo da rigima amma dai tun kwana uku da haihuwanta wanzami ya zo ya cire mata belu sannan ya yi mata askin gashin kanta kamar yadda ya zo a cikin sunna. Zuwa biyu da rabi shagalin suna ya kamkama, baki suna ta zuwa ban yi tunanin zan tara mutane haka ba ni da ban damu da zuwa suna ba, duk sun saka ankon su sai suka yi kyau sosai. Maijidda Bala daman ta zo garin lokacin da na haihu da ya ke mijinta ya samu aiki a Dutse sun koma can da zama ita ce ta yo mini gayyar su Samira da Hauwa jamilu sai da na yi ƙwalla da suka kawo min pampers da mayukan jiki da hoda na jarirai sai safa da huluna suka ce kuɗin da a ka haɗa mini ne suka siya mini da shi, duk da ina ba da wa in na gani amma ba kowanne na ke yi ba, amma dai tabbas na ji daɗi na kuma martaba wannan karan da suka yi mini, sun kuma saka ankon su gwanin ban sha’awa. > Janaftybaby: Muna cikin bedroom ɗina tare da su muna hiran yaushe gamo. A nan Rahila ta kawo musu abinci sinasir da waina sai alale da ruwa da drinks can cikin gida kuma su Munnira na ta ji da baƙi.

    Suwaiba da Jamila sun zo mini suna da wuri amma ko Gimbiya sai wajen uku na rana ta zo tare da Halima da Naja. Mimisco daman ta ce mini tana Abuja amma yaranta ƙananun suna nan, Anty Maimuna ba ta zo ba sai can wajen la’asar suka zo ita da Anty Bahijja. Su Nasara da suke kusa duk sun zo mini suna kuma an ba su abinci kamar na kowa ba nuna bambamci ko da suka zo na sauya kaya na saka anko da suka shigo suka ganni sai da mamakinsu ya nuna tun ballantana da suka ga gefen gado na cike da kayan arziƙin da a ke kawo mini. Gimbiya ta ta ba ni saƙo a leda Anty Bahijja ma ta ba ni leda Babba cike ta ce na su ne gabaɗaya daman haka suke yi bai ɗaya suke mini hidima in har na haihu. Naja ce kawai ta ɗauki Yunma amma bayan ita haka suka fita ba su ɗauke ta ba sun fita fuska ba daɗi domin ba haka suka so su ganni ba. Ga shi sun tarar da ɗaki cike da mutane su da ba su yi anko ba sai suka ga su ne ma dabam a wajen domin kowa ya yi ban da su.

    Ba abin da zan ce ma mutane sai godiya domin sun yi mini karam kaya sai da na koma jefa su a ƙasa saboda gadon nawa ya cika kowa ba ya zuwa hannu rabbana in ba a bani saƙo a leda ba za a ba ni kuɗi hatta Ya Abubakar da Ya Muntari sun tura mini kuɗi sannan matan su ma sun zo sun kawo mini turame, sai da a ka yi sallar la’asar sannan mai hoto ya zo a haraban gidan shi da yaran shi suka yi decration na ɗaukan hoton. Mamaki kawai na ke ba ma su Anty Bahijja sun kasa magana na fito da tawagata mun sha hotuna zafafa na shiga na fita da kaya sama da kala biyar ni da Yumna, na kuma gayyaci su Anty Bahijja zuwa hoton sun shiga amma a cunkushe Gimbiya ma mun yi ni da ita sannan mun yi da yara. Muna cikin hoton ne sai ga ƴa’ƴan su Anty Bahijja da na Anty Maimuna waɗanda ke gida wasu sun yi aure wasu kuma suna makaranta. Ana gamawa da hoto suka saka kiɗa a speaker suka yi connecting da waya daman Munnira na da home thearter ita ta zo da su daga gida saboda ta ce chasu za su yi ni dai na sulale na koma cikin gida na kira Musbahu na tambaye shi Yallabai ya ce yana office tare da Kawu sai na ce ya zo gida ya karban musu abinci ba daɗewa sai ga shi ya zo na saka Mubeena ta je ta kai mishi har da na shi gabaɗaya.

    Sun ta saka kiɗa su suna ruwa ni dai ban shiga ba, ina da ɗinki a ƙasana duk da ya kusa warkewa amma gwara na kiyaye amma da Munnira da Hauwa da Amina suna rawa na shiga na yi musu manni, Yumna ta na hannun Sameena itama ta shiga tana juyawa, har su Suwaiba duk sun shige daman su ai ba ruwan su ana cikin shagali ana ta farinciki suma Gimbiya da tawagarta suna wajen Anty Maimuna dai da Anty Bahijja sun yi mini sallama za su tafi na saka Munnira ta salleme su da ledan su ta ce mini sai da Anty Bahijja ta taɓe baki kafin ta ce”Lalle Tafida ya riƙe ma Sadiya kan macijin har da wani leda ne in mutum zai tafi? Duk abincin da aka ci bai isa ba? Ni dai a yadda ta faɗa mini ta ce ba ta tanka ba amma ni na san ƙarya take yi sai ta ba ta amsa. Sun tafi sun bar su Gimbiya da yaran su ina ga sai daga baya suma za su tafi.

    Ana cikin shan wakar ado gwanja na kujeran tsarkar gida, Munnira ta sauya zuwa kirarin uwargida. Kirari ne da wani mawaƙi ya yi ga uwargida je, kuma tabbas kirarin ya yi sosai ni dai ina ta dariya da farinciki su ka ja ni cikin fili suna kuma bin kirarim suna nuna ni.

    “Uwar gida ran gida in babu ke gida ya ɓaci. Haka zalika kowa ya zo ke ya tarar. Ke ce Amarya kuma ke ce uwargida, ke kika fara kafa gida saboda haka kowa ya zo ke ya tarar. Ke ɗin dai ce Uwargida haka za su gan ki kuma haka za su bar ki, hassadansu sai dai ta koma kansu. Allah Ya barki da Alhaji Tafida ya kuma kashe ki a ɗakin Tafida.
    Takalmin kaza mutu ka raba.” > Janaftybaby: Ina ta dariya saboda duk in da a ka ce Megida sai su sauya suna su kira sunan Yallaɓai. Jin daɗin kirarin ya saka na fiddo kuɗi a jaka ta sabbin yan ɗari bibbiyu da Khaleesat ta ba ni na riƙa manna musu. Daga baya ma Jamila kashe speaker ɗin ta yi ta ɗaga muryanta ta na rausayawa a gabana ta fara faɗin.

    “Yau taken naki ne Uwargida a gidan Tafida. Uwar gida ran gida shalele a wajen Tafida. Kowa ya zo ke za ya tarar. A buga a bar ki sai ta Allah ta yi Uwargida sai gaban ki in da kike so. Wallahi ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya. Mun sani mun kuma tabbata da tsohuwar zuma ake mgani. In ka ji ana a wasa a wasa ba kaifi, ke ce wakiliyar Tafida kowa ya zo arziƙin ki ya ke ci, kin zama Tafida Tafida ya zama ke, maganarki a ke yi wa ke batun yan karere. A matsa a matsa ga Uwargida Sadiya a gidan Tafida ta hallara na ce a matsa a matsa.”

    Kaina na ji ya fashe,na ji na yi girim girim nan da nan na zazzage musu kuɗaɗen dake jakata sai shewa da ihu ya ta shi Amina da Munnira suka ɗora da guɗa. Har da Sameena a wajen ni ban ma lura da Gimbiya ba, ballantana na ji cewa ina yi da gayya ne sai bayan mun baro haraba zuwa cikin gida Hauwa ke tsegunta min ga Sameena can naja na yi mata faɗa wai ba ta kishin ƴar’uwanta ta biye mana a na yi ma yaruwanta habaici. Na riƙe haba cikin mamaki ina faɗin habaici kuma? Hauwa ta ce wallahi su haka suka ɗauka sai kawai na ce to Allah ya kyauta ni dai fata na mu rabu da kowa lafiya.

    Ai ko na gan su da Sameena a can haraba bayan mangariba lokacin da na fito zan raka su Samira. Su ko salla ma ba su yi ba suna nan suna mganganu har da Halima a wajen, suna ganina suka yi shuru Sameena ko daga gani ranta ya gama ɓaci domin juyawa ta yi ta shige ciki a fusace kamar za ta tashi sama ni dai ban ce komai ba iyaka dai na ce musu ya kuka tsaya a nan? Sai Halima ta ce minI wai tafiya za su yi sai na ce su je su karbi saƙo a wajen Munnira sai ta amsa mini da to.

    Ni na dawo cikin gida ban san me ya faru ba Sameena ɗayan ɗakin ta shige nima ban neme ta ba kawai muna cikin ɗaki ni da su Ya Aina suna ta ƙwashe min kayan da na samu nawa da na Yumna sai ga Khaleesat ta shigo tana faɗin wai ga Amina can suna hayaniya da ƙanwar mijina mamaki ya kamani ina tambayan kaina me ya haɗa su? Gabaɗayan mu muka fita can falon Yallaɓai muka iske Amina da Halima suna cacan baki ga su Gimbiya zaune Munnira ce me ke jan Amina da cewa ta yi shuru amma Halima da rashin kunya ina falon ta ce ma Amina.

    “An zo an samu banza an tattare, za a kai gida. Saboda babu a house ɗin tsoho sannan a house ɗin miji ma babu.”

    “Ke Amina me ke faruwa! Me ya haɗa ki da ita?

    Na faɗa ina shiga tsakiyar su saboda Amina ta ta so tana faɗin” Wallahi ƙarya kike yi. Kin san ko daga yanayin mu za ki san mun fi ƙarfin wannan abun da kike haƙilo a kan shi. Ni mijina ba mai kuɗi ba ne amma yana da rufin asiri kuma a gidan ubana mun fi ƙarfin abincin shekara. Kaf yayyena suna gidan mazajensu cikin rufin asirin mazan kuma akwai ma’aikacin banki da ma’aikacin bankin kuɗin duniya wato CVN kin ga ko tsakanin ni da ke sai a nemi wanda ke rigima kan tsire. Tsiren da dubu biyat ɗin ki ta gama biya miki bukata amma kin tsaya kina ta da jijiyan wuya. An daɗe ba a gamu ba miyau ya tsinke ƙwadayi ya tashi ba.”

    “Amina.”

    Haka na ke kiran sunanta amma ce min take yi” Ya Sadiya don Allah bar ni na ga karshen rashin kunyar yarinyar nan.”

    “Ni ba mara kunya ba ce. Sannan yarinya na bayan uwarta.”

    “Ke Halima.”

    Na daka matsa tsawa domin raina ya gama baci na ga tana shirin zagar mini uwa ne a gaba na kuma a gidana.

    “Ni da gidan yayana ke ɗin banza?

    “Ƙwarai kin fita iko da shi. Abin da a ka hana ki ma ai yayan na ki ya siya ko?

    Naja ta shigar mata, Amina na ja ina mata faɗa.

    “Me ya haɗa ki sa’in sa da ita?
    “Ya Sadiya ni fa ban shiga harkan ta ba, ba kin ce na riƙe na bakin mu a hannuna ba, kawai ta na ganina da shi ta ce sai na ba ta leda ɗaya ni kuma sai na ga ai ga shi nan a hannunta Munnira ta ba ta, amma matar nan ta na ce sai na sake bata sai na ce ita ta samu wasu ba su samu ba ta bari a sallami waɗanda ba su samu shike nan ta fara zagina ta na gaya mini > Janaftybaby: mangaganu duk yadda na kai ga haƙurina sai da ta ƙure ni.”

    “Nima na zo ina yi ma Haliman magana tana neman yi mini rashin kunya.”

    Munnira ta faɗa tana kallona sai na kaɗa kai ina faɗin” Amina dauka ki ba ta. Ko ba yayanta ya siya ba matar yayanta ce ta siya. Ko guda goma take so ki ba ta ai arziƙi ne a zo wajen ka har kana da abin da za ka ba da.”

    Ina faɗin haka sai Amina ta miƙa mata leda ukun da ke hannunta, su Ya Aina ma suka ce shikenan ko rigima ta ƙare.
    Amma sai Halima ta ƙi karɓa sai ma falati da ta yi da ledan daga hannun Amina. Suka watse mini a tsakiyar falon na yi jagale ina kallon Halima na ɗauka iya nan za ta tsaya amma ba ta tsaya ba kamar ta na jirana.

    “Ai ni nafi ƙarfin wannan abun. Ke dai ki kara akai gida.”

    “Kin fi ƙarfin shi kike rigima don an hana ki?

    Munnira ta katse Halima. Ya Balki ta saka baki da cewa kowa ya yi hakuri ta duka ta na kwashe wanda Halima ta zubar Hauwa ta amshe ta. Amina za ta sake mgana Ya Aina ta tare ta ni ko daman ina ta danne zuciyata ne amma ba domin haka ba wallahi Halima ba ta isa ba. Gimbiyar ta su na zaune ta haɗa kafafu tana kaɗawa

    “Na gode Halima. Tun da masalahan da na nema da ke baki yarda ba, ba na son tashin hankali zo ki fice ki bar mini gidana.”

    Na faɗa ina nuna mata hanya. Yadda ta kalle ni cikin mamaki ne ya sa na ƙara haɗa rai na.

    “E ki fita ki bar mini gidana na gode da sunan da kika zo amma ni ba na son rigima”

    “In fita fa ba kika ce?

    “E ki fita na ce”

    Na ina ƙara jadadda mata sai ta juya tana kallon su Naja suma da mamakina a fuskokinsu.

    “Sadiya ƙyaleta kawai. Ai Aminar an shiga da ita ciki maganar ta ƙare.”

    In ji Ma’u sai na juya ina kallonta kafin na ce” Wallahi sai ta bar mini gida. Ta zo ta fita kawai.”
    Na faɗa cikin ɓacin rai, ina sake nuna mata hanyar fita.

    “To ba zan fita ba.”

    Ta faɗa tana ƙara cijewa har da riƙe kugu.

    “Ba zan fita ba, tun da nan ɗin ai ba gidan ki ba ne.”

    “Ok to ke gidan ki ne?

    Na katsete cikin ina saita kaina domin wallahi in na harzuƙa zan iya jawo ta na yi mata bugun tsiya ba ruwana da aurenta ballanta ya’yan ta.

    “Ba gidana ba ne amma gidan yayana ne na fi ki iko da shi. Kuma ai nan ɗin ba gidan ubanki ba ne”

    A bazata na ji maganar duk lalacewata a idanuwan Halima ban ɗauka za ta iya zagin ubana ba.

    “Ke Halima Sadiya kika zaga?

    In ji Suwaiba da ta shigo falon yanzu daman na bar ta a ɗakina tana salla.

    “Ita wace ce da ba za a zage ta ba. Na ga za ta nuna mini iko ne da gidan Yayana. Alhalin ba ta isa ba ita ɗin banza abanza k”

    “Tas!

    Sai ƙaran saukan mari suka ji na sharara ma Halima mari sai ga ta dafe da ƙuunci.

    “Ko giwa ta mutu ba ta yi lalacewar da kiyashi zai ja ta ba. Ba ki isa ki zo har gidana ki ci kasuwa a kaina ba ƙaryan ki yarinya gwara tun wuri ki shiga hankalin ki, ki kuma kwashi jikinki ki fice mini a gida kafin raina ya ɓaci wallahi na yi miki dukan tsiya”

    “Ni kika mara?

    “In ba ki fice mini a gida ba duka zan yi miki wallahi.”

    Na faɗa ina nuna mata zan iya ya ɗin. Munnira ta kwashe da dariya Suwaiba da Jamila suka ce da kyau.

    “Me ya sa kika mare ta a kan gaskiyan ta?

    Naja ta miƙe tana challanging ɗina.

    “Na mare ta ko za ki rama mata ne?

    Na faɗa ina kallonta domin kaɗan na ke jira yanzu sai na saka a yi musu dukan tsiya su bar mini gida amma sai na ga Gimbiyar ba ta yi magana ba.
    Kuma ba ta tsawarta ba.

    “In nan gidan Yayanta ne ni kuma matar yayanta ne da gidan da shi kan shi yayan nata a ƙarƙashin ikona suke. Kuma ko shi bai isa ya zo yana mini wulaƙanci ba, ballanta ita ɗin banza. Duk wacce ba lafiya ya kawo ta ba, ta zo ta fice mini a gida kafin na haukace muku.”

    Kawai sai na fara masifa ina faɗin ni da gidana ba shege ko shegiyar da ta isa wallahi. Amma suka ƙi fita na ce zan yi ma Halima duka Ya Murja da su Rahila suka rike ni ashe tun fara faɗan Gimbiya ta kira Yallabai ana cikin haka sai ga su shi da Kawu ashe ma suna hanyar zuwa ne ta kira shi wai gani nan na kori Halima har ina marinta. Lokacin da suka shigo na gama harzuƙa yana tambayan ba’asi ni ban bi ta kan shi ba Suwaiba ce da su Munnira ke ma yar musu da zence. > Janaftybaby: “Wallahi sai Halima ta bar minI gida in kuma ba ta fita ba ni zan fita na bar mata gidan.”

    Na faɗa ina numfarfashi Kawu ne ke ba ni haƙuri har yana cewa” Gwara da kika mare ta. Kuma kina dai-dai da ki kore ta tun da, ba ta da kunya.”
    Yallabai da suka yi tunanin zai goyi bayan su sai ya kware musu faɗa ya yi mata kaca kaca ya kuma ce ta fita ta bar gidan tun da ba alheri ya kawo ta ba.

    “Amma Uncle.”

    Naja ta tare shi za ta kare ma Halima.

    “Rufe min baki kawun me? Me ya sa ba ki tsawarta mata ba?

    Ta yi shuru ta kasa mgana Gimbiya ma tas ya yi mata ya ce ta iya kiran shi ta faɗa masa na mari Halima amma a gabanta Haliman na yi mini rashin kunya ba ta iya mata mgana ba.

    “Ni miye nawa a ciki? Na saka baki sai a ce kishi ne. Ba ruwana kar ka sakani a ciki “

    Ta faɗa tana wani tura baki ni saboda haushi ciki na koma ban san yadda suka ƙare ba amma na so wallahi na yi mata dukan tsiya. Kuma ta ƙara dawo mini gida ta gani sai ta raina kanta. Sameena ke faɗa mini daman suna jirana ne sunq ta zagina wai na yi albuzurranci da kuɗin Tafida na ce bakomai na isa ne. A nan ta ke faɗa mini yadda suka yi mata wai ta shige mini saboda munafunci ita kuma ta ce tana tare da ni tuntuni saboda Gimbiya ba za ta ja baya da ni ba.

    Ranar raina ɓace na kwana da safe a hanyar mu ta zuwa asibiti ya ke sake ba ni haƙuri na ce bakomai. Mun je an duba ɗinkina suka ce ya kusa warkewa sannan an sake yi ma Yumna allura. Mun dawo gida na iske suna ta suyan ragunan da aka kawo su a yanke yau da safe. Daman na san magana za ta je ta dawo sai da Anty Bahijja ta kirani wai me Halima ta yi mini na mare ta? Na ce rashin kunya ta yi mini buɗe bakin ta sai ce mini ta yi ashe ba daɗi ni ba na yin rashin kunyar ne? Ni kuma na ce ni ban bi kowa gidan shi na yi masa rashin kunya ba itama gidana ta zo kuma ko yau ta dawo wallahi ta ƙara mini rashin kunya duka zan mata ba ma mari ba. Ai sai ta ce to kar na fasa mu ka kashe waya zukata na ƙuna.

    Ranar yini na yi zuciyata ba daɗi da wuri suka gama suya suka ɗibar mini nawa. Sai na su na can Gwammaja. Na saka su Ya Aina suka ɗiba na su har da y’an can gandun albasa. Nima na ɗibar ma su Hauwa a ka raba da yaji kafin yamma gida ya watse har su Laila suna koma Ɗorayi za su kwana washegari su ɗau hanya. Ina ta musu godiya na su Samira Rahila na ba mawa na ce ta aika ma Maijidda za ta kai ma su Samira. An yi taron suna an ta shi lafiya gyaran gidan washegari Saude da Marwa da Mubeena suka gyara mini tun da sai ranar da Yamma Kawu ya zo ya ɗauke ta suka koma rano.

    Tun da a ka yi suna a ka gama na mai da hankalina wajen renon Yumna. Ta tsiri rigiman dare ba ta barina na yi barci ɗan kumarin da na yi duk na fara sakewa. Ga shi Yallaɓai can gidan Gimbiya yake kwana nan ya gama cika mini baki shi bai amince ya koma can ba amma sai ga shi an gama taron suna gida ya watse amma bai dawo ba ni kuma ban yi masa magana ba daman na san can munafumcin ne irin na su na maza. Sai dai ya zo duba mu safe da yamma.
    Daga ni sai yara suma suna zuwa makaranta sai yamma asabar da lahadi kuma Tahfez Jidda har ta kusa sauka izifinta hamsin da biyar Baby kuma ta na cikin izifinta na ashirin. Ni kaɗai a gida ga fama da aiki ga fama da Yumna wacce ta cika rigima ga tsotso mintina kaɗan ta fara rigiman nono shi ya sa ta zama wata burkuta da ita.

    Muna da kwana goma sha biyar da haihuwa na ga Yallaɓai ya dawo kwana a gida na kamar zan yi masa magana sai dai ban yi ba. Kwana biyu tsakani kuma sai ya ɗauke kafa ya koma can ni sai na koma kawai na zura masa ido saboda na ga jeka ka dawon da ya ke yi, na kasa gane nufin sa.

    Sai a tsakanin Munnira ta sake leko ni a bakinta nake jin rigima ce suka yi shi da Gimbiyar ta sa har sai da Nene ta shiga ciki. A kan dai maganar kuɗin da ta ce ya ara mata na shipping ɗin kayanta ya ce ba shi da kuɗi amma ni ya ba ni kuɗi na yi suna har ina kiran mai hoto. Ita ko abin ya tsaya mata a rai ta ce mini ranar ta na gidan a ka yi har da su Maman farko a shigar maganar shi kuma ya rantse ba shi ya ba ni kuɗin wasu abubuwan ba da kuɗina na yi, amma ba ta yarda ba ita a dole ya yi rashin adalci. > Janaftybaby: Wato dalilin dawowan shi gidana kenan sannan kuma ya koma bayan sun shirya. Ni dai na ce ma Munnira Allah ya kyauta can su ƙarata.

    Sai da ma muka yi maganar hotuna da Munnira sannan na tuna na tura ma mai hoto ragowan kuɗin sa ya turo mini hotuna. Washegari ko carbi na yi a status ɗina hotuna ne ba adadi na saka.
    Na farko nawa da Yallaɓai na saka da yara wanda Amina ta ɗauke mu ranar suna da safe.
    Na yi caption da cewa” Shekaru ashirin da albarka ƴaƴa uku. Alhamdulillah.”
    Sai na saka wanda muke mu uku ni da shi da Yumna. Shi ke riƙe da ita ni kuma sai na shafa sajen sa. A ƙasan hoton na saka sticker ɗaga hannu na za a saman kai sannan na ce” Jama’a na ba ni Yallaɓai na ne na ga ya fara furfura”
    Ai ko na sha comments har Ya Hamza sai da ya yi mini mgana da cewa. Ke kina nufin ya dauwama a saurayin da kika aura ne? Sorry yarinya.”

    Maijidda Bala ta yi dariya ta ce” Sadiya rayuwar auranki da Yallaɓai a bar sha’awa ce Allah ya bar ku tare.”
    Na amsa mata da Amin ba ta san tarin ƙalubalen da na fuskanta ba ne. Ba su san ma an yi mini kishiya ba sai a sunan Yumna na faɗa musu suna ta mamaki ai ni yanzu na yi hankali na kama jama’a. Ni dai ban ɗora hoton Gimbiya ba amma ma tura mata wanda ta ke ciki haka ma su Anty Bahijjs. Yan gidanmu duk na tura musu sun ɗora mu. A gidan su Yallaɓai da ga Mimisco sai su Suwaiba su Munnira daman nawa ne, mazan kuma daman Musbahu da Adnan suka yi ta ɗora mu suna addu’a. Yallaɓai ma turamai na yi wajen guda hamsin sai turo mini emojin mamaki ya yi ni kuma na ce masa miye? Da alaman tambaya sai ce mini ya yi wai wa ya ba ni kuɗin waɗanan hotunan? Na ce tun da bai bai ba ina ruwan shi sai ya turamin na emojin baki da zip kuma ina tunanin bai buɗe hotunan ba, shi ya sa ko a status bai saka ba. Ban damu ba sanin halin Yallaɓai wani lokacin ba ya yin abin da a ke zaton shi da shi sai saɓanin haka

    Har Shemau Ma’un ta kirani ta mini barka saboda ma yafe ma Ma’u shi ya sa itama na ji na yafe mata. Ta ce mini in ta shigo garin za ta shigo ta ga Baby na ce sai ta zo so. Kara an yi mini shi sosai kuma na gode ni ce na tara turamen atamfa kaɗan ne babu a hamsin bayan kayan jarirai da sabulai da sauran su da masu tura mini kuɗi. Da na nuna ma Yallaɓai sai da ya jinjina kai kafin ya ce wai ni da kaya sai nan da shekaru biyar na ce bai isa ba. Ya saka albarka yana dariya a ciki na nemi shawaran shi na ce zan ba ma Gwaggo ɗaya Nene ɗaya sabulai kuma na ba su Maman farko da su Inna Mariya ya ce duk yadda na yi dai-dai ne tun da kayana ne. Ban damu ba sanin halin shi, shi ya sa na yi gaban kaina na ware musu da niyyar in na yi arba’in in na je gaishe su na kai musu.

    Mun shigo watan december ƙarshen shekara. Ina ta jego na ina kula da kaina gefe ɗaya bikin Alhaji Mustapha na ta ƙaratowa. Ma’u duk ta damu ni ce ma ƙarfin gwiwanta. Sai ma Allah ya sa a ka ɗaga bikin sai Jan ƙarshe.
    27 ga watan december na yi arba’In a ranar da na yi arba’in Gwammaja na yini na kai ma su Nene saƙon su suna ta godiya tun da na je Yumna na tsakanin ɗakunan su Maman farko da Hajiya iya sai da zamu fita. Washegari kuma na yini a ɗorayi na kai ma Alhajinmu matarsa nan da nan ya ce shi kan ya saki jidda ya samu sabuwa Gwaggo na dariya ta ce da tsohuwar zuma dai a ke mgani. Ranar ma a wajen Alhajinmu ta yini kuma ikon Allah ba ta yi rigima ba, a jere na haɗa fitan na je gidajen su Ya Aina na je har can gandun albasa wajen su Inna Mariya. Na je gidan Munnira da Hauwa na yi musu yini da ban gajiya wajen kwana goma har Yallaɓai ya ce ba zan sake fita ba duk gari an gama gani na kullum sai na fita sannan na samu natsuwa a gida na fara gyara kaina.

    Surayya dee ce mai kayan ɗa’a ta gyara ni da haɗin kazar sababi na masu jego. Daman kuma bayan haihuwata na dage da cin kayan marmari da ganye da kuma kifi domin ƙarin ni’ima. Sannan Amina ma ta aiko mini da Gumba na sha da madara Yallaɓai na ta rara gefe na hana shi sai da na ji na yi tsab sannan na gayyace shi. Ranar na sha sambatu amma na gane ba ni da wayau, domin Yallaɓai kaca kaca ya yi wajen ɓarnan ruwa sai da ya famshe kwanakinsa har yana haɗa wanka ma.

    *Janafty*

    Note
    error: Content is protected !!